KARAMAR BAZAWARA COMPLETE
(¯*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai mai kowa mai komai wanda ya bani ikon rubuta wannan littafi, ya Allah ina roƙon ka kasa yanda na fara shi lafiya na gama lafiya ka tsare min alqalami na daga rubuta abin ƙi ka kare mana imanin mu sannan ka sanya mu cikin aljannah ba don ayyukan mu ba*+
_this novel is 100% fiction so any resemblance to it should be considered as coincidence_
بسم الله الرحمن الرحيم
01🧝🏻♀️
24/sha’aban/1442
10:31am
Bankaɗo ƙofar office ɗin aka yi da ɗan ƙarfi hakan ya jawo hankalin wanda ke zaune a ciki ya zuba ma ƙofar idanu don ganin waye zai shigo, wani matashin saurayi ne at his late 20s wankan tarwaɗa majiyin ƙarfi kyakkyawa na ajin farko ya shigo da ɗan gudu hannun shi ɗauke da jirgin wasan yara,
Bayan shi kuma yaro ne wanda ba zai wuce shekaru 5 ba yana jan rigan shi ya marairaice fuska kaman zai fasa ihu yana ɗagyalgyal saboda ya samu tsayin shi ya kai na wannan saurayin ya karbe jirgin dake hannun shi,
Da yaga babu sarki sai Allah sai kawai yaja gefe ya tsaya with a sad face cikin magiya yace
“Uncle ZAYYAD please give back my aeroplane na fasa wasan da kai”
Dariya mutumin yayi har saida dimples ɗinshi masu tsananin zurfi suka lotsa sannan yace “ai kuwa baka isa ba yaro, saida ka gama haɗa kan ƴan sweets ɗina ka shanye shine zaka ce yanzu ba zakayi wasa dani ba? To naƙi wayon, indai kana son na baka jirgin ka saidai kasa dadyn ka ya biya ni sweets ɗina” ya ƙarasa fada yana gwada mutumin dake zaune wanda tun lokacin da suka shigo yayi musu kallo ɗaya ya watsar yaci gaba da ayyukan gaban shi,
“Dady please kace ma uncle Zayyad ya bani toy ɗina su aunty Sulthana suna jira na zamu tafi gidan umma”
Wani mugun Kallo kawai ya watsa mishi ba tare da yace komai ba Zayyad yayi saurin miƙa mishi jirgin yaron yana murna ya fita, ƙarasawa kujeran dake gaban table ɗin mutumin yayi ya zauna yayi shiruuu murmushin da ya shigo da shi ɗauke a fuskar shi batt ya bace, lokaci ɗaya yanayin shi ya sauya zuwa na damuwa kuma alamu sun gwada a kwai magana a bakin shi,
sake ɗagowa yayi ya kalle shi sai ya aije pen ɗin hannun shi ya jingina bayan shi da jikin kujeran da yake kai, cikin wani salo na taƙama kaman wanda bakin shi yake ciwo yace “me ya faru? Ko matsalar ne har yanzu?”
Girgiza kai yayi, a hankali yace “Aa bashi bane, it’s Nana!, ta san halinda ake ciki, Nana ta gano sirrin da muke boyewa ya Sulaiman and the worst thing is ta sanar da Sulthana a…”
Bai ƙarasa magana ba Sulaiman ya bugi table ɗin dake gaban shi da ƙarfi cikin tsananin bacin rai
“How on Earth do you let that happen?? Ta yaya akayi kuka barta ta sani? How could you be so careless kuka bar biggest secret ɗinmu yayi leaking? Wannan abun kaɗai is enough to destroy everything it will tarnish your image Zayyad, ƙoƙari na a kullum bai wuce na rufe maka sirrin ka ba amman kai baka taba maida hankali a kai ka dauki abin nan kaman wasa”
STORY CONTINUES BELOW

“Ba laifi na bane ya Sulaiman, sanin kanka ne bani da ikon controlling wannan matsalar da nake ɗauke dashi, kuma bani da ikon controlling movements ɗin ƙannen matar ka a cikin gidan mu tsautsayi ne da ƙaddara, sannan yau da safe Sulthana tazo har part dina tayi threatening ɗina da cewa tunda ta riga ta san abinda nake ɓoyewa idan na yarda aka saka auren mu nan kusa zata rufa min asiri and i couldn’t say no,
Na faɗa mata zan taho na sanar da kai shine tace zata biyo ni sai na sauƙe su a gidan umma kuma ina da tabbacin faɗa mata zasu je suyi Please do something to stop her please” ya ƙarasa hawaye na gangarowa saman fuskar shi, a fusace Sulaiman ya tashi ya fita,
hango su yayi zaune a waiting chair dake jikin office ɗin wurin sakatariyan sa suna zaune ga yaron shi Arif da ya fita dazu zaune a kan cinyar ɗaya daga cikin su yana wasa har ya tsaya a kansu basu san yazo ba hankalin su yana kan waya saida sakatariyan ta miƙa ta sake gaida shi tare da tambayan shi ko yana buƙatar wani abu ne, kafin dukan su suka ɗago suka kalle shi,
“Daga ina kuke?” Ya tambaya yana kallon ɗaya a cikin su wanda nake kyautata zaton ƙanwar shi ce don kamannin su dashi ya fito sakk, itama bata da wani haske amman kyakkyawa ce ba kaɗan ba ga idanuwan ta manya kaman zasu fito waje, sunkuyar da kanta tayi cike da fargaba tace
“Daga gida muke babban yaya”
“Me kuke yi a nan?” Ya sake tambayar ta,
“Umm daman munzo tare da ya Zayyad ne muna jiran shi ne ya fito sai ya sauƙe mu a gidan umman su Sulthana”
“Ok! Idan ita umman ta ne ke kuma me zaki je yi a gidan?”
“Yaya raka ta fa zanyi kuma da wuri zamu…
Bata ƙarasa ba ya katse ta a tsawace tare da gwada ta da yatsa
“Ke!! Kada ki kuskura ki sake ɗaga min murya idan kina magana dani,
“I’m very sorry,
Shiru yayi na ƴan sakwanni yana Hararar ta, haƙurin nan da ta bashi ji yake kaman ya samu fuskar ta ya kwada mata mari, ta dai ci darajan ba’a gida suke ba amman da sai ya ida nufin sa,
Tsaki yaja yaci gaba da cewa ” kuma ku sani wannan maganar da kuke son saka kanku ciki yana da mummunan haɗari kaman yanda ake wasa da wuta, idan baku maida hankali ba sai ya ƙona ku ƙurmus, kun riga kun san ni waye kunsan yanayi na kada kuyi sha’awar saka ƙafan wando ɗaya dani, don haka yanzu na baku 20 minutes ku isa gida kuma dan zo na haɗu daku”,
Da faɗan haka ya juya ya koma office ɗinshi su kuma suka tattari ƴan jakakkunan su da sauri suka fita a building ɗin,
Tsaran napep suka yi Nana tana zumbure_zumburen baki ta shige ciki a yanzu babu abinda tafi tsana kaman shiga public transport ai wannan ma ƙasƙanci ne ta fito daga gidan Naira kuma tana a hulɗa da masu manyan motoci amman ace ta shiga napep? Ganin bata da niyyan magana yasa Sulthana ta faɗa mishi unguwar da zai kaisu ta saka Arif a ciki itama ta shiga suka tafi kafin 20 minutes ɗin da ya basu ya cika ya samu labarin basu isa gidan ba,
Saida yaga tafiyar su ta windown office ɗinshi kafin ya koma wurin Zayyad da ya kife kanshi saman table ya ɗan buga bayan shi tare da faɗin
“Enough now, na tsayar dasu ba zasu fada ma kowa komai ba insha Allah sune na ƙarshe da zasu san sirrin ka zanyi maganin ko wani ɗan iskan da yake shirin kawo mana cikas ga cikar burin mu kaji ko?”
Har wani lokaci yana tsaye a kanshi yana jin yanda yake faman sheshsheqar kuka sannan ya koma seat ɗinshi ya zauna tare da crossing fingers dinshi yana ƙare wa gashin kanshi kallo da tunani birkitai a ranshi, yana jin kaman ma yafi Zayyad tsoron fitowar wannan sirrin shiyasa yafi ƙoƙarin boye shi,
“Ya Sulaiman idan sun riga da sun faɗa ma wani kuma fa? Me zai faru?” Ya faɗa cikin rawar murya still kanshi yana kife,
Dagowa yayi yana kuka kaman ƙaramin yaro fuskan shi yayi caɓa_caɓa da hawaye yana ji a ranshi da ace ana canza gangar jiki da ruhi da kuwa ya canza nashi, ya kalli sulaiman dake zaune a kujera ya haɗe fuska domin yau NANA tayi matuƙar ɓata mishi rai har ya kasa tantance wani irin hukunci zaiyi mata,
STORY CONTINUES BELOW

Shirun da yaji yayi ne yasa yaci gaba da cewa
“Daman nasan tunda matsalar nan ya wuce tsakanin mu har ya fara bazuwa cikin dangi ƙarshe dole na tozarta, yanzu bayan Nana da Sulthana Allah kaɗai yasan yawan wanda suka san da wannan al’amarin”
“Na faɗa maka babu wanda zai sani, ba zan taɓa barin NaNa tayi wani yunƙuri ba idan kuma ba haka ba zan hukunta ta kaman yanda na hukunta Ruma lokacin da ta sanar da Batool, zan iya nesanta Nana daga gare mu a kan wannan maganar idan bata kiyaye ba zan mantar da kaina alaƙar dake tsakanin mu na mata irin hukuncin da sai tayi nadamar gani ma idon ta abinda bai kamata ta gani ba,
Amma kaima ya kamata ka jajirce ka daina bari wanda suke zagaye da kai suna sanin weakness ɗinka, kada ka manta shekaru 2 kawai suka rage mana in the next two years you will be 30 kuma a lokacin ne za’a danƙa maka naka kason na dukiyar ka you will be one of the share holders of this company bayan nan kowa zai iya sanin matsalar ka tunda nasan ba zamu iya rufe shi HAR ABADA ba amman dan Allah kada ka bari muyi asaran shekaru 25 da muka yi muna ɓoyewa be strong please”
Share hawayen idon shi yayi da bayan hannun shi yana ƙoƙarin daidaita kanshi, murya a dishe yace
” Insha Allah ya Sulaiman babu wanda zai sake sanin wannan abun, zanyi ƙoƙari na rufe shi da iya ƙarfi na, duk dokokin da aka kafa min zan kiyaye su domin gujewa matsala”
“Very good, yanzu bari na ƙarasa duba wa’innan takardun sai mu wuce gida duk sunyi spoiling mood ɗina bani jin zan iya wani aiki a yau ɗinnan”
Basu ƙara sama da 1 hour ba yace su tashi su tafi, saida suka isa parking space sannan yace ma Zayyad ya saka drivern shi ya tafi da motar shi gida sai su tafi tare a nashi,
Sosa ƙeyan shi ya fara yi yana kallon shi ta ƙasan ido yace
“Daman..um ni na tuƙo motar ban ɗauko driver ba”
Saida Sulaiman ya duba hagu da dama yaga babu wanda yake kusa dasu tukunna ya matso daff da Zayyad, murya can ƙasa amman a cikin fada yace
“Are You crazy?? Cikin yanayin ka kana ɗauke da matsalar nan kake driving, ban haramta maka driving gaba ɗaya ba? Yanzu idan wani abu ya same ka fa?”
“Kayi haƙuri yaya hankali na yana tashe ne kuma ba zan iya jiran driver na ya dawo ba ya fita aika ma Aunty amarya, drivern Hajiya kuma yaje ɗauko Batool daga school anyi musu hutu”
Baice masa komai ba ya juya Zayyad ɗin ya bishi a baya suka ƙarasa jikin wata blue Porsche Panamera aka bude mishi back seat saida ya saka Zayyad ya shiga kafin shima ya shiga aka rufe musu ƙofar suka kama hanya,
******
*MAFIAS QUATERS*
Daidai jikin wani tamfatsetsen gate Black mai design na golden color naga sun tsaya aka wangale musu gate din suka shiga ciki, gida ne wargajejen gaske amman hawa ɗaya ne gare shi kuma an kasa shi gida biyu saidai ginin da fentin da girman su duka ɗaya,
A maimakon su shige ciki sai suka tsaya gaba da gate din kadan Sulaiman ya zuge glass ɗin side ɗinshi yayin da ɗaya daga cikin masu gadin wanda ya ɗan manyanta ya ƙaraso ya rusuna tare da dunƙule hannun shi yana masa jinjina da kirari “Allah yaja kwanan ranka shi daɗe, Allah ya baka yawan rai” fuskar shi kadai zai nuna maka bayi jin daɗin kirarin da mai gadi yake masa, Zayyad da yasan ba gamawan yanzu ba ya lumshe idanun sa sannan ya kwantar da kanshi a jikin seat dan yasan yanzu Sulaiman zai fara tambayoyin shi masu wuyan ƙarewa,
“Malam lado su waye suka shigo gidan nan bayan fita na?”
Saida ya sake jinjina masa kafin yace “Allah ya baka yawan rai babu wani baƙo wanda ya shigo gidan nan bayan fitan ka, saidai hajiya Nana da hajiya Sulthana sun fita tare da oga Zayyad awa 2 da suka wuce kuma sun dawo awa 1 da ya wuce amman ba tare dashi ba suka dawo”
“Ba zallan baƙi ba a yaran gida babu wanda ya shigo da safe?”
Yayi wannan tambayar ne don yasan yanzu sun ɗauki ƙannen matar shi kaman ƴan gida ne kuma yana so yasan yaushe Sulthana tazo har taje ta tunkari Zayyad da wannan maganar,
STORY CONTINUES BELOW

“Allah ya baka yawan rai direban Hajiya ya ɗauko Hajiya fatima daga makaranta bayan ita babu wanda ya shigo da safe saidai su da suka fita suka dawo amman jiya bayan ka tafi Hajiya Sulthana ta shigo kuma inajin a nan ta kwana”
“Very good, bayan haka kuma sai me ya faru?”
“Ranka shi daɗe Naga Hajiya Rumaisa da oga sadiq tare da junior sun fito daga sashen aunty amarya sun shiga sashen Hajiya amman tafiyar su da tata ba ɗaya ba bata ma daɗe da komawa ba”
“Bayan su akwai wanda ka lura da alamar tambaya a kanshi a cikin ma’aikata ko masu wucewa ta waje?”
Girgiza kai yayi yace “babu Allah ya baka yawan rai, kowa yana aikin shi yanda ya kamata”
“Toh Masha Allah” ya zaro 3k a cikin aljihun wandon Zayyad ya miƙa mishi, yaji lokacin da ya ciri kuɗin a aljihun shi amman ko gizau baiyi ba ballantana yayi magana “aikin ka yana kyau malam lado, kaci gaba da saka min ido a cikin gidan nan kada ka yarda ayi baka gani ba,
“Insha Allah ranka shi daɗe” sauƙe ajiyan zuciya Zayyad yayi jin yau information ɗin nasu ba mai yawa bane, wato tunda Baba ya hana shi installing CCTV cameras a cikin gidan shine ya baza spies suna ɗauko masa komai da komai, ya zamo kaman shine shugaba a gidan gaba ɗaya kowa umarnin shi yake bi, dake baba ba mai yawan faɗa bane shiyasa suka fi tsoron Sulaiman a kanshi,
*****
“Gashi nan ya dawo wallahi” fa’iza ta faɗa ma Sulthana dake ta kai kawo a wurin zuciyar ta cike da fargaban gamuwan su da sulaiman, ko minti ɗaya bata ƙara ba ta shiga part ɗin da ke gaban ta a guje,
Batool dake amsa waya tana ta faman kashe murya ta ɗago tana kallon Fa’iza da alaman tambaya tace “waye ne ya dawo Fa’ee?”
“Oh tambaya ma kike yi? To yaya Sulaiman ne”
“Mtsww to sai mene dan ya dawo zaku fara gudu sai kace wanda kuka ga aljani? Ni bansan dalilin da yasa kuka ɗauki tsoron shi kuka saka ma ranku ba, mutum ba duka yake yi ba, ba zagi ba, bayi shiga harƙan kowa amman duk kunbi kun damu kanku a kanshi”
“To wallahi a halin yanzu da kiyi karo da Babban yaya gwanda kinyi karo da ƙaton aljani me kai 10 domin da safen nan Nana da Sulthana sun taɓo shi a kan matsalar ya Zayyad”
Sauƙe wayar kunnen ta tayi, ba shiri tayi disconnecting kiran a razane ta zaro ido tare da dafa ƙirji tace “dan girman Allah??”
Fa’iza bata tsaya ta ƙarasa sauraron ta ba ta arci na kare ta shige part ɗin da ɗazu Sulthana ta shiga shine na Hajiya mahaifiyar su saboda ta hango shi yana tunkaro su gadan_gadan, Batool ko tsayawa saka takalminta bata yi ba da socks ɗin ƙafanta light green haka ta taka da ɗan iskan gudu ta rufa ma fa’iza baya suna zuwa dukkan su suka ɗuru daki ɗaya suka rufe da key,
Kowa ta ƙame a angle guda zuciyar su yana bugun tara_tara da kalolin salati ɗauke a bakunan su, Nana da tayi mai gaba ɗaya harda hawaye suke gangaro mata saman fuska tasan yau idan ba wani ikon Allah ba sai tayi nadaman zuwan wannan rana,
Yana shigowa yaga babu kowa a main parlo sai Junior dake zaune yana playing video game yana ganin shi ya bari ya ƙaraso wurin sa,
“Kaje ka kira mun duka ƴammatan dake cikin gidan nan” ya bashi umarni a taƙaice,
Ɗakin da suka shiga ya fara zuwa Yana knocking tare da kiran sunan su ɗaya bayan ɗaya yana isar da saƙo, saida yaji sun amsa shi kafin ya fita daga part ɗin ya nufi ɗayan ba’a daɗe ba ya dawo lokacin su Nana suna fitowa daga ɗakin da suka buya, har zasu samu wurin zama yayi saurin gwada musu ƙasa da yatsun shi “on your kneels”
Kaman zasu fasa ihu suka zuba kan guiwowin su, kallon junior yayi tare da tambayar shi “ina Ruma?”
“Tana wanka ne babban yaya amman ta kusa fitowa”
Tsaki yaja ya kama hanya ya fita fuuu bai tsaya ko ina ba sai part ɗin dake gefen wanda ya fito yana shiga ya samu babu kowa a parlo sai masu aiki dake dusting ya wuce ya shiga daki na uku dake ta hannun hagu, yana shiga ya ƙarasa bakin ƙofar bathroom yayi masa wani bugu ɗaya da ƙarfi kaman zai ballashi cikin kururuwa yace “Rumaaaaaa”
Ba don ta rufe da key ta ciki ba babu abinda zai hana ƙofar buɗuwa, Ruma kuwa ta gama saka sabulu a jikin ta harda fuskar ta taji wannan kiran da ya saka ta kunna shower ta sake ma kanta ruwa harda gashin kanta saida ya jiƙe shaƙaf dukda ba wani tsayi sosai yake dashi ba amman saida ya sauƙo ya rufe mata idanu da kunne saboda yana da cika,
Ruwan bai gama ɗauraye ta ba ya sake yi ma ƙofar wani duka a ruɗe ta laluɓa ta jawo towel a jikin hanger ta maida gashin da ya rufe mata ido ta baya ta buɗe ƙofar ta fito, gefen wuyan ta da jikin ƙafanta duk kunfa haka ko hijab bai barta ta saka ba yaja hannun ta suka fita amman wannan karon ta ƙofar kitchen suka fita don shine yake ta baya babu wanda zai ganta, a haka suka shiga part ɗin hajiya tana rungume da towel a hannu,
Har zatayi kneeling yanda taga ƴan uwanta sunyi ya hana ta yace ta zauna a kujera kaɗa garin haka towel ɗin ya buɗe, Ruma baƙaramin basu dariya tayi ba don ta fito sakk mahaukaciya amman duk cikin su babu wanda ya isa ya dara a gaban shi babu ma mai kwanciyar hankalin yin dariya suka baza kunne suna sauraron shi,
“Wato kun zama ƴan iska ko kun kaida mu abun wasan ku??”
Shiru sukayi suna ƙifi_kifi da ido ya sake maimaita tambayar shi a tsawace
“Nace kun zama ƴan iska ko?”
Girgiza kai suka fara yi hawayen da Sulthana take maƙalewa suka fara zubowa da Ruma da bata san mai ya faru ba itama ta saka kuka don duk cikin su itace ƙarama bata da taurin rai irin nasu,
“A’a babban yaya kayi haƙuri dan Allah”
“Duk shegiyan da ta sake buɗe baki ta bani amsa sai naci mata mutunci shashashu wawaye,
kwanaki na tara ku irin haka na muku warning lokacin da mene ya faru?”
Shiru sukayi suna binshi da ido yace “ba zaku bani amsa bane ƴan iskan yara”
Murya na rawa suka haɗa baki wurin faɗan “lokacin da Ruma ta faɗa ma Batool da Fa’iza matsalar Ya Zayyad”
“Wani hukunci nayi mata?”
“Ka maida ita makaranta a Lagos”
“To billahi zan ci muku mutunci ƙananun ƴan iska tunda ku na farko bai zamo muku ishara ba nasan maganin ku ƙauye zan kaiku nayi muku aure a can wallahi idan wani yaji wannan maganar kunji na rantse”
Ai nan parlo ya karaɗe da kuka ko wannen su saida ta zubar da hawaye harda wanda ba dasu aka ce za’ayi ma aure a ƙauyen ba don shi da Nana da Sulthana yake yi, yasan su Batool da suna da niyar faɗa ma wani da sun daɗe da faɗa,
“Kayi haƙuri babban yaya wallahi ba zamu sake ba”
“Ku min shiru ƙananun ƴan iska, sai iya bada haƙuri amman idan aka faɗa muku magana bakwa ji, to wallahi try me and see sai na nemi wanda yafi kowa muni da talauci a ƙauyen da kuka fi tsana na haɗa ku duka biyu na bashi ya aura a sadaka, yanzu haka ma ba barinku zanyi ba kun riga kunyi kuskure daga yanzu babu wanda zata sake day school a cikin ku transfer zanyi muku zuwa University of ibadan………….🤦🏻♀️
*Nasan duk kun damu kuji wani matsala ne Zayyad yake fama dashi, to nima dai haka take a wuri na, na zuba ido naga menene😅 #taguminzamanjira*
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
_no matter how smart you are, if you don’t know how to work with people your dreams will only be dreams_💡
02🧝🏻♀️
“21,22….” “Kayan nan basuyi miki yawa ba Yusrah? Da wani nauyi ɗaya zaki ji, na cikin ki ko na uban zannuwan da kike ta loda?”
“Abban Jannat na faɗa maka na tura yaro ya tsaro mun napep ya kawo shi ƙofar gida sai ka ɗauka min ka saka min a ciki, 23,24,2…”
“To idan kika isa wurin da zaki je waye zai sauƙe miki?
“Shi mai keken mai yake yi? Zai sauƙe min mana ai har cikin gidan zamu shiga da shi, 25, 26, 27,28…”
“Yanzu idan kika kai musu zasu baki kuɗin ki duka, ko kuma a bashi zai ƙare?”
Shiru Yusrah tayi bata kula shi ba yaci gaba da cewa,
“Kuɗaɗen da yawa fah! Hajiya Sadiya matar Sulaiman boss ta baki sauran kuɗin ki na jiya?”
“Twenty nine, twenty ten…”
Dariya Khamis ya saka yana ci gaba da taya ta irgen shirmen da ta fara saboda yanda yake distracting ɗinta “twenty eleven, twenty twelve…
Ɗaya daga cikin zannuwan dake gabanta ta ɗaga ta jife shi dashi, ya caɓe yana dariya,
“Haba abban Jannat sau uku kenan kana ɓatar dani sai lokaci ya gama ƙurewa ban kai musu kayan nan ba idan kana wuri mutum ba zai taɓa ayyana abun arziƙi ba kenan?”
Dariya ya sake yi cikin nishaɗi yace “to ai baki gama bani amsa ta bane kin gwada fifiko ma kasuwancin ki a kaina”
Gyara zama tayi a kan kujerar da take ga cikin ta da ya fito zuƙeƙe aihuwa yau ko gobe tace “tambayi ina jinka”
Saida ya murmusa yace “yauwa nace idan kika kai ma masu wannan zannuwan kayan su zasu baki kuɗin ki a hannu ne ko kuma bashin ku na ƙarshen watan nan zasu ɗiba”
“Wannan ashobe ne ai sun riga da sun haɗa min kuɗin shi, kayan da na kai musu jiya ne sai watan azumi zan samu kuɗin su”
“Ok to balance ɗinki na wurin hajiya sadiya fa? Ta baki?”
“Tun da safe ta tura min dubu ɗari na cus a account jiyan ma wai ayyuka ne sukayi mata yawa bata da lokacin tsayawa tayi min transfer, kaima ka san wannan mutanen basu san karban bashi ba yanda suke da wannan ƙazamin dukiyar idan sukayi sai a tambaye su”
“Nice! To cikin 100k ɗinnan nawa ne naki a ciki?”
Kallon shi tayi a kaikaice tace “ban gane ba? Na taɓa tambayar ka nawa ne salaryn ka?”
“Idan ma baki taɓa tambaya na ba, ba a nan wurin nake zuwa dashi ayi budget ba? Kinsan komai ai”
“Wayo kake son min ko? Idan aka haɗa da wanda ta bani jiya ya zamo 150k riba na 35k”
“Wow! ga kuɗin da zaki karba idan kin kai wannan ga wanda zasu baki ƙarshen wata, idan aka tara gaba ɗaya ko wani month kina da kusan 70k fa kenan, baby kin kusa fina arziƙi ai” ya ƙarasa tare da taɓe baki yana jinjina kai indicating that he is impressed,
STORY CONTINUES BELOW

Suna haka yaron da ta aika ya shigo gidan da sallama ya tsaya a bakin ƙofar parlor ya faɗa mata mai adaidaita ya ƙaraso, daddafawa tayi ta miƙe tana ƙarasa shirya kayayyakin ta, ta miƙa wa khamis hannu tare da faɗin “miƙo min zanin na haɗa su na tafi”
“Da hannun ki fa kika bani kinga sai na kaiwa ƙanwata ta samu ƙarin na sallah”
Ƙarasawa wurin shi tayi ta ɗuka ta ɗauki zanin kafin ta ɗago ya kai mata kiss a saman lips ɗinta,
Miƙewa tayi tana wurga mishi wani irin kallo tace “ba don ana jira na ba da sai na rama”
“Idan kika dawo ma zaki iya ramawa, we have all night for you to avenge ke dai kawai ki dawo da wuri”
“Yauwa abban Jannat na manta ban faɗa maka ba gas ya ƙare idan ka fita kayi mana re-filling saboda girka abincin dare”
“Haba hajiya baby, ki ɗanyi mana Please tunda aljihun ki yayi nauyi”
“Wancan month ɗin ma fa ni nayi dan haka it’s your turn”
Miƙewa yayi ya sunguma mata kayan suka kama hanyar fita yana faɗin “haba ummin Jannat ki taimaka ki bada kuɗin ayi, duk kuɗaɗen hannu na sun ƙare a kan ginin nan yake tafiya ina tarawa ne a samu a kammala da wuri kinji my sweetheart”
“Nima kuɗin aikin Hajji nake tara mana so refill our gas cylinder before I got back, I love you”
Yana tsaye a bakin gate yana kallon ta har saida suka ɓace ma ganin shi kafin ya koma ciki, da yayi shirin fita ne amman yanzu ya fasa tunda babu kowa a gidan Jannat tana gidan Mama gwanda ya kwanta ya huta gajiya kafin su dawo su hana shi,
***********
“Sulaiman dan Allah ka sanyanta ma zuciyar ka a kan zancen matsalar nan, duk kabi ka ɗaga ma mutane hankali harta shi Zayyad da yake ɗauke da matsalar ya shiga damuwa ne kawai a dalilin ka saboda yanda kake kambaba maganar kana assasa mishi tsoro a cikin zuciyar shi,
Abin nan girman shi be kai yanda kake ɗauka ba, kuma tashin hankali da faɗa da mutane da hukunci ko horo bashi bane maganin matsalar nan, dan Allah kayi haƙuri ka ajiye maganar tura yaran nan wani ibadan, idan Nana ƙanwar ka ce kana da iko a kanta Sulthana fa? Yara ma mata za’a ɗauke su a kaisu kudu karatu babu kowa nasu a wurin kuma basu da mai lura dasu basu da mafaɗi?”
Shiru yayi daga inda yake zaune ya ɗago ido ya zuba wa mahaifiyar shi dake zaune a bakin gado ta ɗaura pillow a saman cinyar ta resting her elbows on it,
“Umm Hajiya na riga da nayi magana ma wanda zai shirya mana tafiyar nasu kuma har na tura mishi kuɗin komai daga hutu ya ƙare bayan Sallah zasu koma, na san iyayen Sulthana ba zasu samu wani matsala ba dan na tura ta karatu wani wuri ai ni nake ɗaukar nauyin karatun ta, sannan akwai familyn da na sani kuma ina da tabbacin zasu kula dasu so zan danƙa su a hannun su ba zasu taɓa bari su lalace ba idan Allah ya yarda,
kumaa Hajiya kece kike tunanin matsalar nan ƙarami ne kuma ba wani abu bane amman small mistake, slightest mistake zaisa Zayyad ya rasa komai ni kuma ba zan taɓa juran ganin faɗuwar shi ba, tunda Allah ya jarrabe shi da tauyewa ta wani wurin ya kamata ya samu ta wani wuri ko dan rayuwan shi nan gaba,
Zayyad is a matured man shi magidanci ne da ya kamata ace ya tara abubuwan duniya kaman yanda mu ma muka tara, daga an bashi kason shi zan janye gaba ɗaya makamai na ba zan sake takura ma wani a kan matsalar shi ba”
Gyada kai tayi cike da damuwa don itama abin na damun ta sosai, ba ita ta haifi Zayyad ba amman ta ɗauke shi kaman ɗan cikinta kaman yanda ya ɗauke ta a matsayin uwa,
“To Shikkenan Allah ya tabbatar da alkhairi, amman ka dawo da Ruma gaban mahaifiyar ta dan Allah, yarinyar nan tayi ƙarama da yawa she is just 16 kula da kanta da kanta yana bata wahala ka duba kaga yanda ta lalace bata girma kullum sai ƙara baya take yi”
STORY CONTINUES BELOW

” Kowa ma da haka ya fara Hajiya nima lokacin da kuka tura ni ABU Zaria ba ni nake kula da kaina ba, kuma a lokacin da kaɗan na fita” ya faɗa cikin raha,
Murmusawa Hajiya tayi tace “kai daban Ruma daban, wannan kayan sakalcin kana ganin duk lokacin da za’a maida ta makaranta sai tayi kuka ta saka Amarya zubda hawaye dake itama ta saka son yara a zuciyar ta”
“Shiyasa Ruma take sakalcin ai, ban san da ita da Fa’iza wacece a gaba ba kana taɓa su zasu buɗe maka baki nyeeee”
Dariya suka saka gaba ɗayan su yanda ya furta nyeeeee ɗin a yangance harda karkata baki “amman tana gama ss3 zata dawo gaban aunty Amarya jami’a a nan garin yola zatayi shi, kinsan bata da matsala da ita da ƙatuwar ƙanwanan nan zaytoon, kaii i miss her gaskiya nikam bata dawo daga yawon gantalin tan bane?”
“Kaji min yaron nan ita kuma nata karatun ne ya koma gantali?”
“To ba gantali bane? Duk makarantun dake Nigeria basu ishe ta karatu ba sai ta tsallaka yawo wani ƙasa ta maƙale da scholarship, ni dai ko ina taka kuɗi yarinya bata da aure ba zan barta ita kaɗai single fakitin ta keta hazo ta tafi wani ƙasa da sunan karatu ba ban lamunta ba”
“Tunda haka ne idan ta dawo sai ka nemi mijin da zakayi mata aure su koma tare tunda ka riga ka maida kanka waliyin su tun mahaifin su yana rayuwa a bayan ƙasa, tashi ka tafi gidan ka kaga rana ta kusa faɗuwa”
Saidai fa kada kuyi tunanin Sulaiman yana da sauƙin hali ta wani wurin, yanda yake a turɓune haka yake ma kowa harda matan shi wanda yake kwana yake tashi da takaicin ba don Allah ta aure shi ba, Sulaiman bayi raga ma kowa bayi barin kota kwana, mutum ne mai tsatstsauran ra’ayi mai jin kai da isa mutum ne kaifi ɗaya amman kuma adali ne a tsakanin mutane sonkai shine abinda bai sani ba,
Harta wa’inda yake cewa yana missing ɗinsun idan suna tare dashi basu kwasan ta daɗi, wanda kawai suke ganin rahama da murumshi a fuskar shi sune iyayen shi da aunty amarya kishiyar mahaifiyar shi kuma uwa a wurin Zayyad dasu Ruma sai kuma ɗaiɗaiku a cikin al’umma,
**********
11:02pm
Kwance nake a kan gadon ɗakin suka buɗe ƙofar amman basu shigo ba, kallon yanda na duƙunƙune cikin hijabi Yusrah tayi a tunanin su nayi barci ne ta juya wurin Khamis fuskar ta ɗauke da damuwa, murya can ƙasa tace
“Abban Jannat har yanzu fa babu wani canji daga wurin Saudat, shekaru 2 kenan harda rabi amman bata yi overcoming fear ɗinta ba, kwata_kwata taƙi sakewa a cikin mu wallahi bani jin ɗadin hakan bani son ganin boɗɗi cikin damuwa ko kaɗan”
Jan hannun ta yayi suka bar wurin tare da jawo min ƙofar ya rufe, saida suka shiga bedroom ɗinshi sannan ya zaunar da ita a kan gado ya riƙo kafarta da suka kumbura yana matsa mata su da ɗan ƙarfi don haka suke yi a kowani dare tunda ta kusan shiga watan aihuwan ta, idan ba haka ba bazata iya barci ba tayi ta mitan ciwon jiki kenan,
“Insha Allah wata rana zata saba, tunda tana zuwa makarantar boko da islamiyya tana hulɗa da mutane she will get use to staying with all of us, ai abun ba lokaci ɗaya bane nima daga farkon zuwa na da ita nayi tunanin hakan amman daga baya sai na lura a hankali take sabawa da sabon environment ɗinta”
“Ka gani fa tunda tazo gidan nan yau da yamma banda gaisuwa babu abinda ya shiga tsakani na da ita, ko magana nayi mata saidai tayi min murmushi kawai ga aiki ta hana ni ko ɗaga tsinke”
“Ai hakan ne ya kamace ki baby, kina samun hutu zirga_zirgan ki yayi yawa zaki iya saka wa baby na rashin lafiya, amman kinga lokacin cikin baby Jannat hankali na kwance kina gado abinki kina hutawa”
Qyalqyalawa tayi da Dariya tace “that was the craziest moment”
Shima Khamis dariyan yayi yace “i agree saboda a lokacin ina tsakiyar craziness a lokacin ne nake tashe ina jin kaina wani daban nima za’a aifa min baby, kinsan ance feelings ɗin mai partial craziness is multiple times na mai cikakken lafiya, so abu na saurin faranta mana kuma abu na saurin ɓata mana and we are very sensitive, bansan yaya zanyi miki bayani ba amman komi namu over ne shiyasa na wahalar dake a wancan lokacin kusan watanni 6 zuwa 7 fa kikayi kina kwance a wuri ɗaya kina marisa ba tare da kin sani ba, I’m sorry once again baby”
Saurin saka tafin hannun ta tayi ta toshe bakin shi tana girgiza kai, “stop apologizing please ka bani haƙuri yafi sau a ƙirga, da ace ban haƙura ba da bazan dawo naci gaba da zama tare da kai ba”
Shiru Khamis yayi yana kallon cikin idanuwan ta kafin can ya kwashe da dariya harda tafa hannu, ya kwanta a gadon yana ci gaba da tiƙan dariya, kallon shi Yusrah ta tsaya yi ta rasa dariyan da yake faman yi na meye ɗaya, saida ya tsagaita sannan ya tashi ya zauna idanun shi duk sun tara hawaye yace
“Baby I’m really sorry, kinsan maganin da nake baki a ina nake samo su?”
Girgiza kai tayi alaman A’a
“A wurin masu kurbe_kurben nan, faɗamin sukayi maganin yana kwantar da hankali yana maganin gajiya kuma yana saka nutsuwa da ƙara lafiya shiyasa nayi ta ɗirka miki ashe normal ƙwaya ne na masu shaye_shaye………🤦🏻♀️
Don’t forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💖
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Babban jin daɗin rayuwa shine ki kasance cikin rufin asiri a gidan iyayen ki ko gidan mijin ki, a duk yanayin da muke ciki na ƙasa damu zamu dinga dubawa ba na sama ba, Allah yayi mana babbar ni’ima mu gode masa*💡
03🧝🏻♀️
“Ƙwaya fa kace??”
Dariya Khamis yaci gaba dayi har hawaye suna sauƙa saman fuskar shi, yana gyada mata kai ko magana ya kasa,+
“That means duk abinda nake ji kaman a saman ɗakin nake kwance ko inji na fita hayyaci na ko in dinga ganin abubuwan dake zagaye dani suna motsi da kuma abubuwa da yawa dake caza min ƙwaƙwalwa ko tashi na kasa yi ashe duk effect ɗin ƙwaya ne?”
“Over dose ma kuwa, biyu sukace ake sha ni kuma nake baki uku” ya faɗa tare da sake saka dariya yana riƙe cikin shi, Yusrah kuwa sake baki tayi shaaa kawai tana kallon ikon Allah gaba ɗaya Khamis ya gama goge mata hadda, ta rasa me zatayi masa ko kuma me zata ce masa ɗaya,
“Ashe ba laifin Jannat bane da take da gagara kaman rainon maza, ka gama mata training tun tana ciki” sai kuma tayi tagumi cikin jimami tace “oh Allah yayi yarinya ta tana da tsawon rai ne ba don anyi gaggawar bani agaji ba da na rasa ta, maybe nima da ka daɗe da rasa ni wallahi banyi tunanin zanyi rai ba lokacin da nake kwance a asibiti, ban taba shiga mawuyacin hali irin wannan ba” ta ƙarasa hawaye na zuba a idon ta ba tare da ta sani ba,
Barin dariyan Khamis yayi ganin sauƙar hawayen ta, ya cire hannun da tayi tagumi dashi sannan ya rungumeta suna a zaune yana shafa bayan ta a hankali,
“Shiyasa nake roƙon ki ki yafe min baby, nasan halin da na saka ki abu ne mai wuyar mantawa, it’s ok ma idan baki son ki yafe min amman ki daina zubda hawayen ki don Allah, na faɗa miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba suna ƙona min zuciya sosai”
A maimakon tayi shirun saboda rarrashin ta da yake yi sai ƙara sautin kuka tayi tana yinshi mai gunji
“Wallahi na yafe maka Abban Jannat zuciyata ba zata taɓa iya zama da fushinka a cikin ta ba tana son ka da yawa, i just can’t help it when I think of the past”
“Then it’s better if you stop thinking about it, it might affect my baby ummm” ya fada yana share mata hawayen fuskar ta,
“kinga kin manta ma baki rama kiss dinki na dazu ba, idan ya kai gobe kuma ba zan yarda ki rama ba idan kin yafe kuma Shikkenan”
Jan hanci tayi ta juyo tana kallon shi da rinannun idanuwanta ta murguda mishi baki haɗe da faɗin “na yafe”
“Bazai yiwu ba, idan kin yafe ni ban yafe ba so silently come here ki rama abun ki”
**********
“Tsoro ɗaya? Kinsan Allah yanda naji muryan shi kaman mayunwacin zaki yayi kururuwa wai Rumaaaaaa saida na saki fitsari a jiki na”
Dariya suka saka gaba ɗaya dakin banda Nana da Sulthana da suka haɗe fuska suna faman harare_harare, timm suka ji ƙaran faɗuwan Batool a ƙasa saboda tsananin dariya,
STORY CONTINUES BELOW

siririn tsaki Sulthana taja tayi kwanciyar ta a gadon dake gefen na Nana dake ɗakin gadajen kwanan mutum biyu ne sai tima timan wardrobes daga dungu zuwa dungu da kuma arm chairs guda biyu ta bakin ƙofa, a yanda suka tsara zaman ɗakunan idan zaytoon tana ƙasa lokacin hutun makaranta suna kwana tare da Batool a ɗaki ɗaya saboda sune manya sai Nana kuma sukan kwana tare da Sulthana wani lokaci,
Idan kuma ba lokacin hutu bane, Nana da Fa’iza suke kwana tunda Ruma ba a gari take karatu ba zaytoon da Batool ma haka kuma basu iya kwana mutum ɗaya a ɗaki,
cin fuskan da suke musu ya fara isanta sunfi one hour suna zaune sun kasa su a tray suna tsokanar su suna kwasan dariya, gwanda Nana idan aka faɗa mata wani abun takan mayar musu da martani amman ita bata isa ba tunda a alfarma take zaune cikin gidan,
Miƙewa Batool tayi ta koma seat ɗinta ta zauna still tana dariya tace “ai Rumaisa’u kinyi ƙoƙarin tunda fitsarin kaɗan kika sake bakiyi masa sauran a hanya ba, nifa lokacin da ya shigo dake har dan ɗiba da gudu nayi tunanin yayi gamo da aljana ce a hanya ashe kece kika fito kaman aljana baɗalu”
“Hmm Wai don ma bani nayi laifin ba kenan, kinsan lokacin da na takalo shi saida ya jimɗe ni? A sanadiyar haka har na gama zama na aka gargaɗa ni Lagos ko inuwar ya Zayyad na gani ya shigo wuri bani raɓan wurin”
Fa’iza ne ta amshe da ” ai wallahi suma da ɗan iskan duka ya musu da bulalan timan doki ma da wannan hayaniyar da yazo yana mana bamu san hawa ba bamu san sauƙa ba, ita Nana hafsa saboda shegen iyayi da kaɗifiri kinga abinda bai kamata idanun ki su gani ba shine zaki je ki samu karere ki faɗa mata, gashi ai a sanadiyar haka zaki je ki haɗu da dangin su oduduwa”
Naushin Fa’iza a baya Nana tayi saboda ita ce take zaune a bakin gadon ta, rai a bace tace
“Dalla malama tashi ki fita min a ɗaki tunda ba naki bane, kema ai wata kareren ne”
“Amman dai gidan ubana ne ko? Ba yawon gantali nazo ba?”
Tashi Sulthana tayi ta zauna tana nuna kanta tace “Fa’ee nice mai yawon gantalin?”
“To wa ya sani? Nidai kunji ban kira suna ba ko?”
Sulthana ta buɗe baki zata sake magana Batool tayi saurin dakatar da ita “dan Allah kada ku fara mana faɗa cikin daren nan, ke kuma Nana kyaji da kyashi da baƙin hali kinma samu su wa’inda kike koran sun shigo ɗakin ki ne” ta miƙe tare da juyawa wurin Ruma tace ” Rumaisa’u tashi muje ɗaki na ki ci gaba da bani story”
Miƙewa Fa’iza ma tayi tana wani shaƙar iska a wulaƙance tana fesarwa tace “nima dai bari na bi bayan ku don bazan iya zama a ɗakin nan ba ya cika da warin karere it’s suffocating me”
Dariya suke kwashe dashi suka fice haɗe da rufo musu ƙofar, Sulthana saida ta zubar da hawaye gashi yau Nana bata cikin yanayin rarrashi don irama neman mai rarrashin ta take yi, babban yaya ya gama dagula mata lissafi idan ta tafi bata san yaya alaƙar ta da samarukan ta na MAUTECH (modibbo adama University of technology) zai kasance ba,
Haka Sulthana ta dinga mammatsewa bata son tayi kuka a gaban nana ajinta ya zube don ta tabbatar kallon da su Fa’ee suke mata shi Zayyad yake mata shiyasa har yanzu ya kasa tsayar da ita a matsayin matar da zai aura,
**********
“Haba Sadiya! Ke baki da lokacin magana sai tsakar dare lokacin da mutum yake buƙatar hutu? Kindai san ina da abinyi da safe idan ban samu nayi barci yanzu ba ba samu zanyi da safe ba ko?” Saboda sabo da wulaƙanci yanda yake magana ko kallon wurin da take baya yi,
Hararar shi tayi ta ƙasan ido tana ayyanawa a ranta yanda yake tuhumar ta yanzu kayi tunanin da ranan yana da lokacin sauraron ta ne, ta san idan ba a yanzun tayi mishi magana ba ba lallai ta samu wani damar ba because he is always busy, kuma a irin wannan yanayin ne kawai take da yaƙinin idan ta nemi abu a wurin shi zata samu,
STORY CONTINUES BELOW

“Kayi haƙuri Dadyn Arif maganar ce na gaggawa ne bani son lokaci ya ƙure shiyasa nake so muyi ta yanzu”
Siririn tsaki yaja yace “daman haka kike faɗa ko da yaushe, inajin ki menene?”
“Umm maganar makarantar maimoona ne, nace tunda ka tura ƴar uwarta wani makarantar daban mai zai hana ka haɗa su duka su tafi can ɗin nake ga kaman zai fi”
“Zai fi mene? Makarantar da take a yanzu an daina koyarwa ne?”
Murmushin yaƙe tayi ganin yanda lokaci ɗaya ya juyo ya ƙura mata idanu gashi suna daff har numfashin su yana bugar na juna duk ya rikita ta da idanu, “A’a ba’a daina ba, amman kaga ita kaɗai a nan ɗin ba zata ji daɗin karatu ba, kuma naji ance wancan makarantar tafi kyau da kudi ance karatun da suke yi yafi na nan inganci”
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, halima yaushe zaki canza hali ne? Sanin kanki ne yaran nan a matsayin punishment na tura su can wurin amman ke so kike yi a haɗa da ɗayar ƴar uwarki duka a tura su tare koma meye zai same su a wurin oho, to ban yarda da haka ba kada ki sake min magana akan abinda ya shafi karatun yaran nan tunda ba ke kika saka ni na saka su a makaranta ba kuma ba ke kike ɗaukar ɗawainiyar su ba, duk abinda nayi a kansu kada ki sake min magana na faɗa miki, bansan meye laifin University of technology ba wanda yanzu ɗaiɗaiku ne a ƙasar nan duk makarantun yanzu da b.sc ake fita su kaɗai ne ake b.tech, Muna a nan zata ƙarasa karatun ta naga abinda zai cinye ta” da fadin haka ya kashe bedside lamp ya kwanta tare da bata baya,
*********
Can bayan kusan awanni biyu sulthana ta farka daga barcin wahalan da takeyi a zaune, zuwa lokacin ko ina yayi shiru dan kowa ya riga da yayi barci sai hasken wutan lantarki dake ratsowa ta tsakanin curtains ya sanya ɗakin ya wadatu da hasken da zaka iya ganin ko ina ba tare da ka haska ba,
Sauƙa tayi daga gadon tana matsa wuyan ta da yayi tsami tana faman yamutsa fuska sannan ta saka takalmanta ta fice daga ɗakin ta nufi kitchen da nufin shan ruwa, bude fridge tayi ta ɗauko bottle wata ko cup bata tsaya nema ba ta ɓalle marfin goran ta kafa goran a bakin ta tana shan ruwan a tsaye,
Saida tasha kusan rabi sannan ta sauƙe goran tana ajiyan numfashi, ta maida sauran fridge zata koma ɗaki ta windown parlor ta hango mutum tsaye a waje, daga farko taji tsoro amman daga baya sai ta ƙarasa jikin windown ta ɗan ɗaga labulen tana son gane waye tsaye a wurin,
Yayi ma idanun ta nisa bata gane fuskar shi ba amman tabbas wannan Zayyad ne, dan ya Sulaiman da ya nafi’u ba a gidan suke kwana ba kowa yana da gidan shi daban, a hankali ta laluba ta buɗe ƙofar parlorn ta fita tare da jawo shi a hankali, tana sakin wani shu’umin murmushi ta nufe shi ganin sai faman dube_dube yake yi a ƙasa da Torchlight kaman makaho,
Saida taje bayan shi sannan ta kira sunan shi a hankali, a birkice ya juyo tare da haska ta da toci lokaci ɗaya yaci karo da buɗaɗen wuyan pjamas ɗinta ga numfashin ta sai lugude yake yi ta runtse idanuwan ta saboda hasken Torchlight ɗinshi,
Tangal_tangal tocin yayi a hannun shi gaba ɗaya ya gagara riƙe shi da kyau sai ƙoƙarin kamawa yake yi amman mugun ganin da yayi yasa ya kasa, Torchlight din ya faɗi ƙasa glass ɗin jiki ya fashe shikuma yana karanto “hasbunallahu wa ni’imal wakeel”
Sunkuyawa yayi ya dauko fasashshen torch ɗinshi saida ya kashe kafin ya maida duban shi wurinta yana tambayar “Sulthana me kike yi a nan wurin?”
Matsowa kusa dashi tayi ta riƙo hannun shi tana ƙara kusanto shi tare da bashi amsa cikin wata kasaliyar murya
“i want to apologise for what happened earlier bani da nufin zuwa na sanar ma kowa matsalar ka, hasalima ba a son raina Nana ta faɗa min ba and lokacin da na samu Labarin i couldn’t control myself tausayin ka ya kama ni shiyasa naje na same ka a kan mu ƙarasa maganar mu ayi mana aure nima inason na zama wani ɓangare na rayuwar ka, inason muyi farin ciki tare matsalolin mu ma muyi maganin shi tare bayan haka babu wani nufi a kaina da zuwa wurin ka dan Allah don’t get me wrong ya Zayyad, i just love you that’s all”
Rashin kunyar Sulthana har ya daina bashi mamaki, lokacin da Sulaiman ya auri yarta suka shigo cikin su ita da Muna ba haka ta nuna halinta yake ba, amman yanzu ta gama yawon duniya idanun ta sun bude,
Ganin ya tsaya kallon ta ba tare da ya amsa ta ba tace “me ka fito yi a nan kuma a wannan lokacin? Me kake nima ne naga kana ta dube_dube ko ka yarda wani abu ne?”
“Aa…Aa babu abinda nake nema kawai inaa….” Sai kuma yayi shiru
“Kana mene?” Ta tambaya tana ƙara matso shi jikin su yana cakuɗuwa da na juna, inda_inda ya fara ya ma rasa abinda zai faɗa mata, ita kuma sai gyaɗa kai takeyi alaman ta bashi damar magana saidai bayi da wannan courage ɗin,
Lokaci ɗaya kuma kaman ya tuna wani abu ya hankaɗa ta da ƙarfi ganin abun natq yana neman wuce gona da iri, da ɗan fada_faɗa yace
“Wani irin rashin hankali ne wannan Sulthana? A’uzubillahi minash shaiɗanir rajim kinsan girman laifin da kike aikatawa kuwa? Zaki iya jawo min matsala fah, haɗa jiki da namijin da ba muharramin ki ba haramun ne kinsan wannan amman me kike shirin aikatawa haka ne? Ke ko kunya baki ma ji ba? Kefa mace ce wanda aka fi sani da kunya da kamun kai! Don’t ever try this nonesense with me again” ya faɗa lokacin da ya juya da sauri yabar wurin,
“Amman ai bamu yi laifi ba tunda aure zamuyi nan ku…” Maganar ta ya tsaya lokacin da ta hango shi yayi mata nisa, kaman wucewar walƙiya har ya isa ƙofar part ɗinsu ya wuce ciki,
Tsaki Sulthana taja ranta yana tafarfasa don ba ƙaramin bata haushi Zayyad yayi ba, ta samu wannan damar na neman yanda zata saka shi ya sanya Sulaiman karya alƙadarin shi na kaisu ibadan don bata son abinda zai nisanta ta da Zayyad har ta ɗauke idon ta daga kanshi, she wants to keep him under her control, amman gashi shi ga kanshi ya ɓata mata plan,
**********
26/sha’aban/1442
5:10am
Buɗe ido nayi kamar kullum na farka a muhallin da ba nawa ba, na tashi a gidan da ba na iyaye na ba, gidan da ba na miji na ba, wurin da ba asali na ba, har yanzu zuciyata baƙuwa ce cikin yanayin da na tsinci kaina duk ƙoƙarin da nayi don sabar mata da hakan a banza, har gobe ina begen ganin iyaye na, ina muradin komawa ƙauyen mu da na zamo haramtacciya a cikin ta, ƙauyen da na zamo kaman sharri a tattare da mutanen ciki, ina son na koma tushe na ina so naci gaba da rayuwata kamar da, ina son komai ya zamo kaman bai faru ba saidai ƙaddara ta riga da tayi min tambarin da ba zan iya gogewa ba, kasancewata ƘARAMAR BAZAWARA da kuma kallon da mutane suke min matsayin MAYYA wanda ta cinye mijinta yarima, ta yaya zasu barni na shiga cikin karkarar mu a wannan yanayin??
Sauƙa nayi daga gadon bayan na ɗauki ƴar ƙaramin Torchlight ɗin da aunty Yusrah ta ajiye mun na buɗe ƙofa na fita, toilet ɗin dake gefen ɗakin na shiga nayi alwala sannan na fito parlor nayi sallah,
Bayan na idar na zauna ina ƴan addu’oi na, naga wucewar anty Yusrah ta shiga kitchen saboda tun jiya ta faɗa min yau zata tafi makaranta da wuri saboda tana da test ƙarfe 9 kuma batayi wani karatun azo a gani ba shiyasa take son fita da wuri ta samu ta ƙara wani abu a kai………….🤦🏻♀️
*Fans comment ɗinku na jiya ya sanya ni jimami😅 da masu cewa har yanzu Yusrah bata sayi mota ba, da masu tambayar dalilin da yasa Khamis ya barta take shiga napep bayi kaita duk inda zata je a motar shi, as you know ciwon haukan ya warke yanzu 😂 kuma shi arziƙi ba mafarki bane ballantana duk wanda ya kwanta yayi😆, I REST MY CASE* 🧘🏻♀️
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/+
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*kada kana yanke hukunci a kan mutanen da baka da masaniya a kan manufar su, hakan zai sanya ka maida masoyin ka maƙiyin ka, life is too short ka zauna da kowa da kyakkyawar zuciya*
04🧝🏻♀️
A wannan tafiyar ni ba Yusrah bace
Sunana Saudat Habib wanda akewa laƙani da boɗɗi, ƴar asalin jihar Adamawa muna rayuwa a ƙauyen wuroɓokki nida iyaye na, a halin Yanzu shekaru na 15,
Anyi mun aure tun ina da shekaru 11 da rabi da Yarima babban ɗan mai gari wanda yake da shekaru 20, a wancan lokacin na kasance yarinya mai gata gaba da baya kasancewa ta mace mai cikakken asali an sanmu tun kakani kuma mahaifina ya kasance Malami kuma mai baɗa magani, bangaren kyawu da tsari saidai nace alhamdulillah domin dukda a lokacin ban cika mace ba amman Allah yayi min kyawun fuska shiyasa ma ake kira na boɗɗi wato kyakkyawa,
Wannan kyawun shi yayi destroying rayuwata, wannan kyawun shi ya zamo silar lalacewar farin ciki na da na iyaye na, saboda shi ya jawo ra’ayin Yarima gare ni ya sanar ma iyayen shi na yake so, as you know no body can say no to a prince,
A ƙauyen mu inada ƙawaye da yawa wa’inda muke fita siyar da nono wasu ƙauyukan dake maƙwaftar mu da kuma kasuwannin dake hanyar birni amman tun da nake ban taɓa shiga garin yola ba, babban ƙawata kuma itace furera, muna amintaka sosai don har talle tare muke fita da an ganni to anga furere shiyasa har sirrikan juna mun sani, na riga na san furere tana bala’in son yarima, kai ba ita kaɗai ba ma duk wasu ƴammatan ƙauyen masu ji da kyau da yarinta sun gama haukacewa a kanshi burin su bai wuce su zamo matar magajin mai gari ba, well nima harda ni a ciki inada wannan mafarkin, ai babu wanda yaƙi daɗi ko?
Wannan haukan da mata keyi a kanshi yana Yarima ya zamo mai tsananin girman kai ga tinƙaho, bayi da abokai saidai masu take masa baya harta tafiya a ɓokare yake yi ya wani turo ƙirji gaba yana fankama wai gashi wanda zai zama mai gari nan gaba, duk da mai gari ba adalin shugaba bane amman iskancin yarima da zalunci duk ya take nashi kuma ko sau ɗaya bai taɓa kwaban shi ba,
Idan yarima yazo wucewa a hanya ba ga yara ba, ba ga tsofaffi ba haka zaka ga kowa yana zubewa yana kwasan gaisuwa idan bakayi ba yayi maka mummunan hukunci kuma yasha bulus, amman duk da haka bai hana kwaɗayayyun ƴammata kai mishi buƙatun su da ya aure su ba dukda kowa yayi ma matan fulani shaidan kunya, amman da yawan su indirectly suke zuwa mishi,
Lokacin da Mai gari yace ma Yarima ya fitar da matar aure, yace duk duniya babu wanda yake so sai ni, a ranar daɗi naji kaman ya kashe ni, daga anyi maganar aure ma yarinya zata fara jin kunya amman murnan zan auri Yarima ya kasa ɓoyuwa dukda naga kaman iyaye na basu so ba amman babu yanda suka iya ya zamo musu dole su amince su bada ni,
Tun daga ranar mukayi hannun riga da Furera tun daga lokacin ƙiyayya mai tsanani ta shiga tsakanin mu amman ni ko a jiki na, indai zan auri Yarima komai ma ya faru, idan naje dandali kuwa kada kuga yanda ake koɗa ni ana wasa ni, tun kafin na auri yariman ma sun saka na fara jin kaina a sama nima yanzu na zamo wata, kuma da ikon Allah nida abin ƙaunata Yarima zamu mulki wuroɓokki bayan mahaifin shi ya sauƙa, bayan wata guda akayi mana baiko,
STORY CONTINUES BELOW

GA YANDA AKE WALIMAR BAIKO
Dafari de dangin baki daya zasu taru za’a yanka sa guda bayan an gama yankawa sai a kuma yanka su amma manya manya se a naman a qwarya already dama an hada wuta an ɗaura babban tukunya sai a sa naman nan a tukunya yayi ta dahuwa bayan an kammala dahuwar wannan naman dama already an tatso nono kuma an dafa tsakii to wannan tsakin za’a zuba a cikin nonon se a zubama kowa naman da wannan hadin na nonon se Ana ci Ana rawa da waqa wasu sukan bari se angama sannan suyi rawan,
To ana cikin wannan rawan ne Yarima ya turo yaro ya kira ni a sirrince, a irin wannan lokacin bai dace naje ba amman ido na ya rufe haka na saɓi mayafina na faki idon mutane na fita,
can jikin wata babbar bishiyar kuka na hango shi a jingine, yana gani na yayi gaba ba tare da yace komai ba yana tafiya yana layi kaman zai faɗi, ganin hakan yasa bani da wani zaɓin da ya wuce na bashi, mukayi ta tafiya ba tare da ya tsaya ba kuma ba tare da ya bar layin ba har saida muka fita bayan gari yanda ba mutane da yawa sai gonaki,
Banyi aune ba naji yarima ya riƙo ni yana shinshine jiki na kaman mage, ga warin wiwi mai ɗaga hankali dake fitowa daga bakin sa dukda gaba ɗaya jikinsa ya amsa amman na wurin yafi ƙarfi, tsoro ya kama ni sosai na shiga firgice banda ɓari babu abinda nake yi, saida naji Yarima yana shirin sanya hannun shi cikin riga na kafin na saka wani ƙarfi da bansan daga ina yazo min ba na angije shi, sannan na matsa can nesa dashi ina kallon yanda idanuwan sa suka rine cikin maye ina kuka mai sauti,
Kafin nayi wani yunƙuri ya sake cafko ni yana faɗa min idan na gudu zai fasa aure na, kawai abinda yake gani a waya yake son gwadawa ai suma ance ba masu aure bane
WA’IYAZUBILLAH
Ni bansan me yake faɗa ba, banma gane mai yake nufi ba, abinda na sani kawai shine bani son riƙe ni da yake yi saboda baba ya sha faɗamin duk macen da ta yarda namiji yana taba jikin ta zata ganta da ciki, kuma ance matan aure ne kawai suke ciki ni kuma har yanzu ba matar aure bace,
Ban daddara ba duk da yanda yake tsorata ni da kalaman sa, na sake angije shi da gudu na koma gida, dukda kuwa na san zai iya sakawa a fasan domin sau biyu ana kai mata za’a aura ma Yarima sai magana ya fara ƙargo yace shi bayi so kuma dole a fasa,
A hankali na lallaɓa na shiga gida ba tare da kowa ya lura ba na wuce ɗakin Inna nayi kwanciya ta naci gaba da kuka har yanzu a tsorace nake,
Aikuwa washe garin baikon mu Yarima ya samu mahaifin shi da zancen ya fasa aure na, a nufin shi tunda na wulaƙanta shi zai saka a bar maganar auren sannan daga baya yabi ya lalata ni kaman yanda yake wa sauran yara kuma babu wanda ya isa yace shi yayi, amman mai gari ya katse mishi hanzari, tunda an riga anyi baiko babu maganar fashi dukda mutuncin iyaye na ne zai faɗi ƙasa warwas amman suma nasu mutuncin zai taɓu,
Tun daga son da yarima yake min ya ragu sosai dukda ba wani gwadawa yake yi yana so na ba ji da kai da fankaman shi kaɗai yake zubawa, amman yanzu wulaƙanci ya shigo ciki kuma mun iso gaɓar da ba gudu ba ja da baya,
Bikin mu sauran sati biyu aka fara hidima, mai gari da mutanen shi sunyi ɓarin kuɗi haka nawa iyayen, an zubar da Naira an zubar da jinin dabbobi anyi shagali wanda ba’a taɓa irin shi ba a wuroɓokki amman fa tsakanin amarya da ango har yanzu akwai giɓi,
Lalli duk abinda yayi farko zaiyi ƙarshe, an gama hidiman bikin mu da Yarima yanzu ya riga ya samu abinda yake so daga gare ni saura kuma zaman gaskiya da gaskiya,
Ban wani samu matsala a gidan su ba daga farko, dake nima bani da son jiki na shiga cikin su ana ta hidindimun gida saidai kuma mulkin ogan daga kaina ya fara, yarima jinshi yake kaman sarkin wani babban gari idan yana tare dani ko kallon cikin idon shi ban isa nayi ba, ɗan waya sha biyun da akayi min ma ban isa kwanciya a kanshi ba saidai nayi shimfiɗi a ƙasa na kwanta, kuma na tabbatar da safe kafin ya tashi na riga shi tashi na tattara kayan shimfiɗi na saboda ya samu daman wucewa ba tare da wani tsaiko ba idan ba haka ba jiki na ya gaya min,
Babban matsala, kuma matsala ta biyu da muka samu, bayan auren mu da kusan wata huɗu tsautsayi ya afka a kan babban yayan mu Aminu,
Wurin ƙarfe 8 na dare yana dawowa daga kasuwa bayan yaje saida Sa guda ɓiyu da za’ayi hidimar bikin auren shi nan da sati biyu, har ya wuce jikin wani kango ya dawo ya leƙa ciki saboda kukan mace da yaji yana tasowa daga wurin, leƙawa yayi tare da haska wurin ya hango yarinya wanda bata wuce sa’an boɗɗi ba kwance cikin jini, bai tsaya ɓata lokaci ba ya ciccibeta da nufin kaita gidan su ya ceto rayuwar ta ganin numfashin ta ya fara ɗaukewa
Haka ya dinga gudu da ita har ya shiga cikin ƙauyen su lokacin har 9 ta wuce, daidai ya karyo kwanan da zai sada shi da gidan su yaci karo da dandazon mutane an fito za’a je niman ta shi baima san a ƙauyen take ba dan baima tsaya yaga fuskarta ba,
Furera ce ƙawata Yarima ya keta mata haddi amman babu wanda ya san da hakan, har itama fureran bata sani ba, don saida suka fitar da ita daga hayyacin ta shi da abokin shi kafin suka far mata,
Tsayawa mahaifin ta yayi sakare yana kallon halin da ƴarshi take ciki, ganin haka yasa ya Aminu ya ajiye ta a ƙasa a wurin bata ko motsi kaman gawa, kafin ya samu daman magana yaji sauƙan sanduna a kanshi ta ko ina,
Duk yanda yake roƙonsu su tsaya su saurare shi basu kula ba saida sukayi mishi lilis, sannan suka jashi a wulaƙance har kofar gida wasu ɓarayi daga cikin wanda suka dake shi suka haɗa da kuɗin jikin shi suka ƙwamushe,
Haka Malam Arɗo ya fito ya samu ɗanshi cikin wani hali, ga mutane da sanduna da makamai a kanshi a hakan ma saida sukayi mishi warning cewa idan Furera ta buɗe ido ta faɗi cewa da hannun shi a cikin abinda ya same ta abin ba zai musu kyau ba,
Ina zaune da tray ɗin abincin a gabana na cure wuri guda saboda sanyin da ƙasan yake dashi kuma ya haramta min zama wani wuri da ba zan ɗauki wannan sanyin ba sai yace ina muradin haɗa matsayi na da nashi ne,
A birkice ya shigo ɗakin ganin haka yasa nima nayi saurin miƙewa na nufe shi da nufin tambayar shi abinda ya faru amman jinin da na gani ya ɓata jikin shi yasa na tsaya Turus ina kallo, kardai ace yau ma kumawa yayi? Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, mai yarima yake son maida kanshi ne?
Duk ranan da akayi musu sarin kayan maye to sukan je ne su sami wuri su kebe su sha suyi tatil sai a adana sauran wanda zai kaisu ƙarshen wata kafin a bazu gari kuma komai ta fanjama fanjam!!
Wannan shine karo na biyu da yarima ya shigo min cikin wannan yanayin kuma bani da ikon tuhuman shi,
A gaggauce ya cire kayan ya sauya da wani sannan ya jife ni dashi tare da bani umarnin na tsaftace mishi su, ya zauna hankalin shi kwance ya fara kwasan girkin da aka ajiye mishi dan bayi da wani tsoro ya san babu abinda zaije ya dawo tunda yana da mai gari a matsayin uban shi,
Haka na tattari kayan na fice cikin daren na kama wanke kayan inayi ina zubar da hawaye, nikam naga ta kaina na haɗu da ƙaddarar rayuwa saidai kuma ban sani ba ashe babban ƙaddarar rayuwa tana gaba………..🤦🏻♀️
*Ku ƙaro sharhi, na ƙaro typing*🧘🏻♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
حَسْبِيَ اللَّهُ لَآ إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ
(Hasbiyallahu laa ilaaha illaa huwa aalaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim)
×7 da safe /×7da yamma
_(Seven times)(Allah will grant whoever recites this Seven times in the morning or evening whatever he desires from this world or the next.)_
05🧝🏻♀️
Lokacin da Furera ta farka aka tambaye ta waye ya mata fyade bata ɓata lokaci ba tace musu Ya Aminu ne, amman ta faɗi hakan ne saboda dalilai guda biyu,
Na farko don ta rufa wa kanta asiri, domin taje wannan wurin ne don ta haɗu da miji na Yarima saboda tabi ta matsa mishi kan zancen ya aure ta ta zamo matar shi ta biyu amman hakan ba mai yiwuwa bane saboda aure na dashi ko rabin shekara baiyi ba idan yayi zancen ƙara aure ma mahaifin shi ba zai yarda ba, kuma ga bulus yana gani ba zai bari ya wuce shi ba,
Shiyasa ya bari sai ranar da zasuyi service na miyagun ƙwayoyi su hau kan babban network, ya kwatanta ma Furera jikin wannan kangon taje ta jira shi, suna zuwa shi da ɗaya daga cikin masu take masa baya suka watsa mata abinda yayi saura ta fita hayyacin ta…..
Ta san idan ta buɗi baki tace bata san waye ba aka bi diddigi aka gane cewa ita takai kanta wurin to zata shiga babban Matsala, sannan taji lokacin da ake dukan ya aminu bayan ya ɗauko ta suna faɗa mishi duk abinda ya same ta ya kuka da kanshi don sai sun raba shi da rayuwar shi, shiyasa kawai tace shine,
Sannan dalilin ta na biyu kuma don ta ɗau fansar auran yarima da nayi bayan na san ta daɗe tana son shi,
A karo na farko da munafurcin ɗan Laraba yayi mana amfani kenan, Furere tana gama bada statement ɗin ta mutane sukayi caaa za’a zo a tsire ya Aminu sai kace a lokacin aka fara fyade a garin, abinda ban sani ba ashe Yarima ya lallaɓa ya faɗa wa mahaifinshi shi yayi wannan aika aikan shiyasa Mai Gari shima ya shiga maganar dumu_dumu ya ƙara assasa mishi wuta Saboda ya samu a hukunta yayana maganar ta mutu,
Kafin masu yanke hukunci suzo ɗan Laraba ya ɗibo ƙafa yaje gidan mu ya faɗa ma baba abinda yake faruwa, a take baba ya tarkasa tarukucen ya Aminu ya saka shi ya haura ta katanga ya gudu daga ƙauyen mu gaba ɗaya dan tseratar da kanshi daga laifin da bai aikata ba, kuma har yanzu bai dawo ba,
(Shine yayan jaɗe wanda ya fi iya aikin likitancin gargajiya da kuma bada magani wanda aka ce an kore shi daga garin a littafin Matar Kulle)
Suna zuwa babu niman izini babu komai suka ɗuru cikin gidanmu suna niman Ya aminu basu same shi ba, babu wanda ya taɓa mahaifina don duk taurin kansu ya zamo musu gagara badau domin kaf ƙauyen babu wanda idan rashin lafiya ta taso shi bayi zuwa wurin shi musamman idan annoba ta shigo kaman su muran tsuntsaye da gudda maza da agana da dai sauransu,
STORY CONTINUES BELOW

Dukda kuwa suna da asibiti amman ƙarama ce sosai bai wuce girman dispensary ba, kuma babu likitoci babu kayan aiki ga tsawwalawa da nurses ɗin wurin suke yi,
Amman sunyi ma jaɗe dukan fitan hankali bayan sun tafi dashi sun kulle shi da gargaɗin sai an kai musu ya Aminu kafin su rabu dashi, ran baba yayi mishi zafi sosai amman haka ya barsu da halin su ko hanyar gidan mai gari bai taka ba tunda aka fara case ɗin, da kansu suka gaji da ajiye shi suka sake shi ya tafi,
Amman da aka kwana biyu suka ga ya Aminu bai dawo ba sai suka fara mana ɓarna, idan aka fita kiwo da dabbobin mu sai su kashe wasu ko kuma su sace na sacewa, a haka da ɗaɗɗaya suka fara ƙarewa kullum muna cikin asara, saida aka hallakar da kusan rabi kafin baba ya haƙura da kiwon baki ɗaya ya tarkasa su duka ya siyar suka koma noma, shima dai dan sunga abinda yake nomawan ba wani yawa gare shi bane suka bar mishi don bai wuce abinda zasu ci na shekara ba,
Ranar wata litinin da safe na fito haɗa ma Yarima ruwan wanka wanda ke kwance har wurin ƙarfe 10 yana baccin asara ko sallan asuba baiyi ba, mahaifiyar Furere ta shigo gidan, ban lura da ita ba saboda batayi sallama ba ta kutso kai, na wuce bakin murhu zan sauke tukunya daga kan wuta sai ji nayi an tunkuɗa ni na bugu da jikin bango ruwan zafin dake tukunyar hannu na ya tuntsure wani ya ɓyallu a jiki na,
Taimakon da Allah yayi mun ɗaya ruwan bai tafasa ba domin yarima baƙin rago ne ko ruwan zafi sai yayi masa raki, amman duk da haka naji zafin shi sosai a saman fata na,
Hakan bai isheta ba a cikin kitchen ɗin ta rufe ni da duka, tana jimɗa na tana min Allah ya isa da taga mutanen gidan sun fito suga abinda ke faruwa saboda ihun da nakeyi sai ta saka kukan munafurci amman duk da haka bata bar tima na ba,
Duk cikin su babu wanda yayi yunƙurin ceto na, na gama kwashe ƙasa da kunkuniya dake jikin garu a kayana nayi duƙun_duƙun lokaci ɗaya, saida maman Furere ta gaji dan kanta ta rabu dani, ko ita da tayi dukan sai haki takeyi ballantana ni wanda aka daka?
“Shegiya, mayya, tsinannu kawai, Allah ya wadaran zur’iar ku gaba ɗaya don kun zamo mana masifa da annoba a gari, ƙarshen ku ba zaiyi kyau ba wallahi kun nakasa rayuwar yarinyar da ta gama amincewa dake, to wannan hukuncin da nayi miki ba komai bane a kan wanda zanyi miki nan gaba idan har Aminu bai fito ya miƙa kanshi ba, ki faɗa ma iyayen ki ni Safara’u nace sai naga bayan Aminu duk inda ya shiga ya fita wallahi sai nayi ajalin sa” tana gama faɗan haka fuu tayi waje,
Tunda ta fara magana har ta gama babu wanda ya tanka ta, saida ta fita yadikon Yarima (kishiyar mahaifiyar shi) wanda kowa a gidan yayi mata shaidan rashin kirki ta ƙaraso inda nake ɗuƙe ina kuka ta ɗago fiska na tukunna ta kwashe ni da mari tana gwada ni da yatsar ta manuniya kaman zata tsole min ido,
“Tunda muke babu wanda ya taɓa shigowa cikin gidan nan yayi mana hargowa ko tashin hankali amman gashi saboda ke yau an shigo har gidan mulki an tada mana hankali to kema hankalin ki ba zai kwanta ba daga yanzu ki fara ƙirga kwanakin ƙuncin ki cikin gidan nan sai kin yaba ma aya zaƙin ta”
A taƙaice dai ba shigowar baba Safara’u bane ya samo wannan ƙiyayyar tsakanin mu ba, gaba ɗaya bansan mai nayi ma yadikon Yarima ta ɗauki karan tsana ta ɗaura min ba duk da Yariman ma ba sonshi take ba amman bata iya nunawa tana tsoron saka ƙafa ɗaya da magajin gari don ko uwar da ta haife shi ne ta saka shi a gaba sai ta fuskanci bacin rai,
Tun daga wannan ranar Rayuwa ta ƙara cunkushe min, na ƙara shiga cikin wahala da matsi, yarima da kanshi ya basu go ahead ɗin cin ubana idan nayi ba dai_dai ba daman shikam ya ɗaɗe yana yi,
A wurin kakan Yarima wanda ta haifi Mai gari kawai nake samun mafaka idan suka ritsa ni na gudu wurin ta to na tsira, amman duk da haka duk Ranar da baba Safara’u ta kwaso bala’in ta tazo gidan ta sauƙe min shi tana tafiya ƴan gidan zasu ƙara min nasu kuma su hana ni kuka saboda kada kakan yarima ta ji,
Akwai wani dukan da suka taɓa min saida sukayi min targaɗe a hannu, ai kuwa a lokacin jaɗe yace baiji ba bai gani ba, a kan idon mai gari ya kama Yarima yayi masa kafirin dukan da saida ya suma, ko jin zafin bulalan da bafadai suke masa baiji ba saboda tsananin ɓacin rai, yana gamawa dashi ya shiga har cikin gidan, har ɗakin kwanan mu ya rufa min mayafina ya maida ni gida sannan baba ya ɗaure min targaɗen hannu na,
A ranar a magarƙama jaɗe ya kwana, da safe yarima ya saka aka sake shi don rufe shi da akayi ba amfanin komai zaiyi mishi ba tunda ya riga yayi masa illa yasan ko hukunta shi akayi ba zai damu ba, amman ya ƙudura a ranshi sai ya rama abinda jaɗe yayi mishi a kaina,
Sati na biyu da dawowa Yarima yazo har ƙofar gidan mu sai wani fankama yake yi wai shi yazo bada haƙuri harda bafadai suka rako sa suna ta faman mishi kirari shi kuma kanshi yana daɗa fashewa wai a hakan gyaran aure yazo yi,
Yana wani ciccin magani ya faɗa ma baba ƙudurin shi na yazo maida ni ɗaki na tunda daman tafiya nayi shi ba saki na yayi ba, ko ƙarasa sauraran shi baba baiyi ba ya kora shi da mutanen shin, amman haka mahaifiyata ta zauna ta dinga kuka tana roƙon shi Allah da Annabi ya barni na koma ɗaki na, dan tasan idan har mukayi sake Yarima ya sake ni to tawa ta ƙare a ƙauyen nan dan sai na gwammace da barin cikin ta nayi da zama a cikin ta a matsayin BAZAWARA, BAZAWARAN ma ƘARAMA, ƘARAMAR ma wanda Yariman ƙauye ya saka,
Allah ya gani bani son komawa gidan su Yarima amman bani da wani zabin da ya wuce na rufa ma kaina a siri na zauna a gidan aure na, a shekaru 12 da ƴan kai nayi ƙarama ma ZAWARCI,
Haka baba ya haƙura ya barni na koma amman ya saka min ido sosai kuma yace duk abinda akayi min na tura yaro ya sanar dashi, mutan gidan da sukaji wannan bayanin sun daina taɓa ni, amman shi uban gayyan da bayi duka na sosai a da yanzu idan ya same ni kaman ganga, yayi ta tima na kenan yana huce haushin abinda jaɗe yayi mishi,
A wannan yanayin muka ƙara ƴan watanni kullum ina son sanar ma baba halinda nake ciki amman ina tsoron Yarima, gashi ya koma wani abu daban kaman ba ɗan adam ba saboda shaye_shaye, idan ka ganshi ya rame ya motse sai gingimemen kayi kaman mai kwasharko, wani lokaci idan na ganshi cikin duhu har tsorata nake yi saboda yanzu har tafiyan shi kaman na zombie,
Da abubuwa suka gagara ne kawai ya sako ni a lokacin da na dawo gida na samu baba bayi nan ya shiga daji ɗibo magani sai Khamis dake ta faman jinya wanda bansan daga ina yazo ba,
A zaman da nayi a gida na fara taimakawa baba da jaɗe wurin maganin cutar Khamis, ina kula dashi sannan ina daɗa daukan darussa dukda tun kafin nayi aure na iya ruƙiyya amman a lokacin na maida hankali sosai wurin samun ƙwarewa a fannoni daban_daban, duk da kuwa kullum ana mana bita da ƙulli amman haka na shafe kusan shekara guda ko ƙofa bani fita don yara har jifa na da dutse sunayi suna kiran “ga mayya, ga bazawara”
Wanda suka ɗan manyanta kuma idan suka zo wuce ni saidai naji an tofa min yawu anyi tsaki wasu ma su ƙara da addu’ar neman tsari, shiyasa na shafa ma kaina lafiya nayi zama na a gida har Khamis ya fara samun lafiya lokacin ne kuma miyagun ƙwayoyi sukayi ajalin Yarima mutanen gari kuma suka ɗauki laifi suka ɗaura kin cewa ni na lashe shi kuma sai sun kashe ni,
Da Khamis yaga haiƙan da gaske kashe nin zasuyi shine ya ɗauke ni muka bi dare muka gudo birni ya kaini gidan iyayen shi na zauna, kullum ina zaune ne kawai saidai idan naga mutane suna aiki na fito na taya su amman bani umm bani uhm_uhm,
Ƙannen shi sunyi ƙoƙarin jawoni jikin su na sake dasu amman naƙi suka gaji suka rabu dani, shi kuma wanda ya kawo ni gidan tunda ya shigar dani ya haɗa ni da haɗa ni da mahaifiyar shi ban ƙara ganin shi ba sai bayan wata ɗaya ya dawo daga psychiatry, ya bani zaɓin ko na zauna a nan ɗin wurin iyayen shi ko kuma na bishi gidan shi na zauna yana da mata ɗaya har da ƴa,
Zaɓan zaman gidan su nayi don bansan wani irin kallo matar shi zata min ba idan na bishi, kuma bani son zuwa wurin da zan takura, a cikin watan ya saka ni a makarantar da ƙannen shi suke aka bani primary 2, duk ƴan ajin na girme musu kuma gashi ba gane komai nake yi ba don sun kusan ƙare third term,
A hakandai muka ƙare da ƙyar lokacin na fara sakewa kaɗan dan har nakan je gidan su Yusrah matar Khamis nayi kwanaki har nakan ƙi dawowa saboda yanda maman ta take tarairaya ta don bata da wata ƴa mace a gaban ta daman su biyu ne kuma sunƙi aure,
Hutu ya ƙare na shiga primary 3 amman fa har yanzu dugulum nake, bani gane komai a makaranta ƙwaƙwalwa ta gaba ɗaya a cuse take kuma Allah ya gani ban saka ma raina zanyi karatun bane don bani so, nafi son in dinga business ina samun kuɗi irin na aunty Yusrah saboda na samu na biya Khamis kuɗin ɗawainiyata da yake yi………..🤦🏻♀️
#vote
#share
#comment
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Duk da kinyi nisa amman ban manta ki ba AISHA HAMZA (sweetheart) kinyi zarra wurin iya tsara comment😅😅 Allah ya bada sa’an jarabawa*
*Wannan shafin naku ne*
_my umma Sulaiman, Musmayya, Aisha Isma’il, mom eyman, and khadija mukhtar_
Ku ci gaba da antayo sharhi ina antayo typing 💃🏼💖 ummu Najma tana godiya❤️😍+
06🧝🏻♀️
A hakan muka gama primary 2 muka shiga 3 amman wannan term ɗin saida Khamis yaje ya bada haƙuri ya faɗa musu matsala ta ban fara makaranta daga ajin da ya dace bane kuma ban shiga a kan lokaci ba tukunna suka yarda sukayi min promotion don na 45 nazo a cikin mu 48, ni kuwa ji nakeyi a raina ko banza na wuce mutum 3,
Duk lokacin da na tuna gida na tuna iyaye na zuciyata tana min ciwo, ina jin babu daɗi sosai a raina, nakan yi kuka idan na tuna halin da na barsu a ciki, baban mu yayi mazantaka tunda har ƙaddara masu muni ta faɗo ma yaran shi har biyu amman ya ci gaba da rayuwar shi normal, mahaifiyata kam na san har yanzu bata dawo dai_dai ba,
Wasa_wasa na shekara biyu da rabi a garin Yola banji daga iyaye na ba ko sau ɗaya, koma suna lafiya ko wani abun ya same su? Allah masani,
A makaranta kuma wannan term ɗin ba ƙaramin ƙoƙari nayi ba domin Khamis ya saka ɗaci, yace idan ban dage nayi karatu ba zai maidani gidan su yarima shiyasa na dage nazo na 39 na haye mutane har 6, lokacin da na kaao mishi result babu laifi yace na fara ƙoƙari amman idan har ina son zama tare da su to sai na ƙara ƙoƙari na fara zuwa na 1 ko na 2 a makaranta,
Nidai na san hakan ba zai taɓa yiwuwa ba amman na ƙara jajirce wa har na fara iya turanci irin su IS ME IS YOU,
dukda kasancewa ta shiru_shiru kuma mai sanyin hali amman ba shi yake hana ni faɗa da ƴan ajinmu ba, ban taɓa dambe ba amman ina iyakar ƙoƙari na wajen cacar baki, idan naga yarinya zata ƙure ni sai kawai na haɗe fuska nace mata “I AM MAD” na juya na bar qurin ina tafiyar ƙasaita ko babu komai na zage ta da turanci,
Yanzu haka na gama primary 4 da ƙyar, yau zamu je mu karɓo result ɗinmu ayi mana hutun azumi sai bayan Sallah zamu koma aunty Yusrah kuma ta kusan aihuwa shiyasa shekaran jiya mama ta gargaɗo ni nazo na taya ta zama ina rage mata wasu ayyukan,
Ohh ashe abinda ya kawoni kenan!!
Tashi nayi da sauri na naɗe darduman sallah na ajiye sannan nabi na bude labulayen parlorn har rana ta fito haske ya shigo na ɗauki tsintsiya na fara sharo ko wani kusurwa na gidan,
Ina gamawa ana kawo wutan lantarki, na dauki kettle ɗinta mai kaman buta na cika shi damm da ruwa sannan na jona na wankan mu na same ta a kitchen muka ƙarasa haɗa soyayyen doya da sauce sannan ta tafi haɗa ma Khamis ruwan wanka ni kuma na kama mopping,
Bayan mun gama breakfast, da sauri na shirya cikin uniform ɗina dark green and white, fuskata sai kyallin mai take na ɗauki jaka na na fita, a waje na samu mai napep ɗin da aka ɗauka yana kaimu makaranta ni da Jannat wanda take da shekara 3½ a yanzu, ta gama play class zata shiga nursery one bayan sallah, ya ɗauke ni muka biya gidan mama muka ɗauko ta tukunna muka wuce makaranta,
STORY CONTINUES BELOW

*****
“Alhamdulillah” Khamis ya furta lokacin da ya ajiye cup ɗin hannun shi ya gyara zaman hulan kanshi tare da kallon Yusrah yace “baby hanzarta mu tafi kada kiyi latti kinga yanzu har ƙarfe 8 harda minti 2” saboda shi da kanshi yake kaita makaranta, harƙoƙin kasuwancin ta da sauran abubuwa ne yace ta dinga bawa public transport saboda shima yana zuwa aiki ba ko yaushe yake available ba,
“Ayyah ban ƙoshi bane fah”
Sunkuyawa yayi yana leƙa fuskar ta da ta yamutse shi tana faman wurga loma yace “idan kika faɗi a test ɗin nan blame your stomach not me, tunda gashi ni na gama shiryawa jiran ki kawai nake amman da yanzu wani abu zai faru zaki ce, Abban Jannat ai laifin ka ne bamu tafi da wuri ba shiyasa ban samu nayi karatu ba” ya faɗa tare da lanƙwasa murya yana wani rausaya kai irin yanda take magana, “To kome ya faru babu ruwa na”
Murmushi tayi tace “ai karatun yanzu ba zaiyi min wahala ba 30 to 40 minutes yayi yawa na gama, a kwai wani abokin karatu na da sukayi magana da malamin yace yanzu zai raba mark ɗin test ɗin gida biyu ɗayan ya bamu assignment, harma ya fara min assignment ɗin mutumin yana da kirki wallahi, he is so kind”
Gyara zama Khamis yayi yana hararan ta, tana ganin haka ta tuntsure da dariya,
“Haba habiby sahibul ƙalbi, daga karatu fa sai aji babu abinda zai haɗa ni dashi bayan nan”
“To wannan yaba shi da kike yi a gaba na fa? Na menene?”
“Cewa kawai nayi he is kind, that’s all”
“Shi wannan soooo ɗin da kika faɗa kafin kind ɗin kuma a dalilin me kika saka shi ciki?”
Dariya kawai tayi dan ta lura yau niman magana ya tashi dashi,
“Menene na tada hankali my love? Ka manta akwai shaidan ka a jiki na ne? Babu wanda ya isa ya raɓe ni idan yaga wannan, ka dai ci gaba da mana addu’a Allah ya raba mu lafiya”
Ƙayataccen murmushi ya sake saman fiskar sa tare da faɗin “Amin, amarya kuma uwar gidan Abban Jannat, my rich wife yarinya ƴar kasuwa, daga ke ba ƙari”
“Haka dai ko yaushe kuke faɗa amman halin ku maza sai a hankali, idan kaso ka ƙaro auren ka bazan hana ka ba”
“Oh ke baki kishi na kenan ko? Shikkenan daman kuwa naga wata yarinya ƴar fara ta unguwan ku kinga muna gama gina gidan mu sai mu tare da sabuwar A……”
Bai ƙarasa ba Yusrah ta katse shi da bala’in da bata san daga ina yazo mata ba,
“Kada yarinya ta kuskura wallahi, zan yanka wuyan ƴar mutane idan ta kuskura ta shigo gida na, gwanda ma kada ku fara”
“Yi haƙuri aunty Yusrah” ya faɗa tare da zabga tagumi yana kallon ta, yanda tayi kicin_kicin lokaci ɗaya ya nemi ɗan murmushin da take masa ya rasa,
Ƙaramin tsaki taja taci gaba da cin abincin ta wanda yana kyautata zaton plate na uku kenan,
“kefa yanzu abincin runduna kike ci, ba zaki saka ma baby na rashin lafiya ba kuwa?”
Bata amsa shi ba dan ya gama bata haushi, mafarkin ta bai wuce mijinta ya mallaki gidan kanshi su koma rayuwan su a ciki da ƴan ƴaƴanta ba amman gashi yana son shigo mata da wani zance daban,
Saida ta gama sannan ta tattara wurin ta saka hijab ɗinta ta lanƙaya handbad ɗinta ta ƙaraso inda yake tsaye fuska a tamke tace “muje” bai nuna damuwa da canjin yanayin ta kaman yanda taso yayi ba, ya miƙe tare da sauƙe rigan shi ta baya ya ɗauki key ɗin mitar shi yayi gaba,
Har zai fita daga parlorn ta kira shi ya juyo yana kallon ta,
“Daman nace ka barshi kawai ka wuce wurin aikin ka kada na ɓata maka lokaci, akwai wani aboki na ɗan ajinmu zai zo ya ɗauke ni mu tafi”
Girgiza kai Khamis yayi yana dariya, wato abinda ya faɗa mata ne take so ta rama, Allah sarki baya mai wucewa da a lokacin ne ta faɗa mishi wannan maganar da ya daɗe da haɗa kanta da bango ko cikin jikin ta bazai dame shi ba,
Kusanto ta ya fara yi yana gwada ta da key ɗin hannun shi still yana dariya yace
“You are trying me ko? Allah idan kika yi Wasa makarantar nan sai a fasa shi, daga yau kin bar zuwa”
Murmushi tayi wanda ya bayyana haƙwaran ta gudun kada ta takalo ma kanta fitina ta riƙo hannun shi suka nufi hanyar waje tana faɗin “Allah ya huci zuciyar angon Yusrah, ba ma za’ayi hakan ba”
**********
Sallama yayi da buɗaɗiyar murya, mutanen ɗakin suka amsa tare da bashi izini kafin ya shigo, tsugunawa yayi suka gaisa da mahaifiyar Zayyad kafin ya samu kujera ya zauna yana masa sannu da jiki,
Yafi 20 minutes zaune ba tare da yace komai ba yana jiran ta fita ta basu wuri amman ko kallon inda yake bata yi ta maida hankalin ta kan wayar hannun ta dukda kunnuwan ta yana muradin sauraron abinda zasu tattauna a kai don tunda taga Sulaiman ya shigo da sanyin safiya ta san a kwai matsala,
sannan ta fara gajiya da irin takurawan da yake yi ma Zayyad yana saka shi ɗaga hankalin shi kan matsalar da bata kai ta kawo ba, ta gaji da sanya shi damuwa da yake yi ko wani lokaci ya maida shi matsoraci kuma rago, ya saka ya dawo kaman mace kullum yana ƙunshe a ɗaki,
Tsawon shekara da shekaru yake ɓoye shi a gida, ya hana shi yin abokai ya hana shi yin ƴammata, bata son ko bayi son yayi aure bane a rayuwan shi gaba ɗaya, dan taurin kai da rawan kai da samaruka suke yi idan sunzo gaɓar girma duk Sulaiman ya daƙushe na Zayyad, ita yanzu abin ya fara isan ta, ta jure shekara da shekaru amman hanzu da abu yazo bakin gaɓa bata jin zata ci gaba da haƙuri daman ance aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, yanzu kam tana son sama ma ɗanta ƴanci,
Ganin bata da niyyan basu wuri kuma ba zai iya ce mata ta fita ba yasa ya tashi daga mazaunin shi ya ƙarasa bedside drawe ya tura lamp ɗin dake kai ya zauna yana kallon shi na wasu ƴan daƙiƙu,
Tun kafin yayi wani abu Zayyad ya tsorata a zuciyan shi yana addu’ar Allah yasa ba tsintan abin nan Sulaiman yayi ba, don a daren shekaran jiya Sulthana ne ta hana shi nema da tazo da kalan nata iya shegen,
Bai ƙarasa tunani ba Sulaiman ya saka hannu cikin aljihun jamfan shi ya ciro wata ƙaramar container fari ya miƙa ma Zayyad tare da faɗin
“Wannan abun kaje nema ko?”
Kame_kame Zayyad ya fara dan yasan idan yayi ƙarya tabbas Sulaiman zai gane,
Bai gama laluɓo abinda zai faɗa ba ya jefa mishi wani tambayar
“Yaya akayi kayi sake ka rasa shi?”
“Babban yaya ban san ya zame daga aljihu na bane kum….”
“Me ya fitar da kai wurin a lokacin, kuma mai ya haɗa ka da Sulthana cikin dare? Baka guje ma kanka fitina ko??”
Ba abin mamaki bane don ya san da duka wa’innan abubuwan bayan bayi wurin kuma babu camera dake ɗauka amman yana da munafukai masu barci da ido ɗaya,
Zayyad ya buɗe baki mahaifiyar shi tayi saurin saka bakin ta ciki, daman daman da take nema kenan wanda zatayi mishi complain ɗin abubuwan da yake yi,
“Haba Sulaiman, ka sassauta ma al’amarin nan dan Allah da wanne ɗaya kake so yaji? Halin da yake ciki ko kuma tuhumar da kake mishi?”
A dake kaman yanda yake magana da kowa yace “Aunty Amarya maganin matsalar nake son kawowa baki ɗaya, dan Allah ku tausaya min, shekaru biyu kaɗai tunda na lura ku baku son Zayyad ya samu kason shi to ni ina so, ina mafarkin ganin ya mallaki wani muhimmin abu a duniya saboda yayi farin ciki nan gaba ya samu yayi murmushin da baiyi shi lokacin baya ba, kuma insha Allah duk inda maganin matsalar Zayyad yake sai naje na samo shi”
Da faɗan haka ya wurga mishi containern ya fita,
Tsaki aunty Amarya tayi ta dubi Zayyad da ya sadda kanshi ƙasa kaman mai shirin kuka tace “kayi haƙuri Zayd nasan an takura maka amman ka ƙara haƙuri insha Allah wata rana komai zai zamo kaman ba’ayi ba, zamu fita daga ƙangin sulaiman”
“A’a aunty, abunda babban yaya yake yi shine dai-dai, duk laifi na ne da bani kiyaye dokokin da yake shimfiɗa min wanda zai kaimu ga nasara……….🤦🏻♀️
_Ayi manage, muna tsakiyar gasa ne a kuma taya mu adduan nasara Please_
#vote
#share
#comment
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الَْأرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
(Bismillaahil-lazee laa yadurru ma’as-mihi shay’un fil-‘ardhi wa laa fis-samaa’i wa Huwas-Samee ‘ul- ‘Aleem)
×3 da safe/×3 da yamma
(Three times)(Whoever recites it in the morning will not be afflicted by any calamity before evening, and whoever recites it in the evening will not be overtaken by any calamity before morning.)
07🧝🏻♀️+
Yana so na sosai bayi son ganin faɗuwa na, dukda nasan ko samin kason nawa nayi ba amfani zaiyi min ba saboda wannan matsalar amman zan jajirce naga na samu ko dan babban yaya yaji daɗi”
Sauƙe nannauyan ajiyar zuciya tayi cike da tausayin ɗanta tace
“Shikkenan Zayd, Allah ya kawo mana ƙarshen wannan al’amarin nan kusa, bari naje ko tea ne na kawo maka naga abincin da Ruma ta kawo maka da safe baka ci ba aka fita dashi”
Tana faɗin haka ta ajiye waya da casbin ta a seat ɗin da ta tashi ta fice daga dakin,
Sunkuyar da kanshi yayi a yanda yake zaune an tokare bayan shi da filo ya haɗa kai da guiwa yana jin zafi sosai a zuciyar shi, rayuwar shi ɗaya take da mara amfani tunda bayi amfanan kowa da komai kullum wahala kawai ake yi dashi, harta hankalin wanda suke tare dashi ba a kwance bane kullum suna cikin fargaban ya shiga matsala, basu son ganin kukan shi amman shi ba zai iya hana su kuka ba,
“Ya Allah kaine mai iko a kan kowa da komai ya Allah ka raba ni da matsalar da nake fama dashi, ya Allah ka yafe min kura kurai na ka sanya ni jin daɗin lahira idan duniya ba rabo na bace, ya Allah kaine mai iko akan dukkan komai, kai kake yin yanda kaso da kowa, ya Allah idan wannan matsalar itace jarabawata ka sauƙaƙamin kuma kasa na tsallake ta ya zul jalalu wal ikram” ya faɗa hawaye suna sauƙa daga idanun shi,
******
Da sallama ya shigo parlorn tare da wata mata a gefen shi tana ɗauke da yarinya a hannun ta da ba zata wuce shekara 2 ba, Ruma na hango su da sauri ta ajiye fork din hannun ta taje da gudu ta rungume matar kaman zata kaisu ƙasa,
Da ƙyar ta samu tayi balancing kanta tana dariyan ƙarfin hali yarinya zata ɓarar da ita a gaban surakanan ta,
“Rumaisa wai yaushe zaki yi hankali ne? Baki ganin yarinya a hannun ta ne ba zaki ɗauka mata ita ba sai ki ƙara mata da nauyin ki?”
Lakutan hancin yarinyan tayi tace “wannan mai ƙyuyan ko nace zan ɗauke ta ba yarda zatayi ba ya Nafi’u, sannun ku da zuwa”
Cikin girmamawa ta gaida su da kyar ta samu yarinyar hannun matar shi taje wurinta, suka ƙarasa gaban dining ɗin sukai squatting a ƙasa suna gaida Baba da Hajiya, ɗaya bayan ɗaya yaran dake zaune tare dasu suka fara gaida su yana amsawa tare da tsokanar su,
“Lafiya ƙlau aunty rasai” ya faɗa yana kallon Fa’iza da take faman ture turen baki don tasan wannan zuwan da suka kwaso zuga na tarban Zaytoon ne ita bata san wani dalili bane yasa kowa yake sonta ba kuma hakan na ɓata mata rai sosai, tafi so taga ko ina ana rashin mutunci ko kuma tsakanin mutane babu jituwa yanda zata samu ta caccaki kowa son ranta,
STORY CONTINUES BELOW

Dariya Batool tayi tare da yima Fa’iza gwalo, tace ” ina kwana dadyn husna”
“Lafiya ƙalau kalaye mai kalen magana, baki da aiki kullum sai tsokanar yara kisa su raina ki”
Nana kanma tana jin haka kafin azo kanta ta tashi ta wuce ciki domin ita ƙunci kaman a jinin ta yake, abu kaɗan zakayi mata ta hau ranta ya baci shiyasa wannan wasan da yake tsakanin ta da yayun ta bata son shi don gani take kaman yaɓa mata magana suke yi da gangan,
Ɗaga murya yayi yace “ki dai raba kanki da baƙin hali don baki gaje shi ba”
Ai kuwa tana jin haka ta bankaɗa ƙofar bedroom ɗinta ta shige ciki tare da rufo shi da ƙarfi hawaye na taruwa a idanun ta, cin mutuncin da ta gudan saida ta samu shiyasa ta tsani babban yaya da ya Nafi’u su shigo gidan, gashi Sulaiman kaman maita ko yaushe yana sintiri a tsakani saboda Zayyad,
Murmushi Baba yayi yace, “nana hafsa kenan kwata_kwata baki ɗauko halin mai sunan ki ba gashi an saka min ke a gaba”
“ba haka bane baba gyarawa muke son tayi”
“Gyara a hakan? Ai baku biyo ta sigar gyara ba don tozarta mutum bashi yake saka ya gyara munanan halayen shi ba, zaunar da ita zakuyi kuna ankarar da ita kurakuran ta domin ta gyara sannan ku dinga taya ta da addu’a don wannan ba halin zama cikin mutane bane gashi Allah yayi mu cikin dangi”
Sosa ƙeyar shi yayi yana murmushin yaƙe an fetta shi a gaban ƴan ƙannen shi harda su Junior a wurin, ashe irin hakan da suke ma Nana babu daɗi tunda itama akwai na ƙasa da ita a wurin,
“Insha Allah Baba, babban yaya bai shigo bane?”
Ruma ce ta amsa da “ya shigo dazu amman daga sashin anty Amarya ya fita gaba ɗaya bai dawo ta nan ba”
“Ok inaga ya tafi office ne, nima zan wuce ayi mana addu’a”
Allah ya kiyaye da Allah ya tsare suke masa har ya fita,
*****
“Wannan zuwan na aunty Zaytoona ne ko aunty ummi?” Ruma ta tambayi matar Nafi’u bayan sun shiga ɗakin su Batool sun samu matsuguni a armchairs dake ɗakin,
Murmushi tayi tace “kema kin sani ai, dole nazo tarban ƙawata guda kusan watanni 5 bamu ganta ba”
“Maybe yanzu ta ƙara haɓaka ta daɗa zama buskuɗa dan naga kaman zaman can ƙasan daɗa hura ta yake yi” ta faɗa tana dariya, don ita ba damuwan ta dawowar da zaytoon zatayi bane burin ta bai wuce taga tana tafiya ko wani ɓari na jikin ta yana girgiza ba tayi ta kwasan dariya
Kafin ummi tayi wani magana suka ji ana shewa da ihu a parlor da sauri suka fita don wannan alama ce dake gwada sauƙar ta cikin gidan, farin ciki murmushi da annashuwan wasu ya dawo da zuwan ta ba zata taba ganin su cikin damuwa ta ƙyale ba,
Kaman yanda Ruma ta faɗa yarinyar lutiya ne amman kallo ɗaya zaka yi wa fuskarta ma gane ba wani shekaru gare ta ba don da kaɗan ta girmi Batool kusan kunika ma suke tsakanin su shekara 1½,
Da murmushi a fuskarta suka gaisawa da kowa yara suka shiga mata da kayyakin ta ɗaki Ruma uwar gayya ta fara rabon tsaraba tun kafin zaytoon ɗin ta samu wurin zama don kowa da sunan shi a jikin nashi harda su sulthana da Muna kuwa bata manta da su ba,
Bata zauna ba ta wuce part ɗin aunty Amarya zata duba Zayyad don sun faɗa mata bayi da lafiya,
Tana shiga ta same shi yana sallan walha ta ɗauki dessert da aunty ta ajiye mishi ta zauna ta kama ci tana jira ya idar, saida ya kammala sannan cikin nutsuwa ta tako zuwa gaban shi tayi hugging ɗinshi tana dariyan jin daɗi da murnan haɗuwa da jinin ta, shima murmushi yayi yana ɗan buga bayanta a hankali cikin zolaya yace
“Kwantar dani kike son sake yi tun ban gama warwarewa ba zaytoon?”
Cikin nutsuwa wanda ita kaɗai take da irin ta a cikin su sai Zayyad ɗin da aka saka mishi na dole tace
“Ba zaka mutu ba yaya na sai kwanan ka ya ƙare”
“To yaya hanya yaya kika baro iyayen gidan ki”
“Lfyn su ƙlau hanya kam na kwaso gajiya, yanzu ma barci nake son yi idan na tashi zan zo maka na musamman musha hira” da faɗan haka ta dauki plate ɗin ɗungurungum ta fita dashi
**********
Ɗagowa yayi ya kalle ni ya sake maida idanun shi kan takardan yana duba duba abin da ya gani a jiki, ni kuwa sai addu’a nake yi a zuciyata Allah yasa kada yace zai maida ni gidan su yarima wannan karon dan ba na ɗaya ko na biyu da yace nayi nayin ba,
“Zauna da kyau” ya umarce ni a taƙaice,
Saida hanjin ciki na ya kada jin kaushin muryan sa na gyara na zauna daga tsugunon da nake ina kallin cikin ƙwayar idon shi,
“Yanzu Saudat na 42 biyu kika sake zuwa? A halan ma an cire mutane 3 a ajin naku, da kin fara kaman zakiyi ƙoƙari kin dawo kin faɗi ƙasa warwas?”
Shiru nayi ina ƙifi_ƙifi da ido bansan me zance mishi ba don har yanzu fagen rubutu ko spelling sunana correctly ban iya ba, bani mantawa exams ɗin maths da mukayi, a jikin questions ɗin an mana misalai da oranges wurin addition da subtraction duk zanen orange aka saka, ni kuma da ban gane me za’ayi a wurin ba saboda ban iya karantawa ba dai kawai na ɗauki lemu ɗaya na zana shi ƙatoto a jikin takardan nayi submitting, sauran exams ɗinma shirme na nayi tunda ban iya karatu ba kuma ba karanta mana ake yi ba wasu sai na zauna na kwafe questions ɗin tass nayi submitting, wanda ba zan iya ba kuma sai na bari lokaci ya ciki na basu takardan su yanda suka miƙa min ko suna babu a jiki,
“Kina muradin komawa gidan yarima ko?”
“A’a wallahi” na faɗa tare da fashewa da kuka mai sauti, ” is me is coming is girl paper do me copy me say no she do tauu me do yayyy”
“Hold it please, ni bance kimin turanci ba bayani nake so kimin da harshen hausa”
Ƙara sautin kuka na nayi ina share hawaye da ƙyar na iya buɗe baki na fara mishi bayani,
“Daman wata yarinya ce a ajinmu na gama jarabawa tace na bata ta kwafa da na hana ta shine ta dake ni nayi ta kuka amman taƙi ta bani yanzu ita an bata maki ni kume ance na faɗi kuma wallahi ƙarya ne, Hamma awada muyal useni…….🤦🏻♀️
_Readmores biyar gobe insha Allah😁_
#vote
#share
#comment
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
_Niman maganar ANTIMEE ya ƙare a Kan su FATI cleaner ta AMADULLE😂_
Wannan shafin taku ce tare da
*Aunty Sadiya vice da*
*Haziƙar marubuciyar nan MAIMUNA ABADALLAH (HEROIN)*
_SONKU A CIKIN JININA YAKE❤😘_️+
Jiya nayi mistake wurin numbering na saka page 5 instead of page 7, bear with me please 🤦🏻♀️
08🧝🏻♀️
“Bayan faɗuwar jarabawa hadda ƙarya kika koyo saudat?”
Matso kwalla na daɗa yi tare da matsowa kusa da kujerar da yake zaune na saki kuka, duk yana zaune yana kallon ikon Allah baice komi ba don ba yau na fara irin wannan draman ba,
Duk ranar da result ya fito nayi failing nakan yi kuka kaman raina zai fita amman ba shi zai saka gobe na maida hankali wajen karatun ba domin bayi cikin list ɗina kwata_kwata, ni so nake yi ma idan za’a ko a hutu na roƙe shi ya barni ina saran hanjin ligidi ina siyarwa ma yaran ajinmu don naga masu siyar musu suna ciniki sosai,
“Meye sunan yarinyar da ta ƙwace miki takardan jarabawan ki?”
Naji muryan Khamis ya katse min lissafin riban hanjin ligidi da nake yi, daram naji ƙirji na ya buga dan banyi wannan tunanin ba tukunna,
“Uhmm.. sunan ta..umm”
Ɗan matsowa gaba yayi, ya harda yatsun shi yana jefa min wani serous look don ya lura kaman na ɗauki abun a matsayin wasa ne,
“Listen to me s..”
“A’a ba lisin bane sunan ta, Rahama ne” na faɗa tare da sake fashewa da wani kukan munafurci don bani so ya sake jefo min wani tambayar da bazan iya amsawa ba,
Tsaki yaja a tsawace yace “ki saurare ni nace!! Na ɗago ina girgiza kai hawaye na sintiri kan fuska na,
“Wallahi Saudat idan baki maida hankali ba kudin motan ƙauyen ku ba tsada gareshi ba, wannan shine dama na ƙarshe da zan baki idan har kika zo sama da na 25th position next term a take zan biya kuɗin mota na saka ki a kaiki har ƙofan gidan mai gari ko rakiya ba zan miki ba, dan haka ya rage naki ki dage kiyi karatu ko kuma ki zauna shashanci, tashi ki bani wuri”
Miƙewa nayi ina kuka kaman raina zai fita duk na cika mishi kunne domin a rayuwata ko sunan mutuwa bani ƙinshi kaman yanda naƙi jinin a ambaci sunan mai gari, dole ne kawai na haƙura da burin rayuwa na niman kuɗi na rungumi karatun tunda shi uban gidan na yake so,
Jiki a sanyaye na tashi na shige bedroom ɗin Yusrah don tace idan mun gama nazo na same ta mu ƙarasa gyaran wardrobe ɗin Jannat sannan muyi fitting sabbin kayan da suka siyo na babies a ciki wasu kuma a jera su cikin drawer,
A zaune na sameta saman darduma ta zuba kayan a kan cinyar ta tana naɗewa, dagowa tayi tana kallon yanda nake sharban kuka ta miƙa min hannun ta ɗaya na ƙarasa na zuba a jikin ta har saida ta saki ƙara na buga mata ciki,
“Kada ki ƙarasa ni boɗɗi faɗa min yaya kuka yi dashi?”
Ban ɗago ba na ƙara shigewa cikin jikin ta ina kuka, “aunty Yusrah yace ƙauye zai maida ni gidan su Yarima dan Allah ki bashi haƙuri bani son na koma can”
STORY CONTINUES BELOW

“To ai laifin ki ne boɗɗi, ya riga ya faɗa miki abinda yake so amman kin kasa maida hankalin ki a kai, kinga shi wannan karatun da kike ƙi mutane da dama suna neman damar da kika samu basu samu ba, yanzu a ƙauyen ku waye kika gani yana karatu?”
Jan hanci nayi na share hawayen fukska na da bayan hannu na sannan na daɗa lafewa a jikinta a hankali na furta “Babu”
“to kin gani, wannan karatun shi zai baki ilimin wayewa na zama cikin mutane daban_daban da iya mu’amala da su, ke yanzu kaman wata izina ce ma sauran mutane saboda wahalhalun da kika sha na rayuwa tun baki da wayo har zuwa yanzu, sannan Allah ya kubutar dake ne ba don komai ba sai don ki zamo mai kawo canji a rayuwar mutanen da suke shan wahala irin naki suke azabtuwa a ƙauyen ku,
ke kaɗai ne kike da experience na wahalar da sauran matan ku suke sha dan haka ke kaɗai ce kike da kaman sinadari na kawo ƙarshen wannan wahalan, lallai ƙauyen ku akwai ilimin addinin musulunci amman ba’a amfani dashi, kuna da sani amman kuna danne sanin ku I’m sorry to say amman wani lokacin rayuwar ku kaman na tumaki yake, baku bin hanyar Allah baku bin tafarkin Manzon Allah s.a.w kuna rayuwa ne da son zuciyar ku kawai,
Saidai shi wannan ilimin na boko bawai kawai zai saka ki ƙware a turanci kina yi don ki burge mutane bane A’a, idan kika yishi mai nisa yakan baki wani power ne da zaki iya amfani dashi ki jagoranci al’umma, kuma kinyi min maganar kina son tara kuɗi amman shima wannan karatun bokon idan kika kai wani mataki a cikin shi kika yi Sa’an samun aiki za’a dinga biyan ki albashi ko wani wata,
don ilimi ko wani iri kogi ne bayi ƙarewa idan kika samu dama zaki iya ɗaurawa a kan wancan ɗin sai a ƙara miki matsayi a wurin aikin ki idan kina cikin masu Sa’a ko kuma ki samu wani aikin da ya fishi kuɗin da ake biyan ki sai ya ninka shi, kuma zaki iya haɗa karatu da niman kuɗi kaman yanda nake yi duk da ina da tsohon ciki amman me aka fasa? Kinga ni har uku ma na haɗa ga aure ga raino huɗu ma kenan”
A hankali na ɗago kaɗan tare da leƙa fuskar ta naga itama ni take kallo, ɗaga giran ta duka biyu tayi don ta tabbatar min da zancen tace “yess! Duk abinda na faɗa miki gaskiya ce” sannan taci gaba da cewa
“Rayuwar yanzu da kike gani idan kika ce kwanciya zakiyi to kin ƙulla ƙawance da takaici, ko babu abinda zakiyi da kudin ki neme su ko babu komai kinfi ƙarfin bani_bani, idanma mijinki bai amince miki ki nemi kuɗin ba ya yarda zai dinga baki duk lokacin da kike da buƙata fine! Idan ya amince miki kinyi karatu yace bayi son kiyi aiki fine!!
Duk da haka dai baki ci baya ba sabida zaki amfani yaran ki, sannan Allah ya kiyaye amman akwai mutuwa ko rabuwa idan ɗaya daga cikin su ya faru zaki iya amfani da certificate ɗinki ki dogara da kanki ba sai kin ɗaura nauyi ma iyayen ki ba kuma zaki iya ɗaukan ɗawainyar yaran ki dashi, idan kika samu irin wannan daman ba’a wasa dashi boɗɗi, please don’t waste your golden opportunity mu muka amince zamu ɗauki nauyin karatun ki gaba ɗaya har ƙarshe,
Ko baki son ki samu daman komawa wuroɓokki ki gano halin da iyayenki suke ciki ne? Baki so ki shiga ƙauyen ku a lokacin da kima ga dama kuma babu wanda ya isa ya taɓa ki saboda kina da ƙarfin iko?’
“Ina so aunty Yusrah”
“To ilimi shine kaɗai abinda zai baki wannan damar, ki cire ranki ma kallon TV da kike yi babu dare babu rana, yanzu kaf draman hausa babu sunan actor ko actress da baki riƙe ba, ko kallon ma ya kamata kina sirkawa da na turanci ba don komai ba sai dan ki ƙara ƙwarewa,
amman kinfi so ki zauna kawai kina kallon labarin soyayya ace wance matar wane ne wance tana da cikin shege, wance ta aihu wane ya gudu da wance sunje sunyi aure ba tare da sanin iyayen su ba and stuffs,
you are too young for all of this rayuwar ƙauye ba irin ta birni bane, you are just 15 a can matsayin uwa mai shekarun ki take amman a nan har yanzu ma wasu mutanen zasu iya saka ki a sahun yara, kina da sauran lokaci boɗɗi dan Allah kada kiyi wasa dashi”
STORY CONTINUES BELOW

Gaba ɗaya sai naji jiki na yayi sanyi da kalaman ta, duk abinda aunty Yusrah ta faɗa gaskiya ne, kamata yayi ma ace a yanzu maganar ɗaukar fansa ma yaya na da mahaifi na ne a gaba na,
yanzu ne lokacin da zanyi amfani da dama ta saboda nan gaba na koma na ɗanɗana ma mai gari irin azabtarwan da suka ɗanɗana min na dawo da ya Aminu cikin ƙasar shi ta aihuwa sannan na wanke laifin da aka ɗaura mishi bai jiba bai gani ba,
“Insha Allah aunty Yusrah, me is read book me is no TV”
Faffaɗan murmushi ta sake don dukda turancin ba daidai tayi ba amman ta fahimci abinda take faɗa wato zata yi karatu kuma zata daina kallon TV,
“Allah yasa ƙanwata, daga yanzu ni da kaina zan dinga miki lesson kullum idan mun gama aiki muna hutawa indai abban Jannat bayi nan ko bayan na aihu ne kizo zan dinga miki lesson sannan zan baɗa auntyn ki Nasreen kuɗi ta siyo miki wasu litattafai don yanzu shiga kasuwa yana nima gagara na”
**********
“Aunty dan Allah har yanzu bai amince ba? Azumi sauran kwana uku ko huɗu kuma idan ya tafi Umrah har ya dawo ba gane mishi zamuyi ba, ki min wani ƙoƙari don Allah”
Ƙara ta sake saboda cizon da yarinyan da take shayarwa ta gantsara mata, ta dangwali goshin yarinya da ƙarfi ta kwala kiran nanyn ta, shigowa tayi ta miƙa mata yarinyar ta fita da ita tana jin yanda take tsala ihu saboda bata ƙoshi ba amman ko a kwalar rigan ta daman ba a son ranta take shayar da yarinya mai shekara ɗaya harda wata biyu ba, Sulaiman ne ya matsa mata dole saboda yarinyar bata da ishashen lafiya tana da yawan laulayi, Arif watan shi 10 a duniya ta yaye shi da ta samu ya fara karban cereal,
Yamutsa fuska tayi tana kallon budurwan dake gaban ta wanda nake tsammanin yayar Sulthana ce dan dukkan su suna ɗibi da Sadiya
“Yaya kike so nayi Muna? Kema da ba a gidan nan kike ba kinsan halin mutumin nan idan yace ba zaiyi abu ba sau ɗaya bayi dawowa ya yarda yayi, tunda nake da Sulaiman bai taɓa dawowa a kan maganar sa ba dan haka tsanantawa ma ɓata lokaci ne,
ki haƙura kawai ki ƙarasa karatun ki a makarantar da ya saka ki tunda ya nace da hakan muci gaba da karɓan kuɗaɗen shi kawai”
Tsaki Muna taja ta tashi tabar mata parlorn, ita duk ba haka tayi tunani ba bata ɗauka ba tare da ita za’a tura ibadan ba don har ta fara faɗa ma ƙawayen ta an cire su a MAUTECH za’a maida su makarantar da ya fishi tsada,
Tana shiga wani bedroom ta zube a kan gadon sannan ta jawo wayarta ta danna kiran Sulthana bugu ɗaya ta dauka,
“Ke har yanzu kina gidan baban wulaƙancin nan ne?”
“A’a ina gida, me ya same ki ne aunty muna naji muryan ki wani iri”
“Ba dole ba, wannan mutumin duk ya wargaza min lissafi, me yasa ze kaiku wani wuri ba tare dani bane bayan yasan duk tare muke a makarantar?”
“Aunty Muna na faɗa miki horo fa ze kaimu wurin nan laifi mukayi masa” Sulthana ta faɗa cikin kasashshiyar murya,
“Wani laifi ne wannan dan Allah nima nayi ya haɗa dani ya tura wurin nan ba zan yarda ku tafi ku barni ni ɗaya ba wallahi, ki faɗa min wani laifi ne wannan kafin gobe zan aikata shi na ranste”
“Gaskiya ba zan iya ba aunty maimoona, ina tsoron wannan sirrin kaman yanda nake tsoron mutuwa ta, babban yaya zai iya katse min duk wani jin daɗin rayuwata saboda wannan sirrin dan Allah kada ki saka ni cikin matsala” ta faɗa kaman zata fasa ihu,
Shiru Muna tayi na ƴan seconds sannan tace “wani sirri kenan? A ina yake wannan sirrin naje na bankaɗo shi don nima ayi min abinda nake so? Ki faɗa min yanda wannan sirrin yake yanzu yanzun nan inje na bankaɗo shi kowa yaji”
Kuka Sulthana ta saka tace “A’a wallahi kada ki jawo ma kanki Muna zqki shiga matsalar da fita daga cikin shi sai wani ikon Allah nidai ba zaki taɓa samun wani bayani daga gareni a kan wannan sirrin ba” kitt ta katse wayan bata bata daman sake mata wani tambayar ba,
Shiru Muna tayi tana tunani tare da jinjina girman wannan sirrin da har ƴar uwarta na jini bata so ta sani, dole ne kafin lokaci ya ƙure mata ta san koma menene, dan haka tayi saurin miƙewa ta shirya da nufin zuwa gidan su Sulaiman ta zauna a can dan tana da tabbacin a can wannan sirrin yake kuma ta ɗau aniyar nimo shi duk inda ya shiga ta fito dashi indai shine abinda zai saka itama a tura ta karatu ibadan,2
**********
Zaune nake na saka hannaye na biyu na tallafo fuska na baki buɗe kaman yawu zai ɗiga na saka zango da ali nuhu a gaba ina ƙare musu kallo a TV kaman ba ni bace na gama kukan faɗuwar jarabawa ɗazu ina faɗin IS ME NO TV ba!3
Awa na biyu curr ina zaune ina kallon film ko abinci na kasa tashi naje naci, sallan magriba ma a daddafe nayi don tun bayan da muka gama girka dinner aka kawo wutan nepa,
Aunty Yusrah tayi kiran duniyar nan nazo muyi karatu kaman yanda tace amman kaman wanda na na zauna a kan kunne na banma ji lokacin da ta kira nin ba, har ta gaji da zaman jira ta tashi ta ci gaba da sabgogin ta don bata son takura ni, gashi yau tunda rana ta kusan faɗuwa take jin ciwon jiki musamman bayanta,
Ban tashi daga gaban tv ba har saida Khamis ya shigo gidan gudun kar a sake min zancen komawa gidan su yarima,
1:30am
Naƙuda ya tashi ma aunty Yusrah…….🤦🏻♀️
_ban tsara littafi na a matsayin na kudi ba kuma bani da niyyar maida shi na kuɗi amman Idan har ban samu comments da suka kai 150 a duk groups ɗin da nake Sharing ba in Allah ya yarda daga yanzu na daina turowa a WhatsApp mai son karantawa saidai yaje wattpad_
#vote
#share
#comment.
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
BY UMMU NAJMA
DEDICATED TO, MAI DAMBU
And AISHA ALTO
_Addu’an neman tsari daga maƙiya_
اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ الأَحْزَابَ، اللَّهُمَّ اهْزِ مْهُمْ وَزَلْزِلْهُمْ
(Allaahumma munzilal-kitaabi, saree’al-hisaabi, ihzimil-‘ahzaaba, Allaahumma ihzimhum wa zalzilhum.)
Allah, Revealer of the Book, Swift to account, defeat the groupsO Allah, defeat them and shake them.+
09🧝🏻♀️
Sosai hankalin mu ya tashi ganin yanda take murƙusuwa tana faman yarfa hannuwa cikin azaba, wani lokaci tayi kuka idan ya ɗan sake ta kuma ta kama salati tana tallafe bayan ta, amman abu kaman ƙarawa ake yi duk bayan minti biyu sai ta daɗa shiga wani hali,
Kasancewar bata tare da Khamis lokacin aihuwar ta na farko yasa sai abun yazo masa a sabo duk ya rikirkice ya rasa wani abu ɗaya da zaiyi mata ma yana zaune riƙe da ita sai sannu yake yake faman jero mata yana mata fifita a maimakon ya sunkume ta mu tafi asibiti,
Nice ma mai azancin haɗa kayan da zamu tafi dashi wanda mama tamin bayanin za’a buƙace su don haka da an tashi tafiya da ita asibiti na tattara mu tafi dashi, na zuba kayan a ƴar ƙaramar jaka bayan ta gama galabaita Khamis ya riƙo ta ya saka ta a mota nima na shiga muka wuce asibiti,
Wuraren ƙarfe 4 ta haihu, muna zaune jingum_jingum muna jiran sakamako don ta ɗan dauki lokaci tana naƙudan hankalin mu gaba ɗaya ya tafi jikin ɗakin aihuwan muna jiran muji da wani labari za’a iske mu, doctor na fitowa ya Usman da Khamis suka ƙarasa wurin shi suna tambayar yanda aunty Yusrah ta samu kanta, da murmushi a fuskar shi ya miƙa ma Khamis hannu suka gaisa sannan ya sanar dasu ta sauƙa lafiya ta aifi ɗa namiji yanzu an tura ta ɗakin aihuwa,
(Nace ko Khamis bai lura likita namiji bane ya karɓi aihuwan?) A maimakon yayi rikici ko wani tashin hankali sai niman wuri yayi ya zauna yana hamdala ma ubangiji farin cikin dake shimfiɗe a saman fuskar shi ya gaza ɓoyuwa,
Tashi yayi a nutse ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga tare da rufowa hakan na nuna mana bayi son kowa yabi bayan shi kenan shiyasa muma muka yi zaman mu a waje amman a ƙage nake su gama abinda zasuyi na shiga na gano baby ko shima ya fito irin ‘kuut’ (cute) ɗinnan da ake faɗa,
Dago lumsassun idanun ta tayi wanda suke cike da gajiya ta zuba mishi da ƙaramin murmushi a saman lips ɗin ta, ga babyn da aka shirya aka kwantar mata dashi a saman ƙirjin ta yana jin ɗumin jikin ta,
Daidai saman goshin ta yaje ya sake mata peck tare da lumshe idanuwan sa yana jin wani sanyi da daɗi yana ziyartan zuciyar sa, dariyan Yusrah ne ya sanya shi ɗago kanshi ya zuba mata ido cike da so da ƙauna, he wonders what makes her so happy a cikin yanayin da take,
Cikin kasashshiyar murya tace “abinda naso kenan tun farko, amman Allah bai kaɗɗara da rabo na bane a wancan lokacin, lallai shi mumini kada ya cire tsammani da rahaman ubangiji don bai san a lokacin da zai zo mishi ba, na kusan cire rai da ganin irin wannan ranar Khamis,
STORY CONTINUES BELOW

Na cire rai da farin ciki da jin daɗin rayuwar duniya lokacin da na rasa ka, amman ganin Jannat a gaba na da kuma amincewa da ƙaddara ta a yanda tazo min na yarda cewa Allah yana da ikon canza min ita a lokacin da yaso gashi abubuwa sun zamo kaman ba’ayi ba”
Baice komai ba don baiga alaman ta gama fitar da kalaman bakin ta ba, ya zura yatsun hannun shi a tsakanin nata sannan ya jawo su daidai bakin sa ya sumbata,
Hawaye ne zurr suka fara sauƙa daga idanun ta daga yanda take kwance amman wa’innan hawayen tana zubar dasu ne saboda farin ciki, ji take yi kaman babu wanda ya kaita Sa’a a yanzu because her family is complete kuma tana cikin farin ciki,
Saida ta sauƙe numfashi sannan ta jawo hannun shi dake riƙe cikin nata hakan yasa dole ya ranƙwafo ya daura haɓar shi saman kanta tana jin bugun zuciyar shi, sake sauƙe numfashi tayi a karo na biyo sannan cikin wani irin murya mai ciwo tace
“Banga wannan farin cikin ba lokacin da na aifi Jannat, all i see is tears, kuka suke min suna ambata min kalmar tausayi tare da ƴata, raina ya ɓaci sosai nayi kuka don sun maida min ƴa kamar shegiya, kowa kallon takaici yake mata a matsayin ƴar mutum mara hankali wamda bai iya kula da kanshi ba ballantana ya kula da wasu, saidai tun daga lokacin na saka wa raina wata rana zasu maye gurbin kallon tausayi da ƙasƙancin da suka min da kallon farin ciki suna min murnan kasancewa cikin masu nasara a rayuwa, ba zan iya rayuwa babu kai ba Abban Jannat”
Yatsun ta dake cikin nashi ya fara murzawa a hankali cikin sigar lallashi yana shafa bayan babyn dake kwance a ƙirjin ta, a nutse ya leƙa fuskar shi sannan ya ɗago idanun shi ya zuba mata duk tayi sukuku ga hamwayen da har yanzu basu bar sintiri a fuskar ta ba,
“Allah yayi miki albarka, Allah ya sanya ki cikin aljannah, ke alkhairi ce cikin rayuwata Yusrah, bansan ta yaya zanyi miki bayani ba amman ban taɓa jin abinda nake ji a yanzu ba a tsawon rayuwata, ba don keba maybe ba zan taɓa samun farin ciki ba har abada, ina yi miki so mai zafi ina tsoron wata rana kada ya illata ni”
“Ba zan taɓa bari wani abu ya cutar da kai ba, koda kuwa soyayya ta ce, zan zama jaruman da zata yaƙi duk wani cutarwa da zai sami familyn ta, i will love and protect you with my life”
“uhm_uhm, not with yours but with mine tunda nine shugaba ni aka sani da sadaukarwa ba masoya na va, i love You so much”
Murmushi kawai tayi tana binsu da kallon sha’awa lokacin da ya dauki babyn yana mishi addu’a, kusan bayan 15 minutes kafin ya buɗe ƙofar muka shigo lokacin an fara kiran assalatu na farko,
Hehehe, zanga kuut baby, wani daɗi nake ji a raina na ƙarasa wurin abban shi na karɓe shi baki na har kunne don akwai ni da son yara, Jannat ma dukda ta girma amman ta shiga hannu na tana shan jagwalgwale yaron Aunty Nasreen kuwa sai yayi kuka nake rabuwa da shi, don duk lokacin da aka bani yaro ko yarinya na riƙe to a matsayin mai jin yunwa yake, duk abinda na samu naci haka zan dirka musu kuma dole suci don bani son zama da yunwa,
dariyan jin daɗi nayi na ƙarasa wurin Yusrah da babyn a hannu na nace
“Aunty Yusrah you baby is kuut bilshiful” (your baby is cute and beautiful)
Wani matsiyacin dariya Yusrah tayi tana kama cikin ta da yake ɗan mata ciwo sama_sama tace “Allah ko saudat”
“Wallahi is kuuutttt well well”
Gaba ɗaya ɗakin muka saka mata dariya, sai kuma ta ɓata fuska bata ji daɗin hakan ba, ganin sauyawar yanayin ta lokaci ɗaya yasa dukan mu muka bar dariyan a hankali ya Usman da Khamis suke janta da hira saboda ta sake kaman lokacin farko don duk cikin mu babu mai son ganin ɓacin ran Saudat, muna jinta kaman jinin mu,
Saida aka kira sallan asuba tukunna suka fita bayan ta gama waya da Mama ta karbi yaron hannu na don bani daman zuwa nima nayi nawa sallan, basu dawo ba har gari ya fara haske,
STORY CONTINUES BELOW

Da sallama ta buɗe ƙofar tana sanɗa kaman bata so a ganta fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙaraso kusa da gadon aunty Yusrah ta ɗan zunguri kan babyn a hankali, saboda ya fara gyangyaɗi yana jin an taɓa shi ya fara kuka nan Aisha ta tafa haɗe da saka shewa,
“Yayyyyyy he is alive, gantalin uwar shi bai kashe shi ba”
Cikin mutuwar jiki Yusrah ta kai mata duka tana hararar ta,
“Matar nan kin saka min ido wallahi ban san mai na tsare miki ba, waye ma ya faɗa miki na aihu ne da kika bugo sammako da sanyin safiya kika zo”
“Kaman kinsan inaso na sanar dake na since ƙawance na dake, daga yanzu Nasreen ce besty na, tun kafin a kira sallah ta kira ta faɗa min kin aihu, muga babyn” ta faɗa tana ɗaga shi daga jiki na,
“Kaii tabarakallah masha Allah!! Besty ki kalli hancin yaron nan kaman pencil?”
Farr tayi da ido tace “kema kinsan a wurin wa ya gado dan ta wannan fannin muma ba baya ba”
“Eh lallai yayi kyakkyawan gado amman Allah yasa bai haɗo da halin ba don in dai haka ta faru a kwai ƙura” daga haka muka ci gaba da hira har su ya Usman suka shigo da ya safwan tare da Khamis, Nasreen kuma tana ɗauke da nata yaron da mama da baba harda sauran yayu na suna biye dasu,
Saida baba ya karɓe shi yayi mishi addu’a sosai kafin aka miƙa shi ma Khamis ya tauna masa dabino ya saka mishi a bakin shi, aka mishi addu’a a cikin ruwan zam_zam aka bashi sannan yayi mishi huɗuba,
My heart is dancing with joy, ji nake yi kaman na tashi nayi ta tiƙa rawa saboda murna duk wa’innan abubuwan ni da kaina nayi ma Jannat su, nayi mata sune ina kuka ina zubda hawaye sanin cewa mahaifinta yana raye amman rashin isasshen lafiyan ƙwaƙwalwa ya hana mu kasancewa tare, amman yanzu komai ya dawo kaman ba’ayi ba, alhamdulillah,
Kaman yanda Khamis yayi alƙawari a baya ya saka ma yaron mu sunan mahaifi na Adam za’a dinga kiran shi abulkhairi, tun a lokacin ya sanar mana da sunan da ya saka bai bari sai ranar suna kaman yanda wasu suke yi ba (hakan ba laifi bane)
mahaifi na yaji daɗi sosai, basu daɗe ba yace su koma gida don lokaci ɗaya mun cika ɗakin kaman gidan biki ga ƴan uwan khamis ma sun fara isowa, duk an cika ana ta hidindimu sai wurin ƙarfe goma aka sallame mu na taya aunty Aisha tattara sauran kayayyakin da muka je dashi muka shiga mota muka tafi,
Tunda muka isa gida fa ba zama, muyi wannan muhi wannan har akayi sallan azahar gidan na cike saima daɗa ƙaruwa akeyi gashi har lokacin ko wanka banyi ba, yau ko nutsuwar kallon TV ma bani dashi,
4:30pm
Muka shigo da ƙaton bakko tare da da ƙanwar Khamis muka shiga dashi ɗakin aunty Yusrah, tana zaune a saman gado tayi wankan ta irin na masu jego tasha jewelries dukda babu kwalliya a fuskar ta amman tayi fresh ga ɗinkin jikinta ya zauna daram saboda huruwan ciki da tayi don kayan sun ɗanyi mata ruwa a da,
Aiiye abulkhairi tayi ɗan nesa da ita sannan ta saka muka ɗaura mata kayan a kan gadon tana dubawa,
“Auta kiga ikon Allah, tun jiya nake jiran a kawo kayan nan na kaima masu shi abun su amman sai yau suka iso, gashi babu halin kai musu” ta faɗa tana kallon Nasreen ” dan Allah ki ɗan miƙa gidan su Sulaiman boss mana ogan su Abban Jannat, gidan da muka je dake ranan a MAFIAS QUATERS”
“Gaskiya aunty Yusrah yamma yayi sosai ba zaki bari a kai musu gobe ba?”
“Wallahi baki ji yanda suka matsa min bane auta, kuma kuɗi fa zan samu wannan set na farko ne zan kai musu su fara samun ɗinki kinsan su zannuwa sai latest designs suke sakawa gasu sakalai basu iya shiga kasuwa, idan yakai gobe zan samu faɗuwa sosai don ƙaramin aiki ne su nemi wasu su kawo musu kayan”
Aisha bata isa ma tace zata kai mata ba don ta gama shiryawa ta shirya ƴarta jiran mijinta kawai takeyi yazo su tafi yau ko breakfast batayi ba ta fito don haka dole taje ta tanadar mishi abinda zai ci da daddare,
“To Shikkenan za muje da ya Safwan na miƙa musu sai mu wuce gida ina dai babu abinda za’a karɓo miki”
“A’a gaskiya, zasu bada kudin kayan a kawo min, ku tafi da Saudat sai ta karɓa ki saka ta a keke napep ta kawo min”
“Toh Shikkenan tayi sauri ta shirya sai mu tafi dan ya kusan ƙarasowa”
Saka ni nayi wanka aunty Yusrah tayi, na shirya cikin atamfa orange color da torches ɗin ash na yafa medium sized veil shima ash sannan ta bani babban jaka muka zuba kayan muka tafi,
**********
Ba yau bane zuwa na na farko, amman na sake faɗawa cikin kogin mamaki da al’ajabi, ina jefa tambayoyi ma zuciyata, wannan gidan dai girman shi yafi ƙarfin ginin mutum kuma naga irin su bila adadin a garin nan dukda ban taɓa shiga cikin kowanne ba bayan wannan, shin da elefas (elephants) ne suke gini? Tunda ance sune suka fi ko wani dabba girma hala sune suke dauko musu kayan ginin,3
I was trying hard to conrol myself kada na kwafsa amman kaman ranar farko da na fara zuwa yauma idanuna sun kasa ɗauke wa daga kan daƙararrun motocin dake jere a parking lot, ya rabbi duk ranar da na shiga cikin wannan motar ai sai nayi Mad,
Ba don hannu na dake cikin na aunty Nasreen ba zan iya bata saboda kallo, ko ina a cikin gidan is bilshiful, inji aunty Yusrah takan ce fasfet (perfect),
Maganar da naji ta gefe na shi ya jawo hankali na zuwa gare su, tana biye dashi a baya cikin long sleeve shirt fara tass da wando palazo kanta sanye da irin hulinan zamani ga fuskar ta babu kwalliya amman ta haɗu,
Binshi take yi cikin sassarfa ta shagwabe fuska tana mishi magiya amman bayi da lokacin sauraron ta, yana tafiya cikin sauri yayin da ya ɗago ido sai a cikin nawa karaf don already su nake kallo,
Saurin kawar da kaina nayi don ba ƙaramin kwanjini yayi mun ba zuciyata ta tsananta bugawa haka kawai nayi tsoron shi ya ɗarsu a raina, nayi nadaman kallon cikin idon shi da nayi,
Sulaiman bai san lokacin da ya karbi takarda da biron hannun Fa’iza ba yayi signing ba tare da ya kalli takardan ba shiyasa ma ba a wurin da aka tanadar ya saka nannun ba amman tunda ya saka buƙatar Fa’iza ya biya, da murna ta koma cikin gidan tana faman mishi godiya har taso bangaje mu,1
Shi kuwa ya tsaya a wurin kaman gunki ya rasa tantama yake yi ko mamaki, cikin zuciyan shi yana maimaita
” Ita ne!! Ita ne yarinyar da na haɗu da ita cikin gidana almost a year ago…………….🤦🏻♀️
To fah💃🏼💃🏼, anzo wurin
Tun yanzu zamu raba team ɗinne ko sai tafiya ta fara nisa?😅1
#vote
#Share
#comment
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Masu iya magana sunce “don’t judge a book by it’s cover!” Ta yuyu ta sigar da ka fahimci abu bashi bane zahirin shi*💡+
10🧝🏻♀️
Amman shekara ɗaya kawai kalli yanda ta ƙara girma tayi kyau? Naso na nimi wurin da take koda sau ɗaya ne na sake kallon ta amman ban san ta ina zan fara ba saboda bansan daga ina tazo ba, yau dai ba zan bari wannan daman ya wuce ni ba dole na san daga wani gida take kuma ita ƴar waye,
Duk wannan saƙe_saƙe da yake yi cikin zuciyan shi yana tsaye ne wuri guda bai motsa ba, har ya juya zai koma cikin gida wani mutum ya ƙaraso gaban shi tare da durƙusawa kaɗan ya miƙa mishi wayan shi da ya manta cikin mota lokacin da yazo,
lokaci ɗaya annurin fudkar shi ta ɓace batt ya haɗe fuska ya fito a asalin babban yaya ɗinshi, sannan ya ƙara wayan a kunne tare da yin sallama, “i will be there in 10 minutes” kawai ya faɗa ya juya ya kama hanyar tafiya waje ranshi ba daɗi, amman idan yayi sauri maybe zai dawo ya same ta, ya faɗa tare da shiga mota suka bar haraban gidan,
Hmmm eviritim (everything) a gidan nan is fasfet (perfect), hankali na ya tafi kallon fasfet ban san har munzo jikin main door na part ɗin ba, hankalin aunty Nasreen bayi wuri na ita ta saka kanta a gaba a tunanin ta ina abin da ya kamata ne sai jina nayi dimm, na bugu da jikin mutum,1
for a moment na tsaya ina tunanin anya wannan mace ce? A maimakon na kauce a hanyar ko na bada haƙuri amman ina tsaye ina tunani saida wani dogon tsakin da ya ja ya dawo dani cikin hayyaci na na ɗaga idanuna na zuba mishi,
Ya ƙanƙance idanu cikin masifa ga jiki na manne da nashi dan har yanzu ban tabbatar ko karo mukayi ba ballantana na san me zanyi gaba,
“Sh***t, who is this stupid girl? Ya tambaya a tsawace, ni dai banga kowa a wurin ba, bansan da wa yake magana ba, amman duk inda aka ambaci sitifid (stupid) na san zagi ne, wato zagi na yayi don kawai na bangaje shi ba tare da sani na ba? Dan cin mutunci ma zagin da turanci??4
Saurin matsawa nayi daga jikin shi, yayi saurin wucewa tare da sake jan wani tsakin sannan ya juya ya tafi har ya shiga part ɗin dake gefen wanda zamu shiga ina kallon bayan shi, wannan wani irin zafin rai ne? Na tambayi kaina, shi wannan wani irin mutum ne mai tsanani sai kace wani mala’ika?
“Haba Saudat! Ina hankalin ki yake ne zaki jawo mana magana? Yanzu da ya dake ki fa yanda ranshi yake a bacen nan kuma baki iya bada haƙuri ba?”
“Tabɗijam, sitifid fa yace mun babban zagin da yafi ko wanne a duniya kuma kice na bashi haƙuri? Wallahi da saidai ya dake ni amman duk wanda yace min sitifid ba zan bashi haƙuri ba”
Girgiza kai kawai tayi muka sake kinkiman jakan kayan mu mukayi ciki dashi, babu kowa a parlorn bayan su biyu, sun lunƙuma cikin kujera ɗaya da laptop a cinyar ta tana nuna ma mai waya a hannu wani abu,
Sallamar da mukayi tare da niman wurin zama ne ya jawo hankalin ruma dake riƙe da laptop tana zaune kusa da zaytoon, da fara’a a fuskar su suka tarbe mu muka gaisa sannan Ruma ta nufi ɗakin Hajiya da niyan kira mana ita, Zaytoon kuma ta saka maids kawo mana abun sha,
STORY CONTINUES BELOW

Ina zaune ne a wurin amman hankali na ya tafi yawo kallo kawai nake zubawa tare da saƙe_saƙe a cikin zuciya ta, saida Hajiya ta kira sunana kafin nayi firgit ita kallon ta idanuna a waje kaman anyi min ƙarya,
Murmushi tayi tace “Saudat ranan kinyi min rowan kwana yanzu rowan magana kike mun?”
Murmushi kawai nayi na gaidata ina mamakin yanda tayi saurin gane ta bayan haɗuwar mu ta farko ma a tsatsaye mukayi shi muka tafi kusan shekara ɗaya da ya wuce kenan ma,
“Lafiya ƙlau, kinga har sunan ki saida auntyn naki ta tuna min da ƙyar ma na gane ki, fatan yau zama mana zakiyi ba tafiya ba”
Dariya naji inajin daɗin yanda matan take da kirki sosai, ranar ma da nazo haka ta dinga jana a jiki,
“Kaya muka kawo aunty Yusrah ne ta aiko mu anjima kaɗan zamu tafi”
“A’a ban yarda ba gaskiya, yau tunda kika zo kwana zaki mun, ga ƙawa nan ma nayi miki” ta faɗa tana nuna Ruma,
Ɗaga ido nayi na kalli haɗaɗɗjyar yarinyar da aka kira da ƙawa na, hada idon da zamuyi ta sakar mun kyakkyawar murmushin da yasa beauty point ɗinta suka lotsa, ta ajiye system ɗinta a saman centre table tazo gefe na ta zauna tare da saka hannun ta cikin nawa tana dariya tace
“Aunty Zaytoon to Kinga yarinyar da tafi ya Zayyad kyau kullum sai ki saka shi ya dinga jin kai ma mutane, kira shi yazo ya ganta”
“Ai yanzun nan ya fita inaga bayi jin daɗi ne, har kuwa yana cewa zai tsaya ya taya ni zaɓe tunda ya fini sanin kan gayu da abu mai kyau amman sai fitar shi kawai na gani bai faɗa min dalili ba”
Ohhkkk! Wato Zayyad shine sitifid ɗinnan da ya fita? Tun da ya zage ni nima daga yanzu zagin shi zan dinga yi kuma daga yanzu shima sitifid ne, kuma insha Allah duk randa na sake haɗuwa dashi koda zai dake ni sai nace mishi I am mad, nasan shima zagin zai mishi zafi,
Ina zaune ina faman tsilli tsilli da ido suka cika parlorn damm suna zaban kaya, kusan zannuwa 30 amman a cikin su akwai wa’inda basu samu ba da na ƙirga yawan su basu wuce 8 ba, a lokacin ya Safwan ya fara rangaɗa ma Nasreen kira ta fito su tafi,
“To gashi kuma muna sabon list dan kayan sunyi kyau sosai kinga yaran suna son ire_iren su, ba zaki ɗan jira mu gama ba sai ki tafi mata dashi?”
Murmushi Nasreen tayi tare da miƙewa, tana tashi nima tsugul na miƙe,
“Ai ni ba gidan ta zan koma ba, zan wuce gida ne Saudat ne zata shiga shiga abun hawa ta kai mata, tace ma a faɗa muku ta sauƙa yau da asuba an samu ɗa namiji”
“Alhamdulillah! Masha Allah!! Allah ya raya shi da imani amman bai kamata yarinya ƙarama kamar wannan a saka ta a public transport ba idan ta ɓata fa?”
Duba jiki na fara yi kaman mai niman wani abu, ina son ganin abinda wannan hajiyar ta gani a jiki na ne take kira na yarinya, ai inaga ko ƙauyen wuroɓokki aka saka ni a mota na tafi ba zan ɓata ba ballantana nan da wani unguwa kaɗai,3
“Amman kada ki damu ki tafi abinki kawai zan saka a maida ita har gida”
Godiya tayi mata ta tafi ta barni, and i was like, “how she do is me?” (How could she do this to me) abinda naji aunty Yusrah tana faɗa wani lokaci idan aka yi mata ba daidai ba,
Ina kallo ba don naso ba aunty Nasreen ta tafi na zauna ina jiran su gama, ina jin irin mugun kallon da take watsa min a jiki na, bansan me yasa tun da na shigo take harara ta ba,
ni banma taɓa ganin ta ba don last zuwa na gidan nan tare da aunty Yusrah duk ƴammatan nan basu nan, gidan empty yake babu kowa bayan hajiya part ɗin su stipid kanma a rufe yake an faɗa mana cewa gaba ɗayan su sun tafi Umrah,
To a ina ta taɓa gani na har wani mummunan abu ya taɓa shiga tsakani na da ita da take bina da kallon banza? Saidai ban sani ba ashe baƙin hali da kallon banza a jinin Nana yake indai ta washe ka a kallon farko to taka ta ƙare a wurin ta,2
Haka suka gama abinda zasuyi ina zaune kallon banzan nana ya hana ni sukuni na rakuɓe a wuri ɗaya ina kallon ta ta ƙasan ido, duk sona da ciye_ciye amman ina kallon kayan daɗi haka na barsu,
duk wayo da dabaran da hajiya tayi min don na yarda na kwana firr naƙi, har kiran aunty Yusrah tayi ta faɗa mata cewa sai gobe zan dawo tace babu matsala ta yarda amman nikam nace ban jiba ban gani ba ai babu kowa a wurin ta wanda zai dinga mata aikace_aikace,
Daga ƙarshe dai ba don taso ba ta ɗaga driver ya maida ni gida, har mota Ruma da zaytoon suka min rakiya na shiga, yayin da numfashi na ya tsaya cak wani mahaukacin sanyi yana ratsa ni har ta ƙarƙashin ƙafafuwa na,
Saurin naɗe ƙafafuwa na nayi, nayi zaman tahiya amman duk da haka sanyi nake ji sosai,
lokacin da aka isa gida jina nake yi kaman na zamo ƙanƙara amman ana sauƙe ni na fara fankama ganin hankalin magulmatan unguwan ya dawo kan motar suna son gani waye kuma zai fito daga motar, har na shuge cikin gida ina jin idanuwan su a kaina,1
******
Motar mu na fita ya ƙaraso wurin kaman zaiyi magana a dakatar damu kuma sai ya fasa, to meye ma dalilin bada haƙuri tunda bashi yayi min laifi ba?
Wataƙil ma hala abun da ya faɗa min bai ɓata min rai ba amman duk da haka bai kamata ya furta min wa’innan kalmomin ba, koda banji haushi ba zaiyi ta jin nauyin su a zuciyan sa,
Juyawa yayi cike da damuwa yaga su zaytoon sun tsaya suna ƙare masa kallo har yanzu basu tafi ba,
Ƙaƙalo murmushi yayi yace “yaya ne sisters? Kuna buƙatar wani abu ne?”
Ɓata fuska zaytoon tayi cikin wasa tace “kai zamu tambaya ko kana buƙatar wani abu ne bayan ka tafi baka zaɓa min kayan ba har an gama kwashewa yanzu ko ɗaya bani dashi,
Dariya yayi yana jan kumatun ta yace “ayyah ai bansan cewa kina jiran zaɓin haɗaɗɗe bane da na bar duk abinda nake yi nazo na zaɓa miki, amman yaushe zasu kawo wasu?”
“Ban sani ba amman kafin a fara azumi zasu kawo kaga gobe ko jibi kenan”
Sauƙe ajiyan zuciya yayi tare da faɗin Allah ya kaimu, a ranshi yana jin daɗin zai saku daman bani haƙuri,
*********
1:24am
Kunna bedside lamp tayi tana leƙa fuskar shi har yanzu murmushi yake yi ta rasa na menene ɗaya,
“Dadyn Arif” ta kira sunan shi a hankali,
Juyowa yayi ya zuba mata idanuwa ba kamar kullum ba yau da faffaɗa kuma ƙayataccen murmushi a saman fuskar shi,
“me ya same ka ne ka kasa yin bacci kuma wannan murmushin….. Ko dai riba ya ninku ne??”1
Ƙarakin tsaki yaja amman murmushin bai bar saman fuskar shi ba yace, kina da matsala Sadiya, waye ya faɗa miki kuɗi ko yaushe yake kawo farin ciki? Wani abu na musamman yau na gani wanda zuciyata ya daɗe yana tsumayen sa………..🤦🏻♀️
2
_Masu cewa Sulaiman ya kama girman sa ance na faɗa muku da babban murya BA’A TSUFA MA SOYAYYA😅😅_
2
#vote
#share
#comment
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
11🧝🏻♀️
Na daɗe ina mafarkin sake sake ganin wannan abun sai yau Allah ya gwada min shi a zahiri kuma ina da yaƙinin wannan karon zan mallake shi insha Allah,
Shiruu Sadiya tayi tana binshi da kallo haka kawai ta sami kalaman shi da ɗaure mata kai, don ta san Sulaiman is straight forward amman yau yana mata magana mai harshen damo lallai wannan al’amarin babba ne,+
“Whaaatt?” Ya tambaye ta yana fitar da dariya mai sauti ganin yanda ta zurfafa kanta cikin tunani,
“Kinga ni bani son irin ɗaukan ɗumin nan naki kina shiga damuwa ba gaira ba dalili, ki kwantar da hankalinki ki koma kiyi barci wannan al’amarin bai shafe ki ba, Allah ya tashe mu lafiya” ya kashe lamp ɗin tare da juyar da ita ya lafe a jikin ta yana shafa bayan ta a hankali,1
Wannan sabon yanayi na Sulaiman ya ɗaure mata kai matuƙa, tana dai fatan ba wani abu yake shiryawa ba don haka kawai taji ranta bai aminta da shi ba,1
*****
“Mtssww, ni zai kalla ya kira ni sitifid, wallahi duk ranar da na ganshi sai na rama wannan zagin, dama uwa na ko uba na ya zaga ba zan damu ba tunda wanda ya zagi iyayen wani iyayen shi ya zaga, amman tunda yace min sitifid babban zagin da yafi ko wanne a duniya to sai na rama”3
Ai kuwa ina kai aya abulkhairi ya callara ihu bayan ɗumbin kashedin da aunty Yusrah tayi mun na nabar ƙananun maganar da tun bayan magriba nake faman yi kada na tada mata yaro,
Tashi tayi ta zauna ta kunna Torchlight tare da kaimun duka a cinya daman already idanu na a buɗe suke tsugul na miƙe ina sosa wurin
“Muguwa! kina gani awa na biyu da yaron nan a hannu ina jijjiga shi kafin da ƙyar na samu yayi barci saboda nima na rintsa amman ko minti 30 baiyi ba kin daga min shi”
Bance da ita komai ba don nasan nayi laifi, na zauna ina binta da ido ta ɗauki yaron ta fara feeding ɗinshi sannan taci gaba da cewa,
“Wai a dole muna kwana ɗaki ɗaya dan ki taimaka min da wasu abubuwa amman rana ta farko kin fara azabtar dani, haba da wanne ɗaya zanji?”
Turo baki nayi ina ƙunƙuni, shiyasa ni banso kwanan ɗaki ɗaya tare da ita ba gwanda na kwana ni ɗaya yafi mun daɗi na faɗi abinda raina yake so a cikin barci ko a farke, amman ana niman takura min, kuma ma ai laifin Sitifid ɗin nan ne, yau nayi niyyan bazan ƙullaci kowa ba saboda kada nayi surutu cikin barci amman duk ya shiga ya ɓata min zuciya,
“Ke!!” Ta faɗa tare da taɓa ni, nayi saurin juyowa ina kallon ta tare da zare idanu na saboda yanda na ruɗa kaina bansan lokacin da nayi hakan ba,
“Boɗɗi lafiyan ki kuwa? Anya ke kaɗai ce? Maganganun me kike yi ne ke kuma ana miki magana hankalin ki yana wurin?”
“Babu komai aunty Yusrah me kika ce?”
Sauƙe numfashi tayi tace “ki zubo min ruwan zafi daga plask nasha”
STORY CONTINUES BELOW

**********
Rufe ƙofar tayi ta bayan ta a hankali sannan ta zuba a jikin shi ta saka hannun ta da kullum bayi rabuwa da casbi ta zagaye shi tana sakin marayan kuka,
“Again!! An sake samun matsala Alhaji, innalillahi wa inna ilaihirraji’un”
“Shhh! Ya furta yana bubbuga bayan ta a hankali
“Kuka ba naki bane Madina, ba yau muka fara ganin matsalar Zayyad ba kuma bamu san yaushe ne zamu ga ƙarshen ta ba, dan Allah ki kowa ma kanki jarumta kuma ki zamo mai tawakkali insha Allah sauƙi na nan zuwa”
Tashi tayi daga jikin shi tana share hawayen fuskar ta a hankali take jan numfashi don ta sama ma kanta nutsuwa, yana tsaye ya zuba mata idanu cike da tausayi wannan damuwa na matsar Zayyad shekaru 25 kenan tana cikin sa,
Murya can ƙasa tace “dan Allah kada a faɗa ma Sulaiman maganar nan saboda na san zai ɗaga hankalin shi ne kuma hakan ba canza komai zaiyi ba”
Gyaɗa kai yayi tare da faɗin “insha Allah ba zai sani ba, yanzu muje ki kwanta kinga dare ya raba”
Gaba ta shiga yana binta a baya suka bar wurin
*****
28 /sha’aban/1442
11:07am
Tun asuba muke ta jigila don yadikon Khamis da aka kawo matsayin wanda zata yi ma Yusrah jego na wata 1 bata san zama ba, babban damuwa na ma ba wai zama ko hutawa da bamu yi bane yau gaba ɗaya ban kalli TV ba, sai nake jin kaina kamar mara lafiya gashi jiya sunyi tallen wani sabon film jiya, da garin wucewa naga sun saka tallen shi don jiyan ma bata barni nayi kallon yafi na 20 minutes ba gaba ɗaya ta shiga rayuwata,
“Boɗɗo”
Juyawa nayi ban tanka ta ba don fushi nake yi da ita, yanzu haka ma zaune nake ta haɗa ni da tulin alayyaho ta bani wuƙa wai nayi mata yankan burge mai gida irin siraran nan zata yi miyan taushe aci da rana,
Murmushi tayi don sanin ban cika son hayaniya ba yanzu ma hala ta takura ni ne, take ji a ranta amman dan niman ta ƙular dani ta jawo ni gaban ta dani da robar alayyahon,
Zungurin goshi na tayi tace “ke boɗɗo fillo, baki ji ana miki magana ne da ba zaki amsa ba?”
Nan hawayen da nake maƙakewa na rashin kallon su zango da banyi ba ya fara bin kumatu na, a zuciye na fisge jiki na daga riƙon ta cikin muryan kuka nace,
“Ni sunana ba boɗɗo bane, kuma kada ki sake cemin fillo babu abinda ya haɗa ni da fulani”
Riƙe baki matan tayi tana kallon abin mamaki ganin hawaye shar_shar a fuska na ta bata san na meye ba,
“Ikon Allah ƴar nan lafiyan ki kuwa? Me aka miki kike kuka? Daga na kira ki fillo sai ki fara min kuka ko ke ba bafulatana bane?”
“Ni ba bafulatana bace, ni bahaushiya ce ni ƴar garin nan ne babu abinda ya haɗa ni da garin wa’incan fukanin suci kansu”
Tafa hannuwa tayi tana dariya “heee, lallai zamani, don kin baro su shine zaki yi musu butulci ki raba kanki dasu? Ai shi tuwo duk daɗin shi ba’a canza mishi suna ko ina zaki je a duniyar nan sune asalin ki, kuma da kike cewa ke ƴar garin nan ne ai muma kusan dukkan mu hausa fulani ne kawai rashin riƙe al’ada ne ya kawo haka,
amman dai faɗa min meye ya saka ki kuka? Ko aikin ne baki son taya ni?”
Girgiza kai nayi ina daɗa matso kwalla don ta barni naje nayi kallo, nace, “daman..d..daman bani son a ɗauke wuta ne ina..tna son kallon wani abu..a tv”
“Shine kike kuka? Ta tambaya cike da mamaki, gyada mata kai kawai nayi tace
“Tashi kije” ai kuwa da gudu na miƙe na nufi parlor murmushi yana suɓuce min, nasan yanzu sunyi rabi amman idan na nutsu zan fahimci abinda ake yi,1
*****
“Nikam yanzu al’amarin Saudat yafi ƙarfi na abban Jannat har baba ta ƙare tayi magana, awan ta kusan uku a jikin tv tana kallo saida na kora ta kafin taje tayi sallan azahar, duk ayyukan da ya kamata tayi yau baba ne tayi su….”
Gani tayi kaman maganar ta kawai take yi Khamis kanma bayi sauraron ta, ya saka yaron shi a gaba yana faman mishi wasa dukda ba fahimtan komai yake ba, yana son yin barci sai lumshe idanu yake yi amman ƙaran abinda Khamis yake kaɗawa ya hana shi sukuni,
“Abban Jannat”
“Na’am ummin Jannat” ya amsa ba tare da ya ɗago ko ya bar abinda yake yi ba,
“Kaji abinda nake faɗa kuwa?”
Sai a sannan ya ɗago yana murmushi yace “sorry baby, me kike cewa?”
“Ayyah nafi 5 minutes ina maka magana tun na ɗazu ma nasan ba ji kayi ba, cewa nayi maganar Saudat har yanzu tana kan kallon ta na babu ji babu gani ɗin…”
“Dan Allah kada ki ɗaga min hankalin ki a kan maganar da kinsan yinshi aikin wofi ne, kina buƙatar hutu ki daina saka ma kanki damuwa da yawa, ita kuma saudat ki bari sai baba ta tafi zan sayi bulala ne na kewaya ta a sannan ne zata shiga hankalinta ta daina kallon ta na mamakin nan”
******
Cakalar abincin yake yi ya kasa kai ko spoon biyar bakin shi, tun yana jin daɗin kallon yarinyar nan da yayi jiya har kewanta ya shige shi, a tunanin shi tunda ya dawo kafin ayi sallan magriba idan ya shiga gidan su zai same ta amman shiru, yau da safe ma sau biyu yana shiga gidan amman bata nan kuma ba zai iya tambayar kowa ko ita wacece kuma daga ina tazo ba don baisan wani irin kallo zasu mishi ba,
Da ace yaga Zayyad ne da zai iya tambayan shi game da ita, amman tunda ya shiga gidan yau baiga Zayyad ba, wait!! Baiga Zayyad ba kwata_kwata hakan na nufin kenan… innalillahi wa inna ilaihirraji’un”
Da azama ya miƙe daga dinin table ɗin bai bi ta kan sadiya dake tambayar shi ko lafiya ba ya shiga ɗaki ya saka riga da hula ya fita bai tsaya ko ina ba sai gidan su,
*****
Tunda Muna tazo gidan take saka ido ko zata gane wannan sirrin amman shiru ita bata fahimci komai ba ‘to ko ba a nan sirrin yake bane?’ Ta tambayi kanta,
Tana zaune a balcony tana tunanin yanda zata ɓullo ma Sulthana ta samu ta sanar da ita wannan sirrin dan yau zuwa gobe kaɗai take dashi kafin lokaci ya ƙure,
Wucewar Sulaiman ɓangaren aunty Amarya kawai ta gani cikin hanzari kuma da alaman damuwa a fiskar shi tayi saurin tashi tabi bayan shi tana fatan wurin da sirrin nan yake zai je…1
******
“Gasu nan Saudat kuje yanzu don Allah ta sake kira na wai suna jira, list ɗin nan ki karance shi da kyau dukda sun san kan zannuwan amman ki gand saboda bambancin kuɗaɗen su, dan Allah ki dawo da wuri saudat gashi ƙanwar abban Jannat zata raka ki amman gida zata wuce daga nan, mai adaidaitan da yake kaiku makaranta zai ajiye ta sai ya dawo ya ɗauke ki”
To nace muka ɗauki jakan kayan, yau dake English wears ne a jiki na hijab na saka har ƙasa navy blue, muka fita daga gidan ina fatan Allah ya haɗa ni da Sitifid na rama zagina na jiya,
******
“Lafiya na ƙalau fa babban yaya, da gaske babu abinda ke damu na”
Kallon idon shi yayi yace “you are lying Zayd idanun ka basu nuna hakan ba”
Yaye duvet ɗin da ya lulluba dashi yayi cikin ƙarfin hali ya miƙe tare da fara zagaye ɗakin hannun shi yana reto a iska
“You see, kawai hutawa nake yi but I’m perfectly fine”
Shima Sulaiman miƙewa yayi yace to muje part ɗin Hajiya ka zauna cikin mutane tunda kace babu abinda yake damun ka,
Baiyi musu ba ya bishi suka fita yana murmushin ƙarfin hali maybe idan ya shiga cikin ƴan uwan shi zai daɗa jinshi garas,
Suna shiga part ɗin muma muka shiga da ƙaton jakar kayan mu…………🤦🏻♀️
Ga Saudat…..
Ga sulaiman….
Ga kuma Zayyad 😂 cakwakiya
Fans me kuke tunanin zai faru??
4
#vote
#share
#comment
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Lallai ance yabon gwani ya zama dole to nima yau gwana ta zan yaba*
_To mom twins (Mrs zanna)_❤️
*Na gode da shawarwari, ƙarfin guiwa da goyon baya💖, a duk lokacin da na gaza na gwada bani iyawa kina ƙoƙarin tado ni har zuwa wannan lokacin da na fara hawa wani mataki😍, alkhairin Allah ya isar miki a duk inda kike uwata aunty SAUDAT, Allah yaja kwana ya raya miki yaran ki bisa tafarkin sunna💕*
+
12🧝🏻♀️
Neman wuri Zayyad yayi ya zauna sulaiman yazo gefen shi shima zai nemi matsuguni wayar shi ta fara ringing ya ciro ta daga aljihu yana dubawa, ganin sunan da ya bayyana saman screen ɗin ya saka shi fita daga parlorn ta ƙofar baya, hakan yayi dai_dai da shigar mu bakunan mu ɗauke da sallama,
Turuss nayi lokacin da idanu na suka sauƙa a kan Sitifid ya wani bararraje a kujera ƙafar shi ɗaya kan ɗaya yana hira da ƴan ƙannen shi cikin nishaɗi,
A take ɓacin ran zagin da yamin ya dawo min kuma daman da cikin shi nazo gidan dan na ɗau alwashin ba zan tafi ba sai na rama zagi na,
“Welcome, welcome my daughter” muryan hajiya ya katse min tunani, bismillah ku shigo yau da rana ne Yusran ta ɗago ku?”
Murmushi kawai nayi mata muka ƙarasa jikin kujeran da take zaune muka nemi mazauni a ƙasa muka zauna sannan muka soma gaida ta, saidai rabin hankali na yana kan Sitifid da hankalin shi gaba ɗaya ma bayi wurin mu, tunda muka shigo ko kallon mu baiyi ba hankalin shi yana wani wurin,1
Kaman ance ya ɗago ya kalle ni sai ga idanu na cikin nashi ya kama ni ina satar kallon shi, haɗa fuska yayi ya kawar da kanshi nima nayi saurin kawar da nawa muka fara firfito da kayan da muka zo dashi,
Ko 2 minutes baiyi ba ƙwaƙwalwar shi ta tuno masa da fuska na, nice yarinyar da yayi karo da ita a bakin ƙofa ranar, kaman an razane shi ya juyo da sauri tare da ɗan ware idanun shi, again idanun shi ya sake shiga cikin nawa don nima shi nake kallo,
A lokacin hankalin mutane duk ya tafi kan kallon kaya, hakan ya bani damar murguɗa mishi baki ganin yanzu yana min kallon sani,
Murmushi yayi tare da kawar da kanshi gefe a lokacin ne na gano zurfin beauty points ɗinsa a zuciyata na ja tsaki ina cewa na mata_na mata kawai namiji mai dimples shi ko kunya ma bayi ji yana bari suna bayyana,
Harara na wurga mishi da ya sake kallo na a karo na biyu duk a matsayin ko ban rama zagi na ba nayi mishi abinda shima zaiji haushi, sai kawai ya gyara zama tare da zabga tagumi yana ƙare min kallo, tun da yake a rayuwan shi bai taɓa haɗuwa da funny girl iri na ba,
Ganin budurin nasu da yawa yasa hajiya ta nuna mana kujera a can nesa muka zauna, ƙanwar Khamis ta ɗan zaro waya tana latsawa kafin azo ɗaukan ta, ni kuwa bani dashi ga TVn su film ɗin turawa ake nunawa ba irin wanda nake so ba, kwata_kwata bani gane abinda ake yi ga hayaniyan mutanen wurin ma bai bari naji turancin nasu da kyau,
Tashi Zaytoon tayi da kusan zannuwa 5 a hannunta ta ƙaraso kusa da Zayyad sannan ta zuba zannuwan a ƙasa tare da durƙusawa tana gwada mishi ya taya ta zabe, for a while dukkan mu kowa ya kama harƙan gaban shi, Zaytoon tana faman tattaro mishi kaya yana zaɓa mata ni kuma ina faɗa musu kuɗaɗen kayayyakin,
Saida aka gama tass kafin mai napep yazo aka turo mai gadi yayi magana ma ƙanwar khamis ta fita su tafi, ni kuma na jira idan ya dawo sai yazo ya ɗauke ni,
Tunda ta fita nake jina wani iri gashi har sun kira tailorn da zai musu ɗinki sun tafi bashi kayan da style dan basu so ko kwana ɗaya kayan ya ƙara a wurin su,
Muna kwata_kwata bata jin daɗi, yanzu ta fara cire rai kan maganar makarantar nan dan ta lura munafurtan ta suke son yi, tayi binciken har ta gaji bata gane komai ba, ɗazu ma da tabi bayan babban yaya da taga ya shigo gidan hankalin shi a tashe, a tunanin ta zaije inda wannan sirrin yake ne amman bai wuce ko ina ba sai ɗakin Zayyad, gashi gobe jajiberi tana ji kaman zata iya mutuwa idan ba’a kaita ibadan ɗin nan ba,
Hajiya na barin parlorn don kawo min kuɗin kayan aunty Yusrah na juya na kalle shi tare da sake zabga mishi harara, sai a sannan ya samu damar magana bayan ya murmusa,
“Yarinyar nan lafiyan ki kuwa? Kodai idan naki ne ke miki ciwo?”
Kallon gefe da gefe nayi na tabbatar babu kowa sannan na sake juyawa cike da rashin kunya na murguɗa mishi baki amman me?” Sai ganin wani haske nayi ya kawo ya ɗauke, ban ankara ba naga yana maida wayan shi cikin aljihun wandon shi,
“Yauwa kinga yanzu na hutacar dake, ba sai kin sake wahalar da kanki wurin yin wa’innan abubuwan ba idan ina son kallo ga copy cikin waya na tunda na lura na musamman kike min”
Amman Sitifid ya gama da rayuwata, yanzu ɗauka na yayi ina making funny faces? Ga duka ga tsinka jaka? Ko na jiya ban gama ramawa ba ya ƙara min wani a kai,
Kallon idanu na yayi da suka tara ƙwalla saboda tsananin takaicin shi, haka kawai yaji bayi son na zubar da hawaye saboda shi, ya ɗanyi murmushin gefen baki sannan ya ɗaga hannun shi ɗaya yana shafa sajen fuskar shi tare da sake full murmushin da ya sanya dimples ɗinshi lotsawa yace
“Yaya kike min irin wannan kallon ko a garin ku babu kyawawa ne?”
Bansan lokacin da naja wani dogon tsaki ba hawayen da suka taru cikin idanu na da kansu suka nemi hanyar guduwa saboda tsantsar rainin hankalin Sitifid ɗin nan, wallahi ko ɗan iskan tsohon marigayin miji na Yarima yafi wannan na mata na matan kyau ballantana aje kan asalin kyawawan ƙauyen mu,
Na buɗe baki ina shirin labta mishi magana Hajiya ta shigo parlorn envelope a hannun ta wanda ke ɗauke da kuɗaɗen aunty Yusrah a ciki ta miƙa min sannan ta nemi ta zauna tana jana da hira tare da min wasu ƴan tambayoyi,
Jefi_jefi nakan ɗaga ido na kalli Sitifid ya ƙura ma fuskar wayan shi ido da yatsun shi guda biyu a saman screen ɗin ina gani yake ware su yana sakin murmushi, haka aunty Yusrah take yi idan zata yi zooming abu a wayan ta,
Duk time ɗin da ya ɗago idanun shi ya sauƙe su cikin nawa sai ya kalli wayan ya ɗago ya kalle ni yana gyaɗa kai tare da min alaman jinjina da hannun shi,
Me yake nufi ne?
Yanzu kam na fasa rama zagin ma dan na lura Sitifid yafi ƙarfi na, wannan dagiri(degree) ne a kanshi na rashin mutunci da rainin hankali, amman babu komai zamu haɗu a gaban Allah,
Ɗaga wayan shi yayi ya saka a kunne bayan ƴan sakwanni yace,
“Hello babban yaya ina jiran ka ko ka wuce ne?”
Ɗan shiru yayi yana sauraron abin da ake faɗa yace
“Ok to Shikkenan, nima bari na tafi kawai yamma tayi sosai zan koma ɗaki”
Da faɗan haka ya kashe wayar ko sake kallon wurin da nake baiyi ba ya fita,
Shikkenan ya tafi ban rama zagi na ba! Na faɗa cikin zuciya ta, to Allah ya isa!
Dawowa yayi wurin da nake zaune ya tsaya tare da faɗin “naji duk abinda kika faɗa, saidai ya isar mana tare”
Ya juya zai fita muna binshi da kallon mamaki don ko Hajiya bata ji abinda na faɗa ba,
Saida yaje bakin ƙofa sannan ya juyo ya gwada ya gwada idanun shi ya gwada nawa, wato idona idon shi, da haka ya fita yana dariya, ko banza wannan yarinyar ta saka shi nishaɗi……..🤦🏻♀️
*Gashi nan dai da babu gwanda ba daɗi, ayi manage zuwa dare insha Allah*
*Ummu Najma ce😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
13🧝🏻♀️
Shagwaɓe fuska nayi kaman zanyi kuka Ruma ta janyo ni jikin ta tana dariya,
“Haba ƙawata ba gani nan ba idan ma tsoro kike ji sai muje ɗaki na ki kwana, kinga aunty Yusran taki da kanta tace ki kwana gari babu lafiya ba zamu barki ki tafi ba gaskiya”+
Shikkenan ni rayuwata a yawo da kwanan gidan mutane zai ƙare? Babu gida guda ɗaya da za’a kira da namu wanda nake zaune a ciki daga nayi kwanaki a nan sai a cilla ni can,1
Saka ƙasan hijab ɗina nayi na share hawayen da ya fara sauƙo min, ina ɗagowa naci karo da nana tana watsamin wani mugun Kallo, ta miƙe tare da faɗin
“Idan bata son zama ku barta ta tafi mana! Duk abinda ya same ta ai ita taso” ta ƙarasa haɗe da tsaki ta bar parlorn,
Ohh Allah, ni bansan me nayi wa baiwar Allan nan ba zuwa na gidan nan kwata_kwata baifi awa 4 ba amman duk ta ƙuntata ma ranta tana neman hana ni sukuni,1
“Hmm auntyn sakalci, bamu cinye mutane a cikin gidan nan ki kwantar da hankali na kwana ɗaya dai ko babu komai comfort ɗin yafi na wurin da kika fito, ga kuma luxury”
“Haba Sulthana, wannan wani irin magana ne?” Cewar Batool “idan ba zaku lallaɓa ta ba ku rabu da ita, yau ta fara zama cikin gidan nan amman sai kun nuna mata hali? Ao ko babu komai ita baƙuwar mu ce ya kamata mu karrama ta”
Taɓe baki tayi ta miƙe tabi hanyar da Nana tabi, karere ba’a iya samun wuri ba yanda take bragging ɗin nan sai ka rantse da Allah gidan su ne, don nima abinda nayi tunani kenan itama ƙanwar Sitifid ce,
Muna kam abin duniya ya ishe ta ita bama tamu take ba, ta zurfafa cikin tunanin yanda zata nima ma kanta hanyar tafiya ibadan, niman sirrin nan take ruwa a jallo dan shine kaɗai makamin da zata yi amfani dashi wajen cikar burin ta,
Jin an fara kiran sallah yasa duk muka tashi suka jagorance ni zuwa ɗakin su aunty Zaytoon muka yi alwala, ina fitowa na samu sun shimfiɗa min darduma ga hijab a kai na ɗauka nayi sallah,
Daga nan muka fito wasu suka shiga kitchen suna fito da warmers ɗin abinci wasu kuma suna shirya kan dining, nima don kar ayi babu ni na shiga cikin masu shirya dining saboda manyan ne su aunty Batool, na san ban isa na shiga cikin wa’incan ba yanzu fitinannu biyun nan su saka ni a gaba,
Ruma na ganin haka ta barsu ta dawo cikin mu sai arhantar mun da kyakkyawar murmushin ta take yi, cikin nutsuwa tace
“Saudat amman ke ba ƙanwar aunty Yusrah bace ko?”
Girgiza kai nayi nace “A’a ni ƴar uwan mijinta ne, daga ƙauye nazo zaki ma iya kira na da boɗɗi haka aka fi sani na da…”
Da sauri ta matso jiki na cikin kunne na ta raɗa min “kada kiyi su Nana suji, kawai idan an tambaye ki kice ke ƴar garin nan ne”
Kinji?
Gyada mata kai nayi muka ci gaba da aikin gaban mu,
Muna gamawa aka sake tattare parlor sannan aka sauƙe duka curtains ɗin gidan aka bulbule ko ina da turaren wuta muka shiga yin sallan isha,
**********
“Allah sarki ƴar ƙanwa ta, bansan yanzu a cikin wani hali take ba”
STORY CONTINUES BELOW

Gyara ma abulkhairi kwanciya a jikin shi Khamis yayi, sannan yaci gaba da cin abincin sa, duk yanda nayi ya kawo shi idan ya gama sai ya karɓe shi yaƙi,
“Kada ki damu baby, indai gidan su boss sulaiman take to kisa ma ranki wataƙil dawowa ma ba a son ranta zata yi ba domin akwai su da karamci sun iya karrama baƙo”
“Allah yasa amman ka san rashin sabo, lokacin da tazo gidan nan ma da ƙyar take iya barci hala ne yau ta iya cikakken barci, kuma ba lallai ta samu daman kallon TV ba wallahi tausayin ta duk ya kama ni saboda yanda take son film ɗin hausa”
Ajiye spoon ɗin hannun shi khamis yayi tare da jinjina kai yana kallon ikon Allah, har cikin zuciyan ta wannan maganar yake fitowa dan ta ɗauki Saudat kaman ƙanwar ta Nasreen yarinyar ta shiga ranta sosai,
“Lallai mata kuna da abin mamaki, kece fa kullum mai min complain ɗin Saudat ta cika kallon TV amman yau da ba zata samu daman gani ba kamata yayi kiyi murna kuma kiyi fatan Allah yasa daga haka ta ɗaure amman…”1
Shuru kawai yayi ya kasa ƙarasa magana yana kallon yanda yusrah take ƙifi ƙifi da ido,
“Insha Allah gobe zata dawo sai ki ci gaba da kunna mata TVn tana kallo nidai kada a sake cemin Saudat tayi kaza tunda ke kike bata goyon baya”
********
Wurin yayi shiru sai ƙaran cokula kawai kake ji kowa hankalin shi yana kan abincin shi amman banda ni,
ɗaga ido nayi a sace na kalle su duka tun daga kan mahaifin su har zuwa kan junior dake gefe na sun saka ni a tsakiya shi da Ruma don tun da nazo ya maƙale min wai nice gyalfirens (girlfriend) ɗinsa,1
Gaba ɗaya nayi loosing appetite ɗina, wani iri nake ji gaba ɗaya jiki na babu daɗi, kuma wani abu ma, naga kowa a nan wurin amman banga Sitifid ba kuma naji ɗazu ana magana a kanshi saidai banji mai suke faɗa ba, haka kawai naji zuciyata tana son sanin dalilin da yasa Sitifid baizo cin abincin dare ba tunda ina da tabbacin nan gidan su ne, Allah yasa dai lafiya,
Saida muka gama sannan muka tattara kwanukan muka shigar kitchen maids zasu wanke, aka zuba a parlor ana kallon series film na Philippines ana gamawa aka kai na Korea, gani nan a zaune ina fama da kewar su Ali nuhu tsoron su Sulthana ya hana ni magana,
Ɗaya bayan ɗaya suke fita suna dawowa saidai bansan ina suke zuwa ba, zuwa ƙarfe 10 saura na fara gyangyaɗi a zaune don ba amfanuwa da kallon nake ba, nan ne Ruma tayi min jagora zuwa part ɗin su,
kafin na kwanta saida ta saka nayi wanka a nan ne kuma ake darun, don ma dai yarinyar ƴar gari ce ta lura da ƙauyancin dake jiki na yasa ta nuna min yanda ake amfani da komai na toilet ɗin amman duk da haka fa da ruwan sanyi ƙalau nayi wankan dan Allah ya gani ina tsoron na ƙona kaina ana zaman ƙalau,
Fitowa nayi ɗaure da towel, dan ta bani bathrobe naƙi sakawa banga amfanin ɓata kaya har biyu, na saka wannan rigan nazo na saka wani ba,
Wani lotion mai ƙamshi ta bani na shafa sannan ta bani set ɗin pjamas blue color mai taushi na saka, ta bani hula mai kunnen micky mouse shima blue,
Wani matsiyacin dariya nayi lokacin da na hango kaina a jikin madubi sannan na juyo hannu na riƙe da hancin mouse ɗin jikin hulana na kalle ta tana tsaye a baya na da murmushi a saman fuskar ta,
“Umm…” Na faɗa ina kókarin tuno sunan da naji suna kiran ta dashi, ba don na manta ba sai dan sunan baiyi min kama da na musulmai bane baima yi ma’ana ba kuma bansan asalin sunan da zan kira ta dashi ba,
“Rumaisa! You can call me Rumaisa”
Murmushi nayi nace “na gode sosai Rumaisa kayan sunyi kyau wallahi idan na koma ƙauyen mu ko su Inna ba zasu iya gane ni ba”
“To na baki su kyauta sai kije ƙauyen ki nuna musu, ko kina so na saka a kai ki ne?”
Girgiza kai nayi a sanyaye nace “ba zan iya komawa ƙauyen mu yanzu ba idan naje ba zasu barni da r…”
Sai Kuma nayi shiruu tunawa da kashedin da Khamis yamin na ko a gida bayi son wani ya san labari na, bama dalilin da yasa na dawo birni ba yace ko zancen na taɓa aure kada na faɗa ma kowa idan ba haka ba ya maida ni gidan su Yarima,
“Zo ki kwanta” ta faɗa tare da daga min duvet ɗin gadon, a hankali na taka zuwa wurin na hau gadon tare da kwantawa ota kuma ta rufe ni,
“Bari naje na duba jikin Ya Zayyad ina dawowa” ta faɗa kafin ta fita, kaman nabi bayan ta nima naje duba shi haka naji, ɗazu_ɗazun nan muka rabu dashi lafiya lau to me ya same shi? Allah yasa ba Allah ya isan da na mishi bane ya kama shi indai shine na yafe don bani son in dinga shiga hakkin mutanen da ban sani ba,1
*****
Yanzu kam dole ya san yanda zaiyi ya nemo ta tunda ya kasa cire ta a zuciyan shi, zaune yake ya hakince a kan 2 sitter ga TV a gaban shi sai faman zuba yake yi amman tunanin shi ma bayi wurin,
A kujeran dake gefen nashi ta zauna ta ƙura mishi na mujiya, gaba ɗaya ya canza, al’amuran shi sun juye ba wai ya canza hali ko yanayi ba har yanzu yana nan da tsaurin shi da zafin rai da tsanani da komai amman yanzu shi kaɗai sai kaga yana cikin nishaɗi wanda har yanzu bata san dalili ba,
kwana biyun nan yawancin lokutan shi a gida yake kashe su saɓanin da, da idan kaga ya shigo to wani abu ne ya kawo shi kuma yana gamawa zai fita,
Har ta gama zaman ta bai ko ɗago ya kalle ta ba har ta gaji taje ta kwanta don barci ne sosai a idanun ta ba zata ɓata lokacin ta wurin wannan mutumin ba tunda yau ba buƙatar komai take daga gare shi ba,1
**********
29/sha’aban/1442
Bayan rashin ishashen barci da mafarkai masu abin tsoro, mun wayi gar lafiya cikin hukuncin ubangiji, idan ba ɓata gani nayi ba sai naga kaman safiya a cikin gidan nan yafi daɗi kana zagaye cikin mutane masu yawa to ko ina ƙamshin furannin dake zagaye da gidan ne suke shigowa,
To yau ma gani saman dinin table an haɗa ni da abincin da na kasa ci amman haka junior yasa nake ta turawa, a gaban iyayen shi ko kunya baiji ba ya saka ni a gaba kaman jaririya yana bani abinci a baki, dukda dai yaron ba zai wuce shekaru 11 ba amman ni naji kunyar hakan sosai,
Shigowa yayi da sallama, muryar nan loud and clear kaman ko yaushe, yana sanye da jampha light brown sai baza ƙamshin turare yake yi, dukkan mu ɗaga idanu mukayi muna kallon shi amman idon Sulaiman bai sauƙa kan kowa ba sai ni……..🤦🏻♀️
1
#vote
#share
#comment.
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Wannan shafin naku ne ƙanne na kuma ƙawaye na, Haleesatou ƴar mutan Niger da Saleehatou yar mutan Nigeria😅*
Godiya mara adadi❤️
14🧝🏻♀️
“Dadyn Arif ina kwana” muryan Zaytoon ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula, yafi 1 minute tsaye yana kallo na wanda ni banma lura da hakan ba tunda nayi mishi kallo ɗaya na maida hankali na kan junior yana ci gaba da bani abinci a baki,+
Gyaran murya yayi yana ƙoƙarin tattaro nutsuwar shi sannan ya amsa gaisuwan ta, ɗaya bayan ɗaya suka dinga gauda shi yana amsawa cikin taƙama da jin kai, ganin haka yasa nima na gaida shi amman kuma a maimakon ya amsa sai ya haɗe rai tare da kawar da kanshi daga gare ni ya tambayi Ruma
“Wacece wannan?”
“Umm sunan ta Saudat, ita ƙanwar aunty Yusrah ne wanda take kawo man…”
Dakatar da ita yayi da hannun shi yana daɗa ɗaure fuska yace “bani buƙatar wannan bayanin”
ko Ruma da ya disga saida taji ba daɗi ballantana ni,
He made me feel out of place, ashe ba zallan Nana da Sulthana bane suke da wulaƙanci harda manyan su, daman mutane suna faɗa masu kuɗi basu ganin darajan talaka, wasu hawayen sakalci da na saba dashi naji suna ƙoƙarin sauƙo mun nayi saurin sunkuyawa tare da ɗaukan serviette ɗin dake gefen plate ɗina ina share su,
Babu wanda ya lura da haka bayan shi, ban san me ya shigo dashi ba amman muna haɗa ido bayan na ɗago naga ya juya ya tafi, a zuciya ta ina roƙon Allah yasa har na bar gidan kada na sake haɗuwa dashi don har ga Allah tsoro yake bani,
Tsayuwa yayi a ƙofar part ɗin su Zayyad don bai isa ya shiga ciki a yanayin da yake ba, sosai ranshi ya ɓaci da abinda nayi, matsalar hidima da yara kenan gaba ɗaya basu da hankali, yanzu daga yaƙi amsa gaisuwana na kama kuka, meye amfanin kukan kuma oho!
Lallai yana da aiki a gaban shi indai yana son mallaka na to dole ya tankwasa ni nabi tsarin shi,4
Yana gama ayyana haka ya wuce ciki,
Aunty amarya ya samu itama tana breakfast tare da Fa’iza da sadiƙ , sai a lokacin ya samu damar karyawa don tunda aka kira shi aka faɗa mishi halin da Zayyad yake ciki ya rasa nutsuwar shi,
Suna ganawa ya shiga ɗakin shi, a kwance ya hango shi yana barci yayi wani iri gaba ɗaya jikin shi a sake bakin shi ya bushe, a saman bedside drawer ya zauna sannan ya riƙo hannun Zayyad cikin nashi ya ƙura mishi ido amman ganin raunin dake tattare dashi yasa yayi saurin kawar da kai tare da jan dogon numfashi da yayi sanadiyyar farkawan Zayd,
A raunane yake kallon cikin idon yayan shi da ya kaɗa yayi jaa yace
“Kayi haƙuri babban yaya ba abun da kake tunani bane”
“Zayd yanzu ka yarda zaka barni na tambaye ka matsalar ka? Tunda yanzu idanu na sun gane mun baka cikin yanayi mai kyau, Zayd me yasa kake ma kanka haka ne? Baka kiyaye abinda zai saka hankalin mu tashi”
Da ƙyar ya iya daddafawa da taimakon Sulaiman ya tashi ya zauna, sai yanzu ya lura da ramar da yayi a wuni ɗaya kawai,
Cikin low voice yace
“Babban yaya nima bansan dalilin hakan ba, kwana biyu na kasa gane wa kaina kwata_kwata, sannan duk wasu sharaɗi da dokoki da rayuwa na ya ɗauru a kai har gobe ina kiyaye su, duk abinda na san zai jawo mana damuwa bani son..
STORY CONTINUES BELOW

“Me ya fitar da kai waje jiya?”
Shiru yayi yana tunanin wani amsa zai bashi ya aminta, don idan ya faɗa mishi asalin dalilin da ya fitar dashi bacin ran sai ya ninka na fitan da yayi,
Yarinyar jiya nan ne ta fitar dashi ba tare da yayi niyya ba, yana dawowa part ɗinsu a jiya ya zauna tare da aunty Amarya a parlor lokacin tana kallon news,
A nan ne yaji sanarwan da akeyi na gari babu lafiya, an tada tarzoma a wasu areas shiyasa ake bada shawarar kowa ya zauna gida kada abun ya rutsa dasu,
Jin haka yasa ya zari key ɗin motar aunty amarya ya fita don ya samu ya tseratar da ita yasan hala ba’a san da hakan ba an barni na tafi,
Amman har ya gama yawon sa a gari baiga alamu na ba, sai a sannan ma ya tuna da ba sani na yayi ba, kuma bai san ma ina zaibi ya ganni ba tunda ba lallai bane ma ya gane ni,
But it’s too late, ya riga da ya makaro baifi 2 hours ba driving ya fara gagaran shi gashi magriba tayi gari ya fara dugu, da ƙyar ya samu ya ƙaraso gida ashe labari tun a lokacin ya isa ma sulaiman bai sani ba,
“Umm…D..daman..nn..wani” daburcewa yayi ya kasa magana don har ga Allah bai san abinda zai faɗa ma Sulaiman ba, babu koda uzurin ƙarya da zai bashi,
Ƙura masa idanu yayi yana son gano gaskiyar zancen sa cikin idanun sa “uhmm ina jinka daman wani mene?”
“Believe me babban yaya wallahi banyi wani abun da bai kamata ba, babu wanda ya san ma na fita babu wanda ya ganni sannan naje har na shigo cikin gidan nan ƙlau”
“Amman da ka dawo gashi ka shiga cikin matsala, duba kaga jikin ka fa? Wani irin uzuri ne wannan wanda har yafi rayuwan ka amfani? Wani uzuri ne wannan da ka zaɓe shi fiye da rufin asirin ka da kwanciyar hankalin iyayen ka? Baka gaji da saka aunty amarya kuka bane Zayyad?”
Da sauri ya miƙe zaune da kyau hawaye na zuba daga idanun shi ya riƙo hannun Sulaiman kaman zai tsinka su saboda bayi son jin maganar da yake yi kwata_kwata, cinkin ɓacin rai Sulaiman ya hankaɗa shi ya koma ya kwanta babu shiri yana matsar ƙolla,
“Yanzu kam na fara gajiya, ba zaka buɗa min kai ba Zayd, ba kai kaɗai bane responsibility na amman kai kaɗai ka hana ni sukuni ko yaushe idanuwa na suna kan ka amman kai baka kiyaye koda the simplest cikin dokokin da nake shimfiɗa maka, duk abinda ya same ka daga yanzu babu ruwa na nidai abu ɗaya na sani shine xanyi ta binne sirrin ka har sai ka mallaki dukiyar ka kaman yanda nayi wa aunty amarya alƙawari kuma baka isa ka sauya min ƙuduri na ba”
da faɗan haka ya fita a ɗakin Zayyad ya dafe goshin shi ranshi yana mishi zafi, me ma yasa yabi bayan ta ne meye ruwan shi da ita? Gashi yanzu ya ɓallo ma kanshi mikin da bai san hanyar gyaran shi ba yayi dana sanin biye wa zuciyar shi,
**********
Gagarumin shiri suke yi yanda kasan gobe ne sallah tunda muka gama breakfast ba zama, ana ta ayyuka naman da aka shigo dashi a gyare a yanke ya kai girman rago guda ga kaji sau shan wuta suke yi,
Ga snacks kala_kala wanda wasu ban ma san sunan su ba an kowa an jibge kayan abinci ma ba dama ni ban taɓa tunanin akwai masu yi ma azumi irin wannan shirin ba gaskiya sai kace wani biki,
Dake bani da ƙyuya na shiga cikin masu aikin gidan ina ta hidima su kuma yaran su taɓa Wannan kaɗan sai a nime su a rasa,
Ina tsaye a kitchen ina suyan doughnut ɗin hajiya wanda aka haɗa mata na musamman babu sugar da yawa a ciki Nana ta shigo, ban san da shigowar ta ba shiyasa nima hankali na kwance nake aikin gaba na ina rera waƙar fulani, da kaganni ka san ina cikin nishaɗi wanda na tabbata hakan ne ya ɓata mata rai,
“Ke wai baku da gida ne?”
Naji muryanta ta baya na, da sauri na juya ina shirin magana amman irin kallon da take watsa min yasa nasha jinin jiki na, tare da sunkuyar da kaina ina kallon ƙasa don har yanzu tsoron ta nake ji,
“Baki ji bane ko kuma yaren da nayi amfani dashi ne baki ganewa? Nace baku da gida ne??”
Murya can ƙasa nace “muna dashi” a taƙaice
“Ok to zaman me kike mana a gida har yanzu baki tafi ba? Idan ma wani abu ya kawo ki to ki sani mu ba wawaye shashashu bane da zamu yarda da duk wanda muka gani yazo from nowhere musamman ƙasƙantacciya irin ki, ki sani kuma ki saka ma ranki baki da matsuguni a gidan nan dan haka ki tattara ƙafafunki da tsumman rayuwanki ki bar mana gida masu idon cin nera”2
Har ta fita tana faman ƙunƙuni ni kuwa bance mata komai ba dukda zuciyata ta sosu amman kuma gaskiyar ta ne tunda yanzu komai ya lafa ya kamata na tafi gida,
Ko ƙarasawa banyi ba na fita daga kitchen ɗin zuwa ɗakin Hajiya na faɗa mata ina son tafiya gida amman matar nan haka firr taƙi ta barni na tafi wai na tsaya sai yamma yayi yanzu rana yayi tsakiya, ba zan iya musu da ita ba shiyasa na haƙura amman banso haka ba tunda har an ƙare anyi min gori ya kamata nima nayi zuciya,
A ranar a ɗakin aunty Batool nasha zama na duk inda na san zan shiga na haɗu da mutane bani zuwa ko da aka zo yin launch ma ina jin za’a shigo kirana na ɗuru toilet da na fito na tada sallah haka har suka gaji da jira na suka ci abincin su,
Aunty Yusrah ta kira Hajiya yafi sau uku amman ko wani lokaci sai tace zasu saka a dawo dani har bayan la’asar shiru, daga ƙarshe Khamis ne ya danne ta da cewa ta haƙura har su dawo dani da kansu tunda ana da tabbacin wurin da nake,
Har zuwa lokacin kuwa babu abinda na saka a ciki na ga wani baƙin yunwa da nake ji har kuka ƴaƴan ciki na suke saboda yunwa gashi ba wani abun kirki ma naci da safe ba, jin yunwa na niman hallaka ni yasa na tashi na shiga kitchen, snacks ɗin da aka ajuye cikin manyan robobi na buɗe na ɗauki cake 3 da soyayyen cinyoyin kaza har biyu dan ji nake kaman idan garin adamawa aka bani gaba ɗaya zan cinye,
*****
Shigowa part din yayi tun daga parlor yake addu’an Allah yasa ya haɗu da Sulaiman saboda ya lallashe shi ya daina fushin da yake yi dashi idan ba haka ba akwai Matsala, yana cikin dube duben shi har ya wuce kitchen ya dawo ganin ƙofar a buɗe kuma kaman ya hango mutum a ciki,
Leƙawa yayi ya hango ni zaune da plate ɗin cake ɗina ina ta turawa amman ban ganshi ba saboda na bashi baya,
Ya kamata yaji haushi na saboda abin da ya faru dashi a dalili na ko ma ya manta dani gaba ɗaya ya fita harƙa ta amman yana jin ba zai iya ba,
Na kai ma cinyar kazan nan wani mugun cizo sai ganin haske nayi ya kawo ya ɗauke, ko cire naman banyi daga baki na ba na ɗago idanuwa na don ganin hasken na menene,1
idanu na basu sauƙa a kan kowa ba sai Sitifid da waya a hannun shi yana ɗauka na photo……….🤦🏻♀️
_Kuyi haƙuri na jina shiru da kuka yi kwana biyu, insha Allah daga yanzu zan dinga update daily_
*Wattpadians kuna ƙoƙarin voting na gode ƙwarai👏🏼😍*
*Ummu Najma ce😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
15🧝🏻♀️
Ji nayi kaman na nutse cikin ƙasa saboda kunya, na miƙe tsaye tare da fito da naman baki na da ban samu daman taunawa ba na zuba a cikin ƙaramin dustbin dake kitchen ɗin, yanayin fuska na yasa Zayyad yaji ba daɗi dukda photo na da ya ɗauka ba wai da nufin bazawa a duniya bane, haka kawai zuciyar shi ta raya mishi ya sake tsokana ta dan ya lura ni ɗin kaman ƴar rigima ce amman yaga alaman ba haka bane,+
Bani da saurin zuciya, idan nace zanyi wani abu ma na san ba iya karawa zanyi da Sitifid ba don tun jiya ya gwada min shi ɗin yafi ƙarfi na,
“Me kike yi a nan?”
Ya tambaya cikin sanyin murya da naji ya ratsa har ɓargo na, ban ɗago ba da yatsana na nuna mishi plate ɗin cake ɗin da nake ci,
Idon shi a kaina yace “baki magana ne? Ko Allah ya isana na jiya ne ya cinye miki bakin?”
Still ban tanka shi ba na ɗago idanuwa na na zuba su a cikin nashi ina ƙare masa cikakken kallo for the first time, for about 2 minutes muna kallon juna,
“Ba zaki faɗa min ba?”
Ya faɗa ba tare da ya san maganar ta fito ba saboda wani yanayi da ya tsinci kansa lokaci ɗaya, ni na fara ɗauke idanu na sannan na sunkuyar da kaina ƙasa kafin nace
“Abinci nazo ci,
“Abinci da wannan lokacin?” Ya tambaya
“Eh, yunwa nake ji”
Taɓe baki yayi tare da faɗin “ok” ya juya zai fita da sauri nasha gaban shi dan idan nace sunan shi zan kira bansan wanne ɗaya a ciki zan kira ba Zayyad ɗin ne ko Stipid,
“Dan Allah ka goge hoton nan filis”
Yatsina fuska yayi kaman bai gane abinda nake nufi ba yace “Wani hoto?”
Saida gaba na ya faɗi ganin yanda lokaci ɗaya yasha mur dukda basu kama da babban yaya ɗin nan amman a haka yayi kama dashi sosai, kallo ɗaya mutum zaiyi musu ya shiga taitayin sa, tattaro ƙarfin guiwa na nayi sannan na kalle shi cikin ido
“Na san ɗazun nan hoto na ka ɗauka amman dan Allah ka goge harda na jiya ma ba zan sake maka wani abu mara kyau ba”
“Oh ashe kin san babu kyau ɗin kika yi? Ke baki san rashin kunya ma babba laifi bane da kika saka ni a gaba kaman sa’an ki kina murguɗa min baki? Ai na riga na ɗauka dan haka babu gogewa wannan shine punishment ɗinki duk ranar da kika sake abu makamancin haka kuma sai na gwada ma yaran gidan nan kowa ya gani ke harda su hajiya ma sai na nuna musu”
Da faɗan haka ya raɓa ta gefe na zai wuce ai nayi saurin sake tare shi idanu na suna shirin zubda hawaye dan gani nake kaman yanzu ma idan ya fita da gaske nuna musun zaiyi, ai kuwa da na shiga uku musamman idan Nana taga hoton da ya ɗauka yanzu inaga kora na zasuyi da zagi daga gidan tunda abinda na ɗauka nake ci ma ban tambaya ba,
“Dan Allah kayi haƙuri ka goge wallahi bazan sake ba kaji na rantse maka”
Naɗe hannayen sa yayi saman ƙirjin sa yana bina da kallon ƙurilla sannan yace “Shikkenan naji zan goge amman bisa sharaɗin duk tambayar da nayi miki zaki bani amsan ta kin yarda?”
Da sauri na gyada mishi kai na zuba kunnuwa don sauraron wasu tambayoyi ne wannan,
“Menene sunan ki?”
“Saudat”
“Shekarun ki nawa?”
Sake kallon shi nayi da mamaki ina tambayan kaina wani irin tambaya ne wannan? Amfanin me sanin shekaru na zaiyi masa? Amman kuma ganin fuskan shi babu wasa yasa na bashi amsa da “15”
Haka yaci gaba da mun tambayoyi ina amsawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwata, ina ne unguwan ku…a wani makaranta kike….ajin ki nawa….ina ne ƙasar ki na aihuwa….iyayen ki suna raye… A taƙaice dai Zayyad yayi mun tambayoyi sunfi ashirin wanda ban san dalilin su ba,
yana gamawa ya ciro wayan shi daga aljihu ya goge a kan idona ina gani ya danna delete photon ya ɓace, but little did i know akwai foldern dake ajiye recently deleted messages a wayan shi wanda sai pic yayi 29 days idan bayi restoring ba sai yayi deleting permanently,
dan haka ya saka ma ranshi da ya bar nan zai maido da abinshi yaci gaba da kallo don yana da buƙata,
Juyawan da zaiyi ya hango ruma tsaye a bakin ƙofa tana faman zabga murmushi, shima baisan lokacin da murmushin ya suɓuce masa ba dan yana da tabbacin Ruma ta daɗe a tsaye daga yanayin tsayuwar da tayi,
Ƙarasawa yayi yaja cheeks ɗinta sannan ya fita tana binshi da kallon tuhuma dan tana hango wani al’amari a cikin wannan murmushin da ya fita yana yi, ta ƙaraso wuri na ta ɗauka min plate ɗin cake ɗina sannan ta jani zuwa part ɗinsu dukda ban so shiga ba dan bani son sake haɗuwa da Sitifid,
Zama nayi a kan cushion seat na ɗakin ina jiranta ta shigo da glass cup da kwalin chivita ta ajiye mun a gaba na tare da jingina tana kallo na cike da sha’awa,
“Finally Allah ya kawo ma ya Zayyad matar aure, yau gani ga budurwan ya Zayd”
Duk da na lura a sigar wasa ta faɗa mun amman kuma kalmar BUDURWA da ta faɗa ya daga min hankali, wannan laƙani bani cikin masu mallakan shi, wannan suna yayi min nisa da HAR ABADA ba zai dawo mata ba, Yarima ya riga ya tarwatsa wannan ƙimar yayi mata tabo a zuciya wanda ba zai taɓa iya goguwa ba,
“Ke!!”
Ruma ta katse mata tunani tare da tafa hannunwan ta saman fuska ta don ta dawo da ni hayyaci na,
Dagowa nayi a firgice ina ƙoƙarin sakin murmushin yaƙe bani son arin Ruma ta gane ina da wani damuwa har ta tambaye ni, don wannan sirri tawa ce da zuciya ta,
“Tunanin me kike yi ne ina ta magana baki ji?”
“Babu komai Rumaisa, me kike faɗa?”
“Cewa nayi yanzu sai mu san yanda za’ayi ki daidaita da ya Zayyad kinga sai ayi abun na wuri ba sai an ɓata lokaci ba tunda kema kamar na gida ne”
“Lallai fa Rumaisa, wa yace miki soyayya muke da kike maganar wani daidaitawa, daga kinga muna magana tare Shikkenan sai ki ɗauki wani tunani ki saka a ranki?”
“Look madam, idan ma baku yi ni zan saka ku fara because i want the two of you to be together, na san ba zan taɓa samun sister in law da zata kai ki ba wanda zata kula da yaya na tsakani da Allah kuma ta kula da matsalar shi”
Juyowa nayi ina kallon ta hannu na riƙe da handle ɗin ƙofar toilet da zan shiga,
“Wani matsala kuma Rumaisa? Ya Zayyad ɗin yana da wani matsala ne???
*****
Me yasa yayi ma kanshi haka ne? Ya samu dama amman yayi wasa da damar shi, da ace ya saurara yaji address ɗin da ruma zata bashi da safe da a yau ɗin nan zai je ya fara fafutukar niman auren Saudat,1
Shi bai damu da yarintar ta ba, indai zata zamo mishi mata ta gari buƙatar shi ya biya, kuma yana da yaƙinin hakan don yarinyar akwai nutsuwa da kamun kai don duk haɗuwan da ya taɓa yi da ita cikin yanayi mai kyau take,….
Tunanin shi ne ya katse saboda ringing da wayar dake saman table ɗin shi yake yi,
Ganin sunan aunty amarya yasa yayi saurin picking tare da sallama,
“Sulaiman kazo dan Allah, ZAYYAD!!………🤦🏻♀️
Battery low😫
Sai yanzu na samu caji kuyi min afuwa😣
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
16🧝🏻♀️
“Aa ba wai wani babban matsala bane, umm.. kawai..babu komai bayi da wani matsala, kawai na faɗa ne don na zolaye ki”
Ta ƙarasa tana dariyan dole don bata san lokacin da tayi wannan ɓare_ɓaren bakin da zai iya jawo mata fitinan da bata san ƙarshen ta ba, idan har tayi sanadin da boɗɗi ta san matsalar ya Zayyad tana ganin ranta ne kawai babban yaya ba zai raba ta da shi ba,+
Ban matsa da tambaya ba tunda na lura bata son faɗa min na shige toilet abuna,
Ina fitowa na samu bata ɗakin, to ina taje? Zama nayi naci gaba da shan juice ɗin da ta shigo min dashi ba’a fi 2 minutes ba ta sake shigowa da sauri ko wurin da nake bata kalla ba ta bude drawer ta ciro wani containern magani fari ta fita,
Ganin haka yasa na saka hijab ɗina nabi bayan ta dan ganin abinda yake faruwa, a ƙofar wani ɗaki naga sun tsaya cirko_cirko aunty Amarya sai tsiyayan hawaye take yi dukkan su fuskokin su ɗauke da damuwa,
10:07pm
“Har yanzu baki faɗa min me yake faruwa ba Rumaisa”
Sauƙe numfashi tayi cike da damuwa gashi na matsa mata tace ” kada ki tilasta ma kanki sanin abinda yake faruwa boɗɗi don sanin naki bayi da amfani kawai idan da hali ki ci gaba da taya mu da addu’a duk damuwar da muke ciki Allah ya yaye mana”
“Ameen” nace ina jin kaina wani iri, Ina kokwanton cikin wani hali Sitifid yake? Me ya same shi da ba’a son faɗa min? Ɗazun nan ya tsare ni da tambayoyi kuma a lokacin yana cikin yanayi mai kyau amman yanzu…
Ringing ɗin wayan Ruma ne ya katse min tunani, tana ɗagowa taga sunan mai kira ta saka hannu ta dafe ƙirjin ta tare da sakin salati kafin tayi picking,
Shiru tayi tana sauraron abin da yake faɗa kafin ta saki kuka wanda ban san dalilin shi ba,
“Wallahi bata san komai ba babban yaya, i will never expose our secret to a stranger, believe me i didn’t take her to his door she went there herself please forgive me”
Kaman tana gaban shi take gyaɗa kai cike da ladabi ga duk abinda ya faɗa mata sannan daga baya tayi godiya ta kashe wayan, yanzu ta fara taraddadin zama na a part ɗin nan don idan har na san wani abu kan matsalar ya Zayyad laifin ta ya Sulaiman zai gani tunda ita ta kawo ni,
Bani jin ƙwaƙƙwaran turanci yasa ban fahimci abinda tace ba kuma na san ta canza harshe ne saboda ni, shiyasa ban matsa naji me ya saka ta kuka ba na bata haƙuri sannan na gyara na kwanta tare da runtse idanu na,
Yauma zan sake kwana cikin wannan gidan wanda dalilin abin da ya faru yau da yamma suka riƙe shi dalili na in ƙara haƙuri zuwa gobe kafin a maida ni gida, Yaya aunty Yusrah zata yi da batun suhur ɗin ya Khamis? Gashi yau sauran kwana biyu kawai raɗin sunan abulkhair,
na san akwai shirye_shirye masu yawa da take buƙatar masu taimako amman wa’innan mutanen sun riƙe ni a nan, zuwa wani lokaci kuma barci ya ɗauke ni har lokacin Ruma tana zaune da waya a hannun ta tana dannawa,
*****
Displaying pic ɗin yayi yana kallo, amman idanuwan shi ne kawai suke kan hoton zuciyar shi ta lume a duniyar tunani,
Wannan ne karo na farko da yaji yana buƙatar wani abu so badly a cikin abubuwan da aka haramta mishi, yana so ya zamo namiji a wannan lokacin duk da yasan ba zai iya ba amman yana buƙatar gwada mazantaka saboda cikar burin shi,
Yana ji a jikin shi ya fara son yarinyar nan Saudat, a yanzu yana buƙatar abokiyar rayuwa yana son yayi aure amman bai san ta ina zai fara kai maganar wurin Sulaiman ba,
Zai sake rejecting ɗinshi ne kawai kaman yanda yayi daga farko da ya kai masa zancen aure da Sulthana lokacin bata fito masa da asalin halayyar ta ba, har yanzu maganar da ya faɗa mishi yana mishi yawo a ƙwaƙwalwa
“Kai ba namiji bane a yanzu Zayd, babu macen da zata iya zaman aure da kai da matsalar ka, ka saka abubuwa masu muhimmanci a gaban ka yanzu wanda kake buƙatar ƙarasa su cikin nasara ba wannan shirmen da kazo dashi ba”
Shi bai yarda da wa’innan kalaman ba, ba zaiyi aure bane saboda wani jin daɗi zai yi shi ne saboda Allah kuma don soyayyar da yake yi ma Saudat, shi bai damu ba koda don saboda kuɗin shi ne ta yarda zata aure shi, zai jira ta har zuwa lokacin da ta isa aure taji ta shirya ma auren sa,
*****
Suhur muke yi insha Allah yau zamu tashi da azumin Ramadan amman sai faman gyangyaɗi nake yi idan nayi spoon ɗaya biyu sai inji idanu na suna rufewa don jiya banyi wani barcin kirki ba,
Abinda na gani cikin mafarki game da Sitifid ya firgita ni matuƙa da yayi dalilin tashi na kuma na kasa komawa barci,
Aunty Amarya, Ruma, dady, junior sadiƙ, Zaytoon, Batool da kuma Ni ne zaune bisa dining ɗin amman saida mutumin yasan yanda yayi ya zauna opposite dani, ga boyfirens ɗina a gefe idan ya fara zubar zancen sa ne nake farkawa,
Murmushi yayi ganin na sake lumshe idanu na spoon ɗin hannu na yana niman faɗuwa, ya kashe flash ɗin wayan shi kafin ya fara ɗauka na a hoto yana dariya ƙasa_ƙasa,
*********
Abban Jannat dan Allah idan safiya tayi kaje ka ɗauko Saudat a gidan mutane, ni wallahi tunanin halin da take ciki ya addabe ni duk na kasa samun sukuni”
“Baby mitan ma cikin dare ba zan huta ba? Da ɗin a nan take zama tare da ke da kika bi kika ɗaga min hankali? Idan kika kwantar da hankalin ki yau ɗin nan zaki ga sun dawo da ita har gida,
ɗauko min ruwan da yafi wannan sanyi please”
Miƙa mishi abulkhairi tayi wanda da ta ɗaga kafaɗun ta daga gado yake buɗe ido ta tashi da bottle water dake gaban shi ta ɗauko mishi wani daga fridge sannan ta zauna, tare da yin tagumi tana ƙare mishi kallo
“Inama ace nima zan samu azumtar watan Ramadana a kan lokaci da yanzu bani da sauran fargaban biya daga baya”
“Uhm..uhm kada ki sake irin wannan maganar Allah ya fiki sanin dalilin kawo miki aihuwa a wannan lokacin kuma babban godiya shine Allah ya sauƙe ki lafiya har kina da daman biya daga baya”
Girgiza kai tayi tare da tambayar shi “amman zaka min rabi ko baby? Tunda kaga kaine sanadi duk da Allah ne yayi ikon shi a kanmu”
“Ai ko duka kike so ayi miki za’a san yanda za’ayi, amman maganar mu ta jiya tana nan ko dan ba zan iya haƙurin jerawan nan ba tun yau nake son ayi budget”
Taɓe baki tayi tare da kawar da kanta gefe tana sakin dariya, rigimar Khamis dai sai shi,
*****
Dariya Zayyad ya saka ganin yanda duk na rikirkice na gigice don azumin yau na buga ni daman bani juran yunwa,
Zama yayi a kujeran dake gefen nawa, sai ya leƙa fuska ta ya kwashe da dariya,
Amman Sitifid akwai ɗan rainin hankali……..🤦🏻♀️1
#vote
#share
#comment
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
17🧝🏻♀️
Shi ko tausaya min halin da nake ciki bayi yi, yau ɗinnan saida nayi wanka sau uku da ruwan sanyi saboda yanda zufa ke tsatstsafo min na azaban yunwa,
“Sannu ko Saudat ɗina, Allah ya bada lada” Ya fada tare da tintsirewa da dariya,+
Gyara kwanciya nayi a kujeran na juya mishi baya ni a yanzu ƙarfin magana ma bani dashi saidai ta zuci,
Sitifid kuwa don ya iya zalunci ai dole ya kira ni da tashi, babu komai a cikin sa banda mugunta zan gani idan na bar musu gidan su waye zai samu ya saka a gaba,
“Ayyah Saudaty ko dai za’a raba ma yara ne? Bani son azumin nan ya ƙarasa min ke a barni da asara, idan kinga ba zaki ba ki faɗa min sai mu faɗa wa hajiya ayi haƙuri da na wannan shekaran ba zaki iya ba”
“Dake ma Hajiya nake azumin ko?” Na tambaye shi cikin kasasshiyar murya,
Lumshe idanu yayi ya ƙara faɗaɗa murmushin sa, oh his dimples… Kawar da kaina nayi daga gareshi shi kuma daman abinda yake so kenan yaji murya na kuma yaga fuska ta,
“To shknn idan kinga zaki iya amman kuma idan kina da buƙatar zaga bayan gida ni zan taimaka miki da abin sha harda abinci ma idan kina so kinji Saudaty bani son ganin ki cikin wahala ko kaɗan”
Ban samu damar bashi amsa ba muka ji muryan Nana ta bayan mu, juyawa yayi yana kallon ta sun shigo tare da Sulthana suna tsaye bakin ƙofa idanun mayyan curr a kanshi tsananin mamaki ya hana ta motsi, muna haɗa ido dasu na tashi na bar parlorn dan har yanzu mugun tsoron Nana nake ji,
Ƙarasowa ciki suka yi Sulthana ta nemi wuri a kujera 2 sitter da yake zaune ta zauna daff dashi jikin su na gogan juna, tsaki yaja cikin ɓacin rai ya matsa yana wurgan ta da mummunar kallo yana cikin yanayi mai daɗi wannan ƴar anacen tazo ta katse mishi,
“Ya Zayyad me kake yi a nan? Ko wani kake jira?”
Maido da mugun kallon yayi gare ta jin tambayar rainin hankalin da take mishi, kafin yace wani abu Sulthana ta rufa mata da
“Maganar me kuke yi da wancan yarinyar darling?”
“A cikin ku akwai mai bina bashi ne da zaku tsare ni da tambayoyi?” Ya faɗa haɗe ta tamke fuskar shi tamau kaman bashi bane suka shigo suka same shi yana dariya,
Basarwa Sulthana tayi tana ƙaƙalo murmushi ta ɗaura hannun ta saman kafaɗar shi tare da kwantar da kanta a jikin shi
“Ba wannan ba darling, akwai maganar da daman nake son muyi da kai…”
Bata samu damar ƙarasa magana ba ya miƙe shima ya fice don yana tunanin idan yaci gaba da zama dokin zuciya zai iya saka shi ya naɗa ma wannan wawiyar yarinyar duka da bata san mutuncin kanta ba a watan Ramadana ma ba zata shiga hankalinta ba,
moreover zata iya haddasa mishi fitina yana zaman_zaman shi yanzu su ɗago babban yaya ba shiri ya dawo daga tafiyar da yayi yazo ya sauƙe mishi buhun masifa,
shi ya tsani mace mai zubar da kanta shiyasa ko tarayyan ƙannen shi da wa’innan yaran bayi so amman babu yanda ya iya Allah ya riga ya haɗa alaƙar su, idan da shi fitinanne ne duk yanda yasan zaiyi sai ya shiga tsakaninsu kuma ya nesanta ƙaramar mara kunyar nan daga gare shi,
STORY CONTINUES BELOW

Babu kowa a parlorn su sai tv dake kunne an saka karatun ƙur’ani, zama yayi a kan kujera tare da jinginuwa ya lumshe idanuwan sa don bawa zuciyar sa daman hutawa, ya san saudat ba lallai ne ta zamo matsala ba, yarinyar da yarinta sosai a jikin ta yana ganin shiga zuciyar ta abu mai sauƙi ne sosai duk da ba yanzu ya shirya ma auren ta ba, sai nan da wasu shekaru masu zuwa,
Saidai babban yaya babban matsala ne, ya ma rasa ta ina zai fara tunkarar shi da maganar idan lokaci yazo, ya rasa ta wani siga zai fito mishi da zarar ya dawo daga tafiyar da yayi yayi masa jagora gidan su boɗɗi a san dashi don kar wani yayi mishi shigar sauri,
Abu mai sauƙi ne Sulaiman ya tarwatsa duk wani farinciki nashi don samun lafiyar shi, kuma samun Saudat yana cikin abubuwan da idan har yana ɗauke da matsalar shi ba zai taɓa yiwuwa ba,
Fatan shi ɗaya Allah yasa Sulaiman ya fahimce shi kuma ya bashi dama don ya jarraba sa’ar shi ko shima yana da rabon ganin jinin shi a doron ƙasa,
*****
Banji daɗin raba ni da Sitifid da suka shigo sukayi ba, dukda tsokana ta yake yi but I’m enjoying his company, tun yanzu har kewar shi ta fara shigana,
Na san wasu zasu yi tunanin nayi saurin saka shi a raina kwana biyu kawai da haɗuwan mu amman kuma mutane irin Sitifid ɗaɗɗaya ne a cikin gidajen masu kudi,
Mutum ne mai sauƙin kai kuma ga daraja ɗan Adam a duk gidan bayan iyayen su shi da Ruma da boyfriend ɗina junior ne kawai basu nuna min banbanci sai kuma aunty Zaytoon,
Ba wani abun mamaki bane don a zaman kwana biyu na fahimci halin kowa a cikin su, zan iya cewa wahalan rayuwa da nasha a baya da kuma ƙwarewa da na samu a wurin mahaifi na ne ya koyar dani hakan amman kuma duk cikin su ma babu wanda yayi ƙoƙarin ɓoye min halin shi don basu ɗauke ni da muhimmanci ba,
Har ƙarfe 5½ ina kwance sallan la’asar ma da ƙyar na iya daddafawa nayi inajin hanjin ciki na kaman zasu tsinke, a yanzu haka suna ta haɗa abincin shan ruwa amman ba zan iya fita taimakon su ba don idan idanu na sukayi karo da abin in nan akwai matsala, duk bayan mintuna goma sai na kalli agogo,1
**********
Fitowa daga ɗakin yayi da laidoji a hannun shi ya nufi kitchen yaga ko tana can, turus ya tsaya ganin Yusrah jikin turmi tana daka ga abulkhairi sai zunduma ihu yake yi amman bata da niyyan sauraron shi,
Ajiye laidojin yayi baiyi mata magana ba saboda ganin yadiko a wurin ya ƙarasa ya since yaron shi daga bayan ta ya fita yana rarrashin shi, ganin haka yasa yadiko tace ta sake aikin ta bishi don babu yanda batayi da ita ba ta bari amman ta ƙi,
“Saboda ban je na dawo da saudat ba ko? Shine zaki yi ma ɗana wannan horon, yaron 6 days amman kika shiga kitchen dashi”
“To babu wanda zai taya yadiko aikin ne yayi mata yawa wallahi tun safe take ta ɗawainiya ga namu ga na gida, shiyasa naje na ɗan kama mata wani abun kuma Abul yaƙi barci balle na kwantar dashi a ɗaki”
“Yanzu karɓe shi ki shayar dashi” babu musu ta karɓe shi, yace “na faɗa miki zainab zata zo anjima kuma zata zauna har lokacin da Saudat zata dawo gidan nan dan Allah kiyi haƙuri kada mutanen nan suga rashin haƙurin mu, ai abin daɗi ne ma a gwada ana son naka, ba wani cutarwa ne yake samun ta a gidan ba”
**********
“Zaku iya tafiya”, ya bada umarni a taƙaice, yana kallon bayan su har suka gama fita aka rufo miki ƙofar room ɗin sannan ya ɗaga wayan shi yana dubawa,
Ajiye wayan kawai yayi ranshi yana daɗa ɓaci tunda ya baro gida ko sau ɗaya iyalinshi bata nime shi ba, bata damu ta san ko ya iso lafiya ko akasin haka ba, ba zata nime shi taji ko yana cikin wani matsala ko damuwa ba, shi babba ne kuma mahaifin wasu amma ba’a girma ma kulawa ko tsoho ma zai buƙaci kulawar iyalin shi ballantana shi mai jini a jika,1
Yana da daɗi ka gwada kulawa ma abokin rayuwar ka hakan zai sanya ko yaushe ka zama a cikin zuciyar shi, it feels so good kasan kana da muhimmanci a wurin wani koda kuwa wanene idan kayi nisa ko yaya ne a nuna anyi kewar ka, amman Sadiya bata san wa’innan abubuwan ba ta saka wasu damuwa daban a gaban ta,
Yana fatan Saudat ɗinshi ba haka take ba, da kuwa idan ya aure ta tafara bashi kulawar da yake buƙata zai bawa sadiya mamaki, zaiyi mata abinda bata tsammani wanda zai saka ta shiga taitayin ta dole,1
tama gode ma Allah shi ba mai bin mata bane amman a yanzu kashi 90 na matan waje dake bin maza sunfi matayen su na cikin gida basu kulawa da tarairaya da kuma iya nuna musu soyayya ba don komai ba sai dan sunfi su sanin darajan mazan,1
Ballanta shi mai shiga wurare garuruwa da ƙasashe da dama donyin business ɗinsu, babu kalan matan da bayi gani, kyawawa wanda suka fi matar shi kyau nesa ba kusa ba da kuma wa’inda basu ma kamo ƙafan ta a kyau ba, amman suna ƙoƙarin suga sun samu mazan da zasu basu kulawar ma ya gagara,
ita matar ɗaki tana ganin ai bata da wani sauran damuwa tunda ta riga ta same shi har tana da yara dashi yanda rabuwa da ita zaiyi mishi wahala, amman meyasa ba zata yi ƙoƙarin mamaye zuciyan shi ba tunda tana da daman hakan?? Ba’a taɓa tsufa ma soyayya!!!2
*****
A ranar muna cikin shan ruwa babban yaya ya kira video call ta system ɗin Batool, ban sani ba ashe dalilin kuran don ya samu gani na ne amman bawan allan nan daga an juyo da screen ɗin fuska na don na gaida shi yayi disconnecting ɗin kiran,
daman nasan hakan zata faru don na lura kaman yafi Nana tsana ta, shiyasa ni ko inuwa ɗaya dasu bani son zama dan gudun wulaƙanci,
A taƙaice dai yauma kwanan gidan nayi, washe gari ma suka hana ni tafiya duk yanda na matsa saboda shirin sunan babyn aunty Yusrah, ban tashi komawa gidan ba sai washegari da yamma bayan ƴan suna sun gama taruwa muke je nida Ruma,
Bata daɗe ba ta koma gida amman tsantsar takuri na Zayyad yasa washegari suka yi list ɗin kaya da za’a kai mata harda takalma suka turo dashi ba tare da Hajiya ta san komai a kai ba,
Ai kuwa buƙatar su ya biya, don da aka kawo kayan ni aunty Yusrah ta tura na kai musu daga nan kima suka ci gaba da riƙe ni,
A hankali na fara sabawa da baƙin maganan Nana da Sulthana da kuma zagin Fa’iza wanda babu wanda ya tsallake shi saidai idan bai faɗo ta kanka ba,
Zayyad lokaci ɗaya ya shiga zuciya na yayi min mamaya ba tare da na sani ba, saboda wani mummunan sabo ne ya shiga tsakanin mu a cikin kwanakin da basu fi a ƙirga su da yatsu ba,
Hhh saboda yanayin da na tsinci kaina na cewa na taɓa soyayya da kuma aure na san banyi yarinta ma soyayya ba dukda kuwa su ta nasu fuskan ba haka suke gani ba, amman na san son sitipid ma aikin banza ne don ba zan taɓa samun shi ba, amman ita zuciya bata da ƙashi, sau da yawa tana saka kanta a abunda baka so ta shiga ba wanda zai saka ka zubar da hawaye mara adadi,
Ban sani ba ko idan ma buƙatar nawa ya biya irin na baya za’a yi, yanda na dinga buri da mafarkin zama ta yarima wanda daga baya kuma hakan ya juye ya zamo min baƙin ƙaddara, ina tsoron soyayya ina kuma tsoron aure ciwon da suka ji min a zuciya har yanzu basu goge ba ballanta na ƙara wani a kai,
Ko wace rana ni da Zayyad mukan zauna can cikin garden yanda mutane basu fiye zuwa ba babu wanda zai san muna can, mu taɓa hira sosai hakan sai ya saka duk yunwa da galabaitan azimi da nake ji ya gushe kuma na ƙarasa wunin Ranar cikin farin ciki da annashuwa,
17/Ramadan/1442
A yau aka kai azumi 17, a yau kuma wannan sarkin zafin babban yaya ya dawo,
Zaune muke da Hajiya a bedroom ɗinta ta tasa ni a gaba hannun ta ɗauke da kwalin magani ni kuma nawa da takardan tayi na karanto sayi iffet (side effect) dake jikin takardan taji saboda glasses ɗinta bayi kusa kuma bata son fara amfani da magani bata san illolin shi ba dukda kuwa doctor ne yayi prescribing,
Ni kuwa sai zufa nake haɗawa na rasa ta ina zan faro, shiyasa nifa ko karambanin turanci bani son yi a gidan nan……..🤦🏻♀️
3
#vote
#share
#comment
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Mrs Naseer, mrs abdulwahab, mrs S hapsy, mrs usman, mrs bash, and all other MRS’s😂 wannan shafin taku ce tare da*
*Ummu hafsat & Hussaina mai jama’a*
Inayin ku sosai dearies, thanks for the love ❤️💙+
18🧝🏻♀️
Nafi 5 minutes riƙe da takardan na ƙura mishi idanu kafin da ƙyar na haɗa letters ɗin na farko cikin rawar murya nace
“He’a_da_ca_he, (headache)”
Saida nayi shiru tare da jan dogon numfashi na furzar sannan naci gaba da karantowa,
“ji_na’echa_o_masti’a(gynaecomastia) di_arrrr_he’a (diarrhea)
To dai na ƙarshen yayi min kama da nonses (nausea)”
Da ƙarfin guiwana na ɗago bayan na gama karantawa sai ji nayi an kifa min ranƙwashi sau biyu a jere zafin su har ƙwaƙwalwa na, na dago naga wannan zazzaɓin, babban yaya tsaye a kaina yanayin fuskar shi kaɗai ya isa ya nuna maka ɓacin ranshi ni ban ma san lokacin da ya shigo ba dan banji sallamar shi ba,
Hajiya kam, al’ajabi, mamaki, firgici da takaici ne suka hana ta magana, she can’t believe mai shekaru irin nawa ƴar birni wanda kuma tana da tabbacin ina zuwa makaranta amman ban iya karatu ba,
“Meye wannan kike yi? Baki da hankali ne ko kuma ance miki ilimi abun wasa ne ko kuma ita ɗin sa’ar wasan ki ne da zaki saka ta a gaba kina mata wannan shirmen?”
Kasa kallon sulaiman nayi na sunkuyar da kaina hawaye na taruwa a idanuwa na,
“Baki ji ina miki magana ne da ba zaki amsa ni ba? Do you think it’s funny?”
“Haba babana kabi mata a hankali mana, meye na fushi a nan ta yuyu bata iya karatun bane, a wani class kike Saudat?” Ta tambaya tana kallo na,
Hawayen da suka gama taruwa min ne suka samu daman ɗigowa a kan hannu na da na ƙudundune shi a tsakanin cinyoyi na, kusan duk haɗuwa na da Sulaiman sai ya saka ni kuka, ina ƙoƙari sosai wajen ganin na kai zuciyata nesa kada na tsane shi amman abu na niman faskara,
Cikin tsawa ya sake tambaya ta sai a sannan na basu amsa da “primary 4”
Zaro idanu yayi cike da mamaki yace “mene? Babba dake kina primary 4!!? What’s your problem? ke wace irin daƙiƙiya ce wanda bata gane karatu as big as you are amman ace karanta simple abu baki iya ba?”
Ban san dalili ba amman abu kaɗan yana sosa min zuciya sosai, maganar da ya faɗa min ba ƙaramin taɓa min zuciya yayi ba na saka tafin hannuna na rufe fuska na hawayen dake ambaliya a idanu na suka jiƙa su,
“A wani dalili yasa har yanzu kike primary 4 kuma a wani makaranta kik..”
“Tashi ka fita a ɗakin nan Sulaiman”
Yaya zaka saka yarinya a gaba kana tozarta ta? Haka aka ce maka ake yi?”
Tashi yayi ranshi a bace wai yau shine da girman shi za’a yi wa faɗa saboda wata har a kore shi a wuri dan yayi scolding ɗinta,
Cike da taƙama ya nufi hanyar fita ina jin mummunan kallon da yake bina dashi a jiki na saida yazo daidai fita ɗakin sannan yace “stupid girl” ya fice, ban san lokacin da na fashe da kuka mai sauti ba shima yayi mun babban zagin nan,
STORY CONTINUES BELOW

Lokaci ɗaya naji tsanar shi ya dabaibaye zuciya ta, wani zafi nake ji a raina wanda banji wannan zafin ba lokacin da sitipid yayi min irin wannan zagin,
a rayuwa ta bayan yarima da dangin shi ban sake tsanan wani ba kaman sulaiman, ban taɓa ganin mutum mai baƙar zuciya irin shi ba kuma ƙarara yake nuna min tsana da ƙyashi tunda ya tsane ni nima na tsane shi,
Buge min baki Hajiya tayi don kuka na ya fara damun ta, na toshe bakin da hannu na ina daɗa matsar kwalla, sai kuma ta janyo ni jikinta ta kwantar da kaina a saman cinyar ta tana lallashi na,
“Kiyi haƙuri kiyi shiru Saudat kinga na kora shi insha Allah ba zai sake takura ki ba kinji?”
Gyaɗa kaina nayi ina daɗa cusuwa a jikin ta, ko dan darajan Hajiya bai kamata na tsani ɗanta ba amman ba abin da zuciyata ya zaɓa min ba kenan
****
Mtsww shi wallahi duk tunanin shi yarinyar nan ta ko ina a haɗe take, kaman yanda take da kyan fuska haka take da ilimi da kuma wayewa amman alamu sun nuna yayi kuskuren fahimta,
Yaushe wahala zai ƙare mishi ne a kan mace? Yaushe ƙwaƙwalwar shi zata daina ɗaukan caji saboda sakarcin mata? Wurin Sadiya ba sauƙi wurin saudat ma bai huta ba? When will he get the PERFECT wife? Ya tambayi kanshi,1
(but is he a perfect husband to deserve a perfect wife???)
Ɗaga wayan shi yayi ya kira wani number bugu ɗaya aka ɗauka, bai tsaya amsa gaisuwan mutumin ba yace
“Ina son ka samo min admission na best school dake garin yola na baka zuwa gobe da safe” kitt ya katse wayan, sannan ya zuba a kujerar tare da cire hulan kanshi yana huci, dole ya canza rayuwar Saudat gaba ɗaya don ba zai iya zama da bagidajiya ba,1
**********
Me ya kawo ta nan wurin a cikin daren nan? Ya tambayi kanshi lokacin da ya hango ni zaune a kan farin ceramic bench da kullum muke zama a kanshi cikin garden,
Juyawa yayi ya kalli Ruma ganin yanda na kifa kaina ina kuka, yace “sis mai ya same ta ne?”
“Wallahi ban sani ba ya Zayd shiyasa ma kaga na kira ka na tambaye ta yafi sau a ƙirga taƙi cemun komai, tun da aka idar da asham ta fito daga ɗakin hajiya take kuka”
Cikin nutsuwa ya ƙaraso wurin wanda ya wadatu da farin haske ya zauna a kujeran dake kallon nawa tare da ƙura min ido, zafin sheshsheqar kukana har cikin zuciyar shi yake jin yana ƙona shi,
Handkerchief ya zaro daga aljihun shi ya miƙa min sannan ya kira suna na cikin wani murya mai taushi,
Bansan Zayyad yazo wurin ba hakan ya saka ni ɗagowa da sauri na zuba mishi rinannun idanuwa na ga hawayen dake faman sintiri saman fuska na,
Da yana da dama da zai haramta min zubar da hawaye gaba ɗaya don bai dace dani ba, a yanzu haka ji yake yi kaman ya rungume ni tsam a jikin sa don bani damar fitar da ciwon dake zuciya ta,
da ace na halatta mishi da zaiyi min irin rarrashin da zai mantar dani duk wani sauran damuwa na, yana da burin dasa farinciki mai ɗorewa a cikin rayuwa ta ba zai so wani abu ya ruguza wannan burin ba,
Karban handkerchief ɗin nayi na share hawaye na sannan na miƙa mishi amman bai karɓa ba cikin nutsuwa ya sake kiran sunana a karo na biyu,
” zaki iya faɗamin abin da ya same ki har yayi sanadin zubar hawayen ki?”
“Babu komai ya Zayd”
“Babu komai kike kuka? Ko an taɓa kuka babu dalili?
Ƙura ma jikin bench ɗin da yake zaune idanu nayi don ba zan iya jure kallon cikin idanun shi ba,
“Ya Zayyad da gaske ni daƙiƙiya ce?”
Waro idanun shi yayi tare da faɗin “what?! Who the h**l told you that?”
“Ko da yake ma ai gaskiya ce tunda bani gane karatun boko ban iya turanci ba, amman ina da haddan alƙur’ani na san abubuwa da yawa game da addini na kuma nayi karatu mai zurfi a kansu saidai na lura a wurin mutanen birni wanda baiyi karatun boko ba shine daƙiƙi”
“Could you stop beating around the bush and tell me waye ya faɗa miki wannan kalman?”
Auu ashe ɗazun ma tambaya na wanda ya faɗamun yayi da turanci?
“Zaki faɗa min ne ko sai ranki ya ɓaci?” Ya faɗa cikin ɗan ɗaga murya jin nayi shiru “Wa ya bada daman wani ko wata ta faɗa miki wannan mummunan kalman a cikin gidan nan, a kan wani dalili?
ta yaya ma za’ayi na faɗa ma sitifid abin da yayan shi yayi min? Wani tunani shi ɗin zaiyi a kaina? Ko dama ace zai yarda dani bai kamata daga zuwa na cikin gidan in kawo saɓani a tsakanin su ba dan na tabbata yanda na hango ɓacin rai a idon sa ba zai bar wanda ya ɓata min rai haka nan ba,
“Ni na haƙura na yafe, ka barshi kawai ba kowa”
“To ni ban haƙura ba, ban kuma yafe ba duk wanda ya zage ki ko waye shi a gidan nan tabbas sai ya fiskanci hukunci”
**********
A firgice ya fito daga bedroom ɗin ganin bayi ciki, cikkn tashin hankali yaje yana buga ƙofar aunty Amarya bugun da ya saka ta yanke Sallah babu shiri ta fito a kiɗime don idan taji irin haka tabbas Zayyad ne,
Fitowan ta ke da wuya taci karo da sulaiman tsaye sai zazzare idanu yake yana tambayan ta inda Zayyad yake sai dafe ƙirji tayi tana salati cikin zuciyan ta tana maimata ‘an kuma, Allah yasa ba sake shiga cikin wani matsalan yayi ba, kuma Allah ya kare mata shi a duk inda yake’
Ganin haka yasa ya fita da gudu yana kwala masa kira har ta part ɗin Hajiya sai da ya duba amma wayam babu shi babu labarin shi, haka ya koma bakin gate don sake tabbatar da bai fita ba duk da an faɗa mishi hakan kafin ya shigo,
*****
“Ba zaki faɗa min ba ko?” Ya sake tambaya ta,
Sai a yanzu nayi nadaman faɗa mishin da nayi ganin yanda ya tashi hankalin shi sosai ina ci gaba da zubda hawaye, gashi saboda sakarcina na ɗauki ƙaramin abu na mulmula shi ya koma babba, sai me dan yace min daƙiƙiya? Da ace na faɗa ma Zayyad wani ya kira ni sitifid ban san me zaiyi ba idan yaji babban zagin nan ai daƙiƙiya ƙaramin alhaki ne,
Juyawa yayi zai tafi nayi saurin shan gaban shi ina bashi haƙuri
“Dan Allah a bar maganar nan ya Zayyad ko na faɗa maka ma ba abin da zaka iya yi, kada kayi fushi nace fa na yafe”
“Zaki faɗa min ne ko ba zaki faɗa min ba?”
“Ya Sulaiman ne!” Na faɗa cikin ɗacin murya,
“Ya Sulaiman kuma? Da girman shi da hankalin shi? To a kan mene zai kira ki daƙiƙiya me ya haɗa ki dashi?”
Nan na kwashe labarin abin da ya faru ɗazu a ɗakin hajiya na faɗa mishi
“Ni ba ƴar garin nan bane ya Zayd, a garin mu ba’a karatun boko ban fara ba nima har saida na dawo garin nan da zama gidan ƴan uwana sannan suka saka ni a makaranta, amman a haka ne na zamo daƙiƙiya? Ko kowa ma irin wannan kallon yake min”
Harara ya jife ni dashi yace “look at you ance miki kowa halin shi irin na babban yaya ne?
Ni na riga da na san da hakan tunda na tambaye ki kin bani amsar gaskiya kuma ina fahimtan fashin ƙwarewar ki idan muna zantawa amman tunda har yanzu baki fasa makarantar ba babu wanda ya san gaba idan daɗa maida hankali maybe zaki shiga sahun masu ilimin, bai kamata ya jife ki da wannan kalamin ba kwata_kwata zanje na same shi muyi magana”
“A’a kada kace mishi komai dan Allah”
****
Da gudu ta ƙaraso inda muke tsaye ta riƙo hannun shi ta fara janshi don su bar wurin,
“Ya Zayyad mu tafi ga babban yaya nan zuwa yana ta niman ka a cikin gida”
Ko gizau baiyi ba ya tsaya a wurin yana jiran ya ƙaraso dan ya fuskance shi yaji a wani dalili zai kira ni daƙiƙiya,
Da tsananin mamaki sulaiman yake kallon su har ya ƙaraso wurin da suke tsaye yana bin Zayyad da kallon sama da ƙasa sannan ya tambaye shi
“Mai kake yi a nan Zayd?”
“Yaya kai ya kamata na tambaya abin da ya haɗaka da wannan” ya faɗa tare da maido da duban shi wuri na………🤦🏻♀️1
*Me zai faru gaba*
*Me zai faru gaba*
*Me zai faru gaba*😝😂
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
19🧝🏻♀️
“Wannan wa?” Ya faɗa yana duba wurin da Zayyad ɗin yake nuna mishi don shi baiga kowa ba,
guduwa kenan Saudat tayi ta barshi a wurin shi da yake shirin sama mata adalci amman ta tafi dukda yace mata ta tsaya wato bai isa da ita ba kenan?+
“Wai maganar wa kake yi ne Zayd? Ni banga kowa a nan ba, moreover babu abin da ya haɗa ni da kowa a gidan nan, kana dai lafiya ko? babu abin da ya same ka?” Ya tambaya yana taɓa gefen fuskar shi cike da kulawa da tausayawa,
“Babban yaya daman yarinyar nan ce Sa…”
“Babu komai fa babban yaya, i was just pulling his leg wasa nake mishi nace naga ran aunty Batool a ɓace kuma ina tunanin akan faɗan da kamata take fushi, to da yaga wucewar ta yanzu shine yake tambayar ka amman babu wani abu” Ruma ta faɗa tana murmushin yaƙe, amma wani zufa ne yake tsatsafo mata ta cikin jikin ta yanda taga Sulaiman na mata kallon tuhuma da rashin yarda, ita dai fatan ta kada gaskiyar magana ta fito a yanzu idan ba haka ba kashin su ya bushe,
“Yaushe ne dawowa na garin nan gaba ɗaya da har nayi faɗa ma Batool?” Ya tambaya fuskar shi babu alamun wasa,
“Uhmm wasa kawai nake mishi”
“Wasa fa kika ce? Are You out of your mind? ko kinga munyi kama da sa’oin wasan ki da zaki saka mu a tsakiyar maganar vanzan ki making my brother go against me? Do you think it’s funny?”
Sunkuyar da kamta ƙasa take yi jin yanda yake daka mata tsawa kaman bai san dare bane, a hankali yanda ba zata ƙara tunzura shi ba tace “I’m sorry babban yaya ba zan sake ba”
Tsaki yaja cike da haushin ta yace ta ɓace masa da gani, siɗin_siɗin ta ja hannun Zayyad wanda yake tsaye dumbfounded a wurin ya rasa wani dalili ne ya saka Ruma yin ƙarya ma sulaiman kuma me yasa ta ɓoye mishi laifin da yayi ma Saudat,
Bai san dalilin ta na yin hakan ba amman dake shi mutum ne mai dogon nazari da tunani yasa bai katse mata hanzari ba ya bita suka bar wurin,
*****
Rufo ƙofar ɗakin shi tayi bayan sun shiga ta juyo tana kallon shi da already ya sama ma kanshi mazauni a armchair dake ɗakin yana jiran yaji ba’asi,
“Ya Zayyad me yasa zaka yi ma babban yaya maganar Saudat bayan na kira ka ne kawai don kayi maganin matsalar ba ka ƙara faɗaɗa shi ba, haƙuri fa kawai zaka bata daga ta bar kuka magana ya wuce”
“Ke! Ni sa’an ki ne da zaki na scolding ɗina?”
Turo baki tayi cike da shagwaɓa tace “I’m sorry tunda yanzu nice kuma mai laifin, shi yayi mun kaima zaka ƙara min”
“Forget it, Just tell me the reason that makes you said that lie, me yasa kika ɓoye maganar nan?”
“Da ace na barka ka tuhume shi da kaine zaka shiga matsala ko ka manta ne? Cikin sharuɗoɗin harda kiyayewa na daga alaƙa keɓantuwa ko kuma raɓan opposite sex wanda ba muharraman ka ba? Muharraman kan ma yaya aka ƙare da matsalar ka?1
STORY CONTINUES BELOW

Duba ka gani fa har yanzu baka gama warwarewa ba, dalilin da yasa babban yaya ya dawo garin yola kenan ba shiri kuma daga zuwan shi ka tare shi da zancen Saudat? Bayan kana sane da dogon kashedin da aka yi maka kada ka raɓe ta don sama ma kanka kwanciyar hankali?”
“And now you are treathning me huh!” ya faɗa tare da jinginuwa da jikin kujeran ” ni banda right ɗin yin soyayya ne? Shikkenan saboda wata jarabawa da Allah ya ɗaura min sai ba zan so raya sunnar ma’aikin shi ba ni ba zanyi aure ba?
Ban ƙetare wani doka da babban yaya ya shimfiɗa min ba don har yanzu ban faɗa ma Saudat ina son ta ba, nafi son sai sauran shekaru biyun da aka ɗiba min sun cika kafin na bijiro mata da buƙatata ta amince da aure na nasan lokacin ta ƙara girma da hankali kuma insha Allah ba zata ƙi amincewa ba saboda nasan itama tana jin wani abu a kaina”
“Duk ka ajiye wa’innan a gefe, nima ina bayan soyayyar ku ina son ganin kunyi aure wata rana, kuma zan tallafa maka da goyon baya har duk wasu burikan ka su cika yayana, amman ka ajiye wannan abu a matsayin sirri tsakaninmu mu uku gudun kada ka saka boɗɗi a matsala,
Yanzu kowa a gidan nan ta lafiyan ka yake, harta Sulthana da aka san da zancen auren ku an ajiye ta a gefe burin kowa yanzu shine ganin ka rabu da wannan matsalar idan allah yaso,
idan har ka bari aka san ka fara son saudat to za’a nisanta ku da juna dan an san tilas wata rana zata san da matsalar ka kaga sirrin mu ya fita daga gidan nan kenan, kuma a dalilin haka babban yaya zaiyi mata hukuncin da ba zata iya ɗauka ba batare da yayi la’akari da cewa ita ba jinin mu bace”
“Ni kuma dake lusari ne na zamo mara amfani sai ina gani ya cutar da ita ban ɗauki wani mataki ba?”
“Kana son saɓani ya shiga tsakanin ku ne saboda ita?”
Murmushi yayi yace “Ruma kenan! A tunanin ki kaman yanda Ya sulaiman yake a wurin ku haka yake a wuri na? We are more like friends than brothers yanda tsakanin mu yake kaman babu tazaran shekaru, har gobe yana faɗa min bayi da wani wanda ya kaini ta yaya za’ayi boɗɗi ta zamo silar samun saɓani a tsakanin mu?”
“Indai a kan matsalar ka ne wallahi zata zamo”
Ta ƙarasa gaban kujeran shi ta zauna saman carpet tare da ɗaura hannun ta a saman guiwowin shi ta ɗan ƙara karya murya dan ta samu nasarar lallaɓa shi ta lura shima wani ɗan taurin kai ne,
“Ya Zayyad”
Ɗagowa yayi ya kalle ta tare da amsawa da na’am saboda yanda yaji tayi ma sunan wani irin kira
“Ya Zayyad dan Allah, i beg you kabi komai a hankali please kada ka ɓata rawan ka da tsalle just keep praying insha Allah saudat taka ce”
“A bari ya huce shi ke kawo rabon wani, ba zan juri rasa ta ba”2
“Ba zamu ma bari ya hucen ba insha Allah, babu zancen matsala babu batun wata Sulthana, a gaba kai zaka auri boɗɗi in Allah ya yarda”
Jan dogon numfashi yayi ya furzar tare da daɗa zamewa a kan kujerar ya faɗa duniyar tunani, abubuwa sai daɗa dagulewa suke yi
**********
Da gudu na shiga part ɗin ta ƙofar baya ina tafiya ina waiwaye kada a biyo ni, da ace wannan zazzaɓin yaji na kai ƙarar shi da yau tusa na ya hura wuta,
Shiga na parlor ke da wuya naci karo da TV na playing film ɗin hausa ga su gabon sai zuba love akeyi, babu kowa a parlorn kuwa sai aunty Zaytoon tana kishingiɗe tana latsa wayar ta,
wayyo daɗi kashe ni!! Ban san lokacin da hannu na ya kai ya share guntun hawayen idanuna ba na gyara zama na saman kujera baki na buɗe na shiga kallo don na ma manta da duk wani baƙinciki da na kwaso da takaicin an kira ni daƙiƙiya kuma Sitifid, heyy dariya nake harda shewa ina tafa hannuwa don abun yana kawo light dake aunty Zaytoon bata da damuwa yasa ko a jikin ta ta gyara zaman earpiece ɗinta taci gaba da danne_dannen waya,
STORY CONTINUES BELOW

Kaman daga sama na ganshi ƙeƙam a gaba na, hanjin ciki na saida suka kaɗa nayi saurin runtse idanuwana don nayi tunanin yanda naga fuskar shi a bai_bai ɗin nan zabga min mari zaiyi,
Shiruu nayi ƙirji na yana lugude ina jiran naji sauƙan mari amman shiru, sai jin hannun shi nayi ya fisge remote ɗin dake hannu na ya canza channel sannan ya wurge ni dashi,
Bai tsaya a ko ina ba sai a kan goshi na, an gudu ba’a tsira ba kenan, matso ƙwalla na fara yi ina sosa wurin da ya jife ni don ba ƙaramin ƙwaluwa nayi ba na zuba mishi idanu a karo na farko ina ƙare mishi kallo,1
Ga kyan siffa sai baƙin hali dukda bai kai ya Zayyad ɗina ba, don wannan yana da ɗan jiki duk da ba sosai ba amman Zayyad matsalar shi kaɗai wanda ke sanya shi rashin lafiya kusan kullum ya isa ya saka shi tsomarewa,
“Ke!! ba zaki bar kallo na ba?!”
Ya faɗa a fili cikin zuciyar shi kuwa kasa jure irin saƙƙonnin da idanu na suke aika mishi yayi, yana jin wani abu mai ƙarfi na tsirguwa har cikin jinin shi amman ba zai iya jurewa ba bayi son girman shi ya faɗi a gaba na da kuma ƙanwar shi,
“Ke ƙwaƙwalwar kifi gare ki ko? Duk abin da ya faru ɗazu bai ishe ki ishara ba shine kika dawo kika ƙara maidar da hankalin ki gaban tv saboda kina son tabbata a daƙiƙanci baki son yin karatu ko?”
Ina jin wannan kalmar ya sake fitowa daga bakin shi na saki kuka, Zaytoon tana kallo na cike da tausayi amman babu abin da zata iya don itama bata fi ƙarfin a haɗa da ita ba,
Bai damu da kukana ba a yanzu hawayen ta sun daina ɓata mishi rai don tunda ta zubar a ranar farko yake da tabbacin zata ci gaba da zubarwa yaci gaba da cewa
“To bari kiji daga yau nayi miki iyaka da kallon TV a gidan nan very soon zaki fara karatu kuma dole ki maida hankali ki san abinda kike yi don ba zan lamunci zaman ki haka ba”
Da faɗan haka ya fice daga gidan gaba ɗaya, haka aunty Zaytoon ta zauna tayi ta lallashi na daga ƙarshe a bedroom ɗinsu na kwana bata bari hajiya taji abun da ya faru ba ko kaɗan, amman ni na saka ma raina da ikon Allah ko kwana ɗaya ba zan ƙara a gidan ba zan koma gidan aunty Yusrah,
18/Ramadan/1442
“Ban yarda ba ban amince ba kaji na faɗa maka, ka san duk yanda zakayi ka ɗauko ƴar mutane ka dawo da ita gida, kai kanka shaida ne na cewa bani barin ta taje ko ina bayan gidan iyayen matar ka, ba don jego ba ko gidan ka ba zan bari tazo ta zauna ba wallahi amman shine zaka ɗauke ta ka kaiwa wasu mutane can da basu san amfanin ta da muhimmancin ta ba? Ka san girman alƙawari kuwa Khamis?”
Sassauta murya yayi yace “ayi haƙuri Mama insha Allah a yau zanje na ɗauko ta, insha Allah ba za’a sake makamancin haka ba ayi haƙuri dan Allah”
“Gaskiya kam, aje a ɗauko min ɗiya ta ta dawo cikin mu dan a yanzu mune dangin ta, matuƙar ina raye ba zan taɓa bari saudat ta wulaƙanta ba”
“Insha Allah mama zan dawo da ita gida a yau ɗin nan”
Sallama sukayi ya kashe wayan sannan ya ɗago yana kallon Yusrah da ta sunne kanta ƙasa yace
“Kinji daɗi kin haɗa ni da mahaifiya ta ko?”
“Baby kayi haƙuri wallahi na gaji da zaman ta a can ɗin ne, kwata_kwata hankali na ya kasa kwanciya I’m feeling like she is not alright”
“Ai Shikkenan hankalin naki sai ya kwanta tunda kin samu cikar baurin ki idan ta dawo magana ta ƙare”
**********
Zaune nake gaban mirror bayan nayi wanka na saka kaya na fara tsara kwalliya wanda nake kowa wurin aunty Fa’iza da kayan kwalliyan Ruma wanda sai ta gama mini wulaƙanci ta zage ni son ranta kafin ta koya min,
Babu laifi na ɗan fara koyan wasu abu kaɗan daga ciki,
Buɗe ƙofar ɗakin ruma tayi ta shigo tare da sallama da shirin fita ta yafo wadataccen mayafi ta ƙaraso wuri na ta gyara min kuskuren da nayi sannan tace na raka ta,
“Ina zamu je?”
Ta san idan tace min gidan babban yaya ne ba zan je ba shiyasa kawai tace “gidan wata auntyn mu ne zan kai mata wani aika zaki raka ni ina?”
Da sauri na gyaɗa kai tare da miƙewa na zari hijabi na bita a baya na ma manta da zancen komawa na gida a yau wanda nayi alƙawarin sai na tada hankalin hajiya ta saka an maida ni muka fita ina mararin shiga haɗaɗɗiyar mota,
Muna fita muka ci karo da Sitifid wanda shima fitowar shi kenan zai shiga ya same ni, yayi kyau sosai cikin ƙananun kaya,
Cikin girmamawa da ɓoyayyar soyayya wanda ke madaƙe cikin zuciyata na gaida shi ya amsa feeling the same, sannan ya tambaye mu wurin da zamu je da sanyin safiya,
Ruma bata ɓoye mishi ba tace mishi gidan aunty Sadiya shi dake ya gane waye sai yace ba zamu je ba dukda kuwa ya san babban yaya bayi gida amman bayi son na sake shiga ɓacin rai yau ma,
Amman ni dake sahibar yawo ne haka nayi biris da zancen shi na ishe shi da mita da magiya da yasa bai so ba ya barmu muka tafi tare da mana addu’an Allah ya dawo damu lafiya…………🤦🏻♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Idan ba zaka iya amfanar mutum ba kayi ƙoƙari kada ka cutar dashi*💡
20🧝🏻♀️
Shatin karan hanci na saida ya fito a jikin glass ɗin windown motar saboda yanda na manna kaina a jiki ina kallon gari unguwannin mutanen nan kawai abun kallo ne, so silent and peaceful babu kowa a waje bayan masu tsaron mutanen cikin gidajen, wannan idan a ƙafa kake tafiya sai a sace ka babu wanda ya sani,+
Bamuyi tafiya mai nisa sosai ba muka ƙaraso gate ɗin gidan driver ya kutsa kan motar mu ciki, yana parking wani yaro yazo da gudu ya buɗe side ɗin da Ruma take yayi hugging ɗinta,
Jan cheeks ɗinshi tayi yana dariya
“aunty wacece wancan?” Ya faɗa tare da gwada ni da yatsa,
“Sunan ta Aunty Saudat ka gaida ta”
Babu gardama yaron ya miƙo min gaisuwa nikam tunani na ne ya ɓace yayin da na hango kamar zazzaɓi (Sulaiman) ƙarara a fuskar shi, saida muka fita daga motar na tambayi Ruma yaron waye tace min ai ɗan babban yaya ne kuma gidan shi muka zo,1
Saida na saki iska ban sani ba wallahi saboda tsoro cikin zuciyata ina jero addu’oi,
Ni Saudatu nayi shirin barin gidan su sitifid ne saboda zazzaɓi gashi kuma na kawo kaina har cikin gidan shi, hala ma dalilin da yasa Hamma Zayyad ya hana ni zuwa kenan naƙi ji,
A daidai entrance na main door naja na tsaya tsoro ya gama shiga na, na riƙo hannun Ruma da hannu na ɗaya wanda yake faman karkarwa saboda tsoro
“Gaskiya nikam mu koma ba zan iya shiga gidan nan ba”
“A kan me? Saboda babban yaya wai?”
Gyaɗa mata kai nayi “Allah a tsorace nake Ruma ba zan iya sake haɗa ido dashi ba”
“Habawa boɗɗi yayan nawa sai kace dodo? To kwantar da hankalin ki bayi nan wurin matar shi muka zo ba wurin shi ba”
Sauƙe ajiyan zuciya nayi nabi bayan ta muka shiga hannun ta riƙe da na Arif,
A hakince muka sami matar tasha lace ƴar ubansu jewelries ɗinta na gold sai sheƙi suke taci kwalliya tana baza wani ƙamshi mai daɗi harta ƙafarta hill shoe ne 4inchs kai kace wani wurin zata, amman ba daga nan ba Sadiya akwai iya ado da ɗaukar wanka saidai tana fama da wauta da ballagazanci gashi Allah ya haɗa ta da miji ɗan duniya,
“Sannu da hutawa aunty halima”
Murmushi tayi tare da faɗin “yauwa Rumaisa sannun ku da zuwa, lallai kam kin cika alƙawari kinyi sammako, ke da ƙawar ki ne?”
“Eh aunty itama zata taya mu ne”
“Very good na gode sosai, yaya sunan ki ƴammata?”
“Sunana saudat” na faɗa cike da jin haushin Ruma, ita da tace nazo na rakata ta kawo aika yanzu kuma naji ana maganar tayi kalan zazzaɓi ya dawo ya same mu?
“To muje ko?” Ta miƙe tare da jan hannu na, bani da wani zaɓin da ya wuce nima na bitan ba don raina ya so ba muka shiga bedroom ɗinta muka fiddo da kayan dake jakar da muka zo dashi, ashe ba aika bane kaya ne da zamu saka muci aiki gashi nifa tun yanzu na fara jin azumin nan,
STORY CONTINUES BELOW

A kitchen muka riski Sulthana da Muna, ta gama zaman banzan ta cikin gidan su sitifid bata samu komai ba shine ta haƙura ta dawo, yanzu haka sunyi rakace_rakace a kitchen ana ta hidiman haɗa abinci kala_kala saboda da rana Sulaiman zai tarbi wasu clients ɗinsu arna da zasu zo gida su tattauna hidiman business shine fa yace Sadiya ta shirya musu abinci abun harda gayya, bayan ƙannen ta biyu da kuma maids ɗinta,
To fa gani ga ƙaramar kishiya ta, tun da Sulthana ta lura da kusanci na da Zayyad ta ɗora min karan tsana dan ta lura yafi bani lokacin sa fiye da abubuwa da yawa bare azo kanta da takan yi kwana uku bata saka shi a idon ta ba banda yanzu da nake saka shi fitowan dole,
Shiga cikin su mukayi kowa ya kama nashi aikin, ina kamawa Sulthana ta sake ta fita daga kitchen ɗin gaba ɗaya ba’a fi 30 minutes ba Muna ta fara mitan gajiya itama ta sake aikin ta tafi,
daman Hajiya sady kanma bata wurin ta koma parlorn tana ci gaba da zuba mulki tana kallon ta hankali kwance aka barni da Ruma sai maids muna ta kiciniyar haɗa abubuwa, banje ta wurin kaji kajin nan ba don ganin su suna nutso cikin mai kaɗai ya isa ya karya min azumi,
Sai bayan 2 hours muka samu aikin ya ragu dake akwai hannu da yawa mun kammala abubuwa da dama muka bar musu ɗan sauran da ya rage muka fita don hutawa har wani algarara_algarara nake gani,
Luckily ina shiga toilet naci karo da baƙo na yazo daman yau ko gobe nake tsammanin shi amman banji daɗi ba da ya riske ni a gidan mutane don Allah ya gani ba zan iya rufe baki na har asha ruwa ba ni abinci na zan narka,
Haka na gama abinda zanyi na fita na faɗa ma Ruma batayi ƙasa a guiwa ba ta faɗa ma aunty sadiya, Matar nan harda ɗan tsokana na ta saka aka haɗo min kan abinci me rai da lafiya ga tsokoki a kai gefe kuma kiwi smoothie ne da muka haɗa an ciko cup himm dashi,
Da naga matar nan ta sake min fuska tana jana a jikin ta kawai na rashe a parlo na baje girki ina haƙa muna hira, kaman daga sama sai ga babban Yaya ya shigo parlorn, bamu ji sallamar shi ba har saida muka haɗa ido yayin da na buɗe baki ina shirin kai spoon baki na,
Nayi saurin mayarda spoon ɗin tare da sunne kaina ƙasa dan sosai kunya ya kama ni, ya riga da ya gane halin da ake ciki, shikuwa ko a jikin shi ya wani basar kaman bai taɓa sanin mu ba ya wuce ciki abinshi, amman hajiyar tashi ko ta miƙe tabi bayan shi don taji abinda yake tafe dashi ta sha zaman ta tana tsokana ta uhmm wai mijin ta ya kama ni da tskar rana ina cin abinci,
Yana gama abinda yake yi da kanshi ya dudduba abubuwan da aka haɗa kuma babu laifi ya yaba ma ƙoƙarin mu don baiyi tsammanin sadiya zata yi abin da ya kai wannan ba, daga nan kuma ya fice gaba ɗaya,
Banyi tunanin haka na iya faruwa ba, har ya shigo ya fita bai nemi ya ƙuntata min ko ya saka ni kuka ba, amman ina tunanin saboda idon matar shi ne bai kula ni ba,
******
“Kun kasa haƙuri ka biyo ƙanwar taka har gida ko Khamis?”
“Ba haka bane Hajiya uwar gidan ne bata jin daɗi to kuma babu kowa a wurin ta ga jariri, shiyasa gwanda ta ɗan je ta zauna tare da ita”
“Haka ne amman idan ta samu sauƙi ka dawo mana da ita dan Allah itama ta zamo mana ƴar gida yanzu kaman yanda kake, gashi ma baka zo a Sa’a ba ita da Rumaisa sun tafi gidan yayan su amman bari a kira su dawo” ta faɗa tare da ɗaukan wayan ta dake hannun kujera ta fara laluɓan numbern Ruma
“A barsu kawai hajiya, nima yanzu daga office nake kuma can zan koma, idan suka dawo dan zo na ɗauke ta”
Da haka sukayi sallama Khamis ya tafi
********
“To ta ina ya shiga ne?”
Fita harabar gidan nayi da babu kowa a wurin hannu na riƙe da kwalban magani ni ko motsin Arif banji ba amman ina da tabbacin yana wurin tunda naga fitan shi da gudu, Cikin sanɗa nake tafiya ina leƙe_leƙe ko zan ganshi,
Juyowa yayi a kasalance daga cikin motan da yake zaune ya zurfafa kogin tunani na, abin shi mamaki ma yake bashi wai ƴar wannan yarinyar har tana fashin azumi shi baiyi tunanin ko su Nana sun kai ba tukunna, kayan haushin kuma shine da ya shigo ban gaida shi ba, yana tsumayen jin murya na tun jiya amman sai rowan shi nake masa ya fara gajiya gaskiya ba zai iya ba,
Wani gauron numfashi ya sauƙe ganin na cafko Arif muna ta kokuwa dashi zan bashi maganin yana tuburewa ina dariya,
A irin wannan yanayin ya soma gani na, ranar farko da na fara zuwa gidan tare da aunty Yusrah yana zaune a cikin mota ba kuma fita zaiyi ba sai dan ya zamo masa ɗabi’a, wani lokaci hankalin shi yafi kwanciya idan yana zaune a wurin akan ya tafi wurin Sadiya don a wurin shi da shiga ciki da zama shi kaɗai duk ɗaya ne don the same loneliness yake experiencing tunda ba bashi attention ɗinta take yi ba,
Mun ɗan jima da shiga yaga na fito hannu na a cikin na Jannat muka nemi wuri muka zauna sannan na ɗaura ta a kan cinya na muna wasa da dariya da irin murmushin da ya gani ɗauke a fuska na a yau,
Ina gama bashi maganin na bashi bottle water da na fito dashi ya sha ya koma ciki da gudu sannan na juya zanbi bayan shi yayi saurin ɓalle marfin motan ya fito daff zan shiga ciki naji ya kira ni da irin yanda ya saba wato “ke!”
Slowly na juyo kaina a ƙasa ina jin yanda ƙirji na yake dukan 70_70 saboda tsoro, nayi tunanin mutumin nan ya tafi ai me kuma ya sake dawo dashi?
“Me ya kawo ki gidan nan?”
Kaji wani tambayar rainin hankali? Bance dashi komai ba na ɗago ido na kalle shi na ƴan sakwanni sannan na sake maida kaina ƙasa,
Talk, talk, talk please Saudat, i really want to hear your voice, ya faɗa cikin zuciyar shi,
Ƙara ɗaure fuska yayi yace ” ba zaki bani amsa bane? Me ya shigo dake cikin gidan nan ke waye ne da zaki shigo min gida?”
Har yanzu bani da niyyan buɗe baki na ince wani abu, saidai idanu na suna fitar da saƙon dake cikin zuciyata ta hanyar zubar da hawaye mai ɗaci, Sulaiman ya zamo min ciwon ido, ya gama takura ma rayuwa ta,
Cikin zafin nama ya finciki hannu na ya fara jana da niyyan idan har banyi magana ba saka ni a mota zaiyi ya fitar dani daga gidan zuwa inda na fito,
Ƙoƙarin ƙwace kaina daga riƙon shi nake yi na kasa, cikin muryan kuka nace “dan Allah ka sake ni, na rako Ruma ne ni bansan gidan ka bane wannan da ba zan zo ba”
Finally… Sake hannu na yayi yana bina da wani mummunan kallo
“Yanzun ma bata ɓaci ba tunda kin san gida na ne zaki iya tafiya domin baki samu matsuguni a cikin ta ba tukunna”
A fusace na juya na shiga cikin gidan, duk yanda aunty sadiya ta matsa na faɗa mata abinda ya same ni naƙi firr na ɗaga hankalin Ruma babu shiri ta fito muka fita har lokacin yana wurin, saida yaga fitar motar mu tukunna cikin ɓacin rai ya daki jikin motan da hannun shi,
Shi ba haka yaso ba, bayi son kullum muna ƙarewa cikin faɗa amman ni ɗin ne na cika taurin kai gashi na kasa wayewa ballantana na dace da tsarin rayuwan shi abubuwa su zo mishi da sauƙi,1
Alla_alla nake mu isa gida naje na koka ma sitipid don shi kaɗai ne mai iya share mun kuka na, yanzu kam zan faɗa mishi ya saka yayan shi ya fita harƙa na don yana takura min sosai……..🤦🏻♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
Writer of
*Har abada*
*Kama da wane*
And *Matar kulle*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
21🧝🏻♀️
“Ina kuma zaki je?” Ta tambaya tana kallo na cike da mamaki ganin na ɗauki hanyar corridor da zai kaini ɗakin Zayyad, juyowa nayi ina kallon ta har yanzu da hawaye kwance cikin idanu na Sulaiman ya fara kaini bango, rainin hankalin shi ya ishe ni,+
“Ruma faɗa ma Hamma Zayyad abinda babban yaya yayi min zanyi ya ɗauki mataki, idan ba haka ba kuma yau zan bar gidan nan wallahi daman saboda shi nake zaune har yanzu”
“Mtsww ke a tunanin ki akwai abin da ya Zayd zai iya aikatawa mishi ne? Waima menene abun kai ƙara a ciki ba zagin ki yayi ba bakuma duka ba amman kinbi kin ɗaga hankalin ki, wannan halin na takurawa a cikin jinin shi yake don muma haka yake treating ɗinmu”
Ta ja hannu na muka juya zamu fita daga bedroom ɗinta tace
“Kawai ki manta ki cire duk wani damuwa a ranki, and I’m sorry ba zan sake kaiki gidan babban yaya ba kada ƙai ƙaran ki ya ƙara ma yaya na rashin lafiya daman yanzu ma bayi jin daɗi”
Ji nayi maganar ya cakke ni a zuciya, al’amarin harda abin mamaki don da safen nan muka rabu dashi lafiya “Subhanallah! Rumaisa mai kuma ya same shi? Yaya ma akayi kika sani bayan tare muka dawo?”
Ta yaya za’ayi ta faɗa mata asalin abin da ya faru bayan ɗazu aunty amarya ta kira ta tana tambayar ta inda ta ajiye containern nan, tunda taji haka ta san kawai akwai error,
“U..hmm..d.. ɗazu ne aka kira ni aka faɗa min” ta faɗi hakan ba tare da ta ambaci sunan kowa ba saboda gudun tambayoyi,
har yanzu Saudat bata cancanci sanin matsalar Zayyad ba da ta faɗa mata amman with time dole da ta san komai in dai tana tare dashi,
Fita tayi tana faɗin bari naje na kira miki shi yazo har wurin da kike da kanshi sai ki mishi ƙaran,
**********
“Gaskiya yarinyar ta birge ni dadyn Arif a ina Ruma ta samo ta haka? Ƴar gidan waye yarinya mai zafin nama da fara’a gata kyakkyawa masha Allah”
Siririn tsaki yaja don surutun ta ya fara damun sa, shi niman hanyar gyara abinda ya ɓata yake yi yana kokwanton ko yaje ya bata haƙuri ne ko kuma ya bari ta gama fushinta ta sauƙo ne bai sani ba, kada yaje girman shi ya faɗi a wurin yarinya daman gata sakaliya ta daɗa lalacewa
“Ni Ruma ce da zaki na tambaya ta inda ta samo ta?”
“Gani fa nayi tare suka zo ko hala distant relative ne ko kuma ka san daga inda take don naga yawancin mutanen dake mu’amala da ƴan gida ka san su”
Maida hankalin shi kan system ɗin gaban shi yayi tare da tattaro dukkan nutsuwan shi yana fatan concentrating ko na minti 10 ne saudat ta fita daga tunanin shi ya ƙarasa aikin gaban shi,
“Amman ka san gidan su dadyn Arif? Ko kasan iyayen ta?”
“Ya rabbi!! Amfanin me sanin hakan zaiyi miki? Idan har da gaske muradin samun ta kusa dake kike yi ki kwantar da hankalin ki kwanan nan zata dawo cikin gidan nan da zama sai ma kin gaji da ganin ta”
STORY CONTINUES BELOW

**********
“Babe’s please tell me waye ya taɓa min ke, bani son ganin fushin ki kiyi magana dan Allah”
Rau_rau nayi da idanu ina jin daɗi a raina saboda yanda Zayyad ya nuna min kulawa, sannan cikin shagwaɓa nace,
“Hamma zayd yau zan bar gidan nan wallahi, ba zan iya ci gaba da zama ba”
Gyara tsungunon shi yayi a gaban kujerar da nake zaune ya zuba min idanuwa, we were so close yana ji a ranshi kaman ya haɗiye ni saboda yanda ji na a ranshi,
Har wani kalmasa murya yayi yanda zai nuna he really cares yace
“Subhanallah, me yasa Saudat? Ko wani abu ya faru ne ban sani ba?”
“Abin da babban yaya yake min ne bani so, ni ban san abin da ya haɗa ni da shi ba amman ya saka ni a gaba babu dalili”
“amman kin tabbata ba wani rashin ji kike masa ba Saudat?”
Girgiza kai nayi Ruma tace “wallahi ya Zayd babu wani rashin ji da take mishi, kaima ka san halin babban yaya idan ya saka mutum a gaba ko baiyi komai ba ma yayi laifi”
“Huhh” ya furzar da numfashi yana kallon ƙasa ya maida idanun shi cikin nawa sai faman cika nake ina batsewa
Shiru yayi yana nazarin kalaman ta don tabbas abin da ta faɗa gaskiya ne wani lokaci ɗabi’un sulaiman har kamanceniya yake yi da na Nana shi dai ya fita kyakkyawar zuciya amman ba kowa bane ya gane hakan,
“kiyi haƙuri Please, ina baki haƙuri a madadin shi kuma insha Allah zanyi mishi magana amman kema da laifin ki tunda jiya saida nace miki ki tsaya muyi magana dashi kika gudu da hakan bata faru ba”
Turo baki gaba nayi nace “ai banyi tunanin zai sake matsa min bane da na tsaya jiyan ka mishi faɗa”
“Hhhh hajiya boɗɗi shine sama dani fa! Ta yaya za’ayi na iya mishi faɗa? saidai nayi mishi magana na lallashe shi ya daina takura miki”
*****
Yana dai zaune ne ya zuba musu idanuwa amman abun da suke tattaunawa sam bayi samun isa cikin ƙwaƙwalwar shi, idan ya tsinci magana a sama ne sai ya jefa musu wani umarnin yaci gaba da saƙe_saƙe cikin zuciyan shi,
Sai wuraren la’asar suka kammala duk abubuwan da zasu yi suka tafi shima yabi masallaci daga nan ya samu daman komawa gidan su don ganin yanayin da Saudat take ciki hala har yanzu ma tana fushi dashi, ya ayyana a ranshi bayan ya shige part ɗin su Zayyad yana son fara ganin lafiyan ɗan uwanshi kafin yayi abinda ya biyo baya,
*****
“Kaii! Madam rigiman ki da yawa ina dai kin haƙura ba zaki tafi ba?”
Sai wani shan ƙamshi nake ina ɗaɗɗaga kai jin ana roƙo na, “Please! Please! Please! Kiyi haƙuri ki zauna dan Allah”
“To shikkenan naji zan zauna, sai nan da kwana 5 zan tafi,
na faɗi haka saboda ban ma san abban Jannat yazo ɗauka na ɗazu ba dan tunda muka dawo ko part ɗin Hajiya ban shiga ba na biyo daɗi masoyi,
“Zan iya tafiya yanzu?”
“Yaya jikin naka? Rumaisa tace min baka da lafiya”
“Da sauƙi sosai babe’s, nama warke da naga fuskan ki
Bansan lokacin da murmushi ya kuɓuce min ba nace “ok zaka iya tafiya”
“Godiya nake ranki ya daɗe” ya faɗa tare da miƙewa ya gyara zaman rigan shi sannan ya fice ina bin bayan shi da kallo,
Da ace ni budurwa ce kuma na cancanta da nayi fafutuka wurin nemo soyayyar Zayyad don ina ganin har duniya ta naɗe ba zan taɓa samun irinshi ba,
Aunty amarya tana zaune a parlour tana lazimi as always, sulaiman ya shigo ya nemi wurin zama sannan suka shiga gaisawa don yau bai shigo gidan ba gaba ɗaya sai yanzu, suna cikin haka Zayyad yazo wucewa ya dawo da fara’a ganin su zaune shima ya zauna saidai gaba ɗayan su sun shiga Ruɗani mamaki ya kama su matuƙa, shi kuwa kaman ma bai san abinda ya faru ba har saida Aunty Amarya tayi magana
“Zayd! Me ya kaika ɗakin ƴar uwarka? What’s wrong with you? Me yasa zaka je ko iyakan da akayi maka da hakan ne ka manta?”
“Aunty I’m fine, magana kawai naje muka yi ki kalli babu abinda ya same ni” ya faɗa tare da nuna jikin shi,
“Me yasa kake min haka ne Zayd? Kullum kafi son gani na cikin damuwa a kanka ƙananun dokoki ma baka iya kiyaye su? Kafi son ganin kanka cikin wahala duk abinda ake faɗa maka baka ji? Saboda kada takurawan yayi yawa yasa fa nake barin ka kana zuwa duk inda kake so a cikin gidan nan amman hakan ma bai ishe ka ba sai ka ƙetare iyakar ka?”
“nifa ba Yaro bane Aunty ba zan taɓa yin abinda zai cutar dani ba ku fahimceni dan Allah”
******
“Heyyy dariyan me kike yi ke kaɗai kaman wata taɓaɓɓiya” Ruma ta faɗa yayin da ta zuba a gefe na bayan ta idar da sallah tana leƙa fuska na,
“Faɗa min mana boɗɗi meye ne ya faranta miki haka lokaci ɗaya gashi kaman kin manta fushin babban yaya da kika dawo dashi”
Murmushi nayi ina shafa zanen tafin hannu na cike da kunya nace
“Rumaisa yayan ki is beri nesh (very nice)”
Yamutsa fuska tayi ko kalma ɗaya bata gane cikin abinda na faɗa ba,
“Nifa nace ki daina min fulatanci idan muna magana kindai san ba ganewa nake yi sosai ba, menene kuma wani bari nesh?! Ko zagin shi kike yi baki son na gane?”1
Maman Naxee: “haba niɗin banza” na faɗa ina dariya “ai ban kai wanda zan zagi hamma Zayyad na zauna lafiya ba bacin shi ɗin garkuwa na ne”
“awwwn? Do you love him? Umm.. ki faɗa min dan Allah idan kina sonshi wallahi zanyi farin ciki da hakan”
Kallon ta kawai nayi zuciya na yana tsananta bugu, babu abinda ya faɗo min a rai a lokacin sai Yarima!! Wuroɓokki, Inna ta da baba na da kuma ya aminu!
Har inada kwanciyar hankalin sake soyayya bayan da wa’innan a gaba na?”
Saudat!! Muryan ta ya katse min tunani, “ajema a matsayin yanzu baki son yaa Zayd amman da alal misali ace kece matar da zai aura, to ana daff da auren ku sai kika fuskanci yana da wani matsala da zai iya kawo cikas ma rayuwar auren ku, zaki yarda ki aure shi?
Shiru nayi ina kallon ta tare da ƙoƙarin gano inda zancen ta ya dosa, wannan ne karo na biyu da Ruma tayi zancen matsala kuma ta danganta shi da Zayyad, me hakan yake nufi? Akwai wani ɓoyayyen al’amari a kanshi ne?
“Baki bani amsa ba”
“Rumaisa hamma Zayyad ɗin yana da wani matsala ne?”
“Bani son ki ɗaura min wani tambaya a kan tambaya ta idan kika bani amsa ta zaki samu amsan ki a cikin ta, zaki yarda ki aure shi a hakan?”
“Ƙwarai kuwa indai ina son shi da gaske zan aure shi saboda ina da tabbacin inda ace ni ke ɗauke da wannan matsalar Zayyad ɗin da na sani ba zai taba gudu na ba”
[1/6, 7:55 PM] Maman Naxee: “kin amince dashi kin yarda dashi sosai bayan haɗuwan ku gaba ɗaya kwanaki 20 ne, how comes?”
“Ban sani ba Rumaisa domin bani na amince dashi ba zuciyata ce ta amince dashi kuma taƙi sanar dani dalilin hakan, ban san yanda akayi yayan ki ya shiga jiki na haka ba kuma ina fatan kada yayi tasiri gudun ɓacin rai”
******
Saboda yanda ran Zayyad ya ɓaci a yau cacan baki saida ya saka su kaman zasu bugi juna da Sulaiman, shi ba uban shi ba amman matsayin da ya ɗauka cikin rayuwar shi yafi na iyayen shi girma,
hayaniyar su ne ya ɗago mu daga ɗakin Ruma fitowar mu keda wuya muka ci karo da Zayyad ya zube a ƙasa……..🤦🏻♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
22🧝🏻♀️
Tunda Sulaiman ya faɗa ma Sadiya wa’innan kalaman hankalin ta ya kasa kwaciya ta rasa gane abinda yake nufi da Saudat zata dawo zama a gidan su har sai ta gaji da ganin ta kenan auro wannan yarinyar zaiyi??+
Tafi hour 1 tana tufka da warwara ta rasa wani hukunci ne ɗaya ya dace da abinda ya faɗa tunda a kaikaice yayi mata maganar ko dai ya faɗa ne don ya kawar da maganar da take mishi da kuma wanda take son isar mishi cikin hikima wato neman wasu kuɗaɗe daga gareshi a lokacin? Idan kuma da gaske yake fa yake?
Ganin ba zata samu amsan hakan ta hanyar tambayar kanta ba yasa ta ɗauki wayarta tana jin yanda ƴarta take zunduma ihu amma a yanzu bata da nutsuwan kulata, ƙarshe kiran nanny ɗinta tayi tazo ta ɗauke ta ita kuma taci gaba da trying numbern Sulaiman,
********
I was Shocked!! For a moment zuciyata ta kasa gaskata abinda idanuwa na suke gani har saida naga Zayyad yana buga jikin shi a jikin ƙafar Centre table wanda ko shi ba ƙaramin girgiza yake yi ba, jikin shi ya ƙame kaman mai farfaɗiya sai ihu yake yi abun gwanin tausayi,
Babban mutum magidanci, that kind and sweet Zayyad, my heart desire wanda a ko yaushe nake mafarkin kasancewa tare dashi shine a cikin wannan yanayin da ko ƙaramin yaro ba za’a so mishi ita ba?
“Rumaisa ina containern maganin shi da yake wurin ki? Ban samu nawa ba!” Shine maganar da ya fargar dani amman na kasa ayyana komai jiki na ya mutu ina tsaye a wurin Ruma ta koma ɗakin ta da gudu da nufin ɗaukowa Sulaiman kuma yana ƙoƙarin riƙe shi da duk wani ƙarfin shi amman ya kasa sai ji ma kanshi rauni yake yi a garin haka shima yaji masa ciwo a ƙafa, da kuma guiwan hannun shi,
Amman haka ya riƙe ɗan uwanshi ba tare da ya damu da halin da yake ciki na cutarwa ba dan basu iya controlling ɗinshi idan ba su uku shi da dady da Nafi’u ba, a hakan ma da ƙyar,
Fitowa riƙe da wannan dai farin ƙaramin containern Ruma tayi ta miƙa wa Aunty Amarya ita kuma ta buɗe ta mika ma sulaiman da nufin ya shafa mishi amman abin yayi mishi yawa ba zai iya ba, yana karba Zayyad yayi ball dashi wanda su kansu basu san ina ya shiga ba,
Zan iya taimakon shi, ina da sani a kan hakan amman ta yaya? Ta wani hanya zan taimake shi ba tare da mun aikata zunubi ba? Iyakacin ruƙiyya da na taɓa yi a rayuwata ma mata ne zallah, ta yaya zan iya haɗa jiki na da namiji da sunan nema mishi sauƙi daga wurin Allah?
Amman ganin idan na bar Zayyad a haka ba tare da nayi wani abu ba zai cutu yasa nayi shahadar ƙarasawa kusa dashi dukda tsoron shi ya kama ni amman a hakan na durƙusa na fara rero ƙira’a, saidai fa matsatstsakun kan bawan allan nan sai toshe kunne naga yana yi yana ƙoƙarin kawo min gwabza,
A taƙaice dai ruƙiyyan nan bai kammalu a haka ba saida babban Yaya ya riƙe min shi, na manna baki na a saitin kunnen shi ina karatu ina kuka irin wanda mahaifiyar shi take yi tana mishi addu’a,
Munji jiki kam babu ƙarya dan kunsan hidima da namiji kuma majiyin ƙarfi ga ƙarin wani ƙarfin na mutanen ɓoye dake jikin sa,
Allah ya yafe min ko dan tsarkakuwan niyya ta amman lokacin da yayi wani yunƙuri ya birkito ni ina jin yanda ƙirjin shi yake gogan nawa wasu sakwanni na tsohuwar ƴar hannu yana isa cikin jikina dukda shi baima san yayi hakan ba taimakon da Allah yayi min ɗaya bani azumi a ranar da shima ya kama hanyar garin su,
STORY CONTINUES BELOW

Bai ɗauki lokaci sosai ba abun ya lafa a wurin su saboda yakan fi hour 1 da rabi wani lokaci ana abu ɗaya shiyasa idan ya tashi yake jinya na tsamin jiki da raunukan da suke jawo masa, amman a wuri na ya daɗe sosai tunda har ya jigata haka,
Ruwa na buƙaci su bani a kofi suka kawo min na zam_zam wanda basu rabuwa dashi saboda Zayyad, na karɓa nayi addu’a a ciki sannan na miƙa ma sulaiman ya bashi aka shafa mishi sauran a fuska, ya kira mutumin dake bashi rahoto kullum saboda shine amintaccen sa a gidan suka tattare shi zuwa bedroom ɗinshi,
Na bisu da kallo ina taraddadin tsawon lokacin da Zayyad ya ɗauka yana fama da wannan laluran, tun a yarinta suka shige shi ko da girman sa? Koma gadan shi yayi? Allah masani,
Saida suka kwantar dashi yanda zai samu hutu sannan suka fito daga ɗakin tare da rufo ƙofar har lokacin muna tsaye a parlorn Aunty Amarya sai zuba min godiya takeyi tana saka min albarka kaman bakinta zai tsinke abun tausayi yanda matar nan take kuka,
Zaunar da ita mukayi muna lallashin ta ni da Ruma tare da faɗa mata kalamai masu sanyi duk da bani da tabbaci amman ina da yaƙinin Zayyad zai iya warkewa na dinga nusar da ita tana haƙuri kuma tana yawan godiya ma Allah don wannan jarabawar da Allah ya ɗaura musu zai iya datar dasu a lahira,
Yana zaune a kujerar dake kallon namu ya ƙura mana idanu ga aunty Amarya ta kwantar da kanta saman kafaɗa na ta lafe kaman wata ƙaramar yarinya, tunda wannan matsalar yake tashi bayan a wurin dady babu a inda take samun comfort idan bayi nan sai yau a wurin ƴaƴan ta,
“Daƙiƙiya! Daƙiya!! Daƙiƙiya!!! Lallai jiya ya faɗi kalmar da ta zamo mishi guba a yau, ya jife baiwar Allah mai ɗumbin ilimi mai amfani da sunan da ake kiran ƙasƙantacce dashi, gashi wanda yake kira da daƙiƙiya tayi abinda shi ya gagara yi tsawon shekara da shekaru,
Lallai kada ka wulaƙanta ɗan adam a duk halin da ka ganshi don baka san wani irin baiwa Allah yayi mishi ba,1
******
5:40pm
Sake duba agogon hannun shi yayi kusan 30 minutes kenan yana zaman jiran dawowar su boɗɗi amman shiru, gashi an kira Ruma yafi sau a ƙirga bata yi picking ba daga ƙarshe ne aka kira Aunty Sadiya ta shaida musu mun daɗe da dawowa tun kafin ayi sallan la’asar muka bar gidan, sai aka tura junior yaje part ɗin su Zayyad ya duba ko sun dawo,
Yana zaune suna taɓa hira da Hajiya sulaiman ya shigo part ɗin cika da girmamawa Khamis ya miƙe ya miƙa mishi hannu tare da ɗan durƙusawa suka gaisa sannan ya koma ya zauna yana binshi da kallon tambaya,
Bakin shi bai furta komai ba amman kallon da hajiya taga yana miƙa ma Khamis yasa ta gane yana niman ƙarin bayani tace
“Ya zo ɗaukan ƙanwar shi ce Saudat yanzu aka je kira mana ita”
Haɗe fuska yayi gaban shi na faɗuwa, ya gama sakankancewa zaman Saudat zai ɗaure a tare dasu shi da har ya saka ta a makaranta ya shigar da ita cikin tsarin rayuwan gidan da mutanen cikin ta sai kawai azo a tafi da ita?!
Noo! Ba zai bar hakan ta faru ba, ya gama shiri ya tsara duk yanda yake so abubuwa su kasance, sannan the worst part shine yanzu Saudat ta san sirrin da suke ɓoyewa shekara da shekaru idan ya barta ta tafi wani wuri kaman ya buɗe surrin ne ma kowa ya gani, ba zai bari wani daga sama ya wargaza mishi plan ba dole kawai yayi wani abu a kai,
******
“Dan Allah ki bar kukan nan haka boɗɗi, tun ɗazu bakiyi kuka bq sai yanzu da hankalin mu ya kwanta?” Ruma ta faɗa itama tana shirin zubar da hawaye “ɗazu fa ke da bakin ki kike faɗa ma aunty Amarya wannan lalura ƙaddara ce amman kema gashi kina yi kaman baki aminta da ƙaddarar ba na yau da kika gani kawai?”
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, Rumaisa ina jin kaman zuciyata zata tarwatse na kasa sabanta mata da jarumta a kan abinda ya shafi Hamma Zayyad,
duk lokacin da wani abu ya same ni shi nake fara samu na faɗa mishi don ina da tabbacin zai kore min shi, amman yanzu na farko ma na gagara mishi wani babban taimako nayi sake na fita daga cikin hayyaci na har na barshi yaji rauni”
“A’a kinyi bakin ƙoƙarin ki wallahi Allah ya saka miki da alkhairi mun gode sosai boɗɗi”
“Muje mu sake duba shi kafin a sha ruwa dan Allah”
Fita mukayi a bakin ƙofa muka ci karo da junior dake bai san abinda ya faru ba yasa da fara’ar shi yazo gaba na yana fankama shi a dole wai saurayi na yace “Girlfriend”
“Na’am boisfirens (boyfriend) ɗina yaya akayi?”
“Hmm ashe baki sona?”
Saida dariya ya suɓuce ma Ruma ganin yanda ya haɗe rai yana cin magani kaman wani babba,
“Haba my junior, ina sonka mana sosai ma me ya faru?”
“To gashi nan wannan yayan kin yazo ɗaukan ki zaku tafi gida ki barni, kuma yanzu aunty Ruma ta ɗauke hankalin ki ko hira ma baki zuwa wuri na, idan kika tafi kika yaudare ni a wani wurin na barki da Allah daman na san ba wani sona da yawa kike yi ba” ya ƙarasa maganar yana tafiya muka bishi da kallon mamaki yanda yaron nan yake zubar zance,
Sam banso haka ba, banji daɗin zuwa Khamis a wannan lokacin ba musamman yanzu da nake son kulawa da Zayyad da kuma lafiyar shi amman har duniya ta naɗe khamis yana ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa iya musu muusuu ba duk abinda suka sani saidai idan ya kauce ma Shari’a,
Naji daɗin ganin aunty amarya da Sulaiman sun bar parlor hakan ya bamu daman wucewa cikin ɗakin Zayyad cikin sauƙi, yana barci amman ƙaran buɗe ƙofar mu ya tashe shi,
Kallo ɗaya nayi masa na sake fashewa da kuka tare da toshe hannu na da tafin hannu na ina ganin yanda ya kwaile jikin ƙafan shi wurin yayi fari sol dan ba’a saka mishi magani ba tukunna bisa umarnin sulaiman ne kada a bari wani ya raɓe shi har sai ya dawo cikin hayyacin shi koda kuwa doctor ne,
Daddafawa yayi ya miƙe ya zauna tare da jinginar da bayan shi jikin pillow yana kallo na, yayi ta kallo na ba tare da ya san abinda zai faɗa ba,
“I broke your heart I’m sorry, nasan kinyi tsammanin Zayyad da kike gani kullum mutum ne cikakke mai hankali da lafiya, mutum ne mai nagarta wanda ya dace dake kuma zai iya ɗaukan duk wani nauyi da ɗawainiya naki,
Amman wannan Zayyad ɗin miskini ne marili wannan Zayyad ɗin bayi da amfani a wurin kowace mace, wannan Zayyad ɗin ba ɗan uwa bane, ba saurayi bane kuma ba mijin aure bane, wannan Zayyad ɗin da ki same shi da babu shi duk ɗ…”
“Dakata dan Allah! Ka dakata?” Na tare shi da hannu na tare da runtse idona kalaman da ya faɗa suna gasa min zuciya,
“Ki yafe ni da na saka miki false hope, na gwada miki abinda bashi bane zahiri na gwada miki zamu iya kasancewa tare bayan ko da ƴan uwana na jini bani da wannan daman,
Yanzu kinsan gaskiya boɗɗi, gaskiyar da shine amsar tambayar da kika min kwanaki bani zuwa aiki kaman sauran ƴan uwana kuma bani son shiga cikin mutane to wannan matslar shine amsar su, ina da Makarai since when i was 5 so yanzu na shirya rasa ki tunda gaskiya ta futo ba zaki iya ci gaba da kasancewa tare dani ba”
“Da ace nima mutum ne mara matsala kamar kowa kuma mace mai cikakkiyar daraja ko matsalar ka tafi haka muni wallahi zan zauna da kai nayi jinyar ka tun daga farko har ƙarshe saboda kai ɗin na daban ne a cikin zuciyata hamma zayd…. Allah ya baka lafiya”
Nayi saurin ficewa jin kuka na niman cin ƙarfi na nakoma ɗakin Ruma na ɗora daga inda na tsaya bayan nasan Khamis na can part ɗin Hajiya yana zaman jira na gashi da azumi a bakin shi kuma an kusan shan ruwaz
Da ƙyar Ruma tazo ta rarrashe ni duk kayan ta da nake sakawa lokacin da nake zaune a gidan ta tattara min su da sunan ta bani kyauta harda pjamas, ta cire sim ɗin ƙaramin wayanta mai keypad tasa wani na cikin babban wayanta wanda bata amfani dashi ta bani tace zamu dinga waya,
Haka kafin na tafi ƴan gidan suka dinga haɗa min goma na arziƙi ni kayayyakin har suka bani tsoro ga kuma garin kuɗi wanda a cikin masu bayarwan harda Zazzaɓi amman duk da hakan bai saka naji haushin su ba,
Cikin kyaututtukan da aka min babu wanda ya burge ni naji daɗin shi har cikin raina kaman wani zoben azurfa wanda ya fito daga hannun abun ƙaunata Zayyad, yace a bani a matsayin tukuicin taimakon shi da nayi sannan ya zamo abinda zan dinga tunawa dashi idan na gani don yaso ya bani da kanshi ne amman na tafi bamu ƙarasa magana ba,
Saidai fa da na saka duka yatsu na yayi musu ruwa harda babban ma kuwa!……….🤦🏻♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
23🧝🏻♀️
Tunanin halin da Zayyad yake ciki ya addabe ji tunda na dawo gidan aunty Yusrah na rasa sukuni, aikin ranan ma dai kawai inayin shi ne amman hankali na bayi jiki na domin yau ya zamo min ɗaya daga cikin baƙin ranaku da na gani a rayuwata,
Ga abinci amman na kasa ci ga TV abin sona amman na kasa kallo, duk yawan surutu na bakina ya mutu abin har mamaki ya bawa aunty Yusrah don bata saba gani na a haka ba,+
Dukda basu kallo a azumi amman na musamman ta kunna min draman hausa bayan munyi sallan tarawih da mamakin ta ko kai duba na wurin da tvn yake banyi ba na koma ɗaki, na ɗau alƙur’ani ina karantawa ko zan samu sauƙi a cikin zuciyata,
sannan ita Al-ƙur’ani ayoyinta waraka ne ga duk wani cuta idan Allah yaso,
Koda nayi musu sallama na nufi ɗaki da niyyar kwanciya, barci ƙaurace ma idanuna sukayi ina ji a jiki na Zayyad ma baiyi barci ba kuma yana cikin damuwa gashi bani kusa dashi balle na taimaka mishi da wani abun,
Tashi nayi na kunna Torchlight sannan na buɗe jakar da na dawo dashi na ciro zoben da Zayyad ya bani na cire wani chain ɗin necklace ɗina na zura a jiki na saka a wuya na, na koma gado na sake kwanciya naci gaba da tunani,
******
Sulaiman bai san da hawan ruwan da ya saka ma sadiya ba har saida ya shiga mota zai koma gida don a nan ya bar wayan nashi, yana dubawa yaga 35 missed calls ta ajiye mishi, ba mamaki ba har tsoro sai da ya kama shi don ya san haka siddin ba zata kira shi a waya ba saidai idan wani abu take nema,
“Allah yasa ba wani abu ne ya faru ba” ya furta a fili sannan yaja motar ya bar gidan,
Da shigan shi ya same ta a parlo sai kai komo takeyi idanun ta sunyi jaa alamun tasha kuka, amman duk da haka ba ƙaramin tafiya dashi tayi ba shigan ta ya matuƙar birge shi, tasha lace da jewelries ko ina sai ƙyalli take yi ga ɗaurin kanta ya zauna amman fuskar ta babu kwalliya ko kaɗan,
“Sadiya kenan, damuwa bayi hana ki gayu” ya faɗa a ƙasan maƙoshi tare da gimste murmushin shi gudun raini ya shiga haɗe da sallama,
Bata amsa sallamar ba sai tsayawa tayi tana kallon shi cike da takaici har ya ƙaraso kusa da ita zai wuce,
“Tun kafin ka ƙaro auren ne zaka fara wulaƙantani?”
Cakk ya tsaya sannan ya juyo yana kallon ta kishi ya gama cinye ta ji takeyi kaman tayi bindiga, sai yanzu ne ya gano inda ta nufa wato maganar da sukayi da safe ne ya tsaya mata a rai shi yama manta,
“Dan Allah kai ko kunya baka ji ba idanma kishiya zaka min sai da wannan ƙanƙanuwar yarinyar sa’ar ƙanwar ka na 7! Ni ban hana ka ƙara aure ba amman kayi min adalci indan zaka yi aure ka auro babba wanda nasan zan iya haɗa ƙirji da ita mu bugu idan ta nemi raina min hankali ba yarinyar da zan zaune ta ba haba!”
Bata yi tsammanin zai tankata ta ba kwata_kwata, amman sai jinshi tayi yana dariya ta kalle shi with full suprise, dariyan shi shine abinda zata iya ƙirgawa a rayuwan ta, ta yuyu ma yanzu ma wani muguntar yake shirya mata shiyasa yake yi,
STORY CONTINUES BELOW

Ya san a yanzu kwanciyar hankalin Sadiya shine zaman lafiyan shi dan yau ba ƙaramin gajiya ya kwaso ba shiyasa gwanda ya bita a sannu don ya samu biyan buƙata,
“muna tare da ke a gidan nan yaushe kika ji nayi maganar ƙarin aure halima?”
“To da safe da kace zaka ɗauko wancan yarinyar talakawan ta dawo gidan nan har sai na gaji da ganin ta mai kake nufi kenan?”
“Don nace zan dawo ta ita gidan nan ba ina nufin auro ta zanyi ba, naga dai alaman kina son zqmanta kusa da ke ne shiyasa nake son cika miki burinki nothing else!”
Juyawa tayi ba don ta yarda da zancen shi ba zata shiga ciki yayi saurin jawo hannunta ta dawo jikin shi, yana son yayi ƙoƙarin romancing nata ko zata sake mishi ta canza halin gidadancin nan, ya fara ƙoƙarin tsara ta da kalamai masu kwantar da hankali,
“Kisha kurumin ki uwar gida ran gida kuma amarya hasken gida bayan ke babu wata duk wanda zai faɗa miki wani abu saɓanin haka ƙarya yake koda kuwa nine da kaina, ina yara na??”
Ɓata rai tayi ganin yau mutumin nata da salon da ya dawo, ta san abinda zatayi mishi ta cutar dashi dan haka sai ta rama wulaƙancin da yayi mata a baya babu yafiya,
A yatsine tace masa “sunyi barci” amman bai lura ba don hankalin shi bayi kanta,
“Ok then! let’s go inside please”
Ƙwace jikinta tayi daga riƙonshi kaman zata saka ihu tace “ni gaskiya ba yanzu ba akwai abubuwan da ban gama ba kuma bani da maiyi mini su”
“Ok haka zakice ko? To Shikkenan idan na tashi ƙara aure sai kiyi gola ki caɓe tunda ke ba zaki iya kula dani ba zan samo wanda zata sadaukar da rayuwarta saboda ni”
********
“Come in sister” ya faɗa lokacin da yake tashi zaune, ruma ta ƙaraso ciki tana kallon ciwon shi wanda a yanzu anyi dressing an rufe da bandage da plaster
“Ya zayd jikin da sauƙi ko? Ko shine ya hana ka barci?”
“Da sauƙi Rumaisa ina tunanin Saudat ne, ban san a wani yanayi take ciki ba, maybe tana cikin damuwa saboda nasan tana sona , Ruma i can see love for me in saudat’s eyes ko ke baki lura ba?
“Na gani ya zayd amman yanzu ba shi bane abun damuwa ba lafiyan ka shine a gaba kafin komai”
Ƙura mata idanu yayi kaman yana son gane wani abu sannan ya ja dogon numfashi yace
“Ruma na fara ji a jiki na kaman idan babu saudat a cikin rayuwa ta mutuwa zanyi,
Bayan ta zamo sanyin idanuwa na yanzu ta zamo jin daɗi da kwanciyar hankali na itace farincikina”
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’n shine kawai abinda take maimaitawa a yanzu bata da tabbacin yana cikin hayyacin shi tunda bai samu kowa da wannan zance mai girma ba sai ita,
“Kada ka ɗaga hankalin ka a kan wannan maganar ya zayd inda rai da lafiya komin daren daɗewa zaka mallaki boɗɗi insha allah”
“Ba zan iya jira dare da daɗewan suzo kafin ta zamo tawa ba ina tsoron ayi min sakiyar da ba ruwa, ina tsoron nayi sake wani ya sace zuciyan ta har ta soshi fiye da yanda ta soni ba zan jure ba idan kina da wani hanyar taimako na a kan hakan please help me”
Bata ce komai ba ta ɗauki wayan shi ta saka mishi numbern wayan da ta bawa boɗɗi ta miƙa mishi,
“This is the least i can do! Talk to her and make everything better, saida safe”
19/Ramadan/1442
10:55am
Ke Saudat!! Yadiko ta daka min tsawa na juya a firgice ina kallon ta,
“Me yake damun ki ne ƙarama dake kinsa ma kanki wani tunani ana miki magana baki ji, lafiyan ki kuwa?”
Kafin nayi magana aunty Yusrah ta fito da abulkhairi a hannun ta tace na shigo ciki, babu musu nabi bayanta muka zauna taci gaba da shayar dashi sannan ta dubeni,
“Dan Allah boɗɗi idan akwai wani abu dake damunki ki faɗa min, tun jiya da kika dawo gidan nan na lura baki cikin nutsuwar ki duk kinyi sukuku babu wani kuzari ko walwala a tare dake, ko sunyi miki wani abu ne a gidan su boss?”
Girgiza kai nayi ina ƙaƙalo murmushi nace, “babu komai ummin Jannat kawai bani jin daɗi ne”
“Kinga Saudat, ni kamar babban yayar ki ne duk wani matsalar ki zaki iya faɗa min ko ba zan iya miki maganin shi ba zan iya baki shawara a kai ki faɗa min koma menene nayi miki alƙawarin babu wanda zaiji”
Ɗago kaina nayi da mamakin ta taga hawaye shar_shar a kan fuska na, cikin kuka nace
“Wallahi ni kaina bansan me yake damu na ba aunty Yusrah, ina son taimaka ma hamma Zayyad ya samu lafiya amman ba zan iya ba kuka yana shan wahala sosai”
“Waye kuma Zayyad, kuma me yake damun shi?”
******
Ƙanin Khamis ne ya fito daga gidan ya ƙarasa jikin motar da Sulaiman yake tsaye sannan cikin mutuntawa yayi masa iso ciki har suna ɗan taɓa taɗi a hanya,
Ya san ba zai samu Khamis a nan ba dukda iyalinshi ba a nan suke rayuwa ba amman har ya gama abinda ya kawo shi ba zasu haɗu ba koda by mistake ne don saida ya saka aka tula mishi aiki a office kafin ya fito,
Da sallama ya shiga parlorn ya rusuna har ƙasa ya gaida mahaifiyar Khamis sannan ya sama ma kanshi matsuguni saman kujera,
“Sunana Sulaiman Nazir Sardauna nine ubangidan ɗanki Khamis a wurin aiki, dalilin zuwa na yanzu shine akwai wani charity foundation da muke running na tsawon shekaru,
muna taimaka ma mutane da dama ta hanyoyi daban_daban don ganin sun kaiga cikar burin su, so to cut it short akwai yarinyar wurin ki wanda take zaune a gidan khamis ɗin yanzu haka, haulat suka ce sunan ta ko?”
Da sauri mama ta gyara mishi da “A’a Saudat take”
Kaman bai sani ba ya gyaɗa kanshi irin ta tuna mishi ɗinnan yaci gaba da cewa ” mun sama ma student guda 20 admission a international academy kuma alhamdulillah harda ita cikin wanda suka samu wannan damar……….🤦🏻♀️
M.a.n.a.g.e😁
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
24🧝🏻♀️
Shiru mama tayi tana nazari, Sulaiman kuwa yana mararin jin amsarta don ya samu ya maida saudat gidan Hajiyar shi da zama kafin kuma yazo yin mai gaba ɗayan,
Ji yake yi kaman ma ya yanke hukunci ba tare da izinin ta ba, kuma hanyar da yabi shine kaɗai wanda zai kaishi ga nasara cikin sauƙi,+
“Ai alhaji sulaimanu da baka daku kanka kazo da kanka a kan wannan ƙaramin al’amari ba, babu wanda yaƙi ilimi kuma babu wanda yaƙi ci gaba, a cikin dubban mutanen da kuka tsallake kuka zo kanmu da alkhairi babu abinda zamu ce muku sai Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziƙi idan ita Saudat ɗin tazo mukayi magana da ita ta amince tana son sauya makaranta tayi a wanda kuka sama mata falillahil hamd”
Saidai ta faɗi hakan ne ba don ta yarda kai tsaye ba al’amarin ya ɗaure mata kai, ta yaya akayi Sulaiman ya san Saudat a gidan khamis take zaune? Kuma mai yasa zai bada muhimmanci a kan karatun ta? Ko taje ta buɗe musu sirrin rayuwar ta ne da ita da Khamis suka haramta mata sanar dashi ma kowa suka ji suka tausaya mata?
“To Shikkenan mama ni zan koma bakin aiki duk yanda kuka yi da ita sai ku sanar dani” ya faɗa tare da ajiye musu card ɗinshi yayi mata alkhairi sosai da sauran mutanen gidan kafin ya tafi zuciyar shi cike da takaici wai yanke ƙaramin hukunci ne sai an tambayi ƴar wannan yarinyar ra’ayin ta,
A ganin shi duk abinda ake so tayi ko aka ga ya dace da ita umarni kawai za’a bata ko bata so inya so daga baya zata iya sabawa har taso abin,
******
“Saudat kibi a hankali dan Allah kada ki kai kanki wurin da Allah bai kaiki ba, kin sanar dani waye Zayyad kin ɓoye min abinda kika ce yana damun shi bansan ko menene ba, amman ina so ki sani shi son zuciya ke jawo ɓacin ta, bance idan kina da hali kada ki taimaka mishi ya samu lafiya ba saboda na san irin baiwan da Allah ya miki da familyn ki ma gaba ɗaya,
Amman wa’innan hawayen, da damuwa da kuma canjin yanayi daga gare ki yana nufin wani abu ne daban, kada ki bari zuciyar ki ta saka ki son abinda kika san ba zaki samu ba, zaki iya kuka da nadaman hakan daga baya”
Kallon ta kawai naci gaba dayi a raunane, aunty Yusrah ta nuna damuwa sosai a kaina amman lokaci ya riga ya ƙure, na daɗe da kamuwa da ciwon son Zayyad saidai ko a yanzu daman ban saka ma raina zan iya zama tashi ba kasancewar shi saurayi nikuma BAZAWARA bamu ma dace da juna ba kwata_kwata,
“Ki bar wankin zan ƙarasa, kije kisha magani ki kwanta ki huta nasan bakiyi barci sosai jiya ba”
Shiga ɗaki nayi dan ina ɓukatar hutun kam, na ɓalli paracetamol guda biyu nasha sannan na hau gado na kwanta daidai lokacin da waya na ya fara niman agaji, na san ma mutanen Rumaisa ne suke niman ta na ɗago wayan da nufin amsawa sunan da tayi saving numbern shi a kan layin ya bayyana “bro Zayd”
Taɓe baki nayi ashe Ruma ma ina ganin ta Sallah_sallah ta iya wulaƙanci na ƙin ƙarawa, saurayin nata da bata so ne shine harda saving sunan shi da zagi wai ‘b***’uba Zayd’ shine ta gajarce shi da bro dan kar a gane ko darajan irin sunan yayan ta da yake dashi ba zata ɗaga mishi ƙafa ba don sitifid ma wani lokaci nakan ji suna kiran shi yaa Zayd,
STORY CONTINUES BELOW

Receiving nayi na saka a kunne na tare da yin sallama kaman jira yake yi yace “Babes”
Tsirrr naji jini na ya tsinke yana gudana, muryar shi kaɗai ba ƙaramin tasiri yake dashi a kaina ba,
“Hello babe, are you there?”
Daman ma Hamma Zayyad Ruma ta saka zagi?
“Boɗɗi kina jina kuwa?” Ya faɗa cikin sanyin murya,
Saita kaina nayi cikin nutsuwa nace “Ina ji Hamma Zayyad ina kwana”
“A’a kin manta shaƙuwa ne ba Hamma ba, you are not romantic in anyway, ke bakiji sunan da na saka miki bane mai ma’ana mai daɗi amman ke ko gajarta nawa baki yi don ya ɗan fito unique”
“Eh lallai kura tayi lafiya, zai kuma ɗaura daga inda ya tsaya” na faɗa a cikin zuciyata, a zahiri kuma cewa nayi “yaya jikin ka?”
“Ban sani ba nima, sai kin bani amsa ta tukunna”
Murmushi mai sauti nayi wanda ya saka shi murmusawa nace “ai sunan ka a hakan ma da daɗi Hamma Zayyad, amman tunda kace baka so zan koma kiranka Hamma Zayd ɗin ko kuma inyi maka naku na hausawa Yaya zayd, yayi?”
“Noo! Gaskiya baiyi min ba, wannan duk sunaye ne gama gari ya kamata mutum mai muhimmanci a gareka yana kiran ka da suna mai muhimmanci, ko ke baki san kina da muhimmanci bane a zuciya ta?”
Rass!! Naji gaba na ya faɗi da jin wannan kalaman nashi, naga alaman fa kaman sitifid da gasken gaske yake yi, to lallai akwai ƙura,1
“Kina da muhimmanci sosai a rayuwata saudat, matsayin ki daban yake a zuciyata nifa wani lokaci nakan ji zuciyata yana faɗa min sonki nake yi amman naƙi sauraron ta kinsan me yasa?”
Girgiza kai nayi kaman yana gaba na jiki na yayi luƙus da jin kalaman shi yaci gaba da cewa
“Saboda ban sani ba ko zaki yarda kiyi ƙuntacecciyar soyayya da mai jinnu…”
“Ya zayd me kake faɗa haka ne?”
“Ki barni na gama magana Saudat don bani da niyar miki wani ɓoye_ɓoye dole ne na faɗa miki gaskiyar halin da nake ciki don idan abu uwa zasu tafi yanda naso a tsakanin mu ba’a taɓa gina soyayyar gaskiya mai inganci a kan ƙarya ko kuma ɓoyayyun sirrika,
So basu bari na nayi komai, rayuwata ba irin rayuwan sauran mutane bane, kaɗaici har yabi jinin jikina don shekaru 25 ba wasa ba,
Bani da abokai bayan wanda suke ƴan uwana na jini, ban iya soyayya ba ban taɓa gwadawa ba kuma ba sai a kan Sulthana wanda take ƙanwa a wurin matar babban Yaya, na so Sulthana a lokacin da bansan menene ma’anar soyayya ba, nayi tunanin daga kaga mace ta burge ka ko tayi maka kyau na lokaci daya shine soyayya amman lokacin da na haɗu dake sai tunani na ya canza baki ɗaya,
Ni da kike ganina babban baƙauye ne don bansan ko ina ba a garin nan saidai wuraren da ake ɗauka na a kaini ba de naje da kaina ba, driving ma ba a son ransu suka koyamin ba saboda ba’a so in dinga fita,
Kullum anfi ƙaunar gani na a ɗaki all alone with just my phone and the internet, babu abinda na ƙware a kanshi a duniyar nan duk dagewa na a kai sai sun kayar dani,
Saidai da ina da lafiya, da zanyi ƙoƙari na yawaita saka ki farinciki zan saka idanuwan ki su gano ƙayatattun kayan morewa na duniya kuma nayi ƙoƙarin taya ki mallakan lahira amman hakan ba mai yiwuwa bane, all i have is the love for you…….i just love you…..
I LOVE YOU SO MUCH SAUDAT
*****
Jujjuya kujeran yake yi yana karkaɗa biron hannun shi cike da nishaɗi don ya fara hango ma kanshi nasara a cikin shirin shi, da ya samu an amince da maganar komawar Saudat international academy Shikkenan zai samu daman maida ta ƴar gidan su don ba zai yarda taci gaba da zama a kalolin gidan da ta tashi ba, domin shi ba zallan wayewa da ilimi yake so ta ƙara ba she has to maintain her beauty, fatan ta yayi kyau taci abinci masu inganci da gina jiki daɗi ya samu matsuguni a jikin ta sosai, shiyasa ba ƙaramin shiri zaiyi a kanta ba dole ne kawai ya mallake ta,2
*****
“Ki kalli bayan allan nan yana rejecting call ɗina?”
Sadiya ta faɗa fuskar ta ɗauke da tsantsar damuwa tana kallon Muna,
“To ki rabu dashi mana aunty halima, kinfi kowa sanin halin babban yaya idan yayi fushi babu abinda mutum zaiyi masa da zaisa ya sauƙo sai lokacin da yaga dama, ki bari da kanshi zai dawo ya neme ki”
“Na bar mene Maimoona kina ji yana min maganar kishiya wai aure zai ƙara? Tun jiya fa Sulaiman yaƙi kula ni yau da sassafe ya bar gidan nan hankali na ya kwanta ta ina?”
Miƙewa tayi da wayar ta a hannu ta saka takalminta sannan ta ɗauki hanyar cikin ɗaki tana
“Wannan mijin naki ya zamo mana jaraba wallahi bayi mana komai bayan saka mu a damuwa Allah dai ya raba mu lafiya”
******
Ni banga amfanin PCM da nasha ba don bayan gajiya da damuwa harda ciwon kai sitifid ya saka min,
Wannan maganganun nashi ta ɓangare ɗaya yayi min ɗadi sosai amman ta ɗaya ɓangaren ya zamo kaman ruwan kifiyoyi ne masu guba, don ni da Zayyad ba zamu taɓa kasancewa tare ba musamman ma idan ya san Asali na ya san labari na kuma ya san ni ba BUDURWA bace,1
“Kada ki damu kanki ba gaggawa nake yi ba kuma wannan ba al’amarin da za’ayi wa sauri bane, idanma kina ganin kaman yanzu yayi wuri zan iya jiran ki zuwa wasu shekaru nan gaba saidai kawai ina fatan kasancewa ne a cikin zuciyar ki HAR ABADA, ki nutsu kiyi tunani bye kada na cika ki da surutu,
Ya san ba zanyi magana ba yasa kawai ya kashe wayan ba tare da ya jira wani amsa daga gare ni ba,
Zubewa nayi a kan gadon ina jin yanda kaina yake sarawa da ƙarfi ga hawayen dake sintiri a gefen fuska na, na kama salati ina kiran sunayen Allah don samun mafita daga gareshi,
*******
20/Ramadan/1442
Da Mama ta faɗa ma yadiko ta nemi shawari na kan maganar makarantar nan banka tsaya na saurara ba nace na basu wuƙa da nama suyi yadda suka so dani, don tabbatar musu da suna da cikakken iko a kaina,
Da tayi magana da Khamis ya nuna mata babu matsala sai suka kira shi suka faɗa mishi sun amince, murna da sulaiman yayi a ranar da ya koma gida kaman ya goyi sadiya, ita wawiyar ta ɗauka ya sauƙo ne yana sake niman wani abu a wurin ta amman bata san tsiyan da yake shuka mata a ƙarƙashin ƙasa ba,
Zayyad bai sake kira na ba sai washe gari da yamma ina kallon wayan na barshi ya yanke ina kuka dan ba zan iya rejecting ɗinshi ba kuma ba zan barshi yabi hanyar da ba zai ɓulle ba, ai kuwa saida ya tado da matsatstsakun shi a ranar ya sake gutsure azumin…………🤦🏻♀️
Love You my fans😍
#Team SS💙
#team SZ❤️
*Ummu Najma ce😂*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
25🧝🏻♀️
22/Ramadan/1442
Yau da zazzafan ciwon kai na tashi domin tun jiya da Ruma ta kira tana kuka ta faɗa min jinnun Zayyad sun motsa na rasa sukuni don matsawa sukayi wai sai nazo,
Da ƙyar muka shawo kan matsalar ta waya ina faɗa musu abinda zasuyi mishi, basu sani ba amman ni nasan nice sanadin hakan tunda ni na ɓata mishi rai,
Bazan so na shiga rayuwar bawan Allah bayan wahalan da yake ciki na ƙara mishi wani a kai ba,
11:07am na fito da kwanukan da mukayi suhur dashi zan wanke dan tun a daren jiya na samu tsarki shiyasa dani akayi tahajjud, ban samu barci a daren jiya ba ko kaɗan shiyasa yau na makara,
A gaggauce na fara aiki na don na samu gamawa nayi wanka na tafi gidan mama kafin azahar tayi, kwankwasa ƙofar gate da akeyi ya jawo hankali na, na miƙe tare da shiga ciki na saka hijab akan pjamas ɗina sannan na fita duba mai knocking,
Tsananin mamaki na ya gaza ɓoyuwa yayin da idanuna sukayi tozali da aunty Amarya fuskar ta yayi fayauu kaman mara lafiya, kaman ko yaushe hannun ta ɗauke da casbi,
“Zan iya shigowa saudat?”
Tattaro nutsuwa na nayi, nayi saurin matsawa a hanyar don bata daman wucewa, murya na yana rawa nayi mata sannu da zuwa na shigar da ita parlor dan nasan tabbas a kan Zayyad tayi tattaki,
Gaisawa mukayi sannan na shiga na kira aunty Yusrah da yadiko suka fito suka gaisa sannan ta fara sanar damu abinda ya kawo ta,
“Ban sani ba ko kun samu labarin abinda yake faruwa da yarona daga wurin Saudat to shine abinda ya kawo ni nan nazo niman alfarman ki saudat…..”
“babu wanda ya sani aunty, daga ni sai ku sai kuma Allah, ba zan faɗa ma kowa abinda na gani ba tare da izinin ku ba” nayi saurin katse ta kada ta sanar dasu,
Murmushin jin daɗi tayi tana ƙara yabawa da hankali na, bata yi tsammanin ba za’a samu matsala daga ɓangare na ba lokacin da na fahimci ciwon Zayyad amman gashi saima waraka da sauƙi da ake daɗa samu daga gareni, yarinya ƙarama amma akwai sanin yakamata, ta faɗa a zuciyar ta,
“Naji daɗi kuma na gode sosai saudat da kika mutunta mana sirrin mu kuma kika taya mu ɓoye shi, Allah yayi miki albarka” “ameen Aunty”
Ta maida dubanta wurin su yadiko da suke zaune “dan Allah idan ba zan takuraku ba, ina son ku ɗan bani aron Saudat in tafi da ita can gidan namu idan babu matsala, a halin yanzu wani ƙaramin matsala muke fuskanta a gidan, kuma saudat tana da daman magance mana wannan matsalar ko kuma ta sauƙaƙa shi, don Allah kui min wannan alfarmar ku ceci rayuwar wanda yake a halin gangara”
My words sounds like a puzzle to them, duk sun shiga ruɗani musamman yadiko, gwanda ita Yusrah ta san wani abu kaɗan akai, tana da yaƙinin maganar nan da akeyi a kan Zayyad ɗin nan ne dukda bata san komi gane da hakan ba, amman yadiko kam an saka kanta a baƙin laida,
STORY CONTINUES BELOW

Ganin girman zancen da ya haɗa harda iwana a baƙon wuri yasa tace “hakan ba zai gagara ba Hajiya amman a bari yayan nata ya dawo daga wurin aiki ta nemi iznin shi in yaso sai tazo daga baya”
“To Shikkenan hakan ma yayi, na gode, na gode sosai, zan tafi yanzu amman ki ɗan zo da wuri saudat dan Allah”
“Insha Allah aunty yana yarda zan zo”
Daga haka muka mata rakiya zuwa gate su Yusrah suka tsaya muka ƙarasa har mota na bata addu’a da zasuyi mishi kafin nazo, mukayi sallama suka wuce,
*******
Dube_dube yake yi cikin drawern fuskar shi ɗauke da murmushin da ya bayyana haƙwaran sa, ya baza kunnuwa ne kawai yana jin endless lissafin sadiya, yana comparing duk wani action nata da na boɗɗi a cikin ƙwaƙwalwar shi ko zai samu banbanci, he just love the silent fulani babe so much!
“Dadyn Arifff kana sauraro na ma kuwa?”
“Inajin ki mana momyn Arif just continue” ya faɗa lokacin da ya ciro wasu takardu daga draqern ya zuba a kan bed yana arranging ɗinsu a cikin file,
Murmushi tayi jin amsar shi, lallai yau ranar sa’ar ta ce shiyasa tunda taga mood ɗinshi kwana biyun nan is lightened take tatsan shi yanda taso, yauma ba zata bari ya wuce ba sai ta samu babban kaso,
“Yauwa to kaga bayan shi, akwai 200 thousand na takalman baby set 5 na Arif set 7 da nawa i think 5 ɗin zasu isheni saidai idan zaka ƙara a kai sai na ƙara yawan su, then kuɗin tailor shima i think dubu ɗari da…”
“Wait dan Allah, kinsan bani son irin wannan gutsi_gutsin lissafe lissafen ƙwaƙwalwa na ya gaji da ɗaukan caji, a nan wurin kinyi mun lissafi almost 1 million, ke baki san ana shan wuya kafin a samu kuɗi bane?”
Ɓata fuska tayi ganin yanzu ya ɗago yana kallon cikin idanun ta
“Yanzu ba zan samu ba kenan?”
“Zaki samu mana, daman wahalan ai maku akeyi idan baku amfana dashi ba arziƙin bayi da amfani kenan”
Nan da nan annurin fuskar ta ya dawo ta hau washe haƙwara tana zuba mishi ruwan addu’oi da godiya,
Murmushi yayi yace “halimatu kenan kada ki damu indai ta fannin kuɗi ne baki da matsala dani,akwai ma wani abu da nake buri nan gaba kaɗan, idan na samu nayi miki alƙawarin a ranar credit card ɗina a hannun ki zai kwana ki ciri duk amount ɗin da kike so ko nawa ne! Kawai ki taya ni da addu’a ki saka yara na ma suna min addu’a kullum Allah ya sa buri na ya cika nan kusa zaki sha mamaki wallahi”
“Ya Allah ka dube mu da idon rahama ka cika ma wannan bawan naka burin shi ko menene shi, ko menene wannan buri ya Allah ka cika masa idan ba alkhairi bane ka maida shi ya zamo alkhairi ka bashi ya Allah albarkacin watan Ramadan, ya zul_jalalu wal ikram, ya rabbul arshil azeem, ya rahaman ya raheem Allah ka biya ma mijina dukkan buƙatun shi na duniya,
Insha Allah ka samu wannan abun, just wait and watch how your wishes are going to be fulfilled in a blink of an eye” ta ƙarasa tana sake murmushin da ya bayyana farincikin dake , zuciyarta ta kusa kwashi ganima, don tayi alƙawarin duk ranar da ya danƙa mata card ɗinshi a hannun ta sai ya zubda hawaye,
Sulaiman couldn’t help but to laugh hesterrically ya tattari file ɗinshi ya fita yana dariyan da yafi shekara baiyi irin shi ba, ta zaƙe tana taya shi niman cikar burin zhi wurin Allah amman duk ranar da ya samu hakan sai ta zubda hawaye…
******
“Abinda na guda kenan tun farko baby, bani son abinda zai saka ina wasa da lamarin Saudat, ita amana ce, kullum ina tunatar da zuciyata ita amana ce a wuri na bani son abinda zai kawo mata cutarwa ko kaɗan”
Numfashi taja tana ganin yanda yabi duk ya shiga damuwa, sunyi masa tabaibayi ba zai taɓa iya rejecting ɗinsu ba saboda matsayin da suke dashi a wurinshi,
“Babu daɗi kam amman kada ka ɗaga hankalin ka tunda taimako zata je yi, ta yuyu idan ta taimaka itama Allah ya dube ta da idon rahama yayi ya kawo mata sauyi vikin ƙaddarar ta saboda ta taimaki musulmi”
“Kina maganar taimako, kinsan wani irin taimako ne zatayi musu idan taje ɗin? Idan ita ta cutu wurin taimaka ma wani fah, me zance ma Allah?”
“Allah ma ya kiyaye, ka daina saka irin wannan tunanin a zuciyar ka, gashi last time da taje ta dawo babu abinda ya same ta saima kumatu da ta ƙara irin naka, ta fada tana lakatan shi a kunci zuwa jikin shi da sigar tsokana ta samu bacin ran ya barshi,
Janyo ta jikin shi yayi yana dariya “bakiyi 40 ba tukunna baby, i told you to stay away from me kada ki sani yin abinda banyi niyya ba”
*******
Mutanen nan basuyi haƙuri har na shirya na tafi da kaina ba, ƙarfe 3 sharf suka turo da mota, kaya na ma sama_sama na haɗa kada na bar driver yayi ta jirana na fita muka tafi,
Fitowar shi kenan daga part ɗin aunty amarya ya nufi motar shi da akayi parking a filin gidan don bai wani daɗe da shiga ba ya fito,
Har an bude mishi mota zai shiga ya tsaya ganin shigowar motar mu yana son ganin wanda zai fito a ciki,
Haka kawai naji a jiki na ana kallo na, banga kowa ba kaman na wuce ciki amman na tsaya ina waige_waige caraf idona a cikin na baban yaya yana min kallon ƙurilla amman yau banga tsana da kyara da ko yaushe yake gwada min ba kawai yana kallo na ne normal amman kuma kallon ya wuce mizanin Shari’a ko kyafta ido bayi yi,
Banyi karambanin ƙarasawa na gaida shi ba gudun kada ya sake yarfa ni, na wuce part ɗin Hajiya abuna,
Shima bai damu da hakan ba don bayi son na cika rawan kai, amman yaji daɗi mara misaltuwa tunda yanzu na dawo gidan ba zai taɓa bari na tafi ba ko ta halin ƙaƙa,
Saida na shiga muka gaisa da Hajiya da aunty Zaytoon da Batool suna ta murnan gani na sannan na fito na ɗauki hanyar part ɗin oga Sitifid,
Tsaye yake jikin window yana leƙe na yana dariya ganin yanda nake tafiya kaman ina kan ƙaya Finally yayi nasara wurin dawo dani kusa dashi tunda shi bayi da daman zywa inda nake ba zai taɓa bari na sake yin nesa dashi ba,
Har na shigo muka gaisa da aunty muka gama tsalle_tsallen mu da Ruma yana tsaye yana leƙen mu ta ƙofa amman yana ganin mun nufo ɗakin yayi saurin komawa ya hau gado ya ƙudundune cikin duvet,
Duk sallaman da mukayi yana ji yayi biris damu san muyi tunanin yana cikin mawuyacin hali da gaske, cike da tausayawa Ruma take masa sannu yana ji yana dariya ƙasa_ƙasa amman cikin rashin sa’a na jishi,
Koda yaso yayi acting na tashin aljanu ba zai iya ba, kenan da gangan yasa aka ɗauko ni ba wani abu ne yake damun sa ba da gaske?
Ƙarasawa jikin flower vast nayi na ture shi a ƙasa sannan na saki razanannen ƙara sai kawai naga Zayyad ya duro a gaba na ya riƙe hannu na yana duddubawa, wani electric shock naji ya ratsa ni tun daga hannu na da ya riƙe har tsakar kaina zuwa ƙafafu na,
Shi Zayyad baisan cewa ni ba irin shi bace?
Saurin ƙwace hannu na nayi daga riƙon shi kada ya samu nasarar gutsure min azumi, naja baya kaɗan hakan yasa yasha jinin jikin shi shima ya matsa baya yana ƙare min kallo don ya tabbatar lafiya nake…………..🤦🏻♀️
Jiya banyi replying comments ba ayi min hakuri dan Allah
Love You my fans😍
#team SS❤️
#team SZ💙
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
26🧝🏻♀️
“are you okay?” Ya tambaya yana kallon cikin idanu na wanda ke cike da ɓacin rai na sanin Zayyad lafiyan shi ƙlau amman yasa aka je har gida aka ɗauko ni bayan ko kwana 3 banyi da barin gidan nan ba ya saka an maido ni,+
“Babu abinda ya same ki ko? Baki ji ciwo ba ina” ya canza harshen shi sanin cewa turancin nawa ƴar dagiya ne sai a hankali to ba lallai na gane abinda yake nufi ba,
Nanfa na daɗa ɗaukan zafi, laifi biyu, yayi ƙarya kuma yanzu ya raina ma aji na, a tunanin shi bani jin turancin gaba ɗaya ne ko mene da are you okay ma sai ya fassara min? Kawai mayarwa ne bani iyawa daidai sai kuma rubutawa,
” i don naw (i don’t know)” na faɗa tare da kawar da fuska dan ya fahimci fushi nake yi sosai, shiru kawai yayi ba tare da yace min komai ba yana ƙare ma fuska na kallo, Ruma ma ta maida mu TV ne kawai tana kallon show ɗinmu da bayi ƙarewa,
Da na gaji da tsayuwan shirun na juya tare da murguɗa mishi baki a karo na farko murya na a ƙasa amman cikin faɗa_faɗa nace
“Me yasa zaka min haka? Kuma kana yi kaman ma baka san laifin da ka aikata ba?”
“Wani laifin kuma nayi babes?”
“Oh kana tambaya ta kenan baka ma san abinda kayi ba? Ka kalli fa lafiyan ka ƙlau babu abinda ya same….mtsww” kasa ƙarasa magana nayi na saki ƙaramin tsakin da bansan lokacin da ya fito ba yayin da na ɗauki barin ɗakin,
Har na kai ƙofa yayi saurin nuni ma Ruma ta jawo ni baya tana taya shi bani haƙuri, ni kuwa na sha murr ina kallon su duka cike da masifa a idona wanda dukkan su basu san ni dashi ba _uhm, ko nima bansan kaina dashi ba_ saidai yarinta na ya bani duk a cikin love ne nima zan fara zuba mulki na tunda na san ana ji dani
“auntynah kiyi haƙuri dan Allah, wallahi da gaske ne bayi da lafiya kawai ganin mai maganin shi ne ya saka shi warware wa ko ba haka ba ya Zayd?”
Saurin gyaɗa kai yayi making a sympathetic face, tace
“Ka gwada mata ciwonka ta gani ta tabbatar”
Jan hannun rigan shi yayi suka gwada min wani tsohon raunin da a lalace ya kai sati biyu, ina ganin ma tun kafin nasan da ciwon shi yaji raunin don har ya soma warkewa, amman mutanen nan suka dage wai shekaran jiya da daddare yaji, bani da zaɓin da ya wuce na yarda dasu tunda sun nace,
Haka na biye musu na zauna ina tambayar shi abubuwan da yake ji kaman da gaske, a cikin su harda ciwon kewa da ciwon zuciya ya zayyano,
Idan yayi wani abun na kalle shi sai naga ya koma min yaro ɗan shekara goma sha, bayi da zafin kai ko kaɗan kaman na zazzaɓin yayan shin nan, yana da daɗin mu’amala da sauƙin sha’ani shi yasa ya dabaibaye zuciya ta cikin ƙanƙanin lokaci don na wahala da halin Yarima wanda yayi kama da na sulaiman a wancan lokacin, yanzu ina buƙatar canji…
*******
Tafiyar da ya rage musu su isa office bai fi kilometer 1 ba amman yasa driver ya juya ya maida shi gidan su don idan baiyi mata magana a yanzu ta san mai suke ciki ba baisan lokacin da zata fuskance shi ba,
STORY CONTINUES BELOW

Da ya shiga saida ya tabbatar bamu fita ba daga wurin mai ɗauko mishi rahoto sannan ya shiga part ɗin Hajiya unlucky to him, bani wurin sai kawai ya wuce part ɗin aunty amarya ta baya yana da tabbacin zai same ni a can,
Daidai zai shiga wayar shi dake aljihu ya fara ringing, cirowa yayi amman bai amsa ba saida ya isa cikin parlourn ya sama ma kanshi wurin zama kafin yayi picking ya saka a kunnen shi tare da yin shiru yana sauraron mai magana,
“Dadyn Arif ina ta jira fa, na jika shiru baka turo min kuɗin nan ba kuma zanyi ordern kayayyakin nan ne yau”
“Ina tsaka da wani abu ne yanzu Sadiya, ba zaki iya jira na dawo gida ba?”
Saida ta sassauta murya ta shagwaba shi tace
“Ayyah kayi haƙuri idan da hali kayi min tranfer yanzu, basu turo kaya ne har sai an tura musu kuɗi kada muyi jinkiri a kwashe masu kyau ɗin”
“Naji” kawai yace sannan ya fara ƙoƙarin tura mata ba tare da ya nemi inda nake ba,
**********
“Can wurin shima yana ciwo?”
Gyaɗa min kai yayi tare da tauna labben bakin shi na ƙasa saboda yanda yaji lokaci ɗaya kaman ana watsa mishi tafasasshen ruwa ana kwaile mishi fatan jikin shi, ni kuwa ina ganin kaman hakan ma da yake yi duk shiri ne,
_Daman ya san haka zai faru kuma ya shirya ma hakan tunda ba yau ya fara faruwa ba, amman idan a kan saudat ne? Ya shirya shanye duk wani ƙunci da azaba_
“Amman yaa Zayd kana yin duk addu,o,in da na baka?” Na tambaya babu wasa cikin murya na,
Gyaɗa kai yayi ya ƙura min na mujiya yana ƙoƙarin ɓoye abinda yake ji ta hanyar shimfiɗa min simple smile a saman fuskar shi,
“Na safiya da maraice fa, kana yin su duka?”
Gyaɗa min kai yayi tare da faɗin “yeah, kewar rashin ki a cikin gidan nan ne kawai bani kiyaye wa wajan hana zuciyata yi, da kuma tsumayen jiran amsa na..”
“Ya zayd bari na je wurin Fa’iza na karɓo abu ina dawowa” Ruma ta faɗa tare da rufe littafin dake hannun ta wanda ta ɗauko cikin jerin littattafan dake ɗakin da aka ajiye su na musamman don ɗebe ma Zayyad kewa, ta maida shi wurin zaman shi ta fice,
Saida naga ta rufo ƙofar sannan na juyo ina kallon shi daman already ni yake kallo,
“Nayi tsammanin zan iya jira na tsawon lokaci kafin na nemi jin ra’ayin ki a kaina amman na kasa haƙuri, ki faɗamin dan Allah ko na samu wuri a zuciyar ki”
Sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina wasa da zoben hannun na, ina ƙoƙarin danne murmushin dake ƙoƙarin suɓuce min, I can’t help but to blush, duk lokacin da na tuna nima wata ce a zuciyar Zayyad a halin yanzu, nakan ji sanyi da daɗi ya mamaye zuciya ta kaman na tashi nayi ta tuma tsalle ina murna, bansan me yasa nake son shi da yawa ba,
“Babe dan Allah kice wani abu this silence is killing me”
“Mmm n..ni..ni b.bani da w..wani amsa..a..yanzu”
Na faɗa murya na yana rawa wanda bansan dalili ba, kunyar sa sosai ya kama ni,
“Dan Allah ki nemo, ni ko ƙarya ne kiyi kice kina sona, please!”
“Uhmm Sitifid kenan ai Allah yana kallo na, ƙarya bayi da kyau”
“Me kika ce?”
Ya tambaya yana bina da wani irin kallo don ni karan kaina ban san da sunan da na kira shi ba, siɗin_siɗin na miƙe na bar ɗakin ina ƙunshe dariya na,
Ina fita parlor na ja birki na tsaya don tunda na fito ban lura dasu ba ina ta faman baza murmushin haɗuwa da masoyi, idanu na suka shige cikin na babban yaya da ya saka Ruma a gaba ta tsaya kaman sabuwar soja,
duk tambayoyin da yake jero mata bata samu amsa ko ɗaya ba, tsoron fitowa na ni kaɗai daga ɗakin Zayyad take yi dukda kuwa Sulaiman ya san amfani na gareshi amman kaɗan daga aikin shi yanzu ya birkice mana,
A wannan lokacin ban ɗauke idanu na daga cikin nashi ba saidai murmushin dake fuska na ɓatt ya ɓace, na tsaya rama kallo na tunda ai yanzu ni budurwan ƙanin shi ne haka kawai ba zai dinga kallo na kuma ya kalli banza ba,
“Zaki iya tafiya” ya faɗa idanun shi still a kaina, ko a jiki na na juya zan tafi da sauri yace “ba keba, ita nake nufi” ya nuna Ruma da yatsa,
Da jin haka ta juya ta fita tana hamdala tunda bai ɗau zafi ba, tana fita yace min “ƙaraso magana zamuyi”
Zuciyana yana lugude up and down na ƙarasa tsakiyar carpet dan zauna da sauri ya dakatar dani tare da nuna min kujeran dake gefen nashi, “zo ki zauna a nan”
_ya Allah kasa ba laifi nayi ba, ka tsare ni daga fushin zazzaɓi_
Cikin takun nutsuwa na ƙarasa wurin da ya nuna min na zauna na sada kaina ƙasa, with every movement i took his heart away yayi kewana fiye da tunanin mai tunani na rashin gani na da yayi kwana biyu,
Ba don karatu na yana da muhimmanci ba da ba zai jira nayi ba zaiyi zancen auren mu, amman ba zaiyi gangancin hakan ba don dariyan Sadiya kaɗai ya ishe shi jin kunya, ya auro gidahuma don yanzu kam ya daina kiran ta daƙiƙiya,
“Wani shiri kika fara yi na makaranta” naji tambayar shi ta faɗo a sama,
_ni kuma wani shiri zanyi?_ na tambayi kaina,
“That’s what I hate, ina magana ma mutum yayi min banza, talk dan allah”
Ɗagowa nayi da tsananin mamaki, jin yau maganar shi soft and calm, babu tsauri babu tashin hankali a cikin muryan shi, anya wannan babban yaya ne?
“Kinsan boarding school ne dole kiyi masa shiri dukda dai zaki dinga dawowa gida duk weekend, and idan nace gida ina nufin nan gidan kenan saboda ina lura da al’amuran karatun naki don kinyi baya da yawa Saudat”
Kutt, daman har ya san sunana ko yau ya fara jinsu?
“Ba shiru zaki yi min ba fahh I don’t have all day, ki faɗa min abinda kike so na makaranta Shikkenan ba cewa nayi ki mutu ba balle ki tsaya kokwanto” ya faɗa wannan karon a ɗan kausashe,
“Uhm b..babu ni bani buƙatar komai”
“Haka zaki tafi single kenan, baki da kayan sawa babu abinci babu komaii?”
_nifa banma san abinda zance mishi ba, yanzu tsirara ya ganni da zai min maganar kayan sawa ko yaga alaman ciwon yunwa a jiki na?_
“Wayan waye wannan a hannun ki,” ya faɗa lokacin da idanun shi suka hasko mishi ƴar ƙaramin wayar da Ruma ta bani mai keypad,
“Nawa ne, Rumaisa ne ta bani”
_Nice, ta iya bada amsa yanda ba sai mutum yasha wahalar tambayoyi masu yawa ba zata bashi gamsashshen amsa_
Ya ciro dalleliyar wayan shi Samsung Galaxy S20 ya miƙa min
“Here, samin digits ɗinki a nan”
Tsantsin wayan kaɗai ya sanya min tsoro kada ya suɓuce ya faɗi ya fashe, luckily ya saka a kan dialer so bansha wahalar saka numbern ba na miƙa mishi wayan a hannun shi, bai sake ko tari ba ya tashi ya fita,
Daga nan na wuce part ɗin hajiya luckily sulthana bata gidan sai mataimakiyan ta hajiya nana, har aka sha ruwa ban je ko ina ba mukayi tarawih sannan muka kutsu ɗakin aunty Zaytoon yin hira wanda yawanci su sukeyi ni nawa ido don yanzu bani gangancin yin kallo a gidan saboda shi,
Ina zaune Ruma tayi pillow da cinya na wayana ya shiga ringing, da saurin na ɗaga ina tunanin Zayyad ne sai kuma naci karo da baƙon number………….🤦🏻♀️
Love you my fans😍
#team SS💙
#team SZ❤️
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Don’t be afraid of making mistakes, as it is the only route that you must follow to reach success*💡
27🧝🏻♀️
Ɗaga kan Ruma dake saman cinya na nayi na Miƙa mata wayan,
“Gashi ki amsa, inaga ke ake nema”+
“Anya kuwa? Bani kiran kowa fa da layin bayan ƴan gida kuma suma na faɗa musu na daina amfani dashi, bama kowa ne yake da wannan contact ɗin ba amman kawo mu gani” ta faɗa tare da amsan wayan ta saka a kunnen ta tare da yin sallama,
Sulaiman dake study room yana zaune, ya tasa takardu a gaban shi amman ya kasa komai haka kawai yake jin shi wani iri cikin ɓacin rai, he doesn’t have someone to talk to, yanzu kuma ya kira Saudat don yaji muryan ta ko zai samu ranshi yayi mishi sanyi wannan mahaukaciyan yarinyar ta ɗauka zata ƙara ɓata mishi rai,
Haɗe rai yayi kaman tana gaban shi ya ɗaure fuska ɗan murmushin dake saman fuskan shi ya ɓace cikin kaushin murya yace
“Bata wayan ta kafin yanzu ranki ya ɓaci”
Bata sake magana ba tayi saurin miƙa min wayan tare da faɗin “gashi, babban yaya ne” wanda hakan ya jawo hankalin ƴammatan ɗakin dukkan su suka juyo suna kallo na cikin firgici da jin abinda Ruma ta faɗa, don dukkan su sun sha mamakin ƙarfin dalilin da har babban yaya ya sami contact ɗina ya kira ni a wannan lokacin it must be something very big,
Kallon su kaɗai ya dasa min tsoro a cikin raina, kaman wanda tayi wani laifi irin wannan kallon tuhuma haka ? Sun zuba kunnuwa suna sauraron jin ba’asi, jiki na yana rawa na saka wayan a kunne tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi na,
Lumshe idanun shi yayi ya ware akan wrist watch ɗinshi ƙarfe 10 har da mintuna 8,
“Ki tashi a cikin mutane, da ke kaɗai nake son magana ba da gayyan ƴan uwan ki ba”
Kalkon su nayi ɗaya bayan ɗaya naga har yanzu hankalin su bai bar kaina ba suna jiran jin abinda zan faɗa bayan sallaman da nayi basu ƙi ma nasa musu wayan a handsfree suji komai ba, ga kuma umarnin oga kwata_kwata,
Ignoring their looks na miƙe a hankali na fita daga ɗakin na zauna a parlo amman abinda ban fahimta ba shine yanda akayi mutanen da nake zauna dasu saboda wani dalili na ƙanƙanin lokaci suka zamo ƴan uwana, ko daya ance musulmi ɗan uwan musulmi ne, rasa abinda zan faɗa nayi har saida ya tambaye ni “kin tashi” na amsa da
“Eh” a taƙaice,
Shiru ne ya ratsa tsakanin mu na ƴan sakwanni kafin nayi saurin gaishe shi “ina wuni” ba tare da saka ran zai amsa ba,
“Lafiya ƙlau”
“Hmm..” na furta saboda rasa abin faɗa,
“Uhm.. me yasa Ruma take amsa kiran ki? Ko shima baki iya bane?”
“A’a na iya, banyi tunanin kai ka kira bane”
“Ohh..” ya faɗa tare da ɗan zaro ido “daman akwai wa’inda kike jiran kiran su ne?”
“A’a ba haka bane” nayi saurin kare kaina “sim ɗinta ne a wayan, na ɗauka ita ake nima”
“Ok, amman ki kiyaye, yanzu karatun ki shine zaki sa a gaba, bani son wasa Saudat, ban yarda da shagala ki zauna tara ƙawaye kuna abinda bai kamata ba, dukda size ɗinki yafi shekarun ki amman you are too young, just focus! kada ki kuskura wani samari ya ɓata miki daman da kike dashi ya saka ki bar lokaci ya ƙure miki baki amfana da komai ba, a yanzu karatun ne kawai gatan ki idan lokaci yayi zaki samu wanda ya dace dake kin jini?”
STORY CONTINUES BELOW

Baki na a sake shaa kaman yawu zai ɗiga, na ɗago wayan na duba da kyau sannan sake mayarwa kunne na,
_anya wannan babban yaya ne ba aljanun Hamma Zayd ne suka kira ni ba? Irin wannan surutu? Daman yana magana haka da yawa? Kuma a sani na ya tsane ni sosai me yasa yanzu kuma ya damu dani?_
Murya na rawa nace “mmn…na..naji insha Allah”
“Good, meye size ɗinki? Tsayin rigan da kike saka da….a..and stuffs” ya faɗa a karo na farko muryan shi na rawa dan ya kusan sakan layi, ya sakankance har zai tambaye ni abinda bai dace ba ya manta wannan Saudat ne ba baby sadyn shi ba, itama dai rabon da ya saya mata wani abu da kanshi tun tana Amarya, yanzu tafi gane tayi komai da kanta dan ta samu ƴan canji,
“Ban san sayis (size) ɗin ba, ƙanwar Hamma Khamis ne take min ɗinki kuma bata faɗamin idan ta gwada”
“Toh! Shikkenan daman ina ganin ya kamata mu fara shiri ne don lokaci ya ɗan ƙure mana sauran kwana 14 zuwa 15 a koma school zaki buƙaci kayayyaki da yawa, amman ki bawa Ruma wayan zamu ƙarasa magana da ita”
“Toh!”nace na miƙe na nufi hanyar ɗakin
*****
“To meye na tada jijiyoyin wuya kun zauna kuna ta musu a kan abinda bai shafe ku ba? Kun san dalilin da yasa ya kira ta ne?” Faɗin Zaytoon
Fa’iza ne ta amsa da “bamu san dalilin da yasa ya kira ta ba aunty Zaytoon amman kuma menene dalilin da zaisa ba zatayi mishi magana a nan muna ji ba sai ta fita? Eh meye ne dalilin da yasa ta fita?”
“Munafurci mana!! Babu komai banda munafurci, ni ai na daɗe da lura da ita yarinyar nan ba ƙaramar makira bace kina ganin ta kaman wata saliha tun ba yau ba tabi ta shige ma ya Zayyad duk yanda bawan Allahn nan yake baya_baya da mutane saida ta san yanda tayi ta samo attention ɗinshi,
yanzu kuma annamimancin nata bai tsaya a nan ba tana son shima ya Sulaiman tayi mishi mamaya don ta samu gindin zama a gidan nan to ba zai yiwu ba wallahi” Nana ta ƙarasa tana fitar da huci kaman ni ɗin ce take gani a gaban ta
Ajiye wayan hannun ta Batool tayi ta tashi ta zauna tana fiskantar su
“Wai ku ina ruwanku? Banda shiga uku da baƙin hali menene ruwan ku da ita? Ke! idanma son ta babban yaya ya kira ta yace yana yi mai ruwanku tunda ba mijin ku bane ballantana ta zamo muku kishiya?”
Suna cikin musanyar kalamai na shigo ɗakin da sallama sannan na miƙa ma Ruma wayan nace “gashi wai zaku yi magana”
Tana karɓa itama ta miƙe ta fita sanin bayi son hayaniya na samu wuri na zauna sai tsilli_tsilli nake da ido, babu wanda yace min komai a cikin su amman ina kallon a cikin idanun da yawa daga cikin su,
******
12:07pm
Bubbuga ni take yi da ɗan ƙarfi wanda hakan yasa ni tashi a firgice na zauna ina murtsuka idanu,
“Me ya faru Ruma Lokacin tahajjud yayi ne?”
“A’a ki tashi dan Allah ciwon ya Zayd ne ya tashi ya…”
Ban ko ƙarasa jin bayanin ta ba nayi wani tsalle na dura daga gadon sannan na zura a guje babu ko mayafi a kan pajamas ɗin dake jiki na,
Na ƙarasa part ɗin su da gudu ta ƙofar baya banga kowa a parlo ba na zarce bedroom ɗinshi, na gano shi cikin yanayi marar daɗin gani aunty Amarya ma ta kasa shiga ciki tana tsaye a ƙofa sai kuka take yi….
***
Zayyad yana shan wuya sosai, ɓangare ɗaya akwai yiwuwar samun sassauci idan case ɗinshi yaje hannun mahaifina a ɗaya ɓangaren kuma akwai sirri na da kuma sirrin shi,
Kaina ya kulle wallahi na rasa wani mataki zan dauka wajen samawa mutumin da nake ƙauna lafiya ba tare da an samu wani matsala ba, ba tare da wasu sun san sirrin shi ba kaman yanda babban yaya da sauran ƴan uwan shi suka buƙata kuma ba tare da sunje ƙauyen mu an faɗa musu ni BAZAWARA bace kuma korarriya, ba lallai bane ma su barni na shiga garin tunda rayuwata suke nima,
Malam Arɗo bayi yarda yaje wani wuri da sunan yin magani saidai aje wurin shi, koma ace yana zuwan… Idan na ɗauko shi nayi babban laifi tunda nayi shishshigin ƙetare iyakan da sukayi min,
Wa zan shawarta a kan wannan lamarin ne? Rumaisa ne ko aunty Yusrah? Kowa daga cikin su sai na sanar dasu abinda basu sani ba game da kowani ɓangare kafin su iya bani shawarar da zai amfanar,
Haka na ƙarar da daren ina saƙa da warwara, daidai za’a tashi suhr barci mai nauyi ya ɗauke ni wanda ya saka ni makara ban tashi ba har saida aka idar da salla a masallaci, Tirƙashi!! Ɗaure fa kenan zanyi? Amman Ruma ta cuce ni da bata tashe ni da ƙarfi na dole ba, nayi suhur ɗin ma yaya aka ƙare ballanta a kaiga tazarce?
24/Ramadan/1442
Ba tare da dogon bayani ba yau da yunwana na tashi, tun karfe 9 wani mahaukacin yunwa ya riƙe ni banda zufa babu abinda ke keto min idanu na zuru_zuru ko ƴar yatsa na bani iya motsawa ina tsoron na karya na ɓaro 60,
gashi yau mai yaye min damuwa na ma yana cikin damuwa, ba ƙaramin rauni yaji ma kanshi ba ƙaryan ciwo ya jawo mishi na gaskiya, ko shiga banyi na duba shi ba don ba lallai na iya sake jure kallon shi ba nayi zama na a part ɗin Hajiya zuwa azahar bani komai bayan maimaita kalman shahada amman haka ana la’asar babban yaya ya ɗaga ni kuma dolen ƙaniyana na tashi ko gigin mishi musu banyi ba,
Ina ganin algarara_algarara har muka isa shopping mall daga ni sai Rumaisa ta fara jida min kaya kaman hauka amman da ta kira ta faɗa mishi yawan su yace yayi kaɗan a ƙara,
A wannan ranar na yarda babban yaya shine baƙin ƙaddara ta, don bamu bar wurin ba sai da aka sha ruwa don ƙarshe zuwa yayi da kanshi yaga muna mishi shirme,
Tsoron abinda su nana zasu faɗa wannan karon idan suka ga tulin kayan nan ya kama ni tunda har suka yi judging ɗina a kan wancan ɗan ƙaramin abun inaga wannan lokacin asiri zasu ce nayi mishi,
Saidai kuma abinda na lura dashi shine da ina zaune wuri ɗaya wahalan da zansha na azumin ɗaure sai yafi wanda nasha a gararin siyayya,
_all thanks to Hamma Sulaiman, na sha ruwa lafiya_
******
25/Ramadan/1442
“What’s all this dadyn Arif? What are you trying to prove?”
Daga kafaɗun shi yayi tare da ɗan kaikaitar da kai yace “nothing! I don’t need to prove anything to you halima”
“Baka yi kama da maƙaryaci ba amman idan kace min babu wani abu a tsakanin ku ƙarya kake yi, haba! Abinda kake mata is too much so much attention for her for nothing…hankali ma ba zai ɗauka ba, idan kuma kana son na yarda da kai yanzu kaje ka kore ta daga gidan ku tunda ba wai rasa matsuguni tayi ba, she is not homeless!”
“Ok since that’s the case, naso na kawo miki uzuri da taimako amman bani da buƙatar hakan a yanzu, one more thing
Na riga da na gama magana kuma kin san idan nayi niyyan abu bani fasawa, SAUDAT zata dawo wurin Hajiyan mu ta zauna kuma ni zan dinga daukan gaba ɗaya ɗawainiyar ta, kada kiyi musu dani Sadiya domin matsawar ki a kan lamarin nan zai saka na ɗauki matakin da ba zaki ji daɗin shi ba kwata_kwata………🤦🏻♀️
*Jiya banyi posting ba saboda bani ɗan jin dadi ayi min afuwa, and i can’t focus saboda matsalar idona shiyasa kwana biyu har comments bani samun daman replying*
*Inajin daɗin yanda kuke gwada ƙaunar ku wa ƙaramar bazawara comments ɗinku yana ƙayatar dani yana saka ni nishaɗi matuƙa,🤩 thanks so much for the love ❤️ ummu Najma tana kaunar ku sooosaii💃💃*
#share& comment
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
28🧝🏻♀️
“Ka daɗe baka yi min kishiya ba Sulaiman! Allah wadaran halin ka mai budurwan zuciya,
Yo idan aure zaka ƙara ka nimo babban mace mana wanda zamu haɗa ƙirji ni da ita mu daku a cikin gidan nan ba wannan tatsitsiyar abun ba, me akayi akayi Saudat?? Me ka zama samu jikin wannan ƙwailar ne?”+
Sulalewa yayi ya jingina bayan shi da jikin armchair da yake zaune ya ɗan miƙe ƙafar shi yana kaɗawa cike da taƙama,
_lallai cikin sauƙin kan da yaso yi ma Saudat yayi sake Sadiya ta shigo ciki har ta samun daman raina shi_
“Are You done?”
Shiru tayi bata amsa ba saboda takaici, da tasan hakan zai faru tuntuni da ta daɗe da gyara ma yarinyar nan wurin zama dan har yanzu bata shirya zama da wata a cikin gidan ta ba,
“Let me tell you something, a yanzu idan kika ga mutum baiyi abu ba to bai samu dama bane, i have money!! Ina da kuɗin da zan ɓarar na saka ko wace yarinya ta soni idan nayi niyya, kaman yanda nayi miki a baya,
Allah ya kiyaye amman ko mahaifina ne yanzu yace yana son Saudat matuƙar yana da dumus a cikin aljihun shi baiyi mata tsufa ba tunda ba yanzu aka fara ba, annabin mu (s.a.w) ma yayi, so do whatever you want amman wallahi idan kika ga ban auri Saudat ba…..inaga na shiga cikin ƙabari na ne!”
Ya kwashi wayoyin shi ya miƙe yana kaɗa kai irin na maza ƴan duniya tare da sake mata shu’umin murmushi yazo ta gefen ta zai wuce nan tayi kukan kura zata cukumo wuyan rigan shi yayi saurin hankaɗeta ta zuba a gado tana tsiyayar hawaye,
“Ko a mafarki kada ki saka ma zuciyar irin haka, sanin kanki ne ni ba lusari bane wanda bai san abinda yake yi ba ki maida hankalin ki gudun gani ba dai_dai ba” da faɗan haka ya fita daga ɗakin yana jin yanda take kuka tana kururuwa yaja hannun Arif suka bar gidan gaba ɗaya, za kaishi ma ɗaya uwarshin tun yanzu su fara sabawa,
********
“Sweetheart, dear, baby, boo, my heart, ga dai su nan da yawa sai wanda kika zaba”
“Idan munyi aure fa? Ko shima shaƙuwan naki zaki ci gaba da kira na?” Ya faɗa idanun shi still a cikin nawa ko kyafta su bayi yi, ban samu bakin magana ba Ruma ta amshe da,
“A’a haba ya Zayd! Ai zuwa lokacin kuma matsayin ka ya ƙaru sai kuma a koma irin su honey, darling, my soul, my love, sahibul ƙalbi, nisful hayat, noorul ayn and so on,
Kaidai kawai ka kwantar da hankalin ka wannan ƙawar tawa zata kula da kai kaman jariri, zata shagwaɓa ka ta lalata ka da soyayya, har sai yace ya ishe shi ko Saudat?”
Juyowa nayi na banka mata uwar harara sannan na miƙe daga kujeran da nake zaune,
“Hamma Zayd zan wuce tunda naga jikin naka da sauƙi sannan gobe zan koma gida muje mu ƙarasa shirin Sallah yau sauran kwana 4 ko 5 gashi ko ɗinki na ban karɓo daga wurin tela ba”
“Amman babes ban gama samun sauƙi ba, ki duba halin da nake ciki mana don Allah, ki tausaya min ki zauna har na warke gaba ɗaya sai ki tafi” ya faɗa cikin raunanniyar murya kaman ba shi da ƙanwar shi bane suka saka ni a gaba yanzu suna min tsiya,
STORY CONTINUES BELOW

“Kayi haƙuri ka barni na tafi aunty Yusrah nake ji wallahi, ita kaɗai fa zatayi shirin hidiman sallah da na yarinyar ta ƙarama ga kuma ƙaramin goyo, babu yanda zatayi ne wallahi amman nasan da tuntuni ta saka na koma”
“To idan muka yi aure kuma aunty Yusran taki yaya zata yi? Ko dan kina tausayin ta sai kije kiyi mata nata hidiman ki bar naki?”
_lallai ma ya Zayd zancen yake so_
Turo baki nayi gaba ina faman ƙunci dan na lura so yake yi firr ya hana ni tafiya ni kuma ba zan yarda ba,
Idan muna musayya a tsakanin mu Rumaisa bata cika saka mana baki ba saidai ta nimi wani abu na daban ta maida hankalin ta gare shi,
Shima baice min komai ba ya zuba mun idanu yana ganin yanda nayi kicin_kicin na haɗe gabas da yamma gashi pouted lips ɗina looks kissable for him, only if he got the chance!!
“Hamma Zayd filis ka barni na tafi, ko kana so nayi sallah babu sabon kaya ne?”
“Ba bayanin ba kenan Saudat, indai sabon kaya ne nan gidan shi kika zo zaki same su da yawa daga wurin mu amman sabida tausayin ki ga aunty Yusran ki zan barki ki tafi ba don raina ya so ba” ya ƙarasa in a sad voice nima saida ya bani tausayi,
“Zan zo da sallan na duba jikin naka kaji? Kada kayi fushi a sake samun matsala indai da gaske baka son tsayar dani”
Dariya mai sauti yayi wanda ya bayyana beauty points ɗinshi ya tashi ya zauna da kyau sai a lokacin na daɗa lura da yanda aka rufe raunuka da yawa a jikin shi,
“Duk abinda baki na zai faɗa miki tun daga zuciyata yake zuwa dan haka kada ki damu kanki kije ki taimaki aunty Yusrah ba zan saka a tsayar dake ba”
“Love birds, time up!! Yanzu aunty zata shigo bada magani dan haka mu ware” Ruma ta faɗa tare da jan hannu na mukayi hanyar ƙofa,
“Bye babes, ki kular min da kanki i will miss you”
Murmushi nayi ina ɗaga mishi hannu nace “bye gandai, a dage gobe ayi azumi filis”
******
“Suna part ɗin aunty ne? Gyaɗa kai Fa’iza tayi tace
“Eh!” Ɗazu suka shiga ina ganin zasu yi zaman su a can ne har a sha ruwa don banga alamun zasu fito yanzu ba”
“Na tambaye ki ne??” Ya faɗa yana jifan ta da mummunan kallon da ya sanya nan da nan ta sha jinin jikinta “A’a! Kayi haƙuri”
Baice komai ba ya juya hannun shi cikin na yaron shi zasu fita tace “babban yaya a bar mana Arif a nan kai kaje ka dawo”
“Naƙi! Ko zaki sanya ni dole ne?”
Saurin girgiza kai tayi tace “A’a sai kun dawo” yana bada baya ta kama mishi gwalo tana hararan bayan shi har saida ya mata nisa sannan taja tsaki tace “uban Nana a hali, Allah mana katanga tsakanin mu da shaiɗanun da suke yawan tunzura ku, a wata mai alfarman ma ba’a huta ba”
*****
A parlo suka samu Aunty Amarya tare da farouk da junior suna tilawan al-ƙur’ani sai kuka yake yi wai yauma zai karya azumi shi ba zai iya ƙarasawa ba ita kuma ta hana,
Har waje ana jiyo ihun shi yana yi kuma bai fasa karatun ba, lokaci ɗaya kaman anyi ruwa an ɗauke suka ji ɗiff yayi shiru, har saida tsoro ya shige aunty Amarya a tunanin ta wani abu ne ya same shi, ɗagowan da zata yi ta hango Sulaiman riƙe da hannun Arif baice dashi ƙala ba amman ya nemi sakata ya saka wa bakin sa sai zuru_zuru yake da idanu,
Sallama yayi ya shiga parlorn suka gaisa amman ya rasa ta ina zau fara tambayar inda Saudat take,
Yafi 10 minutes yana zaune yana sauraron karatun nasu sannan wani tunani ya faɗi masa yace
“Aunty ina Rumaisa? Ina so ta mayar da Arif gida ne idan ansha ruwa don ni ba wurin zanyi ba gaskiya akwai abubuwan da zanyi da daren”
STORY CONTINUES BELOW

“To Shikkenan kayi tafiyar ka kawai zan saka ta maida shi tana ciki ita da Saudat” ta dubi Farouk tace “ɗauke shi ka kai shi wurin su ya ƙaraci rigiman shi a can nima na yaro na ya ishe ni”
Murmushin biyan buƙata Sulaiman yayi ya mata sallama ya tafi amman yaso ya kalli fuskar ta ko sau ɗaya ne ko ranshi zai mishi sanyi,
*****
Fitowa na daga wanka kenan ɗaure da towel, har wa yau naƙi sabawa da saka bathrobe don a matsayin kaya na ɗauke shi, banga amfanin ɓata kaya biyu haka kawai ba,
Da gudu ya shigo ya rungumi Ruma yana ƙyalƙyala dariya amman yana gani na ya fara ɓuya a bayan ta,
“Aunty Rumaisa ɓoye ni ga aunty mai magani”
Ƙarasiwa kusa dashi nayi ina murmushi na miƙa masa hannu na da nufin yazo amman fir yaƙi,
“Aunty Rumaisa kice ta rabu dani I don’t like her”
“Aa Kaje ku gaisa ba zata baka magani ba, itama auntyn ka ce she is very nice and sweet”
“Are You sure?”
Gyaɗa masa kai tayi ya ƙaraso a ɗarare yayin da na sunkuya a kan guiwowi na don daidaituwa da tsayin shi yayi min light hug ya juya da sauri ya koma wurin ta, amman kafin mu bar ɗakin saida na san yanda nayi na jawo shi jiki na ya sake dani sosai yana min taɗin shirmen shi ina amsawa dake nima wata shirmammiyan ce muka ƙarasa kitchen na fara ɗirka masa ɗa’ami kaman zanyi kuka gashi ina gani amman babu daman ci,
Sai wuraren 9 kafin Ruma ta ɗauke shi zata maida shi gida saboda maman shi ta matsa da kira don ita taso ya kwana a wuri na ne, nima haka,
Ƙin tafiya da ita yayi saida na shiga motan yana maƙale a jiki na har muka isa gidan suka yi yin duniyar nan na fito mu shiga ciki naƙi don har yau ban manta gorin da babban yaya yayi min ba, ni kuma nayi alƙawarin ba zan sake shiga cikin gidan shi ba har abada,
26/Ramadan/1442
“Da ke wata ne sai ki bari zuwa gobe kafin ki tafi amman kaman kina zaune a kan ƙaya sai Alla_alla kike ki tafi ki barmu”
Kaman ba dani take maganar ba, ta maida hankalin ta kan akwatin kayana tana haɗa min harda abubuwan da ba nawa ba da ɗinkin da Hajiya tayi min lace 2 da atamfa 1ni kuma ina gyara wanda sulaiman ya siya min na makaranta da nufin zan barshi a gidan sai zan tafi makarantar tukunna na ɗauka,
Tayi mitan har ta gaji naƙi kula ta Zayyad ma da na shiga mishi sallama kaman bashi bane jiya yace ya amince na tafi ba yanzu kuma ya sani a gaba wai sai lallai_lallai na zauna zuwa gobe, bansan meye a goben da babu a yau ba kuma bansan me ƙarin kwaba ɗayan zai amfane shi dashi ba,
“To ni ba wata bane, babu kwana ɗayan da zan ƙara amman idan ke wata ce ki bini gidan mu mune mu zauna a can mana! Ai nayi ƙoƙari”
“To wallahi bari ki gani, indai babban yaya ya amince babu abinda zai hana ni binki mu tafi tare, kuna zan baki kunya don sai mutanen gidan naku sun gaji dani sun koro ni gida”
Daga farko na ɗauka da wasa take yi amman muna gama shirya kaya na ta ɗauki waya ta kira shi,
_kaga ikon Allah, mutumin nan da ƙoƙari, bata nemi iznin ubanta da ko yaushe yake cikin gidan ba amman gashi tana niman nashi da yake can wata uwa duniya_
******
Gama wayan su kenan da sadiya har ta gama fushin ta sauƙo tana niman sulhu amman shi bai shirya ba tukunna, basu taɓa sa’insa da har ta nemi mishi rashin ɗa’a ba sai a kan maganar auren Saudat, shi harma ya fara tunanin raba musu gida kada idan bayi kusa ta cutar da yarinya,
Shikan ma kwana 1 kenan harda wuni ɗaya baiyi tozali da ita a idanun shi ba, yana son ganin ta sosai amman baisan ta wani hanya zaibi ya samu ganinta ba tare da an zarge shi da wani abu ba kuma itama yarinyar bayi so ta gane ta raina shi,
Tsaki yaja ya jawo wayar shi dake fantsama ihu yayi picking ganin sunan Rumaisa ya saka a kunne tare da yin shiru yana sauraron abinda zata ce,
“Good morning dadyn Arif”
“Go straight to your point bani da lokaci”
“Yaya daman saudat ne zata tafi gida….” dumm ƙirjin shi ya buga jin ana nima ɓata mishi plan, yayi tunanin yanzu komai zai daidaita saudat zata saba da luxury life amman ana niman maida ta cikin talauci,
” shine nake so na bita mu tafi ran jajiberi sai na dawo”
“Babu inda zaki je” ya faɗa a dake ba tare da ƙarin bayani ba ya kashe wayan sannan ya saka hular jamfan shi ya fita da sauri ya faɗa mota tare da bawa driver umarnin ya kaishi gidan su,
******
Harda aunty Amarya aka fito min rakiya wannan karon a matsayin ta na wanda taje har gida ta ɗauko ni itama ta zuba min kaya masu yawa, hannu na a cikin na junior muna tafiya kaman zaiyi kuka gashi malalacin saurayi ko handbag ɗina ya kasa riƙewa sai surutu da kwainane,
Da wani speed motar ta shigo gidan wanda har ya jawo hankin mu gare shi, ya fito a motar da sauri ya nufo inda nake yana tamabayan “ina zuwa?” Kaman bai sani ba,
Da ƙyar cikin tsoro na amsa mishi da “gida zan tafi”
“To ba zaki tafin ba, makarantar fah?!……….🤦🏻♀️
Love you my fans😍
#team SS❤️
#team SZ💙
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
29🧝🏻♀️
“Zaki ɓace min da gani ne ko sai na ɓaɓɓalla ki?”
Ku gane min ikon Allah mutum da ƙarfin hali, ba shi ya kawo ni gidan ba kuma ba shine dalilin zuwa na ba amman yana min dole sai na zauna?
Kallon shi nayi sai faman muzurai yake yana hura hanci halin shi da ya ɓace na kwana biyu ya dawo sabo tarr, ban motsa daga wurin ba har saida yazo ya fincike jaka na yayi wurgi dashi tare da daka min wani uban tsawa,+
“Wuce ki koma ciki nace!!!”
na tsorata sosai da yanayin shi amman na kasa bin umarnin shi ya rufe idanu sai faɗa yake yi wani sa’in ma ba jin abinda yake cewa nake yi ba saboda ɓacin rai don har cikin zuciya ta ina muradin komawa gida sosai, ina so naje na duba aunty Yusrah domin banyi wa kaina adalci ba tunda na musamman aka ɗakko ni daga gidan mama aka kai mata saboda ina taya ta ɗawainuyan jego amman gashi nazo nan nayi zama na, idan na ƙara koda kwana ɗaya ne ban kyauta ba,
“Ka barta ta tafi mana Sulaiman ai tace zata dawo kuma makaranta ba sai bayan sallah a koma ba?”
“Za’a fara mata extra lesson ne aunty, kuma daga yau zai fara banga amfanin komawan ta gida ba, so kindly take your luggage and go inside bani so in sake magana saudat” ya ƙarasa maganar yana kallo na da idanun shi da suka rikiɗe suka koma jajaye lokaci ɗaya,
Yi nayi kaman ban jishi ba na sake yima su Ruma da junior sallama na raɓa ta gefen shi zan wuce,
A zuciye ya hankaɗa ni baya har saida na kusan faɗi ƙasa da taimakon akwatin hannu na nayi maintatining balance ɗina sannan na ɗago ina kallon shi, ɓacin ran na menene kuma?
Dady bayi gida, Hajiya kuma tana can ciki bata san ma me akeyi ba daman aunty amarya ba wani jin maganar ta sulaiman yake yi ba, saboda yanda yake nuna min isa yasa ba zan ji maganar shi ba don ko Khamis da ya ɗakko ni yake kula dani bayi min irin haka,
Haka na tirje ina mishi tsayayya daga ƙarshe muka hau cacan baki yana faɗa ina mayarwa hawaye na tsiyaya a idanu na babban yaya ji yake yi kaman ya saka ni a turmi ya kirɓa ni, bayi son tsayayya da taurin kai shi yana so a ko wani lokaci mutum yabi umarnin shi kawai,
Na buɗe baki zan sake magana Ruma ta tare ni a kunne na ta raɗa min “Mu tafi ciki dan Allah boɗɗi ki daina magana haka nan, zamu roƙe shi ya barki kije gidan daga baya for now just cool down please”
Kwace jiki na nayi daga riƙon ta cike da rashin kunya na wuce zan tafi tare da bari musu jakan kayan a wurin, motar da aka ajiye zai kaini gida ma ban kula shi ba na nufi gate abuna ko mai zai faru ya faru indai babban yaya ne saidai ya kashe ni amman nikam sai na tafi,
Cikin sassarfa ya nufo ni tare da finciko hannu na, na zube a ƙasa amman haka yake jana a wulaƙance duk suna gani babu wanda yayi koda magana dai-dai lokacin da saƙo ya isa kunnen Hajiya ta fito don ganin abinda yake wakana amman kafin tayi wani magana yaji an buge shi a ƙirji,
Ɗagowa yayi idanun shi suka sauƙa cikin na Zayyad da yake aika mishi wasu sharp look, ranshi yayi matuƙar ɓaci da abinda ya gani amman bai nuna hakan ba a fuska,
Buge hannun shi dake jiki na yayi tsugul na miƙe na koma bayan shi na laɓe ina kallon sulaiman da ya zamo confused don Zayyad ya shammace shi sosai,
STORY CONTINUES BELOW

“F**k off bro, me kake yi haka ne?”
Nuna kanshi yayi da yatsa yana tunkaro shi yace “Zayd!! Are You using this abusive word on me your own brother?!”
“To a kan me idan kalmar baki tayi maka zafi zaka wulaƙanta wata? Kai kaɗai ne mai zuciya da idan akayi maka abu zaka iya yin fushi amman wani sai kayi mishi abun da kaga dama?”
“Are You stupid?! Kana cikin hayyacin ka kuwa ka san da wa kake magana”
“I’m not stupid but you are, ka taka kowa yanda kake so ciki harda ni ba zanyi magana ba saboda dukkan mu kana da iko a kanmu amman ka kuskura ka sake ƙoƙarin cin mutuncin Saudat ba zan bari ba ya Sulaiman i will use all my power to protect her”
Daga kallon idon Zayyad na gane cewa ba shi ɗaya bane, bani tunanin zai taɓa ɗaga muryan shi saman na babban Yaya indai yana cikin hankalin shi saboda tsanin yanda yake girmama shi yake masa biyayya,
hakan na nuna min cewa aljanun shi ba kurame bane kaman yanda nayi tsammani daga farko duk iya ƙoƙari na wajen gane hakan na gaza domin ba wani ƙwarewa nayi ba kuma yanayin sautin da yake fitarwa idan sun tashi baiyi kama da masu budaɗɗen murya ba,
Tasa ƙeya na yayi a gaba zai fitar dani waje, ko shima bai san me zaiyi min idan mun fitan ba amman sai tafiya kawai muke yana riƙe da jakan kayana, riƙo shi da Sulaiman zaiyi ya taƙarƙare ya kai mishi naushi a ciki dukkan su biyu suka zuba a ƙasa,
***
Yau naga tashin hankali fari da baƙi harma da ja, bayan na gama amsan laifin da ya faru wanda ya kasance nice musabbabin faruwar komai kaman yanda Sulaiman ya faɗa an kuma haɗa ni wuri ɗaya da Zayyad don nima mishi lafiya,
It hurts ganin shi a cikin wannan yanayin ga raunuka a gefen fuskar shi har saman hancin shi a kuje yake, aunty ta fara kokwaton abun da yake ɗago su akai_akai domin kwanakin baya ya kan shafe kusan 1 month ko fiye da haka lafiya lau, amman yanzu bayi sati guda ƙwaƙƙwara cikin ƙoshin lafiya,
Ina gama aiki na muka fice aka rufo mishi ɗakin sannan kowa ya kama gaban sa ina jin mugun kallon da sulaiman yake watsa min a jiki na da nazo wucewa,
Ban bar gidan a ranar ba don ina son tabbatar da lafiyan Zayyad kafin na tafi, ban koma part ɗin aunty Amarya ba gudun haɗuwa da zagi da habaicin su nana don nasan bakin su ba zai mutuwa ba sai sunyi sharhi a kan abinda ya faru a yau, dukda bani can ɗinma Batool ta faɗa min sunyi amman banji ba ballantana raina ya ɓaci,
Washe gari babu wanda ya tare ni da maganar don kusan tashi mukayi da babban yaya a gidan tun 8 yazo gashi lokacin Zayyad ya farka har doctor yazo anyi dressing ciwukan shi, ina so na tafi amman ina tsoron kada wani abu ya sake faruwa,
Ina jikin sink ina wanke naman da za’a haɗa ma Zayyad abin da zaici tunda yanzu azumi babu shi Rumaisa ta shigo “dan Allah saudat kije ya matsa yana son ganin ki, ko sai kin gama ja mana rai ne”
“Ke da yayan naki duk baku da haƙuri wallahi ku bari a gama wannan sai muje gaba ɗaya kada a ya zauna da yunwa”
Bata ce komai ba ta taya ni muka gama sannan muka nufi ɗakin shi da tray ɗin abincin a hannun Ruma, muna shuga muka ci karo da aunty Amarya tana zaune tana tofe shi da addu’oi shi kuma ya saka agogo a gaba yana kallon awa ɗaya kenan harda ƙari da ya tura Ruma ta kira masa ni itama taje ta zauna kaman an aiki bawa garin su,
Yana jin sallamar mu a birkice ya juyo yana shirin min magana nayi saurin dakatar dashi ta hanyar ɗora yatsa na a saman baki na nayi masa nuni da aunty amarya,
Shiru yayi ya koma ya jingina da jikin gadon duk inda nayi yana bina da ido, a tunanin shi aunty fita zatayi amman sai gani yayi ta saka spoon a cikin abincin da muka zo dashi ta kai saitin bakin shi,
Yana tsananin son magana dani amman ba zai taɓa iyawa a gaban ta ba tunda har yanzu bata san me muke ciki fa,
Kaman ƙaramin yaro haka ta dinga bashi abincin a baki har sanda yace ya ƙoshi sannan ta tattara ni da Ruma muka fita wai a barshi ya ƙara samun hutu shikuwa ba haka yaso ba,
Ina shiga bedroom ɗin Ruma naci karo da missed calls ɗin aunty Yusrah guda 9 ban ko zauna ba wani kiran ya shigo, tsayawa nayi ina kallon wayan yana ringing gaba na yana faɗuwa haƙurin ta ya kai ƙarshe tunda har ta ƙare ta kira ni,
idan nace zan tafi gida a halin yanzu babban yaya yana nan ban san wani kalan rigima za’a sake yi ba gashi ciwon Zayyad yanzu yana niman yafi ƙarfi na dole ne idan ina son ganin shi cikin ƙoshin lafiya na danganta shi da wurin mahaifina ko za’a dace, amman yin hakan yana nufin bankaɗar sirri na a idanun duniya,
Ba zallan Sulaiman da ya tsane ni ba ba harta Zayyad da yake sona zai san ni bazawara ce da kuma dalilin da ya saka na bar ƙauyen mu, hala kuma sanin hakan ya sanya Zayyad ya sauya ra’ayin shi a kaina don nasan ko yayi haka bayi da asara tunda akwai matan da suke shirin auren shi a haka da matsalar shi, amman ni fa?
Ko Zayyad ya rabu dani ba zan iya rabuwa da shi ba kuma hanya ɗaya ne kawai zai saka shi ya kasance tare dani har ƙarshen rayuwar shi shine ɓoyuwan sirri na, amman shi ramin ƙarya ƙurarre ne dole wata rana gaskiya zai bayyana,
A yanzu na kasa tantancewa na sadaukar da soyayayyar da nake yi ma Zayyad ne don sama mishi lafiya ko kuma na sadaukar da lafiyan shi don soyayyar mu ta ɗaure??………🤦🏻♀️
_kada ku damu da gajercin page ɗin yau zan haɗa sauran shi da ya rage a kan na gobe insha Allah amman akwai buƙatar nima ma saudat mafita a yanzu haka so fans ku fito ku faɗi ra’ayin ku_
*Ta haƙura da son da take mishi ta nima mishi magani ne ko kuma ta jinkirta har sai ta samu cikar burinta a kanshi da kuma ingataccen ilimin da Sulaiman yake nima mata???*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
30🧝🏻♀️
Bismillah nayi na ɗaga wayan tare da sallama
” Saudat lafiyan ki kuwa? Kinje kinyi zaman ki Mama sai kira take yi tana tambayan ki, ba zaki dawo bane?”
Miƙewa nayi na saka ma ƙofar key na rufe sannan na koma can ƙuryar gado na zauna ina fitar da numfashi a hankali cikin ƙunar zuciya ba dan naso ba zanci amana don na samu mafita, ina tuna lokacin da Aunty take roƙo na Allah da annabi kada na faɗa ma kowa matsalar da Zayyad don sanin shi kaman tonon asiri ne a wurin su dukda bansan dalilin ta na faɗan hakan ba, kuma a lokacin nayi mata alƙawarin babu wanda zan faɗa wa gashi yanzu zanci amanar su,
“Kinyi shiru”+
Jan dogon numfashi nayi murya can ƙasa nace “Zan dawo aunty Yusrah akwai matsala ne”
“Matsala kuma? Wani abu ne ya same ki?”
“A’a bani bace, Zayyad ɗinnan ne wanda nace miki…..aunty Yusrah kina ganin Hamma Khamis zai yarda aje wurin baba na a ƙauye?”
Nayi mata tambayar ne don na san hanyar da nake son bi za ɓulle ne ko kuma A’a don rashin amincewar shi zai iya ruguza komai bayan na riga na lalata shi,
“Kaman yaya? Su waye kuma suke son zuwa wurin baba”
“Zayyad nake son kaiwa! Aunty Yusrah bayi da lafiya sosai kuma yana buƙatar taimakon baba indai zai iya taimakawa amman ban sani ba ko Abban Jannat zai barni na kaishi”
Shiruu tayi tana nazari sanin wanene Khamis, ta san da wuya ya amince da abinda na bijiro dashi don ta lura a yanzu bayan familyn sa babu abinda ya riƙa da muhimmanci sama dani kuma ya saka dukkan iko nashi wajen ganin ya rufe min sirri na don na samu ingantaccen rayuwa nan gaba,
“Boɗɗi babu wani wurin magani ne da ba zasu kaishi ba sai lallai wurin baban ki? Idan anje can ɗinma babu tabbacin zai samu waraka gwanda dai su jarraba wani wurin ga masu magani na islama birjik a gari ga kuma asibitoci”
“Aunty Yusrah cutar Ya zayd ba na asibiti bane, kuma familyn shi suna sirrinta shi basu son kowa ya sani shiyasa har yanzu suka kasa fitowa su nima mishi magani”
“Su suka nemi taimakon ki nema musu magani daga wurin baban?”
Girgiza kai nayi nace “A’a”
“Indai haka ne ina baki shawaran ki fita cikin abinda babu ruwan ki gudun kada ki shiga matsala, Saudat sirri da alƙawari manyan abubuwa ne guda biyu wanda idan kika saɓa su kin cika babban mayaudariya domin yarda dake da suka yi shi ya jawo suka buɗe miki sirrin su, yanzu ace kin faɗa min kin faɗa ma Khamis kinga mutane biyu kenan suka sani kuma daga nan baki san yawan mutanen da zasu ji ba don ba zaki yi tunanin zamu faɗa ma wasu ba kaman yanda kema baayi tsammanin zaki faɗa mana ba,
So it’s best ki fita cikin wannan maganar kawai ki bishi da addu’a Allah ya bashi lafiya”
Dafe goshi na nayi cikin damuwa, abinda aunty Yusrah ta faɗa gaskiya ne saidai bayi da sauƙin aikatawa, ina tsananin son Zayyad ba zan iya ci gaba da ganin shi cikin wahala kuma ina zaune banyi komai a kai ba,
STORY CONTINUES BELOW

“Yaushe zaki dawo?”
Sauƙe tagumin nayi na ɗaya daga kaina ina kallon wall clock sannan nace “can yamma in Allah ya yarda”
“Alright Allah ya yarda amman kiyi ƙoƙari ki dawo a kan lokaci kada abban Jannat ya biyo sawun ki”
Da “insha Allah” na amsa na tambaye ta lafiyar abulkhairi muka yi sallama na kashe wayan sannan na fita daga ɗakin, mutumin na nan a parlour ya baje kaman na gidan shi, ɓata rai nayi kaman ban ganshi ba na juya zan tafi saida na kusan ficewa naji ya kira sunana tuni na arta a guje don ko minti 1 bani son sake kashewa tare dashi haushi Sulaiman yake bani,
Komawa part ɗin hajiya nayi na sha zama na saida nayi sallan azahar kuma muka zauna tilawa yau junior baiyi musu ba ko kaɗan ya kwata abinshi a kan cinya na yana bin baki na shiyasa na ɗauka mana sura masu sauƙi muna yi,
Tun daga suratul Nas muka fara kafin mu shiga suratul humaza Farouk da Fa’iza suka shigo suka jona mu don dama karatun a bayyane muke yi, Ruma ma ta shigo cikin mu daga ƙarshe sai gashi dukkan su sun fito harda Hajiya itama zaman ɗaki ya ishe ta, but one person is always missing ‘NANAH’ ita kam ma bata gidan tana wurin ƙanwar uwar ta Sulthana,
Kana doso part ɗin Hajiya zakaji yo muryoyin mu a sama yana fitar da sautin ƙira’a mai daɗi everyone is trying to be the best reciter, saida muka kai suratul Jinn kafin aka dakata aka yi ma Zayyad addu’a kafin kowa ya watse, bayan sallan la’asar na sake wanka harɗa ƴar kwalliyana na shirya tafiya sannan na ɗauki Ruma muka shiga yima Zayyad sallama lokacin babban yaya ya tafi,
Zaune yake yana game a waya fuskar shi duk faci saman idon shi ɗaya kuma ya kumbura suntum sai kamar shi ya sauya gaba ɗaya, ajiye wayan yayi ya sauƙar da ƙafafun shi dake cikin ash colour socks ƙasa yana fuskantar mu,
Kallon Ruma yayi yace “sister if you don’t mind excuse us for a minute please”
Gyaɗa kai tayi kawai sai gani nayi ta fita ta jawo mana ƙofa ba tare da na fahimci abinda yace ba, tazaran dake tsakanin mu ya kai taku 5 amman naga ya tashi ya ƙaraso wuri na ya zauna a couch din da nake kai can nesa dani, to me Zayyad zaiyi min a ɗaki daga ni sai shi??
Kawar da tunanin nayi a raina, shi mutum ne mai nagarta ba zai taba taking advantage ɗin son da nake masa ba,
“Saudat ina son magana dake ne a kan zancen makarantar nan da naji ɗazu babban yaya ya saka ki”
Tattaro duka nutsuwa na nayi ina sauraron shi yaci gaba da cewa “ba wai bani son kiyi karatu bane Saudat amman ina tsoron canzawar al’amura don har ga Allah ni da gaske nake nake ƙaunar ki kuma ina son auren ki, amman muna cikin wani yanayi ne da abubuwa sukayi mana tufka kuma bamu da hanyar warwara, dan Allah babes ki haƙura da karatun nan sai bayan munyi aure, nayi miki alƙawarin ni da kaina zan saka ki a duk kalan makarantar da kike so a faɗin duniyar nan indai ina da hali amman ki bar wannan please”
“Arm sari (I’m sorry) hamma Zayyad gaskiya ba zan iya haƙura da karatu na a yanzu haka ba don gaba ɗaya burikan rayuwa na da nake son cika su wata rana a kanshi suka ta’allaƙa sannan bani nake da iko da kaina ba, bani na amince da shiga makarantar da babban yaya ya saka ni ba hasalima ni bansan wani makaranta bane, amman tunda iyayen gida na sun amince bani da tacewa a kai kuma ba zan iya komawa nace musu bani so ba”
Iska ya furzar daga bakin shi yana rubbing ɗin forehead ɗinshi cikin rasa abin yi,
“Saudat zan faɗa musu halin da muke ciki, zan sanar dasu abinda ke tsakanin mu ba zan yarda ki suɓuce min ba”
“Lafiyar ka fa hamma zayd?! Lafiyar ka yafi mana komai a yanzu kayi haƙuri har ka samu lafiya sai ayi komai yanda kake so” na faɗa cike da kunya dan naji kalaman ma sunyi min nauyi a harshe,
“Lokaci da yanayi yana canja mutane babes ba wai nace idan kika sanu ma duniya zaki guje ni bane amman ina tsoron faruwar hakan, ina tsoron ki samu wanda ya fini ki rabu dani ina tsoron kiyi min nisa bayan na ƙwallafa rai a kanki”
Ƙwalla na hango kwance cikin idanuwan shi wanda suka saka idon ya daɗa haskawa na taɓe baki a raina ina ayyana Zayyad akwai rago ko taurin rai irin na mazan nan bayi dashi abu kaɗan sai kaga yana shirin kuka, da shine yake da pressure na rayuwa daje kaina maybe ba zai sake murmushi ba saboda ƙunci, gwanda ma ya gode ma Allah mutanen dake zagaye dashi suna son shi kuma kowa na ƙaunar ganin shi sannan shi ba korarre bane,
“Kada kayi wannan tunanin a kaina babu abinda zai canzar dani in Allah ya yarda kaman yau ne zaka ga nayi makarantar na gama nima ina son naji an daina kira na daƙiƙiya” ya dai jini da kunne amman wannan kalamin nawa basu isa zuciyar shi ba, don na daɗa kwantar mishi da hankali na ƙara karya murya sannan naci gaba da faɗin
“sannu_sannu ba zata hana zuwa ba saidai mu jima bamu je ba amman indai ta fanni na ne nayi maka alƙawarin komai ruwa da iska, duk tsananin zafi da sanyi, cikin daɗi ko wahala ba zan taɓa barin ka ba ya Zayd koda kuwa kai zaka barni ruhi na ba zata rabuwa da kai ba HAR ABADA, kawai ka kwantar da hankalin ka babu inda boɗɗi zata je zata kasance taka har iya ƙarshen numfashin ta”
******
“Buge_buge bai dace da kai ba ai da ka koyi shan giya ne tun yanzu don ɓacin rai baka ga komai ba tukunna, ba ka haɗa sabga da ƙaramar yarinya ba? Hmm wani kayan ɓacin ran ma sai ka auro ta kuna kwance ta tsula maka fitsari a gado angon jaririya”
Cakk ya tsaya tare da riƙe punching bag ɗin a tsakanin hannuwan shi yana maida numfashi jikin shi ya jiƙa sharƙaf da gumi, juyowa yayi yana kallon Sadiya shi bai san lokacin da ɓera ya sace hankalin ta ya kai gidan shi aka cinye ba,
Tsaki yayi ya fita daga ɗakin da ya kasance personal gym ɗinshi with sweat dripping down his body yaje yayi wanka baice mata ƙala ba ya ɗauki ƴarshi ƙaramar bayan Muna ta haɗa mata madara suka bar gidan,
******
“Wayyo Allah, Ruma kiyi sauri dan Allah ko yaushe ke kike makarar dani, ina son na tafi kafin yayan nan naki ya sake waiwaiyan mu”
“Kin fiye mita wallahi bodɗi kaman baki ga saurin nake yi ba, kina cewa ni da yaya na bamu da haƙuri amman kin fimu ujila da rashin haƙuri” ta faɗa tana rufe zif ɗin basket ɗin gaban ta wanda ke cike dam da kalolin abinci sannan ta miƙo min shi,
“Gashi! Yauma ba zamu yi sake ladan ki ya wuce mu ba zamu ciyar dake lokacin shan ruwa”
Karɓa nayi ina washe hakwara, irin abin yayi min daɗin nan nace “thank Rumaisa, me is you sweet”
Dariya mai sauti tayi ta rungume ni “you are sweet too my dear, love you”
Da sauri_sauri muka ƙoma mua fito da kayan da already a shirye yake saidai da fitan mu waje muka ci karo da babban yaya a tsaye kaman daman fitowan mu yake jira,
Pa basket ɗin hannu na silently ya shiga dasu ciki ya ajiye sannan ya fito ina tsaye a wurin da ya barni na kasa koda motsawa hawaye kawai nake jira suzon na basu daman zuba, lallai Sulaiman ya zamo min jaraba yanzu,
Dawowa yayi ya riƙo hannun Ruma ita kuma ta riƙo hannu na ya ja hannu na har ta baya wurin da aka jera wasu fararen kujeru da table a tsakiyan su, ga wani mutumi tsaye da zungureren whiteboard hannun shi riƙe da marker,
“He is your lesson teacher and ur classes will begin right away, sai ki saku wuri ki zauna”
Ya juya wurin mutumin yana nuna mishi yatsa yace “ina sake jaddada maka no mercy!, bani son sassauci ko kaɗan bani son wasa” ɗan duƙawa yayi cike da girmamawa ya gyaɗa kai “insha Allah boss”
Ganin su kawai nayi sun juya sun barni tsaye a wurin bani da zaɓin da yafi na haƙura nabi umarni kawai, malamin nan yanda ka san ciki ɗaya suka fito da boss ɗinshin shima dai babu sauƙi,
Wasa_wasa tafiya na gida ya gagara malamin lesson ɗina sau biyu yake zuwa a rana kuma idan aka fara karatu tun 8 bayi tafiya sai 1:30 da yamma kuma tun 3:40 sai an kusa shan ruwa,
Tun bani son karatun har na saka ma raina na fara ganewa don duk abinda aka koya min a rana sai nazo na juye shi ma oga kwata_kwata da daddare………….🤦🏻♀️
Love You my fans
#team SS💙
#team SZ❤️
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*I’m back*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Mun dawo zamu ɗaura daga inda muka tsaya kuma babu wani tsaiko sai mun kai ga gaci insha Allah🤩jinjina gareku masoyan gaskiya😍 kun nuna min irin ana kyawun taren nan🤗 na gode sosai da soyayya da kulawa Allah ya biya ku da gidan aljanna🥰*+
31🧝🏻♀️
Zaune nake a gaban board dawowan mu kenan daga saloon mutumin nan ya tsare ni ko cikin gida ban shiga ba, na saka lesson teacher na a gaba na kalle shi nabi na kalli littafi na,
kusan 10 minutes kenan ya bani class work amman ko karantawa na gagara ballantana nasan mai zan rubuta mishi, gashi mugun nayi_nayi dashi yace ba zai karanta min ba,
“Sir… Idan kana ƙaunar maman ka da babanka ka fassara min, wallahi ni ban gane abinda kace nayi ba kwata_kwata” na faɗa a gatsale,
Riƙe baki yayi kawai ya juya ya ƙara wani question a kan wanda ke jikin board ya kuma saka time 20 minutes idan ya cika ko ban gama ba zai karɓa, sannan ya tafi ya barni zaune a wurin da waya a kunnen shi yana amsawa, daman yayi alƙawarin ɗaukan fansar zagin da na jawo mishi jiya a wurin babban yaya saboda ya gyara min spelling, shiyasa ya ɗau alwashin daga yanzu ba zai sake min komai ba idanma ban iya ba ruwa na tunda shi yana kwasan kuɗin shi,
Ajiye pen ɗin hannu na nayi kawai na zabga tagumi ina ƙare mishi kallo tunda abun nashi baƙin hali ne na lura mugunta kawai yake son mun ba komai ba, yafi kowa sanin ban iya komai ba amman ya rubuta min wasu manya manyan turanci ya tafi ya barni a wurin,
Cikin sanɗa Ruma ta ƙaraso wurin da nake zaune tana waige_waige ganin ta a haka yasa hankali na ya tashi ina tambayan ta ko lafiya,
Riƙe hannu na tayi cikin damuwa tace “kiyi haƙuri Saudat na jawo miki…”
“Kaman yaya kin jawo min? Me ya faru?”
“Yanzu babban yaya ya shigo, bansan wani dalili ya shigar dashi bedroom ɗina ba amman daga ganin shi yana cikin farin ciki, ganin haka yasa nima na saki jiki dashi yana ta min wasu tambayoyi a kan karatun ki da ban gane kansu ba amman na ɓoye mishi halin da ake ciki,
To muna zaune muna hira sai na tashi na shiga bathroom kafin na fito na samu ya buɗe drawer ya ciro litattafan ki ainihin wanda lesson teachern ki yake marking yana dubawa, yanzu ya gane duk scores na assignment da test da ake kai mishi mu muke yin marking da kanmu amman na ƙaryata hakan, yace idan har da gaske baki karatu ba zai barki ko makaranta kiyi a garin nan ba, kuma idan kika tafi sai kin gama tass kafin ki dawo nan da shekaru kusan 6 kenan, yace idan ƙarya nayi mishi ba zai barki ki sake komawa gida ba sai kin ƙare karatu ko bikin sallah a nan zaki yishi yaya zamuyi kenan?”
Dafe gashi na nayi cikin takaici ina maimaita “hasbunallahu wa ni’imal wakeel”
Zuwa yanzu raina ya fara ɓaci haƙuri na ya kusa ƙarewa, na gaji da yanda sulaiman yake juya ni kaman waina a cikin kasko, shi waye da zai dinga yanke hukunci a kan rayuwa na ba tare da izini ko shawara ta ba? Menene haɗi na dashi duk yabi ya takura min ya hana ni sakewa, ya maida ni ha’ina maƙaryaciya ƙarfi da yaji,
STORY CONTINUES BELOW

Jefar da littafin nayi a ƙasa nabi da takalmi ina takawa a kan idon lesson teacher na shima mamaki ya hana shi magana don a gaban shi sulaiman ya kashe min warning idan yaga ko ƙwarzani ne ya samu littafin nan na kuka da kaina, naja hannun ruma mukayi part ɗin hajiya,
“Wannan masifa da me yayi kama? Wallahi idan kika ga ban tafi gida yau ba to mutuwa nayi a hanya” Ruma dai tana biye dani a baya taga ikon Allah ko wani irin mataki ne zan ɗauka,
na tura ƙofar bedroom ɗin hajiya sannan nayi sallama cikin kasashiyar murya ina matsar ƙwolla,
Zaune take tana karatun ƙur’ani da reading glasses a idon ta, saida ta kai aya sannan ta ɗago tare da amsa sallaman mu,
“Subhanallah mai ya same ki saudat?”
Zama nayi a jikin ƙafar ta na kifa kaina tare da fashewa da kuka, ta ɗago ni tana share min hawaye amman gudun kada ta gane kukan ƙarya ne na sake kwacewa na kifu ina ƙara sautin kuka na,
“Rumaisa mai ya same ta?”
“Gata nan a gaban ki hajiya wallahi ban sani ba”
“Saudat tashi ki faɗamun wanda ya taɓa ki yanzu su fuskanci fushi na” murmushin jin daɗi nayi da jin haka ina sauƙe ajiyan zuciyan munafurci na fara kwararo bayani,
“Hajiya yanzun mama ta kira ni, babyn aunty yusrah babu lafiya yau kwana biyu kenan da kwantar dasu a asibiti shine baba yake ta faɗa da bai ganni ba yace idan ban dawo yau ba sai ya saɓamin”
“Toh shine kike kuka? Je ki haɗa kayan ki a maida ki gida daman bai ma kamata ace yau jajiberi kina gidan nan ba, inyaso bayan sallah sai ki dawo”
Jan hanci nayi na ɗago tare dayin fuskar tausayi “hajiya ai babban yaya ne ya hana ni tafiya, tun shekaran jiya na faɗa mishi rashin lafiyan abulkhairin amman yace ba zanje ba”
“Maganar banza ma kenan, tashi kije ki shirye naga wanda ya isa ya hana ki tafiya idan shi yake da iko dani ba ni nake da iko dashi ba”
Yess!! Na miƙe ina ji kaman na taka rawa a wurin, idan sulaiman yayi sake na tafi yau wallahi ba zan dawo ba, sake gani na ma sai yayi da gaske dashi da lesson teachern sai naga ta iyawan su,
Cikin nishaɗi nake zuba kaya na a cikin akwati ina yi ina rera waƙa Ruma ta shigo,
“To wai kije inji shi tunda kinje kin haɗa mishi wuri”
“Inji shi, shi wa?”
“Babban yaya mana, ba kinje kin haɗa mishi bomb wurin hajiya ba, Kika faɗi abinda bai faru ba?”
Ɗaga kafaɗa nayi cikin halin ko in kula nace “to ina ruwa na? Ai komai ya faru shi ya jawo tunda shi ya fara min dole, mai tsoron ta kife shine gawan fari”
“Haka ne kam zancen ki gaskiya shiyasa ma da nagan shi yazo da bulala ban wani damu ba saboda nasan keɗin jaruma ce, kawai kije ya shargwaɗa miki su a gadon baya ki tashi ki kaɗe mishi a wurin” ta ƙarashe tana dariyan mugunta,
Har na kai ƙofa da gudu na dawo wurinta, cike da tsoro jiki na har mazari yake yi nace “dan Allah da gaske kike Rumaisa? Duka na zaiyi?”
Bata bar dariyan ba ta gyaɗa min kai ” eh mana ba kince mai tsoron ta kife shine gawan fari ba? Bismillah jaki ki gamu dashi”
“Ke baki san wasa bane? Wasa fa na miki, dan Allah duka na zaiyi? Muje ki bashi haƙuri a madadi na dan Allah nasan ke zai saurare ki” kafin na kai ƙarshen magana na har idona ya fara tara ruwa,
“Hhhh matsoraciya kawai, wasa nake miki da’allah, muje na raka ki kinsan yayan namu bayi son jira ba kaman masoyin ki yaa Zayd bane”
“Wassh har kin ƙara min bugun zuciya da kika ambaci sunan shi” na faɗa hannu na a kan ƙirji na ina faman lumshe ido,
STORY CONTINUES BELOW

Duka ta kai min a kafaɗa sannan ta ja hannu na da ƙarfi muka fita daga ɗakin tana faɗin “lallai yarinyar nan idon ki ya buɗe tun kafin ki tafasa kina niman ƙonewa”
*****
Murmushin fuska na ne ya canza zuwa fuskar tausayi yayin da naci karo da babban yaya zaune a ƙaramin parlorn aunty amarya ya wani hakince a kan kujera ƙafar shi ɗaya kan ɗaya kaman wani gidan shi,
Gaban shi na ƙarasa na tsuguna kaina a ƙasa nace “gani babban yaya”
“Na ganki ai ban makance ba” ya faɗa ba tare da ya kalli wurin da nake ba ballantana na saka ma raina zai bani izinin zama
Saka wa baki na sakata nayi naci gaba da kneeling a wurin kaman wanda aka sakani Ruma na can gefe a tsaye har sanda yayi niyyan magana,
“Uhm kince yaron auntyn ki babu lafiya a wani asibiti ne aka kwantar dashi?…………amsa nake nima ba cewa nayi ki zuba min idanuwan kin nan ba”
“D..d..dama..umm…aa..nan….”
“Wait! Manta sunan asibitin kika yi ko da suka kira kin basu faɗa miki bane?”
“Eh! Na manta ban tambaye su ba”
“To ki kira ki tambaye sun, idan sun faɗa miki sai kizo ki same ni a mota muje a duba shi, kema ki shirya Rumaisa sai mu tafi tare” ya miƙe tare da maida hulan shi ya saka wayan shi a aljihu sannan ya kama hanyan fita,
“Aa anfa sallame su, yanzu suna gida ne”
Juyowa yayi yana min wani irin kallo sannan yace “to shikkenan sai muje gidan a duba su”
“Nima zan tafi tare daku yaya”
Juyawa mukayi duka muna kallon shi, zayyad ba dai fara’a ba kullum fuskar shi a sake yana zuba murmushi ga tukuicin dimples dake ƙawata shi,
Ƙarasawa wurin shi sulaiman yayi yana jan hannun rigan shi ya duba lafiyar shi saboda ɗazu ya shiga duba shi ya samu yana barci
“Haba bro don’t embarrass me in front of these kids mana”
“Ya zayd mu ɗin ne kids ɗin? Harda ehem.. ɗinka ita ma kid ce?”
“Just shut up Rumaisa!” Ya faɗa yana dariya “nayi dana sanin barin ki kisan sirrika na you are nothing more than a blaster”
“Wasu sirrikan ne naka da Ruma ta sani ni ban san dashi ba? Yana da dangantaka da saudat ne? Cos i can clearly understand that she is referring to her”
“Of course not bro! It’s nothing serious kada ka ɗaga hankalin ka mu tafi ko?”
***
Ko da muka shiga mota a baya na zauna tare da Ruma sulaiman da kanshi yake driving Zayyad na zaune a passenger seat, dukda ina matuƙar jin daɗin sautin ƙira’ar sheikh sudais da yake bi kuma karatun na sanya ni nutsuwa, amman hankali na a tashe yake saboda ina ta kiran aunty yusrah bata ɗauka ba, da alama text ɗin da na tura mata ma bata gani ba don na tabbata zatayi replying idan ta buɗe,
Tsayawa mukayi a hanya muka sayi fruits masu tarin yawa sannan muka ci gaba da tafiya,
“Sai ki mana jagora mu shiga ko?”
Yaya akayi sulaiman yasan gidan khamis? Ko da yake ba abun mamaki bane tunda ma’aikacin shi ne, yasan gidan mama ma ballantana nan? a hankali na buɗe kofar na fita sannan suka biyo ni a baya zayyad na janye da akwati na, ina ta salati a zuciyana kada a gano ƙaryar da na shirya,
A watan Ramadana ma ba’a bar gulma ba, idanun ƴan unguwan mu kaman zai faɗi ƙasa an ganni da manyan samaruka masu hannu da maiƙo sai binmu ake da kallo har abun ya damu zayyad tunda shi bai saba shiga cikin mutane ba,
Saida nida Ruma muka fara shiga muka nima musu izini kafin suka shigo muka yaɗa zango a parlor sannan aka shiga gaisawa, yadiko sai kaffa_kaffa take dasu,
“Yaya mai jikin dai?” Sulaiman ya tambaya yana kallon abulkhairi dake kwance a hannun Ruma yana barci,
“Mara lafiya kuma?” Yadiko ta tambaya?
Nan da nan aunty yusrah ta harbo jirgin, ta san bai wuce ƙarya na sharara musu dan na samu dawowa ba,
Janyo hannun jannant tayi ta tura mishi ita “gata nan jikin da sauƙi”
yarinya sai ƙifi_ƙifi take da ido taga ana turata wurin baƙon da bata taɓa ganin shi ba, ta canza hanya da gudu tazo jiki na ta ɓuya tana leƙa shi,
“Amman kaman namiji ne aka ce bayi da lafiyan ko?”
“B..ba.ba namiji bane ita ce mantawa nayi”
“Oh itace abulkhairin kenan!!”
Dariya zayyad ya saka Ruma da aunty yusrah suna taya shi, tsaban mugunta harda sunkuyawa yana ƙyalƙyalawa, sai ya ɗago ya kalle ni ya sake kwashewa da dariya,
“Ke dai saudat Allah ya shirye ki yasa ki daina munanan daɓi’u” cewar yadiko,
Caraf ruma ta amshe da “Haba yadikon mu, har wasu munanan ɗabi’un take dashi bayan wannan”
“To wannan ɗin ance miki karamin abu ne? Ko ƙarya ɗabi’a ce mai kyau?” Ta maida duban ta wurin babban yaya da ya haɗe gabas da yamma duk dariyar nan da ake ko murmusawa baiyi ba shi abun ma haushi ya bashi don yana da tabbacin nayi ƙaryar ne don na guje mishi,
“Yaya sunan ka ma baba na?”
“Sulaiman”
“Yauwa sulaiman to saudat ƙarya tayi muku daga Jannat har abulkhairi babu mara lafiya, bansan wani dalilin bane yasa take mana wannan mummunan fatan ba…………..🤦🏻♀️
2
#vote
#share
#comment
*Ummu Najma ce😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
32🧝🏻♀️
Horn ɗin motar khamis ya kuɓutar dani daga faɗan yadiko, hamdala nayi caraf na miƙe na fita buɗe mishi gate sannan ya shigo da motar shi ciki,
Tattaran laidodin kayan da yazo dashi a mota nayi dukda ya hana ni ina binshi ina ɓuya a bayan shi har muka shiga parlorn shima da mamaki yake kallon mutanen dake zaune a ciki,+
Bai taɓa tsammanin akwai ranar da Allah zai kawo sulaiman boss cikin gidan shi ba shiyasa da ya ganshi harda ƙaramin oga zayyad hankalin shi ya tashi sosai don a tunanin shi wani abun naje na ɓaro mishi dukda kuwa ya san ni ɗin ba fitinanniya bace,
Gaishe su yayi ya zauna a parlorn ni kuma na ɗauki hanyar kitchen da kayan hannu na tunda na shiga naƙi fitowa inajin yadiko tana mayar ma khamis abinda ya faru, faɗan da bata yi min da ba sai yanzu take juye mishi, yayi shiru yana jinta idan ta kai comma ya bata haƙuri kafin taci gaba, Saida su zayyad suka saka baki kafin ta haƙura tayi shiru,
Ban fito ba har saida naji sun tashi tafiya a hanyar fita daga kitchen ɗin naci karo da khamis, har nayi shirin amsan nashi faɗan amman baice min komai ba bayan
“Kinyi dai_dai, gidan ku da dangin ki sune mutuncin ki ba bare ba”
Wannan kalaman nashi saida ya sosa min tsohon tabon dake zuciyata, ina kewan gida sosai ina kewan iyaye na da dangi na, ya Allah ka gwada min ranan da zan koma wuroɓokki in gano halin da iyaye na suke ciki,
****
Duk sun fita waje amman shi sai baya_baya yake yana son yaga fitowa na don ba zai iya tafiya ba idan bamuyi sallaman ƙarshe ba, yasan zaisha kewa na amman bayi da yanda zaiyi dole ya dinga haƙuri a halin da ake ciki,
Har jikin motar su mukayi musu rakiya abun mamaki sulaiman bai min zancen ranar komawa na gidan ba ya sa kai cikin mota ya make,
Saida ya faki idon kowa kafin ya buɗe baki ba tare da ya fitar da sauti ko kaɗan ba ya furta I LOVE YOU ta yanda wanda ya kalli bakin sa ne kawai zai iya fayyace abinda ya faɗa,
Murguɗa mishi baki nayi na kawar da kaina gefe saboda yasan dariyan da ya min ɗazu ya ɓata min rai, ya dafe ƙahon zuciyan shi tare da yin fuskan tausayi kafin cikin salon ɗazu ya sake furta ‘I’m sorry babes’
“Zayd mu tafi ko?”
“Oh..ok..muje” ya shiga motar sulaiman ya tayar, har suka bar layin Rumaisa tana ɗaga min hannu nima haka, shima yayi amfani da wannan damar a fakaice yake waving ɗina,
he wished akwai ranar da zai zo da zamu zamo masoyan sunna bisa inuwan aure mu buɗe soyayyar mu ma duniya kowa ya sani, a wannan lokacin ba zaiyi waving ɗina kaman matsoraci ba, he will shower me with lot of kisses yanda har ya dawo tunanin shi ba zai bar zuciyata ba ko na second ɗaya,
*****
A daren ranar aka ga wata ya kama gobe ne sallah, daman mai lallen mu tana ready tazo aka shera mana ja da ɓaƙi, duka lallen ya karɓe ni abunka da farin fata, ya fito darr yayi kyau, haka kawai naji inaso na nuna ma zayyad don sau da dama yana faɗa min yana son yaga hannun mace da lalle yana mishi kyau sosai amman ba zanyi gigin zuwa wurin da yake a halin yanzu ba saboda irin rabuwan da mukayi babban yaya ko yawon sallah ba zanje musu ba kada su sake riƙe ni,
STORY CONTINUES BELOW

Nayi ƙoƙarin kwanciya da wuri don nasan gobe ba hutu,
1/shawwal/1442
Tunda aka wayi gari muke ta kai komo ana ta hidiman gyara gida da shirya abincin sallah, ƙarfe 6 gari bai gama haske ba na ɗauki jannat muka fita kai markaɗen kayan miya,
Ina zaune ina jiran layi yazo kaina message ya shigo waya na nayi saurin ɗagawa na duba don nasan idan ba wai network bane to saƙon shi ne,
”’good morning babes…..kin kyauta da kika nesanta kanki dani gashi yanzu na kasa barci saboda tsoron wani abu zai iya faruwa dani kuma baki kusa balle ki kare mun, i miss you die”’
Murmushi nayi inajin raina fari tass, na ƙara janyo jannat jiki na matse ta a ƙirji na har saida ta saki ƙaramin ƙara, ta kai min duka da tsintsiyan hannun ta
“Aaauch aunty saudat kyaki kayya ni” ta ƙarasa haɗe da turo baki tana kallo na,
Ban kula ta ba na mayar mishi da saƙo kamar haka,
”’barka da safiya hamma zayd, kada ka damu kanka Allah ne yake bada lafiya kuma shi yake karewa insha Allah babu abinda zai same ka”’
Saida na duba spelling na tabbatar banyi kuskure ba gudun ajina ya zube sannan nayi sending na juyo wurin jannat dake faman jero ƙananun tsaki nace,
“Sauƙa min a kan cinya baƙa mara kunya”
“O’o naƙin ummi tace in makale miki ko kuma ki bayi a sace ni, tace wai baki da wayo”
“Lallai to shikkenan kuwa zan gwada muku rashin wayo na, zanga dawa zaki je masallaci amman idan dani ne saina ɓatar dake da shegen surutu kaman aku”
“Ni abbana zanbi ba zan tafi dake ba”
Ko 2 mins ba’ayi ba ya sake turo wani saƙon, hakan yasa na fita sha’anin ta na ɗaga wayan ina dubawa
”’maganar ki haka yake saudaty amman kuma ɗan adam shi ya kamata ya fara kiyayewa, sannan Allah ya riga ya bani maganin matsalar da nake tsoro saidai kaiwa gare shi ne yayi min wuya, shiyasa nake tsoron kamuwa da ciwon zuciyan masoya”’
Murmushi kawai nayi dan na gano kan zancen nashi na share zancen ganin har an gama min markaɗen gashi jannat ta ishe ni da surutu na biya su kuɗin muka nufi gida ba tare da nayi masa reply ba shima bai sake turo komai ba,
Muna komawa na ɗaura shi a kan wuta sannan na shiga da jannat nayi mata wanka na shiryata sosai na cancaɗa mata kwalliya don babu laifi yanzu na fara ƙwarewa na feshe ta da turarukan uwanta da na ubanta sannan na koma ɗaki nima na faɗa wanka,
Wani daɗi nake ji na musamman ina fito da sabon ɗinki na da jewelries harta undies sabo ne, lallai adon sallah daban yake ga wani nishaɗi da mutum yake ji babu gaira babu dalili, azumi ya saka jiki yayi lafiya sai kaji ka sakayau babu sauran damuwa a tare da kai,
Shiryawa nayi tsaff amman banyi kwalliya ba na tanada sai idan na dawo ban kuma saka turare ba sanin haramcin shi sabida zan iya cuɗanya da maza a hanyar tafiya don a ƙafa zamu,
8:30 na safiya yadiko ta gama shiri taje ta sauƙe miyan tuwon ta aunty yusrah ta ɗaura na shinkafa don ta matsa sai anyi abinci kala biyu, tare da khamis muka wuce masallaci,
10:17 muka shigo gida a gajiye na zuba a kujera don munci tafiya saboda tsakanin gidan da masallaci akwai ɗan tazara, ga gaishe_gaishe da aka tsaya yi da mutane ana ma juna barka da sallah kuna hanyar da muka je ba shi muka bi muka dawo ba kaman yanda yazo annabi (s.a.w) yakan saɓa hanya yayin zuwa masallacin eidi da komowa (amma mustahabbi ne saidai akwai falala a cikin sa)
Haka yadiko tazo kaina ta gama surutun ta ina jinta don bani jin zan iya taɓuka wani abu a yanzu amman duk lokacin da nayi niyyan yima mutanen nan tamɓele na tuna irin halarcin su gareni sai na fasa, a haka na ƙarasa kitchen na sha ruwan sanyi naci gaba da aiki,
*****
dawowar su daga masallaci kenan suka yaɗa zango a parlor, sulaiman ko damar shigowa ciki bai yau yana jinshi wani iri babu walwala shi ba mai saka wa ranshi damuwa bane shiyasa bai iya shiga damuwa ba,
A yanayin yanda ya karanci saudat gaba ɗaya bata son kusancin shi a tare da ita, tana sakewa da kowa amman idan yana wuri sai ta koma kaman baƙuwa, ba wai raini irin wada take masu zayyad da nafiu bane yake son ya shiga tsakanin su ba Aa, amman yana son tana ɗan sakewa dashi tana faɗa mishi damuwowinta ba tare da ya tambaya ba, ko na kuɗi, ko na shawari ko wani abu da take son a shige mata gaba tana samun shi ba zayyad da yake marili ba,
Ko sonshi ne bata yi? Mata da yawa suna falling mishi saboda wani dalili nasu, wasu kuma saboda arziƙin shi amman me yasa ita ta zamo na daban dukda ya bata ƙofa ta soshi zai amince da ita amman ta kasa ganewa, abin yayi tsanani yanzu har gudun shi take yi, me yasa ta kasa son shi? Maybe yarinta ke hana ta gane soyayya amman yasan definitely nan gaba zata fahimci tana ƙaunar shi, for now zai bata space ne yaga gudun ruwan ta,
Fitowan hajiya yasa suka sarara da ɗauke_ɗauken hotunan da suke yi suna binta da kallo fara’a bayyane a fuskokin su kowa yaci ado cikin shiga ta burgewa haka itama hajiyan,
Zaytoon ne ta fara ƙarasawa gareta ta rungumeta ta gefe kaɗan
“Barka da sallah mama”
Ɗan buga bayanta tayi a hankali sannan tace “barka da sallah zaytoonah fatan anyi sallah lafiya”
“Lafiya ƙlau”
“To Allah ya maimata mana”
Da “ameen” ta amsa ta gaisa da sauran yaran parlorn suna ma juna barka da sallah ana cikin haka aunty amarya ta shigo aka ci gaba da gaishe_gaishe saida duk cikin rundunan nan babu babban yaya,
“To mu fita ta waje ko photographern namu ya iso ta can kaman zaifi kyau”
Yuuu aka sake zuga aka bi bayan ya nafi’u daga can suka ɗaura daga inda suka tsaya sun saka iyayen su a tsakiya ana ta ɗauka, shi kuwa yana tsaye yana kallon su he wonders me yasa ake son kowa amman shi kaman ba’a son shi, he is not his parents favorite a wurin hajiya zatoon ne a wurin dady kuma zayd a wurin matar shi kuma kuɗi sai wani lokaci ƴaƴan ta, har yarinyar da ya bata zuciyan shi ma ya kasa gane alƙiblan ta wataƙil shima ba shine na ɗaya a zuciyan ta ba,
Hannunta ta ɗaura a saman nashi tana mamakin yanda akayi har ta iso gaban shi bai ankara ba,
“Dan Allah sulaiman, na yau kawai ka saki ranka ka shigo cikin ƴan uwanka kada zuciyoyin su ya sosu”
Hannun shi na hagu ya saka ya sosa ƙeyan shi idanun shi kan hannun ta dake riƙe da ɗayan nashi, he is strong he can fight all his problems alone ba zai bar kowa ya san matsalar shi ba don shi ba rago bane,
“Sule” ta sake kiran shi cikin nutsuwa, a firgice ya ɗgo yana kallon ta bayi son sunan ya tsani a ɓata mishi suna,
“Hajiyaa menene kuma wani sule, Please kada ma kiyi suji I don’t like it”
Murmushi tayi irin nasu na manya, tace “nayi hakan nen don na samu attention ɗinka don na lura wani abu ya tafi min da nutsuwar ka” duk yanda sulaiman ya kai da girma amman har yanzu kallon yaro ƙanƙani take mishi, ita ta raine shi tayi mishi tarbiyya rabin halayen shi training ɗin ta ne don haka it’s impossible ya ɓoye wani abu ta kasa ganewa.
“Yanzu damuwa ba abun damuwa bane Hajiya mun riga mun saba dashi kullum mu fita cikin wannan mu faɗa wancan kawai kuci mana da addu’a da albarkan ku muke ganin nasara a ko yaushe”
“To shikkenan Allah ya shige mana gaba, amman kaje ka sallami yaran nan dan babu wanda ka bada goron sallah a cikin su”
Ɗan Sakewa yayi kaman ba komai ya shiga cikin wasu pics ɗin aka ɗauka yayi ma ƙannen shi rabon kuɗaɗe iya yanda zai ishe su kafin ya koma ciki yayi zaman shi,
****
Zuba yayi a kan kujerar yana kiran sunan Allah ya kalli sulaiman da already shi yake kallo da ƙawataccen murmushi saman fuskarshi dimples ɗinshi suna masa sallama,
“Yaya ina so zamuyi magana if ur free saboda abu ne mai muhimmanci kuma ina so kayi mun kyakkyawar fahimta”
Yana fatan idan wannan ƙudurin shin ya cika zai bawa saudat goron sallan da babu wanda ya taɓa mata irinshi, zai mata albishir da zata zamo nashi, zai mallaka mata kanshi da zuciyan shi a yau idan babban yaya bai kawo masa cikas ba,
“Umm..hmm.. ina sauraron ka”
“Aure nake son yi yaya, amman kuma a lokacin da kaga dama saidai don Allah bani so ya wuce ƙarshen shekarar nan…………..🤦🏻♀️
2
Love You my fans🥰
#team SS💙
#team SZ❤️
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
33🧝🏻♀️
Kallon shi yayi cikin rashin fahimta yace “aure kuma zayd? A irin wannan lokacin?…….Wani abu ne ma yasa kaji kana sha’awar yin aure bayan kasan matsalar da kake tattare dashi”
Gyara zama yayi ya fuskanto shi yanda zai fahimce shi sosai in a serious tone yace
“Yaya nifa ɗan adam ne kuma ajizi, bani da lafiyar ruhi amman ina da lafiyar jiki dole watarana nima naji ina buƙatar yin aure, shekaru na 28 fah dan Allah ka duba lamarin nan a san yanda za’a yi”
Murmushin takaici sulaiman yayi yana girgiza kai, ya rasa me yasa zayyad ya girma amman kuma bayi da tunani kullum shi kenan ayi ta maimaita mishi magana ɗaya kaman karatu?+
“Remains only 2 years, shekaru biyu kacal suka rage mana da sun cika bama sai da izini na ba zaka auri ko mata 4 ne kake so a lokaci ɗaya, kayi haƙuri na shekaru masu yawa na 2 yrs sai ya gagare ka? zuwa lokacin kaima kana da naka abin da zaka riƙe su dashi na gashin kanka ba sai ka roƙa an baka ba kuma babu wani tsoro ko fargaba a tare da kai bayan wannan lokacin idan Allah yaso ma zaka iya samun lafiya ka warke tangaras, domin duk inda ya kamata mu shiga mu fita zamu je a nima maka lafiya ba tare da damuwan rasa komai ba, ka haƙura ka ajiye wannan batun Please”
“Amman yaya ba zata iya jira na har zuwa lokacin ba…”
“Then just let her goo!! Let…her..go!” Binshi kawai yake yi da ido ya lura bai san girman abinda yake shirin saka shi aikatawa bane, saudat tayi tsiron da ba za’a ce ya cire ta cikin zuciya na kuma ya iya aikata hakan ba,
Ya tashi daga zaunen da yake ya ɗauki babban rigan shi a hannu ya zuba wayoyin shi a aljihu yana son tafiya don bayi son su ja maganar kada ranshi ya ɓaci daga ƙarshe cus so much is already going in his mind,
“I believe ko a wuni ɗaya kayi deciding auren wata macen bayan ita za’a iya kammalawa kafin dare a kaita ɗakin ka tunda kuɗi ne yake yin aure just let her be ko ita waye kuwa koda Sulthana ce ka rabu da ita zaka samu wacce ta fita”
“Ba Sulthana nake son aura ba…”
“Koma waye kace ta jira idan ba zata iya ba ta ƙara gaba, kada kabi na mata zasu saka ka rasa komi naka ba tare da ka shirya ba, ni zan wuce gidan umma na gaida su”
Da faɗan haka ya fice abunshi ya bar zayyad cikin jimami, bayi da wani zaɓin da ya wuce yabi umarnin babban yaya a yanzu idan ba haka ba kuma saɓa mishi zai iya jawo babban ɓaraka a tsakanin su kuma ba zai taɓa bari hakan ta faru ba,
Shima ɗaukan nashi babban rigan yayi yana gani ana setting dining don cin abinci yayi shigewar sa ɗaki dan bayi jin zai iya saka ma cikin sa wani abu,
Cire rigan jamphan shi kawai yayi ya ɗauki waya ya kira saudat…..
*****
“Kai aunty Aisha ta daina fah, arba’in ɗinsu da saura ina zata je a…….” magana ta ne ya katse saboda ruri da waya na ya ɗauka na bishi da kallo tare da ɗauka ina duba mai kiran sunan zayyad na gani kasa picking nayi na barshi ya yanke a take wani kiran ya sake shigowa,
STORY CONTINUES BELOW

“Ɗauka mana! Ko sirikin nawa ne kike jin kunya”
Dariyan yaƙe nayi nace “A’ah fah, wata ce ki bari kawai zan kira ta daga baya idan na koma gida”
“A kan me? Idan kuma wanj babban uzuri ne fah?”
Miƙewa nayi na nufi hanyar fita da ƙarfi ta jawo ni na dawo na zuba saman kujera,
“Munafuka, babu inda zaki je ki ɗauka a nan naji waye tunda nace kina da saurayi kin ƙaryata ni”
Bani da zaɓin da ya wuce nayi picking na ƙara a kunne tare da sallam ina ƙifi_ƙifi da ido,
Daga yanda naji muryan zayyad nayi sensing akwai wata matsala don banji shi cikin fara’a da dariya kaman ko yaushe ba, gaida shi nayi cikin ladabi bai amsa ni ba sai cewa
“Babes I’m very sorry lallai na zamo miki ɗawainiya har yanzu abinda nake son bai samu ba”
Kallon aunty Aisha nayi wanda ta ƙura min idanu na sake sauƙe kaina sannan cikin ƙasa da murya nace “wani abu ne ya faru hamma zayd?”
“Bani so kiyi tunanin yaudaran ki nake yi Saudat, har cikin jini na nake son ki amman kiyi min alfarma ki jira ni nan gaba kaɗan, for the maximum of 2 years zan saita komai ya zamo dai_dai yanda za’a bani auren ki indai ina da rai, kada ki amince da wani Please wait for me”
Shiru nayi na kasa amsa shi saboda nauyin amsan da nake son bashi da kuma idon aunty Aisha amman shi yayi tunanin request ɗinshi bai karbu bane yasa yaci gaba da roƙo na,
“Please, Please ki taimaki rayuwata baby, zuwa lokacin na zamo mai ƴanci na tashi daga ƙarƙashin kulawar iyaye na da babban yaya kuma zan iya kula dake harma da yaran da zamu aifa nan gaba but please wait for me”
Tashi daga zaune Aisha tayi da nufin bani wuri ganin hawaye na zuba a idona nayi saurin riƙo hannunta ta dawo ta zauna domin ina matsanancin buƙatar shawara a yanzu sannan na katse kiran ina fashewa da marayan kuka,
“Meye haka saudat? Waye ya kira ki? Me ya saka ki kuka?” Ta faɗa tana share hawayen idona da ya kasa yankewa,
“Kiyi magana mana saudat, zan ɓata miki rai fa bani son sakarci”
“Aunty ban san yaya zanyi ba dan Allah ki bani shawara….. ni ba mayaudariya bace amman garin rufe sirri na nayi masa ƙarya kuma na barshi cikin rashin fahimta, bai san ni wacece ba, bai san matsayi na ba bai san asali na ba gashi yayi nisa a sona, na kasa faɗa mishi gaskiya aunty Aysha”
“Kinyi kuskure babba Saudat da kika ɓoye masa ke wacece, don ba’a taba ɗaura soyayya a kan ƙarya, abinda ya fara cutar da auntyn ki yusrah kenan rashin cikakkiyar sani a kan wanda take zaune dashi…”
“Duk abinda zan faɗa mishi a yanzu ba zai saka ya aminta cewa bani da niyyan yaudaran shi ba aunty…. bai taɓa ɓoyemun komai ba harta rashin lafiya da yake fama dashi na jinnu da ake ɓoyewa duniya ya bayyana gare ni, sannan duk lokacin da zai buɗe bakinshi ya furta min wata kalma yakan kasance gaskiya ni kuma a ko yaushe akasin gaskiyar nake faɗa mishi”
“Ita gaskiya dokin ƙarfe ce Saudat, zata iya jin ciwo ma wanda yake kai amman ba zata taɓa bari ya auka ba, ta yuyu gaskiyar zai mishi ciwo amman ko babu komai zuciyar ki zata samu nutsuwa zaki samu sauƙi daga dukkan fargaba”
“Ba lallai na same shi ba, saboda zayyad yayi min nisa, kada nayi kuskuren sanar ma kowa sirri na domin hamma khamis ba zai taɓa yarda da hakan ba ya kawo ni nan ne don tseratar dani daga al’amarin da ya gabata a rayuwa na da kuma wanda yake bibiyar shi, aunty yusrah ta gargaɗe ni sau tari da wa’innan kalaman ba zan iya ba aunty Aisha……inaga kawai haƙuri zamuyi da juna °i no desty to is him (I’m not destined to be with him)” na ƙarasa tare da saka ƙasan gyale na ina share hawayen dake faman sintiri saman fuska na kuka na daɗa kufce min,
Cikin zafin nama Aisha ta fincike hannu na tana bina da mugun kallo,
“A kan me zaki nemi taimako daga wurin wanda ta kasa tsaida ma kanta decision ɗaya lokacin da take cikin halin da ya kusa fin naki muni,
Yusrah aminiyata ce na santa ciki da waje amman sai yanxu na fahimci ita ɗin mai son zuciya ne kanta kawai ta sani…. A irin haka ne ta kasa yiwa khamis hukunci lokacin da ya dinga azabtar da ita, bata nuna mishi ita ɗin mai ƙima bace ta koma wurin shi cikin sauƙi bayan ya dawo gare ta, ba don shi ɗin masoyin asali bane yanda ta nuna mishi zallar soyayya da tuni ya watsar da ita a kwandon shara,
Yanzu ta zaɓi ganin hawayen ki da kasancewar ki maƙaryaciya a kan farin cikin ki? Ta zaɓi ki rasa komai wajen rufe abunda watan wata rana dole ya fito? Wa ya faɗa mata zayyad yayi miki nisa? wa…ya…faɗa..mata? Oya ɗauki waya ki kira shi ki faɗa mishi duk gaskiyar ki ai aure kika yi a can baya ba zina ba”
Ɗaukan wayan nayi da ƙarfin gwiwa don kalaman ta sun shige ni sosai har danyi dialling numbern zayyad sai kuma na fasa na juyo don tambayan ta,
“Idan abban jannat ya samu labari fa! Yaya zanyi?”
“Wani lokaci sai munyi taking eisk kafun mu samu wasu abubuwan a cikin rayuwar mu, indai yana son ki da gaske kaman yanda kika faɗa khamis saidai ya samu kyakkyawar labari a sanadin hakan da kikayi, kira shi yazo”
“Allah yasa” nace lokacin da kiran ya shiga kaman mai jira ya ɗauka, nayi mishi kwatancen gidan aunty Aisha a kan yazo zamuyi magana sannan na kashe wayan,
****
“Na san na ɗaga maka hankali na saka ka fito daga gida kayi haƙuri”
“Babu komai boɗɗi, ki sanar min abinda ya saka kika min wannan kiran gaggawan Allah yasa ba wani abu ne ya kuma faruwa ba”
Ya faɗa yana kallon fuska na da yayi jaa ga kan hanci na kaman wanda aka baɗa wa yayi, idanu na sunyi ciki_ciki alamun nayi kuka duk kwalliyan fuskana na goge shi a jikin gyale na garin share hawaye bai ankare ba sai gani yayi wasu hawayen suna bin kunci na, kafin yayi magana nayi saurin tare shi,
“Kayi haƙuri ya zayd, ba zan iya auren ka ba don ban dace da kai ba”
“What?! What are you saying? Ban fahimce ki ba”
“Ni BAZAWARA CE hamma zayd, na taɓa yin aure da wani a baya”
Shiru ne ya ratsa tsakanin mu na ƴan sakwanni, ya kasa gaskata abinda kunnuwan shi suka ji, ta yaya za’ayi yarinya mai shekaru 15 zuwa sha shida kacal a duniya ta kasance bazawara? Me yake faruwa ne? Ya tambayi zuciyar shi,
Jin yayi shiru yasa na fara masa bayanin abinda ya faru gudun zargi “ni ba ƙanwar khamis bace, iyayen shi ba su bane nawa kuma bamu haɗa wani dangantaka na kusa ko na nesa dashi ba, iyaye na suna can ƙauyen wuroɓokki kuma a can nayi aurena na farko” daga nan na kwashe labarin aure na da YARIMA da zama na dashi har izuwa mutuwan shi da kuma yanda baro ƙauyen, zuwa lokacin idanun zayyad sun gama tara ruwa ƙiris ya rage su sauƙo saman fuskar shi,
Ɗaga kanshi sama yayi iskan fanka yana fifita mishi idanun shi ko zai samu ya iya controlling kanshi,
“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel….. La ilaha ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin”
“Yanzu ni korarriya ce, bani da ikon shiga cikin wuroɓokki domin da sun ganni kashe ni zasuyi, tun ba yau ba ma naso kaika wurin mahaifi na mu gwada magani ko za’ayi nasara amman saboda wannan dalilin na gagara, ta yaya korarriya ta dace da mutum mai gata gaba da baya irinka? Kada ka manta kai saurayi ne ni kuma sauran wani”
Kifa kanshi yayi saman cinyar shi zuciyar shi yana suya, shi yayi tunanin ƙaddarar shi shine mafi ƙunci da wuya amman ashe akwai na wanda yafi nashi ƙuntatuwa, tunda shi yana cikin ƴan uwan sa ko wani garin Allah idan ya waye yana ganin Mahaifiyarsa tare da mahaifin sa ga ni’ima da wadata da Allah yayi musu,
“Saudat koda ƙaddarar ki tafi haka muni bani da matsala kuma na yarda dake a hakan nake son ki, ban damu ba, kuma ba zan saurari maganganun wasu mutane ba,
Ba kyanki ko kuma budurcin ki nake so ba, ke ɗin nake so zuciyar ki nake son samun matsuguni, buri nake ki zamo uwar ƴaƴa na kuma surkuwar mahaifiya ta, muradina kawai ki kasance ƙarƙashin inuwar aure na”
“Amman dangin ka fa? Zasu amince?”
**********
Anyi Sallah da sati 2 kowa ya watse muka ɗau hanyar makaranta, sabon tafiya sabon rayuwa,
Fiye da rabin damuwa na sun ragu don tun daga ranar da na bar gidan su zayyad babban yaya ya fita sha’ani na kwata_kwata ko magana mai tsayi bayi shiga tsakani na da shi amman bai fasa min kowa ba cikin hidiman da ya saba, kafin na tafi school ma saida su aunty yusrah suka kwashi rabon su don idan ya waiwaye mu mukan jiƙa sosai,
Na fuskanci abubuwa da dama wanda suka ɗaure min kai lokacin da na shiga makarantar don a lokacin da za’a kaini ganin niƙi niƙin shopping da sulaiman ya saka a kaini dashi nayi tunanin yawan shi ya tsananta amman da naje naga yaran dake rayuwa a wurin irin tsadadden rayuwan da akeyi na ƙarya da tsananin gaye, jinkai, competition na nuna dukiya, da kuma gasar ilimi sai na ganni ni ba kowa ba a gaban su………….🤦🏻♀️
Love You my fans🥰
#team SS💙
#team SZ❤️
*Ummu Najma ce😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
34🧝🏻♀️
*2 years and 7 months later*
“Congratulations on your first day in office bro”
Juyowa zayyad yayi daga jikin windown da yake tsaye yana ƙarewa farfajiyar companyn kallo daga sama har ƙasa, sanye yake da single breasted suit black colour ya ɗan yi ƙiba kaɗan yayi fresh,+
Kallon cake ɗin da sulaiman ya shigo ɗauke dashi yayi cike da mamaki gami da jin daɗi a cikin ranshi, ya tako zuwa inda yake tsaye yana ƙarewa cake ɗin kallo cikin birgewa, anyi decorating ɗinshi da edible office tools irin su stapler, pen, memo,sticky note, scissors da kuma pins, cake ɗin ya ƙawatu sosai,
“Woww this looks like a table” suka saka dariya gaba ɗayan su sannan ya karɓi cake ɗin ya akiye a kanshi ya juyo ya dubi babban yaya, saida ya bari ya karɓi box din hannun mutumin da suka shigo tare ya fita sannan yace,
“Na gode sosai yaya, ko birthday cake ɗina be kai wannan ƙawatuwa ba, bayan kuma duk nasaran da aka samu ta sanadin ka ne, kaine ka jajirce ka zaƙe wajen ganin mun cimma wannan matsayar…. Allah ya saka maka da alkhairi”
“ameen zayd….Well inaga ni ɗin kawai nayi abun da ya kamata ne kai kuma kaci nasaran biyayya, rayuwan ka ta ƙuntata sosai na shekaru masu yawa amman daga yanzu komai ya wuce zayd, ka saka ma ranka kaman babu abinda ya taɓa faruwa, kayi rayuwan ka cikin aminci da salama”
Ya ɓude box ɗin sannan ya fara firfito da kayan ciki yana ajiye su saman table,
“Here’s your passport” murmushi yayi ya ƙarɓa yana juya shi
“yanzu kaima ka samu freedom na transportation, sai kaje duk inda kaso ba tare da izinin babban yaya ba”
Dariya zayyad yayi lokacin da ya danƙa mishi abu na biyu “your car keys, brand new Porsche irin nawa da ko yaushe kake muradi…. Saidai wani hanzari ba gudu ba” ya ƙarasa yana tsare gida kaman bashi bane mai murmushi yanzu,
Shima zayyad shiru yayi da ganin sauyin yanayin shi yana jiran yaji mai zai fada, saida ya maida hankalin shi gefe sannan yace
“Na banbanta mana kala don bani son ka dinga jera kanka dani, na girme ka so respect me”
Dariya ne ya kubce masa ya ƙame kaman sabon soja sannan ya sara masa “gaisuwa babbban yaya”
Cike da jin kai ya amsa da “uhm hmm” yana ƙunshe dariyar abinda yaga zayd ɗin yayi, ya miƙa masa na gaba,
“Your credit card sai a cika mana account da kuɗi yanda zamu dinga wadaƙa da dukiyar ƙanin mu…….. and here’s some cash wanda zaka ɗan riƙe a hannun ka zuwa wani lokaci sai ka ɗauki abinda zai maka ka ajiye sauran a safe, na gama maka iya abinda zan iya”
Runguma shi zayyad yayi idanun shi suna tara ƙolla, “na gode Ya sulaiman, kayi yaƙi kayi fafutuka wajen ganin ci gaba na Allah ya saka maka da mafificiyar alkhairi kuma ina roƙon Allah nima ya nuna min ranar da zan sadaukar maka da wani abu don ganin farin cikin ka”1
“Kada ka sha mamaki ranan yana nan zuwa, yanzu dai sake ni a gajiye nake ko hutawa banyi ba na biyo nan”
Sake shi yayi ya zura hannayen shi cikin aljihun wandon shi,
“Yaya banyi tunanin zamu ci nasara ba da naga baka nan, haka kawai nake ga kaman sirrikan mu zasu bayyana a gaban su, amman da wakilin ka kaɗai mun sami abinda muke so”
STORY CONTINUES BELOW

“Zama na a nan ɗin amfanin shi ragagge ne shiyasa ban dawo ba na ci gaba da mana addu’a a ɗakin Allah and here we are, komai ya tafi cikin sauƙi sai kuma mu ɗauki abu na gaba ko?… Nima maka lafiya idan Allah yaso”
Sosa ƙeya yayi yana dariya ƙasa_kasa yace “yaya maganar aure na dai ko?”
“Toh shikkenan tunda ka kasa haƙuri, ko da yake banga laifin ka ba don ka fara shiga sahun manyan tuzuraye….. Yanzu dai ka bari idan ka dawo gida zamuyi maganar don inason na huta a yanzu gaskiya”
“Shikkenan nima yanzu wani wuri na nufa, idan na dawo ɗin sai mu zanta”
“Wani wuri ina? Daga ranar farko har zaka fara yawo ko? Ka maida hankali fa zayd ka nutsu ka san abinda kake yi”
“Wurin ta fa zani yaya, anyi musu hutun school yau dole naje nayi picking ɗinta up”
“Hmmm dalilin da yasa kake sintirin hanyar international academy kenan? Zuwa ganin budurwan ka ko, Ko kayi tunanin ban sani bane?”
“Hhh yaya ba kace yanzu na samu freedom ba sai a barni naje na ɗauko aba ta na kaita gida, kaga tun yanzu ya kamata tasan cewa ni ɗin zan dinga bata kulawa”
dukan wasa ya kai mishi a kafaɗa yace “da nasan ɓata gari irin ku suna zuwa har cikin makarantar su ɗauki yaran mutane da ban kai Saudat wurin ba”
“Yaya kenan kwantar da hankalin ka basu bari baƙo ko bare yaje wurin kowa, itama ɗin kaman dangi take ka santa farin sani kawai ma ka bari na Musamman zanje na kawo maka ita”
“Hakan yayi, ni zan wuce sai ka dawo, amman ka kula da kyau Please…ayi driving a hankali”
*******
Yana tsaye jikin sabuwar motar shi baƙa wuluk hannayen sa harde a ƙirjin sa idanun sa sanye da sunglasses saboda rana da ake ƙwallawa ya zuba mata ido cikin su,
Takowa take a nutse sanye take da uniform light blue da wandon shi wanda yake combination na blue, black and ash dankwalin ta ma ash colour da madaidaiciyar hijab ɗinta wanda sauran kaɗan ya ƙarasa guiwa, idanun ta maƙale da farin reading glasses wanda idan ba wanda ya san tana da matsalar ido bane babu wanda zaiyi tunanin ba na fashion bane saboda yanayin case ɗinshi da kuma yanda ya ƙarbi fuskarta,
tana janye da luggage ɗinta kanta a ƙasa kaman mai ƙirga interlocking dake ƙasan wurin, wannan nutsuwar tun da tana ɗauke dashi ne ko kuma a yanzu ne da ta karanci rayuwa ta san ciwon kanta ta san mai take ciki ne ta samo shi?
Shigowar ta international ya koyar da ita darasi da dama domin dukda cewa ta shigo da suturu masu kyau da tsada kuma tana da duk wani abun buƙata na rayuwa amman sai ta zamo kamar wata almajira a cikin su kowa na mata kallon ballagaza galau_galau, saidai kasancewar ta special student wanda aka ɗauke ta a special unit ya canza komai,
Su uku ne kacal a wannan unit ɗin amman suna da malamai kusan 11, yawancin su malamai ne a makarantar wanda suke aiki overtime don samun ƙarin kudi suna daɗa basu wuta wurin karatu, guda biyu kuma sune na musamman sun ta’allaka ne wurin koyar da rayuwa da tsari masu tsauri irin na turawa, kama daga shiga, yanayin cin abinci, profer diet, workout, magana, zama, kwanciya…. Bla.. bla..bla… Saboda raya bidi’a har catwalking ake koya mana lokacin da muka fara ƙwarewa a wasu abubuwa muka fara gogewa, har fatan jiki na saida ya canza saboda irin mayukan da nake amfani dashi amman ba masu ƙara haske ba,
Cikin shekara ɗaya muka gama komai sannan muka maida hankalin mu kan zallar karatu wanda muke yin shi tsantsa babu wasa, harta lokacin hutun mu ragagge ne sai a lokacin na fara shiga cikin mutane nayi ƙawaye don a yanzu ajina yayi dai_dai da nasu,
Yanzu na fara banbance dai_dai da ba dai_dai ba, na ƙara hankali da sanin ya kamata, a yanzu ina jin zafin iyayena sosai abinda akayi mana a wuroɓokki kuma na ɗau aniyar ɗaukar fansa ko ba daɗe ko ba jima,
Dake a jss1 aka saka ni muna gama jss2 babban yaya yasa dole nayi jssce aka hawar dani ss1,
Nasha wahala sosai kafin nayi coping don karatu ba ƙaɗan sukeyi ba kuma mai wahala, yanzu haka munyi hutun third term nan da wata guda da satittika zamu shiga ss2 kuma alhmdllh yanzu ma na 9 nazo cikin mu 40,
Cikin sassarfa yarinyar ta ƙaraso ta jera dani itama janye da akwatin kayanta, uniform ɗinta irin nawa itama kyakkyawa ce babu laifi,
“My dear da nace ki jira ni ne zakiyi tafiyar ki?”
Dubanta nayi nace “baby Hanan na faɗa miki anzo ɗauka na tun dazu aka sanar min kinga ba zan zauna na barsu da jira…..”
Magana na ne ya katse saboda wani ashar da Hanan ta lailayo wanda yanzu ya zamo kaman wani abun ado ne ga ƴammata kaji suna jifan junan su da zagi marasa dadin ji ko kuma suna laƙani ma junan su da miyqgun laƙani irin su “shegiya, jahila, jaka” da sauran su kuma samm ashar ba tarbiyya mai kyau bace ba’a taɓa shaidan mutanen arziƙi dashi,
“Baby are you seeing what I’m seeing?”
Ɗaga ido nayi don ganin abinda take gani ɗin idanu na suka sauƙa kan fuskar zayyad dake ɗauke da murmushin da kusan za’a iya kiran shi da dariya saboda yanda beauty point ɗinshi suka zurma,
“Dear your brother is damn handsome, wallahi kullum ƙara kyau yakeyi I’m already crushing…ohh go..”
“Hey, hey..cut it….cut that gut feeling off shi ba yaya na bane, he is my fiance auren shi zanyi”
Ɗan waskewa tayi cikin kunya tace “ohh I’m sorry” ban sake ce mata komai ba har muka ƙarasa wurin su,
“Hola chica (hello girl)” ya faɗa yana gyara tsayuwar shi, caraf Hanan ta amshe da
“Hola guapo (hi handsome)”
Wato harshe suka canza suna yaren da bani ji ko? Zanyi maganin su ne, na koma gefe ina binsu da idanu,
“Cómo estás(how are you)”
“Estoy bien mi hermano (I’m fine my brother) esper que estés cuidando bien a mi amigo (i hope you are taking good care of my friend)”
Murmushi yayi yace “kada ki damu baki da case dani”
Murmushi tayi sukayi sallama ko sake kallon ta banyi ba inaji tana min magana na share har ta tafi ga wani kishin shi da naji yana taso min, me yasa ma zaiyi kwalliya yazo da mota mai tsada cikin ƴammata?
Zagawa nayi na shiga front seat na make ba tare da nace daahi ƙala ba, ya shiga driver seat ya tayar, saida muka fita daga farfajiyar makarantar sannan ya dubi yanda nake cika nake batsewa yana gintse dariyar shi yace
“Babes babu gaisuwa ne?”
Kaman wanda ya zage ni na fara zazzaga mishi masifa da fillanci nan ya tsuke bakin shi yayi shiru har muka isa gidan aunty yusrah ya ajiye ni a sace ba tare da ya bari anga fuskar shi ba a saba’in ya bar unguwan don kowani lokaci driver ne yake dawo dani,
Bayan na huta da yamma na fara zaga cikin ƴan uwa ziyara kafin safiya kuwa har mun shirya da sahibina ya rage gidan su ne kawai banje ba,
Suna tsaye ƙofar part ɗin aunty amarya da waya a kunnen shi sulaiman ya ƙura mishi idanu yana kallon ikon Allah wai yau zayyad ne yake hira da wata mace a waya,
“Babe har yanzu baku kusan ƙarasowa ba?”
“Mun kusa hamma amman fa ni wallahi bani son haɗuwa da kai a cikin gidan mu don ba wurin ka dan zo ba har bani son haɗa ido da aunty”
“Ina ruwan ki? Kede kizo kawai zan gabatar dake ga mutum na musamman hurry up please”
Shigowar mu farfajiyar gidan ya saka na katse wayan na gyara zaman mayafina ina ji a raina da surakanai na zan haɗu, kunyar haɗa ido da ƴan gidan gaba ɗayan su nake ji, a hankali na taka zuwa part ɗin hajiya hannu na janye da jannat tare da share kallon ƙurillan da sulaiman da zayyad suke min
“Gata nan! SAUDAT dinmu ta gidan nan itace yarinyar da nake so na AURA”
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
🌹🌹🌹FEEENAH MATAR SOJA 🌹🌹🌹
💃ina masoyan feenah matar soja marubuciyar ✍️✍️✍️✍️
+
HARAMTACCIYAR SOYAYYA
AURAN SOJA
YAYAN GATA
KUSKURENA
BARIKI AURAN SOJA
WANAKE AURE
😍wannan karonma ta dawo muku da sabon littafinta mai suna 👉 ZANYI BIYAYYA😌 ina masoya hausa novels toga dama ta samu littafin ZANYI BIYAYYA 😌 yaxo muke da solo 💃💃 daban daban
domin san ku fadakantu ,waaxantu dakuma nishadi ku biyota awannan shahararran littafinta ZANYI BIYYAYYA😌 masu iya magana nacewa anayi dakai yafi ba,ayi dakai karku bari abaku labari koda kudinka akace sai da rabanka🤸♀️🤸♀️🤸♀️🤸♀️🤸♀️
gamasu bukatar biya ku hanxarta karku bari abaku labari kubiya ku karanta cikin Aminci, katin Airtel 200 zaku turo normal VIP 500 kuturo katinku ta wannan number 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 NAFISA SANI fcmb yan niger🇳🇪 masu bukatar biya kunemi wannan number +225 48 15 39 03
35🧝🏻♀️
Shiru sulaiman yayi yana kallo na har na wuce gaba ɗaya gaɓoɓin jikin shi sun sun daina motsi, tsananin mamaki da al’ajabi ya hana shi magana,
Ta yaya za’ayi ƙanin shi yaso abinda yake so? Ta yaya za’ayi su haɗa nima da ɗan uwan shi na jini?
Saida ya gama ɗawainiya da Saudat ya gyara ta ya maida ita mace cikakkiya mai wayewa gami da ilimi ya ɓarar da dukiyan sa a kanta ya ɓata shekaru kusan 3 yana jiran ta dace da matsayin shi…..da yaci Nasara kuma zayyad daizo yana son ta?
Jin yayi shiru yasa zayyad ya ɗaga waya ya sake kira na,
Daidai zan shi parlorn na tsaya daga ƙofa na zaro glasses ɗina daga cikin jaka na maƙala shi a idona saboda ina gane abubuwa ba tare da nayi musu kallon ƙurilla ba kasancewar ina fama da short-sightedness,
Kafin na rufe jakar waya na ta ɗauki ruri cikin Sa’a babu kowa a parlorn bayan tv da yake ɓaɓatunshi shi kaɗai hakan ya bani daman zaro dalleliyar Samsung Galaxy S7 edge wanda sulaiman ne ya siya mun da ƙyar da suɗin goshi Khamis ya barni na fara amfani dashi don tursasawa yayi a mayar mishi ai shi bai kasa ba kuma ba wai ba zai iya siya min wayan bane kawai ya bari ne nakai wani mataki a karatuna na san ciwon kaina kafin ya siya min, da ƙyar Yusrah ta danne shi tana mishi nuni da cewa babu kyau maida hannun kyauta baya a hakan ma sai da suka kusan kai ruwa rana kafin ya yarda don shi Yanzu duk duniya babu wanda yake bashi haushi kaman Sulaiman saboda katsa landan da yake masa cikin al’amuran shi saidai babu yanda ya iya tunda boss ɗinshi ne,
Kaman da gayya zayyad ya saka wayan a speaker yanda sulaiman zaiji,
“Hello babes, kina ganina kika ƙyale ni kaman baki sanni ba ko?”1
Ɗan ƙaramin murmushi nayi mai sauti na nemi kujera na zaunar da Jannat nima na zauna sannan nace “I’m sorry hamma na, babban yaya fa yana nan ta yaya za’ayi na iya tsayuwa nayi magana da kai a gaban shi”
STORY CONTINUES BELOW

“Ya rab! Amman ban faɗa miki zan haɗa ki da wani mutum na musamman ba? Shine kuma zaki bani kunya? Babban yaya kaman aboki yake a gareni kuma ai kema na gaisa da ƙawar ki jiya kema sai ki fito yanzu ki gaisa da aboki na”
Hannu na ɗaya na saka na dafe goshi na ina ɗan murzawa a hankali nace “nikam ba zan iya ba hamma zayd, ina ganin babban yaya kaman mahaifi na ne….”1
A firgice ya juyo yana kallon zayyad tare da zare manyan idanunsa cikin firgici wanda zayyad ba shi yake kallo ba, idanun shi suna kan ƙofar part ɗin Hajiya kaman zaiga fitowar ta ɗinne…
“Kambu…What did she just said?! Ni ɗinne take wa kallon mahaifin ta?” Ya faɗa cikin zuciyar shi yana taraddadin dalilin da ya saka ta faɗa hakan,
Duk wannan soyayya da kulawa da yake nuna mata a fakaice har yanzu ƙwaƙwalwarta bata ganar da ita sonta yake ba shine tsaban wulaƙanci ta rasa matsayin da zata bashi sai na mahaifin ta? Ko yayi kama da wanda ya isa ya aifi sa’ar ta ne? Dududu shekaru 4 kacal ya bawa zayd “am i that old?” Ya sake tambayar kanshi, ganin bayi da amsa sai kawai ya ci gaba da sauraron su,1
“…mai ɗaukar ɗawainiyata ta yaya za’ayi na iya fuskantar sa a matsayin girlfriend ɗinka ina jin kunyar sa gaskiya”
“Finally!!” Zayyad ya faɗa yana dariya “las_las kinyi admitting ke girlfriend dina ne and I’m happy to hear that, yanzu yaushe kike son ki fara kiran kanki matata?”
Ganin yana niman canza wa hirar akala yasa na katse shi ta hanyar jefo mishi tambaya,
“Kama tunamin….mai kacewa baby Hanan jiya banji ba?”
“Ehh!!! Miss jealous ba mun ƙarƙare maganar nan jiya ba, Please ki daina damun kanki a irin wannan dukda kuwa na san ni ɗin mai tsada ne amman naki ne ke kaɗai sai yanda kika so kiyi dani,
And it’s not fair da kika saka ma ƙawanki such a lovely name amman ni kika barni da hamma, gaskiya ki sauya zani ban yarda ba”
“Hamma zayd Hajiya tana kira na ina zuwa”
Na faɗa tare da katse wayan jin motsin mutum kada wani ya fito ya tarar dani a haka,
Fa’iza ne ta fito cikin riga da wandon jeans tasha hula irin wanda akewa laƙani da baby cakwai hannun ta riƙe da plate wanda aka gama cin abinci a ciki daga gani kitchen zata maida shi,
Mikewa nayi na kira sunan ta da “aunty Fa’iza” kaman yanda na saba fuska na ɗauke da murmushi don dukda tana da wuyan sha’ani wurin aibanta mutane da rashin kunya amman tana da kirki dai’dai gwargwado,
“Aarrrhhh international babe, our makauniya yaushe a gari? Oyoyo” ta faɗa tare da ware hannunta ta rungume ni ba tare da ta ajiye plate din ba,
Ta ɗan rusuna tana cakalar kumatun Jannat tana mata wasa, itama murmushi ta maida mata ta gaishe ta don sun saba sannan ta mana jagora cikin bedroom ɗin hajiya daga nan tayi wucewarta kitchen ɗin,
*******
“Hhh Saudatu kenan iyayen kunya, yaya kaga taƙi yarda ku haɗun gaka sirikin ta”
Tsananin takaici ya hana sulaiman magana yana jin zuciyar shi kaman zata yi aman wuta yayi saurin juyawa ya bar wurin, yama kasa fasalta abinda yake faruwa, a wani babi zai ɗauke ta? Anya kuwa Saudat ba twins bane? Anya ba hussainan Saudat bane take tare da zayyad suke son gwada shi? Anya babu wani ƊAURIN ƁOYE cikin wannan lamarin, ko fansa zayyad yake nima na ƙuntata rayuwar shi da yayi yasa ya fara soyayya da abun ƙaunar shi, dukda bai gaya ma kowa ba amman yayi tunanin kowa ya fahimci tuntuni yana son ta, yana tsananin sonta yana ƙaunar ta yayi tattalin ta ba zai bari ta suɓuce mishi lokaci ɗaya ba,
Daidai an buɗe mishi back seat na motar shi zai shiga zayyad ya cim mishi tare da janyo kafaɗar shi ya dawo baya yana ƙare ma fuskar sa kallo ganin yanda idanuwan sa suka rikiɗe sukayi jaa lokaci ɗaya,
“Lafiya kuwa babban yaya?”
Haɗiye wani abu mai ɗaci yayi da ƙyar ya iya buɗe baki yace “indai da gaske kake yi ba gurguwar fahimta nayi wa abun ba to KACI AMANATA zayyad”
“Cin amana kuma? What are you talking about….ban fahimci komai ba”
Da kaman ba zai sake tanka shi ba sai kuma yaga idan yayi hakan zai cutu ya tura ƙofar motar ta baya da ƙafan shi ya rufu kada driver ya saurari maganar da zasu yin ganin haka yasa wanda ya buɗe mishi mota ma yayi gaba sannan ya fuskanto shi,
“Tell me zayyad…wani mummunan abu nayi maka wanda ban sanda shi ba har ka zaɓi ɗaukar fansa ta wannan hanyar? Dame na cutar da kai a rayuwa da har ka dage wajen ganin maƙurar ɓacin raina”
Shiru yayi yana nazartan kalaman shi har yanzu ya kasa ɗago haske, ya kasa fahimtar saƙon da ɗan uwan nashi yake isar masa cikin ƙunar rai wanda a zahiri ya nuna,
“Kayi amfani da damar da na samar wa kaina ka sace zuciyar ta, kayi amfani da wasu siddabaru naka ka saka ta saki jiki da kai tana maka hira mai daɗi tana maka laƙani da nata tana lanƙaya sunan ka da rayuwar ta don kawai ka cutar dani??
Ba uwa ɗaya ce ta aife mu ba amman ban taɓa la’akari da hakan ba na ɗauke ka matsayin tsoka da jini ɗaya ke gudana a jikin mu domin na ɗauki mahaifiyan ka matsayin nawa kaman yanda naga ka ɗauki tawa a matsayin naka, tun kana ƙarami nake ƙoƙarin inganta rayuwar ka dukda nima ina halin ƙuruciya amman na san abinda kai baka sani ba yasa nayi fafutukar ɓoye aibin ka wajen ganin na sama maka gata kaman yanda ni da Nafi’u muke dashi, ka mallaki abinda zaka riƙe kanka harda da ƴan uwan ka idan mahaifin mu ya kasa amman a maimakon haka irin sakayyar da zaka min kenan?
Saida ka san cewa nayi nisa a ƙaunar Saudat zaka shiga tsakani na da ita zayd? A wani dalili?”
Daram..daram…dum…dum!! haka ƙirjin Zayyad ya fara lugude jin kalaman sulaiman na ƙarshe don sai yanzu ya fuskanci inda ya dosa, murya na rawa yace
“B..b..yaya k..kana son… Saudat fa kace?”
“Don’t pretend please zayd, na sanka tun kana yarinta you are very cunning sometimes, amman ban taɓa tunanin you can stoop so low don kaga ka kaini ƙasa ba dan Allah me nayi maka” ya ƙarasa maganar a tsawace,
Ƙarasawa kusa dashi yayi zai taɓa shi yayi saurin ja da baya “bansan menene manufar ka ba, bansan shirin ka na gaba a kaina ba, daga ƙwace saudat bansan gaba mai zaka sake ƙwacewa ba amman dan Allah ko dan darajar iyalina da mahaifiyata da ya rataya a wuya na kada ka raba ni da rayuwata”
Zayyad baisan lokacin da hawaye mai tsananin zafi ya zuba daga idon sa ɗaya bisa kuncin sa ba ɗayan kuma a bushe, irin kukan nan ne da akeyi na takaici yayi sakare yana kallon babban yaya, fuskarsa kaɗai ya isa ya nuna kalaman sa daga zuciya yake fitowa,
Ko me Zaid ɗin yayi mishi kallon hawayen shi abu ne mai matuƙar wuya wanda yake saurin tsinka mishi zuciya, juyawa yayi saidai ko taku ɗaya baiyi ba ya jiyo muryan zayd yana faɗin,
“Bansan kana sonta ba yaya, da na san da haka ko kallo na biyu na shauƙi ba zan sake mata ba ballantana har na bar zuciya ta tayi zurfi a sonta”
“Ƙarya kake yi zayd, daga kai har saudat har kowama ya san da cewa ina ƙaunar ta, tayi lacking ilimi na sama mata shi, tayi lacking wayewa na sama mata shi, ina ƙoƙarin tankwasa zuciyar ta don ta furta min kalman so koma ta nuna hakan ba tare da faɗa ba amman ta fahimta kuma taƙi, shekaru 3 na ɓata ina jiran tsammani amma…..”
“Wallahi ko kusa bamu da masaniya a kan soyayyar da kake mata, baka taɓa furtawa ba yaya kum….”
“Kuma ko ban furta ba amman ai na gwada, bayan matata ka taɓa ganin na kashe lokaci na a kan wata ƴa mace ne bayan Saudat??”
“Wannan mun ɗauke shi a matsayin taimako ne, irin wanda ka saba yiwa mutane saboda Allah”
“Taimako? Da lokacin nawa ne zanyi taimako? There is nothing left to say you BETRAYED me kuma ba zan yafe muku a kan hakan ba, idan Saudat ce kuma gata nan na bar maka ita ina fatan hakan zai sanya ka farin ciki”
Ya juya kaman da gaske ya haƙuran ne saida ya shiga mota har sun fara ƙoƙarin fita daga gidan saboda jaraba ya buɗe ƙofar motar ya fito har lokacin zayyad na tsaye ƙeƙam a yanda ya barshi,
“Ban ɗauki soyayyar saudat don na sauƙe ba, don haka ni da kai mu zuba mu gani wanda zaiyi nasara………..🤦🏻♀️
4
_Amman seriously baku ga kaman Sulaiman yafi dacewa da saudat ba saboda hidimar da ya faɗa yana mata😜😝😅
8
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
🌹🌹🌹FEEENERH MATAR SOJA 🌹🌹🌹
💃ina masoyan feenah matar soja marubuciyar ✍️✍️✍️✍️
HARAMTACCIYAR SOYAYYA
AURAN SOJA
YAYAN GATA
KUSKURENA
BARIKI AURAN SOJA
WANAKE AURE
😍wannan karonma ta dawo muku da sabon littafinta mai suna 👉 ZANYI BIYAYYA😌 ina masoya hausa novels toga dama ta samu littafin ZANYI BIYAYYA 😌 yaxo muke da solo 💃💃 daban daban
domin san ku fadakantu ,waaxantu dakuma nishadi ku biyota awannan shahararran littafinta ZANYI BIYYAYYA😌 masu iya magana nacewa anayi dakai yafi ba,ayi dakai karku bari abaku labari koda kudinka akace sai da rabanka🤸♀️🤸♀️🤸♀️🤸♀️🤸♀️+
gamasu bukatar biya ku hanxarta karku bari abaku labari kubiya ku karanta cikin Aminci, katin Airtel 200 zaku turo normal VIP 500 kuturo katinku ta wannan number 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 NAFISA SANI fcmb yan niger🇳🇪 masu bukatar biya kunemi wannan number +225 48 15 39 03
36🧝🏻♀️
Na gaji da sadaukar maka da abubuwa masu daraja don na lura kai ɗin BUTULU ne mai saurin manta alkhairi, ga fili ga mai doki idan ka isa kada ka fasa karawa dani a yaƙin niman soyayyar saudat, ni kuma zan manta duk wata alaƙar dake tsakanin mu na gwada maka isa ta…ba don wai muhimmancin ta ya kai hakan ba A’a sai dan na ɗanɗana maka zafin yaudara ta da kuka yi,
“Koda ita ɗin BAZAWARA CE zaka nemi soyayyar ta a haka kuma ka aure ta?”
A firgice sulaiman ya juyo tare da ƙanƙance idanun sa yana watsa ma zayyad kallon tambaya don yaji maganar tashi tayi mishi nauyi ainun,
“Indai ka aminta ka yarda zaka aureta a hakan ni kuma nayi maka alƙawarin zan haƙura da Saudat, zan yayyafa ma zuciya na ruwan sanyi na bar maka ita”
“Bazawara kuma? Are You serious??”
“Ƙwarai kuwa! Saudat bazawara ne kuma da bakinta ta faɗamin haka nasan ba zata min ƙarya ba, akwai faɗi tashi da ƙunci a rayuwarta wanda kai baka sanda shi ba, sannan ita ba ƴar garin nan bane har yanzu dangin ta da iyayen da suka haife ta da kuma dangin tsohon mijinta suna ƙauye, kuma ita ba jinin su khamis bane, ceton ta yayi daga mummunar ƙaddarar dake bibiyar rayuwar ta ya kawo ta cikin garin yola”
Istigfari yayi a zuciyar shi lallai ya shiga sahun maciya amana tunda ya buɗe sirrin da ɗaiɗaiku kuma amintattu ne Saudat ta sanar dasu amman yaya ya iya! Nima ma kanshi mafita yake yi don ya san tabbas babban yaya yaji maganar nan ba zai yarda da wata alaƙa dake tsakanin su ba ma ballantana aje ga batun aure,
Kuma hakan ne ta faru, yana gama ji daga bakin zayd ɗin cikin tashin hankali, juyayi, kullewar kai da ruɗani ya faɗa mota a ɗari suka bar gidan, zayyad najin wani tuƙuƙin baƙin ciki a ranshi har numfashin sa yana sama, hannun shi na dama ya ɗaga ya ɗaura a kanshi da yaji kaman ana sarawa da adda a take ya yanki jiki ya faɗi!!2
STORY CONTINUES BELOW

*******
Gaisawa da hajiya mukayi irin gaisuwar da muka saba irin ta uwa da ƴa don sosai take nuna min ƙauna, kuma nima ina sonta ina tana da tsananin ƙima a idanu na, mun ɗan taɓa hira kaɗan ta kuma tambaye ni makaranta kafin daga nan muka wuce part ɗin aunty amarya kasancewar Zaytoon ta samu miji a can garin da take karatu, Muna tare da Batool sunyi aure Fa’iza ma an saka mata rana, da anso haɗawa da Sulthana don har wani ya fito taƙi firr tace ita sai zayyad,
Bansan wurin wa danje ba a ɗakin su tunda mutum ɗaya ne muke ɗan shiri da ita a cikin wa’inda suka rage kuma mun riga mun gaisa, a parlor na tarad da Ruma tana zaune gefen aunty suna buga lissafi a jikin takarda wanda bansan na menene ba,
Jin sallama na yasa ta miƙe da azama tana sakin ihu calculatorn dake cinyar ta ya faɗi ko a jikin ta tabi kanshi ta take da gudu tayiyo kaina ta rungume ni har sanda muka fillu gefe har muna niman faɗuwa,
“Oyoyo bestie naa” ta kira ni da sunan da muke wa juna laƙani dashi kasancewar kyakkyawar alaƙa da amintaka da ya shiga tsakanin mu a shekaru kaɗan baya da suka wuce,
A hankali cikin kunnen ta na raɗa mata “besty aunty na kallon mu fah”
“Toh miye a ciki?….. Ohh sorry na manta ashe surkuwar mu ce” sake ni tayi tana dariya ƙasa_kasa ta ja hannun Jannat muka ƙarasa shiga ciki,
“Ah ah… Maraba da zuwa ƴata”
Durƙusawa nayi a gaban ta cike da kunya na gaidata ta amsa da fara’a tana tambaya na yanda na baro gida,
“Lafiyan zu ƙlau sunce a gaishe ku”
“To madallah muna amsawa”
Hirar mu bata yi tsayi da armashi da aunty kamar yanda mukayi da hajiya ba saboda tsananin kunyar ta da nake ji, muna zaune Ruma ta wuce da kayan ciye_ciye shaƙe a tray cikin ɗakin ta sannan tazo ta shigar damu,
Idan kaga mun rasa abun zantawa saidai bamu haɗu ba ko kuma bamu ji muryar juna ba, hakan yasa muna shiga muka haɗa Jannat da kayan maƙulashe ta zauna tana haƙarsu sai iyayi take yi wai itama ta fara zama ƴammata ƙannen ta har biyu, kasancewar ta Radio mai jini muka ƙule can ƙarshen gado sannan muka buɗe chapter saidai bamu yi nisa ba aka bankaɗo ƙofar ɗakin har saida muka razana, aunty ne ta shigo fuskar ta ɗauke da tsananin tashin hankali ta sanar dani makaren zayyad sun tashi bansan lokacin da na dira daga gadon ba nayi waje a gujee.
******
Jingina kanshi yayi da jikin seat yana ji kaman shima yayi kukan ko zuciyar shi zata samu salama,
Me yake faruwa ne? Me ya same shi ne? Ɓoyayyun abubuwa sun faru birjik a bayan idanun shi amman ya akayi bai gane su ba sai yanzu? Mutane biyu da ya aminta dasu yake ƙaunar su matuƙa saboda matsayin da suke dashi a zuciyar shi sun ha’ince shi irin ha’incin da a yanzu yaka jin yana ragargaza masa zuciya,
“Ƙwarai kuwa! Saudat bazawara ce kuma da bakinta ta faɗamin haka nasan ba zata min ƙarya ba”
Ya sake taryo kalaman zayyad ɗin a kwakwalwar shi,
Ta yaya za’ayi saudat ta zamo bazawara? Yanzu shekarun ta 18 kacal lokacin da tazo gare su bata fi 15 ba yaushe har tayi aure ta fara zawarci? Anya maganar kuwa gaskiya ne ba shirya shi aka yi don ayi masa harbi biyu cikin rami ɗaya ba?
Amman ya sota kuma har yanzu yana sonta, da ace ɗan adam ke ɗaura ma kanshi soyayya da Saudat bata shiga ko cikin jerin kaso na 10 cikin kalan matan da yake so ba, amma tun tana tatsitsiya yake sonta tun a lokacin yake mata kallon ƙwaila amman hakan bai saka shi ya janye ba, saidai yanzu dole ne ya janye ɗin dan ba zai taɓa auren ta a matsayin bazawara ba musamman ma a yanzu da baisan dalilin da ya fito da ita daga ɗakin mijin ta ba idan ta tabbata bazawaran ce da gaske kenan,
Da ƙyar ya iya jan jiki ya fitar da kanshi daga cikin motar cikin wani kasala da ya dirar masa saboda baƙin ciki ya shiga gida yana layi kaman wanda yayi maye,
a yanxu Sadiya ta fara saduda tayi sanyi kusan rabin makaman yaƙin ta tayi watsi dasu don faɗan yafi ƙarfin ta a yanzu gashi bata da mataimaki, saboda the more tana ƙoƙarin hana faruwan wannan al’amari tsakanin Saudat da sulaiman sai taga kaman daɗa angiza shi take yi tana ƙara ma wutan fetir,
Ta kaɗa ta rawa abu yaƙi ci don har sharri suka taɓa yi ma saudat a lokacin bikin Muna kan cewa ita ta sace gold ɗin sadiyan wanda yafi kowanne tsada bayan ita da hannunta ta ɗauka ta bata kan tasa, da taƙi daga farko sai sadiyan ta nuna fushinta sosai tana cewa ita bata ɗauke ta kaman dangi bane yasa take maida mata hannun kyauta baya, da ta matsa sai Saudat ɗin ta amince gudun ɓacin ran babban yaya da taga kaman ma ba sakawa zatayi ba sai ta saka mata shi a wuya kuma ta hana ta cirewa dashi dole taje dinner,
Ana tsaka da biki wuri yayi wuri taro na manyan mata da haɗaddun maza masu ji da isa da kuma dukiya a tsakiyar su Sulthana tazo ta fizge sarƙan har saida taji ma saudat ɗin ciwo a wuya, ƙarar da ta sake da tsawan da Sulthanan take mata ya sanya wurin yayi tsit hankalin kowa ya dawo kansu,
Har akayi komai aka gama Sadiya bata ce komai ba dukda rantse rantsen da Saudat ɗin take yi haka ma babban yaya yana zaune ƙeƙam kaman gunki ya zuba musu idanu ɓari ɗaya na zuciyar shi yana ayyana mishi da gaske sata tayi wani ɓari kuma yana tunatar dashi irin nagartan Saudat din,
Zayyad!! Mutum ɗaya wanda da ƙyar ya samu zuwa bikin saboda zaman wuri ɗaya ya ishe shi shine kaɗai mutumin da yazo gaban kowa da kowa ya take mata ya aybanta abinda Sulthanan tayi don itama da nata haushin ta ƙwace mata saurayi, ganin shirin su yana niman faɗuwa ƙasa warwas yasa ta yi maganar “dalilin da yasa Sadiya bata bawa saudat sarƙan haɗe da ɗan kunnen shi ba indai a gaske batan tayi”
Shima zayyad ya mayar musu da cewa “ai ita ba doluwa bane da idan ta sata zata saka kuma ta shigo cikin su dashi har ta bari su gani” wannan kalamin shi ya tabbatar ma sulaiman duk abinda ya faru shiri ne kawai don a sanin shi Saudat batayi wayon da zata saci abu mai tsada kaman wannan har ta siyar ba yana da tabbacin bata san darajar shi ba,
A sannan ne zayyad ya raba gari da Sulthana ita kuma uwar gayya consequences ɗin da hakan ya jawo mata yasa tayi danasanin fara shi a rayuwar ta don taga tashin hankalin da bata taɓa ganin irinshi ba a wurin mijin nata,
Kallon shi tayi cikin wannan yanayin amman tosashshen ƙwaƙwalwarta bata faɗa mata taje ta tare shi taji me ya same shi ba har ya wuce ciki, shi kuma a lokacin yana tsananin buƙatar mai kulawa ko mai sauraro daman saudat ɗince yakan kira wani lokaci koda tana makaranta ya saka a bata waya ya ɗan tambaye ta shawarin ta a kan wasu abubuwa wanda bata ɗauki hakan a matsayin wani abu ba amman yau Saudat ɗin ita taji masa ciwo.a zuciya,
Zayyad bai faɗa min komai da ya faru a ranan ba, bayan ya farfaɗo ma da aka kira sulaiman aka faɗa mishi ciwon shi ya tashi bai gwada wani matsanancin damuwa ba, bai yashi hankalin shi ya daburce kuma ya dawo a kan ƙafar shi kaman da ba, sai kawai yayi masa addu’a ya kashe wayar kan cewa za’a fara nima mishi magani kwanannan insha Allah,
Aunty ta jingina hakan ne da cikar buri da biyan buƙata da suka samu zayyad ya riga ya fara aiki shiyasa babu sauran damuwa,
Cikin sati biyu rikici sosai ya ɓarke a tsakanin su suka dawo basu yin ko ga maciji ina gefe bansan me yake faruwa ba saidai ya rage kirana a waya yanzu bamu yin dogon hira, kullum muryar shi cikin damuwa ina ji a jiki na akwai abinda yake ɓoye min amman idan na tambaye shi sai yace min babu komai,
A wannan yanayin da suke aka samu mai maganin da aka fara kai zayyad kuma alhamdulillah yanzu ana samun dama dama kaɗan tunda magani sai a hankali……….🤦🏻♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Team sulaiman how market😝 sunfa dage suna caccakar babban yaya fah daga kawai an tambaye su ra’ayin su😒*
*naga sis Zaheera ma tace ita ma khamis taso a bada boɗɗi saboda Yusrah ta ɗanɗana kuɗan ta don ta gane namiji ba ɗan goyo bane har yanzu abun da tayi a matar kulle yana bata haushi🙄*
*Amman khamis ɗinmu ɗan goyo ne harma da zani😌 koya kuka ce😎*
37🧝🏻♀️
Cikin abinda bai wuce sati biyu ba komai ya canza a tsakanin su idan kaga yanda suke mu’amalantar juna kaman ba ƴan uwa ba, babu jituwa sam yanzu a tsakanin su wanda har iyayen su suka shiga cikin maganar, anyi_anyi da ɗayan su ya faɗi abinda ya shiga tsakanin su haka amman kowa yaƙi faɗan komai daga ƙarshe nasiha kawai dady yayi musu ya ƙara nuna musu muhimmancin alaƙar dake tsakanin kada su yarda su bari wani abu ya shiga tsakani ya ruguza shi,+
Godiya sukayi, a gaban su sukayi sallama ma juna kowa fuskar shi ɗauke da fara’a kaman da gaske, dukda shi zayyad bai ɗauki abun can da zafi ba amman saboda zaɓin da ya bawa sulaiman na idan ya amince zai aure ta a matsayin bazawara zai bar mishi ita bai yarje mishi akan hakan ba yasa shima ya tirje kan koda ya yarda daga baya ba zai bar mishi ita ba,
Suna fita daga parlorn dady sulaiman ya zari tissue ya goge hannun sa saboda musabahan da sukayi a gaban iyayensu su, har yanzu yana ji a ranshi yaudaran shi zayyad yayi har yanzu yana danasanin alkawarin da yayi musu wanda yake ganin sakayyar sharri da yake masa a halin yanzu,
Kamfanin da suke tun da har zuwa yanzu suke samun duk wani rufin asiri daga gareshi ba nasu su kaɗai bane companyn haɗin guiwa ne amman mahaifin su alhj. Muhammad jibril yana da babban kaso a ciki, kusan 42% na abinda kamfanin ta ƙunsa duk nashi ne, saboda yafi kowa saka hannun jari lokacin da ake constructing ɗinshi,
Lokacin da girma ya kama shi a lokacin yaransa sun taso sun fara kawo ƙarfi hakan yasa suka haɗa meeting da share holders na kamfanin cewa yana son a kakkasa nashi kason ma ƴaƴan sa kuma suka yarda saboda nagarta da suka ga yaran suna dashi ta ɓangaren karatunsu da sauran al’amura na rayuwa amman sun ƙayyade cewa ba zasu bawa ko wani ɗaya daga cikin su ya wuce kaso goma ba saboda ba zasu yarda a karya alƙadarin kamfanin ba saboda sunyi imani cewa yaran basu san darajar shi ba don a sama suka same shi basu sha wahalar nima ba kuma har sai kowannen su ya kai shekaru 30 a lokacin ne suka san ciwon kansu da har zasu iya kula da wasu a ƙarƙashin su,
A kan wannan hukuncin aka tsaya, daga fari aka fara mallakawa sulaiman nashi Nafi’u ya biyo baya amman shi zayyad yana da matsalar makarai wanda suka shiga jikin shi tun yana shekaru 3 a duniya a cikin garden ɗin gidan su yana ƙwallo a lokacin almuru ana sallan magriba ya buge aljanu,
(a irin lokacin da ake so iyaye su killace ƴaƴayen su cikin ɗakunan su har zuwa lokacin da za’a kira sallan isha, harta jaririn da yake barci ba’a son barin shi a kwance saboda sheɗanu da suke sauƙowa a lokacin ana son uwa ta kasance tana karanta adduoi ma yaranta wanda suke da wayau kuma a koya musu sunayi don kariya daga sharrin sheɗanu da aljanu kada su shafe su,
STORY CONTINUES BELOW

Koda ace basu shiga jikin yaro ba sukan iya shafan shi sai kaga lokaci daya yaro ya zama kuntali bayi jin magana ko kaɗan, iyaye muyi haƙuri muna ƙoƙarin basu lokacin mu kada nan gaba ƴaƴayen mu suzo suna kuka damu, Allah yasa mu dace, amin)
A take zayyad ya faɗi a wurin bai tashi ba sai da aka zo aka ɗaga shi da kariya a ƙafarshi, kariyan da saida yayi shekaru 4 yana jinyan shi bai warke ba, sai anyi ɗauri daga baya ace baiyi kyau ba haka za’a sake karya ƙafar ayi wani ɗaurin shima daga baya yazo baiyi ba,
Bayan ya samu sauƙi da qyar daddy ya haɗa shi da ƴan uwanshi aka fitar dasu karatu ƙasar waje a wani private school don kar asirin su ya bayyana, a daddafe zayyad ya gama primary lokacin sulaiman na shirin shiga jami’a,
A haka shida Nafi’u suka dinga kula dashi da tashin ciwon nashi da kuma ƙoƙarin rufe abun kada ya bayyana ma duniya, don tabbas ba zasu taɓa barin shi ya samu komai ba idan suka san bayi da cikakken lafiya, shiyasa sulaiman yayi alƙawarin ɓoye masa sirrinsa har zuwa lokacin da zai samu nashi matsayin,
saida ya haɗa kwalin shi a can sannan suka tattaro suka dawo sulaiman ya fara nashi aikin, a lokacin ne ya kafa wa’incan dokoki masu tsauri ma zayyad wanda daga farko ko bakin ƙofa bayi fita ƙannen sa da aka aifa daga baya ma basu sanshi ba saidai su ganshi a hoto, sai lokacin da Ruma ta fara ganin tashin aljanun san ne sulaiman ya fara barin shi yana shiga ko ina a cikin gidan har zuwa yanzu da burin su ya cika shima ya sanu ƴanci kaman kowa….
Takowa yayi zuwa gaban shi ya fuskanci zayyad fuska babu alamun rahama sai bubbuɗa hanci yake yana ɗaga ƙirji, ko yana tunanin hakan zai saka zayyad ɗin yaji tsoron shi ne oho!
“Ba’a yarda sau biyu da maciya amana, zan sarara don an sasanta amman idan na tabbatar akwai yaudara a ciki zanyi amfani da dukkan ƙarfi na in ɗauki fansa……a yanzu ba a kan saudat nake magana ba zanyi yaƙi ne a kan alaƙar dake tsakani na da kai wanda ka daɗe da gurɓata shi”
Taɓe baki kawai zayyad yayi yana kallon cikin ƙwayan idon shi ba tare da yaji shakku ko tsoro a cikin zuciyan shi ba yace,
“Allah ya kawar da shaiɗanin dake sanya waswasi a zuciyan ka, abinda da kake yi ba girman ka bane”
Daga nan ya fice abinshi bai sake waiwayan shi ba,
*****
Washe gari aka dawo masa da result ɗin binciken da akayi mishi a kan Saudat don kwata_kwata bai aminta da abinda zayyad ɗin ya faɗa mishi ba, saidai harda labarin abinda bai sanar dashi ba ya samu nan zuciyar shi ta kasu gida biyu,
Rabi yana son yarda da auren Saudat don har a yanzu akwai burbuɗin sonta cikin zuciyar shi don yayi mata soyayya na gaskiya a baya wanda babu algus a ciki amma wani ɓangaren yana faɗa mishi ya rabu da ita, ya fita harƙan ta gaba ɗaya don bata dace dashi ba taje su ƙarata da zayyad ɗin,
Rasa matakin da zai ɗauka yasa ya tunkari mahaifiyar sa da zancen, tana zaune a parlour ita kaɗai tana sauraron wa’azi a TV ya shigo, ganin ita kaɗaice yasa bai nemi keɓewa da ita ba ya zauna ya fara zayyano mata damuwan shi daidai lokacin da Nana tazo wucewa,
har ta nufi hanyar bedroom ɗinta jin abun da suke faɗa yasa ta dawo ta bayan labule ta laɓe tana sauraron su,
Sauƙe nannauyan ajiyan zuciya yayi cikin murya mai bayyana damuwa yace “ni ba wannan nake gani ba Hajiya, a da naso auren ta amman kuma itafa matar wani ce, na san dai batq da laifi a abinda na faɗa miki ya faru da ita amman akwai banbanci sosai tsakanin ta da sauran ƴammata, rayuwan ta ba zai taɓa tafiya dai_dai ba saboda haka ina gudun samun matsala daga gareta Hajiya”
Jin haka yasa Nana gyara tsayuwa tana daɗa zuba kunnuwan ta don tasan tabbas zancen babba ne amman bata fahimci akan waye suke nufi ba,
“Babana! Nagartan mutum da nasabar shi shi ake dubawa yayin aure ba wasu ƙyale_ƙyale ba, sannan Boɗɗi matar wani take a da amma banda yanzu kuma Allah ya halarta auren bazawara ballantana mai ƙananun shekaru irin nata ma babu wanda zai san da hakan bayan mu da kai”
Zaro idanu tayi cikin son rashi gaskata maganar take girgiza kanta a hankali ta ja juya ta shige ɗakin ta tana maida numfashi sai kuma ta sheƙe da dariya tana tafa hannuwa,
“Eh lallai nesa tazo kusa! Ashe ƴar anacin ma tsohuwar guzuma ce, ba zallan babban yaya ba har ya zayd sai kin rasa shi matsiyaciya” bata jira komai ba ta ɗauki waya ta kira Sulthana da ta fita yawon ta zubar cikin gari tun safiya ta shaida mata wannan labari mai daɗi,
Sunfi 1 hour suna kintsa munafurci da yanda zasuyi ma tufkan hanci, su ƙulla wannan su warware wannan kafin daga ƙarshe suka yanke shawarar abinda zasuyi su wulaƙanta Saudat yanda wataƙil har abada ba zata sake samun mashinshini ba sannan sukayi sallama,
*******
10:06am
Ganin haɗuwan motar da ta shigo cikin karkaran yasa yara harma da manya sukayi zuga suka biyo ta dan sun san dasu samu daga wurin mai ita,
A wurin da ɗan jagoran nasu ya tsaya sukayi parking daga shi har driver suna hamdala saboda baƙin wahala da suka sha saboda gurɓata ciyar hanya,
Umarni yayi ma divern da kada ya buɗe ƙofar motar ya zauna ciki yana ƙarewa mutanen dake zagaye dashi kallo zuciyar shi yana tsananta bugu saudat bata san da abinda ya aikata da abinda yake aikatawa ba saidai yana fatan zata aminta da hakan,
Kuɗi ya ciro daga aljihun sa ƴan ɗari biyar_biyar wanda baisan iya adadin su ba kafin ya buɗe motar da kanshi ya fita ya danƙa kuɗin ma babban su ya ratsa ta tsakanin su ya wuce gaba ɗan jagoran shi yana gaba har zuwa ƙofar gidan nasu wanda kwararraɓewan da yayi a yanzu har yafi na da,
Kallo yake ƙare ma gidan yana jin nauyi sosai a zuciyar shi, wai yanzu Saudat ɗin tashi daga wannan wurin ta fito? A cikin wannan kangon tayi rayuwa?………..🤦🏻♀️
_but who is he?🤔 Sule ne ko zayd?_2
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
38🧝🏻♀️
Ashe matsayin da yake tunanin ta taka ma bata kai ba? Lallai idan haka ne yarinyar mai Sa’a ce yanda ta samu canjin rayuwa a lokaci ɗaya kuma tayi saurin adjusting da rayuwar da ta tsinci kanta a yanzu,+
Tura yaron yayi ya shiga yayi sallama da mai gidan, saidai kafin ya dawo wasu gangun matasa sun ƙaraso wurin da sulaiman ɗin yake tsaye da makamai a hannun su suka tare ƙofar shiga gidan nasu,
Tsayawa kawai yana ƙare musu kallo ba tare da yaji ko ɗarr cikkn zuciyan shi ba, cikin bossy voice ɗinshi yace
“Ku kuma lafiya?”
Ɗaya daga cikin su ne wanda yake riƙe da wani adda mai tsatsa ya matso gaba bakin shi baƙi wuluk kana ganin shi kaga tantagaryan ɗan shaye_shaye dan a wani lanƙwashe yake tafiya,
“Ehh! baba m..me yak.. kawo ka ww..wannan barzahun..nne! KKo…k kaima..kkana muradin…ba…baƙuntan lahira nan…….kusa ne”
Girgiza kai kawai yayi yana sakin miskilin murmushi “A’a ko kusa saidai ku idan kuka hana ni shiga zaku iya baƙuntan lahiran”
“Kaiii!! billahil axeemi zamuyi maka bille a gadon baya kasan su waye mu kuwa?? Kada ka ganka wani buzu_buzu wallaye zamuyi maka ɓawo_ɓawo idan baka bar nan ba” Wani daga cikin su ya faɗa yana karta nashi makamin a ƙasa ta wurin da sulaiman ɗin yake tsaye alaman da gaske saran nashi zaiyi idan bai matsa ba,
Drivern sulaiman ɗinne yayi saurin fitowa daga cikin motan da yake zaune a can nesa yana kallon su hannun shi ɗauke da bindiga da gudu ya ƙaraso wurin da suke tsaye tare da ɗana kunaman bindigan yayi pointing ɗinshi a kansa,
“Idan kunfi ƙarfin mutanen gari ai baku fi ƙarfin hukuma ba, idan kuka yi wasa wallahi babu mai kwanan gidan su a cikin ku yanzun nan zaku tafi gidan yari”
Ja da baya sukayi da jin kalaman su, idanun su zuru_zuru cike da tsoro hakan na tabbatar musu drivern police ne don wandon jikin shi ma na uniform ne ya ɗaura baƙin T shirt a kai,
Waya drivern ya ciro ya kira ƴan uwanshi sannan suka ci gaba da tsayuwa a wurin har zuwa wani lokaci basu motsa daga wurin ba kowa yana tsaye da makami a hannu sun kasa taɓuka komai, sai wani daga can baya ne yayi ƙarfin halin cewa
“Amman dai ka san ba’a shiga wannan akulkin ko? Wannan gidan da mutanen cikin ta duka haramtattu ne an shafe su daga cikin ƙasar nan, a yanzu basu cikin jerin mutanen da ke da ƴancin rayuwa a tare da mu mai gari ta riga da ta kore su daga cikin yankin ta”
yamutsa fuska sulaiman yayi yana jifan wanda yayi maganan da wani irin kallo wanda ya sanya shi shan jinin jikin shi, ba ƙaramin kwarjini mutumin yayi ba don yana da cikar zati matuƙa,
“Shi mai garin Allah ne da har zai iya haramta ma wani rayuwa a wani yanki na cikin doron ƙasa?” Ya faɗa cikin ɗaga murya tare da waigawa yana kallon dandazon mutanen da suka fara taruwa a wurin,
Shiru sukayi duk cikin su ba’a samu mai bashi amsa ba, yaci gaba da cewa,
“Shi yana can a kwance zaizo ya saka ku cikin matsala kuce mishi yazo ya fuskance ni mana! Na shigo ƙasar shi babu izinin shi kuje ku faɗa mishi ya ɗauki mataki da kanshi ba ya turo marasa aikin yi irin ku ba,
Ku sani ana girmama mutumin da ya girmama Ubangijin shi ne kuma ya daraja ɗan adam don mutum ba abun wulaƙantawa bane sam!
Wait!! Meyene mutanen gidan sukayi muku da kuke musu irin wannan hukuncin? Babu mai shiga gidan kun hana su fita su nemo abinda zasu ciyar da kansu da ƴaƴan su, kun hana su fita su biya sauran buƙatun su na rayuwa, kun daƙile musu duk wani jin daɗi a wani dalili?”
STORY CONTINUES BELOW

“Shaboda an riga da an shine ma juyi’an boɗɗi kuma ba tsinuwan ba zai barsu ba har sai mun kama shi mun kashe shi, shine ya kashe Yarima mai jiran gado don haka ba zamu barshu ba har sai sun fito da ita daga wurin da suka ɓoye ta”
Takawa wurin ɗan tsohon yayi wanda ke riƙe sandan sa na dogarawa saboda tsufa har wani tankwarawa yayi kusan rabin hakwaran bakin sa babu sun fita amman saboda ƙarfin hali sai ɗaɗɗaga jijiyoyin wuya yake yi kaman idan an barshi zai iya taɓuka wani abun ne,
“Yanzu baba saboda girman Allah.. da me hallaka yarinyar nan zai amfane ka kaida ka kusan gangarawa?”
A hassale tsohon ya ɗago ya kalle shi yana jifan shi da harara mai ban tsoro saboda yanda naman fuskar shi ya motse
“Aradun Allah baddon ke kaɗɗo bace da na mare ki”
“Ni kuwa ko girman ka ba zan gani ba zan hukunta ka..don haka ka maida hankali”
Da haka fitina ya ɓarke a tsakanin su suka hayyaƙo ma Sulaiman da drivern shi sai wasu ne daga cikin mutanen ƙauyen wanda suke ganin rashin dacewar abinda akayi ma boɗɗi da iyayentan ne suke tare mishi har motocin police suka ƙaraso suma suka kasa suka tsare saida sulaiman ya shiga gidan,
A soro ya tsaya yayi sallama ko rufe baki baiyi ba jaɗe dake tsaye tun lokacin da suka fara case ɗin ya bayyana a gaban shi,
Sanin da yayi ma boɗɗi tun shekaru 3 da suka wuce shi kaɗai ya bashi daman ganin kaman da sukeyi da wannan matashin saurayin wanda a shekaru ma ya san ba zai ƙarasa Zayyad ba,
Ba zallan yunwa da wahala ba harda datti da ɗauɗa sun kama jimin jaɗe, ga baƙin rama da yayi har a fuskan shi ya nuna he looks very sad idanun shi sun tara ruwa kaman zasu zuba,
Daga ƙarshe dai yana da yaƙinin sauƙi yazo musu bayan azabtuwa da sukayi da wahala, daga ƙarshe dai bayan shekaru 5 fuskar rahama ya sake leƙowa cikin gidan, daga ƙarshe dai bayan saƙon yayan shi Aminu da yake turo musu ana bin dare domin kawo musu suna ci suna sha daga gareshi wani yazo garesu don ya taimake su,
Miƙa mishi hannu yayi a ɗarare jaɗe ya amsa sukayi musabaha sannan shige cikin gidan sulaiman ya bishi a baya ba tare da ya nemi wani bayani daga wurin baƙon da yau ne ya kasance haɗuwar su dashi na farko ba,
Gidan kaman ba a cikin ƙauyen yake ba, yafi dacewa ayi kwatancen shi da maƙabarta don baiyi kama da wurin da mutane ke zaune a ciki suna rayuwa ba,
yara ne barbaje ko ina raman jikin su kaman masu kwasharko wanda yagaggun tufafin su yake bada daman hango ƙashushuwan ƙirjin su wasu kuma babu suturan a jikin su gaba ɗaya, bakunan su a bushe idanun su sunyi kwarmi basu da ƙarfin wasa kaman sauran yara ko,
Sulaiman baisan sa’in da hawaye yayi nasaran sauƙa daga idanun shi zuwa ƙasa ba, yayi saurin dakatar dasu da handkerchief wanda ya ciro shi daga aljihun wandon shi yana jinjina girman zalunci da rashin imani na mutanen ƙauyen da shuwagabannin su gaba ɗaya domin duk abinda ya faru ya riga da ya sani a binciken da yayi,
Zubewa jaɗe yayi a kan guiwowin sa yana kuka ya riƙo kafafun sulaiman,
“Kaɗɗo ban shanki ba, banshan me ya kawo ki gare mu ba amman na roƙe ki don girman Allah ki taimaki innar mu kada ya mutu, bashi da lafiya amman bamu da hanyar mishi magani, ki taimake mu dan Allah duk hanyar da kike so zamu bi mu biya ki, ki taushaya”Sunkuyawa yayi ya ɗago jaɗe baice dashi komai ba ya ƙarsa inda yake hango malam ardo zaune, baude yi tagumi ba amman irin damuwan da yake fuskar shi zaisaka ka gwammace mishi dama tagumin yayi,
Sake fuska yayi kadan cikin dattako suka gaisa sannan yayi jimm yana kallon Sulaiman har saida ya gama mishi bayanin kanshi tass, ya faɗa musu matsayin shi wurin Khamis a matsayin sanadin da ya haɗa shi da saudat saboda shi kaɗai suka sani,
“Allahu Akbar! Allahu Akbar!!! Shine kalmar da ya dinga maimaitawa tare da ɗaga kanshi sama yana ƙoƙarin tare hawayen dake ƙoƙarin sauƙo mishi, ganin abun yake yi kamanr mafarki, baiyi tsammanin zuwan haka a irin wannan lokacin da babu zato babu tsammani ba, saidai shi mumini bayi cire rai da rahaman Ubangiji,
Kafin malam ardo yayi wani magana yarinyar jaɗe ta fito da gudu tana haki cikin harshen fillanci take sanar musu jikin inna ya tashi,
******
“To yaushe kike tunanin ya kamata muje ƙauyen mu duba su?”
Rintse idanu na nayi ina tuna halin da na baro iyayena a ciki sannan na ware su a hankali kaman Zayyad ɗin nake gani a gaba na cikin murya mai rauni nace
“Ina tsoro hamma zayd”
“Tsoron me kuma babes?”
“Ba lallai bane idan na shiga na samu damar fitowa da raina, ba lallai bane idan naje wuroɓokki na ga dangi na a cikin yanayi mai kyau, ina tsoron rasa wani a cikin s….”
“Shhh…. Ki bar kukan haka nan dan Allah don’t burn my heart, insha Allah zamu sami kowanne daga cikin su cikin ƙoshin lafiya, just fix a date da ya kamata muje tunda yanzu nima na samu ƴancin kaina zan taya ki fafutuka har sai kin samu naki….. zan nemi taikon babban y…” Sai kuma yayi shiru ba ƙarasafaɗan abinda yayi niyya ba tunawa da giɓin dake tsakanin su a yanzu,
“Thank you so much hamma zayd, babu abinda zance muku saidai Allah ya saka muku da alkhairi kai da dadyn Arif, kun tallafi rayuwata sosai na g…”
“Shhhh… please shhhh….bani tunanin akwai godiya tsakanin mata da miji don duk abinda zanyi miki kaman ma kaina zanyi, Allah dai ya bani iko kawai kuma ya kaimu lokaci”
Da “ameen” na amsa mishi daga nan muka ci gaba da hirar mu irin ta masoya zuwa wani lokaci, da ƙyar ya barni na tashi nayi alwala nayi sallah lokacin har ƙarfe 4 ya gota,
bayan na idar ne naci karo da missed calls ɗin sulaiman har guda 3, ban ƙarasa ninke sallayan hannu na ba na ɗauki wayar nayi calling back don nasan tabbas idan kaga kiran shi toh ya ɓaci ne,
Bugu biyu yayi disconnecting sannan ya kira ni,
yau muryar shi yasha banban dana kullum, akwai wani ɓoyayyen sanyi, taushi da nutsuwa a cikin ta abin har yaso kulle min kai,
Mu shirya mu fito nan da minti 30 zamuje wani wuri shine kawai abinda ya faɗa min ya kashe wayar sa,
Zamu je wani wuri ina? Mu shirya nida wa? Ganin bani da mai bani wannan ansan yasa na tashi na shiryan kaman yanda ya umarceni na faɗa ma maman aunty yusrah abinda ya faɗa min sannan na zauna zaman jiran shi,
Wajajen ƙarfe 5 da ƴan kai sulaiman ya sake kirana na fito, a cikin motar shi naci karo da khamis zaune tare dashi a back seat ɗayan kuma hamma Nafi’u ne yake ja aunty yusrah ne kaɗai zaune a baya sai Jannat a gaba, yaje ya ɗauko su daga farko ne don yayi tunanin a gidan khamis nake har yanzu.
To ina zamu tafi ba tare da hamma zayd ba? Na tambayi zuciyata, kafin na lalumo amsa wayana dake jaka ya ɗau ruri ina cirowa naga shine ban wani damu ba na ɗaga abuna,.
“Assalamu alaikum hamma zayd, Please ka bari idan muka dawo zamuyi magana”
“Ina ne zaku je?”
“Nima ban sani ba amman tare da dadyn Arif zamu tafi yace ba daɗewa zamuyi ba zamu dawo”
_”A yau ɗinnan zan nuna maka matsayi na, a yau ɗinnan zan gwada maka wustiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa ni na riga da nayi maka nisa, a yau koda ƙarfi koda yaji saina ƙwace Saudat daga gareka kuma HAR ABADA ba zata sake zama taka ba, ka shirya ma zubda hawaye zayyad don nasan kana jin daɗin fitar dasu sosai”_
Kalaman sulaiman kenan wanda ya faɗa mishi kafin ya baro gida ɗazu ya dawo yana mishi yawo a ƙwaƙwalwa, cikin tashin hankali yace,
“A’a babes kada ki bishi dan Allah, kada ki yarda kije Please”
“Idan baki je gareta a yanzu ba zaki iya rasata har abada, idan baki je gareta yau ba inajin har ki mutu ba zaki yafe ma kanki ba, kinyi burin ganin su na tsawon shekaru yau Allah ya kawo miki dama zaki barshi ya suɓuce ne?”
_to maganar wa zanbi? ZAYYAD KO SULAIMAN???_
_______________
*Assalamu alaikum readers, saƙon gaisuwa da kuma gajeren ban haƙuri,*
*Kasancewar Ummu Najma ɗaliba yasa zata nemi izini ku ɗan ɗaga mata ƙafa saboda a yanzu munyi resuming school gaskiya dole ina buƙatar lokaci da kuma ntsuwa na karatu amman ba hakan yana nufin ba zamu ƙarasa ƙaramar bazawara bane ba kuma zamu gajarceshi kaman yanda naso yi a farko ba amman yanzu zamu rage yawan posting ya zamo sau 3 ko 4 a sati, a yi mini aikin gafara*
Na gode❤️😘
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
39🧝🏻♀️
A kiɗime na juyo ina kallon shi don ban gane abinda suke nufi ba dukkan su, a dalilin me zaisa zayyad hana ni bin babban yaya? Kuma a kan waye sulaiman yake magana?
Sassauta murya nayi yanda sulaiman dake tsaye a jikin motar dake gaba na ba zai jiyo mu ba nace
“Hamma zayd bamu kaɗai zamu fita ba fah! Kuma baka san inane zamu je ba me yasa zaka ce kada na bishi?”+
“Ok tun yanzu har zan fara jayayya dake?”
Irin tone ɗin da yayi amfani dashi wurin magana yafi kama da na babban yaya ba na zayd da na sani mai magana ko yaushe cikin sanyi da lallami ba, shiru nayi inajin wani iri na kasa komai ga sulaiman da ya tsare ni da idanuwa khamis yana jifa na da mugun kallo, ina taku ɗaya kaman a kunnen shi yace,
“Dan girman Allah boɗɗi kada ki bishi gani nan zuwa inda kuke, kada ki bari ya yaudare ki da kalaman shi ya sanya katanga a tsakan….”
“Mahaifiyarki zata gaji da jira Saudat, iyayen ki na tsumayen ganin ki kizo muje kiga halinda suke ciki”
Kalaman shi da naji dirin sauƙar su kenan cikin ƙwaƙwalwa da zuciyata,
A iya sanin da nayi wa babban yaya babu wasa ko ƙarya a tsakanin mu ko fuskar shi da mutanen da yake tare dasu kaɗai ya isa ya tabbatar min da gaskiyar zancen shi,
Wasu hawaye masu sanyi ne naji sun fara bin kunci na, ban gansu ba amman har naji sanyin ciwon dake cin zuciya ta tsawon shekaru sama da 5, disconnecting kiran nayi ba tare da na sani ba da gudu na nufi motar da naga aunty yusrah a ciki na shiga muka ɗau hanya,
Fakan idon ya Nafi’u wanda Jannat ta saka a gaba da surutu tayi ta Mintsile ni a cinya tana harara na,
“Kina son ku saka ƙafar wando ɗaya da abban jannat ko? Ana miki magana kin tsaya kina shiririta ma mutane sanin kanki ne bayi son rawan kai tun kafin ya saɓa miki ki shiga hankalin ki”
Maganar ta ya shiga kunne na amman banji abinda ta faɗa ba, my mind was absent ganin abunda ke faruwa yau ɗin nayi kaman a mafarki,
kwantar da kaina nayi a saman kafaɗar ta da hannu na zagaye kunkumin ta na rungume ta sannan na saki kuka mai zafi koda zanji sauƙin abinda yake taso min,
Bubbuga baya na takeyi a hankali cikin sigar lallashi ya Nafi’u ya miƙo mata kwalin tissue ɗungurungum tana share hawayen fuska na dashi, ni kuwa ji nakeyi kaman na ƙwace tuƙin motan daga wurin shi don gudun da muke surfawa a titi bayi min sauri babban buri na a yanzu kawai na ganni a gaban Inna ta da baba na,
A maimakon mu ɗauki hanyar wuroɓokki sai naga munyi parking a ƙofar asibiti, rasss naji ƙirjina ya buga ganin suna fita daga cikin motar babban yaya har ya nufi cikin asibitin, hakan kenan na nufin babu lafiya, wani nawa yana cikin matsala,
Ganin bani da niyyan motsawa yasa yusrah taja hannu na muka fita, a hankali take tafiya ina biye da ita a baya zuciyana yana bugun uku_uku baki na ɗauke da kalolin salati har muka isa room 6 ya saka kai ya buɗe sannan ya tsaya a jikin ƙofar yana kallo na,
Zaune take a saman gadon anyi mata matashi da pillow ta jingina bayan ta da jikin gadon, inna ta ƙara tsufa sosai a cikin shekaru 5 kacal saboda wahala da damuwa da har wrinkles sun fara bayyana saman fatar ta, ji nayi zuciyata ta karye lokacin da na saka idanu na cikin nata, kallo ɗaya zakayi mata kasan har yanzu tana jinjiki amman hakan bai hana ta sakin murmushin da na ɗauki tsawon lokaci ban ganshi ba cikin sassarfa na ƙarasa wurinta sannan na zuba a kan guiwa na tare da kifa kaina a kan cinyar ta na shiga rero kuka mai tsuma zuciya,
Babu wanda yayi ƙoƙarin rarrashina don a yanzu kukan shine mafi a’ala domin zai rage min wani abu daga ƙuncin dake zuciyata, munfi 4 minutes a haka wurin ya ɗauki shiru sai sautin kuka na kawai dake tashi, da ƙyar inna ta iya ɗaga hannun ta saboda nauyin da zuciyarta tayi ta ɗaura shi a kaina,
“Tashi boɗɗi am, innar ka tana lafiya ka daina kuka babu abinda ya same mu” shine kalaman da ta dinga maimaitawa har na rarrashi kaina na ɗago ina sake ƙare ma fuskarta kallo, she is my first love, mutum na farko da ta yarda dani sama da kowa dukda a lokacin bata nuna ba,
Hannayen ta na ɗago cikin nawa ina sumbatar su tare da sakin murmushi mai haɗe da kuka abun sai ya bata kunya ta juyar da kanta tana son ƙwace hannun ta amman naƙi bata daman hakan, ni yanzu ban damu ba zanyi ƙoƙarin nunawa iyayena soyayya domin a yanzu niba boɗɗin wuroɓokki matar Yarima bace, yanzu na waye a kan addini kawai nake tafiya babu ruwana da al’ada mai tsanani NO MORE GIDADANCI!
“Ayyo boɗɗi innar ka kawai ka gani ko?”
Zumɓul na miƙe ina dariya mai sauti yayin da idanuna suka sauƙa kan mahaifi na amman har yanzu basu daina zubar da hawaye ba, da gudu naje na shige jikin shi tare da ƙanƙame shi tsamm a jiki na har yanzu dai babu ma wanda nayi magana,
Tsilli_tsilli yake yi da idanu yana kallon dukka mutanen ɗakin tare da ƙoƙarin ɓanɓare ni daga jikin shi amman naƙiya, kunya yaji ya kama shi kaman ya nutse a ƙasa da ace a ƙauye ne hakan ya faru ai sai yayi sati bai haɗa idanu da mutan gari ba, saida na gaji dan kaina na sake shi juyawan da zanyi nayi tozali da ya Aminu tsaye a gefen Jaɗe, duk cikin su shi kaɗai ne sanye da kayan birni T shirt da wando,
Toshe baki na nayi cike da tsananin mamaki don a lokacin ji nayi kaman na kurma ihu saboda daɗi,
“Hamma Aminu kaine??”
Sassanyar murmushi yayi tare da gyada kai yace
“Nine boɗɗin baba kina lafiya ko?”
Ban iya bashi amsa ba na shiga jikin shi da gudu ina sake tambayar shi
“Ya aminu kaine?”
Khamis, yusrah da Nafi’u dai suna tsaye ne suna ƙare mana kallo cike da sha’awa ba’a batun babban yaya da bakin shi ya kusan taɓa kunne yana kwatatanta farincikin da nake ji a cikin zuciyan shi ko a yanzu buƙatar shi ya biya,
Bayan an gama gaishe_gaishe na sake komawa jikin babana lafe ina bin kowa da kallo cike da sha’awa, ɗan ture ni yayi yana karkaɗe min jiki na wai kada na shafe su jiki na ya ɗauki datti, rufe idanu na nayi ma kaman ban jishi ba domin idan da za’a tara duk arzikin duniyar nan a bani ba zasu kaisu cikin rayuwata ba,
“A gashkiya bani da abinda zan shaka miki dashi kamishu, kin riƙe mana amana sakani do Allah, mun gode Allah ya saka miki da mahihicin alkhairi ya saka ki gama da duniya lahiya”
Lumshe idanu yayi saboda jin daɗin addu’ar da kuma farincikin sauƙe nauyin da aka ɗaura mishi na shekaru yace
“Ameen baba, kun riga da kun gama biya na domin ba don kaiba da yanzu bani tare da iyalina ko bani cikin duniyar ma gaba ɗaya, saidai kuma rabin ɗawainiyar Saudat ga wanda ya ɗauke shi” ya ƙarasa yana nuna sulaiman,
“Duk wani canji da kuka gani a tattare da ita yana cikin wanda sukayi fafutukar kawo mata shi, ya bada gudunmawa sosai a cikin rayuwar ta ba tare da an roƙe shi ko an saka shi dole ba”
Sulaiman dai yana tsaye kanshi a ƙasa yana yaƙe, haka kawai yake jin ransa fari tass shima gashi yau ya saka mutane farinciki yana jin sautin dariyan su a saboda shi,
Haɗe hannuwan shi baba yayi yana shirin sauƙa ƙasa sulaiman yayi saurin taro shi yana girgiza kai,
“A’a baba, dan Allah kada ka saka shaiɗan ya shigo cikin tarayyan mu na alkhairi, aci gaba dayi mana addu’a kawai”
Kallon shi kawai nake ina mamaki, sai yanzu na fahimci duk alkhairin da yake faruwa dani gaba ɗaya aikin babban yaya ne, wannan wani irin mutum ne? Wani irin zuciya sulaiman yake dashi da bata gajiya da aikata alkhairi da kyautatawa?
Babu wani kyakkyawan fahimta tsakani na dashi amman yana ta hidima dani babu gajiyawa, duk wasu buƙatuna na rayuwa ya biya min su ba tare da na faɗe su ba, dame zan biya shi???
_amman kuna ganin abubuwan da sulaiman yake yi ma saudat tsakani da Allah ne kuwa??_3
*Ayi manage, kada dai a jini shiru ne yasa nayi wannan zuwa gobe zamuyi mai tsayi insha Allah*
Ummu Najma ce 😘
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Wannan shafin naku ne my Wattpad buddies 🤩🥰 ur comments are killing me ahswear😂 sometimes i wonder inda ace true life story ne babu Abinda zai hana ku zuwa wurin nan ayita ta ƙare na lura baku ɗaukan nonesense😅 you are doing a great job and i love it😍, keep the good work dearies😘😘😘😘*+
40🧝🏻♀️
“Amman…Yaya akayi ka san iyaye na da wurin da suke zaune? Ko hamma zayyad ne ya faɗa maka?” Na tambaya idanu na a kan sulaiman,
Kafin ya bani amsa Nafi’u ya amshe da “Ohh! Wato mu bamu kai a faɗa mana wani sirri ba sai amininki zayd ko….?”
Annurin fuskar shi ne ya kau da jin kalamin shi, har alaƙan dake tsakanin zayyad da Saudat yayi ƙwarin da mutane suka fahimta? In amintakan ne me yasa ba’ace tana yi dashi ba dhi da yake ɓata lokacin shi a kanta sai da zayyad?.
Murmushi nayi nace “ba haka bane dadyn Husna, kasan abu irin haka babu amfanin faɗan shi already na ɗaura muku nauyi ba zan so ƙara wani a kai ba”
“Hakane amman tunda bamu muka ce miki mun gaji ba bai kamata ki hana mu samun lada ba, you have already became part of our family mun ɗauke ki kaman yanda muka ɗauki su Nana, muna maraba da duk matsalolin ki ko damuwan ki kuma zamuyi ƙoƙarin magance miki su matuƙar baifi ƙarfin mu ba, so feel free daga ni har zayyad har ya sulaiman duk ɗaya ne kinji ko?”
Gyda kai nayi fuska na cike da annuri na fara surfo musu godiya su baba suna taya ni, har aka kira sallan magriba muna ɗakin ana basu asalin labarin abinda ya faru ba wanda suka samu daga bakin mutanen gari wanda aka sirka shi da ƙarya ba, kowa ya tofa albarkacin bakin shi daga ƙarshe amman kalmomin da sulaiman ya ambata basu fi a ƙirga da yatsun hannu ba suka tashi zasu tafi,
“Yanzu baba za’a sama muku wurin zama saboda ba zai yiwu dukkan ku kwana a nan ba saidai mutum ɗaya ya zauna a jikin inna”
“Eh akwai mai ɗakina daizo ya kwana a nan ɗin sai yayi mishi duk abinda ake so” cewar jaɗe
“Toh hakan yayi, ku gama shiryawa zuwa anjima zan turo driver yazo ya ɗauke ku sai ya kaiku masauƙin naku”
Takowa kusa da inda yake tsaye khamis yyi cikin girmamawa ya duƙar da kai yace “amma boss da ka barshi kawai ɗawainiyan zaiyi maka yawa ni zan tafi dasu nawa gidan su zauna”
“A’a ba za’ayi haka ba….ai da nasan zan barsu su takura ko kai na takuraka ne da ban ɗauko su munzo nan ba, za’a kaisu wurin da zasu sake insha Allahu, kada ka damu kanka”
Godiya muka sake mishi a karo na babu adadi sannan suka kama hanya harda khamis amman yusrah ma ta zauna tace sai zuwa jimawa itama zata tafi,
Suna fita sulaiman ya cilla key ɗin motan shi ma khamis ya shiga na Nafi’u ya zauna sannan suka ɗau hanya,
Sunyi nisa da tafiya ya ɗan juyo yana duban shi hankalin shi gaba ɗaya ya tattara jikin takarda da ya gani saman dashboard yana karanta abinda ya ƙunsa,
“Babban yaya” ya kira shi a taƙaice, da “uhmmm” ya amsa ba tare da ya juyo ba,
STORY CONTINUES BELOW

“Ka yanke shawarar auren yarinyar ne naga kaman kana son shige mata ta wurin iyayenta?”
“Well… Har yanzu ban gama tsaida zuciyata wuri ɗaya ba tukun, inason na fahimci iyayen nata wasu irin mutane ne kafin nan sa’annan na koya ma Zayyad hankali”
Ɗan ɓata fuska yayi alaman baiji daɗin maganar shi ba yace “haba yaya da girman ka dan Allah me zaisa ka kama faɗa mai kama da gaba da ƙanin bayanka? Dan Allah mai zayyad yayi maka haka ne kuke son nuna ma duniya ku ɗin daban ne ba ba ciki ɗaya kuka fito ba”
“Mtsweeeww it will be better if we could not talk about it”
“But why? Zayyad jininka ne fah, ɗan uwanda a da kowa ya san yafi soyuwa a gareka me yasa zaka bar wani abu ya shiga tsakanin ku har haka?”
Ajiye takardan hannun nashi yayi ya juyo tare da tattaro dukkan attention ɗinshi ya maida wurin Nafi’u dake driving shima yana kallon shi jifa_jifa,
“Kasan sai yanzu nake daɗa da fahitan duniya da abinda ke cikinta, duk son da kake wa mutum kada kayi tsammanin zai soka zuciya ɗaya sannan idan ba ciki ɗaya kuka fito ba yaudaran ka abu mai sauƙi ne a wurin shi”
“Shima wanda kuka fito ciki ɗayan baka da tabbaci a kanshi….wannan haalin ɗan adam ne, amman faɗa mun wani yaudara ne Zayyad ɗin yayi maka?”
Sauƙe numfashi yayi tare da kawar da kanshi gefe yace
“Boɗɗi yace yana so, harma ya saka yarinyar ta fara sonshi bayan yasan ina sonta”
“Ban gane ba! Yasan kana sonta kaman yaya…ka faɗa mishi ne? Don a iya sani na ko ita Saudat ɗin bata sani ba babu ma wanda ya sani bayan hajiya da kuma ni dana tirke ka ala dole ka faɗa min ta yaya za’ayi yasan kana sonta ya sulaiman shi allan misiru ne?”1
*******
“Haƙiƙa wannan kaɗɗo ƴar albarka ne babu abinda zamu ce mata shai Allah ya shaka da alkhairi itama ya albarkaci nata zuyiar, autan Inna ka ganka kuwa? kaman wani bature?” Ya faɗa yatsar shi yana taɓa fatar hannu na a hankali cike da tsoro don gani yake kaman abu kaɗan zai iya sanyawa naji rauni saboda yanda hutu ya zauna a jikina fata na ya ƙara yin laushi da sulɓi haske na ya ƙara fitowa,
Ƙara lafewa nayi a jikin inna ina dariya kasancewar gadon yana da girma abinka da asibitin kuɗi, don tuntuni abinda suke yi kenan shida matan shi da yaran shi da baba inna dai kaman kunyata take ji ya Aminu kuma ya zama wayayye yanzu zahirin shi kaɗai ya isa ya nuna hakan,
“Ka daina kiranta auta fah ka saka ta ƙara sakalci daman yaya lafiyan kura bare taga nama? Kin daiga ƙanwar ki a gaban ki yanzu itace da tutan auntan”
“A’a wallahi, ban yarda ba ita dai tazo daga baya amman ba ita bace auta dan na riga da na cire tutan auta har gobe nice ƴar gaban goshin inna da baba harma daku…nasan kunfi sona a kan kowa”
Yarinyar da aka kira da ƙanwata mai shekaru 5 a yanzu sai tsilli_tsilli take da ido tana bin dukkan mu da kallo musamman ma ni da bata san waye ba kuma taga naje na maƙale ma mahaifiyarta, an aifeta ne watanni 6 bayan guduwa na daga wuroɓokki lokacin da suke ganiyar cin azaban laifin da basu aikata ba, dukda yawancin aihuwan da innata takeyi a gida ne amman bata taɓa shan wahala da azaba irin na aihuwar Aisha ba wanda suke kira da indo,
“Ai dole ne mu soki so mai tsanani saudat, babu wanda ya shiga jarabawar rayuwa irinki, kinsha wahala sosai babu abinda zai kawo miki sauƙi a zuciya bayan soyayya shiyasa muke baki yanzu kuma zamu ci gaba da miki HAR ABADA”
Sassanyar murmushi nayi nace “ai kaima ka shiga jarrabawar ya aminu, kaman yanda na gudu saboda tsoro kaima haka ka gudu saboda tsoro, kaima hankali ya tashi ba’a san inda kaje kuma a cikin wani hali kake ba,…..mundai gode ma Allah tunda ka dawo lafiya lau”
“Nifa namiji ne kuma koda a lokacin na mallaki hankalin kaina, da na tafi ban buƙaci tallafin kowa dan yin rayuwa ba nayi amfani da ƙarfina na nemi halaliya na gina kaina dashi har nayi aure nake kula da iyalina amman kefa? Ba don Allah ya jefa ki a hannu na gari ba inada tabbacin rayuwar ki lalacewa zaiyi”
Tashi nayi na zauna kana na miƙa ma ƙanwata Aisha hannu na duka biyu ina gyaɗa mata kai alamun tazo gareni, bata yi ƙasa a guiwa ba ta ƙaraso da hanzarin ta na ɗaga sannan na ɗaura ta a saman cinyana a kan gadon,
“Baba!…nayi maka alƙawari da kai da inna rayuwar indo ba zai taɓa zama irin tawa ba, idan Allah ya yarda ba zata san meye wahala ba bazata zubar da hawaye mara daliliba matuƙar ina raye, zan jajirce nayi aiki tuƙuru don na zama wata watan watarana don nima na kula da family na nayi musu gata na mantar damu wahalar baya insha Allah, ina sonki Aisha zan inganta rayuwar ki da ikon rabbi”
******
Motar sulaiman na shigowa nashi ya biyo bayan shi zuwa cikin gidan da ɗan iskan gudu, ya riga ya ganshi amman bai gwada damuwa ba dan yasan tabbas za’ayi hakan, shiyasa driver na parking ya buɗe marfin motar shi da kanshi ya fita,
Ko parking mai kyau zayyad baiyi ba ya ɓalle marfin motar ya fito sannan ya nufo sa gadan_gadan cikin sauri yasha gaban shi, saidai suna haɗa idanu yaga yayi mishi mugun kwarjinin da ya saka rabin fushin shi yabi iska,
“Wa kake nima ɗan yaro? Ko yau anyi tunani ne aka zo gaida ni har cikin gida?” Ya faɗa cilin salon rainin wayo,
Sulaiman always look scary amman dukda haka saida yayi ƙoƙarin tattaro sauran kuzarin shi cikin kaushin murya yace
“Tana ina ya sulaiman? Ina ka kaitaa??”.
“Ita wa??….oh Saudat wai?” Sunkuyowa daidai kunnen shi yayi kaman wanda bayison wani yaji abinda zai faɗa ya raɗa mishi “na kaita can da nisa wurinda za’a raba ta da kai tayi maka nisa na har abada, ka saka ma ranka daga yanzu ka fara sallamar boɗɗi daga cikin rayuwar ka”
Sai kuma ya ɗago yana murmushin da ya bayyana fararan haƙwaransa yace “bari na tafi wurin ɗayan iyalinan kada na barta tana jira kasan abinka da wanda ya ajiye ko yaushe dakon sa akeyi ta ko wani siga ana tarairaya shi”
Da faɗan haka ya juya ya shige gida ya bar zayyad daskare a wurin kaman an shuka dusa,
A parlor ya tarar da sadiya taci kwalliya na kece raini cikin shadda sea green da yasha paralysed paintwork har ƙasa saidai yanzu babu tarkacen jewelries tayi kyau fuskarta babu wani kwalliyan azo a gani tana kishingiɗe a kan kujera da glass ɗin juice da bowl ɗin cookies tana ci tana kallo hankalinta a kwance,
Tunda ta amsa sallaman shi taci gaba da hidiman gabanta har ya wuce yaga itqma bai kamata ya barta haka ba sai ya dawo parlorn ya zauna a kujerqr dake gefen nata kana ya cire hulan kanshi ya ajiye ya umarci maid ɗinsu ta kawo mishi ruwa,
“Halima” bata amsa ba ta juyo tana kallon shi saida taga bayi da niyyan sake cewa komai ne tace “na’am”
Ƙaramin murmushi yayi yace “daman so nakeyi nai miki ɗan ƙaramin albishir, alƙawarin da nayi miki na kuɗaɗen da zan baki idan na samu cikar vurina ya kusa cikawa saboda yanzu haka na samu kusanci da iyayen Saudat suna cikin garin yola kuma ba zasu je ko ina ba har sai sun bani aurenta insha Allah………..🤦🏻♀️2
Love You my fans🥰
*team SSFOREVER21*😅
ba dai ni na faɗa ba sis muneerah ce 🏃🏽♀️🏃🏽♀️🏃🏽♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
41🧝🏻♀️
Bai ankara ba sai ganin hawaye yayi zirr a idanunta abin har yaso bashi mamaki dukda yasan za’a rina, gimtse dariyar shi yayi ya ɗan karkace wuya yana kallon yanda ta haɗa kai da guiwa tana matsar ƙolla yace
“Haba baby sady, keda nayi miki albishir ina tsammanin naga murnan ki kuma mai ya kawo kuka? Ko na ɓata miki rai ba tare da sani na bane?”
Wani ƙululun baƙin ciki ne taji ya tsaya mata a rai, koda asiri tayi ma Sulaiman yazo ya karye iyakacin wulaƙancin da zai mata kenan amman tun kafin ya ƙaro auren ya fara cin mutucinta ina ga idan yarinyar ta shigo gidan?
“Yi shiru mana sady baby….ni ba niyya ta na saka ki kuka ba….please ki share hawayen ki”
Banza tayi mai taci gaba da kukanta ƙofar da zai sadaka dq kitchen daga ɗakin yaje ya rufe kada ta jawo masa abin kunya ƴan aikinta su jiwo kukanta ya dawo wurin da take zaune yana ƙoƙarin ɗaga ta tare da bata haƙuri,
“Ka sake ni sulaiman!! Ta faɗa a tsawace sai kuma muryarta yayi can ƙasa a raunane take kallon cikin idanun shi da nata wanda ya sauya kala zuwa jaa, a hankali ta zare ɗankwalin kanta ta jefa shi a tsakar ɗakin kana ta saka bayan hannunta ta goge fuskar ta da maroon janbakinta ya jawu har kan kumatun ta lokaci ɗaya kamanninta ya canza ta fito kaman wata partial mahaukaciya saidai har yanzu ko gizau baiyi ba yana duƙe a wurin ya zuba mata na mujiya,
“Shikkenan ko hankalin ka ya kwanta?….. A haka kake son ganina ko sulaiman? na dawo kamar mahaukaciya saboda damuwa ko? Nifa matarka ce! Uwar ƴaƴanka ba wata maƙiyiyarka ba I’m not your enemy my love… Me yasa azabtar dani ya zamo maka hanyar samun nishaɗi, tunda ka fara nimqn aure wallahi na rasa nutsuwa ta, harfa wani rama nayi baka lura ba?” Ta ƙarasa tana fitar da nishi,
Ji yayi jikinsa yayi sanyi dan ya sani ta wani ɓangaren bai kyauta mata ba, Yana son sadiya har a yanzu saidai kawai irin zaman da sukayi na rashin tattali da damuwa da juna ne ya jawo ma soyayyar naƙasu, a hankali ya ɗaura lips ɗinshi saman nata da nufin tsayar da kukan nata tayi saurin kawar da kanta tana hararar shi,
“I’m useful only when it comes to having pleasure….a lokacin kawai nake da muhimmanci a gareka amman idan girmawawa tausayawa da kuma sauran jindaɗin rayuwar aure Saudat keda su, why?”
fitar numfashinsa kaɗai ya sanya nutsuwa a zuciyan ta dukda kuwa har yanzu tana cikin tashin hankali, Bai saurareta ba saida ya tabbatar ya gama kashe mata jiki luƙus ya sanya mata kasala
“Ban fifita sashe ɗaya akan ɗaya sashen ba saidai kowa ina bashi abinda yake so ne, bani keda laifin abinda ke faruwa ba halima”
“To wayene??!!” Ta tambaya da ƙarfi lokacin da ya kusa ƙulewa ciki, ɗaga kafaɗan shi kawai yayi alamun oho ba tare da ya juyo ba yayi tafiyan shi bata san lokacin da ta sulale a ƙasa ba tahau birgima tana kuka da ihu cikin tafasan zuciya,
“Wallahi saudat ta shigo gidan nan sai na kasheta kaji na rantse sulaiman gwanda ka rufa ma kanka asiri kada kayi biyu babu….
******
“Ko wani dare daku nake kwanciya na sake farkawa daku a cikin raina, ina cikin ni’imar rayuwa amman kullum hankalina bayi kwaciya idan na tuna halin da na barku a ciki an zalincemu ya aminu kuma wallahi ba zamu yafe ba sai mun ɗauki fansar azabtarwan da akayi mana mu da iyayen mu”
STORY CONTINUES BELOW

Girgiza kai jaɗe yayi cikin rashin gamsuwa yace “Kada ma kayi baba yaji wannan jancen boɗɗi, kasan bazai yarda ba, kayi haƙuri mana a kanku aka fara laifi ne ko kun manta harta annabin mu (s.a.w) saida tasha wahala a hannun kafirai amman yashe jata rama ne?…… To ka gani irin abinda baba kullum take faɗa mana kenan idan an zalincemu muyi haƙuri kada mu rama da zalinci, shannan rama alkhairi ga ma hyarri ai ba illa ne ba!!
Yarima ta riga da ta mutu mai ya rage kuma? Yanju haka mai gari da ita da babu ita duk ɗaya tayi muguntan ya dawo kanta saboda shon mulki ƙanin Yarima ya sare shi a ƙahwa da adda mai tsatsa yanju ƙahwar ya ruɓe ance shai anje ashibiti an yanke kuma bashu da ƙuɗin biya, ko hakan bai ishe shu ishaya ba?”
Shiru nayi ina sauron ikon Allah, ƙadiran ala man yasha’u Allah wanda bayi zalinci kuma bayi barin azzalumai, wani mararin zuwa wuroɓokki naji ya taso min, saboda suga yanda Allah yayi ikonshi mutanen da suka so suga sun muzanta sun wulaƙanta a duniya zuri’ar da suka so suga sun watse! Allah ya dawo dasu ya haɗe kawukansu sannan ya sanya musu ɗaukaka,
Cus i believe duk ƙauyen wuroɓokki a yanzu babu wanda ta fini ilimi both boko da addini gashi wayewar da suke mafarkin samun shi basu samu ba ni na samu, bama irin wayewar da suke buri baƙauyen wayewa aje birni a sayi takalman rubber a saka oversized glasses da wando fela ana yawo da Radio ba😅 irin wayewar da ko a gaban ƴan birni ni wayayya ce, domin nasan kaina na san addini na nasan environment ɗin da nake rayuwa,
Wayana da ya ɗauki ruri ne ya katse min tunani nayi saurin ɗagawa ina dubawa, sunan da na gani saman screen ɗinne ya saka ni waigawa na duba ko attention ɗin mutanen wurin yana kaina kafin nayi zuɓur na miƙe ina kallon wall clock, kira na 4 kenan da zayyad yayi Min cikin daren nan kuma duk lokacin da nayi picking ba wani abu mai muhimmanci yake faɗa ba wani sa’in ma sai ya kama kame_kame,
I can sense tension in his breath, nasan yana cikin damuwa amman nabi duk hanyar da zanbi don ya fqdamin yaƙi, bathroom na shiga dan wurin ne kaɗai babu kowa sannan nayi picking na ƙara a kunne na,
“Hello babes”
“Na’am hamma zayyad are You alright?”
“Me yasa kikayi min wannan tambayar?” Ya faɗa a bit annoyed,
“No!.. nothing kawai dai naji kaman kana da wata damuwa ne Please ka fada min ko menene kaji?…….kayi shiru hamma zayd I’m here for you and your problems ka faɗa min koda ba zan iya maka maganin shi ba ai zan taya ka da addu’a ko?”
Lumshe idanu yayi a hankali yana samun nutsuwa a duk lokacin da yaji na nuna damuwata gareshi hakan yana tabbatar mishi har yanzu ginin soyayyar shi yana zaune daram a zuciyata bai rushe ba, inajin sautin murmushin shi murya can ƙasa yace
“Nothing baby, i just miss you… you are so special to me kin gama tafiyar da xuciyata da bani samun nutsuwa idan baki kusa dani Please let’s get married soon wallahi inason aure….amman fa idan tare dake ne”
Murmushi nayi farr na kaɗa eyeballs ɗina kaman yana gabana sai kuma na kare fuskana da tafin hannu na a kunyace, inajin kaina yana fashewa,
“Ya zayd yanzu dai kayi haƙuri abubuwa su lafa mama ta gama samun lafiya duk abinda kake so sai ayi”
“Ummm ko?! To shikkenan amman inda so samu ne a kwanan nan nake so ayi komai ta ƙare amman bari dai na haƙura kada ace nayi azarɓaɓi”
Ɗan turo baki nayi a shagwaɓe nace “hamma zayd banfa ƙarashe school ba faaahh”
“Wannan ba matsala bace saudaty, ke kinsan bqni cikin jerin mutanen da zasu hana ki karatu, kizo kiyi abinki a gidana kuma ma kinga kya ƙara da babban makarantar ABU”
“Wani A.B.U ɗin na Zariya?” Na tambaya cike da murna mafarkayya na suna daff da cika,
“Noo! Wannan tukunna dai, ABU Aure Bautar Ubangiji de…..hhhh wait kafin ki faro min mita inason zuwa na maida ki asibiti da kaina na samu sauraron mitar ki a marmarce gani gaki”
“To ƙorafi bai amsu ba, bani kaɗai zan tafi ba kuma a cikin daren nan bansan da wani suna zan gabatar dakai a wurin su ba, ka bari kawai gobe da safe sai kazo”
“An gama your highness, Allah ya kaimu goben da rai da lafiya”
******
“Again?!” Tsaki kawai yaja yana kallon ƙofar ɗakin sadiya a zuciye ya fita ya nufi mota daga nan ya wuce gidan su,
Tun daga parking lot ya lura babu ɗaya daga cikin motocin da zayyad yake fita dasu, yau asabar babu aiki ina yaje? Ya tambayi kansa dan har yanzu bayi da sukunin rashin kasancewar ɗan ƙanin shi a tare dashi tunda yasan ba isasshen lafiya gareshi ba, share zancen yayi ya shige wurin mahaifiyarshi don su gaisa ya shaida mata halin da ake ciki da iyayen saudat,
*****
“Ki shiga gaba”
Maƙe kafaɗa nayi nace ” A’a gaskiya kai ka fara shiga su fara ganinka don kaine baƙon su bani ba”
“Baƙo ya taɓa shiga wuri ba tare da ɗan jagora bane? Please kada mu tsaya musu su fito su ganmu ki fara shiga”
“Ok” na amsa tare da tura ƙofar da sallama na shiga, ya biyo ni a baya, takawa nayi na ɗale gadon mahaifiyata na shige jikinta har wayau kuwa kunya takeji ina leƙen zayyad daga wurin da nake kwance saman cinyarta,
Sallama yayi yana gyara zaman hulanshi bawan Allan fah mai kyau ne ko wani kalan kaya yana karɓan shi sosai, saidai daga shiganshi suna haɗa ido da baba ko taku ɗaya bai ƙara ba ya zube a ƙasa warwas,
“Subhanah lallai akwai matsala” shine abinda baba ya faɗa amman banga alamun danuwa a fuskarshi ba,
Iya tashin hankali ban taɓa shiga irin wanda yakai wannan ba akanshi don tunani na ɗaya kada Allah ya kawo dalilin da zai saka baba ya hana ni auren zayyad don ina ganin zan iya mutuwa idan banzamo mallakin shi ba.
Sakawa baba yayi su jaɗe suka tattare shi suka shiga dashi ɗakin da yake gefen nasu sannan yabi bayan su………..🤦🏻♀️
*Eyyy school da wahala fah!😥 Idan na fita from dusk till dawn, idan bakuga nayi posting ba ayi min uzuri saidai zanyi ƙoƙarin cika alƙawari masu cigiya a ƙara haƙuri ummu Najma yanzu sai a slowww*1
(¯’*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Ita ɗin masoyiyar masu masoya ce🥰 ita ɗin ɗaya ce cikin zaɓaɓɓu😍 ita ɗin tana zama abin alfahari ne ga wa’inda suka santa da wa’inda ke tare da ita🤩 ita ɗin ZAINAB BAWA ce marubuciyar BIBIYATA AKEYI, AUREN FARI and more💓 wannan shafin sadaukarwa ce a gareki😊 ina miki son so fisabilillahi💝*
42🧝🏻♀️
Gyaɗa kai baba yayi bayan yaji bayanin Sulaiman wanda kallo ɗaya zakayi mishi ka fuskanci tsantsar damuwa da fargaba da yake ciki, daman yasan wannan ranan tana zuwa….ko ba daɗe ko ba jima yasan rana irin wannan zaizo da asirin da yayi ƙoƙarin birnewa tsawon shekaru masu tarin yawa dai buɗu a idon duniya, saidai alhamdulillah tunda ya riga da ya cika alƙawarin da ya ɗauka ma zayyad da familyn shi gaba ɗaya kuma martabar su ya riga da ya ɗagu zuwa matakin da har abada ba zai faɗo ba,+
Numfashi ya furzar a hankali yace “toh shulaimanu shidai lafiya Allah ke badawa shaidai ɗan adam yayi nashi ƙoƙarin wajen shamo magani, yanda aljanu shuka rabu kala_kala cikin jinsuna kaman ƴan adam haka hanyoyin kamuwa dashu da kuma rabuwa dashu shuka rabu kashi_kashi, yanzu dai ba zan baka tabbaci akan Zaidu zai warke ba amman zamuyi iya ƙoƙarin mu da ikon Allah, shaidai zansho shai mun koma wuroɓokki don al’amarin babba ne”
Jimm sulaiman yayi yana tunani, indai hakan zata faru tofa lallai shi zai tsara komai yanda za’a bawa su malam ardo da zayyad kariya yanda mutanen garin ba zasu samu wani dama na cutar dasu ba sannan ya kasance tare dasu don ganin komai ya tafi dai_dai,
Shi da yaso fita harƙan shi gaba ɗaya ya watsar da sha’anin shi saboda yaudaran shi da yayi! Me yasa ƙaddara zatayi mishi haka? Har ƙoƙon ranshi yake ƙaunar Zayyad ba zai taɓa barinshi da ciwo ba bayan sun sami hanyar maganin shi,2
_shikkenan zaiyi masa saboda Allah idan yaga dama yaci gaba da cutar dashi Allah zaiyi mishi maganin sa_
Numfasawa sulaiman yayi yace “shikkenan baba insha Allah za’ayi yanda kace, daga zaran inna ta samu lafiya zamu je ƙauyen dukda dai kaman yanda na faɗa daga farko banso komawan ku can ba naso a sama muku matsuguni a nan ku zauna cikin kwanciyar hankali saidai babu matsala a hakanma, insha Allah ni nayi muku alƙawarin babu wanda ya isa ya sake cutar daku zaku koma gida kuci gaba da rayuwan ku kaman kowa”
Cike da jin daɗi malam arɗo ya gyada kai yana murmushi tare da jinjina karamci da dattakon wannan yaro,
“Allah yasha ka gama da duniya lahiya shulaimanu, banshan dame jan biya ka ba, ka inganta rayuwar shaidatu ba tare da kuna da wata dangantaka ba gashi muma kana ta hidima damu, Allah ya shaka maka da alkhairi, Ubangiji Allah ya kareka daga dukkan sharri da mai sharri,
Da “ameen” ya amsa daɗin addu’an malam arɗo yana ratsa shi, zama yayi kaɗan suka tattauna akan yanda tafiyar zata kasance sannan suka koma ɗakin da inna ke kwance yayi musu sallama kan zai wuce, yana jin kaman ya ɗauki saudat ya tafi da ita amman ba zai iya ba saboda idanun iyayenta,2
Shi karankanshi yasan yayi kewarta sosai gashi kwana biyu yana ganinta a cikin yanayin da yake so dukda a halin yanzu tana cikin tashin hankali amma burinshi bai wuce kullum yaga murmushi a saman fuskarta ba kuma zaifi so ace idan tana tare dashi take yi,
STORY CONTINUES BELOW

Kawar da tunanin yayi a ranshi ya tada motar ya tafi saida ya isa gida ya umarci drivern zayyad ɗin yaje ya ɗauko shi sannan ya wuce wurin dady ya faɗa masa abinda ya faru da safen ya kuma sanar dashi hukuncin da suka akan lafiyqr zayyad ɗin,
Dady ya gamsu kuma yaji daɗin hakan baiyi wani ƙorafi akan zuwansu wuroɓokki ba sai fatan samun nasara, daga nan ko ciki bai shiga ba ya wuce gida don yasan da zaran aunty amarya taji wannan zancen toh babu abinda zai tafi dai_dai musamman idan tasan sulaiman gaban kanshi yayi ba tare da ya shawarce kowa ba, don maganin da sukeyi kwanaki ma ita take kawo musu cikas idan akace su koma rana kaza sai ta saka zayyad yaƙi zuwa ko kuma taƙi bashi maganin da aka kawo, a cewarta wahala kawai suke ƙara bashi da maganin,
Da yammacin ranan dady ya tattari kan iyalanshi gaba ɗaya suka tafi asibiti duba jikin inna harda wa’inda basu so zuwa ba because he consider me as part of his family, saida suka je ne yayi nadaman zuwa da Nana don Sulthana ta fita wayo ita ta kama kanta kaɗan, haka ta zauna ta dinga yaɓa ma iyayena magana a fakaice abin saida ya kusan zama faɗa tsakanin mu domin kalaman da take jifan su dashi yayi tsauri,
Dukda nasha rarrashi a wurin su aunty da su hajiya amman saida nayi kukan takaici bayan sun tafi, nidai Allah yamin katangar ƙarfe tsakanina da yarinyar nan banma san yaya zamu ƙare ba idan na shiga gidansu a matsayin matar Zayyad,
******
Ba zato ba tsammani ya jawota baya ya dungurata a tsakiyar ɗaki sannan ya rufe ƙofar ɗakin, yaushe ya shigo ciki bata sani ba? Tunaninta ne ya katse lokacin da sulaiman ya ɗaga bulala ya shargwaɗa mata a gadon baya ta wani boƙare tare da saka ihu, da gudu ta miƙe ta nufi ƙofa amman a rufe ya garƙame da key,
Ihu nana take kaman wanda ake zare ma rai tana buga ƙofar ɗakin wanda yasa mutane fitowa don ganin abinda ke faruwa, taku ɗaya sulaiman yayi ya sake jawota ya shauɗa mata wani a kan cinya,
bata san laifin me tayi mishi ba, ita dai tasan bayi duka amman bata san me ta masa yake son kasheta a halin yanzu ba,
Taƙarƙarewa yayi ya sake zuba mata wani a take numfashinta ya tsaya cakk sautin kukanta ya daina tashi sai gurnani,
Shi da yayi dukan ma sai haki yake yi ya gwada ta da bulalan hannun shi yana jifanta da mugun kallo yace,
“Na daɗe ina taraki Nana Hafsah yanzu kin fara ƙure ni, wallahi kinji na rantse miki indai ba zaki nutsu kiyi hankali ba zaki sha baƙar wahala a hannu na shashasha mai banzan ɗabi’a, ziciyar ki baƙiƙƙirin kamar fuskar ki shiyasa har yanzu kika rasa mashinshini baki nufin kowa da alkhairi, Allah idan baki gyara ba haɗuwar mu na gaba ba zata kai wannan kyau ba”
Ita dai ta saurare shi sama_sama amman bata iya fassara kalamansa ga numfashinta dake barazanar barin jikinta tana kuka mai haɗe da gurnani, sai yanzu ya kula buga ƙofar da hajiya takeyi tana kiran sunan sa, hankalin sa kwance ya ƙarasa ya buɗe ƙofar ya fita,
“Me yake damunka ne sulaiman wannan wani irin zalunci ne?”
Kallon yanda su Ruma sukayi kanta suna kuka yayi yaja tsaki saikace wanda ya kasheta, Junior kuwa abin yayi mishi sugar don a gaban idanunshi taci mutuncin iyayen girlfriend ɗinshi,
“Hajiya she is just putting a drama ni babu abinda nayi mata bayan barazana, razana ta kaɗan kawai nayi” daga faɗan haka yayi gaba ya bar hajiya da baki sake cike da al’ajabi da kunnuwanta taji sauƙan bulalu amman yace mata wai _barazana_
Bayan ya koma gida bai samu nutsuwa ba saida ya kirani a waya ya ƙara bani hakuri gashi sadiya ta shiga partial yaji don ta zama kaman babu itane cikin gidan harta yaranta ta daina kula su ta daina musu komai wai tana so sulaiman ya gano amfaninta ne yasan tana da muhimmanci a rayuwan dukkan su shi kuma hakan dq takeyi yana kara saka mishi matsuwa na ganin ya auro Saudat tazo ta ɗauki ragamar gidan baki ɗaya sai yaga ta allon ta,
STORY CONTINUES BELOW

Munsha hira na kusan rabin hour dukda taɗinmun ya ta’allaƙa ne akan shirin tafiyan mu wuroɓokki amman hakan ya sama mishi nutsuwa sosai, while a nawa fannin i can tell that sulaiman is becoming soft…so tender indeed da har yasa tsoro da kuma fargaban shi da nakeji a raina ya ragu sosai,
8 days later
7:30am
Annashuwa, nutsuwa, farinciki, ga kuma iska mai daɗi dake kaɗawa a hankali cikin albakataccen daji mai kawace da bishiyoyi daban_daban da tsuntsaye masu shawagi suna daɗaɗa kunnuwan bil adama da sautin muryoyin su masu daɗi,
Zaune nake a passenger seat na rungume kanwata indo a ƙirjina idanu na a lumshe babban yaya zaune a gefe na hankalin shi a kan titi yana driving, mahaifiyata da mahaifina kuma suna back seat, ya aminu, jaɗe, khamis, da zayyad suna motar dake gabanmu da motar police suma guda daya a gaban su motar bayanmu kuma ya Nafi’u ne ke driving da matan jaɗe da na ya aminu sai kuma ƴaƴansu, suma da na police guda ɗaya a bayan su making 5 cars in total,
Na daɗe ina burin irin wannan dawowar, na daɗe ina mafarkin ɗaukar fansa gashi tun kafin muzo babban yaya ya bani wuƙa da nama ni kuma nayi alƙawarin ba zan bar wuroɓokki ba sai na tabbar an kama mai gari wanda ya kasace ƙanin tsohon mijina yarima tacaccen ɗan shaye_shaye aje ayi ta gana mishi azaba a rehabilitation center shima mahaifinshi yaji yanda uba yake ji idan an raba shi da jininshi, kaiii harda ƴan uwan shi da abokan shi dan saka a kama don na rama sharrin da furere tayi wa ya aminu saboda su,
A hankali motocin suka tsaya bakunan mu suna godiya ma Allah sannan baba ya fito, da mamakinsa babu gidanmu a wurin…..tabbas nan ne inda yake amman babu shi a wurin sai wani….wani mai ginin zamani wanda ƙauyen karankaf babu kamarsa,
Juyowa malam ardo yayi kaman zaiyi kuka abin nasu ya fara kaishi bango, koda ace fili ba nashi bane amman ai gida nasi ne shi ya gina da guminsa bai kamata a rushe ba tare da izinin shi ba,
“Mu shiga ciki mana baba! Mai muke jira?” Sulaiman ya tambaya,
A raunane ya juyo yana kallon mu murya can ƙasa yace
“Bamu da wurin da zamu shiga, sun riga sun fitar dani daga garin bani da matsuguni a cikinta a halin yanzu”
“Kaman yaya baka da matsuguni bayan ga gidanka nan? Duk duniya akwai wanda ya isa ya fitar da kai daga cikinta ne bayan ikon Allah?”
Da mamaki malam arɗo ya tsaya yana kallon Sulaiman kanshi ya kasa fassara mishi abinda yake nufi, ganin mutane sun fara cika a ƙofar gidan ciki harda matan aure suna yafo mayafinsu suzo ganin kalan motoci da mutanen da akace saudat tazo dasu,
Muna zuwa shiga zayyad ya yanki jiki ya faɗi amman hakan bai wani dame mu ba saidai a yanzu hankalin Sulaiman ya fara tashi haka suka haɗu suka kinkime shi zuwa ciki,
Saida muka shiga ne akayi ma malam arɗo bayani dalla_dalla sulaiman ne ya saka aka gyara musu gidan, shidai baisan mai zaiyi ma wannan ɗan albarkan ba, yana ganin koda goyon shi yayi ba zai isa ba yayi masa alkhairori masu yawa wanda bayi da abinda zai biya shi dashi saidai yayi ta mishi addu’a, ai kuwa ya shata daga bakin kowa a gidan ni kuwa kuka nake kaman anyi mini mutuwa wani ƙima da daraja na sulaiman na daɗuwa a cikin rayina, ya gama min komai a rayuwa da ace ina da abinda zan biya shi dashi definitely zan biya shi,
Hutawa mukayi zuwa ƙarfe 10 sannan muka ɗau haraman ɗaura abinci ga komai da ake buƙata Sulaiman ya tanade shi ya jibge mana a store ɗin gidan, akace hannu da yawa maganin ….miiya cikin abinda bai wuce awanni biyu ba muka gama abincin mu kala guda biyu da wanda kowa zaici da kuma irin wanda ni da su Sulaiman muka saba dashi na yan birni har zuwa lokacin Zayyad na barci bai farka ba, daga nan nayi wanka nayi sallah aka ci abinci na ɗan zauna ƙarin hutu zuwa sallan la’asar saboda nafison sai rana tayi sanyi kafin na fita yanda zan karaɗa ko ina nayi son raina tunda a yanzu ina da goyon baya,
3:47pm
Wani motar ya ƙaraso ƙofar gidan dai_dai inda sauran motocin suke shima yayi parking, da gudu na ƙaraso na ruƙunƙume ta inajin farinciki mara misaltuwa bayan sintirin da na dinga yi a gidan su Ruma yau itama gashi tazo namu gidan kuma ina alfahari da hakan,
Tare suke da Yusrah da mahaifiyar khamis da mahaifiyar ita yusran harda Nasreen amman duk cikin su babu wanda yazo da yara dukda haka dai munyi full house,
Har zamu wuce muryan Fa’iza ya jawo attention ɗinmu, ta fito ta ɗaya ƙofar bayan tana tsaye dare da murfin motan a yatsine take binmu da kallo,
“Hey bush head!! Baku ganin mutane ne da tsiraran kafafunku kaman masilla da ba zaku kulani ba? Dukda dai ke ba laifin ki bane” ta faɗa tana gwada ni “kina fama da makanta ba zanga laifin ki ba idan baki gani”
_wato nana ne kawai bata zo ba! Itace kawai bata taya ni murnan dawowa na mahaifata, toh Allah ya huci zuciyarta_
Cikin farinciki muka ƙarasa muka rungumeta dukda sai ihu take wai zamu saka mata bola kasancewar fararen kaya ne a jikinta muka jasu ciki, gaisawa kaɗan aka zauna sake yi sulaiman yayi shirin tafiya zai kuma bi ya haɗa kan ƴan ƙwayan da zai kaisu rehab su tafi tare,
Unknown to us har motan police ya tattari na tafiya sun riga sun tafi su tsohon mai gari ne ake ta faman artabo dashi ya hana a ɗauki ƙanin yarima sun ɓoye shi a wani wurin da ba’a ma san ina bane,
_wannan tsoho mai ran dalma har yanzu yana raye?_🤦🏻♀️
*Here i comes again, na zama maman excuse gashi bani iya replying comments😣 like seriously yanzu na dawo sai a hankali a ci gaba da hakuri dani a haka dan Allah ana manage😁 saidai duk da haka ina bin sharhin ku ɗaya bayan ɗaya ina karantawa kuma yana sani farinciki matuƙa na gode na gode💃🥰*
*Ummu excuse ce😂😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Alhamdulillah, bayan tsawon jira gashi na sake dawowa a karo na biyu😃 ina bawa masu karatu haqurin rashin jina kwana biyu da sukayi sakamakon ƙaddara data faɗo min har yayi sanadin rasa sim card ɗina sai kuma na ɗan jinkirta dawowa saboda azumin Ramadan. Amman yanzu zamu kammala littafin nan idan Allah yaso*+
43🧝🏻♀️
Buge hannun ta nayi ina ƙara sautin kuka na, ta yaya za’a dake ni a hana ni kuka? Ni lokacin da yarima yake cin ubana a gidan ba suna gani suke kyalewa ba? Ko a cikin su akwai wanda ta taɓa yunqurin dakatar dashi? Saidai idan ya gama cin zalina goggo ta rarrashe ni amman duk yawansun nan taron yuyuyu ne babu wanda ya taɓa wani abun azo a gani akan komai dake faruwa a cikin gidan sai yanzu ne da suka ga babu sarki sai Allah wai zasu rusuna su fara roqona gafara?
To ba za’a yi haqurin ba!!
Sake rarrafowa yadikon yarima tayi tana kuka kaman anyi ma kafiri mutuwa, ta ƙara danƙo kafana daga inda nake zaune tace
“Dan girman Allah boɗɗi kayi mana aikin gafara ka roƙi kaɗɗon nan ta rabu mana da mai gari ƙarami don ya Rashulullahi”
Fisge ƙafana nayi daga riƙon ta na ɗaura daya kan ɗaya ina kuka tana kuka sauran mutan gidan ma suna tsaye suna kallon mu suna taryo duk abubuwan da ya faru dani a baya cikin kwaƙwalen su,
Kwanakin da nayi su mafiya wahala a cikin rayuwana ana treating ɗina kaman wata dabban jeji da bata da uban gida,
Babu wanda ya damu da kuka na, babu wanda ya damu da cina ko shana, azaban da yarima ya bani ko a gidan kaso ba za’ayi min shi ba, he and his family abuses me both physically and mentally.
Zumɓur na miƙe kaman wanda aka razana sannan na dube su dukan su nace
“Yanzu dukkan ku kunyi ma kanku adalci? Bayan cusguna min da kukayi kuka maida ni abu marar ƴanci a baya, yanzu ma kuna son sake rabani da wani ɓari na farin cikin rayuwata?.
Kun manta lokacin da ake hankaɗo ni daga wancan ɗakin..” na faɗa ina nuna dakin da ya kasance nawa da yarima a da.
“… lokacin da ake duka na da sanda kaman jaka, haka zan wuni a kwance a ƙofar ɗakin can cikin jini bayan goggo dakan tallafe ni da abinci ko kallon banza babu wanda wani ko wata daga cikin ku yake jifa na dashi,
Dan Allah bakuji kunyar sake kallon cikin idanuna ba!!! Bakuji kunyar roƙona alfarma ba!!” Na ƙarasa cikin daga murya.
Shiru ne ya ratsa wurin babu wanda yake da bakin ce min komai don fiye ma da abin da na faɗa ya faru, Ruma na ganin ba zata iya jurewa ba ta fice daga gidan gaba ɗaya tana kuka don ita a zaton ta abinda ya faru dani be kai haka ba,
fa’iza ne ta karaso kusa da inda nake zaune ta daura hannun ta saman kafada na tana lallashi na, cikin tausayawa ta riko hannu na ta dunkule cikin nata tace
“Ba halinki bane Saudat ke ɗin mai hakuri ce mai yafiya idan kina tuna baya rayuwar ki ta gaba ba zata yi inganci ba, learn to forgive… please..”
“Aunty fa’iza ganin dangin yarima sun wulakanta kaman yanda suka wulakanta nawa dangin shine kaɗai farinciki na, burina kenan guda ɗaya naga na kawo su ƙasa”
“Amman ba haka kuka yi da yaa Zayyad ba, ba wannan halin da mugun nufin kika gwada mishi ba, idan har kin ɗauke mu da daraja ki bar abinda ya wuce ya wuce, kema zaki samu Allah ya yafe miki laifukan da kikayi na rayuwan ki harma da wanda baki sani ba”
STORY CONTINUES BELOW

Hmm lallai, Fa’iza datayi ɗamara da sunan zata rakoni yin faɗa itace kuma yanzu ta juye take bani haƙuri, ko dayake nima rayuwa ta bani second chance, Ya kamata nima nayi ƙoƙarin bawa mutanen dake cikin rayuwana dama ta biyu
Miƙewa nayi na karkaɗe jiki na sannan na saka bayan hannuna na share hawayen idona, a nutse nake takawa na ƙarasa gaban goggo dake zaune kanta ƙasa, kaman ba zanyi maganana ba na tsaya ina ƙare mata kallo kafin cann nace
“Goggo lami”
Ɗagowa tayi ta amsa da “na’am saudatu”
Na gode da kulawan da kika nuna min lokacin da nake ƙarƙashin ki, kin sanyanta azaban da ɗanki da jikan ki suke gwadawa a kaina, na gode sosai, saidai ba zanyi miki alqawarin ƙanin yarima zai dawo kwanan nan ba amman nayi miki alqawarin insha Allah zan shiga gaba wajen samawa mai gari lafiyan kafarshi duk abinda ake buƙata zamuyi mishi insha Allah”
Zanin da ta yafa ta rufe kanta dashi ta jawo ta rufe idanunta a kunyace sannan ta saka kuka,
Haka mukayi shiru muna sauraron yanda take rero su cike da nadama, hawaye suna zarya a idanun ta, kafin da ƙyar aka saku aka lallasheta ta bar kukan ta ɗago tana fuskantana cikin kasashshiyar murya tace
“Duk abubuwan da suka faru sakacina ne saudatu saboda kowani mutum dake rayuwa a cikin gidan nan a ƙarƙashi na yake, da naso da na hana cuta da zalunci a tsakanin su, amman na zuba idanu nayi oho da duk abinda yake faruwa har abubuwa suka zo suka fi ƙarfin ikona.
da nasan haka zata faru da tun lokacin baya nayi wani abu a kai, da nasan haka zaki dawo da tun baya ban barki kin wulakanta ba”
Kasalallen murmushi na sake jin abinda zuciyata ke tsumaye, tuntuni abinda nake jiran su ambata kenan don na basu amsan da na tanada wanda ya dace dasu, amman sai yanzu ya samu fitowa.
“Daman shi ɗan adam duk yanda ka ganshi kada ka raina matsayin shi ka wulakanta shi don baka san me dai zama a gaba ba,
Tun kafin ku roƙe ni gafara na riga na yafe ma kowanne da ya zslince ni a cikin ku, don ba zan iya ci gaba da ajiye tsatsar ƙiyayya a cikin zuciyata ba,
Sai kuma idan Allah ya sake haɗamu a wani wurin, na barku lafiya”
da faɗan haka na ja hannun Fa’iza muka juya muka bar musu gidan tsitt har muka fice babu wanda ya sake koda tari.
**********
Har ƙofar gidan baba fadawan maigari suka rako mu, suna zuba fadanci kace mai garin ne da kanshi, basu bar wurin ba saida suka ga shigewan mu ciki sannan suka tashi daga wurin da suke zube a kasa sukayi gaba,
Wajajen magriba kowa ya watse suka koma cikin garin yola, sai lokacin na samu daman kiran Sulaiman na roke shi kan zancen cutar mai gari kuma bai musa min ba ya amince zai taimaka a nema mishi lafiya dukda kuwa yana sane da abubuwan da yai min, amman shi bai damu ba saboda Allah yake son taimakon shi kuma saboda soyayyar da yake min babu abinda zan roqa da ya shafi kuɗi a yanzu da bazai iya min shi ba,
Muna gamawa mukayi alwala nida indo, sannan na fito mana da darduma mukayi sallah a nan waje, na taya su inna da matar Jaɗe rabon abinci aka kaiwa kowa nashi ɗaki sai wanda ya rage na Zayyad ne na ɗauka a cikin akushi na nufi ɗakin da aka kwantar dashi,
Cikin nutsuwa na karasa gaban gadon da yake kwance yana barci making sure i make no noise na ajiye akushin a hankali sannan na gyara tsugunona na zuba mishi ido cikin hasken aci-balbal da ya wadaci fuskar sa ina jin gaba ɗaya tausayin sa ya kama ni,
“Ina sonshi, zuciyata tana sonshi sosai, kuma bansan meyasa take sonshi ba, Zayyad shine ɗaya ɓarin jiki na, shine zuciyata, ina ji a jikina kaman duk randa na rasa shi zan rasa numfashi na, b….”
Zancen zucin da nakeyi ne ya katse ganin yana juyin da ya kusa sanya shi mirginowa ƙasa zumɓul na miƙe da nufin tare shi kada ya faɗo amman na tsaya a hanya ganin ya bude idanun shi ya zuba su a kaina ina ta faman tsilli_tsilli da ido tare da sake min murmushin shi na koda yaushe,
STORY CONTINUES BELOW

“Babes!” Ya furta a hankali don har yanzu jikin shi is weak.
Tattaro kuzari na nayi na ƙaƙalo murmushi, na ɗan matsa baya daga gadon nashi sannan nace “sannu hamma zayd, yaya jikin naka”
Dariyan qarfin hali yayi yace “kema kinsan duk wani nau’i na cuta da nake dauke dashi idan ina tare dake ji nake kaman an ɗauke rabi..”
Murmushi kawai nayi na sunkuyar da kaina qasa ina wasa da zobensa dake hannu na, yaci gaba da cewa,
“I’m so happy that I’m staying at same place as you, daga komai yazo ƙarshe, i will be staying with you till forever, zan sanya ki farin ciki saboda kin cancanta Saudat.
Ina kuma daɗa baki haquri kan abinda ya faru dake lokacin baya when I was not there, sai ɗazu Rumaisa take faɗa min abinda ya faru and i was not happy…”
“Kawai kayi min alƙawarin ko me gobe zai zo dashi ba zaka rabu dani ba” nayi saurin katse shi ba tare da nasan zancen dake zuciyata ta fito fili ba,
Shiru yayi ya zuba min ido don bai gane inda zancen nawa ya dosa ba kana naci gaba da cewa
“Ko me zai faru nan gaba, ko wani irin jarabawa zamu fiskanta don Allah kada ka yada ni, an riga anyi ma zuciyata rauni mai girma, dan Allah kada ka barta ta tarwatse hamma zayd”
Tashi yayi ya zauna sannan ya riƙo hannu na na dama ya dunƙule a tsakanin nashi, abinda bai taɓa yi ba har saida naji hanjin cikina sun kaɗa idona a zare nake kallon shi, cikin gaskiya da gaskiya yace
“Koda rayuwata zan sadaukar saboda ke ko kuma don na kasance tare dake ba zan taɓa nadama ba.
Nayi miki alqawarin duk qaddarar da zata faɗo tsakanin mu tare zamu fiskance shi bazan taɓa yada ke ba”
“Allah yasa, kuma Allah ya baka lafiya” na faɗa cikin sanyin murya sannan na miƙe tare da zare hannu na daga cikin nashi a hankali na fice.
Ko babu komai yanzu inada nutsuwar ruhi da zuciya domin na aminta da duk abinda Zayyad ya faɗa min, ina dai fatan Allah yasa in samu farinciki mai ɗorewa a gidan aurena na biyu, shine kawai burina a yanzu.
*********
Kishingiɗe take a jikin shi Abulkhair na kwance saman nata jikin ta riƙe shi da hannu ɗaya ɗayan kuma tana latsa wayan ta fuskar ta ƙunshe da alamun damuwa,
Rage volume ɗin tv khamis yayi sannan ya ɗan ɗago yana leka fuskar yusrah ganin yanayin fuskarta yasa ya tambaye ta abinda ke faruwa,
“Jibi ya kamata Saudat ta koma school abban Jannat kuma kaga har yanzu bata dawo ba gashi akwai sauran shirye_ shiryen da bamu ƙarasa na tafiyan nata ba”
“Ah! Ba na faɗa miki tana hanya ba, munyi magana da boss Sulaiman yace zai tura mota a ɗauko ta”
A ɗan dame ta tashi ta zauna da kyau ta gyara zaman ɗanta a jikin ta, taɓe fuska tayi tace
“To dai gashi ka gani la’asar har ta kunno kai babu labarinta, kuma na kira wayanta yafi sau a ƙirga bata ɗauka ba”
“A gidan su take ba wani wuri ba fah” ya faɗa a bit annoyed saboda yanda yaga take marairaicewa “kuma ni banga wani shiri da ake ma makaranta da za’ace lallai sai saudat tana nan za’ayi shi ba, kawai ki siya mata abinda kike tunanin zata buƙata, that’s all”
Tsuke fuska tayi tana sauraron mitan shi, bai gama magana ba wayanta ya ɗau ruri, shiru yayi ya bata daman amsawa, ta ɗaga tare da murguɗa mishi baki cikin salo tana jifan shi da harara ta qasan idanu,
“Kaga ma ita take kira ba sai ka gama ƙare min tanadi ba”
Murmushi kawai yayi bai tanka ta ba ta saka wayan a kunnen ta tare da sallama
“Boɗɗi har yanzu baku kamo hanya ba?”
Shiru tayi tana sauraron abinda nake faɗa ta ɗaya layin kafin tace
“To shikkenan Allah ya kaimu goben, sai kin dawo” daga nan ta kashe wayan ta dangwala ma khamis Abulkhair a cinyar shi ta tashi ta shige ɗaki.
********
Al’amarin babban yaya ya fara ɗaure min kai kwana biyu, tun wani lokaci da mukayi magana dashi a kan Zayyad ya ɗauke min wuta, kwata_kwata yanzu na kasa gane gaban shi da bayan shi,
Bazan yi ƙarya ma kaina ba, na fahimci sabon dake tsakanina dashi ya fara saka mishi wani abu a zuciyar shi game dani wanda baisan dashi ba, kuma ba zan bar hakan yayi tasiri ba domin duk wani nau’i na alaƙa da ya wuce mutunci ya haramta tsakanina dashi Saboda ni ɗin daff nake da zama mata a wurin ƙanin shi, shiyasa tun yanzu nayi mishi hannunka mai sanda shi kuma ya ɗauki abun da zafi sosai.
Da safiyar yau, ina yanke ma indo farce ɗan aike ya shigo ya sanar ma baba da zuwan shi, banyi mamaki ba don nasan a ranar zan koma Yola saboda makaranta na, shiyasa nayi tunanin shi da kanshi ne zai tafi dani, amman suna gama tattauna abinda zasu tattauna yayi tafiyar sa ko ganin shi banyi da idanuna ba,
Bayan nan na kira shi yafi sau a ƙirga bayi ɗauka, gashi jikin Zayyad har yanzu da saura shiyasa bani son takura shi amman dukda haka saida nayi amfani da wayan shi na kira Sulaiman bai ɗauka ba, sai can da yamma liss aka sake shigowa sallama da baba, kafin ya fita ne yasa ɗan aiken ya tambaya waye ne akace wai baban su hamma Sulaiman ne,
Wani abu na faruwa ba tare da sanina ba, tabbas wasu abubuwa suna faruwa a kwana biyun nan ba tare da sani na ba amman bansan meye ba,
Haka nayi zaune ina jira har ya sallame su ya dawo lokacin ana shirin kiran magriba sannan ya shigo ya shaida mana abinda ya kawo su.
Kafin nan saida ya fara jifa na da tambayar da yayi matuƙar daure min kai cewa “ina son Sulaiman ne?”
Jin tambayar nayi yazo min wani iri, qwaqwalwata ta kasa tantance me ɗaya ya ƙunsa da kuma dalilin da yasa akayi min ita!
Ni kuma? Ta yaya zanso Sulaiman bayan tazaran dake tsakani na dashi mai yawa ne? Ƙaddara da tashi ba ɗaya bace, koda ace babu Zayyad a tsakanin mu ai Sulaiman ba irin mijin aure na bane samm!!!
Jin shirun da nayi yasa baba ci gaba da cewa “wakilan shi ya turo su nema mishi izini ya nemi auren ki….
… Aure na Sulaiman ya turo a nema mishi?…. seriously!!…..me ya ɗauke ni ne? Yayi tunanin yana da ikon da zai iya juya ni duk yadda yaso ne da zai soma neman aurena haka siddin, ba wani proper shiri babu daidaito kaman a zamanin sayen bayi?!
“Saidai ban yarje musu ba domin kuwa yanzu ba da bane, ba zanyi miki dole ba.
Ko a Musulunce yanzu kece da ƴancin sama wa kanki abokin rayuwa, kuma bamu da wani burin da ya wuce ki samu farinciki mai ɗorewa, a saboda haka idan kina son sulaimanu ni mai yarje miki ne ki aure shi, idan kuma bakya son shi to bazan taɓa miki tilas a kai ba”
Sauƙe ajiyar zuciya nayi da jin kalaman shi, saidai duk da haka ba zan iya buɗe baki gaban mahaifina na faɗa mishi zaɓin zuciyata ba. Da ya fahimci haka sai ya bani dama naje nayi shawari a kai, duk abinda na yanke sai na faɗa wa Inna ta ita kuma sai ta sanar dashi zuwa gobe da safe don zan koma yola.
Ba ƙaramin ɗaga min hankali al’amarin nan yayi ba, tun yamma na rasa walwala ina fama da matsanancin bugun zuciya. I can’t imagine my life without Zayyad, bansan yaya zan kasance idan bayi tare dani ba.
Ƙarfe 9 na dare ina kwance a gado Inna ta shigo ta zauna ɗan nesa dani tare da kiran sunana,
Tashi nayi na zauna tare da naɗe kafafuwana na tattaro dukkan nutsuwata da hankalina na bata su.
Shiru tayi kama ba zatayi magana ba tana ta rarraba idanu ta kasa koda haɗa ido dani, sai can kafin tayi gyaran murya a hankali ta juyo ta zuba ma kafafuna kallo cikin jin nauyin maganar tace
“Kinyi tunani akan maganar da kukayi da baban ki?”
Gyada kai nayi da sauri cikin jin daɗi, a hankali na furta “eh” don zan iya cewa wannan ne karo na farko da Inna ta fiskance ni akan wani abu da ya shafi rayuwata, harma take niman jin ra’ayina.
Shiru ta sake yi na ƴan sakanni kafin tace
“Wani shawara kika yanke?”…………🧚
_Well… Zaku ga maganar kowa ya dawo daidai a wannan page ɗin🤓 amman bawai hausa ya zauna a bakin fulanin bane saidai accent din ne nada wahalar fahimta ga wanda ba bafulatani ba shiyasa kawai na gyara shi saboda sauƙin ganewa🤠_
*Ina yima ɗaukacin al’ummar Musulmi barka da Sallah🥳💝, Allah ya maimaita mana.✨ ya nuna mana na shekaru aru_aru masu zuwa🥰*
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
44🧝🏻♀️
“Bani son Sulaiman Inna…. gaskiya ba zan iya auren shi ba”
Daga kallon da tayi mun nasan batayi tsammanin wannan amsar daga gareni ba, harɗe fuskana nayi babu alamun fara’a domin ta daɗa gaskata zancena, haka tayi shiru ta zuba min idanu na tsawon lokacin da bata taɓa yi ba tsawon rayuwarta,+
“Kina nufin ba zaki sake aure ba kenan? Ba zaki shiga ɗakin ki na sunna ki mutu a can ba?”
“Ba abinda nake nufi ba kenan Inna kawai….” Ban ƙarashe magana ba ta katseni muryarta kaman mai shirin kuka tace
“Mun yarda zamu ɗauki duk wani wulaƙancin da za’ayi mana a sanadin haka, musulunci bai hanaki ƙara aure ba kada kibar al’ada ya hana ki”
Matsowa tayi daff dani sannan ta jawoni jikinta ta rungume
“Kiyu haquri boɗɗi kada fushin abinda mukayi miki ya saka ki bari rayuwarki ta tarwatse kiyi sallama da farincikin dake cikin ta.
Tsawon shekaru kusan 6 da kikayi nesa da gida bamu iya mun waiwaye ki ba, bamu sani ba ma ko kina raye ko kin mace, bamu ma san wani irin rayuwa kike yi a wurin masu riƙon ki ba. Munyi buri da fatan sake zuwa gareki amman duk iya qoqarin mu mun gagara…..
Tunda ta fara magana na saka kuka tare da saka hannaye na biyu na qara rungume ta a jiki na ina jin kwatankwacin ciwon da itama take ji a nata zuciyan.
Qarfi da yaji an raba uwa da ƴarta, da ƙarfin cin tuwo aka haramta mata raɓar abinda ta aifa daga cikinta.
“Kiyi haquri dan Allah idan abinda ya ɓata miki rai kenan, ba ko wani namijin bane yake kaman yarima, insha Allah wanda zai aure ki yanzu zai ɗauke ki da daraja kuma ya baki farinciki na duka duniyarnan da miji yake bawa matarsa”
Na gane cewa Inna bata fahimci abinda nake nufi bane amman bashi bane abu mafi a’ala a yanzu ba,
Wannan yanayin da nake ciki yafi min komai muhimmanci, shine abinda nake tsumaye tun yarintana da kuma musamman lokacin da nayi nesa da gida,
A kullum bani da burin da ya wuce ganin ranar da zanyi sharing pain ɗina, farincikina da baƙin ciki na tare da mahaifiyata.
Na faɗa mata damuwowina domin ta taya ni maganinsu dukda kuwa aunty Yusrah da mama suna ƙoƙari ta wannan fannin amman na uwa daban ne.
Shiru nayi na langwaɓe a jikinta sai hawaye ne kawai ke sintiri a fuskana amman na gagara faɗa mata matsalata don nasan raba hankalinsu gida biyu kawai zanyi duba da matsayin da sulaiman yake dashi a wurinsu yanzu ace sun tsallake shi sun bawa qanin shi ni? Abin da kamar wuya! Sannan nima nasan ko sama da ƙasa zasu haɗe a yanzu ba zasu min dole ba, shiyasa na ja baki na na saka mishi sakata… Yanzu na jingina komai ga hamma zayd, na yarda dashi ɗari bisa ɗari ba zai taɓa bari soyayyar mu ta lalace ba.
Muna zaune ina zancen zuci har barci ɓarawo ya ɗaukeni da zazzafan ciwon kai, amman ko banza na zubar da rabin ciwon dake cina a zuciya.
Gyara min kwanciya Inna tayi ta rufe ni da bargo dan ana ɗan taɓa sanyi, sannan ta fita ta kintsa ko’ina ta ɗauko indo ta kwantar da ita a tsakiyan mu kana itama ta kwanta, tana kallon fuskokinmu har itama bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari tun safiya na fara shiri amman kafin na fito daga wanka har driver ya iso don haka da na fito a gaggauce na shirya gudun kada na ɓata mishi lokaci kwata_kwata ban gamu da Zayyad ba.
STORY CONTINUES BELOW

Saida na gama shirina tsaff duka mutanen gidan suka fito zasu min rakiya amman babu shi, dukda kuwa nasan ba iya fitowa yakeyi ko wani lokaci ba amman ya kamata yazo muyi bankwana don bamu san ranar sake haɗuwa ba.
Daurewa nayi nayi ta maza na juya wurin baba sannan nace
“Bari na duba jikin mara lafiyan namu baba saboda na samu abin yiwa su aunty amarya albishir idan naje gida, naga tun jiya ma bai leqo waje ba”
Murmushi yayi yace “A’a hajiyata kun daiyi ta saɓani ne dashi amman ya fito, har hira muka taɓa a daren jiya da kukayi barci kuka barni, saidai bani tunanin ya tashi daga barci yanzu, saboda bai daɗe da kwanciya ba”
“Muje kawai tunda bai farka ba kada mu bari rana tayi miki a hanya” cewar matar ya Aminu.
Gyada kai nayi cikin sanyin jiki, ba dan naso ba na fara jan ƙafana zan nufi hanyar fita waje baba ya dakatar dani.
“Ko yana barcin taje ta ganshi dai, kinga hankali sai yafi kwanciya”
Wallahi ji nayi kaman na ruga da gudu na shiga ɗakin, amman haka na cije na taka a hankali na shiga ɗakin da yake.
A saman gadon shi na hango shi kwance ya bama ƙofa baya sai numfashin sa dake fita a hankali wanda sauƙa da tashin hannun shi dake kan ƙirjin shi ya nuna hakan.
Ƙarasawa kusa nayi na durƙusa a gaban gadon na ƙura ma gashin kanshi ido na tsawon sakwanni 10 kafin a hankali na tashi na zaga ta ɗaya ɓarin ina leƙa fuskar shi.
“Allah ya ɗaga kafaɗun ka hamma zayd, i will wait for you to come and fight for our love, nayi maka alqawarin duk hukuncin da ka yanke zan baka goyon bayana and i will stay by your side and support you, I LOVE YOU”
Da ace a fili nayi magana nasan babu abinda zai hana shi farkawa saboda na fahimci motsina kaɗai ya dame shi, ni kuwa ba zanso farkawan shi a wannan gaɓan ba don bani son tafiya cikin baƙin ciki.
Addu’a nayi na tofa mishi sannan na sulale na fita daga ɗakin.
A waje na samu su baba suna jira na a inda na barsu, daga nan muka ɗunguma sukayi min rakiya har jikin mota, na shiga suna kwarara min addu’o’i muka ɗauki hanya.
*********
Riƙe baki nafi’u yayi cikin tsananin mamaki yana kallon Sulaiman, shikuwa yayi kutun_kutun ya haɗe rai kada ma yayi tunanin ko yana da niyyan fasa abinda yayi niyya ne.
“Amman wallahi bakayi ma kanka adalci ba babban yaya,…..bakayi ma Saudat adalci ba hakama Zayyad.
Ta yaya za’ayi ka shiga ma yarinyar nan ta sama bayan kasan ba kai take so ba?”
“Kunyi magana da ita ɗinne tace maka bata sona?” Ya tambaya cikin tuhuma tare da daɗa tsuke fuska yana tura ma Nafi’u mummunan kallo.
“Allah ya huci ranka yaya, bani na kar zomon ba rataya aka bani.
Amman ka sani ba sai an faɗa ba, Saudat Zayyad take so”
Kallon shi sama da ƙasa yayi a yatsine sannan yace “na fahimci yanzu kuma taya shi yaƙi kakeyi, ka zaɓi half brothern ka akan wanda kuka fito ciki ɗaya”
“It’s not the issue of him being my half brother and you being my complete brother or whatsoever, dukkannin ku ƴan uwana ne kuma abinda kake shirin yi ba daidai bane that’s my point! nima fa kake yi a kan niman ɗan uwanka, haba dan Allah!”
Ya buɗe baki zaiyi magana wayar shi ya ɗau ruri, ganin sunan hajiya yasa babu ɓata lokaci ya ɗauka.
Magana sukayi wanda bai wuce minti 1 ba yace mata yana zuwa sannan ya katse kiran.
Miƙewa yayi yana gyara zaman hulan kanshi yace
“Inaga ka manta wani abu ne amman bari na tuna maka, matar da kake aure a yanzu ba a son ranta ta aureka ba, tana da wani masoyin wanda yake sonta take sonshi amman kayi amfani da iko da dukiya ka shiga mata ta wurin iyayenta ka raba su,
To nima irin naka zanyi da abubuwan da kayi amfani nima zan raba tsakanin saudat da Zayyad”
Zuwa yanzu jikin Nafi’u ya fara sanyi da kalaman Sulaiman, ya rasa yaushe halayyan shi ya dawo haka, mutumin da yake maida damuwan wasu damuwan shi yanzu shine yake shirin saka masoyin shi a damuwa,
A sanyaye yace
“Babban yaya he is your brother, case ɗina da naka ba iri ɗaya bane, Zayyad is your blood!”
STORY CONTINUES BELOW

“Blood my foot!!! Shi ɗan uwan nawa ma ai namiji ne, ya gwada mazantaka mana!
Anyway bari na tafi kada na saka mahaifiyata jira.
Kuma duk abinda zai faru ba zan janye ba, amman shi rabin ran naka zai iya shiga takara idan yaga dama sai muga ni dashi wa zaiyi nasara nidai na riga na fara jefa tawa ƙuri’ar”
**********
“Sulaiman haka aka ce maka ake aure a yanzu ba zaka shawarci yarinya kaji ko tana son ka ko bata son ka ba kawai zaka tura a nema maka auren ta?”
Fuskar nan dai a haɗe kaman ko yaushe ko uwar tashi ma ba sararawa, cikin maganar shi da yafi kama da na umarni yace
“Hajiya a gani na hakan shine dai_dai saboda wannan yarinyar bata yi hankalin da har za’a nemi yardan ta ba kafin a yanke hukunci a kanta, ni naji ina son auren ta zan iya zama da ita saboda tana da nutsuwa sosai ba zan samu matsala wurin shawo kanta ba”
“Naji kaman yanda kace ‘Saudat batayi hankalin da za’a nemi yardarta kafin a nemi aurenta ba, nima bani da hankalin da za’a shawarce ni ne? Ko har kayi girman da baka buƙatan concern ɗina a cikin al’amarin rayuwarka?”
“Haba hajiya, kada kice haka dan Allah!”
“Me yasa bazan ce haka ba bayan kai da kanka ka gwada min bani da muhimmanci a wurin ka da har zaka fara shirin ƙara aure ba tare da sani ba, ina dai fatan ba son ruguza farin cikin yarinyar nan kake son yi ba, bazawara mai ƙananun shekaru wanda rayuwarta na baya ke cike da tarin ƙunci, dan Allah kada ka ƙara mata wani damuwan babana,
Saudat tana da ƴancin zaɓen mijin aurenta da kanta a yanzu, kada kayi sanadin da za’a tauye mata wannan hakkin”
haka kawai yaji zuciyan shi ya fara nauyi da aka fara tuhumar shi akan maganar nan, amman idan ya fasa ma shine zai cutu, yana tausayin yarinyar nan amman kuma yana sonta,
Ba zai aure ta bane don ya ƙara mata damuwa yana son auren ta ne don ya sanyata farinciki kawai.
Numfashi mai zafi ya furzar sannan ya ɗan ɗago ya kalleta kana ya maida kanshi ƙasa kafin yace
“Nima na san da haka Hajiya, kuma babanta ma bai yarda ba yace sai ta amince tukunna, amman ni kawai na gabatar da kaina a wurinsu ne kada a samu wanda ya rigani”
“Hakan nake son ji, gwanda kaje ka nemi amincewar tan kada mu shiga hakkin yarinyar nan ta kuka damu Allah ya kama mu”
“Idan Allah ya yarda ba zan zamo wanda zai cutar da Saudat ba Hajiya, saidai na zamo mata madafa kuma mai tallafawa rayuwarta tayi inganci”
Murmushi tayi tace “toh shknn babana, amman idan lokacin yazo da kaina zan tambaye ta ko ta amince da kai ba wai kaine zaka zo ka faɗa min ba”
Dariya ne ya suɓuce masa irin wanda bai saba yi ba ganin cikin sauƙi ya shawo kanta, yanzu bayi da wani matsala bayan Zayyad.
Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun shi yayi yace
“Bari na wuce Hajiya naga azahar ya gabato”
“To babana, Allah ya maka albarka ya qara tsare gaban ku da bayan ku”
Da ameen ya amsa fuskar shi ɗauke da fara’a ya fita.
**********
“Sannu da hanya Saudat”
“yauwa aunty Yusrah” na amsa lokacin da na zame ɗankwalin kaina don na samu iska ya ratsa gashin kaina da na wanke shi yau da safen nan.
“Na same ku lafiya”
“Lafiya qalau yaya kika baro mutan gida”
“Lafiyan su qalau, akwai ma maganar da nake son yi dake aunty Yusrah”
Tashi tayi ta nufi hanyar kitchen tana faɗin “kici abinci ki huta kafin idan kika samu nutsuwa a jikin ki sai ki faɗa min Maganar, kinga ma zuwa anjima zaku tafi sai kiyi ki gama kintsawa kafin drivern ya dawo”
*******
12:03pm Zayyad ya tashi daga barci, yana fitowa aka tare shi da ruwan wanka yayi kafin suka kawo mishi abinci.
Bai ɓata lokaci ba yaci saboda yasan daga nan sai shan magani wanda kusan kullum ni nake kawo mishi, daga nan kuma na zauna mu ɓata lokaci wurin hira amman da mamakin shi yau jaɗe ne ya kawo,
Duk yanda ya kai da son dannewa saida ya gagara ya tambaya,
STORY CONTINUES BELOW

“Ɗazu da shafe shaudatu ya tafi ai” cewar jaɗe
“Ta tafi shine bata zo munyi sallama ba?”
Ya faɗa ba tare da ya nuna tsantsar damuwar shi cikin zancen shi ba.
“Ya shigo ai kina barci ne Zaidu shiyasa bai tashe ki ba ya tafi”
Jimm yayi kaman mai tuna wani abu kafin yace
“Jaɗe yaushe zan iya tafiya gida”
“Gashkiya ban shani ba Zaidu amman ki bari jikin ki ya ƙara kyau sai baba ya shallameki ki tafi”
Cikin ɗan nuna damuwa yace “inaso na tafi gobe dan Allah, kayi min magana da baban akwai babban uzurin da nake son naje nayi”
“A’a Zaidu tafiyan ki gobe ba zai yiwu ba gashkiya akwai magungunan ki da baki gama sha ba, amman da zaki ɗan ƙara haƙuri shun kushan ƙarewa shai kiyi tafiyan ki mai gaba ɗaya”
Finally! Lokacin da yake jira ya gabato, shi ai tun da basu faɗa mishi ya kusa tafiya gida bane da bazai tashi hankalin shi ba ko kaɗan, yanzu da yabar nan agendan shi na gaba shine AUREN SAUDAT,
Da ya gama da wannan kuma shikkenan! Bayi da sauran wani babban damuwa a rayuwan shi, Allah yayi mishi maganin matsalolin shi gaba ɗaya lokaci ɗaya.
Shikam bayi da abinda zaiyi saidai Godiya daman ance mahaƙurci mawadaci.
**********
“Aunty Yusrah kinji fah, dan Allah ta ina zan fara fitowa nace ma su baba bani son babban yaya? Ta yaya zan bari yaji nace bani son auren shi dan Allah bayan shine ya zamo min Garkuwa a rayuwata?”
Shafa bayana tayi tana bubbuga ni a hankali cikin sigar lallashi tace
“Kiyi shiru dan Allah, meye abin kuka kuma a nan? Share hawayen dan Allah sai musan abinyi amman hawaye basu maganin ko wace irin matsala a duniyar nan”
Bayan hannuna na saka na goge hawayen idanuna ina jan hanci, tace
“Amman menene dalilin da yasa baki son ki aure shi? Ya miki tsufa ne ko kuma a halayen shi ne akwai abinda baki so? Ko kuma dan yana da mata da yara?”
Girgiza kai nayi nace “ko ɗaya!”
“Toh… ko dan saboda Zayyad ne”
Gyaɗa kai nayi da iyakar gaskiya na kana nace “dan Allah Ki saka abban Jannat ya shiga cikin maganar nan, bani son shiga tsakanin wa da qani har na kawo matsala a tsakanin su”
“Amman ba Zayyad kike so ba? Just go for him babu wanda zai miki dole”
“Hamma Zayyad nake so aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawari yaya zanyi?”
“Zuciyan ki bata cunkushe ba, ke kika ruɗa kanki da gangan, shawaran da zan baki kawai shine kada ki zaɓi abinda zaki zo kiyi nadama daga baya,
Choose wisely Saudat, you are an adult now”
Daga wannan maganar ta miƙe taje ta ɗauki ɗanta dake kuka ta barni da aikin tunani.
******
Ƙarfe 4 na yamma driver ya sake dawowa zamu tafi lokacin na gama shiri na tsaff, kafin na bar gidan aunty Yusrah saida na tura ma Zayyad text message na bankwana ban jira reply ba na kashe wayan na ajiye a gidan don bamu zuwa dashi, saidai laptop kawai ko iPad.
Kafin mu wuce saida muka je gidan su khamis nayi musu sallama da gidan su Yusrah daga qarshe ne muka je gidan su Zayyad,
Luckily ban haɗu da sulaiman a can ba, a yanzu banma san dani dashi waye mai ɓuya ma wani ba.
Tafiyar mu baiyi nisa ba ya kira ta wayan driver yace a bani.
Tunda na gaida shi sai naja baki na nayi shiru, abin mamaki shima sai ya tsinci kanshi da kasa cemun komai.
Bayan shirun da ya ratsa tsakanin mu na tsawon minti ɗaya, a sama na jiyo muryar shi yana faɗin
“Kiyi haƙuri Saudat, na san nayi miki ba daidai ba da na isa wurin iyayen ki ba tare da na tuntuɓe ki ba, tsoron rasa ki nakeyi shiyasa”
STORY CONTINUES BELOW

Numfashi mai zafi na furzar haƙurin da Sulaiman ya bani farat ɗaya ba tare da tsammani ba ya bani mamaki matuƙa, sai kuma naji tausayin shi ya kamani idan na tuna duk wannan fafutukar da yakeyi kunya kawai zan bashi daga ƙarshe a lokacin da na juya mishi baya na zaɓi ƙanin shi,
Wani irin kallo zaiyi min?
Anya zan iya kuwa?
“Hello, kina jina kuwa”
Gyara zama nayi da riƙon wayan a jikin kunne na nace “inaji dadyn Arif”
“Ban san menene a tsakanin ki da Zayyad ba kuma bani so in sani, ba kuma zan takuraki ki furta ra’ayin ki a kaina ba a yanzu amman Please find a place in your heart to accept me and become my wife shine kawai abinda nake so”
Sulaiman maganar amincewa kawai yake yi amman yaya batun soyayya? Amincewa da auren shin zanyi ne idan ina so ko bani son shi?
“Idan kuma sadiya ce damuwan ki, zan iya miki alqawarin idan na aure ki in kinso har abada ba zaki sake ganin fuskar ta ba, zan raba muku gida da unguwa zakiyi zamanki kaman baki da wata kishiya, just think about it Saudat you will be satisfied”
Sulaiman is only talking about satisfaction, what about happiness and love? Shi ko convincing mace ma bai iya ba ta yaya za’ayi ya iya narkar mata da zuciya ta mace a kanshi? Wani irin zaman aure za’ayi dashi babu wa’innan muhimman abubuwa guda biyu?.
“Zan jira hukuncin da zaki yanke idan kin dawo, amman ina fatan mai daɗin ji ne, ki dage da karatu kinji ko? Allah ya bada Sa’a”
Sai a yanzu na samu baki na ya motsa da ƙyar na iya furta “ameen na gode”
Babu ko sallama ya kashe wayarshi,
Miƙa ma driver wayan da nayi yayi daidai da furzar da numfashi mai zafi da na tuna irin cakwakiyar da na haɗa, yanzu hawayena ma sun fara kafewa kukan nayi min wahala,
Allah ya fitar dani kawai.
**********
3 weeks later
“Oyoyo…. oyoyo… Maraba lale da farin gani” Hajiya take maimatawa cike da murna lokacin da ta miƙa hannun ta ta rungumo Zayyad da bakin shi ke washe fuskar shi ɗauke da fara’a.
Kowa na gidan sun taru a waje ana murnan dawowa irin wanda bai taɓa yinta ba, dawowa mai cike da nasarori wanda yayi ta cikin bainar jama’a ba a ɓoye kaman ko wani lokaci ba kuma cike da farin ciki.
Daga wurin Hajiya ya ƙarasa kusa da aunty Amarya dake tsaye ta rufe bakinta da handkerchief tana kallon shi tana tsiyayar hawaye.
Tsayawa yayi a gabanta yana kallon ta a fakaice yace “aunty nikam kina murna da dawowa na kuwa?”
Cikin kuka tace “ka rasa hankalin ka ne zaka min wannan tambayar Zayd?”
Riƙo hannunta yayi cikin nashi ganin tana ƙoƙarin birkicewa yace
“Yi haƙuri aunty……amman gani nayi kina kuka, kuma a iya sanina ana zubda hawaye ne a lokacin baƙin ciki”
“Idan farin ciki yayi yawa ya zamo mara misaltuwa shima yana jawo haka Zayd, Ya Allah yasa ƙarshen wahalar ka kenan”
Shigewa jikinta yayi ya ƙanƙame ta don ya samar mata nutsuwa, yana jin tana jan numfashi a hankali har saida ta bar kuka kafin ya sake ta ya koma wurin su Sulaiman shima cike da jin daɗi ya rungume shi a jikin shi yana faɗin
“Welcome back my brother, ina matuƙar farincikin ganinka cikin yanayi mai kyau Allah ya qara maka lfy”
“Amin babban yaya na gode”
Haka suka ƙare wunin Ranar cikin farin ciki, Ruma ƙafafuwanta kaman zasu tsinke saboda sintiri ɗan uwan da ake ji dashi ya dawo.
Har su Nana ƴan baƙin gida suna farinciki a yau, kwalliyar da Sulthana ta shera kaman mai zuwa gidan biki amman shi Alhajin da tayiwa ko kallo bata ishe shi ba.
Bayan ya gama hutawa ne aunty Amarya ta saka shi a gaba ya fara zaga gidajen ƴan uwa yana gaishe su Abinda bai taɓa yi ba a rayuwar sa, sai yaga garin ya ƙara masa girma da faɗi don wuraren da ya sani ya taɓa zuwa basu fi a ƙirga ba, daga ƙarshe bayan sun gama yawon a gidan Nafi’u suka yaɗa zango suna huta gajiya.
“Ya Nafi’u freedom akwai daɗi” ya faɗa yayinda ya kai glass cup ɗin ruwa mai sanyi bakinsa.
“Kwarai Zayyad, ai nake faɗa maka yanzu ne zakayi settling, kaji daɗin rayuwar ka na duniya amma kuma fah kada daɗin yayi yawa a manta da gina lahira”
Dariya zayyad yayi yace
“Lallai wannan saidai a faɗa ma wanda bai jarrabu a duniya ba, amman abinda ya same ni kawai ya isa ya nesanta ni da duk wata shagala na duniyar nan don na san mai ƙarewa ne”
“A’a wai ai ina tuna maka ne saboda hali na ɗan Adam da kuma sharrin zuciya.
Yanzu sai muje kan abu na gaba ko? Wato Aure dan kaji daɗin rayuwar freedom da kyau da kyau”
Ajiye cup ɗin hannun shi yayi a saman table sannan ya ɗan matso tare da faɗin
“Yauwaa kaman kasan kuwa shine a raina, yanzu sai muje ka shige min gaba a wurin dady Saudat ta gaji da jira na”
Jimm Nafi’u yayi yana kallon Zayyad sannan yana tuna maganar da sukayi da Sulaiman akan ita saudat ɗin, yace
“Yanzu da gaske kakeyi maganar auren saudat ɗinnan?”
“Da nayi kama da mai yin wasa ne? Da gaske nake son auren ta mana tun ba yau ba ai na faɗa maka”
“Bazawaran?” Nafi’u ya sake tambaya fuskar shi da ɗan damuwa dan burin shi bai wuce ɗaya daga cikin su ya janye ba rikicin ya tsaya tun daga nan.
Dariya ya sake yi wanda ya saka dimples dinshi lotsawa yace “ya nafi’u itace fa maganin matsala ta, itace maganin matsalar da nafi shekaru 25 ina fama dashi lokaci ɗaya tazo duk wasu damuwa ta ta yaye min su me zai saka na damu don ita BAZAWARA CE? abinda na sani kawai shine ZAYYAD yana son SAUDAT kuma ZAYYAD shi zai auri SAUDAT”
“Amman kasan babban yaya ya tura wurin iyayenta a nima mishi auren ta kuwa?”……………🧚🏼♀️
Longest page so far😅
_Abubuwa sun fara hautsinewa😓 wa kuke tunanin zai haƙura a cikin su???🤷_
*Love You my fans*
#team SS❤️
#team SZ💙
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: Polohttps://my.w.tt/4ZfEeBpVecbp
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
45🧝🏻♀️
Zaune nake a class na tattari hankali na baki ɗaya na zuba akan note da nake jotting.
Shigowan masinja ne ya maida hankalin gaɓa daya student ɗin kanshi don ba’a interrupting dinmu idan muna lesson.
Izini ya nima wurin teachern mu da ya barni na fito wai anzo wuri na daga gida, nayi matuƙar mamaki d jin haka don tunda nazo school ɗinnan babu wanda ya taɓa zuwa wuri na idan ba a visiting day ba saboda Sulaiman baya bari.
To ko shine ya dawo akan maganar mu ta kwanaki? Har yanzu ban tanadi amsan da zan bashi ba wlh, bansan idan naje mai zan ce mishi ba.+
Kyarma jiki na ya fara na tsoro gashi har yanzu ban sanar ma Zayyad abinda ke faruwa ba na bari akan sai anyi mana hutu naje nayi mishi bayanin komai,
A nitse nake bin mutumin ina jero addu’o’i a zuciya na har zuwa ɗakin da aka tanada na ganawa da baƙi.
“Hamma zayd?!” Na furta cike da mamaki lokacin da na hango shi zaune a kan kujera, kwata_kwata banyi tsammanin shi zan gani ba.
Ɗago ido yayi daga inda yake zaune ya zubamin su, ina ganin wutar ɓacin rai a cikin su.
Fita masinjan yayi ya bamu wuri mu gana sai a lokacin Zayyad yayi magana.
“Me yasa kika ɓoye min saudat? Mai yasa tuntuni baki faɗa min ba?”
Sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina wasa da yatsu na saboda na kawar da zancen na gaishe shi da
“Ina kwana, ka iso lfy”
“Ughh.. forget about greetings, rayuwata tana cikin garari har kina da nutsuwan gaisuwa?… Just answer my questions please”
“Na bari sai lokacin da abubuwa suka gama gyaruwa ne ka samu qoshin lafiya kafin na sanar maka”
“Wani lokaci ne wannan kenan? Lokacin da muka riga muka rasa komai babban yaya yayi Nasara a kanmu? Kina tunanin kina cikin abinda zan iya haƙuri da rashin su ne? Yanzu yaya kike so nayi ya riga da ya riga ni?”
Neman wuri nayi ɗan nesa dashi na zauna sannan na ɗago ina kallon cikin qwayar idanun shi tare da yin fuskar tausayi nace
“Ba son babban yaya nake yi ba hamma zayd, har yanzu ban faɗa ma baba na amince ko ban amince ma auren sa ba, amman idan ka fito nayi alƙawarin zan zaɓe ka a kanshi ba tare da wani tunani ba, nima ba a son raina hakan ta faru ba kayi haƙuri”
Ƙaramin tsaki yaja ya kifa kanshi a jikin hannun shi na dama yana murza gaban goshinsa dan ji yakeyi kaman zai tsage ya fashe,
“Kema kiyi haƙuri babes, nasan ba laifin ki bane, ba ke ya kamata na tuhuma ba, raina ne ya ɓaci sosai I can’t control my anger”
Murmushi nayi nace “to bari na baka wani labari, kana so?” gyaɗa min kai yayi alaman yana sauraro na naci gaba da cewa
“A zamanin annabi s.a.w akwai wani mutumi da yazo ya same shi yace ya Manzon Allah kayi min wasiyya,
Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace mishi, kada kayi fushi, sai mutumin ya sake maimata tambayar tashi amman amsa ɗaya Annabi yake maimata mishi ‘kada kayi fushi’
Hakan na nufin akan dukkan abinda zamuyi fushi bazai haifar mana da ɗa mai ido ba, just calm down mu dage da addu’a komai zai tafi daidai insha Allah”
STORY CONTINUES BELOW

Lokaci ɗaya fushi da ɓacin ran da ya taho dashi ya gushe, murmushi yalwatacce ya ɗaura kan fuskar shi, jingina kanshi yayi da jikin kujeran yana jefa min kallo mai cike da shauƙi, yace
“See wife material! You already know how to handle me well I’m surprised gaskiya and I’m indeed very lucky”
What he is doing is affecting me, na kasa hana kaina blushing, yabo daga wurin wanda zuciyan ka yake muradi komin kashin sa yana da matuƙar daɗi,
Kama ƙasan hijabin uniform ɗina nayi ina kanannaɗa shi a jikin yatsa na a kunyace nace “Ina jin bugun zuciyan ka cikin tawa, so I can say duk abinda zai faranta maka da wanda ba zaiyi maka daɗi ba zan iya sani”
“Ina sonki Saudat, Allah yayi ma rayuwar ki albarka”
That words melt my heart wallahi, daɗi kaman zai kashe ni da naji su, gashi ya kafa min ido kaman zai cinyeni bansan ko me yake kallo ba don bayan hannu na ko ina na jiki na a rufe yake,
A haka muka ɗauki lokaci muna hira mai daɗi yana sanar dani irin kewata da yayi lokacin da bani nan, nima hakan yake a wuri na tunanin shi da halin da yake ciki yana hana ni barci, kullum kafin na kwanta sai na karanta wani ɓangare daga cikin al-qur’ani nayi mishi addu’a kafin na samu nutsuwa barci ya ɗauke ni.
Har ya tafi bamu sake ɗago chaptern Sulaiman ba,ni mantawa ma nake dashi da matsalar shi.
*********
Wangale mishi gate akayi ya danno hancin motarshi ciki da gudu yana murza steering motar cikin qwarewa, can daga nesa ya hango Sulaiman tsaye a ƙofar part ɗin aunty Amarya sanye da fararen kaya babu hula a kanshi hannun sa naɗe a saman ƙirjin shi.
A take Abinda yayi ya dawo mishi, daman farincikin da ya nuna yana yi na dawowarshi jiya duk ƙarya ne shi yasan abinda ya tanada.
Haɗe rai shima yayi ya samu wuri yayi parking motar kafin ya nufe inda Sulaiman ɗin yake tsaye,
A tunanin shi idan Zayyad ɗin yazo zaiyi masa magana ne ya samu daman huce haushin shi a kanshi da kyau, saidai yana ƙarasowa ya ratsa ta gefen shi zai wuce ganin haka yasa Sulaiman ɗin juyawa kafin ya shiga cikin part ɗin ya dakatar dashi,
“Me kaje yi wurin sauda a makaranta? Wa ya baka izinin zuwa wurinta?” Sulaiman ya tambaya idon shi a cikin na Zayyad yana jifan shi da mummunan kallo.
Ciza haqwaran shi yayi cikin takaici yana jin ɓacin ranshi yana dawowa sabo, Sulaiman ya gama shiga mishi hanci da ƙudundune ya hana shi shaƙan iska, a hasale yace
“Da ni ban tuhume ka da shige min gaba da kayi kana son mallakar abinda yake nawa bane shine kai har kana da bakin tambayana abinda ya kaini wurinta?
Let me make one thing clear Sulaiman, Saudat…is…MINE!”
“No! She is not” ya amsa a taƙaice ba tare da ya nuna wani damuwa a kan fuskar shi ba.
“She is!!!
Sannan wannan karon ba zan bari kayi nasara a kaina ba saƙon da ka bayar a faɗamin ya riske ni na cewa nima namiji ne na gwada mazantaka na sannan idan inaso zan iya shiga takaran niman auren saudat aga ni da kai waye zaiyi nasara,
To ba takara ni zanyi da kai ba, ƙwaceta zanyi daga wurin ka saboda ita tawa ce, she belongs to mee!!”
Da faɗan haka ya sake juyawa yana fitar da huci kaman wanda zai cike da hayaƙi, zai shige ciki ya tsinkayo muryar Sulaiman na faɗin
“A duk lokacin da kazo da wani matsala naka nakan yi ƙoƙarin maida shi first priority na, ba zan huta ba har sai naga nayi maka maganin shi to yanzu lokaci ne da zaka biya ni wa’innan alkhairan da nayi maka, ka haƙura da boɗɗi ka fita daga rayuwar ta gaba ɗaya dan Allah Zayyad”
Juyowa ya sake yi a karo na biyu ya kalle shi a kaikaice sannan yace
“You know what? Na gaji da gorin da kake min Sulaiman, gaba ɗaya ka saka na kasa sakewa da rayuwata kana saka ni naji kaman kaine ka busa min numfashi ko kuma bani bashin rayuwata kayi da yanzu kake buƙatan na biyaka,
If that’s the case ka faɗi ko meye kake so zan baka, harta abinda ka taimaka min na mallaka ma idan kana so zan iya haƙura na bar maka shi amman banda Saudat!
Bazan bar maka ita ba….bata cikin abinda zaka iya samu daga wuri na saboda ita ɗin mutum ce ba wani haja da kowa zai iya mallaka ba and i respect her alot” da faɗan haka yayi tafiyar shi ya bar Sulaiman tsaye da sakakken baki al’ajabi ya mugun kamashi dan ko a mafarki bai taba tunanin Zayyad zai iya tsayayya dashi haka ba.
STORY CONTINUES BELOW

*******
Ruma ya tarar a parlour ta baje takardu a gabanta tana karantawa dan sun fara text ɗin first semester sai anty dake zaune tana kallon Africa tv 3, Fa’iza kam daman wurin zamanta part ɗin hajiya ne, su junior da Farooq kuma suna makaranta.
Sallama yayi musu suka amsa bai sake ce musu komai ba ya nufi hanyar bedroom ɗinshi, har yayi rabin hanya ya canja ra’ayi ya juya ya nufi hanyar bedroom ɗin dady dake part ɗin.
Shigar shi yayi daidai da fitowar dady daga toilet, gaida shi Zayyad yayi kafin ya nima ma kanshi wurin zama.
“Yaya dai Zayyad wani abu ya faru ne?” Dady ya tambaya yana karantar yanayin fuskar shi.
Sai kuma yaji nauyin buƙatar da yazo dashi yasan zaiyi ma mahaifin nashi banbaraƙwai kuma ba lallai bane ya fahimce shi, amman wannan ne kawai hanya ɗaya da zai iya defeating Sulaiman.
A ɗarare ya fara kwaro mishi bayanai kan cewa yana son Saudat kuma yana so a shiga mishi gaba wurin niman aurenta.
Shiru dady yayi yana nazari kafin yace “wannan wani irin shirme ne Zayyad, yarinyar da kake faɗa ba ita bace ɗn uwanka ya tura mu wurin mahaifinta? Ko baka sani bane?”
“Ban sani ba dady, sai yanzu amman shi babban yaya yasan tunda ita nake so na aura”
Tsaki dady yaja yace “tashi kaje ka kira min Sulaiman ɗin yanzu kuzo tare, wannan ai shashanci ne”
Lokacin da ya fita ya samu har Sulaiman ya tafi, a take dady yasa aka kira shi suka dawo sannan aka zauna zaman Shari’a kusan irin wanda akayi musu kwanaki lokacin da suka ɗau gaba da juna, don kowanne a cikin su fitar da abinda ke cikinsa kawai yake yi, ƙarshe abin da yafi ƙarfin dady saida ya kira wa’inda ya tafi dasu tambaya wa Sulaiman izini suma suka shiga cikin maganar.
Mutum ɗaya cikin su dagewa yayi a kan saidai Zayyad ya haƙura ya nemi wata dan ba zasu koma a kan wannan maganar ba mutuncin su ya zube, dady ma yaso yarda da maganar shi amman Zayyad ya kafe har da musu kuka shi bazai haƙura ba saidai Sulaiman ya haƙura.
Duk abinda akeyin nan su Hajiya basu sani ba har aaka ci aka cinye don yasan halin mata kowacce cikin su bayan ɗanta zata bi daga ƙarshe kawai sallaman su yayi yace suje zasu ƙarasa tattaunawa a tsakaninsu manya duk hukuncin da suka yanke zasu sanar musu.
****
Tun wannan lokacin da akayi magana har yanzu shiru kusan wata guda kenan dady baice ma Sulaiman ko Zayyad komai ba, gashi har su Saudat sunyi jamb sun fara shirin zana exams.
Aikin office ya taru yayi ma Zayyad yawa tunda suka samu matsala da Sulaiman yake masa mugunta saboda shine a saman shi yana sashi over working, shi kuwa Zayyad haka yake jurewa don kawai yasan idan ya gwada abin bai dame shi ba Sulaiman zaifi jin haushi.
Ganin shirun yayi yawa gashi Saudat ta kusa dawowa ayita ta ƙare yasa ya sake tunkarar Dady da maganar, da yaga da gasken gaske yake yi shine yace masa yaje zasu yi shawara da Khamis tunda shine kaman wakilinta a yanzu kafin ya musu hanya su ƙarasa wurin mahaifinta.
Washegari da yamma dady ya tura aka kira khamis, irin tarban da suke mishi a kowani lokaci wanda yake ƙara mutuncinsu a idon shi, shi sukayi masa kafin nan ya shiga ganawa da dady ya shaida masa abinda ke faruwa.
Ran khamis idan yayi dubu ya ɓaci har ya gagara ɓoyewa dady kuma ya fahimci hakan, amman haka yayi ta lallaɓa shi har ya yarda zai shige musu gaba su sake komawa wurin baba ba don ranshi ya so ba,
Yana tunanin irin kallon da dattijon mutumin nan zaiyi mishi da kuma tunanin wani kalan riƙo yayi ma Saudat wanda take matsayin amana a gare shi, gaskiya shi basuyi mishi adalci ba kaman ba manyan mutane masu nazari da tunani ba,
Ko dayake it’s obvious, daman hankalin wasu iyayen yakan gushe a kan buƙatun ƴaƴansu.
*****
Yana fitowa ya hango Sulaiman zaune a balcony yana ƴan danne_danne a waya gaban shi da kayan motsa baki amman shi bai lura da Khamis da ya ƙura mishi idanu cike da tsana da jin haushi ba,
Cikin ranshi yana ayyana irin rashin aiki da hankali da mutanen gidan gabaki ɗaya sukeyi musamman shi Sulaiman dake amfani da kuɗi yana shiga jikin kowa da kowa, daman ya riga da yasan double promotion da akayi mishi a wurin aiki kwanaki ba don Allah bane kuma ya shirya rabuwa da komai indai a kan Saudat ne.
Bai gama tunani ba sai ganin Sulaiman ɗin yayi a gaban shi har ya ƙaraso bai sani ba.
“Assalamu alaikum” ya faɗa tare da miƙa mishi hannu sukayi musabaha,
“Uhmm.. khamis kayi haƙuri da abinda yake faruwa nasan an ɗaga maka hankali, kasan sha’ani na rayuwa ya gaji haka dukda har ga Allah banso ayi dragging ɗinka cikin rikicin nan ba, Zayyad har yanzu tasowa yakeyi nutsuwa bai gama zama mishi ba shiyasa ya aikata haka dan Allah ka manta da abinda aka faɗa maka kada ka sa shi a ranka kuma ba sai an kaiga iyayen Saudat ba, ni zan zame mata irin mijin da take so insha Allah”
Sai yanzu ya daɗa tabbatarwa Sulaiman na da ƙarancin tunani don tabbas hannunka mai sanda yayi masa, baisan me yasa suke tunanin saudat abin wasa ne a wurin shi ba, ko dan ya sake musu sun ɗauki ragamar kulawa da rayuwarta shine suke so su gwada mishi bayi da iko da ita?
“Bani da ikon haɗa abinda Allah ya raba, kawai ku bari mu gani meye zai zaɓa mana domin nashi zaɓin shine daidai” shine kawai abinda khamis ya faɗa yayi mishi sallama kana ya tafi ya barshi tsaye a wurin.
*****
“Damn it… Damn all of them!” khamis ya faɗa a tsawace tare da buga cup ɗin hannun shi a jikin garu, da taimakon Allah ba glass bane da tuni ya tarwatse, Yusrah dai tana zaune tana kallon ikon Allah dan tunda ya dawo daga gidan Hajiya ya juye ya dawo kaman wani taɓaɓɓe.
“Abinda fa yasa na kasa faɗa maka komai tun da farko kenan saboda ina tsoron reaction ɗinka, Zayyad soyayya sukeyi da Saudat don itama ina da tabbacin tana sonshi sai kuma daga baya Sulaiman ya fito kan cewa shima yana sonta har ya samu ya shiga tsakanin su ba tare da sanin Saudat ɗin ba, yarinyar nan tayi kuka sau ba adadi, da ƙarancin shekarunta sun taru su biyu sun saka mata damuwan da babba ma ba zai iya ɗauka ba.
She is really suffering abban Jannat, Saudat is the real victim in all this mess….”
“Amman dan girman Allah me yasa kika ha’ince ni Yusrah? Har irin wannan abin zai faru a gidana a kan amanar da na sauƙo amman baki faɗa min ba? Why??”
“Saboda tsoron irin wannan yanayin, kayi haƙuri nayi tunanin matsalar ba zata ƙara girma bane sh…..”
“Amman gashi kin lalata komai ai” ya katseta a tsawace.
“Kada ki sake min irin haka wallahi idan bakiso ranki ya ɓaci, su kuma bazanje na same su na faɗa musu dukkan su babu ma wanda zan bawa ita wallahi” fuuu yayi hanyar ƙofa da sauri Yusrah ta miƙe ta riƙo hannun shi.
“Haba abban Jannat, ka tsaya muyi magana mana don Allah baka ji ƙarshen bayani ba kawai ka ɗau zafi?
“Babu abinda zanji YUSRAH ai wannan ma maganar banza ce in dauko yarinya amana a maida ita kaman zanin sayarwa a kasuwa saboda rashin mutunci? Dan K…..🙊 Ubansu daga Sulaiman boss ɗin har Zayyad ɗin babu mai auren ta a cikin su idan sunga dama sai su kore ni a aiki mutanen banza kawai,
Wallahi ni zanje in samu baba na sanar dashi su wasu irin mutane ne ya hana su duka sai inga mai zasu iya, jahilai masu ƙaramin tunani………….🧚🏼♀️
This chapter is quite challenging 🤧
#vote
#share
#comment
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: Polohttps://my.w.tt/4ZfEeBpVecbp
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
46🧝🏻♀️
Girgiza kai baba yayi da murmushi a kan fuskar shi, ba wanda yake nuna yana farinciki ba saidai mai nuna alama ta yana ganin mutuncin su dady amman ko kusa bai taɓa tsammanin mutane masu dattako irinsu zasu yi irin wannan tunanin har suzo su same shi a kan wannan maganar ba.
Haka iyaye suka zamo akan son zuciyan ƴaƴansu? Ba kunya ba tsoron Allah Kaman ba hausa Fulani ba!.+
“Alhaji kiyi haƙuri amman gashkiya bazan amshi buƙatar ku ba badan wai na raina ku ko baku kai ku nemi wani abu a wuri na ba, amman Shaudatu yaro ne mai raunin gashke, a zahirin gaskiya ba zan iya washa da abinda ya shafi farincikin shi ba, don Allah ya bani irin wannan daman daga farko nayi wasa dashi wanda har hakan yayi sanadin zuwanta Wurin ku amman wancan ƙaddara ce, shaidai idan na kushkure na jawo abinda zai sake kawo mishi tsangwama da kyara a ƙarkarar nan to zai zamo sakaci”
“Na fahimce ka malam arɗo nima Saudat kama ƴa take a wuri na ba zanso ganinta ta shiga wani hali saboda wani na ƙyale ba ballantana kuma a sanadiyya na, amman dan Allah ka ƙara duba lamarin muma ba yana tafiya mana a yanda mukeso bane, ba zamu saka saudat yin Abinda bata so dole ba shiyasa suma na faɗa musu ra’ayinta za’a bi duk wanda tace tana so shi za’a bata si ɗaya ya janye”
Ƙara faɗaɗa murmushin shi malam arɗo yayi ya juya ya kalli khamis da yayi kicin_kicin ya haɗe rai don fin ƙarfi suka gwada mishi ƙarara amman da kafin azo nan duk ya gama cin ubansu an huta.
“Lalle kunyi min alkhairai da dama kuma zan kashance mai godiya a gareku har ƙarshen rayuwata, amman mutanen wannan ƙauyen bashu raina abinda zai jawo mutum ya zamo abun la’anta a wurin shu, shu gallaza ma rayuwar shi, boɗɗi shi shaida ne a kan hakan domin har rayuwan shi shuka sho ɗauka, bazan bari hakan ya shake faruwa da shi ba dan Allah kuyi haƙuri ku yafe min, amman wannan zancen a barta kawai”
With so much excitement khamis yayi tsugul yace “shikkenan ba za’a basu auren ba kenan? Dukkan su?”
“A’a khamishu, idan nayi haka ko ma kaina bayi adalci ba ballantana ma shaudatu ko su maneman nata, saidai zanso daƴa a cikin shu ta hakura tun yanzu, ko ita babban ta haƙura ta janye ko kuma ƙaramin ta haƙura”.
Ya maida hankalin shi wurin dady sannan yaci gaba da cewa
“Alhaji da ace ba jini ɗaya suke ba koda sunfi biyu yawa zan basu duka ikon neman ta saboda bai saɓawa addini ba, amman yaya da ƙani ya saɓa ma al’adun mu, ban taɓa jin yanda akayi irin haka ba dan Allah kayi haƙuri kada a fara kafa tarihi damu, ni nayi alƙawarin wanda shaudatu ya gwada yana so a cikin su zan bashi ita ba tare da wani damuwa ba insha Allah”
Sam hakan baiyi ma khamis daɗi ba don har cikin zuciyansa baiso a bawa ko ɗaya daga cikin su Saudat ba don basu cancanta ba, amman tunda bashi keda hurumin nima mata miji ba zai bita da addu’a kawai yanzu dai ya riga da ya sauƙe nauyin amanar dake kanshi.
“In Allah ya yarda zanje na zaunar dasu mu yanke hukunci a tsakanin mu, nima na aminta da wannan shawaran da ka yanke don future’n Saudat ba abu ne da za’ayi wasa dashi ba, muna godiya da karamci da kuma dattako da kake nuna mana a ko wani lokaci, insha Allah zamu kama hanya yanzu kada dare yayi mana a hanya”
STORY CONTINUES BELOW

Tashi baba yayi sukayi sallama cikin girmamawa, kafin su fita saida ya kira su ya Aminu da jaɗe sukayi musu rakiya har jikin mota saida suka tafi kafin suka koma ciki.
**********
Fitowan Zayyad kenan daga wanka yaci karo da Sulthana zaune a bakin gadon shi wanda yayi a sanadiyyar zazzaɓin da ya sauƙa mishi da yamman nan tsananin tsoron da yakeyi na abinda zaije ya dawo daga wurin baban Saudat.
Saurin komawa ciki yayi ya datse ƙofar saboda towel ƙarami ne kawai ɗaure a ƙugun sa sauran suffa na jikinsa duk a bayyane, daga bayan ƙofar cikin ɗaga murya yanda zata jishi yace.
“What are you doing inside my room Sulthana?”
Lumshe idanunta tayi da jin tambayar shi don ita ta riga da taga abinda ya birgeta ya kore mata duk wani ɓacin rai da tazo dashi, ‘Zayyad has a very wonderful figure’ ta ayyana a ranta, yana daga cikin abinda yasa kullum take jin yana daɗa shiga ranta saboda shi ɗin mai kyau ne, tana son namiji mai broad chest and her Zayyad have it too.
Leƙowa yayi da yaji shiru a tunanin shi ko ta fita ne amman ya hango ta zaune a wurinda ya barta wannan karon idanunta a rufe,
“Ba magana nake miki ba kikayi min banza? I said what brought you to my room?”
Buɗe idanunta tayi ta ɗan haɗe rai sannan tace
“Ka fito Ya zayd magana nazo muyi”
“Ok to fita parlourn aunty ki jira ni bari na shirya sai na fito muyi maganar”
Share shi tayi kaman bata ji abinda yace ba ta jawo wayanta taci gaba da dannawa,
Tsaki yaja da ganin haka ya koma cikin bathroom ɗin ya ɗauko T-shirt da ya cire a laundry basket ya mayar da ƙyar ya iya fitowa gabanta a hakan don tunda yake bai taɓa tsayawa a haka gaban wata mace ba, kuma bazai iya yayi wanka ya sake maida kaya mai datti ba.
Dakewa yayi ya tsaya a gaban gadon ɗan nesa da inda take zaune yana mamakin ganinta da yayi yau da hijab har ƙasa, bai sani ba ko izala ta shiga amman da yayi mata murna tunda dai ya sakata nutsuwa.
“Yaya akayi?” Ya tambaya a takaice.
Kashe wayan tayi ta ajiye sannan ta tashi tsaye don ta daidaita tsayin su dukda kuwa ya mata tsawon da har sai ta ɗaga kanta sama take kallon fuskar shi.
“I heard that you are preparing to get married to that Saudat girl”
“Yess and so?”
Shagwaɓe fuska tayi kaman zatayi kuka tace “hakama zaka ce, ni kuma fah? Bayan duk alƙawuran da kamin lokaci ɗaya ka zubar dani a kwandon shara without any warning did i really deserve that?”
Ajiyan zuciya ya sauƙe ganin idanunta ya tara ƙolla gashi ya tsani ganin kukan mace haushi yake bashi, cikin lallami yace
“Sulthana! I’m sorry for giving you false hope, da gaske ne daga farko naso auren ki amman daga baya sai na fahimci you and I are not meant for each other, son da nake miki na ƴanuwantaka ne da kuma ɗan shaƙuwa da muka samu a tsakanin mu, Nothing more”
“Seriously? Is it because of Saudat? Me tayi muku ne that you and babban yaya are going crazy over her? Me tayi maka….me ta baka da ka liƙe mata ka manta da wanda tayi zaman jiranka tsawon shekaru har ka samu lafiya? Meye kake buƙata a wurin mace da bani dashi? Ka faɗamin nima zan baka” ta ƙarasa tare da zare hijabin jikinta tayi wurgi dashi.
Filluwa baya Zayyad yayi kaman wanda aka hankaɗa shi har towel ɗin jikin shi na niman faɗuwa saboda mugun ganin da yayi, da sauri ya tattaro shi ya sake gyara mishi ƙulli tare da kawar da kanshi ƙirjin shi na bugun hamsin_hamsin.
“Woooh!!! Meye haka Sulthana? Are you crazy?”
Sake satan kallonta yayi still tana tsaye da bikini yayi saurin ɗauke kanshi yana salati sai haki yake kaman wanda yayi tsere don abin yazo masa a bazata, this is the first time da yake kallon mace a haka, that too ba a TV ba zahiril ayni a gaban shi
“Get out of…my room”
Ya faɗa cikin fisgar maganan, amman a maimakon ta fitan kaman yanda ya umarta sai ta fara takowa zuwa inda yake zaune daɓas a ƙasa.
STORY CONTINUES BELOW

Durƙusawa tayi tana faman karkaɗa jikinta yanda tasan zata daɗa ɗaga mishi hankali, shikuwa sai ƙoƙarin kawar da idanunshi yayi har ta iso shi itama ta tsunguna tare da ɗago hannun shi ta ɗaura a saman ƙirjinta, zatayi magana sai sauƙan mari taji a kumatun ta, kafin tayi wani yunƙuri ya miƙe cikin zafin nama ya fara kutubol da ita a tsakar ɗakin don baiyi zaton ƙasurgumar mahaukaciya bace Sulthana sai yau.
Kaman wanda aljanun sa suka motsa haka yake wujijjigata a tsakar ɗakin tun tana iya daurewa har ta fara zunduma ihu.
Jin ihunta yasa Sulaiman da ya nufo ɗakin saurin ƙarasowa ya ɓuɗe ƙofar yayinda yaci karo da Sulthana na gudundule a ƙasa bakinta da goshin ta a fashe Zayyad kuwa sai zuba mata masga yake yi.
Tana ganinshi ta jawo hijab ɗinta cike da munafurci ta fara kuka tana ƙudundune jikinta tare da fara ja da baya yanda Sulaiman ɗin zaiyi tunanin ko wani abun daba Zayyad yayi mata,
wani wawan tsawa ya daka mata da saida ya saka numfashin ta tsayawa cakk na wucin gadi
“Shut your filthy mouth up and get out of this room kafin na baki mamaki Sulthana!!!”
Jikinta na tsuma ta zumbula hijabin kafin ta tashi da sauri da jan ƙafa zata fita, saida tazo wucewa ta gaban shi ya bita da wani disgusting look tare da faɗin
“I will deal with you later”
Hakan ya ƙara kaɗa ruwan cikinta taji ta tsure, duk rashin hankalinta bata wasa da fushin babban yaya.
Bayan ta fita ya maido hankalin shi kan Zayyad da ya dafe bango yana maida numfashi duk jikin shi ya gama mutuwa kaman shi aka daka ba shi yayi duka ba, ƙaramin tsaki yaja yace
“Ka shirya ka fito muna jiran ka a parlour.
And don’t waste our time abu mai muhimmanci ne”
Da faɗan haka ya wuce Zayyad ya bishi da kallo, yasan koda na minti ɗaya Sulaiman bai zarge da komai ba da yaga halin da ƙanwar matanshi take a cikin bedroom ɗinshi saboda dukda babban giɓin dake a tsakanin su Sulaiman trusted his little brother so much.
Nitsar da kanshi yayi kafin ya ƙarasa jikin closet dinshi ya ɗauki sweatshirt da wando ya saka ko turare bai tsaya fesawa ba ya fito,
Zaune ya samu aunty tare da sulaiman fuskar ta babu walwala shi kuma ya rungumi wayar shi ya kinshigiɗe a gefen ta yana buga game, ƙura mishi ido tayi kaman mai son gane wani abu a jikin shi har ya samu wuri ya zauna.
“Aunty gani” ya faɗa ganin ya daɗe da zama bata ce mishi komai ba,
“Na ganka ai, ina dai so na tabbatar ba canza mana kai akayi ba, ina tantama idan wannan Zayyad wanda na sani ne Zayyad ɗana gudan jini na”
“Why are you saying this aunty me ya faru Please?”
“Ashe har zaka iya wani abu a duniyar nan ba tare da sani na ba? Abu mai girma kaman niman aure? Zayyad har bani da kima a idanunka da yakai ka fara nima abokiyar rayuwa ba tare da sani na ba? Under my roof?”
Kallon sulaiman yayi cike da takaici don yasan shine ya haɗa mishi wannan bomb din, gyara zama yayi tare da ɗan gyaran murya bakin shi ɗauke da ɗan ƙaramin shu’umin murmushi.
Ƙasa da murya yayi yace
“Aunty I’m sorry! Wallahi ina zuci_zucin sanar dake ban samu dama bane”
“Muna zaune ƙarƙashin inuwa ɗaya da kai amman kace baka sami daman sanar dani zakayi aure ba ina matsayin uwarka?! Muna tare da safe, da rana , da dare amman ka kasa samun daman sanar dani?”
“Aunty I’m sorry”
“Sorry for yourself Zayyad, moreover da ace wata zaka aura zan iya hakura na amince maka amman indai Saudat ce Baka isa ba wallahi, kayi kaɗan ka jawo mana tozarci da abin kunya Zayyad, kana saurayi sabo fill a laida ka rasa wanda zaka auro sai bazawara? Ai matsalar taka yanzu tayi maka maganin shi ko? To Allah ya bata lada amman ba zan lamunci wannan shashancin ba ko kusa”
“Aunty dan Allah kada mu zamo masu mancewa da alkhairi”
“Zan iya biyan saudat alkhairin da take iƙrarin tayi mana, i can pay her any amount that she demand kawai ta faɗa maka abinda take so mu biya ta zan bata yanzun nan ta fita daga rayuwar mu….”
“Aunty habaa….! Ya faɗa a dan hasale amman kafin ya sake cewa wani abu tayi caraf tace
“Wallahi ko ka haƙura da Saudat ko nayi maka Allah ya isa nono na da kasha”
Har Sulaiman saida kalamin ta ya bashi tsoro, Zayyad kuwa sake baki yayi cikin tsananin mamaki da firgici yana kallon mahaifiyar shi,
“Indai kana so mu shirya da kai to ka haƙura”
Yanda zuciyar shi yake bugu ji yake kaman zai fasa ƙirjin shi ya fito, bai taɓa shiga firgici irin wannan ba, idan yaci gaba da tsayuwa a wurin zai iya rasa numfashin shi da azama ya tashi zai bar parlorn.
“Baka ce komai ba” ta katse shi a hanya.
“Na haƙura” shine amsar da ya bata a taƙaice ya wuce bedroom ɗinshi, Sulaiman ji yayi kaman ya tashi ya daka tsalle ya tiƙa rawa yana kwaso shoki saboda murna, today was the best day of his life.
Zayyad na shiga ɗaki ya danna mata key sannan ya zauna a dandamarin ƙasa tare da dafe kanshi da hannun shi yana rewinding abinda ya faru yanzun nan, shine yace ya haƙura da Saudat? Is he not dreaming? He really reject Saudat? Ya rabb!
Kuka mai gunji ya saka kaman ba namiji ba yana fiffisgan gashin kanshi kaman mahaukaci yake faɗe_faɗe,
Yafi 15 minutes yana wannan yanayin, idanunshi sum zama jazur yana jin kanshi kaman ana sarawa da adda, shaƙuwa ya fara yi babu ƙaƙƙautawa cikin lokaci kaɗan ya gama galabaita ya faɗi a ƙasa yana shure_shure…….🧚🏼♀️
Team SS let’s celebrate anyi ma Zayyad leg over😅💃
I mooove🏃🏻♀️🏃🏻♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Ya Allah 😅 i just can’t stop laughing at the sad faces😟😂 jiya anyi zaman makokin da babu mamaci, everyone is saying ba’ayi ma Zayyad adalci ba🤔, hakan na nuna ƴan hannun daman Babban yaya sun fara hijira zuwa wurin Zayd kenan bayan anyi mishi Leg Over 🤣🤣*
*Keep the sad faces babes😩 don’t forget that I love you! because I love losers more🤭🥰😍*+
47🧝🏻♀️
“Wayyo Allah aunty sadiya… Bayana zan mutu!” Shine abinda Sulthana take maimatawa tana murƙusuwa a ƙasan carpet kwanciyan gadon ya gagareta.
Fitowa Sadiya tayi daga toilet ɗauke da ƙaramin towel fari da kuma roba mai ɗauke da ruwan ɗumi ta tsuguna gaban sulthanan tana danna mata raunukan dake jikinta,
“Kema me ya kaiki Sulthana? Wa ya baki wannan gurguwan shawaran da kika je ana niman lahantaki? Wa yace miki haka ake kwace namiji kalli abinda kika jawo ma kanki!”
Ƙwalla ta daɗa matsowa tana yarfa hannu cikin zafin ciwo kaman zata saka ihu tace
“Aunty Sadiya dan Allah ki kaini asibiti zan mutu”
Rike baki tayi tace “kee ina na isa na taka kafa na a waje ba tare da izinin dadyn Arif ba? Yau sauran auren da nake taƙama dashi ma zai iya saka almakashi ya gutsure shi indai a kan wannan maganan ne, ki kalle shi kawai ki barshi indai a kan Zayyad ne bayi da daɗii..
Bari dai na kira doctor tazo gida kawai ta duba ki”
Taimaka mata tayi da ƙyar ta tashi bayan ta gama dubata ta kwantar da ita a gado ta rufa mata duvet kafin ta ɗauki wayan ta ta fice.
*********
Ƙura ma aunty amarya ido dady yayi kaman mai son gano wani abu a fiskanta amman expression ɗinta bai nuna komai ba, her face is just blank.
“Yanda yaron nan ya matsa min a kan zancen yarinyar nan da mamaki ace lokaci ɗaya ya haƙura ya janye ba tare da ya jira ya saurari abinda mukayi da mahaifin nata ba ma”
Tagumi aunty tayi tace “to Alhaji zanyi maka ƙarya ne? Idan Zayyad bai furta ya haƙura ba ai ba zance maka ya faɗa ba, sa’annan ni banma san yaya kukayi da shi ba sai yanzu da ya sanar mana ya janye”
Jinjina kai dady yayi ya juya ya fuskanci Sulaiman yace “kai tashi kaje ka kira min Zayyad ɗin, ina so naji ta bakin shi saboda a fita hakkin shi”
“A’a shi Sulaiman ya zauna yayi mana shaida bari na saka Rumaisa ta kira shi”
Bata jira amsar su ba ta fara ƙwala ma Ruma kira, babu daɗewa sai gata ta iso.
“Aunty gani”
“Kije ɗakin Zayyad kice yazo muna niman shi”
“Toh”tace ta nufi ɗakin.
Cikin nutsuwarta take knocking har na tsawon wani lokaci no response, tura ƙofar tayi a hankali ta shiga tare da sallama amman babu kowa a ɗakin sai tayi tunanin ko banɗaki Zayyad ɗin ya shiga, har zata juya sai ta jiyo tarin shi, komawa tayi tana bin yanda ta jiwo sautin ta hango shi kwance a can gefen gadon a ƙasa yashe kaman gawa.
Cikin sassarfa ta zaga ta ƙarasa gaban shi ta tsuguna tana kallon yanda ya haɗa zufa idanunshi sunyi jawur kaman garwashi ga jikinsa sai shaking yake yi alaman zazzaɓin sa ya ƙaru.
STORY CONTINUES BELOW

“Ya zayd lafiyan ka kuwa?” Ta faɗa cikin muryar damuwa, abinka da mai arhan hawaye har ta fara zubar masa da su.
Ko motsawa baiyi ba yana nan kwance hancinsa ya toshe sai ta baki yake shaƙar numfashi, girgiza shi Ruma ta fara yi da ƙarfi ta saki kuka dan gani takeyi kaman mutuwa zaiyi yanayin shi ya matuƙar bata tsoro.
“Ya Zayyad mai ya sameka ne dan Allah ka tashi mana ko kayi min magana pleeease”
Shiru yayi kaman wanda take da gunki don bayi da karsashin magana a yanzu ya kwanta ne kawai yana jiran mutuwa yaxo ya ɗauke shi tunda an raba shi da jigon rayuwan shi, baiso shigowan Ruma ba samm.
Miƙewa tayi da gudu zata fita taje tayi BBCn abinda ta gani, da sauran ɗan ƙarfin da ya rage mishi yayi amfani ya riƙo ƙafarta, cikin wani faint voice yace
“Ina zakije?”
“Zanje na faɗa ma su aunty halin da kake ciki ne, ka kalli fah baka da lafiya” tayi maganar hawaye na ci gaba da bin kuncin ta.
Girgiza kai yayi a hankali yace “daman me kika zo yi”
“Aunty ne tace nazo na kira ka suna jiran ka a parlourn dady, amman zanje na faɗa musu ba zaka iya zuwa ba”
“No don’t! I will go”
“Ta ina zaka iya tafiya a cikin yanayin da kake, just stay please zan kira su suzo su duba ka”
“No Ruma! I said i will go” ya faɗa tare da dafa gado yana ƙoƙarin tashi, taimaka mishi tayi ya miƙe tsaye sannan ya fara takawa a hankali kaman mai ciwon ƙafa don gaɓoɓin jikin shi gaba ɗaya sun sake.
Saida suka isa ƙofar parlourn yace ta sake shi zai iya ƙarasawa ciki da kanshi da ɗingishi ya ƙarasa shiga.
Sallama yayi musu duka suka juyo suna kallon shi zuciyan aunty Amarya saida ya tsinke da suka haɗa ido dashi, in a matter of hours kalli yanda ya dawo kaman wanda ya shekara yana jinya?!
“Subhanallahi Zayyad baka da lafiya ne?” Dady ya tambaya in a concerned voice.
Girgiza kai yayi cikin maganar shi da bayi fitowa yace
“Bani ɗan jin daɗi ne kawai, but I’m ok now”
“Which kind of ok bayan gaka nan ko tsayuwa da kyau baka iyawa?! Just go back to your room zan kira doctor ya duba ka”
Jan hanci shi yayi dan ya samu iska ya shiga masa cikin fisgan magana yace “no don’t bother dady, yanzu nasha magani idan na kwanta na huta zanji dai_dai.
Ruma tace kuna nima na”
“Kana cikin wannan yanayin ba zai yiwu muyi maganar da muke so d..”
“Me zai hana Alhaji tunda magana ce ta fatan baki kuma zai iya amsawa just ask him what you want to ask”
“Madina kaman kin daina kulawa da lafiyar ɗanki yanzun, ko dan kina taƙama da yanzu babu abinda muke tsoro ne? Amma kada kiyi sake mu koma gidan jiya fah ki guje ma danasani”
Kawar da kanta gefe kawai tayi bata ce komai ba, ya maida duban sa wurin Zayyad yace
“Zo ka zauna”
Babu musu ya ƙarasa ya sami wuri ya zauna,
“Ɗazu munje wurin iyayen Saudat mun tattauna sosai dasu tattaunawa irin ta fahimta, saidai buƙatar da muka je dashi bai ƙarɓu ba, amman ya tabbatar mana idan yarinyar tana son ɗaya daga cikin ku zai bamu saidai ba zai yiwu ku neme ta dukkan ku a lokaci ɗaya ba.
Toh da na dawo na samu zama da mahaifiyarka da ɗan uwanka na samu labarin cewa kai ka haƙura ka bar mishi ita, da gaske ne?” Ya karashe maganar da tambaya.
Da rinannun idanun shi Zayyad ya ɗaga ya kalli Sulaiman kallo mai cike da jin haushi da tsana wanda wannan ne karo na farko da ya taɓa jin haka a zuciyan shi, babban yaya ya kaishi ƙasa da ƙarfi ya raba shi da farin cikin rayuwarshi.
Gyaɗa kanshi yayi a hankali ƙwalla na taruwa a idanun shi yace
“Eh! Na haƙura!!…if…if you will excuse me i will like to go and rest”
STORY CONTINUES BELOW

“Shikkenan jeka Allah ya baka lafiya, idan kaji sauƙi insha Allah zamu zauna kaima ayi maganar haɗa auren ka da Sulthana, saboda inason ganin kaima kayi settling kana da iyali yanzu right”
What?? Three bombs at a time? Bayan da ƙarfi an raba shi da Saudat an kuma bada ita ma yayanshi yanzu kuma ana son yi masa auren dole da wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyar? Me yasa sai shi? Me yasa ko yaushe shine kawai loser? Bai taɓa winning ko sau ɗaya ba why???
Wani abu mai ɗaci yaji ya tsaya masa a maƙogwaro ga zuciyansa dake zafi kaman ana gasa masa shi,ji yakeyi iskan dake ratsowa ta windown ɗakin da na AC duk ya kasa mishi, kaman an jefa shi ne a wani rami aka rufe, he feels suffocated.
Da azama ya tashi zai bar parlourn saidai bai kai ko bakin ƙofa ba ya faɗi a ƙasa ya fara kwararo amai.
Gaba ɗaya hankalin su tashi yayi sukayo kanshi da gudu, duk sun daburce sun rasa Abinda zasuyi masa ɗaya, yana kan harar da abinda ke cikinsa ne ya samu hawayen da yake ta yaƙin tsaidasu ɗazu suka sauko, yana jin maganganun su a kanshi sama_sama da ihun kiran sunan shi da sukeyi da na neman taimako daga sauran mutanen gidan, a hankali idanunsa yake rufuwa har ya dawo bayi ganin komai sai duhu ya daina jin muryoyin su idanun shi suka rufu ruff……
********
Bayan doctorn ta iso ta duba ta ne tayi mata allura tare da bata pain reliever tasha sai a sannan ta samu barci ya ɗauke ta,
Sauƙe ajiyan zuciya Sadiya tayi tana kallon fuskar ƙanwar tata wanda ta haukace a kan soyayyar wanda ya sota a da amman a yanzu bata gaban shi, tasan ƙaramin hukuncin da sulaiman zaiyi mata shine ya saka ta tattara ta bar mishi gida ta koma gidan su aci gaba da kame_kame.
Fita tayi daga ɗakin jin ana kiran sallan isha, taje tayi alwala tayi Sallah sannan ta zaunar da yaranta tana basu abinci da kanta, tana fatan idan yaga hakan ya sassauta fushin sa a kansu, yau ko me yake so yake buƙata zatayi mishi indai zai fasa hukunta Sulthana.
Har zuwa wani lokaci babu shi babu labarin shi, ta kira numbern shi yafi sau a ƙirga bayi picking, hakan ne ya bata daman yin wanka ta sake tsantsara ado cikin ƙananan kaya wanda ya amshi fatar jikinta tayi kyau ba kaɗan ba, sai baza ƙamshi take duk inda ta ratsa amman Sulaiman har yanzu babu labarin shi.
Wuraren 11 ya shigo gidan da dukkan alamu a gajiye yake, tun daga ƙofa ta tsare shi da magana bai saurareta ba yace
“I’m exhausted Sadiya please allow me to rest, sannan idan Sulthana tana gidan nan ki faɗa mata na bata zuwa gobe da safe bani son na tashi na sameta a cikin gidan nan”
Da faɗan haka ko sake kallonta baiyi ba ya fice, daɗin haushinta da yake ji na cewa da akayi za’a aura ma ƙanin shi ita, indai yana raye ba zai taɓa bari hakan ya faru ba, da yaa aure Saudat zai fara niman hanyar da zai raba wancan haɗin don samm bata dace da ƙanin shi ba.
**********
Ruma ce zaune a gefen Zayyad dake kwance a gado unconcious an saka mishi drip, fuskarta a kumbure wanda ke nuna irin kukan da ta sha,
Shigowa aunty Amarya tayi bayan ta sallami sauran mutanen da suka cike ɗakin da suje ɗakunan su su kwanta itama fuskar nata ya hau suntum.
“Rumaisa” ta kira sunanta cikin dakewa,
Juyowa Ruma tayi tare da amsawa aunty taci gaba da cewa
“Kada naji abinda ya faru a wani waje, bani son kowa ya san abinda ya sami Zayyad musamman Saudat da duk wani nata, nasan yanda kuke ƙawance kece kawai kika san da abinda ke tsakanin su so don’t tell her he is sick”
“Amman aunty me yasa?” Ta faɗa tana shirin ci gaba da kuka
“Bani da wani dalili just do as you are told ok?”
“Ok” ta amsa hawaye na bin kuncinta na tausayin Zayyad da Saudat ɗin, tun yanzu ta fahimci raba su ake son ayi da ƙarfi.
****
Washegarin ranar Fa’iza ta rubuta letter ta tura ma Saudat makaranta a kan halin da Zayyad yake ciki, delay ɗin kwana ɗaya aka samu kafin saƙon ya isa gareta, lokacin da ta buɗe ta karanta abinda ke ciki kuka ta dinga yi wanda har itama ya sauƙar mata da zazzabi mai zafi ta bar cin abinci kullum idan ta zauna bata da aiki sai na kuka abin har ya fara damun staff da masu kula dasu, cikin Sa’a sun gama waec kuma ba’a sa sallamar su harsai sun kammala neco amman saboda akwai ɗan tazara a tsakanin su sai makarantar ta bada dama ta dawo gida tayi jinya.
STORY CONTINUES BELOW

Zayyad kuwa tunda ya farfaɗo ya daina kula kowa bayi yarda yayi magana da kowa a gidan ciki kuwa harda mahaifanshi, idan aka zauna aka matsa mishi da tambaya kuma sai ya juya ya baka baya har sai ka gaji da zama ka tashi ka tafi, ko sannu akayi masa bayi amsawa ya dawo kurman dole bayi uhmm bayi uhm_uhm. Kullum aunty ne mai kwana tare dashi bata yarda wani ya zauna a wurinsa kada somehow a warware abinda suka ƙulla,
Ko wani dare sai ta kawo mishi maganar yayi haƙuri ya cire Saudat a ranshi sai ya juya mata baya yana zuban hawaye wani lokaci har bacci ya ɗauke shi a haka, wayan shi kanma bai san a duniyar da ya jefar dashi ba, wanda Saudat tana ta faman kira switch off, gashi Yusrah ta hana ta zuwa gidan ta ganshi saboda a yanzu kaman surkuwar gidan take, kuma shima ba budurwar Zayyad ɗin ba na yayanshi.
********
02:07am
A hankali ya buɗe idanunshi da sukayi mishi nauyi yana kallon ceiling ɗin ɗakin da yake ciki, bedroom ɗinshi ne ba tantama motsin mutum da yaji a gefen shi ne ya saka shi juyawa ya hangi aunty a saman darduma tana Sallah kaman kullum.
Daddafawa yayi ya tashi ya zauna ya jira har ta idar sannan yace mata zaisha ruwa, jikinta na rawa ta zubo mishi a glass cup ta kawo mishi, hannun shi na hagu ta dunƙule cikin nata biyu tare da ƙura masa idanu yayin da yake shan ruwan shima idanun shi yana kanta, he can see tana cikin damuwa.
Rabi yasha ya miƙa mata cup ɗin ta karɓa ta ajiye, sannan yace
“Aunty dare ya raba tuntuni me yasa baki je kin kwanta ba?”
“You are not fine Zayyad ta ina zan samu kwanciyan hankalin rintsawa?”
“If you care so much about me then why did you do that to me?
Baki tsaya kin saurari bayani na ba kika yanke hukunci? me saudat tayi miki da kika mata irin wannan tsanar? A iya sanina da ita na tsawon shekaru she has been a good girl”
Jinjina kai tayi tace “I’m happy that you finally decided to talk and sort things out.
Ni mahaifiyarka ce Zayyad i know what is best for you, and ban tsani Saudat ba ko kaɗan, idan ban ƙaunaceta da duka zuciyata ba a wurina ta wuce matsayin tsana”
Shiru yayi ya zuba mata ido alaman yana buƙatar ƙarin bayani, taci gaba da cewa
“Tun farkon tasowarka a cikin gidan nan a matsayin mai rauni babu wanda ya nuna maka tsananin ƙauna bayan mu iyayenka kaman Sulaiman.
Yana tare da kai lokacin da kake rarrafe har ka fara tsayuwa kazo ka fara tafiya, lokacin da wannan lalurin ya riske ka ma Sulaiman is always there by your side, a lokacin shima da yarinta sosai a jikin shi amman haka yake taya ni kula da kai, hakan yasa bani da wani addu’ar da ya wuce kada Allah Ya gwada min ranar da kanku zai rabu, ina so ko bayan raina ya zama Sulaiman ne mai kula da kai koda ka kai matakin tsufa kuwa.
Ba sai na tuna maka ba Zayyad kaima kasan adadin sadaukarwar da sulaiman yayi maka masu girma ba zasu ƙirgu ba, me yasa kaima ba zakayi sacrificing wani abu gareshi ba, just once please! Nasan da ciwo sosai amman Sulaiman zaiyi farinciki, he will be happy!”
Sunkuyar da kanshi yayi yana kallon hannun su dake sarƙafe da na juna, he found himself speechless, yana so yayi kaman yanda aunty tace amman yana ji kaman ba zai iyaba
“Da wahala” ya furta cikin raɗa.
“Na sani Zayyad but you have to try! Ka saka ma ranka Allah yayi ba saudat bane matarka ita ɗin kawai ƙaddararka ce wanda aka jefo ta cikin rayuwan ka don a jarraba imanin ka, kayi ƙoƙarin cire ta a zuciyan ka kana addu’a Allah ya musanya maka ita da mafi alkhairi and get back to work soon please too many lives depends on you and keeping yourself busy zai rage maka tunani, kwana biyar kenan kana kwance a ɗakin nan baka bani daman magana da kai ba sai yanzu”
*********
Yau baba ya kirani a kan amincewata kan izinin neman auren na da sulaiman yake yi, na amince ko kuma bana so?
Bayan mun gama magana da baba ne na fito parlour na sami Yusrah tana yiwa Jannat assignment,
Zama nayi a gefenta na rafka uban tagumin da ya jawo hankalin yusran tace
“Saudat ke haka zaki ƙare kenan kullum kina cikin damuwa, daga kuka sai tagumi?”
“Uhmm aunty Yusrah ba dole ba, ban tsallake matsala ta farko ba na sake faɗawa wani, kinga har yanzu ban samu munyi magana da hamma zayd ba gashi baba ya kira ni a kan maganar kwanaki.
Tun ranar da mukayi magana dashi a school yace zaiyi handling komai har yanzu bai bani feed back ba”
Sauƙe ajiyan zuciya Yusrah tayi tace
“Zan shawarce ki da ki haƙura da batun Zayyad ɗinnan Saudat”
Wani banbaraƙwai naji kalaman nata don basu bada ma’ana ba cikin kwakwalwata ma ni za’a cewa na haƙura da Zayyad ? “Huh… Me yasa zakice haka aunty Yusrah? Ba kece kike faɗa min nabi abinda zuciyana yake so ba? and that’s Zayyad!”
“Saudat ki fahimce ni, banyi niyyan ɓoye miki komai ba wallahi amman a cikin yanayin da kika dawo gida bani son sake ɗaga miki hankali shiyasa na bari har sai jikinki yayi kyau na faɗa miki.
Abban Jannat yayi magana da baba kwanaki, kuma shi da bakin sa ya shaida masa cewa Zayyad ya haƙura da auren ki ya janye, yanzu ra’ayin ki da ake son ji kawai a kan boss Sulaiman ne, ko kin amince zaki aure shi idan kuma kinƙi shikkenan sai a bashi haƙuri ke kuma ki jira har zuwa lokacin da Allah zai kawo miki wani mijin ki aura”
Bansan lokacin da hawaye suka gangaro min ba, hannuna na rawa na nuna kirjina tare da faɗin “nice Zayyad yace ya haƙura da ni?…. Ko shine dalilin da yasa ya kashe min waya? Idan na kira ƙannen shi su haɗa ni dashi sai yaƙi magana dani! At least i deserve an explanation, me yasa zaimin haka?”
“Ban sani ba Saudat, kawai kiyi haƙuri Allah zaiyi miki sakayya”
Murmushi mai ciwo nayi nace “hmm daɗin abin ba rasa mijin aure nayi ba harda Zayyad dai tozarta ni haka”
Wayana dake ringing na ɗago na duba cikin Sa’a naga matar ya Aminu ce, dukda nasan ta kira ni ne saboda wani dalili daban bayan nayi picking ban tsaya sauraronta ba nace
“Aunty ki cewa Innata ta faɗa ma baba na amince zan auri hamma Sulaiman………….🧚🏼♀️
_I tried my best to make this chapter quite emotional 😧 i hope team SZ heart will drop a bit😢😩_
😂😂😂😂🤪
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.+
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
48🧝🏻♀️
08:36am
Ruma ce zaune a main parlour cikin shirinta na zuwa makaranta, atamfa ce red a jikinta ɗinkin riga da skirt ta ɗan yafa madaidaiciyar gyalenta a kafaɗa da wayanta a hannu tana dannawa, tana zaman jiran Zayyad da yayi mata alƙawarin zai sauƙeta a makaranta ya gama shiryawa ya fito.
Knocking ƙofa akayi ta ɗago tana kallon wurin tare da faɗin “come in” da ɗan ƙarfi, a take aka buɗe ƙofar kai gadi ya bayyana a tsaye cikin uniform ɗinshi na aiki hannun shi ɗauke da farin envelope.
Miƙewa Ruma tayi ta ƙarasa wurinda yake tsaye suka gaisa sannan take tambayar takardan hannun shi na menene.
“Saƙo ne aka kawo ma oga Zayyad” ya faɗa tare da miƙa mata tasa hannu ta karɓa sannan tayi mishi godiya ya tafi.
Jujjuya envelope ɗin tayi tana nazari wannan dai baiyi kama da wani official letter ba saboda babu tambarin wani Company ko industry a jiki, tukunna ma yanzu ana turo saƙon takarda ne? Idan mail ne ta email ɗinshi ya kamata a turo idan kuma message ne sai a turo mishi ta waya.
Curiosity ba zai barta ta kai ba tare da tasan abinda ke ciki ba tayuyu ma blackmailing ɗinshi ake son yi, hakan yasa kawai ta bude envelope ɗin ta zaro takardan ciki ta warware shi ta fara karantawa kamar haka.
”’Assalamu alaikum”’
”’morning greetings to someone i once called mine. I’m sorry for disturbing you once again, ba zan iya daurewa bane na jure rabuwa irin haka ba tare da munyi kyakkyawan sallama ba. Bansan me ya shiga tsakanin mu har ya maida alaƙar dake tsakanin mu ya zamo haka ba, amman koma me yasa nasan tsarin Allah ne kuma hakan shine daidai.”’
”’well daman na dawo gida ne da na samu labarin cewa baka da lafiya, i was really worried amman an faɗa min yanzu jikin da sauƙi, so alhamdulillah yanzu zan koma naci gaba da karatuna wataƙil kuma wannan ne karo na ƙarshe that i will look at you with affection, I’m getting married now Zayd! wish me luck”’
Your’s sincerely
Saudat Habib.
Jikin Ruma na rawa ta naɗe takardan cikin hanzari ta nufi corridorn da zai kaita ɗakin Zayyad batayi nisa ba ta jiyo muryar aunty Amarya a bayanta tana kiran sunan ta,
Dakatawa tayi tare da juyowa riƙe da takardan a hannun ta,
“Meye wannan? And why are you in a rush?” Aunty ta tambaya lokacin da ta saka hannu ta amshi takardan ba tare da wani tunani ba ta buɗe don ganin abinda ke ciki.
Ruma dai tana tsaye duk ta gama daburcewa ta kasa cewa komai har saida ta auntyn gama karantawa, ranta a ɓace ta ɗago tana kallon ta
“Duk kashedin da nayi miki saida kika faɗa ma Saudat Zayyad yayi rashin lafiya! Kalli Abinda kika jawo, da yanzu takardan ya isa wurin shi mai kike tunanin zai faru?”
Jikinta yana rawa tace “aunty wallahi bani bace, Fa’iza ne tayi mata letter ta tura mata school kuma na faɗa mata kin hana”
Jinjina kai tayi tace “i will deal with her, kuma kada ki kuskura ki faɗa masa komai akai kinji ko?” Gyaɗa kai Ruma tayi tace “ɓace min da gani”
Juyawan da zatayi suka hango Zayyad ɗin tsaye a ƙofar ɗakin yana kallon su.
Jikin su duka mutuwa yayi, shikuwa ganin haka yasa ya ƙaraso bai ko kai idon shi kan takardan ba yayi ma aunty sallama kan zai wuce office ya bama Rumaisa briefcase ɗinshi ta riƙe suka fita.
STORY CONTINUES BELOW

***
Driving yake yi da hannu ɗaya ɗayan kuma ya ɗaura elbown shi a jikin window ya dafe kanshi dashi, rabin kallo ma kaɗai ya isa ya ganar da kai yana cikin damuwa.
Kallon shi Ruma tayi tace “Ya Zayd ba zaka tambayi lettern nan daga wurin wa yazo ba?”
Shiru yayi kaman bai jita ba yaci gaba da driving ɗinshi, tace “daga wurin Saudat ne”
Gyaɗa kai kawai yayi tare da shan kwana suka hau kan wani titin da tsirarun abun hawa ne suke bi don yayi bayan gari da yawa.
Ci gaba tayi da cewa “ba zaka so ka san abinda ke ciki ba?”
Girgiza mata kai kawai yayi, ta ƙura ma fuskar shi idanu tana karanta expression ɗinshi, he is hurt deep inside amman an tilasta mishi ɓoyewa.
“Amman kasan da taji baka da lafiya ta bar makaranta ta dawo gida saboda kai?”
Saurin juyowa yayi ya kalleta cike da mamaki don shi ko labari baiji ba,
“Yes itama tayi rashin lafiya sosai a lokacin aunty ne ta hana mu faɗa maka, but i cannot hold it any longer”
Tana jin sautin songon numfashin da yaja haryanzu dai bece komai ba.
“Sannan a cikin takardan ta rubutu cewa….” Sai kuma tayi shiru tana kallon shi don tasan abinda zata faɗa mishi yanzu zai iya tarwatsa mishi zuciya
“Cewa zatayi aure” ta ƙarasa murya can ƙasa kaman mai raɗa.
Bata rufe bakinta ba hawaye mai ɗaci ya gangaro da gudu daga idanun shi ɗaya ɗayan kuma na bushe ƙarau, irin wannan kukan ne mai cin zuciya, a cikinta babu wani sauti.3
“Don’t hold it in ya Zayd zai cutar da kai, cry out loud if that’s what’s going to make ur heart ease all the pressure”
Parking yayi a gefen hanya ya kifa kanshi a cikin tafin hannun shi yana kuka jikin shi sai wani irin shaking yake yi, sunfi 20 minutes suna tsaye a wurin kanshi a kife yana zubar da hawaye masu tarin yawa. Patting ɗinshi a baya Ruma ta farayi tana rarrashinsa da kalamai masu kwantar da hankali ganin kukan ya fara yawan da zai iya saka mishi ciwon kai, saida ya nitsar da kanshi kafin suka ɗauki hanya
**********
Sulaiman na samun labarin an bashi dama babu ɓata lokaci ya sake ɗaga su dady a Ranar suka kai goro da sadaki aka saka aure sati biyar lokacin Saudat ta gama neco da sati guda kenan, lokacin da ake can ana tattaunawa shi kuma ya saka ta haɗa kayanta a kan cewa yau da kanshi zai maidata makaranta don su samu daman zantawa.
****
Saida Zayyad ya ajiye Rumaisa a school kafin ya ɗau hanyar office.
Da shigan shi yasha mamakin ganin table ɗinshi almost empty, yayi tunanin fashin kwanakin da yayi zai dawo ya samu files sun cika table ɗin har suna zuba saboda yawa amman Sulaiman duk yasa an tattara su don dama da mugunta yake tara masa aiki, file guda biyu ne kacal wanda suke zaman jiran shi su ɗinma don tilas shi ake buƙatar ya duba ya saka hannu ne amman da ba zai samu wani aiki ba idan yazo.
Hakan ya bashi daman zama ya ciro wallet ɗinshi daga aljihu yana kallon hoton Saudat wanda yayi mata shi a ranar da ya fara ganinta a parlourn Hajiya ranar da ta dinga murguɗa mishi baki tana hararar shi.
Hannu ya saka a kan fiskarta yana shafawa a hankali zuciyar sa na tunano masa beautiful moments da sukayi spending tare da ita da Ruma ko yaushe a tsakanin su.
Zare hoton yayi bayan ya gama kallo ya miƙa hannu jikin ɗan dustbin ɗin dake gefen kujerar shi zai jefar sai kuma ya fasa, zuciyan shi ba zai barshi ba, he cannot get rid of her memories just like that.
Koda bai sameta ba zai bari memories ɗinta suna rage mishi kewarta don koda ta auri Sulaiman bayi tunanin zai bar sonta, he will always love her… always!!
*********
Tunda na shiga motan nake jina a takure, ga tunanin Sulaiman mai sanyin ƙamshin da a duk lokacin da najishi yana saka min tunanin Zayyad don shi kwata_kwata bayison irin turaren, yafi son saka wanda daga nesa kafin ya ƙaraso ƙamshin zai riske ka amman bayi bumbuɗa shi da yawa yanda zai saka wanda ke tare dashi mura ko ciwon kai.
STORY CONTINUES BELOW

Kwantaccen murmushi ne a fuskar shi daga gani yana cikin nishaɗi wanda ni kuma opposite ɗinshi ne a gare ni, saida na ganni gani ga babban yaya nake danasanin hukuncin da na yanke fushi kuma a sanadiyyar haka zan kasance tare dashi har abada.
Tunda na gaida shi naja bakina nayi shiru saida tafiyan mu yayi nisa kafin ya fara magana
“Yanzu auren mu sauran 5 weeks, that’s one month and a week”
Dummm naji ƙirjina yayi wani mugun bugu abinda nake tunanin da nisa yazo kusa ban sani ba.
Murmushi mai sauti Sulaiman yayi yace
“I will finally get to be with you, zaki kasance a ƙarƙashin inuwar aurena ni kuma zan zama uban ƴaƴanki, I’m happy! Kefa?”
Da ƙyar na iya gyaɗa kaina tare da kallon ƙasa ina murza yatsuna da ƙarfi cikin zafin zuciya, kallo na yayi a taƙaice ya maida duban shi kan hanya tare da yin dariyan da zan iya cewa yaune rana ta farko da na fara ganin irinsa a fuskar shi.
“You are shy ba? Don’t worry kwanan nan duk wani hijabi na kunya dake tsakaninmu zai yaye”
Sai naji zuciyana ta sake wani nauyi babu wanda nake gani a idanuna sai Zayyad, maybe he is in pain maybe he is not.
Ina taraddadin wani yanayi yake ciki a yanzu i really want to know how he is doing.
Hawaye ne naji sun fara sauƙo min ba tare da sani na ba, saurin saka ƙasan hijab ɗin uniform ɗina nayi na goge ba tare da na bari ya lura ba.
“Well bani son mu fara maganar shirye_shirye tun yanzu ne kada ya hana ki karatu gwanda idan kin gama exams ɗinki sai ayi duk abinda za’ayi ko?”
“Eh” na amsa a taƙaice dan kada yaji shiru na yayi yawa ya kawo wani abu a zuciyan shi.
A haka muka isa ya taya ni fitar da shirgin da muka zo dasu daga booth ɗin mota masu aikin makarantar suka karɓa suka shigar min dashi daga nan mukayi sallama dashi ya tafi.
Tun daga wannan ranan nake saka kunne ko zanji zuwan wani saƙo daga wurin Zayyad amman har yanzu shiru, nayi kuka nayi baƙin ciki har na gode ma Allah ƙawaye na na makaranta duk sun shiga damuwa da sabon canjin yanayi na, wani lokaci muna cikin exams ma idan abun ya taɓani sai na yarda biro na saka kuka gashi idan za’ayi min tambayar duniyar nan bani taɓa cewa kowa komai.
Dalili kenan da yasa lokacin da abin ya ishe su suka kira Sulaiman yazo shima yasa ni a gaba wai sai na faɗa mishi abinda yake damuna.
Inada wani babban abin damuwa da ya wuce shi ne? Shima dai haka ya ƙaraci fitinar shi ya tafi wai yayi fushi amman na tsorata sosai da yanayin shi shiyasa tun daga ranar na kama kaina na daina yawan koke koken nan har muka samu muka gama exams lfy.
*****
Tashin hankali wai ranar Aure na ne nake iya ƙirga su da yatsun hannu na, sauran 6 days fah! Gashi har sun fara min wani gyaran jiki da ni ba amfani zaiyi min ba saidai shi Sulaiman hala ya amfana, sun matsa min da wasu shaye_shaye da dure_dure haka nake binsu ina tayi babu musu dan bani mararin abinda zai ƙara min wani damuwan akan damuwata komin kashinsa kuwa.
Yau da safe na shirya sulaiman daizo ya ɗauke ni zamuje ayi wa indo registration ɗin makaranta yace idan mukayi aure zata zauna tare damu ne taci gaba da karatu ba zata koma wuroɓokki yanzu ba.
Saboda delay ɗin da muka samu wurin cike_cike gashi yana da wurin zuwa yasa ya tafi ya barmu a wurin ya turo driver yazo ya jiramu idan mun gama sai ya maida mu gida.
Bayan mun shiga motan ne nayi ma drivern kwatancen gidan aunty Aisha ƙawar aunty Yusrah saboda yafi kusa da office ɗin su Zayyad, nace ya sauƙe mu a can ba gida direct zamu ba inyaso daga baya sai ya dawo ya ɗauke mu.
Yana tafiya na shiga na ajiye indo a wurin aunty Aisha na fito da ƙyar don taso riƙe ni saida nayi wasu ƴan dabarbaru na haɗa da ƙarya sannan na samu ta barni, ina fitowa na tsari keke napep ya kaini companyn su.
Tun da na kalli wurin naji zuciyana yana tafarfasa tunawa da mutumin da nake hora zuciyata a kanshi yana cikin wannan building ɗin yana gudanar da hidiman business ɗinshi ba tare da wani damuwa ba, sanin cewa babu wanda ya sanni a wurin ballantana a kaiwa Sulaiman gulma, cikin Sa’a nasan floor ɗin da office ɗinshi yake da direction ɗin wurin don komi na Zayyad idan yayi sai ya sanar dani.
STORY CONTINUES BELOW

Lifter na shiga ya kaini floor ɗin kaina tsaye na wuce inda office ɗin yake zan shiga sakatariyan shi ta dakatar dani, dake raina a ɓace yake ban tsaya binta a hankali ba haka na tsaya cecekuce da matar da aƙalla zata bani shekaru uku ko huɗu abun har yaso kaimu ga faɗa don dagewa tayi da bazan shiga ba.
Muna cikin kokuwa na samu hannu na yakai jikin handle ɗin ƙofar office ɗin na buɗe shi.
Yana zaune a saman babban working table ɗinshi ƙafafunsa a kan chairs da aka tanada na baƙinsa hannun shi riƙe da iPad yana duba samples na design ɗin sabon project ɗinsu.
Sanye yake da farin T-shirt da baƙin jeans sai fararen booths a ƙafanshi kayan ya amshe shi sosai da ya rage nuna damuwan da yake ciki.
Ɗago ido yayi yana kallon yanda nake faman kokuwa da sakatariyan shi baisan lokacin da ya durƙo da sauri ba yana daɗa ƙura min ido dan tabbatarwa ni ɗince yake gani da gaske amaryan kwana shida.
“Khadijah let her go!!” Ya faɗa a tsawace da ya saka sakatariyan tsayawa cakk tana zazzare idanu don ya shammaceta matuƙa, bata taɓa jinshi ya ɗaga ma wani murya ba ballantana yayi ma wani tsawa.
“Saudat?” Ya kira sunana cike da mamaki, ban amsa ba sai juyawa nayi na rufe ƙofar a kan fuskar sakatariyan tashi na juyo har lokacin yana tsaye a wuri ɗaya, sai kuma naji duk fushin da nazo dashi ya riƙide zuwa baƙin ciki jin haushi da kuma kewa.
Rabona da ganin shi yafi watanni uku ta yaya ma akayi na iya rarrashin zuciyana bata tarwatse ba har yanzu? I missed him like hell.
Hawayen da a yanzu suka zamo abokan rayuwana ne suka fara zubowa, nayi wurgi da jakan hannu na sannan na ɗa mikar da hannayena sideways.
“Look at me Zayyad! Ka kalle ni!! Look at what I have became because of you!!!
Did i look miserable enough to make you happy?”
“Saudat me kike faɗa haka ne?” Ya faɗa cikin murya mai rauni,
Dai ci gaba da magana nayi saurin dakatar dashi
“Kayi min shiru dan Allah, baka da abinda zaka faɗamin a yanzu ka riga da ka yaudari zuciyata Zayyad.
Nayi zaton kai jarumi ne da zakayi yaƙi don ganin mun kasance tare but you gave up without a try, how unfortunate!”
“Saudat listen to me….”
“What will i listen to? Baka da abinda zaka faɗamin Zayyad, daman nazo ne na faɗa maka daga wannan lokacin kada ka kuskura ka sake gwada min fuskarka, i don’t want to see you ever again!!”
Da faɗan haka na suri jakana fuuu na wuce, saurin bina a baya yayi yana kiran sunana naƙi sauraron shi har muka fita a office ɗin yana biye dani, ganin rangaɗa min kiran da yake yi ya fara jawo attention ɗin mutanen wurin kanmu yasa na juya tare da gwada shi da yatsa.
“Stop following me Zayd! I’m warning you!!” Da haka na zabga mishi harara na juya na bawa khadija ma nata nayi gaba abuna.
Suman tsaye mutanen dake kai komo a floor ɗin sukayi ganin ƴar ficilan yarinya tana kashewa ogansu warning harda gwada shi da yatsa amman ya kasa min komai, abin ya matuƙar sha musu ruwan kai bawai don shi mutum ne mai zafin rai ba A’a saidai yanda yake bayi hulɗa da kowa bayi magana ma kowa musamman ƴan watanni da suka wuce mutanen da suka sanshi a wannan lokacin ma idan ba an faɗa musu ba sukanyi tunanin kurma ne.
**********
Zuwana wurin Zayyad kaman ƙara min fushi yayi ba rage min ba,
Zama nayi nayi karatun Alqur’ani sosai sannan na ɗanji dama_dama, sannan na hau gado na kwanta gashi yanzu bani aikin komai an hana ni koda shara ne shiyasa duk nabi na gundura da zama.
Wayana na jawo na kunna data don na ɗan sami abinda zai ɗebe min kewa.
Ina shiga whatsapp kaman a mafarki naga Zayyad online,
Babu ɓata lokaci na hau kan numbern shi na fara tura masa messages.
“Ka cutar da zuciyata,
Ka saka ni kuka Zayyad ba zan yafe maka ba,
Saida ka tabbatar ka dasa min sonka a zuciyana ka tafi ka barni,
i will never forgive you,
I will never love someone like you again,
I don’t want to see you again,
I miss you no more,
I don’t love you anymore,
I hate you.”
Duka a jejjere nake tura masa ina ganin blue tick alamun yana gani a lokacin.
Baisan me yasa ma ya hau online ba gashi yana ganin abubuwan dake ɓaɓɓalla mishi zuciya.
Rasa me zai cemin yayi, idan yace zai furta wani abu ko zai rubuta fallasa sirrin zuciyan shi kawai zaiyi.
Ina zaune ina jira naga shigowan audio da sauri na buɗe, it’s that my favorite song, that song that will express all his feelings, the feeling that shows how much he miss me. I MISS YOU BAD by mr Eazi ft burna boy.
Playing waƙan nayi ina kuka banji yafi rabi ba na kashe, don ji nake kaman yana faɗa min Zayyad na ƙaunata har yanzu.
Cikin fushi naci gaba da tura masa messages.
“Maƙaryaci,
Mayaudari,
Ka ha’ince ni Zayyad
You are a cheater
I hat…”
Tsayawa nayi da rubutu ganin dpn shi ɓatt ya ɓace lokaci ɗaya kuma saƙon tick ɗaya yake gwada min ba biyu ba alamun yayi blocking ɗina kenan, daga nan na jefar da wayan na rungume pillow a ƙirjina naci gaba da kuka.
*******
Ba zai iya jure kalmar tsana daga wanda yake ƙauna fiye da kowa a matan duniyan nan ba, shiyasa kawai yayi blocking ɗinta kada ta ƙarasa shi.
Da ta san irin azabtuwan da yake yi nata ba komai bane, yau kawai da ya ganta yaji hankalin shi ya ɗan kwanta,
Saboda rashin ganinta he becomes miserable, baya cin abinci bayi bacci, bayida kwanciyar hankali bayida nutsuwa. All he needs now is Saudat.2
*****
Kwanaki sun shude kaman ƙifatawar ido, yaune ranar da duniya zasu shaida Saudat a matsayin mallakin sulaiman idan Allah yaso.
Jiya sukayi walima da ita da ƙawayenta don tace ita bata son komai kuma Sulaiman ya goya mata baya don shima bayi son kayan hayaniya, da ƙyar aka sakata yin waliman ma a dole don dayawan mutane basu san da cewa ita bazawara bace, ana gamawa aka tattareta aka maida ta gidan ubanta don a can garinsu za’a ɗaura aure.
Ɗakin a cike yake ango da abokansa suna ta faman shiri, Ahmad ne ya shigo cikin ɗan damuwa yace
“Sulaiman banga Zayyad bafa”
Ƙaramin tsaki yaja yace “yanzu kuma ina yaje dan Allah yana ganin lokaci na ƙure mana? Ka duba bedroom ɗinshi?”
“Yes nah, tuntuni na faɗa maka yana rufe”
Fita yayi da kanshi yaje part ɗin aunty Amarya daidai yana shiga ita kuma tana fitowa, gaba ɗayanta a dame take ta gama birkicewa.
Kafin yace wani abu tace
“Sulaiman ka taimaka ka taya ni niman Zayyad security sun tabbatar yau ko ƙofa bai fita ba yana cikin gidan nan amman bansan a ina yake ba kada wani abun ne ya same shi, help me pleease”
Da gudu ya ƙarasa ƙofar ɗakin shi yana bugawa da dukkan ƙarfin shi kaman ance mishi nan yake amman yaƙi buɗuwa, kitchen ya shiga ya ɗauko tukunyar gas ya dawo yana dukan ƙofar dashi, cikin Sa’a aka samu ya buɗe.
Daga can suka hango Zayyad kwance a ƙasa a sume jini na fita daga bakinsa………..🧚🏼♀️
Love You my fans❤️
#team amarya da ango 🥰🤧
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Sorry for the delay👏👏, ina ɗan fama da mura ne na kwana biyun nan irin mai saka ciwon kai shiyasa kuka jini shiru*
49🧝🏻♀️ (A)
kwance nake a ɗaki tare da wasu daga cikin ƙawayena dake ta faman shiri domin da an sauƙo daga ɗaurin aure za’a zo ɗaukan amarya saboda wuni ɗaya za’ayi a yau ɗin za’a kaini ɗaki na.
Wani irin mummunan bugu zuciyata tayi yayin da na jiyo sautin guɗa daga tsakar gidan mu da shewan mata suna faɗin shikkenan an ɗaura, ɗaukan wayana nayi na kunna ina kallon lokaci 11 har da minti 30, kifa wayan nayi a kan gadon da nake kwance na fasa ihu ina birgima inajin zuciyata na ƙonewa.
Shikkenan rayuwata ta gama lalacewa daga yanzu nayi bankwana da abin sona har abada, Zayyad ya riga da ya haramta min ni da shi mun tashi daga matsayin abu guda mun koma abubuwa guda biyu ma banbanta. Rayuwana ta ƙare….. I have no reason to live anymore…..+
Kuka nake yi kaman raina zai fita, wallahi sai yanzu nasan nayi kuskure da na zabi auren babban yaya, indai ba Zayd na samu a mijin aurena ba da haƙura nayi na ƙarasa rayuwana ba tare da nayi aure ba zaifi min.
Shigowa Hanan da innata sukayi da sauri da sula jiyo kukana, ta hawo gadon tana riƙoni ina zamewa kaman karkashi.
“Lafiyan ki kuwa Saudat? Ko wani abu ne ya faru dake ki faɗamin Please”
Murmushi Inna tayi hawaye na bin idanunta ta, tasan wataƙila saboda taraddadin sabon rayuwan da zan shiga ne nake haka, wataƙila baƙin cikin sake rabuwa dasu ne ya jawo haka, wataƙila kuma don sai yanzu ne na girma nayi hankali nasan mai aure yale nufi shiyasa haka. Amman a aurena na farko ban gwada wani act na kunya ko damuwa ba illa murna da rawan kai da na dinga yi har saida na jawo musu magana wurin mutane.
Riƙo hannuna inna tayi ta ciro ni daga jikin Hanan sannan ta saka ni a jiknta ta rungume tana ƙoƙarin tsaida hawayenta don ta sami daman rarrashina.
Sake ruƙunƙumota nayi kuka na yana daɗa ƙuntata, inajin kaman na faɗa ma Innata na fasa auren na yafe. I cannot imagine living in the same place as Sulaiman, lying on the same bed as him, serving him, bayan ga Zayyad ɗina a can yana rayuwa shi kaɗai.
Har saida naci kukana na ƙoshi kafin Inna ta gyara min kwanciya a kan gadon tace nayi barci na huta kafin muzo tafiya kada kaina yayi min ciwo.
Ciwon kai na gobe kuma?
Tattaran sauran mutanen ɗakin hanan tayi suka fita don a barni na huta, ina ganin haka bayan ƴan mintuna na siɗaɗa na gudu daga gidan ba tare da na bari wani ya lura ba.
*********
Tsugunawa Sulaiman yayi a gaban aunty Amarya dake zaune a kan waiting chair na asibiti tana sharɓan kuka, riƙo hannunta ɗaya yayi ya dunƙule cikin nashi don ya sama mata nutsuwa shima idanunshi sun gama kaɗawa sun sauya kala.
“Aunty” ya kira sunanta cikin nutsuwa, “Zayyad will be fine i promise you, ki daina damuwa, ki daina kuka and pray for him, he will be alright insha Allah”
Ɗayan hannunta ta saka ta share hawayen dake zubo mata cikin kasashshiyar muryaa tace “idan wani abu ya shame shi fah? Ba zan iya yafe ma kaina ba, duk halin da ya shiga nine sanadi, what if zuciyan shi ta buga and i happen to lose him” ta ƙarashe maganar tare da sakin kuka mai gunji.
STORY CONTINUES BELOW

“Stop crying please, Zayyad wil be alright insha Allah kukan ki ba amfani zaiyi mishi ba”
“Duk abinda nake so Zayyad na ƙoƙarin yimin shi bai taba gajiyawa ko sau ɗaya amman gashi a karo na farko ya kawo min tashi buƙatar na gaza har ina niman saka mishi ciwon zuciya, what kind of a mother am i?”
“It’s not your fault aunty, idan akwai wanda ya kamata a ɗaura mishi laifin abinda ya samu zayd to nine, amman na daidaita komai yanzu insha Allah, Zayyad Saudat yake so kuma yanzu ya sameta, yanzu SAUDAT MATAR ZAYYAD CE, an riga da an ɗaura musu aure ta zamo tashi da mun samu ya farka babu sauran wani damuwa, so cool your mind please” ya ƙarasa tare da tashi ya koma gefenta ya zauna tare da saka hannu yana patting bayanta a hankali yana jin yanda take sauƙe ajiyan zuciya.
**********
Da guduna na shiga gidan su furere, gidan da ya kasance min wurin ɓuya ko ince wurin tsira lokacin ƴammatanci na kafin ƙaddara ta zo ta raba tsakanin mu, ko laifi nayi a gida ko ina wasan ɓuya da ƙawayena bani da gurin ɓoyewan da ya wuce gidan su furere, ita da mahaifiyarta na hango zaune suna aiki, da ganina ta miƙe bata san ma ta kifar da garin da ke kan cinyarta tana tankaɗewa ba, dage ƙirji tayi tare da ƙwalalo idanu tana kallona ta kira sunana cike da mamaki don ko a mafarki batayi tsammanin bayan abinda ya shiga tsakaninmu da ita mukayi hannun riga da kuma matsayin da Allah ya ɗaura ni a kai yanzu zan sake taka ƙafana a cikin gidan su ba,
Banbi ta kan expression ɗinta ba na ƙarasa kusa da ita na janyo hannunta ina ƙoƙarin janta cikin ɗakinsu
“Fure dan Allah ki taimake ni ki ɓoye ni bani son na tafi, kinji dan Allah”
Tsayuwa tayi ƙeƙam a wurin hawayen farincikin sake gani na yana wanke mata fuska, she doesn’t have the courage to go close to me, tana tunanin idan tazo mugun wulaƙancin da zanyi mata ba zata iya jurewa ba shiyasa tayi zamanta a gida kaman bata san abinda yake faruwa da labarin aurena da ya gama karaɗe wuroɓokki da kewaye ba,
Janyo tayi na dawo gabanta na tsaya tana girgiza kai cikin muryan kuka tace
“Bansan me kike shirin aikatawa ba, amman ba zan baki mafaka ba wannan karon, na riga na ruguza auren ki na farko ba zanyi dalilin ruguwan shi a karo na biyu ba,
dan Allah Saudat kiyi haƙuri ki koma gida kada ki saka iyayen ki kukan baƙinciki…dan girman Allah”
Sai yanzu abin ya faɗo min, babban kuskuren da zanyi yanzu shine gujewa ƙaddarata idan nayi wasa hakan ya zamo sanadin rasa rayuwan iyayena,
Da gudun da na ɗebo na shigo dashi na ɗiba na fita ban damu da mutanen dake kan hanya wanda ke tsayawa suna suna kallona har saida na isa gida.
Hanan ne ta fara tunkaro ni tana magana ƙasa_ƙasa da alama ba kowa bane yasan da fita na
“My dear ina kikaje? Mun zo dubaki baki nan, kin ɗaga ma Inna hankali sosai”
“Sorry baby Hanan na zaga nan baya ne na ɗan samu fresh air tunda na kasa baccin”
Cikin zolaya tace “Don’t try that again, kinsan yanzu ke mallakin wani ne ya kamata ki tambayi izinin mijinki kafin ki fita ko ina, kinji ko?”
Gyaɗa kai nayi ina murmushin dole tace. “oya muje mu shirya sun kusan ƙarasowa”
Saida na shiga nayi wanka kafin na dawo na samu ta baje min kayana da duk wani abun da zan buƙata, na shafa mai da turaruka na saka kaya sannan na zauna Hanan ta fara shiryani.
“My dear” ta kira sunana kaman yanda ta saba lokacin da take saka min necklace,
Da “uhmm” na amsa ina kallonta ta cikin mirror.
“You are very lucky boɗɗi, kiyi haƙuri I don’t mean to insult you amman ban taɓa zaton daga ƙauye kike ba saboda kin samu rayuwa mai cike da wadata gashi yanzu ma zakiyi aure a gidan wadata, bakiga gidan ki bane so masha Allah wallahi.
Shiyasa nima na yanke shawarar yanda na fito daga gidan daula ba zan bari soyayya ya kaini ƙasa ba wallahi, ni zan iya auren mai fitinannen arziƙi koda bani sonshi amman duk tsananin son da nake yi wa guy idan talaka ne ko kuma be kai gidan mu arziƙi ba toh gaskiya saidai a rarrashi zuciya amman ba zan iya ba”
STORY CONTINUES BELOW

Murmushi kawai nayi ina nazarin kalamanta a kaina, I’m very much sure Hanan have never been in love ammam da ta taɓa sanin menene soyayya na gaskiya da ba zata taɓa furta wa’innan kalaman ba. Ni koda ace Zayyad bayi da komai to zan zaɓe shi sau dubu akan Sulaiman because I love him so much.
“Baby Hanan you don’t know what is love, amman indai kin tabbata wannan shine burin ki na rayuwa to zan shawarce ki da ki dinga roƙon Allah to not make you know what is love, musamman kiso wrong person idan kuma ba haka ba rayuwan ki zata ƙuntata dukda tarin dukiyan da kike ciki”.
Ta baya ta sako hannayenta ta rungume ni muna kallon fuskar juna ta madubi cikin raɗa tace
“Yanzu na fahimci abinda yake damunki, amman Please ki daure ki koya ma zuciyan ki son mijinki you will find happiness somewhere, Allah ya baki ikon cinye jarabawan ki na rayuwa”
Zan saka kuka tayi saurin dakatar dani “don’t! Kada ki maida min da aiki baya dan Allah, now smile”
Murmushi nayi dukda idanuna suna niman tara ƙwolla amman na dakatar dasu.
Har muka tafi ban sake ganin furere ba, naso ace tana cikin mutanen da zasu rakani ɗakin mijina a matsayinta na tsohuwar aminiyata amman hakan bai samu ba.
In moderate speed convoy ɗinmu yake tafiya har muka shiga cikin gari.
Muna zuwa wurin wani roundabout motocin dake gaban mu da bayan mu suka ɗauki wani hanya daban zallan wanda nake ciki tare da Hanan ne yabi wani hanya wanda bamu san ina zai kaimu ba, dukda ni kaina na rufe da mayafi bansan bidirin da ake ba amman Hanan na ankare da abinda ke faruwa.
Matsowa tayi kusa da kunnena tace “dear ina zamu jene? Naga sauran ƴan ɗaukan Amarya sunbi hanyar da ze kaisu gidan ki amman gashi mu a nan Wannan ze tafi damu wani wuri, ko sace mu akayi ne?” Ta ƙarasa tare da ƙwalalo idanu.
Saurin yaye gyale na nayi ina kallon hanyar, no wonder mana suka sako ni a mota ni kaɗai babu irin tsoffi ƴan rakiyan nan.
Leƙa fuskar me tuƙa motan nayi naga Ya Nafi’u ne, ban gama mamaki ba sai ganinmu nayi a ƙofar City hospital.
“Asibiti kuma? Me ya kawo mu asibiti ya Nafi’u?”
“Wurin mijinki muka zo” shine amsar da ya bani a taƙaice.
Dumm naji ƙirji na ya buga, ko wani abu ne ya samu Sulaiman ɗin?
Ban samu damar tambayar shi ba don tuni ya riga da ya fice daga motar, ya zago ya buɗe mana muka fita sannan muka hallara ciki.
Muna yanko kwana na hango Sulaiman zaune kan waiting chairn da suke zaman jira tun safiya.
To kodai bashi bane mara lafiyan? Wa suka kawo? Me ya same ta ko shi?
Duk wa’innan tambayoyin ma kaina nakeyi na kas buɗe baki na tambayi shi wanda muke tafiya tare dashi.
Muna ƙarasawa inda yake zaune ya miƙe tare da buɗe ƙofar room ɗin da nake kyautata zaton a wurin aka kwantar da patient ɗin namu.
“Get in” ya faɗa cikin kasawar murya.
Ganin ban fahimci dani yake ba yasa ya sake cewa
“Ki shiga kiga halinda mijinki yake ciki”
Which kind of mijina?… Wait… Does that mean? Innalillahi wa inna ilaihirraji’un.
Tsayawa nayi na kafe Sulaiman da idanu cikin matsuwan jin ƙarin bayani, wani ɓoyayyanen numfashi yaja yace
“You got married to Zayyad and not me, saidai tun safe muka same shi a ɗaki unconcious har yanzu kuma bai farka ba”
A firgice na faɗa ɗakin, ina shiga ya jawo ƙofan ya rufe.
Kwance yake kaman babu rai a tattare dashi, fuskar shi tayi haske bakin shi a bushe, sai zara_zaran lashes ɗinshi da ya ƙawata idanunshi, my Zayyad always look great.
Zama nayi a kujeran dake gaban gadon shi, tunawa da nayi da sulaiman ya kira shi da sunan mijina yasa na janyo hannunshi na kai saitin bakina na bashi peck hawaye masu zafi suna bin kunci na.
Me yake faruwa ne? Abubuwa da yawa na son nesanta ni dashi.
A da lokacin da yake cikin ƙoshin lafiya an shiga tsakanin mu an raba mu yanzu kuma da na riga na zamo tashi gashi nan yana kwance rai a hannun Allah what happened to him.
Daɗa riƙo hannun nayi na rungume a cikin ƙirjina naci kuka na sosai na ƙoshi ina jin kaina kaman ana sarawa da wuƙa har bacci ya ɗauke ni a haka.
****
6:06pm
Buɗe idanun shi yayi ya zuba ma fiskana da na kwantar da kaina a kan gadon shi ina bacci ina ajiyan zuciya ga shatin hawaye da ya bushe na kukan da na sha.
Murmushi yayi tare da tashi zaune ya fincike kanulan dake jikin ɗayan hannun shi ina manne da ɗayan matt.
Hannu yasa ya ture kallafina da daman ƙiris ya rage ya kama gabanshi, cike da birgewa yake shafa gashin kaina da yasha gyaran amarci.
Jin ana taɓani yasa na buɗe idanu tare da ɗago kaina ina kallon shi, kaman a mafarki nake ganin murmushin da yake sakar min wanda beauty point ɗinshi suka daɗa ƙawata shi, tashi nayi na zaune tare da matsawa daga kusa dani ina gyaran murya.
“Na san sun bani ke Saudat, tunda na buɗe idanuna na ganki tare dani nasan ke tawa ce a Yanzu, don’t tell me otherwise please”
Tamke fuska nayi nace “Bari naje na faɗa musu ka farka” na faɗa tare da juyawa zan fita, cikin azama ya diro daga gadon ya fisgoni sai ji nayi na faɗa a jikin shi ya rungume ni tsam,
Wani irin shock naji tun daga yatsun ƙafana har zuwa tsakiyar kaina, ba don riƙon da yayi min ba na wasa bane da tuni na zube don ji nayi gaɓoɓin jikina gaba ɗaya sun sake, ga ɗumin numfashin sa dake sauƙa a gefen wuyana yana daɗa sakar min da kasala.
“Please stay… Stay with me…. please…stay,” ya furta cikin jan numfashi.
Koda ina da ƙarfin gujewa daga gare shi yanzu ya riga da ya gusar dashi.
“Nayi kewarki sosai babes please kada ki zauna cikin fushi zaki cutar dani, you know that I’m madly in love with you, mafarki na a kullum shine na samu na aure ki, yanzu da na samu kika zamo tawa bazan iya jurewa kaman yanda na jure a baya ba, kada ki guje ni dan Allah”
Ji nayi jiki na ya daɗa mutuwa, fushin yafe soyayya ta da yayi da nake ji a duk lokacin da nayi ido huɗu dashi presence ɗinshi kusa dani ya tafiyar dashi, i have no other option than to hug him back, a hankali na daga hannayena har suka kai gadon bayan sannan nan hawaye suka fara sintiri saman fuskana na ɗaga kaina sama saboda yaji abinda zan faɗa don yayi min tsawo sosai.
“Hamma zayd…” Na dakata lokacin da kuka yaci ƙarfi na, kaina da babu ɗankwali ya saka hannu yana shafawa cikin sigar lallashi, yana juyi dani a tsakar wurin a hankali.
“I was afraid of loosing you! My life is filled with fear saboda kai hamma zayd because idan na auri wani ba kaiba ina tsoron ba zan iya masa biyayya yanda ya kamata ba, ina tsoron ba zan iya bashi zuciyana ba, ina tsoron ba zan saka shi farinciki, ina tsoron zama matar da mijinta zai auri gangar jikinta kawai Azaban Allah zai iya tabbata a kaina a saboda haka”
Ranƙwafowa yayi ya daidaita tsayinmu sannan cikin raɗa yace “maybe a da idan kina hawaye ƙona min zuciya kawai suke yi amman yanzu hakki ne a kaina in hana ki kuka” da faɗan haka ya haɗe bakinsu wuri ɗaya, UMMU NAJMA ma daga nan ta tattari masillan ƙafafuwanta ta bawa wa’innan sabon auren privacy………..🧚🏼♀️
*Three more pages to go insha Allah*
*Ku faɗi ra’ayoyinku a kan wannan haɗin, yayi muku ko baiyi ba, idan na duba ni kuma zan faɗa muku nawa dalilin da yasa ba’a bawa Sulaiman boɗɗi ba*
Love You my fans ❤️
Team SZ forever 21
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
*Tunda na fara rubutun wannan book ɗin ban taɓa shiga farin ciki da jin daɗi irin na jiya ba💃💃😇🥳 lallai na yarda masoyi alkhairi ne a rayuwar mutum duk yanda yake🤩 saƙonni daga ko ina sai tuttuɗowa kawai suke😃 dukda dai wasu na rashin jin daɗin haɗin da akayi ne😩 har bacci ɓarawo ma da ƙyar ya samu ya ɗauke ni🥰 yanda kuka saka ni farinciki kuma Allah ya saka ku kwatankwacin shi😍😘*+
50🧝🏻♀️
Inaso in hana shi, amman zuciyata tana ingiza ni, ina so na dakatar dashi na tuna masa irin wurin da muke amman shine mai controlling ɗina a yanzu, ya tafiyar da tunani na gaɓa ɗaya babu abinda nake gani a gaba na sai shi ina amsan saƙonnin da yake tura ma duka ilahirin jiki na.
Ban gane halin da muke ciki ba har saida Zayyad ya kusan kaiwa ƙasa ƙafafuwan shi sun kasa ɗaukan shi, jikin shi na son tuna mishi har yanzu shi mara lafiya ne bai gama warwarewa ba tukunna.
Saurin saka hannu nayi na riƙo shi ta taimakon ƙarfen jikin gadon da ya kama be kai ƙasa ba, na saka dukkan ƙarfi na don na taimaka mishi ya tashi dai_dai lokacin da aka fara knocking ƙofa.
A hakan dai na taimaka mishi ya koma gadon ya kwanta na gyara mishi kwanciya na rufe shi da duvet sannan maida ɗankwali da gyalena na ƙarasa jikin ƙofar na buɗe.
Fa’iza da Ruma ne rike da niƙi_niƙin basket na abinci sai Sulaiman biye dasu a baya. Hanya na basu suka shige ina musu sannu, alhajin na kwance kaman patient din tsakani da Allah ya saka fiskan tausayi kaman bashi bane ya gama murje ni yanzun nan ba.
Karɓan baskets ɗin nayi na ajiyesu a wurin da ya dace suka miƙo min ƴar ƙaramar jaka wanda kayan da zan sauya yake ciki.
Me suke nufi? Kwana suke so nayi a nan?.
Ban gwada reaction din komai a fuskana ba muka gaisa dasu saidai tun bayan kallo ɗaya da nayi ma Sulaiman ɗazu ban sake yarda mun haɗa ido dashi ba, bansan ma da wani ido zan kalle shi ba tsananin kunyar shi ya gama kama ni.
Kaina a ƙasa na tambayi Fa’iza “aunty Fa’iza ina aunty?”
Murmushi mai sauti tayi tace “ai yanzu na tashi daga kujeran aunty kin hau kin zauna, aunty kuma babban yaya ya tura ta gida sai gobe da safe zata dawo duba ku insha Allah, ina dai babu wani abinda kike buƙata?”
Girgiza kai nayi tare da faɗin “babu”
Idanun Sulaiman na kan Zayyad amman kunnuwan shi suna jiyo mishi sautin muryata sai ƙoƙarin yaƙi da zuciyar shi yake yi, ‘yanzu ita matar ƙaninka ce, don’t feel anything for her please’ shine abinda yake faɗa ma kanshi.
“Inaso zamuyi magana dashi, give us privacy please” ya faɗa ba tare da ya juyo ya dube mu ba.
Hannu na su Ruma suka ja muka fita daga ɗakin sai murna takeyi na yanzu burinta ya cika na dawo cikin su dindindin.
Muna fita Sulaiman ya juyo wurin Zayyad da lokaci ɗaya ƙwalla ya cika a idanunn shi ƙiris suke jira su zubo don har can ƙasan zuciyan shi yake jin guilt ɗin abinda ya faru, yasan yayi ma Sulaiman maƙura na rashin adalci da bai iya danne zuciyan shi ya haƙura ya barshi ya auri boɗɗi ba, ya kasa controlling zuciyan shi ne duk yanda yaso yayi ƙoƙarin cire ta farat ɗaya ya gagara a maimakon haka ma sai koma baya da ya samu saboda tursasawan da yake yi ma zuciyan shi.
Gashi babban yaya ba tare da wani tunani ba yayi mishi sadaukarwan da harga Allah idan da shine ba lallai ya iya mishi ba.
STORY CONTINUES BELOW

“I’m sorry ya Sulaiman! I’m very sorry” ya faɗa kaman zai fasa ihu idanun shi a cikin nashi,
Murmushi Sulaiman yayi ya ɗan buge shi a kafaɗa tare da faɗin “it’s ok Zayd, nine ma wanda ya kamata ya baka haƙuri saboda na nuna son kaina sosai, ni mai baka abu ne matsayin ka na ƙaramin ƙani na ba mai kwacewa daga gareka ba, and that’s what I finally got to do.
ni babba ne nafika sanin ya kamata, bai kamata ace na bari mace ta shiga tsakanin mu ba, macen ma wanda da babu ita a cikin rayuwar mu a da lokacin da muke gwagwarmaya, tun kafin abubuwa su lalace ya kamata na dakatar da komai but i failed to do so har na barka kaso cutar da kanka”
A ɗan firgice yace “wallahi ba abinda kake tunani bane babban yaya, i did not poison myself ko su doctors ɗin sunce an samu poison a cikin jini na ne? Nifa musulmi ne nasan hukuncin wanda ya kashe kansa da gangan why would I even do that?”
Lumshe idanunshi yayi bakin shi ɗauke da ɗan ƙaramin murmushi yanda Zayyad ya marairaice ya tuna mishi da lokacin da suke yarinta, idan akayi laifi tun kafin azo a bincika aga waye yayi zai tunkari Sulaiman ya fara rantse_rantse har sai yarda ba shi ɗin ne yayi ba kafin hankalin shi ya kwanta, don dukda yanda suke tare yafi tsoron Sulaiman sau ɗari a kan dadyn su dan shi mutum ne da Allah yayi shi bayi da tsanani.
“Koda sunce min sun gani ba zan yarda dasu ba Zayyad, nasan dukkan abinda zaka iya aikatawa da wanda ba zaka iya aikatawa ba.
And to be honest i love Saudat amman son da nake mata be kai wanda nake maka ba jini na, you are the brother that I love the most kuma har yanzu babu ya kai a wuri na, kaidai ka ci gaba da roƙon Allah ya tabbatar da zaman lafiya da ƙaunar juna a tsakanin mu, Happy married Life bro”
*******
“Ina ne nan?”
“Shima exit ne da zamu iya bi mu fita daga asibitin, yauwa aunty Saudat kinsan me?”
“Meye?” Na tambaya a little bit annoyed ganin yanda suke cikin wani jin daɗi da farin ciki kaman ba yayan su bane kwance a gadon asibiti ba lafiya gashi nima sun fito dani yawo, duk girman asibin nan gaba ɗayanta babu inda bamu zaga ba, su ko ɗan damuwan rashin lafiyan shin basu ji ne?
“No! bake ba, na tuna yanzu ke baki isa kisa ƙafanki ki fita can…” ta faɗa tana nuna gate “ba tare da izinin yaya Zayd ba, don haka… Aunty Fa’iza kinsan me?”
Girgiza kai kawai tayi Ruma taci gaba da cewa “naga wani gift shop a ƙarshen titin nan, kinga kuma bamu haɗa ma wa’innan newly weds ɗin gift ba, so i think we should go and check it out kafin babban yaya ya fito”
“Ok, amman kuma dare yayi sosai fah Rumaisa, past 11 yanzun idan wani abu ya faru fah? kinsan halin babban yaya”
“Babu abinda zai faru sai alkhairi, da driver zamu je fah ni wallahi bani son tsoron kin nan wani lokaci kema kaman ba teruwa ba”
“Ohk to ki bari ya fito aje a kan idon shi mana sai muga ƙarshen teranci, ƴar rainin sense kawai”
Haba! Abin yaso ya bani mamaki ganin sun haɗu wuri ɗaya ba’a taɓa yar hali ba, ni banma san lokacin da suka fara shiri har haka ba, banyi aune ba sai jin muryar su nayi daga nesa suna faɗin.
“Aunty saudat ki koma ciki wurin angon ki, sai anjima”
Sanyi akeyi sosai shiyasa ban tsaya ɓata lokaci ba na koma ciki gashi ko sallan magriba banyi ba ballantana isha na tsaya ɓata lokaci a jikin Zayyad.
A hanya muka ci karo da babban yaya, har n buɗe baki zanyi mishi magana ya ɗaga kai kaman bai taɓa ganina ba ya wuce, abin ya ɗanyi min zafi kaɗan dan da ko sallama mayi kafin ya wuce.
Shigana ɗakin na samu Zayyad ya shiga toilet, zama nayi a bakin gadon na jira shi ya fito da towel ɗaure a ƙugun shi jikin shi na ɗigan ruwa alamun harda wanka yayi,
Oh gosh, why ne? Me yasa wannan mutumin zai fito gabana ba riga haka?
Yaso ya tsokane ni amman ganin Sallah ne a gaban mu yasa yace
“Babes shiga kema kiyi alwala ki fito muyi Sallah” ya faɗa tare da shimfida mana darduma,
Cire jewelries dina duka nayi na saka su a drawer sannan na ajie gyalena na shiga wurin da ya gwada min a matsayin toilet ɗin, tsayawa nayi ina kallon wurin shikkenan ni kuma abinda ƙaddarata tazo min dashi kenan a asibiti zanyi spending daren amarci na, taɓe baki nayi kada na ɓata mishi lokaci nayi alwalan ina fitowa na samu har ya gama shiryawa na same shi muka tada Sallah, mukayi magriba da isha sannan na zauna ina lazumi shi kuma yaci gaba da jero sauran sallolin dake kanshi,
STORY CONTINUES BELOW

Kafin ya idar na firfito da kayan abincin da aka kawo na ajiye komai ready, saida ya idar sannan nayi serving ɗinshi na tura mishi plate ɗin gaban shi yana dai kallo baice min komai ba, saida na jawo wani plate ɗin dan zuba nawa yayi caraf ya riƙe hannuna yana aika min da harara.
“A da kenan da nake cikin kaɗaici zan iya cin abinci ni kaɗai amma yanzu ina dake i don’t have a reason to be lonely anymore”
Ajiye plate ɗin nayi na ɗauki wani ƙarin spoon zan saka a cikin abincin shin da nufin muci tare kaman yanda yaso ya karɓa ya wurgar, bani son wani abinda zai saka mu faɗa kaman yanda mukeyi over a small issue a da, shiyasa bance komai ba na ɗauki cokalin da na saka mishi ɗin na fara ci,
“Babes horo da yunwa zaki mun ne? Won’t you feed me?”
What? Ni ko cin abinci a kwano ɗaya ban taɓa ƴi da yarima ba but Zayyad wants me to feed him.
Kaina a ƙasa na saka spoon ɗin hannuna na dibi abincin na kai bakin shi still yaƙi karɓa ba.
To me yake so ne?
” Da yatsun hannun ki nake son kiyi feeding ɗina ba da ƙarfen nasara ba” ya bani amsa kaman ya karanta zuciyana.1
Nanma babu musu na ajiye spoon ɗin hannuna na tsoma yatsu na na fara bashi, a first bite ya riƙe min hannu a bakin shi yana faman tsotse min yatsu cikin salon neman magana amman naƙi kulashi, ina jiran ya sake min hannu ne naci gaba da ciyar dashi idan kuma yaƙi mu kwana a haka.
Cire hannun daga bakin shi yayi ya riƙe a hannun shi tare da leƙa fuska na.
“Babes are you shy? Ko tsoro kike ji first night ɗinmu yazo a hospital?”
Dumm naji ƙirji na ya buga ni samm ba abinda yake zuciyana ba kenan,
“Don’t worry bazan takura ki ba, i will wait for you until you are comfortable, amman idan kinaso a nan ɗinma babu wanda zai gane, zanyi kaman babu abinda ya far…..”
Ban ƙarasa jin abinda zai faɗa ba na saka hannu na biyu harda mai datti na rufe kunnena tare da rintse idanuna gamm, irin Abinda nake gudu kenan shiyasa banso kwana wurinshi ba dama sun barni na kwana a gidan aunty Yusrah ne idan ya warke yazo ya same ni.
“Inajin yunwa babes feed me Saboda na samu ƙarfin yin…..”
“Please stop it hamma zayd!” Na faɗa cikin magiya “stop it please”
You are my wife now, me yasa xan bari? Ke yanzu zuciyata ne, sirri na, farin ciki na, jin daɗi na, zahiri na da baɗini na, yanzu babu hijabin kunya a tsakanin mu”
“Toh naji, ka bari amman ba a nan ba Please”
“Hhh yanda kike matata a can haka kike matata a nan, ohk naji zan bari amman sai kin canza min sunan hamma ne ko attishawan kin nan, give me a lovely name sai na bar daren yau ya wuce mana lafiya”
“Of course you are my darling mana!”
“Uhmm not bad amman darling yayi min ƙauyanci”
Langaɓe kai nayi nace “Honey?”
“Uhmm wannan ki bari sai takaba na ya hau kanki tukunna”
“Ok! Baby love”
“Toh it’s nice i love the name, but i want you to always treat me like a baby you love kinji ko, love me… And pamper me alot”
Tafin hannu na nasa a ɗan kunyace na rufe idona ɗaya nace “ok done Chona”
“Yeah nafi son wannan dukda bansan ma’anar shi ba but I’m sure it means something great”
A lalace muka ƙarasa cin abincin, daga yace wannan sai yace wancan kaman ba mai jinya ba, saida muka gama doctor yazo ya bashi magani ni kuma na shiga tattara wurin.
Nafi 30 minutes ina tattare tattaren da nima bansan dalilin yinshi ba, i just want to avoid Zayyad inaso yayi bacci ne sai nima nayi shimfiɗina nan ƙasa na kwanta nasan idan idon shi biyu kam ba zai yarda ba.
“Babes come here” ya kira ni hankalin shi a kan wayanshi fuska ba yabo ba fallasa, ƙarasawa nayi jikin gadon shi na zauna tare da cewa “gani”
Bai ɗago ba yace “haka suka ce miki ake kwana da miji ba zakiyi wanka ki shirya ba kin saka ni zaman jiran ki uhmm?”
Yanda yayi maganar yafi kama da mai roƙo
“Ko inzo nayi miki ne?” Sai a sannan ya ɗago ya kalleni, nayi saurin girgiza kai,
“No, i will do it”
STORY CONTINUES BELOW

Ni karan kaina nasan ba zan iya bacci da kayan jiki na ba saboda nauyin su, kuma duk gudun hakan ne yasa naƙi canzawa gashi na gudu ban tsira ba, hala zaiyi tunanin ma ni ƙazama ce.
Yi nayi kaman yanda ya umarta nasa wasu kayan bacci da su Ruma suka kawo min riga da wando na silk masu ɗan girma, na dawo gaban gadon shi na tsaya inason ɗaukan pillow ɗaya.
“Don’t try this joke with me, i think ko mutane 4 ne gadon nan zai iya ɗaukan su ballantana ni da ke, oya come here”
Ya faɗa tare da ɗaga ni cakat, rintse idanuna nayi har sanda naji ya dire ni a gefen shi ya rungume ni a jikin shi yana wasa da gashin kaina.
“Babu abinda zanyi miki just sleep”
**********
“Not now please dadyn Arif, ba tun yanzu ya kamata na fara ganin wukaƙanci daga gareka ba ka bari sai nayi maka wanu abun da bai dace ba, and i will never do that i promise”.
Shi bata san abinda ke damun shi bane, da tasan irin ƙusan da akayi mishi da bata tare shi da wannan zancen ba, gashi ta saka shi a gaba ko zama baiyi ba tazo ta kanainaye shi da jikinta wanda ya ɗauki zafin zazzaɓi.
“Nasan bai zamo maka dole ka sallameni kafin ka tafi wurin amaryar ka ba, amman inaso ka sani kaman yanda Saudat take sonka nima ina sonka haka wataƙila ma nawa yafi nata, I loved you first Sulaiman maybe tun Saudat bata da wayo i loved you since then! I love you know! And i wll continue to love you till forever, ka cire shakkan sonka da nakeyi daga zuciyanka, i will do anything for you… Anything harda abinda kake so baniyi i will do all of it, zan kula da kai zan kula da yarana zan kula da gida na, ba zan bari ƙanne na su diga ɓata maka rai ba, kawai ka mance Saudat and come back to me, mu koma rayuwar mu kaman lokacin da muke amarya da ango ko lokacin da muke soyayya a waje ko yaushe muna marmarin jun…..”
Jin yanda jikinta yake shaking saboda zazzaɓin da ya rufe ta yasa ya ɗago fuskanta yana kallo, idanunta a rufe suke sai hawaye da suka jiƙa su tana faman sumbatu daga gani bata cikin hayyacinta ga jikinta da yayi zafi kaman garwashin wuta.
Mayar da kanta yayi ya manna a jikin ƙirjin shi yana shafa bayanta a hankali.
“Shhh Halima you are sick, stop talking please”
Har yamzu bata daina ba saidai tana yi tana ajiyan zuciya kaman zata shiɗe, zuwa yanzu kan ma shirme take haɗawa ta faɗa kaman wani ɗan giya da yasha ya bugu.
Sunkuyawa yayi ya ɗauke ta cakat har yayi hanyar bedroom ɗin shi da ita ya juya zuwa nata da ya manta rabon da saka ƙafan shhi a cikin ɗakin.
Sadiya akwai sakaci kam amman bata bari a bar wuri da ƙazanta ɗakinta maids sun gyara shi tsaf gata uwar son ƙyaleƙyale tayi decorating ɗakin sosai se ɗaukan idanu yake yi ko shi Sulaiman abin ya burge shi.
Kwantar da ita a kan gado yayi zai tashi ta saka hannu ta riƙo rigan shi tare da buɗe kasassun idanunta
“My love Please don’t leave me, kada kaje wurin Saudat dan Allah ka zauna dani a nan” ta faɗa tana shirin saka kuka.
“Don’t cry leemah I’m not going anywhere, a nan zan kwana a gefen ki kinjiko?” Idanunta a rufe ta gyada kai with excitement.
“Ok to yanzu ki sake ni zan shiga bathroom ne”
Babu musu ta sake shi taci gaba da baccinta.
Toilet ɗinta ya shiga yaga kayan tarkacen gyaran fatan ta da yawa, shi a rayuwa bai taɓa ganin mace mai tsananin son ado irinta ba, don yanzu ma da take cikin halin ha’ula’i kada kaga adon da ta caba dukda babu kwalliya a fuskarta.
Ruwan sanyi ya fito dashi a ƙaramin bowl da ɗan ƙaramin towel ya zauna ya rage mata kaya da tarkacen ornaments da ta tara a jikinta ya fara danna mata jikin ko zi samu zafin ya ragu, har saida ruwan da yaɗibo yayi ɗumi zazzaɓin nata kuma ya sauƙa kafin ya bari, ya bɓallo mata magani ya bata ta sha, ya saka mata yale yalen duvet ya rufe ta sannan ya kunna mata AC kaɗan, ya tafi ɗaki don ya samu yayi wanka shima ya huta.
Yana mamakin kanshi yanda wai har shine me tsayawa ya kula da mace har haka, ko da yake hala don yasan tsadan su da darajan su ne yanzu da ya nima ya rasa, bai koma ɗakin ba sai wurin ƙarfe ɗaya na dare yana shiga ya samu yaye abun rufuwan ta wurgar dashi a gefe itama tayi can gefe daban.
Hawa gadon yayi ya sake gyara mata kwanciya yasan zata iya farkawa ta buƙaci taimakon shi shiyasa kawai yayi kwanciyar shi a nan ɗin da ƙyar da suɗin goshi ya samu barci ya ɗauke shi.1
STORY CONTINUES BELOW

**********
Yana kishingiɗe ya zabga tagumi yana ƙare wa kyakkyawar fuskarta kallo, tun daren jiya bai samu bacci ko na second ɗaya ya ɗauke shi ba, ina farincikin cikar burinshi da kuma tunanin yanda yanzu rayuwar su zata kasance zai barshi ya rintsa?.
Tunani kawai yake akan yanda zai inganta rayuwar Saudat ya saka ta farinciki da kuma yanda zai biya haƙƙoƙinta da ya rataya a wuyan shi a matsayin ta na matar shi a yanzu, yana so ya zamo mata mijin da take buƙata lokacin da take kuka da lokacin da take dariya, mijin da zasu shiga wahala da daɗi a tare, mijin da idan saɓani ya shiga tsakanin su zaiyi ƙoƙarin ganin sun shirya cikin ƙanƙanin lokaci.
He have to cloth her, feed her, and give her shelter, above all…make her happy.
Kiran sallan farko a cikin kunne na, ɗan ƙaramin miƙa nayi kaman yanda na saba idan ina bararraje a kan gado na na makaranta ko na gidan aunty Yusrah amman akasin na yau sai din hannuna nayi sun tokare mutum,
Saurin buɗe idanuna nayi na zuba su a kan fiskar Zayyad da ya sake min tsadadden murmushin sa,
Saurin rufe idanu nayi nima ina murmushi, this is the best morning ever!!!”
Matsowa yayi yana shirin kissing dina nayi saurin ja da baya tare da saka hannuna na toshe baki na,
“Ban wanke baki na ba fah!”
“Mtsw who cares?” Ya saka hannu ya cire hannuna sannan ya manna min peck a lips sannan ya jawoni muka sauƙa daga gadon tare da nufin shiryawa ma sallan asuba.
****
“Ina kwana hamma zayd”
Shiru yayi kaman ya kurmance idon shi yana kaina yana tura min mummunan kallo da jin abin da na faɗa.
Sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina dariya ƙasa_ƙasa,
“Good morning baby love” na gyara
Murmushi yayi ya kai min peck a goshi tare da faɗin “morning babes, kin tashi lafiya?”
Da lafiya ƙalau na amsa na tashi don buɗe ƙofar da ake knocking.
Nurse ce ta shigo da magungunan Zayyad wanda zaisha kafin yaci abinci da wanda zaici bayan yaci abinci, bani tayi fita tana tafiya su aunty Amarya suna shigowa, daɗin abun da hijab ɗin da nayi sallah a jiki na.
Fuskanta a sake take amsa gaisuwa na, don taji daɗin ganin yanda jikin Zayyad ya warware a kwana ɗaya ya maida kumarinsa.
Zama tayi tana tambayan shi jikin shi sai a sannan take faɗa mana wai flight ɗinmu zai tashi nan da hour huɗu zuwa Maldives don a duba lafiyan zuciyan zayyad.
Babu ɓata lokaci muka fara shirye_shirye nidai ina ganin rayuwa da ƙaddara ta Ubangiji, komai kawai faruwa yake cikin gaggawa ba tare da sani na ba.
********
Da addu’a a bakinta ta tashi ta zsune tare da dafa kanta da har yanzu yake sara mata, ita gata nan dai an rufeta amman she did not see Sulaiman anywhere around,
Bata gama tunani ba ya shigo ɗakin da plask ɗin ruwan zafi a hannun shi ya kawo ya ajiye,
Murmushin jin daɗin ganinshi tayi tace dadyn Arif kana nan dama?”
Gyaɗa kai yayi tare da ajiye plask ɗin a gefen gadonta fuskar shi babu laifi yace “yess ina nan, ki tashi kiyi Sallah sai kici abinci in baki magani”
Gyaɗa kai tayi kamar ƴar yarinya with so much excitement ta yunƙura zata tashi sai kuma ta koma ta zauna.
“Baka tafi wurin Saudat ba?”
“Eh ban tafi ba”
“Me yasa” ta fada fuskarta na nuna alamun rashin jin daɗi,
“Saboda kince kada naje wurinta”
“Amman me yasa ka saurareni? Kawai ɓacin rai ne ya saka na faɗi haka da kuma kishi bai kamata a shiga haƙƙin yarinyar nan ba”
Murmushi yayi yace “je kiyi abinda na saka ki idan kin fito zamuyi magana”
Tana kammalawa ta samu ya haɗa mata tea da bread and butter saboda shine kawai simple breakfast da zai iya haɗa mata da kanshi bayan shi bai iya dafa komai ba koda ruwan zafi kuwa.
“Zo ki zauna a nan” ya umarceta a taƙaice, dawowa kan gadon tayi ta zauna kaman yanda ya umarta amman fuskarta da damuwa.
“What happened Sadiya? Ko a kan Saudat ɗinne yanzu kike fushi?”
“Yanzu bani da ikon hanaka samun kusanci da ita tunda igiyan aurenka ya riga ya hau kanta”
“Kin daina jin kishin nawa ne?”
Girgiza kai tayi tace
“A’a amman bani da ikon canza hukuncin ubangiji”
Jinjina kai yayi yace “i think babu wanda ya kira ki yayi miki gulman an fasa auren ko?”
A razane tace “Are You serious?”
“Yeah da Zayyad aka ɗaura, yanzu ma haka suna hanya zasu tafi inda za’a duba lafiyan zuciyan shi, yau da safe yayi collapsing saboda ita, it was pathetic”
Allah sarki Sulthana, she will be heartbroken shine abinda ta ayyana a ranta,
“Amman me yasa naga yanzu kuma kina nuna damuwa a maimakon kiyi farinciki?”
“Na sani ne ko Saudat ko ba saudat ba idan kayi niyyan ƙara aure sai ka ƙara, and they say the devil you know is better than the angel you don’t know, gwanda saudat na san halinta na san tana da hankali yarinyar akan kaje ka auro wanda ban sani ba wanda zata ɗaga min nawa hankalin”
Jinjina kai yayi cikin gamsuwa da kalamanta……………🧚🏼♀️
Hikimar rashin aurawa sulaiman Saudat da akayi.
(Daga farko dai ƙarin aure ba shi bane maslaha na kowace irin matsala a gidan aure, wani lokaci idan aka ƙaro auren ɓata biyu kawai za’ayi ɗaya bai gyaru ba musamman a situation irin na gidan babban yaya, shi mutum ne mai zafin rai ga nuna halin ko in kula ma iyalinshi akan buƙatunta saidai idan nashi buƙatan ya taso ya buƙaci ganin dai-dai, bai damu da damuwanta ba amman yana so ita ta damu da damuwan shi, kuna tunanin wannan matsalan zata kau ne idan ya ƙaro aure? This story and twisted tale of love is not all about wa yafi cancanta ya auri boɗɗi ko waye yafi mata sadaukarwa, idan rayuwan Sadiya ya shiga cikin garari na ƴaƴansu ya shiga, idan na ƴaƴansu ya shiga mafari kenan a kan rugugewar komai.
Aje ma ace Sulaiman ya auri saudat amman fa itama ba son shi take yi ba, koda yana nuna mata so da kulawa ba lallai bane ta so shi kaman yanda ake tsammani saboda already zuciyan ta akwai wanda yake muradi, idan ya gaji da trying shi kuma zai gaji daga nan sai ya fara tunanin ƙarin aure, na uku ma wataƙil a sake repeating same process da ita na huɗu ma haka, shikkenan ko shi ya fara bin matan waje ko idan matan ba masu tsoron Allah bane suma su fara yawo daga nan shikkenan sai su zamo masa sanadin shiga wuta ya tara iyalai bayi iya kulawa dasu.
Idan kuma ace duka bai faru ba ta soshi kaman yanda kuke tunani to wataƙil zai iya tashi ranar qiyama a cikin sahun maza masu shanyayyen ɓarin jiki saboda yana yi ma Saudat so mai tsanani ba zai iya adalci tsakanin su da Sadiya ba, shiyasa yafi dacewa ta auri Zayyad amman a gani na)
Saidai bansan ko wasu ra’ayi na har yanzu baiyi musu ba ko kuma akwai kuskure a ciki ƙofa a buɗe take domin amsan gyara dukda dai akalan labarin ba canzawa zaiyi ba.
Musamman sis BAHIJJA inaso ki nazarci wannan review ɗin,😅 don jiya ke kadai kika tashi hankalin mutanen group kina zancen ba’ayi muku adalci ba,😩
Team Sulaiman har yanzu kuna tunanin ba’ayi muku adalci ba?😃
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*Wannan shafin sadaukarwa ce gareku kawaye na da ƙawayen ƙawayena🤣🤣😉*
*Sadi_sakhna*
*Maimuna abdallah (heroin)*
*Nimcy sarauta*
*Real smasher*
*Haseenatou autar manya*
*Zm chubaɗo*
*Miss untichlobanty*
*Hadiza D auta*
*Leemert pinky*
*Miss flower*
*Ameerah Adam*
*Fateema sunusi rabi’u*
*Anup mrs balarabe*
*Ummu maher (miss green)*
*Nabeela dikko*
*Billy queen*
Zaƙaƙurai kuma jajirtattun marubuta, Allah ya ƙaro mana manganaɗisun soyayya da zaman lafiya, ya ƙara muku kaifin baseerah❤️😘+
51🧝🏻♀️
Jinjina kai yayi cikin gamsuwa da kalamanta yace “jiya nayi nazarin wasu kalamai a cikin abinda kika faɗa min, which is why not mu koma rayuwar mu kaman lokacin da muke amarya da ango ko lokacin da muke soyayya a waje ko yaushe muna marmarin juna,
i wanted that Sadiya, ni yanzu bani da niyyan ƙara aure kaii bani ma da sha’awar ƙara aure, nafi son na gyara irin rayuwar da mukeyi dake a cikin gidan nan, idan wani abu ya faru ko na ci gaba ko akasin haka ya zamo ba ƙoƙarin ɓangare ɗaya bane, let’s build a beautiful family together Sady, will you support me?”
Yunƙurawa tayi bata bari ya ƙarasa maganar da kyau ba ta saka hannun ta around his neck ta rungume shi sannan ta saka kuka,
“I’m sorry habiby, I’m very sorry for everything, kasa daurewa nayi na kuma yi saurin sarewa, wataƙil da na daɗa jajircewa da relationship ɗinmu bai lalace haka ba, had i tried harder we would have been happy, I’m sorry for giving up on you”
Maida mata runguman yayi ya riƙeta gamm a jikin shi yana jin zuciyan shi na bugawa da sauri, idan bai manta ba yaso Sadiya irin so mai tsananin zafi tun yana zuwa jami’ar su tana ja mishi aji har itama ta folla mishi dukda ma dai bata wani bashi wahala sosai ba don ta lura ba ɗaukan nonsense, har yanzu kuma yana sonta yana begenta amman saken shi yasa duk zuciyoyin su sun manta da wannan.
Saurin ɗagowa tayi tana share hawayen ta,
“It’s enough now, let’s put our words into action, kaga nice ma ya kamata na kulada kai ba na wahalar da kai ba, let me go”, ta faɗa tare da yunƙurin sauƙa daga gadon, riƙo hannun ta yayi ya dawo da ita yana mata wani irin kallo
“Keda baki da lafiya me zaki iya”
Hannu tasa a fuskarsa tana shafa sajensa da babbar yatsanta “I’m a woman Habibi, i can fight my sickness with love, kuma ma idan nasha magani zan warke” ta miƙa hannu ta ɗauki maganin da ya kawo mata a kan side drawer da ruwa ta sha
“You see yanzu na samu sauƙi, let me hurry up na shirya yaran nan kada suyi lattin islamiyya”
“Nima zanje office, akwai aikin da nake son gamawa kafin monday”
“Ok Habibi” tayi mishi peck a goshi sannan ta sauƙa da hanzarinta tayi toilet, shide kawai binta da kallo yake yi kaman wani gaula, she seems so excited rabon shi da ganinta a cikin farinciki irin haka tun ranar da yayi mata alƙawarin maƙudan kuɗaɗe da zai bata idan Burin shi ya cika na auren Saudat, haka kawai sai yana jin daɗi wani sanyi ya fara ratsa zuciyar shi,
Yana cikin zaune a wurin shi karan kanshi baisan me yake i ba ta fito daga wanka ɗaure da madaidaicin towel, kawar da kanshi yayi daga kanta don akwai jibgin aikin shi da na da suka tara Zayyad suna jiran shi idan yayi wasa zai iya ɓato lokacin shi a nan wurin.
Rantsatstsiyar lace ta saka wanda yaji rantsatsen ɗinki ta fara tumbuɗe tumbuɗn turare, saida ta gama ta buɗe drawern jewelries ɗinta, har zata saka sarƙanta na gold sai ta fasa ta ɗauki fashion mai kyau ta saka, tana ganin kaman idan ta saka gold ɗin gidan jiya zata koma because they were the love of her life a da amman yanzu mijinta ya amshe matsayin su.
STORY CONTINUES BELOW

Saida ta gama bata ɓata lokaci wajen kwalliya ba tazo ta jashi suka fita daga ɗakin zuwa nashi bedroom ɗin, setting temperaturen ruwan wankan shi tayi sannan ta fito ta tura shi ciki bayan ta tabbatar komai da zai buƙata akwai shi a ciki, tasan Sulaiman yana da weird taste ba lallai bane ya zamo idan ta fitar mishi da kaya yaso zaɓinta ba shiyasa kawai ta ajiye mishi singlet da bxrs ta fita zuwa bedroom ɗin yaranta.
Tashin su duka biu tayi da kanta tayi musu wanka ta shirya su cikin uniform ɗinsu na islamiyya daga nan ta fice zuwa kitchen, a canma saida ta tabbatar komai ya tafi daidai an haɗa breakfast kafin ta taya maids ɗinta suka jere a kan dining lokacin Sulaiman ya gama shiryawa har ya fito, a tare suka zauna sukayi breakfast ana raha ana dariya, dukkansu sun lura da farin cikin dake kan fuskar Arif da islaha dan bakin yaran kaman zai tsage don murmushi.
Da akazo rabuwa ne kuma abinka da ba saban ba ta tsaya tana kallon su ta rasa abinda zatayi musu ko waving ta kasa tana tsaye jikin ƙofa har suka shiga mota suka har gidan,
*******
“Baby love are you alright?” Na sake tambaya ganin tunda muka kusa landing yake ta faman rintse ido yana cisgan numfashi kaman breathing mask ɗin da suka saka mishi ya dame shi.
Buɗe idanunshi yayi lokaci ɗaya har sun sauya kala zuwa ja, ya gyaɗa kai tare da faɗin
“Yeah babes I’m… I’m alright, kawai my heart is beating so fast kuma inajin raɗaɗi sosai kaman zai faɗo ya fito”
“Hasbunallah! Zuciyan ka ba zata faɗo ba Chona” na faɗa tare da saka hannu na a daidai saitin zuciyan nashi inda ya riƙe, cikin murya mai nuna damuwa nace “u will be fine insha Allah bari na kira nurse ɗin ta sake duba ka”
Girgiza kai yayi tare da matse hannu na a kan ƙirjin nashi yace
“No, just leave it. Hakan ma ya ishe ni har naji kaman ciwon ya tafi da abinda nake marari yaje kusa dashi,
I don’t need the nurse bata san maganin ciwo na ba ke kaɗai ne zaki iya sakawa naji sauƙi, just stay here please!”
Bance komai ba na ɗaura kaina a saman kafaɗan shi, hannu na na riƙe a cikin nashi manne a saitin zuciyan shi, inajin yanda yake sauƙe ajiyan zuciya a hankali.
Muna sauƙa muka samu asibitin da zamuje ɗin har sun turo ambulance da zata ɗauke mu airport ɗin, muna shiga suka kwantar dashi suka fara bashi taimakon gaggawa ganin yanayin da yake ciki, hannun shi riƙe da nawa yaƙi sake ni har sanda akaje ɗakin da na’urar da za’a saka shi ciki don ganin ainihin matsalar shi yake kafin suka saka shi dole ya saki hannu na.
Samun wuri nayi na zauna a waiting chair damuwa fall a raina ina roƙon Allah yasa idan aka bincika abinda yake damun shi a zuciyan a samu ba abune mai girma ba, banfi 10 minutes zaune ba wata baturiya tazo ta tsaya a kaina sannan ta kira ni da “Mrs Zoyyad Mohamad?”
Ɗagowa nayi na kalleta tare da jin yanda ta kwaɓulo sunan, amsawa nayi da “yess”
“Oh hi I’m Cynthia, your husband’s childhood friend”
Gaisawa mukayi cikin harshen turanci sai yanzu nake tunanin da ace har yanzu naƙi makaranta irin wannan ranar tazo min da bansan yanda zanyi ba don tabbas za’ayi kwaɓa.
Zama tayi tana faɗamin kan cewa babban yaya ne ya turo ta Saboda maganar masauƙin mu da wurin da zan zauna kafin mu isa masauƙin.
Ta buƙaci na bita gidan ta na kwana a can naƙi don yau ba zasu bani dama naga Zayyad ba sai sun gama binciken su, da ƙyar na yarda muka tafi tare mukaje gidanta babban gida da yaranta guda biyu da mijinta suka bani ɗakin kwana sannan suka turo min dinner, ban wani Ci ba dukda bawai abincin da ba zan iya ci bane na taɓa ɗan kaɗan na bari,
Washegari da safe ma ko breakfast banyi ba suk yanda taso zaunar dani na ƙi na kamo hanya na dawo asibiti dan tunjiyan ake ta kirana daga gida ana tambayana jikin Zayyad.
Ina isa har ɗakin da suka kwantar dashi suka kaini, da shigana na samu yana shirin fara breakfast.
“I’m sorry babylove banso tafiyaba wallahi Cynthia ce ta matsa sai na bita….” Na faɗa cike da damuwa idanu na akan nurse din dake tsaye a gefe da spoon a hannunta sai rarraba idanu takeyi don bata yi tsammanin wannan patient din da budurwan shi yazo ba shine ta matsa wai bayi da lafiya ita zatayi feeding ɗinshi.
STORY CONTINUES BELOW

“Shh…cool down baby, it’s ok gwanda da kika je kika huta, nasan ɗawainiyan akwai gajiya, kina ƙoƙari i appreciate it”
“Haba hamma Zayd stop saying that ina wani gajiya a nan, its my duty which I’m not even doing properly”
Bai sake cemin komai ba ya juya wurin nurse ɗin dake tsaye tana binmu da idanu
“You can leave Venessa, my wife is here she can help me thank you”
Ba haka dai taso ba ta ajiye mana spoon din sannan ta juya zata fita.
“Babes zo ki ciyar dani da hannun ki masu albarka”
Murmushi nayi na ajiye jaka na sannan na shiga toilet na wanko hannuna na fito na saka a cikin abincin na fara bashi a baki.
“Babylove yaya akayi har kasan sunan wancan arniyar?” Na tambaya tare da turo baki cikin shagwaɓa.
“Ohh someone is jealous! Ofcourse she is my nurse, kuma ita ta faɗa min sunanta kafin ta fara attending ɗina so babu laifi idan na san sunanta ko?”
“Eh dai dukda haka da kayi addressing dinta as nurse ɗinta kawai ya isheta, ni bani son mata suna kalla min kai… And don’t you dare to smile again a gaban wata koda kuwa ni ka gani bani son su kallamin dimples dina”
Dariya mai sauti yayi ganin yanda nayi kicin_kicin na ɓata rai
“Tsare gida kenan babes? Kada ki damu ai kin riga kin gama dani tunda har kika kwantar dani a nan wurin”
Murmushin da banyi niyya bane ya suɓuce min ina jin kaina wani a sama, a haka na ƙarasa bashi abincin da muka gama na haɗa shi da su aunty a waya…..
*********
Ba wai ainihin aiki bane ya saka shi zuwa office din, he needs space to think da irin sabuwar rayuwar da ya tsinci kanshi, dole ya yaƙi zuciyar shi ya zamo mai haƙuri sannan ya rage zafin zuciya da fushi uwa uba ya ajiye girman kai idan yana son samun lafiya tsakanin shi da Sadiya,
He have to make their marriage work dole ya saka ma ranshi kaman yau sukayi aure yanzu ne zasu fara shimfiɗa Foundation na rayuwar auren su, haka ya zauna daga shi sai securities a companyn ya taɓa aiki ya taɓa tagumi har yamman tayi kafin ya tattara zai tafi,
Har ya kusan isa gida yaga bai kamata ya koma musu haka hannu na dukan cinya ba, a wani mini store ya tsaya ya saya musu kayan maƙulashe kaɗan sannan ya tafi.
Yana isa da gudu su Arif sukazo suka rungume shi ganin shopping bag a hannun shi yasa dukkan su suka fara kai hannu zasu karɓa,
Jan bag din yayi baya fuskar shi ɗauke da fara’a ya ciro chocolate manya daga ciki ya bawa kowa nashi a hannun shi suka shiga cikin gidan da gudu suna murna,
Sadiya dake tsaye a jikin labule tana kallon su ne tayi murmushi tare da miƙo masa hannunta da yasha jan lalle ga bangles dinta sai daukan ido sukeyi.
“Welcome back dadyn Arif, ina nawa tsaraban”
Riƙo hannun yayi ya kai bakin shi yayi kissing, ji tayi kaman an watsa mata abu mai sanyi a zuciyanta daɗin wannan sabon yanayin nashi yana ratsa ta, bata da abinda zatayi yanzu da ya wuce godiya ma Allah, abubuwa lokaci ɗaya sunata gyaruwa.
” Lallen yayi kyau sosai habibty”
“Awnnn thanks Habibi, daman ma kai akayi tunda ka yaba shikkenan ya biya”
“No bai biya ba gaskiya, yanzu dai karɓi tsaraban ki” ya faɗa tare da miƙa mata laidan hannun shi “danzo na bada tukuicin shi daga baya”
********
Kwanan mu 4 a asibiti Zayyad ya ɗaga musu hankali saida suka sallame mu don har office din doctorn dake kula dashi yaje ya tada ma bawan allahn nan hankali saida ya rubuta mishi takardan sallama don haka kawai yayi aure ba zasu saka shi yaci gaba da zama a matsayin gwabro ba, he needs to go and rest with his wife.
Nayi_nayi na hana shi ya bari jikin shi ya ƙara kyau tukunna amman yace fyatt shi baisan da wannan zancen ba, harda gwada min ƙarfin iko tunda shine gaba dani dole nabi ra’ayin shi, har iyayen shi saida suka saka baki amman yaƙi sai cewa yayi ai ba barin ƙasar zaiyi ba, yana nan babu yanda zaije kuma zai dinga zuwa checkup amman zama kam ba zaiyi ba.
Babu yanda suka iya haka suka sallame mu, muka shiga taxi da ze kaimu masauƙin mu dake a bakin wani beach.
“Beach?! Seriously?” Na tambaya a firgice tare da ƙwalalo idanu cike da tsananin mamaki,
“Yeah, daga elite hospital yanzu zamu tafi cocoa island beach”
“Kasan me kake faɗa kuwa chona? Beach fah! Musulmai damu zamu je beach? Wurin da mutane suka zuwa rabin jikin su tsirara?”
Ware hannayen shi yayi yace “to yaya zamuyi babes a wurin masauƙin mu yake, i have a house there ko inada nawa muhallin kinfi son muje hotel mu kwana? Toh hotels ɗinma suma a bakin Beach suke, we are living in an island everywhere is sorrounded by water please understand”
Turo baki nayi na koma jikinsa na gyara na kwanta ina ƙunƙuni zanga yanda za’ayi yau musulmai suyi rayuwa a beach.
Kaman yanda na tsammaci wurin zai kasance…. Toh abinda idanuna suke gani mun a yanzu yafi ƙarfin tunani na ma ballantana tsammani na, Maldives yana ɗaya daga cikin jerin farko na ƙasashen duniya da suke da yawan beaches don kuɗin shigan su ma yafi yawa ta wurin saboda yawan baƙi da masu yawon ɓude idanu dake zuwa wurin dan shaƙatawa a beaches ɗin da babu kamar su,
Mata kawai nake gani rututu da bikinis suna yawo kusan tsirara kaman wasu tumaki maza kuma daga su sai shorts, saboda yanayin shigan mu har muka zamo musu abin kallo muna wucewa ana nuna mu da yatsa, don ni flawless gown ne peach color a jikina sai nayi rolling da gyale kaina da farin dankwali, Zayyad kuma normal sweaters ne a jikinshi sai nurse din da aka haɗo mu da ita kuma uniform din aikinta ne a jikinta.
Hannu na a cikin nashi muke tafiya da kafafunmu kafin muje inda zamu shiga abun hawa na gaba.
“Babylovee” na kira shi tare da ja na tsaya,
Juyowa yayi yana kallon yanda na haɗe rai, yasan wannan fushin akan menene maganar ɗaya ne bayi wuce kishi, shi da zai gwada mata kalan nashi kishin nata wasan yara ne.
“Yaya kuma akayi boɗɗi?”
“Me yasa kake waigawa kana kallon matan can” na faɗa tare da turo baki ina gwada su da yatsa.
Numfashi ya furzar sannan ya ɗan juya ya kalli nurse dake biye damu daga ganinta a kugun takure take, na farko tun kafin ta fara niman abinda take so ta rasa shi gashi boɗɗi is pissing her off.
“Ni banga matan da kike faɗa ba, banda gine_gine babu abinda nake gani a nan, Please stop being such a baby kina ɓata mana lokaci fa lokacin la’asar ta kusa kurewa”
“Ohh u are politely saying I’m pissing you off? Shikkenan nima bari naje cikin su na zauna maybe a cikin gine-ginen da kake gani zaka gano mai kama dani, I’m off” na faɗa tare da ƙwace hannuna daga cikin nashi na nufi bakin beach ɗin ga idon wasu daga cikin mutanen curr a kanmu suna kallon draman ƙauyawan couples anayi ana sipping cocktail haka na matse nayi kaman bani ganinsu.
Da gudu ya biyo ni a baya ya sunkume ni ya raɓa a kafaɗa kaman wata kaya, sai wuntsila ƙafa nakeyi cikin salon niman magana amman yaƙi kulani, tafiya kawai mukeyi muka je muka shiga wani mota da zai tafi damu a kan ƙasan beach ɗin ba tare da matsala ba ya kaimu reserved area inda mutane da yawa suke siyan gidajen a wurin suna zama.
Gidajen wurin duk kalan su daya ginin anyi da katako a sama da matakalan da ze kaika ciki number ne kawai ya banbanta su sannan ko wanne a kewaye yake.
Daidai ƙofar namu aka ajiye mu tare da nurse ɗin ta taya unpacking muka hallara ciki,
Roses ne tun daga bakin ƙofar madaidaicin parlourn ko ina a rufe wurin yayi duhu sai haske da ƙamshin scented candles da Zayyad yasa ayi arranging, wurin yayi matuƙar ɗaukan hankali na it’s so romantic.
Saida ya bari nurse ta shige cikin ɗaya separate room ɗin kafin yazo ta baya na ya saƙalo kanshi ta gefen wuya na yana jin sautin dariya na dake fita a hankali saboda farin ciki,
I hope you liked it, and zaki bada dama ya zamo wurin da zamu ci amarcin mu, just assume that honeymoon mukazo ba jinya ba, abinda nake so kenan…………..🧚🏼♀️
*Ummu Najma ce 😘*
(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя’s αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd
*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
52🧝🏻♀️ (GRAND FINALE)
“You are not serious” na faɗa cikin fitar da sautin dariya tare da juyawa zan bar wurin, da azama Zayyad ya riƙo waist ɗina ya dawo dani jikinshi yana bina da wani irin kallo mai nuna shauƙi da tsaftacacciyar ƙauna, ” then let me show you how unserious I am”
saurin dakatar dashi nayi ganin yana matso da fiskan shi kusa da nawa nace “babylove bamuyi sallan la’asar ba fah! And it’s 5 already”+
Furzar da numfashi yayi yace “zamu haɗu ai bayan sallan la’asar ɗin, ina nan tare dake babu inda zanje and our honeymoon is starting today!” Yaja hannu na muka shige bedroom ɗinshi wanda ke ɗauke da bathroom a ciki mukayi alwala sannan mukayi sallah a tare sai ya sake fita parlourn saboda alluran da nurse zatayi mishi a lokacin.
Wurin akwai sanyi kaɗan amman ganin ruwan zafi available a heater yasa banji kyuyan wanka ba, a gaggauce nayi na fito har lokacin Zayyad bai dawo ciki ba.
Jakan kayana wanda su Ruma suka haɗa mana na buɗe ina duba kayan da zan saka, yawanci gowns ne irin na jikina sai atamfofi da laces suma basu fi a ƙirga ba sai jibgin ƙananun kaya.
Hannu na nakai kan wata ƴar ficikar riga armless pink color mai shegen kyau amman ina mamakin yanda za’ayi wannan ɗan abun ya shiga jikin mutum mai girma kama na, sai da na ɗaga naga saman nada faɗi tsayi ne kawai bata dashi sai wani da zaka ƙulle rigan ta ƙasa ya zamo yana showing cibiyan ka.
Saka rigan nayi a jikina na ƙarasa gaban madubi ina kallon yanda ya amshi fatata kaman don ni akayi shi, haka kawai naji ina son in zauna dashi a jikina, na ɗauko leggings golden brown kalan adon dake gaban rigan na saka.
“Woww” shine abinda na furta lokacin da nake kallon kaina sama da ƙasa a mirror, Black scarf nayi ɗauri mai kyau dashi saboda almuru gudun aljanu.
Turare kawai na bulbula na saka takalmi da confidence ɗina na isa bakin ƙofar da zai sada mu da parlour sai kuma naji ruwan ciki na yana kaɗawa na gagara fita.
Zayyad mijina ne, ya kamata ina ado mai ɗaukan hankali don na burge shi amman kuma ban saba ba, ban taɓa yi ba koda a gidan aurena na farko sai inajin wani iri a jiki na.
Sake tattaro dukkan ƙwarin guiwa na nayi na fita parlourn a tunanina zan iya samun su har yanzu a wurin amman shiru babu labarin kowanne daga cikinsu, leƙa ɗakin nurse ɗin nayi itama bata nan sai kawai na koma na ɗauki medicated glasses ɗina da pencil da paper na fita ta ƙofar baya wurinda ke a kewaye babu wani daga waje da zai iya hango wanda ke cikin wurin.
Takalman ƙafana na cire na zauna ɗan nesa da bakin ruwan ina zanen waves, iskan wurin mai ɗan ƙarfi haɗi da niima yana kaɗani har kusan 30 minutes Zayyad bai dawo ba, komawa ciki nayi na ɗauki wayana na kira shi saiga wayan shi na ringing a kujeran parlour hankali na ya kai maƙura wurin tashi, na Farko bayi da lafiya gashi bai faɗa min inda zaije ba kuma magriba ta gabato har yanzu bai dawo ba, ji nayi tsoron gidan ya kama ni gashi yunwa nake ji annan bani da nutsuwan cin abinci haka na koma bakin ruwan naci gaba da zama.
Daga nesa na hangota zaune ta haɗa kai da guiwa da ɗan ficilar riganta da yabar rabin bayanta a buɗe,
Ƙarasawa wurin yayi ya mata sallama saboda bata san da zuwan shi ba kada ta firgita
Ban amsa sallaman ba sai miƙewa nayi a dame ina dube_dube a jikin shi kaman mai son gano wani abu.
“Babylove where have you been? Hankali na ya tashi sosai, da ka sanar dani katin ka fita Pleease! I was really worried”
STORY CONTINUES BELOW

Ƙaramin murmushi yayi idanun shi na kan ciki na da yake buɗe ya matso daff dani sannan yayi hugging dina ina jin hannunshi a kan bare skin ɗina.
“I’m sorry babes looacin da na fita kina wanka and i forget to take my phone, naje na sanar da management plan din zaman mu ne saboda daily service da kuma ordern abinci. That’s all, I’m safe”
Gyaɗa kai nayi nace “and what about the nurse?”
Wani shaqiyin dariya yayi yace “daman kina tsammanin zan barta ta zauna tare da mu ne? I send her off nazo honeymoon ba zanbari wata aba can tazo ta tare min shan iska ba, i want us to be alone, just me and you”
Jinjina kai nayi na tattari tarkace na “mu tafi ko” na faɗa lokacin da na ratsa zan wuce ta gaban shi,
“Kin iya ruwa?” Ya faɗa tare da riƙo hannuna.
“No! Ina da aquaphobia tun ina yarinta, ko a rigan mu ma bani iya shiga rafi,
“Come here” ya faɗa tare da zubar da kayan hannu na, matsawa nayi kusa dashi ya riƙe hannuna duka biyu sannan ya fara jana kusa da ruwan, wani gauron numfashi naja lokacin da naji ƙafafuna sun fara luntsuma cikin ruwa, a take naji jiri ya fara ɗiba na,
“Hamma Zayd bazan iya ba, I’m really scared”
“Tsoron me zakiji bayan ina tare dake? Babu abinda zai same ki as long as I’m here”
Ya faɗa daidai lokacin da ruwan ya haura saman ciki na har yana ɗaga rigan jikina, tsantsi naji ya ɗibe ni da azama na wuntsila jikinshi sai gamu fanjam mun faɗa a cikin ruwa ni a saman shi, saurin miƙewa nayi tare da shiɗewa numfashi na yana niman ɗaukewa, tashi yayi ya rungumo ni a jikin shi yana shafa gashin kaina a hankali ga ɗankwali na da tuntuni ya bi ruwa.
“Are You okay?” Girgiza kai nayi ina daɗa ruƙunƙumeshi a yanzu bani da burin da ya wuce na fita daga cikin ruwan nan ko zan samu nutsuwa a ruhina,
“Let’s do it again you will be ok”
Saurin girgiza kai nayi, idan ba wai a wani ɓangare na zuciyan zayyad akwai burin kashe ni bane to halan ƙure muguntan shi yake son yi a kaina,
“A’a hamma Zayd bazan iya ba, mu fita Pleease”
“Just relax babes, believe me it will be fun” ya faɗa da murmushi a saman fuskarshi shi, shikkenan ni tawa ƙarshen yazo a hannun mijina tun ban haihu naga jini na ba, duk yanda na ƙi haka Zayyad ya dage saida ya sake danna kaina a cikin ruwan nan.
Wannan karon kam ƙiris ya rage min ban mutu ba, wai ance mishi phobia wasa ne?? Ɗagoni yayi yana kallon fuskana idanuna duk sun juye numfashi na ya gagara fita sai gasping nake yi.
Sunana ya kira a dan razane yana buga kumatu na, ganin bani responding ne yasa ya ɗaura bakin shi a kan nawa yana hura min iska,
Ji nayi jikina ya sake…. Duk kokuwan da nake yi na niman numfashi ya tsaya, sassauta riƙon da na mishi nayi ina neman faɗuwa da azama ya riƙo ni tare da canza salon tafiyan nashi, wannan karon cikin zaƙuwa da kwarewa……..
“Did you enjoy it?” Gyaɗa kai nayi slowly ina ƙoƙarin ɓoye murmushin dake ƙoƙarin kufce min,
“To mu sake….are you ready?” Gyada kai na sake yi, ya jamu muka koma cikin ruwan for some seconds kafin muka sake fitowa wannan karon ina dariya mai fitar da sauti.
“Are You ok, ko har yanzu kina buƙatar agaji?”
Tangal_tangal nayi kaman zan faɗi da gangan, ganin haka yasa ya saki dariya tare da janyo ni jikin shi,….ehem…daga nan muka ci gaba da nutso😅
8:35pm
Zaune nake a ƙasa a bakin wuta na jin ɗumi yanzu dogon riga ne mara nauyi a jiki na sai pink towel da na ƙudundunu a ciki, gama cin abincin mu kenan mukayi sallan isha Zayyad ya shiga bedroom yin waya da aunty.
Fitowa yayi ya nemi wuri a gefe na ya zauna sannan ya ɗaura hannun shi a saman nawa da na ajiye a ƙasa yana murza yatsu na cikin nutsuwa.
“Ka fito babylove? Yaya su auntyn? Kowa lafiya ko?”
Murmushi yayi yace
“Duka tambayoyinki jam’i zanyi musu na amsa dan sunyi min yawa,
“Eh lfy lau. Tunanin me kikeyi haka? I can see you are lost somewhere”
STORY CONTINUES BELOW

Faint smile nayi nace “yaune karo na farko da naji inaso in fiskanci dukkan abinda nake tsoro da ƙwarin guiwa, saidai kash! Tun kafin nayi wani yunƙuri ka riga ka magance min su, you get rid off all my phobias at a time babylove, yanzu bani da sauran abinda nake tsoro, koda kuwa ZAWARCI ne, ko kaɗaici, ko ƙasƙanci, ko soyayya, ko yarda, koda kuwa shiga ruwa ne, sannan zan kasance har karshen rayuwata mai godiya ma babban yaya da yayi min maganin jahilci, Allah ya saka mishi da alkhairi ya. Albakaci zuriyan shi, zanso nima wata rana na biya shi koda kwatankwacin halaccin da yayi min ne”
Jinjina kai yayi tare da faɗin “ameen” “amma mu ɗin kasancewar mu tare yana nufin maganin matsalolin mu tare ne, even i have phobias and thankfully samun ki cikin rayuwana ya magance min masu girma daga cikin su sai guda ɗaya ya rage….”
“Then zanso insan menene abinda kafi tsoro mai girma?” Na katse shi with little excitement ba tare da na tsaya naji menene guda ɗayan da ya rage ba.
Ɗan ƙaramin murmushi yayi ganin expression dina sannan ya ɗaura da cewa
“Abinda nafi tsoro shine kadaici, duk yanda na kai ga girma na shekaru da karfin iko ina tsananin tsoron ƙadaici saboda shine abinda na azabtu dashi lokacin da nake yarinta, a wannan ƙasar…, a wannan garin.., a cikin wannan gidan ni kaɗai nake rayuwa duk lokacin da babban yaya bayi tare dani sai masu kula dani saboda ko familyn Cynthia da aka danƙa ni a hannun su lokacin da nazo karatu ma ba’a son su san da rashin lafiyata, nan ne wurin ɓoyo na, bakin ruwan da kika je kika zauna ɗazu kuma a ko wani rana bani da burin da ya wuce wata rana inzo da wani nawa, wanda ke mallaki na ni kaɗai in kasance tare dashi a wurin saboda inyi maganin ƙaɗaici na.
For years family na ne kawai sukan zo suyi ta nishaɗi a wurin idan sunzo min visit, nakan ji daɗin ganin su sosai a wurin amman haka kawai nakan jini not satisfied, amman yau dukda tsoron da kike dashi kin yarda dani kika barni na shiga dake wurin da kinsan yana da hatsari ga rai da lafiyan ki, and you smiled in that process, i know feel happy and satisfied.”
“Zo abinka babylove ɗina” na faɗa tare da ware mishi hannuna, dariya yayi ganin yanda na mishi kaman wani ɗan yaro ya matso sannan ya shiga jikina na rungume shi tsamm tare da rufa mana towel din dake jikina.
“Ni lokacin da na sami aquaphobia tun ina 9 years, akwai wata rana da mai gari da yarima suka fito ran gadi, it was that time when i was crushing on him wuni nayi ina binsu duk inda suka shiga suka fita kaman wani ibada kuma inayi ne bani so su ganni don zan iya shiga babbar matsala a sanadin haka.
Nabi yarima har bakin rafi da mutanen shi suka so kama ni ne na faɗa a ruwa domin tsearatar da kaina daga hukuncin su,
I almost died babylove, nafi 30 minutes a cikin ruwan nan a sume, saboda shi yariman yasan ina ciki yasa suka tsaya a wurin suka ƙi tafiya, daga ƙarshe wasu yara ne da suka zo ɗiban ruwa suka fitar dani, tun daga wannan rana tsoron ruwa ya shige ni, ko kusa dashi bani iya zuwa, amma saboda ni sakarya ne i agreed to marry that demon..wannan shaiɗanin da yaso ɗaukan rayuwata… I hate him to the core”
Na ƙarasa tare da fashewa da kuka,”i hate him hamma Zayd!, na tsane shi!!” Ɗaukana yayi cakat shiga bedroom ɗinshi sannan ya kwantar dani a saman gado yana share min hawaye, “ki daina kuka babes, ya riga da ya wuce yanzu babu wanda zai sake cutar dake ba zan bar hakan ta faru ba, kinji?”
Gyaɗa kai nayi jikina yana kyarma saboda sanyin da nasha ɗazu a ruwan waje har yana niman saka min zazzaɓi.
” Har yanzu sanyi kike ji?”
Girgiza kai nayi “ki faɗamin gaskiya, i can help you get rid of your coldness” ya faɗa tare da ɗago hannuna ya dunƙule a cikin nashi, “ina buƙatar ki a yanzu babes, let’s become one please”
Kawar da kaina gefe kawai nayi bani jin a yanzu akwai wani abu da Zayyad zai nema daga gareni da zan iya hana shi, koda kuwa rayuwata ce.
Ba zan iya mishi musu ba,……
Ba zan iya bijirewa umarni ko son zuciyan shi ba,…….
Duk inda zai tafi na amince zan bishi…..,
ko a wani lokaci……1
STORY CONTINUES BELOW

Hakan ne kuwa ya faru,
Wannan daren ya zamo mana ɗaya daga cikin muhimman dararen da ba zamu iya mantawa dashi ba har ƙarshen rayuwan mu.
Ranar da muka tashi daga abubuwa guda biyu muka koma ɗaya mai inganci,
Mun sauƙaƙa ciwon zuƙatan mu, mun magance ƙishirwan mu, hankalin sashi ya kwanta da samun nutsuwar sashi…….. Amincin Allah ya tabbata akan manzon tsira S.A.W da iyalensa da sahabbansa baki ɗaya.
***********
Shigowa bedroom ɗin sadiya Sulaiman yayi ya hango ta zaune a jikin bedside drawer tana ciro abubuwan dake ciki.
Sallama yayi mata kafin ya karasa ciki tayi saurin tashi tare da ajiye sarƙoƙin dake saman cinyan ta tun kafin ya karasa inda take ta karaso shi ta karɓi briefcase ɗinshi tare da mishi brief hug tana masa sannu da zuwa.
“Sorry dadyn Arif bansan ka iso bane, zauna bari naje na kawo maka ruwa kasha”
Fita tayi takai jakan nashi bedroom ɗin ta ajiye sannan ta koma kitchen ta ɗauko ruwa mai sanyi da cups a kan tray ta dawo ɗakin,
Hulan shi da takalmin kafanshi ta karɓa ta kaisu maxaunin su na asali sannan ta ɗauko mishi kaya da kuma takalman yawo a gida wanda zai canza dasu idan yayi wanka.
Dawowa gefen shi tayi ta zauna cikin kulawa tace
“Yaya aikin, wanka ne first ko cin abinci?”
“Aiki alhamdulillah my Sady, bari na fara wankan dai tukunna garin a ɗan kwai zafi, amman wannan jewelries da kika bazasu a ƙasa haka me zakiyi da su?”
Kallon su tayi sannan ta ɗago tana kallon shi fuskarta a sake tace
“Gold ɗina ne, Siyar dasu nake son inyi”
“Saboda me yasa? Kina da wani bukata na kuɗi ne da ba zaki iya tambaya na ba sai kin sayar da gold ɗinki?”
Girgiza kai tayi tace”no I don’t need any money bani buƙatar su ne a yanzu nake son in siyar na baka kuɗin”
“A dalilin mene? Did i ever mention to you that i am broke kuma ina bukatar kuɗi daga gareki?”
“That’s not the case Habibi, inaso in kawar da duk wasu distractions da zasu iya shagaltar dani a hanyar niman aljannata ne, lokacin da abubuwa suke a jagule golds da sauran kayan kuɗi da ƙawa sune suka zamo abinda suka fi soyuwa a zuciyata fiye da gudan jinina da rabin raina, shiyasa yanzu nake son in salwantar dasu saboda sharrin zuciya kada ina comparing son da nake wa family na dasu”
“Wannan ai saka damuwa ma kai ne Sady, ta yaya za’ayi wai kayan ado suna distracting ɗinki daga kanmu? You are a changed person now, kin canza baki buƙatar salwantar da komai don samun wani abu, kin cancanci samun komai na jin daɗin rayuwa ki cigaba da saka gold ɗinki kina min ado dashi ina gani ina jin daɗi kinga ma sai su zamo miki silar shiga aljannar”
Girgiza kai tayi da murmushi a kan fuskar ta
“A’a dadyn Arif, thank you for trusting me amman ba zan iya ba, na riga nasan kaina idan zanso abu ko menene bani masa so kaɗan, zan saku fashion masu tsananin kyau naci gaba da maka ado dasu amman wannan kam idan ma ba zaka karɓa ba a sayar ayi amfani da kuɗin ma marayu ko a raba ma ƴan uwa, ko cikin kids account din su Arif ma a siya a ajiye musu nikam bani buƙata”
Taɓe baki yayi yace “to shikkenan duka za’a haɗa ayi, Allah ya baki lada ya albaekaci niyyan ki, amman ko ɗaya ki cire ki ajiye ya zamo miki kaman kadara saboda tasowan emergency tunsa bamu san ne gobe ta ƙunsa ba”
Saboda baiyi mata musu a nata ra’ayin ba yasa shima babu jayayya tace toh. Da hannunsa ya ɗauka mata wani wanda ya ɗan fi tsada don da hannunshi ya siya mata shi a Dubai tun lokacin tana amarya.
******
9:05am
Tsaye nake a gaban cooker ina tafasa tea mai kayan ƙamshi, ta baya naji an rungumo ni tare da placing light kiss a kafaɗana dake a buɗe,
Ko ba’a faɗa ba nasan mutum ɗaya ne zai iya min haka a duk duniya.
Murmushi na ɗaura a saman fuskana na juyo tare da sauƙe kaina ƙasa don wani mugun kunya da nauyin Zayyad nake ji a yanzu,
“Ina kwana babylove”
STORY CONTINUES BELOW

“Lfy lau, yaya gajiya”
“Gajiya yabi lafiya” na faɗa can ƙasan maƙoshi tare da juyawa naci gaba da antaya abinda nake zubawa cikin tukunya.
“Ai na tabbatar da ke ɗin mai lafiya ce so nasan dole kin gaji amm…..”
Da sauri na rintse idanuna jin na takalo ma kaina jangwangwam, “Babylove dan Allah kayi shiru.. Please” na faɗa still idanuna a rufe.
Dariya yayi da ganin haka yace “Allah ya tsaga ma ɗan adam baki don yayi magana ne amman ni sai ace nayi shiru? Anyways me kike dafawa ne bayan kinsan anytime odern mu zai uya ƙarasowa? Bani son kina wahalar min da kanki a nan idan kina son gajiya ne just take care of me.. i will make you tired”.
Girgiza kai nayi ni bansan lokacin da Zayyad ya zamo haka ba, magana ba magana ba sai ya hau fassara kan al’amari.
“Na sani, nayi kewar shayin gida ne nake son in haɗa irin shi na samu na ɗan watstsake jini”
“Ohh sorry na tara miki gajiya kou?”
Ban kula shi muka ja maganar da nisa ba don nasan abinda yake so kenan, ya ƙaraso jikin gas ɗin yana leƙa abinda ke cikin tukunyar a ɗan tsorace,
“Woooh! What’s with these bubbles? Baki jin tsoron zai ƙona ki “
“Tafasan ruwan ne zanji tsoro baby kaman ba mace ba? Idan da kuma tuka tuwo ne ba zaka iya gani ba, da zafin shi haka za’a dinga jujjuya shi”
Jinjina kai yayi looking impressed ” kinsan ni ban taɓa shiga kitchen ba, koda wani abu ne na uzuri ya kaini saidai na tsaya a bakin ƙofa…aunty bata taɓa barina na shiga tana tsoron kada idan naje kusa da wuta ciwona ya tashi wani abu ya same ni a dalilin haka”
“Allah ya saka ma aunty da aljannah da ta kula da kai bata barka ka cutu ba, she is truly a good mother and a role model”
na juya zan bar mishi wurin don zuwa na maida sugar a wurin zaman shi ya dauke ni cak ta baya hannayen shi a kan cikina yana juya ni a hankali a tsakar kitchen ɗin tun ina ƙanƙame jikina har na sake na ɗaura kaina a gefen wuyan shi tare da lumshe idanunna ina shaƙar turaren shi mai daɗin ƙamshi zuciyata tana daɗa tsananta bugu,
“Kin cike min gurbin zuciyata Saudat… Thank you” murmushi nayi da jin haka, ina jin daɗi a ko wani lokaci idan Zayyad ya buɗe cikinsa yana faɗa min kalamai nasu daɗi, suna matuƙar sakani nishaɗi “ina ƙaunar ki babes, yanzu kece komai nawa”
Hannuna na saka a gefen fuskar shi ina shafawa, cikin raɗa nace “na gode da ka bani dama, thanks for choosing me babylove… I love You”
“Yauma mu koma bakin ruwan nan ko? I want to swim”
Da sauri na buɗe idanuna jin ƙaran tafasan tea dina a kan gas wanda har ruwan ciki ya kusa ƙarewa, nayi saurin sauƙa daga jikin shi ina girgiza kai naje na kashe cookern na sauƙe tukunyan a kai.
“A’a har yanzu fah bawai na daina jin tsoron ruwan bane, phobia sai a hankali yake tafiya a ɗan ɗaga min ƙafa zuwa wani lokaci idan tsoron ya ragu sai mu koma”
Tunda na juyo na fara mishi magana ya ƙura ma lips ɗina dake ƙyallin lipgloss idanu
“Tsoron ruwan kike yi har yanzu da gaske ko kuma tsoron wanda zai shigar dake ruwan?” Ya faɗa tare da ɗage giran shi ɗaya, yana daɗa takowa zuwa inda nake tsaye “idan ma da gaske ruwan ne you know nasan yanda zan kula dake…ba zakiji tsoro ba i promise” ya ƙarasa tare da manna lips dinshi saman nawa…….
…..banyi KUSKUREN zaɓen Zayyad a matsayin namijin da nakeso na karashe rayuwata dashi ba, ko zan iya cewa banyi KUSKUREN roƙon Allah ya bani Zayyad ba, dukda ina kaunar shi a zuciyata amman na zaɓi na roƙi Allah yanin zabin alkhairi, ya bani miji na gari wanda zai kula dani ya bani farincikin da ban samuba a gidan aurena na farko, shiyasa banyi mamaki ba da canzawar al’amarin ƙaddara ta lokaci ɗaya saboda nasan Allah mai iko ne a kan dukkan komai, kuma mai canza abinda yaso a lokacin da yaso, sannan a duk lokacin da yaso zartar da al’amari zaice kasance ne…sai ya kasance.
Zayyad mutum ne mai kulawa, kyautatawa, adalci, haƙuri, da kuma tarin soyayya a tare dashi, sannan nima ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin nayi masa biyayya, na kyautata mishi…. honestly lokacin da nake ƙuntace a wuroɓokki a wannan ɗaki mai duhu da zafi a ƙasƙance a wulaƙance ga tarin azaba daga wurin wanda yake a matsayin shugaba wanda ya kamata ya zamo adali a gareni…..ban taɓa tsammanin akwai ranar da zan kuɓuta ba, ban taɓa tunanin akwai ranar da zan fito na canza matsuguni harda matsayi ba, amman duk wanda ke cikin wani matsala ya yarda ya fawwala ma Allah komai tabbas wata rana abubuwa zasu sauya domin babu yanayi mai tabbatuwa a duniyar nan walau na daɗi walau akasin shi ko shi duniyar ma gaba ɗayanta ba matabbata bace.
STORY CONTINUES BELOW

Sai gashi nima Allah yayi min sauyi da mutumin da ko yaushe yake ƙoƙarin tabbatar da ina cikin farinciki koda a lokacin da bayi cikin ƙoshin lafiya bayi barina cikin ƙunci, he always make sure that I’m smiling.
Watannin mu shida muna faman jinya a Maldives, nasan ba zakuyi mamaki ba idan nace yanzu haka ina ɗauke da cikin wata 5 dukda shi patient ne amman bayi wasa, har ga Allah banso ɗaukan ciki da wuri haka ba amman kuma da labarin abin ya riske shi naga irin farincikin da ya shiga sai naji hankali na ya kwanta nima na shiga cikin farinciki ko babu komai yanzu Allah ya kawo min lokacin da zanga gudan jini na, shima ba da ƙasƙantaccen bawa irin yarima ba, da sarkin dake mulkin zuciyata a Yanzu bawan Allah na gari mai kiyaye dokokin shi.
A watan mu na takwas muka ɗauki hanyar 9ja lokacin cikina nada wata 7 ya fito ɗan ɗul abinshi gashi nayi ƙiba na ɗanyi duhu saboda sanyi amman jikina fresh alamun na samu hutu na ciko na ƙara kyau masha Allah.
Kunyan haɗa ido da aunty Amarya da innata nake ji kaman yanzu na fara aure, naso ma da zaman mu mukayi na aihu abina a can saidai kawai su ganni da yaro ko yarinya amman da na faɗa ma Zayyad ra’ayina ban samu amsan komai ba sai kallon da ya jefa min irinna ‘yarinya har yanzu yarinta na damunki’ ai kuwa cikin satin ya tattaro ni muka dawo.
Tun daga airport kada kuso kuga tarba, murna biyu ya tara wannan dandazon mutanen, da murnan dawowan Zayyad gida cikin ƙoshin lafiya da ɗokin ganin cikin jiki na da tun satin shi guda a duniya labarin shi ya gama bazuwa a cikin dangi.
Tunda mutanen nan suka ga tsulun cikina suka rasa yanda zasu saka ni su saka kansu saboda murna sai kaffa_kaffa suke dani wasu cikin su ji suke kaman idan tafiya ma ba zan iya ba na basu suyi min,
gidan aunty Yusrah aka wuce dani saboda Innata a can ta sauƙa kuma ba daɗewa zatayi ba zata koma, shiyasa aka roƙa min Zayyad da ƙyar shi da aunty amarya suka yarda naje na ƙarasa wuni mata sai da dare ya ɗauko ni mu dawo.
Yanzu haka zaune nake a gaban plate ɗin abinci dukda yunwan cikina na kasa cin abinci Inna ta saka ni a gaba sai risgan kuka takeyi kaman Allah ne ya aiko ta.
Numfashi na furzar ga tarin gajiyan da na dibo a zaman jirgi kafafuna sunyi tsami amman bata barni naci abincin va ma ballantana na kwanta na huta,
“Inna dan Allah kiyi haƙuri ki daina kukan nan, ya isa haka please”
Zaran tissue ɗaya tayi daga cikin kwalin shi da na ajiye mata a gabanta ta share hawayen idonta sannan ta ɗago tana kallona wani kukan na shirin kwaçe mata,
“Kukan daɗi ne boɗɗi dan Allah ka barni nayi, har yanzu banshan wani irin godiya zanyi wa Allah ba da tarin niiman da yayi mana ki kalle ki fah!”
“To shikkenan tunda kuka kikeyi na koshi da abincin bari na tashi na tafi ko zaki bar zubar min da hawaye kada azabar Allah ya sauƙa a kaina” na fara ƙoƙarin tashi
Saurin share hawayen tayi wannan karon da bakin hijabinta ta riƙo ni na dawo na zauna sannan ta saka ni na fara cin abincin har na gama bata sake koda tari ba.
Ƙarfe 8 sharp aunty Amarya ta taso keyar Zayyad yazo ya ɗaukeni, itama yta kasa ta tsare kan ba zamu koma gidanmu ba har sai na aihu, muna zuwa naga ta tarkaso min kalolin abinci bayan naje na gama ciko cikina a gurin aunty Yusrah don har awara da dankali suyan gefen titi saida nasa aka siyo mana mai shegen yawa muka ci duk ba tare da sanin Zayyad ba don nasan ba bari zaiyi ba idan ya sani.
Duk yanda naso fahimtar da ita a ƙoshe nake ta kasa ganewa ta tasa ni a gaba ina tura abincin nan, da na samu ta kauce na janyo ɗanta yazo na ɗura mishi saida ya kusan cinyewa tass na kore shi kafin ta dawo.
Kafin mu kwanta duk mutanen dake rayuwa a gidan saida suka zo muka gaisa suka taya mu murna banda mutum ɗaya tol a cikinsu wato NANA, har gobe bani tunanin duk abinda zanyi wa yarinyar nan zata soni, haka Allah yakan halicci mutane wani babu abinda kayi mishi baka ci mishi ba baka sha mishi ba amman haka kawai yaƙi jininka.
Daga bakin ƙofar parlour junior ya tsaya yana kuka tunda muka zo gidan yaƙi shigowa part ɗin aunty,
Zuwa Farouk yayi yana janyo shi da karfi amman yaƙi shigowa, saida ni da Zayyad muka tashi muka isa wurin da yake a tsaye Sannan ya fara ƙoƙarin guduwa don daman a dole aunty ta saka shi yazo ya gaida mu.
STORY CONTINUES BELOW

“Boyfires yaya akayi ne? Wa ya taɓa min kai kake kuka?”
Ɗago ido yayi ya galla min harara gashi a yanzu tsayin shi har ya kusa ɗare nawa.
“Ni kada ki sake kirana boyfriend ɗinki tunda kin yaudare ni kinje kin auri ya Zayyad bayan da kika zo gidan nan kafin kowa ya kula ki ni na fara kula ki amman kika ce shi kike so bani ba, ko dan shi yana da dimples ne ni bani dashi? Na dai san ba fini kyau yayi ba”
Riƙe baki kawai nayi ina kallon yaron nan, ban taɓa tsammanin abin nashi da gaske bane sai gashi zoƙai_zoƙai dashi yana ɓare mana baki.
Hannu Zayyad ya ɗaga ze kai mishi bugu nayi saurin rike shi.
“Easy bab… hamma Zayd ka bari mu sasanta wannan case din namu ne mu biyu, ni nayi yaudara ni zan gyara kuskure na” na juya wurin junior dake faman share hawaye nace “ka gani boyfires kayi haƙuri da yaudaran da nayi maka ba laifi na bane yayanka ne yayi maka overtaking kuma kaga yanzu ni nayi maka lutiya ko kana son lutiyan mace?”
Girgiza kai yayi nace ” to yanzu dai ka bari idan ka gama makaranta kayi babba irin yayanka idan ƙanwata indo tace tana sonka zan baka ita kaji?” Saurin washe baki yayi yace “wannan sistern ki fara kyakkyawan nan… Wata idonta irin na cat?” Gyaɗa kai nayi kafin na bashi amsa Farouk yayi wuff yace “Aisha nawan ne kike alƙawarin zaki bawa wani yaro bayan na riga da nace ita nake son na aura idan ta girma?”
A firgice na juya muna kallon kallo da Zayyad 😳, idan ba Sa’a ba tarihi ne keson ya maimata kanshi…. Lallai akwai cakwakiya…….
***********
“A’a fah! Ni na faɗa maka babu inda zaka je tunda fitan ba wani mai muhimmanci bane dan Allah ka zauna, i am enjoying your company here please stay habibi”
Sadiya ta faɗa cikin shagwaɓaɓɓen murya hannunta zagaye a wuyan Sulaiman, gashi tasha ado taci kwalliya cikin lace yar ubansu jikinta na fitar da wani sassanyar nitsatstsen ƙamshi dukkan su sun bawa ƙofa baya har muka iso muka yi sallama basuji ba hankalin su ya tafi can duniyar masoya.
“Business meeting nefa kike cewa ba mai muhimmanci ba habibty?”
Turo ɗan cukulin bakinta tayi tace “ai idan ka tafi mantawa kakeyi dani shiyasa ya zamo mara muhimmanci”
“Stop being dramatic”
“I’m not being dramatic, duk abinda zai mantar dakai ni zan hanaka yinshi ina da daman hakan” ta ƙarasa tare da yin farr da ido, lashes ɗinta da suka sha mascara ga eyeliner a samanshi sunyi matuƙar yi mishi kyau da tayi haka,
“Kiyi haquri i will text you once I get there now let me go please”
“Idan kuma ka manta da tsarabana gobe ba zaka fita ko nan da bakin ƙofa ba agree?” Gyɗa kai yayi tare da amsawa da “agree!”
Ta sauƙe hayyanunta daga wuyan shi “Allah ya kaika lafiya ya dawo min dakai lafiya my happiness, Allah ya bada Sa’a” ta faɗa hannunta a kan cheeks ɗinta tana nuna mishi yayi kissing ɗinta a wurin.
Saurin gyaran murya Zayyad yayi kafin sulaiman ya aikata abinda aka umarce shi suka juyo suna kallon mu.
“Mai tumbi!! Welcome… welcome… Ku shigo daga ciki” ta karaso taja hannun Saudat suka shige ciki suka bar Zayyad da sulaiman tsaye a wurin.
Murmushi Sulaiman yayi yazo ya rungume ɗan kaninshi dake tsaye a bakin ƙofa yana ta faman washe haƙwara
“Welcome back bro… Munyi kewarka”
“Nima nayi kewarku babban yaya, ina yarana suke”
Jan hannun shi yayi shima suka shiga ciki yana faɗin,
“Har yanzu basu dawo daga school ba amman sun kusan tasowa”
Babban yaya bai daɗe a ciki ba ya tafi wurin aiki tare da tunasar ma Zayyad da ya gama hutawa kujeran shi yana nan yana jiran shi, shima bai wani jima sosai ba sukayi sallama da Sadiya ya tafi kan cewa anjima zai dawo ya ɗauke ni,
Nayi tunanin zatakullace ni da wani abu saboda case ɗin Sulthana amman har cikin zuciyanta babu wannan a ciki ta riga da ta cire shi tuntuni, itace ma take bani labarin wai baban su yace idan bata fitar da miji nanda one week ba zai aura mata wanda yaso don ya gaji da ganinta a gabanshi.
Munsha hira da raha da sadiya har yamman zubur kafin Zayyad ya dawo ya tattare ni muka koma gida, as expected muka samu abincin aunty na zaune yana jiran mu, haka yauma ba don yaso ba da wayo na ɗura mishi don ni na gama cika nawa cikin a gidan babban yaya.
Kwanci tashi asaran mai rai…..yau da gobe bata bar komai ba…..na aihu lafiya na samu ƴa mace a bisa tursasawa na Zayyad ya saka mata sunan aunty Amarya MADINA muna kiranta da MAMIi yarinya kyakkyawa mai kama sakk da ubanta harda dimples ɗinsu sai a kala ne kawai ta ɗibo ni, ai kuwa abin yayi ma aunty Amarya daɗi ta rasa yanda zata saka mu saboda murna har ta zamo ma kaman itace mai rainon mami saboda tsananin so, takwaranta daga ɗan da yafi soyuwa a zuciyanta ko nice na ɓata wa mami tofa sai naga ɓacin ranta shiyasa da yarinyar ta fara tasawa na dage ma Zayyad muka tashi a gidan muka koma namu don indai tana gaban aunty Amarya ina tsoron ba zan iya mata tarbiyya yanda ya kamata ba don zata iya tashi mun a sangarce ni kuma ba zan lamunta ba.
*
*
*
*
*
Haka rayuwa taci gaba da tafiya mana, yau zuma gobe maɗaci…yau a shirya gobe a ɓata…yau ayi farin ciki gobe ayi baƙin ciki……yau a ƙaru gobe a ragu….
Duk sa’ar da kake dashi a duniyar nan babu yanda za’ayi ace kullum kana samun abinda kake so ne ɗari bisa ɗari, don haka aci gaba da haƙuri da rayuwa ana addu’a Allah zaiyi mana mawafaqa.
Shekarun mami 1 da rabi a duniya na sake samun wani cikin, Zayyad ya kasance miji na gari kuma yana iya ƙoƙarinshi wajen ganin ya zama uba na gari amman babban abinda yafi maida hankali a kai shine da zaran magriba tayi indai yana gari da kanshi zaije ya tattaro yaranshi ya shigo dasu cikin gida ya rufe ƙofa sannan ya bisu da addu’o’in kariya irin wanda Annabi S.A.W ya koyar damu gudun kada suma su faɗa a cikin halin da ya tsinci kanshi lokacin yana yarinta.
ALHAMDULILLAH
Ina daɗa godiya ma Allah da ya bani ikon fara wannan littafi da kammalashi lafiya, alkhairin ciki Allah ya tara mu a cikin ladan kurakurai kuma Allah ya yafe mana.