KIBIYAR KADDARA CHAPTER A

 KIBIYAR KADDARA CHAPTER A

Had’a ido sukayi duk saida gabansu yafad’i  dasauri Amina tamik’e tsaye tare da murza idonta , shima kallonta yake cikin mamaki yana rufe idonsa yana bud’ewa domin ji yake kamar mafarkin da yasaba yi ne tabbas ko ba a fad’a mashiba ya san wannan itace wadda yake nema koda ta canza ba kamar da dayasantaba, tambayar kansa yake me yakawota nan ko gizo takemin k’ara murza idonsa yayi yaga dai itace a gaske,

Itama Amina kokwanto tashiga yi a ranta shin shine guy d’inta ko bashi bane? Cikin ranta tace ammah ai shi wancan d’an fashine kuma a katsina nabarshi kai it can’t be possible wannan bashi bane… maganar mummy ce takatse mata tunani tace ya dai Amina?

Dafe kanta tayi tak’irk’iro murmushi tace mummy am just feeling headache, cikin tausayawa tace ayyah sorry sannu nan kowa yayi mata sannu ammah banda fahad da yake ta faman tunani.

Mummy tace kuzo muje muyi lunch sai kisha magani nasan harda gaganiyar aikin da kikasha, my son kutaso.

Dakyar ya iya mik’ewa yanufi dining d’in nan fatima tayi serving d’in kowa shidai tura abincin kawai yake baisan dad’insa ba domin kwalwarsa duk a cunkushe take da tambayoyin da yarasa amsarsu ido yazuba ma Amina yana kallonta,

Itama a 6angarenta juya cokali kawai take a cikin abincin tana satar kallonsa a duk lokacin da tad’ago zata kallesa sai sun had’a ido  kan dole takoma kallonsa ta gefen ido, cikin ranta tace kai dole intambayi fatima  akan wannan d’an uwan nata chan kuma gefen zuciyanta tace mata shi da ba a nan k’asar yayi karatu ba kuma gashi d’an gayu ya ma za ayi ace ya ta6a fashi  me suka rasa a gidansu kuma ko a labari fatima ta ce mata basu ta6a zuwa katsinaba, dafe kanta tayi tare da kawar da tunanin domin tana ganin yana shirin rikita mata kwalwa mik’ewa take shirin yi kawai sai taga sun mik’e lokaci d’aya da fahad nan suka fara kallon kallo dasauri ita tazauna.

Daddy yakallesu yace ina zakuje Amina tayi karaf tace ba ko’ina daddy, fahad ya k’ak’aro murmushi tare da safar sumar kansa yace daddy na k’oshine inaso inje ind’an huta domin agajiye nake.

Mummy tace my son har yanzu kana nan da rashin son cin abinci ko?  A’a mummy zan ci Fatima takawo min a d’aki idan nahuta zan ci, toh shikenan my son ni gani nake duk ka bi ka wani canza fuskarkaka ta canza me yake damunka ne?

Murmushi yayi yace no mummy kar kidamu bakomai hutawa kawai nakeso ind’anyi, toh shikenan my son ahuta lafiya, kallon Amina yayi da taketa juya cokali a cikin plate sannan yakalli Fatima yace kikawo min abincina a d’aki in kingama, tace toh yayana zan cika umurninka, dariya aka sanya gaba d’aya Aunty khairat tace ina ruwan mai yaya kafin yafara hantararki, shidai wucewa yayi yanufi d’akinsa jiki ba k’wari.

Mummy kallon Amina tayi tace tun d’azu fa ina lura da ke ba cin abinci kikeba ko duk ciwon kan ne? Murmushi ta k’irk’iro tace mummy ina ci.

Oya toh yi maza kici sai kisha magani, toh mummy daganan kowa yacigaba da cin abincinsa.

Tunda yashiga d’akinsa bakin gado yazauna tare da dafe kansa yana tunani shin itace ko kuma watace? Toh wai ma in itace me zai kawota kaduna? Inma itace ita da take katsina? Tsoki yaja Jin tunani yana neman rikitashi yace ko wa zai ban amsar wannan tambayoyin? Dasauri yace yauwa Fatima ce ba kowa ba murmushi yayi sannan yajawo waya yakira fatima bugu d’aya tad’auka tare da sallama amsa mata yayi yace idan kin gama kisameni a room d’ina.

Toh yaya da fatan dai lafiya ko?

No lafiya lau saidai kinzo bai jira jin me xataceba yakashe wayar.

Jin ana Kiran sallar azahar yasa yatashi tafad’a toilet yad’auro alwallah sannan yafito suka nufi masallaci tare da daddy.

Tunda Amina tak’ar6i magani wajen mummy takoma d’akinta zagaye d’akin tashiga yi tana tunani tace tabbas wannan bashi bane ammah suna kama sosai saidai wannan ya fi wanchan kyau da gayu da fari kuma wanchan batasan sunansaba, jin tunanin yana neman rikata mata k’walwa yasa tafad’a toilet tad’auro alwallah tazo tagabatar da sallah.

Ko da yagama sallah bai tsaya gaisawa da kowaba yabaro daddy yayi tafowarsa gida, d”akinsa yakoma yafad’a saman gado yakwanta bai dad’e da dawowaba sai ga salma ta shigo da sallamarta hannunta d’auke da tray d’in kayan abinci nik’i-nik’i tana tafiya tana karairaya ko inda take bai kallaba ajewa tayi gabansa tace yaya fahad ga abincin nan, batare da ya kalletaba yace kin iya tafiya idan kin aje,

Ta ji haushin yadda yabata amsa ammah ya ta iya dole tajuya zata tafi yace am idan kinje kituro min fatima, toh tace sannan tafita.

Fatima ce tashigo da sallama ya amsa mata batare da ya kalletaba sannan yatashi yazauna gefen gadon kusa da shi yanuna mata itama tazauna tare da maida hankalinta garesa domin jin kiran me yake mata.

Murmushi yayi mata yace ya karatun kina dai maida hankali sosai ko? Eh yaya sosai ma, toh Allah yataimaka

Ameen yayana.

Yauwa wanchan wacece wadda nagani d’azun naga ban santaba ko a cikin family d’inmu, murmushi fatima tayi tace oh Amina? Sai da gabansa yafad’i domin zai iya tunawa tabbas shine sunanta da mahaifinta yakirata da shi lokacin da sukaje gidan a’a Amina bana son su cutarmin da ke ni nayi masu laifi kaina yakamata su d’au fansa, kalaman ne suka shiga yi mai yawo a kwalwa dogon numfashi yaja sannan yace wane gari take? Me taxo yi gidan nan? Miye alak’armu da ita?

Tambayoyinsa sunba fatima mamaki domin a yadda tasan yayan nata babu ruwansa da abunda bai shafesa ba ammah yau sai gashi yana tambaya akan abinda bai shafesaba murmushi tayi a karo na biyu tace yaya garin katsina take,

Me tazo yi mu da bamuda kowa a katsina? Yaya kasaurareni mana infad’a maka komai.

Numfashi yaja yace ina saurarenki fatima,

Amina ‘yar garin katsina ce iyayenta sun rasu ta ta6a aure ta dalilin rabuwarta da mijinta yasa tabaro garin……. nan takwashe komai akan labarin da Amina tabasu tafad’a mashi.

Tashin hankaline k”arara yabayyana a fuskar fahad nan da nan kamanninsa suka sauya cikin ransa yace ta ta6a aure har da d’iyarta shin ko ba ita bace noo wannan itace anya zancen gaskiya tafad’a masu? Toh in irace me yarabota da iyayenta ko bayan rabuwarmu suka rasu? Tabbas amsata tana wajen yarinyar chan,

Maganar fatima ce takatseta yace yaya fahad ya naga duk ka canza? Me yake faruwane? Murmushi ya k’ak’aro yayi mata yace yarinyarce taban tausayi gaskiya mijinta baida kirki da har ya iya rabuwa da marainiya, kwallah tacika idon fatima tace wlh yaya na ji haushinsa ga Amina babu ruwanta tana da kirki sosai domin duk zaman da mukayi da ita ko da sau d’aya babu wanda yata6a kuka da ita daga gani laifin mijin ne, yace gaskiya da alama, Allah dai yakyauta, zubamin abinci inci Toh yaya.

Bayan ta zuba mashi yace tana iya tafiya, dakyar yaci kwatan abincin sannan yatattara kwanukan dakansa yafito yanufi kitchen ko da yafito yayi sa’a ba kowa tsakar gidan  duk suna d’aki , kwanukan ya aje a kitchen sannan yafito yanufi d’akin Amina da sallama yashiga sannan yamaida yakulle k’ofar jin bata amsaba yasa yafad’a d’akin kwance yahangota saman gado kanta yana kallon cillin duk gashinta a baje yake da alama ta yi nisa cikin tunanin da take………..

Da alama ta yi nisa a tunanin da take batasan shigowarsa matsawa yayi daf da ita yana k’are mata kallo tabbas itace domin kamanninta basu canzaba ko da a yanzu ta fi da kyau ba zai mance da kamanninta ba gyaran murya yayi, firgit tayi ta tashi zaune saida gabanta yafad’i ganinsa a tsaye bakin gadon ya tsareta da manyan idanuwansa itama tashi tayi tsaye tace malam lafiya me yakawoka d’akina?

yamutsa fuska yayi yace ke zan tambaya me yakawoki gidanmu? harararsa tayi tace ban saniba,

d’aga kafad’a yayi yace ohk tafowa yayi kamar zai wuce kawai sai taji ya jawota tafad’o jikinsa yace Amina na san kece kuma kin san komai kifad’a min gaskiya,.

gabantane yafad’i tace ni kasakeni ban san komai ba wai me kake nufi?

hmm kin san abinda nake nufi idan kuma mancewa kikayi tohm bari intuna miki jawota yayi yak’ara matseta a jikinsa duk yadda taso taturesa ammah ta kasa, hannunsa taga yana shirin tura mata cikin riga zaro ido tayi tace wai fahad meye haka kake shirin yi ba na son iskanci.

had’e fuskarsu yayi waje guda yana murmushi yace na ga kin mance shine nake son tuna miki, turesa takeson yi ammah ta kasa hawayene suka shiga kwarara daga idonta tace fahad kasakeni daman kaine kacutar da rayuwa ta? wlh sai Allah ya sakamin duk wani hali da nashiga ta dalilinkane kaine sila.

runtse idonsa yayi cikin takaici yace Amina kar kikamani da laifin da ba nawaba Web *k’addara ce* kawai, d’aga murya tayi cikin kuka tace k’addara ce fa kace? k’addara ce tasa ka6atamin rayuwa fahad? mutane suna min kallon ‘yar iska? ni karabu da ni kasakeni ko yanzu inyi maka ihu.

sakinta yayi yace kiyi hak’uri Amina, harararsa tayi dan duk haushinsa takeji yanzu, yace kizauna inbaki labarin komai wlh ba laifina bane,

cikin d’aga murya tana kuka tace toh laifin wanene? please kafitar min daga d’aki bana buk’atar jin komai daga gareka fadawa tayi saman gado tare da fashewa da sabon kuka mai ban tausayi.

gefenta yazauna tare da dafe Kansa, sunyi kusan minti biyar a haka sannan yad’ago idanuwansa da suka canza kala suka koma launin ja yace Amina kitashi ki sauraran please inaso inwanke zargin da kike min

cikin kuka tace babu abinda zan saurara katashi kafitar min daga d’aki kar su mummy suzo suganka. cikin d’aga murya yace sai me dan sun zo? ai ni nafi son suzo Susan komai

da sauri tatashi zaune tace dan Allah kar kabari susan wannan maganar, ba tare da yakalletaba yamik’e tsaye yace idan har kika saurareni kuma kika fad’amin gaskiya toh shikenan ba wanda zai san maganar nan

gyara zamanta tayi ta share hawayen fuskarta tamaida hankalinta gareshi domin jin abinda zai fad’a mata domin a yanzu ba ta son abinda zai rabata da su mummy dan ji take kamar sune iyayenta idan tarabu dasu batasan hannun wad’anda zata fad’a ba.

STORY CONTINUES BELOW

bakin side bed yazauna yana fuskantarta yace kamar yadda kika sani sunana fahad umar kuma haifaffen nan garin kd ne…….. nan yakwashe komai yafad’a mata har labarin dalilin barinsa gida da haduwar sa da su ogah kai har dawowarsa gida da zuwan da yayi nemanta babu wanda ya6oye mata.

Amina ta tausaya masa sosai har da kukanta tana jin sonsa yana k’ara shiga a ranta ammah tadanne bata nuna mashiba dan batasan ko shi ba sonta yakeba.

Murmurshi yayi wanda bai kai zuciba yace kin ji labarina Amina wlh duk abinda yafaru ba da son raina hakan yafaruba domin inkare maku mutuncinku ne ke da iyayenki dan Allah kiyi hak’uri kiyafemin.

Runtse idonta Amina tayi hawaye suna zuba tabbas itama ta san fahad ya taimakesu a lokacin, muryarsa yana cewa Amina inaso kibani labarinki dan Allah dagaske ne wai kinyi aure? Kuma Ameerah d’iyarki ce?

Bud’e ido tayi takallesa tare da wurga masa harara tace eh na yi aure Ameerah d’iyar mijina ce? Dasauri yamik’e tsaye yace what!!! Da aurena kikayi aure Amina??

Kallonsa tayi a wulak’ance tace ni babu wani aurenka a kaina kar kamance *k’addara ce* kawai tahad’ani da kai Kuma mun rabu toh me zai hana inyi aure,

Ke! Bakida hankali?  A lokacin ai ban sakekiba aure kan aure kikayi? Ta tsorata da tsawar da yayi mata ammah tadake tace wannan ai auren wucen gadine mukayi da kai, mugun kallo yawurga mata  yace ammah ai ban sakekiba Kuma kar kimance har sadaki nabayar kuma and’aura mana aure.

Jikin Amina duk yayi sanyi tabbas bata ta6a tunanin hakan ba duk iliminta ammah ta mance da hakan sai a yanzu toh ya hakan ta kasance duk rayuwar da tayi daman da aure akanta? Maganar abbah ce tafad’o mata a rai lokacin da yace Amina ga sadakinki da aka baki, cikin kuka tace abbah bana sonsa banson auren, kiyi hak’uri mamana aure dai ya d’auru nima ba a son raina ba ammah kiyi addu”ar sake ganinsa domin amaida mashi sadakinsa kuma yasakeki nima banason d’an fashi yakasance mijinki mamana burina ki auri mutumin kirki, kikwantar da hankalinki kinji ko? Share hawayenta tayi tace toh abbah, yauwa mamana Allah yayi maki albarka….

Maganarsa ce takatse mata tunani yace kifad’a min gaskiya Amina da auren nawa kika auri wani?? Shuru tayi takyalesa hawaye suna zuba daga idonta.

Matsowa yayi daf da ita tare da rik’o hannunta cikin d’aga murya yace ina saurarenki kibani amsa nace miki.

Fusge hannunta tayi itama cikin d’aga murya tace idan nak’i fa ? Me zaka iya yi? Murmurshin takaici yayi tare da jawota tafad’o jikinsa kallon tsakiyar kwayar idonta yayi saida ta tsorata ganin yadda ida nuwansa suka rine  yace zan d’au mataki kuma dole kowa yasan labarin nan.

Jin ya ce kowa zai san labarin yasa hankalinta yak’ara tashi domin batason su mummy suyi mata kallon mak’aryaciya kuma mazinaciya, kwace jikinta tayi tace ni kasakeni, gaba tawuce tajuya masa baya hawaye suna ta kwaranya daga idonta ba tare da ta kallesaba tace idan ka shirya da anjima kadawo inbaka labarina,

Ni yanzu nakeso kibani.

Cikin kuka tace ba kaji ana kiran sallah?  Numfashi yaja yace ohk shikenan idan nadawo masallaci kishirya zan zo.

Zaro ido tayi tare da juyowa takallesa tace no kar kazo kabari bayan sallar magrib muhad’u a guarding area  sai muyi Maganar a chan.

‘Dage kafad’a yayi tare da ta6e baki yace ohk shikenan Allah yakaimu bai jira jin me zata ce ba yabud’e d’akin yaficce.

Saman gado Amina tafad’a tare da fashewa da sabon kuka tana jin sonsa yana k’aruwa a ranta dafe k’irjinta tayi jin yadda zuciyarta take bugawa tare da lumshe ido tayi kusan minti goma a kwance ga ciwon kai da yake matsa mata sauk’inta ma tana fashin sallah, ko da Ameerah tashigo ganin zata dameta yasa takorata har da d’an dukanta tayi saboda ta d’aukar mata waya ta yarda a k’asa da kuka Ameerah tafita daga d’akin.

Bayan sun idar da sallah duk yadda fahad yaso yagudu gida ammah ina daddy yatsaida shi saida yagama gaisawa da mutane sannan suka tafo gida tare, hanyar d’akinsa yanufa daddy yace kazo muje ciki mana ba dan ya so ba yabi daddy suka shiga gidan a parlour suka tadda su mummy zaune suna hira dan da suka gama sallah nan sukazo suka yada zango nan su ma suka zauna,

Ameerah ce tashigo dagudu tana kuka tanufo jikinsa, d’aukarta yayi yana dariya yace sarkin rigima wa kuma yata6a ki? K’ofa tanuna mashi cikin gwaranci tace momo she, dariya salma tayi tace yaya wai tana nufin mummy ce,

Dariya duk su Aunty khairat sukayi sukace ina ruwan Ameerah da gwaranci. Wai ni Amina shuru maimakon tafito ayi hira ammah sai tak’unshe d’aki,

Fatima tace wlh Aunty khairat haka Amina take ko ma ta fito ba k’asafai take magana ba miskilanci gareta. Mummy tace ai ko ba zatayi magana ba zama cikin mutane ai yana da dad’i kije kikarata.

Ko da Fatima tashiga d’akin kwance tataddata murmushi tayi tace manyan mata ana ta hutawa, murmushi kawai Amina tayi batare da ta ce komai ba,

Fatima tace wai me d’iyata tayi miki kika doketa?  Dakyar Amina tabud’e idonta da suka canza kala murmushi tayi a karo na biyu tace wlh ba ta jine ta shigo ta taddani a kwance shine take ta hawana ganin ban kula taba sai tad’auki wayana tayarda a k’asa nikuma sai na korata waje shine tafita tana kuka.

Dariya fatima tayi tace kin dai duketa zaki ce yanzu dai kitaso muje parlour ana can anhad’u ana ta hira kekuma kina nan, a’ah fatima kije kawai na gajine so nake in d’an huta, harararta fatima tayi cikin wasa tace wlh mummy ce tace inkiraki inkuma baki zuwa inkoma infad’a mata ince kince baki zuwa ,

Dasauri Amina tatashi tare da jawo hijab tasanya tace na san halinki fatima k’aramin aikinkine kifad’a mata hakan, dariya fatima tayi tace dagudu ma wannan hijab d’in da kika sanya fa sai kace wata matar liman, daman bakisan ita bace? Ai naga alamar hakan ni dai kizo mute kar ajimu shuru.

Fatima tana gaba Amina tana biye da ita a baya har suka shiga parlourn cikin siririyar muryarta tayi sallama tunda tashigo yakafeta da manyan idanuwansa waje tasamu gefen aunty khairat tazauna………..

Kallonta mummy tayi tace Amina ko ciwon kan ne ya6oyeki? Murmishi tayi tace mummy ai na ji sauk’i, toh Allah yak’ara sauk’i, gaba d’ayansu sukace Ameen.

Ameerah ce tata6o fahad da yake ta kallon Amina sun6uro baki tayi tata6e fuska kamar zatayi kuka tace kalamamin dukan da momo tayimin, lakuce hancinta yayi yana murmushi yace toh zan rama miki kinji ko my angel kar kiyi kuka.

Dariya su mummy sukayi, Aunty khairat tace Ameerah k’arar mummy aka kawo kenan, toh ke mummy meyasa kika doketa , murmushi Amina tayi tare da sunne kai k’asa tace Aunty khairat kin dai san halin Ameerah wlh ba ta ji,

Toh ya za ayi yaran ne sai hak’uri

Hakane, satar kallon fahad tayi taga wasa kawai yake da Ameerah kamar bai ma san maganar da sukeba ta6e baki tayi tace ka ji dashi.

Daddy ne yace fatima kunna mana news mukalla dasauri fatima tatashi tace toh daddy, murmushi mummy tayi tace kallo zamuyi kenan Alhaji,

Toh me zamu jira ai k’ara musan halin da duniya take ciki,

Hakane kuma, kallon salma mummy tayi da take ta dannar waya tace salma je kid’auko mana kunun ayan da Amina tayi d’azun kitafo mana da cups, aje wayar salma tayi tace toh mummy angama.

Fahad yakalli fatima yace muga wayarki my lil tashi tayi takai masa bai dad’eba yamaida mata.

Salma bata dad’e da fitaba tadawo da jug biyu da cups saman tray ta aje sannan tazuba ma kowa tabi kowa tabashi koda tazo kan fahad ahankali tace yaya fahad ga shi, ko kallon inda take baiyi ba, cikin shagwa6a tace yaya fahad please kakar6a, a gadarance yace kin iya ajewa ai,

Aje masa tayi takoma tad’auki nata sannan takoma mazauninta kusa da shi tazauna ta ji haushin yadda yayi mata ammah sai tayi hamdala da ba wanda yakula da dizgin da yayi mata ,

Ita dai Amina tana kallonsu ta gefen ido, ahankali taga ya jawo cup d’in ya kai bakinsa, yana kur6a taga ya lumshe ido ko ba a fad’aba ansan ya ji dad’in kunun ayan,

Murmushin jin dad’i tayi  a ranta taji sanyi, itama tad’auki nata tafara sha, d’akin yad’auki shuru kallo kawai ake gwanin sha’awa itadai Amina sai satar kallon fahad take yana burgeta domin komai nasa cikin aji yake yinsa, tana lura da salma itama da taketa satar kallonsa duk haushinta da kishi suka kama Amina domin gani take kamar salma itama sonsa take,

Ahankali ake d’an ta6a hira ganin lokacin magrib ya gabato yasa daddy yace akashe kallon kowa yaje yayi shirin sallah dukkansu suka amsa da toh tare da mik’ewa tsaye kowa yanufi d’akinsa .

Bayan sun idar da sallah direct fahad guarding yanufa domin amatse yake yaji labarin Amina saman d’aya daga cikin plastic chair yaxauna yana jiranta.

STORY CONTINUES BELOW

Kasancewar bata sallah zaune take saman gadonta tana azkar wayanta ce taji tana ruri janyo wayar tayi ganin number ce ke kiranta ba suna yasa taji kamar kar tad’auka aje wayar tayi har saida takusan tsinkewa sannan tad’auka tare da yin sallama,

Daga d’ayan 6angaren wata murya mai dad’i taji ta amsa mata ji tayi ance ina fa jiranki na baki 5 minutes inkuma ba hakaba yanzu inzo d’akinki batare da tayi magana ba taji ankashe wayar.

Ko ba a fad’a ba tagane wanene tsoki taja tace wannan mutumin yana son takuramin sharewa tayi tacigaba da abinda take tunowa tayi da ya ce in bata zoba toh yana nan tafe dasauri tatashi tajawo hijab d’inta dan ta san halinsa he has no fear for d out come.

Tun daga nesa tahangosa a zaune yana ta dannar wayansa sallama tayi masa, batare da yad’ago ya kalletaba ya amsa mata, kujerar da take facing d’in tashi tajawo tazauna ahankali yad’ago yakalleta dariya taso tabashi ganin yadda tayi kicin-kicin da fuska, murmushi yayi bai tanka mataba yacigaba da dannar wayansa,

Haushi Amina taji ganin yadda yayi kamar bai san da zamantaba, batare da ya kalletaba yace idan kin shirya ina saurarenki, itama d’auke kanta tayi gefe tace banga alamun hakan ba daga gareka, murmushi yayi yace ohk ai kunne yakeji,

Nikuma idan ba zaka aje wayar ba sai infasa, kallonta yayi yace ina saurarenki kuma ina so duk abunda zaki fad’amin kifad’i gaskiya kar kimin k’arya.

Harararsa tayi sannan tacigaba kamar yadda kasani kokuma bana tunanin ka san hakan sunana Amina Ahmad haifaffar k’aramar hukumar mashi dake cikin garin katsina mahaifina d’an kasuwane, mahaifiyata ta rasu tun ina k’arama daganan rik’ona yadawo hannun kishiyar mahaifiyata………………… nan takwashe komai tafad’a mashi bata 6oye mashiba har zuwanta gidan hajiya maimuna da dalilin dayasa tabaro gidan, da dalilin da yasa ta6oye ma su daddy gaskiyar labarinta domin kar suma su kyamaceta su gujeta domin ba kowa takega zai yadda da maganartaba,

Cikin sheshek’ar kuka tace ka ji gaskiyar labarina tabbas Ameerah d’iyarka ce wlh ban ta6a aureba kuma ban ta6a zina ba, hankalin fahad in yayi dubu toh ya tashi kwalwarsa nema tayi tarikice masa saida yakusan firgicewa jin Ameerah d’iyarsa ce innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai yake nanatawa dafe kansa yayi yace wannan wace irin *K’addara ce* nikuma tawa kalar k’addarar kenan, Amina kuka kawai take a tsorace take domin kar yak’i kar6ar Ameerah a matsayin d’iyarsa domin batasan yadda zatayi ba idan bai yarda ba,

A k’asan zuciyarsa yana jin tausayin Amina sosai musamman ma da yaji tarihin rayuwarta da gwagwarmayar da tasha,

Ahankali yad’ago idanuwansa da suka k’arance saboda tashin hankalin da yashiga yasafkesu akan Amina da take kuka ammah ta tsaresa da ido dakyar ya iya tattaro nutsuwarsa cikin tashin hankali yace Amina *k’addara ce* da rabo suka had’ani da ke na amshi wannan kyautar da Allah yayi min na san jarabtace daman Allah yana jarabtar bawansa domin yaga k’arfin imaninsa ni da ke gaba d’aya ya kamata mucinye wannan jarabawar kikwantar da hankalinki na yi miki alk’awali zan baku kulawa daidai gwalgwado  ba zan cutar da ku ba zan kula dake kamar yadda Abbanki yakula dake na san ta dalilina duk kika shiga wannan matsalar dan haka insha Allahu ba zan barki kik’ara kuka ba zan baku kulawa bakin gwargwado

Cikin kuka Amina tace nagode fahad tabbas kacika musulmi da har kayarda da k’addara kuma ka amshi Ameerah a matsayin d’iyarka batare da ka yi jayayyaba, murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace Amina kenan wa ye zaiyi jayayya da ikon Allah wlh tunda nad’aura idona akan Ameerah naji tashiga raina sosai ashe jinana ce kar ki damu Ameerah zata samu kulawar da bata samuba ta mahaifi yanzu zan bata ita kamar yadda kowace d’iya mai gata take samu wajen iyayenta.

Dariyar jin dad’i Amina tayi cikin kuka, hankalinta a tashe tace fahad dan Allah kar kabari su mummy susan wannan maganar ina tsoron yadda zasu d’au maganar,

Murmushi yayi yace kar kidamu su mummyna basu da matsala zasu fahimcemu, a’a fahad dan Allah kar kabari susani dan Allah inaso kayi min taimako d’aya,

Wane kalar taimako ne kifad’a zan miki, please ina so ka sauwak’e min aurena da ke kanka, cikin tashin hankali yakalleta yace kinsan me kike fad’a Amina kina da hankali? Share hawayen fuskarta tayi tace na sani fahad cewa nayi kasakeni domin inason wannan maganar tazama sirri a tsakaninmu,

Toh d’iyarmu fa?

Kayi hak’uri kabarta wajena ni zan cigaba kula da ita,

Saboda baki sona ko?

A’A ba haka bane fahad baka dace dani ba kafi k’arfina kasamu daidai da kai ka aura kaduba kaga karamcin da su mummy sukayi min bai daceba ace naso d’ansu,

Amina wannan ba hujja bace,

Runtse idonta tayi tana kuka tace fahad ba zaka fahimta ba,

Shuru sukayi na kusan minti biyar fahad ji yake kamar ta soka mashi kibiya a mak’ogwaro damuwace k’arara a fuskarsa kogin tunani yafad’a kallonsa Amina kawai take domin jin amsar da zai bata, murmushi taga yayi har saida gabanta yafad’i ko da ita tanemi surabu ammah dan ba yarda ta iya batasan yadda su mummy zasu d’au maganar ba tana tsoron su rabu da ita ga karatun da ta kwallafa ma ranta ta samu tana yi ta san shima zai iya watsewa.

‘Dagowa yayi yakalleta yace na ji na amince da maganarki gabantane yacigaba da fad’uwa nan sabbin hawaye suka cigaba da zarya a kumatunta,

Ammah da sharad’i d’aya

dakyar tahad’e wani miyau da yatsaya mata ne tasamu tahad’e tace wane kalar sharad’i?

Tasowa yayi cikin tafiyarsa ta k’asaita yazo gabanta yatsaya yace sharad’in shine ba zan rabu da ke ba sai nan da wata shidda kuma dole kidinga min biyayya idan kuma kika k’i toh ba zan sakekiba.

Cikin tashin hankali tace wata shidda fa kace dan Allah karage,

‘Daga kafad’a yayi yace haka naza6a inkuma bai mikiba toh dole su mummy susan komai,

Dasauri tace wlh ya yi min dan Allah kar kabari su mummy su sani.

Murmushin samun nasara yayi yace toh shikenan tashi kishiga gida kar afito a ganki, Dasauri tashare hawayenta tatashi tanufi cikin gida,

Binta yayi da kallo har tashige murmushi yayi cikin ransa yace lallai yarinta daban ce, wucewa yayi shima yanufi masallaci saboda kiran sallar isha da yaji ana yi.

_*WAIWAYE ADON TAFIYA*_

___________________

Ummah tunda Amina tabar gidan  hankalinta yakwanta daman burinta kar Amina tasamu gado a cikin abinda alhaji yabari, duk wani abu da tasan Alhaji yana da shi a hannun mutane saida tabi takar6o,

Duk wanda yatambayeta Amina cewa take ai ta shiga yawon duniya ta ce karuwanci ya fiye mata daman chan tayo cikin shege har tahaife d’iyar, ummah nan take zama takimtsa ma mutane maganar k’arya akan Amina har da kukanta wai ta hana Amina tafiya shine Amina taci mutuncinta ta zazzageta tatafi,

Mutane dayawa sun yarda ammah ita dai gwaggo ladi kallon ummah kawai take dan ta san halinta sarai,  addu’a kawai take Allah yabayyana Amina a duk inda take, tayi neman har ta gaji ammah babu Amina babu dalilinta kan dole tahak’ura tacigaba da addu’ar Allah yabayyana ta

Ummah facaka kawai take da kud’in yar uwarta suwaiba mai zugata tun Alhaji na da rai tana yadda taga dama a k’arshe gidan tadawo suna ta cin karensu babu babbaka,

Bayan wata shidda ummah tafara cinikin wani company na had’a takalma Bayan sun gama ciniki sukasa ta tatura masu kud’in duk wani abu da tamallaka saida ta saida tahad’a da kud’in dasuke banki, bata tsira da komai ba sai gidan da take ciki da naira dubu hamsin ko da tatura masu kud’in ashe ‘yan 419 ne nan suka bata takardun k’arya,

daga ranar bata k’ara ganinsu ko Jin labarinsu ba, ko da taje companyn nan tasamu labari wajen ma aikatan company banasu bane har wajen shugaban mai companyn aka kaita duk yadda takwatanta masu mutanen ammah ba wanda yaganesu ko ta kira wayarsu bata shiga takardun ma aka shaida mata ba na companyn bane aka bata, nan hankalinta yatashi a k’arshe zubewa tayi nan aka kwasheta aka kai asibiti nan ake shaida ma ‘yar uwartata paralyse ne yakamata a 6arin jikinta na dama,

A k’arshe gida suka dawo aka cigaba da jinyarta………..

Ummah bata iya komai saidai akwantar atayar kullum bata da aiki sai kuka da nadamar abinda ta aikata tabbas ta san ta zalunci mijinta da matarsa a lokacin da suna da rai kafin sutafi subar duniyar ko alkalin Amina aka barta dashi itama ta san ba zata kai labari ba tabbas ta san alhakine yake bibiyarta domin Allah ba azzalumin bawansa bane duk abinda mutum yashuka shi zai girba, tabbas ta san *k’addara ce* kawai tahad’ata da mutanen nan har suka damfareta ammah babu yadda ta iya tunda har da hak’k’in marainiya taci, a duk lokacin da tafara tuno rayuwar da tayi a baya hankalinta tashi yake tana nadama tana cewa ina ma taga Amina ko ta nemi gafararta domin tasan ta cutar da marainiyar Allah ayanzu ta yi nadamar abunda ta aikata tabbas ta san Allah ba azzalumin bawansa bane, danginta ne suke samu suna lalla6ata a duk lokacin da tashiga kogon tunani irin haka domin yanzu jininta ya hau sosai, ummah duk ta rame ta yi bak’i idan ka santa a da kaganta yanzu ba zaka ta6a cewa ita bace, rayuwa kenan mai juyi-juyi kar kazalunci wani domin bakasan yadda k’arshenka zai kasanceba, kar mu mance Allah dakansa ya hana zalunci, kar ka cutar da bawan Allah domin bakasan matsayinsaba a wajen ubangijinmu Allah yasa mudace.

_______________________

A 6angaren hajiya maimuna tunda Amina tabar gidan babu wanda yasan da tafiyarta sai lokacin da za suyi bacci babah salame taji shurun ya yi yawa domin Amina ba ta kai har tsawon wannan lokacin batare da ta fitoba kuma abinda yak”ara bata mamaki rashin jin kukan Ameerah,

‘Dakin Amina tabud’e tashiga hankalintane yatashi ganin ba kayansu Amina saida tabincike d’akin tas ammah bataga 6ar6ashinsuba nan babah salame tafara ta6a hannu tana salallami dasauri tafito duk sauran d’akunan da ke gidan saida tashiga ammah ba Amina,

‘Dakin hajiyane kawai bata jeba domin alokacin hajiya ta yi bacci,

Tun da tagama sallar asuba d’akin hajiya tanufa bayan sun gaisa hajiya maimuna tace babah ladi lafiya naganki a wannan lokacin? Akwai abinda kuke buk”atane?

Babah ladi tace lafiya lau hajiya daman Amina ce naga batanan bata kwana gidan ba shine nace ko kinsan inda taje?

Cikin tashin hankali hajiya tace ban fahimcekiba mi kike nufi da ba nan ta kwana ba?

Toh hajiya nidai tun jiya bayan la’asar rabonmu da Amina,

Dafe k’irji hajiya tayi tace na shiga ukku kar dai ace Amina ta gudu, zaro ido babah salame tayi tace ta gudu kuma?

Hajiya arud’e take dan haka dasauri tafito daga d’akinta tanufi d’akin Amina ganin babu kayan  Amina yasa hankalinta yak’ara tashi arikice takalli babah salame tace salame kuje kubinciko min ita dan girman Allah,

Hajiya wai meyake faruwa ne ya akayi Amina tagudu wani abu akayi mata? Yanzu fa ko munje babu inda zamu ganta dan tun jiya tabar gidan nan,

Nashiga ukku asirina ya tonu yau ni ya zanyi ? Hajiya wai miyake faruwane?

Numfashi taja tace bakomai salame kuje kucigaba da aikinku,

Toh Allah yakyauta Allah yasa tadawo, ficcewa tayi daga d’akin cikin jin takaicin tafiyar Amina.

STORY CONTINUES BELOW

Hajiya zagaye d’akin tashiga yi cikin tashin hankali, ya zanyi da Alhaji idan yaji labarin guduwar Amina? Ya zanyi idan yace inbiyasa kud’insa da nacinye nashiga ukku, kwala ma babah salame kira tayi dasauri babah salame tazo tace gani hajiya,

Kallonta hajiya tayi tace babu inda kike tunanin Amina zata je a anguwar nan ko gidan inda suke mutunci?

Eh toh hajiya gaskiya Amina babu inda take zuwa bata shiga gidan kowa domin Amina ba ta da shige-shige asalima ba ta da sakin jiki da mutane,

Cije yatsa hajiya tayi tace toh shikenan kina iya tafiya,

Toh hajiya.

Fitowa hajiya tayi takoma d’akinta cikin fargaba domin tana tsoron had’uwarta da Alhaji Faruk, a ranar hajiya bata ci abincin kirkiba saboda tashin hankali kowa na gidan saida yasan hajiya tana cikin tashin hankali duk a tunaninsu saboda tafiya da Amina tayi ne domin gani suke kamar hajiya tana tausayin Amina ne.

Bayan sati d’aya Alhaji Faruk yazo gidan, hankalin hajiya in yayi dubu toh ya tashi a nan take shaida mai guduwan Amina, ran Alh Faruk a 6ace yace hajiya ban ce miki ki lalla6ata kar kibari wani abu yasametaba?

Duk”ar da kai hajiya tayi cikin kwantar da murya tace ka ce min d’an la6ai wlh ban san tafiyarta ba,

Kuma shine tun lokacin baki fad’a min ba?

Shuru hajiya tayi.

Toh bari kiji inma had’a baki kukayi kika sata tagudu toh wlh sai kin biyani duk kud’in da nakashe kije kid’auko min kud’ina dan ni ba mutumin banza bane ni zaki yaudara?

Jikin hajiya yana 6ari tace Alhaji wlh ba ni nasa Amina tagudu ba wlh ko ‘yan aikin gidan nan zaka tambaya toh katambayesu kaji bamusan lokacin da taguduba,

Ke!! Kirufemin baki ba na son munafunci baki san halina bane ko kin d’auka kud’ina suna ciyuwa a bazan? Toh ba haka bane ni Alhaji faruk banda mutunci ko dan kinga shekara ukku baya ina zuwa cin abinci gidanki shine zaki yaudareni? wlh baki isaba kishiga kid’auko min kud’ina ko ind’au fansa a kanki,

Zaro ido tayi tace a kaina kuma Alhaji?

Eh kina jin wasane? Wlh minti biyar nabaki kid’auko min kud’ina inkuma ba hakaba zaki gani,

Harararsa hajiya tayi tace kai faruk dan kaga ina lalla6aka shine kake nema kaci min mutunci? To wlh baka isaba kuma kud’i ba za a biyaba,

Dariya yayi yace yau zan gwada miki ni cikakken d’an duniya ne wajen hajiya yanufa ta tsorata da yanayin da taganshi nan tafara ja da baya tana rok’onsa shikuma yana biye da ita har tashiga bed room d’inta dasauri tamaida k’ofa zata rufe cikin zafin nama yarik’e k’ofar rok’onsa tashiga yi ammah baisan tana yi ba ihun duniya babu wanda hajiya bata yi ammah kasancewar d’akinta ya yi ciki dayawa kuma duk ma”aikatanta suna wajen aiki saisa babu wanda yajita.

Saida yagama biyan buk’atarsa sannan yatashi yabar hajiya nan kwance dariyar mugunta yayi yace hajiya maimuna kenan ya kika ga abun na fanshe kud’ina a wajenki ko da maneji nayi dake, gobe ma idan ance kiyaudari wani ba zaki k’araba  sanya kayansa yayi yace na barki lafiya hajiya,

Ficcewa yayi daga gidan yana dariyar mugunta duk takaici ya cikata da nadama cikin kuka tace na cuci kaina tabbas na jawo ma kaina fitinar da tafi k’arfina daman ita rayuwa haka take kar kacuci d’an kowa kar kaxalunci d’an kowa miyasa ban d’auketa a matsayin d’iyaba? Daman ramin magenta k’urarrene, lallai bahaushe ya yi gaskiya da yace in zaka gina ramin rugunta ginasa gajere domin baka saniba ko kai zaka fad’a toh nidai yau ganinan tsundum na fad’a k’ara fashewa tayi da kuka tace na shiga ukku daman *k’addara ce* tahad’ani da wannan baiwar Allah gashinan kwad’ayina ya ja min lallai na yarda da maganar bahaushe da yace kwad’ayi mabud’in wahala inba kwad’ayi ba wulak’anci fyace majinar hancinta tayi tace nidai yau an wulak’antani wannan ya zama darasi agareni insha Allahu ba zan k’araba, dakyar tatashi  tanufi toilet Jikinta sai ciwo yake mata domin Alhaji faruk mugunta yayi mata, takaici duk yacika tace Allah ya isa da girmana da yarana aka wulak’antani wannan ya zama darasi agareni.

Alhaji faruk ko da yafito bai zame ko ina ba sai gidansa yana yin parking d’in motarsa yanufi cikin gida tun kafin ya ida shiga yaji hayaniya tana tashi dasauri yak’arasa matarsa karima ce yaga tana dukar d’iyarsa kamar zata kasheta dasauri ya k’arasa ya janyeta cikin 6acin rai yace karima bakida hankali sai kin kashe min ita? ita d’aya fa Allah yabani ko ma mi tayi miki ai yakamata kiyi hak’uri,

STORY CONTINUES BELOW

Hawayen bak’in cikine suka zuba daga idon karima tace Alhaji kabarni inkasheta wannan abun kunyar da tajawo mana ina zamu kai shi, me ummi tanema tarasa a gidan nan?

Wlh ba zaki kashe min d’iyaba ni ina son abuna,

Harararsa karima tayi tace Allah wadai wannan halin naka toh ai gashinan d’iyar taka tazo ta kwaso maka abun kunya cikine gareta,

Zaro ido yayi yace ciki kuma?

Eh gatanan katambayeta sai tayi maka bayani idan baka yardaba,

Kallonta yayi yace ummi dagaske ciki gareki?

Cikin sheshek’ar kuka ummi tace daddy kayi hak’uri wlh ba zan k’araba.

Zuface tashiga kwarara daga jikin Alh faruk hularsa yacire yana fita sai nanata innalillahi wa’inna ilaihiraji’un kawai yake ya kasa ta6uka komai,

Hajiya karima yakalla yace kitambayeta wa yayi mata shi, aikam hajiya karima kamar jira take tajawota tacigaba da duka ummi cewa take kutsaya wlh zan fad’a tukur driver ne yayi min, shine kullum idan zai kaini makaranta sai y biya da ni wani gida.

salati hajiya tashiga yi tace nashiga ukku Alhaji ka ji mun yarda da tukur ammah shi abinda zai saka mana da shi kenan toh wlh dole akamasa

Shidai Alhaji faruk yakasa motsin kirki domin ya san abunda yake aikatawa ga ‘ya’yan wasu shine aka aikata da d’iyarsa tilo wadda yafi k’auna a rayuwarsa bai ta6a nadamar abinda yake aikatawa ba sai yau tabbas ya san alhaki kwikwiyone, lallai ya yarda *duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka* (my second novel 😍) dafe k’irjinsa yayi jin yadda zuciyarsa take bugawa baice komaiba yaja k’afarsa dakyar yanufi part d’insa maida k’ofar yayi yakulle yajingina jikinta zuciyarsace tacigaba da bugawa nan da nan yafara aman jini duk yadda yaso yayi magana ammah ya kasa duk ya bi ya galbaita nan yazube k’asa idanuwansa suka fara kafewa,

Hajiya dakanta tad’auko waya takira police ba a fi minti biyarba sai ga police nan suka shiga boys quarters aka damk’o tukur aka tafi da shi.

Ita dai ummi kuka kawai take, hajiya bata k’ara bin ta kantaba tawuce tanufi d’akin Alhaji faruk domin hankalinta ya tashi ganin yanayin da yashiga, tura d’akin tayi tashiga k’ara tasaki ganin Alhaji a zube, ummi da take ta faman kuka dagudu tanufi d’akin ganin mahaifinta a kwance yasa tayi kansa tana kuka tace baba dan Allah kayi hak’uri katashi wlh ba zan k’araba, cikin kuka Hajiya karima tace yi sauri kije kikira min mai gadi dagudu ummi tafito tazo takira maigadi nan shima yashigo a kid’ime kama Alhaji sukayi sukayi suka nufi wajen mota aka sakashi hajiya karima taja motar suka nufi Federal Medical Centre nan da nan aka zo aka d’aukesa aka nufi emergency da shi, nan suka fara sintiri bakin k’ofa Ummi kuka kawai take tana nadamar rayuwar da ta jefa kanta a ciki domin ta san ta zalunci kanta.

Bayan minti talatin doctor yafito daga d’akin yana zufa dasauri su hajiya suka nufi wajensa suna tambayarsa jikinsa, kallon hajiya karima yayi yace hajiya saidai kuyi hak’uri domin Alhaji ya rigamu gidan gaskiya saboda zuciyarsace tabuga… tun kan yak’arasa hajiya karima tazube k’asa a sume dasauri suka d’auketa aka shigar da ita nan doctors suka hau kanta domin ceto rayuwarta, ummi kasa motsin kirki tayi kukanma k’in fitowa yayi, addu’a kawai takeyi, bayan minti ashirin hajiya karima tafarka nan ta dasa sabon kuka saida baba maigadi yazauna yayi masu wa’azi yafad’a masu illar kukan mutuwa sannan suka yi shuru suka cigaba da yi mashi addu’a.

baba mai gadine yayi waya gida akazo aka d’auki gawar suka nufi gida, tun kan su isa hajiya karima tatura ma dangi message, Dan haka lokacin da suka isa gidansu ya fara ciki da mutane

Nan akayi mashi wanka aka shiryasa akayi mai sallah aka nufi dashi gidansa na gaskiya _(Allahu akhbar kullunafsin za’ik’atul maut, daman haka rayuwa take babu Wanda yasan lokacin tafiyarsa mutuwa tana kan kowa duk abinda mutum yashuka shi zai girba in khairan to zai gani inma sharran shima zai gani, ba a fitar da k’auna daga rahamar Allah, Allah yasa mudace, Allah yasa mucika da imani idan tamu ta zo_

Ahaka acigaba da zaman gaisuwar Alhaji faruk, bayan wata ukku ummi tahaifi d’anta namiji anan tamaida mashi sunan daddynta, hajiya kharima ta yi sanyi sosai ta kar6i d’an shegen da d’itarta tahaifa amatsayin *k’addarace* da rabo ta yarda ita rayuwa babu mai iya tsallake abinda ubangiji yak’addara mashi.

Allah yasa mudace.

*CIGABAN LABARI*

_________________

Amina ko da takoma gida d’akinta tashiga tafad’a saman gado tacigaba d’s kuka kamar ranta zai fita ita kanta ta rasa kukan minene takeyi saida tayi mai isarta sannan tayi shuru nan bacci yayi awon gaba da ita.

Fahad ko da yagama sallar isha’i bai dawo gidaba abokinsa ne yusuf yajasa suka shiga gari basu suka dawoba sai wajen k’arfe goma, ko da yadawo d’akinsa yanufa wanka yafad’a yayi bayan ya fito yashirya cikin kayan bacci yataje sumarsa.

Ba ita tafarkaba sai wajen karfe goman dare mamaki tashiga yi yadda bacci yad’auketa har takai tsawon wannan lokacin bata bi takan Ameerah ba domin ta san tana d’akin babah mairo dan wani lokacin wajenta ko wajen fatima take kwana,

tashi tayi tacire kayanta tanufi toilet tawatsa ruwa bayan ta gama towel tad’auro daidai cinya tafito tana tufke gashinta, wajen gado tanufa domin tad’auki rigar baccinta da ta aje saida tazo daf da gadon taga mutum kwance saman gadon ya tsareta da manyan idanuwansa gabantane yafad’i…………….

”’It was a horrendous nyt tsaya take a cikin ruwa yana dukanta karkashin wqta bushiya tunanin rayuwar ta take yi na tsawon shekara 10 anan ganin yanda gurin yake duk da haka bata lura da akwae bushiya a gurin da take ba”’

”'”Gsky da in koma inda na fito gwanda na zauna a nan, dan zuciyana tafi aminta da nan gurin da nake koda ko mutuwa zanyi””’

”’Labeebah  had  unwittingly become comfortable with the chain of slavery for the past 10 years. Here she was  was  contemplating freedom. Freedom ?”’

”’Ruwan ya fara qoqarin tsayawa, nan taga duniya ta koma mata sabuwa. Nan ta fara tunanin ganin taxi in zaezo” toh inama zae kae ni” ta fada a zuciyar ta “amma dae koma Ina ne bari dae yazo mu gani” she smiled dryly”’

”’Gani tayi mota qirar Honda Accord blue tayi passing dinta kusan sau uku in different directions in the last five mins. A wnn karon taga flashlight ya hasko ta inda take tsaya parking yyi  bata ji tsoro bah sbd tasan irin rayuwar wahalar da tasha na tsawon shekara 10.”’

”’Data tuna rayuwarta a baya sae ta fara mgn da zuciyar ta”I have done all a human could do to be happy, it seems the more I try the more  my pains increase. Babu Wanda zae gane wahalar da na sha da irin bakin cin da na shiga yau da kullum dama mae wnn motar zae buge ni na mutu da na huta wlhi, my story would end once and for all. Amma bazan iya gudu nace ma wnn driver din ya buge ni bah, it will be suicide and that would mean eternal trouble with God Dan Allah yace kar mu kashe kanmu””’

”’Tsayuwa tayi tsayuwa dan izuwa yanzu ta fara gajiya amma tuna nin ta shine wane taxi driver ne zae dauke matured woman  a wnn daren to gaskiya ko nice drivern bazan dauke ta bah dan bansan mae ya fito da ita bah a daren nan. Gashi dare sae kara shigowa yake as far as she concerned, idan duk duniya ne zasu taru kanta baza ta damu bah sbd condition dinda take ciki  ta gama assignment din duniya saura na lahira ya rage mata.”’

”’Horn dinda taji ne yasa ta juya  wnn motar dazu ta gani tsaki kawae tayi ta dauke kae haka shima drivern ya cigaba da horn ba kakkau tawa ita kuma sae faman tsaki take dan gani take wlhi duk ya takura mata.”’

”’Wani saurayi ta gani da bazae wuce shekara 31 to 32 bah  fitowa yyi daga motar dauke da lema a hannun sa☔ bayan ya karaso inda take aransa yace”duk yanda akayi akwae matsala tattare da wnn matar amma koma miye zas tambaya yaji” it now or never Sameer mattered under his breath”’

STORY CONTINUES BELOW

”'”Me kike yi anan ke kadae without even an umbrella over ur head madam?” Ya tambaya”’

”’Amma ta masa banza ya kuma cewa it’s rather late; Ina zaki? Kina jiran wani ne koh in taimaka miki?”  He prodded further.”’

”’Amma still bata amsa shi bah ya kuma matsawa kusa da ita  sae ya ganta pretty and attractive even in her present state. Labeeba ta masa kyau sosae duk da halin da take ci bae hana kyanta fitawa ba.”’

”’Sameer ya samu kansa da mugun mamakin ta me a duniyar nan ke damunta wnn matar koh dae tana da mental problem ne? Amma ae kuma Bata yi kama da su bah . But inata mata mgn amma bata masa ba koh dae kurma ce?””’

”’Nan yyi tuna nin ya kara mata mgn yace”madam I hope u don’t mind my interference? Ina aiki na ne a matsayina na security agent akan street din nan. Aiki nane to give account of u as u stand out here now, pls ki timaka min inyi akina banzo dan na cutar dake ba wlhi koh na miki kama da mugu ne “”’

”’Saw a wnn lkcn ta kallesa a karo na farko nan ya samu courage din kara mata mgn “kiyi mgn mana”ya kuma fada”’

”’Labeeba tayi gyaran murya alamun yin mgn lkcn ta ciro handkerchief dinta ta goge face dinta “sunana Labeeba coming from somewhere to no where” ta fada”’

”'”me kike nufi da coming from somewhere to no where””’

”’tace”eh kamar yanda na fada maka malam bani da agurin zuwa anan amma idan law dinku tace a’a to tayi abunda zata iya””’

”’Sameer yaga alamun damuwa qarara a face dinta  sae lkcn ya kulanda hannunta dauke da zoben aure aransa yace”oh God koma menene matsalar ba zae wuce iyali bane amma I will make hr understand taimakonta zanyi””’

”’ya kalleta yace”koma mae ke damunki kituna Allah na tareda keki tuna duk baqinciki ba dauwamaa yake yi ba kumae rintsi zae tafi sae farinciki da walwala su maye gurbinsa gaba daya zae iya yiyuwa wanine ya saka ki cikin wnn halin kuma ya nisanta ki daga duk mutanen da kika yarda dasu amma ki sani shi Allah ba azzalumin bawansa bane ki riqa tuna yanzu ba matsalar da kike ciki ya kamata ki dinga damuwa ba a’a yanda zaki warware wnn matsalar komae naki ya dawo sabi””’

”’ita dae Labeeba kawae shiru tayi tana juya maganganun  sa dan har ga Allah mgnr da ya fada mata gsky ne amma taya zata fara hakan”’

”’Ruwan ya tsaya cak amma jikinta ta sae zubar ruwa yake tundaga gashin kanta har kasa tambaya taji ya mata daga sama” kina da aure ne?””’

”’tace”eh nayi a shekara goma da suka wuce ba yara my husband Hydar lives about ten pole from here””’

”’yace” oh thank God abun yazo da sauki nayi tunanin ko kina da nisa ne daga nan zan iya mayarda ke gida” ya tambaya”’

”’Labeeba tace”Allah ya kyauta ka gawana bana so a maida gidan shi ballantana da raina”’

”’Sameer yayi matukar mamakin furicinta tay za’ayi tayi rejecting komawa gdan ta lallae ba jaramin abu bane yasa ta yin hakan yace”zan iya samun address da phone no din mijinki””’

”’Nan da nan tsigar jikinta ta tashi dan taji mgnr da ya fada akan ya kira mijinta kwatsam sae ta tuna akan idonta aka fara ruwan nan kuma tana tsaye a gurin aka gama jikinta ne ya fara raww sbd sanyin dake shigarta ta ko Ina ta fara rokonshinya barta nan din ma ya mata amma mgnr komawa kam ya barta dan ba inda zata je”’

”’sameer yace” a wane daliline zan barki anan gashi sae fada ake a gari sakamakon zaben da za’ayi na governors kowa so yake ya ga shine yaci hakan yasa garin ya rabu gda biyu kowa da gangs dinsa ba Wanda ke fitowa da anyi sallahr magrib sbd tsoro””’

”’ tace”eh naji ka barni ana din dan Allah””’

”’yace”ba kya so ne naga mijinki?””’

”'”karka fara tuna nin hakan kawae ka barshi,bana son kowa ya dame ni ana””’

”’she countered”’

”’Labeeeba bata ma damu da gangs din da ke street din bah sbd ta shirya ma mutuwa akan ta cigaba da rayuwa a cikin wnn halin””

”’Hmm Labeeba komae ke damunki ae bae kamata ki rika son mutuwa ba koh dan baki ga tazo miki bane😁”’

”’Sameer yayi iya qoqarinsa na ganin ya kajta gidan yan uwanta ko kaawayenta  amma taki duk yanda yaso taimakonta taki yarda haka yasa shiga mota ya tafiyan sa”’

”’Bayan ta fiyar sa da kamr 10mins taji ana harba bindiga hankalinta ya tashi sosae””

”’nace ashe dae ba son mutuwar kike ba 😂”’

”’Dama Sameer ba tafiya yyi bah gaba daya gefe kawae ya samu yyi parking jin sun fara harbi yasa shi dawo wa inda take ya tsaya ba shiri ta shiga motar suka tafi”’

”’wayyo ai da kin tsaya mana kinmutu tunda shine burinki ba mutuwa kike so bah ashe 🤣🤣 ita rayuwa ko yane tana da dadi ai”’

”’Hotel ya samu ya kaeta bayan an basu key din room dinda zata zauna Sameer ya mata saeda safe ya tafi”’

”’Zan cigaba ne kawae idan naga kuna son book din so kuma zan gane hakan ne ta comments dinku”’

”’Washe gari da misalin karfe 10am Sameer yyi parking a bakin hotel din jiya bae tsaya bata lkc bah ya shiga knocking kofar dakinta bata bata lkc ba ta bude masa ta gefenta ya bi y shiga dakin tare da zama kan sofa din da ke ciki ita kuma ta zauna bakin gado shiru ne ya biyo baya na kusan 10mins ba Wanda yyi mgn cikin su sae daga baya Sameer ya katse shirun dake tsakanin su yace”morning how was ur night?””’+

”’kunya ce ta kamata tace”Alhmdllh I slept well after  I prayed nagode da qoqarin da kamin na taimakona da baka zo ba da bansan y zan qare ba a daren jiya””’

”’yace” ya isa ynzu mu bar wnn mae zaki ci” tace”ba komae na koshi”

Yace “aa baza ayi haka bah kinga idan kin ci abinci sae ki ban lbrn ki”

Tace”mae yasa kake son jin lbr na”

Yace”sbd ina son na San mae ya saka wnn santaleliyar madam a damuwa snn kuma mae yasa kika fito daga gda a wnn dare cikin ruwa snn idan akwae hali zan iya taimakawa amma kafin nan Ina son jin lbrn ki so ki fara cin abinci kafin”

Bata ce masa komae bahsae qasa da kanta ma da tayi shi kuwa Sameer ya kira masu ordering abincin hotel din yace sukawo masa breakfast mae rae da lpy  ba a dau lkc ba sae gashi an kawo abincin godiya ya masa ya ajiye a gabanta yace”u eat first dan bae kmata ki zauna da yunwa bah”

Bayanda taso haka ta dan tsakuri abincin tana ci bayan ta gama tasha ruwa daga nan ta mike zuwa baki window tare da janye cotton din gefe

Sameer yace”am all ears 👂 u can go on”

“Sunana Labeeba Ahmad kani am d only child of my parents kamar yanda kakata ta gaya min babana asalin dan garin Chad ne sun hadu da mama na a maiduguri a wani zuwa da yyi gaeda yan uwansa. Bayan aure sae suka koma abuja da zama inda mama ta samu aiki a wani hospital a matsayin nurse  babana kuma babban dan kasuwa ne. Daga baya suka koma United kingdom da zama inda suka barni a gurin kakata akan zasu dawo su dauke ni after thet settled.

Kakata na mutuwar kauna ta couse my mom is d only female child she has sae sauran siblings dinta maza.  Bayan an saka ni a murtala Muhammad nursery and primary skl bayan tafiyar su. My parents were still communicating and sending gift to me and my grandma from tym to tym.

Lokacin da bazan taba mantawa ba arayuwa ta shine bayan na gama wasa da frnda dina a a waje sae na dawo naga halin da grandma take ciki, sae na samu tana kuka she tried to clean up her tears as soon as she saw me enter, amma is too late bata San na gani ba  da gudu naje inda take nace”grandma me ya faru mae yasa kike kuka”. Tace”ba komae yarinya na” ta qara matso dani jikinta trying to console herself “kin San na taba gaya miki kafana na  ciwo toh yanzun ma shine” she lied

Na sunkuya kasa ina dan danna mata kafar a lokacin na tuna tana saka wani magani hakan yasa na tafi da gudu na dakko na shafa mata haka tayi deceiving dina ni kuma na yarda.

STORY CONTINUES BELOW

About 2hra sae ga uncles dina sun shigo their eyes looking red smiling kawae suka dinga yi sbd kar na shiga damuwa haka na gaeda su jiki a sanyaye na koma daki su kuma suka dinga mgn kasa² duk lkcn da na fito sae suyi shiru alokacin ina jss2 I can differentiat bad and good dole akwae abunda suke boye min amma toh mae yasa everyone is trying to act smart”

Later dat day, mutane suka fara zuwa gidan kuma yawancin su yan maiduguri da chad ne sae frnds din grandma dabara ce ta fado min kanna boye bakin parlour koh zanji wani abun da yasa aka taru a gidan haka. I wanted to hear what was causing dis tension. Babu alamun walwala a fuskar kowa.

Mama Hadi ce ta shigo gidan tan ihu da kuka kamar mara hankali tana mgn ta na kuka hae naji tace”shikenan yar yayata ta rasu gashi ita kadae ce sae maza”

“Toh dama abunda ke Faruwa kenan the whole tension, grandma’s mood and the fake arthritis pain?  akan mamana ta rasune aka taru haka? ba an kara ba najini a kasa ina qoqarin fara kuka I was heart broken as much as my grandma she could no longer look into my eyes because of the pain in them.

Bayan sati biyu na koma skl teachers dinmu da frnds dina suka min jaje . Haka na cigaba da karatu na sbd nasan ko ba komae inada baba da kuma grandma harda uncles biyu . I focused on my studies and came out with good grades . Grandma na matukar so na kuma tana min duk abunda nake so .

Kamar mutuwar mamana bata kare ba grandma duk ta shiga damuwa. Bayan doctor ya duba t yace jinin ta ya hau kusan 110 over 200 that was very high

Wata rana Ina dakin t ina gyara kayan cikin wardrobe sae naji faduwar grandma a toilet hakan yasa naje da gudu na taimaka mata muka fito bayan ta shirya na kaita hospital. She was addmitted after the doctor observed she had stroke doctor din yace”I know ur grandma ta shiga damuwa sosae mgnr lpyr ta kuma sae dae mu tsaya muga baunda Allah zaeyi.

Dr. Khaleel ya bani shawara akan na kira uncles dina na  gaya musu I went to Uncle Ahmad office first he works with ministry of education bayan na isa na samu baya nan kuma sunce sae 4 zae dawo na bar masa sako na tafi.

Daga nan na tafi office din Uncle Mahmood duk  a  wuse shine autan grandma bayan na shiga office ya taso da sauri ganin yanda idona suka koma red “me ne kuma” nan na bashi lbrn abunda ya faru ya ji tsoro sosae yabkoma kan kujera ya zaune yana tunani “toh mae yasa hajiya baza ta hkr ba since Muna iyakar kokarin mu ganin mun faranta mata what the hell no dis earth wrong with hr”

“Wane hospital ne”

Nace”lamides hospital”. Yaji dadi sosae da har na iya samun courage din kaeta asibiti.

Haka muka koma tare gaba daya grandma bata cikin hayyacinta  abubuwa take abnormal haka uncle Ahmad ya same mu shima kuka na samu sosae ina tunanin itama zan rasata haka uncles dina suka dinga bani hkr suna tsoron kar wani abu ya same ni.

Bayan kwana biyu da yamma na dawo daga skl direct hospital na tafi bayan na isa na tarar da uncles dina a waje dauke da tashin hankali a fuskarsu na tambaye su ya jikin grandma suka ce alhmdllh tace ma na dafa mata abinci Dan yanzu ta fara mgn.

I smiled as I hugged my two uncles who pretended vto be happy as well “bari n gaida ta sae n tafi” suka ce aa tayi bacci yanzu muje kagin mu dawo ta tashi nace”ba matsala muje”

Bayan mun isa gida uncles dina ba Wanda kema wani mgn nayi tunanin ya kamata ace kowa na cikin farin ciki yanzu ai “uncle Ahmad yaushe ne zata dawo gida “

Yace”maybe gobe”

Uncle kabeer yace”aa dr. Yace sae banda gobe”

Nace Allah ya kaimu

Bayan na gama abincin na zuba su uncles dina Nima na zuba nawa naci na grandma kuma yama basket.  Bayan na gam nace ma uncles dina mu tafi.

Uncle Ahmad ne ya kirani yace”Labeeba zoki zauna zamuyi mgn “

Nace”mu fara kaima grandam abinci akfin”

Yace”karki damu zata ci anjima”

Bayan na zauna uncle kabeer yace” Labeebah ya skl” na amsa da fyn

Dawo kusa da ni sukayi tareda hugging dinna suka fashe da kuka kamar mace”me yasa kuke kuaka kuda ya kamata kuyi farinciki”

“What is hau to my uncles ? Why are they crying when they should be happy that their mother is out of coma? Wait a minute, could it be they lied to me? What on Earth could make both of them crying like babies?” Haka tambayoyi da tunani suka dinga min yawo a kae.

Uncle Ahmd ne daga qarshe yace”grandma ta rasu Labeeba ta tafi ta barmu” ya karasa fada yana wani kuka mai ban tausayi.

Wani abu naji da ban taba jinsa ba koh da rasuwar mahaifina.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, uncles dina ba  abunda basa min sae dae matsalar uwa.

Wata rana da safe na tashi na shirya zuwa skl, bayan bus din da na shiga ta tsaya na sauka  wata mata da shekarunta baza su gaza 42 bah tace”yammata kinyi staining koh pad dinki ne baki saka da kyau ba”

Maganarta ta matukar bani mamaki dana duba  naga nayi staining da jini nace”toh me yasa meni koh ciwo naji ne ban sani ba”

Matar da taji ni tace”koh wnn ne karo na farko da kika fara ganin hakan”

“Ehh amma naji wasu a class din suna cewa wae suna menstruating nayi ta jira inga yazo amma shiru sae yanzu kuma”

Matar ta siyo pad a shagon dake kusa da inda muke tsaye. Gidanta ta kae da taimakon ta na gyara jikina ta tambaye ni Ina mamana nace mata ta rasu a shekar da ta wuce kakata da nake zaune  a gurinta itama ta rasu.

Hugging dina tayi tace”karki damu sunana Sarah and am a civil servant” .   Bayan nan ta bani abinci naci bayan na gama ta zaunar dani tace”kina da saurayi”

Nace”aa”

Ta cigaba da cewa”karki bari namiji ya taba ki dan zaki iya samun ciki abunda ya faru yanzu na nufin kin girma kin kae mace. Kiyi hakuri idan kinyi aure zaki haifi yara da yawa kinji kuma ki jira wani after dis month ” A haka ta dinga nuna min yanda zan kare mutuncin kaena.

Da yamma na kira uncle Ahmad yazo ya dauke ni ya kuma yi mata godiya  da alkawarin zamu qara dawo wa……..

‘Rayuwa ta cigaba da tafiya, so da kauna na kara shiga tsakanin mu da mama Sarah da sauran mutanen gda musamman Fareeda yarta dan itace mate dina.

+

Wata rana muna zaune da uncle Ahmad sae ga uncle kabeer ya shigo bayan mun gaesa yace tafiya zaeyi zuwa Cyprus dan ya samu ya karo karatunsa. Ina jin haka jikina yyi sanyi sosae dan a tunani na shima idan yaje bazae dawo ba. Bayani ya min mae gamsarwa sosae kuma na fahimta.

After three days muka rakashi airport sae da muka ga tashin flight dinsu kana muka dawo. Direct gdan girlfriend din Uncle Ahmad muka je  ina kiranta da Aunty Azeema. Tana matukar kauna ta kamar yanda uncles dina kemin.

Hmmm amma daga baya na gane ashe son karyane. Bayan anyi aure na dawo gdan da zama toh daga nan fah wahala ta tashi kullum cikin tashin hankali nake yanda nake bautar gdan ta bana tunanin ko nayi aure zan iya ma gda na haka..

Bayan na rubuta JAMB tun asubar fari nake tashi bana komawa bacci kuma sae dare abincin gdan ma ba ci nake ba dan bata bani kawae a matsayin baiwa ta daukeni koh pant da bra idan ta cire ni zan wanke mata. Zagi kuma ai ba’a mgn har cewa tayi ni na hanasu samun haihuwa sbd ni mayyace ni na kashe mamana da grandma. Ban taba gaya ma uncle dina bah dan a gabansa nuna take batada kamana duk duniya so nasan koda na fada he will never agree.

Wata rana tana cikin duka na da muciya ta daki fuskana sae hakorina daya ya fita. Bangaya ma uncle dina ba washe gari da safe ya dinga kwalamin kira jin shiru ban amsa ba yasa shi shigowa bedroom a dina yaga koh lpy. Kwance ya tarar dani zazzabi ya rufeni kuma kaena ya kumbura suntum.

Hankali tashe ya karaso kan gadon tare da yaye blanket din cikin tashin hankali ya kira Azeema da gudu ta fito amma is too late dan yariga yaga condition dinda nake ciki. Karya ta zauna ta shimfida masa bayan nan ya dauke ni sae clinic.

Bayan mun shiga mota ya tambaye ni nan na bashi lbr duk abunda ya faru tundaga zuwa na gdan sa har yau. Ranshi in yyi dubu ya baci.

Bayan mun isa clinic aka saka min artificial tooth

*******

A hotel din Labeeba ta tsaya da mgnr da take ta nuna ma Sameer haqorin da aka saka mata ta cigaba da fadin

*********

Da yamma Aunty Azeema ta fara ruwan zagina akan ban wanke mata kayan ta ba. Uncle Ahmad zuba mata ido kawae yyi yana kallonta,

After she finished the dinner we eat 2geda with my uncle.

Bayan na fita ya kira Aunty Azeema ya zaunar da ita ya labarta mata duk abunda na fada masa, hankalinta ya tashi sosae nan ta fara aikin qaryar ta sae da ta tabbatar da makircinta yyi tasira kana tayi shiru.

Bayan wasu kwanaki na ga uncle dina ya fara canzawa ba kamar da, bani da Wanda zan kaewa kuka na sae dae kullum da dare na jiqa pillow na.  Wata rana ina jinta tana waya da frnd dinta akan zuwan da zasuyi gdan malamin su.

Bayan sati daya da zuwansu gurin malam, na dawo daga kasuwa na tarar da uncle dina zaune a compound na gaidashi amma yyi min banxa na tambayi kae na”what have I done to again”. Nan dae na tsaya ina jiran mummunan hukuncin da zae biyo baya nasan dole aunty Azeema ta kitsa mae wani abu. Solution dinsu daya ne su koreni amma shi uncle Ahmad bashida gurin da zae kaeni. Gashi tace mishi wae idan ina gdan toh baxasu taba haihuwa ba kuma karshe aurensu mutuwa zaeyi.

Shiru dae har yanzu ba wani bayani sae kawae na saki jiki. Ba zato ba tsammani naji uncle dina na kwala nin kira da sauri na fito yace”ke zoki fitar min daga gida and don’t come back again if not…” Ba yanda na iya naci kuka har na gode Allah.

Nan na fara tunanin ina zanje yanzu mama Sarah ce ta fado min a rae, gidanta na wuce direct, nasamu tarba ta mutunci dag gurinta bayan na huta na bata lbrn duk abunda ya faru tace”ba komae kiyi hkr makirci ne  kawae na mata” naji dadin zama gdan sosae.

Bayan sati biyu da barin gdan uncle dina result din JAMB ya fito nayi tsalle nayi hugging frnd dina da itama ta rubuta exams din. Kwana biyu da fitowar results mama Sarah ta bamu kudi muje jamb office dibo results.

Bayan mun isa office din mukayi joining queue, wata mata daga gefenmu naga alamun tana kallona tun lokcn da muka shigo, bayan layi ya kawo kanmu tace idan na duba result dina na dawo na sameta.  

Bayan mun duba dukan mu munji ddi ganin results dinmu yyi kyau, sae muka dawo gurin wnn matar kamar yanda ta bukata tace” my lady u re beautiful” ta fada tana smiling

“Kinyi aure” ta tambaya.

I asked myself why will she be asking me dis question anya kuwa tana cikin hankalin ta ma kuwa ya zata kalli yar shekara 16 tace tayi aure.

Ta kara cewa”my dear did you get my questions?”

Nace”ehh amma banyi aure ba kuma banida niyar auren, yanzuma nazo duba result dina ne insao na shiga University maganar aure yanzu bata gabana”

Tace”karki damu duk da haka zaki je skl, I have a brother Hakeem he lives in Port Harcourt he saved his service there amma ke a ina kike zama? Ka bani address dinki so that I may see ur parents tareda kanina, shi kadae ne dani dan iyayen mu sun rasu gaba daya. Nasan ba zae hanaki karatu ba, shi engineer ne kuma kinga yasan mahimmanci karatu”

“Ni  aure  wnn ai mgnr banza ce duka2 shekarana nawa amma s dae bari ta gama mgnr na kama gabana” i thought to myself.

Faeedah dake tsaye tana kallon ikon Allah tama kasa mgn daga karshe ta bani complementary card dinta akan kowane lkc zan iya kiranta idan ina bukatar wani abu.

“My dear ikon Allah baya karewa a duniya” na fada ina jan hannun Fareeda muka fita

Tace”hmm wnn matar na tabbata da yarta ce baza ta fara fadan haka bah”.

A gida mama Sarah da mijinta sunji ddi ganin shigiwar mu dama suna tsayene a tsakar gidan da gudu taje tayi hugging dinsu tace”mom dad i made it score dina is very high  yanzu admission kadae nake jira” nan suka kara jin ddi da ganin result din yarsu.

Wani hawaye ne da bansan lkcn da suka zubo na fara ji kan kumatuna nima da parents dinna na nan da sun taya ni murna sosae. Ganin ina hawaye yasa dukan su suka wo kaena hugging din tayi tareda karbar result dina tace na dae na kukan ya isa haka.  Da yamma muka fita gaba dayan mu evening vibes.

Daren ranar banyi bacci ba gaba daya duk tunanina akan idan na samu admission ba mae biya min kudin skl sau biyu ina wanka sbd zafi da wnn tunanin bacci ya tafi da ni.

”’Washe gari da safe,mama Sarah ta kiramunbedroom dinta bayan mun gaesa tace mu  zauna ba Musa muka zauna a bakin gado ta  ta kalli Fareeda tace “”yata kin samu admission ina tayaki murana sosae kema Labeeba kin samu a port Harcourt ina taya ku murna sosae” Nan muka dinga murna da farinciki bayan nan shiru ya biyo baya,abun ya matuqar bani mamaki ko dae ta gane ni mayya ce tana neman hanyar da zata koreni ne kawae amma ta kasa sae ji nayi tace”Labeeba kiyi hkr wlhi bani da kudin da zan dauki nayin karatun kune ku biyu kinga baban ku ba aiki yake yi ba, ke ma a matsayin ya na daukekk bana so ki kuma shiga wani halin rayuwa”. Nasan tamin komae shi yasa ba damu ba, tamin abinda uncle dina ya kasa yi, toh banga dalilin da zan damu ba dan bata biyamin registration fees bah “mama nima abunda ke damuna kenan tun ranar da muka karbo results dinmu  amma ba komae Allah na tareda ni insha Allah”
Fareeda ma ta shiga damuwa sosae amma sae na nuna mata a rayuwa ba komae ake samu ba muyi hkr kawae mu barma Allah komae namu. Kullum da tunani daya nake kwana nake tashi.
Matar da muka hadu da ita a JAMB office ta fado min a rae da sauri na dakko complementary card dinda ta bani a jaka wani tunani yazo min arae”toh meye ma idan na gani bayan nasan office dinta gobe kawae zan shirya naje” amma dana tuna da auren qaninta sae kuka yazo min a haka har nayi bacci.
Washe gari da safe na shirya dan naje na samu aunty Salama muyi mgn, bayan na gaya ma mama Sarah tamin addu’ar samun nasara ta kum bani kudin mota nayi godiya na fita.
Ban samu abun hawa ba har kusan 12pm addu’a na itace kar naje ace ta tashi. Bayan na isa office din na samu bata nan na tambayi matar dake zama kusa da ita”dan Allah ina aunty Salama taje”
Tace”ta tafi ta kae daughter dinta hospital”
“Amma zata dawo” na tambaya
Tace”no from there zata je market kuma daga can zata tafi gda”
Nayi mata godiya na tafi. Bayan na isa gda na gaya musu yanda akayi amma mama Sarah tace na kara jarabawa gobe nace toh dan I have no any other option daya ragemin
Washe gari da safe na tashi na shirya da wuri dan karnayi late . Bayan na isa muka gaesa taji ddin ganina sosae tace”ykk”
Nace”lpy ya gd”
“Jiya ance kinzo bananan”
“Eh ance kinje kae daughter dinki hospital hw is she feeling now”
“Alhmdllh she is feeling better”.
Bayan nan muka danyi fira dan matar akwae son fira da ganinta. Tuna nin abunda ya kawoni na farayi taya zan fara fada mata da sauri na dakko admission letter dina na bata byn ta karanta tace”wow am so happy for u dear port Harcourt amma yaushe zakije ne kina da relatives acan ne”
Wasu hawaye ne masu zafi suka fara zirya a fuksana da sauri ta dago kae tace”meye ne kuma my dear”
Nace”ni marayace banida kowa”
Tace”karki damu indan wnn ne zan dauki nauyin karatunki”
Da sauri na dago nace”karatuna “
Tace”ehh idan ma da wani abu da kike so ki fada ni zan Miki”
Nace”aa wnn ma ya isa gsky ban san da wane words zanyi amfani ba na gode Miki”
Tace”ba komae idan kin shirya qanina yana jiranki zae kula da karatun ki  da sauran abubuwa” nayi mata godiya daga nan mukayi sallama na tafi.
Yammacin ranar kowa na gdan yaji ddi sosae da wnn lbrn. Amma kamar baba baeji ddi ba sbd wnn matar ba don Allah takeson taimaka min ba sae dan zan auri qaninta.
Ranar da bazan taba mantawa itace ranar dana taka zuwa Port Harcour. Da safe  mama Sarah da baba suka kirani suka bani shawara da ta dace, naji ddi sosae dan ko iyayena iya abunda zasu gaya min knn itama Fareeda a ranar zata tafi. Munyi kuka sosae dan zamu rabu da juna.
Bayan mun isa motor park muk shiga motar da zata kawo mu nan daman ta kira Hakeen ta sanar dashi akan zuwa na da kuma kalar kayan da nasa bae sha wahala ba gurin ganeni. Ya dauke sae gda bayan mun isa nayi wanka na shirya na fito dining cin abinci.
Ba qarya Hakeem is handsome fiye da tunanin mae karatu he is well educated. Ya bani kulawa sosae amma bae taba min mgnr aure ba dan haka nima na saki jikina kawae
Wata rana da safe na shirya cikin atamphana fa Hijab muka dauki hanyar skl. Bayan nayi sati biyu da fara karatuna a HOME MANAGEMENT SCIENCE DEPARTMENT  Hakeem baemin mgnr aure ba har lkcn shi yasa ba tada hnkl na ba .
He proposed to me after my first year in a world where I was really free to, choose, i wouldn’t have accepted to marry him because I saw certain traits that I wasn’t  particularly comfortable with. Ya cika zafi snn kuma baya tsayawa yyi bincike akan abu he just conclude. Amma  banida yanda zanyi  i also observed that he also picked and dumb girls like chewing gum wata rana ana weekend ya dauke ni ya kaini gda akan zanmae abinci i felt insulted seeing those girls winking at me. Hakeem na da wayo fiye da tunanin ka yasan ko wace shanya da zae bi dan na yarda na aure shi sbd sae da ya fara karantana tsab.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *