KASHE FITILA CHAPTER 1 BY BATUUL MAMMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Hankalin malamin Civic Education da kusan duka daliban yana kan monita wadda aka sanya rarraba takardun test da akayi satin da ya wuce. Wannan ya bawa ‘yan mata biyu cikin daliban da suke zaune a layin farko daga tsakiya damar karasa shirin abin da suke kullawa tun safe.
Daya daga cikinsu ce ta rike ciki tare da kwalla kara iya karfinta sannan ta sulale a kasa ta kwanta. Kafin malamin da sauran su ankara dayar ta durkusa a gabanta tana jijjigata a hankali da muryar kuka take cewa “Rumana me ya sameki, tashi don Allah, wayyo….”
Murmushi ne yaso kwacewa Rumana ai kuwa taji kyakkyawan mintsini daga wurin Yusra kawarta “don ubanki idan kika tona mana asiri wallahi cewa zanyi ba dani akayi ba”
Tsabar tsoro ne yasa Yusra yin zagin. A lokacin malamin har ya iso, sauran ‘yan aji duk an zagaye su ana tambayar me ya faru. Yusra harda kukanta tace haka kawai ta ga Rumanan ta fadi.
Health prefect aka kirawo daga ajinsu tare da taimakon Yusra da wata malama suka kai Rumana karamin asibitin cikin makarantar. Sannan aka nemi numbar makusancinta wanda ya kasance kawunta aka kira shi.
Bayan an saka mata allura ana yi mata karin ruwa ne kowa ya fita sai likita da Yusra. Suna jin shiru Rumana ta bude idanu tare da saukowa daga kan gadon ta durkusa a gaban likitan “doctor ka taimakeni idan Uncle dina yazo ka fada masa ulcer ta kusa cinye hanjina”
Duk da ya dauki maganar rainin wayo amma bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Sai kuma yayi saurin daure fuska. “Nayi miki kama da abokin wasanki ne ko me?”
Yusra ma durkusawar tayi “idan baka taimaketa ba wallahi yunwa zata kasheta a gidansu. Ulcer din gaske ce zata kamata”
Juyawa yayi zai fita Rumana wadda ta tabbatar idan hakkansu bai cimma ruwa ba yau kila banda yunwa jikinta sai ya gayamata a gida bata san lokacin da ta fizge hannu daga jikin allurar ta ruga ta tare kofar ba “idan baka taimaka min ba wallahi zanyi muku hauka a asibitin nan. Ka fada masa mugun ciwo ya kamani a kaini gidanmu kada na mutu a nan”
Saroro yayi yana kallonta. Bai ankara ba ya ga ta nufi gadon dakin ta daga shi da yake ba wani nauyi ne dashi ba ta kifar. Dan tebur din kusa da gadon ma hantsila shi tayi tana ihu da kuka. Yusra wadda tare sukayi shirin ciwon karyar ma sai da ta tsorata ganin da gaske Rumana tana neman yin hauka.
Suna haka likitan yana kokarin riketa taji muryar kawunta daga dan karamin reception din yana tambayar inda take. Idanunta cike da hawaye ta sake kallon likitan alamun roko da neman agaji.
Tausayi ta bashi, ita kuwa Yusra kuka take yi.
Awaisu yana shigowa dakin ya ganta biji-biji kamar anyi wasan kura da ita. Ga hawaye ya wanke mata fuska. Da saurinsa ya karasa inda take ya rikota “Rumana me ya same ki? dena kukan ki fada min abin da kike so”
Kasa magana tayi sai kukan da ta cigaba da yi. Ba a son ranta tayi wannan abin ba amma idan ba gaban iyayenta ta koma ba bata jin zata iya cigaba da hakurin zaman gidansa.
Hankali a tashe ya dubi likitan “me ya sameta?”
Hadiyar yawu yayi yana kallon yadda ‘yan matan suka tsare shi da idanu “uhmm a binciken da nayi yarinyar nan tana fama da ulcer sosai har tana neman lahanta mata hanji” mamakin kansa yayi da biye musu harda aron kalamansu.
Girgiza kai yake yi alamun rashin yarda “Ulcer, ulcer ciwon yunwa? Mtsew, ba dai a gidana ba wallahi.”
“Abin da bincike ya nuna kenan ranka ya dade” Tuni likita ya fara tsorata kada a daga maganar gaba.
Harzuka yayi “kasan ko ni waye zaka kira min ciwon yunwa? To ko maigadin gidana bazai kira yunwa ba balle ‘yata”
Gaban likita ya fadi a zuciyarsa yace ‘yarsa kuma, wace ‘ya ce zata yiwa iyayenta sharri irin wannan. Harara ya jefa musu duk da ba kallonsa suke yi ba.
Awaisu ya katse masa tunani ” kaga ka sallameta zan kaita babban asibiti.”
Bai jira amsarsa ba ya ya durkusa ya dauko takalmanta ya saka mata sannan ya kamata suka fita. Wani irin tausayinsa ya kamata. Sai dai ko ana muzuru ana shaho da yardar Allah sai ta koma garinsu.
Suna shiga mota taji ya umarci dreba da ya kaisu asibitin kudi da iyalan gidansa suke zuwa. To kada karyarta ta kare kawai sai ta sandare masa tana mimmikewa. Hankalinsa ya kara tashi. “Uncle babu inda zani, ka mayar dani gida na mutu gaban Mama. Kada na mutu ban sake ganinsu ba”
A take ta karyar masa da zuciya. Asibitin dai yasa suka karasa sai dai a binciken gaskiya an tabbatar masa da gaske bata da kuzari. Tana bukatar hutu da abinci mai gina jiki.
Wannan jawabi ya sanya shi cikin rudani. Duk yadda yaso su kwantar da ita fafur taki yarda ita Mama kawai take son gani.
Gida suka koma yayi ta fadan yaya akayi bata cin abinci ba’a sanar dashi ba. Maamu mahaifiyarsa ita tayi jinyar Rumana a ranar. Da gaske ta rinka sambatu tana kiran babarta ko runtsawa basuyi ba. Dole washegari yayi shiri shi da dreba zai mayar da Rumana gida. Sai dai yana tunanin me zai fadawa dan uwansa a matsayin dalilin da yasa ya dawo da ita.
Suna fita Maamu ta leko ta tagar dakinta tana kallonsu. Hawaye taji ya taho mata mai zafi tana tunanin yadda karamar yarinya ta samarwa kanta mafita. Ita kuma ta yaya zata ta bar gidan dan da ta haifa a cikinta?*Fika LG-Yobe State*
Yara ne suke ta tsalle-tsalle a tsakar gida saboda yau alhamis babu makarantar Islamiyya. Masu dan girman kuma musamman matan kowacce ta kama aikin gida tana yi.
Sallamar da suka ji ce tasa suka tashi babu babba babu yaro suka tafi tarbo mai yinta. Murnar ganin Kawunsu suke yi sai dai ganinsa rike da Rumana tana tangadin karya yasa suka yi cirko cirko. Sarkin surutun gidan ne ya ruga ciki yana sanarwa ga Rumana ta dawo.
Mahaifiyarta wadda ta kasance mata ta biyu cikin matan gidan bata san lokacin da ta janyo hijabi ta fito ba. Addu’a take yi Allah Yasa ba wani abin Rumanan tayi ba Kawunta ya kasa zama da ita.
Ko da ta fito sauran matan gidan wato uwargidan da amaryar duk sun fito suna musu maraba. Ganin yanayin Rumana yasa suka san babu lafiya. Maman Antu kamar yadda ake kiran uwargidan ita tayi saurin riko hannunta suka shiga babban dakin da yake mazaunin falo a gidan. Tuni Awaisu ya wadata musu shi da kayan kallo da kujeru masu kyau.
Bai bi bayansu ba ya wuce dakin Baaba Hure. A zaune ya sameta tana jiran shigowarsa tun bayan taji an ambaci sunansa da na Rumana. Sai da ya gaisheta cikin yarensu na Bolewan Fika sannan yayi mata bayanin dalilin zuwansu.
“Kuma ka tabbata ba aljanu bane da ita?”
“Ko daya Baaba, jiyan nan dai ta bani tsoro shiyasa nace bari na kawota ta huta kwana biyu. Makarantar tasu zanje sati mai zuwa duk da sun san bata da lafiya na sanar musu halin da ake ciki”
“To Allah Ya sauwake, ina ‘yar uwata? Kwana biyu ko a waya idan nace yayanka ya kira ba ma samunta”
Dan murmushi yayi “tana nan lafiya, kinsan sai ta ajiye wayar ta manta inda take ma. Yaya Harisu bai dawo bane?”
Kafin ta bashi amsa suka jiyo muryar Harisu yayansa. Dakin ya karaso suka gaisa inda ya sake labarta musu dalilin zuwansu. Wannan karon harda matan gidan da Rumana a wurin.
“Zancen banza” cewar Harisu “Shine zaka biye mata ka baro aikinka ku taho”
Rumana ta tsuke baki, fatanta kada Baba ya bata shirin da suka kwashe sati uku suna yi ita da Yusra yace ta koma wannan kurkukun. Ita yanzu ko sunan Abuja ma bata son sake ji.
Shi dai Awaisu lallabata yace ayi kuma a tambayeta dalilin kin cin abinci. Domin ko mutan gidan suna ganinta sunyi korafin ramarta. Yarinyar da ko da tana makarantar kwana kafin komawarta Abuja da kibarta. Ita ko ramar nan ta kewar gida bata yi.
*****
Washegari da sassafe Awaisu da drebansa suka kama hanya.
Sai da Rumana taji tashin motarsu tayi wata kyakkyawar ajiyar zuciya. Za taci karenta babu babbaka, ta mike kafa taji dadin rayuwarta. Abinci kuwa tun daren jiya take yi masa cin hauka.
Bayan kwana biyu da dawowarta suna daki ita da babbar yayarsu da tazo daga gidanta. Hira suke yi Rumana tana bata labarin horon da akeyi musu a gidan Kawun nasu. Karshe ma tashi tayi tana kwatanta irin abin da tayi a clinic din makaranta. Mahaifinsu ne yazo ya tsaya yana sauraren bayaninta batare da ta sani ba. Ita kuma Maryama yayarta da ta ganshi ta kasa cewa tayi shiru sai kai da ta sunkuyar. Tana cikin nuna mata sandarewar da tayi a mota ta kula da Baban. Nan jiki ya fara rawa, kanta yayi yana duka ko ta ina.
“Har kinyi wayon yiwa dan uwana sharri Rumana?”
Ihu take yi tana kuka “Wallahi Baba ba karya nake ba. Ba’a bamu abinci sosai a gidan. Daga ni har Maamu bama koshi”
“Rufe min baki sakarai mara godiyar Allah. Sharrin naki harda Maamu a ciki? To zan kira Awaisun da kaina muyi magana”
A fusace ya fita ya shige dakinsa. Ko zama baiyi ba aka sanar dashi Baaba tana kiransa. Ya tashi ya fita.
“Ina gidan nan kake hukunci irin haka ko? duk kiran da nayi maka kuma baisa ka dena ba”
“Kiyi hakuri Baaba wallahi banji ba”
Abubuwan da Rumana ta fada ya maimaita mata. Gyada kai ta rinka yi har ya gama.
“Babu abin da ya dace kayi da ta fadi maganar nan sai bincike ba duka ba.”
Cike da mamakin rashin gaskata zancenta yace “bincike kuma Baaba? Awaisu fa ake magana”
“Na sani, fada maka ne kawai banyi ba amma dan zaman da nayi kwanakin baya banji dadi ba. Kuma kasan Maamu da zurfin ciki”
Kallon mahaifiyarsa yayi yana mamakin maganganunta.
Fita yayi yasa aka kira masa Rumana. Ya tsareta da jan ido yace ta fada masa komai tsakani da Allah. Kamar an kunna rediyo haka ta rinka bashi labari kuwa. Tana yi tana kuka, shi kansa Harisu idanunsa kamar gauta don bakinciki da bacin rai. Sallamarta yayi da gargadin kada kowa yaji maganar nan sai ya gama bincike.
Wayar kaninsa ya kira suka gaisa tare da taba barkwanci sannan yace ya hada shi da Maamu. Anyi sa’a yana gida da kansa ya kai mata wayar.
A zaune take sanyin AC yana neman illata ta amma ta kasa kashewa saboda karamin dansa Safwan ya kwashe batiran remote din ya saka a game dinsa. Da ya shiga hankalinsa bai kai kan rawar darin da takeyi ba balle ya taimaka mata. Wayar kawai ya mika mata.
Tana karawa taji muryar Harisu sai kwalla wadda tayi saurin mayarwa. Rabon da suyi magana wane wata biyu. Gaisheta yayi ta amsa muryarta tana rawa. Hakan da yaji kawai ya fahimci tana cikin matsala. Bai zurfafa tambayoyi ba yaje ya sanar da Baaba gobe zaije Abuja taho da Maamu.
Ganin ransa a bace sosai yasa ta dakatar dashi yana kokarin fita “kada ka manta Awaisu danta ne na cikinta, bata nemi taimako ba kada kayi shisshigi. Garin neman kyautata mata ka shiga hurumin da baza’ayi maraba da kai ba”
Cak ya tsaya yana auna maganar Baaba Hure.
“Yanzu sai kawai mu zuba ido idan har gaske ne tana cikin matsala a gidan?”
“Ba ido kawai zamu zuba ba kuma bazamu yi gaggawa ba. Komai na duniya a sannu ake binsa har a gano bakin zaren. Misali yanzu Rumana karya tayi mana, da wane ido zaka kalli kaninka ko Maamu idan suka ji?”Tuna baya*+
Da alamun gajiya ya shigo gidan yana daga kafa da kyar. Baaba ce ta fara ganinsa ta taso da sauri. “Yaya Awaisu an dace?”
Girgiza mata kai yayi a hankali zuciyarsa a cunkushe da bakinciki.
“To kada ka damu, rabon mutum komai nisan lokaci zai zo gareshi. Ka wuce dakina abincinka yana can”
Cikin sanyin jiki ya wuce ta bishi da kallo. Sai da ta ga fitowarsa da kwanon abincin ta mayar da hankalinta ga Maamu da take zaune tsakiyar matan Harisu guda biyu tana tayasu tsinkar zogale.
Dan daure fuska tayi cikin wasa tace “Kina kallon dana ya dawo ko sannu balle ki tambayeshi yadda akayi?”
Maamu murmushi tayi “tunda kina kusa meye nawa a ciki. Da dai bakya nan sai nayi muku kara”
Baaba ta hau mita ita Maamu bata kyauta mata ba. Matan Harisu suka sa dariyar rigimar surukansu.
Da suka gama Maamu ta tashi ta shige dakinta ta dan turo kofar. Hawaye ne ya taho mata ta sanya habar zaninta ta goge. Tun dawowar Awaisu tana ganin yanayinsa zuciyarta ta karye. Daurewa kawai ta rinka yi tana yaken dole. Shekara biyu kenan yana neman aiki har yanzu shiru. Ita kam Allah Ya sani ta kure matakin jin kunyar Baaba Hure da Harisu. Wanda ya kawota gidan ya jima da rasuwa gashi nauyinsu ya dawo wuyan dansa.
Lokacin da ta auri Mal Sa’adu Abali da danta na auren fari Awaisu tazo. Shekararsa biyu mahaifinsa ya rasu. Yana da shekara hudu ta hadu da Malam har sukayi aure. Taso mayar da shi wurin dangin mahaifinsa amma sam Malam yaki yarda yace bai ga amfanin auren mace kuma a kyamaci ‘ya’yanta na wani gida ba. Zaman lafiya suka yi sosai da Baaba Hure. Ita Baaba mutuniyar Katsina ce. Cirani ya kawo iyayenta garin shiyasa ta tashi da iya yarensu. Amma duk da haka tana Hausa da ‘yan uwanta. Malam da Maamu wadda ainihin sunanta Safara’u duk ‘yan Fika ne, yaren Bolanci sukeyi. Kuma haka duka gidan har yara da shi suke tashi sai dai suna Hausa kadan kadan saboda cudanya da Hausawan cikin gari.
Baaba Hure yaranta hudu. Baraka, Harisu, Ummukulsum da autarsu Zakiyya. Mace ce mai kyaun hali da sanin ya kamata. Sannan mai jajircewa wurin tarbiyar yara. Domin yaran sunfi tsoronta akan Maamu mai sanyi. Ita dai barta da yawan murmushi ko da ranta ya baci.
Haka suke zamansu gwanin sha’awa. Malam ya sanya Awaisu a makaranta Harisu ne yake rakashi domin autarsu ma ta girmi Awaisu da shekara shida.
Yana aji biyu a sakandire Malam Sa’adu ya rasu. Maamu ta shiga tashin hankali saboda bata haihu ba a gidan tana gudun su bukaci ta tashi bayan an raba gado. Sanin cewa yanzu gidansu ko ta koma babu inda zata zauna saboda yayyenta duk sunyi aure da matansu a cikin gidan iyayensu yasa Baaba Hure tace ta cigaba da zama dasu tamkar gidanta. Karatun Awaisu kuma ‘yar buga bugar da Harisu yake yi da nata jarin suka hada suna biya masa kudin makaranta.
A haka ya kammala ya fara shirin jami’a. Maamu ta sayar da gonarta ta biya masa kudin ya tafi Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) ta Bauchi inda ya karanci Banking and Finance. Lokacin nauyi ya fara yiwa Harisu yawa ya soma tara yara.
A haka dai da karume karume suka rinka tallafawa har ya gama da sakamako mai kyau. Ga shakuwa tsakanin ‘ya’yan gidan wanda bai sani ba bazai taba gane cewa Awaisu ba dan Malam bane.
A halin yanzu aiki yake nema ruwa a jallo abu ya gagara. Maamu kullum burinta ya sami abinda suma zasu gwadawa Baaba Hure da zuri’arta karamci ba don su biyasu ba. Sai don kawai ta nuna musu cewa bata taba manta alkhairinsu ba gareta.
Harisu ya kara aure iyali suna ta karuwa. Ya ciyar da dolensa ya ciyar da ita da danta. Wannan yasa take jin babu dadi.
***** Bayan kwana biyu Harisu yaje Kano saro kaya a Kantin kwari kamar yadda ya saba duk karshen wata. Sunansa yaji an ambata ya juya yana neman mai kiran.
Murmushi ya saki tare da sassarfa wurin karasawa wurin wani mai shago suna dariya tare da rungume juna
“Harisu Abali”
“Saminun Kano”
Sake rungume juna sukayi sannan Saminu ya ja hannunsa suka shiga cikin shagon atamfofi. Lemo mai sanyi yasa aka kawo masa sannan ya bayar da kudi a siyo musu abinci.
“Ikon Allah, ashe rai kan ga rai” cewar Saminu yana kara kallon abokinsa.
“Ga zahiri dai, sama da shekara biyar sai yau Allah Yayi ikonsa”
Hira sukayi sosai ta yaushe gamo. Saminu yayi zaman Fika inda suka saba sosai da Harisu. Daga baya ya dawo garinsu Kano ya cigaba da kasuwancinsa. A hirar yake tambayarsa kaninsa ya fada masa ai har ya gama jami’a.
“Aiki fa?”
“Nan fa daya, yanzu ma tare muka zo zai fara tayani kasuwanci kawai kafin aikin ya samu. Yanzu ma yana Wambai wurin masu robobi”
Harisu da Saminu sun sha hira sannan suka yi sallama da alkawarin haduwa washegari kafin su koma Fika.
****
Washegari kafin azahar sun isa shagon Saminu yi masa sallama. Yana ta tsokanar Awaisu an girma an dena kiran Yaya da an taba shi. Ya hada musu ‘yar tsaraba daidai misali sannan ya ja Harisu gefe.
“Mutumina nayi maka karambani fa, jiya bayan rabuwarmu naje gidan wani tsohon dan kwangila da nake sayar wa shadda”
“Kana nan da shige shigen ka mutumina” Harisu ya fada yana murmushi.
“Me za’a fasa..yanzu dai mu bar wannan zance. Cikin hira nayi masa bayanin ina da kani da ya gama karatu yana neman aiki. Sai dai anyi rashin sa’a bansan me ya karanta ba. Shiyasa bayanin nawa bai cika ba”
Farinciki sosai ya bayyana a fuskar Harisu ” da gaske kake?”
Murmushi yayi ganin abokin nasa yaji dadi “yanzu dai yace sati mai zuwa zashi Abuja wurin wani kusar gwamnati. Shine yace idan zai yiwu Awaisu ya same shi a can ranar alhamis”
Kati ya dauko mai dauke da sunan mutumin da nambar wayarsa ya mika masa.
“Gashi Allah Yasa a dace. Idan yaje sai ya fada masa cewa shine kanin Saminu Zawachiki”
Harisu ya rike hannuwansa ya ma rasa kalmar godiya “idan munje zaka ce. Ai dole na rakashi. Allah Ya baka ladan zumunci.”
Yafito Awaisu yayi da hannu ya matso kusa dasu ya fada masa halaccin da Saminu yayi musu. Shima godiyar yake yi kamar zasu ari baki su biyun.Ranar laraba da yamma Harisu da kaninsa suka isa Abuja. Da tambaya suka karasa gidan Alh Mudi Maibuta, dan kwangilan da Saminu ya nemi taimakonsa akan neman aikin Awaisu.
Gida ne babba irin na mutanen da naira ta zauna musu. Daga bakin gate din maigadi ya tambayi sunansu da abin da ya kawosu. Suna fada ya saki fuska tare da sanar dasu Alhaji ya bayar da umarnin yi musu iso da zarar sun karaso.
Wurin wata katuwar bishiya ya rakasu inda Alhajin yake zaune yana shan iska. Gefensa ‘yan mata ne guda biyu sanye da kaya iri daya.
Tun tahowarsu Awaisu wurin babbar ciki ta kafe shi da ido tana murmushi. Shi kuwa hankalinsa bai ma kai gareta ba. Cike da girmamawa suka gaishe da Alh Mudi. Shima fuska a sake ya amsa musu sannan yace su shiga wani daki kusa da na maigadinsa.
Abinci yasa aka kawo musu aka yi musu tarba a mutumce. Sai da suka ci suka koshi sannan ya dawo ya karbi takardun Awaisu. Murmushin fuskarsa ya fadada “Ikon Allah ashe kaima Bauchi kayi karatu. Kila ma ka taba haduwa da Gimbi.”
A ladabce Awaisu yace “Wane ne hakan?”
Alh Mudi ya hau dariya “Yarinyar wajena ce, sune a zaune ita da kanwarta shigowarku dazu. Da yake sunan mahaifiyata gareta shine nake kiranta Gimbiya. To kuma kasan mutane, a hankali sunan ya koma Gimbi.”
Harisu da Awaisu suka gyada kai suna Allah Sarki.
Alh Mudi ya cigaba da bayaninsa “Shekararnan ta gama ATBU din amma Business admin ta karanta. Nayi magana da wani sun karbeta a banki zatayi bautar kasa. Shine kaga ina dariya da na ga kaima bangarenka kenan, to zan tura masa takardunka gobe. Kaga abin ma duk zaizo da sauki”
Godiya da addu’a suka rinka yi masa. Murmushi kawai yayi “Saminu akwai kirki. Kaya kawai nake saya a wurinsa amma ina jinsa kamar dan uwa saboda iya mu’amalarsa da mutane”
Harisu yace hakane domin shima shaida ne.
Daga nan Alh Mudi ya yace lallai sai Awaisu ya zauna a Abujan domin idan ya bayar da takardun washegari mai yiwuwa zuwa litinin a bukaci ganinsa a bankin. Sannan yayi alqawarin bashi makwanci har zuwa lokacin. Harisu ya rasa bakin godiya. Mutanen kirki basa karewa a duniya. Sai dai haduwa dasu dace ne. Duk kudin Alh Mudi Maibuta bashi da dagawa da girman kai.
Da safe Harisu ya koma Fika bayan yaja kunnen dan uwansa akan ya kula da kansa kuma ya kame mutumcinsa. *****
Tun tafiyar yayansa baya fita ko’ina. Kullum yana daki sai sallah da take fitar dashi wadda Alhajin ko wani saurayi da Awaisu bai tantance matsayinsa a gidan ba suke jagoranta. Safe, rana da dare maigadi zai miko masa abinci ya karba da godiya.
Yau lahadi sun idar da sallar magariba Alh Mudi yace ya shigo falonsa su gaisa da iyalin gidan. Domin idan har ya sami aiki an barshi a nan Abujan to dole kafin ya sami wurin zama nan zai cigaba da zama tare dasu.
“Ni kuma ba mazauni bane, shiyasa na ga ya kamata kasan mutanen gidan suma su san ka”
A baya ya bishi suka shiga wani falo wanda aka kawata da duk wani abu na jindadi. Kafin su zauna wata mace ta shigo sanye da hijabi da alamun sallah ta idar. Sai ‘yan matan ranar da suka zo biyu da wani yaro da suke sallah tare wanda bai wuce shekara goma ba.
Awaisu ya gaisheta ta amsa da fara’arta ta tambayi sunansa.
Kafin ya amsa babbar wadda yake tsammanin ita Alh Mudi ya kira da Gimbi tace “A.S Abali, Mama shine yayi vice president na S.U.G a makarantarmu”
Da mamaki ya dago yana kallonta. Shi dai bazai iya tuna fuskarta ba amma dai abin da ta fada gaskiya ne. Kyaunta kuwa tuni yayi tasiri a zuciyarsa.
Maman tace “Gimbi rawar kai, ai ba ke na tambaya ba. Naga yayi shiru ne shine nake son jan shi da hira ya sake damu.”
Ta koma tana kallonsa “Alhaji yayi min bayanin komai game da kai. Allah Ya bamu ikon zaman gaskiya da amana”
“Amin Hajiya nagode. Allah Ya kara girma”
“Amin, sai dai Mama ake kirana ba Hajiya ba”
Daga nan sun dan taba hira wadda hankalinsa gabadaya yana kan Gimbi. Tunda ta fadi sunansa dazu zuciyarsa take kawo masa sabon tunani game da ita. Sai dai a wurin ya yakice shi. Ai ido ba mudu ba amma yasan kima. Ina shi ina ‘yar babban gida irin wannan. *****
Washegari da sassafe ya tashi ya shirya kamar yadda Alh Mudi ya umarce shi. Yana wurin maigadi suka fito tare da Gimbi. Taci kwalliya tayi kyau sosai.
A bayan mota ta zauna kusa da babanta shi kuma Awaisu yana gefen dreba. Babu inda ya gane a wurin da suke tafiya sai dai kawai yaga an rubuta Zenith Bank. A reception Alh Mudi ya barsu shi da Gimbi ya wuce wurin manaja.
Hira suke tabawa jefi jefi saboda shi dai ya kasa sakewa da ita duk kuwa da cewar ya fahimci sakon da yake boyewa a zuciyarsa itama shine a cikin ta ta zuciyar.
Ba jimawa Alh Mudi ya fito ya bukaci Awaisu ya shiga wurin Manaja. Shi kuma suka shiga wani dakin daban da Gimbi. A nan ne aka yi mata bayanin aikin da zata rinka yi.
Shi kuma Awaisu takardu ne aka bashi yayi ta cike cike. Bayan ya gama aka sanar dashi zai dawo washegari interview sannan yaje Lagos sati na sama training na wata daya daga nan ya jira posting.+
Abu kamar wasa sai gashi komai ya kankama dangane da samun aikinsa. Awaisu ya koma Fika sanar da mutan gidan halin da ake ciki da tafiyar da zaiyi Lagos.
Kafin ranar tafiyar Maamu ta tura shi wurin yayanta ya karbo rago biyu cikin tumakin da ake yi mata kiwo ya sayar. Da kudin wanda ko sisi bata cire a ciki ba tace yayi kudin mota da guzuri.
Kamar kullum kyakkyawar addua yayi mata tare da godiya. “Ba godiya zakayi min ba. So nake idan kaje ka dage yayi abinda ya kaika. Lokaci yayi da ya kamata ace kana da iyali kaima sannan ka fara ragewa dan uwanka nauyi. Ga zuri’a Allah Ya bashi sosai. Kaga yanzu cikin yaran sai ka rinka biyawa wasu kudin makaranta idan ka fara daukan albashi”
“Maamu kenan, Allah Ya bani iko. Nifa babban dana ma sunansa Haris. Tun yanzu ya kamata ki fara kirana Abu Harith irin na Larabawa”
Neman abin da zata buga masa tayi saboda rashin kunyar da yake yi a gabanta. Ba shiri ya tashi ya gudu.+
Bayan kwana biyu Harisu ya raka shi tasha ya wuce Lagos. Watansa daya wurin induction din sababbin ma’aikatan banki. Ana gamawa ya koma Abuja domin jiran posting. A wannan lokacin ne kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsa da Gimbi. Tun yana ja da baya har ya amince. Ji yake yafi kowa sa’a. Mace kamarta tana soyayya da talaka irinsa.
Da taimakon Alh Mudi ya samu aka barshi a Abuja maimakon Ilorin da aka tura shi da farko.
Ganin yana da kwanaki goma kafin lokacin fara aikin ya hada kayansa sai gida. Gimbi harda kuka da zai tafi saboda sonsa take da gaske. Alkawari yayi mata cewa bazai wuce sati ba zai dawo sannan suka rabu.
Yana isa gida yara suka fito ana ta murnar dawowarsa. Ya shiga ciki nan ma su Baaba sai murna aiki ya samu. Nan yake jin kwanaki hudu da suka wuce matar Harisu ta biyun ta haihu. Kai kace shi aka yiwa haihuwar ya fita neman dan uwanansa yana murna.
*****
Washegari suna zaune a bakin shagon Harisu suna hira Awaisu yace ya zabawa jaririya suna Ummu Ruman. Amma Rumana za’a kirata.
“Kai kuma a ina kaji wannan sunan” Harisu ya tambaya yana kallonsa.
“A littafin tarihi”
“Idan munje gida sai kayi mata huduba dashi” cewar Harisu
Duk da cewa ya riga yayi mata da suna Aisha amma baya son batawa kaninsa. Shima kuma Awaisun da yasan da hakan bazai taba kawo wani sunan ba.
Sai yamma suka koma gida. A bakin kofa ya tarar da dansa na biyu yana shirin fitowa.
“Sarkin yawo ina zaka da yamman nan”
“Baba kayi bako daga Kano. Shine aka ce na kirawo ka”
Harisu ya shiga ciki dakin Baaba inda suke yana tunanin waye yazo.
Abin mamaki Saminu ya gani tare da matarsa da yaransu biyar. Tsabar murna ya rungumeshi suna dariya.
“Bala dreban tifa ne ya fada min haihuwar nace to lokacin tada zumuncin mu fa yayi. Dole mu hada kan iyalinmu.”
“Sosai kuwa, sannu yaya hanya”
Matar Saminu mai suna Amina da yaransa duk suka gaishe da Harisu. Ana ta barkwancin yadda zasu rinka magana tunda Hausa a gidan bata zauna sosai ba. Baaba da Awaisu sune masu Hausar sosai. Awaisun shima ya shigo suka gaisa. Fita yayi sauran kudin hannunsa yasa ya siyo lemo, kaji da kwai ya bawa Maman Antu uwargidan Harisu domin karrama baki. Yaushe zai manta Saminu a rayuwarsa.
**** Kwanansu hudu a gidan duk an saba kamar sun dade tare. Yaranma kowa da abokin sa ban da babbar wadda ta girmi duka yaran gidan.
Ana gobe zasu tafi ne Harisu da Saminu sun zauna hira da daddare Harisu ya sako zancen da yake ta son yi.
“Mardiya shekararta nawa ne yanzu?”
“Ka ganta tayi tsayi ko? Shabakwai zatayi da azumi. Badi zata gama sakandire in sha Allah”
Harisu yayi murmushi “To Allah Yasa abin da zan zo dashi yayi maka. Nace mai zai hana mu hadata da Awaisu?”
Saminu ya kalle shi sosai “da gaske kake yi?”
“Indai ka amince. Wallahi Saminu ban taba ganin mutum irinka ba. Halayenka abin koyi ne ga wasu. Idan na bari damar nan ta wucemu ai na cuci zuri’ar Awaisu. Mai alkhairi irinka dole a kyautatawa ‘ya’yanka zato”
Saminu ya kama hannunsa kam “in dai haka ne na bawa Awaisu Mardiya halak malak inyi maka ta yara”
Dadi ya kama Harisu suna dariya “in sha Allah Awaisu bazai bamu kunya ba. Dama watan da ya wuce na gama biyan su Zakiyya kudin gidan Malam da ya fada rabonsu a gado. Gyara shi zanyi sosai kafin shekara mai zuwa shima Awaisun ya tara abin da ya tara sai su zauna a ciki. Ba munyi maganar a Abuja zaiyi aiki ba? To muna sa rai zai sami muhalli kwanan nan. Kaga sai su koma can ya sa ta cigaba da karatu ma”
Saminu farinciki ya cika zuciyarsa. Shi yana yiwa Harisu kallon mutumin kirki. Shima Harisun kallon da yake yi masa kenan.
Sun yanke shawarar sanar da Mardiya babbar ‘yar Saminu da Awaisu shawarar da suka yanke domin jin ta bakinsu da kuma basu hakkinsu don kada a zalinci kowa.
Awaisu wanda yake bayan kofa tun bayan yaji an ambaci sunansa ya fasa karasawa wurinsu. Ji yayi kamar an dora mada dutse a kansa. Shi kadai ya soma magana a hankali “yanzu wannan yarinyar da bata gama zama mace ba za’a bani? Wallahi da sake. Ko ban hadu da Gimbi ba babu inda zan kai wannan yarinyar”