KINA RAINA CHAPTER 8
_I appreciate each and every of your comments wallahi Allah ne kadai ya san farin ciki da nishadin da comments dinku yake sani na gode sosai._
+
“I can’t believe yau Kin barni nazo ganinki” Tahir ya fada cike da farin ciki,murmushi tayi tace “ai na gaya maka komi lokaci ne we take one step at a time gaggawa aikin shedan ne.2
Sipping juice dib dake hannunsa yayi yace “haka ne,i just wish kaman yanda kika barni nazo gidanku zaki bani daman gabatar da kaina ga babanki.”
Rolling idanuwanta tayi tare da kara gyara zama tace “Tahir yanzu dai na gama ce maka mu bi komi a hankali inshaaAllahu ni da kaina zan gabatar da kai wajen daddy in lokaci yayi right now lets focus on knowing each other.”1
Shiru yayi amma ba haka yaso ba,ya so ace ya gabatar da kansa a wajen magabatanta ya san in har manya suka shiga cikin maganan komi zai zo misho da sauki ko da ace wani matsala ta bijiro mishi daga baya.2
“Shikenan! I wish zan iya zuwa in ganki gobe a office but i have a lot of work kin san mondays,beside ranan yah marwan yayi min kashedi da soyayya lokacin aiki da na daure na shigo ko na 20 minutes ne.”
Murmushi tayi tace “karka damu ni karan kaina aiki yayi min yawa cos ka san wannan week din na bar mubeena da aiki.”1
Fito da jikinsa yayi daga cikin kujeran da yake zaune ya daura hannuwansa akan guiwarsa ka fin yace “zan iya tamabayanki wani abu?”
Dan daga kafadu tayi tace “why not? Ina jinka”
Numfashi ya sauke yace “how close are you girls are dan yanda relationship din ku yake is kinda…i dont know..” Ya watsa hannayensa irin bai san kalmar da zai using ba.1
Murmushi tayi tace “mubeena is a nice person tana min kirki sosai tana sona,in few weeks zamu yi passing out amma ita she want me to take her position in tayi aure which i doubt in haka zai taba yuwuwa.”1
Ba tare da tunanin komi ba yace “thats very good!”
Kallon mamaki tayi mishi kafin ya farga da abinda yayi ta jefa mishi tamabayn da ya sashi rudewa “why is it very good? Me yasa ma baka son mubeena ne after all you are family?” A dan rude yace “eh bana i mean ba wai bana son ta bane .”3
“Toh meye? You even told me not to tell her about us and she has been nothing but good to me,me yasa baka son ta sani.”
Kama kansa yayi tare da furta innalilalhi,ya salaam! Ni bana nufin komi da hakan kawai bana son surutu ne nafi son sai komi ya tabbata yanzun tana ji she will get excited alhalin har yanzu ban san makomata ba a wajenki.”
Murmushi tayi tare da rufe fuska wai bai san makomarsa ba yau Tahir ne is sounding so serious ba wasa.1
Dan hira suka taba yayi mata sallama ta fito rakashi motan khalid ya shigo juya idanu tayi ta san korafi kuma assalamu alaikum.
Tahir ya taba ganinsa so daya yazo daukanta amma bai ce komi ba ya shiga motarsa ya fita a gidan taji dadin hakan ta san da Marwan ne da an shiga uku yau.1
Karasawa inda khalid yake tsaye a jikin motarsa tayi fuskar nan tasa a hade ita kam ma sai abin ya bata dariya duk fushin na meye?4
“Barka da yamma dict dan fulani.”
Bai amsa ba sai na jefa mata tambaya da yayi “munah wanene wannan da tafin?”
Gira daya ta d’aga tare da harde hannunta a kirji tace a takaice “bakona ne”1
“Bakonki? Bako maimunatu bayan kin san da magana na kike entertaining wani namijin?” Ya fada ransa a mutukar bace
Waro idanu tayi tace “ban gane na san da magananka ba last i checked ba sunana Habiba ba in makuwa kayi ba ri in tuna maka sati me zuwa daurin aurenka da yar uwarka habiba sannan ni kace zaka hanani sauraran wani?”4
STORY CONTINUES BELOW

Kasa yayi da muryarsa yace “na sani na sani kiyi hakuri ba zan hanaki tsayuwa da wani namijin ba but pls maimunatu kar ki bari a rabani da ke ina da daman auranku ku biyu ke da habiba pls maimunatu.”1
“Mmm” tace kawai kara marairaicewa yayi yace “pls munah”
Ajiyan zuciya ta sauke tace “ni baka gane ba,ba wai ina son in bari a rabu bane ko in ki auranka or anything,nace maka in har ka gabatar da maganana a gidanku da wajen habiba i assure you zan aureka but ka kasa me kake tunanin zanyi tunani?”2
“I know,i know! Na miki alkawarin ana auran mu da habiba zan gabatar da maganarki.”
Da sauri tace “shi yasa nace maka ka bari har zuwa lokacin kafin mu cigaba da maganan soyayyyah.”2
Cusa hannunsa yayi a kwantaccen gashin fulaninsa na rasa abin yi nan da nan fuskarsa tayi ja abinka da farin mutum kallo daya zaka masa ka san ransa a mutukar bace yake amma bai son ya nuna hakan dan ya san fushin fari ba nasa bane nashi lallashi ne a wannan yanayin yayi mata sallama ya tafi, sosai taji tausayinsa but thats the least she could do for him.1
Marwan kam tunda ya tafi ya kasa samun sukuni ji yake yi kaman ya juyo ya dawo babu abinda yake son gani kaman maimunatu mami kadai ke kwantar masa da hankali amma shi kadai ya san halin da yake ciki, ji yake yi anya zai iya wannan sati biyun?2
Bangaren maimunatu haka nan ta daina ganin sa ba karamin tashin hankali ta shiga gashi babu wanda zata tambaya tun tana sa ran ganinsa anymoment har satin ya kare bata gansa ba har wani karamin rama tayi ta missing dinshi sosai take son ganin sa ko ba zai mata magana which ta san ba dai marwan ba sai dai in bai sata a ido ba babu abinda zai hanashi takalanta.3
Ta bangare d’aya kuma soyayyarsu suke sha da Tahir,sam baya zuwa wajenta a wajen aiki sai dai ya sameta a gida ta sani deep down bata son Tahir kawai she enjoy his company saboda yana da barkwanci.2
Khalid na kiranta kullum duk da an fara hidimar bikinsa amma hakan bai hanashi kiranta sai da tace mishi gwara ya mayar da hankalinsa kan shirin bikinsa sannan ta smau sukuni gefe daya sam bata jin zafin aurensa.
Marwan ya saka wani soja ya bi bayan maimunatu in zata gida saboda yana son sanin inda take dan su daddy suje nema masa auranta.2
The following week mubeena take cewa maimunatu ba zata dinga shigowa office kullum ba saboda habibinta zai dawo weekend sannan zasu prewedding pictures dinsu kasancewar bikin nasu ya karato so dole ta zauna tayi gyaren jiki.1
Wani kallo maimunatu tayi mata tace “yanzu duk wannan freshness din naki sai kin kara wani gyaran jiki kafin kuma kizo kiyi na aure? Ke ba wai shiga rana kike ba,gida ac,mota ac,office ac amma sai kinyi wani gyaran jiki” Wani har tayi da manyan idanunta tace “ba zaki gane bane habibi is a classy person that deals with classy people,so kinga dole in zama presentable da wannan dark skin din nawa.”1
Galala maimunatu ke kallonta can tace “you have a beautifull skin wallahi sannan ke kanki kin san you are classy without even trying ke dai kawai kice kina ji da wannan habibin naki.”1
Wal tayi da idanu tare da dafe kirjinta da hannu daya tace “wallahi kam sosai nake ji da habibina saboda habibi mutum ne na kwarai yayi min abinda da duk duniya babu wani namijin da ya kwatanta yi min haka he is one of a kind yayi min taimako a lokacin da nake tsananin buqatan taimakon ke kanki da zaki ji abinda yayi min sai kin ce min mubeena ki ninka son da kike yiwa bawan Allahn nan dan ya cancanta.”1
“Woahhh irin wannan kodi haka gaskiya ko me yayi miki kina ji da abin nan.” Cewar maimunatu cike da mamaki limshe idani mubeena tayi tace “tabbas ya min abu me girma da ya dasa soyayyarsa a zuciyata i wish zan iya gaya miki hadina da habibi but wani sirri ne na rayuwata da na gaya miki ba wai dan ba trusting dinki bane ya sa ba zan fada miki ba,sam! Dan yanda nake jin adda mufli haka nake jinki sai dan abin ba na fada bane.”1
Dafa hannunta maimunatu tayi tace “ba komi i understand,kowa yana da hidden skelaton a drawer din sa ki cigaba da rike sirrinki.”1
Daga wannan ranan sam mubeena bata zauna ba bata zuwa office miamunatu ke kula da bangarensu.
Ranan wani friday maimunatu ta shigo office tana sanye da pencil trousers tare da karamar riga dai dai cinyanta tare da rolling gyale a kanta hips din nan ya fito tsam duk inda ta wuce kowa sai ya kalleta sam ita bata ma san suna yi ba.1
Tun daga automatic glass door din reception din mutane ke binta da kallo marwan ke tsaye tsakiyar reception din yana kallon expression din da fuskokin security dinsa da sauran ma’aikatanshi da ganin maimunatu.2
Sai da gabanta ya fadi ganinsa dan bata yi tsamanin ganinshi ba tun tana sa ran ganinshi har ta hakura danne mamakinta tayi ta karasa cikin reception din.1
Ba tare da wani tunani ba ya daka mata wani uban tsawa “maimunatu what on earth are you wearing?” Kallonsa tayi ta kalli kanta tare da tabe baki ta karasa jikin elevator ta danna “maimunatu ba dake nake magana ba?” In kujeran da nake zauna ya amsa toh itama ta amsa.
Amma ranta in yayi dubu ya baci da wannan mulkin mallakan na shi a gaban mutane5
Cike da fushi ta shigo office dinta tare da banging kofar,goshinta ta dafe tana sintiri a tsakar office din yayin da ta rike kugunta da hannu daya “me marwan ke nufi da ita yanzu ba da bane da zai juyata son ranshi wallahi bai isa ya shiga rayuwarta ba.
Turo kofar da aka yi da karfi yasa ta waigawa tsaki taja ta karasa wajen kujeranta tana tattara wasu files1
“Mimi what was that? Ina miki magana ki wuce ki bani waje a gaban employees dina.?” Bata bari ya karasa ba ta katse shi da fadin “saboda ka shiga hurumin da ba naka ba.”1
Kin fi kowa sanin jikinki da kayan da zaki sa hurumin da ya shafeni ne.”1
Gira daya ta daga tare da fad’in “oh really? Last i checked jiki nawa ne ni nake da iko dashi so i wear what i want to wear in naga dama inyi yawa tsirara ba ruwanka.”1
Dam gabanta ya fadi ganin yanda jijiyan kanshi ya tashi saboda bacin rai amma ta daure tare da nade hannunta a kirjinta
Dafe table din yayi yace ” you know damn well that i fucking own you,mimi ki cigaba da flaunting curves dinki and believe me zan kwakule idon duk shegen da ya kalleki then you have yourself to blame….And who are you to tell me what to do?” Ta fada tare da hard’e hannunta a kirjinta.
Tsaye ya mik’e daga durk’uson da yayi ya dafa table suits dinsa ya gyara yana murmushi yace “Ni ne Marwan mamallakin maimunatu,you know that better than i do.” Baki ta tab’e tace “maimunatu bata da mamallaki har yau,sai mijin da ta aura shine zai zama mamallakinta but as for now babu wani d’a namiji da yake da iko dani.”2
Ba tare da jin zafin magananta ba ya zagaya ta inda take tsaye yace “ni zan aureki miemie,a shirya nake na aureki ko da yau ne pls miemie ki daina wahalar damu ki sassauta wannan fushinnda kike yi mu fuskanci juna,me yasa kika bar cyprus? Ko kuma dont answer that let bygone be bygone pls miemie i really do love you and you know that.” Ya karasa maganan cikin muryar da ya san yana kashe mata jiki.1
Kwayar idonta ta saukar kasa hakan ya tabbatar mishi da trick dinsa worked,sosai maganganunsa da muryar da ya using ya ratsata amma in ta tuno da wahalar da ta sha na rashinshi duk sai taga marwan ba sonta yake tsantsan mayaudari ne kawai.1
Wata yar karamar dariya tayi ta zaga ta fita daga tarkon da yayi mata tace “Marwan ni da kai mun sani ba ka sona jikina kawai kake so yanzu da kaga ba zaka samu ba shine zaka bullo min ta maganan aure? Toh anki a aureka marwan,ba ayi! Wai kai wani irin mara zuciya ne nace bana yi ko dole ne? Ni bana sonka ko wancan lokacin ma da na yaudaru a hannunka dan ban san me nake yi bane saboda haka ka fita hanyata bana sonka kuma ba zan tab’a sonka ba!” Ta karasa maganar ta na haki dan ji take kaman ta gudu ta boya kar ya dira a kanta.1
“Karya kike yi munafuka! Karya kike yi! Kina sona kuma sai kin aureni,wallahi wallahi wallahi kinji na rantse maimunatu and ba zaki sa ni kaffara ba da iznin Allah i will make you mine sai ki aureni kin dau cikina kin haifa min yara.”2
Cikin ihun masifa tace “Allah ya tsareni da haifan yaran mazinaci wallahi ni ba zan aur…..” Dal ya dane bakin dafe bakinta tayi idonta taf da hawaye a hankali tace “wannan mugunta ne.” Kai ya gyada yace “eh saboda ba zan iya dukan mace,macen ma wacce nake so!”1
Zumbura baki tayi tace “malam ni ka daina cewa kana sona dan jikina kake so ba ni ba,mugu kawai mayaudari,dan iska.”
Waro mata kwala kwalan idanuwan sa da suje ladabtar da ita yayi yace”ni kike zaki?” Ita kanta bata san ta inda courage ya zo mata ba ta murguda mishi baki tace “kai ba mayaudari bane dan iska? Da ka samu dama da tuntuni ka gama da rayuwata shine yanzu zaka lallabo ka wani zo min da kalmar so da aure toh ka sake lale wannan jikin…..” Ta nuna jikinta “ya fi karfin mallakarka.”1
“In anyi magana sai kice jikinki nake so wanda in da naso ajiya dana a cikinki tun shekarun baya da na ajiye ke kin sani i never press akan son kusantarki da na dage babu abinda zai hana baki bani ba kin san me yasa? Saboda kema kina son abinda nake miki you enjoy every part of it,ai ba forcing dinki nayi ba you always moan my name and hold me tight in ecstasy ashe duk mu biyun yan iska ne Allah kadai ya san sleepless nights din da that i had dan in tayaki rike virginity din naki da naga kina so kaman ranki,duk dan karki accusing dina wata rana da sha’awarki kawai nake tsk tsk tsk had i know i would have fuck you to my satisfaction yanda ko ance miki maimuna rabu da Marwan sai inda karfinki ya kare.” Ya fada a hankali yana limshe ido dan gaba daya ta sa mishi ciwon kai,kansa wani irin sarawa yake yi2
“Ni ba yar iska bace,kaine dai dan iska ka koya min iskanci Allah ya tsiratar dani ba wai dan baka ga daman uhm uhm..” Tama rasa kalmar da zata using “uhm yin abu dani bane Allah ne ya kare ba wai iyawarka ba.”1
Bai ce mata komi ba ya juya ya fita dan ya lura in ya biye mata ranshi ne zai yi ta baci.1
Yana fita reception din company din masu gulman abinda ya faru suka yi dip kaman anyi ruwa an dauke,bai saurari kowa ba ya saka kai ya fice securities dinsa suka mara masa baya. He cant believe takanas ya taso dan ya sakata a idanunsa saboda ya kasa samun sukuni amma ta sashi a gaba ta yaba masa magana son ranta.1
Kansa ya dora kan kafadarta cike da damuwa yace “mami tace bata sona,tace ba zata aureni ba.”
Hannunta ta dora bisa kansa tace”haba marwan ka zama namiji mana ka nutsu ka fada min me ya faru.”2
Rintse idanu yayi ya kwashe yanda suka yi da maimunatu ya fada mata,itama nata idon ta rufe tana tunanin yaushe marwan zai bar wannan wutar cikin.1
A hankali ta dago kanshi ta riko fuskansa da hannunta dukka biyu tace dubeni nan marwan bude idonsa yayi me kama da na mahaifinsa ya tsura mata ido mur ta sha tace “yaushe zan fada maka abu kaji? Ina ce nace maka ka barta har sai an nemi iznin iyayenta? Shine kaje ka aiwatar da son ranka ko? Toh madallah sai kaje ka nemawa kanka auren kai da karan kanka.” Ta saki fuskansa tare da kau da kai.1
A matukar rude ya dire guiwowinsa a kasa ya dafa nata yace ” dan Allah mami kiyi min rai na tuba,na bi Allah na biki wallahi ba taurin kai bane na rasa yanda zanyi ne ina tsananin son miemie gashi ta kasa fuskantata mami ya zanyi? Mami dan Allah a dau wani mataki in ba haka zan iya rasa raina ko nutsuwata ” ya fadi haka tare da dora kansa bisa cinyanta yana ji dama hawaye zai zubo masa ko zai ji saukin abinda yake ji.2
Wani tausayinsa ne ya kama mami ta wani bangaren taji ina ma miemie zata ga halin da ta saka marwan kila ta tausaya mishi ta saurareshi,kila hakan zai ankarar da ita tsananin son da Marwan yake yi mata. Ta wani bangaren kuma ba zata so ta ganshi haka ba so vulnerable a ta dalilin soyayyarta ko dan kar tayi amfani da soyayyar wajen cutar dashi.1
Kaman daga sama yace “mami wallahi ba sha’awarta nake ba,sonta nake yi mami zan iya zama da ita ko a yaya take amma taki ganewa mami tace ba zata aureni ba,ba zata hada zuriya da mazinaci ba,mami nafa tuba na tuba mami kullum cikin istigfari nake mami ni kam ma bana iya yiwa wata macen wannan kallon tun a kanta mami,ita kad’ai ne bana iya resisting tabawa….”1
Cikin tausayawa tace “inda matsalar take kenan marwan ka daina taba ta ka daina kai hannunka jikinta ka tabbatar mata da tubanka,har kullum ina gaya maka ka bar wannan halin banzan saboda akwai ranan nadama amma sam baka ji ba yanzu gashi tun ba aje ko ina ba jikinka na gaya maka (ni kam nace bai ma yi nadama ba tukun) yanzu ka kwantar da hankalinka a halin yanzu ina ganin in daddynku bai gana da mahaifinta toh yana gab da ganawa dashi.”2
Da sauri ya dago kanshi fuskarsa fal annuri yace “mami pla kar kice min da wasa kike yi.” Wani harara ta galla masa tace “ashe na dawo abokiyar wasanka.” Shafa suman kansa da yake a saisaye yayi yana murmushi yace “sorry ma’am.”
1
A ranan duk inda maimunatu tayi ma’aikatan company din binta suke da kallo kowa so yake ya san me ta taka tayiwa marwan wannan tijaran kuma har yanzu take cikin ma’aikatar amma babu daman tambayanta tun da ita tun dama can ba wani shaharariyar alaka ne tsakaninta da ma’aikatan wajen ba sosai suke shakkanta wasu na mata kallon mai girman kai wasu kuma na mata kallon miskila tunda tana girmama kowa daidai gwargwado in ka ga mai kushe ta ma is just envious.1
Da dare tana kwance a dakinta tana kallon hotunan auran khalid dake ta trending a internet kiran daddy ya shigo wayarta kan tazo kasa yana nemanta.1
Dogon hijabi ta zira kan kayan baccinta ta fita zuciyarta na dokawa adduanta daya Allah yasa ba uncle sufyan bane ya ballo mata rigima.
A zaune kan 3 seater ta sameshi shi da sarauniyar tasa kamar ko yaushe can gefe ta rakube ta gaishe dasu.2
Gyaran murya daddy yayi yace “mamana dazu da safe nayi baki.” Dan tattare giranta tayi amma bata ce komi ba. Ya cigaba “sun zo min da son samun izni na,na zuwa nemawa yaransu marwan auranki,nace hakan ba wani matsala bane amma su ban lokaci sai na gana dake tunda baki sanar min da zuwansu ba shin ke kika turo su da amincewanki suka zo ko kuwa.”1
Tunda ya ambaci marwan ta gigice dan sam bata taba zaton marwan zai biyo mata ta haka amma in ya san wata bai san wata ba.
A hankali daddy yace “ke nake sauraro maimunatu ” cikin inda inda tace “amm ni dai ni daddy toh ni dai ah ah.” Cikin confusion yace “ban gane ke dai ah ah ba,ki min bayani dalla dalla.”3
Cikin saurin magananta da sai tana rude yake fitowa tace “ni dai daddy bana sonsa…………”
Shiru daddy yayi momy kuma tayi wani mmm tare da tab’e baki ta kawar da kai gefe dan tsab daddy yayi mata bayanin su waye suka zo nemansa
“Mamana me yasa baki son shi?” Kafin ya bayar da amsa mami tayi carab tace “me yasa kuwa banda tana nan tana like da son wancan yaron me shago da ya juye ya koma security ina ganin ma yau ake auransa.” Daddy bai ko kulata ba ya mayar da hankalinsa kan maimunatu sadar da kanta tayi tace “kawai ni dai daddy ban jin sonshi,ban ma fa sanshi ba.”1
Murmushi daddy yayi yace “toh ai neman izni suka zo ba neman aure ba ki bashi dama in kun daidaita toh in kuma baki ji son nashi ba sai ki kawo min wani.”2
Gyada kai kawai tayi tana wasa da yatsunta yace “good,innarki khadija ta kirani a waya wai zato zo ta daukeki ki zaga dangi tunda baki son zumunci da su,me yasa baki kiran kakarki maimuntu?” Dan satar kallon inda momy take tayi ta dan yamutsa fuska tace “daddy in na kirata sai tayi ta amsani wani iri wai ni na cika magana a hankali kuma wai ni bani da hankali bana zuwa dubata,itama din ba son ganina take ba.” Dariya daddy yayi yace”kunyanki mama take ji kasancewar kin san ai mahaifiyarki ce yar fari sai kawunk sadam,sai fitinanniya khadija in kuka hadu zaki sha fada wajenta tun tana yarinya take da fitinar fada mamanki ne dai ba ruwanta sanyin halinta yayi yawa Allah sarki Allah ya haskaka makoncinta ameen.” Tsam mami ta mike dan taga hirar ba nata bane. Da kallo suka bita har ta kulle,daddy yace “yauwaa mamana wani sako sufyan yace zaki bani?” Maimunatu dake zaune bata san lokacin da tayi zaman dirshan ba, da kallon mamaki dady ya bita yace lafiya?” Murmushi ta kakalo tace “amm dama dama kan masu zuwa neman iznin ne.” Ta fada tana kara sadar da kai ita kanta bata san ta inda karyar ta zo ba
Murmushi yayi yace “ja’irar yarinya da kika ce baki san da zuwansu ba,anyway it is all good.” Hira suka cigaba da yi inda daddy yake ta bata labarin mamanta da familynta she cant remember when last suka yi irin hiran nan da daddy.3
Sai wajen 11pm ta mishi sai da safe ta nufi dakinta, wallahi har ga Allah tsoron marwan take ta san shi shu’umin mutum ne u cant guess what he is thinking,da gaske yake yana sonta? In ko da gaske yake sai yayi mata bayanin dalilin da yasa ya tafi ya barta ba tare da ya waiwayeta ba kafin ta yarda da auransa. Teddy bear dinta ta dakko wanda ya bata a 18th birthday dinta ta pressing tsakiya tana sauraron muryan teddy din.3
Rungume teddyn tayi tana murmushi a hankali ta furta “Marwan i so love you i was only laying da nace maka bana sonka,kaine soyayyata and yes na ansa sunan munafukar da ka kirani dan duk bugun zuciyata yana bugawa da soyayyarka ce kawai ina bakin cikin tafiyarka ba tare da ka waiwayeni ba,na kasa amincewa da soyayyarkaka fitar dani a cikin duhu ka bayyana min soyayyarka ta usul ba tare da ka rabi jikina ba dan kai yaren taba jiki shine soyayyar da ka sani.3
Da sassafe marwan ya saka daddy a gaba sai dai ya tuntubi baban maimunatu daddy ya shareshi,haka marwan ya like mishi yana ta magiya ganin ba zai kyaleshi ba ya sashi daukan wayarsa ya kira dadyn miemie a mutunce suka gaisa sannan daddyn marwan ya bukaci jin ko anyiwa marwan din izini murmushi daddyn mimi yayi yace ba laifi marwan din na iya neman yardan yarinya godia yayi mishi suka yi sallama sannan ya dawo da dubansa ga marwan “toh mahaifin yarinya ya amince ka dinga zuwa zance har ka sami amincewar yarinya kafin ayi maganar aure.”1
Marairaice fuska yayi yace “daddy ai na zata kawai kudin aure za a kai wani neman yardanta kuma?” Waro manyan idanunsa daddy yayi yace “ahhahh ban gane kai kudin aure ba,sai kace yar tsana. Auran dole kake so suyiwa yar su?” Fuskarsa cike da damuwa yace “daddy ba auran dole bane tana sona amma taurin kai gareta,sam taki saurarona shi yasa kawai nake son a mana auran in anyi na san zamu shirya.”2
STORY CONTINUES BELOW

“If you are so confident cewan tana sonka toh ka nemi yardanta mana,ni ka ban kunya a man like you dont know how to win a lady’s heart hmm ashe ma duk iya shegen naka na bogi ne tunda ka kasa shawo kan yarinyan da kake so,malam if you really love that girl and u want to make her your woman go and woo her ba ka zo kana bin ta bayan gida ba,so kake a wanke mata a kai maka ba tare da kasha wahala ba? How selfish of you.”1
Kara marairaice fuska marwan yayi daddy ya tabe baki yace “in kana jin yunwa muje table dan ni dai yunwa nake ji.” Girgiza kao yayi yace “ban yi morning work out ba,sai anjima inyi breakfast.” Turare daddy ya fesa jikin jallabiyarsa ya fita a dakin murmushi marwan yayi har kullum daddy da mami na burgeshi yanda kullum suke son impressing juna ji mutumin nan har da wani fesa turare.2
Side din mubeena yayi dan yau yana son ya samu number din miemie,dan knocking kofan yayi sannan ya dan dakata ba a dau lokaci ba tazo ta bude kofar kunnenta makale da ear piece baya raba dayan biyu da muhammad take waya aikin kenan.1
“Habibi will call you,yayana na nemana.” Hannunsa ta riko tace “yayana good morning.” Kanta ya dafa da dayan hannunsa yace “morning auta,dan ban aron wayarki.” Gira daya ta daga tace “wacce a ciki?” Dan jim yayi kafin yace “dukka” shiru tayi tare da rungume wacce take hannunta a kirji tace “ah ah sai dai in baka business line ban da family line.” Dariya yayi yace “shi wannan din fa.” Ta girgiza kai tace “lah! Wannan sirrinmu ne da habibi.” Waro idanuwa yayi yace “ban gane sirrinku ba auta pls dont tell me you guys are doing something bad” ya fada hankalinsa a tashe da sauri ta girgiza kai tace “billahi yayana ba ma wani abu mara kyau ni da muhammad ka yarda dani,ga wayar ma.” Ta mika masa wayar idonta cike da hawaye girgiza mata kai yayi yasa thump dinsa ya dauke hawayen yace “i trust you auta,bar wayanki ki ban business line din.2
Wawakeken dakin nata da ya sha kyau ta koma ta dauko wayar ta bashi ba tare da ta tambayesa me zai yi dashi ba,murmushi yayi mata ya tafi da wayar a hannunsa dakinsa na gidan ya shiga ya fara bincika contact din cikin sa’a yaga *mems sec* ko tantama babu ya san number miemie ne.1
Kwashewa yayi zuwa nashi wayan true caller ya kuma tabbatar masa da number dinta ne galary din wayar ya shiga duk abubuwan ciki is related to aiki cikin sa’a yaga hotuna biyu daya na maimunatu tana ta aukin rubutu daya kuma su biyun ne fuskokinsu dauke da murmushi mubeena tayi musu selfie ba tare da bata lokaci ba ya turasu cikin wayarsa sannan ya mayar mata.1
Maimunatu na zaune kiran marwan ya shigo wayarta tun kafin ta dauka ta san shine saboda true caller kaman ba zata dauka ba ta dai daure ta dauka shiru tayi hakan ya sanar masa da ta san waye a hankali yace “barka da safiya babe.” Dan har da idanu tayi fuskarta dauke da murmushi yayin da ta cika da mamaki marwan ke sauke kansa haka.” Gyaran murya tayi tace mmm kawai2
“Babe kiyi magana mana!” Nan ma shiru tayi bata ce komi ba.
“Shikenan tunda ba zakiyi magana ba zan shigo in ganki anjima.” Sai lokacin tace “marwan nace ka rabu dani pls kar ka zo gareni,wai ana dole ne?” Rintse idanu yayi dan sosai yaji zafin maganganunta yace “kiyi hakuri zan zo,kuma da yardan daddy zan zo.” Ba tace komi ba ta katse kiran dai dai time din da kiran mubeena ya shigo wai zata zo ta dauketa suje gidan adda muflee bata jin fita amma dan ta gujewa marwan ta amince.2
Mufliha tayi farin ciki da ganinsu sosai haka su ikram hira suka sha sosai maimunatu ma ta sake har adda muflihan tayi mata kitso suna zaune ne suna cin abin a kwano daya a tsakar sit room mufliha tace “maimunatu wai ya labarin uncle Tahir ne da fatan kun daidaita?”2
Wani irin kwarewa da mubeena tayi ne ya dawo da hankalinsu gareta sannu suka yi mata maimunatu ta bata ruwa sai da tarin ya lafa tace “ban gane sun daidaita da tahir ba,wani tahir din?” Harara mufliha ta galla mata tace ke ban son iya shege ta kara mayar da hankalinta kan maimunatu ina jinki?”1
Murmushi tayi tana boye face tace “gamu nan dai.” Adda mufliha tace “toh Allah yayi zabi.” Mubeena tace hmm.
Haka suka gama wuninsu wayar maimunatu a kashe saboda kiran da marwan ya dinga mata yasa ta kashe shi kam sarkin yan zuciya ya kulu sosai.3
Bai kara kiranta ba har ranan monday amma fa ka’ida ne zai mata text safe da dare.
Ranan monday tayi lattin zuwa office saboda ta makara tana isa ta samu mubeena zata fita sai cewa tayi “yauwa munari dan kaiwa yayana wannan ki dawo in miki bayanin schedules din yau dan fita zan yi wayarta da jakanta ta ajiye ta ansa sakon tana taradaddin ya zasu kaya da gogan.1
Ba tare da ta damu ta knocking kofarsa ba ta saka kai ciki me zata gani safina ce kwance kan kafadar marwan shi kuma ya saka hannunsa yana shafan kanta zuwa bayanta bakinsa dai dai kunnanta,bude kofar da tayi ne ya jawo hankalinsa ba ta ce komi ta juya ta fita,bata ganin komi idonta wani duhu ne ya mamayeshi zuciyanta baki kirin she cant believe what her eyes just saw. Me yasa marwan bashi da hali ne? Shine har take kokarin bashi wani chance din? Ashe dai bai canja hali ba.2
A cikin wannan yanayin taje ta iske mubeena da wayarta a hannunta ba tare da mubeenan ta lura da halin da take ciki ba tace “Tahir ya kiraki.” Ok kawai maimunatu tace tana kokarin daidaita kanta
“Tahir sonki yake?” Gyada mata kai tayi tace “toh ki rabu dashi.” Cike da mamaki maimunatubta kalleta tace “a bisa wani dalili?” Ba tare da mubeena ta kalleta ba tace “ni dai nace ki rabu dashi!” Cikin tsawa dan ranta a mutukar bace yake tace “baki da right din da zaki ce min ga abinda zan yi a rayuwata,me kuka dauki kanku ne? Pls in baki da tangible reason na cewan in rabu da tahir kar ki kara nanata min kalman.”3
Dan lashe bakinta mubeena tayi kanta a kasa tace “i am sorry in kina ganin na miki shishigi zan gaya miki dalilin da yasa nace ki rabu da Tahir dan shi din guba ne a rayuwarki,Tahir shine mutumin da na fara so nayi kuma dana sanin sanin shi da sonshi saboda shine namijin da ya karbi budurcina ya kuma rabu dani cak numfashin marwan da ya biyo bayan mainunatu ya tsaya…….. “
Waro idanu maimunatu tayi bata san lokacin da ta damko hanun mubeena ba tace cikin rawar murya tace “ban gane ta kawar da budurcinki ba yau mun shiga uku,fyade yayi miki ko mi?”
Girgiza kai mubeena tayi fuskanta dauke da murmushin takaici idonta cike da kwalla tace babu ko daya.
“Kin sani Tahir kanin baban ikram ne ko?” Gyada kai maimunatu tayi cike da zakuwa numfashi ta sauke tace
1
“Alhaji buba daura shine mahaifinsu abokine wajen daddyn mu tare suka yi secondary har university daga baya kuma kowa ya kama aikinsa inda alhaji buba yake aiki a state govt na Katsina yayin da daddy ke aiki a nan Abuja.1
Amma ana ziyarta juna sosai a haka har alhaji buba ya dawo abuja da zama yaransa biyu yah Abdul da Tahir da girmanmu suka dawo abuja inda lokaci daya yah abdul ya nuna yana son adda mufliha iyayenmu sunji dadi sosai ba a jima ba aka sha bikinsu kasancewar ta riga da ta gama makaranta lokacin shima yah abdul din yana aikinsa.1
Ban wani san Tahir ba cos time din yana Australia yana masters dinshi bai tashi zuwa ba sai lokacin bikinsu adda mufli tunda ya kyallara idanunsa akaina shi kenan ya hanani sukuni na san zuwa yanzu kim san cewan Tahir mutum ne me barkwanci da saurin shiga rai tun ina ja mishi aji har nazo na saki jiki dashi muka fara soyayya me zafi.1
Dan Tahir ya rungumeni ko ya pecking dina ba wani abu me wuya bane a wajensa tun ina nokewa har na saba da intimacy din namu ya zamana ko bai rungumeni ba ni zan shiga jikinsa in sakar masa shagwaba iri iri.1
A cikin wannan yanayin ne abin namu ya kara tsamari inda ta kai ta kawo Tahir zai kissing dina son ranshi wani sa’in har hannunsa suyi yawo cikin jikina
Wallahi hakan ba karamin tsoratani yake yi ba amma in na duba yanayin girmansa da kasashen da ya ziyarta da kasashen da yayi karatu sai in ga hakan ba komi bane a wajensa.
1
Wata ranar monday lokacin ina gab da zana finale exams daidai da lokacin da ya rage saura 2 weeks Tahir ya koma makaranta shima ina cikin makaranta yazo ya daukeni,bai zarce dani ko ina ba sai gidan adda mufliha kasancewar sunje bikim suna ita da momynsu Tahir din so gidan babu kowa girki ya sa nayi mana yana tsokana na in munyi aure haka zamu zauna mu biyu a yanzu haka ma jin shi yake kaman munyi aure.1
Bance komi ba banda dariya da nayi bayan na gama girki ina wanke abubuwan da na bata ban ankara ba tsam naji an daukeni bai direni ko ina ba sai dakin dake manne da palon cakulkuli ya fara min ina dariya tare da kokarin zillewa sai da ya kashe min jiki sannan ya fara aika min da wani romance me zafi da kashe jiki.1
Ban ankara ba ya rabani da kayan jikkna tare da nashi kafin in farga da abinda yake yi tuni ya fara neman hanya rokan sa nake yi amma sam bai saurareni ba sai da ya samu biyan buqatarsa.” Ta karasa fadin haka tare da fashewa da wani irin kuka maimunatu ma kuka take yi bakinta na furta innalillahi sabida ji take yi wannan labarin shigen nata.5
Marwan kam notin kansa tuni sun kunce daga kafarsa yayi da niyyar shiga inda suke sai yaji mubeena ta cigaba da fadin” ko kin san tun daga ranan Tahir ya mayar dani kaman matarsa?” In na nuna mishi ban son abinda yake yi sai ya hau fushin ai shi zai aure ni (katuwar kalmar yaudarar kenann Allah ya raba na gari da mugu) shi in banda lokaci ya kure da babu abinda zai hana bai tafi dani a matsayin matarsa ba.1
Haka ya kwashe sauran kwanakinsa yana moreni har ya tafi. Toh sai de me? Yana tafiya sai ya canza min baya kirana ko na kirasa sai ya ga dama ya dauka in kuma ya dauka dai yace min karatu yake yi zai nemi ni toh fa shikenan ba zan sake jin duriyarsa ba.
Wata rana na kirasa sai nayi sa’a ya picking ina mishi magana sai naga kaman ba a cikin hayyacinsa yake ba infact ina iya jiyo saund din kiss in nace kana jina sai yace uhmm? Mmm ke da ga karshe ma sai naji saukar numfashin mace hakan ya nuna min yana tare da wata macen ne ashe Tahir sha’aninsa kawai yake yi ya manta da wata mubeena a irin wannan yanayin ne na gane yazo Nigeria bashi da abin debe kewa ne yace yana sona har ya hillaceni ya samu abinda yake so.
3
Tun daga wannan ranan ban kara bin ta kan Tahir ba na cigaba da sabgogina ina neman tuban Allah nayi kuka har naji ba dadi katsam ba sai na fara ciwon mara ba me azaban radadi ga wani itching da gabana yake yi yana fitar da ruwa me kauri ba nasha anti biotic sai abu yayi kaman ya tafi sai ya dawo gashi banga period dina ba ai sai tsoro ya cikani.2
Ba shiri na nufi general hospital dan ban ma san wani a gida ya fuskanci halin da nake ciki sai aka yi rashin sa’a likitan da zan gani na mijine kallo daya nayi mishi zuciyata tayi wani irin bugawa wani kunyarsa duk ta lullubeni tambayata yayi me ke damuna nace ciwon mara ya tambayeni ko na al’ada ne na girgiza kai toh fa tun daga wannan duk tambayar da yayi min na kasa ansawa yayi yin duniyar nan amma ni mubeena na zama kurma a gaban likita dan wani mugun kwarjini yayi min.2
Karshe dole da nurse ya hadani tayi min tambayoyi sannan taje ta gaya masa tests ya rubuta min naje na yi na dawo na kawo mishi ya dade yana kallon reports din kafin ya dago yana kallona
“Kin taba aurene?” Shine tambayar da yayi min wanda ya hautsina tunanina shikenan ni mubeena yau na yo cikin shege. Cikin rudu na girgiza mishi kai tare da fara hawaye tissue ya cire ya mika min yace “toh meye kuma na kuka daga tambaya? In baki taba aure ba me ya hadaki da STD (sexual transmitted disease) waro idanu nayi na kife kaina jikin table dinsa ina kuka sosai tare da sambatun da ni kaina ban san me nake fada ba da kyar likitan nan ya shawo kaina na fada masa me ya faru ya tausaya min sosqi ya kuma yarda ni ba fasika bace ya dade yana min nasiha tare da nuna min illan abinda na aikata.2
Magunguna ya rubuta min tare da allurai sannan ya ansa number na yace bayan 2 weeks in dawo.
Haka nayi ta shan magani da allurai har na warke ranan da yace in dawo na koma aka kuma yin test inda saura kadab ya rage a jikina kawai ba tare da shawara dani ba yasa wannan nurse din tayi min stitches ko da ta dubani ta fada mishi bana buqata wallahi ba karamin kunya ne ya rufeni ba. Na san taimakona yake sonyi.
1
A haka shakuwa me tsanani ya shiga tsakanina dashi gefe daya soyayyar na nukurkusa na amma bani da yanda zanyi tunda shima bai fito yace yana sona ba har sai da muka kwashi shekara guda dashi sannan ya fada min yana sona yana kuma son in bashi izni ya nemi aurena ban tsaya wani jan aji ba na yarda aka sa auranmu 18 months wanda yau bai fi saura 5 weeks ba.1
Bayan sa auran mu da watanni biyu Tahir ya dawo inda ya tsinci labarin aurena a bakin yayansa ya so ya ci min mutunci da barazanan in ban dawo gareshi ba duk wanda na aura ba ganin mutuncina zai yi ba tatas nayi mishi na huce haushinsa da nake ji ranan shine yanzu zai lallabo yace yana sonki dan ya rainawa kansa hankali dan Allah maimunatu ki rabu da Tahir wallahi bana son abinda zai taba mut….”
3
Bata gama rufe baki ba taji an shakota tare da kyalla mata mari ko kafin ta dawo hayyacinta an jata zuwa office dinta an rufo kofa……Maimunatu kam ma ta kasa fahimtan me ya faru. Girip din da taji na rufe kofar tare da juya mukuli ne ya dawo da ita daga inda ta tafi firgit tayi tare da nufar kofan da sauri.+
Wurgi yayi da ita cikin office din ya fara zare belt tuni ta fara kuka tare da had’e hannunta waje daya amma ta kasa magana haka kuma ta kasa dago ido ta kalleshi sai sheshekan kuka take ta sani yau me kwatan ta a hannun yayanta da ya fi kowa sonta a duniya sai ya shirya.1
Saukan belt taji a jikinta wanda ya sakata gantsarewa tare da zube guiwowinta a kasa ta kwala kara wani dukan ya sakar mata ta rintse idanu tare da toshe bakinta da hannunta gudun kar ta kuma yin kara wani irin tausayinta ne ya dirar masa ya wurgar da belt din yana haki kaman wanda ya daki duniya.
Yana jiyo ihun da maimunatu da magiyar da take mishi na ya bud’e mata kofa. Ba tare da ya kara kallon gefen da mubeena take ba ya bude kofar tare da ture maimunatu gefe ya wuce.
Tabe baki tayi ta shiga ciki da gudu,inda mubeena take durkushe tana kuka ta isa ta dafata shatin belt dinsa ne kwance a kan kafadarta kasancewar dinkin off shoulder ta saka waro idanu tayi a fili tace “lafiyar marwan kuwa?” Rungume juna suka yi suna kuka
Cikin dasashiyar murya mubeena tace” maimuna yayana yana fushi dani,yaya zanyi? Maimuna yayana yana cikin tashin hankali yanzu gashi ba zan iya tunkararsa ba kaicona na zama silar bacin ran dan uwana mafi soyuwa a wajena na bi son zuciya naje na aikata aikin da na sani wanda be kareni da komi ba sai bakin ciki.”
“Shshsh ki bar fadan haka ai dole ya miki is as good as he raped you,kar kuma ki damu da sha’anin yayanki in ya huce sai kije kiyi mishi bayanin raping dinki Tahir yayi tunda ai kin nuna baki so….”
Cikin sauri ta katse maimunatu ta hanyar cewa “in ranan farko rape ne sauran da suka biyo baya fa maimuna? Pls mu daina yaudarar kanmu kawai dan laifi na tafka babban laifi innalillahi yau bacin ran yayane ya rudar dani ina ga wanda shi nayiwa laifi wanda yake da wuta da aljanna? Allah na tuba Allah na tuba Allah ka amshi tubana ka yafe min”ta fashe da kuka tare da kara kullewa jikin maimunatu dake tayata kuka.
Karar wayarta dake can waje kan table din maimunatu ne ya katse har ta share sai kuma ta zabura tare da fashewa da kuka tace “Habibine.”
Zare mata dankwalinta da ya since maimunatu tayi daga kanta tana gyara mata gashinta tace “do you want to talk to him?” Gyada kai tayi tace “na san ya iso yana waje yana jirana ne? Mems ya za ayi in fita a wannan yanayin kowa ya kalleni ya san akwai matsala.
Kafin maimunatu ta bata ansa wayar ta kuma fara ringing mikewa maimunatu tayi taje ta dauko wayar tare da mika mata a hankali ta picking tare da sawa kunnenta cikin muryar kuka tace “habibeeee…” Gyada kai tayi kaman tana gabansa tace “yah marwan ne.” Sai kuma tayi shiru can kuma tace “ka shigo” sannan ta kashe wayar.
Ba ayi minti goma kyakyawa ba sai gashi ya shigo matsakaici ne bashi da tsawo bashi da gajarta yana da dan fadi kadan dan ba siriri bane can idonsa yana dauke da farin glass yana DA kyau dai dai misali kuma sun dace sosai da mubeena.
Hakalinsa sam bai kai ga maimunatu ba da sauri ya isa inda habibiyar tasa take a cikin mini palonta na office din ya zauna a hannun kujeran da take zaune yace “habibty me ya hadaki da yah marwan naga har da duka?” Yana me nuni da shatin belt din dake kafadarta gurin ta kalla da manyan idanunta sannan ta kalle shi da idanun da suka rine suka yi ja suka kuma kara kulu kulu a hankali tace “he knows” tattarw gira yayi yace “ya san me?” A hankali ta limshe ido sannan tace “wancan incident din.” She doesnt have to repeat what incident ya san wanne. Rintse idanu yayi bakinsa na motsi da alama salati yake yi yace “ya aka yi haka? Ba na gaya miki karki karo tuna da wannan abin ba yaya zaki bari har wani yaji?” Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da hannunta tace “kayi hakuri akwai dalili ne.”
“Shine har da duka?” Karyar da wuya tayi tace “he is just been a protective brother,put yourself in his shoe.” Numfashi ya shaka ya fesar sannnan yace “tashi in kaiki gida you re not working or going anywhere today.”
Marairaice face tayi tace “habibi ta yaya zan fita a haka.” Maimunatu da ke shirin fita ta basu waje dan taga alamun sun manta da ita a wajen tace “back door! Kuyi amfani da back door!” Murmushi mai ciwo mubeena tayi mata tace “thanks mems.” Itama murmushin tayi mata tana tausaya mata bata taba ganin lively mubeena a irin wannan yanayi ba sai yau dan ta kwato ta daga fadawa halakan da bata san yayanta ya kusa ya halakar da ita ba.
Waro ido tayi da sauri tace “marwan!” Ai ba shiri ta nufi elevator. Da sauri sauri take tafiya dan tsakanin wing dinsa da nasu akwai tafiya shi yasa ta haura sama kawai ta cigaba da tafiya yanzun ta samu secretary dinsa azaune a mazauninta sabanin dazun da ta zo.
Tayi kokarin dakatar da ita tare da fada mata baya buqatan ganin kowa yanzu.
Wani kallo tayi mata tare da bude kofar office din na sa da sauri ta durkusa saboda wani uban harbi da aka yo da goran ruwa ya wuce cikin reception dinshi waro idanu tayi tare da shiga ciki ta rufo kafar.
Mas’uda(sec) kam daskarewa tayi da mamaki wai me ke faruwa ne yaushe yarinyan nan ta balaga haka me ma ke a tsakaninta da marwan?
Da sauri ta janyi wayarta ta latsa number din yar uwarta safina.
“Ke wannan copper din bata gama service dinta bane?” Daga dayan bangaren sakina ta ja tsaki tace “ai tun dazu nake nemanki in baki labari dazu wai ta zo ta same mu da mr moh ta wani fita a guje shima ya bita abin ya dade yana bani mamaki tunda rungume mace a gaban kowa ba bakon abu bane a wajen shi sai dai in da wani abu a kasa ko kuma tana rage mishi lokaci.”
Humm mas’uda ta sauke numfashu tace “toh da alama kuwa dan yanzu ita ta biyoshi a guje bayan ya dawo ransa a mutukar bace ina ma yarinyan nan magana kinga wani shegen kallo da tayi min? Ke naji kince a rungume,rungumesa kika yi?”
Dariya safina tayi tace “long story auntyna,ai zuwa nayi nace mishi abba yace in fitar da miji ni kuma ban san wa zan fitar ba ai kawai sai na fashe da kuka na fada jikinsa,kin san yana rungume su mubeena tunda kannensa ne nima sai nabi sawu dan jim yayi kafin ya fara lallashina sai wancan uwar kinibibin mubeenan ta shigo duk su biyun sai suka firgice kaman wacce ta kamamu muna wani abu.”
Dariya suka kyalkyale tace “ai ke naga alama ko wani abun za ayi ba zaki hanashi ba.”
Murmushi safina tayi tace ba zaki gane bane.”
Kallon waccce ta shigo yayi ya kau da kai tare da juya baya ya daga kansa sama wallahi har cikin ranta tausayinsa ya tsarga mishi amma bata jin zata barsa haka nan ba tare da ta fargar dashi laifinsa ne ba.
Cikin dauriya tace “ba don mubeena ce a irin wannan halin ba da ina shigowa kyalkyala dariya zanyi in tafa hannu sannan in tambayeka ya kake ji a ranka, sai dai kash mubeena ce and mubeena did nothing but love me unconditionally.” Cikin kakkauran murya me cike da takaici tace “kaga abinda mummunan dabi’arka ya janyo ko? Ka sa hakkin da ka dauka ya fada akan wacce bata san hawa ba bata san sauka ba.” Juyowa yayi yana mata wani mugun kallo tace “yes ka kalleni duk yanda zaka kalleni marwan amma ina kara maimaita maka abinda kayi ne ya dawo maka ya fada kan kanwarka, they funny part wai sai kafi kowa fushi ashe mu ba a sonmu? Iyayenmu ba sonmu suke ba kake lalata mu….” Cikin datse hakora yace “woman i never took your virginity.” Gira daya ta daga tare da harde hannayenta tace “sauran matan da ka kwanta da su fa? Daga sama suka fado ko,ya kake tunanin iyayensu da yayyinsu zasu ji suka san ka aikata abu dasu? Marwan har kullum ina samun signs na kar in aureka i really fear for my kids ba zan aureka ka sasu a halin da ka saka mubeena ba marwan ba zan tab’a iya auranka ba…..”