KASAR WAJE CHAPTER 18 BY MARYAM DATTI

KASAR WAJE CHAPTER 18 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yace zan amince bisa sharad’in idan kika dawo zaki ajiye aikin café ki yi zamanki gida zan riqa iya qoqarina wajen biya miki dukkan buqatunki a matsayina na mijinki wanda ni Allah ya d’orawa nauyinki..+

Kallonsa take sosai bata fahimta ba sosai.. Yace kin amince.? shiru tayi ta d’an sunkwi da kanta qasa yasa kyawawan hannayensa ya tallafo fuskarta yana kallonta yace.. ” baby wlh sam banason yadda kike wahala a café sannan uwa-uba café kamar hotel yake kowa na shiga a riqa kallonmin ke duk inda na ke hankalina baya kwanciya da sanin wani na kallonmin sirrina mallakina kawai daurewa na ke yi sabida na san kina buqatar aikin ya d’anyi shiru yana kallonta..

Ta saki hawaye mai tsawo a ranta tana ayyana idan ya ganta a fation parade qila zuciyarsa bugawa za tayi kenan wasu hawayen suka sake biyo kuncinta yana kallonta hannunsa yasa a hankali yana share mata yace ” baby ina sonki kamar yadda na ke fidda ko wani iska na numfashina” wannan yasa ina jin kishinki fiye da yadda na ke son rayuwa a wannan duniyar pls ki taimakamin ki kiyi haquri da sharad’ina ki zauna a gida na miki alkawarin zan fara dawowa gida brk daga supermarket sannan ko mun fara school da zarar ba  mu da lecture zan dawo gida gurinki zan daina barinki ke kad’ai zan saya miki katifa na saka a d’akina na masallaci muna tafiya aiki tare kina baccinki zan… Tasa d’ora bakinta kan nasa tana sakin kuka sosai…

Shiru yayi ya rungume ta tare da runtse idanunsa a yayinda tana kuka tana tunani bata tab’ajin dana sanin kasancewarta model ba kamar yau dana sani take ta maimaitawa a zuciyarta na maiyasa ta fara

.? mai yasa bata hakura da aikin café kawai ba..? Mai yasa da ta fara sonsa bata fad’awa mominsu gaskiyar waye shi ba ta kuma fad’a mata tana sonsa a haka zata zauna dashi ba wayyo ta qara sakin kuka still tana rungume jikinsa..

Sosai suka dad’e rungume kowanne da damuwarsa hakan yasa suka manta da rungumar domin ko wannensu na jin cewa yana buqatar hakan a yayinda a karon farko Yusuf ya kyale hayfa tayi kukanta mai isarta kafin ya d’agota yana kallon yadda har idanunta sun kumbura

A hankali ya zare ta daga jikinsa ya mik’e zuwa falo ya bud’e fridge ya d’auko mata fresh milk ya dawo ya zauna ya fara bata a hankali take karb’a tasha sosai kafin ya ajiye ya shafa fuskarta ya mata peck yace “baby ina zuwa” toh tace a hankali ya fito ya bar gidan 

Bayan fitarsa ta d’auki wayarta ta jefa layin Armando..

Bugu d’aya ya d’aga “queen”.! Ajiyar zuciya tayi ta fara gaisheshi saidai bai idda ansawa ba ya fara tanbayarta me ke faruwa jin muryarta da ta dashe da kuka..

fashe masa da kukan ta qara yi tace “daddynmu ne ya rasu” ajiyar zuciya yayi ya fara lallashinta yana tanbayarta yaushe mai kuma ya faru da shi nan ta bashi labarin komai kafin ta fad’a masa tanason ya mata bucking na jirgin safe gobe

d’an shiru yayi domin gaskiya yanzu baya son ta motsa ko ina koda a cikin Canada bare har Nigeria jin shirunsa tace “babu fly goben ne”?

Yace No queen ay ko wane rana akwai fly na Nigeria kawai banason tafiyar ne yanzu bai kamata ba ko kinsan dukda irin shirmen da kike kwanan nan amma kin samu vote sosai a result d’in wk d’in nan kuma bama a turo da results d’in America da Italy da Paris ba jst Brazil da Colombia da Venezuela da Spain ne yake qasa inada tabbacin akwai alamar Zaki samu gala amma kinata wasa yanzu kuma tafiya why “Queen”?

Shiru tayi.. Ajiyar zuciya yayi yace zaki yafi but pls jst 4dys ki dawo in ba haka ba wlh zaki sakani rigima da Bunill haka kike so nayi ta samun problem da Bunill da su Raudha a kanki..? Ah ah tace a hankali

STORY CONTINUES BELOW

Yace to pls my queen kije ki dawo a 4dys da na baki suma 4dys d’in na tabbata sai munyi rigima da bunill..

Toh tace.. Yace yawwa yanzu zan miki bucking sai a kawo miki ticket d’inki da tsaraba ki kaiwa su khairat in jini..

Toh tace ta masa godiya su kayi sallama.. Tayi shiru tana nazarin yadda aikin models ke kafa mata qa’idoji ko mijinta da ke da mallakinta baya kafa mata haka..

Kallon liliana raudha tayi cikin b’acin rai tace ga shegiyar nan naga 2dys bata jigata sosai da alcohol d’in ko jininta ya karb’eshi ne ..?  Liliana tace ko kuma Angel d’inta ya gano shirinmu ya ruhuza ba..

Tsaki raudha tayi tace wlh kuwa bazan tab’a hakura ba ko ta wani hali sai na hanata samun gala d’in nan ta jefa layin Vivian..

Vivian tayi tsaki kafin ta ansa.. Raudha tace kina aikinki kuwa..?

Vivian tace sosai ma domin yanzu a gabana ma take ci ta sha

Raudha tace kuma yana fara aiki a gabanki in tasha ko taci..? Vivian tace eh domin ita da Armando ma kullum rigima yanzu last tana ma zaune a nan ya kirata tsaki ta masa..

Raudha ta saki murmushi tace to Ya yayi da ta masa tsakin.? Vivian tace wlh ko a fuska bai nuna ba yana son yarinyar sosai gaskiya..

Raudha tayi tsaki tace munafiki ba zan kuwa rabasu taci gaba ki maida hankali kici da aikinki da kyaw ta tsinke wayar tana tsaki tana bawa liliana labari

Vivian ta saki tsaki tace munafukai sakarkaru taci gaba da aikinta..

9:34pm ya dawo gidan tana kwance d’an bacci ne ya fara d’aukarta ta d’ago ta ganshi da kaya niqi-niqi ta zauna ta jingina bayanta da gado tana kallonsa ya ajiye ya d’auko akwatinta empty ya fara jera mata kaya ya d’an juya yana kallonta yace kwana nawa kike son yi..?

Itama kallonsa ta keyi zuciyarta duk ta gama karyewa amma tace 4dys..

“Yace OK ya ci gaba da jera kayan ya saka mata kala 10 wato ya saka mata komai ya maida ya kulle akwatin ya had’a kayayyakin da ya shigo da su da bata san menene ba a wata kyakykyawar jakar supermarket d’in su Yusuf d’in ya jingine jikin akwatin ya shiga wanka yayi ya fito suka yi sallah tare kafin tace zata je masallaci suka shirya da abincinsu suka wuce hannunsu na sarqe. tuni Armando ya gamawa hayfa komai aka aiko mata da ticket da kayan 6:am kamar yadda ta fad’a masa..

Suna masallaci tana aiki a laptop ganin msg d’in Armando wai fly d’inta na 9:22 am ne ta jira Yusuf ya shigo daga patrol ta ke fad’a masa tayi bucking ta fad’a masa tym d’in tafiyarta..

Shiru ya d’anyi yana mamaki sosai yadda komai na ta kamat na manyan mutane ta keyi saidai bai kawo zargi ba ya shafa fuskarta yace Allah ya kaimu.. “Amin” tace tana kallonsa itama ta furta “ina sonka yadda ko wani irin kalma zanyi anfani da shi wajen bayyana maka bazai gamsar da ni na fad’i matsayinka a zuciyata ba”.. Lumshe idanunsa yayi ya qara shafa fuskarta a hankali ya janyota jikinsa ya rungume sosai suna sakin ajiyar zuciya a tare..

*********

Suna zaune gun makoki taji wayarta na ringing ta miqe a hankali ta fito tana kalle-kalle kafin taje can stor ta shiga d’aga wayar..

Wait mai yasa bakada hakuri ne akan hayfa..?

Ajiyar zuciya kamal yayi yace na jiki shiru tun jiya.. Qaramin ajiyar zuciya tayi tace 50k fa kace za ka bani sai nayi maka wasa..?

Tace wlh bata zo ba kuma na bugi cikin Suwaiba amma tace basusan program d’in hayfar ba kasan yayyun na ta duk kamar ita suke mugun jan kai da zurfin ciki kabari muyi komai a hankali indai za tazo zan sani

Ajiyar zuciya yayi yace “OK” sai na jiki t
oh..

Ajiyar zuciya itama tayi tace IA ta kashe wayar ta koma kiching zasu fara rabon abincin rana..

STORY CONTINUES BELOW

Ammah dai har yau ba um bare um um anyi anyi gashi hawayen ma babu ko d’is inda hakan ya fara d’aga hankalin goggo alje da Suwaiba yayinda babansu yace su kwantar da hankalinsu daga baya zata yi IA..

Gidan rasuwar kamar gidan biki abincin ma order suka bada anayi safe rana yamma ake kawowa…

4:55am Yusuf ya fad’awa Hamzad maganar tafiyar hayfa ya musu ta’aziya suka baro masallaci zuwa gida suna hanya yayi waya da yasir ya suka iso yana ma qofa yana jiransu suka shiga gida su duka ukun inda yasir yayiwa hayfa ta’aziya kafin suka shiga direct wanta ta shiga Yusuf ya fito falo ya had’a mata brkfst yasir yace shi d’umame ma zaici Yusuf ya d’umama masa shinkafa da wake jolof da tea ya karya ya shiga ta fito wanka ta fara shiryawa doguwar wata abaya ta saka mai azababen tsada a aikin Ontario aka bata rigar a naira rigar ta kai 211k da qaramin gyalensa tasa d’an lauffers d’inta mai kyaw na kamfanin Zara flat sosai ta D’aura agogo ta nad’e kanta ta zauna yana kallonta yana jin yadda wani masifar sonta da sha’awarta ke qara huda ko ina na zuciyarsa da jikinsa…

A hankali ya gama bata bread da tea d’in tasha ya kwaso mata kaya ya fito da su yana falo tayi maza ta bud’e gaban wani akwatinta ta d’auko wayar da bunill ya basu ta ajiyewa salma za ta bayar a ajiyewa salmar domin tace nx mth zata shiga Nigeria itama..

Koda ya shigo tana tura wayar a jakarta bai gani ba a hankali ya qarasa gabanta yayi shiru yana kallonta kafin ya sunkuya ya d’ora tattausan bakinsa a kan nata ta lumshe idanunta a hankali sabida a duk sadda wani gab’a nasa ya sauka a jikinta ji take kamar tana kan gajimare

A hankali yake mata wani hadd’ad’en sihirtaccen kiss yana tsotsar bakinta kamar yana shan sweet da ya kusa qarewa itama tana tayashi da dukkan sadaukarwa na zuciyarta da ruhinta wanda numfashin da take ja kawai ya sanyashi wani irin d’an rawar jiki wajen janyota ya qara mannata da jikinsa kamar yana shirin shigar da ita jikinsa

Kusan 20mnts suka d’auka suna yi kamat zasu cinye harsunansu da labb’ansu domin kuwa tas sun gama zuqe yawun juna kafin a hankali ya d’agota yana kallonta da idanunsa da suka gama rinewa itama duk ta gama hargitsewa gashi bata warke ba bare su rage zafi kan ta wuce

A hankali ya manna mata peck a goshi ya riqo hannunta suka fito yasir na waje yana jiransu suna tsaye aka taxi ya tsaya wani ya fito ya miqawa hayfa ticket da wata qaramar paper bag ya musu sallama ya wuce suma suka tsaida nasu taxi suka shiga sai airport..

Koda a ka kira matafiya har a d’an k’wallah tayi inda suka manta da wani yasir suka rungume juna sosai yasir ya juya zai fit a sai ga wasu y’an jarida suna biyo wani mutum da gudu yaqi magana da su suna binsa

A hankali suka rabu inda bai ko k’ara magana ba ya juya ya dafa kafad’ar yasir a kan su wuce sun fara tafiya yasir ya juya saidai yaga y’an jaridar sun zagaye hayfa tana qoqarin wucewa sun hanata mamaki ya juya ya fad’awa Yusuf yaga tuni yayi gaba tsayuwa yayi yana mamakin why suke binta ita da mutumin..?

da sauri ya juya ya fara komawa saidai ko kafin ya isa gurin hayfa ta samu tserewa y’an jaridar har ta shiga wuce abinta a wasu ya gani ya matsa kusa da su yake tanbayarsu “mai waccan yariyar tayi y’an jarida ke binta”..?

d’aya budurwar tace “to aikinsu kenan ay bin taurari”.

Cikin rashin fahimta yasir yace taurari kuma..? Yarinyar tace “eh mana ay yarinyar tauraruwa ce..

Yasir dai still bai gane ba yace “tauraruwa na me”..?

Yarinyar ta bud’e jakar system d’inta ta d’auko jaridar “Canadian Summer” ta bud’e tana nuna masa hayfa tana qarawa da bayani yarinyar sabuwar fuska ce y’ar Nageria ce amma ta shigo duniyar d’inki da qafar dama..

Ruggg Yasir yaji zuciyarsa nayi zaiyi magana yaji muryar Yusuf daga nesa yana kiransa a hankali ya d’ago yana kallon Yusuf sam ya kasa furta komai Yusuf ya masa alamar zai tafi ya barshi ya kalli yarinyar yace “pls zaki iya bani magazine d’in”?

Shiru tayi kafin tace “OK” ta mik’a masa ya mata godiya sauran duk sunata kallonsa

Bayan wucewarsa d’ayan baturen da suke tare da yarinyar yace da ganin yaron irin fan d’in nan ne da ke kamuwa da son abinda ko cikin baccinsu ba  zasu samu ba

Sauran suka fashe da dariya…

Suna taxi yasir yayi shiru hakan bai saka Yusuf ya fahimci komai ba kasancewar shima shirun yake har yasir ya sauka pool Yusuf ya wuce supermarket ko t.shirt bai saka ba sai a can ya ansa extra da ake ajiyewa in case..

Tunda yasir ya gama aiki ya zauna ya fara bud’e magazine yana kallon hayfa da itace ta cika magazine d’in sai hotunan turarruka da wasu kayan cosmetics da ake tallarsu suna nan ya fara tariyo a lot tink kallon da su Albert suka riqa mata yawan kashe kud’inta ajiyar zuciya yayi ya miqe da sauri yaje barandar pool inda a ke ajiye magazines na masu zuwa shan iska ya fara dubawa d’aya bayan d’aya inda kuwa ya riqa Karo da hayfa a mafi yawan magazine d’in tunda duk na kayan kwalliya ne da suturu

Sosai hankalin yasir ya tashi tayaya..? Why..? Mai yasa tayiwa Yusuf da ke mutuwar sonta da kishinta haka.?

Wani irin Zafi shi kansa yaji zuciyarsa na masa a yadda duniya ke taruwa kallon Fation parade “amma sam mata basu da amana ya furta a ransa” a hankali ya miqe ya nufi d’ayan pool ya fara aukinsa..

Hayfa na jirgi tana hawaye tare da addu’a sosai na fatan Allah yasa Yusuf bai ga yadda y’an jaridan suka biyota ba hannu tasa jakarta saidai ta tuna lokacin kunna waya ya wuce jirgi ya riga ya lula samaniya a dole ta haqura da fatan tana sauka Nigeria za ta neme shi da wannan tunanin taji ta samu d’an samu nutsuwa a zuciyarta..

Yana supermarket yana aiki yana jin kewarta inda ya zaro wayarsa ya jefa layin innarsa suka fara hira

Tace shine baka kira tun ranar ka sanar da mu ba..? Ajiyar zuciya yayi yace ayyuka ne su kayi yawa amma ko bakwai ay baayiba yaci gaba zan bawo Aliy saqo kuyi kud’in hanya sauran a bawa su Qassim

Ajiyar zuciya tayi tace kada ka damu dakwai kud’i sosai gurinmu sauran wanda ka turo kwanaki sannan su Kansu suncemin sunada kud’i hannunsu domin harma sunyi jari suna d’an kasuwanci a makaranta

OK yace suka ci gaba da hira sun dad’e goggo yalwatu na bacci don haka suka yi sallama ya kashe wayar yana turawa Innar lambar Ammah.

A kamfani Bunill ya kalli Armando cikin tsananin b’acin rai yace amma gaskiya kana wulaqantani da muqamina yanzu wannan y’ar tatsitsiyar yarinyar ce take juyaka yadda taga drama .? Armando dai baice qala ba  bunill yaci gaba in banda wulaqanci ka bar yarinya ta sangarce a tarihin kamfanin nan wace model ce ta tab’a tafiya a watan Gala bare a some wk na Gala..?

Armando dai yaqi kulashi tunda ya fad’a masa babanta ya rasu don haka dole su mata uzuri haka bunill yayita bala’insa a qarshe ya hakura ya bar office d’in ransa kamar ya fashe  ya fito su Raudha a na ta aiki a gym an matse har an gaji ganin yanayin da Bunill ya fito daga office d’in Armando suka san rigima ce akan hayfa hakan ya qara faranta musu rai suna murnushi suka gaisheshi ko kullansu baiyi ba ya wuce abinsa Jirginsu na sauka Abuja ko b’ata lkc ba tayi ba wajen d’aukar shatar mota zuwa kaduna..

A kano Innarsu Yusuf ke yiwa goggo Yalwa bayanin rasuwar ta gidansu Hayfa inda goggon tace amma yaran zamani basuda hankali yanzu surikinsa ya rasu sai yau zai sanar da mu maimakon tun narar ma a ce da mu akayi janaza

Itadai Inna bata ce komai ba haka goggon tayita fad’a tace shi Isuhu na lura muguwar kai gareshi kamar ta Inzo Haru su baka sanin cikinsu toh yanzu yaushe zamu tafi..?

Inna tayi ajiyar zuciya tace Na kira Aliyu shi zaizo ya samo mana mota sai mu tafi in muka sh
iga kadunar mu tsaya mu d’auka su Qassim  mu je gaba d’aya

Goggo tace eh hakan ma tunani mai kyaw ne sai mu tashi gobe In Allah ya kai mana rai.. Inna tace IA suka ci gaba da hirarrakinsu na wasu al’amuran rayuwa inda goggon ke cewa Layla ta fiya yanga samari suyita zuwa gurinta tana qin fita ita dai inna bata ce qala ba sanin cewa Layla ta fad’a mata sai ta samu admission zata fara hira da ko waye lokacin hankalinta yana kwance tasan karatu zata fara kawai ..

Koda suka iso Kuse road sosai hayfa ke mamaki ganin tun daga nesa mutane ne a qofar gidansu cike

Toh rayuwar kenan ta zamani indai abu ya faru gidan masu kud’i ko an sansu ko ba’a sansu ba  za a je musu bare nan Ammah na gaisawa da mutane sosai game kyawta lokacin azumi haka tayita rabon abinci da kud’i wannan dalilin yasa nan da nan ta shahara a area d’in kamar ta shekara 20 a kabala

Hayfa ganin cikowa tayi yawa tace mai mota ya shiga da ita har cikin gidansu inda ya wuce dama gate d’in an barshi ne a bud’e suka shige mai motar yayi parking d’an nesa da mutane ya fito ya zago ya bud’e mata a hankali ta sako qafarta waje duk jikinta ya qara sanyi na qara tabbatarwa da tayi tabbas daddynsu ya bar duniya wallet ta d’auka ta sallami mai mota ya wuce mai gadi ya fara shiga mata da kaya tana takawa a hankali ana gaisheta tana ansawa tana wucewa mominsu kawai ta ke so taje ta gani..

Falon ma maqil yake da jama’a wasu dangin babansu wasu bata sansu ba ta fara gaishesu ana mata sannu da zuwa ta gama da su ta nufi saman

A hankali ta Ke shiga d’akin da ke cike Luba na zaune kusa da Suwaiba Luba ta qurawa Hayfa idanu ganin yadda hayfa ta koma tsaf baqa amma kamar haihuwar turai a hankali take ratsa mutane har ta isa gaban ammah da ke zaune kamar zautacciya ta fad’a jikinta tana sakin kuka

Ammah da tun ranar rasuwar bata qara hawaye ba  sai yanzu akaga tayi ajiyar zuciya ta fara hawaye

Mamaki duk d’akin keyi banda suwaiba domin suwaiba tasan yadda ammah ke tsananin son hayfa don haka ganin hayfan ne ya sanyaya mata zuciya taji dama

Sosai ta qara sakin kuka suka fara tare tanayi ammah nayi babu mai bawa wani haquri sun dad’e kafin aka fara lallashinsu da nasiha inda da kyar suka yi shiru suka koma hawaye babu gunjin kukan..

Luba ce ta miqe a hankali ta ratsa mutane ta fito ta shiga wani d’aki a gefen na ammah kamar d’akin hayfa ne ta kulle ta jefa Kira..

Yana Office aiki ya masa yawa domin ya koma CBN saidai yanata bibiyar aikin project d’insu hayfa da Abdulmalik

Kallon wayarsa da ke ringing yayi kamat bazai d’aga ba ganin Auntynsa ya maza ya d’aga baiyi magana ta furta “ta iso yanzu”..!

Ajiyar zuciya yayi yace yanzu zakiga alert na 100k ma namiki qarin 50k akan alqawarinmu, baki ta washe tafara masa godiya su kayi sallama ya fara tunanin zuwa da yamma sannan dole ya bita ya san movement d’inta a Canada domin a yanzu bayaso su b’ata lokaci wajen yin aure..

STORY CONTINUES BELOW

Bayan ta gama Ammah ta d’an kalleta tace ta shiga bayi tayi wanka da alamar gajiya a tare da ita “toh” tace ta miqe a hankali ya shiga bayin na ammah kusan 20mnts ta fito ta shirya cikin blue abaya mai matuqar kyaw da tsada ta yane kanta Suwaiba ta kira Laraba ta kawo mata abin karyawa saidai wani sabon labari ana kawo mata miyar taushen da masa bayan taci tafara jin tashin zuciya mai nauyi inda ko 40mnts ba  tayi da ci ba tafara sharara amai kamat da wasa ta amaye komai ta ma gama gigicewa Ammah tace ta kwanta aka had’o mata tea da kaninfari shima kad’an tasha ta fara maida baccin hanya…

Liliana ta kalli Raudha tace wai haka shi mutumin yace miki Baiga wata mace a gidan ba tun safen da yake qofar gidan..?   Raudha tace eh wai shi da d’ayan d’an uwansa ne ya gani shi da kayan supermarket kuma inda suka shiga taxi

Shiru liliana tayi tace OK amma dukda haka yaci gaba da binsa musamman a kwanakin nan kafin mu wuce Milan kisan matsayarku ke dashi ko zaki samu nutsuwa

Raudha tace eh haka na fad’a masa, Liliana tace jiya Vanessa ke bamu labari lokacin kin fita.. Raudha tace labarin mene.?

Liliana tayi tsaki tace labarin Vote ko kinsan Shegiyarnan taci qasashe takwas..? Zaro idanu raudha tayi cikin tashin hankali tace inji wa..? Liliana tace kinsan Vanessa yayanta Samuel yana aiki office d’in vote na Paris wallahi shi ya bata sunayen inda ya fad’a mata a Canada Khadija da Lorin ne suka ci

Mugun tashi hankalin Raudha yayi ta kasa magana sai kallon Liliana, itama liliana tsabar tashin hankali shirun ta yi a qarshe ganin irin qoqarin da suka yi amma duk ya tashi a banza kenan ….

Yasir wuni yayi duk duniyar ta masa d’aci inda wajajen 5:11 yaga kiran Yusuf amma sam ya kasa d’agawa har call d’in ya tsinke Yusuf d’in ya qara kira a hankali ya daure ya d’aga

Kana ina ne..?

Yasir yayi ajiyar zuciya yace ina hanya.. Yusuf yace OK za muyi jogging ne inason da na tsaya aski.. Yasir yace no yau ba najin jikina why not mu had’u kawai after magrib b4 mu wuce aikin dare..? Yusuf yace OK latter to su kayi sallama shi Yusuf yana mamakin yanayin da yaji Yasir d’in kamar an masa rasuwa shi kuma Yasir yana cike da tausayin Yusuf yana ayyana gaskiya mata basuda amana..

Sai wajajen Asar hayfa ta tashi bacci ammah tace tayi sallah Suwaiba ta kaita taga likita asan mai yake damunta tace “toh” ba tare da ta zargi komai ba..

Bayan tayi sallah aka kawo mata shinkafa da stew da vegetables shima ta kasa ci don haka ta jefa hijabi suka fito ita da suwaiba ko iyayenta bata leqa ba tukuna tunda ta iso ammah tace ana cike ta bari zuwa dare bayan mutane sun ragu sai taje..

Babban asibitin Cristal garden suka je Suwaiba ta bud’ewa hayfa fayel inda suka shiga ganin likita tashin farko ya gano tana d’auke da qaramin ciki saidai dole yace ayi test domin tabbatarwa

28mnts aka kawo result tana d’auke da cikin 3wks wanda canjin ruwan da weather tsakanin Nageria da Canada  da ta samu ne yasa cikin ya bayyana kansa

Hankalin hayfa rabuwa yayi biyu ga farin ciki ga fargaba na yadda zasu qare da Armando idan ya gano tanada ciki saidai hankalinta ya d’an kwanta da ta tuna ay saura qiris ta gama contract lokacin cikinta bai fito ba don haka bazata bari kowa ya sani ba sai in lokacin fitowarsa yayi..

A gefe wani irin farin-ciki taji naq yadda sai yanzu take jin ta mallaki Yusuf wannan cikin shine Soyyayar da suke wa juna suwaiba na magana da Dr yana rubuta mata drugs da hayfan ke buqata hayfa hannunta na mararta tana ayyana halin farin cikin da Yusuf zai kasance idan yasan da cikin nan saidai ba zata fad’a masa ba sai ta koma yadda zata tayita masa shagwab’a ta saki d’an murmushi

Suwaiba ce ta riqo hannunta tana d’agata suka bar office d’in..

A gida Suwaiba ta fad’awa Ammah labarin cikin hayfa wani irin farin ciki ne mara iyaka ya ziyarci ammah duk kuwa da halin da take ciki.

Suwaiba tuni taje ta sanar da iyayensu sunata murna da fatan Allah ya raba lafiya..

Itama hayfa sai wajajan 9:pm ta qarasa b’angaren iyayen ta fara gaishesu da yi musu ta’aziya inda Abba sosai shima yaji dad’in zuwan hayfan suka fito shi da ita suka zauna can wajen filawoyi yana tanbayarta komai lafiya tace lafiya ya bata labarin abinda ya faru zuwansa sokoto saidai yaci naji qanshin biyan buqata IA saka ran su kirani da labari mai dad’i

Itama tayi farin-ciki sun dad’e suna zaune maigadi yazo Koran hayfa wai anzo yi mata gaisuwa abba ya tanbayeshi waye..? Yace wai “Kamal”..

Shiru Abba yayi kafin yace kije amma kada ki sakar masa ko kad’an

“Toh” tace tana miqewa duk jikinta ma ya mata tsami..

Yana tsaye jikin motarsa bucatti tun kan ta qaraso imaninsa ya koma kanta yana jin kamar yaje ya d’auketa ya had’iyeta saidai yafi kowa sanin hayfa da girman kai don haka ya d’an kame shima gudun kada ta qasqantashi dayawa ganin itama yanzu mai
kud’ice tama fishi nesa ba  kusa ba..

Tsayuwa tayi d’an nesa da shi tayi shiru.  Ajiyar zuciya yayi ya d’an saki murmushi ya ce “barka da zuwa ranki ya dad’e”..

Ajiyar zuciya tayi kad’an itama tace barka, yace kin iso lafiya ya hanya ya aiki ya qarin haquri

D’an shiru tayi kafin ta ansa lafiya alhdl “Nagode”.. Tace bari na wuce Nagode

Yi yayi kamar zai riqota ya kame yasan halinta tun da can ma bata yadda da irin wannan sakarcin duk wayewarta wannan yana d’aya daga cikin dalilinsa na mutuwar sonta

Pls yace ki d’an tsaya.. Kallonsa tayi kad’an tace yau na iso and inada gajiya I need rest so nyt pls tnx ta juya.. Shiru yayi saidai bai damu yasan zai shawo kanta saida ma yaga shigarta gidan tukuna ya shiga motarsa ya tayar cike da shauqinta..

Tana komawa ta qara shiga sun dad’e da y’an uwanta kafin ta wuce d’akinta saida ta gama rage kayan jikinta tayi shirin bacci ta kulle qofarta kafin ta fara nemansa..

Kasancewar safiya ne a Canada yanzu ya dawo masallaci yana had’a musu brk shi da Yasir kiran ya shigo ya d’aga

Shiru tayi.. Shima haka kusan 5mnts kafin yayi ajiyar zuciya yace “kin isa lafiya”.?

Shanye muryarta ta qara yi kafin tace”shine kaqi kirana kai bayan kasan kasani ciwo kuma ban warke ba  hat yanzu”.! Tayi maganar kamar za tayi kuka.. Ajiyar zuciya yayi yace baby kinsan banada no kuma inata kiran na Mommy off .. Shiru tayi still cikin sigar lallashi yace inanan ciwon rashinki ya kamani jiya inata yiwa mutane shirme a gurin aiki amma kuma dukda da haka yanzu ana d’oramin laifi.. Shiru tayi still

Lura yayi shagwab’a take ji don haka ya fara ” am so so sorry babyna zuciyata pls 4give me” ajiyar zuciya tayi tace “me kake yi”..? Yace ina had’a brkfst ne

Dariya tayi kad’an kafin suka ci gaba fa hirarsu sam basu gajiya da junansu kusan 29mnts suna fira domin hayfa katin 50k ta saka a wayarta da k’yar ya furta “baby bari na barki kikwanta love u”.

Ajiyar zuciya tayi ta furta ” love you more mine” d’an shiru su kayi suna jin kewar juna kamar sun shekara basu tare kafin daga bisani ya qara furta “miss u much baby” lumshe idanu tayi tace me too a dole suka yi sallama kowa da tunaninsa..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *