KIYAYYAH KO SON ZUCIYA COMPLETE
***
BABI NA DAYA
Cikin sasaarfa take tafiya tana yi tana duba agoggon hannunta. Bisa dukkan alamu yanayinta na nuna, kome take son aikatawa cikin gaggawa take son aikata shi. Dai-dai lokacin data kawo kan kwanar fitowa daga lungun ne wata mota kirar _prado_ ta kawo kai. Gaban Haidar ya yanke ya faɗi ganin cakwalin da yake gabansa, kasancewar an yi ruwa jiya mai matukar yawa. Ya ja wani nannauyan abu daya tokare masa wuya, hangota a gabansa ya sanyashi sakin murmushin mugunta ya bawa motar wuta koba komai zai cimma burinsa duk da ɓacin motar yafi komai damuwa cikin ransa. Cikin shammata ya faki idon mahaifinsa dake bayan motar yana jansa ya fi gefan
kwatamin bata yi aune ba gaba ɗaya kwatamin ya wanke ilahirin jikinta. Ta yi tsaye tana karewa kanta kallo komai nata fari ne, in ka ɗauke ɗankwalinta wanda ya kasance _(pink colour)_ kalar launin hoda. Sai jakarta baka rataye a kafaɗarta zuciyarta tazo iya wuya. Tsakin da Haidar ya saki ne yasa mahaifinsa ɗagowa daga duban jaridar *Fikra* da ya ke karantawa mai ɗauke da kayatattun labarai. Karaf! Idonsa ya sauka kan kan yarinyar dake tsaye ta kankane gaban motarsu tana hucci da alamu tana jiran kota kwana ne.
“Haidar lafiya, wacce ce wacan data tsare mana hanya?”.
Sosa kai ya yi,
“mtsss! Daddy share bagidajiyya tazo ta tsaremana hanya kawai”.
Cikin sauri ya kai dubansa ya sake kallonta, amma ya kasa gane wacece ita.
“Innalillahi wa inna ilairraji un. Haidar baka da hankali ne? Ina tunaninka ya ke? Wace ce wacan ka yi wa haka?. Dama har yanzu hallayarka tana nan?”.
Jikinsa ya yi sanyi sossai nan da nan ya dubeshi yana faɗin,
“Daddy ka yi hakuri”.
“Fita ka bata hakuri!”.
Yana ciccije baki ya buɗe ya fice ya nufeta, zuwa lokacin hawaye ya gama wanke fuskarta. Ganin yanayin daya fita yasa mahaifinsa biyo bayansa ba tare da saninsa ba. Tunda ya tunkarota take tana din kundin masifar dazata sauke masa, idanunta sunyi fici-fici kamar an jefa ɗan buda cikin ruwan barkono.
“Ke dan baki da mutunci kika tsaya kusa da hanya saboda in bigeki ko?. To idan ma na bigeki ai na bige banza, me za a iya yimin? Waye gatanki banza ‘yar matsiya…….”.
Kafin ya dire ta ɗaga hannu ta zabga masa mafi ta sake zabga masa a karo na biyu.
“Dakata Haidar! Waye kai? Meka tara? Me kuma aka tara maka? Bafa tsoranka nake ji ba, tsabar rashin darajar kai duk dukiyarka da ilminki sun kasa tsinana maka komai sai girman kai……”.
Maganar ta katse sakammakon hango mahaifinsa a bayansu, kanta kansa ta yi duru-duru da ita ga mutane sun soma taruwa cikin sauri ta juya zata bar wajan yayin da hawaye ke bin fuskarta. Haidar kuwa mamaki da takaici sun daskarar dashi, ga mamakinta sai taji muryarsa cikin kunnuwanta.
“Amira dama ke ce?”.
“Ni ce Baffa”.
Ta amsa murya a sanyayye, rissinawa ta yi ta gaisheshi ya amsa yana duban Haidar yana murmushi,
“sai ka juya muje ai dama rayuwa ta gaji haka. Rashin mutunci abune mai kyau sai ka ɗauki ɗamarar yinsa, in sani ya jure wani ko naman jikinsa kake yanka bazai jura ba. Amira shiga mota mu tafi gida”.
Taso yin musu amma saita hango rashin dacewar hakan, bin bayansu ta yi suka shiga motar ya tayar jiki a sanyayye suka ɗauki hanyar gidansu.+
***
“Nabila gaskiya ina son yayanki da yawa”.
“Kina bani mamaki Aunty Fadila nasan kina sonsa, amma menene abin damuwa tunda shi ma yana sonki kuma auranki zai yi. Kawai ina hango miki ne abin da kuke yi baya dacewa. Saboda abu mawuya ci ne kinga masu irin rayuwarku sun yi aure!”.
“Ban gane ba Nabila kina nufin Haidar bazai aure ni ba? Hmmm! Taf! Sabon saɓoma kenan wai raɗa a kunnuwan Liman wallahi abu ne mara yiwuwa wallahi”.
“Hmm! Allah dai ya kyauta kawai”.
“Amin bakinki ya sati ɗanyar kashi yar bukulu”.
Da gudu ta kwasa ta bi bayanta suka ranta ana kare.
***
Kasancewar babu nisa cikin mintuna da bazasu gaza goma ba Haidar ya yi wa kofar gidansu Amira tsinke. Suna yin _parking_ ta fito ta faɗa cikin gidan tana sharar hawaye, ta barsu tsaye suna gaisawa da mahaifinta tana shigowa mahaifiyarta ta bita da kallon mamaki kafin ta tanka ta faɗa banɗaki kai kawai ta girgiza ta cigaba da kauda kayan dake tsakar gidan. Shiru bata fito ba lamarin ya ɗaure mata kai. Tana shirin magana shigowar mahaifinta ya katseta ta washe baki ganin wanda suke tare tana yi musu barka da zuwa shimfiɗa ta yi musu suka zauna daga bisani suka gaisa.
STORY CONTINUES BELOW

Bayan sun gaisane Baffa yakeƴyi musu bayanin abin da ya faru. Sossai mahaifinta ya dinga faɗa kan abin da ta aikata ya ɗora da faɗin,
“kwata-kwata Amira bata yi halin Ummunta ba ta cika zafin zuciya”.
“A’a fa dan kana mahaifinta ba zaka tauyeta ba shi baka dubi girman laifin abin da ya aikata ba? Sai ita zaka hukunta?”.
Cewar Baffa kenan yana ɗaure fuska, ya sassauta murya
“amma yaya ai sama da ita yake”.
“Ai shi bai duba kankanta ba ya zallunceta ko?”.
Duk suka yi shiru, nan ya dinga surfa faɗa sanin bashi da sauki yasa suka yi gum harya gama. Amira na banɗaki saida tasha kukanta ta gama sannan ta fito Baffa ya dubeta yana murmushi.
“Mamana kin fito?”.
Kanta a kasa ta amsa,
“eh! Baffa”.
Ta wuce ɗaki Ummu ta rakata da kallin mamaki wai Amiran dake tsoron Haidar yau ita ta mareshi lallai bahaushe ya yi gaskiya daya ce abin da ke baka tsoro……sun jima suna tattaunawa daga bisani suka yi musu sallama suka wuce gida.
***
Tafe suke kan hanyar komawa gida amma babu mai magana tamkar kurame, kowane da abin da yake sakawa cikin ransa. Haidar tunani yake wai yau fuskar dakewa mata kwarjini aka mara? Maccen daya raina ajinta da kimarta ya ɗauketa makaskanciya yau ita ta kaskantar dashi. A haka suka karasa kofar gidan, wawwan hon ɗin daya saki ya tabbatarwa ma abota zaman gidan dawowar zakinsu. Nan da nan kowa ya shiga nutsuwarsa, ya shiga aguje yana hucci ya yi parking. Baba maigadi sai rawar jiki ya karasa yana buɗe murfin motar bakinsa na rawa,
“ranka ya daɗe sannu da zuwa, afuwan na ɗan zagane bayan gida”.
Ganin fitowar Baffa cikin motar ne yasa zuciyarsa yin sanyi ya tabbatar zai samu sasssucin hukuncin Haidar. Ilai kuwa wani birkitaccen kallo ya watsa masa idonsa jajjur tamkar an watsa barkono ya ɗauke kai cikin sauri yana murmushin yake saboda haɗa ido da suka yi da Baffa. Hannu Baffa ya mika masa suka gaisa, zuciyarsa fes daga kuɓutar daya yi. Kai tsaye ciki suka wuce ya rakasu da ido yana nemawa Haidar shiriya fanni ɗaya yana yaba dattako irin na Baffa.
Yana rike da brief case ɗin Baffan suka shiga fallon gidan. Fuskar nan ɗaure tamau. Zaune take hamshakiya tana kallon tv. Ganin yanayin Haidar ɗin ya bata tabbacin a kwai matsala mikewa ta yi tana dubansa,
“my son lafiya waya taɓomin kai?”.
“Hmmm! Mommy kyaleni kawai basai kin ji ba”.
“Haba Haidar!”.
“Mommy wai ni aka mara, kamarni?”.
“Mari Haidar!”.
“Hmmm! Mommy marinma wai mace, kaskantaciyya!”.
Ya yi furucin cikin kunar rai, mahaifiyarta ta dubeshi cikin ɗacin rai.
“‘Yar uban waye? Nace maka waye ubanta?. Har akwai ɗiya macen da zata mareka a doron kasa ina numfashi ban ɗauki mataki ba?……”
Maganar ta katse sakammakon tsawar da Baffa ya daka mata, yana dubansu ɗai-ɗai cikin fusata.
“Ashe ke kike ɗauremasa kugu yana wulakanta mutane ko Sadiya? Kaico da wannan muguwar ɗabi’ a taki mara tushe da madafa. Shin kin tambaye shi me ya yi wa ɗiyar mutane? Ko ita da ya mara ba ‘ya ba ce kamar kowa? Ko ance miki bata da uwa mai sonta kamarki?!”
Ta cuno maki ya kare ya sha bugu ta ce,
“ko kusa kadaina haɗa ɗana da ita, koma me yayi ai baza a mareshi ba ai wannan kaskancine!”.
“Ba kaskanci bane Sadiya haɗuwa ya yi da wadda bata jurar raini, kuma naji daɗi gaba sai ya kiyayye”.
“Wai waye ubanta a garin nan Haidar!”.
Ta yi furucin da amo, cikin karaji shi ma ya maida mata martani.
“Ni ne ubanta!”.
Take ta kuyo a hargitse tana yi masa kallon mamaki idanunta cike da kallon tuhuma zuciyarta na tukuburi yayin da kwanyarta ke tariyo kalaman tana maimaitasu kan harshanta cike da raɗa tamkar bata son wani yaji.
“Ni ne ubanta!?”.
Ta yi furucin da alamun tambaya
Cikin mamaki take dubansa,
“banfa gane ba anyi yamma da kare? Yimin bayani yadda zan fahimta”.
Kai tsaye ya bata amsa,
“Amirah ce kuma kinsan bata da uban daya fini!”.
“Amirah kana nufin Ummi?!”.
Ta faɗa tana kafe Haidar da ido, kai kawai ya ɗaga mata ai kuwa mai jiran kaɗan ta mako ta maguzawa cike da baki ta maka tana dubansu sai tada jijjiyoyin wuya take.
“Haka zaka cemin ɗiyar wannan matsiyacinm……”.
“Kafin ta dire wasu taurari suka gilma suna shawagi a idanuwanta, ruhinta ya yi tafiyar wucin gadi ta ɗago a mammakance tana dubansa. Kansa Haidar lamarin ya ɗaure masa kai duk shi ɗin shaidane kan kaunar da Daddynsa ya ke wa mahaifin Amira amma mamaki ya daskarar da shi. Zuciyarsa ta dinga zafi yana jin ina ma yana da kumaji ko nuna kwanji akai yau da Mommynsa tasan ta haifi ɗa amma kuma Daddy fa?. Sai ya sadda kansa kasa yana numfashi a hankali muryar mahaifin nasa ta cigaba da fita.
“Kin sani sarai ba zan juri kaskanci da rashin mutunci ba, nasha gaya miki kisan irin furucin da zaki yi a kansa da ahalinsa wallahi zan iya komai a kansa kinji na yi miki ratsuwa!”.
Ratsewa ya yi ya bar ɗakin zuwa sashinsa, a hankali ya karaso ya sassauta murya.
“Mommy kiyi hakuri duk da nasan bamu kyautawa Daddy ba, amma hukuncinsa ya yi tsauri AKAN IDONA Mommy ya yi miki haka. Amma kema ya kamata fa ki san kalaman da zaki akan wancan mutumin mudun kina gaban Daddy, sarai in baki manta ba sillar Amirah kika rasa igiyar auranki, ke kika faɗamin kuma tun daga haihuwarta farin cikinki ya yi kasa ya kamata kisan matakin ɗauka”.
“Dakata Haidar ! Kana nufin kafi son farin cikin Daddynka a kan nawa?”.
“Ba manufata kenan ba, ina faɗa miki ne don ki kiyaye Mommy”.
“Ga zahiri kana nunamin Haidar sun fini a wajanka”.
“Ko ɗaya Mommy dukkanku ina sonku amma kibi taka tsantsan”.
“Naji”.
Ta faɗa a gajarce ba dan gamsuwa ba, bis alamu maganar takeson yankewa. Ratseta ya yi ya nufi _corridor_ ɗin da zai sada shi da sashinsa zuciyarsa ta yi tsai yana duban sashin mahaifinsa. Wata na shawarce shi da zuwa wata na gargaɗinsa kawai ya yi kundun bala ya nufi sashin cike da karsashi. Yana gab da karasawa suka yi karo da Rabi mai wanke-wanke wata wawwar ingiza ya yi mata ta tafi rica! Kayan hannunta suka watse a kasa ya take mata kafa ya wuce abinsa yana huci ko kallonta bai ba. Sum-sum ta mike don tasan kota faɗawa Momnynsa hantara ce da zagine zasu biyo baya Daddyne mai kwatar musu ‘yanci shi kuwa mudun ka faɗa masa ya yi hukunci to washegari Mommy zata wartaka ka ‘kyauyanku an yi hakan yafi sau shurin masa’ki. Wayarsa ta yi kara ya ɗaga babu fara a,
“Fadeela zan nemeki!”.
Bai jira cewarta ba ya katse kiran tare da tura kofar ɗakin ya shiga, sanyin Ac ya buge shi ya lumshe ido yana ajiyar zuciya shiru babu kowa ya karasa cikin _bedroom_ ɗin. A zaune ya same shi ya yi tagumi bisa dukkan alamu ya yi nisa cikin dogon tunani, ya karasa da sanyin jiki yana sauke idonsa a kansa ya mike a zafaffe yana huci.
“Meya kawoka ɗakina? Fita bana bukatarka tafi kabani waje!”
Cikin sauri ya zube a gabansa, tare da rike kafafunsa
“Daddy bazan kuma ba ka yi hakuri Yarinyar ce ta bani haushi!”.
Ya zuba masa ido yana mamakin halinsa, amma zuciyarsa ta yi sanyi ganin kwalla ta taru cikin idanunsa. Ya sunkuya ya ɗagoshi,
“Haidar ka sauya hali don Allah”.
“To Daddy zan sauya”.
Juyawa ya yi ya nufi hanyar fita harya kai bakin kofa ya juyo da sassarfa, ya kalleshi da mamaki.
“Ya dai yarona?”.
“Daddy baka ce Allah ya yi albarka ba”.
“Oh! Haidar to Allah ya yi maka albarka, ubangiji ya shirya min kai”.
“Amin Daddyna!”.
Ya faɗa tare da ficewa da ɗan gudunsa yana dariyar farin ciki ganin Fadeela yasa shi yin turus ya sha kunu kamar wani wanda aka faɗawa sakon mutuwa. Tasowa ta yi tana karairaya,
“Haidar dan nazo gidanku shi ne kake fushi?”.
“A’a Fadeela ba haka bane kinga Daddyna yana nan kuma banason ransa ya ɓacci. Wai ma bana ce miki ki bari zan kiraki ba, nifa bana son binbini kin sani sarai”.
“Mtsss! Man ɗinka ya fiya tsauri”.
“Ke! Dakata karki gayawa mahaifina magana, bar ganin ina sonki wallahi tattakaki zanyi”.
Fuuu! Yabar ɗakin ta taɓe baki cike da takaici ta shige ɗakin Mommy ta mika mata sakonta ko Nabila bata nema ba, don tasan tana makaranta kai tsaye gida ta koma abinta.
***
BAYAN KWANA UKU..
STORY CONTINUES BELOW

Kasancewar Asabar ce ranar hutun karshan mako daga Daddy har Haidar suna gida. Kwance ya yini ko babu in da yaje sai bayan sallahr azahar ya fito cikin shirinsa na shada fara tas. Dinkin yan zamani ya ƙkarɓeshi sossai, sumarsa baka siɗik irin ta fulani ta kwanta luf tasha gyara hannunsa ɗaure da agogon azurfa sai takalminsa kirar kamfanin S square. Sai zuba kamshi yake ya kufo fallon, Daddy da Mommynsa ne zaune suna da alamu har yanzu akwai sauran rina a kaba saboda babu wani abu dake nuna alamun nishaɗi tare da zaman nasu wanda ya zama bakon abu a gareshi. Cikin kasaita ya karaso wajan ya risina yana gaishe su suka amsa kowane na kokarin nuna masa kulawa wani nishaɗi ya shigeshi ya sunkuyar da kai,
“Mommy Daddy zan ɗan fita”.
“Zuwa ina Haidar?”.
Suka haɗa baki wajan tambaya.
“Wajan Ahmad zani ya min rakiya zan je in gaishe da Abbun Ummi “.
Tuni ta shaka tare da gimtse fuska, bata kuma tankawa ba. Daddy ya yi murmushi.
“Da kyau Haidar ka gaidamin shi sossai”.
Kai ya sosa har ya kai kofar fita murya a cuɗe ta ce,
“abinci fa?”.
“Zanci wajan Ahmad Mommyna”.
Sanin matsayin Ahmad ɗin ne yasa ta gintse bakinta ta koma ta yi lakwas ya fice yana dariya kasa-kasa Daddynma mikewa ya yi ya bar ɗakin. Tsaye ya yi yana karewa motocin gidan kallo idonsa ya sauka kan wata bakar mota mai kyau wadda Daddynsa ya siyo masa watan da ya wuce, ya saki murmushi ya karasa tare da shiga cikinta ya cila kan titin da zai sadashi da unguwar su Ahmad.
Tafe yake yana tunanin sauyin da ya gani tsakanin Mommy da Daddy yaja tsaki dai-dai lokacin daya kawo kofar gidansu Ahmad ya yi horn. Kasancewar mai kula da shige da kuma ficen wajan yasanshi farin sani da saurinsa ya zo, yana rawar jiki ya buɗe masa ya bula masa kura ƴya yi gaba abinsa. Cikin harabar gidan ya ajiye motar ya fito suka gaisa da Abdurrahman mai kula da shukokin gidan yana mika masa hannu suyi musabasa, ya dubeshi.
“In gaisa da wa? Mtsss da wannan kazamin hannun naka matsa bani waje ni Ahmad na ciki?”.
Abdurrahman sarkin zuciya sai ya bar wajan ba tare daya tanka ba, sai Mustapha mai wanki ne ya bashi amsa ya wuce ciki yana takun kasaita. Lokacin daya shiga ciki bai samu Ahmad ba sai Fadeela ɗare-ɗare a kan gadon Ahmad ɗin tana dane-dane cikin wayarta ganinsa ya sa kirjinta harbawa ta mike ya dubeta idanunsa a kankance cike da zargi.
“Meya kawoki nan?”.
Tuni ta aro juriya,
“duk tsiya nasan nan zaka yi week end kai nake jira dama tunda ka hanani zuwa gidanku”.
Ta karashe maganar cikin sanyin kuka, rauninta ya haifar masa da wani yanayi amma zuciyar mazantakar ta motsa ya kanne tare da faɗin,
“is ok Fadeela mu zauna”.
Kusa dashi ta dawo ta nannike, ya dubeta kawai ya yi murmushi tare da shafa fuskarta,
“bana so fa”.
Dai-dai lokacin Ahmad ya shigo, wani abu ya daki zuciyarsa ya kanne yana jifan Fadeela da wani kallo a sace. Haidar ya mike yana faɗin,
“muje ka rakani”.
“Ina kuma?”.
Ya bukara fuska ɗaure tamau,
“gidan Abbu zani”.
“Ok muje ba matsala”.
Fadeela ta marairaice murya,
“princess wannan wulakanci ne dan kai fa nake zaune a nan ko”.
“Kiyi hakuri zan zo gida in sameki idan na dawo”.
Bata rai ta yi ganin hakan ya ɗaure fuska tuni ta shiga tai tayinta tana kallo suka fice Ahmad ya juyo ya yi mata signa ta ɗauke kai. Tafiyar mintuna talatin ta kaisu unguwar da suke son zuwa, lokacin da suka yi parking Amira ta dawo makarantar safe sauri take taj ta yi wanka ana la asar ta wuce ta yamma sai kuma magarba. Haidar ya taɓo Ahmad,
“tsaida yar jagaliyar can ta yi mana iso zuwa cikin gidan”.
Bai musa ba ya fito ya tunkareta,
“Assalamu alaiki”.
“Wa alaika salam”.
Ta amsa da sirririyar muryarta mai daɗin sauraro, tana shirin shafcewa ya yi saurin dawowa hayyacinsa.
“Am ammm don Allah in kin shiga ciki kice, zamu shigo daga gidan Alhaji Mukthar muke”.
Cikin murmushi ta ce,
“ok”.
Wucewa ta yi ba tare data lura da Haidar ba, mintuna biyar ta dawo.
“Zaka iya shiguwa”.
Bata jira cewarsa ba ta wuce ciki abinta.
Haidar ne ya fito suka bi bayanta da sallama suka shiga saida takai tsakiyar ɗakinsu muryarsa ta ratsa kunnuwanta, takaici ya kumeta tabbas da tasan tare suke ba zata saurare shi ba. Shimfiɗa Ummu ta yi musu suka zauna ta mike ta kwala mata kira,
“Ummin Abbu kawo musu ruwa”.
Ciki-ciki ta amsa,
“Ummu ina zuwa”.
Haidar ya yi murmushi,
“wato Ummu kema Ummi kike cewa ba Amiran ba?”.
“Wallahi Haidar na saba Ummi yafi min daɗi da yawa ma Ummi suka santa in ba makaranta ba da suka bata matsayin Amiran kuma yake neman binta”.
“Gaskiya ko Daddyna ma Ummi yake cewa”.
Dai-dai lokacin ta karaso ta ajiye ruwan a gabansu ta wuce abinta, suka rakata da kallon mamaki ko alamun sassauci babu a fuskarta hakan ya taɓa zuciyar mahaifiyarta amma ta kanne kawai suka cigaba da gaisawa da su. Tana gab da shiga ɗaki ta tsinkayi muryar mahaifinta yana sallama. Da ɗan gudunta ta juyo,
“oyoyo Abbuna”.
“Oyoyo Ummyterna”.
Kayan hannunsa ta karɓa ta kai ɗaki ya sauke idonsa kan Haidar da yake gaishe shi ya amsa cikin jin daɗi ya ƙlura akwai ɗan sauyi tattare dashi sossai ya zauna yana tambayarsa mahaifinsa. Sun ɗan taɓa hira ya dubeshi,
“Haidar karatu kuma ya kare ko?”.
“Eh! Abbu mun kammala har na soma aiki”.
“To Allah ya taimaka, amma dai ya kamata a san a girma. A soma yunkurin ajiye iyali Aliyu kaf sa aninka wasu ma sun soma ajiye yara”.
Shafa kansa ya yi,
“za a duba Abbu”.
Basu wani jima ba suka yi masa sallama suka wuce kuɗi masu kauri suka ajiye masa da kyar ya karɓa yana mamaki. Sun soma tafiya Haidar ya dubi Ahmad ya ja tsaki,
“yarinyar can Ahmad na fahimci miskilancinta harma da girman kai, kana kallo ko gaishemu bata yi ba”.
“Hmmm! Ni kuwa ban gani ba”.
“Ina zaka gani dama baho da kai, naga kuna ɗasawa ka bata shawara ta daina don girman kai sai mai girman aljihu amma talaka irinta wuya zai ci. Amma fa wasu lokutan tana birgeni”.
“Saboda me?”.
“Kome ka yi mata in baka kureta ba fuskarta bata nunawa, tana da tsiwa amma ko tsiwar zata yi fuskarta akwai alamun murmushi gata mayyar saka hijabi bagidajiya kawai”.
Ahmad ya yi murmushi,
“ban da kai Haidar ai irinsu ake so sune matan aure”.
Wata muguwar harara ya watsa masa amma ina bai ma lura ba. Kawai ratabo zance ya ke yi sai da ya kai masa duka ya kauce yana dariya kasa-kasa.
“Ashe ma matar aure?”.
“Kwarai kuwa Haidar”.
“Ina hujjar take?”.
“Ni kuwa nake da hujja in baka karamin misali yanzu tsakaninka da Fadeela kana tunanin idan kuka yi aure zaka lankwasata? Abu na biyu baka isa hanata fita harkar aikinta ko kasuwancin ta ba, daga randa kuka soma haihuwa sai kasa ayar tambaya ya ya yaranka zasu kasance?”.
“Naji tsari master ya ishe ni Fadeela dai nake so”.
“Hmm! Allah kar ka ki zancan wasa ba zan auri yarinyar da muka yi life tare ba, domin tsakaninmu akwai zargi da raini tsakanin juna kaga kuwa matsala ta afku”.
Bai tanka ba har suka karasa gida ya sauke Ahmad ya yi nufin jan motarsa ta dakatar dashi,
“Fadeela fa?”.
“Shareta zan kirata”.
Bai jira cewarsa ba yaja motar, ya yi murmushi ya wuce ciki.
***
Bayan tafiyarsu Haidar Abbu ya fita zuwa gidan abikinsa Ummu ta dubi Ummi ta ce,
“yanzu Ummi kin kyautawa kanki kenan?”.
“Me na yi Ummu?”.
Dakuwa ta watsa mata,
“naci tuwan gidanku mara kunya, ina kallo ko ki gaishe da Haidar. Wato ke abu baya wucewa a wajanki ko? Anya rayuwa ta yi haka Ummi?. Wallahi ki rage fushi da zafin zuciyar nan taki, haɗarine karfa ki manta gidan wani zaki in baki sauya ba sai yaushe?”.
Kwalla ta taru cikin idonta, Ummi sarkin kuka shar sai hawaye Ummu ta yi dariya.
“Gaki da saurin kukan tsiya, gaki da miskilanci da fushi wallahi ki daina kinji Umnyter”.
Ta faɗa tana sassauta murya, sai ta share hawayan tana faɗin,
“Ummu insha Allahu na daina”.
“Yauwa ɗiyar albarka”.
STORY CONTINUES BELOW

BABI NA BIYU…..
…
A MAKARANTA…..
Zaune suke karkashin bishiyar darbejiya suna duba littafinsu, zaman wajan ya zame musu tamkar farillah a nan suke zama kodayaushe koda kuwa ɗaya cikinsu bata zoba. Wajan ne abin ɗebe kewarsu. Fizgar littafin da akai daga hannunta yasa ta ɗago kai, amma ganin wadda ta aikata hakan yasata ɗauke kai tana kallon wasu yan jiniya da suka zo wucewa suma ita suke kallo da alamu suna bukatar wani abu a wajan ta, amma ganin abin da ke faruwa suka sakata idanu.
“Ke ‘yar matsiyaci”.
Aka faɗa da kakkausar murya, Hindatu ta mike zata tanka ta dankwafeta da idanunta. Lakwas ta zauna babu kuzari ta cigaba.
“Wai ke me kika ɗauki kanki ne? Banda cusa kai ma ai _school_ ɗin nan ba ajinki bace. Mtss! Da dai bamusan asalin balbela ba sai muce daga masar tazo”.
Ummi ta dubeta ta yi mata ɗiban karan mahaukaciya ta watsar, hannun Hindatu ta kama suka yi niyyar barin wajan. Caraf! Aka dakumo hijabinta wankakke fari tas dashi. Tas ta mutsuke mata manjan hannunta. Ummi taruntse ido tana jin raɗaɗi cikin ranta, ta juyo a fusace ta wanke mata fuska da mari ta rike hannun katamau ji kake ɓaras! Ta ɓalashi ta birkitota ta makata cikin cakwalin wajan ta damalmala kayanta. Wani giggitacan ihu ta saki ko ajikin ƳUmmi ta kwashi caɓin ta tura mata cikin baki,
“ba tsoranki nake ji ba Nabila shiru-shiru ba tsoro bane gudun magana ne kawai wallahi ki shiga hankalinki”.
Cikin fushi taja hannun Hindatu suka bar wajan. Sun soma tafiya wasu gungun ɗalibai suka saki ihu suna faɗin,
“sai Amirahn makarantarmu, wallahi kin birge sossai kin fida raini”.
“Muje Hindatu!”.
Babu musu tabi bayanta sunyi tafiya mai nisa ta dubeta,
“kin fa birgeni kin daki wa kin daki kanwa”.
“Allah ko?”.
Ta faɗa cikin bagararwa,
“sossaima dan ma kinki bani farkon labarin banzas”.
“Saukinta ma kinsa s wato nida ke kenan”.
Dariya suka yi ta ɗan ci kunu.
“Ummu bakya son zuwa gidanmu ko?”.
“Ko ɗaya son shige miki ne bana yi saboda abin da bana so gori kuma kinga Nabila shi ne aikinta”.
“Ina ruwanki da Nabila menane haɗina da ita?”.
“Gaskiya in dai zan duba matsayin mahaifinki da wuya in taka gidanku Hindu hanyar jirgi daban”.
“Ummi _why_?”.
“Hindu mahaifinki fa…”.
“Sai me Ummi? Na ce saime? Waye shi Ummyter kina bani mamaki wallahi bakisan yadda na ɗaukeki cikin raina ba shi yasa kike kawo wani karamin abu kan iya zama shamaki tsakaninmu amma wallahi ko kusa bana tunanun ranar da zaki sani wani abu makamancin gori a wajena. Kinga Yaya Khalifa har gori yake min komai in ce ke amma baki taɓa zuwa ya ganki ba gashi duk sati in nace zani gidanku sai ya yimin gori”.
“Karki damu zanzo ƙki shirya zuwana in Abbu ya bari wannan satin”.
“Yeee! Na gode tawan!”.
“Aminu ne naki ni ta Abbuna ce”.
Suka saki dariya gaba ɗaya, dai-dai lokacin wata yarinya yar aji uku ta karaso,
“Amirah kizo in ji Malamin kimiya”.
“Ki ce ina zuwa”.
Ta bata amsa a gajarce, cike da murmushi ta ce,
“muje Hindu case ɗin Nabila ne nasani”.
Tare suka rankaya zuwa office ɗin Malaman, kaf Malaman Makarantar sun hallara a gefe ta hangi Abbunta da kuma Haidar mamaki ya cikata saninta ne akwai numbobin wakilin kowane ɗalibi cikin makarantar amma bata yi tunanin faɗansu zai yi tsamari haka ba. In kiya ta yi wa Hindatu alamun ta koma jiki ba kwari ta juya da sallama ta shiga office ɗin. Malama Jamila Umar mai ɗaukarsu islamic ta amsa mata tare da nuna mata kusa da ita ta zauna. Kanta yana kasa musamman yadda Abbu ya ke watsa mata kallon takaici tasan yau ta kureshi matuka.
“Amirah me ƴya haɗaki da Nabila?”.
Muryar principle ta duki kunnanta, kanta bada amsa muryar Abbu ta doki kunnunta.
“Tambayar me kuke mata ku doketa kawai, ta karya yar mutane ku tsaya tambayarta?”.
Ta ɗago a razane suka yi ido huɗu da Haidar ya maka mata harara ta rama tare da murguɗa bakinta. Karaf a idon Abbu ya yo kanta da bulala ai kuwa kan Malaman suyi aune ya zaneta tas. Ummi ta dinga kuka tana share hawaye Haidar kansa sai da ta bashi tausayi bayan komai ya lafa ne principle ta tsare Ummi.
“Amira sanina ba kya laifi menene ya haɗaku?”.
Tiryan-tiryan ta zayyane mata komai, aka kira shaidun da aka yi gabansu yadda ta yi bayani haka suka yi jikin Abbu ya yi sanyi. Nan aka yi musu nasiha dukansu daga nan Ummi ta wuce aji ta samu Hindatu ta yi zugui da saurinta ta tareta sai ta fashe da kuka. Hakuri ta dinga bata harta yi shiru. Kai tsaye Haidar ya wuce da Nabila aka duba hannunta aka gyara ashe targaɗe ta yi sai da ya koma gida ya yi wa Abbu bayani sannan ya nufi gida. Mommy ta dinga surfa ruwan masifa da kyar Haidar ya lallasheta yana gaya mata an hukunta Ummin. Ummi da ɗanyan jiki ta koma gida sai da Ummu ta gaggasa mata jikinta sannan ta samu ta yi bacci faɗa kuwa tasha shi sossai.
Tsayin kwanaki Nabila na jinyar hannunta sai da ya yi sati biyu cikin na uku sannan ya warke. Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji su Ummi suka zana jarrabawa aka yi musu hutu, satinsu biyu da hutu safiyar Laraba ta samu Abbu kan tana so ya barta ta je gidansu Hindatu ranar Asabar kasancewar islamiyya ma an basu hutu cikin satin zasu koma babu jinkirtawa kuwa ya amince mata.
***
RANAR ASABAR…..
Misalin karfe sha biyu da rabi ta shirya cikin doguwar riga ta material mai kalar sky blue an masa fulawa da _green_ launin kore mai haske da kuma ratsin _pink_ launin tsami gaye. Rigar ta kamata kaɗan daga sama kasancewar tana da wadatar dukiyar fulani daga kasa kuma ta buɗe ta ɗaura ɗankwalinta tare da hijabi karami iyakarsa tsintsiyar hannunta. Takalmin kafarta pink ne mai ratsin baki mara nauyi. Fuskarta babu kwaliya sai hoda data mutsuka _countrol oil face._ Sallama ta yi wa Ummu ta ɗauki hanyar gidansu Hindatu hannunta rike da leda mai kyau wadda Ummu ta bata kaya dangin kayan girki su kirfa da habahan citta dakakkiya da ɗanyan masoro kuka da kuma kuɓewa da tugande.
Cikin nutsuwa ta sami take tafiya harta kai bakin titi kasancewar gidansu da bakin titi babu nisa sossai. Mai adaidaita sahu ta samu kai tsaye ta faɗa masa gadon kaya zai kaita layin mai danshin arziki ai kuwa nan da nan ya ɗauki hanya cikin mintuna arba in zuwa hamsin suka je kasancewar sun sami go slow a hanya sakammakon haɗarin da a ka yi a hanyar. Suna kawowa ta sallami mai adaidaitan ta shiga cikin gidan, akwai hayaniya da dama cikin gidan jikokkin gidan sun zo bisa alamu tunda ranar hutu ce. Da sallama ta shiga fallon amma babu kowa shiru sai ta samu kanta da wasi-wasin ina ta jiyo hayaniyyar ta yi tsai da ranta tana tunani cikin sakanni ta gano a garden ɗin gidan ne. Juyowa tayi da niyyar barin ɗakin karaf! Suka yi karo ta yi taga-taga zata faɗi cikin hanzari ya rikota. Suka zubawa juna ido na yan sakanni cikin sauri ta kauda kanta.
“Sannu”.
Ya furta da murya mai sanyi, gaba ɗaya jijjiyoyin jikinta suka aika mata wani bahagon sako fitowar Hindatu yaja hankalinta tana faɗin,
“yaya Khalifa ka dubamin assigm….?”.
Bata karasa ba ta saki karar murna,
“oyoyo my Ummyter!”.
Ai kafin mintuna goma ta cika gidan da ihun murna nan da nan aka jagaye Ummi ana murna cikin dariya ta ce,
“ga dai Ummyter ka gani”.
Hajiya Khadija mahaifiyarsu ta yi murmushi ta ce,
“ai tana zuwa badai ya taɓa ganinta ba”.
“Mommy karatu yasa, amma yau naga Ummyternmu”.
Dariya aka yi Ummi ta saci kallonsa suka haɗa ido ta ɗauke kai ta mikawa Mommy sakonta suka shige ɗakin Hindatu ya rakasu da ido yana lumshe Mommy na lura da yanayinsa ta girgiza kai ta wuce kawai.
STORY CONTINUES BELOW

Suna shiga ɗaki Hindatu ta dubeta,
“my Ummyter naji daɗin zuwanki nida kowa nawa”.
“Nasani Hinduna naga alamu kuma harma babban yaya”.
“Hmmm! Bari kedai sarkin miskilancin gidanmu kenan. Ai nayi mamaki wallahi daya yi miki dariya da wuya kiga dariyarsa”.
“Allah to ya ɗorani kansa”.
“Lallai kam”.
Sun jima suna hira karfe uku Ummi ta mike Hindatu ta yo mata rakiya a harabar gidan suka yi kiciɓus da Khalifa. Yana murmushi ya taresu,
“kanwata kun fito?”.
“Eh! Yayanmu zan rakata ne”.
“Haba dai don abin ƙkunya ai koni ban kaita ba asa driver ko Hinduwa mai daddawa”.
Ta cuno baki suka sa dariya, ya yi kyar da idonsa yana dubansa Ummi da ke yin dariya _dimple_ ɗinta _beauty point_ ya fi komai kayatar dashi. Hindatu ta lura da kallon da yake mata, cikin ranta daɗin hakan take ji tabbas abin alfaharine gareta mudun harsashanta ya tabbata. Sun kai ruwa rana sannan ta amince ya kaita gida, suka yi sallama ita da Hindatu daga bisani suka ɗauki hanyar unguwarsu. Tafe suke kowa da abin da ya ke sakawa cikin ranshi, Khalifa ya yi ta maza ya dubeta.
Cikin akasi suka haɗa ido ta yi saurin janye idanuwanta. Kanta a kasa tana wasa da zaran jikin rigarta ya saki murmushi yana janta da hira kaɗan-kaɗan mamaki fal ranta yadda yake mata hira, a baya Hindatu na faɗa mata miskilanci irin nasa sai take ganin abun duk a hagunce. Kafin su karasa gida duk yadda take kaucewa sai gashi ta saki fuska suna magana hadda wasa da dariya har gida ya kaita tare da bata salahun ta isar da gaisuwarsa wajan Ummunta. Khalifa na komawa gida ya tsare Hindatu da tambaya kan Ummi ta kuwa bashi cikakken bayani mai gamsuwa sossai ya yaba da ɗabi a da tarbiyar yarinyar. Washegari kuwa sun sha dariya tare da mamakin yayan nasu. A hankali Khalifa ya soma isar da sakon zuciyarsa ga Ummi cikin kankanin lokaci da taimakon kanwarsa ya sami karɓuwa a ranta suka yi wata irin shakuwa kaf dangin su Hindatu sun san da zaman Ummi sai ɗai-ɗaiku. Matsalar Khalifa guda ce Ummi ta hana ya zo gidansu bale asan da zamansa sai dai suna soyayyarsu ne ta hanyar rubutacen sako ko waya a wayar kanwarsa. Hakanma a ɓoye saboda dokar makaranta. Khalifa ya kasa jurewa hakan ranar wata Asabar kwatsam Ummi na gida ya aika ayi sallama da ita. Hankalinta yatashi sossai jikinta ko ina rawa yake Ummu ta kafeta da kallon tuhuma ta saddar da kanta kasa.
“Jeka kace in ji wa?”.
“Yace in an tambaya in ce in ji Khalifa”.
Ummu tayi jim tana tunani ganin lokaci naja yasa ta sallamar yaron ta dubeta.
“Ummyter waye Khalifa?”.
Kanta kasa ta amsa,
“yayansu Hindatu ne”.
“Oh! Na fahimta tashi kije amma bawai hira nace ki je ba, ki fita ki bashi tabbacin yazo da dare ya samu Abbunki su yi magana kan neman izininsa na zuwa wajanki. Mintuna goma na baki karki ɗara”.
“To Ummuna!”.
Hijab kawai ta saka har kasa ya rufe kowace kafa tata in ka ɗauke fuskarta ta zura takalmi ta fita. Ummu ta rakata da ido tana murmushi. Tunda ta nufi wajan gabanta ke faɗuwa haka shima, tana zuwa ta risina ta gaisheshi a gajarce ta yi masa bayanin komai tare da lokacin da aka ɗibar mata, mintuna bakwai ta dire bayanin ta kalleshi.
“Zan koma ciki”.
“Ok Ummyter sai nazo ɗin”.
Ta juya zuwa gidan tana murmushi. Cikin ikon Allah kuwa Khalifa a daran ya dawo wajan Abbu, kasancewar yasan da zuwansa basu wani jima ba yayi masa gamsashan bayani kan waye shi. Daga bisani Abbu ya dubeshi,
“Khalifa aure nufine na ubangiji, bazan yi alkawarin baka auran Ummi ba domin babu wanda yasan mai gobe zata haifar ni da kai da Ummi babu wanda ƴyasan mijinta sai ubangiji amma bazan hanaka nemaba zan tayaka addu a ubangiji ya tabbatar da alkhairi”.
“Amin Abbu nagode”.
Tun daga ranar Khalifa ya samu kafar zuwa gidansu duk sati biyu ko ɗaya, hakan ya karamusu kauna da shakuwar juna sossai cikin wata biyu da haɗuwa suka samu kansu cikin zazzafar kauna juna.
WAYE KHALIFA…….?
Abubakar Mustapha Sani ɗa ne ga Alhaji Mustapha Sani. A salinsu mutanan gabas ne zama ya kawosu garin Kano. Iyayansu su shida suka haifa yayarsu Rukayya na aure a Maraɗi bata taɓa haihuwa ba, sai Aisha wadda ke aure a Zariya tana da yara uku sai Safiyya wadda ke Kaduna tana da ɗa ɗaya sai Khalifa da Mubashar da kuma Auta Hindatu. Mubashar na karantar business a B.U.K. Khalifa ya kammala digiri ɗinsa fanin kasuwanci shekaru huɗu da suka wuce. Yana da shekaru ashirin da shida cif daga shi har iyayyansa suna zaune unguwar gadon kaya. Misline sossai kaf kannansa shakarsa suke baya wasa da yaro. Shi ne yake kula da duk wata dukiya ta mahaifinsu, mahaifinsu mutum ne mai wadatar dukiya sossai sun taso cikin jin daɗi da kaunar junansu. Mahaifiyarsu macece mai karamci da kyautattawa mai suna Hajiya Maijidda. Kaf abokan Khalifa wasu sunyi aure wasuma da yara amma kokusa sha awar auran bata gabansa wannan ya farune sakammakon har zuwa wannan lokacin baiga macen da tayi dai-dai da tsarinsa ba kwatsam ubangiji ya kawo Ummi cikin rayuwarsa cikin kankanin lokaci suka yi wata irin shakuwa.
***
Kwanci tashi asarar mai rai, komai na tafiya yadda ya kamata Ummi rayuwarta take cikin kwanciyar hankali har zuwa lokacin bata sake haɗuwa da Haidar ba shima kuma bai dawo gidan ba. Kwatsam ranar Asabar Baffa ya kawo musu ziyara nan ya samu Ummi ya dinga caccaketa kan bata son zumunci. Jikinta yayi sanyi sossai ta dinga hango rashin kyautawarta a kala tafi shekara rabanta da gidan ko hidima ake sai dai Ummu taje kanta a kasa ta dinga bashi hakuri ta wuce islamiyya zuciyarta cike da tunanin yadda zata sabawa kanta da zuwa gidan.
STORY CONTINUES BELOW

***
Zaune suke ranar Lahdi Ummu nayi mata tsifar kanta ta muskuta tana son furta abin da ke cizon zuciyarta.
“Ummu ina son zuwa gidan Baffa amma wallahi wulakancine bana so”.
“Hmm! Ummyter nafiki gudun wulakanci amma kisani shi zumunci abune mai matukar kyau da tasirin dai-daita lamura. Ki kauda komai ki rungumi kyautattawa musamman ga masu kuntattamiki da sanu zakiga ribar rayuwa”.
“To Ummu zan gwada amma wallahi lamarin akwai ɓaccin rai duk juriyarka sai ka gaza”.
“A a Ummyter juriya bigirece na cikar burika”.
“Allah ya yi mana jagora Ummu”.
“Amin Ummyter kinga gama kaya daya aiko cewar za ayi taro karshan wannan wata, saiki daure kiba mara ɗa kunya kije”.
“Ummu taron menene haka?”.
“Ummi nima ban sani ba yadai nemi ganinmu baki ɗaya hadda ke”.
“Zan je Ummu insha Allahu, me zaki musu ne game da taron”.
“Kamar kinsan tunanin da nake kenan Ummi”.
“Kimusu kunun ayarki mai daɗin nan”.
Ta karashe tana dariya itama dariyar tayi tare da cewa,
“kyalesu kawai tun da ba sanin taron kona menene ba a tari gaba”.
“Allah ya nuna mana Ummu”.
“Amin”.
***
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji, har kwanakin taron suka karato ana gobe taron da da dare Ummi na ɗakinta tana aikin da aka basu a makaranta wayarta kirar tecno p5 tayi kara ta saki ajiyar zuciya ganin mai kiran ta sa hannu ta ɗauka cikin nutsuwa ta yi sallama.
“Assalamu alaikum”.
“Wa alaikisala Aisha!”.
Yar! Tsigar jikinta ta motsa saboda yanayin daya kira sunan nata, mamaki fall ranta Khalifa baya kiran sunanta kai tsaye sai zai mata batu mai muhimmanci jikinta ya yi sanyi ta amsa a dausashe.
“Na am Sadauki”.
Sunan da take kiransa kenan lokuta da dama, ya cigaba.
“Zuciyata kullum cikin begenki take, burina auran mace mai tarbiya yau gashi na samu nagartaciya. Karki gujemin duk runtsi!”.
Ya ɗan tsagaita,
“Aisha zuciyata ta zaɓeki matsayin wadda zata zamo abokiyar rayuwata, ina fatan kikasance tare dani duk tsanani kamar yadda nake burin kasancewa tare dake har darussalam insha Allahu”.
Maganganunsa sun gama kashe gaɓan jikinta, tana zargin Khalifa na cikin fitar hayyaci amma ta kasa gasgata hakan saboda muryarsa ras take babu alamun maye. Tayi saurin fatattakar tunanin daga zuciyarta ta numfasa.
“Sadauki zuciyata ta gama amincewa dakai, ina burin zama mallakinka kullum addu ata ubangiji ya tabbatar da alkhairi cikin rayuwarmu. Ka gama mamaye duk wani gurbi na zuciyata”.
Sun jima suna musayar kalaman zahirin kauna daga bisani suka yi sallama cike da kewar juna. Ummi ta dafe kai tare da sakin numfashi tana mamakin kalamansa wanda bai taɓa yi mata kwatankwacinsu ba duk da ita ɗin shaidace kan kaunar da ya ke mata.
Mikewa ta yi ta nufi malallautarsu ta ɗauro alwala, gab da zata gota ɗakin Ummu kunnuwanta suka jiyo mata sautin Abbu yana magana kasa-kasa.
“Maryam magana nake so muyi dake kan batun Ummi”.
Muryar Ummunta ta amsa,
“ina jinka Abbun Ummi”.
“Yayane yazo da batun yana son haɗata aure da Haidar”.
Das! Gaban Ummi ya faɗi cikin sauri ta wuce tabar gun kafaffunta na rawa sun gaza ɗaukarta tana zuwa ta zube yaraf kan katifa. Ta dafe kanta tana furta duk addu ar data zo bakinta kanta ya sara kirjinta ya yi nauyi ta rufe idonta dum! Ji take kamar in ta buɗe zata riski makanta ne ta cije leɓanta tana karanta innalillahi…..zuwa wani lokaci nutsuwarta ta dai-daita ta yi zugudum tana tunanin abin da ya ke shirin faruwa da ita.
Dare aka ce mahutar bawa in ji yan magana, amma ga Ummi abun yazo a hagunce ne kwata-kwata ta rasa nutsuwarta kanta banda zafi babu abin da yake. Ga wani sanyi daya ke kaɗata tamkar mai rawar mazari cikin kankanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeta har haɗa hakora take gab-gab. Zuciyarta tayi tsai wajan tunanin yadda rayuwar Khalifa da tata zata kasance, wani fanin tana nusar da ida kan cewar.
“Haba Ummi yanzu akwai abin da iyayyanki zasu nema ki gaza yi musu? Sun lura dake da rayuwarki tarbiyarki tun kina tsuma har zuwa girmanki ba tare da sun gaza ba dame zaki sakamusu bayan biyyaya?”.
Lokacin da tazo nan a zancan zucin saita sami kanta da sakin ɓoyyayar ajiyar zuciya taja zani ta rufe jikinta saboda sanyin da take ji. Haka ta kwana sake-sake washegari ta tashi sukuku tayi fiyau da ita babu zazzaɓin sai kanta da yake sarawa jefi-jefi.
Haka ta kasance har zuwa tafiyarsu, Ummu na lura da yanayinta sossai saita ta alaka hakan da rashin son zuwa kiran. Karfe sha ɗaya na safiya suka yi wa gidan tsinke kasancewar akwai rashin nisa a kafa suka zo. Tun a harabar jikin Ummi ya yi sanyi ganin uwar dukiyar da aka makare a wajan motocin hawa kansu sun kai goma ta yi mamaki matuka ganin irin gyaran daya sha.
Cikin shakku suka karasa cikin gidan. Abbu ya nufi ɓangaran Baffa su kuma suka wuce ɓangaran matar gidan da sallama suka shiga aka amsa babu yabo ba fallasa. Suka zauna jigum tsayin mintuna goma ko ruwa babu wanda ya basu, Ummi ta gaji tana jin kishirwa ta mike ta nufi hanyar da take tunanin zata kaita _kitchen_ cikin nutsuwa. Gaisawa suka yi da Mama Ladi mai wanke-wanke ta bata ruwa ta juyo, kwatsam suka kiciɓus da Haidar a bakin sirririyar hanyar da zata dawo da ita falo ta haɗe fuska tayi kicin-kicin cikin turo baki ta ce,
“bani hanya in wuce”.
Yatsurawa ɗan karamin bakinta ido, wani abu na fizgarsa ya saki murmushin mugunta ya kai hannu ji kake ɗil ya ɗani baki ai kuwa taji zafi ta dafe gun tana jijjiga kai. Bata yi aune ba ya sureta chak! Bai zame ko ina ba sai ɗakinsa dake babu tazara sossai.
Yana direta ta mike ta soma ja da baya tana yi masa kallon tuhuma, bata yi aune ba ya jefa mata tsintsiya a fuska harta karceta ta saki sirirriyar kara ya zare mata ido.
“Sharemin ɗakin nan tas”.
Ta murguɗa baki ta hararreshi,
“anki ɗin ai ni ba Baiwarka ba ce”.
Zare _belt_ ya yi yana dubanta, fuska tamke babu fara a.
“Ai dama mun saba, kada Allah yasa ki share wallahi mugun duka zan miki!”.
Ya faɗa ƴyana huci, ganin babu sarki sai Allah yasa ta soma tattare ɗakin sai da ta kwashe kayan kasa ta sauya _bed sheet_ ta tattare kayan wankinsa ta haɗa masa waje ɗaya. Ta ɗauki mofa ta gyara ɗakin tas tasa _air freshner_ ta zuzzuge labulayan take ɗakin ya yi ɗum ya ɗauki kamshi. Ta gaji sossai ta zauna yaraf! Buɗe firinji ta yi zata sha ruwa saboda bushewar da makogwaranta ya yi dam! Gabanta ya faɗi.
STORY CONTINUES BELOW

Hannunta ya hau rawa zuciyarta ta hau bugawa cikin sauri ta maida ta rufe. Ta runtse ido tare da fitar da huccin iska mai zafi. Jiki a sanyaye ta mike ta gyaro banɗakin ta fito duk ta yi sakaro da ita. Dai-dai lokacin suka shigo ɗakin su uku Fadila da Ahmad da kuma Haidar. Cikin tuhuma Fadila ta jefa masa wani birkitacan kallo,
“wannan fa?”.
Ta nuna Ummin kamar taga kashi. Ya sosa kai yana murmushi,
“mtss! Na manta nasa wannan kwailar ta yi min shara”.
Ya dubeta tare da zare ido.
“Ke! Dilla fice ki bani waje, kin tsareni da ido kamar jigar mayyu _get out of my room_ fice min daga ɗaki”.
Cikin sauri ta fice har tana tuntuɓe, saida ta saisaita nutsuwarta sannan ta shiga fallon. Ummu ta dubeta,
“ina kika tsaya?”.
“Ina wajan Baba Ladi ne”.
Ta yi mata karyar kare kai. Fitarta keda wuya ya soma duban tsarin ɗakin gyaran ya yi masa sossai ya faɗa banɗaki ya watso ruwa ya fito ya shirya ya dubesu.
“Zamu amsa kiran Daddyna, ku ɗan jirani”.
Cikin murna suka yi masa fatan alkhairi yana fita suka kashewa juna idanu suka hau aikata abin da suke tunanin zai fishesu.
***
Dakin mahaifinsa ya yi wa tsinke, duk sun hallara shi ake jira, yana shiga ya haushi da faɗa Abbu ne ya dakatar dashi suka buɗe taro da addu a daga bisani mahaifinsa ya fara bayanin nasarorin da aka samu a dukiyarsu na wannan shekarar tare da kammala karatun Haidar har ya gangaro kan makasudin tarasu.
“Alhamdulillah Haidar tun dawowarka karatu nasa ido kan ko zaka fito da MATAR AURE amma shiru hakan yasa muka duba babu cancantar zamanka haka don haka mun yanke haɗaka aure da kanwarka Aisha”.
Tashin hankali wanda ba a samasa rana, take wani gumi ya dinga tsattsafowa Haidar duk da sanyin _Air conditioner_ dake sanyayya ɗakin. Ummi kuwa kasa kataɓus ta yi ɗakin yayi ɗif kowa da abin da yake rayawa cikin ransa. Bangare daya Maman Haidar kuwa ji tayi tamkar saukar aradu a kanta amma ganin babu wasa a fuskarsa yasa ta cin laya tace,
“amma ya dace aji ta bakinsu…..”.
Ya katseta,
“duk cikinsu babu wanda ban isa dashi ba don haka bana son kanannun maganganu”.
Gum tayi da bakinta ya cigaba,
“ga wannan mukulin gidanane na kijikin gidan nan ka ɗauka na baka ga takardun nan, akwai motoci guda biyu a ciki suma naka ne sannan nabuɗe maka shagon saida shadda da atamfa da kuma lessuna ka dinga saidawa shima nakane ka dinga juyawa bana bukatar ko sisi dan gane da riba cikinsa na bakane don ka kula da iyalinka”.
Kasa cewa komai yayi don farin ciki sai hawaye dake bin fuskarsa ya yi godiya hakama iyalansa. Mommy daskarewa tayi a wajan tsabar mamaki da takaicin abin da mijinta ya yi taja numfashi da kyar ta mike cikin ci da zuci ta furta,
“dan me zaka yanke hukunci babu shawara, ai nima iyalinka ce ina da hakki akai”.
“Dan kina IYALINA dukiyata taki ce?”.
“Idan ni ban da hakki akai Haidar fa?”.
“Sai ku bari saina mutu saiku sarrafata daga ke harshi ɗin”.
“Gaskiya wannan zalluncine…..”.
Kafin ta dire ya kaiwa bakinta wani duka da sauri Abbu ya tareshi yana faɗin.
“Haba-haba yaya ba girmanka ba ne a gabanfa yara muke”.
Cikin huci ta furta,
“barshi-barshi ya dake ni ya daki auransa, igiya ta ɗaureshi har tayi rara, munafikin banza munafikin wofi ni za a nunawa karyar zumunta?”.
Cikin shammata ya kwace rikon da Abbu ya yi masa ya zabga mata mari, ya nunata da yatsa.
“Ni zaki tozarta? Wallahi na shirya wa komai a kan auran nan ciki hadda rabuwa dake wallahi”.
Ya nuna Haidar yana huci,
“kai kuma kabi uwarka ka nuna min ita ta isa dakai ba ni ba”.
Fuu! Ya bar wajan yana hucci da sauri Abbu ya rufa masa baya. Ta yi tsaye tana mamakin yau ita yake faɗawa magana dangas, ta sauke idonta kan Ummu dake bata hakuri ta wurga mata bahaguwar harara.
“Lallai Maryam kinyi nasara, kinyi nasarar rusa duk wani shirina karo ƙbiyu zuwa uku kenan mijina na marina sanadiyar ‘yarki wallahi wallahi sai kinyi nadama ko zanyi yawo tsirara saina kuntatta rayuwarku keda ira-iranki”.
Fuu! Tabar fallon, Ummu ta yi doguwar ajiyar zuciya ta sauke idonta kan Haidar daya kai karshan fallon ta kasa tantance yanayin daya ke ciki. Tausayin Ummi ya tsirga mata matuka cikin ranta.
Haidar na shiga ɗaki ya riski Ahmad da Fadila na kallo, babu fara a ya zauna ta dawo kusa dashi ta nannike ya tureta ta mike tana muzurai,
“jeki saina nemeki”.
Ganin babu wasa yasa ta fice tana gunguni. Tana fitowa ta riski Mommy na bada labarin abin da ya faru hankalinta ya tashi sossai harda hawayenta tana faɗin “wallahi Mommy kusan matakin ɗauka kan batun nan”.
Hajiya Karima taja doguwar ajiyar zuciya tace,
“ai duk laifinkine Hajiya Sadiya da anyi magana kice asiri baya cin mijinki ai ga irinta nan zaki rasa tillin ɗanki!”.
“To ya zanyi?”.
Ta faɗa kamar zata yi kuka, raɗa ta yi mata a kunne suka tafa suna dariya.
***
Abbu ne ya dinga lallashin Baffa har ya sasauto daga bisani ya zaro wayarsa a aljihu ya kira layin Haidar. Dai-dai lokacin daya tsiyaya ruwan shansa cikin kofi ya zuba mata ido yana tunanin yasha ya samu sassauci wata zuciyar na tuna masa Daddynsa na gida ya gama amincewa shanta ne mafita a yanayin daya ke ciki. Yana kafa _cup_ ɗin a bakinsa ƙkiran mahaifin nasa ya shigo ya dire tare da saisaita muryarsa ya amsa. Umarni ya bashi ya zo ya kai su Abbu gida su soma haɗa kayansu zuwa jibi su tare cikin girmammawa ya amsa tare da ajiye wayar. Mikewa ya yi ya bar Ahmad na kwankwaɗarta ya ratso fallon yana jin sautin Momnynsa na masifa ya yi murmushi,
“Mommy faɗa ba naki bane, Daddy yayi fushi kema kinyi fushi wazai taushi wani. Kibari ya sauko sai musan abin yi, shiyasa Ummu ke burgeni wani……..”.
Yana furucin yana barin fallo karaf! Suka yi karo da Ummi data kawo kai cikin fallon dukkansu suka yi baya fuskar kowa a tamke,
“kazo in ji Baffa”.
“Banza bakauyiyya Daddy ake cewa”.
“Anki a faɗa ɗin mara mutunci”.
Yana niyyar cafkota mahaifinsa ya karaso,
“zo ka kai su”.
“To Daddy”.
Ya juya suka rufa masa baya ba magana kowa na sakar zuci.
Har gida ya kaisu ya dawo kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya zuciyarsa kwar cike da kunci. Ya buɗe ma adanar sanyi ya hau kwankwaɗa sai da yaji ya yi mankas sannan ya ajiye ya sawa ɗakin mukuli ya kwanta. Bashi ya tashi ba sai tara na dare jinsa ya ke kwakwalwarsa _fresh_ kai tsaye wanka ya yi ya ɗauki _key_ ɗinsa ya nufi _Hauronbiya club_ yana da tabbacin a can zai sami Fadila…….TUSHAN LABARIN….
Alhaji Muktar tare da ɗan uwansa su kaɗai iyayyansu suka haifa. A salinsu mutanan jihar Katsina ne cikin kauyan sayaya, sun taso cikin rufin asirin ubangiji mahaifinsu bame hali bane sai dai akwai wadatar zuci. Duk rashin wadatar kuɗi da yake da ita hakan bai hanashi tsayawa kan karatun yaransa ba. Bangarorin biyu boko da arabiyya duk suna maida hankali kansu. Mahaifinsu mutum ne mai tsantseni tare da kawaici, manomine sossai yana noman rani da damuna aikinsa kenan. Inna Aisha ita ce mahaifiyarsu, mace mai karamci da hangen nesa. Sun taso cikin so da kaunar juna Muktar ya girmi kaninsa da shekaru biyar. Lokacin da Muktar ya kammala karatunsa na _secondary_ mahaifinsa ya yi cuku-cuku ya nema masa gurbin karatu a babbar makarantar dake Katsina, dake _result_ ɗinsa ya yi kyau bai jinkirta ba ya samu akai yan dabaru ya wuce makaranta. Zamansa a makaranta Allah ya haɗashi da wani aboki mai suna Hamza. Sun shaku sossai dashi komai tare suke yi, tun haɗuwarsu wasu al amuran suka yi wa Muktar sauki kama daga _handout_ da sauran hidindimun makaranta. Iyayyan Hamza masu haline suna zaune cikin Katsina a unguwar Sanamu su biyune wajan mahaifansu shida Kanwarsa Sadiya. Shakuwarsu tasa ko hutu aka yi gidansu Muktar yake yin hutunsa.
Hakan ya haifar da shakuwa tsakanin Muktar da Sadiya, yayin da ita kuma gefe guda so ne ya yi mata dabaibayi duka duka lokacin tana _jss three_ tun tana ɓoyewa harta kai ga furtawa da fari ya ɗauka wasa take amma daga bisani sai ya fahimci da gaske take hakan yasa ya soma janyewa zuwa gidan hankalin Sadiya ya yi matukar tashi nan da nan ta kwanta ciwo abun abin tausayi.
Nan da nan hankalin mahaifanta ya tashi, Sadiya sangartaciyar yarinya ce data taso cikin so da kulawar iyayye uwa uba dukiya ga mahaifansu suna da matukar san yaya hakan yasa take taɓararta yadda take so komai ta yi daidaine. Cikin kankanin lokaci mahaifanta suka soma neman in da Muktar yake basu sha wuya ba suka samoshi aka tasashi gaba da lallashi tuni ya bada kai bori ya hau nan da nan soyayya ta kule a tsakaninsu Hamza kuwa aminta saita kara gaba yayin da Muktar ya zama ko gida sai jefi-jefi yake zuwa hakan ya damu mahaifansa sossai musamman mahaifiyarsa. Kwanci tashi suka kammala digiri ɗinsu tsayin shekara huɗu, a lokacin Sadiya ta gama makaranta nan da nan Muktar ya turo magabatansa aka sa maganar aure. Al ammura sun cigaba da tafiya lokacin Muhammad kanin Muktar yana aji huɗu a makaranta kuma daidai gwargwado mahaifinsu na kula dashi sossai shima yana taimaka masa wajan aikin gona don kwata kwata hanashi yin noma ya yi sai dai yayi shi ɗays a haka aka soma hidimar bikin Muktar wanda zuwa lokacin sun soma gudanar da kulawa kan dukiyar mahaifin Sadiya wato sirikinsa. Biki ya kayatar sossai amarya ta tare a unguwar sa ɗaka tazararta da gidan mahaifanta kaɗan ne. A shekarar ne kuma mahaifin Sadiya ya buɗe kamfani guda biyu a garin Kano da Sakwato wanda aka bawa Muktar ragamar na Kano shi kuma Hamza Sakwato, cikin ikon Allah suka soma gudanar da komai lafiya lau zirga-zurga nasan yiwa Muktar yawa hakan yasa aka siya masa gida madaidaici a unguwar Gauron dutse ya tattara suka koma can shida Katsina sai jefi-jefi bale Sayaya. Lokacin da Muktar yake garin Katsina ba laifi yana kulawa da ahalinsa amma tun komawarsu Kano sai komai ya taɓarɓare ya zamo tamkar rakumi da akala cikin gidansa.+
Rai da mutuwa duk na hannun ubangiji, kwatsam ranar wata laraba mahaifin Sadiya da mahaifiyarta suka rasu sakammakon gobarar da ba asan dalilinta ba, ko tsinke ba a ɗauka ba a gidan. Babu wanda bai ji mutuwarba cikin tsarin ubangiji kuma shima Hamza yazo dashi aka yi komai daga nan ya koma Sakwato a nan wajan mutuwar ya haɗu da kawar Sadiya Karimahtu har yaji ta kwanta masa suka soma fuskantar juna Sadiya kusan zarewa ta yi don tashin hankali saida aka dinga haɗa mata da tofi da addu o i. Su Inna Aisha sun zo gaisuwa saida aka yi bakwai suka juya zuwa Sayaya tun daga lokacin ganin Muktar ya zamewa iyayyansa wahala tun suna sa ran ganinsa har suka hakura a haka suka shiga matsi da yanayin rayuwa.
Cikin ikon Allah Muhammad ya samu gurbin karatu a college, haka ya dinga faɗi tashi har Allah yasa ya dace amma kash tilas ya hakura da karatun kasancewar shi ne karfin gidan domin mahaifinsu ciwo ya kwantar dashi tsabar damuwa hawan jini ya mammayeshi kuma ya kamashi sossai, ganin babu mafita yasa Muhammad rantar kuɗi ya nufi Kano gidan yayansa, tun safe yazo sai biyar ya samu ganinsa kasancewar ranar karshan makone Sadiya ta kasa ta tsare ta hanashi fitowa haka ya yi ta zama har biyar sannan ya saurareshi bayan yaji kokensa ya haɗashi da dubu biyar. Hankalin Muhammad ya yi matukar tashi ko kuɗin mota dubu ɗaya ya aro gashi bashi dana komawa ciki zai ɗauka ya maidawa wanda ya ara a lisafinsa saura dubu uku me dubu uku zata yi masa?. Ya tambayi kansa kwala ta tarar masa a cikin ido Muhammad mutum ne mai hakuri sossai amma yana da zuciya da gudun wulakanci sunkuyawa ya yi ya ajiye masa kuɗi ya kaɗa kai ya fice daga gidan yana sharar hawaye abinsa. Da taimakon Allah ya haɗu da wani driver ya ɗaukeshi har gida tun a hanya yake kuka da takaicin irin matar da yayansu ya samu sai dai kash yana zuwa gida ya riski tashin hankali daya fi wanda ya baro. Gawar mahaifinsa shimfiɗe a gidansu ga Innarsu na zaune tana tasbihi ga ubangiji, kawai zubewa ya yi a wajan sumame har aka haɗa gawar bai farka ba washegari kuwa dashi aka yi mata sallah aka kaita makwancinta. Tabbas mutuwar ta girgizasu hata Muktar abin ya taɓa zuciyarsa a washegarin daya sami labari ya haɗo kayansa ya nufo garin batare da Sadiya ta biyoshi ba saboda birthday ɗin kawarta tace yaje tazo daga baya hakan ya yi masa ciwo sossai bai jirata ba ya yi tafiyarsa. Hankalinsa ya tashi da irin tarbar da mahaifiyarsa ta yi masa da kyar aka shawo kanta ta saurareshi sai ranar uku Sadiya tazo kuma a ranar ta tursassashi suka bar garin zuwa cikin Katsina saboda ita bazata iya zama a garin ba Hamza kansa ya ji zafin Sadiya a lokacin ya dinga yi mata faɗa amma ta yi masa kwanciyar magge tamkar taji yana barin garin suma suka ɗaga. Inna Aisha ta yi kuka sossai da idonta, duk yadda taso Muhammad ya yi karatu kamar yayansa haka ta hakura.
STORY CONTINUES BELOW

SHEKARU BIYU……..
Tsayin shekara biyu Muktar bai zo gida ba, cikin shekarun an samu sauyi da yawa Muhamad ya yi aure ya auri ɗiyar kawar Inna mai suna Maryam. Haka ma Hamza an yi bikinsa da Karimahtu cikin shekarar Muktar ya tattara duk wata dukiya ta Sadiya ya damkawa yayanta a hannunsa shima ya tsaya da kafaffunsa ya soma cin gashin kansa. Hamza kuwa ya tataro iyalansa sun dawo Kano da zama unguwar Kofar Na isa tazararsu babu nisa da su Muktar. Kawance tsakanin Sadiya da Karimaht sai abun da ya yi gaba, musamman da suka fara yin odar kaya daga kasashe da kansu a shekarar suka je saudiyya suda mazajansu duk sun zama manyan hajiyoyi masu zaune da kugunsu. Bangare ɗaya kuma sun ɗauki ɗamar bankar magungunan hana ɗaukar ciki a ganinsu zai takura musu matuka wajan tafiyar da rayuwarsu daga bisani ne kuma suka hango wautarsu daidai lokacin da mazajan ke yunkurin kara musu abokan zama tuni suka yi fatali da kudirin hana ɗaukar ciki suka bi Malamai aka yi ruwa aka yi tsaki aka murkushe batun aure. Allah cikin ikonsa ashekara Sadiya ta sami ciki, cikinta mai tsanani wahalar laulayi da gajiyarwa komai saidai a yi mata har yayi kwari cikin yarjewar ubangiji. Kwanci tashi cikinta ya isa haihuwa ta haifi sankacecen yaronta wanda yaci sunan Aliyu ake kiransa Haidar ansha artabu wajan saka sunan dan dojewa ta yi sai dai asa sunan mahaifinta amma Alhaji Muktar ya kafe kan nasa zaisa. Haihuwar Haidar ta kawo sauyi da yawa cikin rayuwar Muktar da kansa ya taka har garinsu ya sanar da mahaifiyarsa ta yi murna sossai domin addu arta kullum ita ce Allah ya jyo da hankalinsa. Bai baro garin ba sai da ya cikawa Muhammad shago da kayan masarufi ƴya dinga saidawa ya yi ta mamakin ganin ya yi aure ga matarsa nitsattsiyar mace mai sanyin hali da kawaici ya so maidashi makaranta amma Muhamnad ya dage kan baya so ƴhaka ya hakura ya ɗauko Inna da Maryam suka nufo Kano dan hallatar suna. Zaman da suka yi na ɗan lokaci kafin suna sunsha mamaki da takaici, hata abinci sai an ga dama a basu a haka suka yi ta hakuri har aka kammala suka yi haramar tafiya Alhaji Muktar ya haɗa musu sha tara ta arziki sossai ya salamesu. A hanyar komawarsu suka yi haɗari Inna ta rasu, mutuwar ta gigitasu sossai haka suka ninko Kano suka dawo dake basu yi nisa da gari ba washegari aka je aka taho da Muhammad aka sallah ce aka kaita makwancinta. Tsayin kwanaki bakwai taron mutuwa ya watse dama bawani dangi ke garesu ba Muhammad ya soma haramar komawa shida iyalinsa amma yayansa ya hana gida yasama masa madaidaici nan kasa da layinsu ya biya kuɗin ya basu suka tare, ya wadatasu da kayan abinci sutura da kuɗin kashewa. Ganin hakan ya ɗaga hankalin Sadiya nan da nan ta soma shige da fice cikin kankanin lokaci ta rabashi da kaunar gidan ko hanyar baya bi koda wasa, nan da nan su Maryam suka shiga damuwa da tashin hankalin abin da zaije ya dawo kasancewar ana kawo wuta sossai Maryam ta durfafi saida kunun aya da ruwan sanyi sai kankara kafin kace kwabo ko ina an san da zaman sana arta a unguwa gata da tsafta da son gayu hakan ya karawa sana ar farin jini sossai. Muhammad kuwa dako yake fita kasuwar singa tun asuba sai yamma wata rana ma asamo wata rana kuma ba sa a saidai ma ya dawo a kafa. Rayuwar auansu rayuwa ce mai kyau da shafta.
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji shekarar Hajiya Sadiya uku da haihuwa aka haifi Fadila ɗiyar Alhaji Hamza lokacin Haidar nada shekarar huɗu aka saka shi makaranta, mai zaman kanta da tsada yana samun ƙkulawa sossai. Shekarar Fadila biyu akasata nursery ɗin su Haidar kasancewar tana surutu sossai tare suke tafiya driver ɗaya aka ɗaukar musu sai ya ɗauki Haidar ya biya ya ɗauki Fadila kasancewar makarantar na gaban Kofar Na isa sossai a lokacin Haidar yana _primary two_ duk in da zashi tana makale dashi hakan ya haifarmusu da tsananin shakuwa sossai. Shekararsa tara ya kammala kasancewar a _primary five_ suke zana jarrabawa. Ita kuma Fadila a shekarar ta shiga _primary_ Cikin ikon Allah ya shiga makarantar gaba da primary wadda take kusanci da makarantar su katangarsu ɗaya still dai suna tare da Fadila. Haidar ya shiga _secondary school_ mai suna F. S. S. S _Fikra science secondary school_ yana aji biyu ya ƴhaɗu da abokinsa mai suna Ahmad shi ma ɗan gata ne gaba da baya su huɗune a gidansu amma shi ne auta yayyansu duk matane sun yi aure mahaifansa na zaune unguwar Kofar Na isa a shekarar ne kuma Alhaji Hamza ya gina kerarran gida a unguwar tal udu suka dawo sun sake samun kusanci da juna sossai shida Alhaji Muktar. Fadila kuwa kullum tana gidansu.
***
Maryam haihuwa shiru babu amo ba labari, gata da son yara sossai amma babu kullum cikin addu a take Allah ya bata masu albarka. Cikin ikon Allah saiga hudowar ciki a jikinta tare da Hajiya Sadiya, babu wanda bai yi murna da samun cikin ba cikinsu domin kuwa suna bukatarsa. Kwanci tashi cikin ikon Allah Hajiya Sadiya ta riga haihuwa saboda bakwaini ta haifa. Ta haifi ɗiyarta mace wadda taci sunan Nabila, an yi bushasha sossai. Maryam ta cigaba da rainon cikinta cikin so da kulawa, cikin yardar ubangiji Nabila nada wata huɗu a duniya Maryam ta tashi da matsananciyar nakuda a wata safiyar Asabar.
Gashi Muhammad baya nan haka tayi ta murkususu ita kaɗai a gidan, can saiga shi kamar an jehoshi ya dawo ko dakon bai samu ba hankalinsa ya tashi sossai game da yadda ya sameta. Ya rasa in da zai je tunaninsa Muktar ne amma kuma yana tsoron tunkararsa kai tsaye gidan Alhaji Muktar ɗin ya nufa bai samu kowa ba sai Hajiya Sadiya a babban fallo da sallama ya shiga ta ɗago shekkeke tana yi masa duban hadarin kaji ya yi karfin halin tambayar,
“ina yaya yake?”.
Cikin bagararwa ta ce,
“ajiyarsa ka bani ne?”.
Bai tanka ba ya yi jigum zuciyarsa naga tunanin yanayin daya baro Maryam a ciki can ya kasa jurewa ya tanka.
“Ki taimakamin Maryam ce zata haihu don Allah”.
Wani lallatacan kallo ta watsa masa ta sheke da dariya.
“Shi ne ka kwaso jiki tsomo-tsomo ya kazar data faɗa ruwa kazo mana? Uban wa ya yi mata cikin kai dashi?”.
Ya ɗago a razane yana dubanta ta cigaba da surfa masa ruwan bala i da masifa kansa a kasa ya kasa ɗagowa cikin takaici ya juya zai bar ɗakin yana hawaye.
“Dakata Muhammad”.
Muryar yayansa ta karaɗe kunnuwansa ya juye cikeda mamaki suna fuskantar juna abin da basu sani ba tun zuwansa yana tsaye yana jinsu ya ɗora idonsa kan Hajiya Sadiya yana yi mata wani birkitacan kallo. Ras! Gabanta ya faɗi.
“Kin kyauta Sadiya amma wallahi kar in sameki a gidana in na dawo!”.
Hannun Muhammad yaja suka bar gidan cike da ɗacin rai, cikin sauri suka fice gidan kai tsaye suka wuce duka ɗauki Maryam sai asibiti mafi kusa _ivory_ cikin ikon Allah basu gaza mintuna goma ba ta haifi sankacecciyar ɗiyarta kyakyawa da ita nan da nan aka gyarasu tsaf da yamma aka basu sallama. Siyayya sossai yayansa ya yi musu dangane da kayan hidimar suna dana baby kota kan Hajiya Sadiya bai bi ba hasalima murna yake da rashinta don duk a gama saitaƴhaddasa fitina a gidan suna. Sai bayan sunane Muhamnad ya farga bata nan shi ya matsa aka dawo da ita. Yarinya taci sunan Aisha amma Ummi ake kiranta dashi. Shekarar Ummi uku cif Haidar ya kammala makarantarsa yayin da Fadila na form one . Ummi yarinya ce mai kazar kazar amma miskila ce takin karawa ko abin dariya aka yi da wuya ta yi dariya sai dai murmushi. Cikin shekarar Alhaji Muktar ya tarkatasu ya sasu makarantar su Fadila ita da Nabila kasancewar suna da girman jiki ƙkuma akwai mai musu lesson kullum a gida direct aka kaisu primary one . Hajiya Sadiya ranta bai so ba sabida kuɗin da aka kashewa Nabila shi ake kashewa Ummi amma babu yadda ta iya don kwata kwata aikinta ya daina cin Alhajin shiyasa take duban haihuwar Ummi a matsayin kaddararta. Haidar ne yake kaisu makaranta haka suke haɗuwa a hanya suci zalin Ummi dan a mota tsakiya suke sata Fadila ta mintsina Nabila ma haka tana yin kuka kuwa Haidar zai daddana mata zagi dole take yin mukus da bakinta. Rashin hakuri irin na Ummi suna zuwa aji take kama Nabila ta haye tayi ta bugu a rasa mai kwatarta gata babu karfi sai dai taci kukanta wata rana ta kaita kara idan anje kuma ta yi mirsisi tace tsokanarta take tilas aka raba musu waje. Ummi taci wuyar Haidar sossai gata da son zuwa gidansu saboda Allah ya yita da son shukoki amma ba dama saboda tana zuwa Haidar zai kamata ya zane koya kulleta a ɗaki tare da kuikuyon karansa rayuwar Ummi ta tsani kare matuka. Idan kuwa tazo gaishe da Alhaji Muktar mudun suka yi kiciɓus da Hajiya Saɗiya saita rankwasheta in akai katari kuma Fadila ta kwana su haɗu da Nabila su zaneta haka zata taho tana kuka tilas mahaifiyarta ta hanata zuwa gidan saida bada saninta ba daga bisani data kara wayau saita hakurewa zuwa gidan.
****
Fadila na form three result ɗin Haidar ya fito na makaranta su Ummi kuma primary three. Bayan komai ya lafa sakammako ya yi kyau nan suka fara karatunsu shi da Ahmad a jami ar Bayaro ta Kano. In da Allah ya taimakeshi yana da nacin karatu ba kamar yadda wasu yayyan gatan ke yin rayuwa ba. Haidar tun yana nursury akwai kwanya da farin jinin malamai har zuwa jami a a nan ne ya taka rawar gani sossai sabida kasancewarsa kyakkyawa ga iya ɗaukar wanka. Fikrarsa na birge wanda ta sanshi gashi da miskilancin tsiya ko kaɗan baya sakin fuska gudun raini. Da dama na kawo masa farmakin soyyaya amma ko kaɗan hakan baya gabansa hidimarsa kawai yake. Ahmad kuwa ɗan abi yarima asha kiɗa matane kawai abokansa ga ɓarin dukiya da yake musu kamar hauka, ganin yadda Ahmad yake da dama suka ɗauka Haidar ma haka yake domin abokin ɓarawo ɓarawo ne, kuma na shiga ban ɗauka ba bata fitar da ɓarawo. Sheakarar Haidar Huɗu da kammala digiri ɗinsa na farko a shekarar Fadila tana level two a Bayaro in da take karantar accounting Ummi da Nabila kuwa suna matakin farko a secondary school. Cikin shekarar ne mahaifinsa ya nema masa gurbin karatu a kasar _Germany_ in da yake so ya zama cikakken likitan mata shi kuma Ahmad accounting zai karanta duk gari ɗaya aka sama musu. Soyayya mai zurfi ta kullu tsakanin Haidar da Fadila wadda ya kasa tantance so ne ko shakuwace ta kasancewa waje ɗaya aka ya tattara kayansa ya bar kasa sun rabu suna kewar juna sossai kowa na takaicin tafiyar Haidar amma banda Ummi har party tayi don murna.
Alhaji Muktar yana son Ummi sossai, Baffa shi ne sunan da take faɗa masa yayin da mahaifanta take kiransu da Ummu da Abbu. Daidai gwargwado tana samun kulawa wajan mahaifanta, yarinya ce mai nutsuwa sossai bata da kwaramniya da tashin hankali gaba ɗaya lokutanta suna ga karatu in ta tafi makaranta tun safe sai ɗaya suke tasowa daga nan kuma zata tafi islamiyya karfe ɗaya da rabi sai shida na yamma haka duk lokutanta ke tafiya bata da hutu sai dare. Domin mahaifinta bai amince da makarantar dare ba suna aji uku a makaranta a ka bata mukamin Amirar makaranta hakan yasa sunan Amirah ya yi tasiri sossai a kanta ƴhar unguwarsu ma Amira ake ce mata.
Rayuwar Haidar a Germany rayuwa ce da za a ce Allah ya kyauta da farko karatunsa kawai yake, a hankali Ahmad ya dinga kwaɗaita masa rayuwa da mata tun yana kwaucewa har yayi nasara a kansa sossai idonsa ya buɗe da mu amala da mata tare da amfani da barasa. Sai dai yafi mu amala da mata sossai fiye da barasar sun zame masa jiki, idan kuwa suka zo hutu gida to Fadila ce abar ɗebe kewarsa lokuta da dama tare suke yini a _horounbiya club_ ta zamo tamkar wata matarsa tsula tsiyarsu kawai suke a binda kuma bai sani ba a bayan fagge Fadilan farkar Ahmad ce don tasha zuwarwa Ahamd hutu Germany ya kama mata hotel ba tare da sanin Haidar ɗin ba.
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji komai na tafiya cikin kwanciyar hankali, Ummi bata da kawa ko ɗaya sai Hindatu Mustapha. Su Ummi suna form two Haidar ya zo hutu gida a lokacin takai wata biyar bata je gidansu ba kwatsam ranar wata talata ta tashi da son zuwa gidan. Misalin karfe uku na yamma ta shirya cikin cikin doguwar riga da hijabi ta tafi gidan. Gidansu Hindatu ta soma zuwa amma kash bata sameta ba da niyyarta tajata su tafi tare amma bata yi sa aba. Jiki a sanyaye ta juyo ta ɗauki adaidaita ya dawo da ita Goron dutse cikin ranta tana hango wautarta na nemo rakiyar Hindatu dake nisan duniya. Cikin ikon Allah ta karaso gidan da babu kowa a harabar gidan kai tsaye ta wuce abinta abin mamaki gidan shiru babu motsin mutane hakan yasa jikinta sanyi sossai harta juya zata koma ta hango kofar fallon baki a buɗe ta karasa shiru babu kowa ta juya taza fito wani sautin nishi yaja hankalinta cikin sauri ta kai idonta wajan ras! Ras!! Ras!!! Gabanta ya faɗi
Cikin kaɗuwa ta jefa idannunta wajan da take jiyo tashin numfarfashi, take hankalinta ya yi masifar tashi ganin Haidar da Fadila a wani yanayi mai mugun fassaruwa. Numfashinta ya soma kai komo yana barazanar ɗaukewa. Haidar ne daga shi sai gajeran wando, tunda Ummi take bata taɓa ganin namiji haka ba. Gefansa Fadila ce tayi matashi da cinyarsa ya sunkuyo ya kama bakinta tamkar wata alawa. Cikin hanzari tayi baya zata bar ɗakin amma ta makaro tsale ya yi ya taɗeta ta faɗi bakinta ya datse da hakori sai jini. Da sauri ya yi wa Fadila in kiya ta mike tasawa ɗakin mukuli ya birkito Ummi dake kokarin fasa ihu ya rufe mata baki.
“Allah ya isa”.
Ta furta bayan tayi kasarar kwace bakinta, ya kuwa fusata ya daddage ya ɗauketa da giggitacan mari. Kuka tasa amma saboda naci bata daddara ba ta murguɗa baki ta ce,
“ɗan iska”.
Cikin dariya ya ce,
“zaki ga karewar iskanci”.
Bata yi aune ba ya rungumo Fadila suna kyalkkyala dariya take ta runtse ido tana neman tsari da abin da suke aikatawa, can Fadila ta yi masa raɗa a kunne suka kwashe da dariya ya nufo Ummi gadan-gadan zatonta dukanta zai ta soma ja baya har suka kai karshan fallon cikin tsoro ta buɗe baki zata yi magana ya jefa bakinasa cikin nata hankalinta a tashe ta kasa kwatar kanta dabara ta faɗo mata ta daddage ta gantsara masa cizo ba shiri ya yi baya yana faɗin,
“ashhhhh!”.
Cikin sauri ta sunkuya ta ɗauki kwalbar lemon coke dake gabansu ta bugata a bango ji kake tarats! Ta bada sauti tana huci ta nuna shi,
“wallahi duk wanda ya matso saina raunatashi”.
Sak! Suka yi suka kallo ta zare sakatar ta yi waje da gudu a harabar gidan ta wanke fuskarta ta nufo gida tana tafe tana share hawaye. Zuciyarta cike da tausayin Baffa yana can ba tare da fahimci ƴhalin da ɗansa yake ciki ba. Ummi bata sake komawa gidanba harya koma hutunsa daga nan bai sake zuwa gida ba harya kammala karatunsa ya dawo gida.
CIGABAN LABARIN………
Abbu ne ya dubu Ummu cikin taishin murya,
“wai kuwa Maryam kina hango alfanun auran Ummi da Haidar?”.
Ummu ta yi murmushi irin na ma abota kunya ta ce,
“Abbu komai nufin Allah ne bana tunanin Ummi zata bijire mana”.
“Ba wannan nake ji ba Hajiya Sadiya da kuma Khalifa nake ji”.
Ta yi jim tana tunani ta numfasa daga bisani ta ce,
“Hajiya Sadiya bata yi ya yin ubangiji ba, Khalifa kuwa ka iya bashi hakuri domin baka yi alkawarin bashi Ummi ba”.
“Allah ya yi mana jagora kawai Maryam”.
“Amin”.
Ta furta a sanyaye, Ummi dake ɗaki ta dafe kai wani sabon son Khalifa na hankoro a zuciyarta.
****
STORY CONTINUES BELOW

Cikin kwana biyu aka kammala shirin tashin su Ummi daidai da tsinke Baffa bai bari na kayan ƴhidimar gida sun ɗauka ba kwata-kwata. Tsarin gidan ya birge Ummi sossai komai da komai irin na gidan Baffane sai dai abin da ya tayar mata da hankali yadda Baffa ya rufe hanyar shigowarsu ya buɗe babbar kofar gidan wadda zai zamto mahaɗar gidan ta zama abu guda ne wato da tasu data gidansa. Ta jima tana tunanin yadda zasu rayu gida ɗaya da Haidar da Nabila ga kuma Mommy. Komarasu Ummi gidan ya haifarmata da takura sossai musamman da Baffanta ya ɗaukar musu driver ɗaya ita da Nabila hakan ya haifarwa Ummi nakasu sossai cikin tafiyarta makaranta don da gayya take kin shiryawa da wuri.
***
Tunda aka yanke batun haɗata aure da Haidar ta koma wata sukuku, kullum cikin tunani take saukinta ɗaya Khalifa yake Cairo saro kaya ƴhakan ya rage mata fargaba saboda tana tunanin fitikarsa. Ummu na kula da yanayinta sossai amma taki tankawa tausayinta yafi damun zuciyarta. Bangaran Khalifa hankalinsa ya ki kwanciya da yanayin da Ummi take masa a waya duk sai tafiyar ta fita ransa ko ya matsa mata da tambaya amsar ɗaya ce ba komai. Kwatsam ranar Lahdi da dadare ya doko mata waya kan yana tafe ranar Littinin da yamma, ka idarsa ranar daya duro garin to kuwa da dare zai tako gidansu. Hankalinta ya rabu gida biyu ta rasa yadda zata yi ƴhaka ta kwana sukuku da ita idonta duk ya tasa saboda kuka.
***
Ranar Littinin da wuri Ummi ta shirya cikin _uniform_ ta yi wa Ummu salama zata wuce makaranta ta kafeda da ido wanda yasa jikinta sanyi matuka ta sadda kanta kasa tana kokarin maida ɓoyyayan hawayan daya ke shirin zubo mata.
“Ummi”.
Ta kira sunanta a tausashe, ta amsa murya a raunane.
“Na’am Ummu”.
“Kisa Allah a dukan lamuranki, sai ya taimakeki”.
Ta buɗe baki zata yi ƙmagana, ta ɗaga mata hannu.
“Je ki bana son jin komai, Allah ya yi miki albarka”.
Murmushi ta yi ta maida hawayan ta wuce abinta. Gidansu Haidar ta faɗa ta samu Mommy zaune a falo ta gaisheta ta amsa a dakile bata damu ba ta zauna lokaci zuwa lokaci takan kali agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta ta share mintuna kusan goma ta ga dai miskilanci bazai mata ba ta numfasa ta ce,
“Mommy Nabila bata nan, ko bazata makaranta ba?”.
“Bata jin daɗi bazata ba”.
Dum! Taji saukar maganar, ranta ya ɓaci ta duba taga takwas saura mintina uku. Tana shirin magana ta ji muryar Baffa da Haidar suna gaisawa ta risina ta gaishesu.
“Ummyter lafiya baki tafi makaranta ba”.
“Lafiya Baffa Nabila na jira ashe bata da lafiya amma yanzu zan tafi insha Allahu”.
“Asha! Allah kara afuwa, maza je ki ya kaiki karki makara menene ya sameta ne?”.
Ya yi tambayar yana duban Momy, sai da ta yi yatsina ta amsa.
“Fever ne, driver kuma na aikeshi”.
Ya kafeta da ido,
“amma kinsan time ɗin yan makaranta ne ko”?.
Ganin zata ɓata masa ya rai ya dubi ƳHaidar,
“mu je ka kaita”.
Ya yi gaba cikin sauri suka rufa masa baya ta rakasu da harara.
Cikin nutsuwa suka bi bayansa har bakin motar Haidar Baffa ya rakasu yana sa musu albarka, gidan gaba ya buɗe mata ta shiga ya yi baya da motar ya bar harabar gidan. Tafiya suke tamkar kurame kowa da abinda yake sakawa cikin ransa ya kai hannu ya kunna rediyon motar wakar matashin nan korodebello mai taken african queen. Cikin salon gwanancewa yak e bin wakar sunyi rabin tafiya wayarsa ta yi kara ya kai hannu ya rage sautin rediyon yana murmushi ya ɗaga wayar. Ya buɗe muryar wayar duka ya furta,
“Hi my queen”.
“Hey prince”.
Aka faɗa daga ɗaya bangaran.
“Ya ne tawan?”.
“Ya fa?”.
Ta furta cike da ginshira, ya ja numfashi yana rage gudun motar.
“Bansan damuwa fa Fadila”.
“Kaima kasan damuwa dola ce, zuciya bata tare da kulawarka”.
“Hmm! Fadila kenan”.
“Haidar mu aje batun wasa wai dagaske wannan kwailar yarinyar zaka aura?”.
A ransa ya furta,
“mahaukacine ni zanki bin umarnin mahaifina?”.
A fili kuwa sai ya furta,
“haba Fadila kema kinsan ke kaɗaice macan da nake so, kuma kinsan ra ayina ni MIJIN MACE DAYA ne. Kisama ranki ko auranta na yi to kuwa kece matar ita dai sai yarinyar gida”.
Cikin kukar rai Fadila ta furta,
“kanama mafarkin auranta?”.
“Please! Fadila kinsan fa bana son saurin fushi wallahi, ke banda kema ce ina da lokacin lalashin wata mace ya kike so in yi ne? Zan ɓatawa Daddyna saboda ke?”.
Jin yadda ya taso mata haikan yasa ta sassauta,
“shikenan to my prince”.
Da haka suka kashe batun suka dinga musayar kalamai tsakaninsu suna dariya Ummi ta fahimci so yake ya bakanta mata hakan yasa ta kanne taki dubansa haka fuskarta wasai da ita ko ido suka haɗa murmushi take sakar masa ai kuwa ya kule matuka salama ya yi wa Fadila ya maida hankali kan tukinsa yana yi yana kwafa can ya dubeta,
“ke banza bagidajiya wai ba kya fushi ne!?”.
Dariya ta kama Ummi ta maida a barta tana dubansa daidai lokacin ya yi parking a harabar makarantar. Bata tanka ba ta buɗe murfin zata fita, ya yi saurin dana wani madani murafan motar suka rufe ruf suka datse yatsanta ta saki kara da sauri ya buɗe yana dariyar mugunta ta fice da sauri ya wurga mata jakarta yana shirin jan motar ta gyara tsayuwarta tana murmushi ta kira sunansa.
“Haidar!”.
Ya juyo a hanzarce suka haɗa idanu…..ras gabansa ya faɗi…..
STORY CONTINUES BELOW

9
Cikin tashin hankali da mamaki yake dubanta, yadda ta dake tana kallonsa,
“mugu kawai ban yafe ba”.
Ta faɗa tare da murguɗa baki tayi gefe guda yayo kanta da mota ta kwasa ta yi cikin makaranta tana dariya amma babu alamun ɓacin rai a fuskarta sai dai cikin zuciyarta yafi gidan buredi kuna. Tana shiga suka yi kiciɓus da ƳHindatu ta dubeta tana dariya, amma akasin hakan kallon tuhuma take mata,
“yadai Hinduwa”.
“Yafa na je gidanku jiya a rufe ina kuka je ne? Na kuma aika driver bakwa nan duk kin tadamun hankali”.
“Mun tashi ne sisty”.
Ta bata amsa kai tsaye, ta dubeta da mamaki.
“Ina kuka koma?”.
“Jikin gidansu Haidar”.
Ta amsa tana maida kwalar data kawo idanunta bata tanka ba suka shiga aji suka zauna kowa da abin da yake sakawa cikin ransa. Suna shiga Malaminsu na _Biology_ ya shigo yana yi musu darasi kwata-kwata hankalin Ummi baya kansa har ya yi ya gama ya kama nasa waje yana fita ta kafeta da ido.
“Waike Ummi menene yake damunki?, nafa lura dake cikin kwanakin nan baki da walwala kwata-kwata kuma sai nayi magana kice babu komai”.
“Babu komai Hindu”.
“Hmmm! Babu komai, kullum haka naga randa zaki ajiye wannan ɗan iskan miskilancin naki Ummi ayi mutum sai zurfin cikin masifa kwata-kwata yau wallahi a hargitse kike wai menene ko Yaya Khalifa korafinsa kenan kwana biyu kin sauya masa gashi yau zai dawo shiyasa ma jiya naje gida ban samekuba dan dubo masa lafiyarki ashe kun tashi bakin hali ya hanaki faɗa please Ummyter menene?”.
Ta faɗa tana shirin yin kuka.
“Hmmm! Hindatu babu komaifa”.
“Dilla Ummi karki maidani karamar yarinya, bance sai naji matsalarki ba amma fa kisani ina jin ciwo wallahi. Na rasa ya kike dubana, kwata-kwata ba kya san ina shiga sabgarki saɓanin ni duk abin da ya shafeni saina sanar dake bakin ciki ko akasinsa kece mutum na farko bayan mahaifana da nake tunkara da matsalata. Amma shikenan hakan bazai sauya miki matsayi cikin raina ba domin aminiya na ɗaukeki saɓanin ke”.
Cikin hanzari ta tsaida ita,
“dakata Ummi!”.
Ta faɗa tana share kwallar da suka zubo mata.
“Don Allah kiyi hakuri Hindatu, bawai bana son kisan damuwata bane ina duban yadda zaki ɗaukenine musamman keda Yaya Khalifa”.
Gabanta ya faɗi ras! Ta cigaba da dubanta baki a sake.
“Bangane ba?”.
Ta yi murmushin takaici,
“Hindatu wallahi abun ne is my family issue that is why bana son fasawa ne”.
“Ok! Na fahimce ki amma ki dinga kokarin ɓoye damuwarki tana takurani matuka uwa uba Yaya Khalifa”.
Hankici tasa tana sharewa Ummi hawayan daya kwaranyo mata cikin nutsuwa take tausarta da kalamai masu taushi. Ummi ta yi tsai tana dubanta, duk ta tashi hankalinta kan damuwarta sai taga rashin kyautawarta komi nata tasani amma ita tana ɓoye mata nata sirrin a haka suka koma aji.
***
Karfe goma aka fito dasu _break_ suna zaune Nabila tazo wucewa ta wajansu ko kallo basu isheta ba, mamaki ya cika Ummi na ganinta kawai saita basar Hindatu ta dubeta,
“aminiyansi kin koyawa kanwarki hankali fa”.
“Gidanku Hindu tafa girman”.
Dariya suka yi ta muskuta,
“Hindatu kiyi ƴhakuri da abin da na yi miki ɗazu”.
Cikin nutsuwa ta bata labarin komai game da haɗata aure da Haidar. Kafin ta gama gaba ɗaya gumi ya wanke Ummi tsabar tashin hankali kawai Yaya Khalifa take hangowa da ƴyanayin da zai kasance in ya samu labari
10
Haka suka kasance cikin makaranta sukuku har aka tashi kowa da abin da yake ayyanawa cikin ransa. Karfe ɗaya da kwata aka tashesu suka rabu Ummi na zuwa gida fargaba ta haifar mata da zazzaɓi da ciwon kai tilas ta hakura da zuwa islamiyyah hankalin Hindatu ya tashi sossai ganin Ummi bata zo USMAN BIN AFFAN ba ta tabbata cikin ɗaya akwai biyu taso biyowa da aka tashi amma ganin yamma ta yi daga Gadon kaya zuwa Gauron dutse akwai tazara tilas ta hakura da zuwan kai tsaye ta wuce gida. A harabar gidan ta iske Yaya Khalifa da murmushi ta karasa wajansa amma abin da ta gani ya razanata duk ya faɗa ya yi baki kamar bashi ba bakinta na rawa ta furta,
“ciwo kayi ne Yaya?”.
“A a kanwata ba ciwo na yi ba fargabar meya samu Ummyter nake ina yawan mafarnta tana kuka kuma ke kincemun lafiyanta lau na tambayi driver ya ce min baku sameta ba da kuka je”.
Cikin dakiya ta aro juriya ta ce,
“Eh tashi suka yi sun koma kasan layinsu jikin gidan Alhaji Muktar wan mahaifinta”.
Ajiyar zuciya ya saki har saida ya tsorata Hindatu ya bata hanya ta wuce tana tafe tana waiwayansa zuciyarta fall tausayinsu.
STORY CONTINUES BELOW

***
Ummi na kwance kiransa ya shigo wayarta ta amsa da sayin jiki ya bata tabbacin yana tafe da anyi sallahr isha i. Ganin magarba ta gota ya sata mikewa ta sake gyara ɗakin bakinsu duk da a gyare yake. Kitchen ta shiga don sama masa abin motsa baki ta yi tsam tana dube-dube dabara ta faɗo mata ta haɗa masa kirkir.
KIRKIR
Wani ice cream ne na labarawa da matansu suke haɗa musu. Yayin da uwargida zata yi kirkir zata bukaci abubuwa da dama.
ABIN BUKATA…..
Kwakwa
Sugar
Madara
Flavour
YADDA AKE YI
Zaki wanke kwakwarki ki tsaftaceta ki kankare bayanta ki gurzata kanana. Saiki wanke tukunyarki tsaf ki zubata kikawo zuwa kizuba yasha kanta ba kindimba saiki kunna abin girkinki. Yana tafasa saiki ɗauko madararki kikwaɓata da kauri kamar zaki kulin gasara ki kwara akai zai ɗaure kisa sugar da flavour shi kenan. Ana iya yiwa kunun gyada ma haka a yi da kwakwa maimakon shinkafa wannan dahuwar ruwan da kika yi da kwakwar zaisa kunnun yayita kamshinta.
Cikin mintuna talatin ta gama tasashi a maadanar sanyi ta faɗa banɗaki mintuna goma ta sala wankanta ta fito.
Ta jima tsaye tana karewa kanta kallo a madubi ta kasa taɓuka komai, mai kawai ta shafa tare da body spray mai kamshi ta janyo wata doguwar riga baka siɗik ta saka daga samanta robane kasan ta buɗe sossai an yi mata tattara da jar kala _red_ da kuma ratsin _gold_ rigar tana da siririn hannu saita saka karama daga ciki mai dogon hannu ta tsaya a jikinta cas ta fito da ita. Hoda kawai ta mutsuka ta taje gira tare da saka man leɓɓe daidai lokacin wayarta ta yi kara ta ɗaga a sanyaye.
“Assalamu alaiki”.
“Wa alaika salam Yaya Khalifa ina yini”.
Shiru ya ratsa tsakani mamaki da saiyin Ummi makare a kirjin Khalifa ya daure ya wurgar da komai tare da aro juriya ya yafa.
“Lafiya lau Ummyter na iso”.
“Ok!”.
Ta faɗa a takaice tare da katse kiran ta nufo fallon da Ummu take da sanyin jiki ta shiga tana sanarmata zuwansa ta bita da kallo.
“Ummi haka ake rayuwa, duk kin bi kin kwantsame kan abin da bai kai ya kawo ba?”.
Ta cije leɓe, kirjinta ya yi nauyi dundrus. Yau da wanine ya ke faɗar haka Allah kaɗai yasan abin da bakinta zai furta masa. Murmushi ta yi ta mike tana faɗin,
“afuwan Ummu”.
Kai tsaye ta fita ta yi wa Mansur mai wankinsu magana ya yi wa Khalifa iso zuwa ɗakin baki. Ya kai mintuna shida da zama sannan ta iso kanta yane da jan mayafi me ratsin gold ta sake risina ta gaisheshi. Idanunsa kyam a ƙkanta kirjinta ya dinga harbawa yana son karantar yanayinta amma taki bada fuskar ƴhakan.
Tilas ya hakura ya ɗauke idanunsa ta jawo karamin table ta soma shirya masa kayan motsa baki. Da kanta ta zuba masa komai ruwa kawai yasha tare da dubanta yana murmushi ya ce,
“Ummi naji abin alkhairin da kuka samu na sauyin da kuka samu Allah sakawa Baffa da alkhairi ya kara zumunci”.
“Amin ta faɗa a ɗarare”.
Ya numfasa,
“abu na gaba inasan sanar dake cewar su Daddyna zasu zo neman auranki don haka ki sanar a gida”.
Ta ɗago a hanzarce tana dubansa,
“a dakata Yaya Khalifa”.
Ya tsura mata ido sossai, bakinsa na rawa.
“Dakatawa Ummyter? Me kike nufi nifa na kasa fahimtarki tun kafin na dawo duk kin sauya kin sakwarkwace da an yi magana kice babu komai menene?”.
Idonta ya kawo hawaye,
“kayi hakuri Abubakar da abin da zance maka”.
Gabansa ya tsananta faɗuwa ta cigaba,
“kayi hakuri su Abbu sun yanke haɗani aure da Yayana Haidar shi ne ZABINSU”.
Wani abu ya tokarewa Khalifa kirji ya taso a razane bata yi aune ba ta ganshi rike da hannunta,
“Ummyter me kike faɗamin kina nufin na rasaki?”.
Kawai ta ɗaga masa tana shasshekar kuka zuciyarta kamar zata fasa kirjinta.
Ta kwace rikon da ya yi mata ta kufce ta yi gida da gudu tana kuka Ummu na kalanta ta yi banza da ita, kuka take mai kuna a haka ta tsinkayi tashin motar Khalifa cikin matsanancin gudu gabanta ya yanke ya faɗi.
***
Gudu kawai yake shararawa Allah ne ya kaishi gida lafiya yana parking ko rufe motar baiyi ba ya shiga gida a guje a falo ya haɗu da Hindatu ya yi mata wata wawar cafka zata yi ihu ya zare mata ido sai ɗakinsa.
“Ni zaku munafunta Hindatu, hadda ke?”.
Gabanta ya faɗi ta dake,
“bangakeba Yaya?”.
Hannu ya ɗaga ya zabga mata mari yana huci ta fashe da kuka ya hankaɗata tare da dafe kansa.
“Shi kenan sis na rasa Ummi da haɗin bakinki na gode”.
Jikinta ya yi sanyi lokaci guda tsanar Ummi ta dirar mata a cikin zuciyarta.
Mikewa ta yi ta baro ɗakin cikin tsananin gudu sai ɗakinta, jikinta har kakarwa yake ta dana kira wayar Ummi lokacin da kiran ya shigo kasa ɗauka tayi sai da ya kusa katsewa……kukan da Ummi take yi ya fi komai ɗagawa Hindatu hankali jikinta ya yi sanyi duk abin da ta tattaro sai taji ta gaza aiwatarwa sai kawai tana shirin datse kiran ne lokacin mahaifiyarta ta shigo a ruɗe tana sanar da ita Khalifa ya yanke jiki ya faɗi karaf a kunnuwan Ummi ta kwala kara tana kuka. Cikin sauri suka nufi ɗakinsa saida ya jima sannan ya dawo hayyacinsa. Hankalin mahaifiyarsu ya tashi cikin faɗa take tambayar abin da ya wakana Hindatu bata ɓoye mata komai ba ta yi jim tana dubansu ta mike ta bar ɗakin. Daidai lokacin wayarsa tayi kara ya duba yaga Ummi ce kamar bazai ɗaga ba ya daure ya ɗaga. Kuka ya sarketa ta kasa cewa komai ya daure ya ce,
“Ummi kiyi shiru bana so”.
Taja ajiyar numfashi,
“kayi hakuri nasan ba a kyauta maka ba amma karka manta nima mai bin umarni ce”.
“Ummi kema kin daina sona kawai ban da haka miyasa zaki amince dama ba sona kike ba?”.
Kanta ya sara ta cije leɓe,
“karka ce haka yaya wallahi ina sonka”.
Kalmar ta dakeshi amma ina shaiɗan kara kawatamasa soyayyarta yake a ransa ganin zaisa mata rigima yasa ta yi dabarar lallaɓashi suka yi salama.
***
Washegari Khalifa da kansa yaje wajan Abbu kan jin gaskiyar lamari sai dai abun takaici hakuri ya bashi tare da jadaddamasa ya bada auran Ummi a lokacin Haidar yazo gaisheshi harya nuna masa shi suka yi kalon-kallo sallama Khalifa ya yi masa ya wuce gida jikinsa ɗauke da zazzaɓi mai zafi. Haka suka kasance tsayin kwanaki huɗu basuga juna ba kuma babu waya Khalifa ya rame ya yi tsuru-tsuru dashi ƴhakama Ummi da Hindatu. Hindatu tafi kowa damuwa domin a makaranta Ummi yini take kuka gida kuwa Khalifa ya tasata gaba ko abinci baya ci.
***
Kwance take kan gado bata da aiki sai kuka. Ji take kamar ta kurma ihu tsabar takaici da kuncin zuciya, duk ki take ta tsani kanta. Saboda duk wata damuwa ta nuna amma mahaifanta babu wanda ya kula da lamarinta. Babban takaicinta ta kasa raba zuciysrta da son Khalifa ta numfasa tana tunani a zuciyarta Abbunta ita kaɗai ya haifa, ya bata tarbiya ya ɗauki ɗawainiyarta da daɗi babu daɗi. Ya bata farin ciki fiye da kansa babbar matsalarta ta ina zata iya rayuwa babu Khalifa?.
Tunaninta bata taɓa kawo rabuwa da Khalifa ba, bare ta yi tanadin hakurin wannan rana, ta numfasa wata zuciyar tana bata tabbacin ta maida lamuranta ga ubangiji ta hakura bata komai sai addu’a sai kuka hata karatun ta watsar da shi. Wayarta kuwa tun ranar bata sake waiwayarta ba tama kasheta ta sakata a jakarta ta jawo ta kuna kamar wadda ake jira sai ga sakwanni a kala guda goma. Sakwannin sun ɗaga mata hankali tare da rikita mata kwakwalwa ta yi saurin saka wayar a silent ta ajiye kasan fillo ta kwanta.
Washegari tun safe ta shirya cikin uniform ta nufi ɗakin mahaifinta. Ta gaisheshi ya kafeta da ido yana murmushi,
“Ummyter kin zama mallama mai tsayuwar dare”.
Ta ɗago kai a hanzarce ya jinjina mata kai ya ci gaba da magana.
“Akwai sauyin da kika gani a sallolin da kike rattabawa?”.
A zaune take amma saida ta rankwafa,
“Ummyter ba ayi wa ubangiji wayau kuma bazaki ce bakya addu a ba sai matsala ta sameki”.
Mamaki ya cikata ashe Abbunta duk yana kula da motsinta bata sani ba.
“Ummyter ta yaya zan haifeki in cutar dake? Ke kaɗaice fa ɗiyar dana mallaka duk duniya akwai wanda zai soki bayana da Ummunki da kuma Baffa?. Wallahi kinji na rantse ko ki nutsu ko ki ki nutsuwa aure babu fashi bazaki ɓata tsakanina da ɗan uwana ba”.
Kafin ta yi yunkurin magana ya fice ya bar ɗakin, Ummu ta dubeta cikin tausayawa ta ce.
“Ummi Allah ubangiji maɗaukakin ya halicci kunci ko jarrabawa a rayuwar duniya ta yadda sai bayinsa da ke aiki da hankula da kwakwalensu ke samun rayuwar farin ciki. A cikin hikimar wannan jarraba akwai kyakkyawa kuma sassaukan tsarin manufa mai saukin fahimta da sabuntawa. Amma wadanda ba sa yin duba da idon basira, irin wanda Allah ya bayyana mana a cikin Alkur’ani, wadanda kuma ba sa lura da abubuwan da suka zo a cikin Alkur’anin, ba za su iya fahimtar wannan sassaukar manufa da ke ɓoye cikin jarrabawar ba.+
Saboda haka suke shafe yawancin rayuwarsu cikin yanayin kunci da tashin hankali; wato rayuwa marar amfani mai cike da yawan damuwa da bakin ciki. Duk lokacin da wadannan mutane suka sami kansu cikin mawuyacin hali, su kan dube shi a matsayin bala’i da ba shi da magani ko mafita. Tabbas irin wannan tunani yana nuna fita daga hayyaci da toshewar basira, wanda tasirinsa kan sanya masu wannan siffa su debe kauna ta yadda ba sa zaton samun kansu cikin wani yanayi daban sabanin wannan mawuyacin da suke ciki. Amma hakikanin lamari shine, duk wanda fahimtarsa ga jarrabawa da kunci na wannan rayuwa ta duniya tana bijirowa ne daga mahangar Kur’ani, to ba za ka taba ganinsa cikin rudu da daburcewar al’amura ba, ko ka gan shi kullum cikin kunci da tashin hankali irin na rashin nutsuwar zuciya ba. Akwai wasu al’amuran hakika wadanda duk mutumin da ya yi imani da Allah zai gaskata su kai tsaye. Wannan ilimi kan taimaka wa mai imani wajen yanke hukunci da ya dace da kyakkyawar koyarwar Alkur’ani ta hanyar yin amfani da tunaninsa. Bayanan hakika na Kur’ani su kan yi tasiri ga wanda ya gaskata su a dukkan al’amuransa na yau da kullum. Idan mutum ya ci karo da matsaloli ko wahalhalun rayuwa, to tunda kuwa ya gina rayuwarsa ne akan koyarwar Alkur’ani mai tsarki, babu wata jarrabawa, wahala ko kunci a fadin wannan duniya da zai hadu da su, duk kuwa tsanani da girmansu, face sai sun zo masa da sauki kuma ya sami maganinsu. Irin al’amuran rayuwar da ke haddasa mummunan bakin ciki, da bacin rai ko tashin hankali da kuma da-na-sani ga mutanen da babu darsashin imani a zukatansu.
Ina shawartarki ki ajiye komai ki mikawa ubangiji lamarinki shi zai miki maganin komai”.
Tsam ita ma ta mike ta barta, Ummi ta mike tana hawaye ko ganin gabanta da kyar take iya yi ta faɗa mota driver ya tafi kaita makaranta……
***
Khalifa zaune a fallo Hindatu ta wuce shi zuwa makaranta ya bita da kallo tare da jan tsaki. Mahaifiyarsa ta dubeshi,
“Khalifa ya kamata kasawa zuciyarka hakuri game da lamarin nan kasani wani fa baya auran matar wani”.
“Haka ne Mama amma ai auran dole za ayi mata kuma babu kyau ni dai ni take so. Aima bazata yi wa mijin biyayya ba Mama tunda bata kaunarsa”.
Murmushi ya suɓuce mata ta ce,
“Nasani Khalifa kuma kafini gaskiya domin dai dabi’ar ɗan Adam ce duk wani motsi nasa in dai akwai soyayya a cikin wannan abun ya fi yin sa cikin gamsuwa ko kuma a jere- a jere. Amma idan tsantsagwaron jajircewa ne ka wai a cikin aikin zuciyar babu wani sofane na soyayyar abinda yake yi, to babu shakka cikin kankanin lokaci zai sare. Tilas a lamarin aure ana son koyayane ya zama akwai soyyayya sai dai ka yi mantuwa”.
“Mantuwar me Mama?”.
“Khalifa Ummi ɗiyace da ta samu nagartaciyar tarbiya barganin tana sonka wannan bazaisa taki auran wanda bata so ba kodan farin cikin mahaifanta kuma koni zan iya bin bayanta domin duk ɗa na kirki yana bin umarnin mahaifansa”.
Idonsa ya ciko da hawaye yana dubanta ta kauda kai,
“Mama ya zan yi da son Ummi?”.
STORY CONTINUES BELOW

hakikanin gaskiya Khalifa kowa da yadda yake ɗaukar kaddara a rayuwarsa, wasu sukan ɗauketa da sauki wasu kuma su kan sanya nutsuwa da farin ciki ga ma’abota imani, da yake sun yi riko da kyakkyawar mahanga. Domin kuwa abin ya danganta ga imanin mutum shi kuma dalilin samun wannan saɓanin fahimta ta mahanga a tsakanin muminai da marasa imani shi ne saboda su muminai sun kasance masu ilimi da kuma bada gaskiya da abin da ke cikin Alkur’ani mai girma. Hakan kuwa ya kasance ne saboda sani da kuma imaninsu akan cewa. Allah iliminSa ya game komai, Allah mai matukar adalci ne. Allah yana fitar da bayinSa daga halin kunci da masifa. Mika al’amuranmu ga Allah Ubangijinmu, masani mai tsananin hikima da adalci, da rahama da soyayya ga bayinSa, it ace hanyar lumana. Mutane suna rayuwa ne kan abin da aka kaddara musu, kuma koda za su rayu a duniya marra dubu, ba za su wuce kadarinsu ba wanda Allah masanin halitta ya tsara musu. Duk abubuwan halitta da mutane suke gani a sararin duniya ba zaman kansu suke yi ba; komai nasu yana gudana ne da umarni da kuma ikon Allah da ya kage su. Kyakkyawan al’amari ko mummuna yana zuwa ne daga nufin Allah, mutane ba su da iko akan tunkude sharri ko jawo alheri akansu. Bai halatta ga mutane su rika gaba da junansu ba, domin cewa su kaskantattu ne kuma raunanan halitta wadanda ke rayuwa a bisa iko da kaddarawar Ubangiji, kuma ba su da ikon yin komai sai abin da ya nufe su da shi. Mika wuya ga Allah da bada gaskiya da hukuncinSa, da yin nazarin falala da kuma hikima a cikin al’amarin halittu, wajibi ne kamar yadda Alkur’ani ya bayyana. Haka nan kuma, babu batun bakin ciki, da kunci ko debe kauna a tafarki na koyarwar Alkur’ani. Tashin hankali da wahalhalu su kan kasance wata rahama ce ta fuskar samun lada a ranar lahira, kuma nuna juriya a halin wadannan wahalhalu alama ce ta karfin imani. Ya zo a cikin Alkur’ani cewa za a jarrabi masu imani da tsananin al’amura a rayuwa, saboda haka wahalhalun da mutum ya sami kansa ciki gaskatawar abin da ayoyin Kur’ani suka nuna ne. Burace buracen duniya makiya ne da ke halakar da mutum. Don haka yakar son zuciya saboda imani da fifita son Allah akan komai yana samar da babban matsayi a gurin Allah. Shaidan ya yi alkawarin batar da mutum, don haka yake yin amfani da alatun duniya don ya shagaltar da masu imani. Sai dai kuma Allah ya tsare musulmi daga fadawa tarkon rudinsa. Bala’i da wahalhalu da ke samun muminai a rayuwar wannan duniya su kan kasance wata dama ce gare su don jaddada soyayyarsu da kuma mika wuya ga Ubangiji..Yardar Allah ta fi kowace iri baiwa ko ni’ima da mutum zai samu a wannan duniya, yayin da kuma Allah zai tabbatarwa da masu imani rayuwar farin ciki da nutsuwa wadda ta zarce duk wata ni’imar duniya da za su samu. Koda mutum ya kasance mafi farin jini a duniya kuma koda ya mallaki komai na rayuwa irin wanda ransa yake so, duk da haka zai iya kasancewa ya rasa kwanciyar hankali da jin dadi idan – Allah ya kiyaye – Allah yana fushi da shi. Amma kuwa in ya rungumi rayuwa da dabi’a masu kyau wadanda ya san Allah ya yarda da su, sannan ya dage a kan imani da mika wuya ga Allah da kuma sallama al’amuransa gareshi a cikin kowane irin yanayin rayuwa da ya sami kansa a ciki na kunci ko wahala, to wannan zai more rayuwar farin ciki da aminci da bai taba samun irinta ba a rayuwarsa, koda kuwa sauran mutane suna kin sa. Kuma a kan gane mutumin da ke cikin irin wannan rayuwa ta zahirinsa da kuma yanayin tunaninsa. Muhimmai daga cikin wadannan alamomin da a kan gane shi sun hada da: A kan ga alamun farin ciki da hasken imani a fuskarsa. A kan ga yanayin farin ciki, tunani da kuma babi’arsa ba sa canjawa a cikin halin ni’ima ko kunci. Ba a ganin alamun kasawa a magana da dabi’unsa. Ba ya furta kalaman da suka sabawa koyarwar Alkur’ani, ko nuna halayyar rashin imani da yin tawaye ga Allah mahalicci. Haka kuma ba a jin lafazan debe kauna da gushewar tunani wadanda suka sabawa Kur’ani, a cikin kalamansa. A kullum halayyarsa ta da’a ce ga Allah Ubangiji, kuma kyawawan dabi’unsa koda yaushe su kan nuna tsantsar imani da mika wuyansa ga Allah, kamar yadda ya ke da imani a kan cewa akwai amfani da manufa a cikin halittar kowane abu, da kuma cewa mutane da gabadayan al’amura suna karkashin iko da kulawar Allah mahalicci mai taimakon muminai. Ya yi imani da cewa rayuwar wannan duniya takaitacciya ce (kamar cin kasuwa), inda kuma rayuwar lahira ita ce matabbata ga masu imani. Saboda haka ba ya damuwa ko ya yi bakin ciki saboda rashi ko hasarar wata ni’ima ko kayan alatun duniya. Sannan ya yi imanin cewa abin da ya rasa na ni’imar rayuwar duniya zai zame masa alheri ne a lahira. Sakamakon haka duk wani kunci ko masifa da ta same shi a nan, ni’ima ce gare shi a can. Duk irin tsananin hasara ko kunci da ya shiga, zuciyarsa tana cike da dangana da kyakkyawan fata na samun soyayyar Allah da kuma yardarsa, wanda samun wannan ya fi masa samun duk wata ni’imar duniya. Mutumin da ya san kowane abu da manufa a ka yi shi, kuma ya san cewa jarraba da kunci suna zuwa ne daga Allah, sannan ya fuskance su da imani da tawakkali zai kasance mai nuna soyayya ga sauran halittu. Tun da yake ba a raba mumini da adalci, tare da farin ciki da son daidaito, don haka ya kan kauda kai da yin afuwa ga wadanda suka cuce shi ko suka ci zarafinsa ta hanyar nuna kauna a gare su. Babu abin da ke kautar da shi daga kan koyarwar Alkur’ani, don haka fushi da kiyayyar mutane ba sa yin rinjaye a kansa. Ya san cewa kura kuran da mutane ke aikatawa haka Allah Ubangiji ya kaddaro musu don a nuna musu su gane gaskiya. Shi ya sa ba a ganin mummunan nufi a cikin mu’amalarsa da sauran mutane. A sabanin haka ma, saboda zurfin imanisa a koda yaushe ya kan nuna soyayya da tausayawa a dukkanin mu’amalolinsa da sauran mutane. Khalifa kai musulmine kuma ka yadda kaddara na cikin babin rayuwar kowa ne musulmi kasa a ranka Ummi Kaddararka ce”.
STORY CONTINUES BELOW

Jikinsa ya yi matukar sanyi duk sai ya muzanta ya dinga jin kamar Maman tasan muradinsa na shirya guduwa da Ummin a saɓule ya mike ya bar wajan yana sharar hawaye ta rakashi da duban tausayi.
***
Tunda Ummi taje makaranta hankalinta ya kasa kwanciya a haka Hindatu ta sameta suka zauna sakaro ta numfasa ta ce,
“Ummi ya kamata kisawa zuciyarki hakuri domin komai mukadarine. Kar wani ciwon ya kamaki a banza. Shifa aure ni a hangena sai an zaune ake fahimtar auran akai wani sai kiga an yi auran soyyayar amma an karke da zage-zage Allah ya tsare wani kuma……”
“Dakata Hindatu”.
Ummi ta faɗa da sauri tana shasshekar kuka.
“Shifa so daban yake Hindatu ki daina kwatanta rayuwata da Haidar”.
Nasani Ummyter na kuma gamsu domin wani mafalsafi na cewa idan ka jajirce, za ka iske zai yuwu ka yi babban abu guda d’aya. Amma da taimakon soyayya sai ka yi gaggan abubuwa masu d’umbin yawa. Tabbas soyyaya na haifar da kwanciyar hankali cikin rayuwar al ummah sai dai faɗin Rabi’atul Adawiyya R.A cewa.
“Lallai ni Soyayyata ga Allah ta hanani shagaltuwa ga kin shai’an. Kuma karki manta cewar shi ruhi tamkar iska yake :- idan ya yi karo da abu mai kamshi sai ya d’ebo kamshin ya kawo, idan kuwa ya yi karo da mushe sai ya d’ebo warin ya kawo. Yi kokari wajan yin karo da abu mafi kyau domin kyautatta rayuwarki. Yi dogon nazari wajan son abin da ya dace da rayuwarki nasani Khalifa ɗan uwana ne amma wallahi bana goyon bayan ki bijirewa mahaifanki saboda shi domin duk duniya wanda zai soki bayansu ne”.
Ummi ta yi shiru tare da kwanto da kanta kan kafaɗar Hindatu. Hindatu ta shafi fuskarta tana murmushi a haka Malami ya shigo duk suka mike don gaishe
Koda aka tashi makaranta har gida Hindatu ta raka Ummi tare da drivernsu daga bisani ta wuce gida abinta.
***
Harabar kayatacan club ɗin cike da matasa masu ji da kansu. Kowa ka duba da abin da yake yi wani sigari yake zuka wani ruwan shaiɗan yake korawa. Haidar na gefe ga kwalbar whisky kusa dashi an tsiyayyata cikin kofi ga kankara kanana nata linkaya a cikinta ƴya zuba mata ido fuskarsa na nuna yana cikin zuzzurfan tunani. Nan da nan gumi ya tsattsafo a saman goshinsa yasa hannu biyu ya talabe kumatunsa tare da limshe idanu. A haka Ahmad ya sameshi ya taɓo kafaɗarsa tare da furta,
“hi prince”.
“Mtss! Freindy kyaleni kawai, ina kewar Fadeela ta yi fushi da yawa ni kuma banda lokacin lallashinta”.
“Hmmm Haidar kenan kawai ka share zo muje ga Roosy ce na kwaɗayinka kawai ka faka”.
Wani mugun kallo ya watsa masa, tare da kankance idanunsa da suka yi jajjur dasu ya furzar da huci mai zafi.
“Sanin kanka ne Ahmad niba kwazami bane, an faɗa maka kowane rami nake shiga?”.
Dariya taso kwacewa Ahmad ganin yadda ya yi kicincin amma ya waske ya sake dubansa.
“Afuwan nawan”.
Da haka ya lallaɓashi ya sauka daga fushin amma barasar da be shaba kenan ya mike ya bar wajan cike da takaici.
***
Kwanci tashi tsakanin Ummi da Khalifa haka suka dinga jinyar zukatansu. Kowa ya kalesu yasan akwai abin da yake damunsu baya Ummi data fige ta lallace tun Ummu na shareta harta soma janta jikinta tana bata shawarwari. Bangaran Hajiyar Haidar tafi kowa tashin hankali da damuwa yadda taga Baffa ya dage kan maganar tana lura da yadda yake tursassawa Haidar soma zuwa hira wajan Ummi amma ya yi biris har zuwa lokacin yaki kataɓus kan hakan.
***
A hankali Ummi ta soma mancewa da Khalifa, saboda sun rage yin waya ko kiranta yayi saidai su gaisa ya kashe. Kwatsam ranar wata Laraba ya kirata yana sanar da ita zai koma karo karatu. Hankalin Ummi ya yi matukar tashi tabbas ya tabbata ta rasa Khalifa ranar haka ta yini sukuku da ita har zuwa lokacin tafiyarta islamiyya ta shirya ta yiwa Ummu salama ta wuce kai tsaye.
Cikin nutsuwa take tafiya harta gangaro bakin titi, tana shirin tsalakawa saboda yawaitar abin hawa ta jinkirta wata motace sumammiya ta yi parking a gabanta kirar kamfanin *ZAIDS* cikin hanzari ta kauce tare da jan tsaki amma ga mamakinta ita motar take bi hakan yasa ta tsaya cak tana karemata kallo bata yi aune ba glass ɗin motar ya buɗe baki ɗaya Fadeela ce gefanta kuma Nabila ce suna watso mata shu imin kallo amma ko haɓar zaninta saita ɗauke kai tare da tsalakawa ta nufi hannun da zai sadata da makaranta ko ajikinta.
Tafiya take tana sakar zuci a ranta, kwata-kwata yanzu Abbu baya sakarmata fuska ko wasa da dariyar da yake mata ya daina zuciyarta ta yi zafi data tuna duk dalilin Haidar komai yake wakana shi yana can yana sharholiyarsa babu abin da ya dameshi amma kasa ranta data tuna biyyayar mahaifa tafi komai saita yi hanzarin kauda tunanin daga zuciyarta. Daidai lokacin ta shige makaranta tana murmushi.
STORY CONTINUES BELOW

Tunda taje makaranta take waige-waige amma bataga Hindatu ba, hakan ya motsa ranta sossai har aka fita sallah suna shirin komawa sallah ne ta hango motar Khalifa ya ajiye Hindatu a cikin makaranta ta zuba masa ido tare da lumshesu tana buɗewa hawaye ya kwaranyo mata daga in da yake ya gama fuskantar yanayin da take ciki hakan ya taɓa zuciyarsa sossai cikin sauri ya yi wa Hindatu sallama ya wuce yana hangenta ta wuce aji da sauri. Hindatu ma bata wani jinkirtaba ta rufa mata baya, a durkushe ta sameta tana kuka karkashin benci kasa cewa komai ta yi sai ɗagota data yi kanta ya yi zafi sossai jijjiyoyin kan duk sun tashi ta dubeta.
“Ki daina kuka sisty”.
“Dole in yi kuka Hindu shikenan na rasa Khalifa?”.
A ran Hindatu ta ayyana, “kin rasashi kuwa Ummyter domin iyayye na gaba da komai”. A filli kuwa saita furta,
“aaa Ummi kidaina faɗar haka, kisawa ranki hakuri dan Yaya Khalifa ma ganinsa da kika yi yanzu barin garin zai yi karo karatu zai tafi shekaru uku”.
Cikin kaɗuwa take dubanta tana girgiza kai,
“Khalifa ya barni Hindatu shikenan shima ya yi fushi”.
“Koɗaya Ummi ba haka bane, Khalifa ya yi nisa dake ne saboda wani dalili amma ni baimun bayani ba ga wannan yace in baki”.
Ta karasa furucin tana mika mata wata leda nannɗe da wani abu mai sheki.
“Samin a jakata”.
Ta faɗa cikin dakakkiyar murya tare da mikewa tabar wajan, haka suka kasance da juna har aka tashi babu wani mai kwakkwarar walwala cikinsu. Lokacin da Ummi ta koma gida bata buɗe ledarba saida tazo kwanciya, ƴba komai ciki sai takarda da zoban azurfa mai kyan kira an masa ado da harafin A capital letter guda biyu ɗaya ya harɗe cikin ɗaya hankalinta ya tashi da jin kalaman Khalifa kalamnsa na karshe sunfi komai ɗaga mata hankali.
_”Ummyter ina sonki nabar mahaifata saboda ke, saboda in yi nisa dake in daina ganinki ko zan samu sassaucin kaunarki. Kibi mahaifanki kibi mijinki hakane kaɗai zai baki kwanciyar hankali kimin addu ar samun macen da zata maye gurbinki na miki alkawarin insha Allahu ɗiyata ta farko sunanta Aisha Ummyter_”.
_Yayanki Abubakar Mustapha Abubakar Khalifa._
Kuka yaci karfinta ta kifa kanta cikin matashin kai, tana tuna shuɗaɗɗiyar alakarsu. Ta jima daga bisani ta mike ta ɗauro alwala ta soma kaiwa ubangiji kukanta tana idarwa ta ɗaga hannuwanta sama tana kwararro addu’a.
_”Ya ubangiji kai kace mu rokeka zaka amsamana, gani gurfane a gabanka ina neman agajinka. Allah kabani karfin zuciyar da zan farantawa mahaifina bisa umarni akan sunnahr masoyinka Annabi Muhammad (S.A.W). Allah ga bawanka Khalifa ubangiji ka kareshi da kariyarka ka shiga lamarinsa a duk inda ya kasance kabashi sa a abisa karatunsa tare da ɗaukacin musulmi”._
Tana shafawa wayarta na yin kara ta ɗaga cike da nutsuwa shiru na tsayin mintuna sai shassheka r kuka ta daure tare da furta,
“Yaya Khalifa ka daina kuka, kukanka zai sanyayya guiwata abisa kudurin daka ɗorani akai na biyyayar mahaifa”.
“Ummyter me kike baki bacci ba? Damuwa ko Ummyter?”.
“A’a Yayanmu sallah na yi”.
Ajiyar zuciya ya saki tare da furta,
“Allah ya yi miki albarka ya baki miji mai tausayinki fiye dani”.
Cikin ranta ta ayyana”hmmm Yaya kai kaɗai nake so”.
Sun jima suna musayar maganganu daga bisani ya yi mata nasiha mai ratsa jiki suka yi sallama.
***
Khalifa suna gama waya da Ummi ya karya layin tare da share kwallar data zubo masa. A ransa yana yiwa Ummi fatan alkhairi.
Komai ya yi farko zai yi karshe, cikin ikon Allah su Ummi suka zana jareabawar NECO da WAEC sun ƴyi murna sossai haka ranar rabuwa sun sha kuka kowane ɗalibi na murnar kammala makarantarsa amma banda Ummi domin dai zaman gidane ya soma gundurarta sakammakon takurawar da Haidar ya soma yi wa rayuwarta hakan ya tilasta mata son zaman garden tana duban tsintsaye suna ɗebe mata kewa amma ina nan ma bata tsira ba. Gashi kwata-kwata in ba islamiyya ba Abbu ya hanata fita. Hata da gidansu Hindatu saida kwakkwaran dalili take zuwa.
***
Zama tsakanin Ummu da Momy kuwa sai godiyar Allah. Duk da kasancesar kowa da muhalinsa amma takanas take shigowa taci mutuncinta ta fice, gashi Haidar ya tsiri zuwa cin abincin Ummu a cewarsa girkinta yafi masa daɗi da tsafta hakan ya rura wutar kiyyayar Ummu a zuciyar Momy ko sunanta ta tsani a kira bale taganta Abbu da Baffa kuwa kansu ya haɗe komai zasuyi tare da shawarar juna suke yi. Hakan ya ɗaga hankalin Momy sossai ɓangaran Ummu kuwa daɗin haka take ji na cikar burin Inna da Malam amma kash *CIKAR BURI BAYAN RAI*.
***
Kasancewar bikin Hindatu ya matso, kwata kwata Ummi bata da nutsuwar kanta saboda hada-hada. Takanas har gida Hindatu tazo ta nemi alfarmar Abbu kan ya aramusu Ummi saboda hidimar bikin. Komai za ayi tare da ita ake yi, duk abin da suke idanuwan Haidar nakai yana kula da ita kawai jira yake ta afka tarkonsa.
Tunda ya kasance saura sati ɗaya biki aka soma yi musu gyaran jiki, harya rage ana gobe kamu a ranar ne da yamma suka je gyaran gashi. Sunyi kyau tubarkallah Ummi hartafi amaryar kyau saidai wannan kamala ta aure ita ta bambantasu don mace komai muninta aka ce amarya ce saita fita daban da yan matan amarya. Ranar kamu suka yi kamu da lakca a harabar gidansu Hindatu. Bayan taro ya watse kowa ya kama gabansa. Masu haramar kwana na yi Ummi duk tabi ta takure saboda bata iya sakewa a gidansu Hindatu tun batunta da Haidar. Mommy kuwa janta take a jiki sossai tamkar da. Misalin karfe takwas na dare suna zaune Hindatu ta dubeta tana murmushi.
“Gaskiya Ummyter baki kyautaminba, bikina guda baki gayyaci Yallaɓai ɗinki ba. Haka ake rayuwa?”.
“Wasa kike Hinduwa in rasa wazan gayyata sai kuma Haidar? A wana dangin zai zo? Keni damuwata in ga Yaya Khalifa ance yazo amma koda wasa banga mai kama dashi ba”.
“Yimin shiru Ummi ya kamata kiyi karatun ta nutsu, yazo mana tunda harshi bai nemeki ba kija ajinki mana. Yausha raban daya kiraki? Yausha raban daya miki message kisan abin da yake gabanki malama. Daya damu dake yana shigowa kezai nema bayan danginsa, bana san sakarci”.
Zuciyarta tayi dum kwarai ta ɗauki ɗumi da kalaman Hindatu. Muryarta ta yi mugun yin kasa ta dubeta.
“Amma kinsan banasan Haidar ko!?”.
“Nasani amma koba komai yaci darajar yan uwantaka ke ni na rasa KIYYAYA CE KO SON ZUCIYA kukewa juna wallahi? Koba bu soyyaya tsakaninku ai akwai dangantakar jini”.
“Hindatu ki fahimce ni dagani har Haidar bama ra ayin juna, haka mahaifiyarsa kaf danginmu ni kaɗai ta ɗorama tsana. A tunanin babu cancantar in shigema lamuran Haidar”.
“Nasani Ummi da ciwo kabada kulawa in da ba a damu da lamuranka ba amma fa……”.
“Ya isa Hindatu na miki alkawarin gayyatarsa is ok”.
Mamaki ya kasheta ganin yadda ta yi kicin-kicin tilas ta ajiye batun gefe suka koma tattauna yadda lamarin dinner zai kasance. Karfe takwas da rabi Abdul jikan gidansu Hindatu ya shigo da ɗan gudunsa ya faɗawa Ummi jikinta. Ta ɗagoshi tana murmushi tana son yaran saboda duk yafi kama da Khalifa ta shafa kansa.
“Ya dai yarona,?”.
Hindatu ta yi gwalai tana kallonta,
“Aunty kizo an zo ɗaukarki in ji wani ɗan gayu”.
Duk sukasa dariya ta mike ba tare data bawa batunsa muhimmanci ba suka wuce ta yi wa Mama salama. A dai-dai corridor ɗin ɗakin idonta ya sauka kan Khalifa sunkuye gaban wata matashiya wata zata yi tsararta fara tas da ita. Ya takarkare sai zuba lallashi yake, ita kuma tana ɓotsarewa gabanta ya faɗi ta dubi Hindatu ita kuma ta gyaɗa mata kai alamun gargaɗi, saita aro mazantaka ta dake. Suna karasawa wajan suka risina suka gaisheshi duk saiya diririce hakan ya bata haushi ta dinga ganin bekensa basu tsayaba suka nufi hanyar waje. A ranta ta dinga tuna diramar da suka yi da Bahijja ɗazu shiyasa duk inda ta yi saita ga tana hancininta wannan shi ne harara a duhu. Ashe budurwar Khalifa ce? Shi kansa bayan tafiyarsu kasa cigaba da abin da yake yake yi domin kwata kwata Ummi ta haukatashi tsakin da Bahijja taja ne yaja hankalinsa ya dawo da nutsuwarsa kafin ya yi wani yunkuri tabar wajan.
STORY CONTINUES BELOW

Bahijja ya ce ga yayar Mommynsu Khalifa, Bahijja ta daɗe da kammala karatunta na digiri fakin kasuwanci. Tana matukar son Khalifa amma kwata kwata bata gabansa. Lokacin data samu labarin lallacewar auransa da Ummi kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, amma kash saita samu labarin barin garin da ya yi hakan ya ɗaga mata hankali sossai. Duk tabi ta rame ko aiki bata zuwa cikin ikon Allah ta samu numbarsa ta soma da yi masa message duk friday. Tun baya kulawa harya soma reply tafi tafi suka soma soyayya a hankali tana ɗebe masa kewar Ummi sai gashi tsulum cikin kulawa da lamarinta amma babu batun soyayya domin zuciyarsa naga Umminsa. Takurar da Khalifa yake samu daga yan matan turawa yasa ya soma sha awar auro Bahijja a wannan zuwan da ya yi ya tafi da ita saboda gudun faɗawa tarkon shaiɗan. Tunda ya soma batun zuwa Bahijja ke tunanin haɗuwarsu da Ummi shima tunaninsa kenan shiyasa tun da yazo yake kaucewa haɗusarsu.Yanzu haka batun suke tattaunawa Ummi ta riskesu…..cikin sanyin jiki Khalifa ya mike ya so rufa musu baya amma saiya tsinci muryar Bahijja a bayansa.
“Shiyasa kwata kwata banso zuwanka ba walahi, saboda nasan har yanzu zuciyarka gareta take”.
Tausayinta ya kamashi ya juyo tare da kafeta da ball eyes ɗinsa ya tausassa murya. Cikin mintuna goma ya lallasheta suka koma tattauna yadda zasu fuskancin mahaifansu da batun auransu. Ranta wasai ganin bai kuma koda kama sunan Ummi ba.
***
A harabar gidan Hindatu ta daɗe tana ba wa Ummi hakuri tare da nuna mata ta saki jiki taja Haidar jikinta. Ummi kawai jinta take rabin hankalinta ya tafi kan tunanin Khalifa a haka suka karasa gaban motar hakan ya yi daidai da zugewar glass ɗin motar ras ras ras gabansu ya faɗi sakammakon ganin mazaunin motar…..
Cikin kaɗuwa ta kali motar ranta na ayyana “meya kawo Haidar wajanta?”. Sossai fuskarta kwar cike da damuwa suka karasa suka gaisheshi ya amsa ba yabo ba fallasa. Wayarta ta yi kara ta ɗauka saita riski muryar Ummu tana yi mata bayanin ta yiwa Haidar kwatancan gidansu Hindatu yazo ɗaukarta ta aiki driver ne. A sanyaye ta amsa tare da katse kiran tana jinsu suna fira da Hindatu tana faɗa masa ya daure yazo dinner gobe cikin mutuntawa ya amsa mata da zaizo. Mamaki fal zuciyoyinsu ƴhaka Hindatu ta buɗe mata gaban mota ta shiga tsamo tsamo da ita. Daidai kunnanata ta sunkuya ta yi mata raɗa,
“kisaki jiki malama kija ra ayin handsome guy kina fa yawa”.
Hankaɗeta ta yi tana cuno baki, suka yi dariya gaba ɗaya harshi ta saci kallonsa saiya birgeta ashe yana dariya? Ta tambayi kanta. Hannu yasa ya zaro rafar kuɗi yan ɗari biyar ya bikawa Hindatu,
“amarya ayi hakuri lamarin yazomin a kurace ga wannan kiɗan yi maneji”.
Dakyar ta karɓa tare da yi masa godiya yaja motar suka wuce. Khalifa yana hangosu zuciyarsa fall kunci nan da nan yaji zazzaɓi na neman rufeshi ya ɗauki motarsa ya bar wajan
***
Tafiya suke tamkar kurame, takaicin Ummi sai biye biyen gidan abokai yake suda suka fito tun takwas da rabi gasu har tara da rabi. Gashi wayarta babu caji tana son kiran Ummu ba dama. Haidar kuwa ransa kal ganin yadda ta ɗauki ɗumi domin ya samu hanyar kuntatta mata a wannan bikin amma kuma wani fanin yanajin kudurinsa bai kyautawa Hindatu ba.
Suna dosar gate ɗin gida gabanta ya faɗi, Haidar kuwa dadi yaji badan komai ba sai dan ganin Abbu a tsaye yana kai komo cikin harabar gidan.
“Ya kika karaya da wuri haka mara kunya?”.
Idonta ya yi rau ta ɗauke kai, tare da buɗe motar ta fice ta murmushi ta karasa.
“Abbu sannu da gida….”.
Kallon da ya yi mata yasa miyan bakinta kafewa ta sunkuyar da kai kasa daidai lokacin Haidar ya karaso ya risina yana gaisheshi ya amsa ciki ciki.
“Daga ina kuke da wannan daran?”.
Suka yi shiru ya daka musu tsawa, Haidar ne ya yi gyaran murya ya furta.
“Abbu kayi hakuri biki taje gidansu Hindatu kuma ance kasan da bikin”.
“Eh nasan dashi dalilin daɗewar nake tambaya”.
Suka yi tsuru-tsuru Haidar murna yake ya samu sararin rama abin da ta yi masa saiya gyara murya.
“Am Abbu dama dana je ɗaukarta ne na iske suna hira da Khalifa namata magana tazo mutafi taki ta soma yimin rashin kunya ni kuma na kyaleta suka kammala saboda Ummu ce tace in ɗaukota bazan iya barinta ba”.
Tashin hankali wanda ba a samasa rana, tuni Ummi ta soma lalluban a duniyar da take ta dubi Haidar karo na farko tun batun haɗasu aure suka yi kallon cikin ido gabansa ya faɗi. Tama manta gaban Abbu take bakinta ya suɓuce ta furta.
“Haidar kaji tsoron Allah wallahi”.
Bata rufe baki ba Abbu ya tsinka mata mari ta dafe wajan cikin kuka,
“ashe baki da kunya Ummyter? Yaushe kika zama haka? Fice ki bani waje cikin kaɗuwa ta shiga gida da gudu tana kuka. Ummu na zaune ta shigo tare da faɗawa jikinta tana kuka mai cin rai tambayarta take amma ta kasa magana. Bata yi aune ba sai saukar duka a bayanta Abbu ne yake dukkanta tako ina da bulallar Baba maigadi ihu take sossai Ummu ta kasa kwatarta. Ganin zai nakasa mata ya yasa ta bazama kiran Baffa amma kafin suzo Ummi ta sume Baffa ya ɗagota amma bata motsi Ummu ta girgizata tare da kiran sunanta a kiɗime.
“Ummmmmmmytah”.
STORY CONTINUES BELOW

Babu numfashi ko kaɗan cikin hanzari Baffa ya sureta suka nufi asibiti gaba ɗayansu. Nan da nan likitoci suka dukufa a kanta bata farfaɗoba saida ta share sa a ɗaya Ummuma ta sadakar ta mutu, nan Baffa ya dinga faɗa in da yake shiga ba nan yake fita ba a daran duka baro asibitin bayan an bata magungunan ciwan jiki. Haidar kansa jikinsa ya yi sanyi da ganin yanayinta ga wani kallon KIYYAYA daya fuskanci Ummi tana yi masa.
Washegari tun safe aka ɗaura auran Hindatu da Aminu Khalifa da Bahijja hankalin Hindatu ya yi mugun tashi tana gudun kar Ummi ta samu labari sai kuma taga shiru babu zuwanta nan ta sake shiga ruɗu ta kira wayarta a kashe dabara ta faɗo mata ta kira Ummu ta ƴhaɗasu a wayarta ai kuwa da kuka Ummi take mata bayanin abin da ya faru babban takaicinta rashin hallatar bikin Hindatu musamman yadda taci burin dinner. Cikin lallashi tace,
“Ummyter wallahi an soke dinner tunda baki da lafiya kuma dalilina hakan ƴya faru kiyafemun”.
Kafin Ummi ta yi wani yunkuri ta katse wayar ta bi wayar da kallo sarorro, aikuwa Hindatu ma ranta ya ɓaci take ta bugawa Aminu waya tace a soke dinner bazata yi ba. Bai ji daɗi ba amma yadda yake sonta bai musa ba uwa uba bayasan a kallesa mata. Alfarmarsa ta nema kan ya barta ta je taga jikin Ummin bai musa ba ta yi masa godiya ta wuce taja Mommy gefe ta yi mata bayanin komai. Mommyn kanta bataji daɗi ba, wasu yan mata taja guda huɗu tasa su yi wa Hindatu rakiya karaf a kunnan Bahijja ta tubure saida ta bisu.
Lokacin da suka karasa gidan a haraba suka yi kiciɓus da Haidar da Ahmad. Yan matan suka gaishesu kowace na rawar jikin ya taya amma Hindatu kallo bai ishetaba tasa kai cikin gidan kai tsaye ɗakin Ummi ta faɗa suka rufa mata baya. Jikin Bahijja yayi sanyi ganin cewar Ummi ba mutsiciya bace kamar yadda ta zata. Ummu na kokarin bata magani suka zauna suna gaisheta Ummu ta ɓata rai,
“Hindatu da izinin wa kika fito? Bayan an ɗaura miki aure koba a ɗauraba?”.
Mai kanzagin cikinsu ta yi caraf tace,
“an ɗaura harma da Yaya Khalifa ga matarsa”.
Ta karasa batun tana nuna Bahijja.
Gaban Ummi ya faɗi suka yi kallon kallo da Bahijja ganin Ummu ta ramfota yasa ta saisaita kanta ta maida hankalinta kan Hindatu.
“Tambayarki ake madam”.
Cikin jin nauyi tace,
“Ummu shiya bari na tambayeshi”.
Murmushi ta yi ta mike tare da dabarar janye su Bahijja zuwa falo tabarsu su biyu suna fita hawayan idon Ummi ya kwance.
“Sisty Khalifa ya yi aure ko?”.
Kasa bata amsa ta yi sun jima a haka ta yi kokarin rike hannunta.
“Ummi kifida Khalifa a ranki don Allah”.
“Khalifa fitarsa a raina sai a hankali sisty, shinafara so karkiga laifina shiya koyamun ya zan soshi amma kaddara ta riga fata insha Allah daga yau zan haramtawa zuciyata dubansa a masoyi sai dai ɗan uwa ubangiji ya basu zaman lafiya”.
“Amin sisty”.
Sun jima suna tattaunawa daga bisani ta matsa suka ci abinci tare tasha magani suka fito falo tayi mamakin yadda Bahijja ta sake sukaita hira da Ummu da zasu tafi Ummu ta sake haɗa Hindatu da Bahijja ta na dubansu ta ce,
“Nidai nasihata gareku ku bi mazajanku musamman ke Bahijja da zakiyi nisa da gari.
Miji komai lalacewar,komai talaucinsa,ko mai mugun halinsa sunansa mijinki indai.da igiyar auransa a kanki In har kina matsayin matarsa to kuwa da hakokinsa a kanki da dole sai kin sauke su, babu ruwan Allah da shi wane irin hali ne da shi me kyau ko mara kyau, in yana miki abinda bai dace ba wannan shi da Allah, amma ke fa dolen ki ki bishi kiyi masa biyayya a abinda bai sabawa Allah ba.
Kar ki yi gangancin cin zarafin mijinki ko yi masa maganganu marasa daɗi dan wai shima yana yi miki, shi da yayi miki shi da Allah, ke kuma ladan hakurinkinna wurin Allah (me neman aljanna ina ruwansa da wani). Ki cire a ranki cewa wai mutum kike wa biyayya,kisa a ranki Allah daya halicce ki shi kike yi wa, dan Allah ne yace kiyi aure kuma kibi mijinki shi ne hanyar aljannarki. Da yawa mata na kuskure wai suce su zasu katarwa kansu yanci da cin zarafin miji, da bijere masa da kin yi masa biyayya, to kin samu ‘yanci kin rasa aljanna me kika yi kenan?. Amsarki ita ce shirme domin babu wani yanci tunda a kasansa kike kuma dole kibishi kamar yadda addinni ya ƙkoyar. Duk yancinki da kike takama dashi da wani asali ko dukiya baki kama kafar Nana Faɗima ba. Haka kyau amma ta yi biyyayar aure abar koyi da kwatance a gidan auranta.
Ko kuma kiga mace tana cewa miji wai me ka ta ɓai mun? To wallahi Manzan Allah yace,
“irin wannan matan ba zasu ji kanshin aljanna ba ma, haka kuma wasu matan musamman na wannan zamanin abu kaɗan sai mace tace miji ya saketa to ku kiyayi kanku wajan aikata hakan haram ne mace ta ce,
“miji ya sake ta ba tare da wani dalili mai karfi ba”.
Babu wani dalili ko hujja da Allah zai karɓa daga wurinki duk randa kika tsaya a gabansa da laifin cin mutuncin miji, rashin biyayya da cin amanarsa da kuma wulakanta shi. Miji yana da girman da sai da Manzan Allah s.a.w ya ce,
“da za’a umarci wani ya yi wa wani sujjada to da an umarci mace da ta yi wa mijinta”.
Ku kalli fa sujjadar da Allah kaɗai ake yiwa amma ace wai da za’a yi wa ni, ba’ace Annabi ba, ba’a ce iyayenki ba ba’a ce malaminki ba sai aka ce miji, kinga kuwa lallai ana so a nuna miki ne bayan Allah da Manzonsa babu wanda ya chanchanci biyayya irin mijinki. Mijinki yafi iyayenki, haka addinin musulunci yace, amma da an faɗa nasan zaka ga wasu suna kunfar baki to ba haka mata masu ilimi suke ba. Daga randa aka yi miki aure iyayenki basu da wani kataɓus akanki sai abin da miji yace, girman da musulunci ya bawa miji ba kadan bane. Kubi mazajanku! Kubi mazajanku!! Kubi mazajanku!!!”.
STORY CONTINUES BELOW

Jikinsu ya yi sanyi gaba ɗaya, suka yi mata sallama suka wuce gida. A hanya Hindatu tanata jinjina nasihar Ummu cikin ranta saɓanin Bahijja da take ɗaukar kawai Ummu nasan bautar dasu ne tamkar wasu gidaddawa
Da suka koma gida Hindatu ta yi wa Mommy bayanin nasihar da Ummu ta yi musu sossai ta kirata tana yi mata godiya da yammaci aka ɗauki amarya zuwa gidanta dake janbulo Bahijja kuwa nan zata zauna sai Khalifa zai tafi ya tafi da ita.
***
Bayan kwana uku cikin ikon Allah Ummi ta samu sauki sossai, amma har lokacin Abbu fushi yake da ita saida taje da kukanta ta bashi hakuri ya yafe mata. Jarrabawarsu ta fito hakan yasa Baffa ya soma cuku cukun sama musu addimition amma Abbu ya dakatar dashi ya ce ya bari in sunje gidajansu mazajansu sun amince sayi karatun. Hakan ya konawa Ummi rai don Hindatu harta soma zuwa makaranta.
Kasancewar cikin wata Nuvember ne har ya yi nisa su Abbu suka tsaida bikinsu karshan December. Hakan yasa kowane ɓangare suka soma shiri gadan-gadan Ummi kuwa kalansu kawai take tana ganin bekensu yayin da Mommy ta tayar da kaya baya tijarar safe daban ta dare daban.
Tunda ya rage saura sati uku bikin Ummu ta hana Ummi aikin komai. Sai cin kayan itattuwa tare da motsa jiki. Sai kuma gyaran jiki da take mata da kanta gashinta kuwa wani irin haɗin mayuka take bata tana sawa ya kara tsayi da santsi sossai.
***
Bangaran Hajiya Sadiya abun ba a cewa komai. Kwata kwata bata da nutsuwa daga ita har Fadila da mahaifiyarta sun rasa yadda zasu ɓulowa al amarin gashi Baffa ko sauraranta baya yi. Hata lefe yace baya san gutsuri tsoma da kakanun maganganu in amarya taje gidanta taga kayanta hakan yayi musu ciwo sossai. Sun so ya bada damar kai lefan kodan suyi tijara son ransu Haidar kuwa babu abin da ya dameshi harkarsa yake in ba mahaifiyarsa ko Fadila suka yi masa maganar ba koda wasa baya tayar da batun har Ahmad ya fishi hoɓasa kan al amarin.
***
Bangaran Baffa katon gida ya ginawa Haidar mai part biyu a unguwar jan bulo. Hakan yafi yi wa Ummi komai daɗi gata ga Hindatu. Shirya-shiryan biki Hindatu ta tsara komai Ummi da Haidar kuwa ba wanda yaga wani cikinsu komai Ahmad yake jagoranta.
***
Rana bata karya inji yan magana, ranar alhamis suka yi kamu, an yi faɗarwa sossai daga bisani aka yi rabon akushi shake da kayan kwaliya. Misalin karfe takwas na dare aka fita dinner abun takaici Haidar dai bai halata ba yana can gidan Ahmad tare da Fadila yana aikin lallashi. A cewarsa hakan da ya yi kaɗaine zai nuna mata yana sonta kuma auren Ummi da ya yi baya nufin yana sonta. Sossai taji daɗin abin da ya yi ta kuma yadda ita ɗin daban ce wajan Haidar. Ummi taji takaicin rashin zuwan Haidar koba komai an tozartata matuka sai dai abin da ya ɗaure mata kai ganin babu wanda ya damu da ƴhakan. Haka aka gama dinner aka tashi. Washegari ɗarurruwan mutane suka shaida ɗaurin auran Aisha Muhammad Aliyu Matazu tare da angonta Aliyu Mukthar Aliyu Matazu. Ummu ta yi kuka ta yi kuka mai cin rai Ummunta ta yi mata nasiha sossai daga bisani Hajiya Sarrinah kawar Ummu mutuniyar Damaturu ta kamo hannunta zuwa sashin Hajiya Sadiya duk da basu sami wata tarba ta mutunci ba daga nan aka sada amarya da gidanta dake jan bulo block three Hindatu na block two.
Gidane daya amsa sunansa gida Baffa ya yi rawar gani, an tsara gidan yadda ya kamata yana ɗauke da katuwar haraba mai girma wadda aka kawatata da abbaban more rayuwa shukokine birjik masu kayatarwa suka zagayeta. Daka shigo ɗakin maigadine a farko, sai ɗakin mai wanki tare da mai kula da shukokin harabar gidan. Gefe guda daga hagu motocine guda shida rufe cikin tamfal. Daya ta aike ce zuwa kasuwa irin doguwar motar nan school bus. Sai guda uku kirar motocin zamani kamfanin ZAIDS fara da ash da kuma baka wanda suka kasance mallakin Haidar ne sai biyu kyautar da Baffa ya yi wa Ummi ce. A gefan dama kuma rumfa ce guda biyu manya ɗaya an yi karamar buka buɗaɗɗiya cikinta an zagayeta an kawatata da shukoki kanana sai tsuntsaye dangin kanari masu kukan dake saka nishaɗi ɗayar kuwa rata yayun kujerune masu shila mutum cikinta. Sai sai siririyar hanya da idan aka bi zata sada mutum da lambun gidan wanda ya kawatu da shukoki masu kayatarwa dangin umbrella, mangwaro da goba da sauransu a cikin wajan daga hagu akwai wajan motsa jiki da wakan wasan yara. Babbar kofar da zata sadaka da cikin gidan kana shiga akai karama wadda in ka bita zata sadaka da wani corridor kana gaba kaɗan sai kitchen mai kayatarwa wanda cikinsa akwai store sai falon Ummi kato mai ɗauke da ɗakuna uku da bandaki ɗaya cikin kowane ɗaki akwai banɗaki. Yadda part ɗin Ummi yake a bayanta akwai wani irin sa sai dai a rufe yake. Yan kawo amarya sai santin gidan Ummi suke, haka kowa ya watse sai Hindatu da Hajiya Mas udah suka sake gyara mata gidan suma suka wuce gidajansu a motarsu.
STORY CONTINUES BELOW

Gidan shiru babu motsin kowa sai kukan tsuntsaye da kaɗawar ganyayyaki hakan yasa ta soma jin sanyi. Mikewa ta yi ta rage kayan jikinta tare da ɗauro alwala ta shimfiɗa darduma ta tayar da sallah. Raka a biyu tayi tare da ɗaga hannuwanta sama tana addu a idonta taf hawaye.
_”Alhamdullilah Allah na gode maka da ka bani ikon cika umarnin masoyinka bisa biyyayar mahaifana. Allah na rokeka kabani kwanciyar ƴhankali da farin ciki a wannan gidan don isarka. Allah ka shiryarmin da mijina bisa turbar addininka, ka sanya biyyayarka tare da tsayar da zuciyarsa abisa tsoronka. Allah ka kauda duk wata fitina da zata tunkaro rayuwar aurena, ubangiji ka kare kasata da Al ummata daga fitinttinun rayuwa”._
Tana shafawa ta sauke ajiyar zuciya tare da mikewa ta kudundune cikin bargo ta kwanta zuciyarta cike da tunanin raban data ga Haidar cikin idanunta.
***
Haidar na can suna sha aninsu gidan Ahmad sai shewa suke, kansa Ahmad daya ke ɗaurin kugun abun saida Haidar ya bashi mamaki ƴya dinga kallon wautarsa mutumin da aka kaima sabuwar amarya yana nan ya nannike wajan Fadila duk sai yaji haushinsa so yake kawai ya bar wajan ya janyeta su keɓe amma ya kasa ya tsare. Da kyar suka rabu da juna misalin karfe ɗayan dare. Lokacin daya dawo gidan ta daɗe da yin bacci baibi ta kanta ba kawai sashinsa ya nufa ya watsa ruwa ya mimmike kan katifa take bacci ya yi awan gaba dashi.
Kiran sallahr farko ya tashi Ummi ta mike tayo alwala tare da bin jam i tayi sallah. Tana idarwa ta sake kowama bacci. Washegari karfe takwas ta farka tana buɗe ido haske ya yi mata sallama ta limshe ido tana furta,
“Alhamdullilazi ahayana badama amatana wa illaihinnushur”.
A hankali ta karewa ɗakin kallo tas baya bukatar gyara dan haka banɗaki ta faɗa ta yo wanka tare ta fitowa ta shirya cikin doguwar riga kirar dubai ja mai duwatsu farare ta yane kanta da mayafin rigar tana shirin fita falone wayarta ta yi kara ta ɗauka tare da sakin murmushi.
“Hinduwa ɗiyar Mama”.
Ta faɗa da sigar tsokana,
“ke dilla kyaleni na aiko driver da abinci tare da Basmah kanwar Aminu ki buɗe ki karɓa”.
“Hmmm! Sanunki da kokari tawan”.
Dariya tayi suka yi sallama ta karasa ta buɗe kofar, suka sakarwa juna murmushi ita da yarinyar da bata gaza shekaru sha biyu ba. Tare suka karaso suka jera kayan a daining ta yi ta yi ta tsaya amma Basmah taki cewarta Aunty ta hanata tsayawa godiya ta yi mata ta rakata bakin kofar falon ta dawo.
Zama tayi ta tsattsakuri abincin ta mike ta kunna tv tana kallon zee aflam tayi sa a sun saka film ɗin da take naci kabibush kabi gam. Ta sakankance tana kallon wani sirnanin kamshi ya ratsa kofofun hancinta ta lumshe ido tana son tuno ina tasan kamshin amma hakan ya gaggara bata gama farfaɗowa daga suman da ta yi ba ta jiyo sautin muryarsa yana amsa waya,
“kai dilla Ahmad me zan kwasa a nan kayan takaci?”.
Ya yi dariya, taka satar kallonsa can kuma ya haɗe gira kaɗan tare da tsare gida.
“Ya isa Ahmad gani nan zuwa”.
Yana katse kiran yasa kai ya fice ko in da take bai duba ba ta rakashi da kallo cikin cikarsa ta kayan likitoci. Yana fita taja tsaki abinta ta cigaba da kallo. Shuɗewar mintuna ashirin ya sake dawowa ya wuce a lokacin ya ɗan tsaya yana dubanta kome ya tuna kuma? Sai ya dalla mata harara ya yi gaba abinsa.
Karfe goma sha biyu motocin gidan Baffa suka yi parking a harabar gidan. Nan yan biki suka soma shugowa ciki hada Nabila da fara arta ta taresu ta shiga kitchen ta kawo musu lemo da ruwa. Nabila sai rawar kai take tana sakin habaice habaice ko in da take Ummi bata kala ba. Karfe ɗaya Fadila ta shigo gidan tana yatsina suka saki shewa ita da Nabila ta yiwa Ummi kallon up and down ta ɗauke kai tare da maida hankalinta kan kofa ta mike tana murmushi ganin Hajiya Sarrinah tare da wata Dattijuwa da matashiyar yarinya da bata gaza shekara takwas ba. Cikin mutuntawa ta gaisheta ta amsa tana shafa kanta suka zauna ta kawo musu kayan buɗa baki a nan ta yi mata bayanin mai aikice aka kawo mata Dattijuwar da jikarta. Ummi ta yi jim tsarinta bata son mai aiki amma girman gidanta koba komai sa ɗebe mata kewa dan ƴhaka fuskata ta washe da fara a ta yi mata godiya tare da tambayar sunanta. Mintuna goma ta mike ta bar mata ɗiyarta Sabahnatu don ta tayata hira. Bayan fitarta ne Ummi ta mike tare da Sabah suka shiga kichen suka zuzzubawa baki abincin da Ummu ta aiko dashi. Karfe biyu kowa ya yi haramar komawa gida banda su Nabila Ummi ta cikasu da kayan gara dana shafa suka tafi sunata godiya. Gida ya rage daga ita sai Iya mai aiki da Habiba ɗiyarta da kuma Sabah dasu Nabila. Sabah ce ta taimaka mata suka kintsa gidan daga nan suka zazzagashi anan suka gano boys quaters suka raka Iya can ya zama mazauninta.
STORY CONTINUES BELOW

Ta yi mata bayanin aikin da zata dinga yi mata shara da gyaran falo da gogge kichen Habiba kuwa ta dinga wanke-wanke tana binta kitchen dan kama wasu aiyukan. Karfe biyar Nabila da Sabah suka bar gidan suma bata barsu haka ba Ummi akwai kyauta. Har magarba Fadila na gidan kan Ummi ya ɗaure da lamarin sossai suna zaune aka kawo wuta daidai lokacin Haidar ya buɗe kofar ɗakinsa. Fuskarsa ta faɗaɗa da fara a ganinta, suka nufi juna suna masu nuna tsantsar farin ciki kan fuskokinsu. Ummi tayi sororo tana dubansu takaici ya kumeta koda bata san Haidar bazata juri wannan kazantarba. Dabara ta faɗo mata ta shiga kichen basu yi aune ba sun shagala rungume da juna ta sheka musu ruwan sanyi sumame.
A zarane suka ɗago kai ta kafe shi da manyan idanunta masu zaiba-zaiba kwayar baka siɗik babu alamun tsoro tare da ita. Cikin muryar jarumta ya furt,
“Ke! Bagidajiyyar ina ce? Dama baki da hankali?”.
“Bagidajiyar gidan Dr Aliyu ce, hankali kuma naka nake biɗa ka bani aro sarkin masu nutsuwa”.
Mamaki ya kasheshi ya tsirawa ɗan karamin bakinta ido das dashi samansa akwai shape ya fita fit ya cije leɓe. Maida hankalinsa ya yi gurin Fadila yana aikin lallashi ita kuwa takaici ya hanata magana. Juyawa ya yi zuwa ɗakinsa tana ganin hakan ta faɗa kichen ta rasa abin da zata ɗauka idonta ya sauka kan robar yaji tasa hannu ta ɗauko ta saki murmushin mugunta. Buɗewa ta yi ta zuba cokali biyu ta zuba ruwa a ciki ta ɗauka ta fito lokacin data karaso harya bawa Fadila wasu riga da skert ta saka english wears ne. Suna ganinta suka kwashe da dariya,
“Bagidajiya”.
Kalmar ta yi mata ciwo saita yi murmushi ta rankwafo daidai fuskar Fadila tana murmushi ta furta.
“Akwai irin mutanan da basu dace da rayuwa ba”.
“Me kike nufi matsiyaciya?”.
Bata bada amsa ba saboda buɗewa da kofar falon ta yi Ahmad ya shigo yana murmshin ya zauna kusa da ƳHaidar suka yi dariya ganin hakan sai jikin Ummi ya yi sanyi ta yi niyyar barin ɗakin. Cikin shammata Fadila ta riko hannunta,
“ina zaki Bagidajiya?”.
Ahmad ya dubesu yaga wana mataki Haidar zai ɗauka don dama bai gama fita daga mamakin ganinta gidan a lokacin ba ya kuma samu kalamanta cikin kunnansa sai yaga rashin dacewar abin da suka aikata yana shirin magana ya tsinkayi muryar Fadila tana kururuwar idonta. Sai lokacin Haidar ya ɗago yana huci an taɓa gimbiyarsa, tuni Ummi takai kofar ɗakinta ta kira sunansa tana dariya.
“Haidar!”.
Bai amsaba saboda ya rikice da ihun Fadila,
“uban me kika yi mata Ummi?”.
“Hahaha! Yaji na watsa mata a ido idan yaso idon da take hararata ya tsiyaye, ka faɗa mata karta kuma shigo min gida daga ita har wannan mugun abokin naka”.
Cikin zare ido Ahmad ya ce,
“ni ne mugun?”.
“Kaine Ahmad ka wani shigowa mutane gida sakaka kamar gidanku baka dace da rayuwar AHALINA ba kai mugun abokine wanda ke shagaltar da aboki musamman ma a irin guraben da ba wanda zai yiwa wani fad’a”.
Cikin takaici Haidar ya yi kanta zai daketa Ahmad ya dakatar dashi saboda suji da Fadila ta sheke da dariya ta cigaba.
“irinku ne mugaye Ahmad masu huɗubar tsiya saboda kuna takamar matsayinku na aminai wannan yakan baku dama ku yi abun da suke so na aikata sharholiya da duk wasu abubuwa na muradan zuciya wanda ya sa6a da addini, hankali da kuma al’ada ba tare da nazartuwa da cewa Allahn da yake ganinku a gaban mafad’a shi ne a nan inda ba mafad’an dama a ko ina ba. Kudin annobane ko da mutum ya ginu a kan kyakkyawar tarbiyya , abota da irinku miyagun mutane za ta iya yin tasiri a kansa matuka ta gur6ata masa kyawawan halayensa su zama ba-kama”.
Bam! Ta rufo ɗakinta ta shige ta barsu anan, Ahmad takaucin duniya ya galabi zuciyarsa da kyar suka samu idanun Fadila ya buɗe nan ya lallaɓa ya haɗata da Ahmad ya maida ita gida. Ummi na shiga ɗaki ta sheke da dariya dan bakaramar kasada ta yi ba ta faɗi hakan kasan ranta.
Tsayin kwana goma ana wasan ɓuya tsakaninta da Haidar amma bai samu nasarar kamata ba. Duk ƴhanyar da tasan zasu ƴhaɗu tana kauce masa. Tana jin dadin aikin Iya da Habiba saboda suna tsafta sossai. Fadila kuwa tun daga ranar bata sake dawowa gidan ba iyakaci su haɗu da Haidar su sha sharholiyarsu. Hakama Ahmad babu abin da suka fasa wajan gudanar da mu amalarsu ta bayan fagge.
***
Bahijja tunda suka tattara suka bar Nigeria take farin ciki, saboda koba komai Khalifa ya yi nisa da Ummi kwatsam kuma bayan auransu da wata huɗu har tana da karamin ciki wata uku nan ta samu labarin auran Ummi ta hanyar Hindatu. Hakan yasa ta saki jiki lallai Khalifa ya zama nata ita kaɗai. Matsalar farko da suka fara fuskanta Bahijja muguwar kazamace gashi ta haɗu da laulayi mai matukar wahala. Khalifa mutum ne mai tsananin kyankyami nan da nan suka fara haurawa amma daya lura tana fama da laulayi hata karatun ajiyeshi yake ya kula da ita da gidan. Saboda yadda ya ɗora kalata a kan cikin burinsa kullum Allah ya bashi baby girl yasa mata Aisha Ummyter duk kudurinsa bai taɓa gigin furtawa Bahijja ba saboda duk yadda takai da fara a ya sake yayi wani batu kan Ummi to kuwa zasu haura bale taji wannan batu.
Haka Khalifa ya cigaba da kulawa da ita har cikinta ya shiga wata huɗu zuwa lokacin ta daina amaye-amayen amma sai Khalifa ya lura kazantar ba cikin ne kaɗai ya haifar da ita ba tun asali ɗabi arta ce nan fa suka soma dambarwa tsakaniksu ya zama sai hancinin juna da hattara. Bai kara shiga tashin hankaliba saida ya shiga ɗakin baccinsu wanda ya kaurace masa ya koma na saukar baki saboda tace bata son turaransa shi kuma baya iya hakura da kamshi. Duk tabi ta ɓata bangon da miyau har wani hamammi hamammi ɗakin yake kansa har wani juyawa yake ya fito yana kwala mata kira cikin kiɗima.
“Bahijja! Bahijja!! Bahijja!!!”. Tana jinsa taki amsawa a haka ya risketa a fallo ta yi kaca-kaca da shi tana shan ice cream. Turus ya tsaya yana karemata kallo cikin takaici.
“Bahijja wannan wane sabon salon wulakancine? Kina ji ina yi miki maga kika yimin banza?”.
Saida ta yi yatsina sannan ta kaleshi kallon uku ahu ta numfasa tare da rike kugu ta kaleshi.
“Gaskiya dai Khalifa baka da imani, ka manamin ciki ina fama sannan kazo kana yimin ihu aka kamar wata ɗiyarka?”.
Mamaki da takaici suka kashe Khalifa amma ya kane ya sassauta murya.
“Bahijja sanina dake yar gayu na sanki, amma dubarki cikin kazanta kaya daban-daban bama wannan ba Bahijja kinji yadda ɗakinki yake tsamin miyau haba My wife kamar bake ba”.
Wata dariya ta saki da tasa Khalifa tsayawa kyam yana kare mata kallo ta cigaba da kyakkyatawa sannan ta dubeshi galala.
“Khalifa amma wallahi kai mugune, dame kakeso inji? Kana kallo bacci gaggarata yake saboda cikinka amma wai kake tuhumata da rashin gyarama gidanka to ni wallahi bazan jura ba don haka saidai ka zaɓi ɗaya yar aiki dana bukata tun fari kaki ɗaukowa wai kai kyankyami gareka yanzu ɗaukarta ya zamema wajib ko kuma ka maidani kasata”.
Mamaki takaici suka yi masa rubdugu bai tanka ba ya bar mata ɗakin, zagewa ya yi ya gyara ko ina na gidan har ɗakin girki nan ya dinga karo da kwanikan busasshan abinci kayan miya kuwa wasu duk sun ruɓe haka ya gyare tsaf ya kuna turare. Sai kusan magarba ya gama tun la asar sannan ya dafa ruwa ya tasata gaba har banɗaki ya yi mata wanka ita kanta tsami take kanta kuwa uwar anakiyya ce dankare makare ya saɓeta tas yana mita tare da nuna mata illar abin da take yi amma jinsa kawai take yi shi ma wanka ya yi ya fito suka ci abinci yana ta janta da hira. Suna gamawa ya kwashe kayan ya kai kichen bai fito ba saida ya wanke ga mamakinsa bata falo yana shiga bedroom ya riski harta kwanta cikin ɗaure fuska ya dubeta,
“kin wanko bakinki”.
Turo baki ta yi tana gunguni, ta kular dashi amma ya kanne ta wuce ya rakata da idanu ta yo jika-jika ta dawo.
Hannu ya kai da niyyar janyota jikinsa ta daka tsale tana huci tamkar mesa,
“wallahi ba zaka taɓani ba fita kabarmin ɗaki”.
Ransa ya ɓacci baisan sanda ya kwaɗa mata mari ba ta dafe wajan tana dalaro harshe sai ya fice ya bar mata ɗakin.
Tsayin kwana goma ana wasan ɓuya tsakaninta da Haidar amma bai samu nasarar kamata ba. Duk ƴhanyar da tasan zasu ƴhaɗu tana kauce masa. Tana jin dadin aikin Iya da Habiba saboda suna tsafta sossai. Fadila kuwa tun daga ranar bata sake dawowa gidan ba iyakaci su haɗu da Haidar su sha sharholiyarsu. Hakama Ahmad babu abin da suka fasa wajan gudanar da mu amalarsu ta bayan fagge.
***
Bahijja tunda suka tattara suka bar Nigeria take farin ciki, saboda koba komai Khalifa ya yi nisa da Ummi kwatsam kuma bayan auransu da wata huɗu har tana da karamin ciki wata uku nan ta samu labarin auran Ummi ta hanyar Hindatu. Hakan yasa ta saki jiki lallai Khalifa ya zama nata ita kaɗai. Matsalar farko da suka fara fuskanta Bahijja muguwar kazamace gashi ta haɗu da laulayi mai matukar wahala. Khalifa mutum ne mai tsananin kyankyami nan da nan suka fara haurawa amma daya lura tana fama da laulayi hata karatun ajiyeshi yake ya kula da ita da gidan. Saboda yadda ya ɗora kalata a kan cikin burinsa kullum Allah ya bashi baby girl yasa mata Aisha Ummyter duk kudurinsa bai taɓa gigin furtawa Bahijja ba saboda duk yadda takai da fara a ya sake yayi wani batu kan Ummi to kuwa zasu haura bale taji wannan batu.
Haka Khalifa ya cigaba da kulawa da ita har cikinta ya shiga wata huɗu zuwa lokacin ta daina amaye-amayen amma sai Khalifa ya lura kazantar ba cikin ne kaɗai ya haifar da ita ba tun asali ɗabi arta ce nan fa suka soma dambarwa tsakaniksu ya zama sai hancinin juna da hattara. Bai kara shiga tashin hankaliba saida ya shiga ɗakin baccinsu wanda ya kaurace masa ya koma na saukar baki saboda tace bata son turaransa shi kuma baya iya hakura da kamshi. Duk tabi ta ɓata bangon da miyau har wani hamammi hamammi ɗakin yake kansa har wani juyawa yake ya fito yana kwala mata kira cikin kiɗima.
“Bahijja! Bahijja!! Bahijja!!!”. Tana jinsa taki amsawa a haka ya risketa a fallo ta yi kaca-kaca da shi tana shan ice cream. Turus ya tsaya yana karemata kallo cikin takaici.
“Bahijja wannan wane sabon salon wulakancine? Kina ji ina yi miki maga kika yimin banza?”.
Saida ta yi yatsina sannan ta kaleshi kallon uku ahu ta numfasa tare da rike kugu ta kaleshi.
“Gaskiya dai Khalifa baka da imani, ka manamin ciki ina fama sannan kazo kana yimin ihu aka kamar wata ɗiyarka?”.
Mamaki da takaici suka kashe Khalifa amma ya kane ya sassauta murya.
“Bahijja sanina dake yar gayu na sanki, amma dubarki cikin kazanta kaya daban-daban bama wannan ba Bahijja kinji yadda ɗakinki yake tsamin miyau haba My wife kamar bake ba”.
Wata dariya ta saki da tasa Khalifa tsayawa kyam yana kare mata kallo ta cigaba da kyakkyatawa sannan ta dubeshi galala.
“Khalifa amma wallahi kai mugune, dame kakeso inji? Kana kallo bacci gaggarata yake saboda cikinka amma wai kake tuhumata da rashin gyarama gidanka to ni wallahi bazan jura ba don haka saidai ka zaɓi ɗaya yar aiki dana bukata tun fari kaki ɗaukowa wai kai kyankyami gareka yanzu ɗaukarta ya zamema wajib ko kuma ka maidani kasata”.
Mamaki takaici suka yi masa rubdugu bai tanka ba ya bar mata ɗakin, zagewa ya yi ya gyara ko ina na gidan har ɗakin girki nan ya dinga karo da kwanikan busasshan abinci kayan miya kuwa wasu duk sun ruɓe haka ya gyare tsaf ya kuna turare. Sai kusan magarba ya gama tun la asar sannan ya dafa ruwa ya tasata gaba har banɗaki ya yi mata wanka ita kanta tsami take kanta kuwa uwar anakiyya ce dankare makare ya saɓeta tas yana mita tare da nuna mata illar abin da take yi amma jinsa kawai take yi shi ma wanka ya yi ya fito suka ci abinci yana ta janta da hira. Suna gamawa ya kwashe kayan ya kai kichen bai fito ba saida ya wanke ga mamakinsa bata falo yana shiga bedroom ya riski harta kwanta cikin ɗaure fuska ya dubeta,
“kin wanko bakinki”.
Turo baki ta yi tana gunguni, ta kular dashi amma ya kanne ta wuce ya rakata da idanu ta yo jika-jika ta dawo.
Hannu ya kai da niyyar janyota jikinsa ta daka tsale tana huci tamkar mesa,
“wallahi ba zaka taɓani ba fita kabarmin ɗaki”.
Ransa ya ɓacci baisan sanda ya kwaɗa mata mari ba ta dafe wajan tana dalaro harshe sai ya fice ya bar mata ɗakin.
***
Kwanci tashi Ummi ta share wata guda, tsakaninta da Haidar sai ido kawai ta saki jiki rayuwarta take yi shima ƴhaka babu ruwan wani tsakaninsu. A haka addimission ɗin ta ya fito Baffa da kansa ya tako ya kawo mata ta yi murna sossai cikin satin ta soma zuwa makaranta.
Da farko bata da matsalar komai amma bata share wata biyu ba Haidar ya ɓulo da wata tsurfa sai ya daidaici tafiyarta makaranta yake aiken driver hakan yasa ta jingine driver take tuka kanta zuwa makaranta. Suna waya sossai da Ummu da Abbu da kuma Baffa haka duk ranar juma a Baffa kan kawo musu ziyara in baizo ba wani satin wani zaizo ƴhakan yasa duk juma a da rana tafi yin girkin gargajiya saboda Baffa.
***
Da wuri ta dawo makaranta kasancewar bata da lacture, tana tura kofar falon warin sigari ya yi mata salama ta toshe hancinta idonta ya sauka kan Ahmad daya haɗa mata karamin hadari a fallo. Ganinsu tare da Fadila yasata yin murmushin mugunta ta cusa kai ɗakin tare da sallama babu wanda ya amsa cikinsu ta wuce ɗakinta kai tsaye gudun karsu ɓata mata rai.
“Yar kyauye”.
Muryar Haidar ta katseta ta juyo a fusace ya jefa idanunsa cikin nata take ya nemi hautsinata ta ɗauke kai ya cigaba.
“Ke yanzu da wannan katon hijabin kike zuwa makaranta kamar matar liman wallahi nidai an gama dani?”.
Dariya suka sa gaba ɗayansu, cikin tsiwa ta furta,
“faɗi muradinka ina da aikin yi in kuma kaki in kama gabana”.
Taku uku ya yi mai karfi sai gashi gabanta ya danke bakinta ya haɗa da mukulin hannunsa ya datse take wajan ya fashe sai jini, bakinta ya hau motsi zata yi magana amma tana shakarsa ya nunata da yatsa.
“Dilla jeki kimin abinci, nagaji da cin na kanti kuma kikaimun kwaɓa duk yawansa saikin cinye”.
Har zata juya zuwa ɗakinta saitaga rashin dacewar abun ta ajiye jakarta kai tsaye ta faɗa kichen ta soma wanke bakinta sannan ta buɗe ma adanar kayan abinci. Komai akwai a ajiye dan haka ta janyo ta soma haɗa abin da take ganin zata iya haɗawa jallop ɗin kuskus ta yi wadda taji kayan lambu da lemon zoɓo mai haɗe da gwaba cikin kankanin lokaci ta kammala ta jera kan daining kanta a kasa ta karasa in da suke,
“nagama”.
Ta faɗa murya a sanyaye bai tankaba ta kwashi hand out ɗinta ta shammaci idonsa ta takewa Fadila kafa da tsinin takalminta ta wuce da sauri tana jin ihunta kota juyo bale ta dubi kurarsu. Tana shiga ɗaki ta watsar da kayan hannunta tana sharar kwalar takaici wai ita ta yi wa Fadila girki ta jima zaune sannan ta faɗa bandaki ta sakarwa kanta ruwa. Ummi na bada baya suka mike zuwa daining ɗin, Ahmad na buɗe abincin kamshi ya yi masu salama musamman daya hango mutumin Chuchu wato kihi nan suka himmatu wajan ci sai karar cokula ke karaɗe ɗakin Ahmad kuwa faɗi yake,
“Haidar kai ai kana da gidan abinci a gida”.
Shi kuwa ya tsare gida sai ciccin magani yake. Fadila kuwa ta shaka karshema ture abincin ta yi ta kasa ci. Tas suka cinye abincin suka mike da niyyar barin gidan har sun kai bakin kofa Haidar ya juyo Fadila ta tsareshi da ido,
“ina zuwa prince?”.
“Ina zuwa tawan”.
Cikin sauri ya tura kofar ɗakin Ummi daidai lokacin ta fito daga banɗaki ɗaure da tawul ya yi kuri yana dubanta cikin sauri ta yi wuf ta suri hijabinta ta zura ya kama kame-kame ta sadda kai kasa.
“Ki dafa min abinci kafin na dawo”.
Kafin ta yi wani yunkuri ya fice ta lumshe ido tare da sakin ajiyar zuciya.
Haidar na bada baya Fadila ta dubi Ahmad,
“boss meka fahimta da sauyin man ɗin nan”.
“Hmm! Fadila mamaki kike ban kawai kibarsu suyi rayuwarsu in fa kika matsa aka yi auran nan zamu cutu mu duka. Saboda zakimin nisa”.
Ta yi masa kallon uku kwabo,
“kama rainamun wayau boss wallahi kai mugune kana tunanin in bar Haidar da waccan kwailar. Wallahi bazata saɓu ba kana tunanin zanci gaba da rayuwa hakane? Alakarmu dakai babu abin da zai sauya kasan cikin wata nan zan soma aiki nayi apply bankinku kuma sun ɗauke ni”.
“Da gaske kike Fadila?”.
“Da gaske Ahmad!”.
Dariya suka yi tare da tafa, daidai lokacin Haidar ya kawo kai harabar gidan karaf a kan idonsa ras gaban Fadila ya tsinke ya faɗi.+
STORY CONTINUES BELOW

[
ƊCikin kaɗuwa Fadila ta janye hannunta ya ɗauke kai tamkar bai gani ba ya shiga mota. Jiki a sanyaye suka rufa masa baya suka shiga amma dake yan duniya ne jansa suka hau yi da hira tamkar ba abin da ya faru. Shi dai bai tanka ba har suka sauke Fadila suka sake ɗaukar hanya Ahmad ne ya ɗan tsaraka da shi ya dubeshi,
“prince su Muhammad nasan zuwa suga madam nace su bari in tuntuɓeka”.
“Kasa lokaci nida kai ai duk ɗaya ne”.
Ya bashi amsa a gajarce jikinsa a sanyaye ya amsa da,
“to”.
***
Da dare Ummi ta shirya masa lafiyayyan abinci ta ajiye ta wuce ɗakinta hakama da safe. Abin mamaki tas yake cinye abincin cikin kankanin lokaci ya yi sabo da abincinta ko ina yaje yaci sai ya riski bambancin ɗanɗano na abincin. Ummi kuwa karatunta take cike da kwanciyar hankali bata da wata damuwa saboda tayi maganin Fadila zuwa gidanta kasancewar duk randa ta tako gidan sai tayi silar sata kuka.
***
“Yanzu kai Haidar sai yaushe ne zaka yi maganar auranku da Fadila ka duba fa anshare wata huɗu da kwanaki da auranka?”.
“Mommy kiyi hakuri ina so ne ko wata shida a kara saboda banasan Daddy yaga laifinki ina fara batun haka zaice kece kika sani”.
Ta yi jim sannan ta nisa,
“haka ne Haidar kafini tunani a nan amma ka kiyaye ina sane da sirangalin da kake yi tsakanin wajan mahaifinta da uwarta kana gani yanzu duk wata dukiya ta mahaifinka ubanta yake juyata ai duk ma kai kaja ka karanci business ka ɓige a wani karatun likita”.
Murmushi ya yi tare da shafa sumarsa,
“Mommy kenan ni kuma shi nake so”.
Bata tanka ba ya yi mata sallama ya fice, yana bada baya Nabila tabi bayansa saɗaf-saɗaf sai da taga shigarsa gidan Abbu sannan ta dawo tana kunkuni.
“Hmmm! Mommy ai na gaya miki can yake zuwa rannan fa har abinci nagansa yana ci a gidan”.
Cikin kaɗuwa Hajiya Sadiya ta zaro ido tana kaɗa harshe shigowar Baffa ya katse musu zancan.
***
Cikin gajiya ya shigo ɗakin tun daga main parlour ya soma kiciɓus da robar ruwa d a tarkacan chaculate ya yi tsaki ya wuce kai tsaye yana gab da shiga ɗakin baccinsu yaji wani suuuuu luuuuu yaf ya faɗi kasa kansa ya bugu da kujera ya na shirin mikewa hannunsa ya tankwaɓi wata roba karama wani karni ya daki hancinsa. Yammm! Tsikar jikinsa ta zuba zuciyarsa ta tsinke sai amai ya taso masa. Daidai lokacin ta taso da katon cikinta ta fito ganinsa a kasa ta gwale ido tana mamaki.
“Khalifa lafiya?”.
Wani takaici ya mamayeshi bai tanka ba ya mike ya wuce ɗakinsa ta saki tsaki tana faɗin,
“aikin banza mutum sai mitar tsiya”.
***
Tsakanin Hindatu da Ummi aminci sai abin da ya yi gaba musamman da suka kasance a makaranta ɗaya kuma department ɗaya gashi duk abu ɗaya suke karanta. Kamar ko yaushe zaune suke sun fito kafteriya Hindatu ta dubi Ummi tana faɗin,
“wallahi Ummi cikin nan ya soma yimin nauyi kuma duka duka wata biyar kenan fa”.
Ummi ta kwashe da dariya tace,
“da alama ɗan Baba ko ɗiyar Baba zata yi nauyi”.
Suka yi dariya daidai lokacin wayar Hindatu ta yi kara ta ɗaga da walwala tana faɗin,
“yaya ina yini ya aiki?”.
Fuskarta ta sauya daga yanayin fara ar tana tuna tsantsar tausayi da damuwa,
“kayi hakuri zata sauya yaya na rasa menene yake damun Bahijja wallahi?”.
Sun jima suna magana sannan ta katse kiran tare da sauke ajiyar zuciya,
“waɗansu matan basu da kai Ummyter”.
Ummi data fahimci da Khalifa ake magana saita yi dabarar kauda zancan.
“Allah dai ya kyauta Hinduwa”.
“Allah Ummyter tausayin yaya nake ji Bahijja wahal dashi take ga muguwar kazanta”.
“Ina ga aikin ne ya yi mata yawa kibashi shawara ya nema mata mai tayata koda shara ne ita taji da girkinsa da kuma gyaran bed ɗinsu”.
“Shikenan Ummi bari in masa message amma fa mata da yawa muna kuskure shiyasa sai kiga maigida ya juyamana baya bayan laifin duk yana wajanmu. Wata hata kwaliyar kanta bata iya ba bale azo batun tsara abinci uwa uba gyaran gida ga rashin iya tsara zancan daya dace a furtawa miji komai yazo bakinsu kwaɓawa suke kamar sa anin juna. Nan da nan kiji ana tashin jijiyoyi tsakanin ma aurata aure ko shekara ba a rufa ba”.
Tana karasa maganar tana turawa Khalifa message ɗin ya yi mata reply da ya gode Ummi kuwa murmushi ta yi kasan ranta tana jin kamar da biyu Hindatu ke mata wannan bayanin lokaci ya yi daya kamata ta saduda aure dai an ɗaura kotana so kobata so sunan Haidar mijinta. Karfe ɗaya dai-dai suka bar makaranta ko wace ta shiga motarta sai gida kafin Ummi ta karasa gida ta haɗa gumi tsabar tunani tana zuwa ta yi parking ɗin motarta ta yi wa Baba maigadi sallama ta wuce ciki.
A tsakar gida ta yi kiciɓus da Habiba cikin riga da zani na atamfa duk da sunsha jiki amma a goge suke tsaftar yarinyar na burgeta suka gaisa saiga Iya ta fito cikin hikima Ummi tace,
“Iya wai Habiba bata zuwa makaranta ne?”.
“Eh! Bata zuwa ban sata ba”.
Jinjina kai ta yi ta ce,
“ya kamata asata amma kibari zan tuntuɓi maigidan”.
Godiya ta yi mata sossai ta wuce ciki suka wuce sashinsu. Karewa ɗakin kallo ta yi ya yi tsaf ta yi murmushi ta faɗa bed room ɗinsu tsaf ta gyarashi ta yi wanka ta ɗaura alwala ɗaya da rabi ta yi sallah ta fito. Tunanin farko daya zo mata in da zata sami mabuɗin ɗakin Haidar saita tuna kofofin iri ɗaya ne dan haka ta ciri na kofarta ta wuce sashinsa saida ta biya ta sake duba sashin su Iya ta tabbatar sunci abinci sannan ta wuce.
Cikin nutsuwa ta buɗe sashin wannan shi ne karo na farko data shiga sashinsa tun zamanta a gidan tsayin wata biyar. Tsaruwar ɗakin ya bata mamaki kamar na mace saidai rashin gyara kura amma komai a tsare yake a muhalinsa tsaf. Banɗaki ta fara shiga nan ta riski singlet ɗinsa cikin kwandon wanki guda takwas da wandunansu duk farare tattaresu ta yi ta jikasu a wani botiki karami ta zuba ruwan hypo data gani a ajiye cikin banɗaki ta tattare zaninta ta yi ta hau wanki banɗakin fes ta wankeshi sai sheki yake cikin mintuna sha biyar sannan ta jawo kayan data jika kwamin wanka ta shiga ta wankesu tsaf karfe biyu daidai ta kammala ta fito ta shanyasu a harabar sashinsa. Ta koma ta hau goge kurar ɗakin saida ta tabbatar da tsaftarsa lokacin biyu harda rabi da minti biyar ta kule ɗakin bayan ta fesheshi da abun kamsassa ɗaki. Kai tsaye sashin Iya ta nufa ta ɗauki Habiba suka wuce cikin gida ta bata aikin firar doya ita kuma ta nufi ɗakinta ta ɗan kwanta ta huta zuwa mintuna.
Misalin uku da rabi daidai ta mike ta koma sashinsa ta riski kayan sun bushe kwashewa ta yi ta shiga ciki ta zubesu tana shirin fitowa suka kawo wuta babu wani jinkiri ta goge kayan fes, lokacin agogo ya nuna mata karfe uku da minti arba in da biyar ta mike kenan zata bar ɗakin ta tuna bata gyara masa cikin firinji ba dan haka cikin sauri ta karasa ta buɗeshi ras gabanta ya faɗi sakammakon ganin tarin kwalaban giya kanta ya sara ta dafe tare da furta,
“ya Allah!”.
Hawaye ƴya kwaranyo mata tausayin kanta dana Baffa ya tsinka zuciyarta, yanzu haka Haidar yake rayuwa a haka zasu rayu da juna karkashin turbar ɓata lallai yanzu ne ya kamata ta yi karatun ta nutsu ta cecci rayuwar ɗan uwanta tilas ta ajiye KIYYAYA gefe ɗaya ta rungumi rayuwarsa duk cikin zuciyarta take wannan tunanin. Tsaf ta kwashesu ta je ta yi floshing ɗinsu a masai kwalaban kuma guda huɗu ta haɗesu tanata dube-duben in da zata sami leda ta ɗaure can ta hangi wata leda viva baka kusa da kayan kallo cikin azama ta janyota ta zazzage kayan ciki ai Ummi saita karasa sumewa babu komai ciki sai tarin blue film ƴhata numfashinta tafiyar sauri sauri ya dinga yi ta yi maza ta kwashesu buɗe ɗankalinta ta ɗauresu kwalaban giyar kuma ta naɗesu cikin ledar ta kai sashinta ta ɓoye.
STORY CONTINUES BELOW

Saida ta yi sallah sannan ta mike ta haɗa film ɗin da kwalaban cikin wata ledar babba ta ɗaure ta bawa Mansur tare da gargaɗinsa kar ya kwance yaje can wajan gari ya yasar a juji. Cikin sanyin jiki ta dawo cikin gida ta kwashi turarrukanta masu tsada taje ta jera masa kan mirror anan sake mummunan gamo da pics ɗinsa da Fadila marasa kyan gani ɗibarsu ta yi ta yi musu gutsi-gutsi ta watsar a shara ta baro ɗakin ranta a jagule duk sai taji ta kara tsanar Haidar lallai Fadila gubace cikin rayuwarsu. Kicin ta nufa ta zamu Habiba ta ɗora doyar harta kusa dahuwa dan haka ta zauna suna ɗan taɓa hira tare harta isa yi ta sauke suna hira tana nunamata yadda ake dakan sakwarar tana yi tana naɗeta a leda tana gamawa ta ɗora miyar agushi haɗe da ganyan ogun ta yi masa farfesun bandan kifi da kunnun aya sai magarba suka kammala ta zuba musu nasu ta basu ta wuce ɗakinta ta yi sallah tare da zama tsakanin sallahr magarba da isha i karfe bakwai da rabi aka kira isha ta mike ta bi masallaci ta ɗora shafa i da wuturi tana idarwa ta faɗa banɗaki ta yo wanka ta fito.
Cikin doguwar rigar atamfa ta shirya rigar bata da ado amma samanta da roba aka yi ɗinkin ta kamata cif ta fito da zubin dirinta. Ummi doguwar mace ce mai zubin kwalbar lemo coca cola tatarta kuwa chaculate ce mai haske tana da manyan idanu masu haske ɗauke da kwayar ido baka siɗik hancinta bashi da kara sossai yana da ɗan faɗi shiyasa Haidar kece mata mai nannan hanci. Fuskarta doguwa ce sossai bakinta madaidaici kif bata da yalwar gashin kai iyakarsa kafaɗa amma ya wadaci goshinta wanda hakan yasa wasu ke mata duban mai gaggarumin gashi girarta bata da cika sossai amma baka ce tana da shape da tsayi kamar an gyarata. Bata yi wata kwaliya sossai ba hoda kawai ta murza tasa man leɓe tare da gyara girar ta yane kanta da karamin mayafi kalar atamfar tasa takalmi flate ta fesa turare ta fito falo. Zama ta yi tare da lumshe ido tana tuna abin da tagani ɗakin Haidar kwala ta taru cikin idonta tana kokarin maida ida aka turo kofar ɗakin ta yi hanzarin kai idonta kan kofar das gabanta ya faɗi suka yi kalon kalo da shi wata muguwar harara ya watsa mata tayi saurin ɗauke idon ta cikin karfin guiwa ta mike ta tunkari in da yake duk da gargaɗin da zuciyarta take yi mata.
Cikin tafiyar jan hankali ta karasa bakin kofar tsaye yake hannunsa rike da rigarsa ta ma aikatan jinya cikin nutsuwa ta sunkuya tare da furta,
“yaya Haidar sannu da zuwa”.
Bai amsaba ta karɓi rigar tare da jakar hannunsa tsananin mamaki ya daskarar dashi ya yi ta maza ya kanne ya bi gefanta ya wuce ya bi siririn corridor ɗin da zai kaishi sashinsa. Ta cije leɓe tare da bin bayansa saida ya kusa minti biyar da shiga sannan ta bi bayansa yana tsaye yana amsa wayar Fadila ta ajiye kayan bakin gadonsa sannan ta juya zuwa banɗaki ta ƴhaɗa masa ruwan wanka cikin zuciyarta wautarta kawai take hangowa tare da ganin ta bada kanta amma ta daure ta cigaba ta fitowa ta samu ya cire uniform ta sadda kanta kansa,
“yaya na haɗa maka ruwan wanka”.
Jim ya yi ƴyana kallonta kome ya tuna sai ya tsagayeta ya nufi banɗakin kafin ya fito ta shirya masa abincin ta fita zuwa sashinta saida ta daidaici ya gama cin abincin sannan ta dawo ta kwashe kayan ga mamakinta ya ci sossai. Ta kwashe ta mike zata fita ya tsaida ita,
“Ummi ina kayana na cikin firij?”.
Dam gabanta ya faɗi kafaffunta suna neman gaggarta tsayuwa cikin rawar murya ta furta,
“wane kaya?”.
“Ke! Ummi wasa nake miki zaki rainamin hankali? Ina kayana?”.
Cikin dakiya ta juyo tana gatsina fuska,
“Dakata Haidar na zubar saboda banga fa idar ajiye kayan ɓarna a cikin gidana ba!”.
Wani kyakkyawan mari ya zabga mata yana ficikota ta yi taga taga zata faɗi ta jingina da bango ajiye kayan hannunta ta yi dukkansu huci suke kamar zakaru ya nunata da yatsa.
“Ni zaki nunawa ɗanyar kai? Ina ruwanki da rayuwata? Rayuwarki ce bance miki bana son shishigi ba?”.
Cikin tsiwa ta tareshi,
“rayuwarka tawace Haidar!”.
Cak! Ya tsaya yana kare mata kallo wani abu yana zagaya kofofin jikinsa ta cigaba.
“Saboda kai ɗin JININA NE bazan juri ganinka cikin gurbataciyar rayuwa ba”.
Wata shu umar dariya ya yi tare da kaiwa bakinta cafka da hannunsa ta yi tsale tana kara mara sauti suka soma zagaye ɗakin Allah ya bata sa a ta fice a guje ta yi sashinta tana numfarfashi. Tana shiga ɗakinta ta zube tana kuka mai cin rai nan da nan kanta ya hau ciwo.
Washegari bata daddara ba abinci ta sake shirya masa sannan ta wuce makaranta, duk da tana cikin damuwa amma tana kokarin ɓoye damuwarta har suka tashi daga nan ta wuce gida. Tsayin sati biyu aikin Ummi kenan kula da sashin Haidar da cimarsa sossai ya yi sabo da hakan a hankali suka soma sabawa ka idane kullum saita gaisheshi cikin girmamawa hakan yafi komai yi masa daɗi. Bangaran Ummi dauriya kawai take yi amma ko ganinsa bata muradin yi gashi ta lura kallon blue film da shan barasa ya zame masa jiki shi yasa kullum suke faɗa mudun zata je shara saita zubar dasu.
***
Bangaran su Mommy abu kam yaci tura sabida duk yadda suke wa lamarin duban sauki amma yasha kansu hakan yasa suka soma yunkurin ɗaukar mataki ta hanyar karkashin kasa.
***
Tun safe Ummi bata hutaba kasancewar Asabar ce suna hutun karshan mako Haidar na zaune kan kujera yana kallon labarai tana ɗakin girki taji an buɗe kofar falo jim kaɗan taji ya yi godiya ya koma saɗaf-saɗaf ta koma ta leka karaf idonta ya sauka kan kwalbar daya ɗaga zai kai bakinsa a sukwane ta fito daga kicin ɗin tana huci cikin shammata ta daki kwalbar hannunsa ta faɗi ji kake taratsatsa ta wargaje a tsakar ɗakin mamaki ya kamata ganin ya cire duk wata takarda dake nuna giya ce ya cukuikuyeta ya ajiye a gefe illa kawai murfin dake kan center carpet ɗinta. Cikin takaici ya kankance idanu yana dubanta sun kaɗa sunyi jajjur dasu zai yi magana kenan aka turo kofar tare da yin sallama. Gaba ɗaya suka juya a rikice jin muryar Baffa da sauri ta suri murfin da takardar ta tura karkashin kujera ta mike tana faɗaɗa fara arta.
Sanahsmatazu.wordPress.com
1
STORY CONTINUES BELOW

“Oyoyo Baffa sannu da zuwa”.
Cikin dabara ta biyo dashi sashin da kwalbar bata watsuba ta ɗauko abin kwashe shara ta kwashe ta dawo hannunta ɗauke da ruwa da kuma damammiyar fura da bata rabo da ita ta rusuna,
“Baffana ga fura”.
“Da kyau Ummyterna aaa sai murna take taga Baffanta”.
Cikin murna ta washe hakoranta farare tas tsayayyu masu hushirya a tsakiya gasu dogaye tsaf. Haidar yana gefe sai kallonta yake sai yaga ta yi masa kyau kamar bata ita ba. Sun jima yana yi musu nasiha mai ratsa jiki karshe ya tsare Ummi da tambaya kan ko akwai wani abu da Haidar yake mata. Ta sunkuyar da kai kasa murya a raunane ta furta,
“babu Baffa lafiya muke zaune”.
Boyyayar ajiyar zuciya ya saki daga shi har Haidar ɗin wadda su kaɗai duka san manufarta mikewa ya yi yana sa musu albarka ya wuce.
Tun bayan tafiyar Baffa Haidar ya shiga dogon tunanin sossai mamaki yake yadda Ummi ta sakaya aibunsa a idon mahaifinsa. Ya tabbatar yau data bayyanawa Baffa zaman da suke da tsine masa kaɗai zai yi yaji sanyi cikin ransa saboda kullum suka haɗu nasihar kenan ya rike masa Ummi amana ya kula da ita. Duk sai yaji ya muzanta wani tausayi da wani abu daya kasa tantance ko menene a kan Ummi ya dinga zagaya zuciya da jijjiyoyin jikinsa. Mikewa ya yi ya nufi ɗakinta karo na biyu tun auransu da ita ya tura kofar ya shiga yana shiga gabansa ya yi muguwar faɗuwa.
20
Ganin Ummi ya yi ta yi zaune tana kuka, idanunta sunyi jajjur da sanyin jiki ya karasa ya zauna gefan gado. Kwata-kwata ya rasa ta inda zai tunkareta ya daure ya yi ta maza,
“Ummi ki daina kuka kinji”.
Mamakin kalamansa ya tsaida kukanta cak! Haidar data sani mutum mai iza da takama yau shi ne yake lallashinta bata kara mamaki ba saida kalamansa suka ratsa kunnuwanta.
“Ummi na gode da karamcin da kikai min ubangiji yasaka miki da alkhairi”.
Ai saita karasa sakwarkwacewa can wata zuciyar ta tunasar da ita,
“ke Ummi Haidar nefa kawai dankin fitar dashi ne wajan Baffa yake lallaɓaki amma bari kiga a kwana biyu”.
Kallonsa ta yi tana son yi masa futsara amma ya yi mata kwarjini saita sunkuyar dakai,
“babu komai yaya Haidar amma don Allah kadaina shan giya”.
Ya yi jim duk saiya tsani kansa, wai saboda bakin hali karamar yarinya kamar Ummi yake shaka,
“inshaa Allahu Ummi zan daina ki tayani addu a”.
“Zan maka yaya Haidar amma kaima ka guje mata bama ita kaɗai ba duk abinda kasan zai gusar maka da tunani gƴdun zubewar mutunci. ƊDomin yana daga cikin manyan manufofin musulunci kiyayewa ɗan-Adam Hankalin shi, domin hankali bakaramar kima yake da ita ba, wannan nasan koda ban kawo ayoyi da hadisai a kan haka ba kaida kanka zaka shaida, yaya musulunci ya ba wa hankalin dan-adam hakikanin kulawa ta yadda ya tsaftace shi daga barin dukkan abinda zai gurbata masa hankali, akan wannane musulunci ya haramta dukkan abinda yake gusar da hankali kamar :, Giya, Wiwi, Koken da dukkan wani abu da za’a sarrafa ta kowacce irin hanya muddin yana taba hankali to haramunne, Ma’aikin Allah yana cewa
“Dukkan abinda ke sa maye giya ne, kuma dukkanin giya haramun ce”.
Bukhari da Muslim suka ruwaito, sannan koda baya sa maye sai an sha da yawa to ko kaɗan ne haramun ne kamar yadda Ma’aikin Allah yake cewa,
“Dukkan abinda meyawan shi ya ke sa maye to kadan dinshi ma haramun ne”
wannan fa shi ne hakikanin gatan da musulunci yayi mana, domin yadda giya da mukarrabanta muggan kwayoyi suke cutar da gangar jiki likitoci sun yi ittifaki akan haka da kuma yadda take sanadiyyar aukuwar cututtuka masu hatsarin gasket wasu suna kaiwa ga salwntar rayuwa, yan zu mutum ya sha wadan nan kwayoyi sun yi sana diyyar rasuwar shi haka zai zo ranar kiyama yana kamfatar waɗan nan kwayoyi kamar yadda bayanai suka gabata, ga yadda suke bata dabi’u, abin kunya kaga wani yasha ya taho yara su ns yi mishi ‘ya yi marisa ya sha kafso’ wani kuma ya kwararawa iyalin shi fitsari a kwance, wannan ya zama amalala, da kuma yadda take bata hankali ta kurɓata tunani, domin kowa yasan waɗan su muggan lefukan da ake tafkawa basa yiwuwa cikin cikakken hankali sai an bugu, lallai giya ta tabbata abar Allah ya yi wadaranta, wannan yasa malamai suka yi saɓani kan aukuwar sakin mai-maye idan ya saki matar shi yana cikin maye. Sabo da haka kamar yadda bayani ya gabata aka haramta dukkan wani abu da akai mai kowacce irin dabara ta yadda ya ke sa maye, ko meye kuwa, koda fura ce akai mata wata dabara ta zama tana sanya maye to ta zama haram, kamar yadda hadisin ma aiki ya yi nuni da nisantar kayan maye. Don Allah yaya Haidar ka daina sha”.
Ta karashe maganar tana sharar hawaye, Haidar yayi shiru yana jimami cikin ransa sai ya mike cike da nauyin jiki ya bar mata ɗakin.
Ranar haka suka yini sukuku kowa da abin da yake ayyanawa cikin ransa. Da azahar Haidar ya fita ya bar gidan duk saita takura ganinta kamar abar zaije ya sha shi kuwa can keɓantancan waje ya samu ya killace kansa yana dogon tunani kan abin da ya faru tsakaninsa da Ummi. Bayan fitarsane ta samu bakuncin Hindatu sun jima suna hira daga bisani ta wuce gidanta. Sai bayan magarba ya shigo ta mike tana yi masa sannu da zuwa ya amsa yana ɗan murmushi kaɗan a kan fuskarsa ya wuce ɗaki ta yi tsaye jim daga bisani ta yi shahadar kuda ta bishi da abincinsa can yana zaune ta ajiye ta kalleshi,
“yaya in zuba ko sai kayi sallah?”.
“Ummi nayi sallah cikin gari kinsan suna rigamu sallah kuma nanma akira ya aka yi baki ba koda yake naga alama hutu kike?”.
Kunya ta kamata ta sunne kai kasa, mamaki take yadda ya gane hakan, zuba masa ta yi yaja flate ɗin gabansa yasa cokali tare da yin bisimilla ya ɗiba ya kai cokalin bakinta ɗauke kai ta yi tare da ɗaure fuska bai bi takanta ba kawai ya ci abincinsa ya yi kat. Saida ya gama cin abincin ya fuskanceta hakuri ya sake bata kan abin da ya faru ta mike ta wuce sashinta. Tun daga ranar zamansu ya sauya salo Haidar na kula da motsinta sossai da safe zai shigo yaga lafiyarta haka da dare ɓangaran Ummi kawai gani take saboda rufa masa asiri data yine amma da aka kwana biyu sai ta fuskanci ya sauya sossai wasu lokutan tana jiyo hirarsa da masu aikin gidan Haidar da ko sakar musu fuska baya yi amma shi ne hada hira. Hata ɗakinsa an samu sauyi ciki saboda tadaina karo da giya da kasussuwan batsa hakan yasa ta kara zage dantse wajan yimasa addu tare da kaiwa ubangiji kukanta kan Allah ya kara shiryar dashi.
STORY CONTINUES BELOW

***
Hankalin Fadila ba karamin tashi ya yi ba kwata kwata Haidar ya sauya mata waya in ba ita ta kirashi ba ya daina kiranta hakan yasa ta datawa Hajiyarta da Hajiya Sadiya hankali kan batun auranta da Haidar ga Nabila na kara zugata saboda akan idonta yake sauke Ummi a makaranta ya kuma dawo ɗaukarta. Hakan ya ɗaga musu hankali matuka Ummi kuwa babu abinda ya dameta karatunta take damuwarta ɗaya gashi harta shiga wata na shida amma ya hanata zuwa ko ina ko gidan Hindatu bata jeba duk da kusancin da suke dashi kwatsam ranar Asabar Hindatu ta kirata tana shaida mata ta yi ɓari hankalinta ya tashi sossai ta sameshi tana yi masa bayani hijabi kawai yace ta ɗauko suka nufi gidan nata. Lokacin da suka je har sun dawo asibiti daga nan fa hira ta ɓarke tsakanin Aminu dashi ashe ma asibiti ɗaya suke aiki rashin sani tun daga lokacin duk sati biyu ko uku sukan ziyarci juna.
*** Bangaran Khalifa shawarar Hindatu ya bi ya ɗaukarwa Bahijja yar aiki a hankali saiya samu saukin aiyukansa ga karatu da ya tasoshi gaba ga kuma hudimar kula da shige da fican kayan mahaifinsa daga nan Canada inda yake karatu zuwa Nigeria ga kuma cikin Bahijja daya shiga watan haihuwa. Hakan yasa bashi da lokacin kansa ko abinci a daddafe yake tsakurarsa. Kamar kodayaushe da wuri ya dawo aiki gidan shiru mai aikinsu ta gama ta tafi ya karasa falon saiya riski Bahijja tanata murkususu a rikice ya yi kanta yana faɗin,
“Bahijja lafiya?”.
Cikin jigatuwar ciwo ta furta,
“Khalifa cikina zan mutu”.
Ai bai jira cewarta ba ya suri Bahijja ya yi waje da ita, nan da nan suka karasa asibitin daya buɗe mata file kafin awa ɗaya Bahijja ta haifi sankaacceciyar ɗiyarta kyakkyawa kamar Khalifa nan da nan murna da farin ciki suka baibayeshi aka salamesu suka wuce gida sai murna yake yana bubbuga waya yana shaidawa dangi an samu ɗiya mace. Kai tsaye ya nufi katafaran kati ya jibgowa baby da mamanta siyayya. Bahijja ta dinga mamakin Khalifa da irin siyayya da kuma rawar kafar daya ke yi kan haihuwar Mommy baki har kunne take musu barka.
Kwana huɗu da haihuwar da yammaci yan Nigeria suka duro Canada cike da farin ciki. Tawagar tafiyar daga Hindatu sai kannan Bahijja guda biyu Ikilmaht da Wasila. Tayi murna da zuwansu sossai ana gobe suna duk suna zaune a falo Khalifa ya shigo yana fara a kan fuskarsa Hindatu ta dubeshi,
“nifa yaya banjin sunan babynmu ba”.
Dariya ta kwace masa ya shafa sumarsa,
“ke Hinduwa ki rabani ga kalatacan mijinki can ya biyo ki har nan”.
Dariya ta saki tana faɗin,
“ka cika zolaya dama ai akwai abin da zaizo yi”.
Dariya suka yi ya saci kalon Bahijja da take kokarin yanka kankana babyn na cinyar Wasila ya ce cikin dakiyar zuciya,
“sunanta Aishatul Humaira amma Ummyter za a dinga kiranta”.
Hindatu ta daka wani wawwan tsale ta mike,
“kai gaskiya yaya kayi rawar gani….”.
Saita katse azarɓaɓin da take yi sakammakon karar da Bahijja ta saki duk suka bita da idanu cikin mamaki ashe kaɗuwar data yi yasa wukar hannunta ta yanketa cikin masifa ta shaki wuyansa tana wujjijjigashi tamkar wani karamin yaro……..
“Khalifa nizaka wulakanta ka tozarta a idon duniya? Ka rasa sunan da zaka sama ɗiyarka saina tsohuwar budurwarka? Wallahi baka isa ba sai ka sake mata suna!”.2
Dauketa ya yi da giggitacan marin daya sa numfashinta tafiyar wucin gadi ta sheka barzahu ta dawo. Duk fallon suka zuba masa ido ganin yadda yake huci tamkar wanda ya yi gudun shekara ya nunata da yatsa,
“Bahijja ni zaki nunawa iko kan abin da yake JININA NE? Lallai yau na kara tabbatarwa baki da wayau”.1
“A’a fa yaya wannan tauye hakkine, da baka yi shawara da ita ba ka yanke hukunci haka ake rayuwar auren wannan ai cin zarafine?”.
Cewar Wasila tana taunar cingum, mamaki ya cikashi kawai sai ya juya ya bar ɗakin da sauri Hindatu ta bi bayansa a ɗaki ta sameshi ya yi tagumi ta kira sunansa.
“Yaya ka yi hakuri nasani an ɓata maka amma kaima da kai meyasa baka tuntuɓeta ba? Ita ma ai tana da hakki ɗiyarta ce fa ya kake tunanin zata ji musamman data san matsayin wadda kasa sunan dominta?”.
“Hindatu idan ba lallashina kika zo yi ba tarewa yar uwarki kika zo yi to fita kibani waje. Diya dai tawa ce kuma nike da hakkin raɗa mata suna don haka Aisha naga damar sa mata kuma wallahi babu sauyi”.
Wayarsa ce ta yi kara ganin sunan Mama yasa shi risina ya amsa kiran cikin girmamawa amma bata amsa ba ta haushi da faɗa.
“Abubakar ina hankalinka yake? Dukan matarka ka yi anya kuwa kaine menene yake damunka?”.
“Mama ki fahimce ni Bahijja duk ta wuce tunaninki, ni wallahi ma tunda saura shekara ɗaya in dawo to tare zan haɗosu da su Hindatu su dawo gida. Mama nagaji da Bahijja kwata-kwata bata dace da rayuwata ba”.
Ya karashe kamar zai yi kuka, jikin Maman ya yi sanyi sossai ta numfasa,
“lafiya kuwa me take maka?”.
“Mama basai mun yi tone-tone ba amma ki dinga yimin addu a don Allah ya bani mace daidai da tsarina”.
Duk sai ta yi sanyi maimaikon faɗa ta koma lallashi Khalifa dai ya kafe kan bame sauyawa ɗiyarsa suna da haka suka yi sallama. Lokacin da Hindatu ta fito har lokacin kuka Bahijja take ta dubeta,
“Bahijja ki daina kuka don ƙAllah suna dai shi aka samata haka Allah ya hukunta saiki dangana”.
“Dillacan munafuka rufamun baki, ai bakinku ɗaya kin san kuwa yadda nake jin KIYYAYAR Ummi a raina?”.
“Ba KIYYAYA bece Bahijja SON ZUCIYA ne kawai irin naki an taɓa kishi da matar dake auran wani daban ba mijinki ba wannan ai shirimene?”.
“Kimin shiru Hindatu kar kisamun ciwan kai, wallahi bazan shayar da wannan yarinyar nono ba mudun bai sake mata suna ba”.
Fuu! Suka bar ɗakin suka barta rungume da yarinya tana tsanyara kuka haka suka yini yarinyar tana kuka kamar wadda ake mintsini bunu bunu Khalifa ya shigo yayin da Bahijja ta ɓame kofa ta kulle ita da kannanta.
***Misalin karfe huɗu na yammacin ranar Lahdi Fadila ta shirya cikin shigar atamfa wadda tela yaci mutuncinta ɗinkin ya zauna das a jikinta ta ɗauki na suga. Kai tsaye office ɗin Haidar ta nufa tana tafe tana tunani ira iran waɗanan ranakun kafin ta nemi Haidar ya nemeta amma yau ita take nemansa yana guduwa ta share kwala daidai lokacin da ta yi parking a harabar kayatacan asibitinsu ta sauka ta kukkule motar ta kutsa kai cikin office ɗin.
Zaune ta sameshi shida Ahmad ta karasa rana murmushi babu yabo ba fallasa Haidar ya tareta sun ɗan yi jim na mintuna goma ya mike yana duban agogon hannunta ya nufi hanyar fita. Wani abu ya tokare makoshinta murya a shake ta furta,
“ina kuma zaka bayan kasan wajanka nazo?”.
Bai juyo ba bai kuma tsaya ba ya furta,
“Ummi zan ɗauko a makaranta me zan miki?”.
Ya faɗa tare da juyowa ya tsareta da ido duk saita muzanta ta sassauta murya.
“An ya Haidar ka kyautamun kuwa? In taso kafa ya kafa tun daga gida domin kai amma ka wofintar dani? Kwata-kwata ka sauyamun kota batun auranmu baka yi”.
Jikinsa ya yi sanyi shi kansa yasan bai kyauta ma Fadila ba amma a yanayin daya ke dubanta bazai iya auranta ba saidai yana shakkar furta mata sabida koda yana yiwa Fadila duban lallataciya shi ne silla shiya fara buɗe mata ido da rayuwar clube kuma shi shaidane shiya fara saninta kansa ya ƴyi nauyi kawai saiya fice ya bar office ɗin. Fadila sunkuya wa ta yi ta fashe da kuka mai cin rai tausayinta ya tsinka zuciyar Ahmad ya dinga yi mata duban wauta,
“Baby ki hakura da Haidar kawai kizo miyi rayuwarmu zai fiye miki”.
“Bazai yiwu ba boss bazan iya rayuwa babu Haidar ba tabbas nayi kuskuren sarayar da yancina gareshi amma wallahi bazai ci bulus ba duk da ba iya kansa na tsaya da rayuwata ba amma shi ne sillar komai dan haka yadda na ɗanɗani takaici sai shima ya ɗanɗana wallahi mu zuba”.
Fuuu! Ta bar ɗakin Ahmad ya ɗaga kafaɗa ya wuce abinsa. Haidar kuwa kai tsaye makaranta ya wuce ɗaukar Ummi lokacin daya karaso tana tsaye tare da Sabah ɗiyar Hajiya Sarrinah sallama ta yi mata ta shiga motar suka cilla kan titi.
Kamar kurame haka suka dinga tafiya har suka karaso gidan yana yin parking ya yi saurin maida sucuirity ɗin motar ya rufe. Ummi ta yi tsamo-tsamo cikin motar ya dalla mata harara,
“waike baki iya yi wa mutum godiya ba aikinki kawai ki share ɗaki ki gyara gado kazama kawai ko gadonma baki iya hawa ba”.
Cikin gungunin da baisan abin da take faɗa ba ta ce,
“ainafi wani wallahi”.
Bata yi aune ba ya cafke bakin ya dinga murzashi da hannunsa a zaba ta isheta tasa hannu biyu ta na kici kicin kwacewa ta kasa shi kuwa laushin hannunta ya shagaltar dashi ya rasa a duniyar daya ke bai aune ba ta kwace rikon da ya yi ma bakinta ta zabga masa cizo ta buɗe motar ta yi waje da gudu zuwa cikin gida. Ya jima yana jinjina kokari irin nata wani fanin ma dariya take bashi kaɗa kai ya yi ya shige gida abinsa.
***
Washegari tun safe Khalifa ya tashi Hindatu saboda kwana suka yi basu yi bacci ba sai asuba saboda kukan da Ummyter take yi. Kai tsaye asibiti suka nufi sabida yadda yarinyar ta yi mugun galabaita. Zuwansu asibiti ba daɗewa aka sawa babyn drip saboda taji jiki daga nan suka wuce office ɗin likitan nan ya dinga masifa kan me aka barta da yunwa?. Cikin nutsuwa Khalifa ya yi masa bayanin Mamanta ce bata da lafiya, don haka suka kawota don abata madarar yara saboda gudun ciwo ya kamata. Likitan ƴya ƴyi mata duban tsaf sannan ya ce,
“yallaɓai ka yi hakuri bazamu baka madara haka nan ba saimun tabbatar da abinda ka faɗa dan haka inmun sallameku zuwa anjima sai kuzo da Maman babyn mu dubata”.
“Yanzu likita babu taimakon da zakai mana?”.
“Babu yallaɓai domin zuwanta zaisa mugane menene ainihin matsalar in za a bata maganine a bata in kuma babu damar hakan sai mu muduba wanne mataki zamu ɗauka abin da kuka sa fahimta shi ne.+
Nonon uwa na da amfani ga jariri kwarai da gaske kuma yana dauke da ruwa da abinci da sinadarai da dama waɗanda jariri yake bukata a watanni shida na farkon rayuwarsa. Akwai bambanci a lafiyar jaririn da aka ba nonon uwa da wanda aka ba shi nonon saniya (ko na akuya). Koda an ga jaririn da aka ba madarar shanu ya yi kato, sinadaran da ya sha a madarar (milk) ba ɗaya suke da na nonon uwa ba.
Yawanci akan samu sinadaran da suke karanci a madarar shanu, a samu wasu kuma sun yi yawa. A na uwa kuwa komai na nan daidai da bukatar jariri. Ruwan madarar (milk) uwa da abin da ke ciki canzawa yake idan jariri na girma. Kalar madara a kwnanakin jariri na farko ba fara bace, za a gan ta ɗorawa-ɗorawa (yellow in color,) wanda ba madara kawai ba ne a ciki, sinadaran sa wa jariri kwayoyin garkuwar jiki don hana kamuwa da cututtukan (infections) jariri. Bayan wadannan kwanaki sai ruwan ya canza kala (olor), ya kara komawa fari, ya kara suga (sugar) da sinadarai masu gina jiki, haka har yaro ya kai wata shida (six months), kafin ya sake canza ɗanɗano, ya kara yawan suga har ila yau da sinadarai daidai bukatar jariri. Haka dai har a yaye jariri. Sai an tabbatar (make sure) uwa ba ta da isasshen ruwan madara ne ake hakura a kara da madarar shanu (cow milk).
STORY CONTINUES BELOW

Ko kuma idan uwar tagwaye (twins) ta haifa, wanda a wannan yanayi zai wuya nonon uwa zalla ya ishe su. Ba a hada ruwa da ruwan nono (don’t compare breasth milk with water) tunda shi nonon yana ɗauke da iyakacin ruwan da jariri yake so. Manufar hana jariri ruwa a watannin farko (1st months of life) ba wai mugunta ba ce irin ta likitoci makar yadda wasu suke faɗa, a’a ana jiye wa jariri shan kwayoyin cuta ( to avoid infections) da ke cikin ruwan ne. Da yaro ya fara girma, kwayoyin garkuwar jikinsa sun yi karfi a wata biyar ko shida, to za a iya fara ba shi ruwa tsabtatacce (clean water), wato wanda aka tace aka tafasa. Ko ruwan roba ne ko na leda, an dai fi son a tafasa (boiled cooled water). Kayan ba da ruwan ma makar bulunboti, ana so duk bayan kwana biyu a tafasa. A waɗannan watanni ne kuma akan iya fara ba yaro dan abinci mai ruwa-ruwa, yawanci irin abincin gwangwani wadanda aka sa wa sinadarai na kara kuzari (a healthy supplement) da lafiya, wanda ba zai iya samu a nonon uwa ba.
An yi amanna yaron da aka yi wa irin wannan gatan da wuya ya samu matsalar gudawa (diarrhoea,pylorospasm and cough & catarrh)ko ta ciwon ciki ko mura da tari, wadanda cuttutuka ne da jarirai suka fi samu ta hanyar shan ruwa da kayan ba da ruwan irinsu cokali da kofuna (spoon & cup). Ko ya samu ciwon ma nan da nan zai fafi, domin kwayoyin cutar ‘yan kadan zai samu ba kamar wanda aka ba ruwa madarar tsabta ba. Ban da karin lafiys, shan nonon uwa na da muhimmanci wajen kara soyayya (mothers love) uwa da jariri. An yi amanna cewa jariri na son uwarsa fiye da kowace mace a duniya saboda shayar da shi (breasthfeeds) da take yi. Ba a taba ganin jariri ya guji mahaifiyarsa, duk saboda albarkan da ke cikin shayarwa”.
Jiki a sanyaye suka baro office ɗin Khalifa yaci layyar cin mutuncin Bahijja awarsu biyu suka bar asibitin zuwa gida.
Bahijja…..
Tun tafiyar Hindatu da Khalifa hankalinta ya tashi sossai, musamman yadda taga sun fita da yarinyar kamar mataciyya kannanta nata yi mata hira amma ta tafi kan tunanin wuyar data ci wajan haihuwar Ummyter karshe saita sa kuka duk suka saki baki suna dubanta ta dinga zazzaga musu masifa kamar taci babu ana haka taji tsayuwa motar su Khalifa ta kwasa ta yi wajen window tana lekensu babyn kwance a kafaɗar Hindatu tasa hannunta a baki tana tsotsa abu biyu ya tsirgamata lokaci guda tsoro da tausayi a haka suka ɓacewa ganinta suka shigo falon gidan ta sake kwasa tabi hanyar dazata sadasu da juna.
Suna shiga gidan ya soma kwalawa Bahijja kira,
“Bahijja! Bahijja!! Bahijja!!!”.
Tana laɓe tana jinsa tsoro ya hanata amsawa cikin sauri Hindatu ta tareshi,
“haba yaya wallahi na lura duk kai ka rikita lamarin nan wannan wana irin kirane? Ka cika zafin kai da saurin fushi duk kai kaja ta yi fushi mai tsanani haka kan me kaki jin ra ayinta kai kaɗai keda hakin sama ɗiyarka suna ne?. Ka bari in bita a sannu mu daidaita”.
Yana shirin magana ta katseshi,
“kabarmin komai”.
Da sauri ta nufi hanyar sashin Bahijja suka yi karo a bakin hanya suka yi turus suna duban juna sai ta sa hannu ta ɗauki yarinyar tana sharar hawaye hannunta taja suka nufi ɗaki ta zaunar da ita suka fuskanci juna sossai taga nadama a fuskarta ta dubeta.
“Bahijja daga yadda naga fuskarki nasan kin yi nadamar abin da kika aika. Hakan bazaisa hana in tunasar dake abin da kike neman yi wa kanki ba wauta ce baba Bahijja yau a wayi gari ɗiyarki ta mutu waya rasa? Kece idan fa yaso wata zai auro ta haifa masa wata kuma yasa mata sunan da bakyaso dole ki buɗe ido kikala. Abu na gaba kisani muhimmancin dake tattare de nononki a yanzu ya fi wa ɗiyarki komai a rayuwarta ta jarirantaka.
Bari in koma miki kan abin da muka tashi cikinsa kuma muke tafiya kan turbarsa. A mahangar addinin Musulunci yana ɗaukar mace ce a matsayin uwa mai muhimmanci a fagen rayuwa, saboda kasancewar mace a matsayin uwa hakan baya nufin kakkaɓeta daga hakkokinta ko katangeta daga gudanar da ayyuka da hidima a fagen rayuwar zamantakewar jama’a, don haka nau’in halittar mace da dabi’arta wasu babbar dama ce gare ta da zai bata sukunin samar da yara lafiyayyu kuma nagari ga al’umma. Duk da cewa babu mai musun cewa tabbas a lokacin da mace take dauke da juna biyu da lokacin haihuwa da kuma lokacin shayar da jaririnta da kuma tsawon lokacin tarbiyyantar da shi tana fuskantar tarin matsaloli da wahalhalu, amma ɗabi’ar kasancewarta mahaifiya da kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da jaririn da ta haifa hakan zasu shafe mata dukkanin wahalhalu da matsalolin da ta fuskanta a tsawon wadancan lokuta tare da jin yarda da aminci a zuciyarta.
STORY CONTINUES BELOW

Tabbas matakin da wasu mata suke dauka a wannan zamani a sassa daban daban na duniya na nisanta daga yaransu sakamakon ayyukan da suke gudanarwa a wajen gida, a fili yake cewa babu wani abin da zai maye matsayin uwa tare da zaman madadinta, saboda duk wani wajen rainon yara bai zai taba maye gurbin uwa a fagen nuna jin kai, tausayi, rarrashi, nutsuwa da kwantar da hankalin yaro ba. Sakamakon haka addinin Musulunci ya jaddada matsayin uwa a fagen rainon danta domin gadar masa da nutsuwa, kwanciyar hankali, aminci da zaman lafiyan jiki da na ruhi. Don haka yaron da ya samu babban rabo a tsakanin al’umma shi ne wanda ya samu cikakken kula da raino daga mahaifansa musamman karkashin kulawar uwa.
Haka kuma a kimiyance ma akwai bayanai sossai game da muhimmancin nonon uwa Bahijja. Hakika nonon uwa shi kadai zai iya rike jariri har zuwa watanni shida tare da gadar masa duk wasu matakan girman jiki da lafiya, don haka a tsawon wannan lokacin babu bukatar shayar da shi ko ciyar da shi wani nau’in abinci.
Ya zo cikin ruwaya cewa: Imam Ja’afar Sadiq {a.s} yana wasici ga matarsa cewa; Shayar da jariri nono daga dukkanin bakin nono biyu yana wadatar da jariri daga ruwa da abincin da yake bukata. Wato shayar da jariri daga bakin nono guda yana matsayin ruwan da yake bukata ne, sannan shayar da shi daga daya bakin nonon yana matsayin abincin da ke bukata.
Haka nan bincike na ilimi ya tabbatar da cewa; Ruwan nonon da ke fara fitowa mai ruwa-ruwa a lokacin da mahaifiya zata shayar da jaririnta, to wannan nonon yana matsayin ruwan da jariri ke bukata ne kuma yana kawar masa da kishin ruwa, sannan ruwan nonon da ke ci gaba da fitowa daga mahaifiya mai kauri, shi ne yake matsayin abincin da jariri ke bukata a rayuwarsa na wannan lokacin.
Haka nan farkon nonon da ke fitowa daga kirjin uwa bayan ta haihu mai launin yalo, wannan nonon yana dauke da wasu sinadarai masu amfani da kima kuma wannan ruwan nonon yana matsayin riga kafi ne ga jariri domin kare shi daga nau’o’in cututtuka, sakamakon haka mahaifa su tabbatar sun shayar da jariransu wannan ruwan nonon.
Har ila yau nonon uwa shi ne nau’in nonon da yafi duk wani nonon da za a shayar da jariri tsabta saboda nono ne da zai zuka kai tsaye daga jikin uwa, sabanin nonon da za a tatso daga dabba, ko nonon da ake sarrafawa daga kamfanoni inda a wani lokaci wannan nonon zai iya cin karo da wata kayar cuta kafin a kai ga shayar da jariri.
Hakika a kullum nonon uwa tsabtatacce ne kuma sabon nono da baya tsufa, sabanin sauran nonon da ake sarrafawa watakila akwai tsawon lokacin da ake diba masa domin yin amfani da shi, wato da zarar ya kai wannan wa’adi to nonon ya lalace kuma zai iya zama guba da zai cutar da lafiyar jariri.
Tabbas wasu kwararrun likitoci a fuskar kiwon lafiya da masana harkar shari’a suna da ra’ayin cewa; Nonon mahaifiya hakkin yaron da ta haifa ne, kuma babu wani mutum da ke musun cewa nonon uwa yana da tasiri a fagen samar da kwanciyar hankali da nutsuwa ga jarirai. Bahijja kada SON ZUCIYA ya rufe miki idanu don Allah”.
Kuka Bahijja take yi sossai tamkar ranta zai fita ta rungume jaririyar wani irin kaunar babyn ke shiga ranta. Da kanta ta yi feeding ɗinta daga bisani taje ta bawa Khalifa hakuri ranar haka suka yini suna walwala da farin ciki da yammaci Hindatu ta kira layin Ummi ta yi wa Bahijja barka tare da yi mata albishiri an mata takwara ai kuwa tasha murna sossai ta yi musu godiya amma bata yadda sunyi waya da Khalifa ba tadai ba Bahijja sakon ai mata godiya ita kuwa hakan da Ummi ta yi ya mata daɗi ta yadda yanzu Ummi bata ta tashi. Har musayar numba suka yi tare da alkawarin turomata hotunan Ummyter ta whattApp chat. Washegari su Hindatu suka baro Canada zuwa Nigeria Bahijja tasha kuka Khalifa keta aikin lallashi.
Kwanci tashi zama tsakanin Ummi da Haidar ya mika amma babu wata jituwar kirki cikin sati basu yi faɗaba su yi sau uku kuma shike takalarta. Tun da Haidar ya janyewa Fadila sai ya zama kullum cikin takura ya ke kasancewarsa mutum mabukaci kuma a tsarinsa ya raina Ummi gani yake rainashi zata yi hakan yasa ya soma kauracewa haɗuwa da ita baya dawowa gida sai tayi bacci makaranta ma ya daina ɗaukota amma ya hana kowa ya kaita ita take kanta da dawo. Hata ranar weak end baya zama a gida ficewa yakd training tun safe sai sha biyu da dare kuma makaranta ya yanki form yake zuwa cikin masallacin Usman bin Affan rayuwar Haidar ta koma abin sha awa shi kansa mamakin kansa ya ke bale kuma Ahmad. A gefe guda kullum Ummi cikin mikawa ubangiji kukanta take kan ya daidaita rayuwar Haidar bisa tafarkin tsira.
Misalin karfe takwas na ranar littinin Ummi ta shirya wa Haidar lafiyayan abin ci kan daining shiru bai dawo ba har tara ta mike taje ta sake yin wanka tasa kayan bacci harta kwanta taji ta kasa kwanciyar ta ɗauki waya ta kirashi wayar ɗif a kashe sai ta dawo falon ta kwanta kan doguwar kujera ta mike ba jimawa bacci ya yi awan gaba da ita kasancewar ana zafi ga kuma iska na kaɗata fil-fil.
Karfe goma daidai Khalifa ya kukkule ko ina na gidan ya shigo, yana sauke idonsa kan daining ya saki murmushi ganin abinci a kai saida ya bubbuɗa sannan ya juyo zai nufi sashinsa. Karaf idonsa ya sauka kan Ummi data mimmike tana kwasar baccinta.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin mutuwar jiki ya karasa wajan, ya daɗe yana kallonta gaba ɗaya gaɓɓan jikinsa sun amsa da wani irin amo mai wuyar fasaaruwa leɓanta da suka fita das madaidaita gasu pink sunfi komai fizgarsa. Bai yi aune ba ya samu kansa da sunkuya wa daidai bakinta ya ɗora laɓɓansa kan nata hannunsa kan dukiyar fulaninta kamar an tsikara mata allura ta farka. Bata gama tantance yanayin da take ciki ba ta yi masa wata muguwar ingiza ya yi baya ya zame tim a kasa ta mike tana kyalkyala dariya ta gyara rigarta. Ya yi kuri yana dubanta ta galla masa harara,
“kazamar kake taɓawa? Hmmm! Tafɗi jam kayi abin kunya”.
Kunya takaici mamaki suka hana Haidar kataɓus ta mike tare da gyara tsayuwarta ta rike kugu,
“kamanta sunana ne? Bari in tuna maka kwaila Bagidajiyya duk ni ka raɗawa dan haka ka kiyayi shiga rayuwata”.
Ta kaɗa kugu ta nufi hanyar ɗakinta ya rakata da ido, ya jima a zaune sannan ya mike ya wuce sashinsa abin takaici kaca-kaca ya sameshi bata gyara ba da kyar ya tattare ya watsa ruwa ya fito yana jinjinawa Ummi kasan ransa kuma yana jin zafinta bisa abin da ta yi masa zuciyarsa ta yi zafi kwaɗayin giya ya ɗarsu a ransa ya dafe kai yana gumi duk da ac dake ɗakin surar Ummi kawai yake yake hangowa cikin rashin sanin madafa ya mike zuwa ɗakinta.
Ummi tun lokacin data koma ɗaki ta yi tagumi tana tunanin rashin kyautar abin da ta yi wa Haidar amma tana tunanin dole ta nuna masa kuskuransa tunaninta ya katse lokacin daya shigo fuska ɗaure tamau sai ya fito mata zahin Haidar ɗin data sani cikin karfin hali ta murguɗa masa baki.
“Malam fitarmun daga ɗaki!”.
“Tashi ki zuba min abin ci kona tattakaki wallahi”.
Tuni ta mike jikinta na rawa dariya taso kwace masa ganin yadda ta tsorata sum-sum tabi bayansa suka nufi daining ta soma zuba masa. Tana gamawa ta mike zata bar wajan ya dakatar da ita,
“zauna in gama”.
Zama kawai ta yi tana gunguni da ɗan bakinta. Murmushi ya dinga zubawa yana kwasar gara tsiwarta ta daina bashi haushi kwata-kwata yanzu birgeshi take saida ya ɓata lokaci sannan ya mike,
“muje kimin aiki”.
Ta yi jim ya daka mata tsawa ta doka kafa,
“haba Yaya nifa nifa ni wallahi bacci nake ji”.
Yanayin da ta yi maganar yafi komai jan hankalinsa ya langaɓe kai yana dubanta sai ya yi gaba babu yadda zata yi haka ta bishi saɓalo-saɓola suna shiga ya wuce banɗaki,
“ki gyaramun ɗakina kamar yadda kika saba, kazama kawai kin barmun waje kaca-kaca”.
“Nifa ba kazama bace kaine kazami, inama laifina danake taimaka…..”.
Kallon da ya yi mata yasa tayi gum tana karasa batunta cikin ranta.
Zagewa ta yi tana kwasar aikin ga bacci na ɗaukarta ga aikin da yawa, shi kuwa ya fito banɗaki ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana dubanta komai nata cas yake yafi mamakin gashinta mai yawan tsiya amma iyakarsa kafaɗunta ya yi tumus a bayansa babu shanfo ba komai amma yana da santsi da baki sirrin gashin Ummi kuwa ruwan aloevera ne take shafawa lokaci lokaci man zaitun da man kwakwa da man kaɗanya kuma dasu take gyara gashinta dasu sai kusan karfe sha biyu saura ta kammala ta mike tana gangaɗi ya dakatar da ita,
“ina zaki?”.
Turo baki ta yi,
“kwanciya zanyi fa”.
“Kwanta a nan!”.
Cikin kaɗuwa ta ware ido tana dubansa.
***
Washegari da wuri Ummi ta tashi mamaki take wai ita ta kwana a ɗakin Haidar wani lokacin ta yi dariya wani lokacin ta ji haushin kanta abun duk ya ɗaure mata kai. Kwanci tashi haka suka shafe sati biyu tana kwana ɗakinsa wani lokacin in ta farka taganshi ya dukufa yana aiki kan kwamfuta wani lokacin kuma yana juyajuyye. Bangaransa kuwa kawai juriya yake kamar yau tun karfe goma suka kwanta amma misalin karfe sha biyu ta farka ta hangi Haidar a gefan gado yana juye-juye cikin tashin hankali ta birkita ta tashi gaba ɗaya tsoro ya gama mammayeta ta mirgina kusa dashi hannu tasa ta birkitoshi jikinsa ko ina rawa yake hakoransa suna karawa gab-gab ta kiɗime ta rasa yadda zata yi kawai saita kuka.
“Yaya me yake damunka?”.
Cikin rawar murya ya ce,
“Ummi cikina!”.
Sai idannunsa suka kafe ta saki kara da gudu ta mike ta nufi hanyar kicin har faɗuwa take a hanzarce faɗa kitchen ta suro ruwa mai sanyi ɗaya hannunta kuma lemon tsamine mai ɗan girma. Ruwan ta watsa masa amma ga mamakinta baya motsi, ta ɗaga hannunsa ya koma yaraf! Ta saki wata giggitaciyar……….
Ta saki wata giggitaciyar kara,hakan ya yi daidai da sakin kofin ruwan da tayi kan fuskarsa ya saki wata doguwar ajiyar zuciya yana kallonta kasa-kasa. Bata lura da farfaɗowarsa ba ta cigaba da raira kukanta, ya dinga kallinta dishi dishin idanunsa wani abu ya dinga zagaya zuciyarsa game da ita motsin da ya yi ya ankarar da ita ta yi saurin dubansa tana faɗin,
“sannu”.
Duk kuma sai ta ji kunya ta baibayeta ta zame daga jikinsa tana yi masa duban tausayi yunkurin jingina yake da gadon ya kasa fahimtar hakan yasa ta taimaka masa ta jingina shi.
“Ummi cikina ciwo yake”.
Ya faɗa yana rutse ido, ta yi diri-diri saboda yadda yaja hannunta ya ɗora kan mararsa yana danawa. Cikin dakiya take murza masa gurin yana numfashi kaɗan-kaɗan har ya soma sauke gumi ta yi dabarar janye hannunta ta matsa leman tsamin ta matsa masa a baki. Da kyar ya haɗiye sannan ya koma ya kwanta ta ɗan kishingiɗa kusa dashi. Ta jima tana juyi yana kallonta ya yi lamo kamar ya yi bacci sai da ya tabbatar da ta yi nisa a baccinta ya janta zuwa faffaɗan kirjinsa ya rufesu da mayafi saboda yadda jikinsa ya ke rawa.
***
Washegari haka suka tashi jikin da sauki, Ummi na kula dashi ƴhar zuwa yamma abin da ta yi masa ya yi masa daɗi sossai kuma ya kara mata matsayi cikin zuciyarsa.
***
Kwanci tashi asarar mai rai zumunci tsakanin Bahijja da Ummi ya mika sossai suna waya suna musayar msg ta chat hotunan little Ummyter kuwa basa kirguwa cikin wayarta. Hata Haidar ya san da zaman yarinyar saboda yadda Ummi take ji da ita akwai hotunanta guda biyu manya datasa aka yo mata ta kafesu a falo tanata dariya kowa ya shigo sai ya yaba hotan. Hindatu taji daɗin amincin Ummi da Bahijja a hankali suka haɗe kai suna wayar da ita illar abin da take, saboda tana yawan kawo karar Khalifa suka dinga nusar da ita sai gashi cikin kankanin lokaci ta zamo mace yar gaban goshi wajan Khalifa har mamaki yake yadda take sakin jiki tana faranta masa musamman fanin cima da bukatun gida.
STORY CONTINUES BELOW

***
Rayuwa na tafiya yadda ta kamata, al ammura da dama nata faruwa masu daɗi da akasinau. Cikin ikon Allah ranar Lahdi ɗaya ga watan july wanda ya yi daidai da cikarsu Ummi watanni takwas da aure. Zaune take tana ƴhaɗa ƴhandout ɗinta ya shigo babu sallama ya zauna ta saci kallonsa kasa-kasa.
Sai huci yake kamar wata mesa,
“mistss!”.
Yaja dogon tsaki ta sassauta duban da take masa,
“lafiya kake tsaki?”.
Ya tsareta da ido kamar zai furta ina ruwanki komi ya tuna sai ya kara jan wani tsaki.
“Ki shirya zamu je gaishe dasu da Daddy yanzu”.
Bai sake magana ba ya juya ya nufi ɗakinsa, wani tsale ta daka ta soma tika rawa kamar mazari ya juyo ya kalleta ta murguɗa baki kawai ƴya girgiza kai ya wuce sashinsa.
Cikin mintuna goma ta fito cikin shigar lafaya pink ta yi mata kyau sossai tasa takalmi hill baki da karamar jakarta baka sai zuba kamshi take ya dinga satar kallonta kai tsaye mota suka wuce ta ya tayar suka cilla titi. Gidansu Haidar suka soma shiga tun daga amsa sallamar da Hajiya Sadiya ta amsa musu jikin Ummi ya yi mugun sanyi. Suna zaune Baffa ya shigo yaji daɗin ganinsu sossai ya dinga yi musu nasiha daga bisani suka yi musu sallama suka nufi gidansu Ummi. Sun sha tarba sossai Ummu ta yi mamakin kyan da Ummi ta kara duk da cewar akwai rama tare da ita. Da zasu taho ta cikata da tsarabar turare da kayan girki suka yi sallama suka nufi gida.
Tafiya suke kowa da abin da yake rayawa cikin ransa har sun gota titin tal udu ya yi ribas ya juya kan motar ya sa hancin motar ta nufi layin mai akwai ta kasa tantance manufarsa kuma ta gaza hoɓasar tambayarsa a haka ya yi parking ɗin motar ya kasheta tare da furta,
“gidan uncle ɗina na kawoki bari mu shiga ku gaisa”.
Bata yi musu ba ta ɗaga kai tana karewa gidan kallo ras! Gabanta ya faɗi ganin gidansu Fadila amma saita ɓoye razanarta a filli ta furta.
“Ayya ashe ma gidan Mommyne?”.
Murmushi kawai ya yi ta kauda kai a ranta tana ayyana duk miskilancinka na fika.
Har suka shiga gidan babu wanda ya tankawa wani, sun shiga babban falon gidan suka riski Mommyn Fadila saida gabanta ya yi mummunar faɗuwa ganinsu tare ba wata kykkyawar tarba haka suka gama gaisawa suka mike jiki a saɓule kasa jurewa ta yi ta ce,
“Haidar wai ya maganar auranku da Fadila ne?”.
Dum! Maganar ta saukar masa kamar saukar aradu, amma ya kanne yana sosa sumarsa.
“Mommy babu ra ayin kara mace a tsarina ni MIJIN MACE DAYA ne ita kanta Fadila ta sani nasha faɗa mata matar da Baffa ya yi min ta isheni rayuwa ta yi hakuri in ta sami miji ta yi aure”.
Kasa magana Hajiyar ta yi ta dinga kallonsa a lallace saita sauke idonta kan Fadila data karaso ɗakin idonta taf hawaye.
“Haidar HAKA ZAKA YI MIN? Ni zaka tozarta ka wulakanta a idon duniya? Ina yi maka rantsuwa da Allah kasawa zuciyarka wannan shi ne BABBAN KUSKURE da zaka tafkawa rayuwarka”.
“Ya isa baby barsu su wuce sauri suke!”.
Cewar mahaifiyarta tana kokarin sakayya damuwarta, jiki a mace suka wuce suna bada baya ta saki kuka Ummi ta rintse ido tana jin kukan har cikin ranta saita sami kanta da jin zafi da tsanar abin da Haidar ya aikata koba komai mahaifiya ai komai ce danme zai tozartata a gabanta hakan yasa ta kwafeshi cikin ranta har suka je gida yana janta da fira amma kanzil ta kasa furta masa.
Fitarsu Haidar keda wuya Hajiyan Fadila taja waya ta soma yi wa Hajiya Sadiya tijara ai kuwa ta sosa mata in da yake mata kaikayi hakuri ta dinga bata ta suri wayar Nabila ta kira Haidar bai ɗaga ba yana banɗaki tana shirin sake kira Baffa ya kirata saita mikawa Nabila kiran daya soma shiga daidai lokacin Ummi ta ɗauka saboda yana ɗakinsa wayar na falo da sallama ta soma amma sai Nabila taja wani mugun tsaki,
“mitssss! Duk abin da aka haɗa da jaki sai yaci kara, ke yanzu ko kunya baki ji ba an tsamoku cikin talauci shi ne kika shiga kika fita kike kokarin hana Aunty Fady shigowa gidan da tuni dama dan ita aka yishi? Karfa ki manta ubanki ɗan dakone”.
“Dakata Nabila!”.
Ta faɗa cikin karaji da tafasar zuciya,
“ashe baki da kunya baki da mutunci? Nayi mamaki kwarai da kika ɗauki ɗabi ar gori tare da yayyata alkhairin da ka aikata koda yake abun gadone. Ina so kisani ruwa ba sa an kwando bane kuma wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa ina yarinya ma bari in tuna miki saikun haɗu ke da shi da Fadilan kuke nasara kaina bale yanzu kunyi sake yar zakanya ta girma. A karshe ina shawartarki.
Idan kika kyautatawa mutane kada ki ta6a zaton samun wani abu daga gare su a madadi. Idan za ki yi abu ki kyautata niyyarka ki yi saboda Allah kawai ba saboda halin mutane ba, wasu tun can dama ba su da kirki. Kuma da kike ikirarin an taimakawa ubana ki faɗamun wa ubanki yake dashi a duniya madadin nawa uban? Na gode Allah komai rashin kirkin ubana wallahi ya fi….hmmm Nabila kenan ki sani idan za ki tuna cewa a lokuta barkatai kin yi wa mutane dare sun maki rana, a lokuta na gaba kuma masu zuwa ba wanda za ki tura inuwa dan haka ki yi kokarin gyara zuciyarki wallahi. Kar ki taba ɗaukar dabi’ar yayata alkhairi ko kyautarki ga makaskantanki, misali kin yi ta cewa na yiwa wane abu kaza a lokuta kaza, waɗannan duk batutuwa ne da za su zo6ar da ladanka koda yake na fahimci gado…..”.
Maganar ta katse sakammakon fizge wayar da aka yi, ta ɗago a hanzarce tana dubansa idanunsa sunyi jajjur dama tana ciki dashi saita kara jin tsanarsa fal ranta ta kankance ido tana yi masa duban baka isa ba.
Kallon kallo suke yi tsakaninsu, ya dinga jin kamar ya shaketa ya huta a hankali laɓɓansa suka motsa ya furta,
“hasbunallah”.
Sai ya juya ya samu bakin gado ya zauna, Ummi duk saita muzanta tasani sarai ya gano shaguɓan da takewa Nabila da Mommynsa take saita samu kanta da jin zafin abin da ta aikata zubewa ta yi tare da rike kafaffunsa,
“don girman Allah ka yi hakuri”.
Sai yaji zuciyarsa ta yi sanyi, mikar ta ida ya yi tare da furta,
“is ok! Kidinga tauna magana kanki furtata kedawa kike waya?”.
Kanta kasa ta kasa ansawa sai ya ɗauki wayar ya duba murmushi ya saki tare da cewa,
“dama wai Nabila ce, ni na ɗauka da Mommy kike waya”.
Ita dai bata tanka ba ya mike tare da cewa,
“oya jeki ɗauro alwala kizo mu yi sallah”.
Gabanta ya faɗi dam! Amma ta kanne murya na rawa tace,
“nayi sallah”.
“Wata zamu kara umarni na baki ba shawaraba”.
Mikewa ta yi saɗaf-saɗaf ya raka bayanta da idanu tare da lumshesu yana mamakin abin da ke fuzgarsa game da ita. Cikin nutsuwa ta fito ya shimfuɗa darduma ya tayar da sallah bayan sun idar ya dinga kwararo addu a mamaki ya daskarar da Ummi saida ya gama ya shafa sannan ya dafa goshinta ya yi addu a tare da sauke hannunsa. Da kansa ya taimaka mata ta sha fresh milk mai sanyi tare da kankana daga bisani ya kashe musu hasken ɗakin.
*ASUBA TAGARI A SQUARE*
*************
Washegari Ummi tasha sa albarka wajan Haidar ko falo bai barta ta fito ba hata break waya ya yi wa Aminu Hindatu ta aiko musu dashi haka suka kasance har zuwa dare ko motsi ta yi sai ya tambayeta,
“Ummyter lafiya? Me kike so? Ina yake miki ciwo?”.
Misalin karfe takwas na dare suna zaune a falo yayi mata matashin kai da cinyarsa duk kunya ta dabaibayeta a hankali ya lallubi kunnuwanta.
“Ummyter wannan kunyar zata bari ki nunamun kulawa kuwa?”.
Ta turo ɗan bakinta tana tureshi,
“ni dai ka daina kunyarka nake ji”.
“Hmmm! Ayshaaaaat!”.
Yanayin daya kira sunan yasa tsigar jikinta zubawa,
_”when i say that i want to be by your side, to hold your ƴhand, to treasure you in the morning and in the noon-tide, to be next to you, to be held close to your heart now and for the rest of my living years, to comfort you, dry your tears and calm your most frightenning fears, to fight your battles and show no shame to scream my love for you out loud all over the land_”.+
Ma ana
”’Yayin da nace ina san kasancewa kusa dake, na rike hannunki na yi tattaki dake da safe hakama cikin farin wata, na zamo majiɓancin al ammuranki, na karɓu a cikin zuciyarki. Yanzu da kuma dukanani shekarun da suka ragemin. Na sanya ki cikin nishaɗi, na share hawayanki sannan na kwantar da dukkanin tsoron da yafi damunki, nayi faɗa a madadinki sannan kuma na cire kunya wajan shelanta soyyayata a gareki kowa ya ji”.”’
Kasa motsawa ta yi gaba ɗaya ya yi mata dabaibayi wajan jin kunyarsa, wani abu data kasa tantance ko menene ya dinga zagayata jikinta gaba ɗaya ya sauki rawa fahimtar yanayin data ke ciki yasa ya sureta cak sai shimfiɗar baccinsu.
*ASUBA TAGARI AL’ASH*
***
Hankalin Fadila da Mommynta ya tashi sossai, musamman yadda suka fara ɓarin kuɗi wajan Malamai amma kash abun babu wani cigaba sai tulin wulakanci da take samu daga wajan Haidar ko wayarta ya daina ɗagawa. Rayuwar Haidar ta zamo abar sha awa shi kansa har mamakin kansa ya ke. Duk wani wajan sharhiliya ya ajiyeshi gefe baya tatashi bale giya kwata-kwata baya mararin shanta duk kuwa randa aka yi saɓani ta bijiro masa ya tsotsa tu kuwa yana shiga gida ƳUmmi idonsa kaɗai take duba ta gane hakan nan zata tsurashi da tambaya in kuwa ta samu tabbaci kwana suke rigima dashi babban horan da take masa shi ne kauracewa shimfiɗarsa hakan yafi komai ɗaga masa hankali.
***
Ranar Littinin da yamma Haidar ya dawo aiki da wuri kasancewar bata da lacture a gida ya sameta ta yi kwaliya cikin english wears data fahimci yafi kaunarsu da murmushi ta tareshi ya kanne ido,
“tawan wani kyau kike karawa wallahi, karatunma baya wahalar dake wai menene sirrin?”.
“Hmm kai ne sirrin ai”.
Ta faɗa tana har da ido ya kwashe da dariya, ya wuce sashinsa ta bi bayansa ya juya yana ɓale maɓalan rigarsa ta kwanta tare da sakala hannuwanta a wuyansa ta lumshe ido shima haka sassanyar ajiyar zuciya ta saki tare da furta,
_”The pain in side my heart is no more, the chemistry that felt was like mistery. All the hidden thing now are unhidden. We are now, two hydrogen, bonded together that is true love Haidar! I love you_”.
Ma ana,
_”Zugin dake zuciyata ya gushe, abubuwan da naji a baya ya zama tamkar almara. Dukkan abubuwan da suka ɓuya a gareni yanzu sun bayyana. Mun kasance yanzu tamkar sinadarai guda biyu da muka haɗe gu guda wannan shi ne son gaskiya Haidar ina sonka!”._
Ta karasa furucin da sautin jan hankali, ya birkitota tare da kafeta da tsauraran idanuwansa,
_”Ummyter tell me do you love me?”_.
_”Yes i love you”._
Ta faɗa tana sadda kanta kasa alamun kunya, ya girgiza kafaɗarta,
“repeat it again please Ummyter…..”.
Saita zame tana dariya ya kai mata cafka ta kauce haka suka dinga zaga ɗakin, har suka fito falon da kyar ya cafketa suka zube suna dariya tare da maita numfashi. Daidai lokacin aka turo kofar falon, ya runtse ido cikin sauri ya cukuikuyeta ya yi mata rumfa ruf ya kifu a kanta murya a kaurare ya so ma magana,
“Ahmad ubanwa ya ce ka shigo min gida babu izini? Konan ma bariki ne wannan ai iskanci ne”.
Ahmad kasa motsi ya yi cikin karaji ya furta,
“ka fita nace maka!”.
Sai ya yi baya kamar mai bin umarni ya fice a hankali ya ɗagota tare da sakin ajiyar zuciya yana kallon kwanciyar kwala a idonta ransa ya ɓacci sossai,
“kiyi hakuri Ummyter”.
“Ya wuce kai zan ba hakuri, amma ka yi kokarin nusar da Ahmad kuskuransa idan kuma bazaka iya ba kabarshi babu alfanun abota da mutum mai raunin ɗabi a. Ibn Hibban yana cewa: lallai mai hankali kada yayi abota da kowa sai mai kyakkyawan ra’ayi, mai Ilimi da Addini, domin hakan yana nuna kai mai hankali ne. akwai wani tsohon Karin Magana da ke cewa “gaya mun abokin ka sai in gane kai waye (show me your friend I tell you who you are)”.
STORY CONTINUES BELOW

Tsam ta mike ta bar falon ya rakata da idanu, zuciyarsa fal takaici dan ma ya godewa Allah kayan jikinta ba wasu masu bayyana jiki bane dogon skert ne sai riga me dogon hannu kanta kuma hula ce kalar kayan amma sun mata das!.
Da sauri ya fita waje yana shirin ci masa fuska sai ya tsaya turus ganin ba shi kaɗai bane ya yi kokarin aro juriya ya nufesu yana mimmika musu hannu abokansa ne dukkansu Sulaiman da Abdullahi sai Mahmoud da kuma Ahmad ɗin bayan sun gaisa ya zaro wayarsa,
“Ummyter zan shigo da baki”.
“To”.
Kawai tace a takaice murya a cunkushe ya yi sakaro sai ya wayance ya yi musu izini suka wuce ciki saida hayaniyarsu ta lafa sannan ta fito cikin hijab dogo har kasa mai hannu suka gaisa ta mike zuwa kicin ta kawo musu ruwa da lemo sai snack sannan ta soma tunanin abin da zata shirya musu. Cikin mintuna talatin ta shirya musu jallop ɗin makaroni data ji kayan lambu ta shirya daining ɗin. Ta ajiye tare wucewa sashinta cike da nutsuwa Abdullahi ya bita da ido Haidar ya kai masa duka cike da haushi,
“daina kallonmun kayana”.
Dariya suka yi Ahmad dai baki ya mutu ya kasa magana shi ya kagu a bude abincin kamshi ya cika masa ciki ganin basu da niyyar buɗewa yasa ya buɗe abincin zai kai baki Haidar ya dakatar dashi,
“kai baho baka yi basmala ba fa”.
Dariya suka yi Mahmud ya ce,
“ya yi mijin ustaziyya”.
Sulaiman ya yi murmushi ya ce,
“wallahi rayuwar Haidar birgeni take, ku dubi yadda ya yi fresh dashi sai dai kuki faɗar gaskiya nidai da Abbunta nada ɗiya wallahi sai naje na aura domin ni dai naga illar auran wayewa”.
Haidar ya lumshe ido yana tuna hirarsu da Ahmad ta kwanaki, Mustapha ya ce,
“hmmm! Wallahi maganar Sulaiman gaskiya ne babu wani mutunci ga auran macen da take takamar yanci duk da ba dukane suka zamo ɗaya ba amma na kirkin kalilan ne shi yasa ake musu kuɗin goro in ka aura kai babu kwanciyar hankali babu cimma mai kyau bale tsaftar gida da muhalin kwanciya sai kaga kan aje ko ina aure ya mutu ana yayyato”.
“Hmmm! Duk da wannan Sulaiman kuma da rashin gina soyayya da muke kan tafarkin addinni mun kauce hanya dole muga ba daidai ba”.
Cewar Haidar yana shafa kansa duk suka ɗauka,
“hakane Allahsa mu dace amin”.
Sun jima suna tattaunawa, daga bisani suka yi musu sallama suka bar gidan sunata santin rayuwar Haidar har waje ya rakasu ya dawo shiru babu motsinta ya tura kofar ɗakin gabansa na bugun uku uku.
Ajiyar zuciya ya saki ganinta wasai ya buɗe hannuwansa da sauri ta faɗa kirjinsa ya maida ya rufe ya dinga zagaya ɗakin da ita.
***
“Gaskiya Fadila ki kara sauri garin fa akwai nisa wallahi”.
Cewar Hajiya Kharimahtu kenan wadda ke gefan Hajiya Sadiya ita ko ta yi jigum tana mamakin ina Karimatu tasan wannan kungurmin dajin mai nisa?. Nabila ta yi murmushi ta re da saka earpice a kunne sai da suka yi tafiya mai nisa suka karaso wajan wani katon fili mai kwazazzabai sannan ta ce Fadila ta tsaya suka fito tare da yin cirko-cirko. Wasu kataine suka bayyana aifa Nabila kurma ihu ta yi suka daka mata tsawa ga mamakinta sai taga sun nufi Mommy Karimatu suna gaisuwa kuɗi ta mika musu sannan ta basu ajiyar mota ta dubesu,
“uban arna yana nan?”.
“Yasan da zuwanki?”.
Wata murya ta karaɗe ilahin fillin, take Nabila ta saki fitsari a wando gaba ta yi suka bita a baya tafiyar awa ɗaya suka isa wani katon tsauni mai matattakala nan fa suka hau tattare zannuwa suka haye matattakalar Fadila kuwa bata da matsala dama wando tasa dogo.
Tunda suka shiga Nabila take karewa bokon kallo, murjejen mato bakikkirin dashi hancinsa katoto idanunsa manya hakinsa wagege komai nasa kato ne yana katon tumbi ga wata suma kansa cukurkuɗaɗɗiya tumus hakoranankuwa yalaye shar sai tashin wari ya ke yi suka zube Hajiya Sadiya sai makyarkyata take ya dinga kyalkyala dariya wadda ta dinga amsa amo cikin dajin daga bisani ya yi gum. Hajiyan Fadila ce ta yunkura zata yi magana ya dakatar da ita,
“kun zone kan batun Ummi da ɗanki ko?”.
Ya faɗa yana tsaida idonsa kan Momy ta ɗaga kai da sauri. Ya yi dariya tare da ɗauko izgar bakin doki ya yarfa wani ruwa mai tsananin ɗoyi a jikin wani madubi a hankali ya yi duhu sai kuma ya washe walai saiga hotan Haidar zaune a office yana yi wa wani yaro allura duk suka cika da mamaki ya janye hota sannan ya sake watsa ruwan shiru babu komai. Ya runtse ido yana karanta wasu dalamusan tsafi ɗakin ya ɗauki girgiza ga wani zafi kyau amma babu hotan komai madubin yayi jajjur ji kake tas! Ya tarwatse bokan ƴya saki karar takauci. Su kuwa saida suka sami kurumta ta ɗan lokacin.
“Wannan tafi karfinmu amma da sannu za miyi galaba a kanta, shi kuma wannan yana addu a amma ita tafishi himma dan haka dashi zamu soma da zarar ta shiga gidan aikin zai yi sauki”.
STORY CONTINUES BELOW

Sake nuna wani mudubin ya yi hotan Haidar ya sake bayyana kansa ya nuna kirjinsa take hotan zuciya ya fito ya cigaba da nunata wani bakin abu ya dinga shigarta har bakin abun ya kare. Ya yi wata shu umar dariya take hotan ya ɗauke, ya ɗauko wani bakin yanki ya mika musu.
“A yanka bakin sa a taro jinin a kofi a zuba a yanki a ajiye hadimanmu zasu zo su ɗauka. A tabbatar yayin zubawar babu wanda ya gani”.
Jikina rawa Hajiyan Fadila ta zube masa kuɗi naira dubu ɗari biyu suka fito har bakin motarsu suka bar wajan. A hanya suka dinga yi wa kansu dariyar tsoratar da suka yi Nabila kuwa duk saita raina kanta tana jin wani abu yana damun kirjinta kamar damuwa game da batun amma ta kasa gasgata hakan.
***
Haidar yana zaune cikin office ɗinsa ya dinga jin wani ɓacin rai naba gaira babu dalili haka ya daure har zuwa dare gashi yana da marasa lafiya da yawa sai isha ya wuce gida. Ummi ta wani ganshi a birkice ba yadda ta saba ganinsa ba sai ta yi masa uzurin aikine kawai haka suka kammala komai suka shirya suka kwanta.
***
RUDANI……….
Cikin matsanancin gudu take wuce tsaunika tare da tarin bishiyu, taka ‘kayoyi take amma hakan baya d’aya daga cikin abinda ya dameta, burinta kawai ta tseremata daga mummunan nufinta a kanta, Fadila ce ke binta da wata shafcecciyar suka sai sheki take tana kyalkkyala dariya shi kuma Haidar na gefe yana ɗaɗɗaure cikin wata irin sarka sai kuka yake yana kiran sunanta, cikin rashin tsamani ta taka wata
‘katuwar ‘kaya mai tsanani kaifi. Take ta ‘kwala giggitaciyar ‘kara hakan yai dai-dai da farkawarta. Cikin hanzari tabi ‘kafarta da kallo abinda yai matu’kar tsorata ta. ‘Kayar data taka a mafarki gata a tafin ‘kafarta ga jini na bin
‘kafafunta cikin tashin hankali ta soma waige-
waige. Shiru garin babu motsin bil’adama sai
kukan karnuka da tsuntsaye. A hankali takai kallonta kan ‘kofar d’akinsu cikin sakan guda cikinta ya bada wani sauti. ‘Kuuuuuuuuuu! Sakammakon ganin inuwar mutum ya gilma da wuka ta takarkare ta saki karar data farkar da Haidar ta rugungumeshi tana faɗin,.
,”zata kashe ni Haidar zata kasheni”.
Mamaki ya rike shi ya kasa motsi, cikin tsoro ta dinga ja da baya tare da karanto duk adu’ar data zo bakinta. Ta runtse idonta ta jiran ‘karasowar ‘KADDARARTA ya ƴyi hanzarin riketa tare da mannata a kirjinsa kunnuwanta ya lalluba yana karanta mata innalillahi a hankali ta yi ajiyar zuciya ya dinga jijjigata kamar baby ta yi luf a jikinsa. Sun share kusan awaya ɗaya tana firgita daga bisani bacci mai nauyi ya ɗauketa, ya jima yana kallonta kannan ya kwantar da ita ya mike ya ɗauro alwala. Da asuba da kyar ya tasheta ta yi sallahr asuba ta ta kwanta.
Washegari har takwas da rabi Ummi bata farka ba, sai misalin karfe tara lokacin Haidar ya kammala komai ya tasheta ta buɗe ido tana karewa hasken daya ratso kallo ta sauke idonta kan agogo wanda ya nuna karfe tara ta mike tana zare ido kai tsaye banɗaki ta faɗa ta wanke bakinta tare da kintsa jikinta ta ɗora zani kan rigarta gaisheshi ta yi ya amsa yana murmushi mamakin ruɗewarta yake yana kallonta ta fice ɗakin yabi bayanta a falo suka yi kiciɓus tana shirin dawowa.
“Muje kiyi wanka muzo muyi break please Ummyter”.
Ta kafeshi da ido,
“a sanina baka cin abincin yan aiki, bani nayi ba taya zaka yi break ko Hindatu kasa?”.
Cikin basarwa ya shafi sumarsa, ya ware hannu alamun ban saniba ta langaɓe kai tana dubansa cikin shagwaɓa.
“Allah ni saika faɗamun”.
Dariya ya yi yaja hannunta har kusa da daining ɗin sannan ya bubbuɗa tea ne da agade da soyyayan kwai,
“fansarki na yi Ummyter banasan katsemiki baccinki naga kinajin daɗinsa shiyasa kuma jiya baki yi bacci ba”.
Murmushi kawai ta yi suka suce ɗaki ta yi wanka daga nan suka dawo suka yi break. Duk yadda yaso ta fada masa abin da ya tsoratata taki kawai sai dai tace masa ya taya ta addu a da haka suka yi sallama ya wuce ƙoffice. Bayan fitarsa ta kira Ummu ta yi mata bayanin komai jikinta ya mugun yin sanyi ta numfasa ta ce,
“ki cigaba da addu a Ummyter musamman azkar ɗin safiya da yamma”.
“To Ummuna na gode a gaida Abbu”.
Da haka suka yi sallama.
***
Kwanci tashi a hankali rayuwa ta soma yi wa Ummi tsanani, dan ma mace ce mai juriyar addu a kwata-kwata Haidar ya daina sakar mata fuska ko abinci ta yi baya ci ga tsananin haushinta daya ke ji shi da ita sai hantara sai gwaliya nan da nan suka koma zaman yan marina. A bangare ɗaya kuma alakarsa da Fadila ta koma sabuwa fil, sai ya kai sha biyu bai shigo gida ba. Hankalin Ummi ya yi masifar tashi kullum cikin kaiwa ubangiji kukanta take. Ga wani zazzaɓi da take fama dashi sai dare ta yi ta rawar sanyi abin da bata sani ba karamin cikine take ɗauke da shi wanda bata san da shigarsa ba. Hata Hindatu ta fahimci sauyin dake tattare da Ummi amma in ta tambayeta amsa ɗaya ce ba komai.
***
Ganin yadda Haidar ya dawo wajan Fadila wuta, wuta yasa suka ɗaga maganar aure bab jin kirtawa ya amince ya tinkari mahaifinsa bai hana shi ba nan da nan aka tsaida lokaci su Abbune suka kai kuɗin aure aka tsaida komai sossai mahaifin Fadila ya yi murna da auran dan ya gaji da ganinta sakaka a gida kuma bai da damar magana mahaifiyarta ta ce ya matsa mata. A haka aka cigaba da batun aure har ya rage saura kwana biyar ɗaurin aure. Ummi dai taga an buɗe sashin bayanta an gyarashi tare da goge kurarsa bata kawo komai cikin ranta ba saboda wanda zai mata bayani baya tatashi wani lokacin ta yi kuka tana hangen dama Haidar yaudararta ya yi kawai ya yi ya rabata da abin da yake kulafuci. Wani sashin kuma na zuciyarta na karyata hakan.
***
Ranar littinin tun da ta farka ta yi shirin makaranta gabanta yaketa faɗuwa, haka ta daure a daddafe ta wuce makaranta bayan ta sauke Habiba a makarantar tahafiz ɗin data sata wadda take zuwa daga safe zuwa yamma. Bayan sun fito lacture suna zaune ita da Hindatu suna duba littatafansu ta hango tawowar Nabila gabanta ya faɗi ta ɗauke kai daidai lokacin data karaso wajan ta dubesu a lallace tare da faɗin.
“Shi ne kika ɗauke kai kamar kinga kashi?” .
Bata tanka ba daga ita har Ummin suka mike zasu bar wajan ta watsawa Ummi wasu katuna kan fuskarta da sauri ta wuce zata bar gun Hindatu ta sunkuya ta kwashi katunan take idanunta suka fito fuskarta na nuna razana da abin da tagani bakinta ya suɓuce ta furta,
“Haidar!”.
Nabila ta kyalkkyale da dariya cikin shammata Hindatu ta yi niyyar ɓoye katin caraf! Ummi ta warta ta soma karantawa.
Runtse ido ta yi wani gishiri gishiri taji a bakinta cikinta ya yi wata muguwar murɗawa a hankali ganinta ya dusashe bata sake sanin in da take ba………
STORY CONTINUES BELOW

Cikin matukar tashin hankali take jijjiga Ummy bakinta na faɗin,
“Ummyter! Ummyter!! Ummyter!!!”.
Amma bata motsi ga jini na bin kafaffunta ta rikice da kyar ta samu yan ajinsu suka taimaka mata ta sata a mota gudu take na tashin hankali kafin ta karasa ta yi parking ta kira Aminu tana yi masa bayani daidai lokacin yana tare da Haidar bai kasa a guiwa ba ya sanar masa. Suna tsaye cirko cirko ta yi parking duk suka nufota suna tambayar dalili cikin tsana ta dakatar da Haidar.
“Karka taɓata mugu kaine sillar komai dama so kake ta mutu!”.
Baibi takanta ba ya sureta duk jini ya ɓata motar suka yi ɓangaran taimakon gaggawa da ita. Yana direta ta buɗe ido ta kalleshi,
“Haidar!”.
Ta furta daga nan idonta ya yi lau komai ya daina motsi a jikinta tamkar ta mutu. Duk yadda likitoci suka kai ga bincike Ummi dai bata farfaɗo ba, sun dai yi nasara jinin ya daina zuba haka ta kwana cikin yanayin rai kwa kwai mutu kwa kwai
Two days………….
CIKIN ASIBITI
A hankali Ummi ta soma buɗe idanunta harta kai ga buɗesu duka, cikin rashin fahimta ta dinga duban mutanan dake kewaye da inda take. A hankali ta fahimci a asibiti take idanunta ya sauka Ummu dake share hawaye sannu a hankali komai daya faru ya soma dawowa cikin kwakwalwarta ta dafe kai tare da kwala kara duk hankalinsu ya dawo kanta suka ɗiba ɗuuu sai bakin gadon. Cikin kuka take nuna Haidar,
“karka karaso in da nake wallahi”.
Gaba ɗaya jijjiyoyin jikinsa suka ɗaure ya dinga satar kallon Ummu babu sauyi ko ɗaya tatare da fuskarta bai tanka ba ya fice Hindatu ta rakashi da harara. Haidar ya yi jigum a waje ya rasa abin da yake damunsa a haka Hindatu ta riskeshi tazo wucewa ya dinga yi mata magiya ta faɗa masa matsalar Ummi da kyar ta tsaya ta yi masa bayani ai kuwa ya shaka ya dinga makakinsu saboda su suka hanashi sanar mata wai karya tayar mata da hankali baice komai ba kawai ya wuce gida a falo ya samu Nabila babu tambaya ya zare belt ya yi mata dukan tsiya.
Bayan fitar Haidar ne Ummu ta dinga yi wa Ummi nasiha, jikinta ya yi sanyi sossai ta dinga share hawaye. Kwananta uku a asibiti kullum sai Bahijja ta kira ta yi mata ya jiki Abbu da Baffa duk sun zo dubata amma banda Nabila da Momy da kuma Fadila hata mahaifin Fadila ma sai da yazo dubata. A ranar kwana na uku ne da dadare aka salameta suka koma gida. Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji jikin Ummi ya yi sauki shirye-shiryan biki babu abin da aka fasa tana kallonsu ta zuba ido.
Ana gobe ɗaurin aure da yamma Haidar ya shigo sai washe baki yake ta kalleshi ta ɗauke kai, ya wuce kunnansa like da waya yana amsawa tamkar babu mutum a wajan ta runtse ido tana jin takaicin abin da ya yi mata amma data tuna cewar likitoci sun ce ta daina damuwa saboda cikin jikinta saita mike ta wuce ɗakinta bata fi minti biyar da zama ba aka turo kofar ɗakinta ta ɗago fuska taf hawaye ganin Ummu yasa jikinta yin sanyi tana kokarin ɓoye hawayen amma ta makara saita taso da gudunta ta rungumeta tana kuka sun jima a haka daga bisani ta jata suka zauna.
“Ummyter nasani da ciwo amma kiyi hakuri kowace mace haka take ji in za a kara mata abokiyara zama kada ki ɗauketa kishiya ki ɗauketa abokiyar zamanki hakan zai sama miki sassaucin kishinta cikin ranki sannan abu na gaba ki kula da kanki kada zafin kishi yasa ki sauya wa mijinki daga kyawawwan ɗabi unki zuwa wasu daban shi namiji ba a nuna masa haukan kishi domin lokacin da kike bore lokacin yake ɗaura ɗamarar yin abin da zai kuntata miki. Ki zamo mace mai hakuri da kauda kai abisa duk abin da zai aikata miki ba ruwanki da shiga sabgar daba taki ba karki kasance mace mai riko shine idan an aikatama wani laifi kabar abin a ranka ba tare da ka yafe ba uwargida ta riki maigida a zuci sakamakon wani abu ko maigida yana sa ta fita daga zuciyar miji duk sanda namiji ya yi miki wani abu yana sani ko bai sani ba to ki samu wani lokaci da yake cikin nutsuwa ko yake cikin nishadi ki nuna masa cikin tausasa harshe misali
“wane kayi min kaza nasan in Allah ya yarda zai ɗau kuskuren shi kuma za ki kuma shiga zuciyar shi
YAWAN MITA
Mata da yawa nada yawan mita-duk macen da take da yawan mita in anyi abu baya wuce wa to zata dinga sanewa maigidanta kuma bata fiya darajab. Ko kuma kiga mace abu kaɗan ta ɗauki fushi mai tsanani ki sani duk mace mai yawan fushi idan sun dan samu sabani da maigida mafi yawanci da namiji idan kuka sami dan sabani in ya fita ya manta to ke ki ringa yin fushi ko ya dawo ki dra sabon fushi yana sa mace ta fita daga zuciyar namiji yana da kyau mace ta dunga kai zuciyarta nesa. Babbar matsalar matan yanzu musamman matasa rashin inya girki, wasu kuma sun iya son jiki ne kawai da kuiya to fa kisani girki-wani ginshiki ne na sinadarin zaman aure rashin iya shi yana kawo matsala tsakanin maigida da uwar gida in dai har baya samun jin dadin abincin da uwargida ke yi har yaji abincin da zaici na waje yafi na gida dadi matsala ta faru domin yana ragewa uwargida daraja iya girki yana sa maigida yaso uwargidansa idan maigida ya wadata iyalinsa da abinci to yakamata uwargida ta tsaya tsayin daka wajan ganin ta iya salo -salo na tasarinfin abinci a hakikanin gaskiya tattalin arziki yana tasiri wajan wadata komai to amma bahaushe yace da ruwan ciki wai ake jan na rijiya don haka yar uwa in dai har zaki kula da abin da maigida zai ci ba wai kullum abu daya ba ki kasance ko wane fanni na girki kin kware akwai marubuta da sukayi kokarin rubuta littafan koyon girke girke yana da kyau uwargida ta nazarci irin wadannan littafan don koyon salo salo na girki duk sanda maigida ya dawo zai tarar kin gama komai na abinci sannan akwai wani sirri na girki da yawanci maigidanta suka fi so shi ne duk sanda mace ta kawowa maigida abinci ta zauna a gabanshi yana ci kina yi mishi hira mai dadi rashin haka yana sawa mace ta fita daga zuciyar namiji.
Sai babban batu Ummi bar ganin ni mahaifiyarki ce wannan bazai zama shamaki tsakanina da ke ba na in warware miki abin da zai amfaneki ba komai nauyinsa rashin biyawa maigida bukatarshi wajen kwanciya illah ce babba da take kawo taɓarɓarewar aure duk sanda maidiga zai neme ki za ki yi raki ko ki tsaya jin kunyarshi yana sa mace ta fita daga zuciyar maigida amma in har mace zata zama mai jure bukatar mijinta tare da rashin gajiyawa ko tana so ko bata so karta yadda ya gane ko da tana cikin halin _(period)_ ne akwai hanyoyi da dama da zaki gamsar da shi”.
Kanta a kasa ta furta,
“Ummu na gode”.
Sun jima suna hira tana kara bata shawarwari daga bisani suka yi sallama ta wuce, bayan tafiyarta ne saiga Hindatu da Sabah natu sun taimaka mata sossai ta gyara ɗakinta harda guzurinsu na base flowers da kuma tarin kwalaban turare cike da turare da labulaye sababi duk suka sauya nan da nan ɗaki yasha kwaskwarima ya haɗe. Ranar Juma a ɗaukacin mutane duka shaida ɗaurin auran Aliyu da Fadila an yi bushasha an yi ɓarin dukiya sossai da yammaci aka kawo amarya sashinta Ummi tasha habaice-habaice amma dake yar halak ce ta tafasa bata ce musu ba bale ta kone. Bayan watsewar yan kai amarya ta zauna jingum saboda Hindatu ta tafi ganin tunani zai mata yawa yasa ta mike ta ɗauro alwala sai goshin asuba bacci ya ɗauketa.
Washegari da wuri ta tashi ta gyara _part_ ɗinta ta haɗa break ta yi shirin makaranta saida ta shiga mota sannan ta rubuta masa sako _in short_ a takaice ta tura. Tana sanar masa ta haɗa musu _break_ ta wuce makaranta. Lokacin da sakon Ummi ya shiga wayarsa yana zaune yana duba computer ɗinsa ya yi jim yana duban wayarsa zuciyarsa ta yi nauyi ya tuna raban daya sata idonsa kwana biyu kenan tun ana gobe ɗaurin aure sai yaji babu daɗi ya mike yana shirin fitowa ya ji karar motarta ya yi saurin ɗaga labulan _window_ yana dubanta harta gama ficewa daga harabar gidan ya saki ajiyar zuciya.
STORY CONTINUES BELOW

Tsayin wata ɗaya Ummi na fama da faffutukar girki amma saboda rashin tsoron Allah Fadila bata karɓi girki ba. Kuma koda wasa Haidar bai tunkari ɗakinta ba gaisuwa kawai ke haɗasu ita ma a iya fallo abun ya dameta amma babu wanda take faɗawa. Kullum cikin addu a take zaune take tana chat a wayarta ita da Bahijja tana haska mata hoton baby Ummyter ta soma mikewa sai dariya take can ta turo mata wani posting ta yi jim tana dubawa cikin nutsuwa.
Mommyn Ummyter
“Tsafta aba ce dake taka muhimmiyar rawa a zamantakewar rayuwar aure. Idan aka ce tsafta ta dangaci muhimman abubbuwa da dama masu cike da gamsuwa ɓoyyayu da bayyannanu. Mata da yawa na fuskantar barazanar saki daga mazajansu dalilin rashin tsaft a yau zamu ɗauki wannan maudu i muyi bayani a kansa dala-dala. I dan a kace tsafta ya kama tun daka kan gangar jiki zuwa wasu sassa na jikin ɗan Adam bari mu fara da baki. Baki daga cikin tsaftar jiki akwai tsaftace baki, a kalla awanke baki da maganin wanke baki ko aswaki sau biyu ko uku a kullum, kuma daɗi akan haka ya kamata mace ta rika amfani da alawa (sweet) mai dadi mai bada daddadan qamshi a duk lokacin da zata kusanci mijinta.
Aski: Anan ana nufin aske wurin da suke tara gashi, kamar hammata, mara da sauransu, wanda dama yana cikin fitra guda biyar da Manzon Allah S.A.W ya fada, akalla mace ta tabbatar tana yin wannan aski duk bayan kwana arba’in.
Kumba in ji Katsinawa wato (Farce): Shi ma yanke kumba yana daya daga cikin fitra guda biyar wanda shi ma jigo ne sosai a cikin duniyar tsafta. Idan so samu ne ya kamata a kalla a yanke qumba a cikin kowanne sati, amma sai kaga wata farcenta kamar ta gwagwgwan biri.
Kaushi: ya kamata uwar gida ta kula da kaushin kafa tabi hanyoyin da zata bi wurin kawar dashi ko magani ko wankewa ko zuwa saloon dss. Wata hanya da mace zata iyayin maganin kaushin kafa shibne ta samu ruwan zafi ba sosai ba ta zuba shampoo a ciki sai ta saka kafafauwa a kalla minti goma sai ta goge kafar da dutsen goge kafa sai ta fitar ta shafa mai kamar basilin ko zaitun sai ta sanya qafar a cikin leda kamar minti biyar amma ba wai sai zata tafi unguwa ba. Tsaftar Gida Tsaftar gida ya hada da wurare kamar haka:
Banɗaki: dole mace ta kula matukar.kulawa a wajen tsaftace bandaki a kullum tare da amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta da kuma masu sa wuri qamshi in harda hali, duk da cewa basu da wata tsada, rashin dai wasu basu saba ba, idan kuma babu halin saya wankewar da kawar da yanar gizo-gizo a kullum, sai a kula tare da watsa kalanzir a wasu lokutan ko kullum musamman bandakin da yake na kowa da kowa ne.
Dakin Girki (Kitchen): Kitchen yana daya daga cikin wuraren da ake tantance mace mai tsafta da qazama, saboda haka dole mu riqa kulawa da tsafatar kitchen kuma kasancewar wuri ne da ake dafa abinci wanda munsan abinci yana daya daga cikin jigon rayuwar ‘dan Adam, sai muka ga ya zama wajibi a kula da wajen da ake tanadarsa.
Tsakar Gida: Dole mu riqa kulawa da tsaftar tsakar gida, domin hakan zai taimaka wurin tabbatar da tsaftar sauran wurare kamar kicin, bayi, dakin kwana dss, dadin dadawa duk wanda ya shigo gidan zaiga gidan fes-fes wanda da ma a matsayinki na mace ana buqata a kowanne lokaci ki kyautata ganin Maigida da sauran jama’a a matsayinki na makaranta mai tarbiyyantarwa, da kuma tattara kayayyaki ko wane a sa shi a muhallinsa, na kicin akai kicin, na bayi a kai bayi, na daki kuma a shigar dasu daki, ba wai a barsu a tsakar gida ba ko da an wanke bare ace ba’a wanke ba.
Dakin Kwana: ‘Dakin kwana dole ne mu kula da gyaranshi fiye da ko’ina a cikin gida, domin nanne wurin da Maidiga yake samun cikakken nutsuwa da hutawa da samun kwanciyar hankali da dai sauransu. Saboda haka dole ne mu riqa kula da gyaranshi qwarai da gaske, da kuma kokarin kawatashi da duk abinda Allah ya hore, da kokarin sanya turare da abubuwa masu sa kamshi a kowannen lokaci musamman lokacin kwanciya. In har Allah ya hore yana da kyau ayi amfani da turare na ruwa ko na hayaqi kala daban-daban, kina iya amfani da kala hudu ko biyar a lokaci daya kowannen ki sa shi a bangare daban. Misali na zanin gado daban, na filo daban, idan filon yafi daya kowanne ki sa masa nashi daban, na labule daban, na tsakar daki daban, na kujeru daban dss. Hakan zai bada wani irin qamshi mai tada hakalin Maigida ya rasa wanne irin qamshi ne wannan kuma daga ina yake fitowa !!!
Tufafi.
STORY CONTINUES BELOW

Tsaftar Tufafi: Dole ne mace ta kula da tsaftar tufafinta da na ‘ya’yanta da na Maigidanta, mu sani cewa yawan kayan sawa wata baiwa ce daga Allah, amma tsafta da wanki da guga da fesa turare idan ana gida shi ake nufi da tsafta, da wannan ne mace zata amsa sunanta na mace.
Kwalliya: Ya kamata mace ta kasance mai yawan kwalliya da cancanja salo kala-kala ta zamani domin Maigidanta, ba abin kunya bane dan mace taje koyon kwalliya, ka da ta tsaya ga sa hoda da jagira kawai, akwai yanayin kwalliya kala-kala, hatta su kansu kayan akwai yadda zaki sa su su birge Maigida.
Wajen Girki: Ana bukatar mace ta kula da tufafinta a lokacin da take girki dan haka shi zai qara tabbatar da tsaftarta. Saboda haka sai ta riqa amfani da qyalle ko tusmma na goge-goge, hakan zai taimaka kwarai wurin zama da kwalliyarta ko da tana girki kamar yadda bayani ya gabata, in kuma ta gama girkin sai tayi wanka idan akwai buqatar hakan amma bada ruwan kanzo ba!”.
Ummi ta saki ajiyar zuciya tare da turawa Bahijja alamar jinjina,
“sisty ina kika samu wannan?”.
“Wallahi a wani group na samu Ummyter”.
“Kina nufin kina group chat?”.
“Eh! Ina yi amma guda ɗaya ne shima saboda samun irin waɗanan shawarwarin”.
“Hakane amma ki kara kulawa ki kuma san dawa zaki yi mu amala”.
“Shikenan Ummytee Momyn Ummyter na gode”.
Dariya suka yi ta rufe datar ta cigaba da bibbiyar posting ɗin tana karantawa. Tana zaune ta jiyo horn ɗin mota daga waje bata damu ta duba waye ba ta cigaba da abin da take can taji an yi _knock_ ɗin kofarta tare da yin salama ta amsa tare da bada umarnin shigowa. Dimbin mamaki ya daskarar da ita ganin Nabila a sashinta gabanta ya faɗi a ranta tana ayyana ba alkhairi ne ya kawota ba zama ra yi tare da faɗin,
“wash! Ummi sannu da gida ya ki ke?”.
“Lafiya lau Nabila ya su Momy da Baffa?”.
“Kedai kin saba da Baffa ni fa in ba Daddy kika ce ba ɓatar dani kike”.
Dariya suka yi gaba ɗaya,
“yau ziyara kika kawo mana?”.
“Eh! Wallahi ko gun Au
ntyn ma banje ba na fara shigowa gun uwargida”.
Mamaki ya kara kama Ummi jikinta ya bata da wata a kasa yaushe raban Nabila da wajanta. Ita kuwa Nabila ganin cikin Ummi ya fito ji take kamar ra kasheta saboda KIYYAYA amma data tuna kudurinsu saita kanne ta saki fuska ta mike tana duban Habiba data shigo,
“ke ki biyoni da haɗin fruit sashin Aunty Fadila”.
Ta wuce tana kaɗa kugu tana tauna kas! Kas!! Kas!!!. Ummi ta yi murmushi tana faɗawa Habiba taje ta shirya mata ta kai mata.
Tun tafiyar Nabila gaban Ummi yake faɗuwa saita mike ganin la asar ta kawo kai ta ɗaura alwala ta zauna tana istigifari kafin a kira. Nabila na shiga ɗakin Fadila suka tafa suna dariya ta fito da wata leda baka ta mika mata ta soma yi mata bayanin dabarar da zasu yi daidai lokacin Habiba tazo kawo mata fruit ta yi tsaye jin ana ambaton sunan Ummi.
“Mudun kika yi amfani da wannan yadda aka tsara ba Ummi ba uwarta ma ta kaɗe wallahi Fadila. Ana yin sane yayin da mutum yake zaune baya komai ko yana wata sharholiya shiyasa yanzu na biya naga babu abin da take chat ma take yi tashi zaki yi muyi aikinsa. Kinga wannan mutum mutumin shi ake ajiyewa a zuba masa wannan ruwan maganin kina gamawa aljanin jiki zai fita zuwa jikin wanda kika ambata amma fa idan kika yi kuskure Malam ya ce zai yi fushi, kuma duk aikin da kika yi wa yaya zai karye saiki kula. Wannan kuma binewa zaki inaga shi mu bineshi a garden”.
“Kai amma Nabila na gode zo muje garden mu bine sai muje toilet zaifi sirri mu zubawa mutum mutumin”.
Da sauri Habiba tabar wajan ta nufi wajan mahaifiyarta jiki na rawa ta bayyana mata komai. Hankalinsu ya tashi sossai taja hannunta zuwa sashin Ummi lokacin da suka isa Ummi bata falo tsayin mintuna goma sunata shawarar abin yi kawai iya ta ja hannunta suka nufi garden sai dube-dube suke ko zasu gano in da aka yi binan amma sun kasa haka suka juyo zuwa ɗakin Ummi kawai Iya ta yi shahadar kuda suka tura kofar suka shiga suka zauna kasan carpet.
Lokacin da su Nabila suka gama rufe kayan tarkacansu sai suka juyo zuwa ɗaki suka ajiye mutum mutumin suka zuba ruwan take ya soma motsi yana girma suka dinga ja da baya sabida munin hallitarsa cikin rawar baki Fadila ta furta,
“kaje ka haukata…….min Ummi”.
“An gama shugabata”.
Sai ya bi bango ya datsa ya wuce suka saki ajiyar zuciya. Ummi na tsaka da sallah tana tahiyar karshe kawai sai jin abu ta yi yif! Ya sauka a gabanta bata ko dubi gun ba ta cigaba da ibadarta Habiba ta kankame iya tana ihu da kurari ta bige bakinta tana jan addu ar data zo bakinta. Hannu ya ɗaga yana nuna Ummi da shi, wata wuta koriya da ja na fita daga hannun tana nufo Ummi amma sai wutar ta dinga komawa kansa maimakon ita. Sai ya koma aman wuta da baki amma kansa take komawa ya soma kona kansa sai ya soma kara mai firgitarta yana murkususu da gudu ya yi sama ya fice. Ummi ta saki ajiyar zuciya tana sallama ta jima tana addu a sannan ta sauke idonta kan Iya da Habiba daketa sharɓar kuka. Ita kanta sai yanzu wani tsoro yake shigarta jikinta ko ina rawa ya ke. Ta dubi Iya,
“lafiya dai Iya?”.
Cikin makyarkyata ta yi mata bayanin abin da Habiba ta bayyana mata jikinta ya ɗauki rawa ta mike,
“kuzo muje”.
Kai tsaye suka nufi garden ɗin suka soma neman in da aka yi binnan.
***
Lokacin da aljanni markahussabusha ya ɓace a ɗakin Ummi bai bayyana ko ina ba sai ɗakin Fadila yana kururuwa da matagugun wahala. Ya nuna Fadila da yatsa yana faɗin………
®
30
Cikin karaji ya dinga kururuwa duk suka cakuɗe waje ɗaya. Nabila kuwa tuni ta saki fitsari a wajan sai ya yi sama ya bar ɗakin, duk suka saki ajiyar zuciya Fadila ta dubeta rai ɓace,
“yanzu kina nufin komai ya lallace?”.
“Eh!”.
Ta bata amsa a takaice, cike da kunar rai ta ce,
“amma kin cucceni Allah ya isa, gashi nan bani ga tsuntsu bani ga tarko”.
“Kut mesi ke wallahi Fadila kaza ce ci ki goge baki, ban da iskanci ina laifin taimakon dana yi miki?”.
“Sannu kiki ma kaka kinji Nabila, ai ni na godewa Allah ba…..”.
Maganar ta katse sakammakon hamɓare mata baki da Nabila ta yi nan suka hau dambatawa da kyar suka rabu suna zagin juna.
***
Su Ummi sai lallube suke cikin garden ɗin gidan tun huɗu da rabi, har kusan biyar basuga inda akai ramin ba suna shirin fitane wata umbrella ta faɗo bakin bishiyarta Ummi harta gota ranta ya kwaɗaitu da san shanta saita sunkuya zata ɗauka idonta ya sauka kan barbajin kasar wajan kawai ta sami kanta da yin basmallah ta soma tona wajan. Sai gashi ta fito da wata kwalba wani abu sai sihiri kwalbace karama amma cikinta wani abune kamar zuciya ta ciki raɗau ana hango yadda sunayansu ita da Haidar raɗau a rubuce ga wani bakin abu na zagayashi. Kai tsaye ta yi wa Iya nuni da kwalbar suka gyara wajan, saida suka jika kanwa suka watsawa kwalbar sannan suka yi bisimillah suka fasata wata kara ta fita mai karfi saida duk mazauna gidan suka ji. Fadila ta kara ruɗewa zatonta aljanin ne ya dawo.
***
Tsayin kwana biyu Haidar na samun sauyi tattare da al ammuransa, amma ya kasa gane abin da yake damunsa. Ummi na hankalce dashi hakan yasa ta soma maida hankalinta kan lamuransa ya zama ko aiki zaisa daga ɓangaran Fadila yake kiranta a waya ya ce yana san abu kaza lamarin na nuna mata nasarar da aka samu don haka ko sata ya yi babu musu take aikatawa. Kwatsam ranar Lahdi ya yo mata text kan yana marasa lafiya ya fita amma yana san da dare ta shirya masa sakwara bata yi masa reply ba ta kyaleshi ta cigaba da sabgoginta. Misalin karfe biyu ta ɗauki mukuli ta zaga sashinsa ta soma gyarawa, tun daga carpet ɗin tasan ɗakin ya yi missing shararta zagewa ta yi ta gyara shi tsaf ba ita ta gama ba sai karfe biyar da kwata.
Kicin ta nufa ta soma shirya masa abin da ya bukata, ba ita ta kammala ba sai ana gab da kiran magarba ta yi wanka ta yi sallah ta zauna jiran sallahr isha i. Sai da aka yi sallah ta mike ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando blue da ratsin fari kayan sun amsheta sossai ta kamsassa ko ina na jikinta da turare ta wuce sashinsa tare da shirya masa abincin a can. Tana zaune tana jiran dawowarsa suna taɓa hira da Hindatu da Bahijja Fadila ta shigo tana fizge-fizge ta zauna tare da kulle volume tana sauraran tv.
Haidar yana hanya amma gaba ɗaya tunanin Ummi ya gama dabaibayeshi a haka ya karaso gidan ya yi parking tare da shiga ciki kai tsaye sashinsa ya wuce. Yana shiga ya sauke idonsa a kanta ta ɗago tana murmushi beauty point ɗinta ya loɓa ya saki ajiyar zuciya tare da ware hannayansa ganin Fadila na wajan yasa ta kauce tare da karɓar kayan hannunsa ai kuwa ta shaka fuu tabar ɗakin cike da takaici. Jagora ta yi masa ya yi wanka suka dawo wajan cin a binci har sun zauna ta mike tare da faɗin,
“bari in kira Fadila”.
Kafaɗa kawai ya ɗaga mata, saida ta gama jan rai sannan tazo har sunci rabin abincin ta zauna ta hauci babu wanda ta tankawa suna gamawa ta mike tabar musu ɗakin. Ummi ce ta kwashe komai takai kicin ta gyara ta dawo tare da zubewa a kusa da Haidar ya shafa kanta yana murmushi tare da kane ido. Nan da nan suka kiɗime kowa nasan farantawa ɗan uwansa, sunyi nisa cikin faranta rayuka bugun kofar ya dakatar dadu da kyar Haidar ya saisaita kansa ya dubeta, kanta a kasa ta mirgina tare da ɗorashi kan filo ya mike ya buɗe. Tsaye take kikam kamar doki takaici yasa ya furta,
“lafiya Fadila?”.
Cikin masifa ta ce,
“kace lafiya mana, ka satomin kwana ka kawo nan kuma kake tambayata wai lafiya?”.
Takaici da mamaki suka hanashi kataɓus shi tunaninma yake yana me ya auri Fadila, bai gama samun amsarba ta nemi hankaɗeshi zata wuce ya daddage ya yarfamata mari ta dafe gun tana kaɗa harshe cike da mamaki.
“Kinsani sarai bana ɗaukar raini da wulakanci, ni ba rago bane Fadila daidai nake da duk wani iskancinki wallahi”.
Cikin sauri Ummi ta dakatar dashi,
“haba yaya ba girmanka bane wallahi”.
Kanta rufe baki Fadila ta kaimata duka a ciki ta kauce da zafin nama tana zare ido. Aikuwa Haidar ya yi kanta,
“kashemin mata zaki?”.
Ya faɗa yana huci, ta murguɗa baki belt ya zare ya dinga sambaɗarta da kyar Ummi ta kwaceta suka shiga daki suka barta a nan falo tana gunjin kuka. Fadila haka ta kwana da takaici kafin safiya ta bazawa su Mommy labari amma ga mamakinta Hajiya Sadiya bata ɗauki abun da zafiba kamar zatonta, hasalima faɗa ta rufeta dashi kan me ta dakarmata Nabila. Dukkansu cikin zafi suke don haka ba a sami wani fahimtar juna ba.
Washegari har kusan takwas da rabi Haidar bai fita ba yana zaune a ɗakinsa Ummi ta sameshi ta kwanto kan kafaɗunsa ta baya,
“naga alamu yau bazaka fita ba, kali agogo fa me kake a gida?”.
“Yau ranarki ce ba inda zani”.
Ya faɗa yana birkitota, ta yi tsale gefe guda tana kaɗa harshe tare da dira kafaffu.
“A’a nidai kazo ka fita aiki wallahi”.
Ya tsareta da ido,
“bakya so in zauna tare dake? Bakya sona ko Ummi?”.
Sai ya juya baya alamun fushi, da ɗan gudunta ta karaso tare da ɗaneshi,
“aa yaya ina sonka, ina son ka kasance tare dani ina son kullum in zauna tare kai amma marasa lafiya ma na bukatarka fiye da bukatar da nake maka”.
Ta sassauta murya daidai kunnansa ta furta,
“Haidar!”.
“Na am ƳUmmyter!”.
“Ina kaunarka”.
Murmushi ya yi tare da tallafo kanta,+
_”touch my heart you will feel, listen to my heart you will hear, look in to my eye you will see, that you will always be a special part of me_”.
Ma ana:-
_”Taɓa zuciyata zaki ji, ki saurari zuciyata zaki ji, ki kalli cikin idanuna zaki gani cewa ke kin zamo wani ɓangare na musamman nawa”._
Dariya ta saki tana dukkan kirjinsa cikin wasa da haka ta taimaka masa suka wuce gun cin abinci suna nishaɗi har zuwa fitarsa office.
***
Kwanci tashi Ummi da Haidar suka koma tamkar baya rayuwarsu a bar sha awa, hankalin Fadila ya yi mugun tashi ganin yadda kwata kwata ya fice sabgarta saita mike da fitsara da rashin kunya da sunan karɓar yanci wannan yafi komai ɓata rawarta da tsale duka yake naɗamata. Ganin babu sarki sai Allah yasa ta hakura ta soma neman mafita. Cikin kwanankin ta matsawa mahaifiyarta suka koma gun na kan tsauni amma kash binciken farko ya tabbatar musu aiki ya lallace sakammakon kona masa aljani da Ummi da tayi tilas suka zuba wasu makudan kuɗin aka sake sabon aiki amma kash daga Haidar har Ummi babu wanda ke tasiri kansa saboda karfin addu ar da Ummi take yi gashi duk sati saita yi saukar al kur ani.
Kwanci tashi cikin Ummi ya shiga wata na tara, sossai Haidar ya ke kulawa da ita hata makaranta shi yake kaita ya ɗaukota motsi kaɗan ya kira waya yana faɗin,
“Ummi ya ki ke? Ba abinda yake damunki?”.
Ira-iran kulawar da yake bata yakan asasa kaunar da take masa.
Misalin karfe huɗu na yamma sun fito ɗakin karatu, haka kawai Ummi sai fushi take ita dai Hindatu na kallonta saidai ta yi murmushi Sabah ce ta kasa daurewa ta dubeta,
“waike Ummyter me yasa kike ta fushi ne?”.
Ta kauda kai,
“ba komai sisty haka na tsinci kaina”.
Hindatu ta tareta da faɗin,
“daina damun kanki Sabah haka masu ciki suke riskar kansu masifafune wata rana”.
Cikin zare ido ta dubeta,
“ban fahimta ba Hinduwa?”.
“Hmmm! Kin gane ko sisty yawancin mata tun farkon shigar ciki sukan fuskanci canji a tare da su da dama. Ta fanin lafiya, wasu za ki ga sun rasa kuzari, ciwon, jiki, amai, zazzabi, kasala, mugun bacci, ciwon kai, jiri, ciwon kirji, da makamantasu. Akwai wadanda za ki ga ko ruwa suka sha, sai sun amayar ko yawu yai ta taruwa a bakinsu, dole sai da taimakon likita suke samun sauki. Shi ya sa in mace ta samu ciki kafin ta haihu, zaki ga ta rame ta yi fari fat, saboda rashin lafiya da rashin zaman abinci a ciki. Wata kuma bacci ne da ta zauna sai bacci kaman wadda kudan tsando ya ciza, shi ya sa ita kuma kullum a ciwon jiki take. Wata kuma za ki ga kullum tana tofe-tofen yawu kaman mai surkulle da sauran makamantan haka.
Shiyasa faɗin ubangiji mata kan kasancewa cikin rauni ƙkan rauni ya yin ɗaukar ciki da haihuwarsa. Abu na gaba da yawancin mata halayyarsu kan sake yayin da suka samu ciki kuma yawanci halin na su za ka tarar fushi, faɗa, kuka da sauransu. Ya Allah ko don canjin da suke samu ne, ko rashin natsuwar jiki da ciwo. To koma mene ne dai, halinsu kan sake shi ya sa Musulunci ya lallashi maza a kan saurin saki, yayin da mace ke da ciki. Saboda da yawa za su yi abu ne wanda ba dabi’arsu ba. Misali, wata da zarar ta samu ciki sai ka ga ta rage tsafta, saboda ciwon jiki da kasala. Wata ta ce mijin nata ma ba ta son ya matso kusa da ita, bare ai zancen tarayyar aure. Wata ta ce ba ta son warin girki don haka ba ta iya yi. Wata kuma da ka yi magana, ka ga ta taso da fada.
STORY CONTINUES BELOW

In muka yi nazari za muga ai da ba ta haka. Don haka anan dole sai miji ya kauda kai ya kiyaye da saurin saki, ko saurin fushi yayin da amarya ta samu ciki. Don da yawa za ki ji suna korafi, ‘da ba haka take min ba, tana samun ciki ta sauya,’ to ka gane wannan cikin shi ya kawo sauyin. Shi ya sa muka godewa Allah a kan ni’imar Musulunci domin ba abin da ya bar mana a rufe, sai dai a ce ba mu kai gare shi ba”.
Cikin ci da zuci Sabah ta tareta da faɗin,
“Hindatu naji kin faɗi rauni kan rauni me hakan yake nufi?”.
Murmushi ta yi sannan ta ce,
“eh! Saboda na taɓa sauraron wa’azin wani shaihin Malami a kan uwa, na ji yana cewa uwa kan haifi da cikin rauni a kan rauni, ma’ana cikin wahala. Sai na yi mamaki da jin zancen domin a lokacin ina tunanin ba wani wahala a ciki sai dai ko nakuda shi ma dan na taba ji wata ta zo haihuwa aka ce ta kwana uku, tana shan wahala, karshe ta suma sai da aka kaita asibiti tukunna aka yi aiki aka fiddo da ɗan. Wannan ta sa na ɗan fahimci kila haihuwar yaro kawai ke da ɗan wahala. A haka watarana na ci karo da irin ayar da malamin ya karanta cewa mahaifiya kan dau ciki rauni bisa rauni.
Da farko na ganta a cikin Suratul Lukman aya ta 14, ina yin kasa, na gan ta a Suratul Ahkaf aya ta 15. Sai na shiga tunani domin na san Allah (SWT) ba ya faɗar maganar da ba ma’ana a cikinta, domin Shi Hakimun ne shi ne wancan bayani da na yi miki a baya kuma shi ma duk a bakinsa naji bayanin”.
“Hmmm! Sannu Mallama ya sunansa!”.
Cewar Ummyter tana dariya, sannan ta cigaba.
“Bansaniba sarkin tambayar tsiya!”
Gwalo ta yi mata tare da sakin dariya.
“Wallahi duk abin da kika faɗa ina jinsu”.
Dariya suka yi daidai lokacin Haidar ya zo ɗaukarta suka yi sallama suka wuce.
***
Hankali Fadila ya yi matukar tashi ganin babu sarki sai ubangiji yasa ta nemi shiri da Nabila suka koma suka ɗinke. Tafiya suka shirya zuwa Jos babu sanin kowa Ahmad ne ƴya kaisu ya dawo dasu babu musu ya amince bai kuma damu dame zasu je suyo ba tunda dai shi burinsa samun jikin Fadila available. Ai kuwa a ranar suka je suka dawo an gama komai kawai mahaɗin maganin suke nema kumbar Ummi da gashin kanta.
Fadila tsayin sati biyu tana fakon Ummi amma ta gaggara samun abin da take so, Habiba kuwa ko magana bata haɗasu bale ta ribace ta cikin hikima ta fara shiga sashin Ummi da sunan tayata hira da farko Ummi ta tsaraka da zuwan nata amma daga baya data ga komai ya mika saita saki jiki suna hira kaɗan kaɗan.
Hajiya Sadiya ta rasa yadda zata fuskanci al ammarin gidanta gaba ɗaya maigidanta ya tattara komai nasa ga ɗan uwansa tunda Haidar kasuwanci bai dameshi ba. Bata da buri daya wuce nakasa Abbu amma takasa saboda tsayayyan mutum ne mai riko da addinni tasha aika masa mugun aiki ya tako har gida ya yi mata gargaɗi ta hanga ta hanga babu abin da zai nakasa Abbu face nakasar Ummi gudan jininsa wannan yasa ta kara kaimi wajan iza wutar kiyyayar Ummi a zuciyar Fadila da Hajiyarta uwa uba ga mai agaza mata Nabila.
Ɓ ***
Ranar _friday_ Juma a Ummi na zaune tana gyara kumbarta, Fadila ta shigo tana daddana waya wani farin ciki ya ziyarci zuciyarta ganin Ummi na yankan akaifa saita zauna ta washe baki,
“uwar biyu yau tsafta ake ji kenan dama jiya na gama gulmarki yausha raban da kiyi gyaran kai duk baby ya saki kazanta”.
Murmushi ya kwace mata ta ce,
“ai kuwa ɗazu nayi gyaran kai kinma tunamin wallahi gashin na kan mirror bari in kira Habiba ta ɗauke kar yaya ya dawo bayan gashi”.
Cikin jin daɗi ta kanne,
“bari in ɗauke ai ba a tashi me ciki ba”.
Hanyar ɗakin ta yi ta shiga, sossai gabanta ya faɗi karo na farko a rayuwarta data shiga sashin bed room ɗin Ummi duk saita raina kanta. Sauri ta yi ta yagi gashin ta cusa a bureziyarta ta ɗauko sauran harta kusa fita ta hangi wayar Ummi sai ta yi maza ta ɗauketa ta danna numbobinta ta yi flash ɗin kanta ta fice da sauri. Ummi ta kalleta sai taji gabanta ya faɗi ta dake,
“ina gashin?”.
Ta faɗa a sanyaye cikin murmushi ta nuna mata saita karɓa tare da furta,
“bari insa a abun da nike adanawa”.
Tana bada baya ta yi mata gwalo tare da furta,
“kin makara”.
Sun kuyawa tayi ta dangi akaifar ta fice tun kafin Ummin ta dawo. Da rawar jiki ta karasa ɗakinta ta haɗa da maganin da aka bata ta hautsina ta mike ta samo rushi ta zuba a kai hayaki ya tashi sama wani abu mai tsananin haske ya fice a ɗakin talau!.
Ummi koda ta dawo bata ga Fadila ba bata kawo komai ba saita nemi waje ta zauna ta cigaba da gyaran kumbarta. Tana nan zaune ta ji wani abu na motsi ta ɗaga kai amma bata ga komai ba taji faɗuwar gaba sunkuyawar da zata yi wanke talau! Ya ratso window ɗinta ya daki cikinta take cikin ya murɗa ta saki wata giggitaciyar kara hakan ƴ ya yi daidai da shigowar Haidar.
STORY CONTINUES BELOW

Da sauri ya nufeta yana tambayarta amma babu amsa sai gumi take tamkar wadda ta haɗiyi kunama jikinta ko ina rawa yake cikinta yana hautsunawa tamkar kayan wanki ta buɗe baki a hankali,
“yaya cikina!”.
“Sannu Ummyter!”.
Haka suka kasance har dare da Baffa yazo ya dinga faɗa basu je asibiti ba, tilas ya sasu suka shirya zuwa asibiti an yi bincike amma basu ga komai ba haka suka dawo gida cikin ya ɗan lafa. Tun daga lokacin Ummi ta soma fama da wani irin matsanancin ciwan ciki in ta soma har suma take anyi binciken anyi binciken amma an kasa ganin matsalar. Hankalin Haidar ya yi mugun tashi haka take daurewa tana tausarsa.
Tsayin sati uku Ummi na fama da wannan ciwon ciki, kwatsam kuma sai cikin ya daina ciwo sai wata irin motsewa lamarin daya ɗaga musu hankali suka nufi asibici amma binciken farko likitocin sunkasa ganin komai hasalima babu ciki babu dalilinsa. Haidar ya kaɗu matuka har fita da ita ya yi amma amsar ɗaya ce babu ciki Baffa ne ya bada shawarar su dawo aka soma sauke mata alkur ani mai girma wanda ake tofashi cikin zam-zam tana sha. Cikin ikon Allah sauki ya soma samuwa ciwon ya ragu sai kuma wasu kuraje manya da suka feso mata suka sata muni sossai. Ga wata tsana da hantara da Haidar ya ke nuna mata, lamarin daya kara asassa damuwarta kenan duk tafita hayyacinta ta kwantsame abun tausayi.
Fadila duniyarta take ci da tsinke ganin ta soma samun sake yasa ta soma yi wa Hajiya Sadiya iskanci do-do-do ƴhata Nabila yanzu shakarta take. Yawo da Ahmad kuwa kullum suna manne a wajan aiki, ƴhakan ya daga hankalin Hajiya Sadiya saboda yanzu wata tashan dukiya ya ke yi, saboda sun soma kasuwanci shi da Mahmud da Aminu suna shigo da kaya daga waje. Komai nasa ya koma hannunta gaishe da Mommy kuwa yafi wata bai je ba hakan ya dameta ta shirya ranar karshan mako da safe ta nufi gidan.
Zaune take a falo tsayin mintuna talatin da zuwanta ta yi tsaki yafi sau goma. Can ta muskuta Ummi ta zo ta gaisheta tare da ajiye mata abin motsa baki, ta karɓa ba yabo ba fallasa ta ɗan zauna suka taɓa hira ta wuce sashinta mintuna goma saiga fitowarsu shi da Fadila sai yatsina take tana turo baki suka zauna Haidar ne kaɗai ya gaisheta Nabila ta shaka ta ɗauke kai takaici ya hanata magana ƳHaidar ya mike ya shiga sashinsa Nabila ta yi tsaki ta ce,
“gaskiya Fadila bakya kyautawa ko Momy bata haifeki ba ai aminiyar Mum ɗinki ce kuma kanwar ubanki ce….”.
Bata karasa ba Fadila tasa ihu wanda yaja fitowar Ummi da Haidar turus Ummi ta tsaya Haidar yana huci ya dubeta,
“menene?”.
“Zagina ta yi dear!”.
Ta faɗa tana nuna Nabila bai yi wata wata ba ya kwashe Nabila da mari ta yi tsale tana kuka. Yana ɗauke hannunsa Hajiya Sadiya ta zuba masa nasa marin, tana huci ta nunashi da yatsa,
“a gabana Haidar?! Eh! Lallai wuyanka ya yi kauri”.
Ta juya kan Fadila tana nunata da yatsa,
“kin bani mamaki lallai *’DAN ADAM* (Auntyn Fikra Ruffy) butulu ne. Kin manta nice tsanin kafuwarki a cikin gidan nan?”.
Cikin sauri ta tari numfashinta,
“a’a fa Momy bana son tone-tone ke ɗin wa? Wallahi ki iya bakinki kaza garin tone-tone take tono wukar yankanta. Ni dai kowa ya san ba *KIYYAYA CE* tushan kafuwar aurena da Haidar ba don haka bana son shisshigi a *GIDAN AURENA* (Aunty Soffy)”.
Momy ta tunzura ta ɗauke Fadila da mari, aikuwa cikin tsiwa tasa kuka tana faɗin,
“dear kana kallo fa kana kallofa!”.
Cikin fitar hayyaci ya dubeta,
“Fadila me kike so in yi? Faɗi inji ki faɗa!”.
“Ka saki Ummi Haidar kaiwa Mommy iyaka da zuwa gidan nan daga ita har Nabila”.
Ummi bata san sanda bakinta ya suɓuce ba ta furta,
“amma Fadila baki da hankali wallahi!”.
“Au! Hankali Ummi? Hankali hahahhha! Zaki ga rashin hankali zalla. Haidar da kai nake”.
Jiki na rawa ya furta,
“Ummi na sake ki saki ɗaya!”.
Ya juya kan mahaifiyarsa ya buɗa baki zai yi magana ta yanke jiki ta faɗi kanta ya bugu da hannun kujera na tsantsar katako. Da sauri su Ummi suka yi kanta suna kuka da taimakon masu aiki suka sata a mota Nabila taja motar suka nufi asibiti suna zuwa asibitin da Haidar ya ke aiki suka nufa da hanzari Mahmud ya karɓesu suka wuce emergency. Tsayin awa biyu likitoci na kanta amma bata farfaɗiba tilas su Ummi suka je gida suka ɗauko Ummu hankali a tashe.
Babu wanda hankalinsa bai tashi ba, haka suka yini a wajanta da dare iyayansu Maza suka zo. Su Ummi koda wasa sunki faɗin dalilin faɗuwar Momy da an tambaya amsar ɗaya ce zamewa ta yi yayin da likitocin suke musa hakan saboda binciken da suka yi ya basu tabbacin wani abune ya razanar da ita wanda har taɓa zuciyarta. A ranar kwana na uku ne ta farfaɗo amma saboda yadda zuciyarta ke harbawa aka sake yi mata allurar bacci. Baffa na lura da rashin zuwan Haidar amma in ya yi magana saisu Ummi suce yana lekowa gashi kokiran wayarsa ya yi baya ɗagawa. Haka Ummi da Nabila da Ummu suketa zarya wajan jinyar Momy amma babu Fadila babu mahaifiyarta. Mahaifinta zuwansa uku. Fadila kuwa babu abin da ya dameta kawai rayuwarta take yi babban takaicinta ɗaya tun asirin da suka yi wa Ummi Haidar ya daina haɗa shimfiɗa da ita kwata-kwata da fari ta yi korafi amma daga bisani data nemi ɗaga hankalinta mahaifiyarta ta dakatar da ita saboda kuɗin da suke shaka daga wajansa kawai saita watsar dashi tunda gata da Ahmad.
***
Kwanci tashi ta share sati biyu babu wani sauyi hakan yasa aka maida ita asibitin koyarwa na AKTH zuwa lokacin ta samu sauki amma bata magana sai dai ta yi ta kallon mutane hakane yasa suka yanke yi mata gwajin kwakwalwa. Baffa kullum cikin yin korafi yake kan rashin haɗuwa da Haidar amsa ɗaya ce ya zo uwa uba yadda yaga Ummi na ɗawainiya da Hajiyar gashi cikinta ya mike ya yi wani irin girma inta zauna ta yi ta nishi saboda ya haura wata sha ɗaya. Ranar daya gaji da kansa ya shirya yaje har gida ya je ya sameshi ya yi masa tas amma abin da ya data masa hankali yadda yake ciccijewa yana mayar masa da magana jikinsa ya yi sanyi sossai ya baro gidan. Mamakinsa ya karu daya nufi sashin Ummi yaganshi da kwaɗo a datse sai lokacin ya shiga tunanin yawancin lokuta a gida yake ganinta. Kai tsaye gidan ɗan uwansa ya wuce suka tareshi da murna kasancewar ranar Nabila suka bari ta kwana a wajanta. Ransa a jagule yake tambayar me Ummi take a gida aka rasa mai magana Ummince ta yi ta maza ta faɗa masa sun rabu. ƳHankalinsa ya tashi sossai ya dinga faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba su dai hakuri suke bashi.
Washegari misalin karfe uku na yamma Ummu da Nabila da kuma Ummi suna zaune, Ummi na gyarawa Hajiya Sadiya farce Haidar ya yi sallama tare da Daddynsa suka shigo wata muguwar zabura Momy ta yi ta buɗe baki tana son magana saita kakkafe. Da sauri suka yi kanta amma bata numfashi cikin hanzari suka kira likita ya daɗe a kanta sannan ta farfaɗo ya juyo yana dubansu,
“meta gani ta tsorata haka? Tunaninta na gab da dawowa”.
Duk suka yi jigum Baffa ya furta,
“Haidar ne”.
“waye hakan? Meye alakarta dashi?”.
Likita ya bukata da sauri,
“Dan tane”.
Baffa ya bashi amsa, ya juyo yana maimata.
“Danta?”.
Duk suka yi shiru ya yi jim,
“Alhaji kasameni office”.
Bayan zuwansa office ɗin likitan ɗan siriri ya dubeshi,
“Alhaji gaskiyar magana akwai ɓoyyayan sirri kan Hajiya domin yadda lokaci ɗaya ta firgita ina tunanin akwai alaka tsakanin faruwar fargabarta da shi Haidar ɗin da ka faɗa”.
Baffa bai yi musu ba amma tunani yake menene musababbin hakan. Dabara ta faɗo masa ya kuna wayarsa ya kira Nabila yace ta sameshi office ɗin likita mintuna biyar saigata.
“Nabila so nake ki faɗamin abin da ya razana Momynki harta faɗi”.
“Daddy ban….ban..ni ban sani ba”.
Cikin daka tsawa ya furta,
“ba dake nake ba?! Ba tare kuka fita ba? Mema ya kaiku gidan Haidar ranar?”.
Daidai lokacin Abbu ya shigo office ɗin yana faɗin,
“kai mata a hankali mana yaya”.
Ya mikawa likitan hannu suka gaisa sunyi sabo dashi a ɗan tsakanin. Nabila hankalinta ya tashi amma ganin yadda ran Baffa ya tashi sai ta yi shahadar kuda. Tiryan-tiryan tun daga zuwansu Jos har zuwa sakin Ummi da faɗuwar Momy. Kafin ta dire gumi ya gama rufe Baffa ya dubeta cike da takaici,
“kinyi asara Nabila dake aka haɗa baki aka cutar da yar uwarki?”.
Ganin yana yunkurin dukanta yasa Abbu rikeshi ya korata ta fice tana kuka kamar ranta zai fita. Tana zuwa ta samu babu Ummi da Ummi saita zube ta cigaba da kukanta.
33
STORY CONTINUES BELOW

Haidar tunda ya koma gida tunanin ya adabeshi,kansa ya dinga juyawa sossai kukan da Momy take ya dinga nukurkusar zuciyarsa. Fadila ta dameshi da tambaya, bai ɓoye mata komai ba karshe sai ta yi tsaki ta bashi waje.
Lokacin da Abbu ya dawo gida bai ɓoye ma Ummu abin da ya faru ba. Sun yi mamaki kwarai amma da suka tuna mugayan mafarkan da Ummi take sai suka godewa ubangiji da ɓoyyayan sirrin ya bayyana. Washegari Ummu da suka je asibiti koda wasa basu nunawa Nabila kyara ko hantara ba hasalima janta ta ƴyi ajiki ta dinga yi mata nasiha. Kwana uku da faruwar lamarin Baffa ya je can Karaye wajan wani Malami ya yi masa bayanin komai ya yi jim yana tunanin. Daga bisani ya bada ganyan magarya guda bakwai da ruwan tofi a jarka ya ce a ba marasa lafiyan susha tsayin kwana bakwai daga bisani a zo da marasa lafiyan. Godiya ya yi masa tare da yi masa alkhairi mai yawa, amma bai karɓa ba. Ummi tunda Baffa ya dawo take shan maganin, Haidar ne sama da kasa aka rasashi Baffa da Mahmoud keta zaryar nemansa tsayin kwana uku amma sun rasashi. A ranar kwana na huɗu ne Baffa ya yi katarin samunsa a office ɗinsa, da zafinsa ya shiga amma ganin ramar da ya yi yasa jikinsa mugun sanyi ba shiri ya ji kwalla na neman zubowa cikin idonsa. Ya zuba masa ido yana kallonsa, ya saukar da kai kasa.
“Haidar haka ka zaɓawa rayuwarka? Ka duba duk yadda ka rame ka lallace. Menene ya ke damuwarka? Mahaifiyarka bata lafiya kaki zuwa ka dubata”.
Jikinsa ya yi sanyi ya dinga fitar da numfashi kwala ta ciko idonsa.
“Daddy ka yi hakuri, ni kaina bansan abin da yake damuna ba”.
“Shikenan Allah ya kyauta”.
Nasiha ya dinga yi masa daga bisani ya fita ya ɗauko ruwan jarkar a motarsa ya dawo. Ruwan ya tsiyaya masa kofi ɗaya ya tura masa,
“ɗauki kasha!”.
Dauka ya yi ya shanye tas, tun daga ranar kullum sai Baffa ya zo office ya bashi ruwan yasha. Cikin kwanakin Fadila ta rasa gane kansa ga wata doka daya samata ta hana fita bunu-bunu kuma ya yi sashin Ummi ya dawo. Ranar nan da dare ya kasa jurewa ya tambayeta ina Ummi? Cike da tsiwa ta ce,
“ajiyarta ka bani?”.
Wata wawwar shaka ya yi mata daidai lokacin Allah ya kawo Ahmad da kyar ya kwaceta yana tambayar,
“Haidar lafiya?”.
“Wai dan ya tambayi Ummi nace ajiya ya ban shi ne yake dukana”.
“Wace Ummi bayan Ummin daka saki?!”.
Wata sarawa kansa ya yi ya kaiwa Ahmad duka a baki saiga fitar hakora guda biyu,
“ubankane ya sakarmun mata? Wai kai ban hanaka shigomin gida ba?”.
Tun a lokacin Ahmad ya san Haidar ya dawo hayyacinsa, da kyar ya kwaci kansa ya yi waje da gudu ya bishi. Amma kash ya guje masa dafe kai Haidar ya yi ya zube a ƴharabar gidan sai ga Mahmud ya yi parking.
Da sauri ya karasa wajansa ya cukuikuyeshi,
“Mahmoud ka faɗamin kai ma ka yarda na saki Ummyter?!”.
Tausayin Haidar ya kamashi musamman daya ga ramar da ya yi,
“baka saketa ba freindy kayi hakuri waya ce ka saketa?”.
Kamar wani zararre ya ware hannu,
“yauwa ni nasani BAN SAKETA BA”.
Dabara ta faɗowa Mahmoud,
“hau mota muje wajan Abbu ka ganta”.
Babu musu yabishi suka tafi Mahmoud bai zame ko ina ba sai asibitin da Hajiyar Haidar take suka nufi ɗakin da aka kwantar da ita. Kowa na cikin ɗakin suna zaune da alamama hira suke. Harda Hajiya Sadiyar wadda keta kallon bakunansu ta kasa magana shigowarsu yasa suka maida hankulansu kan kofar babu wanda fuskarsa bata washe da farincikin ganin Haidar ba in ka ɗauke Ummi da mahaifiyars.
Cikin karaji take nunashi tana faɗin,
“Fadila Haidar ni kukewa haka”.
Gaba daya yan ɗakin suka mike suka yi kanta, ta dafe kai tana kara mai karfi da gudu Nabila ta yi waje ta kira likita Haidar kuwa zubewa ya yi a wajan yana gursheken kuka da kyar mahaifinsa ya fita dashi suka bar likitoci a ciki. Saida suka shafe a waya ɗaya suka fito dukkansu fuskarsu da walwala suka basu tabbacin zata farka nan da awa uku kuma insha Allahu cikin hankalinta.
Mahmoud da Haidar na zaune a harabar asibitin, can ya hango Nabila a rakuɓe tana kuka ya yafitota da hannu ta taho jiki a sanyaye saboda nauyin Mahmoud take ji sossai tunda ya furta mata kalmar so. Tsugunawa ta yi,
“yaya gani”.
“Nabila nasan kinsan komai, ki warwaremun abin da yake faruwa kuma wallahi kikamun karya saina yi miki duka”.
Ta yi shiru Mahmoud ya fahimci zamansa a wajan ne ya haifar da hakan sai ya mike taji daɗin hakan sossai sai ta watsake kawai ta soma bashi labarin komai abin da ya wakana. Ya yi shiru zuciyarsa ta dinga zafi ganin yadda idonsa ya yi jajjur yasa ta mike ta bashi waje karya mazgeta.
Washegari ahalinsu Ummi da farin ciki suka tashi sabida daidaituwar tunanin Hajiya Sadiya, gaisawa take da kowa takuma kira sunansa Haidar ne kaɗai taki yadda su gaisa kwata kwata da kyar Baffa ya sha kanta ta hakura ta suke gaisawa amma daga gaisuwar basa kara komai. Kwananta biyu aka sallameta suka koma gida. Tun da suka koma Ummi ce take kula da ita duk da cikin dake jikinta ita kuwa kullum faɗa take mata kan ta rage zirga-zirga.
Fadila ta rasa gane kan Haidar, yanzu sai tayi kwana uku bata sashi cikin idonta ba gashi ya hana maigadi ya barta ya fita. Ahmad kuwa kota kira wayarsa baya ɗauka. Haidar kullum yana gidansu, duk yadda yaso Ummi ta sakar masa fuska abin yaci tura haka Momynsa gara ma Nabila da Ummu sunfi sakar masa fuska sossai. Ranar da su Ummi suka cika sati cif Baffa ya ɗaukesu zuwa Karaye wajan Malamin daya basu magani.
STORY CONTINUES BELOW

Saida suka huta suka ci abinci sannan Malamin ya nemi ganinsu. Ya tsaida idonsa kan Haidar ya yi murmushi kawai ya furta,
“kai har yanzu da sauran aiki a kanka”.
Wani kasko ya jawo ya sa aka kawo rushi ya zuba hayaki ya turashi gaban Haidar yasa ya sunkuyar da kansa a kai hayakin ya dinga shiga hancinsa ko gezau bai ba amma Ummi tana sheka idanunta ya birkice ta soma juje juye Haidar ya riketa gam sai Malamin ya soma jan ayoyi take ta saki kara firgitaciya,
“Malam kadaina konani zan fita zan fita wallahi!”.
“Makiyin Allah kana cutar baiwar Allah bata ji ba bata gani ba”.
“Wallahi turoni akai!”.
“Waya turoka?”.
“Fadila ce”.
Gaba ɗaya suka ɗauki sallalami, an yi nasarar fitar da aljanin har musuluntar dashi Malamin ya yi ya basu addu o in da zasu dinga yi ya kuma gargaɗesu da yin azkar sossai Baffa ya yi masa godiya tare da bashi naura dubu ɗari amma hamsin ya cira da kyar suka yi sallama suka koma gida.
Cikin jin daɗi suka baro wajan, kai tsaye gida Haidar ya wuce ko a fuska bai nunawa Fadila wata damuwa ba ɗakinsa ya wuce ya iskeshi kaca-kaca ya yi murmushi saboda tuna Ummi zagewa ya yi ya gyarashi tsaf daidai lokacin Fadila ta shigo tana yatsina fuska ya dubeta,
“Fadila zanci abinci!”.
“Abinci?!”.
“Eh! Yunwa nake ji”.
“Ok! Bari insa kuku ya yi maka”.
Saita fice da hanzarinta tana murna ya fara dawowa hannu shi kuwa sai ya rakata da murmushi. Kwala ta taru a idanunsa yasa hannu ya goge. Tun daga ranar ya sauya taku kulawa yake da ita sossai a hankali a hankali ya dinga karɓe takardun kaddarorinsa da suke gunta duk wani abu daya dangaceshi wanda yake hannunta saida ya karɓesu tsaf. Ya yi mamaki daya shiga accont ɗinsa ya samu an masa ɓarnar kuɗi sossai bai wani tsaurara ba ya buɗe sabon account a hankali ya dinga kwashe kuɗin yana mayarwa sabon.
***
Ranar Littinin da misalin karfe bakwai na dare Ummi ta haifi kyawwawan yaranta guda biyu duk mata. Kafin karfe goma labari ya samu Haidar ta hanyar Nabila ai kuwa saboda murna naira dubu hamsin ya bata kyauta kafin kace kwabo gida ya ɗinke da jama a kowa murna da mamaki yake haihuwa a gida amma saida Haidar ya matsa suka je asibiti aka binciki lafiyarsu.
Tunda aka yi haihuwar kullum Haidar gidan yake yini tun abun baya damun mahaifiyarsa harya fara damunta don ya ta gane take takensa na son matarsa ta koma gidansa. Kuma a saninta dai Ummi ta gama idda. Shi ma Haidar a ɓangaransa abun ya soma damunsa, yafi son a yi suna Ummi na gidanta amma baiga alamun nasara ba Mahmoud ya fara ɗauka suka jewa mahaifinsa da batun ya ji daɗin hakan amma ya nemi su kara masa lokaci. Haihuwar yaran ta karawa Haidar wata kaunar Ummi ya saki jiki sossai siyyaya yake musu ta bajinta Fadila hankalinta ya tashi musamman da mahaifiyarta taje barka ita da mahaifinta taga irin kyautukan da yaran ke samu tunkan suna ko mahaifinta dubu ɗari biyu yaba Ummi ai kuwa ta karasa ruɗewa ta dinga kuka hakuri ta dinga bata tare da alkawarin zata zo su koma gun Malami ko ince bokansu.
Misalin karfe shida na yamma Haidar ya nufo gida, shiru babu motsin kowa ya yi mamaki sossai ransa ya ɓacci zatansa fita ta yi kai tsaye ɗakinta ya nufa falon shiru ya sake dubawa kai tsaye bedroom ɗinta ya nufa ya tura kofar ras! Ras!! Ras!!! Gabansa ya yi mummunar faɗuwa ya runtse idanu yana faɗin…..Sanahsmatazu.wordPress.com. Ummu Beenah.
Cikin kaɗuwa ya dafe kai yana rike da kirjinsa ya juya har haɗa hanya yake ya fice zuwa sashinsa. Yanayin daya ga Fadila da Ahmad ya fi komai daga masa hankali tabbas ya yarda zina bashi zina masifa ce duk yadda ka ɓata yar wani sai an ɓata wani naka ya runtse ido yana tausayin yaranshi yau matarsa aka taɓa yake jin zafi haka a ransa yana ayyana da yaranshi ne fa ya zaiji kuka Haidar yake sossai ko ɗar baiji zai hukunta Ahmad ba bale Fadila ya dinga juyi yana tunanin watansa a kala uku bai kusanci Fadila ba to yaushe ta fara harka da Ahmad? Idan haka ne shi ne babban mai laifi matarsa ce tana da ƴhakki a kansa wata zuciyar ta nusar dashi da kai Haidar kasan tsayin lokacin da suke tare. Zabura ya yi kamar mahaukaci ya nufi window yana kallon fitar Fadila a mota da alamu ma kuka take. Kaya kawai ya sauya ya wuce office lab ya wuce akai masa gwajin jini saida ya tabbatar normal yake sannan ya sami nutsuwa.
STORY CONTINUES BELOW

Fadila kai tsaye gida ta wuce tana rizgar kuka kamar zata mutu, mahaifinta ya yi tambayar duniya taki magana ya gaji ya hauta da faɗa ai kuwa kamar maijira mahaifiyarta ta taso masa sai ya fice ya bar gidan dama haka take so ta hau tambayarta,
“Fadila lafiya?”.
Bata ɓoye mata komai ba, ta kaɗu iya kaɗuwa ta dinga zagin Fadilar tare da jinjina kokari irin nata amma yadda taga tana kuka ta bata tausayi ta kalleta,
“ya sake ki ne?”.
“A a bai sake ni ba”.
“Share hawayanki da sauki gobe zamu je Jos”.
Tsale ta daka tare da rungume mahaifiyarta suna dariya, washegari suka ɗauki hanyar Jos saida suka je suka kullo komai a hanyar dawowa suka yi haɗari a shigowarsu garin Kano. Motarce ta kifa mutanan ciki suka hantsula mahaifiyar Fadila garin gudun mutuwa babbar mota ta taketa ta talitse kan titi kamar an taka ɓera Fadila kuwa cinyarta ɗaya ce ta cire, wayar Fadila aka ɗauka aka kira mahaifinta yana tsaka da aiki haka ya taso a ɗimauce a asibitin koyarwa na MARYAMA HOSPITAL dake titin YAHYA GUSAU ya samesu. Zuwansa har an bata gado an mata allurar bacci ya yi jigum yana dubanta yana tsiyayyar da hawaye. Lokacin data farka kuka ta dinga yi tana bashi labarin abin da ta aikata kansa ya ɗaure ta dinga rokansa kan ya rokarmata afuwar Ummi da Haidar a daran tace ga garinku nan.
Mahaifinta ya dinga kuka nan da nan ya fice hayyacinaa, lokacin da Ummi ta samu labari kuka ta dinga yi tana faɗin ta yafe mata Haidar kuwa buɗar bakinsa sai cewa ya yi,
“Allah ya kara”.
Babu wanda bai yi mamakin furucinsa, ranar suna yaran Ummi suka ci sunan Karima da Mukarama takaici ya cikata dan me za a asamata sunan Momyn Fadila amma data ji ance Baffa ne yasa saita dangana. Mahaifin Fadila kuwa ya ji daɗin hakan sosaai bisa karar da aka yi masa.
Kwanci tashi su Ummi suka shafe kwana talatin Abbu ya gaji da zaryar Haidar gidansa. Ranar da suka cika kwana arba in aka sake sabon ɗaurin aure a ranar kuma aka ɗaurawa mahaifin Fadila nasa auran da Hajiya Sarrinah mahaifiyar Sabah. An yi bidiri sossai hata Bahijja ta hallata tare da budurwar ɗiyarta yar shekara uku Ummyter yarinyar kwai farin jini kowa sonta yake yi mahaifinta ya ji daɗin hakan sossai nan da nan zumunci ya sake kulluwa.
Ummi zaune a ɗakinta shiru bayan tafiyarsu Hindatu, Haidar ne ya turo kofar yana murmushi suna hana haɗa ido ta ɗauke kai. Ya girgiza kai tare da karasowa ya ɗauki Mukarama yana shilata ta lura bai cika son ɗaukar Karimaba saita ɗauke ɗiyarta suka bar musu ɗakin. Jikinsa ya yi sanyi sai ya wuce ɗakinsa ya ajiye yarinyar kan gado ya shiga ya yo wanka ya fito ya yi mamaki yarinyar bata da rigima yasa hannu ya ɗauketa ya koma sashin Ummin lokacin daya shiga harta shirya kwanciya ita da Karimah ya kafeta da ido,
“Ummi menene haka?”.
Bata tanka ba sai kwalla fal idonta ta ciza ta furzar,
“Aliyu!”.
Yar! Tsikar jikinsa ta zuba ya zuba mata ido ta cigaba cikin muryar kuka.
“Kaiwa Allah karka rabamun kan yara na lura kwata kwata baka san ɗaukar Karimah tun muna gida shin meye laifin yarinyar nan? Koda shawararta aka samata sunan?”.
Kansa ya ɗaure duk yaji ya muzanta ashe tana kula dashi.
“Kiyi hakuri Ummi insha Allahu ba zan sake ba”.
“Na gode!”.
Sai ya yi murmushi ya mika mata yarinyar ta donta gyarata komawa ya yi ya ɗauki yarinyar ya zuba mata ido saita ɓangale masa baki yaji tausayinta yana neman hukuntata da laifin da bata ji ba bata gani ba. Ya runtse idanu saiga hawaye zuciyarsa na tuna abubuwa da dama. Ummi data daɗe a kansa ta dubeshi,
“Haidar ka sassautawa kanka”.
Ya sauke ajiyar zuciya,
“Ummyter DAWA ZANYI KUKA? Nabila kanwata? Koda Momy mahaifiyata? Ahamd aminina ko kuma da Fadila matata da surukata?”.
Tausayin Haidar ya nunku a ranta ta karɓi babyn ta kwantar da ita ta ɗago haɓarsa,
“Haidar komai MUKADARINE a rayuwar bawa kuma baya gujewa kaddararsa ina son ka ajiye tuna shuɗaɗɗun al amura masu cike da kunci cikin zuciyarka. Matukar zaka juri hakan wallahi bazaka sami farin ciki ba, kawai ka manta da damuwa ka tunkari abun da yake gabanka zai fi fata ubangiji yasamuyi kyakkyawan karshe”.
“Amin Ummyternah! Na gode”.
Daga haka suka kwanta.
ASUBA TAGARI AL’ASH.
Kwanci tashi su Ummi suka kwashi sati huɗu yaranta sunyi ɓul-ɓul dasu. Zumunci tsakaninta da su Bahijja sai abin da ya yi gaba kasancewar Khalifa ya dawo Nigeria gaba ɗaya kuma basu da tazara sossai.
Ummi na zaune tana feeding ɗin Mukarama Karimah na bacci Haidar ya shigo sai zuba kamshi yake ta sauk idonta akansa ya yi mata kyau shar dashi ta ce,
“Daddyn MK ina kuma zaka irin wannan fita fes haka?”.
“Hmm! Unguwa zani ina ruwanki ma da wankana?”.
Ta yi rau da ido,
“zance ko?”.
Shar! Saiga hawaye ai kuwa ya kwashe da dariya ya tafa hannu,
“ya isa beautyna bana son kukanki share taso ki rakani”.
Da murnarta ta shirya yana tayata suka fita. Kai tsaye gidansu Haidar suka fara zuwa Momy na zaune Nabila na shafa mata man ciwon kafa da ganinsu ta mike ta yi cilli da murfin man tana murna. Hajiya Sadiya ta dinga jin wani nishaɗi a ranta sun jima sossai ta dinga neman yafitar Ummi tare da Haidar Ummi ta numfasa tace,
“ba komai Momy Allah ya yafe mana baki ɗaya, amma Momy kisa Haidar ya yafewa Fadila har yanzu banji ya furta hakan ba”.
A nan ta dinga yi masa nasiha ya sunkuyar da kai ya furta,
“na yafe musu Momy”.
Yana rufe baki wayarsa ta yi kara ƴya ɗaga, sai ya dafe kai yana faɗin,
“innalillahi wa inna illaihirrraji un”.
Duk suka hau tambayarsa murya a dakushe ya ce,
“Ahmad ne ya rasu”.
Duk suka ɗauki salati nan ya bar Ummi ya wuce gidansu aka yi jana izarsa tare dashi. Sai yamma ya dawo suka wuce gida.
Kwanci tashi Ummi da Hindatu da Nabila da kuma Sabah suka kammala karatunsu aka yi graduate, sai dai kirikiri Aminu da Haidar sun hana aiki amma sun sakarmusu kuɗi sun haɗa kai su uku da Bahijja sun soma kasuwanci dama Bahijja da Ummi kansa suka yi karatu Hindatu ce data karanci aikin jinya Aminu ya buɗe mata ɗaki guda cike da kayan amfani take duba mata a gida. Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji ranar Asabar 16 ga watan December aka ɗaura auran Nabila Muktar Matazu da kuma Mahmoud Muhammad Kurfi. Sai kuma Sabah Hamza Katsina da Shamsudeen Suraj Kudan. ‘Daurin auran daya tara manyan likitoci yan kasuwa da kusoshin gwamnati. Da yamma aka yi walima aka kai amare gidansu. Nabila na tudun yola Sabah na rijiyar zaki.
SHEKARU BIYAR…….
Al ammura da dama sun faru masu daɗi dana cigaba ciki hadda haihuwar da Hindatu ta yi dakuma Sabah da Nabila. Haidar ya samu cigaba ya kara zama babban mutum magidanci. Haka lamura suka cigaba da wakana cike da kwanciyar hankali.
Hajiya Ummi zaune a katafaran falonta ɗiyarta mai kimanin shekaru uku ta shigo da gudunta,
“Mommah kinga Aunty Mk tana tsokanata wai bazasu gidansu yaya Ummyter dani ba”.
Daidai lokacin suka karaso yan matan biyu yan kimanin shekaru shida suna dariya suna yi mata gwalo. Tadira kafaffu alamun shagwaɓa daidai lokacin Dr Haidar ya shigo da sauri suka yi gunsa suna dariya Karima ta amshi jakarsa Mukarama ta amshi rigar likitoci ya ɗaga karamar yana faɗin,
“Nyc one Chuchunmu”.
Turo baki ta yi,
“Daddy kaima irin na Aunty Mk kake ko? Chuchu?”.
Ta faɗa tana narai narai da ido duk sai suka yi dariya suka zube kusa da mahaifiyarsu dake murmushi. Karimah ce ta kama hannun yarinyar,
“zo muje me sunan Mom in baki chakuletinki”.
Ai kuwa da sauri ta bita mahaifinsu ya rakasu da ido suna bada baya ya sauke idonsa kan Ummi yana murmushi.
“Yadai Madam!?”.
“Ya dai Drna?”.
Ya ja hancinta,
“yarinyar nan bakya tsufa, menene sirrin?”.
“Akwai sirrin Ummi daya wuce Dr Haidar ne?”.
Gaba ɗaya suka sa dariya cike da farin ciki…..
Mashaa Allahu.
Tammatabihamdullah.
Alhamdulillah………
K’arshe…………
Nan na kawo karshan wannan takaitacen labari mai suna KIYYAYA CE KO SON ZUCIYA?. Ina fatan ya zamo izina ga masu aikata rayuwa kwatankwacin ta taurarin cikin labari fatana a duba abin da yake da kyau na ciki a yi amfani dashi a kuma watsar da marasa amfanin ubangiji yasa mu dace. Har gobe kofa a buɗe take game hango gyara tattare da ɗan karambanin da nake na rike ALKALAMI ta hanyar Sanahsmatazu.wordPress.com ko kuma ta hanyar Sanahsulaimam96@gmail.com ni ɗin yar Adam ce akwai ajizanci tare dani.
Godiya ga ma abota bibbiyar wannan rubutu, har gobe ina alfahari da soyyayarku gareni na gode na gode sossai a karshe na sadaukar da wannan rubutu ga yar uwata MARYAM IDRIS KATSINA ubangiji ya saukeki lafiya.