KALLON KITSE COMPLETE

 KALLON KITSE COMPLETE

Cikin kuka ta cire glishin (glass) idon ta ta kalle shi tace " Abban *Bilal* me na yi ma ka? Wane laifi na aikata da har za ka hukunta ni ta hanyar yi min kishiya? Abban Bilal ka dai na so na ne ko me? Me na rage ka da shi da har za ka k'ara aure a wannan lokacin? *Shekara goma sha uku* mu na tare da kai, ba ka k'ara aure ba sai yanzu, sai yanzu da na fi buk'atar ka a kusa da ni? Me ya sa? Me ya sa za ka k'ara aure? Ka gaji da zama da ni ne? Ko kuma dangin ka ne su ka saka ka k'ara aure, saboda har yanzu ban k'ara..."

Yasan me za ta fad'a, dan haka ya yi saurin rufe mata baki, manna kan ta ya yi a k'irjin shi ya na shafa bayan ta ya na fad'in "Haba Momyn Bilal, me ya sa za ki bari har shed'an ya shiga zuciyar ki ya rik'a raya mi ki wannan tunanin? Ni na fad'a mi ki kin min laifi? Ko kuma na fad'a mi ki zan k'ara aure ne saboda na dai na son ki? Haba dan Allah, ki nutsu mana, sannan ki saurare ni, ta hakane kad'ai za ki fahimce ni."

Da k'arfi ta d'ago daga jikin shi tace "Fahimta? Na fahimce kama ka ke cewa? Ai ni da k'ara fahimtar ka kuma har abada, ka riga da ka ruguza yarda da fahimtar da na ke ma ka a baya, Abban Bilal, wallahi ba zan sake sauraren ka ba, ka cuceni, ka zalunce ni,
DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *