KANDALA CHAPTER 5

KANDALA






CHAPTER 5









Da asussuba aka tura driver ya dakko K’ande saboda aikace aikace cikin rashin jin dadi ta tawo tana dawowa taga gidan kamarna kaje haka tafara gyarawa…

” A’a harkin dawo?

” eh yaya nadawo…

” hamza ne yace pleace ki soyan chips…

” ajiye kije ki huta malama…

” Tohm tace dama tagaje kwanciyar datayi ba dadiwa taje an cillo mata tsintsiya…

” mama farida lpya?

” kifito ki dura break fast ki gyara gida, shiyasa nasa aka dakko ki da hurhuri…….

” cikin takaice K’ande tace wai mai kukeso kumayar dani ne?

” bazakije bani kokuma sai na hadaki da mai gidan?

” ai gani nakeyi gidan mijinku ne kuma lada zaku samu bawai ace komai ne zandinga yi ba…

” ke ai amatsayin mai aiki kike agidan nan gwara ma in zaki tashi ki tashi kafin na hada miki tukk’u…

” wane dogon tsaki k’ande taja sannan ta huce ta gaban mama farida tare da fadin kinfi kowa sanin *Ne ta dabance!*…

” murmushin mugunta tayi sannan ta hau sama aa alhaji har ka shirya?

” eh saboda munada meeting yau…

” ayyah dakasani kabari na shirya ka…

” mata ta takaina bakomai next time sai…

” Dariya tayi sannan tace Alhaji ‘ya’yan k’a bansan me nayi musu ba basa ganin girma na ko gaishe ni basayi ko sun manta nima matsayin uwarsu nake?

” kibarne dasu zanyi maganin su…

” cikin bak’in ciki takarsa soya chips din tana cikin kwashi wa hamza ya shigo…

” sannu da aiki dear!!!..

” ko gyaran murya batayi ba!

” sister kingama soyan chips din?

” plate ta dauka taje tajera a dinning…

” hamza ya shiga cikin tunani i can’t understand ko nafada son k’ande ne!…

” haruna ne ya katse masa tunani cikin sallama…

” cikin murmushi ta Amsa yaya har ka shirya?

” hamza ne yayi zuciya ya fita yakoma palour ya zauna!..

” yes Na shirya please inkin dawo daga skull ki gyaramin room dina!

” okay no prblm i will inshaa Allah…

K’ande tana cikin ajiye tea sai ga Alhaji da mama farida…

” ina kwana dady?

A’uwata kintashi lpya?

” lpylou mutan kauye suna gaisheka!

” Farida tace firdausi jiye min karfin hali danAllah…

” firdausi tace su kaza har ansamu lafiyar yin kwai ba!

” k’ande ce tayi hanyar shiga D’aki dady yace come back, from today kidinga zama ana cin Abinci da ke!tohm ta samu guri ta zauna sai hararar juna sukeyi itada firdausi!!!… +

” Dady ne yace hamza what wrong kasamu guri daya kazauna!

” k’ande cikin zuciyarta tace sai kace wane mumine ba!

” Am okay Alhaji…

” Amma uncle baka jurar zama da yunwa fa! Cewar farida…

” banza yayi mata…

” uhm Alhaji gaskiya sunan da yaran nan suke gayamin baya yimun dadi su dinga cimin Anty mana!

” yauwa mumy ince bakiyiwa yaranki tarbiya bani?

” badai muyi masu ba!

” from today Anty zaku dinga cewa mama farida, kuma yadda zaku gaida ne haka zaku gaisheta tunda itama uwarku ce!

” K’ande da dariya ta kusa kubuce mata tace tohm Alhaji baba yadda kace haka za’ayi…

” yauwa uwata!..

” uhm Alhaji maganar dinki na fa wazai kaimun?

” uwata ta kai miki inda takai nata!

” A’a ita k’ande dak’ina zata gyara min sai dai firdausi takaimin!…

” firdauci cikin gadara tace tabbijan!!!!

” will u shoutup idiot!

” mumy ce tasaki baki…

” Any time antynku tana magana kunayi mata gardama sai Na mugun saba muku!

” uhm Alhaji kadawo lafiya…

” farida da Abun ya isheta tace wallhi mumy bazata sabo ba taje tayi asiri zata rabamu da dady…

” mik’ewa mama farida tayi tace ina mace har sai nayi asiri zan mallaki mijina? Allah yabani iya magna kissa da ladabi to in har bakwayi mun biyayya kamar yadda kukeyiwa gyatumar ku toh kun fara ganin kaidi….

” ita dai k’ande uffan batace ba ta mik’i tabasu guri….

Hamza dake faman daddana waya yarasa me ke yimasa dadi wayar ya cillar sannan ya nufi motar sa kifa kansa yayi akan sityari k’ande ce tafito sanyi da kayan Makarantar islamiyya, baba ina yini?

” lafiya lou, har Anshirya?

” eh baba Na shirya…

” da sauri hamza yafito zomuje na kaiki…

” cikin hadewar fuska tace ai babu nisa makaranta!

” please kizo na kaiki!…

” kabarshi nagode zanje da kaina!

” Dafi kansa yayi yace ohhh shit!!!

” tunda k’ande tafita take faman tunani me hamza yake nufi da’itane haka takarasa makaranta batare da tabawa k’anta Amsa ba!

” bayan fitar malam jabir k’ande ta kalli fatima yar’uwa lafiya yau duk bakya walwala!

” cikin k’unar rai fatima tace ina cikin k’uncin rayuwa!

” kamar yaya fatima?

” bazaki gani ba kawata!

” karkice haka fatima sanadiyar gayamin dazakiyi zuciyar ki zata rage wane radadi da k’una!

” Sunana fatima mahaifina ya rasu tun ina shekara 10 mahaifiyata kuma tayi aure awane gari mai nisa!

Na kasance ina hannun kawuna, bai damu dani ba bai kula dani daga shi sai yayansa, hatta makarantar nan danake zuwa da kudina Nashiga!

” k’ande tace kamar ya da kudinki!

” komai ma dakikagani da kudina nakeyi ina sana’ar dinki sosai, dalilin haka yace bazai iya yimun komai ba nema na tashi na nema! Komai nawa babu dadi babu ruwansa da irin halin da zan shiga, baka kin maganganu kuwa har na saba dasu!” innalillahi ince kina addu’a fati?

” Cikin kuka tace Add’u’ar ce take rufamin Asiri, Wallahi maraice bashida da dadi yanzu kudin term na islamiyya banida yadda zanyi na biya…

” toh samarin ki fa?

” A duk lokacin da suka zo sai ya fita yace ai yanada ‘ya’yan da suka fine tarbiya!

” hasbunallah, karki damu fati komai lokaci ne, Nema kinga 2000 ce kudin makarantar Amma karbe Ne nasamu daga baya kibiya…

” nagode Aisha ke ta dabance…

” bani zaki godewa ba Allah ne yabaki…

Hamza yana shiga office ya zauna!

” Abdul ne ya shigo maza meke faru ne? 2days kazama so silent fa!

” hamza daya juya kujerar sa to me zance maka maza?

” ur problem mana!

” To ne dai ganinan don’t know real abunda ke damuna but Nasan zuciyata ta wada k’aunar wata yarinya…

” hahaha kace heart anyi kamu, to wacece wannan ta samu fine man..

” Ai bakasan ma takaice ba abaya na wulakanta ta…

” Tana sonka ne?

” wai wallhi ko kulani batayi yanzu…

” haba maza karka bayar dani mana duk kudinka duk iliminka aci u can’t control her! A beg show her love mana!….

” she’s stil young fa don’t think ta karasa 20, bama kasan wane abu ba idan Nasameta matsayim wife Na warki fa!…

” duk da haka show her you’re In love with her, komai kaga tana so try to do it for her! Always Suprise her, make her laugh, if kuka fuskan ce juna tahaka love zai fada!…

” hamza yaji wane dadi yace dadi na dakai idea’s…

” maza ai nafeso ace biki soonest…


Sallamar dataje ya tabbatar mata da uncle isyaku ne!

” Aisha me isa kike wahalar da zuciyar datake sonki?me isa kike wulakanta soyayya ta? Wallhi kaunar ki nakeyi tsakani da Allah my wishes is ki zama matata!

” k’ande ce tace kadaina kwadayin zuciyar da tariga ta saka wane, bana wahalar dakai, bakuma na gudun soyayyar ka sai dai tsoron kada ka fada tarko daga karshe yazame maka matsala….

” ki barne na gwada tawa baseerar kuma kinfi kowa sanin matar mutum kabarin sa! Why bazaki barni na nuna tawa baserar ba?

” Tohm uncle as u wish, please ina bukatar novel’s tomorrow zan tawo maka da kudin!…

” a’a kibar kudin…

” kada soyayya ta tabamin karatu cux zan iya rabuwa da kowane akan karatu!

” hmm Aisha kenan kayan islamiyyar suna yimiki kyau…

” Na karaso gida so bye bye!…

” bye dear…

Shigar ta cikin gida ta tarar da mama farida tana shan rake ta gabanta ta huce takarasa dak’inta bayan ta cire kayan makarantar ta shiga kitchen domin girke….


” bayan farida ta dawo daga lecture su mumy tagani a daki itada firdausi!

” mum na dawo!

” sannu dama jiranki nakeyi bakomai nakeso nagaya muku ba illa Abunda zai Amfani ku atakaice dai kunga ku ‘ya’ya nane ina kuma fatan kusamu miji nagare, Amma ga mazaje nan masu hankali da tarbiya!

” hakane mumy…

So inaso kuma kudan dinga gyayu kuma kuna ladabi ko Allah zaisa suce suna sonku kunga ayi yar gida…

” hoo mumy hakane zamu fara from today…

” Yauwa ‘yayana!!!…


Bayan k’ande ta gama Abinci wanka taje tayi sannan ta kara duba books dinta gurin tara ta tuna bata gyarawa haruna dakin sa ba sauri tayi ta mik’i domin gyara masa!

Tana shiga ya miki cikin masifa ya matso daf da ita tun yaushe kika dawo daga skul?

” Tun tun tun

” gayamin mana!

” tun 6 nadawo cikin k’inkina takara maganar…

” yanzu karfe nawa?

” karfe 9…Cikin wane mugun kallo irin na haruna yace ne kin raina ne i don’t have respect in ur eyes inda hamza ne jikinki yana bare zakiyi masa tunda kina sonsa! +

” wane muguwar faduwar gabace ta saukar mata duk ta dubur burci wallahi mantawa nayi yaya bangyara maka ba kayi hakuri!

” Ai hakurin ne yasa nace inda hamza ne da tuni kinyi masa!

” wallhi bana son uncle bana sonsa ko magana cikakkiya bamayi!

” acewar ki ba soon zanyi aure matata tagyara min tunda ke kanwata baki gyara min ba…

” idonta kawai yake kalla yadda yayi wuri wuri a hankali sai hawaye, to bari nagyara maka!

” kije banaso…

” please yaya Am sorry…

” kije kiyiwa wanda kikeso kokuma kiyiwa hamza!…

” jikin ta babu kwari wane mugun kuka tasaka bashiri ta wanke fuskar ta tafita dining, zama tayi kujerar dake kallon hamza tana cikin cin Abinci Haruna ya fito yace firdausi zo!…

” tune k’ande ta kware…

” hamza ne ya miko mata ruwa k’arbe..

” Ansa tayi tana kallon idom yaya haruna su yake kalla!

” firdausi kuwa cikin murna ta mik’i…

” hajiya dake faman murmushi, burin su zai cika!

” ahankaki hamza yace sai da safe sis!

” ita dai kallo kawai take binsa dashi…

Da safe zata tafi makaranta taga haruna a gate!

” ina kwana yaya?

” lpya…

” Namanta ban gaya maka ba iya tana neman ka!

” ai da hamza ne da tune kingaya masa…

” ita dai bataci k’ala ba tatafi makaranta…

” bayan Antashi daga makaranta suna tafe ita da nafeesa tace walhi uncle hamza ne ya takura min da kallo da shishige…

” hahaha kice tun yanzo ya kamu da sonki?

” Allah ya kiyaye me zanyi dashi?

” Nafeesa tace oho miki, sai gobe!

” okay…

” Tana isa gida hamza yace Aisha Aisha…

” banza tayi masa..

” Ga novels nasiyo miki…

” Cikin fara’a tajuya tace dagaske…

” ya k’ada mata kai Alamar eh…

” haruna ne yashigo yaga sai murna takeyi…

” bama tasan yananan ba tace yeap nagode uncle…Tana isa gida hamza yace Aisha Aisha… +

” banza tayi masa..

” Ga novels nasiyo miki…

” Cikin fara’a tajuya tace dagaske…

” ya k’ada mata kai Alamar eh…

” haruna ne yashigo yaga sai murna takeyi…

” bama tasan yananan ba tace yeap nagode uncle…

Haruna ne ya k’alli hamza!

” hamza dake faman murmushi yace oh wannan kanwar tamu akwai rigima!…

      ” ah haba kace rigima takeyi maka?

     ” murmushi hamza yace as you say!

   ” Hakan yasa haruna yace good sannan ya shiga cikin daki tare da waya da Amira!

     ” haba sweety kwana biyu lpya?

   ” am well!

        ” why not in nakiraka baka Amsawa?

   ” am always busy that’s why!

     ” amma kabar zuciyata cikin tanani ko laifi nayi maka…

    ” cool down dear ba komai ba jikina ne some how, when am okay i will call…

     ” cikin bak’in ciki takashe wayar!

     ” firdausi ce ta shigo salam yaya?

     ” tadaga kansa yayi yace what wrong?

    ” indomie na dafa maka da zobo kafito kaci….

      ” tsoro tsoro takeji kada yace baya ci cikin kissa tace yaya bai kamata kana zama da yunwa ba!

    ” okay shige muje…

    ” tunda k’ande ta shiga daki littafi take faman Karanta wa, kiran sallah shi yakatse mata karatun mikewa tayi sannan tayi Alwala tare da sallah uniform tasaka sannan ta tafito domin tafiya islamiyya…

    ” fitarta palour ke da wuya taga haruna da firdausi a zaune sunata hira harun yace sister wannan indomie taki da dadi tak’e….

     ” cikin rausaya ido tace what about zobo?

     ” so sweet wallhi….

        ” k’ande ce tayi tsaki sannan ta bar gidan tafiya takeyi har ta’isa makaranta malam jabir ne yafara karbar hadda suna gamawa fatima tace kawata yanaga yau duk ranki abace?

    ” hmm rayuwa fati wallahi zuciyata ce tafada son wanda baya sonta!

    ” ke kuwa garin yaya Allah ya baki kyau ga ilimi kidinga kodayin kasancewa da wanda baya sonki! Ai bari kije kowanene yace yana sonka to masoyin ka ne!

    ” aduk lokacin dana ganshi da wata fati hankali yana mugun tashi….

    ” kidaina damuwa da wanda baya sonki, kidamu da wanda yace yana sonki ko bakya sonsa a hankali zaku saba!

  ” tohm zan kokarta naga in zan’iya…

     ” firdausi ce ta hau sama aguje tare da rungume mumy yafara sona mum…

    ” yi ahankali kada ki ballane kicigaba da tararrayar sa nunamai kulawa kinje?

     ” okay i will, bari na tafi skul inada lecture!okay… +

       ” sallam!

       ” mama farida ce tayi tsaki lafiya kikazo kika tsayan akai?

    ” mukullin motar dady zaki bani zan tafi skull!

     ” bazan bayar ba kizo ki kwata inkin isa!

        ” ke kin isa cewar firdausi dak’inta ta shiga ta dakko mukullin, na dauka in na ubanki ne sai ki kwata ta nufi mota….

   ” Farida tace da uban naki zan hadaki ai…

  Tunda aka taso K’ande ke zuba ido ko zataga uncle isyaku amma shiru hakan yasa duk taje ba dadi…

     Amincin Allah ya tabbata agareki ya sayibata!!…

    ” A tsorace ta juya ai nayi fushi sai yanzu zakazo?

     ” am sorry my dear sister nayiwa assignment yanzu ma haka takara tambaya ta dangane da haddace farakon suratul kahfi wai nakawo mata hadisi ni kuma hadisin ya kwanta mini….

    ” ayyah An karbo daga Abid Darda’i Allah ya qara yarda a gareshi yace tabbas Manzon Allah SAW yace : “Duk wanda ya haddace ayoyi goman farko na suratul Kahfi to za’a kareshi daga DUJAL”Muslim
Sannan acikin wata riwayar itama daga Muslim cewa : “Duk wanda ya haddace ayoyi goman qarshe na suratul Kahfi…-shima za’a tsareshi daga Dujal…

  ” Amma nagode Allah yabada ikon haddacewa…

   ” Ameen..

   ” Aisha me isa bakida waya?

    ” ba’asiya min agida bani!

   ” kinason nasiya miki?

       ” A’a nagode!

          ” me isa kike gudun karbar abu agurina? Hakan yakansa naje wame iri…

   ” Wallahi bakomai kawai dai nace kabarshi ne!

     ” tohm ai shikenan…

     ” bye bye nazo gida see you tomorrow…

    ” kiyi mafarki na mai dadi…

    ” Dariya tayi ta shiga gate…

Tana shiga palour ta tarar da mama farida sai karkada kafa takeyi ko kallonta batayi ba ta huce…

     ” ke k’ande ke k’ande??? Badaki nake magana ba?

    ” wannan kira haka ko goggo bazatayi mun kiran nan ba!

    ” Dallah malama kije kidura Abinci kuma ki hada mango juice…

     ” oh yan kauye har Ansan mango juice lallai kin samu wuri…

    ” zakije ki dura kokunma sai ranki ya bace?

    ” ran mu dai yabace kallonki zandinga yi kina gayan magana!..

    ” lallai k’ande kin rainani!

    ” raine na haushe? Ai nadadi da rainaki sai dai kiyi sorry!

   D’aki tashiga ta chanja kayanta sannan ta shiga kitchen din!

Karfe shida baba ya dawo mama farida tahada masa gaskiya da karya duk tagaya masa!

    ” mumy ke mumy mumy???

    ” Dady wannan kiran sai kace ba lafiya!

    ” firdausi tace ne wallhi har kaban tsoro sharafff ya mari firdausi yakara mata wane!

   ” mama farida takara fashewa da kuka Alhaji har hadawa tayi da iyayena….

    ” wannan shine nafarko da karshe kada kikara zagenta in bahaka ba wallhi sai kin barmin gida…

    ” mumy tace haba dady!

   ” yimun shiru malama dama keki ke sasu kowaccen ku tashiga tattayin ta farida matata tace kuma inasonta fiye daku….

   ” firdausi da ke riqe da fuska kasa magana tayi…

   ” k’ande kuwa kitchen ta koma tare da fadin Akwai gwara ma agaba….

Gurin 9 hamza yana palour ya kalle farida sis me yasa bakwa tafiya da Aisha makaranta?

   ” wai k’ande kake nufi?

   ” Yeap..

    ” Allah yakiyaye Natafi da wannan village girl din…

    ” oh haka zakice anyway ne zan kaita ai…

    ” kamar yaya?

” kamar yadda nafada…

   K’ande da akasamu novel luf kake jinta a hankali taje an turo kofar dak’in ta….

   Uwata kije ki dafawa antynki tea..

  ” dady da kanka? Banda ka turo akirane…

   ” bakomai gobe ma zan siyo miki waya ma…

  ” nagode Dady Bari na dura Maka…

Da safe Bayan tagama aikin ta makaranta ta huce yau maths sukayi jarabawar tayi zafi!…

    ” A hanya taga wane kanti tashiga tasiya mayafi sannan takarasa gida!

    ” awaje tatarar da haruna tace ina yini yaya?

   ” lafiya! Inkin shiga ki turomin firdausi…

   ” wane irin kallo tayi masa sannan tashiga palour ke firdausi kije kije inji wancan mutumin…

   ” ba shida suna?

         ” bansani ba ..” firdausi ce ta daga hannu zata mari k’andr ba shiri ta rik’e hannun k’ande ta wankawa firdausi…

   ” kutmar uba nikika mara nan danbe ya kaura fada suke sosai har sai da haruna su momy sukazo sannan aka rabasu…

   ” Kande tace banza nai fada akan namiji akan yaya zaki shak’ine ko kina tunanin ina sonsa ne me zanyi dashi, sha sha sha marasa hankali, makarantar ake zuwa amma anki anutsu asan angirma…

    ” haruna ya dak’amata tsawa ba shiri tayi tsit D’ak’inta ta shiga…
  
    ” firdausi sai banbame takeyi kubarni naje nace ubanta naga wanene gatanta…

    ” mama farida ta saka dariya, kubarta taje indai kande ce dukan tsiya zatayi mata….

   ” mumy kina gane ko kina gani…

    ” shige mutafi malama…

   K’ande dake zaune kan sallaya hamza ya shigo tare da sallamar sa!

   ” Amsa masa atayi sannan yasamu guri yazauna cikin murya mai dadi yace Aisha please zaki aure ne?

    ” Aure? Aure?? Malam fitar min adaki bana sonka bana kaunarka bana kuma tunanin zan soka!

   ” Aisha karkiyi min haka wallahi ina kaunarki i can’t express sonki dankiye but na barki lafiya kIyi tunani….

   ” Mamaki ne ya kamata gaba daya…

   Karfe 1 Nadare suka farajin bindega yan fashi ne suka hauro gidan k’ande da cikinta duk ya kada tana jiyo i hun su dady saiji tayi firdausi tace akwai kwai….

   ” fadi abunda zaki fada ko na fasa miki kanki…

    ” cikin tsoro tace Akwai wata achan dak’in…

   ” elisu jeka fito da’ita…

   Cikin k’ande ne yakara kada wa sai kuka…..Aisha k’arkiyi min hak’a wallahi ina k’aunarki , ina kuma sonk’i but na barki lafiya k’iyi tunani….

   ” Mamaki ne ya kamata gaba daya…

   Karfe 1 Nadare suk’a farajin bindega yan fashi ne suka hauro gidan k’ande da cikinta duk ya kada tana jiyo i hun su dady saiji tayi firdausi tace akwai kwai….

   ” fadi abunda zaki fada ko na fasa miki kanki…

    ” cikin tsoro tace Akwai wata achan dak’in…

   ” elisu jeka fito da’ita…

   Cikin k’ande ne yakara kada wa sai kuka…..

Lokacin da aka fitar da k’ande cikin ta duk ya tsure!

   ” mama farida dake faman kuka elisu ya wanka mata mari…

    ” kowanne aciki su sai rawar kyarawa yakeyi…

    ” me kukeso? Kufadi abunda kukeso wallahi zanbaku!

    ” ubanka mukeso kakara magana sai mun faskara maka kanka!

    ” wayyo dady dan Allah kada ku kashesa…

    ” elisu ne yasaka kafarsa ya tankada farida nan ta wadi asume….

     ” karubuta mana check na million biyu yanzun nan!

    ” cikin rawar d’ari yace yana dak’i zan baku yanzu!

    ” suka nuna k’amde da hannu ke! Jiki maza maza ki dakko kije kidakko nace…

    ” gudu gudu sauri sauri da rarrafi takarasa dak’in dady check din ta dauka sai ga dabara ta wado mata wayar mama farida tagani nan da nan ta dauka gashi bata haddace number ya haruna ba!

    Ahankali tatuno lokacin da Amira take fado mata Nan tafara saka number takasa gani ta karshe da kyar tasamu numbarsa…

    ” kusan 20 miss call bai dauka ba tana cikin ajiye wayar kenan ya kira..

    Hello yaya yan fashi agida….

    Aguje takarasa palour mari yasakar mata shigeya mai kama da alade…

    ” rubuta mana komu harbe ka!

    ” Dady yana cikin rubutawa sai k’ande ta ka tseshi…

    ” dady kada kabasu kabari su kashe mu hakkin rai ma ya ishesu, Allah yayi muku ni’ima yayi ku musulmai Amma kuna mugayen aiyuka bakwa tsoron ranar haduwar ku da Allah! Murna da annashuwa suntabbata ga Mutumin da Tunanin hisabi ya hanashi tara dukiya ta hanyar Haramun, wallahi kudinnan bazaiyi muku Albarka ba….

    ” karasawar ta keda wuya ya buga mata wata gora nan da nan ta suma….

   ” jiniyar yan sanda ce takatse kowa Nan da Nan suka shigo tuni suka fita da ‘yan fashin guda 5…

   ” Suna fita mumy tace wayyo Allah mungode maka!

   ” mama farida da tafara cewa haruna waya kiraka?

    ” K’ande ce…

        ” Ai k’ande ta dabance cewar dady kuduba lafiyar su….

    Ranar kwanan zaune akayi haruna yana k’an kande harta farfado…

    ” sannu kande…

        ” ina suke?

” ki kwantar da hankalin ki babu wanda suka taba!wane zafaffan hawaye ni ya cika mata idon tah cikin zuciyar ta kuma tana fadin daman haka zasu kasance ita da ya haruna!.. +

   ” menene na kuka kuma babu Abinda sukayi miki…

    ” Ahankali tace zan sha ruwa..

   ” dakko mata yayi tadaga hannunta zata karba yace barshi na baki kinje!

  ” wane zafaf fan kallo takeyi masa shikansa sai da yaji wane iri ajikinsa!

    ” Mik’ewa yayi yace sai da safe!

    ” kamar tace karya tafi sai kuma tayi Shiru….

Da safe Dady yana palour kowa yana zaune banda k’ande tana dak’i a kwanci…

   ” haruna tayaya k’ande ta kiraka awaya…

   ” Nidai bata kirane ba, don’t know ta yaya takirane…

     ” mama farida tace ai k’ande ta dabance yanzu sai ya yihu lokacin da akace ta dakko check ne!

   ” firdausi tace koma menene Allah ya tsiratar damu…

    ” mumy tace Alhaji ya’isa haka anyi nafarko ankuma yi na karshe bambancin dakake nunawa akan yayana wallahi nagaje in bahaka ba sai mu rabu….

    ” haruna yace subhanallahi hajiya ai bai dace ba….

    ” firdausi tace mum aidama kinada kudinki sai kisiya gida…

   ” will you shoutup idiot!

    ” Mama farida tace kiris nake jira ketafi na bararraje….

   ”  Dallah kama kanki wacce batasan harkar arzuki ba!

    ” k’ande dake faman shirin makaranta tana gamawa ta fito sanyi da uniform ta gaidasu…

   ” bazaki huta ba kande?

   ” dady weac zamu fara kuma 8:00 zamu shiga…

  ” firdausi da farida sai faman harararta sukeyi har tafita….

  Tafiya takeyi cikin nutsu hango wata mata tayi sai kuka takeyi tana ambatar ta shiga uku!

  ” Hankalin k’ande ce yatashi matsawa tayi kusa da matar wata kodaddiyar atampha ci ajikinta sai jaririyar da kana ganinta kasan ba’a yayeta ba!

   ” baiwar Allah me akayi miki kike kuka?

      ” Namije dan zakarane, bashida kirki bashida mutunci wallahi bazan zauna acikin gidan ba sai dai…

    ” haba baiwar Allah wannan maganganu masu tsaure duk banza fa mijinki ne!

    ” kadan ma kikaje wallahi daga ya shigo bangama girke ba, kuma wane lokacin yaya sunyi min yawa dole nayi kazanta, kuma bana gyara masa dak’insa, alallai sai na zauna ina tararayarsa sai kace jaririna? Wacce soyyayah zanyi yanzu girma yaja? Shine yace kishiya zai kara harda marina dan na zageshi!….

    Oh ne K’ande! Baiwar Allah *DUNIYA CE*…. yanzu dan rashin sanin daraja da kibarki ta ‘ya mace shine kika fito kina Ambatar k’in shiga uku? Me isa k’uke jawowa k’anku masifa da bak’unan k’une? Idan baiyi miki kishiya ba me zaiyi miki?

    ” kamar yaya?Yayanki ne kekika haife su in baki kula dasu ba wazaki kula dashi? Kiyi musu tarbiya domin Alumma su amfana dasu… +

  ” ke kina mace ma sai ance ki gyara jikinki kiyi tsafta bakisan tsafta tana sanya kauna da soyayya acikin zukatan mu ba idan aiki yayi miki yawa kisamu almajiri mana ko yar aiki!

    ” Dubi kayan jikin ki ko naira biyar bana tunanin za’asiye ki! Ya Kamata kizama Mai hakuri, Mai kamun kai mai zurfin tunani domin rashin zurfin tunanin ki ne yasa baki gane mijin yana sonki ba, ki dinga sallah kina neman yafiyar mijinki….

    ” cikin murmushi tace yaya sunanki?

” Sunana Aisha (kande) Idan maganar dana gayamiki tabata miki kiyi hakuri,  ki kuma cire *SON ZUCIYA* ki dubi maganata…

   ” Wallahi Aisha ke ta dabance Nagode Na kuma jidadin maganarki da gida zankai kara Amma yanzu Nafasa komawa zanyi domin nagyara Aljannar ta….

    ” bakomai bari natafi…

Lok’acin data isa makaranta ba adadi dafara jarabawa ba haka ta shiga tafara tata bata dawo gida ba sai gurin karfe 5…

     ” Tayi wanka ta dauki wane kayan da akasiyo musu tasaka shudeyar doguwar riga ce amma irin ta robar nan masu bin jiki tana cikin daura Dank’wali taje sallama….

    ” kujerar girma, kujerar daukaka tare da ta tsare ta tabbata agareki k’anwata!

    ” batasan lokacin da tayi murmushi ba tare da sunkuyar da k’anta yauce rana ta farko data tabajin taje dadin kalamin sa…

    ” Farida ta kirane ashe kuma haka abu yafaru! Hope dai basu miki komai ba?

    ” ita dai kanta A k’asa takasa cewa komai…

      ” kiyimun magana konaji dadi wallahi jiya kasa bacci nayi tunanin ki ya rinjayi zuciyata…

    ” kamar yata tunani na?

      ” hannunta yarike kalle cikin idona Aisha zakiga so da kauna Aciki, He deserves nothing but praise, praise and continuous praise Nasamu abubuwa dadama arayu I’m more than happy for the blessings,
mercies and favours he’s bestowed on me that’s why am in love with you, so please ki soni esha….

     ” daga i’donta da zatayi taga alamun hawaye, zuciyarta ce ta karaya, Am sorry uncle ta mik’i idanuwanta ciki da hawaye zata fita kenan haruna ya riko ta jiyowar da zatayi ta wada jikinsa….kamar yaya tunani na? +

      ” hannunta ya rike kalle cikin idona Aisha za kiga so da kauna Aciki, He deserves nothing but praise, praise and continuous praise Na samu abubuwa da dama a rayuwa I’m more than happy for the blessings,
mercies and favours he’s bestowed on me that’s why am in love with you, so please ki soni esha….

     ” daga i’donta da zatayi taga alamun hawaye, zuciyarta ce ta karaya, Am sorry uncle ta mik’i idanuwanta ciki da hawaye zata fita kenan haruna ya riko ta jiyowar da zatayi ta wada jikinsa Kusan mintunan su uku suna kallon Juna!

   ” Har cikin zuciyar ta taji dadi dama su kasance tare a hankali ta tureshi tace uhm lafiya ka rikeni?

    ” murmushi yayi yace bakomai naga zaki huce tagaba na ba gaisuwa!

   ” am sorry banganka ba, Daman inason in tambayi ka?

     ” Murmushi yayi har sai da hushiryar sa tafito yace Allah yasa ba laifi nayi ba!

    ” gera ta daga tace ina amira? Yaushe za’akai kudine?

   ” jiyaye kamar ta zuba masa ruwan zafi ajikinsa chan yace sokikeyi nayi aure ne?

     ” yes uncle kafa girma mundago mufara ganin babys suna yawo….

     ” Karki damu soon zasu gani!…

    ” Zadai mugani, anyway bari nafita nayi bak’o awaje!

    ” wanene?

      ” tana cikin tafiya tana magana tace wanda zan aura!….

    Juyar da k’ansa dazaiyi yaga hamza yafito daga dak’inta! Tiriss yayi…

     ” hamza cikin fara’a yace babban yaya ashe kana tsaye anan!

    ” eh ina tsaye yanzu nashigo daukar wasu files…

       ” Nema nazo gurin mutuniya ta kasanta da riqema…

    ” ah gaskiya…

   ” farida da firdausi ne suka sakko sanyi da after dress sunyi kyau sosai….

    ” Haruna yace ‘yar kanwata irin wannan kyau haka?

     ” firdausi cikin rausayar da ido tace ai siyar kwalliyar zak’ayi….

    ” hamza yace to ne nasiya ta farida dubu daya…

    ” Farida tayi dariys tace ko nawa kasiya No prb dama prom zamuje tunda gaku please sai kukaimu…

    ” firdausi tace tunda ya haruna na nan ne shi zai kaine….

     ” hamza ya yamitse fuska to aidama bance zan kaiki ba!

    ” haka suka fita suna dariya…

     ” Mamaki ne ya cika kande gata a tsayi gaban Uncle isyaku Amma bata fahimtar komai!….

   ” tiriss hamza yayi yayin da yaga kande ta juya baya sai magana take da isyaku…

    ” kande ko naje mugaisa ne?

    ” nop uncle basai kaje ba!

    ” mota suka ja sannan suka fita murna gurin firdausi ba’acewa komai…..

   ” ya haruna inada question…

   ” Ask me mana!

      ” please kanada budurwa?

      ” kallonta yayi yana driving so kike kisani?

    ” Eh

     ” inada so yasaka dariya…

   ” baki ta turo au bama daya baciba gaskiya ne ban yarda ba!

    ” haruna yace cool down baby banda budurwa yanzu but…

   ” Dont say anything hakan ma daka fadan is okay….

   ” Hamza ne ya daki sityarin mota yes Am in love…

    ” farida dataje wane dadi har cikin ranta…

     ” hamza dake faman kallonta yadda yaga tana Annashuwa…

Gurin karfe daya da rabi K’ande tayi sallah tasaka kayan islamiyya taje sallamar hajiya..

   ” ina zakije uwar gantali nidai Allah yasa ba bin maza kikeyi ba!

    ” k’ande da idonta yakusan cika da kwallah tace makaranta zanje mumy….

    ” toh bangaya miki zakiyimun tsifa ba dan rashin da’a shine zaki tsallaki ne ki fita?

   ” namanta ne Amma kiyi hakuri…

    ” mumy ce tasamu guri ta zauna agefen gafon tace oya dakko kibiya ki tsefemin…

    ” tana cikin yi mata tsifar wayar mumy tayi kara alamu kiranta akayi…

    ” Duba sunantayi yaga Aminiyar tace mansura cikin murna tace Duniya takuce!

   ” hajiya mansura tace ina Ai doke mu barta, ina matsiyaciyar yarinyar nan ne?” Ai tananan in gayamiki tazama kamar yar gida!!! +

      ” wallahi in bakuyi da gaske ba sai ta aure samarin gidan kina ganin kishiyar ki…

    ” hajiya ce tace zankiraki anjima,tayi mamakin abunda kawar ta tace mata gwara suyi da gaske….

    ” mumy nagama!

      ” to sai ki tafi inda zakije…

Fitar da k’ande zatayi tayi karo su firdausi sun dawo sannu sukayi mata!

   ” yauwa tace tare da murmushi da kowa yagane zaisan na yak’ine…

    ” ya haruna yace malama k’ande har kin fito? Yakamata afara bamu lecture…

    ” Dariya suka saka mata har hamza!…

     ” babu abunda ta tsana irin wulakanci kana ganin fuskarta kasan da bacin rai aciki…

    ” ko baza akoyar damu bani?

   ” banxa tayi masa tabar gidan!

  Sanadiyar yau Ana Rana tafiya k’ande take Kamar Kar ta taka kasa, da alamu Dai ranar ce ta dameta shan kwanar dazatayi ta hango uncle isyaku yanata kallonta!

   ” yau ce Rana tafarko dayataba yiwa k’ande cikakkin kallo sanyi take da uniform brown duk da dai ita ba fara bace wankan tarwada ce Idanunta darara ga kuma hanci daidai ita, ita kanta bakinta yana bata sha’awa sanadiyar dan karamine!!

   ” Tabarakallah uncle yaketa faman fadi…

    ” lokacin da takarso tace Kai uncle irin wannan kallo haka Allah ne kaban tsoro!…

   ” ina kallon abar alfaharina, matata Anan gaba uwar yayana lokacin da zan kalleki son ran na babu mai hanani….

    ” cikin ya tsenan fuska k’ande tace nifa wannan kalaman naka bana fahimtar inda suka dosa!..

STORY CONTINUES BELOW

    ” ai su kallamai na sakko ne zuwa zuciyarki indai har sun isar watarana nema zaa bani sakon nakaiwa zuciya ta….

    ” hmm yanzu dai nazo makaranta see you later….

    ” har ta shige yana kallonta nan yace ya Allah kacikan burina…

   Lokacin da tafara bada hadda sai tini akeyi mata!

    “Malam jabir yace anya lafiyarki Aisha yau yadai?

   ” wallahi nema bansaniba…

    ” kins bukatar tulawa kije zuwa gobe k itabbatar kin bani daidai…

    ” Toh tace sannan ta koma gurin zamanta!

   ” lokacin da mlm umar yashigo tambaya yakeyi sosai kuma layi layi akebi wanda bai iyaba dukansa yakeyi…

   ” Fatima ce ta zungure kande…

     ” ahankali tace fati menene?.
    
     ” DanAllah in antambayi ne ki gayamin Amsar kinje?

   ” Tohm karki damu..

Assalamu alaikum kamar yadda kukasani yau tambayoyi ne da Amsa mutane 4 su zasu amsa Na yau tafarko shine auwal farouk!

    ” labbaika…

         ” Auwal farouk kamar yadda muka karanta acikin hadisi akwai wane hadisi da yake magana Akan Qarshen suratul bakara! Bukari yakawo shi wanne hadisi ne?

     ” hadisi ne mai lamba 5009 acikin bukari wanda *An karbo daga Abi Mas’ud Allah ya qara yarda a gareshi yace Manzon Allah SAW yace:Duk wanda ya karanta ayoyi biyun qarshe na suratul baqara a cikin dare to sun isheshi*…

     “Mlm umar yace me imam annawawy yace?

   “Imam Annawawy Allah yayi masa Rahama yace: Wadan nan ayoyin nada fassarori awajen malamai wasu su kace sun ishi wanda ya karantasu daga sallar dare, wasu kuma sukace sun isheshi sharrin shaidan, wasu kuma sukace daga sharrin komai, ayar zata iya daukar ma’anonin baki daya, qarshen maganarsa kenan…..jazakallahu khair… +

        “Fatima idress kice ta biyu ga tambayar ki acikin sahihil jaami’i wanne hadisi ne yake magana akan masu yawan godiya ga Allah…

      ” shiru tayi can taga kande na rubuta mata sai tace hadisi mai numba 1571 *manzon Allah (saw) yace :Mafi falalar bayin Allah sune Aranar Alqiyama sune:Masu yawan Godiya Ga Allah*

   “Barakallahu fiyki..

    ” sadik mustapha kaine na uku Ana karanta Alqur’Ani acikin ruku’u???

    “A’a ba’karantawa!

       ” menene dalilinka?

     “Domin manzon(saw)ya kasance yana hana akaranta qurani a cikin ruku’u da sujada yana cewa ni an hanani karanta qurani ina rukun’ce ko sujjada ne, acikin ruku’u ku girmama ubangijinku mai girma da buwaya a sujada kuwa kuyi ta kokarin addua hakika zaa amsa muku!…

    ” jazakallahu khair..

       ” Aisha gatambaya ta hudu itace wacce surace idan Aka karanta shaidan yake guduwa daga gidan?

     ” kande ta mik’i tace suratul bakara itace surar Kamar yadda hadisi mai lamba 1824 acikin muslim, An karbo daga Abi huraira Allah ya qara yarda a gareshi cewa manzon Allah saw yace: *kada ku mayar da gidajenku kamar maqabartu tabbas shaidan yana guduwa daga gidan da ake karanta suratul baqara acikin sa*

    ” barakallahu fiykum hadu ranar asabar…

Bayan k’ande ta koma gida tayi sallah abincin da mama farida tayi ta dakko ta ci tana cikin ci farida tazo ta barar da Abincin!

    ” cikin zafin rai kande tace malama bakisan darajar abincin ba shiyasa kika barar da kinsan illar da haramcin dafa abinci da baki zubar ba!

    ” nace ubanki ne yasiyo ko uwarki? Kigayamin ta rike kwalar rigar kande banza kinje kin asirci ubanmu kinzo daga dan iskan kauyen ku shine zakizo kinayi mana iskanci?

    ” kande tace sakar min riga!

     ” ai naga ubana ne yasiya miki, kokawa suka farayi fada sosai kande dataga babu ide sai ta yakushe fuskar farida, haka suka dinga yi, haruna ne ya shigo da sauri ya daka musu tsawa mumy ce tafito da sauri…

    “Ke kande abunki ya isheni yaza’ayi kina cin arzukin ubansu kuma kidinga fada dasu ko ke gidan ubanki ne?

    ” kande ce tafashi da kuka tashiga dak’inta kuka takeyi kamar ranta yafita Allah kajikan majaifina, Allah ka karamana hakuri da juriya! Mai isa mutanen nan sukeyi min bori…

       ” haruna ne ya shigo yazauna ahankali yace kanwata kidaina kuka domin kukanki yana tabamin zujiya Am with you so kidaina damu!…

    ” jajayen idon ta ta bude da hawaye bai daina zuba daga cikin sa ba, tace tayaya kakeson nasan kana tare da dani, kadubi yadda suke zagena sukeyi mun bori nima fa inada gata!

    ” ke yarinya ce yakamata ki daina saka damuwa aranki, kikuma dunga hakuri….

    ” cikin shashekar hawaye tace tohm yaya…

    ” indai kikaye hakuri komai zai huce…

   ” Tohm…

    
     Karfe tara taje hayaniyar su dady hijjabin ta saka tana fita taga Alhaji mahmuda yazo su mumy suna zaune anata hira!…

    ” ina yini kawu!

     ” A’a kande lpylou, su momy sun kwace mana ke!

    ” murmushi tayi ta zauna!

    ” To hamza nagaji da jiranka yau kusan sati biyu kana yimun wasa da hankali to nagaje umarni Nake baka!!!

    ” Dady yace baza’ayi haka ba kai hamza wakakeso?

      ” k’ande ya kallah itama shi take kallo lokaci daya cikin ta yakada…

     ” ba dakai ake magana ba…

    ” abi na samu wacce nakeso……




Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *