KISHIYOYINA CHAPTER B KARSHE
washegari ma haka tayi wan nan wahalar tun safe sai yamma ta huta tana son magana amma ta kasa.+
Wajen takwas na dare tana daki tana kallo, zaman d’akin duk ya gundureta don duk ta gaji ya domin da ta fita falo za su daka
mata tsawa suce ta koma daki su sa’annin ta ne.
Tana zaune gungurungun kallon kawai ta ke amma tunani ne fal a ranta, dangane da yanda zaman gidan ya zame mata tamkar gidan yari.
Haka ta gaji da kallon ta kwanta, hartai shirin kwanciya ta sa kayan baccinta ta kwanta akan a kan gado gashinta da ke tsefe ta cire ribom ya Barbazu a gadon bayanta, fuskarta tai fiyau ta yi kyau.
Taku yayi a hankali ya tsaya a kanta yana k’arewa surarta kallo ta bashi sha’awa ainun, sake matsawa yayi har kusa gadon ya zauna gefe, har lokacin ta lula cikin tunani ba ta san yana dakin ba, hannunsa yakai zai shafa gashinta se ya d’auke ,a razane ta d’ago suka had’a ido da Alhaji, da sauri ta ta tashi zaune tai baya ta jingina da gadon.
“Zahra”
Ya fada yana mai bin sassan jikinta da kallo.
Tsuma jikinra ya fara yi cike da tsoro ta dago dara-daran idonuwanta ta sauke a nasa, da sauri ta sunkuyar da kai cike da tsoro.
Murmushi yayi sakamakon yanda yaga ta tsure. “Zahra me ke faruwane? ina dalilin guduna da kike yi kamar wani dodo, sam kinki bani hadin kai ni mijinki ne fa zahra, kinsan ina da hak’ki akanki haba zahra baby.”
Ta kalle shi idonta na kokarin kawo ruwa “Aa ni kawai ka rabu da ni, ba na son zaman gidan nan , bana jin dadi sai ga hawaye sharrr!!
“Assha! Zahra bar kuka ni ne ko? Ya fada yana mai matsawa kusa da ita.
Ta shi tai da sauri zata shiga toilet yadan jawo rigarta, ta tsaya tare da runtse ido ina zatakai kunyane shi yana babba yana ma yarinya kamarta hakan sai ta kankame jikinta, rungumeta yayi tsam! Ajikinsa, ta hau k’ok’arin
kwacewa.
Murmushu yayi yace “haba zahra nine fa mijinki oya ki sadaukarmini da kanki “
Jikinta ne ya hau rawa tasanya kuka, ” ka yi hakuri ni ba zan iya ba, girman shekarunka yayi min yawa matsayina na karamar yarinya.”
A kunne ya rada mata “waya gaya miki ai namiji baya wa mace tsufa”
Kuka ta fashe da shi,
sakinta ya yi tare da juyawa “zahra kenan
ga wannan” ya dauko ledar da yaaje a kan stool ya mika mata ledar ya fita , jikinta se rawa
ya keyi ta dawo ta zauna.
Alhaji bayan ya koma d’akinsa ya zauna ya dafe kai, haka
Allah ke jarraba bayinsa, shi kam ya ze da k’aunar yarinyr da take kamar jikar sa, dole ya san yanda ze yi yana son kad’aicewa
da ita. Allah ya gani ‘ya’ya ya keso be sani ba ko Allah
ya bashi ta b’angaren ta rok’on Allah ya shiga yi. Domin ayanda yake ji a yanzu ba zai iya k’yale zahra ba, ga matansa ya san duk irin abinda suke mata, amman yakanji ya kasa tabuka komai ba damar yayi magana, amma dole yad’au mataki ya kula suke dada tunzura ta, don da mutuncinsa ba za su zubar masa ba. Ta shi yayi ya mike ya fita dan aiwatar da kudirunsa
STORY CONTINUES BELOW

Babban falo ya fita ya tara Mutan gidan Matansu da
mazansu,ya sa aka kirawo Zahra itama, sai da ta jima sannn ta je, suna zaune duk sunyi jigum- jigum yayi gyaran murya
Hak’ika ba na ji dad’in abinda
akewa zahra a gidan nan, duk da ba ita ta gayamin ba, ni da kaina na fahimta.
To ku sani daga yau na kafa dokar kar wanda ya k’ara sa ta aiki.”
Huci hajiya uwani ta farayi da yake ta fisu bala’i ya ci gaba, “san nan yan ciranin gidan (wato yaran
gidan) ku kuma kowaccen ku wallahi karta kuskura ta kara raina mun mata, muddin na same ku da hakan to kowacce ta koma gidan iyayenta.
Ya nuna su hajia “kunga wad’annan matan! to daidai take da su, yanda za’a basu
girma hakan za abata.”
Hajia zainab tai caraf tace “Alhaji ba zata
sab’uba, yanzu kamar mu kazo kana mana ka shedi akan wannan figalalliyar! Yarinyar har kana daidaita matsayinmu da nata har yaushe tazo duniyar?
Wani kallo yayi mata “na yi! din zainab, ki sani matata ce itama ai na de gaya muku wallahi duk wacce takarya dokar abunda nace wallahi zan d’au Mummunan mataki akanta.” Ya fada afusace.
Hajia Magajiya cikin k’unar rai “lalle Alhaji yanzu abin naka harya kai hakan! ka nuna tafi mu ko?”
Yace “wan nan kuma fad’ar kice, na de gaya muku wallahi zan iya sallamarku
d’aya bayan d’aya akanta”
Cikin zaro ido tare da dafe kirji hajia zainab tace “kai! Alhaji” yace “tabbas!” hajia uwani ce tai Murmushin yaudara “to Alhaji ai abin be kai da hakaba ai Zahra kamar ‘yar cikin mu ce ,insha Allahu za’a kiyaye” kasan yarinyar ta fiya duhun kai sam!ta kasa sakewa da mu”
“Da ya fi muku” ya fada a fusace ya tashi yabar gun.
Ganin ficewarsa daga dakin cikin daka tsawa hajia zainab ta kalli yaran gidan kowacce ta tashi ta basu guri, sum -sum suka bar gun.Zahra kam mik’e wa tai tare da gyara rigarta tana Murmushi tai gaba. Magajia ta bita da kallo tare da k’wafa”
lalle Alhaji zaisan giwar da ya taka.”
Cikin k’arfin hali Hjy zainab
ta tashi tsaye “ba muga ta zama ba wallah kunga yarinyar nan, hmm! d’an hakin daka rena shikan tsokanema ido ,tabbs idan muka kyale muna gani zata mamaye gidan nan mu gashi ba haihuwaba, wallah da ta fara haihuwa se mun rena kan mu” suka ce mun “tabbas!” Zama tai kan bakin kujera shawarar dazan fad’a wallahi dole mud’au mataki, ku de kubar komi
a hannuna da zafi- zafi a kan bugi k’arfe, zanje gun malam me zararota, nan sukai naam da sha warar…
Yauma kamar kullum zahra na daki wajen 9pm ta nutsu wani film take kallo da ake haskawa a tashar arewa24 Jitai an bud’e k’ofa ko kallon gun batai ba dan ta san Alhji ne ya shigo, shi ma ba tare da ya kalleta ba, ya juya ya sa key a kofar ya karasa dakin rike da ledodi a hannunsa ya zauna kusa da ita, kamshin turarensa ne ya sa ta san yana dab da ita, maatsawa tai gefe da sauri, murmushi yayi ya bud’e ledar ya zaro waya sabuwa dal kirar ipon6 ya bata, tak’i karb’a ya aje bakin gado d’ayar ledar kuma less ne masu kyau da atampha har da Jaguard voil sun hadu sossi, tab’e baki tai ta juya.
“Zahra ga kaya nan ga kuma waya sabuwa nan” ta juyo “banso ni ka kyaleni”
“Haba zahra nifa Mijinki ne”,
STORY CONTINUES BELOW

yanzu A matsayinka na tamkar mahaifina wallahi an kassara rayuwata ta fashe da kuka yace
“tsoho da kudi ai yaro ne, ina so zahra ki zama yarinya mai biyayya hakan da kike kamar bijirewa Allah kike da mahaifinki.” Ya fada tarw da rikw hannunta ya kama
ta fusge da sauri ta miki, tai hanyar toilet cikin murmushi ya kauda idonsa daga binta da yayi da kallon, don yanaji yau kotak’i ko taso seya kwashi lada, sai ya gyara tsufansa, gam ta rufe tailet din ta tsayatanajiran ya fita.
Mukulli ya sa ya bude toiket din, ta kwalla k’ara , hannunta ya ja ya fito da ita tana kuka wiwi don takula tsohon nan da shirinsa yazo.
Hajia uwani ce taji kararta domin d’akinta na kusa dana ta, ta side din baya , tashi tai domin dama taga lokacin da Alhaji ya shiga wajen zahra.
Wani turnikin kishine ya turnik’eta “lalle ma Alhaji, futowa tai tazo ta tsaya wajen bakin k’ofa sautin Muryarsa takeji nan ta tsaya tana huci, shi kam
Alhaji a lokacin so yake kawai hakansa ya cimma ruwa, amma zahra se fizge- fizge take da kuka ,tana cewa “ba huruminka ba ne cikin jin
haushi ya tashi yace”
Zahra ko kin san mala’iku na tsine
miki? yanzu hak inde ba ki yarda ba.
ko kulashi bataiba kukanta take Kawai daga bisani ta ce “amma ai ina da wanda nakeso kawai ka sa aka rabani da shi”
Cike da kishin ta kira sunan ya d’auko waya yace “bari na kira Mahaifinki na shaida mai irin tijarar da kike min” cikin zaro ido ta nuna alamar ba taso tare da k’ara fasa kuka. Murmushi yayi.Ya fasa kiran.
A hakan
Alhaji ya samu loganta tana kuka da bata so haka alhaji ya shiga duniyarta.
Hajia uwani anan ta kare tsaye sai yarfe gumi take dan ta riga tasan me afkuwa ta afku se fareti tamkar ‘yar sanda.
. Zahra kam tasha wahala ba kadan ba don har
Karamin suma tai. Alhaji ko wata iriyar nutsuwa ce ta shige shi ya samu nishadi sosai tattare da zahra, ita ko tun bayan kammaluwar komai take kuka har wannan lokacin da aka sallahr asuba har yayi bacci ya tashi ita ko runtsawa batai ba.
Alhaji
yayi lallashin amma a banza kod ya dawo daga masallaci yaga ta gyara jikinta , sai hawaye dake faman sirnanowa a fuskarta, haushinsa kawai ta ke ji.
Gari na dan fisha!!Hajia Uwani ta shigo d’akin ta tab’e baki “wai ni Alhaji bata da lafiyane
ne? Tun jiya nake jin kukanta”
“In ina ya hau yi “eh ba bata da lafiya ne” a yatsine ta kalli Zahra tai hanyar waje, zuciyarta kamar an watsa ta hot watar. Alhaji kam ya rasa yanda ze da Zahra dan ji yayi ta dada kwanta mai zuciya,cikin kunar rai ta kalleshi “cikin kuka tace wallahi ba zan tab’a sonka ba ka cuceni”
yace “zahra ni kike gayawa wannan maganar? da
girmana kike gaya min hakan”
Tsaki ta saki tare da mikewa tai zata fita duk da yanayin tafiyar da take a hankali ce kamar me ciwon kafa, komawa tai ta zauna ta ci gaba da kuka,tsayawakawai yayi yana kallonta sonta na kara huda zuciyarsa.
Hajja uwani ce ta sami Magajiya a d’akinta tace .
Muna nan bono no Alhaji har yayi d’anyn aiki fa”
Dafe
kirji tai “wallah idan mukai sake sekin ganta da ciki, waya sukaiwa hajja zainab shigowa tai da alama Unguwa zata nan suka fesa
mata tace “ku barni dasu yanzu gidan Hajia Rukayya xzani zamu gun malamin nan”
“D yafi de” inji Magajiya.
Hakan kuwa Hjy Zainab ta je gidan Hjy rukayyaa suka rankaya gun malami,bayan zuwan su suka sheda mai bukatarsu yace “kun kawo kuka gidan mutuwa,gyara zama yayi ya kallesu “yanzu Hjy me
ki keso A yi?”
“Malam yarinyr nan tun da tazo Alhaji Ya maidamu
Borori, don a kanta ma yace zai iya rabuwa damu,san nan muna tsoron ta samu ciki.”
Yace ‘ba damuwa yanzu zan ba ku magani ku tabbatar taci! to da wuya ta samu ciki, sannan zan muku aiki yanda zaku mallake ita yarinyar se abinda kuka ce tai shi za tai.San nan ku sani Alhaji na sonta so me yawa Dole sai kun hada da makircinku na mata.”
Godiya
sukai meyawa suka dire mai kud’i ,ya damk’e kud’in nan yana washe baki tamkar gonar Auduga,su Hajia da k’warinsu suka tafi,
tana komawa gida ,suka taru a d’akinta, nan ta zayyane musu komai, magajiya ta rangada guda, sannan guda suka tafa tashi hajia tai tana dariya
“bari na tafi na gudanar da aiki na farko, na yi alkawarin ko zan yawa tsirara saina daidaita zamantakewarsu.
To fh muje zuwa akwai sauran rina akaba.
Direct hajiya kitchen ta yi, sai wake- wakenta ta keyi, farfesu ta had’awa Zahra me dadi tab’ar bad’eshi da Maganinta wanda boka ya bata, bayan
ta gama tai murmushi tai d’akinta,kiran Amira tai take shaida mata takaiwa zahra don Alhaji ne yace ta dafa mata, ta kalleta
“ki tabbatar taci fa! don na ga ke kuna d’asawa da’ita” d’auka Amira
tai taje dakin Zahra shiga tai da sallama ganin zahra tai akan gado ta k’udundune zama tai tana mata sannu dago ido tai
takalli Amira a zuciyrta tace lallema tsohon nan yaje ya wani barbazata k’wafa tai tashi zaune tai, ta ce “Amira yaya dai?+
Abincin ta bata tace “gashi
kici,naga baki fito bane tun da safe shiisa nai miki ferfusu” karb’a tai da godiya, kallon dakin tai ta ce bari na tayaki gyara ma d’akin, ganin hakan yasa ta danji k’warin jikinta ,ta danci farfesun kad’an
godiya taiwa Ameera bayan ta gama, ita kuma ta fita, bacci ne yayi awon gaba da ita se wajen 4 ta tashi ta jita garau k’arashe farfesun nan tai
Alhaji ne da daddare ya dawo ya kasa shiga bangarenta, don yasan yayi mata lefi ,haka dai ya kunna kai tana kan sallaya ,ya zauna yana mata ya jiki tare da tarin kuma jin shaawarta, kallon tara saura kwata tai mai tare da tab’e baki yace “zahra ki denai min abinda kike mun, waike bakya yarda da k’addara ne? ki yarda Allah ne ya tsara nine mijinki duk da tsufana”
Cikin k’unar rai ta dago “Aa waallahi,baka san waceni ba baka san kalata ni kawai a rabu dani”
“subhannallah! zahra da ilminki kike ambatar na rabu dake? Kin manta babu kyau ma,mace ta ce miji ta saketa meke yawo akankine?
“Saboda ba mu
dace da juna ba”
“Zahra ki yarda da ni, ina k’aunar ki ni Masoyinkine wallqh koda yaron kika Aura ba lalle ya soki yanda nake sonki ba” ya fada na sanyin zuciya. Ganin ba zatai magana ba, ya ajje mata bak’ar leda “gashi kici” kallon Ledar tai dashi da sauri tad’au ledar ta watsamai ajiki duk
abubuwan ciki ya b’ata mai kayansa, kallonta yayi yace “Zahra! ta kalleshi “d’aya ma kenan!” yace “ban zaci haka daga gareki ba saboda nasan kina da tarbiya”
kallonsa tai “da kenan amma tunda kai nasarar Aurena na canja hali”
Cikin bak’in ciki ya tashi a fusace ya wuce d’akinsa ya shiga ya dafe kai rokon Allah yake yasa ya cinye Jarrabawar da Allah ya d’ora mai…………….
Washegari!! wajen k’arfe goma na safe Auta
da Aminu suka zo, farko da suka shigo Auta ce agaba Nadiya na kallo a falo ,ta kallesu “ku kuma daga ina wa kuke nema?”
Auta tace “Anty zahra man”,tace “au ho ashe! anzo kwadayine”
Aminu da yake
akwai zuciya yace Allah ya sawwake mi kwadayi”
Ta taso kamar takarye “kai ni za,kaiwa
rashin kunya?”
STORY CONTINUES BELOW

Sama da kasa ya kalletaya tabe baki “see you.”
Zata kuma magama Auta taja shi sukai ciki zahra ce ta fito falon don ta dan dafa abinda zataci, da sauri Auta ta rungume ta tana “yaya zahra” Aminu murmushi ya fara yi zahra kam kamar ta daka tsalle se murna take ,jansu tai da kinta ta kawo musu lemuka
suka zauna suna ta hira ,fita tai jikinta har rawa yake (dan uwa kenan rabin jiki). .
kitchen ta shiga da sauri. Ta dafa indomie da kifin gwangwani ,da kayan lambu se tashin kamshi take tamkar ba indomie ba, Nadiya ce tazo kitchen din t tsaya domin indomien ya bata sha’awa ,da gadara ta dauko fillet zata diba zahra ta doke hannunta nan suka fara fada,da taga ba yanda zatai ta kyaleta ta hakura, da sauri zahra ta juye tai daki da murmushi ta Zauna janyo Auta tai jikinta “hoo my sis nayi missing dinku” Aminu se sunkwi dakai
yake ,ta kalleshi “yau kuma kunyata akeji”
Dariya yayi “ya zahra kin zama
Antyna yanzu”dariya tasa ,”ina baba da su Goggo su ya Atiku yace “duk suna kalau” sunci abincinsu tare se taji
duk bakin cikin ta ya yaye.Bayan sun gama sunata
kallo abinsu suna hira. Tsigai ce ta banko kofar dakin ta tsaya tsegege
“ke kizo inji su hajja” kallon banza zahra tai mata se kizo
ki jani kuma kifita” tsaki tayi ta fita da sauri. Aminu yace”Anty wace
wannan?
tace “a gidan take” dariya yasa. “Amma ta renaki” tace kyalesu ba yanda za suyi da ni”
Ganin kamar ba zata je ba yace kije man, dan jim tai sai kawai ta ce bari naje naji da wacce suka zo ta shi tai ta fita . . . . .
Falon ta shiga ganin su tai birjik tai sun cika mata ido, tafiya ta canja don nuna musu ba tsoro taje kan kujera d’aya ta
Zauna kallon -kallo suka yi daga bisani suka farai mata kashedi
tana jinsu ta tab’e baki tana girgiza kafa.
Sallama akwai wani garjejan saurayi ne ya shigo falon ya
Hankado hula gaban goshinsa irinta matasan zamani, hajja uwani ta washe baki “Aa wa nake gani kamar hamid” yace “nine”
se yau ka ga damar
dawo mana?”
Yace “wallahi aikine ya rike ni”
Nadiya tun da ta ganshi ta rikice se wani fari take mai da sun hada ido, jikinta har rawa yake, sosai nadiya ke mutuwar son hamid amma bai taba nunawa yasan tana yi ba, zama yayi a falon suna hira.
Ta gefe kuma su magajiya sun ci gaba da -tsatstsagewa zahra, magajia ce tace “wallahi
ki kiyayemu! Dan ba zaki zo gidanmu kina mana rashin ta ido ba har yaushe daren yayi ballentana gari ya waye.
Ta kallesu idan kun gama ina da abunyi” takaici yasa suka kasa magana,cikin fusata uwani ta janyota suka mammaketa “gaba ma kya karai mana tsiwa”
kuka tasa t ta wuce dakinta hajia uwani tace “tabdi munyi sake se kallon hjja z inab sukai “wai ya labar ne? dariya tasa dad’ina da ku gajen
hkr.
“Nadiyace tace”kuma hjia munce kubarmu da ita
amma kunki wallah Da tuni mun gyara mata zama tayi waje ,wai sai kuce saboda Alhaji”
suka ce “ai yaki d’an zamba ne” wallah ko tsigai sai tai mata duka. Amira dake tsifa tai dariya saboda tasan
itama Nadiya ba shara wa zatai ba balle tsigai.
Hamid ne ya kallesu waini wace wannan ne?
Hjy tace “ai Matar Alhaji ce”
tabe baki yayi “shima de Alhaji wannan ay jikarsa ce, da ganinta ba zata fi 18 ba”
kai ma ka fada inji Nadiya
Sai wajen yamma su Auta suka fito zasu tafi sun fi to se dariya suke
zahra ta canja kwalliya tai kyau abinta ta kafa dogon
takalminta tafito da gashinta ta gefe har kasan habarta ta kashe dauri bakin nan yasha jambaki red, kamar ‘yar tsana
siket Din ya zauna d’as! ajikinta tana sane ta canja tafiya sunzo dai de
da su dama da gangan tai wannan kwalliya don ta k’ular dasu ne. Nadiyace ta saki baki, sannanta ja waani dogon tsaki.
sukansu su hajiya mamaki suke dama haka zahra ta ke, hamid ko kasa dauke ido yayi akanta lalle dole alhaji ya rude shi kansa ta birgeshi.
bayan ta rakasu ta bawa su sako su kaiwa mamanta, sai taji kamar ta bi Azuciarta tace ai a kusa dawowa ,don na sha
Alwashi sena Auri yaro daidaini ta dawo ta wuce su ,ko kallo ba su isheta ba tai hanyar side dinta Wani wawan numfashi suka saki.
Nadiya tace Allah hjia ku tashi tsaye wallahi kun sakar mata da yawa wallahi kuna zaune zata kwace gidan nan mu kan mu mun kad’e”
Sam sun kasa magana kawai domin kowacce akwai abinda take ayyanawa aranta, shi kam Hamid dakin daya ke sauka ya shige.A zuciarsa yana gskya Alhaji ya
iya zabe tab! koshi da ya ke yaro ba lalle ya samu kamar wannan yarinyr ba,lalle ya yarda da Maganar hausawa da suka ce
tsoho da kudi yaro ne…….
Saida zahra tai kwana biyu sannan alhaji ya waiwayeta ranar ma haka suka sha danbarwa karshe ta hakura, tun zahra na turjiya idan zai amshi hakkinsa, har ta hakura ganin babu sarki sai Allah abun bana kare ba ne.+
Cikin lokaci kankani ya shiga nunawa zahra soyayya kala kala ita kanta tasan tana samun farinciki ta bangarensa, nan da nan ta canja, kota ina kyautata mata yake hakan ya sa ta dan fara rage wasu abubuwan, ta bangarenta da matansa kuwa sai ma abinda yayi gaba. Domin sun tsananta mata
Ba ta isa ta fito falo tai walwala ba, kullum tana daki sai de bata daukan raini, kullum zata fita ta gaidasu idan suna falo bata damuwa Da irin kallon Da suke Mata na wulakanci sai de don ta basu girmansu.A matsayinsu na manyanta.
Da Ameera kawai suke shiri itama ba koyaushe ba sai de tana zuwa suyi hira.
Yau Da rana Alhaji ya dawo da yake a dakin Zahra yake ya zarce tana zaune ta kirawa tv ido Amma yanayin ta ya nuna akwai damuwa aranta.Zahra ya ambata ta d’ago ido ta kauda kai.
Ta gefenta ya zauna,ya ce “meye matsalarki zahra” tace ni kawai na koma gidan mu”
zahra inde wan nan zancen ne sai de kiyi hakuri ya tashi ya fita
Uwani Da magajiya ne a falon kadai ganin sa yasa suka kalli juna wato ranar girkinta ma har zuwa yake da rana. Uwani tace barmu Da su ai munkusa shawo kan lamarin.
Ni sam aikin ma da muke akansu kamar baya tasiri fa, magajiya ta ce nima dai haka na gani, ba mamaki zainab cin kudinmu take, yo wanne mamaki kishiya ce fa, magajiya ta ce hmmm an mun kwatancen wani wani zanje gobe gwanda a hada karfi ba a tsaya a waje daya ba.
Ai tunda ban haihu ba babu wacce ta isa ta haihu agidan nan ta fada a zuciyarta
STORY CONTINUES BELOW

Washegari Hjy magajiya ta tafi gun boka na gangare ba layi yasa ta tusa kai boka yayi dariya meke tafe dake almura”.
Gyara zama tai ta ce “ai boka kishiya garemu” ya tsaida ita “ba sai kin k’arasa ba, aiki bazai tasiri kanta ba saboda tana yawan adduan tsari shiisa duk wani aiki da za kuyi akanta bazai tasiri ba .Amma kisan lokacin Da bata sallah ki gayan” sai nayi aiki akai, zamu sanya mata shiririta yqnda zata kasa addua ma.
Gyada kai tai “tom boka sann sauran kishiyoyina ina so na mulkesu yanda kowacce zata ji maganta. Sannan ai wani abu ta bangaren alhaji da amaryarsa, yanda zai dena kulata.”
“Duk wannan ba komai ba ne ke de ajje kudi kawai, nan ko cike da munanan kuduri ta ajiye ta tafi.
kwana biyu tsakani sai dakon Zahra suke ganin ko bata sallah sai ayau tsigai ta gano musu ai ba shiri Hjy magajiya taima boka waya a take yayi aiki na mallake zahra wato duk abinda sukace ba zata musa ba Sannan ya bata tsakaninta da alhaji,kuma ya tabbatar mata aiki yaci kamar yankan wuka.
Zahra ce kwance saman gadonta tana dan
Latsa wayarta jitai an watso mata ruwa duka jikinta wani sanyi ya ratsa ta, da sauri ta tashi, inuwa ta gani akanta daga kan tai taga hajiyoyin ganin kowacce fuskarta ba Annuri, cakumota magajiya tai ta nuna mata waje ,cike da
tsoro ta tashi don yau kawai jitai tana jin tsoronsu karamin falon suka tsaya duk jikinta na d’igar ruwa.
“daga yau zaki koma yin aikin gidan nan wato alhaji y daure miki kiyi abinda kike so, to ki sani,dokar alhaji ta kau,
a k’allah kin doshi wata 3 a gidan nan in banda rashin mutunci ba abinda kike, to da sake oya muje dama aikin ai ba bakonki ba ne, suka tasa ta a har kitchen dole ta fara goge -goge da wanke wanke, cikin karfin
hali tace” amma hajia ai an dawo da masu aikin naga ko?
STORY CONTINUES BELOW

Hajia uwani ce ta daka mata tsawa “ke meye aikinki, ba,kinyi nasarar shigowa cikinmu ba ? walllahi da k’afa fuwanki zaki bar
gidan nan”
Wasu hawayene suka zubo mata, sam yau ta rasa gane kanta mugun tsoronsu take ji (asiri gaskiyar me shi) nan tadau wajen rabin awa tana aiki har ta gama, a lokacin sun barbaje a falo tazo tace”
ta gama hajia tace ” sai kizo ki goge falo” guga ta hau hi kamar me aiki ,duk ta gaji, bayan ta gama suka ce taje kitchen tai
girki,ta juya zata hajja zainab ta dakatar da ita “kinga wannan aikin daki kai to ko yaushe shine aikinki kina jina?” tace
eh da sauri ta shiga kitchen ta fara hada Girki.
shewa suka suka kalli Hjy magajiya “yar gari ashe kin samo mana mafutar”
“yo ni wasa ce kusa ido kuyi kallo har shi alhajin sai ta dena ganinsa.”
Shiru sukai ganin hamid ya fito.
Kitchen din ya shiga zai dau kofi ganin zahra kawai sai ya tsaya yana kallonta
kamar maye zuciyarsa na raya mai abubuwa kala kala.
Alamun jitai ana kallonta d’ago ido tai ta juya bakin kofa takalleshu ta maida kanta.
Jinjina kai yayi ya fita ya zauna falo suna hira da su hajia ,tunanin sa duk ya tafi gun zahra shi kam yarinyr na
birgeshi, da sauri ya daki kansa sakamkaon tunowar da yayi matar aure ce fa.
.
Bayan ta gama aikace-
aikacenta, ba tai d’aki ba se tai hanyar waje gun fulawowi dake bayan d’akunan su taje ta zauna ,tunani take kala-kala,hawaye sharrr har ga Allah bata son Auren Alhajin nan,ga matansa se takura mata suke ya zatai.Wayarta ta dauka ta shiga whtsap wani group ta shiga hirarsu ya d’au hankalinta nan tamanta ma da b’acin ran data ke ciki,tayi nisa har d’an murmushi take yi.
STORY CONTINUES BELOW

Hon d’in mota taji daga kanta tai taga alhaji ne, sai tamaida kanta. Shiko Alhaji ne yazo wucewa ya ganta zaune jikinsa har b’ari yake yana kiran “yarinyata zahra kina nan”
Batai magana ba, ta dai kau da kai , zama yayi kusa da ita dago sai ta kalleshi duk sai ta diririce a dakile tai mai sanmu da zuwa ta tashi tabar wajen yana kiranta ko inda yake bata kuma kalla ba idan da sabo ya saba kam ,jiki a sanyaye ya tashi
ya shiga falon Allah sarki Alhaji .
Itako haushinsa nke ya dada cikata aganinta kawai da saninsa ake mata cin kashi a gidansa.
Har wajen karfe takwas na dare zahra na kitchen ,ta naiwa hajia wainar fulawa don de abata
wahala.Tsigai ce ta tawo kamar zata karye ,bude cooler tai ta debi abinci shirgege ta kalli zahra tai waje, dariyace tazo mata,”
tace “Acici kawai ci ba kiba asarar dawa” bayan ta gama takai ma hajiya magajiya, ta kalleta seki bamu guri ki tafi daki kar naga kafarki afalo da rawar jiki ta ta tafi,tana shiga tai wanka
tai sallah ta kunna kallonta kasa kallon tai ta kashe
ta dauko wayarta ta hau whtsap,jitai ana knocking kofa tai burus tasan
Alhaji ne ,waya ya bugo ta basar ,haka yagaji ya kyaleta,sai chating dinta take, don group din data ke sun saba da wata biyota
Private tai sunata hira sunanta BILKISu jinin su ya hadu sun dade suna hira ta sauka.
Bayan kwana biyu.
Sam Alhaji yanzu ko kofar dakin zahra baya zuwa domin kwata iwata ji yayi ta fice mai arai sha’awarta ma ya daina ji aransa.
Abin ya so ya dameta abubuwa goma da ashirin sun,hadewa zahra bata jin dadi kota’ina, sai yanzu ta fahimta ashe kulawa da nace mata da alhaji yayi alkairi,ne agareta sai yanzu daya shareta take jin ta dada takura. Hakan yasa kallo daya zakai mata kaga ta rame.
STORY CONTINUES BELOW

Yauma kamar kullum
tasha aiki,tamkar jaka dan har dakunan su ta share ta
gyara, da gangan su Nadiya zasu zubar daa abu don ta
gyara,yau taga ma da wuri wanka taje tai kafin da yamma taci gaba,
kayanta mekyau tasa wani material purple yakarb’eta sosa, falo ta fito zata wuce waje,hajia magajia ce da zainab don hajja uwani bata nan
wani tsawa suka dako mata take kirjinta ya buga,”zonan” da sauri ta tsugunna “wannan uwar kwalliyr fa munafuka?”
“yi kawai na yi
ta fada kanta a sunkuye, “to maza- maza kije ki cire ke in banda abinki har kina da time na kwalliya ,to bud’e kunne kijini da kyau,daga yau kar na kuma ganinki da Super Holland ,ko shadda material da sauransu ,kod’add’un kaya zakina sawa ko
dogwayen Riguna,munafuka me suffar aljanu ,salan ki fita Alhaji na shigowa yayi ido hudu dake,rank’washi magajia takai mata wallhi da k’afafuwanki sekin bar gidan nan mayya,wollahi muna gidan nan ba waccce ta isa ta haihu da Alhaji.”
Da sauri ta taashi cikin hawaye tai daki tare da takaici a zuciarta cire
kayan tai ,tasa wani ,fasa fitowa tai ta kwanta in banda
tunani ba abunda take ,sai tutano ummanta take,tana son zuwa amma babanta yace setai 6 month zata fara fita ,kayanta ta dauko
ta ware masu kyan tabar tsoffin ,wayarta ce tai kara
sunan billy ta gani ,dauka tai suna hira sun gaisa
ta kashe,danne-danne take sai taga nomber din Salim ,mamaki k’arara ya kamata,
wani wawan murmushi ta saki ,cikin karkarwa ta kira shi bugu daya biyu ya daga begane nomber din ba,se ya kashe haushi ya kamata tana son jin information akan salim amma ba dama
Kuma bugawa tayi ya dauka, “da wa nake magana ya fada, cike da sanyin jiki tace “zahra ce.”
Wacece zahra kuma”
Salim kamanta da ni ko?
“Wait bansan wata zahra ba, ina ga kin b’atan layi ne”
” hmm karka cemin haka nasan ka ganeni ka fito a salim dinka mi magana.”
“Zahra na gane ki shikenan, ko kin manta kina da aure ne please ki sa aranki ba ki taba sanina ba kin gane, ni a bangarena na shafe babinki, don na samu madadinki” kit ya kshe wayar.
Kurawa wayar ido tai jikinta na rawa, wani irin kuka ne ya zubo mata tana so tai tunani abubuwa sun cunkushe aranta.
‘Ashe! daman abinda ake fada akan maza hakane! Take burunta ya canja farat daya.
Alhaji ne zaune a cikin mota da alama gida zai koma sai tunani yake, abubuwa sun taru sun mai yawa kuma duk akan zahra, alamuranta duk sun fice mai arai ko kallonta bi san yi a yanzu
To fah
Daga nan direct alhaji gidan wani malami abokinsa ya je duk ya sanar mai yanayin halin da yake ciki na kuncin rai, kan ataimaka mai da addua hakan ko akai ya bashi adduoi sannan ya ce in sha Allahu zai binciki kan lamarin, kuma zai sa a sauke mai alqurani nan suka sallama ya tafi.
+
Yauma kamar kullum ta b’angaren Zahra na ta fama
da aikace aikacenta da ta saba tamkar jaka ta gaji lik’iss,d’akinta ta shiga tana shirin yin wanka Amira ta shigo bayan sun gaisa
tace “hajiya na kiranki, a sanyaye ta amsa ta fita Amira ta bita
da kallo a zuciyar ta tana jin tausayinta hak’k’un.
Da sallama ta shiga d’akin, shewa taji hajiya nayi da alama waya take ta kashingid’a kan kujerar dake d’akinta,cewa tai “hajia gani” kallonta tai “ga kaya can ki dauka ki wanko mun su” da sauri ta d’ago ta kalleta, debo mata kayan tayi “hajia na gaji wallahi
yanzu na gama aiki” dagowa tai ‘lallema ba zaki ba kenan? tsoro ta ji tace “Aa hajiya zanyi” dauka tai ta fita cikin k’unar rai.
**
Haka taje ta fara wankewa ,tana yi tana hawaye a zuciyarta tana cewa wai kishiyoyinta ne ke sata hakan ta rasa dalili, ita ana aure ai kiba rama ta ke,
ga kayan da uban yawa. Haka dukufa. Nadiya ce taci uban kwalliya da alama biki zata ta kalli zahra harda shewa “yau kuma wanki ake?
Ta kuma kwashewa da dariya “kad’anma kika gani bake wai kishi da manyan mata ba hohoho yarinya wasa farin girki”
ko kallon inda take zahra
ba taiba Har ta gama surutunta ta tafi, haka zahra ta gama taje ta shanya. . .
Alhaji ko ko sashin zahra baya kallah kulkum sai dai ya fice ya dawo ba tare da ta sani ba.
Zahra ce ke waya da Mamanta inda take sanar
mata da halin data ke ciki ,Mamanta abun ya tab’a zuciyrta amma ta dan ne tana bata baki tare da hak’ur da yarda da k’addara sannan da
Biyayya ga miji ,san nan tace ta dage da Addua, itama tana nan tana yi mata, hakan tai ta kwantar mata da hankali ,farin ciki ne taji ya shigeta. A lokacin.
Bayan gama wayarta ta tashi tai tayi wanka ta d’aukoWayarta tana latsawa. Billy ce ta tabota a whtsap sun sha hira ,har take sanar da ita tai mata kwatancen gidanta zata zo
nan ta mata kwatance tace “insha Allah zata zo. Tana ajje wayar amirar ta shigo tana dan ta tayata hira har take ce mata tana karanta
Novel kuwa? Tace “ai da tana karantawa nan ta debo mata da yawa taji dadi aranta don zasu na d’ebe mata kewa Godiya tai mata,
ta tashi tafi ta.
****
Da dare Alhaji yana zaune a falonsa, kamar walkiya yaji zahr ta fadomai nuyin da yake ji na tsanarta yayi kasa, kiran wayar zahra ya hau yi yayi, tana gani tai burus tare da jan tsaki, dan wajen sati uku kenan suna wasan buya da shi, wajen 10 miss call.
Shima sai ya share dan da dane biyota har daki zai, sabanin yanzu abin na taba ranta nan ta shiga tunanin kode dan tana mai rashin d’a a ne shima ya canja mata.
Karamar wayarta ta dauka ta kamo Fm Radio ta kunna nan taji ana waazi akan Mata masu yiwa mazan su rashin kirki da irin azabar da ake musu. Nan taji ta tsorata take ta
tuno Nasihar Mom nata jikinta na bari dan tsoron Allah data ji ya shige ta lokaci daya.Cikin wani irin yanayi ta mike.
Abin mamaki sai gashi ya kuma bugowa da sauri ta dauka b’angarensa yace Zahra kina inane nake ta kira?cike da cikin bacin rai tace
“ina toilet ne” yace “don Allah kizo” hijab tasa tai hanyar dakinsa.Hajia uwani ce d’auke da fulas na tea ta futo daga dakin, wani wawan kallon ta watsa mata “ke me zaki aciki?” “Alhajj ke kirana ,tsawa ta daka mata “koma munafuka me zaki mai” haushi ne ya kamata taki tafiya,a zuciarta tana mezan ma da tsohon mijinku rank’washi takai mata da gudu tai baya tana kuka,dadi ne yakama Hjj uwani tai gaba ,shiru shiru Alhaji be ganta tazo ba, tasowa yayi ya nufo dakin ta shiga yayi ya ganta tana kuka da sauri yaje ya ya zauna kusa da ita zahra…..:……………………………………….
STORY CONTINUES BELOW

Tambayarta yake meya sata kuka kuma meya hanata zuwa,kasa motsawa tai tambayarta yayi a karo na uku taso ta dago taimai rashin kunya se kuma ta tuno Nasihar Mahaifiyarta kan biyayya ga miji,a hankali ta d’ago tana share fuska,hankalinsa se taji yabata tausayi a yau taga kamar ya rame kome ke damunsa!
sanar
mai tai kanta ke ciwo, domin ta riga ta d’au alkawarin duk abunda matansa sukai mata ba zata gayamai ba sede ya gani da idonsa, cikin jimami yayi mata sannu magani ya dauko mata tassha se bacci ya dauketa haka ya zauna ya k’ura mata ido
ya kasa tashi, duk da yana,jin wani sashin zuciyarsa na balain,jin haushinta mara dalili amma ya kasa mikewa, bude idonta tai taga Alhajin nanan,
tausayinsa ya kamata ,gashi shi yana sonta ita kam bata sonsa, amma za farai mai Biyayya amatsayin sa na mijinta.
shi kam Alhaji umar yayi mamakin yanda ta sauko. Allah kenan !me yanda
yaso domin baya bacci kullm cikin addua yake, to gashi adduar sa ta fara karbuwa, yau kam a dakin zahra ya kwan cikin farin-ciki ita
kam zahra in banda daurewa ba abinda take,tasha albarka domin
harda kukan sa, tausayinsa ne ya kuma kamata tai alwashin ta dena yi mai wulaknci zata yarda da k’addara domin shine cikar mumini,domin
Aljannarta na ga mijinta.
Da safe yana breakfast yana kallon zahra dake sunne kai agefe lalle bbu abinda yakai addua yaga faidarta dan tun lokacin da mlam wada ya bashi adduoi yana yi yaji duk wasutsanar zahra da yyai ta kau gashi kuma ta daina yimai wulakanci.
A hankali ta numfasa numfasa gyara zama bayn ya kare breakfast din hakuri ta fara bashi da nemn yafiya kan abinda tai ta mai. Dariya yayi “zahra bakimun lefi ba nine nai miki ma nagode wa Allah da yasa kika fahimci rayuwa ki kasan komi daga
Allah ne”
Hawaye ta share, murmushi yayi $zahra fadi duk abunda ki keso in baki” sunkwi dakai tai ba tace komi ba, numfashi yaja
ya kalli mudubi lalle zahra “ke alheri ce gareni dubi
furfura ta har ta fara b’acewa saboda samun kanki na dan kwana biyu” dariya tai kawai mik’ewa yayi yace
Zai fita ,sallama yayi mata ya tafi .
Tunane tunane ta zauna tai tayi karshe ta tashi ta gyara dakinta tafita
domin gudanar da aikinda da ya zamar mata dole, aikinda ba lada se bak’in ciki, tunda ba aikin mijinta bane. . .
35. Goge gogen falo take ga gumi duk ya dame ta
magajia ce ta fito da bokiti a hannunta da gan-gan ta sake shi kash! tace ta kalli zahra “yi hkr na b’ata miki aiki ko? “ko kallonta batai ba “se kizo ki goge bayanda zatai haka ta goge,gamawarta keda wuya ta shiga kitchen tana feraye doya don yau hajia uwani tace shi zasuci ,ta rasa dalili da ta taso zatai musu challenges akan hakan seta kasa, sallama aka doka afalo, da sauri ta fita ganinsu mariya
tai da zainab wato yayunta doka tsalle tai ,wani kallo
Mariya ta bita da shi yanda taga dukta canja dakina ta kaisu tare da kawo musu lemuka zainab ce ta kasa shiru “zahra cuta kikai
ne? da sauri tace” eh Anty Mariya da zancen be shigeta ba ta jinjina kai,cewa tai bari na duba girkin can binta da kallo sukai zainb ce tace “wollahi ni kam Anya yarinyar nan
tana zaune kalau kuwa?” jifa yanda ta dawo! ,duk kyawun zahra amma tai wani iri” ,Mariya tace “haka na gani” zainb tace bar
‘yar banza ay zamu san me ta ke ciki.
Mamaki ne ya ishi zahraa yanda taga an kashe mata gas san nan an zubda ruwan cikin tukunyar data dora ,kawai basarwa tai takuma dorawa.
Nadiya ce tasa wani uban dinki duk
kirjinta awaje se rangaji take ta doso kitchen din,kallon xahra
tai “malama inason amfani da gas din?” Tsaki tai dadin abunde ba gidan mutum bane ,haka kuma ba na gidansu mutum bane”,Nadiya ce tace” “Ieeeeee ni kike gayawa hakan?” Zahra tace “na fada Din domin gidan mijinane”
STORY CONTINUES BELOW

tab’e baki tai “sannu mai miji ai kinci
baya banza kin b’uge da Auren tsoho” zahra tace “tafi can kina cin arzikin mutum kina rashin kunyaa kamata yayi kisamu madafa don naga kinyi kwantai ba mashin -shini ,juyi tayi
nikam matar manya nake “
Wani kululun bakin
ciki ne ya tasowa Nadiya,cafko zahra ta makureta abango kara zahra ta saki wanda yasa su Mariya suka fito a gurguje dan da karfi tai Nadiya bata tsaya haka ba ta kaama dukan zahra nan suka kaure da fada tun suna kitchen har falo.
Mariya tace “ke sakar mana kanwa ke kuma wacece? Kundumawa mariya zagi tayi “bazan saketa ba” Azuciya mariya ta wankawa Nadiya mari ,”baki da hankali god’ed’iya dake zaki kashe mana k’anwa ,cikin tsiwa tahau yiwa Mariya rashin kunya nan falon ya har gitse hajiyoyin ne suka fito.,”mezan gani hakan?” inji hajja uwani “wato ‘yan uwanki kika Gayyato ko zahra?
Hajja Zainab A zuciye ta kamo zahra zata daka zainab tace “wallah ba wadda ta isa ta daketa” da yake Mariya irin masifaffiya ce nan ta shiga tai kace -kace gata irin bata da tsoro ba shiri suka kyaleta. Nadiya kam ta daku se
Zage -zage take Hajia uwani ce ta kamata ,wallah zahra kin d’au bashi. Zainab ce suka ja zahra daki cikin fushi mariya tace yanzu zahra irin ukubar da kike ciki shine kikai shiru?”
Cikin kuka tace”Anty ya zanyi na rasa yanda zan da su, kinsan kuma idan baba yaji nai wani abin sabarmun ze. Zainb tace “da alama ke kike ayyukan gidan ma ko?”nan ta fayyace musu komi cikin
kunar rai sukai mata fad’a akan ta magantu san nan kar ta sake ta sab’awa mijinta tai mai Biyayya iya karfinta “Allah na tare dake zahra ,me hkr shi kan dafa dutse….wanda hausawa
ke cewa har yasha romonsa,duk ta gama jinsu mariya tace “san nan
wollahi duk sanda wata ta kuma dukanki ki gaya mana wallah se munzo munci mutuncinsu tunda su basa jan grmansu idan jika ce ai
sun kusa yi dake .
Snaks din da Alhaji ya kawo mata ne wanda takasa ci duk takwaso musu sunaci suna korawa da lemo dan sunce baza tai girkinba ,wajen la’asar sukai mata
sallama tare da nasiha ,suka jaddada mata lalle taje gida ran friday kai kayan Mujaheed suka tafi, d’aki ta koma ta kulle k’ofa don tace sede su kwan da yunwa yau……….:…..:……….
Tunda tashige dakinta take kuka bayan gama kukan ta dauro alwala tana rokon Allah ya dora ta akan su, salati takeyi tana hailala karshe ta dora da karatun Alkurani.
So take ta fita Amma tana tsoro karsu dake ta har dare tana daki saida Alhaji ya dawo san nan ta bude ya ledodi ne fal ya aje mata kunshin kazarta yace bari ya mikawa su Uwani nan ta hauci da yoghurt don dama yunwa take ji.
Bayan kwana hudu tana son bugawa baba waya don tambayarsa tazo gida don yace sai tayi wata shida gashi tana san zuwa .Number din mariya ta buga mata tace Anty ya batun tafiyar kinsan baba bazai bari ba tace bari na tambayo haba duk fa dangi za a nan takashe.
Kamar mintuna ta bugo ke Zahra ya amince don dakyar ya bari saka tsalle tayi nagd Anty ai da wuri zanzo goben tace to Allah ya kaimu.
Haka kwana 2 ta dena fitowa falo don tace ta daina girki saima dagewa datai da addua don tunda tafara adduar ta daina tsoron su dama ai addua makamin mumini ce…….
Da sassafe ta tashi tai wankanta tayi kwalliyarta tasa shadda Brown ta kafe d’auri tai kyau abunta gyara daurin kanta take taji an banko k’ofa atsorace ta
juya ganin Hajiyoyin tai a tsai-tsaye kallonsu tai d’aya bayan daya ta juya.
Basu ce mata komi ba hakan itama,ta gama shirinta tsaf! tad’au jakarta da wayarta Uwani ce ta kalleta “lalle kin samu sake yarinyr nan” sunkwi dakai tai “ba magana muke miki ba” ta d’ago “to me zance?” “To bude kunne kiji waza
kibari da yauwa” tace “hajia unguwa fa zani”
“to wallahu baza kiba
sekin mana girki,” tace “gaskya kuyi hakuri sauri nake ana jirana”
” iyeeee hakama za kice to bari kiga aiki da cikawa”
dukanta suka hau yi tamkar jaka se ihu take,ba shiri ta banko k’ofa ta fita wajen falo nan ma suka biyota kamar ‘yarsu da gangan hajia taja bayan rigarta suka yaga mata kuka tai tayi me tsuma rai,Hameed ne ya shigo cikin b’acin rai yace “haba hajia wan nan aiba yi bane ,ya zaku kama yarinya kuna
duka haka? Uwani tace to “rasa kunya meye naka aciki?”
nan yace “wan nan bayi bane ina lura wallahi,kunta kurawa Amaryar Alhaji wallahi
ni kam zan sanar dashi” “iyee! don ban haifeka ba shine za ka ce hakan baka kishina ko? Kar ka manta ni k’anwar uwarka ne ba kada had’i da Alhaji don haka ba ruwanka”
“yace Allah hajia sena sanar mai haba! “ai ‘yar adam cefa” ciki yayi tai kwafa.
.
STORY CONTINUES BELOW

Seda suka tabbatar sun mata duka ,suka kyaleta d’akinta ta shige kwanciya tai tana kuka,wayarta ce tahau ruri Mariya ce da sauri ta dauka “kefa muke jira tace gata nan ,k’arfin hali tai ta canja kaya ta wanke fuska ta kuma yin kwalliyarta,fuskarta duk ta kumbura haka ta tafi driver
ya tafi kaita, wani sanyi taji da taga an shiga unguwarsu.
Yau watanta 5 da Aure rabonta da ita mai kayan miya ta gani ya tuno mata da Salim tai sauri ta kauda tunashi har akazo k’ofar gidansu tana tunane- tuna ne seda driver yayi mata magana da sauri ta fita,soron gidansu ta shiga
su ya Atiku da Abbakr ta gani nan ta gaishesu suna tambayarta ya gida tana shiga gidan taga mata birjik aka fara ga Amarya ga
Amarya cikin farin ciki suka gaisa shiga falon tai
ta zauna kusa da goggo suna gaisawa ta gaida su Anty Mariya tashi tai ta shiga k’uryar d’akin goggo ganin zainaba tai aciki suka
gaisa mariya ta shigo “zahra meya samu fuskarki ne? kamar kin kuka”,tace “me kika gani?” Tace “dalla rufen baki ba gashi fuskarki ta kumbura ba nan ta sunkwi dakai “dukanki sukai ko?” ba tace komi ba “ke kam akwai lusara ke kam ki zauna se kace
jaka sede kishiyoyi sita jibgarki. Ke Mijinki be miki ba se su.”
da yake Mariya akwai masifa wallahi semun rama miki dago kai tayi “Aa anty ki k’yalesu akwai Allah””
“ke dallah rufen baki wollahi semun rama miki ,wallahu duk randa suka kuma dukanki
se munzo mun daku dasu”,
Wajen k’arfe uku suka tafi kai lefen a Unguwar rijiyar zaki suna tafiya amota se hargowa suke sun sata atsakiya se caccaka suke ita de tai shiru don ba zata
iya da matan nan ba manya dasu, sunkai an karb’esu cikin mutunci aka basu tukwici, suka dawo wajen 8 driver yazo ya d’auketa tai gida, ana shiga falon
taji hargowar su Nadiyace tsigai ke fada tsaki tai
ta wuce d’akinta ta shiga ta zauna bayan tai sallah ,tahau whtsap inda billy ke sanar mata gobe zata Zo,nan ta aika mata da
kwatancen gidanta sun sha hirar su, bacci ne ya dauketa dauketa ,wajen 10 ta farka ganin dakinta tai duk an barbaza haka wardrop dinta an bude duk anwatso da
kayanta,da sauri ta bude kit dinta taga ba sark’arta.
nan gabanta ya fadi don tasan tsadarta ,itace wadda Alhaji ya bata tukwici ,bakin ciki taji me d’aci nan tahau huci ,ba zata yarda ba Allah Allah take gobe tai wallahi se an futo mata da ita,kuka
ne ya kufce mata sam ba tajin dad’in auren nan saboda ta rasa me taiwa matan nan hawaye ta share tai alwala tahau Salloli don samun sauki agun Allah ku daka ceni.
………………………..
Washegari! Cikin fushi ta shiga d’akin Alhaji yana zaune abakin gado yana duba jarida daya ke yau lahadi beje market ba yana hutawa murmushi yai da mamaki A fuskarsa ya kalleta Malama Zahra da magana A bakinki ko?Eh
Alhaji nan hawaye suka fara kwaranyo mata,take Alhaji ya rikice yana cewa”ashsha! ya da kuka kuma? hawaye sharrrrrrr!
ya soma zubo mata tasowa yai ya zauna kusa da ita,yace”gayan me akai miki?
Tace “sark’ar da ka saimun ce jiya bayan na dawo daga kai kayan yaya Mujaheed,na d’an kwanta bacci ina
tashi naga an watson kaya an bud’e kit d’ina an d’auke
sark’ar lallashinta ya hauyi a fusace ya tashi…..
Babban falo ya futa ya zauna itama Zahran ta zauna janyo ta yayi yana
d’an dukan bayanta alamar lallashi.
hajiya! hajiya!!
hajiya!
Ya bud’e murya yana kiran su da sauri suka firfito,kowacce na ya tsina suka zauna kan kujera ,kallon kallo suka hauyi don
ganin Zahra kwance jikin Alhaji ba’kin ciki ne tamkar
ya kashesu.
Ina wad’ancen yaran?uwani tak’walawa
Nadiya da su tsigai, Amira su hameed da sauransu duk suka hallara in banda hararar Zahra ba abunda suke inka d’auke Amira da Hameed gyaran murya yai “wato duk abinda nake gaya muku kan yarinyar nan bakwaji ko?.nasan fa irin zaman da kukeyi da ita ,da wad’an nan yaran cikin ku waya shigar mata d’aki jiya?”shiru ya ratso falon!ya kuma mai maitawa cikin daka tsawa wai ba magana nake muku ba ya kalli su
uwani, cikin in ina Amira tai magana ya juyo Yana
kallonta “fad’i mana!” kallon su hajiya tai cikin tsoro dama Nadiya
ce jiya ta shiga d’akin lokacin tana bacci nai mata magana ta shareni” juyo da kallonsa yai gun Nadiya “ke meya kaiki d’akinta? Ko sa arki ce? Ehe? sunkwi dakai tai to tashi ki
fito da sark’a” dagowa tai ta kalli hajiya Uwani harara ta watsa mata ,gyara zama tai “ni band’au sark’a ba”
haushi ya kuma kamashi ya tashi tsaye ta inda yake shiga ba tanan yake
fita ba, se daya musu kaca kaca San nan ya kalli Hajiyoyin yace”bana son k’ara ganin ko wacce yarinya a gidan nan, ku tabbatar kowacce ta tafi gidan ubanta”
dafe k’irji
Magajiya tai da zaro ido! hameed dake tsaye yace “Alhaji ai hakuri kullum dama ina musu magana akan hakan basa jin maganata” Alhaji ya kalli hameed ba komi” amma fa dole su fito da sark’a wallahi idan ba haka ba kowacce seta tafi gidan su,
a fusace ya tashi ya d’ago Zahra wadda ke da d’a narkewa don takuma basu haushi, d’akinsa suka shiga ya kulle. . .
Hajiya Magajiya ce ta kalli su Nadiya ta ce “sai ki fito da sark’a,” kallon banza hajiya uwani tai mata, tab’e
baki tai “to mude ki fito da sark’a don ba zaki janyowa
Amira ba, tashi sukai suka shige d’aki uwani ta kalli Nadiya $ina kika kai sark’ar? tace “tana d’akina” abinda na ke so dake ki dauko sark’a ki kawo mun ita nan. Tashi tai ta d’auko mata.
Mamaki k’arara a fuskar ta Lallema Alhaji tunda nake be tab’a saimun kamar wannan ba (to fah kunji halin wasu mata,(komi zaka musu inde ba suda tsoron Allah lokaci d’aya se suce ba a tab’ai musu ba,nhmm Allah ya kiyashemu ) k’wafa tai .Nadiya kuwa da hankalinta ya tashi tasan inta bar gidan ta rabu da shan jarmiya don tun tana k’arama hajiya uwani ta d’auko ta ‘yar k’anwarta ce talakawa ne tibis yanzu idan takoma abinci ma
gagararta zeyi duk da tana ganin gidan iyayenta ne,da
sauri tace “nide hajiya a maida mata a barta.” numfashi taja hakan za ai don akace kin koma gida kunyama ta isheni cikin
yan uwana, suna gani ina auren me kud’i ,don hakan
Kid’au sark’ar ki kai mata d’akinta don naga sun shige d’akin Alhajin ita dashi, Dan wannan sark’ar! ta tabe baki sark’ok’i nawa na mallaka agun Alhaji itace ke nema domin duk a a sarkokina sunfi wan nan ce karama, nanta mikawa Nadiya da sauri ta amsa.+
Cikin sand’a ta bud’e
d’akin ta aje acikin kit din, har tana watsar da kayan saboda tsoro ,da sauri takoma d’akin hajiya nan ta zauna tana
cewa “d’an da k’yar” har had’a gumi take hajiya uwani tace”
“nayi rantsuwa se yarinyar nan tabar gidan nan nifa saboda kar Alhaji ya samu magaji na keso ta bar gidan nan.Nadiya tace “wallahi Hajiya sai nunawa amira bata da wayo yau, munafuka ba duk ita
ke rusa mana aiki ba”
“karde ki kulata Nadiya”
tace “Hajiya ki k’yaleni da ita ,tashi tai ta fita cikin jin
haushin an raba ta da sark’a (kuji Barauniyar zaune tab).
D’akinsu ta shiga Amira na kwance ta fusgota tsigai ta d’ago “meye haka kuma? dalla Malama yi mana shiru”
Amira ce tace”meye hakan kuma zaki shak’e ni? “An shak’e ki d’in ‘yar cirani kawai” dariya tasa ai
kema ciranin ne ya kawo ki kinga duk kanmu nan d’an jumane da d’an jummai”mari ta kai mata tana surfa mata tijara.
Amira
Da ta dafe kunci “kinsan bana fad’a amma wallahi yau bazan k’yale kiba b’arauniya kawai” “laa!laa! Ki ka sake cemun barauniya? nan fad’a ya kaure tun suna d’aki har falo tsigai na ziga k’arar fashewar abu Alhaji yaji yasa shi fitowa shida zahra. . .
A lokacin Hajiyoyin suma sun hau hayaniyar
ko wacce nabin bayan ‘yar d’akinta hameed ma ya
fito daga daki yai tsaki shi kam a zuciyar sa ya tsani Nadiya yasan
itace me tsokana,kullum da ita ake fada,tsawa Alhaji ya daka musu ya nunasu da d’an yatsa yace “wallahi ku shiga hankalin ku ya zaku maidamin gida bariki? to ba za ta sab’uba” ya kalli hajiyoyin wallahi “ku kam..Anyi manyan banza.” Zahra
nan ta fiku sanin ya kamata” cikin fusata Uwani tace” haba Alhaji! ai wan nan cin fuska ne kullum seka nuna ta fimu dan tsabar kai yarinta tahau kanka.” yace “naji ai yanzu ke da girmanki gashi kina abun yaran.”
Hameed ya kalla ya ce samon
bulala.
Da sauri ya d’auko dorina(bulala) yace” yaiwa Nadiya da Amira goma- goma,abin nema ya samu haka ya fara takan Nadiya yai ta laftarta ya zage k’wanjin sa dama yana cike da ita,da yazo kan Amira a hankali yai mata,kuka sosai suka hauyi nan Alhaji
ya umarci zahra da taje ta shirya shima ya tafi duk
sunyi birjik a falon se maida zance ake hajiya
zainab fad’a suke akan taiwa Hameed fad’a.Haka sukaita cece kuce wajen awa d’aya kamar saci babu
Alhaji ne ya fito ya rik’o hannun zahra ta feso uwar kwalliya se walwali take nan ya kalli Hameed yace yazo,,ya kallesu….. A zuciyarsa yana Mamakin yanda duk matansa suka dawo tun bayan da yai Aure,sun maida kansu kamar wasu tab’abb’u,kuma kallonsu yai yace”to
semun dawo..
STORY CONTINUES BELOW

Sakin baki sukai sun ma kasa magana duk se
suka manta da abinda ya faru oh mu ‘yasu Alhaji ya zama taace.
Zahra ce zaune A bakin garden d’in dake gidan ta na son wajen saboda sanyinsa,cikin ta ne taji ya wani hautsina da sauri ta dafe cikin tare da ya tsine fuska,haka a daddafe ta tashi tai cikin gidan ,da yake side na ta akwai k’ofa ta baya inda ze kai ka garden d’in d’akin ta shiga
firij ta bud’e tasha ruwa ko aje robar ba tai ba amai ya biyo baya haka tai ta kwara shi,tashi tai ta gyara gun tai mopin ta kwanta ta na numfar fashi.
Alhaji ne ya shigo d’akin zai ma ta sallama,ganin ta yai ko magana ta kasa
jikin ta zafi zau, k’amshin turarensa ne yasa ta tashi da gudu tai toilet da mamaki k’arara akan fuskarsa da sauri ya bita ya rik’e ta sai da ta gama tsaf san nan ya ruk’o ta waya yai wa
family doctor na sa ,yana nemanta zama yai yana ta
mata sannu, fita yai ya canjo kaya ko turare bai fesa ba saboda karta kuma wani aman.
A lokacin doctor har ta k’araso iso yai mata k’aramun falo checking din ta tayi sosai tace “ta je
tai fitsari agwada bayan ya gama gwaje -gwajenta ta rubuta magani san nan ya tafi,don auno fitsarin,fitar da Alhaji bai ba kenan ya zauna kula da Zahra.
Magajiya ce ta shiga d’akin ta kalli Zahra ta tab’e baki san nan ta kalle shi “Alhaji ni zanfita gidan sunan ummuSamha” kallon ta yai “to adawo lafiya” ta na son tambayar mai ya samu Zahra amma ba fuska,tana futa ba ta zame ko ina ba sai gidan. Aminiyar ta hajia jummai nan suka zauna in banda
zancen gidan boka ba abinda suke lemon dake gaban ta ta d’an kurb’a tare da ajiyan zuciya “kin san wani abu kuwa Jummai?
Tace “sekin fad’a” wallahi yanda zan fitar da shegiyar yarinyar nan na ke” habade! ke ai kin wuce wan nan
wajen” tace” barni de Jummai mai d’aki shi ya san inda yake mai yoyo,tsoron mu d’aya karta d’au ciki.”
“Kinga mu ba haihuwa muke ba, ta ja numfashi ga Alhaji burin shi kawai ya samu magaji kuma kud’insa kullum hab’b’aka suke kin san gwabnan yanzu abokin sa ne don ba kiga kwangilar da
ya bashi ba ,wani tamfatsetsen gida yake ginawa a ‘yankaba dole ki ga mun haukace yanzu da wannan yarinyar ta haihu duk dukiya gunta zatai.”
Jimmai taja wani Numfashi “gaskiya Hajiya kun yi sake tabd’ijam!! ,to bud’e kunne ki ji akwai wani sabon boka a k’auyen digirima ya had’u,ta fawa su kai to ai yanzu ma ba muga ta zama ba kawai tashi mu tafi hmm (Allah ya kiyashe mu zuwa gun boka, Allah subhanahu
wata’ala yace” duk wanda yaje gun boka ko d’an tsubbu Sallahr sa ta kwana arba’in 40 baza akarb’a ba wa iyazu billah Allah ka ka remu) .
Doctor ne ya dawo
gidan bayan taje yai gwaje gwajen sa .Alhaji ke tambayar sa meya samu matarsa? cikin murmushi
Tace”ALLAHU K’ADIRUN ALA MAN YASHAA.Wato…
Alhaji matar ka Zahra na d’auke da ciki na wata d’aya da rabi kid’imewa Alhaji yai tare da d’aga hannu sama yana godia ga Allah abinda ya dad’e bai samu ba gashi yanzu
Lalle hak’uri baya fad’uwa k’asa banza baisan yawan
adadin kud’in daya d’aibo ba ya damk’awa doctor tare da sauran tukwicin da yace ta saurare shi,salllama sukai ciki da sauri-sauri.Alhaji yai side in Zahra.
To fah! kifi na ganin ka mai jarkoma inji hausawa, tsigai ce tsaye bayan kofa tayi firkai-firkai a bayan k’ofa ,duk maganganun da su Alhaji sukai taji a kunnenta da gudu tai shashen hajiya zainab tun da uwar d’akin na ta magajiya ba ta nan,ta na haki ta shiga.Hajiya tace” Aa! tsigai meye hakan? sai kace wa ta k’aramar yarinya zama tai a gefen mudubi.Hajiya wallahi na ji
Doctor sani na cewa.Alhaji wai zahra na da ciki,dafe
kirji tai ta mik’e tsaye hankalinta ya ta shi tace” ciki!
STORY CONTINUES BELOW

Magajiya ce zaune gaban boka.
Jummai na gefen ta,kallon ta yai “na san meke tafe da ke Kishiya ko? da sauri ta ce “eh boka” wata wawiyar dariya ya fasa “fad’i abinda ki keso ai mata” abin nema ya samu ta ce “boka mai kan-kan so na ke ayi abinda baza ta samu ciki ba kai Ama koreta daga gidan”
Gurnani yayi yace. “Hajia kun yi sake domin yanzu hakan tana d’auke da ciki” ya jefa wani abu cikin kwarya saiga zahra suna maganar da alhaji, dafe kirji tai!! “Sannan batun tabar gida wannan bazan cemuki komai akai ba, amma zan baki magani ki tabbatar ta ci,inde kinyi dai-dai to take
cikin zai zube” kud’i su ka zube mai, ya basu magani ya ce” kar maganin ya wuce yau ba ai amfani dashi ba, inde kwa ya wuce yau! to aiki ya b’aci koda taci cikin bazai zube ba” Sallama sukai da boka suka fita ta baya suka tafi…
Bayan sun taho daga gun bokan A hanya
suka sauke Jummai sauri -sauri ta keyi saboda ta na so ta ruski lokacin da zahra ke girka abin da zata ci…Don Alhaji ya hana ta girkin gidan sai na ta kawai, wajen 6 oclock ta shigo gidan Bata zarce ko’ina ba sai kitchen ko zama batai ba tai ba,ganin mai aikinsu tai, tambayarta tayi ko
zahra ta shigo kitchen? ..Mai aikin ta ce “ai hajiya
yau zahra bata shigo kitchen ba saboda bata jin dadi ta na d’akin ta yanzu ma Alhaji ne ya ce na d’an yi mata romon kifi ko za ta iya ci” da sauri tace” yawwa kin dora ko? tace”
Eh Hajiya d’an murmushi tai ta d’auko Kettle ta na
k’ok’arindafa ruwan zafi, kallon Larai tai tace”da ma nima kinga abunda zan dafa”,ganin da tai ta sauke ta zuba A Flaks da sauri ta ce”Larai! Jeki d’aukon babban flaks d’ina a bedrom Da sauri ta tafi Ganin ta fita ta zaro k’ullun maganin nan ta barbad’a ta Juya hardasu karkad’e hannu kallon
k’ofa tai ganin ba wanda ya tawo .Da sauri tai waje ganin Larai tai ta tawo ta ce “mata sai ki zubon aciki ki kawon d’aki” shigar ta d’akin ta wani murmusa wanda ita a ganin
ta aikin ta yaso cinma yi. Domin dama tsoron ta kar yau ta wuce bata zuba, matan ba.
Murmushi ta kuma dokawa, wayar ta Dauka suna waya da Jummai. . . .
Larai ce tai sallama d’akin zahra, shiga tai ta aje mata Flasks din tace”hajiya gashi. Alhaji ne yace adafa miki” kallon ta tai tace” menene kika dafa?” “romon kifi” “bud’e na gani!” don
har taji sha’awarsa,tana bud’ewa k’amshin ya bugi hancin ta da sauri tai toilet amai tai ta kwara rawa,…Larai na ta yi mata sannu. . Kuskure bakin ta tai,ta futo tace “anya! larai zanci romon nan kuwa?” tai d’an tsaki kawai “je ki ku
cinye. Godiya tai mata, sannan ta ce.”Hajiya bakya buk’atar wani abin?” …”Aa Larai jeki kawai” fita tai ita kuma ta kwanta tana d’an kallon TV .
Magajiya suna zaune a falo dukkan su ana ta hira ana kallo,ganin Larai tai da Flaks a hannu kiran ta tai “Larai yadai? Kin kai matan kuwa? kin san Alhaji da fad’a inde akan wannan yarinyar ne” tace”hajiya na kaima ta amma tace bata ci” “to ina yake? “ai cewa tai mu cinye” tsaki tai “seki tashi ki bamu waje” tana barin gun hajiya ta kalli uwani “aiki ya b’aci” tab’e baki uwani tai “barta nasan me nake shirya wa kede saurareni nan da kwana 2 Dariya suka sa.
ALhamdlh zahra jiki yai sauki tana iya cin abinci a yanzu ma sam bata shiga harkarsu kota gansu afalo ,sai dai ta musu Sallama ta wuce, wajen karfe 4 na yamma billy kawarta tazo taji dadin
zuwanta haka ta karramata da kayan motsa baki karamun falo suka fito suna ta hirar su kan wani book da ita billy ke bibiya a group ,suna ta kyalkyala dariya. Nadiya ce ta shigo falon ko sallama babu ta kunna tv harda su canja tasha. Zarha kam tasan tsokana ce ta kawo ta ,da
gan-gan suka tsiri hirar cikinta wanda har wani fari
take. Nadiya kam haushi ya isheta tashi tai tabar wajen Billy tace “am k’awata wai wan nan wace?” ‘yar rukon
kishiyatane” da mamaki k’arara tace “au dama kina da kishiya?” tace “kishiyoyima” suna cikin zan cen sai ga matan nan kamar bukkoki sun tsaya. Nadiya tace “ke zahra!
maimaita abinda kikace “,uwani tace “barta wai har ita zata mana gorin ciki”,kallon juna zahra da billy
sukai .Hajia Zainab tace “yau zaki gane kurenki, magajia tace kwarai ma kuwa” Hannun billy taja suka tashi zasu bar falon da sauri Nadiya ta cakumo kafad’arta ta juyo da ita ,uwani ta kwad’a mata mari
“waike kinyi ciki ko wlh yau se kin gayawa aya zakinta”
kallonsu tai “wallahi duk wanda ya tabani ze gane kurensa ” janyota uwani tai “ke kina yar cikinmu kina yi mana rashin kunya”
“wa! Wallahi baku haifen ba don ko kaza baku aje ba” ita kam billy hankalinta ne ya tashi janyo ta sukai suka hau duka tun tana cizon su har ta kasa.Hajia zainab kam taliyo ta tai ta fadi kasa “wallahi yau se kinji nauyinmu” ihu ta dunga yi billy kam harda su kuka tana basu hakuri.
Ko ajikinsu uwani kan kafarta tasa ta daki cikin nata kara ta saki wanda yasa ta suma ,billy kam wayar zahra ta dauka
tarasa wa zata kira number ta farko datai recieving call
ta kira kuka take daga can akace “zahra” da sauri billy tace “don Allah kuzo zasu kasheta” Anty Mariya dake kitchen tana sanwa tace
“wadin?” Billy tace “nice kawar zahra nazo gidanta
kishiyoyinta sun mata duka yanzu hakan bata motsi.Mariya tace yi hakuri gamunan zuwa idan kinsan no din Alhaji dauka ki buga mai” kashewa tai.
Sukam ganin jini nabun kafa fuwan zahra se duk suka dare cikinsa a kam Alhaji ya bugo dama k’a idarsa ce in zai komo
gida se yayi mata waya ,billy ce ta dauka tare da sallama shaidamai take yi,salati ya hau yi,ruwa ta dauko tana yayyafa mata
amma ko motsi wajen rabin awa sai ga Alhaji nan ko magana beba y sun kuceta sai hospital.
Bayan an kaita asibitin wanda aka shaidawa Alhaji ta samu b’ari. Alhaji har kuka ya yi domin ya d’ora buri akan cikin, rok’on Allah yayi akan ya saka masa, sai wajen 10 suka dawo kobi takansu bai ba Aranar d’akin zahra ya kwana saboda kula da ita.
WASHEGARI!
Bayan Alhaji ya kimtsa Zahra wadda ta d’an samu
sauk’i sai abun da ba’ a rasa ba.Wajen karfe goma sha- d’aya 11:00 sai ga Mariya ,Rukayya da Zainba ,wato yayun Zahra ko zama basi ba su ka hau cewa “,ina matan gidan? tsigai ce ta
fara fitowa ta kalle su “daga ina?” Mariya tace” daga gidanku”
ki kirawo mana iyayen d’akin naki” Juyawa tai ta tafi kiransu.
Magajiya ce ta fara fito wa, kallonsu tai “taimako kuka
zo naima ……?”
Rukayya tace “kinga munyi kama da masu maula? ba wannan ba munzo sanin dalilin
da ya sa ku kai wa k’anwar mu duka har da su zub da
ciki saboda, ku baku haihuwa don tsabar bakin ciki, to baza mu
yarda ba”
tsigai tace “karku yarda din gayyar na ayya” .Mariya da tafisu masifa ,janyo Tsigai tai ta fara
nad’a da sauri su Uwani su kai yo kan ta lokaci kad’an
guri ya hargitse dama ashirye suka zo nan suka yi ta maida maganganu da kai duka .
Wawurar D’an mariya tsigai tayi ta kai kas batai aune ba mariya ta naushe bakinta nan bakin ya fashe take tsigai ta fasa ihu nan waje ya kuma hargitsewa….
-Zainab kam fita tai can waje ta d’au bokitin…..
Maigadi wanda yake cike da ruwan kumfa da alama wanki yake ,da gudu tai cikin d’akin da taga uwani ta fito ta shiga ta kwara duk d’akin ya b’aci …..Uwani ta shiga dakin ta cakumo ta tace “d’akin
nawa zaki zuba mwa Ruwan wanki ?
Tace na zuba, nan sukai ta fad’a dukda hajiyoyin sunfi k’arfin su amma kuma suda yarin ta…
Jikin su sai da su kai kaca- kaca da falon. Ita kuwa Hjy Zainab an turgude Mata kafa ta kasa tashi.
A lokacin Zahra ta fumito
ganin hakan yasa ta fara kuka don ita abun ya fara
isarta,wayar Alhaji ta kiraa bugu d’aya ya d’auka ta gaya mai abin a ke faruwa ,ko awa d’aya bai ba ya shigo gidan…….A fusace! kirjin sa har ciwo yake,dama yana cike da su .
Mariya na ganinsa suka hau kuka,tambayarsu yai ba ‘asi nan suka ce” Munzo duba Jikin zahra ne shine matan ka suka dake mu,”k’irjin sa ne ya ji yana ne man fashewa ,da fewa yai
ya zauna da sauri suka zo.
“Alhaji” ya dakatar da su
tare da nuna musu k’ofa kowace ta bar mai gida karya bud’e ido ya gan su hakan yasa ..Jikinsu yai sanyi suka zari Mayafai kowacce tai wa je.
Don sun san suka tsaya bashi hakuri sayya musu mai gaba daya don in yayi zuciya baya bukatar abashi hakuri har sai ya huce.
Su Mariya kuwa bayan sun duba zahra suka tafi ,tana zaune sai kuka ta ke ita kam auren nan Ya isheta ta rasa yanda zatai,wata zuciayar tace mata ki dage da addua mahakurci mawadaci .
Malam umar wato baban zahra yaje inda Alhaji yake bussness nasa, ganinsa yai ya kwanta tunani yake yi baima san yazo ba, sai daya bubbu ga san nan ya tashi… “Aa malam ne?
zaunawa yai yace “ashe zahra bata ji dad’i ba, naso zuwa gidan to sai na ga rashin dacewar saboda ga mata manya.”
STORY CONTINUES BELOW

Alhaji yace ai
daka zo kuwa kai da gidan surukinka” dariya suka sa,yaja tsaki baban zahra yace
Ya dai? yace ” wallahi duk wata masifa wallahi mata na
ke sani ,nan ya warware mai komai tun auren sa da zahra da kuma zubda mai da ciki da sukai har fad’an da akai yau.Cikin tashin hankali yace” assha !abu be yiba ,beji da d’in abinda su Mariya sukai ba, nan Malam mahaifin zahra
keta bashi baki ya dawo da matansa bae kamata da girman su ace hakan ta faru ba….Alhaji yace “da sun tsare mutuncin su da hakan bata faru ba .Zahra yarinya ce mai sauk’in kai suba
su gane ba” malam kwa a zuciyarsa tausayin Zahra yake ji, sam bai mata dede ba ya san tana da hakuri ,amma bayanda zai da k’addara,haka ya ta shi bayan sunyi sallama da….Alhaji ya tafi gida ransa a b’ace yana zuwa ko sallama baiba, goggo na d’aurin
lemu ta kalle shi .”Aa Malam! yanzu ka dawo” yace “barni kede ashe! abinda yaran nan suka je sukai kenan!”
Suwa din? nan yazayya ne mata komai tafi ta hau yi “lalle ma! amma ba su kyauta ba” ya kalle ta “ina Aminu yake ne ?suna cikin magana sai ga. Mujaheed kallonsa malam yai yace “kai kira mun su Mariya a waya kace ina neman su tun da
yanzu la’asar tayi ,kace” masu Gobe da safe kowacce tazo ina ne manta”
Mujaheed yace to “baba bari na sayo kati”,nan suka cigaba da tattauna wa
akan zuban cikin zahra wanda Goggo tace “gaskiya na raina wayon matan nan ace kun zau na kishi da ‘yar cikin ku wallahi sun kusa jika da ita haba da shirme in banda ma abin na ALLAH ne ina Zahra ina auren Alhaj ni wallahi… Alhajin ke ban tausayi Malam!.kama ta yai kace ya canja wa Zahra gida”
Nan Malam yace “zanyi tunani idan da hali zan gaya mai” d’akinsa ya
shiga . Azuciayarsa yana mai tausayin zahra ya san
tabbas gidan bai dace da itaba amma k’addara ta riga fata wanan kenan.
WASHEGARI!
Kamar wajen k’arfe goma duk su Mariya sun hallara.Malam ya na cikin d’akinsa duk suka je su ka zazzauna suka gaishe shi, amma ko d’aga ido bai ba balle ya kalle su,sai da ya gama abinda yake ya juyo yace “wato abinda kukai kun kyauta kenan?
Shine don ku kashe wa yarinya aure za ku je kuyi fad’a
da mutane ko? to me ya kai ku?
Cikin in ina mariya tace “Baba wallahu bugon waya k’awarta tai tana kuka wai sun kashe ta shine hankalina ya tashi muka je duba ta shine matansa suka kama
mu da fad’a “
“Duk da haka kun deyi kus -kure kun keta haddi tunda gidansu kuka je,to kar naji kar na gani duk abinda zai samu zahra kar wacce ta kuma d’ibar Jiki taje can na gaya muku kuna ji na?”
Suka ce eh” hakan yai ta musu Nasiha san nan ya
sallame su d’akin Goggo suka shiga suna ta maida
magana.Aminu dake zaune ya na break fast ya had’e rai shi kam yana tausayin yayarsa.
Malam kam samun Alhaji yai da zen- cen san ja gida .Alhaji yace “ai ba matsala nima abun ya soma ban tsoro sam matan
nan basa tsoron Allah,ya ce akwai wani gida a Hotoro G.R.A sabo ne k’arami na gina shi da ‘yan haya zansa, amma yanzu sai ta koma can .” gaisa wa suka kuma yi cikin jin dad’i da fahim tar juna.
Zahra kam cikin kwanciyar hankali ta koma G .R.A wanda su Anty Mariya suka taya ta tsara gidan hankalin ta akwance yanda Matansa ke da mota da driver dake kai su unguwa ha kan yasa ya samu k’aramar mota tare da driver wanda zai ringa kaita unguwa ,tare da mai aikinta Lantana.
Sai bayan komawar zahra .G.R.A da kwana 2 san.
STORY CONTINUES BELOW

Malam ya takura wa alhaji ya dawo da su Uwani. Amma ya ce” ban da su tsigai da Nadiya don ya gaji da rik’e ‘ya’yan da basu da
mutunci ,hakan de Malam ya tattaushe shi (“kaji surukan arziki”) da k’yar ya hak’ura za’a da wo har da su Amira d’in.
Kwanci ta shi ba wuya a wurin ALLAH Zahra ta doshi wata d’aya a sabon Gidanta inda zaman lafiya ya dada wanzuwa tsakaninta da Alhaji,tarai taraya kam ta na shantaa gun Alhaji ayanzu zuciyarta ta d’an samu nutsuwa,ga mai aikinta Lantana mai kirki suna zaman lafiya ta je gidan Maman ta
har sau 2, ita kan ta taji dad’in ganin yanda hankalin Zahra ya kwan ta ,domin da duk abinda ta ke ciki ,Aminu na gaya ma ta
Adduar Uwa karb’ab’b’iya ce kullum dare ba ta bacci.
Tanawa ‘yar ta Adduar samun salaama a auren ta wannan kenan.
Suna zaune A falo suna kallon tashar zee alwan Lantana daga gefe suna d’an hira,ji tai ana buga kofa da k’arfi da sauri Lantana taje ta bud’e Mutanen ne su ka fara shigowa. A razane Zahra ta ta shi Amma se ta basar tana ce wa “ai baki mukai” kalle-kallen falon suke, suna jin jina kai ,cike da gadara ko wacce taja
kujera ta Zauna. Uwani tana ce “lalle Alhaji hmmm mmm!” Lemo Lantana ta kawo mu su zahra kam gaishe su ta hau yi Magajiya ta ce” ke ba gaisuwa mu kazo yi ba sannan ba Lemo mu ka zo
sha ba don kin san akwai a gida,wallahi kar kiga kin dawo nan ba k’yaleki mukai ba.” hajiya Zainab ta ce “Jibi gida wai ita kad’ai lalle Alhaji! A komai sai ya nuna rashin adalci Zahra kam ta ta sunkwi da kai tana jan yo addua (ALLAH HUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA AKLIFNI KAIRAN MINHA) eyi take A zuciyar ta tare da karan ta (LAHAULA WALA KUWATA ILLA BILLAH)domin kauce wa sharrinsu don tsoron su kam ta keji hakan su ka gama magan- ganun su da bud’e- bud’en su suka
tafi sun so zahra ta tan ka ,ita kam tai karatun ta nutsu.Bayan fitar su taja ajiyar zuciya da suka fita lafiya.
suna zaune a falo Jummai k’awar Magajiya ta zo tana tambayar su Zahra suka gaya mata ai ta bar gidan ,nan tasa shewa “amma nai muku murna,”Jummai kenan gida fa ya can ja mata” dafe kirji tai kai haba de? Tace” wallahi
amma wallhi kun yi sake ai wannan gwanda ace tana gidan nan yanzu kuka san irin dukiyar da ze na sakar mata kuwa, lalle! na raina kishin ku yarinya karama tana garaku, Uwani ta ce” wallahi kai na duk ya kunce dabara ta k’are,munyi na bokayen abanza.Jummai tace’ se ku had’a da makirci ai mata fa kuke kuma manya ,yo wane dare ne Jemage bai gani ba!” Magajiya tace” sai daren mutuwarsa” tashi tai ta kama kunnen Magajiya ta rad’a mata, nan suka k’yalk’yale da dariya “kai Jummai shiisa nake son zama da ke akwai wayo” dariya ta fasa “nid’in ai ba wasa ba ce” nan ta fesawa su Uwani duk sukasa dariya.
Yau daya ke Alhaji acan gidan matansa yake, shiga yai
cikin fara’ a su ka tarbe shi sai hidima suke mai shi kam mamaki duk ya ishe shi hira aka zauna ana yi. Magajiya ce tasa kuka. Alhaji? yace “ehem me ke faruwa ne? Nan suka hau
bashi hakuri akan abinda duk sukai wa zahra a cewar su sun yar da da k’addara, ganin hawaye a fuskarsu ya yarda ya nuna bakomi,nan kowacce ta tsiri fad’ar matsalarta ta kud’i take duk ya biya musu ,da zai tafi har da cewa agaida
zahra.
Yau zahra ta tashi da amai kace- kace da Jiri ga ta shin zuciya ,bayan dawowar. Alhaji ya sa suka ta fi Asibiti gwajin farko suka ce ta na da ciki 2 month murna kam kamar ya suma ,hakan suka dawo gida.Lantana ke kula da ita hankalinsu kwance.Alhaji kam ba wanda ya gayawa don yatsorata da su hajiya duk da sun tuban.
Alhaji ke shirin fita, da ya ke yau ya na gun manyan matan har ya shiga mota da sauri Uwani ta je harda d’an russunawa. Alhaji dama ina nai man alfarma wallahi ka ga Larai
ta tafi ganin gida ,to dama ko za kace Lantana ta zo?” saboda lokacin data ke gidan nan da tare nake aiken su”,yace” inane ?ta ce “kasuwa ne su suke siyon mai kyau” yace”to inna je zata zo” godiya ta hau hi
Lantana na zuwa suka ja ta d’aki tai mamaki nan ta zauna suna zaune su uku, Hajiya Zainab ta ce “kin san aikin da muke so ki mana”? tace “Aa Hajiya”
kud’i Uwani ta fito da shi,” kinga wannan dubu goma ne kuma naki,” zaro Ido
Lantana tai “Hajiya duk ni kad’ai?” suka ce “k’warai “
Hajiya ku fad’i kome nene zan muku Inde befi k’arfi na ba” yawwa so muke duk wani abu da ke gudana a gidan Zahra kina kawo mana kome ki kaJi kizo ki ga ya mana” tace” ai me sauk’i ne Hajia” Hajiya Zainab ta ce “in de ai kinki yai kyau za mu k’ara miki dubu ashirin” dad’i ne ya kama ta, da sauri tace “ai yanzu
ma Akwai abun da zan ga ya muku , Zahra na d’auke da ciki na wata biyu kamar had’in baki ko wacce ta mik’e tare da zaro ido,tabdi Jam! in ji Hajiya Zainab,nan su ka sallame ta, ta tashi ta tafi dama tana da tsohuwar nokia mai tochlight ha kan yasa su ka karb’i number dinta.
Bayan kwana 2 su ka kirawo Lantana Lokacin su na gyaran d’aki ita da Zahra ,wanka Zahra ta shiga yi,nan su ka Umarce tada ta d’au ko musu Book kowa ne iri ne, inde da Hand
writing din Zahra aciki Lantana tace”Hajiya mene?” Hand
writing tsaki Hajiya tasa da ta tuna Lantana ce ashe,nan tace”Littafi mai rubutun zahra Inde kingan shi Kika tabba tar na Zahra ne kikawo ma na” tace”ba Matsala Hajiya ai mai sauk’i ne,” da sauri
ta kashe jin alamar bud’e k’ofa.
Dama ce ta samu Lantana Inda ta kalli Zahra “Anty naga Jakun -kunanki na Makaranta ina zan saka su”? nan tace” ki kai mun cikin drower” bayan fitar Zahra da sauri ta bud’e cikinsa’ ta d’auko wani 40leaves ta soka acikin Zanin ta, sauri tai ta gama aikace -aikacenta ta gyara ta fita wajen la ‘asar ta nai mi Izini wai Zata gun Mamanta daya ke Maman tata ma na aiki a wani gidan masu Hannu da shuni,hakan kuwa akai fitar ta bata zarce ko ina ba sai
Yakasai,su Hajiya na Zaune a gefe ga wata mai sai da Kaya irin na mata sun barbaje sai siya suke ,ganin lantana yasa Magajiya ta jata d’aki ,nan ta zaro Book din ta bud’e Murmushi tai Kallon ta tai tace”mene Labari? Lantana ta ce” Jiya
ina d’aki wajen k’arfe 8 Anty da Alhaji na falo naji yana tambayar ta watan cikin na wa tace” mai Uku, Sallamarta tai tawu ce gidan inda dad’i ya kashe ta don yau ma sun bata dubu biyar,Ita aganin ta aiki ya bud’e mata (,Hmm Lantana A juri zuwa rafi dai wata ran tulun zai fashe.)
Bayan fitarta suka taru don tsara yanda za su had’a mata Makircin kiran Nadiya sukai akan ta samo musu wani k’wakk’waran wanda ya iya Rubutu ,cikin Murmushi Nadiya tace” ai kam ina dashi”don yan zu Nadiya bata Zaman gidan kullum tana biye -biye ga Shige wa Maza ,ta dad’e da fara School wato Federal College of Education amma in taje banda bin Maza
ba ta Karatun komi,Carry Ovar ne fall akan ta,kuma Duk Alhaji ne yai wahalar School din ,wannan yasa ta d’auki Book din domin ta kaiwa wani Saurayin ta Class Mate nata ,duk suka gaya ma ta abinda za a Rubuta ya zamto iri d’aya dana Zahra wan nan Kenan.
Kwanci tashi ba wuya a gurin ALLAH cikin zahra ya cika wata na takwas, inda take samun kulawa daga gun Alhaji da kuma
gida.
Ab’angaren Manyan Mata kuwa, kullum cikin kawo musu gulma ake amma abi yaci tura,daga suje gun wannan boka se suje can, duk sun tashi hankulan su akan cikin Zahra,wanda Allah ke dad’a ikon sa Akan Al amura.
Alhaji ne gaban doctor shi da Zahra ana yin scanning na ganin abinda ke cikin ta ,d’ago wa Doctor yai suka gaisa da Alhaji,yace mai
“Congratulation Matarka na d’auke da twins duk Maza, da sauri Alhaji ya mike tsaye “masha Allah godiya yai wa Allah daya cika mai burinsa, ya kalli Zahra da ta sunkwi da Kai saboda kunya ,yace” “Lalle Zahra kin kasance mun SANYIN IDANIYATA tauraruwa acikin taurari”
Shi kam Doctor mamaki ne k’arara a fuskar sa yanda kamar Zahra itace matarsa, shi kam afarko ma ya d’auka ‘yar sace, nan ya basar da tunanin.
Tunda suka koma gida Alhaji ke nan nan da Zahra kamar k’wai Lantana da ke aikace aikace, duk gulma na cinta amma babu
dama time da suka shige d’aki har lab’ewa tai,amma taji shiru.
ALhaji ke zaune sai harhad’a Takardu ya ke ya na cikewa, Zahra ce ta shigo ta Zauna ,tana gaida shi ta ce “Alhaji ya kamata na koma gida ko tunda kaga lokacin Haihuwar yazo
,d’ago idonsa yai ya kalle ta “Aaa ki Zamanki in kin haihu sai ki tafi” shiru tai bata ce komi ba.
D’agowa yai ya kalleta ya ce” karb’i wannan ki gani” Karb’a tai tana dubawa ko ina sai taga ansa hassan
and hussain, d’agowa tai tana neman k’arin bayani nan ya ce” mata duk rabin dukiyata da kadarori na duk na saka sunan babies dinki”
kasa magana tai in banda kallo data ke binshi da shi Hawaye ne suka zubo mata ,ta kasa magana abinda ba ta tab’a yi ba Rungume Alhaji tai tana godiya ,bayan ta share
Hawayen ta tace”Alhaji ka aje a wajen ka” yace ba
matsala a,kasalance ta tashi ta fita dakyar.
BAYAN KWANA 2
Zahra na zaune da cikinta duk ya mata nauyi tana shan romon Kifi ,A lokacin tana watan haihuwar ta.Lantana bata nan,gashi tana so ta gyara mata d’aki,sai wajen 2 Lantana ta dawo,adede Lokacin Alhaji shima na faka Motarsa.
Share- share Lantana ta fara yi,nan ta shiga d’akin Zahra ta gama ta fito. Alhaji ne Ya kalli Zahra muje d’akiinki mi Magana nan
suka Shiga, toilet ta Zarce shi kam Alhaji ya kwanta akan gadon Hannun sa ne yaji yana tab’o Kamar Takar da ,d’auka yayi ya bud’e Wasik’a ce ya gani guda 2 da kamar bazai karanta ba, sai kuma yaga kamar irin hand writing in Zahra ya dauka ya fara yaga kamar haka:
_dama ba sonsa nake ba inason gaya ma cikinka yana ta girma_
Tashin hankali ya aje ya dau dayar karanta waya farayi cikin tashin hankali,ba inda ya fi bashi mamaki sai gun da akace” _KI KULAMUN DA CIKIN DAKE JIKIN KI DON INA SONSA MATUK’A ga wasikar da kikai mini nan na maido miki.Daga tsohon Masoyinki._
Tashin hankali wanda ba asa masa rana,kansa ne ya fara juyawa fitowar Zahra da sauri ya b’oye Takardar mamakin ta yake gani tai ya canja tace “mai Alhaji meya faru”? Nan yace” mata kansa ke ciwo tashi yai ya futa,Mamaki k’arara afuskarta sai ta basar Don ta tuno da kashedin likita kan ta dena yawan tunani.
Tashi tai ta shiga d’akin sa ganin sa tai ya sunkuyar da kai ,zama tai kan kujera tace “Alhaji wai meya faru? d’agowa yai taga jijiyoyin kansa sunyi burd’un -burd’un da sauri
Ta tashi ta komaa kusa da shi tace “Alhaji wai meke faruwa ne?
STORY CONTINUES BELOW

Yace” Zahra kin ban mamaki yanzu duk irin zaman da muke dake na d’auki soyayya ta na baki amma ashe amanata
kikeci?
Cikiin tashin Hankali tace” Alhaji ni”! Take hawaye kamar me sukai ta zubo mata,nan ta tsugunna tace” Alhaji wallahi ni ban san Komi ba” D’agowa yai “Ai dama bakya sona shi isa zaki mun hakan.”
Tace “wallahi nasan dokokin Allah da k’imar aure bazan ci amanar ka ba” Zaro wasik’ar yayi ya mik’a mata “karanta ki gani” bud’ewa tai hannun ta na rawa lokacin da ta gama karantawa k’ara ta saki tare da dafe ciki ,kuka takeyi cin k’arfinta Sai kiran
Sunan ALLah mai girma take,da kyar ta tashi ta d’auko Alkur’ ani zata dafa,cikin k’arfin Hali ya k’wace,cewa tai “ka barni na dafa Alkur ani wallahi tallahi ban san da wasik’ar nan ba”
Jikin sane yayi sanyi,kamo ta yayi ya rungume ta tare da bata hak’uri tana kuka tana yiwa Wanda yai mata Allah ya’isa.Zazzabi ne ya rufeta .
Lantana ce a gaban Hajiyoyi tane sanar dasu tabbas ta aje wasikar nan kuma a d’akin ,har take sanar da su ai lokacim da
suka shiga d’akin ta ga lokacin da Alhaji ya fito ransa Ab’ace, nan suka sa dariya “da Alama aikin mu wannan karan zaici”
Sai b’arar gyad’a suke suma afawa abaki,duniya tai musu dad’i Nadiya ce ta shigo falon sai taunar chew gum take nan Uwani tace “Nadiya kinsan kuwa su Amira na gab da aure idan
baki fidda miji ba”.
Tab’e baki tai “zanyi mana ita Amirar wa zata aura? Hajia Zainab tace” ‘yar gida za ai ita da Hameed ashe sun dad’e suna soyayya” tashi tai tace “jaraba gaskiya Amira na shigar
mun hanci da kudun dune saurayin nawa zata aura”
Amira dake shigowa falon tace “A ina ya zama saurayin ki? ja jiki Kawai kije ki nemo naki,Hameed nawa ne”
“Wallahi baki isaba ba cewar Nadiya”
tsigai da ke taje kai tace “kai Anty Nadiya saurayin fa Amira ne waye bai san suna Soyayya ba duk gidan nan”
“Dallah rufen baki ke wama zaice yana sonki “jibar ki fa ko tudin kirki Baki da shi”
Nan Magajiya tasa baki “Aa Nadiya karfa ki zak’e duk anfiki Gaskiya.kuma tsigai da kike kushewa Da me sonta ,ke de zauna kina yawon barbad’a”
Nan Uwani tace “ya isa hakan aiba wani abun take ba.”
Tsigai ta tashi zata shiga d’aki ,ta kalli Nadiya tace “ke kam Anty abu yai miki yawa ,ya kamata kije ki tambayo Ya Hameed in kinga sai ya tabbatar miki da gaskya”
Da sauri ta shige d’aki Nadiya tace “Wallahi dakin tsaya da saina karai-rayaki mai kama da sauro
– Yau Zahra ta tashi duk bata Jin dad’i daure wa kawai take yi Lantana na kula da ita ,zuwa tai tace
“Anty na ga kamar bakya jin dad’i ko zaki je ki kwanta kafin Ai sallar la asar”
Tace “wallahi kam bari naje na kwanta ko na d’anji dama-dama” shigar ta d’aki ke da wiya ta d’auko wayarta ta bugawa su Hajiya Uwani,sai jin -jina kai ta ke Alamar tana gane karatun da suke gaya mata,sallama sukai ta kashe.
Da sauri ta d’au mayafin ta, fita can waje tai tana waige -waige,waya ta d’auko tana kiran Salele ka tawo kuwa?” tun yaushe gani a bayan Layin nan Tace “to Lokaci yayi sai ka zagayo” da sauri ta koma ciki,tana tsaye har ya k’araso duddubawa tai taga ba Maigadi na sharar bacci da sauri su ka shige gidan, adede bayan kofar d’akin zahra Salele ya
lab’e komawa tai ta cigaba da aikinta tanayi tana wak’e-wak’e k’arar hon d’in mota taji ta wani daka tsalle.
STORY CONTINUES BELOW

Alhaji ne ya bud’e falon da sauri ta sunkuya tana gaida shi,tambayar
ta yake ina zahra,nan tace “tana bacci ad’akin ta”
D’akin ya dosa salele na bayan k’ofa yaji Alamar tafiya, da sauri ya fito yana k’okarin sa riga,sai Alamar gudu yake ,wuce Alhaji yai da sauri take Alhaji ya bishi ,Lantana ce ta tashi da sauri Alamar mamaki ta toshe baki. Alhaji bai samu damar kama shi
ba ya gudu.
Cikin huci da k’unar rai ya dawo, Kallon Lantana yai
wanda duk ta wani rikice,(Mara gaskiya ko A Ruwa gumi yake) sai kar -karwa Jikinta ya ke Alamar munafinci yace ” yaushe wannan ya shigo, d’agowa tai “Alhaji ni ban sani ba wallahi don ina d’aki ina guga” tsaki yayi d’akin zahra da sauri Lantana ta d’au waya tana gaya musu, Alamar aiki yai kyau. Alhaji ne ya tsaya bakin k’ofar d’akin ya kasa shiga. Hawaye ne ke zuba
babban Mutum da shi .
Allah sarki baiwar Allah sai sharar bacci ta ke bata san meke wakana ba,tashinta yai mutsits -tsike ido take ,ta kalle shi “Alhaji yaushe ka dawo? hawayen da ta gani Afuskarsa shiya gigita ta, “Alhaji meya faru? dakatar da ita yai yace “kinci Amana ta Zahra ran nan na ga wasik’a kince baki san zance ba yau kuma har gardi ad’akinki WA IYA ZUBILLAHI”.
Saida ya jinjina kai.
“Amma Zahra Albasa ba tai halin ruwa ba,kin bani mamaki”
Kuka take shab’e -shab’e ta rasa bakin magana ce mata yai ta sa hijab din ta,ba musu ta sa suka fita tana kuka. Lantana dake lab’e tasa dariya (Lalle kud’i ba yanda basa maida mutum Lantana kenan)
hakan yaja ta bai zame koina ba sai gidan su, Dede sun tsaya a k’ofar gidan Lokacin Malam ya dawo daga masallaci,sun gaisa yake sanar mai ai
yakawo Zahra ne Malam yai mamaki don sunyi magana da Alhajin sai ta haihu za ta dawo, Mamaki ya isheshi ,sai bece komi ba, akwatin taja ta shiga cikin gidan k’irjinta na dukan uku- uku, shi kam akofar gida sukai Sallama ya tafi.
Malam ke tambayar ta Allah yasa ba takurawa tai ba ,sai ta dawo hawaye ne ke san zubo mata tace “Aa shine yai ra’ayi” shide bai gamsu ba amma ya k’yale tunda basu ce mai komi ba,tunda ta shiga d’akin Goggo take kuka ,da taga alamar
za a shigo sai ta rufe Ido (Allah sarki baiwar Alllah INNALLAHA MA’ASSABIREEN)
Tunda Alhaji ya koma gida ya rasa sukuni ,kamar k’aramun yaro haka yake kuka,bak’in ciki yai mai yawa. shikam ya shiga rud’ani akan cikinta don gani ya ke kamar bana
saba,k’irjinsa ne ya fara ciwo dafe wa yai ,dak’yar ya d’auko Maganin sa ya sha, ya d’an samu relief,muk’ulli ya d’auka ya fito, kiran Lantana yai yace ta shirya ta tafi can gidan ta ciga ba da musu aiki
Sunkwi da kai tai “Alhaji ina Antty ne? ko haihuwar ce” yace mata “Eh tafi gida.”
had’a kayanta tai tafi yakasai,bayan taje duk ta sanar da su Hajiya dad’i ne ya kashe su sai Annashuwa suke don samun nasara.Hajiya Magajiya tace” saura cikin idanta haifeshi ma san yanda za ai”
Tafawa sukai na jin dadi Lokacin da Alhaji ya shigo suna lura da shi sam ba shida walwala,sai tambayar sa suke haka dai suka gama kisisinarsu da sun keb’e su hau dariya ,kwana 2 Alhaji ya rasa sukuni ko abinci baya ci duk ya fad’a (Allah sarki)su kam sai wadak’ar su suke don burun su ya cika,sun fidda Zahra a ganinsu tofah
Tun asuba Zahra ke jin ciwo amma bata ga yawa kowa ba har Saafiya, Goggo na kula da ita sai ta share,don ta kula kwana biyu tunda ta dawo bata da sukuni ta sha ganinta tana kuka.
STORY CONTINUES BELOW

Tana cikin d’iban ruwa abuta cikin ta ya murd’a dafewa tai kuka ta fara Da sauri Goggo ta taso tace
“Zahra kode haihuwar ce? dama ina kula dake” kiran Aminu tai daya shigo tace “ya samo mota” cikin yan lokuta ya samo suka tafi Asibitin da take Awo.Aminu kam waya ya bugawa Malam domin Doctor yace ba zata iya haihuwa da kanta ba dole aiki za’amata. Saboda yaran duk ba adede suke ba. Zuwan Malam yasa aka nemi wayar Alhaji amma ba ta shiga. Ak’arshe dai shi
ya cike Aka shiga da ita d’akin thearter. Auta sai kuka take hakan Aminu duk sunyi jugum-jugum saida Malam yai musu magana
suka daina.
Wajen kamar Awowi Aka fito da babies da sauri Goggo ta karb’a tana “Ikon Allah dama ‘yan biyu ne? gashi duk maza” su Auta nan suka fara dariya,nurse ce ta fito ta karb’esu
Malam ya ce” ina Mamansu tace” tana d’akin hutu.
Kafin kace mai duk su mariya duk sun hallara har da matan su Atiku duk
yayunta dai kowa kagani na murna Ab’an garen Alhaji kuwa rashin lafiya ya kwantar shi tun lokacin da ya dawo daga shigowarsa babban falo yaga ba kowa d’an hayaniya yaji ak’aramin Falo kamar ance ya tsaya yaji Hajiya Uwani na magana “ai Salele ya iya aiki shegiya Lantana akwai iya makirci” gaban sa ne ya fadi yaji suna Zencen
takarda duk wani abu duk yaji su,har yaji sanda suka
bawa Lantana kud’i ta bawa Salele duk ya gama jin komi dafe kirjinsa yai, zama yai akan kujera nan yaji mugun tausayin Zahra tashi yai zaije d’aki ko gabansa baya gani sai kawai ya yanke jiki ya fadi.
Fitowa Sukai Bayan sun gama shewarsu ganinsa da sukai ak’asa yasa suka fasa ihun munafunci Hameed nai ya taimaka aka
kaishi Asibiti……………….
Sun je Asibitin da ya ke zuwa da sauri aka karb’e shi Saboda sun san shi.Su Hajiya Uwani duk sun cika Asibitin da ihu.Sai da wani Doctor ya tsawatar musu,duk sun zauna a reception
sun cika waje ,da Sauri Alhaji tahir ya shigo da Alama su ya ke naima ganinsu Magajiya da yai ya tsaya yana tambayar su ina d’akin da Alhaji yake, a yatsine suke kallonsa ba wacce tace kanzil sai kallon banza.
Tabbas yasan halinsu bazai canja ba. Alhaji bai sa ar mata ba duk sun raba zumunci sun rabashi da ‘yan uwan sa ,yana tsaye Hameed ya tawo yad’an rusuna ya na gaidashi nan ya mai
Jagora inda yake shikan shi da yaga Alhaji ta window sai daya zubda hawaye. Doctor ne ya fito yana tambayar su waye ‘yanuwan Alhaji? da sauri Alhaji tahir yace “gamu ni k’aninsane wan nan kuma yaron gidan sane” kallonsu yai yace
“kuzo muje offfice”.
Bayan sun shiga doctor ya ja dogon Numfashi ya kalle
su yace”Agaskiya Alhaji na cikin mawuyacin hali don.Jininsa ya hau sosai, badon ankawo shi asibiti ba da tuni ya samu ciwon b’arin Jiki,ga zuciyarsa na Alamar ciwo.Agaskiya ya kamata ana kwantar mai da hankali”
Hankalin tahir ya
tashi sai zufa yake ,duk yad’ora Alhakin Akan Matansa duk da yasan bamai d’ora cuta sai Allah,amma tabbas suna da kamasho.
Ab’an garen su zahra kuwa ,ta farfad’o amma in banda kuka ba abinda take sun lallashin amma tak’i shiru sai da Maman ta da ta zo tai Mata Magana ta bari ,duk da ta san akwai abinda
ke damunta.
Malam yaga shiru ba Alhaji,ga shi wayarsa switch off ,k’awai sai ya yanke shawarar zuwa gidan.
Bayan fitarsa ya tafi gidan Alhaji Maigadi ya tarar ya
ke tambayarsa ko Alhaji na nan? take ya sanar mai ai Alhaji ba lafiya yana Asibiti,sallallami ya fara yi yana tambayarsa ina aka kwantar da shi nan ya sanar mai yace ” ikon Allah
Asibitin da zahra ke ciki kenan, sallama sukai ya
koma shigarsa Asibitin suka ci karo da Alhaji Tahir nan suka gaisa yake tambayarsa inda Alhaji yake, take ya sanar mai ai Amaryarsa ma ta haihu twince wani murna Alhaji Tahir yaji ta shige shi Hameed ma ya murmushi.
Ak’alla yau kwanan Zahra 3 a Asibitin Alhaji kuma 2, yau dai ya farfad’o amma baya iya magana Malam ne ya zo yana mai ya Jiki duk jibga -jibagan sun cika d’aki sunki fita sai da suka fita san nan ya kalli Alhaji yace “ka godewa Allah Fadima ta
sauka an samu ‘yan biyu maza”
Murmushi yai tayi sai ga hawaye Hannunsa ya d’aga sama yana Addua ,nan Alhaji yace” ai suna Asibitin nan” take Malam ya fita yai wa nurse magana
yana son akai
wa Mara lafiya ya ga twince da sauri ta debo su cikin ikon Allah ba kowa d’akin. Alhaji har da Hawaye sai kallon su yake yana murmushi Azuciyarsa yana godewa Allah. Alhaji Tahir ma ya shigo ya gansu sun bashi sha ‘awa nan yai musu hud’uba da hassan da hussain ga su Kyawawa.
Satinta daya ka a sallami zahra yau suka biya d’akin Alhaji dakyar ta shiga tana zubda hawaye ta kasa had’a ido da shi hannu ya d’aga yana nuna Alamar tazo ,su malam fita sukai,zuwa tai ta dan jingina da karfen wajen tana neman Afuwan sa, cikin nuna Alamar Nadama da hannu ya nuna bakomi,Magana taji yayi yana cewa “zahra kiyi hakuri ba laifin ki bane don duk naji gaskiya duk sharri da Makircin matana ne Amma Nagode wa Allah daya bani Twince ki
rik’en su Amana wan nan takardun suna nan zan sa ki d’auko ki aje gunki nima jibi a sallame ni,” Ita kam tausayin sa take Ji dakyar ta tafi Goggota shigo tana mai sannu ,ta Jata suka fita.
Zahra sunje hanyar fita taji An bangaje ta ta juya ganin Nadiya tai take ta girgiza kai .Goggo ce tace “ke baki da hankali ba kiga mara lafiya bace? zaki bangaje ta” taunar chewgum take harda su kwai tace “ke tsohuwa bana son shish -shigi.”
Zahra ta juya tace “Goggo kiyi hakuri mu tafi inde wan nan ce zatai abunda yafi hakan ‘yar rik’on kishiyata ne hajiya uwani” fita sukai suka tafi gida.
Hakan Alhaji na kwance a sibitin ya saki bakin aljihu ana ta hidima komi waja-waja agidan su zahra Albarkacin twince.
Alhaji Tahir sai kai kawo yake daya yake an daga sunan aka zabi wata ranar suna aka yanka raguna manya manyan raguna biyu da tirkeken Sa guda daya kaya kam kamarsa magana.
Saboda Alhaji akwai alheri zahra ma kam kullm cikin sabbin kaya take sai dai ba ai suna ba saboda rashin lfyar Alhaji.
Duk wan nan abun da ake hajiyoyin basu san maike faruwa ba,don Alhaji yace kar wanda ya gaya musu ko Hameed shuru yai da bakinsa,yanzu harka ta bude musu kullum cikin karbo wannan karbi wan cen Alhaji Tahir kam kobi takansu baya yi duk Alhaji yasa Alhaji tahir ya debo mai document nasa nan ya ware takardun da yasa sunan twince,su kam in banda suzo su cika asibiti kamar gidan biki,har an gane su suyi ta
ciye-ciyensu su .
Nadiya a d’amo dinki azo aita karairaya gaban nurses maza da Doctors Suna zaune hajiya tace “kamata yai mu fara karbar kudi
musan me muka kama tunda kunga in Alhaji ya mutu ba muda rabo mai tsoka,kunga Hankalinmu yanzu akwance yake tunda ‘yar nacin ya koreta ,kuma boka ya tabbatr mun cikin jikinta ya zube”
Nan suka tafa “to dama zamuyi hasara biyu ne” duk sun sakace kud’aden Alhaji nagidan suka koma kantunansa suna karb’ar kaya da kudi hankalinsu kwance sam basu damu da rashin lafyarsa ba sai dai kawai su cika asibitin don kar ace basu zuwa.
STORY CONTINUES BELOW

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah ZAHRA tayi arba’en sunyi kyau sosai ita da twince babies din kamar ka dauka ka gudu saboda kyau don Zahra na da kyau sosai,duk sai sukai kyanta sai skin din hussain da yai irin na Alhaji da hancinsa suna samun kulawa ta b’angaren Alhaji Tahir Saboda Alhaji ya bude
bakin Aljihu kawai hidima ake musu kuma kullum sai ankai su ya gansu tun kan tai arbain Yau kamar kullum sun shirya don yau ta cika arbarn din nan Malam yayi mata umarni data jegun mijinta ,hakan kuwa akai tafiya sukai itada auta.
Alhaji yaji dadin ganinsu tunda Zahra taje take kuka saboda yanda Alhaji duk ya rame ya dada manyanta, sai dai yanzu yana iya tashi hakan yasa
yad’au twince ,nan da nan Zahra ta hau hidima da shi,sai wajen magariba suka tafi,wanda duk wanan abinda akai acikin matan ba wacce ta shigo ,dama kullum sai aukin zuwa amma ko ruwa basa bashi ,sai dai ‘ya’yan Alhaji tahir maza suke kula dashi kuma
su kwana agun shi wan nan ke nan.
Cikin ikon Allah Alhaji ya warware har an sallameshi,
ya koma gida,kowacce sai ta tsiri nan nan da shi shi kam yanzu yasha jinin jikinsa da su,sam baya son ganinsu amma ba yanda
ya iya kwana 2 da komawarsa Zahra ta koma gidanta,tare da Auta da za ta taya ta aiki da mai aiki d’aya.
Hajia Uwani ce zaune bayan mota suna hira da Driver zai kaita unguwa nan yake mata barkar haihuwar zahra dafe kirji tai “habade wace Zahran?” yace “Amaryar Alhaji yace haihuwa mai albarka twince” jitai ta k’ware sabod kid’ima ba shiri tace ya maida ta gida,tun daga falo ta shiga kiran su, suna fitowa ta gaya musu ,ai bamu ga ta zama ba hakan yasa suka zari mayafai
don yanzu ba sama tambayr Alhaji in zaasu fita,gidan boka Suna zuwa sun tarar ba kowa duk su ukun suka shiga take suka sanar mai nan yace “mai za’ai?” suka had’a baki akashe su boka?”
STORY CONTINUES BELOW

dariya ya busa wan nan mai sauk’i ne take ,ya basu wani laya yace su binne kuma su tabbatar d’aya daga ciki ta fita
a gobe ,taje gidan ita yarinyar ta tsaya a waje zansa d’an kutunba ya fito da Jaririn”
Kamar yanda boka ya sanar musu hakan su kai,Hajiya Uwani ta tafi,tun wajen k’arfe goma na safe tana k’ofar gidan Zahra
sai kace Almajira.Twince na kan gado time an musu wanka ,itama Zahran ta
shiga toilet don yin wan kan Auta na wasa da su kamar ance ta tashi ,sai ta mike ta fita ,fitowar Zahra daga wanka taga ba hussaien sai hassan sai bata kawo komi ba tai tunanin Auta ce ta d’auke shi,shigowar Auta ta tambaye ta hussain nan
tace “Ai anan na barsu na fita na dafa indomie” “to ko sahura ce ta dauka?mai aikin su, Auta tace “anya? na ganta a kitchen ta na Moping”
Take hankalinta yai dubu ya tashi nan suka hau
dube- dube duk gidan ba inda ba su duba ba.
Adede lokacin Hajiya uwani na zaune,taji ku kan baby abayanta take ta Juya ta ganshi ajiye cikin towel Murmushi ta fasa “tabbas shine ga kamannin zahra “,da saurin tana
waige-waige ta d’auke shi,bakin titi ta fita ta hau Taxii Zahra kam sai kuka take harda su suma ,da k’yar Auta ta samo Layin Alhaji tana gaya mai,shima hankalinsa ya tashi,da sauri ya tawo gidan zuwansa keda wiya zahra na farfad’owa kuka sosai take yi hankalinsa ya tashi ,take k’irjinsa ya hau bugawa da sauri da sauri,kansa na juya wa zama yai yasha Maganinsa,Auta ce ta sanar da su Goggo suma hankulansu ya
tashi don sun shaku da twince,har wajen 6pm ba labarin hussaien suman zahra 2 wanda har yanzu d’aurin k’irji ne Ajikinta ba inda ba a duba ba amma shiru ka ke ji,Malam ne ya tafi gun malam mai Almajirai ya sanar da shi take suka fara sauka da k’yar zahra taci Abinci Hassan sai kuka yake kamar yasan An d’auke d’an Uwansa,” Allahu Akbar”
STORY CONTINUES BELOW

Hajiya Uwani kuwa Lokacin da ta shiga taxi sai ta ce ya kaita k’auyen d’an -dalama don Acewar ta yau bazai kwana
Aduniya ba,Tafiya suke don ta ce “karya dau kowa zata biyashi. sun karya kwana zasu mik’a Titin da zaikaisu d’an-dalama hannun d’an Taxi ya k’wace Sakamakon wani d’an keke Napep ya shigo ba dai-dai ba,take su kai karo taxi din ta bigi wata babbar motor.Mutane suka taru sosai aka Zaro su cikin Ikon Allah ba wanda ya Mutu driver d’an kurjewa yai Hajiya Uwani kuma k’afanta ne ya karye da hannun ta,ta kuma bugu A kanta,wani Ikon Allah hussaien ko k’warzane ta ke ‘yan
sanda suka d’auke shi aka wuce da su Asibiti.
Zahra tun data tashi ko Abinci ta kasa ci shikan shi Alhaji daurewa yake tamkar gidan mutuwa.
Bayan an kai su Asibitin wadda Uwani bata san inda kanta,ya ke,ba ko motsi ba tai ,take su ka d’au Jakarta wayar ta suka
duba Last call nata ,nan suka Latso Hameed ,sallama yai nan suka sanar da shi yazo Asibiti akwai mara Lafiya da Jariri,hankalinsa ne ya tashi ,yai Mamakin dalilin da yasa Uwani tad’au hussain ,take ya bugawa Alhaji ya ke sanar da shi da sauri ya mik’e sanar da zahra Abayarta ta d’auka suka d’unguma har da Auta shigar su Asibitiin suka tarar da Hameed da d’ansan dan nan yai musu tambayoyi ya
tabbatar sannan yaba su baby dinsu. Bak’in ciki ne ya ishi Alhaji daya ji wadda ta sace mai Jariri A lokacin ta farfad’o Alhaji akan
ta ya tsaya zuciyarsa na tafarfasa kallonta yai a karo na biyu yace
“zan biya k’udin Magani amma ki sani karki soma dawon gida na sake
ki saki biyu”
Tana kwance akan gado ba damar tafiya sai kuka take tana bashi hak’uri Zahra kam ko kallonta ba tai
ba.
Juyowa yai yace”kuma ki tabba tar kintafi da wan nan ballagazar yar rik’on taki wato Nadiya”
Bayan Alhaji ya maida zahra gida sun nutsu an treatment in hussaien .Alhaji bai zame ko’ina ba sai yakasai,shigarsa ya gansu cirko -cirko take ya nuna Nadiya da yatsa yace ta tattaro kayanta ta bar mai gida don ya sallami Uwar dakinta”
Hankalinta ne ya tashi hardasu kuka tsawa ya daka Mata da k’yar tabar gidan san nan ya kalli Hajiya Magaijya da Zainba nan ya hau musu fad’a ta inda ya ke shiga bata nan yake fita ba sai daya musu kaca -kaca yace” kuma duk wani k’ulli da suke mai ya sani,su kam Jikin su ne yai sanyi suka hau bashi hak’uri kallon su yai “wallah idan baku shiga hankalinku ba duk sai kun bar mun gida wallahi in ban da ta shin hankali ba abun da kuke sani,kunci Albarkacin Hameed da kuma ba zaku kwana A gidan nan ba ,amma kunci Albarka cinsa”
Kowacce tai gum ba bakin Magana fita yai ,duk suka zube a kujera suna mai da Numfashi
Yau watan su ,twince Uku duk sunyi wayo.
Ciwon Alhaji ne ya tashi tun yana daurewa har ya fara sarewa Alama su Hajiya suka gani sai su kai biris dashi
domin Aranar da ciwon nasa ya tashi yana gidan su ,ya fito daga d’akin Magajiya,kawai ya yanke Jiki ya fad’i ganin hakan
ya mik’awa hajiya hannu ta d’aga shi inban da dariya ba abunda take Cikin Ikon Allah sai ga Hameed zai je d’akinta da sauri yazo ya d’ago shi ,take ta fara KuKan Munafirci.
STORY CONTINUES BELOW

Asibiti suka tafi ,Hameed har kuka yayi saboda mamakintak’arara son kashe Alhaji suke,sanda ma suka je bai san
wake kansaba anba shi gado ,San nan ya bugawa Zahra rud’ewa tai suka tawo Asibitin,kafin dare asibitin ya cika da ‘yan
uwa domin har Lokacin Alhaji bai farfad’o ba ,sai wajen 8 na dare ya farfad’o ganin zahra da twince agefen sa yasa yai
murmushi.Alhaji tahir ya shigo haka Malmm, kallon ta yai yace “Zahra na gode miki saboda kin zauna dani bisa Amana duk da nasan ba kya sona.Allah yai miki Albarka.”
Ita kam inban da kuka ba Abinda take,Nan ya d’auko takardun nan ya bata yace “wan nan halak malak na baki
Gidana sabon da nake gi nawa, baya cikin gado ,ya cewa Alhaji Tahir kazama shaida ko bayan raina”
duk idanuwansu ya kawo ruwa suna cewa Alhaji zaka tashi kiran Doctor akai,ya dubashi yayi ya Umarcesu da su fita su barshi ya huta, hakan kuwa Akai time da Zahra zata Fita yace
“Mik’on twince na Kallesu” kaisu tai ya shafa kansu yace
“Allah ya daukakaku ya baku kyakkyawan rayuwa kuje Zahra.”
fita sukai dakyar take jan k’afa ita da Auta driver ya mika su gida, ganin su magajiya tai birjik a reception har tafawa suke tamkar
yara.
Tun da ta koma gida take kuka domin Alhaji ya bata tausayi,ganin su twince sunyi Bacci yasa tai Alwala tai
ta Sallah sai wajen 2 na Dare tai bacci,wajen 6 ta mik’e don jinta take tamkar ba ita ba,sauri -sauri take itada Auta bayan sun gama shiryawa Driver ya d’aukesu ,ganin yad’au Hanyar Yakasai yasa tace “habu ina zamu kuma? Bayan Asibiti” take yace “wallahi ban san dalili ba Ande Umarce ni da muje can din” Jikinta nai yayi Sanyi, sunyi tsuru -tsuru Abayan
Mota Ita da Auta.Ganin Motoci Manya -Manya tun daga bakin Titi har cikin Layin gidan Alhaji,gabanta ne ya fad’i ganin Mutane take tafara kuka. Ita da Auta.Driver ma hankalin sa ya tashi.
Da sauri ta fito suka shiga gidan ,tana shiga taga Mata nata
kuka su hajiya Zainba har birgima suke suna “Wayyo Alhaji ka tafi ka barmu”
Anan ta zube Asume Mata sukayo kan ta.
Bayan ta farfad’o tai ta kuka, tana tuna Jiya kan wasiya da Yai mata Allah sarki take ta d’auko Alkur’ani tana karantawa,Su Hajiya Magajiya kuwa duk sun bazu d’akin Alhaji
suka shiga sai bincike suke duk sauran kud’adensa sund’ebe su Agogo ,kayan abinci kuwa kamar kasa haka Ake kawo wa
sunja Buhunhuna duk sun b’oye Ad’aki,sai da suka kammala San nan suka dawo suna ta matse Hawaye.
Duniya kenan Alhaji tasa tayi kyau don ya cika da Kalmar Shahada,ya barma su Duniyar.
Yau Akai sadakar Bakwai,duk an watse Zahra taso tafiya Amma Malam yace ta tsaya ta gama takaba,Hakan ta zauna zaman ba dad’i don su magajiya sun kane komi na gidan Sai saida Abubuwa suke,kallon su kawai take.
Kwanan Alhaji 20 da rasuwa suka matsa Lamba sai an raba gado,Hakan zasu fita duk da basu gama takabar ba suje har gidan Alhaji Tahir suna bala’i sai an raba Gado. Ran nan zahra na ban d’aki hajiya Zainba taga Auta a falo da hassan A hannunta Murmushin mugunta tai,daukansa tai da gan- gan ta sake shi,k’afafuwansa ta rike kansa na k’asa Auta k’ara tasa sakinsa tai da sauri Auta ta taro shi ,sai
kuka yake.Take taimai targad’e ak’afa,haka ta zauna A kan kujera ana Jijjiga ta. Zahra na zuwa ta d’auketa da mari tace “da ba yanzu bane” ALHAJI TAHIR ta bugawa ta sanar mai take yaturo Doctor aka dubashi.
Kayanta ta shirya suka tafi gida ita da Auta,shigarta yasa Malam ya daka mata tsawa “kina takaba din kike yawo tana Hawaye ta sanar mai neman kashe sun da suke so suyi tunani yai yace” Allah ya kyauta dakinsu nada Ta share suka gyara
ba abinda babu aciki Taci gaba da takabar ta.
Yau take dai de wata hudu da kwana goma ta gama takabar su ,washegari duk aka tarasu a gidan Alhaji na Yakaasai an d’auko wani Malami don Rabon gadon duk an taro mai dukiyar,kowacce acikin matan
ta samu tumunin takaba wato d’aya bisa takwas Sauran dukiyarsa da sha gunansa duk na twince ne,bayan ya gama Rabon ya
ce da kowacce “idan da mai Magaana yayi”.
Take HAJIYA Magajiya ta ta tashi “Gaskiya Malam Rabon nan bai kyau ba ,ba ai dede ba,ta yaya za ace d’an wannan
dukiyar za a bamu” Duk dad’ewar da mukai da Alhaji.Ace wan yarinyar yar cikin mu duk ta kwashe dukiya Ita da yaranta to wallahi ba zamu yarda ba”
Alhaji Tahir tashi yai yace “ke baki isaba wallah don bake kika ce abada ba Allah ne don haka tun da an baku gadonku sai ku bar gidan nan”
Malam yai gyaran Murya “to nide Abinda Allah ya Hukunta dashi nayi amfani da Alama baku da Ilmi ,da ace kuna da Ilmi sai nace ku duba amma duk da hakan zaku iya zuwa aduba Muku cikin SURATUL NISA’I AYA TA 10,11,har zuwa ta 12 to ,ALLAH SUBHANAHU WATA’ALA dakansa ya raba don haka sai ku d’au Rabon ku kuma duk inda zakuje wanwan Rabon za amuku, domin da namiji yana cinye dukiya ne ,kuma yana daukan kaso biyu na mace daya. matan mamaci kuma tumuni komai yawan dukiya idan aka baku tumuninku to su yaran zasu cinye tunda maza ne.”
Hajiya Zainab ta tashi “Agaskiya kun so kan ku mu kam ba zamu gane ba.Saboda Allah Maiyasa baa bamu gidan nan ba,ai mu,ya kamata mu zauna,don haka ba inda zamu”
D’ago wa zahra tai ta kallesu a zuciyar ta tace”
wanda yai nisa baya Jin kira. Allah ya shirya”
Malam kam tashi yai sukai sallama da Alhaji Tahir yai tafiyarsa Ha kan Zahra ta d’auki babies nata ta tafi. Kallon su Alhaji Tahir yai yace” wallahi kafin gobe ko
wacce ta had’a kayanta tabar gidan nan domin an sallame ku idan ba hakan zan nuna muku koni waye.” tafiyarsa
yai akabar su sai maida Zance suke
Washegari Alhaji Tahir ya dawo yana cikin motar sa hakan suka fito don tsabar had’ama wata motar d’ibar kaya k’arama suka d’auko hatta labulaye sai da suka cire na gidan Har kujeru Alhaji Kam kobi takansu bai ba shide kawai su bar gidan sai da suka gama tsab suka tafi.Alhaji ya kulle gidan ya tafiyrsa.
Mintuna Awanni, kwanaki, Satittika, Watanni duk sun shud’e tare da mutanen kwarai da na banza wani yana cikin farin
ciki wani yana b’akin ciki,Rayuwa ba ta taba zuwarwa Mutum iri d’aya Yadda da k’addara kuwa tana ga Musulmi na k’warai
Ayau twince in Zahra sun cika shekara biyu cir. Alhaji kuma ya shekara daya da wata UKU
Tana zaune d’akin Goggo suna shiri zata tafi yi wa twins Shopping, dan tun bayan gama takabarta alhaji tahir yace yana son karbarsu amman ganin yanda bata son ba dasu tafi sonsu agabanta ya kyale mata da sharadin in zatai aure zata kawosu.
Yaran gwanin sha’awa kayan su iri d’aya Motarta ta shiga twince Abaya tana driving A hankli don da k’yar Malam ya barta tana drivin tun tata ce ta gidana da alhaji ya sai mata.
Ga shi t koma makaranta wajen wata shida kenan tana school of nursing
Sunje shoping mall in banda jibgo musu kaya ba abinda take. Yaran sai tsalle suke suna gudu.
Juyawar da zatai taji tai karo da mutum kayan duk suka tarwatse. D’aga idanuwan
ta tai ganinsa tai da hussien A hannu murmushi yai mata, ta dauke kai da nuna alamar bata sanshi ba.
SALIM ta gani Ganinsa sam bai dadata da kasa ba, sunkuyawa tai ta d’ebe kayanta ta zuba a basket suka tafi counting, bayan ta hada kan yaran.
Bayan gamai musu suka shiga motar ta jasu suka tafi. A tsaye ya tsaya ya bisu da kallo yana jin zuciyarsa na harbawa. Tabbas yasan bayan auren zahra ya cireta aransa ya manta da ita amman ganinta kawai yaji sonta yayi fitar burtu ya dawo mai, gashi ta dada gogewa ta waye ta dada girma.
STORY CONTINUES BELOW

koda ta koma gida sam ta manta da shi ma dan tun bayan zamanta da alhaji ya daidaita taji ba wani namiji aranta sai shi, tabbas alhaji ya tafi ya barta da kewa, ta aureshi ba dan tana sonsa ba, amma gashi ya mutu ya barta cikin kewarsa kullum share hawaye tai ta shige daki.
BAYAN KWANA BIYU.
Salim ya zo gidansu zahra daman tumtuni yasan mijinta ya rasu. Koda ya zo dakyar ta fito dan bata manta wulakancin da yayi mata.
Ta fito tsaya ta hade rai sai yaga ta zame mai kamar ba zahra ba
Ya hak’uri Zahara Na Mutuwar mijin ki?”
Ta amsa da godia sunyi shiru karshe ta ce zata koma gida ta tafi.
A b’angaren SALIM kuwa tun lokacin da ya san itqce matar Alhaji umar yayi mamaki Shekara Uku kenan Rabuwarsa da ita Wani wawan sonta ne yaji ya taso wanda dama kullum da shi Aransa, ya sha wahala kan ya lafa.
Bayan rabuwarsa da ita ya kasa son kowacce duk da cewa ya cireta a ransa dakyar ya hadu da wata yarinya yar rikon kanwar mamansa yaji ta kwanta mai ya aura, wata shida auren ya mutu saboda yarinya sam bata da dabia bata ganin mutuncinsa bata biyayyr aure sai rashin kunya karshe suka rabu, bai sake kula wata ba. Ikon Allah sai gashi Allah ya sake hadasu tabbas ZAHRA tasa ce ba abinda ya dada birgeshi da ita sai Idanuwanta wanda suke A lumshe,da can ma suke sakar mai da kasala Zahar ta zama big girl ga wani kyau data kara tamkar yar 18 duk da yanzu Take 21 yrs, bacci ne ya gaga
reshi. Yasan dole ya fuskanci canji daga wajenta saboda wulakancin da yayi mata shikam alokacin yana ganin hakannne daidai
Wajen karfe 8 na dare twince na wasa da baby din Mujaheed wadda suka girmeta da one month,sunzoo gidan Anata hira Amma ban da Zahra in banda doka tunani ba abinda take.
Goggoce ta kalle ta “Zahra kodai mun Samu bazawari ne?”
Idanuwanta ta rufe Goggo na ji da Zahra yanzu saboda tai kud’i domin kud’in gadonta ta ware wasu daga ciki Aka gyara gidansu ta saiwa Malam mota,hakan ta saiwa Mamanta Keke napep ana mata haya,Goggo kuma ta bata Jari domin Alhaji ba k’aramun kudi ya bari ba don sun samu Tumunin ta kaba maitsoka,da sauri ta shige d’aki tana dariya Goggo tace” ja’ira” yaro ne yai Sallaama yace”Ana sallama da Zahra” k’in fita tai don kullum sai Anzo sallama da ita Ikon Allah duk samari ne ke zuwa don Basa d’auka ta
taba aure.
STORY CONTINUES BELOW

Fita tai Taga wata jibgegiyar mota prado tsayawa tai, fitowa yai duk da k’irjinta saida ya buga amma hakan bai hanata hade rai ba.
SALIM
kenan komi nasa ya canja ya zama wani Handsome ga kud’i yace zahra Tauraruwar mata har yanzu kece mai haskawa shekara uku Rabona da ke nayi kukan Rashin ki. Adalilin ki na bar Mahaifata, seda nai shekara 2 na dawo, nai aure amman mun rabu da matar. Na yi rashinki zahra Sai dai banyi bakinciki ba Saboda NA YARDA
da KADDARA sai akaci sa’a kin auri Abokin kanin Mahaifina ma. Mutumin kirki ta dalilin sa na samu Aiki A fedaral don shi ya tsaya
tsayin daka saboda yana da mutane a can, shiisa daga baya dana san ke ya Aura Na koma muku addauar fatan Alheri.”
Yad’an ja Numfashi “Zahra Har yqnzu haskenki na haskawa a raina, ki bani Second chance na zamo abokin Rayuwarki”
Ita kam Mamaki ne ya ishe ta tamkar Radio sai zaro zance yake, take ta basar inaga salonsa kenan, amma kuma
a hankali yake maganar take tad’anyi fari da ido tace ” Alright” ita kam ta rasa dalilin in tana ga ban SALIM take kasa tabu’ka
komi,jikinta mituwa yake tun wan cen lokacin,bare yanzu data san kanta.
Dukda tana jin haushin abinda yayi mata amman har yanzu tasan akwai burbushin sonsa aranta.
Sunkuyowa yai dede fuskar ta yace “ZAHRA ki taimakawa bawan Allah”
Murmushi ta saki ta d’an rufe fuska shi kam yana d’aya daga cikin habit in Zahra dake birgeshi wato kunya,juyawa tai ta
shige gida tana mai maida Numfashi.Aminu dake k’ok’arin shiga SALMI ya tambayeshi number dinta take ya bashi yai mai
Sallama ya Tafi.
Soyayya ta dad’a wanzuwa A tsakaninsu yi suke tamkar dama
basu taba rabuwa ba,satinsu d’aya ayanzu MALAM yai kiranta yace”zahra a yanzu ba zan miki dole ba don kin mun biyayya kuma har yanzu ina shimiki Albarka ,kin
ga kullum sai Anzo guna akan neman auren ki Amma A yanzu na bar komi sai wanda kika kawo dama hakan sharia ta tsara, Sunkwi dakai tai godiya tai ta tashi tamkar had’in baki.
Salim kece mata gobe Iyayensa zasu zo murna ba adadi.
Washegari !
Iyayensa sunzo an saka biki one month farin ciki sosai A b’angare guda kuma tana k’ok’arin zuwa makarantarta, don Salim yace karatu zatai har se ya isheta. ZAHRA sai shrye shirye take don A yanzu ne ta kejin zatai
auren SOYAYYA, duk da cewa daga baya ji tai auren alhajin kamar na soyayya tai saboda kyuautayinsa da kulawa a gareta, lokacin nasu sai kara gaba yake shi sam mantawa ma yake Zahra ta tab’a aure ya rok’i Alfarma a bashi twince hakan
yasa yaje Gidan Alhji Tahir ya tambaya,alhaji tahir ke cewa saide suna zuwa hutu.
Salim yace hakan ma yayi dan yasan daga zuwa hutu zai rik’esu amana domin ‘ya’yan zahra ‘ya’yansane
kuma Alhaji tamkar Mahaifinsa yake dan yayi mai komai.
KOMI AKASA LOKACI
sai yazo yau saura kwana d’aya d’aurin aure Zahra in banda k’alk’alar Jiki ba abinda take ta had’u
ta hade su Anty mariya sai tsuma ta suke,Masha Allah Zahra tamkar d’awisu sai kyalli take.
Washegari !dubban jamaa suka shaida daurin Aurenta da Tsohon Masoyin ta Salim.Ana gamawa Aka d’auki hanya don
mik’ata gidan mijin ta dake babban birnin Tarayya Wato ABUJA gidanta abin kallo ne domin SALIM ya nuna lalle masoyiyarsa ce
zata shiga (to mude sai muce Allah yabada zama lafiya.)
Amarya da ango kam soyayya suke tamkarsa hadiye juna Idan kaje gidan nan ,sai kunya tasa kabar gidan kome sukeyi girki don tayata yakeyi Zahra ta shagwaba Salim hakan shima
Ita kam zahra jinta take tamkar bata tab’a Aure ba domin sai yanzu tasan dad’in aure, Zama Da Masoyi dadi,Salim kosan
fita ba yayi sai murzar junansu suke.
Satinsu 2 suka d’aga dubai suka yada Zango a
Saudiya don yin Umara sunyi adduoi don d’orewar zaman lafiya Zahra tayiwa Alhaji umar addua sosai ya kai rahma kabarinsa.
Bayan dawowarsu Aka kawo su twince wanda Salim ya tsara d’akinsu,jinsu yake tamkar nasa, dattijuwa aka kawo mai kula dasu. Sosai salim ke sansu yana basu kulawa (shiisa aka ce duk abinda kai na alkairi sai ya bibiyeka, Alhaji umar ya rike yayan wasu duk da rashin dabiarsu mai kyau, haka ya zauna da su ya rikesu, gashi shima nasa Allah dafa mai wani zai rike mai cikin aminci)
Da safe ZAHRA na Kshingide a
k’ayataccen falonta ga twince na wasa a gefe SALIM ya shigo da dattijiwar me aikin.
zuwa tayi ta rungume.Shi ta bashi light kiss shima tsam tsam ya matse ta suna sakin nishi sun manta da bak’uwa sai da ta jashi suka shiga d’aki ya gyara “yace oh no in na ganki mantawa nake da kowa na shigo da bakuwa fa zata ringa miki wanke wanke da zu akaimin waya faruq ya sauketa a tasha hajiya ce ta samo.”
Dariya tai “ni wanne aiki ne ma ai babu da yawa, aini da iya ma muna komanmu tare
(me kula d su hussain) “to ai shikenan daman akwai gidansu abokina da ke neman me aiki babba sai akaita can amma kije ku gaisa”
Tom ta ce mai tare da fita da sauri.
Zama tai matar na zaune agefe a kasa se wasa take da gyalenta, magana zahra zatai mata .
D’agowar da tai taga MAGAJIYA ce kishiyrta, gyara zama tayi da mamaki akan fuskarta sosai, ita kam magajiya tuni fuskarta tayi kace- face fa hawaye ganin wai zahra ce matar da zataiwa aiki,nuna ta da yatsa zahra tai ta ce kece “kika dawo haka magajiya! Lalle ALLAH SHINE SARKIN SARAKUNA mai maida Mutum yadda yaso ya maida bawa ya zamo sarki haka kuma ya maida sarki ya zamo bawa jinjina kai tai ta kuma kallon magajiya domin Magajiya ko ina Jikinta k’una ne ta Jeme ta dawo Mitsitsiya fuskar ta duk Alamar k’una.
kuka Magajiya ke ta rusawa tana nai man neman a fuwarta ,zama tai kan tiles tace” Zahra munga Ja’iba,rayuwa ba komi bace kinga ni nan bayan rabon gado hakan yasa na samu
saurayi k’arami da niyar na Aureshi, hakan yasa yai ta karb’en kud’i sai daya karb’e komi,karshe ya gudu sai dana dawo abinci ma bana samu gashi duk ‘yan uwana dama bana zumunci na gujesu,hakan yasa na kama wanke- wanke A tasha gun mai sai da doya, domin kamar mujiya na dawo duk gidan da naje ba a karbata ga ciwon dake damuna duk wata sai kuraje sun feso mun duk kudina sun kare a magani amma ban warke ba.
Wataran fad’an ‘yan jagaliya ya tashi a wajen mai saida doyar aka kwaramin mai duk na toye kowa ya gudu ya barni a hakan nai jinya cikin wulak’anta bame zuwa inda nake ta share hawaye.
Hajiya zainab kam aure tayi ta auri wani Matarsa d’aya da yara shida hakan duk suka cinye Mata dukiya komi ita ta keyi, k’anzo shine abincin ta ga hidimar gida data ‘ya’yan kishiya ,ga shi kullum miji dukanta yake A girme ta girmi matar sa amma hakan itada yaran ta zasu Lakad’a mata duka ko agabansa ne kuwa, kuma yak’i sakinta daga k’arshe ma sayya dena bata abincin sai dai inta tai aikatau ta samu har rasa hannu
tai kan wani duka da yai mata.Gshi itama cuwuka sun isheta kala-kala.
Uwani kuwa tana nan an yanke mata kafa tun Lokacin nan da alhaji ya saketan nan, itama ‘yan Uwanta duk sun gujeta yanzu hakan kullum tana bara abakin titi.
NADIYA kuwa aurenta uku,da tayi take kaso shi, yanzu dai bariki take tukuru.
AMIRA DA HAMEED kuwa sunyi aure suna zamansu lafiya, haka tsigai na gaban iyayenta yanzu hakan tana karatu A legal.
Ni daman aikatau na gidaje na koma yi duk inda naje bana wata daya ake korata bansan dalili ba, nimq me aikin gidan surukanki ce taimin hanya jin hajiya na nema ashe kece wacce zanwa.Rayuwa kenan” ta fada tana hawaye.
“Nasan duk alhakin alhaji ke bibiyarmu da naki alhakin, bakina ba zai iya fadar irin abubuwan mugunta da mukaiwa alhaji ba tun zamanin kuruciya har girmanmu,har ya koma ga Allah.Kema mun dau alhakinki.Ki yafemin.
ZAHRA kam da taji tsoron rayuwa ta shigeta
tace “na yafe miki sai kiyita istigfari domin Alhakin Alhaji bazai barku ba . Amma kiyi hak’uri kije wani gun ki nemi aikin , mijina yace akwai daman gidan dake nema ze kaiki, kud’i ta bata tana ta kuka duk
kayan ta ayage, zahra ta bata kwancen kayanta ma
SALIM ne Ya fito ya ce “zahra wace kuma wan nan? ashe kinma santa zama tai kan cinyarsa tana bashi labarinn irin zaman da
sukai da wahalar da suka bata, yace “Allah ya kyauta”
Rad’a mata abu yai akunne “kin san dai gobe ne ko? Dariya ta sanya ta rufe fuska cike da kunya. Dagowa tai ta kalleshi sai suka kyalkyale da dariya su biyun.
Rayuwar ZAHRA ta zamo abinso ga kowa,duk a family nata da ita suke hutawa ta Janyo Mamanta Jikinta inda Auta ke gabanta tana school ga twinc nata wayo da girma ga sana’ar da take sai habaka take . Ta gama makaranta a lokacin aiki ne de bata fara ba, A kullum tana Alfahari da biyayayyar da taiwa babanta gashi yanzu tana girba.
_Sakamakon hak’urin zahra kenan a k’arshe ita ce da riba Haka nan rayuwa take yau fari gobe baki_
_Duk rabin labarin nan true life story ne Anan na kawo k’arshen littfin KISHIYOYINA dafatan ya wa a zantar tare da ilmantar_
_GODIYA ta tabbata GA ALLAH subhanahu wata ala daya bani ikon rubutu._
_SALATI DA SALLAMA G shaugabanmu Annabi MUHD S.A.W ALLAHya barmu da kaunarsa_
JIGON labarin nan wato HAKURI NE DA BIYAYYA .
Tammat bihamdullah