KAWUNA CHAPTER 5

KAWUNA 






CHAPTER 5





Tun daga wannan ranar Abee bata sake sanƴa kakanta a cikin idanuwanta ba, kullum dai tana shiga tayi masa gyaran ɗaki, da haka da haka dai Alhaji ya soma fuskantar ma’aikaciyar dake gyara masa ɗaki. Duk ma’aikatan da suke aiki a part ɗin sa sosai suke yawan ɗaukar masa kuɗi, amma sabuwar ma’aikaciyar sa daidai da nairan sa biyar bai taɓa samunta da ɗaukar masa su ba, tun daga haka yasan cewa ansama canji sosai. Zaune yake shi da Hajia Nenne a dining area ɗin sa suna kalaci (break fast), jefi jefi suke ɗan taɓa hira can Alhaji ya nisa kafin ya ce ” Hajia wai ni kam in tambayeki mana? shin wai waye ke yimin aiki yanzun?”, Kallon sa Hajia tayi kafin ta ce ” wata sabuwar ƴar aiki ce Alhaji”.
Jinjina kansa yayi kafin ya ce ” Gaskiya tana da amana, ko naira ashirin yaushe rabon da a mun sata a cikin ɗakin nan”, murmushi Hajia tayi ta ce “kai haba?” Ya ce ” kai!, gaskiya ya zama dole in ga mai mun aikin nan ga shi naga canji sosai ana gyara mun ɗaki yan da ya kamata, komai ana a jiye min shi a in da zan gan shi ba tare da na sha wahalar naiman wani abu ba, gaskiya wannan karan kinyi sa’ar samun mai riƙon amana Hajiata”. Murmushi sosai Hajia Nenne tayi ganin Mijinta na yabon ta, sosai taji daɗin Abee yadda ta riƙe amana “gaskia ƴar hannun ce wannan yarinƴar za’a yi nisar tafiya da ita”, Hajia Nenne ta furta hakan a cikin zuciyarta lokaci guda kuma tana sakin ma kanta wani yalwataccen murmushi wanda tabarwa kanta sanin manufarsa. “Alright Alhaji zan aika kiran ta”, Alhaji bai sake cewa komai ba ya miƙe ya koma sitting room ya zauna a kan 3cta ya ɗauki jaridar daily trust wanda a kullum baya wuce sa ya soma karanta labaren da jaridar ke ƙunshe da shi a yau. Hajiya Nenne ta aika kiran Abeedah ta ce ta sameta a part ɗin Alhaji, sosai zuciyarta ke dukan uku uku ko dai wani abin a ka ce tayi?, a tsorace dai ta shigo part ɗin kanta a ƙasa ta ce ” Hajia gani, Alhaji barka da safiya” , ɗago da kansa Alhaji yayi don daga muryar yarinƴar ko ya ce daga yanayin maganarta mutum zai san ba bahaushiya ba ce ita, murmushi ɗauke a samar fuskarsa ya dube ta kafin ya ce “barkan ki dai, ya aiki kuma mainene sunanki?”, Mamakin tambayoyin sa a kanta ya haneta saurin amsa masa su, sai da Hajia ta ce “baki jin ana tambayarki ne?”, Da sauri ta ce “Sunana Abeedah”, jin jina kai yayi ya ce ” Abeedah ko ke wata yare ce?”, nan ma jim tayi tana mamakin wannan al’amarin to ko dai sun gano ta ne? Amma tayaya zasu gane?, bin cike Hajia tasa a ka yi mata a kanta ne ko kuma ganewa suka yi? Ai bata sanƴawa Hajia ido a komai nata ba ballantana ta ce tabi diddiginta, haɗiye miyau tayi kafin ta ce ” Ni igbo ne ranka shi daɗe” , jinjina kai yayi ya ce “mai yasa kike aiki toh? daga can garin ku zuwa nan ai akwai nisa”, dudum ƙirjin Abee ya riƙa bugawa saita kanta tayi sosai kafin ta tattaro dukkannin nutsuwarta ta ce ” Eh zuwa nayi aiki nan don na samu kuɗi naje na haɗa digree, ina da NCE” (tayi karya), nan ma jinjina kai yayi ya ce “Toh shikenan Allah taimaka, ga wannan”, Alhaji ya ciro naira dubu 30ya miƙawa Abee kallon Hajia Abee ta fara yi taga tana mata murmushi, don haka tasa hannu biyu ta amsa tana yi masa godia har ta fice daga cikin falon zuciyarta cike da fargabar abin da ya faru. 

Zaune take shiru a ɗakin su tunani ne birjik a cikin kwakwalwarta, ta kama wannan ta warware wancan ta rasa ta inda zata fara ma tunaninta, dogon lumfashi taja kafin a hankali ta soma yatsina fuskarta ba komai ya sanƴata hakan ba face tuno da ƙa’idar Hammad, ko wani dare haɗuwa a ke da masu aiki wa’inda suka dafa abincin (ba duka ƴan aikin ba), da ƴan gidan a ci abinci a guri ɗaya sa’anan in ana cin abinci ba’a magana har sai an kammala, ga shi a ƙa’idar sa dole ne abi balance diet breakfast haɗin balance diet a ke yi, na rana ma haka na dare kuwa shi ya fi ɓata mata rai don kuwa abincin dare ganƴayƴaki kawai a ke ci da fruits, sam ba’acin abinci mai nauyi da daddare. Shi yasa taga sauran masu aikin gidan suna rage abincin rana da zummar idan dare yayi  su ɗumama su ci abincin dare da shi, a cewar su waye zai iya cin ganƴe da fruit kawai  ya kwana da shi?, a cewar Hammad kuwa ba’a cin abinci mai nauyi idan za’a kwanta baccin dare, shi yasa cutattaki suka yiwa jama’a yawa domin kuwa ba kowani gidan malam bahaushe bane ke bin balance diet, duk abin da malam bahaushe ya samu saka wa cikinsa kawai yake ba tare da bin dokar abinci ba, kwatakwata mutanen mu basu da tsari. (Cewar Hammad) 

Story continues below


“Wai tunanin mai kike yi ne Abedah?”, Harirah wacce ke gefen Abeen zaune tun ɗazun ta wurgo mata tambayar. Murmushi Abee tayi ta ce “babu komai fa”, ba don Harirah ta yarda ba ta ce “Toh ka she mana wutan mu kwanta”, hakan ko Abee tayi, ta kashe wutar ɗakin taja bargonta tayi lulluɓi haɗida tofe jikinta da addu’a sa’annan bacci ɓarawo ya sace ta. 

Wa shegari, Abee bayan ta gama gyarawa Alhaji ɗakinsa ta dawo nata masaukin don ta gyara, kafin ta shiga taje tayi wanka, ƙarar telephone dake gefen side drawer ya katseta daga sharar da take yi, guntun tsaki taja kafin ta ɗaga wayar “Abeedah kije sa shen Asma’u tana son ganin ki wai”, a mamakin ce ta cire wayar a kunnenta tana mamakin kiran nata da Asma’u tayi, mai zata mata? Laifi tayi ne komai? Fuskarta ta ɗan leƙa cikin mirror don ganin ko da wani alamune da zai ayyana kamanninta da ƴan gidan? Ganin babu wani alamu ya saka ta jan dogon lumfashi sa’annan ta gyara mayafin kanta, tafito bakinta dauke da dukkanin addu’oin da suka zo mata. Da sallama ta shigo part ɗin Asma’u ta iske masu mata aiki ne kawai, tambayar su tayi inda zata iske Asma’un suka ce mata taje side ɗin Hammad tana can, gabanta ne taji ya faɗi da jin ambaton  sunan Hammad, a hankali kamar an cire mata lakka a jiki ta fita daga part ɗin Asma’u, jiki a sanƴaye ta shigo part ɗin Hammad wanda shine karon ta na farko shiga side ɗin sa, gani tayi ma karakaf ginin sashinan gidan, part ɗin Hammad yafi ko wani part tsaruwa, tana mamakin irin son da kakanta ke yiwa Hammad. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

A hankali ta ƙaraso cikin falon muryarta a sanƴaye ta musu sallama, bata jira sun amsa mata ba ta kutsa kanta cikin falon daddaɗan ƙamshin turare ya bigi saman hancinta, kallon falon ta shiga yi komai na cikin falon brown and silk brown ne, sosai falon ya mata kyau, sauke idanuwanta tayi a kan su, suna zaune a kujera ɗaya Asma’u zaune daf da Hammad tamkar zata shige cikin cikinsa, falon babu abin da yake fitarwa face ƙamshin turaren Asma’u da na Hammad sai ƙamshi falon ke fitarwa, Asma’u kuwa sai faman magana take wa Hammad ƙasaƙasa tana wani faman kashe ido da rangwaɗa tana zuba dariya. Abee kuwa taɓe baki tayi a ranta ta ce “chab wannan kuma wani kalar abu ne?” 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Ta wutsiyar idanu Asma’u ta kallo Abee, kafin ta taɓe baki ta ce “dama ɗakin Hammad zaki shiga ki gyara”, dum dum taji ƙirjinta na bugawa ita dai har ga Allah bata san dalilin da yasa in dai har a ka ambaci suna makamancin Hammad sai ta tsinci kanta da bugun ƙirji. Ɗago da kanta tayi ta kallo Hammad ɗin wanda zaka rantse kwata-kwata ma hankalinsa baya wajen su, faman danna wayarsa kawai yake yi. Asma’u ce ta kuma katsema ta tunaninta, inda take cewa”ki tabbata kin gyara da kyau, ga ɗakin can” , tayi wa Abee nuni da saman bene dake cikin falon, alamu na nuna cewa ɗakinsa a saman yake kenan, “ɗakin farko a saman can zaki gyara” Asma’u ta kuma ɗaura mata, gyaɗa kai kurum Abee tayi, ta kama kanta ta wuce tahau matakalen benen don sadata da ɗakinsa. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin, daddaɗan ƙamshin turaren wuta ya bugi saman hancinta lumshe idanuwanta tayi kafin ta saka kanta ta shiga ɗakin gaba ɗaya, “wow” Abee ta furta a ƙasan maƙoshinta, ta lura sosai Hammad namiji ne mai tsaftar tsiya ga shi da son ƙamshi tamkar mace. Kallon ɗakin kawai ta tsaya yi bakinta buɗe, komai dake a cikin ɗakin sosai ya burgeta musamman colour ɗin da a ka yi amfani wajen ƙawata ɗakin da shi, komai white and light green. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Shiru Abee tayi tana tunanin mainene abin da zata gyara a cikin ɗakin, don dai ita tsaf tsaf taga ko’ina kakkaɓe gadon kawai ta shiga yi sa’annan ta canxa ma gadon bedsheet da taga an ajiye shi gefe da alamu dai so a ke ta canza wa gadon bedsheet duk da babu abin da ya faru da wanda yake kai tsaf da shi. Bayan ta kammala gyara ko ina ta kunna soket ɗin burner na turaren wuta, ta kunna AC nan da nan ɗakin ya soma lulluɓewa da sihirtaccen ƙamshi mai sanƴaƴa zuciya. Dogon lumfashi taja kafin ta wuce toilet don gyarawa, nan ma< bayin bata wani ga abin gyara sosai ba wanke ko ina tayi tas da sabulai masu ƙamshi sa'anan ta kunna turaren wuta ta fito daga cikin bayin tana miƙa a hankali. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Bayan ta kammala komai, ta fito ta iske su dai still a falon Asma’u sai faman yiwa Hammad labari take kai kace Radio a ka kunna, tana yi tana dariya shi kuwa iya kacin sa ya murmusa mata kawai. wucewa kawai Abee tayi ba tare da ta musu sallama ba, bayan ta fita cikin falon ne ta jiyo muryarsa da zata iya rantsewa yau ne karon ta na farko da taji sa yana magana, don haka tayi saurin maido da dukkanin saurarenta daidai inda muryar tasa mai kama da an masa dole ta soma jin abin da yake tambayar Asma’u ” Ita kuma wannan wacece?”, Zaro idanu waje Abee tayi dama ya lura da zuwanta? Amsar da Asma’u ta ba shi ne ya sata katse tunaninta, ” Mamar Faɗime ce babu lafiya wacce ke gyara maka ɗakin ka, toh shine bayan ta tafi a ka kawo maka wannan, da zummar idan ta warke zata dawo, kasan kuma harda yana yin tsufa”, gyaɗa kai Hammad yayi kafin ya ce “eh waccen ɗin ta iya aiki kam, Allah ya bata lfy, ita ma wannan ɗin babu laifi kamar da akwai tsafta a tattare da ita.” Daga haka kuwa Abee bata sake jin maganarsa ba, sai hirar da Asma’un ke ci gaba da yi masa kawai take ji, don haka ta taɓe baki tayi tafiyar ta. A ranta kuwa tana ganin abin da Asma’u keyi ƙasƙantar da kai ne, taya kina mace kije ki tayiwa namiji hira shi kuwa yata banza dake? Yaƙi kulaki?. Tsaki taja tayi wucewarta ɓangaren su. 

Wa shegari…………. 


Wa shegari, Abeedah ta shirya bayan tayi wanka ta kama hanƴar ɗakin Alhaji don yanzun kam ta tabbata ya tafi office. Da sallama a bakinta ta ida sa shigowa cikin falon, dining area ta fara nufa ta gyara abin da ya kamata sa’annan ta haura zuwa ɗakin Alhajin, gyarawa ta shiga yi kafin daga bisani ta ankara da wasu takardu a kan bedside drawer nisawa tayi kafin ta shiga kimtsa su waje guda. Bayan ta kammala gyara ɗakin tsaf ta fito tana sauke lumfashi don gajiyar da tayi, side ɗin Hajia Nenne ta nufa da zummar kai mata mukullin sashen Alhaji, cikin nutsuwarta tayi sallama a babban falon Hajia Nenne, ganin ba’a amsa mata ba ya saka ta shiga don zuwa ɗayan falon. Da saurinta taja ta tsaya don jin irin maganganun dake fitowa a bakin Hajia Nenne da wata wacce ta tabbata Asma’u ce, tsoro da fargaba ya kama Abeedah laɓewa tayi sosai don jin abin da bayin Allan ke tattaunawa a kai da ya so firgita lissafin Abeedar. 

   ” Wallahi ni sai in saka a kashe shi”
Cikin zafin rai Asma’u ta dubi yayarta kafin ta ce 
” Haba Hajia, ya za’a yi ina son shi kice  a kashe shi? Son shi fa nake kuma na ce miki auren shi zanyi…..” 
“Toh tunda har bazai bi abin da muke so ba, idan bamu kora shi yayi wani gurin ba ai sai mu saka a yi yadda za’a yi da shi ya bar duniyar baki ɗaya, don kin fi kowa sani yanzu Hammad shi ya tare mana iska, ki zauna ki biye wa ruɗin so ya kaiki ya baro ki Ma’u.” Hajia Nenne ta ida maganar cikin ƙunar rai, lumfashi sosai Asma’u ta sauke don a zahirin gaskia mutuwar son Hammad take kuma ba zata taɓa barin Hajia ta cutar da Hammad ko ta halin ƙaƙani-ƙaƙa, kallon Hajia ta sake yi ganin sosai ran Hajian yayi mugun ɓaci ya saka ta ɗan sassauta muryarta kafin ta soma yi mata magana 
” Hajia kin ga wallahi ba sai kin saka an kashe miki Hammad ba, kawai mafita ɗaya shine kisan yadda zakiyi maganar aurena da Hammad ya taso cikin wannan shekarar, Alhaji baya ƙetare maganarki sam haka zalika Hammad bai ƙetare maganar Alhaji sam tunda yanzun babbar makamin na hannunki kawai ki tunkari Alhaji da batun son haɗani aure da Hammad, kin ga muddin na zama matar Hammad toh ko ya riga da ya shigo hannunmu sai yadda muka yi da shi kawai!”. 

Hararar sama da ƙasa Hajia Nenne tayiwa Asma’u kafin ta ce  ” yaro dai a kullum yaro ne, ke Ma’u har yanzun ina ganin baki san waye Hammad ba kin fi kowa sanin malamai, da bokaye sunfi a ƙirga sun kasa da Hammad bare Alhaji, shi mutum ne murɗadɗe babu mai gane gabansa da bayansa ina mai shawartarki karki kuskura ki bijiro da maganar aure tsakanin ki da Hammad if not am sorry to tell you kina ruwa saboda Hammad bazai taɓa aurenki a yanzun ba, ki ci gaba kawai da 
cusa masa son ki a cikin zuciyarsa watarana ke 
zakiyi murna da hakan kuma ki ci ribar jinkiri.” 

Asma’u ta ce “toh mainene mafita yanzun Hajia?”
“Mafita ɗayane shine kawai barin Hammad Duniya”. Shiru Asma’u tayi kafin ta shagwaɓe fuska kamar mai shirin kuka ta ce ” Hajia don Allah karki zama silar barin Hammad Duniya, Hajia ina sha a kan wannan kuɗaɗen ne da zasu shigo Company next week kike tsoron Hammad ya hana shigowar su ta bankin Company sai dai ta bankin sa? Toh mai zai hana wannan karan ma kawai ki saka Alhaji ya turasa wani ƙasar kamar yadda kika saba yi a kullum? Kin ga in a kai hakan babu yadda za’ayi wannan karon Hammad ya sama wa’innan daular dole wannan karan ma shi zai faɗi mu kuma mu ci nasara!” 
Shiru Hajia tayi tana girgiza ƙafa kafin ta ce “Hammad ya jima yana cin Albarkacin ki Ma’u in ba haka ba da tuni na shafe tahirinsa kamar yadda na share tahirin yarinƴar gidan mai kankat ma kenan”. Murmushi Asma’u tayi ganin Hajia ta fara saukowa daga turbar son ka she Hammad, nisawa Hajia tayi ta ce ” is okey zan yi yadda kika ce ɗin Are You happy?”. Murmushin farin ciki ne ya mamaye Asma’u da saurinta ta miƙe ta rungume yayarta ” Allah ya barmin Ke Nenne am, ina alfaharin ka san cewata ƴar uwarki thanks you”. Murmushi Kawai Nenne tayi sa’annan ta miƙe ta bar falon. 

Story continues below


Da sauri Abeedah tabar ƙofar falon tayi maza ta fita ma gaba ɗaya a sashen Hajiar, zuciyarta na dukan tara tara sam bata ma ganin abin da ke gabanta burinta kawai ta isa ɗakinta, ba tare da ta lura ba taji ta buge da abu ɗagowa tayi don ganin abin da ta buge da shi ganin sa tsaye ƙeƙam yana ƙare mata kallo ya saka gabanta tsananta faɗuwa da kyar ta iya haɗiye yawu kafin ta soma haɗa kalmomin da zata iya kare kanta a gabansa, cikin gurɓata ciyar hausarta ta ce ” don Allah kayi haƙuri wlh ban san na shigo gaban ka ba” ta ida maganar cikin rawar murya bai ce da ita uffan ba illa kallon yadda bakinta ke motsi da yadda take hausarta a gurɓace, ganin takai aya ya girgiza kai ba tare da ya ce da ita ƙala ba yabi ta gefenta yayi wucewarsa, ya barta anan tsaye tana mamakin hali irin na Hammad, juyowa tayi don ganin inda ya nufa kafin ta girgiza kanta ta juya da sauri tayi tafiyarta. 

Shiru Abee tayi ta kasa taɓuka komai, burinta kawai shine tasan shirin Hajia Nenne mai take shirin yi? Wani kuɗi ne suke magana a kai? Hammad mai ya tsare musu? Shima Hammad ɗin cutan Alhaji yake yi ne ko ba cutarsa yake ba?
” Hajia don Allah karki zama silar barin Hammad Duniya, Hajia ina sha a kan wannan kuɗaɗen ne da zasu shigo Company next week kike tsoron Hammad ya hana shigowar su ta bankin Company sai dai ta bankin sa? Toh mai zai hana wannan karan ma kawai ki saka Alhaji ya turasa wani ƙasar kamar yadda kika saba yi a kullum? Kin ga in a kai hakan babu yadda za’ayi wannan karon ma Hammad ya sama wa’innan daular, dole  wannan karan ma shi zai faɗi mu kuma mu ci nasara!”. Maganar Asma’u na ɗazun yayi ruri a cikin kwakwalwar Abee, tagumin data yi ta sauke haɗida sauke lumfashi sosai kanta ya ƙulle “Mai Asma’u ke nufi kenan? Hammad ma cutar kakana yake? Kenan dukkan su Hajia da Hammad sun san abin da suke ƙullawa? Ko kuma kowa bai san abin da ɗaya keyi ba? Mai sa Hammad keson dukiyar Alhaji su riƙa shiga cikin asusun bankinsa alhalin kamata yayi a ce cikin asusun kakana komai zai riƙa shiga? Hammad! Hammad? Anya kuwa da gaske Hammad ɗin nan yaron ɗan uwan Alhaji ne? Toh waye wannan Hammad ɗin? ga shi sak kamanninsa da mahaifiyata ya gama ɓaci tabbas Hammad  Baffana ne(Kawu) amma ya zama dole yanzun in miƙe tsayin daka in soma aikin abin da ya kawo ni cikin gidan nan dole na san abin yi, don rayuwar Hammad Yana cikin hatsari tabbas in ya ci gaba da yiwa Hajia Nenne kutse cikin lamuranta dole ta saka a kauda shi a duniya, wajibi ne na farga nasan ta inda zan ɓullowa wannan al’amarin Hajia Nenne ba kullum a ke kwana kan gado ba! Ki jira ranar wa’adin ki Abeedah na ankare dake kuma zan zamo silar taɓarɓarewar ki.” Abee ta ida maganarta cikin furzar da huci tana tunanin ta inda zata fara ɓullo wa al’amarin, ganin ba ta da mafita a yanzun ya saka ta ɗau wayarta ta kira Mancy suka sha labari kafin daga bisani su kayi wa juna sallama.

Da sallama a saman bakinsa ya idasa shigowa cikin falon Alhaji, murmushi ɗauke a samar fuskar Alhaji yake amsa sallamar ɗa mafi soyuwa a cikin zuciyarsa sosai Alhaji ke ƙaunar Hammad saboda yaro ne shi mara son fitina da yawan surutu bai shiga hurumin da ba nasa ba, haka zalika yaro ne mai riƙe gaskia da amana. 

” Daddy, barka da hutawa”
Hammad ya katse wa Daddy ɗan gajeran tunanin da ya faɗa, faɗaɗa murmushinsa Alhaji yayi ya ce ” lale be ɓingel am ( barka da zuwa ɗana)”. Murmushi mai fidda asalin kyawunsa Hammad yayi kafin ya ce ” Yauwa Daddy lale amin (Yauwa Daddy barkan mu dai), zama Hammad yayi kusa da Alhaji kafin Alhaji ya ce ” ya aiki yau ka leƙa Company kuwa?” Gyaɗa kai yayi kafin cikin yaren Fulatanci ya ce ” Eh Daddy ban jima da dawowa ba ma, komai dai yana nan yadda yake Daddy,” , murmushin yaƙe Alhaji yayi kafin ya ce ” ina mamaki kwarai da gaske na salwantar makuɗan kuɗaɗe a dukkanin Companies ɗina, a saran dauloli muke babu kama hannun yaro, wlh na rasa mai ke kawo wannan al’amarin, amma Allah ya kawo mafita kawai”  sauke lumfashi Hammad yayi kafin ya ce ” Ameen Daddy” daga haka ya kame bakinsa yayi shiru, Alhaji ne ganin shirun yayi yawa ya saka shi nisawa ya ce ” tafiya zuwa Italy ya kama ka Moallahidi (wanda Allah keso, haka Daddy ke kiran Hammad), kaje ka shirya zuwa jibi jirginku zai ɗaga akwai kayayyakin da dole sai in kana wajen za mu iya samunsu,  tafiyan wata ɗaya ne kawai”. Shiru Hammad yayi yana sauraran Alhajin har yakai aya kafin ya murmusa kawai ba don ya so ba ya ce ” Allah ya kaimu Daddy” “Ameen Ameen” daga haka Hammad ya miƙe ya bar sashen Alhaji ya koma part ɗin sa ranshi a matuƙar jagule, sosai wannan tafiyar bai son ta amma gudun kar Alhaji yayi wani zargin daban ya saka shi amincewa da tafiyar,  wannan tafiyar har tsawon wata ɗaya sosai zai kawo masa cikas a cikin lamarinsa bai da niyyar sake tafiya kowani ƙasa har sai ya cimma burinsa amma da dukkanin alamu ALHAJI na son dagule komai da ya gama shiryawa, lumshe idanuwansa yayi dalilin tuno da maƙudan ƙuɗadɗen da zasu shigo cikin Company nan da next week ya sani In har wa’innan kuɗaɗen basu shigo cikin bankinsa ba toh shine silar taɓarɓarewar komai da komai anƴa bazai fasa zuwan nan ba kuwa? Ya tura wani kawai a madadinsa kuma ya hana Alhaji sanin cewa bai je Italy ɗin ba?. Ganin bai da mafita ya saka shi jan guntun tsaki kawai kafin ya janƴo system ɗin sa ya soma danne-danne a kai.

Story continues below


” Ku kira urgent meeting ganinan zuwa Company ɗin yanzun nan, karku bare komai ya fita a hannunmu. wallahi In ba haka ba dukkanin ku zaku biya da rayukanku”. Hajia Nenne ta ida maganarta haɗida ka she wayar tana huci, Faruk da Asma’u dake gefenta suka zuba mata ido tana ta huci da kai kawo, ” kai Faruk shirya maza maza ka kaini WASACO yanzun nan, iskancin banza iskancin hofi Hammad kayi kaɗan ka ce zaka iya wasa da ƙwaƙwalwata, kai ƙaramin ƙwaro ne duka duka yaushe ka girma? A gabana ka girma baici a ce kayi tunanin fin malamin da ya koyama faɗa basirar iya dagaa ba!” Ta ida maganar cikin ɓacin rai, Asma’u ta miƙe ta iso gabanta haɗida jan hannuwanta kafin ta zaunar da ita kan kujera ta ibo ruwa a glass cup ta miƙa mata, Hajia na huci ta amsa kofin ruwan ta kafe bakinta a saman kofin ta shanƴe ruwan tsaf a lokaci guda kuwa tana sauke lumfashi. Kallonta Asma’u tayi ta ce ” wai Hajia mai Hammad Ke shirya wa ne?” Cikin huci da ɓacin rai Hajia ta shiga yin magana ” iskancin banza, yana can yana fafatukar hana billion 80 shigowa Company so yake muyi a sara kawai, amma kam ba’a banza ɗan iskan yaron nan ya karanci kimiyya da fasaha ba (computer science) Yana so yayi amfani da dukkanin basirar fasahar karatunsa wajen dagule komai, Faruk ka miƙe kazo mun tafi ko yaa?” Da sauri Faruk ya miƙe Hajia ma tabi bayansa suka bar Asma’u kawai zaune tana saƙa da warwara. Jin motsin buɗe ƙofa ya saka ta saurin barin wajen a sukwane tana fidda huci, bayan sashen Hajia ta wuce tana jera a jiyan zuciya a jere kafin ta dafe goshinta tana tunanin abin yi ” dole in bi Hajia don ganin abin da ke faruwa amma mai Yakamata nayi?” Shiru Abee tayi tana tunanin abin da ya kamata tayi saurin barin wajen tayi da hanzarinta ta koma sashen su ta ci sa’a kuwa ta iske Fadime zaune a ɗakin tana cin abinci. ” Yauwa Faɗime don Allah In kina da niƙaf ki aramin”. Kallonta Fadime tayi kafin ta ce “ke kuwa mai zaki yi da niƙaf?” Murmushi Abee tayi kafin ta ce ” Hajia ta aikeni kasuwa toh ban son fita haka yau ana rana” gyaɗa kai Fadime tayi sa’annan ta miƙe taje wajen kayanta ta cirowa Abee nikaf ɗin ta miƙa mata Abee tayi mata godia ta fice  daga part ɗin su. Bayan gida ta koma inda babu wanda ya cika zuwa wajen, tsayawa tayi cak tana tunanin anƴa abin da take shirin yi bazai tona asirin ta ba? ba tada zaɓin da ya wuce tayi hakan kawai don haka zuciyarta ya riƙa ƙarfafa mata gwiwa, buɗe bakin fanfo tayi kafin ta saka fuskarta ruwan fanfon ya shiga zuba a  saman fuskarta hannunta ta saka ta shiga goge tabon dake fuskar nata sosai ta shiga wanke fuskarta tabon fuskarta kuwa na bin ruwa sai da ta tabbata fuskar tayi ƙal babu wani alamun tabon zane a kai sa’anan ta rufe fanfon tana sharte ragowan ruwan dake fuskarta da tafin hannunta. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Kallon kanta ta shiga yi a showglass window dake a wajen sosai tayi kewar fuskarta, guntun murmushi ta saki kafin ta ɗauki dogon hijabi ta saka sa’annan ta ɗaura niƙab a kai ta kama hanƴa ta fita ta ƙaramin ƙofar gidan da babu wanda ke bi ta wajen, ta sha tafiya kafin da kyar ta sami mai taxi ta ce da shi ya Kaita WASACO Company LMT. Tafiyan mintuna 10 ya kaisu WASACO direban taxi ya dube ta ya ce ” Hajia Mun iso” wage wage Abee ta shiga yi don dai ita kam bata san ko ina ba sunan Company ɗin kawai taji a bakin Hajia, miƙa masa kuɗi tayi sa’anan ta fito zuciyarta na faɗi addu’oi ta shiga yi kafin ta shiga cikin Company ɗin ba tare da ta san abin yi ba, hanjin cikinta ne suka shiga kaɗawa ganin Alhaji da Hammad zaune a farfajian Company ɗin da dukkaninn alamu suna tattaunawa ne kan muhimmin abu, gaban Abee ya shiga dukan uku uku tama rasa abinyi tabbas in har ta juya ta koma sai sun kirata don dukkanin su sun an kara da ita musamman Alhaji data ga yaɗan da kata da yiwa Hammad magana da dukkanin alamu dai suna jiran isowarta ne, tattara dukkanin kuzarinta tayi waje ɗaya tare da saka hannunta ta cire niƙaf ɗin fuskarta kekkyawar surar fuskarta ya bayyana a fili, a hankali ta soma nufowa daf da su ba tare da tasan abin da zata ce da su ba, Alhaji ya zuba mata idanunsa Hammad kuwa kallo ɗaya tak ya yiwa fuskar nata ya janƴe idanuwansa a kanta, ba tare da tasan abin yi ba ta durƙusa a gabansu bakinta na ɗan rawa ta ce 
” Assalamu alaikum”………..::::

” Assalamu alaikum”, idanuwan Alhaji ne yayi azamar saukowa a kan fuskarta, ƙura mata ido sosai Alhaji yayi kamar mai nazartar wani abu. Jin babu wanda yayi yunƙurin amsa mata sallamar ya sata ɗan ɗago da kanta a hankali, caraf idanuwansu ya sarƙe waje ɗaya murmusawa tayi a hankali ta ce ” ina wunin ku?”, ɗagowa Hammad yayi ya ɗan saci kallonta kafin ya amsa a takaice, Alhaji ya ɗan gyara murya kafin ya ce ” Emmata lafiya dai ko?”, sosai ta so daburcewa ganin yadda idanuwan Alhajin suka kasa daina kallonta, da kyar ta iya kamo kuzarinta kafin ta ce ” Lafiya ƙalau, don Allah taimako nake naima”, Alhaji ya ce ” Taimako wacce kala baiwar Allah?”, Murmusawa Abee tayi kafin ta ce ” don Allah aiki nake naima a cikin Company ɗin nan” ta ida maganar a lokaci guda kuma tana nazartan ya na yin da Alhaji zai ƙarɓi maganar na ta, Alhaji ya ce ” toh ai mu bamu ce muna naiman ma’aikata ba a wannan lokacin ba”. ” Don Allah taimako zaku min wallahi ina matuƙar buƙatar aiki don Allah”, shiru Alhaji yayi kafin ya nisa ya ce ” a gaskia bama buƙatar ɗaukar wani ma’aikaci a wannan lokacin, amma dai zan baki card ɗin Company ɗin in har muna buƙatar ɗaukar ma’aikata zaki ga advert ɗin ko a gidan radio da newspapper, ki kira lamban dake kan card ɗin In sha Allah zaki samu aikin, Moallahidi bata card ɗin”, sai a sannan Hammad ya ɗago ba tare da ya ce uffan ba ya ciro card ɗin a gaban aljihunsa ya miƙa mata, da hannu biyu Abee ta saka ta amsa card ɗin tana yi masu godia, miƙewa tayi ta ce ” Nagode sosai sai anjimanku”  har ta fara tafiya ta tsinkayo muryar Alhaji yana kiranta “Baiwar Allah”, a hankali Abee ta juyo tana amsa wa Alhaji da “Na’am”, ” zo” a hankali ta koma ta durƙusa tana jiran ji daga bakin Alhajin. Tsuri Alhaji yayi yana nazartar fuskar Abee kafin daga bisani ya ja dogon ajiyan zuciya ya ce ”  Baiwar Allah ya sunanki?” , Ras Abee taji gabanta ya faɗi a hankali ta tattaro natsuwarta ta ce ” Sunana Fareedah Yusuf yola” ta ida maganar cikin sarƙewar murya, jinjina kai Alhaji yayi kafin ya ce ” sannu Fareedah ke ƴar wacce unguwa ne a nan?”, Hanjin cikinta taji suna son kaɗawa Kar dai a ce Alhaji kamata yake son yi?  ita ko ta ya yake son ta san sunayen unguwannin garin nan bayan ba fita take yi ba? Murmushi sosai tayi wanda har sai da dimples ɗin ta duka biyu suka lotse can ciki, tunowa da tayi ɗazun da tana zuwa ta karanta sunan wani unguwa dake bayan Company ɗin WASACO, a hankali ta ce ” ina unguwan Namtari Manga ne”, gyaɗa kai Alhaji yayi sa’annan ya ce ” toh madallah, Fareedah kin so yimin kama da wata wacce a duniya bana fatar sake haɗa fuska da ita , kamannin ki da ita har ya ɓaci, amma kam ban tunanin kin santa ƙilan kamanni ne kawai,” ranta ne taji yayi mugun ɓaci sosai, wata kau Alhaji har yanzun yana kan bakarsa na tsanar Mancy?, shi ko wani kalan baƙar zuciya gare shi wacce bata yafiya? a ce mutum shekaru aru-aru har yau don kawai ƴarsa taƙi zaɓinsa wanda har ga Allah da tayi biyayya ta bi zaɓin nasa cutuwa zatayi, wai a ce har wannan lokaci bai yafe mata ba, har yana iƙirarin cewa a duniya ya tsani ganin fuskarta? kuma baya shakkar sanarwa duniya? dama wai hannun mutum na ruɓewa ya yanke ya yardar ? Hmmm Kaka kenan watarana sai kayi kuka da idanuwanka, jininka ai jininka ne koman lalacewar sa kuwa. A hankali ta shiga lallashin zuciyarta don wani irin azalzalanta yake ba ta so ta biyewa zuciyarta ta aikata aikin dana sani don haka ta ɗan murmusa haɗida sanƴawa samar fuskarta murmushin da idan ka lura zaka gane cewa ya fi kuka ciwo, a hankali ganin har yanzun Alhajin bai daina kallonta ba ta ce 
” Allah sarki, ƙilan kamannin ne kawai ,Nagode sosai Alhaji bari na tafi” ta ida maganar tana mai murmusawa Alhajin. Murmushi Alhaji yayi kafin ya ce ” madallah, nima Nagode Allah yayi Albarka”
Abee ta amsa da amin sa’annan ta miƙe ta gyara niƙaf ɗin ta, ta ɗaura a saman goshi ba tare da ta saukar da niƙaf ɗin ya rufe fuskarta ba, sallama ta yiwa Alhaji ta wuce zuciyarta cike da fargaban in da Hajia Nenne take, don shine abin da ya fi damunta a yanzun. Tabbas taji da kyau sosai WASACO shine wajen da Nenne ta ce wa Faruk ya kaita, toh kodai WASACO ɗin guda biyu ne? Shine tambayar da ta gaza samun amsar sa. 

Story continues below

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Har Abee ta wuce wa ganinsu Alhaji bai dai na bin wajen da ta wuce da kallo ba, shiru yayi yana wani nazari daban jikinsa duk yayi la’asar, dogon lumfashi ya sauke kafin ya dubi Hammad wanda hankalinsa gaba ɗaya yana a kan wayarsa da yake ta famar daddannawa kiran sunansa da yaji Alhaji yayi ya saka ya ɗauke kallonsa a kan wayar, ya maida kallonsa a kan Alhaji tare da amsa kiran da yayi masa. ” Moallahidi, yarinƴar nan shin da wa tayi maka kama a cikin dangi?”, Shiru Hammad yayi ba tare da yayi wani tunani ba ya ce ” bata mun kama da kowa a dangi Daddy, mai kagani halan?”, Ko tunanin mai Alhaji yayi kuma? Allah masani don haka yayi murmushi ya ce ” kawai taso yimun kama da wata wacce na sani ne da ɗan komawa, yaushe tafiyanka Moallahidi?” ba tare da Hammad ya damu da canzawar maganar da Alhajin yayi ba ya amsa masa da ” jibi zan tafi in sha Allah Daddy” “Toh Allah ya kaimu” “Ameen Ameen”. 

Bayan fitar ta daga cikin Company ɗin ta samu wuri wajen inuwa ta tsaya, tunani fal ran Abeedah tama kasa sanin abin da ya kama ce ta tayi, ina zata nufa yanzun? Ina zata iya binciko inda Hajia Nenne take?. Kamar an ce ta ɗaga ido, caraf idanuwanta suka samu muhallin sauka a kan Hajia Nenne wacce ke ƙoƙarin shiga wani ƙaton gini dake gefen WASACO, da sauri saurinta kuwa, Abee ganin haka ya sa ta soma binta a baya zuciyarta na famar zullumi, tana ƙarasa shiga cikin ginin ta ga Hajia ta shiga wani ɓangare don haka itama ta bi bayanta, a hankali ta riƙa bin bayar Nenne ba tare da sanin Hajiar ba har Nenne ta shiga wani ɗaki da idan ka gansa zaka san cewa hall ne babba, Abee ja tayi ta tsaya tana ƙarewa cikin hall ɗin da mutanen da tagani sama da rai 50 zaune a cikin hall ɗin da kallo, showglass mirror ne hall ɗin mutum dake waje zai hango wanda ke a ciki amma mutum dake a ciki bazai hango mutum dake a waje ba. Daidai saitin ƙofar Abee ta tsaya tana kwaranƴo dukkanin addu’ar da ya fito daga cikin bakinta don ta sani kam in har a ka kamata dubunta ya gama cika , maganar da Nenne ta soma yi ne ya katse ta daga tunaninta. 

” Wallahi tallahi duk yadda za’ayi a fitar da wa’innan kuɗaɗen sai kun san yadda za kuyi ya fito ya shigo hannunmu, don ina da matuƙar buƙatarsu, babu wani ɗan iskan da ya isa ya hana shigowar kuɗaɗen nan hannunmu ba’a haifesa ba, ba kuma za’a taɓa haifansa ba. Na baku nan da kwana 3 tal kafin yaron nan ya bar ƙasar nan nake buƙatar ganin alert, na gama magana ku ta shi ku bani waje the meeting is over!” Hajia Nenne ta ida maganar tana buga teburin dake gabanta da dukkanin hannayenta biyu, da mutum ya kalleta zai san ranta a matuƙar ɓace ne, sai fidda huci ta hanci take Faruk kuwa dake gabanta ya miƙa mata ruwan faro ta amsa ta kafe kai ta shanye tas (Hajia Nenne akwai ta da son ruwa kam sosai😅). Mutanen ciki ne suka soma miƙewa a lokaci guda kuma suna cewa “sorry ma”, da sauri tabar wajen zuciyarta sai dukan tara tara yake, burinta kawai yanzun ta ganta a gida tunda ta riga ta gama jin abin da Hajia Nennen ta tattauna sai dai tana ƙara son sanin mainene dalilin haɗa taron? Su waye wa’innan mutanen?. Shine amsar data gagari samin amsar su, amma ta saka a ranta duk daren daɗewa in har tana lumfashi sai ta binciko komai da komai, a haka ta samu abin hawa ta koma gida ranta a matuƙar tsorace gudun kar wani ya kamata, ta ko ci sa’a har ta shiga ta kuma tsaga tabon fuskarta babu wanda ya shigo, dogon ajiyan zuciya ta saukar a hankali ta furta ” Allah na gode maka”, miƙewa tayi don ta gabatar da sallan la’asar. 

%^%^%^%^%%%^%^%^%^%^%^%^%^%^%^% 

“Wallahi tallahi, kinji wannan shine rantsuwar musulmi ko? Suhailat muddin Ina lumfashi a doron ƙasa wallahi sai kin zubar da cikin dake jikinki!, Sau nawa zan faɗa miki cewa bana buƙatar haihuwa wai? toh don uwar mai garinku a yau ɗin nan ko kina so ko ba kya so wallahi billahi cikin nan zai baƙunci lahira!” Kuka sosai Suhailat ke yi idanuwanta duk sunyi luhu-luhu sun ciko tap da hawaye sunyi jajawur da alamun dai ta yini ta kwana tana kukan, sosai zuciyarta ke mata zafi ita da wanne Sir Salman yake so taji ne wai? Yau watan su 4 kenan da aure amma dai dai da rana ɗaya mutumin nan bai taɓa faranta mata ba, ko wacce mace an san in tayi aure kyau take yi ta murje tayi ƙiba ta ƙara haske gwanin ban sha’awa duk inda taje ata sha’awar ta, amma ita sam bata sami koda rabin ɗaya daka cikin abin da ta lissafa ba, tayi baƙi ta rame sosai, in ka ga Suhailat bara ka so ka kuma sake son ganinta ba, duk kwalisanta nan babu shi, yanzun ta rame ta koɗe tayi duhu sosai. Baƙin ciki safe da rana har dare shi kawai take kwasa a wajen mijinta, a gabanta zai shigo da S fillo (Surayyah) su wuce har kan gadonsu na sunnah suyi ta baɗalar su, tana ji tana kallo mijinta ke zina a gabanta in sun gama ya saka ta dole ta gyara ɗakin, In har kaga Sir Salman ya kusanci Suhailat toh tabbas S fillo bata gari ko kuma sha’awar tasa a kanta yake so, baya damuwa da biya mata tata buƙatar yana gama biyan tasa buƙatar yake tsallake ta yayi wucewarsa, ga shi Allah yayi wa Suhailat mugun sha’awa, sosai take buƙatar mijinta a kullum amma ina sam shi bai san da wannan batun ba, a wajen sa kam in ma mutuwa za tayi sai dai ta mutu bazai biya mata bukata ba sam, muguntar da ya saba yi mata ma kuwa shine sai ya bari ta soma biyan tata buƙatar sai ya janƴe ya mirgina ya barta a kan gado tana juyi tana riƙe ciki. Sosai Suhailat ta fara na damar auren Salman, kuka kullum take tana roƙon Allah ya kawo mata ƙarshen wannan al’amarin. Kullum cikin kiran lambar Abee take amma amsar kullum ɗaya layinta a kashe, da kyar ta samu Hayfah ta soma ɗaga kiranta har ma tazo gidanta, Hayfah macece mai tausayi sosai don haka ta matuƙar tausaya wa Suhailat ɗin anan take baiwa Suhailat labarin barin Abee garin Kano amma ta boƴe mata inda taje da abin da taje yi. 
(karku manta ko Hayfah bata san abin da yakai Abee Adamawa ba, ta sha dai aiki taje yi ɗin kamar yarda Abeen ta faɗi mata). 

Shekaran jia bayan taje asibiti wanda shima da kyar Salman ya barta taje don ya hanata zuwa ko ina ƴan gidansu ma cewa yayi ta ce sunyi tafiya don haka ya saka babu wani nata da ke zuwa gidanta in ka cire Hayfah wacce itan ma sai In Salman yayi tafiya take zuwa. Gwajin farko likita ya tabbatar mata tana da cikin wata 3 daidai, a daa da malamai ke cewa akwai rabon ƴaƴa tsakanin ta da Salman murna take yi har babu kama hannun yaro, a yanzun kuwa baƙin ciki ne taf ran Suhailat yanzun a haka zata haifi ɗa ko ƴa su taso su ga halin da ubansu keyi? Dole ne fa In kayi zina da ƴar wata kaima tabbas sai anyi da ƴar ka. Wannan wani kalar rayuwa ce ta jefa kan ta a ciki? Mai zata cewa ƴaƴanta in sun tambayeta dalilin zaɓa musu uba mazinaci?, Ta ci kuka har ta gode Allah, da kyar ta sanarwa Salman ɗin tana da ciki a tunaninta ko zai tausaya mata tunda har tana dauke da cikinsa. Amma da dukkanin alamu mutumin nan bai san da wannan batun ba, hanka ɗata da yayi tayi gefe ne ya maido ta daga duniyar tunanin da ta faɗa. Kwallo ya shiga yi da ita ya kuma ce kafin ya dawo ta dau maganin zubar cikin da ya a jiye ta sha in ba haka ba ya mata rantsuwar musulmai na lahira sai ya fita jin daɗi………


” Mancy, Allah nayi kewar Adda Abee sosai” Farhana ta ida yi wa mahaifiyarta magana tana shagwaɓe fuska, murmushi Mancy tayi don ita kanta in ta ce ba tayi kewar gudalliyar ƴarta ba toh tabbas tayi babban karya. Numfasawa Mancy tayi kafin ta kallo Farhana sa’annan ta ce ” nima nayi kewarta Farhanatu’am” ƙara shagwaɓe fuskarta tayi ta ce ” toh Mancy ki ce ta dawo hakanan don Allah, ko hutun kwana biyu tazo tayi kinji ba Mancy?”, Murmushi Mancy tayi ta ce ” Farhanatu kodai kema zaki koma Adamawar ne? Kinga kyata kallon Adda Abee ba dare ba rana” Mancy ta ida maganar tana yiwa Farhanatun dariya, itama Farhanar dariya tayi tana cewa ” tadai zo Kano kawai, ai ni innaje a ranar za’a gane komai” ta ida maganar tana dariya Mancy ma ta ɗan ɗara kafin ta tsagaita dariyar ta ce ” humm aiko dai tsabar tsoro irin naki ba ?ƴar nan, kibar boss lady kawai ita tasan yadda zatay da su,” “aiko dai Mancy, bari na miƙe na yanka awarar kar Abbi ya dawo ya iske bamu gama ba” Farhana ta ida maganarta a lokaci guda kuma tana miƙe wa daga zaunen da take, Mancy ta ce ” aiko dai gashi Harees ma bai dawo daga aiken danay mai ba, da tuni na gama haɗin zoɓon nan wallahi, ko ina ya tsaya ?” Mancy bata rufe bakinta ba suka jiyo sallamar Haris in, murmushi Farhana tayi ta ce ” Mancy, kin ga ɗan halas in ana maganarsa ase yana tafe” nan dai suka miƙe suka wuce kitchen suka soma aikin gabansu suna hira abin gwanin ban sha’awa. 

-%%%%^^^^%%%%%%%%^^^%%%%%%%%%% 

Kiɗa da iface ifacen jama’u kawai ke tashi a cikin gidan, kai ka rantse club ne duba da yadda ƙarar sautin music ke tashi a cikin gidan, duk da cewa a ɓangaren Hajia ne suke ta’asar ta su, hakan bai hana sautin waƙar karaɗe dukkanin sashen gidan ba duba da irin ƙure volume da a ka yiwa speaker ɗin. Ƴan mata da samari ne kacokam tsassaye a makeken falon Hajiar dukkanin su babu mai suturar kirki sai faman rawa kowanne keyi, ƴan matan kuwa suna ta jujjuya ƙugu wanda hakan ke janƴo hankulan samarin garesu, su kuwa samarin sai su fasa ihu tamkar dukan aradu don ruɗar da ƴan matan su kuwa a lokacin kansu ke ƙara girma azatonsu burgar da sukai wa mazan ne ya sanƴa su yin hakan. Can na hango muku Asma’u a tsaye, maza biyu sun zagaye ta ita kuma tana tsakiyansu tana tiƙar rawa babu ƙakƙautawa, su kuwa sai faman shige mata suke yi suna romancing ɗin ta hankulansu kwance. 

Duk abin duniya ya haɗe yayi mata yawa, tama rasa da wani tunanin ya kamata ta faro, kanta duk ya ƙulle gam abubuwa sun gama cunkushe ma ta, gashi kuɗaɗen da Hajia take ta son su shigo hannunta sun jima da koɗewa a bankin nata (Hajiar) burinta na mallakar kuɗin ya cika, Hammad na tafiya Italy da kwana ɗaya suka sama damar kwatar maƙodan kuɗaɗen , tabbas ba zata manta ranar da abin ya faru ba, ta shiga yiwa Alhaji gyaran ɗaki bayan ta kammala tazo tafiya Hajia ta kirata ta ce tayi serving Daddy breakfast, anan ne taji Daddy kamar zaiyi kuka ya ke cewa Hajiar ” Hajia na rasa wannan dalilin” ɗan taɓe fuskarta Hajiar tayi kafin ta ce ” wani dalili kuma Alhaji?” Fuska ɗauke da damuwa Daddy ya ce ” na yawan salwantar da dukiyoyina suke yi, tun abin baya damuna har yanzun abin nason hanani sukuni, ko baccin kirki bana iya yi Hajia, ace an rasa mai ke janƴo wannan asarar? ki ga fa yawan kuɗaɗen da suka salwanta wannan karon, na rasa wannan dalili kuma na sa anata bincike amma babu wani progress” shiru Alhajin yayi don ransa wani kalan ƙuna yake sosai, bai son sake jefar da kansa cikin tunani har BP ɗin sa ya dawo, don yanzun yana mugun taka tsantsan don gudun hawan jininsa ya tashi don baya yi masa da kyau muddin hakan ta faru, Hajia Kuwa taɓe baki kawai take yi a cikin ranta kuwa ta na fadin ” kayi ka gama, aikin banza harara a duhu” a fili kuwa marairaice fuska tayi cikin sigar lallashi ta ce ” Alhaji kayi hakuri, In sha Allah komai zai daidaita amma ka bincike accountants na Companies ɗin kuwa?” “Nayi, babu wani good informations suma, amsar kullum ɗaya ce tak, haking data-base ɗin mu a ke and har yau an kasa kama masu yin hakan, har SS a ka sanya wannan karan don su taya mu, don kuɗaɗen sunyi yawan da za’a zuba ido wajen salwantar su hankali kwance” ‘Allah ya kawo mafita”. Shine kawai abin da Hajiar ta ce ranta kwance. Abee kuwa dake gefen su tana sauraren dukkanin maganganun na su, ji tayi kamar tayi tsalle ta isa gaban Hajia, da wallahi babu abin da zai haneta faffasa bakin matar har jini sai ta fidda ma ta, wannan cuta har ina?! da kuma mai yayi kama fisabilillah? Bawan Allan nan tsakaninsa da Allah ya riƙe matar nan and dukkanin wasu hakƙoƙinta da ke a kansa yana iya kacin ƙoƙarin sa wajen ganin ya sauke mata su, but ita in return ga abin da take saka masa da shi, bayan ha’intarsa da take da cin amanarsa da rabasa da kowa na sa har ƴar sa duk basu isheta ba har naiman ran ɗan sa take (Hammad) a yanzun ga kuma uwar uban asarar dukiyarsa da ta saka yayi. Ita kuwa anƴa da zuciyan Musulunci a tattare da ita kuwa? Don a iya saninta dukkanin al’umman musulmai ko ba komai suna da zuciyar imani, Hajia Nenne kuwa a ganin Abee lokacin da a ke raba imani Hajia tana bacci don kwatakwata matar bata da ɗigon imani, infact Abee na mamakin anƴa Hajia Nenne Na tuna ƙiyama kuwa?. “ke kuma mainene kika zo kika yiwa mutane tsaye a kai kamar wacce a ka aiko daga sama?” Hajia Nenne ta watso ma Abee tambayar lokaci guda kuwa ta katse wa Abeen kajeran tunanin da ta afka, cikin hanzari Abee ta saita tunaninta kafin tayi ƙasa da kai tana cewa “Afwan Hajia da..ma daa……ma”. 

Story continues below


“dama mai? Dama da a kayi mai?” Hajiar ta ida maganar tana ballowa Abee harara, wacce duk tabi ta birkice ba ma tasan sa’adda bakinta ya shiga karkarwa ba. A hankali ganin kamar ran Hajian a ɓace ya sa Abee composing kanta(kame kanta) kafin cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce ” Dama Hajia zan ce maki ne mai za’a girkawa baƙin da Alhaji zaiyi anjima?”, Sauke a jiyan zuciya Hajiar tayi kafin ta ce “cook anything sensesable Kawai”. Gyaɗa kai Abee tayi kafin ta juya tabar falon cike da taƙaicin Hajia Nenne, so take ta san weakness ɗin matar but from all indications Hajia Nenne ba ta da weakness don bata ɗaukan kowa ta sa shi a cikin ranta, she just live her own life Kawai, but ta sani ko mu jima ko ba daɗe zata san weakness ɗin Hajiar don ai ita ma mutum ce kamar kowa, and all humans have their own flaws (kowani bil’adama yana da weakness) tsaki Abee tayi sau babu adadi kafin taja ajiyar zuciya. Sautin waƙar dake ta shi duk yabi ya hana kunnenta samun hutu, wallahi ta gaji da irin wannan rayuwar da take ganin ƴan gidan nayi, yanzun ta gama karantar su basa tsoron kowa kuma basa shakkar kowa in ban da Hammad, ko wani rai dake a cikin gidan na mugun shakkar sa don inhar yana gari bara ka taɓa ganin abokan Faruk da Asma’u ba, sai In baya nan ne suke zuwa suci karansu babu babbaka, gidan kakanta ya dawo club ba dare ba rana masu aiki a ta ƙuntata masu, abinci suna yin sa kusan sau shida ko biyar a rana, basu da wani gata sai In har Hammad na gari, shi kuwa ba yawan zaman Nigeria yake ba duk yadda Hammad yaso ya dawo da zama gaba ɗaya a Nigeria Hajia Nenne ta hanesa wannan damar. Allah kadai zai kawo masu ɗauki cewar Abeen, kafin ta ja tsaki tayi shigewarta bayi don yin wanka.

%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%% 

“Hayfah, wallahi ya ce kafin ya dawo na sha wannan maganin ban san yadda zanyi da raina ba Hayfah!, I can’t kill an innocent life, ki taimaka min Hayfah wallahi Salman bai da imani. He can do all it takes to abort this child, ki taimaka min Hayfah.”  Yana yin yadda take maganar ma kawai ya isa mutum zubda hawaye, itama Hayfah harda guntun hawayenta don Allah nagani har cikin zuciyanta tana matuƙar tausayin Suhailat ɗin, ganin yadda duk tabi ta sauya yanzun daga Suhailat mai surutu that jovial lady to Suhailat yar shiru shiru, it really hurts to see her like that amma ya ta iya? Ita da kanta ta siyawa kanta wannan rayuwar babu sisin kowa bare kobo, so she is actually paying for her deeds ( don haka tana biyan dukkanin laifuffukan data aikata). Ganin shirun Hayfah ɗin yayi yawa ya sanƴa Suhailat daɗa ruɗewa cikin dasassiyar muryarta ta ce ” Hayfah!…..” Jim tayi kafin ta sharte hawayenta dake ta faman zirya a saman fuskarta, kafin ta ci gaba da magana muryarta a karye ” kema babu taimakon da zaki iya min ko? dole in haƙura a zubda cikin ko? Hayfah da kaina zan bada gudummawar kisan kai ko? Hayfah mala’eeku su ta tsinemin, Ubangiji ya ɗebe rahamarsa a kaina…….” Kasa ida sa maganarta tayi sakamakon wani ƙaton abu da yazo ya turnuƙe zuciyarta, babu wani mai rai mai zuciyar Musulunci da zai ga Suhailat a wannan yanayin (condition) ya gaza zubda mata da hawaye koda kuwa a ce kaɗan ne, sosai ta dawo abar tausayi, zaka rantse in har ba farin sani mutum yayi wa Suhailat ɗin ba ya gane ta a wannan lokaci, ta rame sosai fiye da tunanin mai karatu tayi matuƙar duhu, kwalisar nan tatah duk babu shi ta dawo tamkar mutum mutumi kawai a watanni da basu wuce 4 ba. Tabbas samun kwanciyar hankali da wanzuwar cikakkiyar natsuwa a tattare da jikin mutum, shi ke wanzar da isasshen lafiya a jikin bil’adama, muddin ka rasa ɗaya daga ciki toh ko tabbas rayuwarka na cikin halin ha’ula’i. Hayfah cikin sanƴin jiki ta ce ” Suhailat toh ki gudu ki koma gidanku mana, wannan shine kawai abin da zai iya ceton ki a yanzun muddin kina son haife cikin dake jikinki”, shiru Suhailat tayi ba tare da ta ce wa Hayfar komai ba, don bata tunanin wannan shawara ce mai kyau, Hayfah ta ci gaba da cewa ” kuma don Allah ki kwantar da hankalinki ki daina irin wannan maganganun Please, Allah ya na sane dake zai kawo miki ɗauki in sha Allah” daga haka Hayfar tayi wa Suhailat ɗin sallama don amsa kiran da mahaifiyarta ke yi mata. Sauke wayar tayi daga kan kunnenta jikinta a sanƴaƴe, idanuwanta duk sun canza launi sunyi jajawur sun kukkunbura sunyi suntum tsabagen kukan da suka sha. A hankali ta miƙe daga zaunen da take sa’annan ta wuce zuwa ɗakinta, toilet ta shiga ta watsa ruwa sosai don sai da ta tabbatar ta fara samun ƴar nutsuwa kafin ta fito, shafa mai tayi ta sanƴa doguwar riga mara nauyi ta ɗaura ɗankwali ta feshe jikinta da turare kafin ta soma ƙarewa halittar jikinta kallo, hmmm ita kanta bata son ta  yarda da cewa wannan ɗin da take gani a cikin mirror ita ɗin ce, ita ɗin dai Suhailat itan ne a cikin mirror, anƴa in ƴan uwanta sun ganta ma zasu amince da cewa ita ɗin ƴar uwar su ce? duba da yadda duk ta rame ta ƙanjame ta dawo tamkar kwarangwal, kwallan dake yunƙurin zubo mata a saman fuskarta ne tayi saurin sharewa tana faking murmushi don a yanzun bata son  abin da zai karyar da zuciyarta, don so take yau a wannan ranar ta kwatar wa  kanta ƴanci a wajen Salman ko ana muzuru ana shawo yau Salman zai sha mamakin ta, zata dawo masa ciwon idanu hakurin ta yayi yawa haka, ba zata zuba masa idanu yana tauyeta ba son ransa shi da karuwar fulaninsa. Zata zama daidai da ƙugunsu da ita suke zancen. (Anƴa Suhailat zaki iya kuwa?🥺) 

Story continues below


************************************************* 

11:30pm
Kwance yake kan makeken lallausar gadon dake a cikin ɗakin, jikinsa sanƴe da pijamas yayi kwanciyar ruf da ciki. Hannunsa riƙe da danƙareriyar wayar da’ake yayin sa a yanzun iPhone 11pro max golden colour. Ƙuri yayiwa screen ɗin wayar da manƴan sexy eyes ɗin sa har baya koda son ƙiftasu ko da na sakanni(seconds). Dogon lumfashi ya sauke yana ƙara ƙarewa halittar fuskarta kallo a karo na barkatai, kai ka ce yana son fidda wani abin ne a cikin fuskar na ta, ko kuma yana shirin zanen fuskar ne ya sanƴasa zaman nazartar face ɗin. Ringing ɗin da yaji ɗayar wayarsa dake gefensa yayi ne ya so katse sa daga dogon tunanin da ya afka, cikin zuciyarsa ya riƙa mitan wani isasshen ne ke kiransa a wannan lokacin da yake kallon abar ƙaunarsa, “abar ƙaunarsa!?”. Ya tsinta kansa da tambayar zuciyarsa, shin son ta wai yake data zama abu mafi girma da daraja a idanuwansa a yanzun? Bai taɓa soyayya ba! bai san yadda a ke yin sa ba bai da kuma masaniyar yadda a ke faɗawa cikinta, shi dai ya sani a yanzun babu abin da yafi darajasa da son kallo a koda yaushe kamar fuskarta, yanayin murmushin dake saɓale a saman fuskar na ta, dimples ɗin ta dake lotsewa can ciki koda kuwa a ce magana take. Baya iya bacci muddin bai sanƴa kekkyawar fuskarta a cikin idaninsa ba, ta zame masa allura cikin ruwa, murmushi da walwala ba al’adar sa ba ce amma yanzun suna son zame masa ɗabi’ar sa, ko aiki yake yi ko magana da mutane in ya tuno da fuskarta sai ya saki murmushi yata fara’a, mutanen su ta mamaki don a iya zamansu da shi sun sani shi ba mutum bane mai yawan fara’a fuskarsa a kullum babu yabo babu fallasa. Jin karar wayar na naiman wucin gadi ya sanƴa sa ɗagawa a fusace ba tare da ya kalla sunan mai kiran na sa ba, shiru yayi ba tare da ya amsa sallamar da a ke masa ba a ɗayan ɓangaren kuwa a ka kuma cewa ” sir your meeting with the minister would commence by 8:30am tomorrow by Allah wills”, Bai ce da ita ƙala ba ya kashe wayar yana jan guntun tsaki haɗida mai da hankalinsa kan hotonta lokaci guda kuma yana sakin mata murmushi a hankali ya furta. “My Senorita”……….. Bai san awowi, mintuna da sakannin da ya ɗauka wajen kallon hotunanta ba har bacci ɓarawo yayi nasarar yin awon gaba da shi ba tare da ya shiryawa hakan ba. 

####################################
” Kika ce mai? dan mai garinku nace ki maimaita abin da kika ce kafin nayi ƙuliƙulin gubra da ke a cikin gidan nan wallahi”. Nan ma shiru bata amsa ba, cikin tsawa wanda har yaso tsorata ta ya kuma cewa ” don kaza kazan ki( ya ƙunduma mata ashar) nace uwar mai kika ce min, kar na sake maimaita kaina in ba haka ba wallahi sai na nakaɗa miki  na jaki yau a cikin daren nan” sosai wani matsanancin tsoron sa wanda bata taɓa yin sa ba ya dirar mata a lokaci guda, bakinta da jikinta ya so ma karkarwa ta ce “babu komai……” Bai bari ta ida sa maganarta ba ya make bakin haɗida wulli da ita ta faɗi ƙasa kafin yayi nuni da ita da ɗan yatsansa, ” look Suhailat! Ni ba sa’an wasan ki bane ko ki faɗin min abin da kika ce ko wlh na lahira ya fiki jin daɗi” ganin ba ta da shirin yin magana ne ya sanƴasa ciro belt ɗin jikinsa ya soma nufarta gadan gadan, Suhailat ganin hakan ya sanƴa ta soma ja da baya don ta san muddin ya riƙo ta yau babu mai iya ƙwatar ta sai Allah don tabbas a rubuce yake jikinta sai yayi mata shi jina jina, ganin yadda ya dumfano ta cikin huci kamar zakin da ke shirin farautar rai, ya sanƴata sadaƙarwa  ita kuma yau nata yazo ƙarshe ɗaga hannunsa yayi zai shauɗa mata belt ɗin a zazzafe ita kuma Suhailat ta runtse idanuwanta tana ambaton sunayen Allah. 
Cak ta riƙe masa hannunsa da yake shirin zabgawa Suhailat ɗin duka da belt ɗin dake riƙe a cikin hannun na sa, tsuri yayi mata yana ƙare wa halittar fuskarta kallo babu ko ƙiftawa mai ya kawo ta gidansa? ya a ka yi kuma ta san gidansa, shine tambayar da ke yawo a cikin ƙwaƙwalwarsa, ita ɗin ma kallonsa take babu ko ƙiftawa sosai take mamaki dama duk cin kashin da take ji ana cewa yana yiwa Suhailat ɗin bai tsaya anan ba kawai harda duka? duka fa? Namiji mai dukar matarsa, matar ma wai Suhailat? Irin mijin da Suhailat ta aura kenan? Shine mijinta? mai dukan nata? Chabɗi jamnan da ranta da lafiyarta kam ba zata taɓa zuba idanu taga ana cin duduniyar Suhailat ba! duk da kuwa Suhailat ɗin ce ta siyawa kanta irin rayuwar, amma hausawa sunyi gaskia da suka ce naka dai naka ne komai lalacewar sa. Jin shiru ba tare da saukar belt a jikinta na wasu mintuna ya sanƴata soma ɗago da kanta a hankali lokaci guda kuma tana buɗe idanuwanta har ta buɗe su reras kan fuskarta, goge idanuwanta ta shiga yi don a zaton ta fuskar ce kawai ke yi mata gizo, ba ita ɗin ba ce a zahiri, sake buɗe idanun tayi a saman fuskarta again! mamaki ne ya cika ta sosai mai ya kawo ta gidan nan ? bayan bata taɓa zuwa ba? rabon da ta sanƴata a cikin idanuwanta kimanin watanni 4 kenan basa waya basa komai, cikin hanzari Suhailat ta soma kwala kiran sunan wacce ke a gaban Salman ɗin suna kallon kallo kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa. Jin Suhailat na kiranta ya sanƴata dawowa daga guntun tunanin da ta afka lokaci guda kuwa tana sakin hannun Salman ɗin cike da tsana tayo kan Suhailat ɗin da sauri tana amsa kiranta da ” Na’am……….” 

Cikin kuka Suhailat ta faɗa jikinta, ganin haka itama ta rungume Suhailat ɗin tana shafa mata bayanta a hankali, sun ɗau kimanin mintuna 15 a haka kafin Suhailat ɗin ta soma miƙewa daga jikinta a hankali. Cikin dasassiyar muryarta ta ce ” Mummy ke ce? Mummy ya a kayi kika san wannan gidan nawa?”, shiru Momyn Suhailat ɗin ta yi a lokaci guda kuwa tana ƙare wa halittar jikin ƴarta kallo, iya tsorata Mummyn ta tsorata ganin Suhailat ɗin a haka, shin ina jikin Suhailat ɗin ya tafi? A iya saninta dai ƴarta na da cikar jiki ba zaka kira ta  ƴar lukuta ba hakanan ba zaka ce ma ta siririya ba, irin jikin Suhailat a ke ma laƙani da duma duma don komai ta haɗa, amma a yanzun duk ta rame tayi fayau da ita tamkar wacce a ke tsotsewa jini a jiki. Ganin irin kallon da Mummy ke bin ta da shi ya sanƴata sunkuyar da kanta ƙasa don ba ta ma san mai za ta cewa Mummyn ba, cike da mamaki Mummy ta ce ” Suhailat ciwo kika yi ne? ramar jikinki yayi yawa, mai ke damun ki dota?”, Shiru Suhailat ta yi ba tare da ta amsawa mahaifiyarta ba, gefen da Salman ke tsaye Mummyn ta kallo yananan a tsaye ƙeƙam kamar wanda a ka dasa a wajen ko ta ce yana nan tsaye ƙeƙam kamar bishiyar da’aka dasa a wajen. Banzar kallo Mommy ta watsa ma sa sa’annan ta kuma kallo Suhailat ɗin kafin ta ce ” ke wai ba tambayar ki na ke ba? Mai ke damun ki? Ciwo kikai ne ? dube ki fa kamar wacce mayya ta kama ko a ke tsotsewa jini Suhailat?!”, Mummyn ta ida maganar ranta a matuƙar ɓace, ganin dai har yanzun Suhailat ɗin ta kasa ce da ita tak ya sanƴata waigowa ta ballawa Salman harara kafin ta ce cikin kakkausar murya ” we need privacy (muna buƙatar sirri)”. Tana faɗin hakan ta juya masa baya, shi kuwa mamakin matar kawai yake wai ta ya a ka yi ta san da wannan gidan? Ya dai sani bayan auren su ya sauya wa Suhailat ɗin gida don bai ma son kowa ya san inda take, kuma sosai ya gargaɗi Suhailat ɗin a kan hakan kenan ba ta ji maganarsa bane komai? ” Yaren da na yi ne baka ji? ko ban isa da kai bane ya sanƴa ka ƙin barin kanmu?”  Mommy ta katse masa tunaninsa, sosai matar tayi masa kwarjini hakanan ya tsinta kansa da juyawa ya basu waje ransa na tafarfasa a lokaci guda kuwa yana ayyana irin rashin mutuncin da zaiwa Suhailat ɗin in Uwarta ta bar gidan. ” Suhailat look at me ( kalleni)”, Mommyn ta umarci Suhailat ɗin, a hankali Suhailat ta ɗago tana kallon Mommyn idanuwanta cike dab da ƙwalla, ɗan nazar tar yana yin Suhailat ɗin ta yi kafin ta ce ” miƙe muje ki kwaso kayayyakin da kika san kina buƙata,” da sauri ta kallo Mummy fuskarta ƙunshe da mamakin furucin Mummyn, mai take nufi kenan? ” ma za miƙe na ce” Mummyn ta katse ma ta tunanin da ta afka, a hankali ta ce ” Mummy ina za ni?” harara ta bankowa Suhailat ɗin ba tare da ta ce da ita uffan ba ta miƙe haɗida ce ma Suhailat ” kin tashin ko kuwa?” Ganin fuskar mumy babu alamun wasa ya sanƴata saurin miƙewa jiki a saɓule tayi hanƴar bedroom ɗin ta, da taimakon Mummy Suhailat ta ibo kayayyakin da take da buƙata suka sanƴa shi a cikin trolley, Mummy ta kulle trolley ɗin kafin ta kallo Suhailat fuska a murtuƙe ta ce ” ki ɗauki mayafinki, ki zo ina jiran ki a falo” da toh kawai Suhailat ɗin ta iya bin Mummyn da shi don ba tada ikon musawa Mummy, ta sani ba zata cuce ta ba komai take yi ma ta a yanzun ta sani is for her own goods, Mummy ta sanƴa kanta tayi ficewarta a cikin ɗakin, tafi mintuna 4 a tsaye ba tare da tayi yunƙurin motsi ba a hankali taja jikinta ta buɗe wadrope ta ɗauki dogon hijabi ta zura sa’annan ta fice a cikin ɗakin jiki a sanƴaye.

*************************************************
Bayan kwana huɗu 

Gyaran closet ɗin Alhaji ta ke ƙoƙarin yi don tsaftace masa wajen, a yanzun babu wani lungu da saƙo da Abee ba ta gyarawa Alhajin. Sosai ya aminta da ita da dukkanin alamu dai Daddy ya yarda da Abeedah ɗari bisa ɗari bai ma ta shamaki da ko’ina ba a cikin ɗakinsa dalili kuwa shine irin yadda ya ga Abeedar ta bambanta da sauran ƴan aikinsa da su ka yi ma sa aiki a daaa, haka kawai ya ji yarinƴar ta kwanta masa a rai ba tare da ya san dalili ba. A hankali ta soma jan wani abu dake kama da frame, ganin shi tayi a can ƙasan closet ɗin don haka ta saka hannunta don ɗauka ta a jiye gefe ta share wajen don lura da tayi wajen yayi ƙura dayawa, bayan ta fito da frame ɗin ta a jiye gefe don sosai ƙura yayi yawa a saman frame ɗin share wajen tayi tas kafin ta ɗauki frame ɗin ta soma gogewa da towel dake hannunta da zummar in ta gama gogewa ta mayar In da yake, fuskokin mutane ta soma cin karo da shi gogewa tayi tas har yana kyalli sosai ta mai da hankalinta wajen nazartar hoton dake cikin frame ɗin, Family picture ne a ƙasan frame ɗin kuma hoton ƴar ƙaramar yarinƴace da ba zata wuce shekaru 5-6 ba, gani tayi kamar ita ce a cikin hoton lokacin da tana yarinƴa don sosai kamanninta da wadda ke cikin hoton ya ɓaci, ci gaba da kallon hoton dake sama tayi, Daddy da Faɗi sai ƙaramar yarinƴar wacce a ka sanƴa hoton ta a ƙasar frame ɗin, and ta na kyautata zaton Mancy ce, hoton sosai yayi matuƙar burgeta har bata san lokacin da ta suri wayarta tana ɗaukan frame ɗin hoto ba , a lokaci guda tana sakin wa kanta ƙayatacciyar murmushi har dimples ɗin ta na lotsewa can ciki. Kallon Faɗi kawai Abee ta sake baki tana yi, yaba kyawun matar kawai take yi a cikin zuciyarta, ga shi dai a cikin hoton ba zata wuci shekaru goma sha 15-16 ba gefenta kuwa Daddy ne suna murmushi sai Mancy dake riƙe a hannun Daddyn wanda a lokacin take ƴar jaririya da alamuma kamar ranar sunanta a ka ɗauki hoton.ƙwalla ne yayi nasarar silalewa a saman fuskarta, tunowa da tayi kakarta  bata rayu sosai da mahaifiyarta a rayuwa ba. Ta sani da’a ce tana raye Mancy ba zata taɓa wulaqanta ba, amma babu mai iya sauke kaddara in Allah ya rubuta, sosai taji ƙaunar kakarta Faɗi na shiganta kuma tana godewa Allah da ya ɗauke ta ba tare da ta taras da abin da ke faruwa a cikin rayuwar danginta ba (family), dogon lumfashi Abee ta sauke tana mai lumshe kwala-kwalan idanuwanta a fili ta ce ” komai Allah ya tsara wa bawansa baya taɓa tsallake wa”, ta sani a duk inda kakarta ta ke a yanzun bata farin ciki da danginta, don haka ne ma Abee ta kuma ɗaukar wa da kanta alƙawarin dawo da farincikin dangin Mancy. Daga haka ta miƙe ta ci gaba da gyarawa Alhajin ɗakin na sa bayan ta mayar da komai mazauninsa, bayan ta kammala komai ta kunna burner nan da nan ɗakin ya soma lulluɓewa da wani kalar sihirtaccen ƙamshi mai sanƴaya ran duk wanda ya shaƙa, fita tayi a ɗakin bayan ta kammala komai da komai kuma yayi mata yadda take so, ta koma part ɗin su cike da jin daɗi wanda ta rasa dalilin wanzuwar hakan. 

Story continues below


################################### 

” Hammad, dawowar ka Nigeria a yanzun yana da matuƙar muhimmanci” Hajia Nenne ta faɗi hakan tana karkaɗe ƙafafuwanta, kallonta Asma’u ta yi kafin ta ce 
” kefa kika sanƴa a ka tura sa can, mai yasa kike da buƙatar sa da wuri haka? Bayan ko sati biyu ba’ayi da tafiyar ta sa ba?,” ƴar ƙaramar harara Hajia Nenne ta wurga ma ta kafin ta ce 
” wai ke kam Ma’u in tambayeki mana?, Shin yaushe zaki daina tunani kamar yarinƴa ƙarama wai? Mutum sai ka ce ba ƙwaƙwalwar manƴa gare sa ba, kullum ƙwaƙwalwarki ya ta tunani tamkar na yara, karki manta fa kin haura shekaru arba’in, kar ƙaramin jikinki ya riƙa yaudarar ki kiyi ta tunanin ko You Are still young, a toh nide na faɗa miki.” Hajiar ta ida maganarta haɗida sakar wa Asma’un harara, sosai maganganun yayarta yayi mugun ɓata ma ta rai, amma sai ta shanƴe don ta na matuƙar son sanin dalilin da ya sa take son Hammad ya dawo Nigeria da wuri haka bayan ba hakan suka tsara ba a baya. 

” Ummm, Hajia ni de ina da buƙatar ƙarin baya Ni don na lura yanzun haɗe min kai kuke shirin yi ke da Faruk, yanzun baku fiye son hulɗar maganar da ni ba” , ta baiwa Hajiar amsa tana cuno sexy mouth ɗin ta waje, dariya sosai Hajia tayi wanda har ya sanƴa Asma’un sakin bakinta a wangale ta na mamakin mai Hajiar ke yi wa dariya haka? maganar Hajiar da ta tsinkayo ne ya ɗan katse tunaninta. 

” Shashasha kawai, ni kin ma bani dariya wallahi, Ohni!. Ma’u wai yaushe ne zaki daina yaudarar kanki?, ki san cewa kin girma ne ke kam?Girman ma ba kaɗan ba, ƙauye kike sarai kin sa ni ke goggo ce a yanzun, sa’oin ki duka yanzun jikokinsu suke aurar wa, ke kina nan zaune tsofe tsofe kamar bishiyar dabino, babu aure bare a kai ga tunanin samun ƙaruwa, ki na nan kina wai jiran Hammad yaro shakaf da shi ina shi ina ke fisabilillah? Ki fa yiwa kanki faɗa Ma’u! Toh ni dai na faɗi miki.” Ranta in yayi dubu toh tabbas ya gama ɓaci, bata ga dalilin da zai sanƴa Hajiar ta riƙa ci ma ta fuska ba har haka. Mai nene laifinta ita? gani tayi dai aure kamar mutuwa yake muddin lokacinka yayi za kayi auren, in lokaci bai yi ba kuma dole mutum ya haƙura, ita kanta ai ba son zamanta a hakan take ba in an tambayeta mainene babban burinta a yanzun babu wani second tunani za ta ce aure! ta ganta a cikin gidan mijinta shine babban burinta. Hajiar kuwa bata tunanin hakan kuma tana mamakin sauyawar Hajiar farat ɗaya a kan aurenta da Hammad a iya saninta daa Hajiar tayi matuƙar goyon bayan hakan, amma yanzun sai take ganin tamkar tana ƙin faruwan hakan ko mainene dalilin ta na hakan? Allah kaɗai ya sa ni da ita Hajiar. 

” yauwa kamar tambayana ki ka yi dalilin son dawowar da na ke bukatar Hammad yayi ko?” Hajiar ta katse ma ta tunanin da ta afka. Da ido kawai Asma’un ta iya amsa ma ta don bakinta ya mutu murus, don tabbas in ta ce zata yi magana toh bakinta ba zai taɓa furta alkairi ba. ” toh duk cikin plans ɗina ne, ki zuba ido kawai it shall end well”, daga haka Hajiar ta miƙe tabar falon gaba ɗaya, da idanuwanta kawai ta iya raka Hajian har taɓacewa ganinta. Numfasawa Asma’un tayi haɗida girgiza kanta kafin ta miƙe tabar sashen Hajiar ta koma na ta part ɗin. 

************************************************ 

Fitowa tayi daga cikin ɗakin sanƴe da hijabi, kallonta Mummy tayi kafin ta girgiza kai cike da tausayin ƴarta. “Mummy na saka” gyaɗa kai tayi kafin ta miƙe haɗida ce ma Suhailat ” kidau trolley ɗin ki same ni a mota” daga hakan Mummy ta sanƴa kanta ta fice a falon gaba ɗaya, ita dai Suhailat bata da ta cewa don haka taja trolley ta fito harabar gidan, babu motar Salman a parking lots hakan ya tabbatar mata da ya fita kenan, samun momy tayi a cikin motarta (motar Mommyn) sanƴa trolley ɗin ta yi a gidan baya kafin ta dawo ta zauna a gidan gaba, tayar da motar Mommyn tayi kafin suka fice a cikin gidan. shiru ne ya ratsa cikin motar babu mai cewa ɗan uwansa komai har suka yi nisar tafiya.
*************************************************
Fitowar sa kenan daga meeting wanda suka shiga tun ƙarfe 8:30am basu suka kammala ba sai karfe 12:30pm, sosai ya gaji kansa har wani sara ma sa yake. Straight ya wuce masaukinsa don ya matuƙar gajia, yana zuwa ya shige toilet ya watsa ruwa haɗida ɗauro alwala kafin ya fito, feshe jikinsa yayi da turaruka masu daɗi kafin ya sanƴa kananun kaya wanda suka matuƙar yi masa kyau. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Sallan azahar ya kabbara, ya jima yana roƙon Allah a kan Senorita din shi ciki kuwa harda son sake haduwa da ita in ya dawo Nigeria. Hammad sosai yake mamakin kansa, ya rasa dalilin da yasa duk ya bi ya damu da yarinƴar nan babu awanni mintuna da sakannin da zasu wuce ba tare da yayi tunaninta ba, sosai yake muradin sake jin daddaɗar muryarta mai shegen amoh da sauti mai daɗi. Ringing ɗin da wayarsa keyi ne ya katse masa tunaninsa da kamar bazai ɗauka ba don ya tsana abin da zai katse ma sa tunanin Senorita Ko kaɗan, sunan Daddy ya gani a kan screen ɗin hakan ya sa shi saurin ɗaukar wayar cike da ladabi ya shiga gaisar da Daddyn, 

” Lafiya kalau my son, fatan komai na tafiya yadda a ke so?” Gyada ma sa kai Hammad yayi tamkar yana gabansa ba tare da ya ce da Daddyn komai ba, sanin halin ɗan na sa da rashin son magana don sosai magana ke yiwa Hammad tsada ba kasafai ya cika magana ba da wuya mutum ya ce ma ka ya taɓa ganin Hammad yayi dogon magana, In kaga fara’arsa ko maganarsa toh tabbas da Daddy yake tare, shiyasa mutane da dama suke ɗaukan girman kai ne yayi masa yawa da miskilanci.
” Dama so nake duk abin da kake yi ka dakatar da shi, ina son dawowarka Nigeria nanda kwana uku” jim Hammad yayi don ya ma rasa yana yin da ya tsinta kansa a ciki farinciki ne ko kuma a kasin hakan? Shi dai ya sani sosai yake marmarin dawowa don naimo abar ƙaunarsa his very own Senorita Ko da bazai mata magana ba kawai ya ganta ko daga nesa ne, ” hello kana jina kuwa ?” Daddyn ya katse wa Hammad tunaninsa, nan ma gyaɗa kai yayi kafin ya ce ” eh Daddy Ina jinka”
“Yauwa Toh, fatan baka da matsala da hakan?” Bai iya musu da Daddy ba Ko kadan hakanan bai iya ƙetare maganarsa, murmushi yayi kafin ya ce ” babu komai Daddy” murmushi Daddyn ma yayi daga ɓangarensa kafin ya ce ” toh madallah, Allah yi maka albarka ta private jet ɗina zaka dawo don we need you urgently” “Alryt in sha Allah ” daga haka suka sauya hira kafin daga bisani suka yi sallama. Murmushi kawai yake sakin ma kansa don a ganinsa yana dawowa zai haɗu da Senorita.Hotonta ya danna dake manne a saman screen ɗin sa yana ƙare mata kallo kafin a hankali ya ce ………. 


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *