KINA RAINA CHAPTER 4

 KINA RAINA CHAPTER 4

Haka tana ji tana gani Marwan ya kulewa ganinta jiki a sanyaye ta fito daga cikin air port din sai sheshekar kuka take yi cab ta shiga tare da kurawa wayar ta ido dan yayi mata alkawarin in har wifi din airline din is available zai kirata har suka isa gidanta bai kirata ba.1

Fita tayi tare da biyan me cab din sannan ta haura zuwa apartment dinta karo na barkatai ta kara duba screen din wayanta ga mamakinta sai taga yana blinking alamun akwai sako,kunnawa wayarta ta gani sai me missed call din marwan ta gani da mesaage daya cikin rawar jiki ta bude message din da yake layi daya

_on board! Called you, you were’nt picking. I love you!_ wani irin kuka ta fashe shi da shi musamman ma da ta gwada kiran layinsa ya ki zuwa cikin kuka ta unlocking kofanta ta shiga dakin ta fada kan kujera tana kuka ya yin da take kara kiran number dinsa amma baya shiga rike cikinta tayi tana tsananta kuka she cant believe ahe missed his call,bata san ya aka yi wayarta ta shiga silent ba har ya kira bata sani ba.1

A wannan halin bayan ta ci kuka ta gode Allah bacci ya dauketa sai cikin dare ta farka tayi sallah kara gwada kiran layinsa tayi still a kashe sai wani sabon kuka har garin Allah ya waye bata samu daman komawa bacci ba wanka tayi da safen tayi shirin makaranta dan bata ga amfanin zamanta a gidan ba har wannan lokacin kuma number din marwan baya zuwa.1

Bakin glass ta saka ta toshe idanunta saboda yanda yayi luhu luhu sanadiyar kukan da ta sha ga wani azababen ciwon kai dake damunta haka tayi classes cikin rashin lafiya da rashin walwala ta koma gida tana kan gwada kiransa amma baya zuwa sai sabon kuka ya barke nan da nan zazzabi ya rufeta.

Kwana uku babu kiran marwan sannan layinsa baya zuwa ga ciwo ga rashin mataimaki so kusan hudu on different occation tana jin door bell dinta amma bata iya tashi taje ta bude sam maimunatu bata jin dadin rayuwarta a kwana na hudun ne a daddafe ta mike dan ta shiga school dan ta ga alama in bata yi gaske ba da alamun ba zata tsinana komi a makarantar ba hakan ya sa ta daure ta shirya zuwa makarantan tana me mamakin me ya hana marwan kiranta har lokacin wrist watch din da ya bata birthday gift ta dakko tana kallo idonta na taruwa da hawaye a hankali ta dora a hannunta tana ji kaman ta fara zuwa gidansa ta ga ni sai kuma tayi tunanin kewan zai yi mata yawa zama tayi a kan kujeran karatunta tana kara gwada kiransa daga tafiyarsa zuwa yau ta kirasa yafi karfin sao dari biyar amma sam layin baya zuwa.

Kamar kullum layinsa was switch off kifa kanta tayi a jikin table tana kuka kafin da kyar ta lallashi kanta ta mike tare da kintsawa ta fita.

School ta wuce direct tana calculation ya kamata ta je groceries shopping cos she ran out of many things tunowa tayi da kafin marwan ya tafi yayi yayi suje shopping taki saboda bata son abinda zai nesantata dashi a wannan lokutan,she cherished every second they spent together.

Bus ta bi da zai kaita sch ko da ta fito da wayanta dan ta kara duba kiran marwan babu ko daya whatsapp dinta ta shiga sai taga bata da message ko daya da yake ita ba ma gwanar chat bace haka ta zaune zuciyarta cike da tunanin ko lafiya marwan yake a haka har ta isa makaranta.

A nitse take tafiya har ta shiga cikin makaranta, da wani yaro da bata gane ba a cikin makarantan ta fara cin karo inda ya kashe mata ido tare da fadin “hey sexy” tattare giranta tayi da mamaki amma bata ce komi ba ta cigaba da tafiya abin mamaki ko ina ta wuce kowa kallonta yake yi ana magana kus kus kus tare da nunata ita dai ta san babu abin nunawa ajikinta shi yasa tayi kokarin ganin abin be dameta ba which is in possible ka ga ana nuna ka baka muzanta ba.1

Balarabiyar ajinsu da suke dan magana sama sama ne ta ja ta zuwa wani lungu cike da damuwa take kallon fuskar maimunatu yayin da ita ma maimunatun take kallonta da alamun tambaya.

Hannu balarabiyar me suna jalila ta sa aljuhun rigarta ta fito da wayarta da wani flayer dan danne danne tayi sannan ta nuna mata screen din wayar dammm gaban maimunatu ya fadi ganin hotonta a tsirara ta tubke gashin kanta kadan hoton an rubuta _feeling stressed? Call me and i will relief you_ kuma an tura da number dinta kwace wayar tayi a hannun jalila tana kara kallon hoton tabbas fuskanta ne amma ba jikinta bane saboda bata mallaki wadannan kananan nonuwan ba amma babu wanda zai ce ba ita bace duk da an samo sirirriya kamanta sannan yanzu an san yan mata da iya ciko so ko wanda ya santa ne in ba wanda ya sna jikinta ba ba zai ce ba ita bace.3

Nan da nan hawaye ya cika idonta ta shiga uku,ba tare da jalila ta ansa wayar ba ta fita daga cikin platform dinsu na makaranta ta shiga wajen status ta veiwing status din maimunatu inda hotuna similar to wanda maimunatun ta gani suka bayyana da write up irin wancan sannan ta presenting mata flayer ta kuma shaida mata yana nan like ta ko ina cikin campus.

Hannu maimunatu ta saka cikin jakarta ta fito da wayarta tana fadawa jalilan “this is not me i swear to you! Wallahi this is not me.” Cike da tausayawa jalila ke kallonta tana gyada kai1

Ga mamakinsu duk abinda suka gani a wayan jalila yana story din maimunatun,wurgi tayi glasses din da take sanye dashi jikinta na rawa tana ta faman yiwa jalila rantsuwa da hausa tana cewa ni dai bani bace ni dai bani bace ni wallahi dai bani bace i swear to you.”

Rungumota jalilan tayi ganin tana shirin fita hayyacin ta duk da ko da ta ga hotunan ta san ba ita bace amma yanayin da ta kara ganin ta shiga daga ganin hotunan ya kara tabbatar mata ba ita din bace ta yaya za ta sanar da ita a wannan halin hukumar makaranta na son ganinta?.1

Kafin jalila ta yanke hukuncin yanda za ta yi da ita wayarta ta fara kara alamun kira, raba jikinta tayi da na jalila dan ta duba me kiranta zaro ido tayi tare da dafe bakinta1Ba kowa ke kiranta ba illah daddy kyar kyar jikinta ya cigaba da kyarma sam ta kasa tattara courage din ansa kiran har ya tsinke mai da dubanta kan jalila tayi wacce ke yi mata kallon tausayi dan taga wanda yake kiran.1

A marairaice take kallon jalilan not knowing what to say or do. A nutse jalila ta dora hannunta bisa kafadun maimunatu cikin sanyin murya tace “look here maiimoonattu calm down and take a deep breath.” A hankali maimunatu ta ja numfashi ta fesar kaman yanda jalilan tace.

“Good.” Shine abinda jalila tace sannan ba tare da ta kalli idanun maimunatun ba ta shaida mata cewan school authority na son ganinta a mugun tsorace ta kalli jalila wani sabon kuka na kubce mata yau ita kam ta shiga uku.

“Shhhhh dont cry i will stay by you.” Jalila ta assuring dinta amma hakan bai sa ta tsagaita kukan da take yi ba da kyar da sudin goshi jalila ta shawo kanta ta dan yi shiru sannan ta rike hannunta zuwa office din VC din makaranta maimunatu na rakube a jikin jalila kaman wacce tayi wa sarki karya kallo daya zaka yi mata ta baka tausayi.1

Da yawa wasu daga cikin daliban kallonta suke yi cike da tausayi dan wanda suka santa sun san ba zata taba aikata hakan ba sun san kawai sharri ne dan attention ya dawo kanta wasu kuma da suke jin haushinta saboda dedication dinta wajen karatu sai isgilanci suke yi mata amma bata kula ba ina ma take da karfin halin kulawa maimunatu ta kalli mutum so nawa balle tayi mishi magana.1

Bata da abokin hira bata yawo bata hulda da kowa babu wanda ya taba ganinta da wani dan uwa ko aboki ko saurayi sai dai wasu lokuta in marwan ya zo daukanta ko ya dropping dinta and babu wanda ya san alakar dake tsakaninsu duba cewan duk su din bakaken fata ne.

In kaga maimunatu da wani toh tabbas aboki ko abokiyar karatu ne kuma karatu ne ya hadasu,abin tambayan a nan shin wa zai aikata mata wannan danyen aikin? Wa ta batawa haka da zai so tozarta rayuwarta? Yarinyan da abokin mutunci ma bata dashi balle na fada.1

Tambayan da ya cika kwakwalwan jalila kenan but she is not in the right position to ask her.

A bakin kofan office din jalila ta dakata tare da kokarin zare hannunta,gam maimunatu ta riketa tana gunjin kuka dan wani bala’in tsoron tunkaran hukumar makarantan take ta yaya zata fara kare kanta? Me zata ce musu wanda zai sa su yarda da ita? A hankali jalila ta dora hannunta kan na maimunatu dake damke da dayan hannunta tare da gyada mata kai kan cewan komi zai wuce. Wani dunkulalen hawaye ne ya zubowa maimunatu a karo na barkatai da sauri jalila ta zare hannunta tare da juyawa tana dauke hawayen tausayin maimunatu sannan ta juyo. Kwarin guiwa ta bata sannan ta murda kofan ta turata ciki ba tare da ta shirya ba.

1

Ko bayan shiganta office din VC din shiru tayi tana sauraran hukumar makarantan ta inda suke shiga bata nan suke fita ba in da suke gargadinta da in zata tallata tsaraicinta tare da tallata sana’arta ba a cikin makarantar ba sannan aka bata suspenssion na semester din gaba kasancewar jarabawar wannan semester din ta karato.

Ita dai maimunatu babu abinda take yi sai kuka bata musa laifin da ake tuhumarta da shi saboda bata da hujja da haka aka sallameta ta fito ta samu jalila a waje tana jiranta.

Jikinta ta fada tana kuka izuwa yanzu hawaye ma basu fita a idonta sai gunjin kukan kawai idonta wani irin azabar radadi yake yi mata haka jalila tayi ta lallashinta tare da janta zuwa wajen motarta.1

Jalila zata girmewa maimunatu da kusan shekaru biyu kasancewar maimunatun ta gama makaranta da wuri ne.

Har gida ta mayar da maimunatu bayan ta bata address din gidanta.

Wannan shine karo na farko da wani a kasar ya san gidan maimunatu bayan marwan,jalila ita ce mutum ta farko da ta shiga jikin maimunatu kuma har ta barta kasancewan tana neman kafadan kuka sai da jalila ta tabbata ta sha tea da aspirin sannan ta bar gidan.

Bacci me nauyi ne ya dauketa wanda ita kanta ta manta rabon da tayi irin baccin saboda jalila har da maganin bacci ta hada mata.

Bata farka ba sai wajen yamma zuwa lokacin idanunta da kanta sunyi nauyi sannan fayau take jinta.

Da kyar ta samu tayi wanka tazo ta jera sallolin da suka wuceta.

Jakarta ta janyo inda ta fiddo da wayarta missed calls ne rututu da text mesaages na mutane dabban dabban ciki har da missed calls din daddynta da su uncle sa’id ta san duk so suke su ji dalilin abinda suka gani a status dinta.

Abin takaici babu missed call ko message din marwan ko daya wasu hawaye ne suka zubo mata me marwan ke nufi da ita ne?

Dora kanta tayi a kan guiwanta tana rera kuka a hankali wayar ta ce ta fara ringing daddy ne damm gabanta ya fadi wayar ta ajiye can nesa da ita tare da kara rakubewa tana kuka kaman tana gaban daddyn yau ita me zata ce mishi tana ji tana gani har kiran ya tsinkewa wani ya kuma shigowa still daddy ne haka shima ya gama ringing bata dauka ba nan kuma na uncle sa’id ya shigo nan ma kara volume din kukanta ta yi anma bata picking ba har ya tsinke.1

Haka kiraye kiraye suka dinga shigowa wayarta da numbers din da ta sani da wanda bata sani ba amma bata dauka ba sai aukin kuka da take ta yi kafin kace me zazzabi me zafin gaske ya rufeta dama ba wai ta gama samun sauki bane.

A cikin wannan halin Jalila tazo ta sameta babu shiri ta danganata da hospital emergency aka kaita dan bata cikjn hayyacinta taimakon gaggawa aka bata har aka samu numfashinta ya dawo dai dai.

Jalila ita tayi ta dawainiya da ita har ta samu sauki aka sallameta,ita ta dinga bata shawarwari tana dada karfafa mata guiwa har ta dan sake suka fara karatun exams har zuwa wannan lokacin maimunatu bata yi magana da kowa daga gida ba sannan bata daukan kiran kowa in ba na Jalila ba.

Dalili daya ya saka bata canza layi ba saboda har kullum tana saka ran jin kiran marwan amma shiru kake ji kaman malam yaci shirwa.1

Suna tsaka da exams wata rana tana karatu ita kadai a cikin dakinta idomta ya fada kan teddy din da marwan ya siya mata lokacin birthday dinta shiru tayi ta kurawa teddy din ido har gobe ta kasa daina mamakin dalilin da ya saka marwan bai kirata ba

Bakin cikinta daya bata san kowa nashi ba,bata san wa zata kira ta tambayi halin da marwan ke ciki ba. Me yasa basu taba introducing wa juna families dinsu ba? Toh ko dai dama Marwan yaudaranta yake dama ya shirya rabuwa da ita ne? Wannan tunanin shi ya dimauta maimunatu ta fashe da wani marayan kuka tare da kife kanta a kan table dinta.1

Door bell dinta aka danna hakan ya sakata mikewa tare da goge idonta dan ta san jalila ce cos tace mata zata zo suyi karatu,hallacin jalila ya sa maimunatu ta kasa koranta a rayuwarta kaman yanda ta saba koran duk wanda ya so kusanci da ita.

Ba tare da ta tsaya ta duba wake knocking ba ta bude kofar sai da numfashinta ya dauke na wucin gadi ganin wanda yake tsaye a door step dinta…..

1

Ni kaina dai wannan page din bai min dadi ba bans on koke koke mtswwwwUncle sa’ad!” Ta furta tare da zaro idanu,gyada kai yayi hannunsa na cikin aljuhun wandonsa fuskarsa dauke da murmushi yana kallon yanda fuskanta ya dawo ya suntime ga ido ya koma ciki ciki alamun kullum sai tayi kuka,har gobe har kullum yana tausayin rayuwar yarinyan amma taimakon da zai iya yi mata kalilan ne.1

Ji take yi kaman taje ta rungume shi amma ina jiya ba yau ba girma ya zo she is not more that little girl he carried,wani kunya ne da tsoro ya dirar mata lokacin da ta tuno da abinda ya kawo shi.1

Sunkuyar sa kanta tayi tana kokarin mayar da hawayen dake taruwa a kurmin idanunta. “Maimunatu” ya furta cikin sanyin murya like always.

Kasa dago da kanta tayi saboda kunyaj hada ido da abokin mahaifin nata wanda ba tantama yana tunanin hoton tsaraicinta ya gani a story dinta na social media.1

Cikin nutsuwa ta amsa ba tare da ta dago kanta ba,gyaran murya yayi yace “je ki saka hijabinki ki sameni a kasa we need to talk.” Gyada kai tayi tare da amsawa da toh.

Cikin sanyin jiki ta koma daki ta daura doguwar riga kan riga da wandon dake jikinta tare da saka hijab dai dai shoulder dinta.

Ko da ta fito ya riga ya sauka  so ita kadai ta bi lifter dan zuwa kasan, a cikin lifter din ta samu daman yiwa jalila text kan cewan ta fita da uncle dinta.

Wani restaurant dake cikin anguwan suka je inda uncle sa’ad ya reserving musu wani booth dake can lungu.

Zaman shiru suka yi after giving their order uncle sa’ad bai ce mata komi ba har zuwa wannan lokacin.1

Itama shiru tayi tana jiran taji ta inda zai fara. Yana shirin magana wayarsa ta dau ringing sallama yayi bayan ya dauka “yeah muna tare da ita yanzu haka,chill mana,nace ka bar komi a hannuna abi abu a sannu tukun.” Dan jim yayi yana sauraran wayar yayin da zuciyar maimunatu ke ba da sautin duka dan tana iya jiyo kuwwan muryan mahaifinta duk sa bata jin me yake fada amma ta san fada yake yi. Sai da ya gama uncle sa’ad yace “toh naji! I will take care of everything here.” Yawu maimunatu ta hadiye tana zazzare ido.1

Sallama yayi da daddy kafin ya mayar da dubansa kan maimunatu dake zaune a daddare kaman za ace mata keh! Ta bace.

“Maimunatu what happened?” Shine tambayan da ya jeho mata habawa sai hawaye girgiza kai yayi tare da d’an yatsansa yace “uhm uhm ba kuka nace kiyi min ba tambayanki nayi kuma nake so ki bani amsa.” Bayan hannunta ta saka ta goge fuskanta sannan ta ja hanci cikin dakushewan murya tace “wallahi uncle sa’ad ban sani ba i really dont know nima haka na tashi na tsince ni a wannan halin.”

Hannayensa ya harde tare da dora habbansa a kai yace “maimuna ban gane ba? Toh hannun waye wayarki ta shiga ranan da abin ya faru garin yaya kika bari aka dauke ki haka har aka samu daman bazawa?”2

Kuka ta fashe dashi tace “ah ah fa uncle ah ah bani bace ba fa,wallahi uncle bani bace face din ne dai kawai nawa amma wallahi bank bace.” Gyada kai yayi yace “i thought as much amma ke maimunatu wa kika tsokana haka da har za ayi kokarin getting back at you ta wannan hanyan?  Yarfe hannunta tayi tace “wallahi uncle ni bana kula ko balle in yi fada da wani ban san wa ya aikata min waannan danyen aikin ba….” Nan ta kwashe mishi halin da take ciki a makaranta.1

“Toh me yasa baki picking calls?  Tabe fuska tayi tace “uncle ni ban san me zance Bane. “

“But that was very wrong kin daukan wayan na dai dai da kin admitting kin aikata laifin ne” kuka ta kara fashewa dashi tana yarfa hannunta “nashiga uku uncle wallahi ban aikata ba.”1

Hanki ya fitar a aljuhunsa ya goge fuskarsa yace “kar ki damu maimuna ko wani dan adam da kalar tashi jarabawar ke kalan naki kenan ki roki Allah ya baki iko da daman cinye wannan jarabtar,daddynki ya turo ni ne dan in dawo dake yace yana ganin zai hakura da makarantar ki ya mikk aure kawai.”2

Dafe kirjinta tayi tana salati yau ta shiga uku kafin tayi magana yace “saboda haka in kina da wansa kike so ki gabatar min dashi in kuma babu sai ki gaya min in san abinyi.”1

Shiru tayi tana tunanin Marwan,yau ga dama ta samu amma babu marwan,bata san halin da yake ba,bata san matsayinta ba a wajenshi a halin yanzu,shin wani amsa ya kamata ta baiwa uncle sa’ad?1

“Ke nake sauraro maimuna!” Uncle sa’ad ya katse mata tunani gyaran murya tayi sannan ta kara sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta cikin sanyin murya tace “babu kowa uncle.”

Gyada kai yayi yace “Allah ya kyauta,yanzu yaushe zaki gama jarabawar?”

“Nan da six days” ta bashi amsa. Good before then ni kuma zan yi kokarin ganin na karban miki transfer dan ki koma tsohon university din da kike karatu ki cigaba in har nayi nasarar shawo kan daddynki saboda haka kiyi kokarin ganin cewan baki bani kunya,zan shiga maganan nan ne dan na yarda da tarbiyarki maimuna na san ba zaki taba watsi da tarbiyar da muka yi miki ba.” Gyada kai tayi tana me jin kunya watsi da tarbiyarta wajen biye marwan suna fasadi gashi yau marwan din ya gujeta babu shi bau labarinsa yau fiye da sati uku,yah Allah ka yafe min shine abinda ta fada a zuciyarta.5

Maimunatu ta zage dantsa wajen ganin jarabawarta ya kara kyau dan kar ta ba uncle sa’ad kunya yayin da shi kuma yake ta faman zirga zirga yana ganin hukumar makarantan dan  ganin an bata transfer ba tare da an mayar da ita baya ba gefe daya kuma ya kaiwa company din layin da take amfani dashi kukan abinda ya faru da ita.1

Bincike suka yi mishi sosai inda suka tabbatar mishi da cewan wani da basu sani bane ya hacking layin nata har ya aikata mata haka suka kuma nemi yafiyarta dan hackers da yawa na waje suna aikata barna.1

Da wannan shaidar hankalin uncle sa’ad ya kwanta ya san shawo kan mahaifinta yanzu ba mai wahala bane. Cikin sati biyu maimunatu ta hada komatsanta suka yi shirin tafiya gida Nigeria.1

A hanyarsu ta zuwa air port take tunanin yaushe zata samu ilimi me  inganci yau tana nan gobe tana can? Kallon garin take ta window din motar inda suke wuce wajeje da yawa da marwan ya kaita.

Lallai marwan cikakken mayaudari ne yau da ta sakar mishi jiki ya aikata zina da ita da ya ci banza ya barta da dora hannu a kai tunda yau gashi an wayi gari marwan ya gudu ya barta,for the last time ta dailing number dinshi labarin dai daya ne number din is switch off murmushi ta saki dan dama ta san abinda zata ji kenan ba tare da tayi tunani komi ba ta wurgar da wayar kan titi mota ta bi ta kanta a firgice jalila ta kalleta amma bata ce mata komi ba.2

Ta yar da wayar ne dan bata son kullum ta cigaba da kiran layin marwan tana ji a kashe yanda ta yar da wayar nan haka zata bar tunanin marwan ta shafe babin rayuwarta da marwan har abada zata cigaba da neman tuba wajen Allah akan abinda suka aikata ita da marwan zata dawo da rayuwarta kwatankwacin na da abu daya ne ba zata cigaba da yi ba shine hana kanta farin ciki.2

Zata inganta rayuwarta da ibada hade da neman ilimi kuma zata cigaba da kasancewa cikin farin ciki tayi hulda da mutane sannan babu wani da namijin da zata bari ya shigo rayuwarta tayi karatun halayen da namiji ba zata bawa ko wani irin namiji daman da ta baiwa marwab ba…Lumshe idanunta ta bude su tar tayi lokacin da ta shaki iskan kasarta,kaman jiya ta tafi yau gashi ta dawo. A hankali take taka matattakalan tana bin bayan uncle sa’ad a haka har suka sakko suka yi abubuwan da ya kamata suka bar air port din zuciyarta na lugude tana tunanin ya zata fuskanci daddynta.1

Addu’a ta kama a bakinta tana neman tsari a wajen Allah. Bayan hannunta ta saka ta goge idanunta tapping dinta   uncle sa’ad yayi tare da furta mata “ki riki Allah komi is going to be alright.” A hankali ta nodding kanta.1

Suna isa gate din gidan gabanta ya tsananta faduwa  a hankali ta saka kafanta ta fito daga cikin taxi din da suka renting ta fito tana kara kama duk adduar da tazo bakinta ji take yi kaman ta sa gudu,toh ta gudu taje ina? Wani gata take dashi da ya wuce daddynta? Bata da wani strong bomd da dangin mahaifiyarta saboda daddynta da momy sunyi kane kane a rayuwarta. Ko hutu bata zuwa musu sai yau kawai ta debi jiki taje lokacin da take da matsala? Will they even believe cewan bata aikata laifin da ake tuhumarta da aikatawa ba?1

Dafa kafadunta da uncle sa’ad yayi shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Dan tattare girarsa yayi yace “baby ba na hanaki tunanin nan ba at this tender age ki dami zuciyarki da kwalkwalwarki da tunani? Sam bana son kara ganin haka in kina so mu shirya. Ko kina in cire hannuna a lamuranki ne?” Da sauri ta girgiza kai tana kokarin mayar da hawayen da yake zuwa mata dan ta san hakan na iya kara bata mishi rai.1

“Good” shine abinda yace dan waigawa tayi tana karewa tulin kayanta da taxi driver ya sauke har ya tafi bata sani ba ta tafi duniyar tunani.

Alamu uncle sa’ad yayi mata da hannu na ta fara yin gaba wani kakkauran yawu ta hadiye sannan ta fara taking steps a hankali bakinta na dauke da addua kaman wacce za a sadata da mutuwarta.1

A hankali ta murda kofar da zai sadaka da babban palon gidan da daddynta ta fara cin karo yana zaune cikin daya daga cikin kujerun palon yana karanta news paper, waro idanunsa yayi a kanta kaman wanda yake mamakin ganinta ita kuma ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya bata ankara ba taji ya eurgo mata flower vase din dake kan side table din dake gefen kujeran da yake zaune da sauri ta koma baya tare da dodging wa vase din tatsatsa yayi a kasan tiles din wajen. Uncle sa’ad ne da yake bayanta ya dan ingizata gaba ta kuma shiga palon. Kau da ita gefe yayi cikin bacin rai yace” Abdul wani irin abu ne haka da ya sameta taji ciwo fa?”1

Shima cikin tsananin fushi yace “ai gwara ya sameta ta ji ciwon ko zan huce haushin ni ciwon da ta saka min a zuciya,haba ace yarinya kaman maimunatu ta san shedananci toh ni ban bawa iyayena wuya ba itama ba zan nari ta wahalshe ni ba,na dauketa a Nigeria saboda kar soyayya ya rufe mata ido sai taje ta kama iskanci? Haba sa’ad haba! Wallahi ba dai dani Abdullahi za ayi danyen aikin nan ba. Ai da tayi zamanta a can da sabbin mutanen da ta zaba a matsayin abokan rayuwarta wai har ni zan kira yarinyan nan taki daukan wayana for more than 3 weeks saboda ta mayar dani sa’anta wallahi kaji na rantse maka sa’ad ni har na hakura da maimuna tunda ta zabi zaman can da rayuwa dasu da halayensu fiye dani ta nuna min fita da ita waje karatu da nayi ba gata nayi mata ba.” Daga haka ya koma gefe yana ta haki kaman wanda yayi tsere maimunatu na tsaye tana ta aikin zabga kuka.2

Kama shi uncle sa’ad ke kokarin yi ganin yanda yake muzurai amma sai daddy ya fizge jikinshi kaman qani yaro, da dan yatsa ya nuna uncle sa’ad  yace “sa’ad matsawar kana son tarayyar mu ta cigaba toh lallai ka fitar min da wannan annobar a gidan.”1

“Subhanallahi Abdul bar aibata diyarka haka mana.” Cewar uncle sa’ad

Rintse idanu daddy yayi yace “wato dai ba zaka fita da ita ba sai na maka radhin mutunci ko?” Ganin yanda jikinsa ke bari dan tsananin bacin rai ya sa uncle s’ad kama hannun maimunatu dake ta faman rusan kuka ya fita da ita daga palon suna fita ya sake ta yana zarya a tsakan compound din gidan.1

Maimunatu kallonsa take ta tsakankanin jikakken lashes dinta tana mamaki da tunanin ashema ba daddy bane ya sa a dawo da ita ba in ta shine kar ma ta dawo. Innalillahi me ta aikatawa rayuwarta haka? Kuka take sosai.1

Tana kallo ya fito da wayarsa tare da danna kiran wani number sannan ya manna a kunnensa dayan hannunsa na rike da kugunsa yana zagaye gidan bai dau lokaci ba ya gama wayar ita dai tana rakube a gefe tana jiran taji me zai ce mata next.1

Duk abinda ake yi a kan idanun momy aka yi tana kallo fuskarta dauke da kayataccen murmushi she feels this time around she has won tayi nasaran raba mijinta da diyarsa ba tare da ta bi boka ba balle malam sannan ta san babu wanda zai zargeta da rashin bawa maimunatu tarbiya she hope and pray saurayin da ya shigo cikin rayuwar maimunatu ya daidaita mata tarbiya.1

Dakinta ta fada a guje tare da danna kiran wanda ta sashi aiki cikin tsananin farin ciki tace “good job! Aikinka yayi kyau,ko da yake daman bana tantama akan cewa aikin naka zai yi kyau saboda yanda ka tsara komi.” Dan shiru tayi tana sauraran abinda na dayan bangaren yake cewa can ta saki murmushi tace “sosai kam ka burgeni wannan lokacin saboda haka ka saurareni nan da wani dan lokaci zaka ji alert.” Daga haka suka yi sallama duk maganan da suke yi cikin halshe turanci suke yi1

Ba a dau wani lokaci me tsawo ba aka yi horn me gadi yaje ya bude gate wani mota ne me kyau na yayi ya shigo cikin harabar gidan tun kafin motar ta gama parking uncle sa’ad dake tsaye gabanta yana bata baki ya rabu da ita ya karasa inda motar take.1

Bude murfin motan aka yi wani kyakyawan magidanci ne ya fito daga ciki yana sanye da kaftan karamin dinki a jikinsa.1

Can kasan breath dinta ta furta “uncle sufyaaaan.” Da sauri sauri gudu gudu ta karasa gabansa tare da…..Da sauri sauri gudu gudu ta karasa gabansa tare da rike hannunsa lokaci daya tana kuka hade da dariya. Murmushi yayi me kayatarwa  tare da dafa kanta yace “Munari an girma.” Babban yatsansa ya saka yana goge mata hawayen dake makale a kan fuskanta tare da fadin “shhhhsh kukan ya isa haka everything is going to be alrighr.” Gyada mishi kai tayi wasu sabbin hawayen na gangaro mata.

1

Cike da izza ya riko hannunta suka kama hanya shiga palon sa’ad na biye dasu dan tirjewa tayi cike da tsoro kallonta uncle sufyan yayi hade da sakar mata murmushi sannan ya gyada mata kai.1

Cike da tsoro maimunatu ke biye dashi dan yanzun bata san matakin da daddyn nata kan iya dauka ba.

Bakin uncle sufyan dauke da sallama ya shiga cikin palon hannunsa a cikin na maimunatu suka shiga palon.

Har daddy ya yunkura zai mike sai kuma ya koma ya zauna tare da kawar da kansa yana muzurai.

1

Kallon uncle sufyan maimunatu tayi taga ya tabe baki tare da cewa “Abdul ai da ka tashi nima kaci mutuncina kaman yanda kayiwa sa’ad dan ya dawo maka da diyarka.” Har lokacin daddy bai ce komi ba sannan bai  juyo daga kallon gefensa da yake yi ba.1

“Mmm ai ni ka ban mamaki ai ni ina tunanin ko kariya daya daga cikin mu ya dakko daya zai tayasa amsansa ba wai ya tozarta sa ba kaman yanda kayiwa sa’ad,ka nunawa diyarka cewan mu bamu da daraja a idonka babu wanda ya isa yaci albarkacinka ta dalilinmu,yau ko lalace maimunatu tayi ya cancanta ka koreta? Haba! Abdul haba!.” Zuwa wannan lokacin jikin daddy yayi sanyi sosai yaga rashin kyautawa abokinsa da yayi sauke kansa yayi yana kallon yatsun kafansa dan kam yaji kunyan sa’ad.

1

Ganin haka ya sa uncle sufyan karasa shiga cikin palon ya sami kujera ya zauna tare da zaunar da maimunatu a kasan kafansa uncle sa’ad ma ya sami waje ya zauna.

Maimunatu ta dade da sanin cewa daddy bashi da wani amini sama da uncle sufyan bashi da wani abokin shawara sama da uncle sufyan da shawaran uncle sufyan daddy ya fita da ita karatu kuma yanzu ma tana da tabbacin uncle sufyan ne ya saka a yi mata transfer ba daddy tunda ga alamu sun nuna bai san da zuwanta a yau ba har sai da ta saka kafa a cikin gidan.

1

“Rahina! Rahina!! Rahina!!” Uncle sufyan ya kwala kiran sunan momy (kar ku manta uncle sufyan shine mijin yayar momy shine wanda ya hada auransu) lokaci daya zuciyar maimunatu da momy dake sama ya doka.1

Wallahi maimunatu ta manta da wata momy ta manta wani bala’in na zaune a Nigeria na jiranta sai dai wannan lokacin ta dau alwashin babu me takata ta bari.2

Cikin lullube ta fito kanta a kasa can nesa ta tsaya tare da rinsinawa tana gaishesu.1

Cike da masifa uncle sufyan yace “Rahina kina zaune a gidan nan da ranki da lafiyarki har Abdul ya kori diyarsa ki zauna cikin farin ciki?” A firgice bata da masaniya din nan kallon kwayar idonta yayi da sauri ta sadar da kai cikin rawar murya tace “wallahi yaya bani da masaniya ni sam ban san cewan maimuna ta dawo gidan nan ba.”1

Duba gefen kofan palon yayi tare da girgiza kai duk wannan tabargazan da akayi tace bata ji ba.1

Kura mata ido yayi yace “Rahina kina sane da abinda maimunatu ta aikata a kasar cyprus.” Kanta a kasa tace “eh yaya.”

“Good toh wani mataki kika dauka akan hakan a matsayinki na mahaifiyarta?” Gaba daya ya daureta da jijiyoyinta duk sai ta firgice ganin haka ya sa daddy cetonta yace “sufyan wani irin magana ne kake yi haka? Kowa ya san iya kokarin da Rahina take yi akan tarbiyar nan amma ta watsar ta bi shedanu.”1

Mayar da duban sa kan daddy uncle sufyan yayi yace “toh shikenan, naji kai yanzu duk tarbiyar da kake ikrari kun bawa maimunatu bai san kun shaidi halinta ba har kake shirin sallamawa duniya ita?”1

STORY CONTINUES BELOW

Dan bata fuska daddy yayi yace “ka rabu da sha’anin yaran yanzu ka haifi da ne baka haifi halinsa ba sannan yanzu dan Adam babu abinda ba zai iya yi akan kudi ba.”1

“Toh kenan duk halin da ta shiga laifinka ne tunda ka kaita wata uwa duniya baka wadatata da kudi ba.” Uncle sufyan ya tari numfashin daddy.1

Harara daddy ya wurga mishi yace “ka san abinda ba zan taba yi ba kenan in tura diyata wani guri sannan ba zan sauke hakkin dake kaina ba.”1

Uncle sufyan na shirin yin magana uncle sa’ad yace “ya ishe ku haka nan kaman wasu yara ku tsaya kuna sa’insa,keh maimunatu tashi ki shiga ciki.” Dan kallon babanta tayi ya kawar da kai gefe a hankali ta tashi sim sim ta haura sama.

1

Bayan fitarta ne uncle sa’ad ya fede musu biri har wuya na abinda ya sami maimunatu cewan ba laifinta bane an tabbatar masa da cewan an hacking wayarta ne.1

Tunda uncle sa’ad ya fara magana zuciyar momy ke tsinkewa tana tunanin shikenan asirin ta ya tonu shiyasa yaya sufyan yake yi mata tambayen kure karya(shi dama mai aikata mugun abu kullum zuciyarsa a dar dar take duk wani motsi da za ayi da bai gamsheshi zai yi tunanin asirinsa ne ya tonu)

1

Daddy kam jikinsa ne yayi sanyi yana tunanin wa maimunatu ta taba da zai mata wannan mummunan sakayyan? Wani tausayinta ne ya tsarga shi amma dai ya dake.1

Uncle sa’ad ne ya cigaba da yi musu nasiha na su kara janyo diyoyinsu a jiki su san halin da suke ciki sosai ya musu nasiha me shiga jiki.1

Uncle sufyan kam bai kara cewa komi ba sai kalman tsoron Allah da yake ta maimaita musu “kuji tsoron allah a lamuranku wallahi zaku ji dadin rayuwarku.” Gaba daya sai momy ta muzanta ta tsargu gani take maimunatu ta fadawa yayanta wani abu shi kuma ya fara zarginta.1

Daga karshe uncle sa’ad ya fadawa daddy abinda suka yi na transferring din maimunatu zuwa university din nan.

Bude baki daddy yayi yace “ni kam sa’ad da an hakura da batun karatun nan haka inda rabon zata cigaba nan gaba toh,amma ni yanzu hankalina yafi bani kan in aurar da ita.”1

Sai lokacin uncle sufyan yayi magana yace “mu kuma mun riga mun yanke hukunci in kuma zaka nuna mana iko a kanta ne toh bismillah,yarinya karama kamar wannan zaka ce zaka yiwa aure bana tunani ko saurayi tana dashi.”

1

Dan kallonsa daddy yayi yace “maimunatun ne karama? Shekaru 18 shine karama? Wallahi sufyan ka cigaba da yaudarar kanka gaku ga maimunatu ku yi duk yanda zaku yi ni dai duk abinda yaje ya dawo kara a sako ni.”1

Da sauri uncle sufyan yace “babu ma abinda zai je ya dawo fal yaqul khairan auli yas mut.”

Toh shikenan Allah yayi taimako ameen.

1

Daga nan kuma suka fada hirarsu kaman babu abinda ya faru ganin haka ya sa momy mikewa ta haura sama zuciyarta bakikirin wallahi ta gama tunanin wannan karon ta raba maimunatu da rayuwar gidan nan na har abada ta manta cewan mutanen da ke zagaye da daddy baza su taba bari tilon diyarsa ta rasa gata ba.

2

Abin haushi ya gashi ta yi sanadin da maimunatu zata kuma zaman gidanta dan daurin gindi har da transfer an rantse karatun nan da bata so maimunatu tai sai ta yi shi.1

In the other hand ga yaya sufyan sam ta kasa gane ina maganganunsa suka dosa ta lura a duk cikin maganganunsa kaman akwai gugar zana lallai ya kamata ta dan fita harkan maimunatu ta san mijin yayarta kaman yunwan cikinta in ya sa mutum a gaba ya shiga uku.

1

Sosai take jin takaicin asarar makudan kudinta da tayi gashi yanzu ma ta completing kudin aikin sannan gashi mainunatu ta wanku tsab a idon mahaifinta tsaki taja tana me shiga bandaki.

1

A bangaren maimunatu tana shiga dakinta ta sauke ajiyar zuciya dakin na nan yanda yake,she cant believe komi ya warware mata a lokaci guda duk wata matsalarta ta kau saura marwan.1

Tsaki taja a fili tace “Na shafe babin marwan inshaaAllah na bar marwan da yaudararsa a kasar cyprus zan yi rayuwa kaman ban taba sanin wani marwan ba.” Dan taba kofarta da akayi ne ya saka ta yin shiru rabi ce yar aikinsu take shigo mata da lugagges dinta bakin nan har kunne dan murna kasancewar maimuna ta kowa ce a gidan kuma tare suke aikin gidan dasu.”1

Rungumeta maimunatu tayi suna murna rabi tace “hajiya naji dadin dawowarki amma duk kin bi kin rame kamar ba kasar turawa kika je ba kaman wacce taje gidan yari.” Dariya maimunatu tayi wanda ta dade bata yi ba tace “kai Rabi ai ba jin dadi naje ji ba karatu fa naje yi.” Dan bata rai tayi tace “toh gaskiya ba ri inje in samo miki abinci dan gaskiya kinyi kaman kin dade baki ci abinci ba.”

1

Dariya Maimunatu ta kuma yi tace “lallai kam,toh ki samo min tuwo inci.” Waro idanu Rabi tayi tace “hajiya yau kece zaki ci tuwo? Halan tunda kika tafi baki ci tuwo ba?” Gyada mata kai kawai Maimuna tayi tana murmushi.1

“Aikuwa dai bari in yi sauri inje in kawo miki.” Rabi ta fita tana rarraba ido dariya maimunatu tayi tana janyo jakankunanta tajita wata fayau rabon da taji farin ciki haka tun kafin marwan ya ce mata zai tafi ya barta1

Tsaki ta ja tuno dashi da tayi “home sweet home!” Ta fada a bayyane murda kofan toilet dinta tayi sannan ta shiga, da wanke toilet din ta fara sannan ta yi wanka sosai take jin gajiya.

Da kyar ta bude daya daga cikin jakankunanta ta dakko kananan kaya tana cikin sawa Rabi ta knocking kofa sannan ta murda ta shigo hannunta dauke da tray dake dauke da abinci ajiyewa tayi akan dan  table din dake gefe a dakin tana kallon kayayyakin maimunatu cikin saurin magana tace “hajiya wadannan kayan yanzu za a gyarasu?” Girgiza kai maimunatu dake gaban mirro tana kama kanta tayi tace gaskiya ba yau ba dan yanzu bacci nake ji sosai ina cim abinci kwanciya xanyi.

Rabi bata so ba dan ta san in dai aka gyara kayan akwai rabonta sosai.

Zama gaban table din maimunatu tayi tare da fadin yawwa mamana wannan abinci haka.1

Rabi sai murmushi take dokawa bismillah maimunatu tayi ta fara cin abincin.

Tana tsaka da ci rabi tace “hajiya!” Maimuna ta amsa da “mmm?” Kin gane wannan me shagon nan,haladu” cak maimuna ta tsaya da cin abinci tace “rabi khalid ake cewa khalid! Me ya same shi.”

“Toh mu ai a garinmu haladu ake cewa,in gaya miki ashe ba me shago bane basaja yayi.” Ai ba shirin maimunatu ta kurawa rabi ido tace “ban gane ba,ban gane basaja yayi ba kamar ya?”1

Watsa hannayenta tayi tana daukan lotion din da maimunatu ta fito dashi a cikin jakanta tace “haka ake ta cewa wai ashe dan sandan farar kaya ne,meye hakan yake nufi?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *