KHAUSAR! CHAPTER 1
By Diamond Meenah
*All thanks to Allah S.W T for giving me the chance, priviledge and ability to write this novel, i dedicate this novel to my sweet siblings and our mum like no other, Allah ya bar min ku Ameen.*
*My special greating goes to my soul (my aboki na rayuwa) Allah ya kare ka, ya biya maka buƙatunka na alkhairi a duk inda kake.*
*I dedicated this page to Hafsat (Autar mam😍) alkhairin Allah ya kai miki har gadon baccinki, thanks for the care love, Allah ya kara Miki basira da daukaka tare da ɗunbin mabiya😍❤️*
*Ina mai sake baku hakuri fan’s sakamakon rashin karasa muku Fatima ko Zahra da banyi ba, kuyi hakuri ku kara hakuri, bani da baki da zan baku hakuri na sani, amma dai tabbas nasan zaku fahimce ni ƴan amanana😍 ku janye dukkan wani fushi da kuke dani, da zarran na samu abinda nake so kuma nake nema zaku jini insha Allah.🙏🏻🥰*
Page 1-2
Kwance ta ke kan makeken gadon a ɗan takure, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci bata jin daɗin baccin, sakamakon juye-juyen da ta ke yawan yi, tana sanye da sleeping gown wacce da kaɗan ta wuce cinyarta, rigan ta ɗan tattare sama, wanda hakan ya bayyana santala-santalan kuma fararen ƙafafuwanta, ta cure waje ɗaya kamar mai tsoron kar wani abu ya taɓa ta ko mai jin sanyi, yayin da dogon gashin kanta dake baje saman filo ya rufe mata kusan rabin fuskanta, net ɗin kanta tayi gefe da alama garin motsin da ta ke yawan yi ne yasa ta zame daga kanta, a hankali take sauke numfashi tare da ƙananun ajiyar zuciya tamkar yaron da ya ci kuka ya gode Allah kafin ya kwanta, kaɗan-kaɗan kuma ta ke ya mutsa cute face ɗinta, kallo ɗaya zakayi mata kayi tunanin idonta biyu sakamon abu-buwan da ta ke cikin baccin, sai dai kuma sam ba haka ba ne bacci ta ke haiƙan, kana kallonta zaka tabbatar da bata jin daɗin baccin ko kaɗan.
Da mugun ƙarfi aka turo ƙofar tamtar za’a karyata, wata ƴar matashiyar mata ce ta shigo ɗakin, wacce bazata wuce shekaru 37 a duniya ba, fara ce tas! kyakykyawa cikin shiga ta alfarma, kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa cikin hutu ta ke da jin daɗi, fuskarnan tata a murtuke babau alamar rahma bare afuwa ko sassaci akanta.
Wani irin mugun kallo ta watsawa yarinyar dake kwance cike da tsantsar tsana, wani irin kwafa tayi tana binta da harara ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin, kallonta tayi na kusan minti ɗaya kafin ta ɗauke kanta, a fusace ta ƙarasa inda ƙaramin fridge ɗin ɗakin ya ke.
Cike da masifa ta buɗe fridge ɗin kamar ana tunzurata, goran ruwa guda ɗaya ta ɗakko mai masifar sanyi, takowa tayi ta ƙaraso gaban gadon, batayi wata-wata ba ta ɓalle mufin goran, babu tausayi bare imani ta juyeshi a jikin yarinyar dake kwance.
A firgice ta farka jikinta na wani irin tsuma, numfashinta kamar zai ɗauke har wai shiɗewa ta ke, ta tashi zunbur ta miƙe a kan gadon tana rarraba ido, kana kallonta kasan ba baƙarin tsorata tayi ba, saboda yadda ta ke wani irin tsuma har lokacin.
Jujjuya ido ta fara yi, har ta sauke idonta kan matar dake tsaye a kanta, da wani irin tsalle ta diro daga kan gadon jikin na rawa, ta kame jikinta waje ɗaya sabida azabar sanyin da ta ke ji.
Wani irin mugun kallo matar ta watsa mata cike da tsana, cikin kakkausar murya ta fara magana, “Sannu uwata! naga alama raini ke son shiga tsakanina da ke munafuka, ƙarfe nawa da har kike kwance ishashshiya? Na ce ƙarfe nawa?.
Ta ƙare maganar cikin daka tsawa, jikinta naci gaba da ɓari hawaye masu zafi na zuba idonta, tuni zuciyarta tayi rauni ga wani zafi da ta ke mata ‘Abbu ya tafi kenan?’ ta tambayi kanta hawaye naci gaba da zuba, bata da mai bata amsar tambayar, hakan yasa kukanta ya tsananta rauni da tausayin rayuwarta ya baibayeta, ‘why Abbu bai mata sallama ya tafi bayan yasan duk duniya bata…’ tunaninta ne ya tsaya cak sakamakon shuren da matar ta kai mata da ƙarfata, wasu hawaye masu zafine suka sake zubowa daga idonta, wani gigitaccen tsawa matar ta sake mata, da yasata zabura tana maƙalewa jikin gadon makar zata shige cikinsa, ta ƙan-ƙame jikinta waje ɗaya.
“Ba da ke nake magana ba iyee? Ubanki ne zai miki aikin gidan da kika miƙe ƙafa kina bacci algunguma!”, jikinta na rawa lips ɗinta na wani irin karkarwa cikin shesheƙar kuka ta ce “kiyi haƙuri Momma bansan lokaci yayi haka…”, dakar mata baki tayi da bayan hannunta tana hararanta ta ce “dama ai bazaki san lokaci yayi ba, tunda mai ɗaure miki ƙugu yana gidan, c’mon kin fito kinmin abinda na ce ko saina kakkarya ƙashinki na zubar munafuka dangin mayu”.
Da sauri ta shiga goge hawayen dake idonta tana sheshsheƙa, cikim wani raunananniyar murya kana ji kasan dab ta ke da sake fashewa da wani kukan ta ce, “to…”, wani dogon tsaki Momma taja tana juyawa ta nufi ƙofa, sai da taje bakin ƙofan snnan ta juyo fuska a tamke ta ce, “ki ɓata min lokacin kuma, ki ga yadda zanyi gutsi-gutsi da namanki ƴar iskar yarinya”, tana kaiwa nan ta fice zuciyarta na tafasa.
Cikin sauri ta miƙe jin maganar Momma ta ƙarshe, dan tasan tas zata iya yin duk abinda ta faɗa, closet ɗinta ta nufa da ta ciro wani gown ɗin, ta cire jiƙaƙƙen na jikinta ta saka wanda ta ɗauko.
Wullar da wanda ta cire tayi nan ƙasa, duk abinda ta ke cikin sauri da rawan jiki ta ke yinsa, dan tasan idan ta ƙara koda minti ɗaya ne mai ƙwatarta a gidan nan sai Allah, ba tare da ta ɗaure godon gashinta dake baje ba, ta zura dogon hijab ta fice daga ɗakin kamar zata kife saboda sauri..
Momma na fita kai tsaye kitchen ta nufa, wata ƴar matashiyar mata ce tsaye tana aikace-aikace, cikin tafiyarta ta isa da gadara ta shiga kitchen ɗin, sake haɗe fuska tayi tana duban matar da batasan ma da zuwanta ba, “Fati ki ajiye aikin nan da kikeyi, sannan kije ki samu Mukhtar ki ce masa ya bar share-sharen nan yanzu!”.
Da sauri matar da ta kira da Fati ta juyo a ɗan tsorace dan bataji shigowarta ba ko kaɗan, cike da girmamawa tanayin ƙasa da kanta cikin sanyi ta ce “toh Hajiya”, sannan ta ajiye wuƙar da ke hannunta a sanyaye ta fita daga kitchen ɗin, kallo ɗaya zakayi mata ka tabbar ita ɗin mai sanyi ce, sam batayi kama da hausawa ba, tafi maka da larabawa ko irin sadaka yallan nan, kallo ɗaya zakayi mata kasan bata da wasu shekaru duk da yanayin wahalar da take ciki sai ka gane hakan.
Cike da mutuwar jiki ta fito daga kitchen ɗin tana girgiza kai, nan-da-nan ɓacin rai ya bayyana akan kyakykyawar fuskarta ta nufi ƙofar fita daga falon, yayin da Momma ta bita da harara zuciyarta na tafasa ta juya ta shiga wani ƙofa…!
Commend and share pls 😍
*Diamond Meenah*