wanda zata tara da wanna matsalar ya share mata hawaye sai shi kansa Bakura.
Ya shiga dakinsa fiye da awa guda bai fito ba, a tunaminta wanka ya shiga^zai fito ya ci abincin don haka ta ci gaba da jira, ta ji shiru bai fito ba, sai ta shiga dakin ta iske shi har yayi wanka ya kwanta ya kashe fitilar dakin.
… Ta tura kofar ta shiga can cikin dakin yayin da duhu ya ..
hana ta hango shi. Ta laluba zata kunna fitilar dakin sai ta ji muryarsa.
Yace “kada ki kunna min fitila na- riga na kwanta.”
Ta laluba ta garasa jikin gadon ta zauna a gefe cikin
sanyi jiki ta ke magana.
Ta ce “Abban Zahra tun dazu ina daning area ina jiranka ka zo ka ci abinci ashe shigowa kayi ka kwanta.”
Ya fada cikin gadara “eh na kwanta, a koshe nake.”.-
Ta rusa kuka kai ka ce mutuwa ya fada mata.
Ta ce “yau me zan gani, yau me yake shirin faruwa da ni? Me nayi na kuskure da har haka yake faruwa da ni, wacece wannan mai matsayi a wajenka wacce har ta fi ni?” Bakura ya ji hankalinsa ya tashi matuka, yayi figigit ya yaye bargon da yake ciki a lullube. Ya kunna fitila ya matso gare™ ta ya na tambaya cike da tashin hankali. Ya ce “Samira lafiya, me yake faruwa? Dan nace na koshi shine abin da zai sa ki duki kukan irin na mutuwa haka? Mu je dining in ci abincin, shikenan?”
Ta sassauta da kukan ta fara goge hawaye. Ta fice yana biye da ita a baya su ka fito zuwa danning area da yake a babban falo, ya jawo kujera ya zauna. Ya dubi teburin yaga abinci ne burjik kala-kala kamar kala shida. Ga taliya fara da miyarta, farfesun kaji, farfesun kayan ciki, ga gasasshen kifi, ga hadaddan salad, Gefe kuma yankakkun kayan marmari ne wato (fruit Salad) ga lemuna nan kala-kala woto (Juices) nikekkiyar abarba ce da markadaddiyar kwakwa kamar yadda ta san Bakura bai cika son lemon kwali ba ko na gwangwani sai dai ta siyo Kayan marmari ta markada ta sarrafa masa a gida.
Yayi murmushi ya dube ta wacce ke tsaye qigam, ido yayi mata jawur don kuka da ta sharba, ta cika ta yi fum kamar za ta fashe don fushi.
Ya ce “Gimbiya zauna mu ci mana, yaya za ki tsaya min a kai?” Ta jawo kujera a can gefe ta zauna.
-Ya yi dariya. Ya ce “haba Gimbiya yau ba za ki zauna a kusa da ni ba ma, balle a bani a baki, ki dawo nan kusa da ni mana.”
Ta girgiza kai ta ce “nan ya isa ba sai na garaso ba.”.
Bakura ya miqe ya jawo kujerarsa kusa da ita ya zauna
ya ci gaba da lallashinta ya na mata magana mai kwantar da hankali har sai da ta saki fuskarta ta fara cin abincin. Bakura zura abincin nan yake yi a cikinsa kawai ba don ya na jin yunwa ba, sai don gudun bacin ranta. Duk lauma- daya da zai kai bakinsa sai ya ji malam Yakubu da iyalinsa sun fado masa a rai, sai ya ji inama zai iya kwashe abincin nan ya kai kofar gidan malam su hadu su ci tare. Sai yake ji kamar rashin adalci ne ya zo gida yana cin dadi shi kadai. Domin Malam ya zame masa tamkar dan uwa na Jini.
Ya na ci yana tunani, daga Samira ta harare shi sai ya* hau yi mata hira don kada ta ci gaba da zarginsa. Bayan sun gama cin abincin ta kwashe kwanukan ta kai kicin ta goge kan teburin tsaf sai ta kunna masa wani wasan kwaikwayo da tasa aka suyo masa yau, wato fim din Boloko a Kano. Su ka koma kan doguwar kujera su na kallo cike da nishadi su na kyalkyala dariya, idan maganar budurwa ta fado ma ta a rai sai ya ga ta tsuke fuska. Mamakinta ya rufe Bakura ya
dubeta. Ya ce “Samira lafiya kina dariya kuma kina fushi?”
Kan ka ce kwabo idanuwanta sun cika da hawaye, ta yi
narai-narai da ido. Ta ce “budurwarka ma tuno, wacce ta fara dauke maka hankali kwana biyu.’ Ya gyara zama ya yi marmushi ya dubi ta. Ya ce “da ban yi niyyar fada miki ba, har abada ba za ki ji wannan labarin ba saboda abunda kika yi min dazu. Baki da wayo ashe har na ke yi miki kallon mai wayo, ai ya kamata ki tsaya ki daure ki ji karshen labarin sannan ki dauki mataki, amma daga farawa kin fara surutu ga shi ke baki fahimci komai ba kin shiga damuwa da sumbatu ki na kuka. To, bana son irin haka daga yau don ki sani.”
Ta matse hawaye ta ce “na yi kuskure Sweety, zan
kiyaye nan gaba.”Ya yi murmushi ya ce ” Allah ya yi miki albarka..Kamar yadda kika san halina, ba na boye miki komai yau idan na hadu da wata na yaba da hankalinta na ji ina son in aure ta a ranar zan sanar miki. Me za ki iya yi min, ko za ki dake nine, ko kuwa zaki zage ni?”Samira ta amsa da “A’a.” Ya ce “ke kin san bana boye
• miki komai, to amma me ya sa kika fara zargin ina cin amanarki ko ina miki nuku-nuku?
Samira tayi kulu-kulu tana muzurai, ba tare da ta san
amsar da zata bashi ba. Ta na rayawa a ranta tabbas ta yi kuskure, da batan basira wajen zartar da hukunci akansa. Ya yi shiru na wani dan lokaci sannan ya ce “wata yarinya ce mai suna Sajida, mai kimanin shekaru goma sha shida. iyayenta sun yi mata tarbiyya amma wani saurayi na kokarin ya rusa mata rayuwa. Nayi kokarain haduwa da mahaifinta na sanar masa, Alhamduliliahi ya dauki kyaukykyawan mataki ya hana ta fita. Mahaifin Sajida Malam Yakubu babban malamin karatun alkur ani ne, don haka
- na zama almajirinsa nake daukar karatu a ranakun Juma,a;, asabar da lahadi zan dinga zuwa tsakanin sallar magriba da isha’ Dadin abunda na yi masa ya sa dúk sanda naje-sai yayi min kyauta, shine kike ganina da leda.
Hankalina ya na tashi matuka akan yadda naga ya boye Sajida ta na zaluntar iyayenta shine yasa na kasa samun nutsuwa ina fargabar kada dai ace Zahra ma haka take yi mana.
Samira ta dafe kirji ta fada cikin fargaba
“Abban Zahra ina Yagana ta sani ko wa ta sani da za ta fita: ba’a sani ba? Abban Yagana kai kanka ka fi kowa sanin halin Yagana, ba za ta yi haka ba.”
Bakura ya ce “tabbas na san Yagana, amma na san zamani ya canja dan haka ki taya ni saka ido sosai ki taya ni da yi mata nasihohi ta sigar tatsuniya ko labaru masu dauke da gargadi - da darasi ki tsoratar da ita.”
Samira ta yi ajiyar zuciya ta sunkuyar da kai kasa. Tace “zan yi mata nasiha Allah ma zai kiyaye ta insha Allah ba zata bamu kunya ba.”
Tsawon lokaci mai dan nisa babu wanda yayi
magana a cikin su,sai Samira ta dubi mai gidanta ta yi murmushi ta maqale murya. Ta ce “Sweety, yarinyar nan nake tunani Sajida, ka ce shekarunta ba su wace goma sha shida ba ta kuwa gama sakandiri?” Ya ce “mahaifinta ya ce sun cire ta daga makaranta
saboda saurayin ta na S.S 2, kuma duk da talaucinsu makarantar kudi mai kyau ya saka ta mai Suna EL-LITININ COLLAGE.
Wani abun daya sake daure min kai shine kamanin
Sajida ya tsaye min a rai, ya zame min wani mummunan fami a cikin zuciyata.”
Ra-ga-gas! Haka qirjin Samira ya buga cikin karkarwa
murya da fargaba. Ta ce “Abban Yagana ban fahimce ka ba. kamar yaya kamaninta sun zaune maka a zuciya? Abun mamaki sai ta ga hawaye ya na zubowa daga Idanuwansa.
Hanakalinta ya sake tashi ta fada a gigice “Abban
Yagana kuka kuma naga kana yi. wai meke faruwa ne?”Ya fada cikin lallausar murya mai hade da Jimami. Yace “yarinyar kamarsu daya da Zuhuriyyata.”
Samira ta zuba masa ido ta na kallo, kallo irin na anya
kuwa ba tunanin zuhuriyya ba ne yayi masa yawa har ya fara yi masa gizau?”
Ya juyo ya dubi Samira yayi murmushi ya ce “yaya ki.ka zuba min ido kina kallona kamar kina kallon tababbe? Ina cikin hayyacina”naga mai kama da Zuhuriyya sak. Shine ma makasudun” da ya sa na dage na nemi gidansu don naga mahaifanta. Na ga uwar, naga uban, naga qaninta basu da alaka da Zuhuriyya. Na damu na shiga rudani, fuskar yaringar nan ta tuno min da Zuhurriya, sai in ji gabana ya yanke ya fadi saboda kamar fuskar Zuhuriyya ce sak, ke har maganarsu iri daya ce sak.”
Samira tayi ajiyar zuciya sai yanzu hankalinta ya
kwanta da ta ji dalilin daya cika maganar yarinyar nan.
Hankalinta ya kwanta, ranta yayi fari kwal musamman yadda ta ga bai yabi tarbiyyar yarinyar ba ta san ba za ta taba burge shi ba.
Hmmm