KAZAFI COMPLETE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Anyi auren Zulai da Abdurrahman cikin ‘kan’kanin lokaci, da farko ta rike yaran da zuciya d’aya tare da yaranta. Ba tare da nuna bambanci ba Abdurrahman ya tura su makarantar kudi, mazan in sun dawo. Suke zuwa koyon kafintanci ko weilder.+
***********************
Lokaci ya shud’e, awanni sun zama kwanaki, yayinda kwanaki suka juye zuwa makwanni, makwanni suka zama watanni har shekaru suka zagayo.
Abdurrahman ya zama babban malamin addini inda majalisan da ya bud’e ya kara hab’b’aka, manyan mutane na zuwa daukan darasi.
Zuri’an marigayiya Aysha sun taso inda Sumayya ke jami’a aji d’aya, yayinda Muhammad da Hamza ke aji hud’u a jamia, Ammar da Yasir na aji hudu a sakandari yayinda Suwaiba da Suwaida ke aji daya a secondary.
Naseer da Mahmud sun gama karatunsu, inda Mahmud ya fara aiki a babban asibitin jihar Bauchi kasancewanshi likita, Naseer shago ya bud’e babban shagon kafintanci kasancewarsa yana da ra’ayin kafa masana’antan aikin hannu.
In kai bak’o ne bazaka taba cewa ba Zulai ta haifi yaran gidan saboda rikon da tayi musu. Amma da zakai yini guda zaka fahimci wahalar da take basu.3
Kullum fadan sheikh Abdurrahman bai wuce na rashin son karatun yaran zulai ba, babban namijin mai suna Manniru ya fara shaye shaye da kawar da kayan da ba nashi ba. Sheikh yayi iya yinsa don ganin ya dena abin ya faskara.
Ana cikin haka mannira ta fara tara samari, bokon ma ta dena zuwa, se taga dama. Idan sheikh yayi fadan zulai ta ce yana na yaranta sharri. Se de ya gani a tare dasu.2
*********************
“Idan ance sannu a fara yi ma mannira sharri, dama. Annabi yace duk wanda yace d’an wani na abu toh ko shi ko nashi keyi, (inji karyan zulai fa) idan an taba mutum ya ce shi malami ne yasan Qurani da hadisi ” Zulai ce tashigo falon,suna zaune suna kallon labaran duniya,ta dubi sheikh
“Audurrahman ka kalli bidiyon nan ka gani.”1
“Atoh Abba yakamata kasha kallo” Fadin Mannira tana mai girgiza kafa.
Gaba d’ayansu dake zaune basu tanka musu ba. Sheikh yayi shiru can kuma ya dubeta fuska daure “Me kenan hakan Zulaikha?” Ta ajiye cd kan tebur “Ai gani ya kori ji ko kuwa? Kai sanya idanuwansa su gane mishi.” Ta fada tana kallon Manniru,da sauri Manniru ya dauka,nan da nan ya gyara saitin komai ya jona dvd kafin ya saka faifan.
Abinda idansu ya gano musu ko makiyinsu basa fatan su gani ciki.
“Ba yanda za’ayi tsarkakakke ya haifi mai yin zina ko ba haka kake cewaba, ina Sumayya tayi gadon zina kenan?” Zulai ta fadi tana mai (forwarding ) zuwa inda aka nuno Sumayya haihuwan uwarta da wani namiji suna aikata masha’a a halin turmi da tabarya.
Fad’uwar da Sheikh yayi ne,ya dawo dasu daga halin mutuwan zaune da suke. Nan ma Sumayya ta bi sawunshi. Zulai da yaranta sukai waje da gudunsu. Tsoronsu kada ya zamto mutuwa sukayi.
….’Kazafiii… ©Ummu Abdoul
(9)
Hankalin ahlin nan ya tashi ainun. Mazan suka kwashi Sumayya da sheikh sukai asibiti dasu. Masu hawaye nayi masu INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN nayi domin kuwa abun yazo musu tamkar saukan aradu.
Mamaki ya cika ni ganin Muhammad ko gezau, asali ma ko binsu asibiti beyi ba. Dawowa yayi ya cire CD din ya kai d’akinsa ya adana. Sannan ya bi su Zulai d’akinsu.
Zawo ne kawai basuyi ba don suna tsaka da magana ya shigo. Amma da alama bai ji me suke fadi ba. Da fara’ansa ya karasa ciki ya zauna kan kujera.
“Mama Zulai Allah ne kawai ze biyaki domin kuwa kinyi jahadi.”4
“Hmmmm kai de mai sunan Baba, ni yanzu tsoro na ace nayi kisan kai, ina shiekhin?.”
“Ko mutuwa yayi ai ‘yarsa ce ta kashe shi, kin sa na tuna wakar da arna ke yi muna makaranta…
Zunubi tudu ne in ka hau naka se ka hangi na wani.”
“Hmmmmn wallahi ko, kasan kwanaki da Mannira ta yi wani shegen al’ada haka jini yai ta digan mata sheikh cewa yayi zubar da ciki tayi, wallahi har saki na yayi akai. Yanzu fa igiya daya ya rage mana “
“Kut.. Wallahi Mama Zulai ki lallaba, kin ga dai tashen kudi yake yanzu. Ki daiyi tunani kafin gobe sai musan abinyi, yanzu bara na koma kafin su isko ni nan.”Yana kaiwa nan ya fice.
“Zulai kinga ikon Allah ko, ai na fada miki zasu yarda.” cewar Mannira.
“Ungo nan!” Tayi mata dak’uwa.
“Kina ganin zai yarda damu akan ‘yar uwarsa. Kinsan yafi kowa min rashin kunya”
“Amma Zulai kina ji yana baki espo, nufinshi fa ki gama da tsohon nan kamin ya sake ki, shima shegen kudi yake so.” Fadin Manniru a cikin muryan sa na maye. Haka suka cigaba da tattaunawardu dai.
*******************
ASIBITI
(Accident and Emergency) aka kaisu na asibitin tarayya dake bauchi (FMC) likitoci sunyi kokari wajen kwato rayuwansu domin zukatansu suka tashi bugawa. Allah cikin ikonsa ya takaita.
Kwanan Sumayya biyu ta dawo hayyacinta amma damuwa ne cike a ranta bazata taba manta hoton da ta gani a akwatin TV wai ita ce haihuwan uwarta. Ya subhanallah. (How, where and when) abinda tayi ta nanatawa kenan.
2
…’Kazafii…. ©UA
(10)
Satin sheikh biyu kafin aka sallame su suka koma gida, Sumayya ko sati bata cika ba aka sallame ta daga gadon asibiti amma tana ma’kale da abbanta.
Ko da suka koma gida, yaci abinci yaranshi duka zagaye dashi se ya tsinci kanshi cikin farinciki. Inama inama mutuwa bata zama mai YANKAR KAUNA ba da Aisha na nan zaune kusa dashi.
Tun bayan aurensa da Aysha wacce ta kasance tsarkakka, nutsatsiya, bai taba samun digon abinda ze sa ya zargeta ba. Tana da rikon amana da kariya ga abinda ya mallaka tun ba ita kanta ba. Ta kaunace shi ta kula dashi ta tarbiyyantar da yaranshi.
Duk acikin yaran yafi son Sumayya. Kasancewa tafi sauran yaran kama da Aisha sannan kyawawan halayyarta da ri’ko da addini yasa yafi sonta.
Tana da shekara goma sha hudu (14) ta haddace kur’ani a ‘kiraan hafsi da k’aloon. Ta haddace hadisai kamar su Bulugul maram, Sahihain, Umdatul ahkam da sauransu.2
Ta kasance gwana a fiqhu, da Usulul fiqhu. Tayi karatuttuka da dama wanda mafi akasari ta haddace.
A iya saninsa Aisha tana kiyaye dokokin Allah, tuncdaga kan sutura har kamala. Meyasa zatai masa haka……
Hannun da yaji a fuskansa ya dawo dashi tunanin da yake. Sumayya ce ta share masa hawayen da ya gangaro masa kana ta zube guiwowinta a kasa alamun neman gafara sannan tace;
“Abba banda bakin da zan wanke kaina amma wallahi wallahi ban aikata ba, na kasa tuna yaushe hakan ya faru. A iya rayuwata hakan bai taba faruwa ba. Ka yafe min Abba na, fushinka ba karamin matsala bace a gare ni.”
“Abba kayi hakuri ka yafe mata, Adda bazata taba aikata hakan ba”. Cewan Ammar yana mai sheshek’a.
Shigowan Muhammad ya ankarar dasu rashinsa cikinsu. Kuma ganinsa tare da Zulai da yaranta yasa kowa ya bishi da ido.
Zama yayi yana wani daure fuska, daukan waya yayi yana danne danne, take wayan shekhi yayi kara, karantawa yayi yana mai murmushi da aje wayar..+
“Assalamu Alaikum wa rahmatullah.” Sallamar sheikh ya dawo da masu tunani daga duniyar tunaninsu.
Tare suka amsa sallaman suna masu natsuwa da mika Masa hankalinsu.
“Abinda yasa na tara mu anan ba komi bane face inyi fashin ba’ki akan mummunan abinda ya faru da ahlin gidanan sati biyu (2) da suka wuce.
Nayi ba’kinciki sosai akan wannan bawai don na yarda ba sai don b’ata ma Sumayya suna da akayi. Tabbas ka haifi d’a baka haifi halinsa ba, amma tunda nake ban tab’a zina ba kuma na tabbata Allah da rahmanSa ze kare yara na musammman matan daga aikata zina….” Kuka ya saki mai tsuma rai domin bidiyon ya dawo masa sabo dal ne a idonsa.
Yaransa suka karaso suna rungume shi. Kowa so yake ya share hawayen ubansu abin soyuwa agaresu. Gyaran murya yayi kana ya cigaba.
“Zulai ina kika samo wannan video din?” Ya karasa zancen yana kallon zulai.
Ta hau daure fuska
“Ai nasan ba yarda zakayi ba, ciki nawa sumayya ta zubar da zaka lauye ni nan. Bidiyo de ya shiga duniya ehe, an de ji kunya”.
“Kar ki fara masa rashin kunya fa, don wallahi akanshi se in miki dan banzan duka.” Fadin Hamza yana mai mikewa a fusace.
“Toh rasa kunya, ita ta sa kanwar ka tayi abin kunya?” Ya kai ma Sumayya shuri tai maza ta kauce. Sannan ya cigaba “Wallahi duk wanda yace ze taba min matar uba gidannan se anyi rigima. An dad’e ana tauye hakkinmu akan sumayya.”
Nan fa rigima ta kaure tsakanin ‘yan biyun da ba’a taba jin tsakaninsu ba. Sai da sheikhi ya tsawatar musu sannan sukai shiru. Farincikin Zulai baze misaltu ba, hatta su Manniru da ke d’an shakku akansa sun fahimci shi d’in nasu ne.
“Abba ina da magana” Nasir ya katse shirun da ya biyo baya.
“Bismillah”
“Abba na gurfano a gabanka ina neman auren kanwata Sumayya, Abba ka taimaka ka yarda ka sanya albarkanka a ciki insha Allah zaka kasance mai farinciki da wannan had’in “
“Tabbas wannan ne kawai (solution) Abba, sai ayi rana daya da nawa kawai” fadin Mahmud kenan cikin farinciki.
Tun da aka fara rigiman nan suka rasa mafita da zasu sanya Abbansu farinciki. Mahmud ya fara kawo shawaran amma fir Nasiru yak’i yarda don wani sashi na zuciyanshi na zargin smSumayya. Fadi yake “Ta ya za’a ganta tana aikata abu muraran, don son zuciyanku kuce ba tayi ba.Video ne fa ba hoto ba.”Duk yanda Mahmud yaso ya fahimtar da shi yaki yarda ya fahimta duk a cewansa ai yaga zahir2
…’Kazafii… ©Ummu Abdoul
(12)
Kowa awajen yai mamaki kuma yai farinciki da wannan kalami na Nasir. Idan aka d’ebe Zulai da yaranta.
“Mtsww aikin banza to aurenta ne zaisa ace bata san namiji ba?” Kalaman Zulai kenan ta kara gaba, ba gardama yaranta da Muhammad suka bita a baya.
Sumayya jin wani sonsa na taso mata tundaga tafin kafanta har zuwa kwanyanta. Bugun zuciyanta ya ‘karu don ko a mafarki Hamma Nasir irin mijin da take gani ne. Miskili ne maras son magana, hakan bai hana mutum ganin yalwataccen fara’a kwance a fuskansa. Mutum ne shi mai kyauta, baya kyashin sadaukar da sisinsa na karshe ga mabu’kaci. Ga yawan ibada da bin dokokin Allah. Hawayen farinciki ne ya gangaro daga idonta.
“Nasiru ka tabbata har cikin zuciyarka ne wannan za’bin?.” Kalaman mahaifinta suka dawo da ita duniyar tunani.
“Eh Abba, albarka kawai zaka sa mana.”
“Allah muku albarka Ya baku zuri’a dayyaba.”2
*********************
Biki nata matsowa. Shirye shirye ake ba kama hannun yaro,Nasir ya kammala gininshi da ke unguwar Nasarawa Jahun. Gini ne wadatacce wanda ya kunshi dakuna uku duk da bandaki a cikinsu da falo wanda a gefensa akwai bandaki shima, se sashin baki da keda daki daya da bayinta a ciki. Daga gefen hagu kuma ‘yar baranda ce (passage) da zai sada ka da kitchen da store. Harabar gidan kuwa furanni ne zagaye kasancewanshi mutum mai son yab’anya zagaye dashi.
Abinda ke damun Sumayya rashin samun kalmar SO daga Hammanta, ba yabo ba fallasa za’a zauna ayi hira kamar da, daidai da rana d’aya bai taba kiranta don su shirya wani abun dangane da rayuwan da zasu yi tare ba. Kodai ze aureta ne don rufa ma mahaifinta asiri? Tunaninta kenan kullum wanda hakan ke jefa ta cikin damuwa…
Zaune suke ita da Hamma Nasir da ya aika kiranta. Sun gaisa kenan se ga Manniru ya taho yana layi
“Baaba na fada maka ka dena daga mana kai, abinda sauran su Jackson zaka kwasa, wane irin bomb ne bamu shuka da ita ba, zaku wani zo ku zauna nan wai zance, mtswwww.”
Dafe kansa yayi, ba don baya son bacin ran Abba ba da ba abinda ze hana shi fasa auren nan. Shi mutum ne mai tsananin kishi,duk sadda kuwa suka hadu sai ya gasa masa magana. Shekaranjiya haka ya watso masa wasu hotuna, duk nata ne da wasu mazan. Bakinciki yasa ya gagara kwashewa har Muhammad yazo ya gansu. Kalaman Muhammad ya tuna inda yace “Hamma Naseer kabi zuciyarka kar ka cutar da kanka”3
…’Kazafii.. 13 ©Ummu Abdoul
Shiru yayi yana kallon Muhammad, “Allah hamma (follow ur mind)” yana kaiwa nan ya fice daga d’akin.
“Hamma’am”
Muryan Sumayya ya dawo dashi daga duniyar tunani. Hawaye ne kwance a kuncinta, tsareta yayi da jajayen idanunsa da suka rine sukai jajir don ba’kinciki.
“Tashi ki koma ciki” abinda ya iya fadi kenan. Zuciyanshi na tausa, da za’a gwada jininshi tabbas da zaa iske ya hau. Alwala kawai yayi ya shige masallacin gidan ya fara sallah yana mika kukanshi ga Allah.
Tashin da tayi d’aki ta shiga tana kuka mai tsuma ran mai sauraro, turo kofan da akayi yasa ta d’ago idanunta da suka kumbura suka rine zuwa kalan jaa. Yayanta ne Muhammad mai sonta a da, tunda abinnan ya faru ko kallo bata isheshi ba.
A tarihin rayuwanta ta San ba Wanda ya so ta in aka cire abbanta sama da Muhammad. Shine abokinta itace aminiyarsa. Kaifin Basiransa da wayon sa yasa take kiransa da SSS, kuma ita ta chusa masa raayin zama hakan.
Duk yanda ka kai ga wayau ko dabara wajen boye laifi kallo d’aya Muhammad ze maka ya gano baka da gaskiya.
Tashi tayi da saurinsa ta fad’a kirjinsa tana sabon kuka, bayanta yake shafara alamun lallashi. Ya juya ya tura kofan d’akin yana mai rungume da ita.
“Bro ka yarda na aikata laifin nan har ka guje ni, ta ya ka kasa gano masu laifi wannan karan? ta ya ka ki yarda da aminiyarka wannan karon?” Duk ta had’o masa tambayoyin nan.
Zaunar da ita yayi gefen gado kafin yace cikin d’aga murya “Saboda kin chanza daga sumayyan da na sani, saboda kin ci amanar marigayiya da ta kasance mafi Alkhairi a cikin uwaye why sumayya?”
Wani sabon kuka ta saki, rungumarta yayi da kyau a jikinta yana mata magana da ni kaina banji ba, fuskan nan nasa a daure. Kallonsa Sumayya take kamar ranar ta fara ganinsa. Yanayinta zance kamar wacce ta hango tsira a lokacin da ta cire rai ga samu.
Daga idon da zanyi Zulai na hango labe a jikin taga farinciki fal a zuciyartaBinsa tayi da kallo har ya fita. Ganin kuka baze fishe ta ba yasa ta tashi ta dauro Alwala ta gana da mai share hawayen bayinsa, Buwayi gagara Misali.
Biki saura sati biyu amma ba abinda ya sauya tsakaninta da Hamman ta, bazatace yana mata wulakanci ba, zasu gaisa, zaayi hira gaba d’aya gidan amma ba abinda ke had’a su.
Ana sauran sati daya bikin sheikh ya tara gaba daya iyalin gidan. Bayan an bude taro da addua yace;
“Dalilin da yasa na tara ku anan ba komi bane se in ja kunnin ki Zulai da yaranki, idan har d’aya daga cikinku yai furucin batanci akan Sumayya har wani da yazo biki yaji, ko cikin danginki ko nawa toh babu igiyar aure tsakaninmu wato abakin aurenki. Idan kuwa har ya dawo kunni na bacin saki se nasa an kulle ku, kin san de zan iya”. Iyakan kad’uwa ta kad’u don shirinsu su bata na kowa rai.
“Tab d’an auren da nake lallabawa balle yanzu da yake tashen kudi, ya sake ni in je ina” abinda take fadi a ranta kenan yayinda a bayyane tsaki ta ja
“Mtswwww hakan ne ze sa ace ba kingin maza bace, kai de Nasiru ka kwasan ma kanka rijiyan kasuwa” tana gama fad’i tayi daki tawaganta suka bita.
“Abba wai me ke damun Muhammad?” Fadin Hamza bayan fitan muhammad din tare da Manniru. Shirun da sheikh yayi yasa suka chigaba da hiransu har shi yana musu nasiha akan rayuwar duniya.2
***
‘Yan uwa daga Gamawa da Azare sun fara iso wa, kowa ka gani da murna fal a cikinsa. An gyara amarya tayi kyau kwarai, fatarta se sheki yakeyi, domin Rufaida Omar’s SPA aka gayyato tazo tayi gyaran amarya.
ALKAWARIN ALLAH YA CIKA
Dubban mutane daga ko’ina a fadin kasar nan suka hallarci daurin Auren Sumayya Abdurrahman da Nasir akan sadaki mafi Albarka 50,000. An shirya walima ga maza bayan daurin Auren. Inda aka ci aka sha.
Cikin gida ma biki ake sosai, anci an batse. Yayinda kannin marigayiya suka sa Sumayya a d’aki suna bata shawarwari da zatai amfani da shi wajen siye zuciyan Nasir. Sun mata gatan da ko mahaifiyarta nada rai iyakanta zaa mata.
Ranar ita da ‘yan uwanta sunyi kukan rashin uwa, mutuwar ta dawo musu sabo haka suka had’u har su Nasir suna kuka, hatta shi sheikh dauriya kawai yakeyi yana basu baki2
… ‘Kazafii.. 15
©Ummu Abdoul
Karfe takwas na dare aka mik’a ta gidanta bayan iyaye sun mata dogon nasiha. Kawayenta da kanninta sun taya ta kwana washegari akai bud’an kai aka watse.
Sunyi nafilan da manzo SAW ya koyar sannan ya mika mata bakin leda ya fita. Babu abinda yake tunawa sai kalaman Zulai gab da zai baro gidan,ta tare shi a harabar gidan “Ahayye wai ango kenan, toh wace irin amarya gare ka don kuwa ba budurwa bace, budurbudur ce ko muna budurwa ko bazawaran budurwa..” Tana kaiwa nan ta kara gaba. Dafa kanshi yayi yana tunani.
A bangaren Sumayya kuwa ko kallon ledan batayi ba, ta tashi tasa ma ‘kofan d’akin makulli sannan ta chanza kaya. Tambayar kanta take ko wace irin zama zatayi da Hamma Nasiru? Dad’i ya mamaye zuciyarta yayin data tuna adduo’in da kwararo masu yana dafe da goshinta bayan sun idar da sallah.
Washegari tun karfe hudu da rabi (4:30am) ya tashe ta, shi ya jasu sallan tahajjud din,wanda ya kasance wutri ne mai raka’o’i biyar. Ya tsawaita musu sujjadar karshe inda itama ta samu damar rokon Allah ya mallaka mata zuciyar mijinta. Ta roka ma iyayenta gafara da daukacin al’umman musulmi.
Inda tayi sallan asuba nan barci yayi gaba da ita. Ba ita ta tashi ba sai karfe 9am. “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun” Ta fadi yayinda taga lokaci.
A falo ta iskeshi har yayi wanka, zuwa tayi ta zauna a daidai kafarsa tace “Hamma ina kwana”
Dago kai yayi yana kallonta, na kusan dak’ik’a hamsin,kafin ya ce
“Lafiya lau, ga abinci can an aiko daga gida kiyi (serving) dinmu don karfe goma zan fita.” Ya fadi yana mai k’ara had’e rai.
Bata ce komi ba d’akinta ta koma tayi wanka ta sauya kaya domin d’aya daga cikin nasihohin da akai mata shine “Kar ki yarda ya fita kina cikin halin k’azanta”
Minti (15) ya dauke ta tayi wanka da kayatarciyyar kwalliyanta da dole ya ba duk wanda ya kalla sha’awa.
A hankali ta bude ma’adanar abincin, masa (waina) akai musu lafiyayya da miyan taushe,ba tare da b’ata lokaci ba ta jona (cordless jug) da ruwa a ciki, cikin minti uku (3) ya tausa ta sake a karamin (water flask) ta shirya a faranti ta kai masa.
Batare da ta nemi shawaransa ba ta had’a masa shayi ta had’a nata sannan ta zuba musu wainar a kwano daya.
“Bismillah food is ready” Ta fadi tana kara gyara masa inda zai zauna a kafet din. Batare da ya ce uffan ba ya zauna, ruwan wanke hannu ta mik’a masa ya wanke kafin su fara ci, suna ci, tana d’an janshi da hira yana amsa mata a gajarce.
Haka suka kammala ta chanzo ruwan wanke hannu ta bashi ya wanke, ba tare da yace uffan ba ya sa kai. Saida ya kusa k’ofa ya juyo yace “Na tafi.”
“Allah bada sa’a Ya dawo da kai cikin aminci” Tayi kokarin fadi, shi kanshi ya ji kunyar me yayi. Tunawa da zantuttukan Zulai da Manniru ke bata masa rai.
….’kazafii… 16
©Ummu Abdoul
Da rana ma an aiko musu da abinci amma ita kad’ai taci don bai dawo ba sai wajen karfe (8) na dare, kamar yanda tayi da safe haka nan tayi, cikin kwano daya suka ci sakwara da miyan egushi.
Suna kammalawa ta tattara kwanukan ta wanke su, ta rufo kitchen d’in sannan taje daki ta kwanta.
Haka rayuwan ta kasance musu tare suke cin abinci. Har sukai sati uku,baya sakar mata fuska amma hakanan zata zauna tana masa hira wanda amsarshi bata wuce eh, a’a, uhum sai wani sa’in yakan mata murmushi.2
An tashi da matsanancin sanyi amma bakincikin da take tattare dashi ya sata yin gumi. Bata b’ata lokaci ba wajen had’a musu karin safe, hawaye ke zubo mata, wato ya yarda da KAZAFIN da akai mata kenan. Tana shirya masa abincin ta koma dakinta ta rufe. Babban abun bakinciki ne namiji ya soma neman raya sunnah dakai ya ja tsaki kuma ya barka,wannan wulakanci dame yayi kama?
Baiyi mamakin ganin haka ba don tabbas yasan bai kyauta ba. Zama yayi ya ci abincin sannan ya fita.
Da daddare ma hakan ta kasance, nan ne hankalinsa ya tashi, daki ya bita ya iske ta kwance rub da ciki tana karatun littafin “You can be the happiest woman na Dr Aaidh ibn Abdullah al-Qarni” Gefenta littafin “LA tahzan (dont b sad) ne da wasu littafan duk na Dr Aaidh ibn Abdullah al-Qarni.
Daukan littafin Don’t be sad din yayi ya fara duddubawa kafin ya d’ago ta daga kwancen.
“Kiyi hakuri ki qara min lokaci komi zai zama daidai”
Bai jira amsarta ba ya tayar da ita ya rugumo ta yana rik’e da littafin dont be sad in da d’ayan hannun. Ba gardama ta bishi har suka kai karamar falon da suke cin abinci, ya zaunar da ita yana bata abincin a baki. Haka har suka cinye. Shi ya kwashe kwanuka ya kai kitchen ya wanke su ko da ya dawo ta koma daki.
Mamakinsa ya cika ta, tunanin abinda ya faru tayi. Sun gama cin abincin dare wanda duk kayan marmari ne, fruit salad ne se cocktail da tai musu ya ji madara. Ko da suka kammala basu ko iya cin jolof din cus cus din da tayi.
Tun da suka kammala ya jawo ta jikinshi, ranar duk shi yayi hiran, fargaba da tsoro ya cika ta a wani b’arin kuma murna take lokacin wanketa yayi.
Shi ya kaita d’akinshi da kanshi domin daukan jarirai yai mata, anan kuma labari ya sauya salo amma me, bata san me ya faru ba tashi yayi kamar an tsikaro shi, cikin fushi ya nuna mata hanyar kofa “Get out!”
Sum sum ta fice tana mai jin tuquqin bakinciki a ranta. Tun daga lokacin ta dauki alwashin janye jiki daga gareshi..
A bangarensa da ya dawo ya iske batanan kuma, hankalinsa ya tashi, fadi yake “Ya Allah ka taimake ni, kar kasa ta tsaneni, ya Allah ka mantar dani zantutukansu Zulai Ya mai rahma mai jinkai.”Tun daga daren zata girka, tayi kwalliya su zauna suci, amma bayan gaisuwa ba abinda ke had’asu. Shima da yake ba gwanin magana ba sai ya shareta, gaisuwan ma ya daina amsawa cikin sakin fuska.
Yau da gobe se Allah, Nasir ya wayi gari da matsanancin son Sumayya, kishinta a ranshi ya karu hakan yasa yadaina zuwa gidan sheikh don duk sadda yaje sai an fada masa zancen da zai k’ara masa tabo a zuciyarsa.
Tunda ya daona zuwa gida yake dawowa da wuri wani sa’in ma tare da matarsa yake cin abincin rana duk da rashin hiran da sukeyi yana jin dadin haka. A haka so da kaunar junansu ke ninkuwa a zukatansu.. ( kira ga mata masu raba kwanon cin abinci da miji, hakan na nisantar da kaunar da ke tsakaninku, cin abinci kwano daya na haifar da soyayya da kauna tsakanin masu ci, haka ku koya ma yaranku cin abinci a tare).
Yau kamar kullum ya dawo da azahar, hayaniyar da yaji yasa yasan da bak’i a gidan. Da sallamarsa ya shiga nan ya iske Sumayya na dariya, farincikin da yagani bayyane a fuskanta in baiyi kuskure ba rabon da ya gani tun kafin fitowar bidiyon nan.
Yafi minti goma tsaye yana kallonta, sonta na kara ratsa dukkan sassan jikinsa. Kamar ance ta d’ago sai ta ganshi tsaye, tashi tayi cikin sassarfa ta karasa inda yake, sumbatarsa tayi a kumatu sannan ta amshi ledan hannunsa tana me cewa
“Marhabanbika yaa Rafeeq”
Murmushi kawai yayi yana mai rungumo ta ta gefen shi, sun ba duk wani ahalin falon sha’awa, sai murmushi suke jefansu dashi.
“Twins ne yau a gidan, (big, bigger) toh ina su (biggest)”
“Sannu da zuwa, ina yini Hamma Nasir” Suka fadi a tare, suna masu farincikin ganin Hamma na kula da yayarsu.
Wani sabon hira aka fara, ya tsokani wannan ya tsokani wancan. Sai bayan magriba ya maida su gida. Duk yanda Sumayya taso aje da ita yaqi.
Son Sumayya ninkuwa yake a zuciyar Hammanta, ko da yaushe gizo take masa, ko yana wajen aiki. Baisan ya akayi ya fara ba amma baya awa daya zuwa biyu bai kirata ba. Bakinsa yayi nauyi wajen fad’a mata kalaman soyayya amma kula kam in aka barta zata iyacewa mijinta yafi na kowa iya kula.
2
… ‘Kazafii… 18
©Ummu Abdoul
Sak’o ne ya shigo wayarta, kamar bazata daga ba don kallon da takeyi ya dauke rabin hankalinta.
“Mssww yanzu haka Mtn ne” Ta fadi tana mai daukan wayarta.
” I feel so lucky and loved when ever I think of u. In you I found every single happiness of my life. I will forever love and cherish you. Missing you so dearly”
Ta k’ara duba lamban sak’on ta ga dai tabbas ‘HAMMA’AM’ din ne rubuce. Ta karanta yafi a kirga sannan ta aje wayar, wani b’ari na zuciyarta na umartanta data maida masa da ko kalmar godiya ne amma saita basar. Sai ma ta tashi ta shiga kicin don daura musu abincin rana.
A bangaren Nasir kuwa zaune yake yana jiran ko zata amsa, kamfanin Mtn kamar sun san yana jiran sak’o sao turo masa da sakwanni sukeyi wanda duk ya shigo sai ya rok’i Allah yasa Sumayya ce.
“Angon sumayya tunanin me kakeyi har na shigo baka ji sallama ba?” Fadin Mahmud yana mai hura masa iska a fuska.
“Kai dai bro ayi sha’ani kawai, ban san sanda na fara son sumayya ba, duk kulawan da nake bata sam bata gani, dazu nayi mata (text) bata ko amsa ba kuma tagani” Ya karasa zancensa cikin yanayi mai nuni da damuwa.
“Toh kai ta lallabata dai, (don’t ever force her). Ni dama na zo ne in fad’a maka Salma (sunan matarsa) na da ciki, kusan wata uku(3).”
“Allah ya inganta Ya raba su lafiya, ni ko ta ina zan fara ma”
“Ta inda kowa ke farawa, shiyasa ban son d’ago zancenku baka jin shawara, aka auri karuwa dai kuma aka zauna da ita inaga wacce babu tabbas a iskancinta, shin ka taba sauke mata hakkinta kuwa?”
“Wallahi d’an uwa zantuttukan su zulai ke hana min komi, da na tuna sai raina ya baci”
“Wallahi Nasiru Allah sai ya tambaye ka, ita din katako ce, ni barni ma kaga tafiyata tunda zaluntar yar mutane kakeyi, Abba bai cancanci haka daga garemu ba dai” Yana kaiwa nan ya mike ya fita.
Tun daga ranar sakonni daban daban yake tura mata mai nuna tsantsan kauna, bata taba nuna ta gani ba don a cewanta kar ya sake mata abinda yayi kwanaki.
Yau tun da ya dawo yake nane da ita, duk inda tayi yana biye, tare sukai girkin dare wanda shi ya zab’a musu, pancake ne da cabbage source.
Bayan sun gama ci ya kwashi kwanikan ya kai kitchen ta biyo shi ya nuna sam shi zai wanke. Bayan sun gama suka zauna kallon labarun duniya sai ya shiga mammatse mata kafa wai yaga sun kumbura. Ganin zai takurata ta tashi tayi hanyar daki.
“Sai da safe” Ta fadi
“Allah bamu alkhairi, zan dauki littafin nan please.” Ya fada mata yana mai cigaba da kallo.
Bayan ya gama ya tashi yayi shirin barci sannan ya bita dakin.
*******************
“Allah miki albarka Sweety, nagode nagode da kika rike tarbiyyanki. Ki mun izini in kai shaidanki gida.”Abinda Hamma ke fadi kenan yana kuka. Kuka sumayya take sosai domin a daren komi ya dawo mata sabo, ta gode ma Allah da bata kasance cikin mata masu sai da mutuncinsu kafin aure ba.
Da safe shi ya musu komi na kari, ya gyara gidan kamar yanda ta saba. Wajen sha biyu ya gama komi ya kai mata wani ruwan tai wanka.
Da rana ma shi yayi musu girkin, ya roke ta gafaran abinda ya mata kwanaki yafi a k’irga, iyayenta sun sha addua sannan ita kanta tasha albarka.
Bayan sallan isha’i ya umarce ta da ta shirya su fita, basu tsaya ko ina ba sai kofar gidansu. Kallon sa tayi cikin sigan addu’a, murmushinsa mai tsada ya sakar mata tare da d’aga mata gira.
Cikin sanyin jiki ta bishi har cikin gidan
5
… ‘Kazafii… 19
©Ummu Abdoul
Tayi mamakin ganin kowannensu hatta Hamma Mahmud da matarsa Salma, wajen babanta ta nufa, ta haye kujeran da yake zaune na mutum biyu ( 2 seater) kwanto masa tayi sai kace kyanwa tasa wani sabon kuka, yana shafata yace
“Haba zaujatu Yaasir ummu ammar ke fa kika fara shahada a musulunci, oya (be strong) kamar takwararki, inshaAllahu kinci jarabawanki”
“Ahayye ai dama na fad’i aurennan baze kai ko ina ba, mai hali kuma.” Zulai ta fad’i yayinda take shigowa.
Babu wanda ya kula ta, ta zauna dogon kujera da yaranta a gefe. Sumayya de na dunk’ule ko fuskanta ta ki bari a gani sai ajiyar zuciya take.
Bayan bude taro da addua da Mahmud yayi, Sheikh ya kalli Nasir yace
“Alh ka tara mu nan muyi abinda ya kawo mu, photocopy din l indo na najin barci, ko summyn Nas.” Ya karasa cikin sigan tsokana, aiko gaba d’aya se da aka dara.
“Abba game da KAZAFIN da akai ma matata kuma kanwata ne, aka nemi b’ata ma Abba na suna shine nake neman izininka in shigar da k’ara”
“Kana da shaidar da zaka bayyana ma kotu ne da zaka shigar da k’ara?” Sheikh ya tambaya yana mai kara zama.
Zani ngado ya fitar ya ce “Abba ga sheda ta, na dad’e ina ‘kaurace ma Sumayya don gudun abin da zan iske, kalaman Zulai,Manniru sun hana ni aiwata komi har sai yanzu da Allah ya tashi wanke sumayya, Abba ni na fara saninta diya mace, ka gafarce ni Abba ban so nayi rashin kunya ba”.
“Hahhhhh ai da ba’asan asalin angulu ba se ace daga ijib(wai Egypt zata ce) ya fad’o, yo budurwai nawa ke fitar da jini yanzu da jini ze zame maka sheda” Zulai ta fad’i tana mai zazzare idanu, da ka ganta kasan tabbas a tsorace take.
“Ai tun daga likita ai se yai mana bayani ko Zulai” Sheikh ya karasa zancensa yana kallon Mahmud.
“Eh toh Abba tabbas hakan ne, yanayin abincin da ake ci yanzu da yake cike da (chemicals) da shekarun da mata kan dauka kafin suyi aure da kuma jinin al’ada, duk wannan kan sa mace ta rasa yanar budurci ko kuma ya kasance mai rauni hakan zai sa bazata fitar da jini ba. Amma duk da haka hanyar zata kasance a matse,akwai budurcin da yake ba na asali ba, walau tasha wasu abubuwa ko aiki a asibiti ko tayi tsarki da wani abun, tabbas zata matse amma hanyar ba zai taba matsewa ba, (hattara dai )
Na sumayya ko Allah zai iya taimakonta da Quwwansa da Qudiransa don ya wanke ta yasa tayi ambaliyan jini ma. Muna godiya muna kara gode masa”
“Kun ma raina ma kanku wayau, hala fim (film) kuke shooting” Zulai ta fad’i tana mai juya idanu.
“Abba in de Hamma ze shiga kotu akan rashin gaskiya Bismillah ni inada da shedu” fad’in Muhammad
“Wildun my boy (weldone my boy) fad’in Zulai tana dariya.
“Yanda ya fadi nasa shedan anan kuma dole ku kawo na ku nan, ni kuma zanyi anfani da usul in yanke hukunci”
Sumayya kallon Muhammad take cike da mamakinsa, “Wato har yanzu bai yarda da ita ba toh se yaushe”Shiru ya ratsa wajen har saida Sheikh ya gyara murya kafin Muhammad ya soma magana.
“Abba naso dai ya shigar da k’aran.”
“Babana in bazakayi bayani ba ka barshi.” Sheikh ya fadi cikin daure fuska
“Farko ina so mu fara da sauraron kallon hotunan nan kafin inyi duk wani jawabi.” Nan ya mik’a ma Shiekh hotuna wanda akai amfani dashi aka sauya sumayya, sai kuma wani guda da ya sauya fuskan macen zuwa wani fuskan.
“Ga kuma wannan bidiyon” Nan ya kunna, abinda aka hasko ne ya ba su Zulai tsoro kasancewar bata ga hotunan ba. Cirewa Muhammad yayi sannan ya sa wani, komi iri daya ne babu bambamci da wancan saidai fuskar yarinyar da aka chanza da na Sumayya.
“Ranar da abin ya faru, yanda naga duk kun rude ya bani mamaki, tabbas fuskan sumayya ne, amma gangan jikin ba nata bane, asali ma gangar jikin tafi ta sumayya duhu.
Ina ganin haka na cire cd din na adana nayi zamana, can naga gara na fara kwatanta aikina kafin in tsunduma ciki, na kama hanya naje dakin Zulai, ina yin kwana na jiyo muryan Manniru na cewa “Aikin Rolex yayi kyau, dama ya mutu mu huta”
“Ai ni nasan irin biyan da nai masa shiyasa bai kuskure ba” Fadin Mannira.
Na karasa na nuna ai ina tare dasu kawai, hakan yasa suka saki jiki dani.
Nayi ta binsu a hankali har na samu ganin Rolex.
Rolex mai aikin kwanfuta ne don kuwa yana cikin masu editing films. Yace min shekaru uku da suka wuce aikin da yakeyi kenan har yayi kud’i.
Yakan tara hotunan yan mata daga facebook da instagram kala kala, sai bidiyon batsa d’aya a maida shi kala daban daban yana samun kudi.
Nayi masa wa’azi sosai kafin ya fada min yanda yayi na sumayya. Raina ya baci amma na daure”
“Sharri zakai mana, wanene kuma Rolex?” Fadin Zulai tana zazzare idon.
Ciro karamar rediyo yayi ya kunna sai ga zantuttukan Zulai ke tashi.8
…. ‘Kazafiii… 21
©Ummu Abdoul
Maganganu dai babu dad’in saurare, duk wani shirinsu Zulai a bayyane suke, muryansu tiryan tiryan haka yayi ta tafiya.
Ihu Zulai tayi lokacin da maganar ta tsaya inda Muhammad ke fad’a musu su kwantar da hankalinsu ai suna dak shaidu,duk abinda za’ayi saidai ayi.
Tsam Sheikh ya tashi ya shiga d’aki. Ashar Zulai ke saki ita da su Mannira, fad’i suke “Sai mun wulakantaku, yan kazan kazan…”.
Ko da Shiekh ya shigo takarda ya bata, “Gashi nan dama igiya d’aya yayi saura tsakaninmu, kuma halinki ya tsinka shi, bazan kore ki ba amma kisani bazan dauki ko wace nau’in alfasha ba.”
“Ahayye toh sai me don ka sake ni? Ai ko minti d’aya bazan k’ara ba gidanka gara na kwana a titi da nayi kwanan shegiyar gidan nan” Fadin Zulai kenan tana mai girgiza jiki.
“Ku tashi kuje ku kwanta gobe da safe sai ku koma gidajenku” Abinda Sheikh ya fad’i kenan ya kama hanyar d’akinsa cikin tsananin fusata.
Tashi Sumayya tayi ta rungumi Muhammad tasa sabon kuka, fad’i take “Nagode kwarai bros. Bansan da wani baki zan gode maka ba.” Shafa bayanta kawai yayi ba tare da yayi magana ba.
Nan fa wani sabon hira ya b’arke tsakaninsu. Farinciki a zukatansu kuwa,ba’a cewa komai. “Hamma Muhammad amma ka iya basaja, kaga yanda kake wani basar damu wai kai d’an Zulai?” Fad’in Suwaida cikin sigar tsokana, gaba dayansu aka sa dariya. Basu suka kwanta ba sai wajejan karfe (3) bayan sunyi nafilfiloli sun gode ma Allah.5
Wannan kennan!!!!
******”********
Rooney (afuwan prev post nasa rolex typing error ne) zaune yake gaban na’ura mai kwakwalwa tun bayan fitan Muhammad daga shagon ya tsani kansa, “Inama zan ga ‘yanmatan da na kwashi hotunansu a facebook, nayi film din batsa (pornographic ko blue films) da su in neme su gafara. Na tara miliyoyin kudi ta site dina da saika biya kake shiga, yanzu meye hukuncin dukiya na?” Ya k’arasa zancensa yana mai zubar hawaye.
“Kaico na ni Ubaidullah, Ya Allah ka yafe min”
5
…. ‘Kazafii…22
©Ummu Abdoul
“Mimi ni wallahi sai nayi kud’i ko ta halin k’ak’a, zan yi kud’i sai nafi Bill gates da Steve Job. Zan fitar da nawa software din da sunanki, sannan zan bud’e (football club ) saboda son Rooney.” Matashin yaro da bai wuce shekara goma sha hudu (14) ba ke fad’i.
Zaune suke su hudu (4), babbansu mai suna Bilal bazai wuce shekara sha bakwai (17) ba,yana aji daya a jami’ar jihar bauchi.
Sai mabiyinsa da ke maganar dan shekara sha hudu (14) yana aji hud’u a makarantar sakandare. Sunansa Ubaidullah
Sai Khabab d’an shekara sha biyu (12) kuma yana aji biyu a sakandare,sannan auta Hindu ‘yar shekara 8, tana aji hudu (4) a firamare.
Mahaifiyarsu Dr Zahida da suke kira mimi, yar asalin jihar Kaduna ce , aure ya kawo ta Bauchi inda take auren Dr Sufyan. Sun hadu a jami’ar Ahmadu bello da ke Zaria.
Tana iya kokarinta wajen gina yaranta amma mijinta na rusa mata, shi baya tab’a b’oye son kudinsa kuma yana cusa ma yaransa ak’idan neman kud’i ko ta wani hali.
“Ubaidullah baka mayi tunanin yin aikin kwarai irin na takwaranka ba, sahabin Annabi SAW, sai wa’innan makamashin jahannama in basu tuba ba” Fad’in mahaifiyar cikin sanyin jiki.
Ta cigaba “Ka rok’i wadatar zuci my darlin se kaga kafi su daukaka duniya da lahira” Ta karasa tana mai rungumarsa.
“Kinga Heeda bana son kina b’ata ma yara na (future), akan me bazaki barsu suyi (living Soji life) ba, in ba kudi ta ya mutum zai nemi lahira, wannan ya zama na karshe, don (I must have d wealthiest sets of inlaws).” Ya kara gaba yana mai jan tsaki.
*************”*””
Tun daga ranar Ubaidullah ya daina daukan shawaran Miminshi don gani yake kwata kwata bata sonshi.
Yana gama aji shida ya shiga jamiar ATBU inda ya samu fannin na’ura mai kwakwalwa (computer science).
Suna aji hudu ya fara kokarin bude site din da zai samu kudi, nan wata kawarshi yar k’asar Japan ta bashi shawaran ya bude na batsa (pornographic) domin babu wanda ya kaishi samun kud’i.
Ta kara da bashi shawaran ya saka wasu software a kan kwanfutarsa wacce zata bashi damar sauya bidiyo d’aya ya zama goma.
Ba tare da bata lokaci ba yayi abinda aka ce, nan ya maida Facebook da instagram wajen zamanshi, yakan kwaso hotunan hausawa, yarbawa, turawa se ya sauya da fuskan masu aikata masha’ar.
Cikin watanni shida ya tara kudi fiye da miliyan goma na Dollar America, kud’insa ya girgiza Dr Zahida duk yanda taso taji silan kud’in yak’i fad’a mata amsarsa kullum (mimi am a computer scientist).
Mahaifinsa kuwa murna yake don yafi kowa cin moriyar kud’in.
***
A nan ina kira ga mata masu sakin hotunansu a social media domin labarin Ubaidullah na daya daga cikin True life part na labarin, saidai gayen ba’a Bauchi yake ba, kuma akwai dubunsa a duniyar nan.
Labarin sumayya ya faru da gaske, wani d’an sauyi dai kawai nayi gudun wadanda suka santa su d’ago ta. Wasu kuma siyar ma turawa hotunan suke, mutuncinki jarinki. Allah Ya kiyashemu,amin.Garin kwashe-kwashensa ya had’u da Mannira, kyawun ta ya daukar masa hankali ba shi ya samu nutsuwa ba har saida ya kaishi da kaita gadonshi.
Bayan ta fahimci yanda ya gwanance a harkan na’ura mai kwa-kwalwa, ne ta sako masa zancen Sumayya, ba tare da bata lokaci ba ya had’a faifan bidiyon amma zuciyarsa ta gagara amince masa da ya siyar da fuskan Sumayya a duniya.
Sati biyu bayan yayi aikin da Mannira ta sa shi, ya had’u da Muhammad. Had’uwan farko hankalinsa ya kwanta dashi yaji ai yasami aminin da ya dad’e yana mafarkin samu.
Cikin sati guda gaba d’aya ‘yan gidansu Roneey sun san Muhammad kuma nutsuwarsa yasa Dr Zahida ta amince dashi.
Muhammad bai tab’a kyamatarsa ba har ya samu ya gano duk abinda yake nema, abu d’aya yayi bai taba yarda sun had’u da Mannira ba.
Ranar da ya amshi fayafayen bidiyo da hotunan da ya harhad’a na Sumayya ya zaunar da Rooney yace
“Ubaidullah kana tunanin mutuwarka kuwa? Kana tunanin kwanciyar kabarin nan kuwa? Ina zaka kai dukiya fisabilillahi naga kana mutuwa da kyallen yadi ‘yar (#70) za’a kaika toh me zakayi da kud’i?”
“Kai amini kudi sune rayuwa.”
“A’a ni ba amininka bane, kana aikin ‘yan wuta ni kuma ina iya kokarin tsare kaina daga wuta, ina amintar mu anan?
Ni na gwammace nayi bara a duniya kai kuma kanason bara a kufai bara inda babu wanda zai jika” (Gaisuwa ga Aminu ALA, ni ba mai jin wakokinsa bace, ranar da naji BARA A KUFAI a napep nayi hawaye na k’aru a imani, ina maka da dukkanin musulmi fatan kariya daga bara a kufai)
Shiru Rooney yayi. Hakan yasa Muhammad ya cigaba
“Kasan hukuncin kallon films din batsa ko karatun batsa? Kamar fa zina ce da ido, kuma ranar lahira idanuwanka zasu bada shaidan abinda suka gani.
Kai baka tsaya a kallo ba,saika yad’a ma duniya kasan kuwa duk wanda ya kalla a sanadinka kana da zunubi kwatankwacin nasa. Haka zalika wanda yayi rubutun batsa.
Duk wannan bai ishe ka ba saika kwashi hotunan kannin mutane, ‘ya’yan mutane da iyayen mutane da basu ji basu gani ba ka na watsa ma duniya da sunan batsa, anji sunyi zunubin sanyawa a media kai kuma fa, ina zaka gansu ka nemi gafara, ina zaka kai zunuban nan?
Duk fa sai an maka hisabi dasu. Ina zaka gansu Rooney?
Kud’in da ka tara me zakace ma Allah a kansu, jiya Bank statement dinka ya nuna $9b ina zaka kai? Ta ya zaka fara shaidan sisi da sule a gaban Allah?
Zan tayaka neman gafaran Sumayya da Mannira ta baka kwangila duk da kun hana mata zaman aure cikin kwanciyar hankali. Na barka lafiya” yana kaiwa nan ya fice ya barshi.2
…. ‘Kazafiii… 24
©Ummu Abdoul
‘Dago fuskarsa yayi da ke jik’e da ruwan hawaye, na’urar da ke d’akin ya kunna, da yake gwani ne cikin mintuna ashirin ya gama had’a (virus), ya had’a ta da (site) dinsa akan mutum na shiga gaba d’aya wayar sa ko kwamfutarsa zata dauke kuma gyarata zaiyi wuya.
Jiki babu laka ya tashi ya gangara gidansu. Bai ga nisan hanyar ba, tafiya yake zantuttukan Muhammad na masa yawo a kwakwalwa, haka har ya isa gida.
A harabar gidan ya iske Miminsa ta rako baffansu zai fita.
“Rooney lafiya kake tafe a k’afa, multi billionaire bachelor da tafiya a ‘kafa. (You are not meant to suffer son)” Ya fad’i yana mai d’aure fuska.
Dr Zahida kam kallonsu take cikin halin tausayawa domin tausayinsu takeyi ganin yanda suka dauki rayuwa.
“Baffa gara na wahala yanzu da nayi ta ‘kiyama, baka taba tambayar silar arziki na ba, yau Muhammad ya taimaka min, banda aminin da yafi minshi” Ya fad’i yana mai fashewa da kuka sosai.
Fitan da baiyi ba kenan, zama sukai gaba d’aya ya maida musu abinda ya faru. Gaba d’aya iyayen sun girgiza da halin d’ansu. Nan take Baffansa yayi nadama don a cewarsa shi ya kaishi ga halaka.2
*************************
Rayuwa mai cike da ‘kaunar juna ke wanzuwa tsakanin Sumayya da Nasir. Ko minti biyar (5) kayi a gidan zaka fahimci soyayyar da ke tsakaninsu.
Wata uku bayan bayyanar gaskiyar, ciki ya bayyana a tare da Sumayya. Kula da soyayya sai abunda yayi gaba.
Watarana suna zaune a falo, cikinta na da wata bakwai, Hamma Nasir na mata tausa, ta na rike da madarar Habib da ya zame mata abinsha akayi sallama.
Wacce ta shigo bayan amsawar sallamar ce ta basu mamaki, Mannira ce jina jina da ita ta kod’e kamar wacce tayi jinya, tun bayan rabuwarsu basu k’ara sanyata a ido ba sai yau.
Bayan sun gaisa ta fara rok’onsu gafara tana mai zubar da hawaye a cewarta ta tuba su yafe mata.
Nan da nan zuciyar Sumayya ta amince da ita, ta ce “Haba Mannira akai ma Allah laifi Ya yafe balle kuma mutum? Ni godiya zan miki ma,da bakiyimin hakan ba yaushe Hamma’am zaiyi tunanin aurena? Kuma kinga ba macen da ta kaini dacen mijin aure.” Ta k’arasa tana sumbatar tsakiyar kansa.
Gimtse fuska ya sakeyi ya tashi ya wuce d’aki batare da ce ma Mannira komi ba
2
… ‘Kazafii… 25
© Ummu Abdoul
Binshi d’aki tayi ta rok’eshi tana mai nuna masa muhimmancin yafiya tsakanin al’ummar musulmi don Allah nason mai yafiya.
Saida Mannira tayi sati biyu (2) sannan ta koma da alk’awarin zata dawo bayan haihuwar Sumayya.
Cikin ikon Allah Sumayya ta haihu lafiya inda aka sami ‘ya mace, murna sosai ‘yan uwa da abokan arziki sukayi. Ranar suna yarinya taci suna Aisha inda ake ce mata Shireen.
Shireen nada shekara (3) Sumayya ta haifi Abdurrahman da suke kira da Sahal. Soyayya da gata babu wanda bata samu daga Hamma Nasir ba.
Ta kammala karatunta don kanta tace bata bu’katar aiki.
Tun bayan haihuwar Sahal take fama da 6ari, da ciki ya kai wata (4-5) zai zube, sunje asibiti likitanta da yake dubata tun haihuwar Shireen ya tabbatar da lafiyarta.
Kwananta goma da wani 6arin suna zaune sai ga kiran likita akan yana son ganinsu a asibiti. Ba tare da b’ata lokaci ba sika tafi. Sun iske shi zaune a ofis yana mai jiransu.
“Ka yafemin d’an uwa bazan iya cigaba da 6oye maka ba.” Likitan ya fad’i yana mai sheshek’a.
“Talk please Doctor!” Nasir ya fad’i cikin k’aguwa
“Wallahi zancen matarka da yaran nan ne” Yaja majina yana mai share hawaye da hankici
“Me ya same su?” Nasir ya fad’i cikin tsawa
“Ka yafemin, daman zan fad’a maka cikin nan da ke fita Madam da saurayinta ke zuwa a cire”
“What!!! Kana hauka ne?” Nasir ya fad’i yana mai cakumo wuyan rigarsa.
“Wallahi iyakar gaskiyar kenan ga ta nan ka tambayeta ko kuje a duba mahaifanta ya kusa samun matsala ma, ko yaran can ba cikinka bane.” Yana maganar fuskarsa na nuna hakikanin gaskiyarsa muraran.
Bai ce komi ba, yaja hannun Sumayya sai Hannu da Yawa clinic inda suka iske Gynea Rufaida. Batayi wata wata ba ta tura su inda ake hoto suka yo.
Ko da ta duba sakamakon rai a bace tace “Kuna da hankali kuwa take shan mugayen kwayoyin nan? Idan bakwa son haihuwa ga tsarin iyali kuyi mana. Yanzu dai dole kuyi hakuri kada komi ya shiga mahaifan har sai ta gama shan magungunan nan” Ta fad’i tana rubuta musu magunguna.
Sumayya hankalinta idan yayi dubu toh ya tashi,kuka takeyi kawai kamar wacce aka aikowa sak’on mutuwa. Nasir bai ko kallon inda take.2
Daga asibiti basu tsaya ko ina ba sai gidan Sheikh wanda yake auran, k’anwa take ga mahaifansu Nasir. Har garin D’ifa aka je aka d’aura aure, bazawara ce amma bata tab’a haihuwa ba, hakan yasa ta rungumi yaran a matsayin nata.
Bayan sun isa, Nasir yayi ma Sheikh bayanin abinda ya faru daga farko har karshe. Bud’ar bakinsa cewa yayi “Zata aikata fin haka, ku tashi ku bani wuri.”
Banda salati babu abunda Sumayya keyi,wai wannan wace irin rayuwa ce? Wannan ma wani sabon Kazafin ne ko kuwa dai? Ya Salam.
Tunda suka koma gida ya umarceta da zaman d’akin bak’i. Ya gagara sakinta don wani sashi na zuciyarsa ya kasa yarda. Sheikh ya hana sauran yaran daukan mataki akan abin.2
***** kuyi hkr zanyi a takaice domin zanyi tafiya ranar alhamis, zan so in kammala kafin nan.