KIYAYYAR ZUCI CHAPTER C KARSHE

 KIYAYYAR ZUCI CHAPTER C KARSHE 

[4/24, 13:58] Hafcie Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 36 📑*
*__________*📖”taya aka yi Kika San poison ne a ciki”.+

Hydar ya tambaya.

“Me na tambaya kuma? Ita ta sa poison d’in mana Amma ba ni ta ajiye ma ba shiyasa ta hanani sha”.

” ni ba muguwa bace kuma duk tsanar da nayi ma mutum ba Zan so ya mutu ba,poison nan ba ni na Saka ba but confirm akwai poison a ciki”.

“Kina nufin ni na Saka ma kaina poison?”

“Ehh ke Kika Saka Amma ba don kan ki ba,Hydar Kika sa ma”.

Kowa kallon Umma yake Hydar kuma Hafsat yake kallo..Salati Umma ta sake tace,

” ni?wace shaida kike da ita?sannan in Hydar na Saka ma garin yaya yazo nan”.

“Allah ne shaida na batun ya akayi yazo nan kuma ni na kawo da kaina”.

” baki da shaida kike tuhuma ta? “.

Juyawa Hafsat tayi tana kallon Hydar tace,

” Hydar trust me wallahi kai ta ajiye ma saboda ni ba sha nake yi ba”.

“Hafsat na San baza ki yi karya ba amma taya Zan yarda ba tare da naga hujja ba”.

Shiru tayi tana kallon sa tace,

” Hydar CC camera “.

Murmushi Umma tayi saboda Tun kan Hajiya Balaraba tazo tayi disconnecting na duk wani camera da ke gidan.

” yah Hafsat kin yi gaskiya “.

Daddy da sauran ‘yan gidan kam kallo suke yi musamman Hakeela sai hararar Hafsat take yi.

Room na Hydar duk suka bi sa yana shiga suka tsaya a falo shi kuma yaje bedroom ya d’auko system nasa Umma kam ko a jikin ta don ta San ba abunda zasu gani..yana connecting suka ga ba komai nan Umma tace,

” to munafuka yanzu kuma kina da Wata hujja ce?wato don d’azun nace kinyi sata Bari nima ki mini sharri ko?”

Shiru Hafsat tayi Daddy yace,

“How dare you?ke har kin kai ki yi ma mata ta sharri?”

“Daddy bar ta yau dai sai ta bar gidan nan”.

Hydar kallon ta yayi yaga kamar she is confused sai ya cigaba da pressing system d’in Ai ko sai ga vedi’on daga sanda Hajiya Balaraba tazo gidan har inda ta bata da kuma yadda ta shigo apartment nasu Hydar d’in ta zuba har yadda Hafsat ta kai falon can..

” alhamdulillah”.

Hafsat ta furta da k’arfi

“Shin yanzu ma zaki ce sharri na miki?Miji na Kika yi niyar kashewa kuma ni don gaba ne yasa na tona miki asiri ba don komai nan”.

Hydar was shocked haka ma Daddy basu ta’ba tunanin muguntar Umma ya kai haka ba..

Mari Daddy ya d’ebe ta da shi Wanda sanda taga wuta yana fad’in,

STORY CONTINUES BELOW

“‘Da na Kika yi niyar kashewa? Kije na sake ki saki d’aya”.

Hannu ta d’aura a kai tana fad’in,

” Dan Allah Alhaji kada ka mini haka”.

Fita yayi daga d’akin nan kowa ya Fara fita Aisha ko tana Allah wadaren halin Umma Khadija ko harara ta banka  Hafsat, Hakeela da Khaleel ma fita suka yi Umma ko tana ihu ta fice Hafsat ko murmushi tayi tace,

“Yanzu aka Fara”.

Suna fita Hydar ya bi Bayan su ya rufe k’ofa yana dawa yayi hugging na Hafsat d’in shiru suka yi na wani lokaci sannan yayi breaking hug d’in ya zauna kan kujera tare da janyota ya ajiye ta a cinyar sa sannan yace,

” thanks for saving me”.

Murmushi tayi tana fad’in,

“Ba sai ka mini godiya ba,wallahi ban ta’ba tunanin zata yi maka haka ba saboda Bayan tafiyar ka sai naje apartment na Baaba Ladi on my way back sai na ganta a apartment nan so daga yadda naga tana dube-dube na San she is up to something shiyasa sai na la’be nan naga ta zuba Abu cikin milk kuma na tabbata guba ce don itama sanda ta sa hand glob”.

Shafa fuskar ta yayi sannan yace,

Thanks once again”.
‘Bangaren Umma kuma tana fita sai kuka take ko kunyar idon yara bata ji ,d’aki ta wuce nan ta Kira Hajiya Balaraba tana picking tace,

” Hajiya wallahi asiri na ya tonu”.

“Garin yaya?”

“Wannan munafukar yarinyar ce ban San garin yaya ba tace Wai na sa poison kuma CC camera nayi disconnecting nashi sai kuma Hydar ya gano yanzu haka Alhaji ya sake ni”.

” k’awa ta saki fa Kika ce,duk lalata rayuwar ki da Kika yi don kawai kici gado sannan yanzu zai ce ya sake ki to wallahi kada ki tafi ki Tara masa manya sannan kuma kiyi tuban muzuru daga nan Bayan komai ya lafa sai kici uban Hafsat “.

” haka ko za’a yi k’awa ta”.
Tana katse kirar ta Fara kiran waliyan Daddy ta fad’a musu Bayan nan kuma ta Kira brothers nashi ta fad’a musu suka ce gobe in sha Allah suna hanya..
Hydar kam sauke ta yayi a cinyar sa yana Jan hannun ta suka nufi bedroom tana ganin sun d’auki hanyar bedroom nashi taja kafa ta tsaya..

“Ya dai?”

“Kowa ya kwanta a d’akin sa”.

” a kan me? “

“Haka kawai”.

‘Daga ta sama yayi yana fad’in,

” ni ba abunda Zan miki”.

“To Ai kaya na na can”.

Bai ce mata komai ba sanda suka Isa d’akin ya ajiye ta kan gado sannan yace,

” ki duba cikin kaya na sai ki sa”.

Toilet ta wuce tayi wanka sannan ta fito ita ma sleeping robe ta saka nan ya ringa mata dariya har ranta ya baci ganin da gaske ranta ya ‘baci sai ya janyo ta jikin sa suka kwantar..
Washe gari kuma sai ga waliyan Daddy a main falo suka sauka sannan aka Kira Daddy da Umma,tana shiga kanta a kasa sannan tace,

“Dan Allah yaya Ku basa hak’uri”.

Kai Munir yanzu me na sake ta da tsufan kun nan?”

“Yaya Hydar fa tayi k’ok’arin kashewa”.

” wallahi yaya sharrin shaidan ne kuma nayi alkawarin bazan Kara ba”.

“Haba Zulai Ai kisan kai wasa bane,don kawai bake Kika haife sa ba sai ki kashe sa?”

Kuka ta ringa yi can yaya ya sake cewa,

STORY CONTINUES BELOW

“Me kike tunani Harda zaki yi k’ok’arin kashe sa?”

Kuka take ta yi kamar zata had’iye ranta tace,

“Wallahi nayi da na sanin abunda na aikata kuma ko yanzu aka Kira su Zan basu hak’uri Amma ni kada Alhaji yace na bar masa gidan sa”.

Shiru suka yi daga yadda take kuka sun San tayi nadama don haka sai aka Kira Hydar nan ko ta basa hak’uri bai ce komai ba ya mik’e sai yaya yace,

” Munir tunda shi Wanda aka yi niyar kashewa ma bai damu ba Ai sai Kayi hak’uri duk Mun San halin Zulai ba kyau Amma kuma ta zama mana kashin wuya ba yadda muka iya da ita ka hakura ka maida auren Ku tunda kun haifi yara”.

Shi Daddy ya San bai Isa yayi jayayya da Yaya ba don haka yace,

“Ba komai Allah shige mana gaba”.

Amma cikin zuciyar sa bai yafe ma Umma ba..godiya sosai ta ringa musu nan suka tashi Daddy ya musu rakiya ita kuma murmushi tayi tace,

” wallahi banga uban da zai raba ni da ke ba Hafsat “..

**

Bayan kwanciyar su sai ta juyo tana fuskantar sa tace,

” Hydar Anya Umma ce ta haife ka?”

Da wuri ya juyo yana kallon ta yace,

“Me yasa Kika tambaya?”

“Gani nayi ba Uwar da zata yi k’ok’arin kashe ‘danta “.

Shiru yayi yana kallon ceiling saboda shi bai shirya fad’a mata dalilin sa na ‘boye mata Ammie’n shi ba..

” tunanin me kake yi?”

“Babu yace yana shafa jikin ta a hankali ya canza salon sa tana ganin haka ta yunkura zata mik’e Amma ya hanata dole ta basa abunda yake so..

Washe gari kuma Tun Bayan sallar Asuba yayi wanka sannan yace da ita zai d’an fita a hanyar fitar sa ne kuma su Daddy suka Kira sa nan yaji ransa ya ‘baci sai ya nufi apartment d’in yana shiga ya kwanta kan kujera..

” lafiya kuwa ka dawo?ina cewa Kayi zaka fita?”

“Kai na ke d’an ciwo yi mini massage Dan Allah”.

Massage take masa Amma tana nazarin sa don ta tabbatar akwai wani Abu a k’asa a hankali tace,

” Daddy ya maka magana ne?”

“Ehh yayan sa ne yazo da batun a maida auren Umma kuma an mayar”.

Sosai zuciyar Hafsat ya buga Amma sai ta batsar shiko har bacci ya Fara yi.. Tsaki yaja sannan yace ina zuwa.mik’ewa yayi ya nufi apartment na Ammie..

Umma ko tana safa da marwa a d’aki yadda zata bulloma Hafsat sai ga Hakeela ta shigo hannun ta d’auke da tea ta ajiye sannan tace,

” Umma ki sha wannan zaki ji sauki”.

Murmushi d’auke a fuskar ta tace,

“Hakeela na San ba wannan bane ya kawo ki fad’i damuwar ki ina ji”.

” ba komai Umma “.

” Hakeela nasan cewa baki son Hafsat wannan dalilin yasa Kika mata sharri da jiya da safe”.

Shiru tayi sai Umma tace,

“Kada ki ji komai fad’a mini”.

” Ehh Umma bana son ta ko kad’an “.

” good, nima ba son ta nake ba Kinga sai muyi aiki tare wajen ganin Bayan ta”.

Murmushi Hakeela tayi sannan tace,

Wannan haka yake”.

yana gab da shiga sai yaji Abu ya fad’i da wuri ya k’arasa d’akin sai ganin Ammie yayi tana k’ok’arin mik’ewa hakan ko ba k’aramin mamaki ya basa ba..

STORY CONTINUES BELOW

Da kyar take numfashi sannan harshen ta ta gagara d’aga sa da wuri ya k’arasa ya tallafe ta tana fad’in,

” Hy..d..a..r. ba…”

Sai maganar ya kasa fita.

“Ammie ina jin ki ba me ba?”

Har wuyar ta take d’agawa don yadda take son masa magana da kyar tace,

“Ba..Malam Musa…bane”.

” shiru yayi can yace,

“Ba malam Musa bane yayi me?”

“Ba..shi..bane…Umman ka..ne”.

Jin tace haka da wuri ya kwantar da ita sannan ya fita yana kwala Kira

” Daddy ka zo Ammie na magana”.

Gaba d’aya ya tada hankalin ‘yan gidan,Umma da ke tare da Hakeela jin abunda Hydar ke fad’a da wuri ta zare allura ta fita da gudu sai d’akin Ammie tana shiga ko ta chaka mata allurar nan Ammie ta koma unconscious nata..

Daddy da gudu ya fito a tare suka shiga d’akin sai gilmawar inuwar mutum suka gani ta window amma saboda hankalin su a kan Ammie yake sai ba Wanda ya damu da inuwar da suka gani..

Mik’ar da ita Hydar yayi yana fad’in,

“Ammie ki fad’a ina jin ki”.

To his surprise sai yaga ta koma yadda take..

” Anya Hydar maganar da ka fad’a gaskiya ce?”

“Wallahi Daddy ta Kira sunana har ma tace…..”

Sai kuma yayi shiru

“Tace me?”

“Babu yace yana jin kamar hawaye zai fita a idon sa,nan ko Hakeela ta kare ma Ammie kallo sai kuma tayi tunanin yadda Umma ta zare allurar hakan ya sa ta Fara tuhumar Umma sannan Tasa a ranta koma mene ne sai ta gano..

Fita tayi su Aisha duk suka fice sai Daddy da ya dafa kafad’ar sa yace,

” take it easy”

Sannan ya fice Hydar ko sa hannun sa yayi cikin na Ammie hoping zata tashi ta masa magana Amma a banza sai ma su Fareeda da yanzu suka dawo daga skull kallon su yayi sannan yace,

“Ku sa ido a kanta tayi bacci Amma kada Ku barta ita d’aya”.

” in sha Allah “

Jikin sa a mace ya mik’e direct apartment nasa ya nufa yana shiga ya tarar Hafsat ta gama shara tana sassake labulaye at the same time tana fesa room freshner..ko inda take bai kalla ba ya wuce bedroom ko gabar sa baya kallo da ido ta bi sa don ta tabbatar akwai abunda ke damun sa,sanda ta gama sannan ta nufi bedroom nasa hannun ta rike da cup na ruwa ba tare da tace komai ba ta mika masa nan ya kar’ba ya sha sannan ta zauna kusa da shi tace,

“Baka da lafiya ne”.
Kai ya girgiza mata saboda ya rasa wace irin tsana ce Umma ta musu da har zata yi k’ok’arin kashe sa shida mahaifiyar sa..

” Hydar you can share ur problem with me”.

Shiru yayi har ta cire ran zai yi magana sai ya rike hannun ta suka fita apartment d’in basu saya ko ina ba sai apartment na Ammie, Hafsat was surprise don baza ta manta ba wannan d’akin ne aka hanata shiga farkon zuwan ta gidan nan.

Kallon falon take yi nan taga enlargement na Ammie wacce ko ba’a fad’a mata ba tasan ita ce mahaifiyar Hydar, haka yaja ta har cikin bedroom sannan yace,

“Lokacin da muke wancan gidan kin tambayi dalilin Kiyayyar gidajen mu,ni kuma wannan shine dalili na na tsanar ‘yan gidan Ku”.

Ya fad’a yana nuna mata Ammie, cire hannun ta tayi cikin nasa tana kallon Ammie haka kawai matar ta shiga ran ta.

STORY CONTINUES BELOW

” Hafsat wannan ita ce mahaifiya ta Ammie na she is paralyzed for note than three years bata ko d’aga hannun ta bare tayi magana”.

Sosai Hafsat taji tausayin Hydar sannan ta mayar da kallon ta kan Ammie a hankali ta rike hannun Ammie nan take Ammie ta bud’e idon ta murmushi Hafsat ta mata Wanda Hydar kan sa ya San Ammie taji dad’in hakan.. Zama yayi gefen Ammie sannan yace,

“Ammie wannan ita ce mata ta kuma surkuwar ki”.

Kallon Hafsat d’in take yi nan Hydar yace,

” Hafsat ki mata magana tana ji,matsalar kawai baza ta iya mayarwa ba”.

Fuskar Hafsat d’auke da murmushi tace,

“Ammie Allah baki lafiya”..

Ciki-ciki Hydar ya amsa da Ameen a hankali kuma Ammie ta lumshe ido sai bacci ganin tayi bacci sai Hafsat tace,

” kace wannan ita ce silar da yasa ka tsaki ‘yan gidan mu?”

“Ehh”.

” ban fahimci zancen ba”.

Mik’ewa yayi ya zura hannun sa a aljihu ya bata baya sannan yace,

“Hafsat ban San farkon Kiyayyar nan ba kamar yadda baki sani ba amma abunda na sani shine,lokacin da nake da shekara biyar a duniya Wata Rana Dani da Sister’s na Mun tafi makaranta lokacin kuma ba’a haifi su Fareeda ba don Khaleel shekarar sa d’aya, Daddy ya fita wajen aiki Ammie da Umma kad’ai aka Bari a gida sai Khaleel don lokacin Daddy bayi da kud’i sosai,Bayan tafiyar sa sai ‘yan fashi suka shigo gidan da sunan an turo su su kashe Daddy Amma sai suka tarar baya nan,don haka sai suka ci zarafin Umma da Ammie to the extend that suka yi rapping Ammie na”.

Hafsat na jin haka ta rintse idanun ta da k’arfi sannan yaci gaba

” Bayan sun gama abunda zasu yi nan suka buga ta da k’arfe har ta suma,fitar su ke da wuya neighbors suka Fara shigowa suna jaje nan aka Kira Daddy aka sanar da shi kuma ba k’aramin tashi hankalin sa yayi ba yana zuwa aka nufi hospital da ita Bayan ta warke sai Daddy ya d’auke mata fuska ko gaisuwar ta baya amsawa nan ta shiga damuwa sosai,abunda zai baki mamaki kuma Abban ki ne ya tura su lokacin ni yaro ne ban San meke tafiya ba sanda na girma Sister Zainab da Maryam..

Mik’ewa tayi tace

“No Hydar Abba na ba zai aikata haka ba”.

” ba Wanda bai San Abban ki ne ya tura su ba wannan dalilin yasa har makobta suke gudun Ku”.

“Wallahi Hydar Abba na ba zai aikata haka ba”.

” Hafsat ko ke ce a matsayi na dole Kice shi ya aikata hakan Amma abunda ya bani mamaki d’azun Ammie tayi magana “.

” magana fa kace?”

“Ehh”.

” for the past three years bata yi magana ba sai yau to tabbas akwai wani Abu a k’asa “.

” yah kuma abunda tace shine ba Abban ki bane Umma ce jin haka sai naje kiran Daddy Amma kan na dawo ta koma wannan condition “.

” tabbas akwai wani Abu,may be allura ake mata wannan dalilin yasa jikin ta ya zama weak shiyasa baza ta ta’ba tashiwa ba don allurar ya kashe duk wani k’arfin jikin ta”.

“Ehh Hafsat maganar ki gaskiya ce saboda lokacin da na shigo naga gilmawar mutum”.

” kaga kenan mai cutar da ita na gidan nan kuma tunda tace Umma ce dole mu sa mata ido”.

“Ehh Amma ta yaya?”

“Hydar kamata yayi mu nemi wani na kusa da ita shi zai ji mana sirrin ta”.

” Hafsat kin San ke kam ta tsane ki k’awar ki kuma ban yarda da ita ba”.

STORY CONTINUES BELOW

“To ya zamu yi?”

“Let’s just watch her steps”.

” yah hakan ma yayi”.

Washe gari kuma kowa na zaune a dining table Hakeela ce farkon zuwa taci ado sosai don tayi impressing Hydar duk Wanda ya shigo kuma sai ta kalle sa don a tunanin ta Hydar.
Hydar na shigowa falon yaga Hakeela zaune a kujerar dining wani bakin ciki ne ya kamsa akan me shi ba za’a ci abinci da matar sa ba amma wannan ko sati bata yi ba har ta samu fuskar zama a dining..

Kitchen ya wuce direct inda ya d’auki cups biyu sannan ya had’a tea ya d’aura akan k’aramin tray nan ya fito kuma sai yanzu Hakeela ta gansa da wuri ta mik’e ta nufe sa

“Ya Hydar ina kwana?”

Cikin kamewa da kuma rashin sake fuska yace,

“Lafiya”

Sannan ya Fara tafiya da wuri ta sha gaban sa tace,

“Dan Allah Kayi hak’uri kan abunda ya faru shekaran jiya”.

Banza ya mata sannan yabi ta gefen ta ya wuce sai yanzu ta Lura da cups na hannun sa.

” lallai Hydar duk sacrifice da nayi na auri Khaleel don na mallake sa amma ace ko kallo ban ishe sa ba,sannan Hafsat kuma tana can tana bacci shi zai kai mata tea Zan San yadda zanyi da ita tunda Umma na sight na”.

Hydar ko yana shiga apartment nasu ya bud’e k’ofar sannan ya mayar ya rufe nan yaji d’akin sai kamshi yake Hafsat d’in tayi wanka ta sanya Riga da skirt sai dai ya Dan matse ta..

Tana kallon sa da tea ta kar’ba ta ajiye a dining tana fad’in,

“Yau kuma a nan zaka yi breakfast ne?”

“Ehh kuma tare da ke Kinga two cups na kawo”.

” ni kam a koshe nake”.

“Me Kika ci?”

“Babu”.

” to wallahi ko d’ura sai na miki”.

Murmushi tayi tace,

“Zan sha fa”.

” da yafi miki kam”.

Ganin ya Dan sake ba kamar jiya ba don sai tunanin Ammie yake nan tace,

“A Dan mini waya na Kira Maama na”.

” Maamar mu zaki ce”.

Sa hannu yayi ya cire wayar sannan ya mika mata nan Tasa number’n ya Abdool Amma sai taga number’n ya fito da suna kallon sa tayi tace,

“Kana da number’n sa ne?”

“Ba dole ba tunda ina son kanwar sa”.

Sosai zuciyar ta ya buga da yace yana son ta duk da ta San cewa daga yanayin sa yana sonta Amma bata yi tunanin zai fad’a ba..

” kallon fa?”

Da wuri ta firgita sai ji tayi ya Abdool na magana cikin wayar

“Wa’alaikasalam”.

Hydar ko kwanciya yayi a jikin ta
” Hafsat ke ce?”

“Ehh ya Abdool ya gida da kowa da kowa?”

“Kowa lafiya Hafsat ke fa?”

“Lafiya ta kalau ya Saudat”.

” tana lafiya Fateema ma taje Katsina”.

“Lallai Sis Fatee shine ko ta sanar da ni”.

” maida wukar favorite Aunt naki ce tace taje by the way ya yake?”

STORY CONTINUES BELOW

“Waye kenan?”

Ta tambaye shi tana murmushi don ta fahimci Hydar yake nufi.

“Hafsat kinci gidan Ku Waye banda Hydar”.

” yana lafiya “.

Tace tana kallon Hydar da ita shima ita yake kallo.
Hira suka ta’ba kad’an sannan suka yi sallama..

” wannan yayan naki akwai sa ido”.

“Yaya na kaje fadawa haka”.

” karya aka masa,Randa aka d’aura mana Aure har da kunne yaja mini Wai kada na kuskura naje kusa da k’anwar sa”.

“Hmm”.

Kawai tace..
Bayan sati biyu!!!

Tun daga wannan ranar Hydar ya daina breakfast da ‘yan gidan su sai dai ya d’eba ya kai musu da Hafsat d’aki sannan Hakeela kuma har yau bata samu fuskar sa ba,shi da Hafsat ko suna rayuwar su yadda ya dace ba tare da kowa yasa musu ido ba..

Yau ma da daddare kowa na dining d’in ya shigo nan ya d’auki plate ya Fara loda abinci Hakeela na ganin haka Tasa hannu ta kar’bi serving spoon d’in ta Fara sa masa shi kuma sai ya d’auki wani ya cigaba da zubawa ganin haka sai ta cire hannun ta.yana gamawa Daddy yace,

” Hydar duk wannan abincin kai kad’ai? “

“Ehh Daddy yunwa nake ji sosai”.

” ohk in ka gama ina da magana da kai”.

To yace ya fice Umma da Hakeela kuma sun San Hafsat zai kai ma Amma ba bakin magana…

Bayan ya kai abincin apartment nasu sai Hafsat ta kar’ba tunda yanzu ta Saba da d’ebo musu abincin da yake sai suka zauna suka ci suna gamawa yace

“Daddy na nema na Bari naje”.

” a dawo lafiya “.

Daga haka ya wuce bedroom na Daddy..

” Hydar dalilin kiran ka ba don komai bane sai rashin cin abinci da mu,bana jin dad’in hakan”.

“Ka gafarce ni Daddy bazan iya cin abinci da Ku ba don gani nake kamar za’a sake cutar da ni”.

” na sani shiyasa Tun farko na maka uzuri saboda so nake Kayi adjusting kan ka sake komawa normal “.

” Daddy akwai Wata alfarman da Zan nema Amma kada ka mini mummunan fahimta”.

“Ina jin ka”.

” Daddy duk da Aure na da Hafsat kan kiyayya aka Gina ta sai gani nake kamar ba’a mata adalci saboda ba yadda za’a yi matar Khaleel ta zauna a dining aci abinci da ita suna hira da Khaleel sannan Hafsat kuma a hanata wannan damar amma fa kada kace don ita na daina cin abinci da ku”.

“Na gane kada ka damu kwanan nan Zan nemo maka mata ka aura”.

Da wuri yace,

” A’ah Daddy ban shirya ma wani Aure yanzu ba sannan da wani ido zamu ga jama’a Aure na da Hafsat fa bai fi Wata 4 ba”.

“To yanzu ya kake so ayi don gaskiya ba Zan iya cin abinci da matsiyaciyar nan ba”.

” Daddy ko me zai Hana mu maza muyi namu daban su mata suyi nasu”.

“A’ah wannan wargaza family ne Amma dai kaje zanyi tunani a kai”.

” ohk na gode”.
Washe gari kowa na dining Harda Hydar Hakeela tazo zata zauna Daddy yace,

“Stop”.

Tsayawa tayi Umma ko sai kallon Daddy take nan Daddy ya tura Wata servant ta Kira Hafsat..

STORY CONTINUES BELOW

Kowa da ido yake bin Daddy Harda Hydar sai can ga Hafsat tazo..

” daga yau na yanke shawarar Hakeela da Hafsat baza su sake zama a dining domin cin abinci ba kowa taci a d’akin ta saboda ni surkin su ne bai kamata mu ringa cin abinci tare ba”.

“Amma Alhaji”

“Dakata Zulai har yau kina da ta’bo a ido na”……

Comment
Share
©Hafciey
[4/24, 13:58] Hafcie Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 37 📑*
*__________*📖wucewa tayi fuskar ta a had’e da alama ta sha kuka hat ta gaji..

“Saudat”.

Lawal ya Kira ta amma sai ta banka masa uban harara ta wuce cikin gida da wuri ya mik’e ya bita amma kan ya Isa ta shiga d’aki sai Maama ya gani a kitchen..

” sannu da aiki Maama”.

“Yauwa Lawal ka shigo kenan?”

“Ehh Saudat na gani ta shigo gida fuskar ta a kumbure da alama kuka tayi”.

” Saudat d’in? “

“Ehh Ima zaune a waje ta wuce”.

” amma yau fa za’a basu hutu to me ya sa ta kuka?”

“Ah hab yanzu na gane zancen tayi wasa result nata bai yi kyau bane”.

” kai zai yi wuya saboda Saudat na k’ok’ari bata wuce lamba ta goma”.

Shiru duk suka yi Saudat ko tana jin duk yadda suke yi can Maama tace,

“Bari na duba ta”.

Yin duniyar Allah’n nan Maama tayi amma Saudat taki fad’a mata abunda ke damun ta don haka sai ta fito taci gaba da aikin ta.sai can Abba ya dawo kuma har yanzu Lawal na zaune, Bayan sun gaisa da Abba sai Maama ta sanar da shi cewa tunda Saudat ta dawo daga makaranta take kuka sun tambaye ta abunda ke damun ta amma taki fad’a nan ya Kira Saudat d’in da kansa…

” Saudat me aka miki a makarantar “.

Cikin Jan majina kamar yarinya tace,

” Abba dama an canza mana form master kuma daga zuwan sa sai yace yana so na ni kuma da ya fad’a mini sai na d’ebi kawaye na muka je muka ci mishi mutunci,Bayan Mun ci mishi mutunci sai yace mini zai yi magani na a zato na zai had’a ni da principal ne sai naji shi shiru hakan ya bani damar masa rashin kunya duk inda na gansa tare da friends na don na sa a raina in ya kai Kara ta zance shi ya Fara cewa yana so ns kuma kawaye na shaida ne..duk abunda nake masa bai ta’ba ce mini komai ba bare yace zai d’auki mataki sai yau Bayan Mun gama exams namu naje kar’bar result na sai na ganni a second to the last rai na ba k’aramin ‘baciwa yayi ba direct office na Vice principal na wuce nan na nuna masa da yake ya San ina da k’ok’ari sai yasa aka kawo masa script na nan ya duba amma sai muka ga duk na fad’i a wajen, sai ya sake kar’ban record sheet na teacher’s nan ma haka ne saboda ga signature ko wani teacher nan yace nayi wasa amma nace Sam ba haka ba sai yasa aka Kira from master’n mu yana zuwa aka ce garin yaya nayi wasa haka?sai cewa yayi a yanzu ban damu da karatu ba sai bin samarin makaranta nan vice principal ya zage ni tas sannan aka bani suspension na Wata 1 Bayan anyi resuming kuma ance in na tashi dawa na dawo da iyaye na”..

STORY CONTINUES BELOW

“‘Dan gidan uban Waye shi?”

Lawal ya tambaya d’aga masa hannu Abba yayi ban taci gaba da fad’in,

“Ina fita a office na vice sai na wuce wajen best teacher na shima holo ya mini a nan yake ce mini duk teachers suna kallon rashin kunyar da nake masa nan aka yi meeting da shi sai ce musu yayi nace ina son shi da yaki shine nake masa rashin kunya iri-iri shiyasa ko wani teacher ya yarda ni don su nuna mini rashin dacewar abunda nayi”.

Tana gama fad’ar haka Lawal ya Mik’e Abba na kiran sa bai saya ko ina ba sai makaranta su Saudat direct wajen principal ya wuce..

Allah ne kad’ai ya San me suka tattauna sai ga principal na kiran Abba nan ya wuce skull d’in yana zuwa aka Fara basa hak’uri kan abunda aka yi ma Saudat sai yace,

” ya San ba’a mata dai-dai ba amma ita ma tana da nata laifi na masa rashin kunya don haka ya na mai basu hak’uri bisa ga rashin kunyar Saudat “.

Nan principal yace ba komai suka kama hanyar gida shi da Lawal a hanya yace,

” Lawal me kace musu ne?gani nayi wannan zamanin ba mai sauraron talaka “.

” ba komai Abba kawai na fahimtar da su rashin dacewar abunda suka mata ne “.

A haka har suka Isa gida nan Abba yace an janye suspension d’in saboda Lawal sannan ya mata holo na abunda tayi sannan ya koma wajen aiki..

Lawal ma mik’ewa yayi ya nufi d’akin su nan Maama ta kalli Saudat tace,

” wato duk da abunda aka miki a makaranta baza ki bar rashin kunyar ba ko?”

“Me kuma nayi Maama?”

“Yanzu kin gode ma Lawal ne?”

Shiru tayi can tace,

“Ai don Allah yayi ba sai na gode masa ba”.

Jefin ta Maama tayi da cup tana fad’in

” wuce kije ki masa godiya “.

Tura baki tayi tana gunaguni ta wuce d’akin a k’ofa tayi sallama ya amsa sannan ta shiga ta tsaya jikin gini..

” ya dai malama Kika tsaya a kai na”.

“Dama nazo na maka godiya ne”.

” hmm”.

Kawai yace sannan tace,

“Na gode”.

” a garin Ku haka ake godiya ne?”

Tana hararar sa tace,

“To ya ake yi?”

“Durkusawa zaki yi”.

” Allah sauwaka”.

Tace sannan ta fita daga d’akin Maama na ganin ta tace,

“Kin masa godiyar?”

Kan ta bada amsa daga d’aki taji Lawal yace,

“Maama bata yi ba”.

” wallahi Saudat Zan dakaki yau”.

Da wuri ta koma amma bata ce komai ba..

“Nifa ba godiyar ki nake so ba kawai alfarma Zan nema a wajen ki ki fad’a mini dalilin ki na tsana ta”.

” Bayan kazo ka takura ma mutani a gidan su sannan kace a fad’a maka dalilin tsanar ka”.

Ta fad’a a zuciyar ta Wata zuciyar kuma ce mata yayi Ai ba don shi ba da yau kun Kara shiga Tashin hankali..

“Ina jin ki”.

Shiru kawai ta masa

” in har baki da abun fad’a to Dan Allah ki ajiye wannan tsanar a gefe mu zama friends “.

STORY CONTINUES BELOW

Da wuri ta d’ago ta kalle sa

” pls”.

A hankali tace,

“Zanyi tunani”

Sannan ta mik’e ta fita da wuri.

Aisha kam yanzu lamarin Abdool ya koma bata tsoro don ya daina kiran ta tsam in ta zauna sai tayi ta tunanin sa amma kuma ba hali ta bayyana masa don ta fahimci kamar relationship d’in ne baya so kuma baza ta Hana sa ba ko da zata iya mutuwa..wayar tace tayi ringing tana dubawa taga sunan Abdool ihu tayi ba tare da tayi realizing su Waye a wajen ba sannan ta wuce d’aki ta gudu tana receiving call d’in Umma ko kallon su Fareeda tayi tana fad’in,

“Aisha ta samo mini d’an gidan manya yanzu auren ta za’a yi wasu kuma haka zasu yi ta zama babu miji”.

Duk sun fahimci da su take amma sai suka yi kamar basu ji me tace ba..
” Hello baby sai yau ka tuna da ni”.

“Ba haka bane wallahi aiki ne ya mini yawa”.

” Ai kullum haka kake fad’a ya kake?”

“Ina lafiya kuma na Kira ne don naji lafiyar ki sannan na tayaki murnar auren da yayan ki yayi”.

” ohh I see,Abdool ina labarin soyayyar mu kuma?”

Tana fad’in haka ya katse kirar ita ko bakin ciki ne ya kamata wato ma baya son maganar..
Lawal da ke gefen sa ne ya kalle sa yace,

“Ya dai Abdool?”

“Wallahi nayi kuskure Tun farko bashi ba hali na gyara saboda Aure na da Aisha ba Abu bane mai yiwuwa in ba haka ba da na Aure ta kawai”.

” Aboki na kace ka fad’a mana,to me zai hanaka fad’a mata gaskiya? “

“Bazan iya ba”.

” kamar ba na miji ba”.

“Ina tsoron halin da zata shiga ne bugu da Kari Hafsat na gidan su ban San yadda zasu yi ma Hafsat ba in sun fahimci ina son Aisha”.

” Kayi gaskiya aboki na to ya zaka yi da Aisha? “

“Kace ya zanyi da soyayyar Aisha😊”.

***

Sulaiman ne zaune gaban  Baban sa  da Maamar sa kansa a k’asa.

” Sulaiman na gama maka shiri sannan kuma na yanke shawarar zaka tafi Dubai Kara karatu tunda Hafsat Allah bai yi zaka Aure ta ba kuma a gidan aboki na Alhaji Bashir zaka zauna”.

“Gaskiya Baba ni ba inda zanje”.

” PhD fa zaka je Kayi a can”.

“Ehh zanyi a nan Nigeria”.

” aiko baka Isa ba tunda ni na haife ka ba kai ka haife ni ba”.

Mik’ewa yayi zai fita Baban sa yace,

“Wallahi in ka Kara fita k’ofar gida Allah ya Isa,baka ba waje har sai Randa ka yarda zaka je”.

Fitar sa yayi ya nufi d’akin sa yana ta bala’i shi d’aya saboda shi ba zai iya barin Hafsat da Hydar ya tafi ba..

Wannan dalilin yasa kowa jin Sulaiman shiru Barka da Hakeela da ya mata alkawarin zasu ringa aiki tare..

Yana fita Baban sa yace,

” Hajiya ki ji yaro alkhairi na kirar sa tsiya na kori,yanzu fisabilillahi in suka dai-dai ta da yarinyar nan Ai munji dad’i har shi kansa”.

“Ai dole mu tashi tsaye Alhaji don wallahi sai Sulaiman ya auri Tasleema”.

STORY CONTINUES BELOW

” barni da shi ke kam”.
Jin Sulaiman shiru har fiye da sati yasa Baban sa sake kiran sa sannan yace in bai amince ba zai tsine masa sannan ya bashi sati yayi tunani a kai..

Ganin ba sarki sai Allah yasa Sulaiman ajiye duk Wata buri da yake da ita a kan Hafsat ya tunkari mahaifin sa da batun ya amince Amma kuma yasa a ransa tunda shekara d’aya zai yi sai ya dawo gare ta.sosai Baban sa yaji dad’i nan ya ringa sa masa albarka sannan yace musu tunda gobe ne tafiyar sa zai je ya sallami Hydar nan suka masa a dawo lafiya..

**

Bayan Daddy ya gama fad’ar decision nasa sai ya mik’e sannan ya dubi Hafsat yace,

“For the fact that na barki a apartment na Hydar sannan nace Ku ringa cin abinci a apartment naku doesn’t mean nayi accepting naki a matsayi Surkuwa saboda matsiyaciya baza ta ta’ba zama Surkuwa ta ba”.

Yana gama fad’ar haka ya wuce Hakeela ko cewa tayi komin yaya akwai lauje cikin Nad’i Hydar ko Sam decision d’in bai masa ba.ganin Daddy ya tafi sai Umma tace,

” Hydar da kai da Khaleel Ku koma cin abinci a apartment naku tare da matar Ku saboda don ba auren soyayya aka maka ba hakan ba zai sa a tauye ma Khaleel da Hakeela hakkin su ba”.

Da jin batun Umma Hakeela ta tabbatar tabbas akwai Abu tsakanin su da Hafsat Hydar ko cewa yayi

“To dama ni me Kika ji nace,ina ruwa na da wani tauye musu hakki”.

Hararar sa tayi can tace,

” sannan kuma daga yau Hafsat da Hakeela Ku zaku na girki Ladi sai dai ta tayaku sannan kuma kwana biyu-biyu zaku ringa yi”.

Kowa dai sauraron ta yake ita ko murmushi tayi a zuciyar ta tace,

“Wannan ita ce damar da zanyi amfani da shi wajen cire duk wani abunda Hydar ke ji game da ke a zuciyar sa saboda na fahimci take-taken sa”.

Mik’ewa Hydar yayi Hakeela ko sai bin Hafsat da kallo take yi, Hafsat d’in ma mik’ewa tayi zata bi Bayan Hydar Umma tace,

” ina kuma zaki Ai yanzu zaki d’aura girkin Rana tunda ke Kika Fara shiga gidan”.

Juyawa tayi ta kalli Hydar d’in Wanda har yayi nisa sannan ta nufi hanyar kitchen zata shiga kenan Hydar ya tsaya daga k’ofar falon yace,

“Hafsat”.

” Na’am”

Ta amsa tana fitowa daga kitchen d’in Umma da Hakeela kuma sai bin ta da ido suke yi ko inda suke bata kalla ba ta fice tana fita ya mata Peck a kumatu sannan yace,

“I am leaving”.

Murmushi kawai tayi tare da fad’in

” a dawo lafiya”.

Sannan yayi waving nata ya wuce parking lot domin d’aukar mota ita kuma sai ta koma ciki a zaune ta tarar da  kam kujera  sai kawai ta wuce kitchen nan ta tarar Baaba Ladi.

“Baaba me zamu d’aura?”

“Hafsat kin San sun fi son Rice da Rana”.

Nan ko ta yanke shawarar d’aura rice and stwe sai cost low da kuma su cabbage Baaba na taya ta kan su gama Umma tayi upstairs Hakeela kuma ta koma apartment nata..

Sun dau lokaci kan su gama nan ta jera a  nan ta Kira kowa d’aya Bayan d’aya suke fitowa Hakeela kuma taci adon ta sai kamshi take ta zauna sai wani hura hanci take haka ma Khaleel da yanzu ya shigo kuma Tun first night nasu ya fita harkar ta..kasancewar yanzu Daddy yayi handling company’n shi ma Hydar sai bai fiya fita ba yanzu ma yana gida so lalla’ba shi Umma tayi da kyar ya fito don haushin ta yake ji har yanzu..

STORY CONTINUES BELOW

Zama yayi sannan Hafsat d’in ta Fara serving nasu Aisha kuma sai murmushi take.. Umma ce farkon kai abincin bakin ta sai ta tsaya dube-dube nan Aisha ma ta kai bakin ta amma sanin Hafsat ce tayi girkin sai bata ce komai ba..Daddy na kaiwa bakin sa ya Fara tari da wuri Umma ta mika masa ruwa ya sha yana gamawa yace,

” Ladi”.

“Me ya faru Alhaji?”

“Wannan borkonon fa?”

“Ai ba Ladi bace tayi girkin Hafsat ce kuma intentionally Tasa borkonon tunda ba yau ta Fara girki a gidan nan ba kuma ta San duk yaran gidan nan basu son borkono”.

Mari ya d’ebi Hafsat da shi sannan yace,

” uban Waye yace tayi girki yau”.

Hafsat kam ba sai hawaye ba nan Umma ta Fara bashi hak’uri tana cewa

“Wallahi nice Bayan tafiyar ka sai nace su raba girki amma nasan mugunta ne ya sata sa borkono”.

” get out of my sight “.

Ya fad’a yana kallon Hafsat d’in nan ta fice da wuri tana jin kamar kuka zai fito..jingunuwa tayi jikin gini tana hawaye don ta San tabbas Umma ce ta sa mata borkono nan taji Umma tace,

” Kayi hak’uri yanzu Hakeela zata yi maka girki mai dad’i “.

Tsaki yaja sannan ya Fara tafiya nan hakeela tace

” Daddy Kayi hak’uri wallahi Hafsat ko a gidan su hak’uri ake da ita don in bata yi niyar abuba ko uban ta hak’uri yake”.

“Ai ubanta Kika ce ni kuma bazan yi tolerating nata ba”.

” to Daddy ka bani damar maka girki”.

“Ohk ki yi amma ban salt saboda ina da hawan jini sannan banda borkono don ulcer”.

Hafsat da ke waje tana jin su tana kuka jin abunda Daddy ya fad’a sai tayi murmushi Wanda ita kad’ai ta San dalilin sa..apartment nata ta wuce sannan ta dad’a gyarawa ban ta kwanta ta kunna t.v a falo Hakeela ko na kitchen sai daman had’a girki take saboda tuwon Accha da miyan alaiyaho zata yi..Aisha ce zaune a falon tana chatting can Hafsat ta shigo falon ta zauna next to Aisha nan Aisha tace,

” Mrs Hydar kin fito kenan? “

“Ehh wallahi na gaji da zama ni d’aya ne kuma na lek’a wajen Baaba Ladi amma ta fita”.

” Eyyah “.

Daga nan kowa ya Fara pressing wayar sa can Hakeela ta fito kallon ta Hafsat tayi sannan tace

” ko akwai abunda Zan taya ki ne?”

“No yi zaman ki kawai”.

Tana gama fad’ar haka ta kalli Aisha tace,

” Ai abun alfahari ne ka shigo gidan surkunaye suna ji da kai”.

Tsarai Hafsat ta fahimci da ita take sai tace,

“Aisha Bari naje ina da aiki”.

” ko dai zaki yi ma ya Hydar girki ba”.

Shiru tayi bata ce komai ba ta fice Hakeela kuma haushin su duk taji..Hafsat ta tafi ne saboda kada wani yayi suspecting nata.
Asr nayi Aisha tace,

“Asr yayi fa muje muyi sallah”.

To Hakeela tace sannan suka fita..

sai can Asr ta koma tana shiga taga falon ba kowa don haka ta wuce kitchen sannan ta bud’e miyar ta juye salt son ranta tana cikin juyewa taji alamar steps na kafar mutum kuma ta tabbata Hakeela ce saboda kitchen ta nufo..da wuri ta rufe niyar sannan ta nufi k’ofar kan ta bud’e Hakeela ta bud’e da wuri ta makale Bayan k’ofa tana ganin Bayan Hakeela ta fice da wuri direct apartment nata ta wuce sannan ta zauna zaman sakamako..

STORY CONTINUES BELOW

Wayar ta ce yayi ringing tana dubawa taga Hydar ne don haka sai tayi receiving

” Assalamu Alaikum”.

“Wa’alaikisalam ya zaman gida madam?”

“Alhamdulillah”.

” Aisha ta fad’a mini abunda ya faru d’azun shiyasa na Kira don nayi confirming ko kina lafiya “.

” Laa ba komai is normal Ai”.

“Da gaske madam”.

” Ehh “.

Tana cewa Ehh kawai taji hayaniya na tashi daga cikin gidan sai ta kashe wayar sannan tayi murmushi ta nufi cikin gidan.
” ni zaki yi k’ok’arin kashewa?kenan d’azun ma ke Kika zuba borkono a abincin “.

” wallahi Daddy…”

Bata k’arasa ba ya d’auke ta da Mari har ta fad’i k’asa

“How dare you ina fad’a kina fad’a dama Ai nasan turo ki aka yi ki kashe ni ba don Allah yasa ban hadiye abincin nan ba da na tabbata mutuwa zanyi”..

” Dan Allah Alhaji Kayi hak’uri na tabbata kuskure ce”.

“Get out of my sight na tabbata d’azun ita Tasa borkono tunda gashi yanzu ta kasa adjusting yadda zata yi nata”.

Kasan sha’anin ka da mai kud’i bayi da yarda a rayuwar sa gani yake kamar kowa na son ganin Bayan sa..

Hydar da dama ya dawo gida but bai San cikin wani hali zai samu Hafsat d’in bane ya sa shi kiran ta jin she is normal sai ya fito daga motar ya nufi cikin gida inda yake jin hayaniya..

Daddy kam birkice musu yayi sai hak’uri ake basa amma kamar zai daka Hakeela don ba abunda yaki jini kamar yana magana Ana mayar masa martani ita kuma Hakeela baza ta iya shiru ba Hydar ne ya shigo ya rike sa sai hak’uri yake basa Ana cikin haka Hafsat tace,

“Daddy”.

Duk da borin da yake sai yayi shiru nan kowa ya juya yana jiran me zata ce..

” Daddy Dan Allah Kayi hak’uri ba laifin Hakeela bane saboda a gidan su basu girki Maamar ta ma a hotel take sayan abinci “.

” ji fa Dan Allah duk wannan aikin Zulai ne,Wai ‘Yar gidan mutunci ma a kasa samowa”.

Nan Hydar ya kai sa upstairs sannan kowa ya Fara wasewa Hafsat ko shu’umin murmushi tayi tana kallon Hakeela irin kallon you know I know sannan ta koma apartment nata Hakeela kuma bin ta da kallo tayi tana mamakin Rama sharrin da Hafsat ta mata Amma kuma Tasa a ranta yanzu aka Fara wasan..

Hafsat na shiga apartment nata sai ta Kara tattarewa tare da shara duk da ba wani Dotti sannan ta jera trow pillows daga nan ta sake labulayen window sannan ta fesa room freshner Bayan ta gama sai ta kunna t.v sannan ta wuce bedroom nata ta sake wasa ruwa,wardrobe nata ta bud’e sai ma ta rasa kayan da zata sa sai kawai ta cire Wata 3 quarter na mata da top nata mai hannun vest Tasa daga haka ta feshe jikin ta da tulare sai tayi parking kanta ko d’an kwali babu a kanta ta fito falon inda ta Kara gudun A.C sai ya gaurayu da kamshin room freshner sai falon yayi sanyi mai dad’i.. Zama tayi a kan kujera tana kallo sai taji anyi knocking k’ofar kuma ta San Hydar ne kad’ai zai shigo sai tace,

“Shigo k’ofar a bud’e”

Turawa yayi tana d’aga ido sai taga Sulaiman ne inda Allah ya so ta normally hijab da sallayan ta a falo yake don haka sai tayi saurin Jan hijab d’in Tasa sannan tace,

“Akan me zaka shigo Wa mutani gida ba tare da ka bayyana kan ka ba?”

“Bayan nayi knocking kince na shigo”.

Zata yi magana kenan sai ga Hydar ya shigo.

” Ahh Sulaiman kai ne a gidan namu yau?”

“Ehh wallahi”.

STORY CONTINUES BELOW

” Hafsat ya baki basa wajen zama ba?”

Yanzu fa shigowar sa”.

Zama suka yi tare da Hydar ita kun ta wuce kitchen ta kawo musu drinks Hydar d’in kuma ta ajiye masa fresh milk sannan ta jera abinci a dining nan ta zauna tana kallon Sulaiman d’in tace,

“Bismillah”.

” godiya nake Amarya “.

Saboda shi tunda yaga shape nata yake ji a ran shi tafiyar sa ba alkhairi bane kuma ya tabbata Hydar ba robot bane da zai ga Hafsat ya Bari kila ma yanzu tana da ciki..

” nayi serving naku ne?”

Ta tambaya tana kallon Hydar.

“No ba yanzu zanci abinci ba kiyi serving nasa kawai”.

Da wuri Sulaiman yace

” no nima naci abinci kan na fito”.

“Fine tunda baza Ku ci ba”.

Hydar kam cire rigar sa yayi ya bar vest yana mika mata rigar sai tayi bedroom Bayan ta ajiye masa sai ta dawo Kitchen nan taji sun Fara magana..

” Sulaiman me naci maka ace tunda ake nema na baka ta’ba Kira na ba”.

“Hydar ba zaka gane bane,na Kira ka layin ka baya shiga sannan abunda ya hanani zuwa Bayan ka dawo kuma Baba na shirin tura ni Dubai yake domin na daidaita da ‘Yar abokin sa nan ya bama Hydar labarin komai..

” to Ai gaskiyar sa ne Sulaiman tunda ka gagara fitar da mata kawai ka masa biyayya “.

Ai dole na tunda yana shirin tsine mini”.

” kasan dai ba zai so maka abunda ba alkhairi bane ba”.

“Wannan gaskiya ce”.

” so kaje kawai ba abunda zamu ce sai Allah tabbatar da alkhairi “.

” Ameen “.

Yace yana hararar Hydar Hafsat ko fitowa tayi daga kitchen d’in tana fad’in,

” sai kun dawo kenan”.

“Ni da Wa?”

Sulaiman ya tambaya

“Da amaryar ka mana”.

Ta ba shi amsa tana d’aga hijab d’in nan Hydar yaga irin shigar da tayi unluckily sai ta zauna kan hannun kujerar da Hydar d’in ke zaune a hankali ya kashe mata ido d’aya sai ta nuna masa Sulaiman da ido shi ko Sulaiman yana ganin duk abunda suke yi..k’ok’arin kai hannun sa cikin hijab d’in yayi ta buge hannun sa sannan ta juya tana kallon Sulaiman tace,

” k’arfe nawa zaka tashi goben?”

“Morning flight Zan bi”.

Ya fad’a cike da soyayyar ta Hydar ko gaba d’aya ita yake kallo jin idon sa a kanta sai ta masa hararar wasa shi kuma sai kai mata peck yayi a take Sulaiman ya mik’e cikin zabura..

” ya dai Man?”

“Zan tafi ne Hydar ko shiri ban gama ba”.

” Allah sarki yanzu ba Zan ganka ba for a year? “

Murmushi Sulaiman yayi sannan yace,

“Amarya na tafi”.

” Bari mu maka rakiya”.

Ta fad’a tana mik’ewa Sulaiman na gaba ita da Hydar suna baya ganin haka sai ya rike hannun ta.. Suna fita Sulaiman ya dau hanyar apartment na Khaleel don rud’ewa Hafsat ko na tsaye a k’ofa taji Hydar na cewa,

“Man zaka je Ku gaisa da amaryar Khaleel ne?”

“Amaryar Khaleel kuma?”

“Ehh naga apartment nasu ka nufa”.

STORY CONTINUES BELOW

” mtsww wallahi tension ne ya mini yawa”.

Ciki Hafsat ta koma Hydar ko da ya raka sa sanda yayi magrib ya dawo yana shiga gida ya wuce apartment na Ammie idon ta biyu tana kallo.matse mata kafa yayi sannan yace,

“Sannu da hutawa Ammie”.

Ido ta lumshe tana kallon sa ganin yau shi kad’ai yazo don cikin sati biyu da suka wucen nan kullum tare da Hafsat yake zuwa kuma su Dad’e suna hira,ya jima don har anyi i’sha sannan ya mata sai da safe ya fita..yana fita falon yaji Umma na cewa,

” Ai ba Wanda zai sa gishiri in ba Hafsat ba”.

Ko inda suke bai kalla ba don hankalin sa na kan matar sa ya wuce Umma tace,

“Shikenan Hafsat ta gama wargaza mini family Hydar baya ji kuma baya ganin kowa sai Hafsat Wallahi yadda nayi Wa Uwar ka haka zanyi na matar ka”.
Hakeela ko koda ta koma apartment nata sai mamakin Hafsat take yi nan Khaleel ya shigo domin bata hak’uri amma ta share sa.Hugging nata yayi yana fad’in,

” gaba Babie kiyi hak’uri mana”.

Ture sa tayi tana fad’in,

“Babie ka bar ni kana ganin cin mutuncin da Daddy ya mini”.

” hak’uri zaki yi”

Ya fad’a yana Kara rike ta ta ture sa

“Wai akan me in nazo kusa da ke zaki na kori na?”

Ganin ya dau da zafi sai ta Fara rarrashin sa yace,

“Har yaushe Zan cigaba da jiran ki ne yanzu satin mu hudu da Aure”.

” tension ne ya mini yawa Babie “.

Da haka ta lalla’ba shi ya tafi sha’anin ka da d’an giya I don’t care ne bai damu da duk abunda suke yi ba.

Yana fita tace,

” wallahi stress na gidan nan yayi yawa ban San wani tsautsayi bane ya kawo ni Wanda nazo don shi ma ko kallo na baya yi amma daga yau Zan mayar da hankali na ga yadda Zan karkata Hydar ya saurare ni”.
Yana tura k’ofar ya mayar ya rufe lokacin Hafsat ta idar da sallah tana nad’e sallaya ya k’araso ya rungume ta ta baya yana cewa,

“A gaban aboki na kike son naji kunya”.

” ko ni ka sani a kunya ba”.

Dike kunnen ta yayi da bakin sa nan taji tsikar jikin ta ya tashi tace,

“Kaje Kayi wanka zanyi serving naka”.

” muje”.

Yace yana Jan hannun ta sun shiga bedroom d’in kenan text ya shigo wayar sa kuma na soyayya ce mai zafi sai ya kalle ta da gefen ido sannan yayi deleting ya shiga wanka ita kuma ta koma falo..yana fitowa yasa plan trouser da T-shirt ya fito falon domin cin dinner sai wayar ta Fara ringing nan yayi receiving

“Ko baka mini reply ba bazan fasa kiran ka ba don duk duniya banda Wanda nake so irin ka”.

Jin haka sai ya juya da wuri ya koma bedroom Hafsat da ke serving kuma taga juyawan sa sai ta bi shi don ta tabbata akwai abunda yake boyewa.

” ke wallahi Kika sake kiran layin nan sai na nemo ki na wulakan ta ki”.

“Nace maka ina sonka”.

” kina so na?”

Ya maimaita karab a kunnen Hafsat…Ita dai kallon sa kawai tayi amma bata ce komai ba ta juya ta fita da wuri ya katse kirar zai bi Bayan ta wani Zuciya yace ba ajin sa bane don haka sai ya d’an jima kan ya fito,yana fitowa ya tarar tayi serving nashi sai ya zauna ci bata ce da shi komai ba sai ma d’aukar wayar ta da tayi ta nufi bedroom da ido ya bita..yana gamawa ya wuce nasa bedroom d’in yayi kwanciyar sa don shi gani yake kamar bata yarda da shi bane ya sata masa haka..a ‘bangaren ta kuma ta rasa me d’aya take ji kishi ne ko haushin sa haka ta kwana juye-juye a kan gadon..

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari kasancewar ita ce da girki a cikin gida sai ta wuce Bayan ta ajiye masa tea a dining yana tashiwa yayi wanka sannan yayi shirin fita sai ya nufi parlour domin breakfast.. Yana shiga ta cire idon ta Hakeela kuma sai bin su da ido take zama yayi ta kalle sa tace,

“Should I serve you”.

” bana so”.

Ya fad’a ko inda take bai kalla ba.. Dadi sosai Hakeela taji..haka ko ya mike bai ci komai ba zai fita sai taji duk ba dad’i gashi yau su uku ne kacal a wajen Khaleel yayi breakfast ya fita sauran ma duk sun gama sun kama gaban su yana fita ta d’auki wayar ta ta tura masa message kamar haka

“I will miss you for the whole day”.

Yana ganin message d’in kuma ya dawo falon sannan ya tsunkuya dai-dai kanta ya bata peck a forehead mik’ewa tayi tana kallon sa da mamaki sai kawai yayi hugging nata nan Hakeela ta yarda cup d’in hannun ta da wuri suka Ankara sai yayi breaking hug d’in yace ma Hafsat a kunne

” ki bata hak’uri kada tace don mijin ta baya kusa ne muka mata haka”.

Sannan ya juya ya bar wajen Hakeela ko ji take kamar ta mutu..
Bayan Hafsat ta gama girkin Rana kuma Hakeela ce zata yi na dare sai ta kwanta domin hutawa daga ita sai bump shot sai vest don ta San ba mai shigowa a falon kuma tayi bacci cikin bacci taji an tura k’ofar da wuri ta farka sai ganin Hydar tayi duba agogo tayi sai taga time na dawar sa bai yi ba da wuri ta d’auki hijab shiko fisgewa yayi yana fad’in,

“Iyehh Ashe haka kike zama abun ki”.

Ita dai idon ta a k’asa don kunya sai cewa tayi

” lafiya ka dawo yanzu “.

” ehh na kammla aiki nane kuma outing nake so muje”.

Taji dad’i sosai don ta gaji da zaman gidan don haka sai suka wuce bedroom ta cire masa kayan da zai sa kuma normally in zai fita outing su yake sawa..k’ok’arin cire mata kaya yayi lokacin da ta shiga wanka Amma ya rasa ita ustaziya ce ko akasin haka saboda ya Saba ganin ta da Hijab yau kuma ga yadda ya ganta..sensing yayi sai ya fahimci yawanci in mata zasu je outing gown suke sawa don haka sai ya cire mata tana fita ya shiga wanka har ta gama shiri bai fito ba sai can ya fito yasa nasa kayan sannan suka kama hanyar waje..

Hira suke k’asa-k’asa suna dariya sai ji suka yi Daddy ya Kira

“Aisha”.

Kallon juna suka yi don sun manta ma da shi kuma sun San ba zai bar su su fita tare ba….
Comments
Share

©Hafciey
[4/24, 13:59] Hafcie Musa: *°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 38📑*

Alhamdulillah a yau 21-4-2020 Zan ajiye rubutu bisa ga gabatowar Wata mai alfarma da kuma albarka..kuma ina mai Baku hak’uri saboda yanzu sau uku ina ajiye rubutun littafin nan  amma in sha Allah wannan ne na karshe Bayan sallah da sati d’aya zamu cigaba in sha Allah..
*__________*📖Sake kallon sa tayi amma sai ya batsar irin kada tace yana tsoron Daddy mana sai yace,

“Ki jira ni a cikin mota”.

STORY CONTINUES BELOW

Yana mika mata key kar’ba tayi shi kuma ya shige cikin gida. Yana shiga ya tarar da Daddy zaune a falo yana rike da magazine sai ya nemi wuri ya zauna..

” Daddy sannu da hutawa “.

” yauwa Hydar “.

Ya fad’a sannan ya cigaba da kallon magazine d’in da yake duk gidan ba Wanda ya fahimce sa irin Hydar sai ya Fara basa labarin yadda company ke developing da kuma wasu advice na yadda company’n zai Kara bunkasa ya basa..

Hafsat ko tana can cikin mota har ta gaji da jiran sa ta kuma sa a ranta ba zuwa zasu yi ba.

” mtsww”.

“Hydar tsaki kuma?”

“Sorry Daddy wallahi na manta Ashe Zan Kira Saif ya kai Hafsat hospital ne saboda Tun d’azun take cewa cikin ta na ciwo”.

” Ai gwara ya kaita kada ta mutu mana ace mu muka kashe ta”.

“Nima abunda na gani kenan yanzu Zan Kira sa”.

” why not ka kaita”.

“No Dad ba Zan iya tolerating nata ba”.

” I know baka ganin shi Saif d’in zai yi suspecting  wani Abu?I trust you ka kaita nasan bata gaban ka”.

“Shikenan tunda you insist”.

Sannan ya mik’e yana murmushi ya nufi mota ita kuma lokacin ta gama ‘bula don haushin sa yana bud’e motar ya shiga ita kuma sai ta cire kai..

” ya dai Madam?”

Ya tambaya yana sa seat belt .

“Kaje ka yi zaman ka ni kuma ka barni kamar kayan shanya”.

” kin San da ya na shawo kansa kowa bye the way tunda zamu je Ai shikenan “.

Murmushi tayi ya tada mota suka bar gidan basu tsaya ko ina ba sai Beach da yake ba wani surutu bane da su sai kallon wajen suke kowa na nasa tunanin daga nan suka wuce eatery a wajen suka ci abinci nan tayi ma Aisha take away sannan suka kama hanyar gida..

Yana parking suka shiga tare.. Umma, Aisha sai Hakeela ne a falon suna kallo..poster Umma tayi tana kallon su da mamaki nan Hafsat tace,

” sannun Ku da hutawa”.

Tsaki Umma taja sannan ta nufi upstairs Hafsat sai ta mika ma Aisha ledar tace,

“Gashi”.

Kar’ba Aisha tayi tana bud’ewa sai taga ice cream ne da kaza Hydar ko cewa yayi,

” tunda kin bata mu tafi ko?”

“Thanks Mrs Hydar”.

Aisha tace Hydar ko yayi gaba ta bi sa a baya ko inda Hakeela take bata kalla ba..

” Bismillah Hakeela “.

Da mugun harara Hakeela ta jefe ta wato ma da sunan ta zata Kira ta amma sai take cema Hafsat Mrs Hydar.

” muci wallahi Hafsat ta had’u duk fitar su sai ta kawo mini tsaraba Gashi mijin ta bayi da matsala “.

” Ayya sun ji dad’i”.

Hakeela tace.

“Kuma kin San me?”

Kai Hakeela ta girgiza

“Ki Lura duk Randa Hafsat ce a kitchen zaki ga ya Hydar na yawan shiga falon nan”.

Jin baza ta iya d’aukar abunda Aisha ke fad’i ba sai ta wuce apartment nata Aisha ko murmushi tayi don intentionally tayi saboda yadda taga Hakeela ke yi ma Hafsat sai taji Hakeela ta fita a ran ta…

STORY CONTINUES BELOW

Sulaiman ko kasa kwanciya hankalin sa yayi sai nemar mafita yake sai kawai ya d’auki motar sa domin zuwa booking flight amma sai aka ce ba zai samu flight yau ba sai gobe don haka ransa ya dad’a baciwa yana komawa gida ya kwanta sai mafuta yake nema nan ya sake murmushi sannan yace,

” absolutely “.
Hakeela ko tana shiga apartment nata ranta ya dad’a baci saboda ta San in tayi sake hawan jini zai kamata don haka sai ta yanke shawarar sake kiran Hydar ko don wargaza musu farin ciki saboda ta tabbata in Hafsat ta gani baza ta ji dad’i ba don haka tayi addu’ar Allah sa wayar a hannun Hafsat yake sannan ta Fara dialing.
‘Bangaren su Hafsat kuma suna shiga ta ajiye abubuwan da suka saya sannan ta zauna kan kujera haka ma Hydar d’in, kallon ta yake yana murmushi sai wayar sa ya Fara ringing da yake yana kan center table sai ya lek’a screen d’in wayar yana ganin number’n jiya ne sai yayi murmushi sannan ya kwanta kan cinyar Hafsat d’in..

Sarai ta Lura da shi sai Tasa hannu zata d’auki wayar yace,

” bar shi kawai ba important call bane”.

Ba tare da tace komai ba sai ta d’auki wayar da wuri ya fisge a hannun ta yana k’ok’arin kwanciya a cinyar ta ta mik’e da wuri yace,

“Yau kuma rowan cinya za’a mini?”

Bud’an bakin ta sai tace,

“Kaje Wanda ke kirar ka ta baka cinya ka kwanta”.

” Hafsat Rainin har ya kai haka?ba laifin ki bane laifin kin ji nauyi nane but mind you bazan yi tolerating raini daga gare ki ba”.

“Kada Allah yasa Kayi”.

Ta fad’a sannan ta fita a apartment d’in ta nufi wajen Baaba Ladi amma yanzu ma bata nan haka kawai take jin bakin ciki a ranta don bata ga dalilin da zai sa ita ya biya duk Wata bukatar sa da ita sannan yaje yana Neman mata a waje Ai wannan ma Rainin wayo ne..

Hanyar gate ta d’auka bata ma San inda take zuwa ba,gate man ne ya bud’e mata k’ofa ta fita sai bai rufe ba ita ko da yake gidan a kan titi yake sai ta tsaya tana kallon ababen hawa nan mota yayi parking a gefen ta kuma ta tabbata tambayar ta za’a yi amma sai aka fisge ta cikin motar sannan aka figi motar da gudu da wuri gate man ya lek’a sai ya d’auki number motar sannan ya nufi cikin gida da gudu Umma ce kad’ai a falo durkusawa yayi sannan yace,

” Hajiya yanzu aka yi kidnapping na matar Hydar “.

Kallon sa tayi kamar ta razana amma a ranta murmushi take tace,

” da gaske?”

“Ehh wallahi har na d’auki number’n motar”.

” to ka iya bakin ka kada naji ka fad’a ma kowa ko da kuwa Hydar ne “.

” amma.. “

“Tafi ka bani wuri”.

Mik’ewa yayi da wuri ya fita Aisha ko taji duk abunda suka ce don haka sai Tasa a ranta zata fad’a ma Hydar Amma sai Umma ta bar falon aiko Umma barin falon tayi domin kiran Hajiya Balaraba ta sanar mata tana tashiwa Aisha ta fice da gudu zuciyar ta na bugawa ta nufi apartment na Hydar d’in ko knocking bata yi ba ta shiga shi kuma vest ne kad’ai a jikin sa tana shiga yace,

” wani irin rashin tarbiya ne wannan ?”
Dama cike yake da haushin Hafsat da bata yarda da shi ba..

“Ya Hydar anyi kidnapping Hafsat”.

Da wuri ya mik’e yace
” what?”

“Ehh yanzu naji gate man yana fad’a ma Umma kuma tace kada ya fad’a ma kowa”.

Rigar sa ya d’auka a hannu sannan ya d’auki key’n motar ya fita waje direct cikin gidan ya shiga, Umma da ta Kira number’n Hajiya Balaraba baya shiga sai ta dawo falon nan Hydar ya shigo a rikice..

STORY CONTINUES BELOW

” fad’a mini number’n motar “.

” me na tada hankalin ka Bayan yawon karuwanci ta tafi”.

Idon sa ne yayi ja sannan yace,

“Kada ki kuskura ki maimaita wannan mumunar kamla a kanta”.

Daddy na jin haka ya fito sai cewa yayi meke faruwa

” Daddy Hafsat aka yi kidnapping kuma taki fad’a mini number motar Bayan ta sani”.

“Me na tada hankalin ka yarinyar nan kila saurayi ta bi”.

Yana jin haka ya fice da Riga a hannu ya shiga mota dai-dai gate yace,

” me number’n motar ?”

Ya tambayi gate man ba ko wasa a fuskar sa nan ya sanar masa..

Da gudu ya bar gidan direct  police station ya nufa nan ya bada number motar daga haka aka yi tracing sai dai kuma basu fahimci Wanda ya saya motar ba amma kuma sunga direction da motar yabi sai suka d’auki mota da niyar bin direction na motar har sun fita sai police d’in yace ma Hydar

“Alhaji sa rigar mana”.

Sa rigar yayi suka shiga motar sa da police d’in a hankali suka Fara bin direction na motar…
Hafsat ko ta zata Hydar ne don haka ya mata lokacin auren Khaleel sai tace,

” bana son irin wasan nan fa Hydar “.

‘Daga fuskar ta da tayi sai taga yasa face mask kuma tsam structure’n shi ba na Hydar bane nan ta tsorata kan ta sake magana Sulaiman ya d’aure bakin ta da handkerchief suka cigaba da tafiya.da yake ya Sara yadda abun zai kasance da dabara sai ya samu lungu ya ajiye motar sannan ya Saka ta cikin wani motar sannan suka d’au hanya..

Su Hydar ko bin direction na motar suke har suka iso wajen Amma sai suka ga 406 ne motar Amma kuma empty,hakan ba k’aramin tada hankalin Hydar yayi ba saboda ya rasa Wa zai yi wannan aikin koma wanene ba zai bar sa ba kuma ya tabbata abokan gaban su ne..

Har sun fita a layin sai police d’in yace su koma baya nan suka koma sannan suka yi parking wajen mai shayi Hydar ya sauke glass sannan police d’in yace,

” sannu dai”.

Ganin uniform na police sai yace,

“Ranka shi dad’e wani irin taimako Zan maka”.

” Dan Allah cikin abunda bai fi minti talatin ba akwai motar da ta shiga layin nan?”

“Ehh tabbas naga Wata 406 ta wuce”.

” Bayan wucewar ta da kamar minti biyar zuwa goma ba motar  da ta shiga sannan ta sake fita?”

Shiru yayi kamar yana tunani yace,

“Ehh Wata starlet  ja da tinted glass ta shigo sannan ta sake fita”.

Da wuri yace,

” wace hanya ta bi?”

“Naga dai ta mik’e straight”.

” ohk Mun gode”.

Hydar tada motar yayi sannan suka nufi straight su kan tsaya a wurare suyi tambaya sai dai Babban abunda yafi damun su shine basu San adadin starlet da suka wuce a titin ba..can dai suka tsaya wajen wani mai kilishi  har sun cire rai sai police d’in yace,

“Dan Allah ba starlet da ta wuce ta nan?”

“Gaskiya ban sani ba amma akwai Wata motar da tayi parking a nan waje na sai wani ya fito ya haye titi ya sayo drinks sannan ya dawo nan waje na?”

“Ya kamanninsa yake?”

“Gaskiya ban Lura da shi ba,Amma sanda ya tsallaka naji Ana buga motar ko da ya dawo sai ya bani dubu d’aya yace na basa na d’ari biyar sai nace masa dabbobi ne a motar da wuri yace yara ne suke fad’a Bari yaje ko canjin sa bai kar’ba ba wannan ya sani tunanin baya da gaskiya shiyasa da naga police na sanar muku”.

STORY CONTINUES BELOW

” zaka iya gane sa in ka gansa?”

“Ko kad’an bazan gane sa ba amma kuma karshen layin nan suka gangara”.

nan ya nuna musu layin gefen sa godiya suka masa kan su gangara..

Gangarawa suka yi sai dube-dube suke Amma ba alamar motar har suka Isa karshen layin saboda cikin kan kogi ne,sosai suke kallon wurin Amma kuma mutani d’aya d’aya ke wucewa sai wani suka gani  a bakin kogi yana wanki don haka sai suka yi parking sannan duk suka fito..

” sannu malam”.

Mik’ewa yayi da wuri don ya tsorata ganin d’an sanda da uniform..

“Kada ka tsorata tambayar ka zamu yi”.

Hydar kam dube-dube kawai yake yi nan police ya cigaba

” cikin abunda bai wuce minti talatin ba  akwai motar da ta wuce ta layin nan?”

“Ai motoci dayawa suka wuce ba ma d’aya ba”.

” starlet fa”.

“Yo Ai Alhaji Ahmadu ma yana da starlet haka ma driver’n gidan Mammadu Starlet yake tukawa”.

” kai Hydar ya girgiza don ya fahimci shirme yake musu kuma shi tsoron sa d’aya kada a cutar da Hafsat d’in..

“Malam wacce mota ce karshen wucewa a layin nan kuma ina ta shiga?”

“Gaskiya ni ban sani ba”.

Ganin har magrib yayi sai suka bincika layin Amma ba Wata alamar su sai police d’in yace,

” Hydar muje maybe zuwa gobe Zan tuno Wata dabara”.

“Expector  ba Zan iya ba”.

” to ya zamu yi tunda bamu gansu ba kila wani wajen suka je”.

Shiru Hydar yayi da kyar police d’in ya lalla’ba sa nan suka bama mutumin number’n sa kan cewa in yaga motar ya Kira su sannan suka tafi ya sauke police d’in a gida tunda yanzu kam sun tashi aiki shi kuma ya nufi wani plaza sabo da Baban sa ya bud’e kuma akwai abokin sa yana da bakery a wajen..abokin na ganin fuskar sa

“Lafiya kuwa abokina?”

“Wallahi ka Bari kawai d’azun aka yi kidnapping mata na”.

” shine kuma kake yawo kai kad’ai “.

” yanzu muka rabu da police “.

Daga nan bai sake cewa komai ba sai tunanin ta yake..

‘Bangaren Hafsat kuma suna shiga gidan ya jefa ta a d’aki sannan ya kawo mata kilishin da drinks sannan ya bud’e mata baki..

“Dan Allah malam me na maka kuma me kake nema Da ni?”

“Shhh”.

Yace Amma sai taci gaba

” malam in har matsalar ka da gidan Alhaji Munir ne kuma ka sate ni don su baka wani Abu  to aikin banza Kayi saboda banda mahimmacin a wajen su sun gwammaci ka kashe ni da su baka abunda kake so auren dole aka mana da d’an sa”.

“Karya kike yi, yadda kuke soyayyar nan zaki ce auren dole?”

Cikin desperate ya fad’a don haka ta kalle sa tana nazarin sa tace,

“Waye kai kuma ya aka yi ka San muna soyayya?”

Da yake yasa Abu a bakin sa sai bata gane muryar sa ba ganin ta’bargazar da yayi da wuri yace,

“Haka nake ji a gari”.

Bayan yace haka sai ta zama confused sannan yace,

” come again Kika ce auren dole aka miki garin yaya?”

“Wannan kuma ba ruwan ka”.+

Toy gun ya cire sannan yasa a forehead  nata cikin tsawa yace,

” zaki fad’a ne ko sai na harbe ki”.

Ganin gun sai tace

“Auren dole aka mana da shi nan ta bashi labarin auren su..

” me tsakanin ki da Hydar kuma?”

Shiru ta masa sai yace

“Anyway ni kud’i nake so Amma kila in Kika fad’a mini na tausayi miki ko ba kud’i na barki ki koma in kuma Kika mini karya har gidan ki zanzo na kashe ki”.

” ni ba komai tsakanina da shi sai kiyayya kawai a idon mutani ne muke nuna muma son juna”.

Sosai yaji tausayin ta Ashe dama dalilin auren su kenan kuma haka take wahala a gidan shine yake Kara munafurtar ta,to wannan ne chance nashi da zai d’auke ta su tafi kasar waje suje suyi rayuwa su cike da soyayya ..

Ita dai so take ya cire Marks na fuskar sa ko zata gane Waye ne saboda Ai ba zai ce suna soyayya ba in baya shiga gidan su kuma sanin Sulaiman baya kasar sai bata kawo sa ranta ba..

9pm

Hydar na zaune a wajen ya rasa me ke masa dad’i sai yaji wayar sa na ringing yana dubawa yaga new number sai yaki picking don dama baya picking new number saboda wacce take kiran sa this days Amma tunawa da yayi sun bama mutumin can number’n sa sai ya d’auka..

“Salamu alaikum ni ne mutumin da kuka bama number a bakin kogi”.

Cikin kad’uwa Hydar yace,.
” an Gan ta ne?”

“Malam bi a hankali mana,Bayan tafiyar Ku sai Wata Jan starlet ta fito har nayi tunanin kiran Ku sai nace Bari dai na dakata kila ba Wanda kuke nema bane so ina wajen har Bayan awa d’aya motar ta kuma dawa sai nabi Bayan ta nan naga gidan da suka shiga kuma Tun da mai gidan ya kaura ba’a sake amfani da gidan ba sai yau”.

Yana gama fad’ar haka Hydar ya kashe wayar sannan ya nufi wajen ba tare da yace ma mutumin yana hanya ba,sai da ya iso sai ya Kira mutumin yace,

” gani a wurin kana ta ina?”

“Ai ni aiki nake a anguwan Amma ba’a wurin nake da zama ba yanzu ina gida ne”.

” Dan Allah malam ko nawa kake so Zan baka kazo ka nuna mini gidan”.

“A kan me Zan bar iyalai na naje wajen ka kuma Ai ban San wani irin mutum bane kai”.

Duk rarrashin duniya Hydar yayi Amma yaki yarda don haka sai ya Kira police d’in,shima rokon sa yayi amma yace ba zai bar gidan sa ba..

Junction na mai kilishi Hydar ya zauna ko zai ga gilmawan motar amma shiru har 2pm don haka sai ya hakura ya nufi hotel a wajen ya kwana duk da bai iya bacci ba..
Washe gari ko sallar asuba bai yi ba ya nufi wajen a wurin yayi sallah sannan ya Kira mutumin..

” malam Anya ko sallah Kayi?”

“Nayi Kayi hak’uri kazo yanzu gani a wajen”.

” ohk yanzu Zan nufi masallaci ina fitowa zanzo “.

Yana kashe wayar ya Kira police shima yace yana hanya tare da sauran ‘yan gidan sa..

Can yaga mutumin bai zo ba sai ya sake Kira yace,

” ka fad’a mini address naka zanzo na d’auke ka”.

“Ka Bari na kusa Isa”.

Isar Mutumin yayi dai-dai da Isar polisawa..

Sai suka kama hanya mutumin na nuna musu hanya har suka Isa gidan.. Tsayawa Hydar yayi yana kallon gidan..gidan Baban Sulaiman ne tsohon guest house nashi Amma da yake in five years back kowa na harkar gaban sa sai yasa Hydar bai San tsohon guest house d’in Baban Sulaiman ba sai sabo..

STORY CONTINUES BELOW

Polisawa kuma surrounding gidan sannan suka sa last speaker suka Fara cewa,

“The house is surrounded don haka kowa should surrender”.

Shiru ba’a yi magana ba don haka sai aka ce polisawa uku su shiga ta gini nan suka dira gidan tare da cire sakatar sannan su Hydar suka shiga.. K’ofar falon a kulle yake Hafsat da ke ciki kuma jin motsin mutani sai ta Fara buga k’ofar tana,

” someone should help”.

“Inspector muryar mata na ne”.

” calm down zamu yi rescuing nata”

Nan aka ‘balla k’ofar sannan aka cire mata sarkar da ya d’aure mata kafa Hydar na bud’e mata hannayen sa da gudu ta shige jikin sa “.

” ina Wanda ya kawo ki nan?”

“Tun jiya ya fita bai dawo ba kuma mutum d’aya ne”.

‘Bangaren Sulaiman kuma jiya Bayan ta gama basa labari sai ya yanke shawarar zuwa ya mata Visa don haka sai ya barta ita d’aya, Bayan yaje airport sai aka tambaye sa passport nata don haka sai ya nufi gidan su ya kwana kada iyayen sa su zarge sa gobe the first thing da zai yi shine yaje ya d’auke ta passport ko a waya ne sai ya mata Visa daga haka su bar Nigeria..

Da safe ya shirya  domin zuwa mata passport yana Isa wajen sai yaga police sunyi surrounding gidan Gashi da Jan starlet yazo don haka sai yayi reverse ya fita da gudu hakan ya janyo hankalin mutani ganin Jan starlet kuma mutumin ya basu labarin cewa kidnapping aka yi da motar sai suka janyo hankalin polisawa ta hanyar fad’a musu nan aka bi Sulaiman shi kuma yana Isa junction sai ya fita daga motar ba tare da barin wani evidence ba ya shiga adai-dai ta sai inda yayi parking asalin motar sa nan ya shiga sai gida gaba d’aya ya gama tsorata. Yana Isa gida a tsatsaye ya sallami Hajiya Ana cewa ya tsaya amma ina ya d’auki kayan sa ya nufi airport dama saura hour d’aya jirgin sa ya tashi ya nufi wajen Hafsat yana Isa airport ko saura 15mins flight nasu ya tashi nan aka Fara kiran passengers ya shiga ba don ransa yaso ya tafi ya bar Hydar da Hafsat ba sai don ya tsorata nan jirgin sa ya tashi sai Dubai..

Tana manne a jikin sa taki samin sa a haka suka nufi mota nan Hydar yasa a binciko masa mai gidan… Account number’n mutumin ya kar’ba a wajen ya masa transfer’n kud’i mai yawa tare da masa godiya..

A hanya ya dube  ta yana fad’in,

“Hope ba abunda ya miki if so kar ki ji tsoron fad’a mini I trust you kuma Zan iya zama da ke a ko wani hali”.

” I promise ba abunda ya mini kawai abunda na fahimta mutumin da ke da hannu a lamarin nan baya son alaka ta da kai saboda he forced me to tell him abunda ke tsakanin mu”.

“And…”

Ya fad’a yana kallon ta

“Karya na masa I say ba komai sai kiyayya wannan dalilin yasa shi Bari na”.

” Amma Wa kike tunanin zai yi mana haka?”

“Umma I guess”.

” yah you might be right “.

Suna Isa gida gate man ya bud’e gate suka shiga sannan Hydar yayi parking tare da zagayawa ‘bangaren ta ya bud’e mata nan yasa hannun sa cikin nata suka nufi falon zasu shiga sai tace,

” No Hydar ina tsoro “.

” tsoron me?”

Da ido ta nuna masa hannun sa da ke cikin nata sai ya sake ta suka shiga a tare..

“Umma da Daddy da kowa ma na falon don hankalin su ya tashi na rashin ganin Hydar through out jiya da gudu Asma’u da Fareeda suka nufe sa nan suka yi hugging nasa Aisha ko Hafsat tayi hugging hakeela kam sai bin su da ido take yi..

STORY CONTINUES BELOW

” ya Hydar kana Lafiya? “

Kan ya bada amsa Asma’u ta d’aura da

“Allah sa ba abunda aka maka”.

” Wai me ke damun Ku ne,wacce ya kamata Ku tambayi lafiyar ta Baku tambaya ba sai ni”.

Kasa daurewa suka yi sai suka juya suna hararar Hafsat d’in suka bar wajen..

Daddy ko mik’ewa yayi ya karaso har gaban Hydar d’in yayi hugging nasa sannan yace,

“Wallahi I was scared to death na zata kai ma an d’auke ka ne”.

” ko  kad’an Dad naje nemar ta ne”.

“Na tabbata abokan kasuwancin mu ne suka d’auke ta ba tare da sanin sun d’auki wrong person ba don wallahi ko kashe ta zasu yi naira biyar na ba zai yi ciwon kai ba”.

” Dad wacce Tasa aka d’auke ta a gidan nan take kuma ba kowa bace illa Umma “.

Zaro ido Umma tayi tana fad’in,

” innalillah Hydar ni kuma?”

“Ehh ke na tabbata ba mai yin haka sai ke”.

” Alhaji wallahi ba ni bane,kila… “.

” shot up Zulai ni kaina na San zaki aikata hakan tunda Hydar kansa kin ta’ba k’ok’arin kashe sa”.

“Wallahi Alhaji bani da hannu”.

” wallahi Zan sa a mini bincike in har na gano kina da hannu a lamarin nan ni da ke har abada”.
“Wancan a baya ne kuma Ai na tuba in har ka samu hannu na cikin kidnapping Hafsat ko court ka kai ni sannan kuma ka mini saki uku ba biyu ba saboda na tabbata Hafsat had’a baki tayi da wasu suka yi kidnapping nata sannan tace ma Hydar nine don ka Kara tsana ta”.

Lallai maganar ta taso yin tasiri a zuciyar Daddy amma kuma baya son ta San haka sai yace,

” wallahi Hydar na fahimci take-taken ka,duk Randa kace zaka watsa mini kasa a ido sai na baka mamaki kuma one more thing wallahi tallahi duk Randa Kayi accepting Hafsat a matsayin mata sai nayi disowning naka cikin ‘ya’ya na sannan na tozarta ka yadda ko kare ba zai kalle ka ba so don’t try me”.

Yana gama fad’ar haka ya wuce upstairs Umma ma takaici ne ya kamata ta rufa masa baya.tana shiga d’aki tace lallai lokaci yayi da Zan raba tsakanin Hydar da Hafsat da kuma Alhaji don tabbas Hydar son yarinyar nan yake in harxban raba su ba ita zata raba ni da miji na..d’aukar hijab tayi sannan ta fita daga gidan..

Hydar ko sa hannun sa yayi cikin na Hafsat yaja ta suka nufi apartment nasu don ya fahimci kalaman Daddy ya girgiza ta sosai..suna shiga yace,

“Hafsat don’t take his words so serious”.

” Hydar ina tsoro in har zai iya maka haka kai da kake d’an sa iyaye na fa?bazan  iya sake jefa su cikin matsala ba”.

“Calm down magana kawai yake yi but ba abunda zai yi,iyayen ki kuma muna tare da su”.

Ita dai jin sa kawai take Amma ba don ta yarda ba haka yaja ta jikin sa yana ta rarrashin ta suna cikin haka wayar sa tayi Kara yaga new number ne sai yasa a hands free.

” Hydar muna Kira ne daga hospital saboda gawan da ake tunanin naka ne har yau ‘yan uwan sa basu bayyana ba”.

Cikin mutuwar jiki yace
“Zan sa ayi tracing a nemo ‘yan uwan sa”.

Haka ko yayi har aka samo ‘yan uwan mamacin nan plaza da ya shiga ma suka Kira sa kan cewa an biya motar sa yazo ya d’auka ya amsa da to..

Umma ko tana fita bata tsaya ko ina ba sai gidan malami nan ya bata abunda zata yi amfani da shi sannan ta dawo gida nan Hakeela ta shigo falon tana fad’in,

STORY CONTINUES BELOW

” Umma sannu da dawa”.

“Yauwa me kike so?”

“Umma dama so nake na San dalilin auren Hafsat da Hydar”.

” in lokaci yayi zaki sani”.

Sannan Umma tayi wucewar ta Hakeela kam ta kasa fahimtar me ke tafiya a gidan..

A ranar haka Hafsat ta kwana bata yi bacci ba Hydar sai kwantar mata da hankali yake duk da cewa shima yana cikin damuwa saboda daga yanayin  Umma ya fahimci bata da hannu a ciki to who is behind all of this? amma ta ki sakin ranta sai ma cewa da tayi,

” Hydar da ni da kai Mun San ba wani abunda ya Hana mu zama miji da mata a zahiri sannan zaka ce na kwantar da hankali na”.

“Ki yarda da ni Dad na ne I know how to handle him”.

Ita fa tsam hankalin ta ya kasa kwanciya..
Washe gari Tun safe police ya Kira Hydar ya sanar masa gidan an sayar ma wani ne sannan kuma ba mazaunin Nigeria bane asali ma da master key aka yi amfani wajen shigan gidan hakan yana nufin kidnapper d’in ya San ba kowa a gidan..

Godiya Hydar ya masa sannan suka yi sallama duk yana jin ba dad’i don Hafsat ta zama kamar Mara lafiya..

A ranar kuma ita ce da girkin dare Hydar ko office bai je ba, Asr nayi tayi wanka sannan tace da shi

” zanje girki”.

“Kin tabbata zaki iya?”

Murmushin k’arfin hali tayi sannan tace

“Lafiya ta kalau fa”.

” ohk take care sai na shigo”.

Fita tayi ta nufi cikin gida Amma ba kowa a falo sai A.C da t.v da ke aiki direct kitchen ta shiga sai ta Fara aiki nan Baaba Ladi ta shigo ta mata jaje sannan ta taya ta aiki har take ce mata ance miyar Daddy daban ne..

D’aura masa nasa miyar tayi Baaba ko ta nufi apartment nata saboda sun gama sauran miyan Daddy.. ta fito da niyar zama a falon kafun yayi sai taga Leda a dining haka kawai ta tsinci kanta da bud’ewa sai taga laya ne da paper cikin paper kuma rubutn alkur’ani ne sai wani wajen an rubuta sunan Alhaji Munir ga gashin mutum kuma a gefe nan jikin ta yahau rawa da wuri Umma ta fisge ta nufi upstairs ita kuma don zafi sai ta nufi apartment nata domin sake wasa ruwa wani zuciyar nace ta fad’a ma Hydar wani zuciyar kuma na hanata haka ta hakura tayi wanka sannan ta nufi cikin gida tana shiga taga Umma na k’ok’arin sa gashin a miyar Daddy sai ta rike hannun ta ta Fara mata wa’azi Hakeela kuma ihu tayi nan kowa ya fito Harda Daddy Umma tace,

“Alhaji dubi abunda Hafsat ke k’ok’arin sawa cikin abincin ka Allah yasa na ganta”.

Yana gani ya d’ebe ta da Mari yana fad’in,

” dama malamai kike shiga don ganin baya na?”

“Wallahi sharri ce”.

Wani Marin ya sake bata nan kowa ya Fara zagin ta Aisha ko cewa tayi,

” Hafsat Allah shirye ki in ke mai shiryuwa ce”.

Ran Daddy a ‘bace yasa aka Kira masa Hydar yana zuwa Daddy ya nuna masa ita kuma Hafsat ta San Hydar kam ba zai mata mummunan fahimta ba sai ji tayi ya d’ebe ta da Mari yace,

“Shashasha kawai matsiyaciya a zaton ki zaki cutar da uba na na barki?”

Rike wajen tayi tana kallon sa cike da mamaki nan Fareeda ta jata har waje ta jefa ta Hydar ko sai hak’uri yake bama Daddy yana jin tsanar Hafsat har cikin ransa Umma ko murmushi tayi don Aikin malamin ta yayi kyau..fita Hydar d’in yayi falon kuma kowa tsanar Hafsat d’in yayi yana shiga apartment nasu tana kuka tace,

“Hydar na San don idon Daddy ne ka mini haka Amma nasan ka yarda da ni Ai bazan aikata haka ba”.

Tureta yayi yana fad’in,

” na tsane ki Hafsat kuma Wallahi na Kara ganin fuskar ki Allah ne kad’ai ya San abunda Zan miki sannan kuma the night we spend together kiyi deleting nashi a memory’n ki don ni na manta da shi ki d’auka kamar bai faru ba”.

Yana gama fad’ar haka ya wuce d’akin sa tana jin yadda ya buga k’ofar a wajen ta durkushe tana kuka mai cin rai Wanda ji take kamar zata iya mutuwa..sosai tayi kuka sannan ta mik’e ta nufi d’akin ta ta kwanta kan gado tana kallon ceiling tace,

“Allah ka San nan ba gidan zama na bane ka kawo karshen wannan auren don nima na manta da duk wani abunda ya shiga tsakanina da Hydar na tsallake wancan Daren daga cikin Daren rayuwa ta.

Sosai tayi kuka tana jin fitar Hydar kuma ta San masallaci ya tafi ita ko tana kawance har i’sha yayi da kyar ta mik’e ta had’a da magrib tana mai kai kukan ta gaban Allah..

**

Yau kwana biyu da faruwar abun kuma ‘yan gidan na rayuwar su normal Umma ko Daddy ya yafe mata haka ma Hydar ya manta da Wata Hafsat don ba mai ambata ko sunan ta..

‘Bangaren Hafsat ko gaba d’aya bata gane ma jikin ta ba cikin kwana biyun Gashi ko abinci bata ci sai dai ta sha ruwa zazzabi sai rufe ta yake yi..can tana tunanin halin ‘yan gidan sai idonta ya fad’a kan always take gaban ta ya fad’i da wuri ta duba date a wayar ta sai gani tayi date na period nata ya wuce da sati biyu last month totally bata yi period ba sannan wannan month har yayi 2 weeks.

” na shiga uku ni Hafsat ciki ne da ni”.

Kuka ta Fara tana fad’in,

“Allah wani zunubi na aikata da kake jarabta na haka?Hydar ba zai so cikin nan ba saboda ba  muyi maganar haihuwa da shi ba,sannan Daddy kuma ya gargad’i Hydar kada ya kusance ni shi ma ba zai ta’ba so ba,bugu da Kari Umma kam sai dai tace a zubar ‘yan gidan mu ni kaina sai sun tsane ni ba abun ciki na kad’ai ba ga su Aisha duk ba mai son cikin..

Kuka sosai take yi sai yanzu ta fahimci cewa ta cuci kanta..
Naso na k’arasa har karshe b4 Ramadan Amma in nayi summarizing book d’in ba zai tafi yadda nake so ba don haka mu had’u Bayan sallah.
Taku har kullum*°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 39📑*

Barkan mu da dawa daga hutu kuma ina yi ma kowa Barka da sallah🥰❤❤da fad’ar anyi sallah lafiya..+

*__________*📖bayan taci kuka ta gaji sai ta shige tiolet ta wanke fuskar ta sannan ta wuce apartment na Baaba Ladi cikin sa’a kuma ta same ta..

“Hafsat sai yaushe zaki bar wannan kukan,nifa nasan sharri aka miki”.

Tana jin haka ta fad’a jikin Baaba Ladi tana mai Kara saurin kukan ta.

” lafiya kuwa Hafsat wannan kukan fa?”

‘Bare ta Baaba tayi daga jikin ta tana kallon fuskar ta tace,

“Fada mini me Hydar ya miki?”

“Baaba ciki nake da shi”.

” ciki a gidan nan?lallai Hafsat baki nemi zaman lafiya ba sannan kin tabbatar ne?”

Kai ta girgiza..

“Kin San baki tabbatar ba Kika ce kina da ciki jira ni a nan zanje chemist na bakin hanya na sayo miki abun gwaji”.

” to”.

Tace gami da kwanciya a kan gadon Baaba ko ta d’auki hijab nata ta fice..

Kan ta dawo ma har Hafsat ta Fara bacci nan ta tada ta sannan ta mika mata gami da nuna mata yadda za’a yi amfani da shi sannan ta shige tiolet..

Addu’a ta ringa yi Allah sa bata da komai, ko da ta d’aga zata ga sakamakon zuciyar ta bugawa ya ringa yi nan take tayi alwala ta fito inda ta gabatar da nafila raka’a biyu kan Allah sa babu cikin sannan ta mika hannu har rawa yake yi ta d’auka domin dubawa..

Tana ganin ya nuna positive ta kankame a hannun ta idanun ta na fitar da hawaye masu d’umi da gudu ta bar d’akin bata jira shigowar Baaba ba,Hakeela ce ta ganta da kuma yadda fuskar ta ya kumbura sai tayi dariya tana fad’in,

“Kadan ma Kika gani daga cikin wulakancin da Hydar zai miki”.

Tana shiga apartment nasu ta wuce bedroom tana kuka da iya k’arfin ta in har bawa Hydar kanta is a mistake to been pregnant is the biggest mistake of her life..

” lallai dole naje gidan mu don na San yadda zanyi da cikin nan Tun kan wani ya Ankara da shi”.

Kuka ta sake cigaba da shi sai ji tayi an bud’e k’ofar da k’arfi tana d’aga ido taga Hydar ne da alama bacci yake ta tashe sa..

‘Daga mata kai yayi yana fad’in,

“Kukan munafurcin nan fa?wato sai ina gida zaki addabe ni da kukan maita ko?to wallahi ki had’iye kukan nan yanzu”.

Ita dai da ido take bin sa ganin lokaci guda ya canza kamar ba shi ba a hankali ta shafa saman cikin ta a zuciyar ta tace,

” bazan ta’ba barin abunda ke ciki na ya San Kaine mahaifin sa ba,kuma d’a na ba zai tashi a gidan nan ba”.

“Kallon fa?”

Juyawa tayi ta basa baya nan yaga PT test a hannun ta amma kuma bai gani mai kyau ba don haka ya nufo ta, jikin ta ne ya bata yana zuwa da wuri ta juya sai ganin sa tayi har ya iso..

STORY CONTINUES BELOW

“Me a Bayan ki?”

Da wuri ta girgiza masa kai..

“Bani nan”.

Nan ma kai ta girgiza masa..

Hannun ta ya fizgo yana k’ok’arin kwacewa tace,

” Hydar don’t “.

” why?Ai ni yanzu ban yarda da ke ba,kila cutar da ni zaki yi”.

“Pls Hydar kabari”.

” to nuna mini”.

Ganin bata da niyar bayarwa sai ya matse hannun ta, zafi dai iya zafi tana ji Amma kuma Tasa a ranta ko me zai mata baza ta ta’ba bayarwa ba..

Wayar sa ce tayi ringing nan ya sake ta yana sa hannu a aljihu ita kuma da wuri ta jefa kasan gado,juyawa yayi ya kalle ta irin kallon Zan dawo sannan ya fice da wuri ta bi Bayan sa tayi ma k’ofar key sannan tayi ajiyar Zuciya game da jingunuwa da k’ofar
“Ur Dad is heartless”.

Ta fad’a tana kallon cikin ta..tsunkuyawa tayi inda ta Ciro PT test d’in daga kasan gado sannan ta bud’e wani tsohon book nata ta jefa a ciki sannan Tasa a drower ta rufe..

Hydar ko yana shiga apartment nasa shiri yayi sannan ya fesa tulare ya fito a falo ya same ta har zai fita sai ta rike rigar sa tace,

” Hydar Dan Allah zanje gidan mu”.

Cikin kasaita ya juyo yana kallon ta ran sa a had’e yace,

“Kice zaki koma wajen malamin ki ya baki wani magani don wancan yayi failing”.

Da wuri ta rintse idanun ta jin bakaken maganganun da yake jifan ta da shi..

” pls”.

“Ba inda zaki je don na tabbata wannan Karon ni zaki yi ma maganin”.

” Hydar gidan mu fa zanje “.

” I don’t care”.

Yace sannan ya Fara tafiya da wuri ta sha gaban sa tace,

“Dan Allah ba don ni ba Abu Zan kar’ba”.

Jin ta ambaci sunan Allah sai yayi shiru sai can yace,

” ki shirya Zan kai ki don ban yarda da ke ba kuma minti biyar zaki yi ko da baki kar’bi abunda ya kai ki ba”.

Kai ta d’aga masa shi ko yayi ficewar sa ita ko wajen Baaba Ladi ta koma.

“Hafsat ke kuma daga gwadawa sai na neme ki na rasa me sakamakon?”

“Baaba akwai”.

” akwai fa Kika ce garin yaya Kika yi wannan gangancin?”

Shiru tayi Baaba ta cigaba

“Gidan nan ba mai son abunda ke cikin ki, ba Wai kuma jikoki sun ishe su bane a’ah na ki ne baza a so ba har Hydar d’in don tsoron mahaifin sa”.

” Baaba to ya zanyi da cikin?”

“Gaskiya ban sani ba don bazan ce ki zubar ba saboda babu kyau Amma kuma ki sani koda Yaron ko yarinya zasu tashi a gidan nan to ba mai son su sai ke uwar su”.

Kinyi gaskiya Baaba in har Hydar ba zai so cikin nan ba banga mai so ba saboda shi kwata-kwata ya goge abunda ya shiga tsakanin mu”.

Ta fad’a a zuciyar ta amma a zahiri sai tace,

” dama nazo na sallame ki ne zanje gida na wuni”.

“Ayya a dawo lafiya kuma ki fad’a ma iyayen ki saboda su San yadda zaku yi”.

” in sha Allah”

Kawai tace sannan ta fice ta shirya cikin Riga da zani atampa sai Dan kwalli da tayi dauri da shi,kallon cikin ta a mirror tayi sai taga bai fito ko kad’an ba nan tayi hamdalah don yan gidan su baza su gane ba amma har cikin zuciyar ta tana jin son abunda ke cikin ta..

STORY CONTINUES BELOW

Zaman jiran Hydar ta Fara yi sai can Saif yayi sallama tace,

“Shigo”.

Shiga yayi Bayan sun gaisa sai yace mata Hydar yace ya kaita gida..bag nata ta d’auka sannan ta rufe k’ofar suka fita a tsakiyar gidan taga Aisha..

Murmushi tayi ma Aisha Amma sai taga ta canza fuska ko kallon ta bata yi ba..

” ba laifin ki bane Aisha ko nice a wajen ki haka zanyi Amma ina mai tabbatar miki akwai ranar kin dillanci”.

Tana gama fad’ar haka ta bi Bayan Saif Aisha ma da kallo ta bita har ta shige motar..

Suna Isa k’ofar gidan su yayi parking zata fita yace,

“Yace minti biyar ya baki so ina jiran ki”.

” hmm Saif kenan je ka kawai ba yanzu Zan koma ba sai anjima “.

” no baza mu yi haka da ke ba,yace na tabbatar na maida ki gida”.

“Saif kaje in yace ka maida ni kace masa ehh”.

Tana gama fad’ar haka ta fice ta shige gidan su Saif ko parking yayi a gefe ya na kallon gidan ko zata fita amma har Bayan hour d’aya bata fita ba sai ya mayar da motar..

Ita ko tana shiga gida ta tarar da Saudat a tsakiyar gida da gudu kamar yarinya ta d’ale jikin ta a zuciyar ta tace,

” na shiga uku zata kashe ma mutani yaro sai kuma ta tambayi kanta su Waye mutanin? Ai d’an ki ne ke kad’ai “.

” Aunty Hafsy ko waya babu”.

Murmushi tayi sannan tace,

“Surprise na mu Ku Ai ina Maama?”

“Yanzu ta zaga ki jira zata fito”.

Zama suka yi a kan tabarma Saudat sai kallon ta take kamar zata had’iye ta

” Saudat kallon fa?”

“Kin canza gaba d’aya”.

Zuciyar ta ne ya tsinke kar fa alamun mai ciki ya bayyana a tattare da ita

” Allah kin yi kyau”.

Ajiyar Zuciya tayi gami da murmushi suna cikin haka Maama ta fito

“Hafsat ke ce a gidan namu?”

“Ehh wallahi Maama”.

Nan Maama ta zauna suka gaisa a haka ya Abdool ya shigo tana ganin sa tace,

” yauwa ina da magana da kai”.

“Ku kam kullum maganar Ku bata karewa”.

” A’ah Maama na yau a gaban ki za’a yi”.

Da wuri ya Abdool yace,

“Kina hauka ne Hafsat”.

” Ehh zauna kawai”.

Dolen sa ya zauna sannan ya kalli Saudat yace,

“Bamu wuri maganar ba na yara bane”.

Da yake duk masu bin juna akwai raini sai Saudat tace,

” to Ai banga maraba tsakanina da Hafsat ba”.

Jefin ta yayi da wuri ta shige d’aki Hafsat ko gyaran murya tayi tace,
“Maama Dan Allah kiyi hak’uri da duk abunda Zan fad’a, wallahi ya Abdool da kanwar Hydar soyayya suke”.

Da wuri ya Abdool yace,

” soyayya fa Hafsat? “

“Ehh karya na maka Ai na San kana son ta”.

STORY CONTINUES BELOW

” innalillah”.

Maama ke maimaita Wa sannan tace,

“Abdool da hankalin ka kuwa?”

“Maama kada Kiga laifin sa nan Hafsat ta bata labarin komai har yanzu salati take sai ya Abdool d’in yace,
” na San nayi kuskure kuma ba yadda zanyi na gyara ki gafarce ni Maama amma wallahi ina son Aisha tsakanina da Allah “.

” Abdool ba Zan Hana ka son ta ba amma kuma Ai kasan Aure ba Abu bane mai yiwuwa a tsakanin Ku,shin ka tuna yadda mahaifin ka zai ji?”

“Maama nasan Abba da Baban ta baza su yarda ba shiyasa na yanke hukuncin nisantar ta amma kuma ban San ya Zan yi ba”.

” well tunda ka tuna haka ni Zan baka shawara kawai ka nuna mata kai mutumin banza ne shikenan na Santa da natsuwa zata tsane ka”.

“In har zata tsane ni a shirye nake da yin haka Hafsat”.

Maama kam da ido take bin su banda Abdool da kuruciya me ya kai sa soyayya da ‘Yar Alhaji Munir ta tabbata duk Randa Alhaji Munir ya sani sai ya kusa kashe sa.
Lawal ne ya shigo yana fad’in,

” aboki na muje ko”.

Da wuri Hafsat ta d’aga ido tana kallon sa a hankali ta saukar da kanta sannan tace,

“Maama Waye wannan?”

Don ta San maza basu shiga gidan su Kai tsaye

“Aboki na ne”.

Ya Abdool ya bata amsa shi Lawal ko cewa yayi

” Surkin ki ne”.

“Surki?”

“Hafsat rabu da shi auta na yasa a gaba”.

Lawal so yake ya nuna ma Saudat cewa yana son ta amma ta Hana sa fuska su Maama kuma sun d’auka zolaya ne..

Daga d’aki Saudat taja tsaki lawal ko gaisawa yayi da Hafsat tunda wannan ne Karon su na farko da suka had’u sannan suka fice nan Maama ta juyo tana kallon Hafsat tace,

” Hafsat ya gidan naki dai?”

Lallai lokaci yayi da zata fad’a ma Maama bata jin dad’in zaman gidan kawai jurewa take yi nan ta Fara bata labari tiriyan-tiriyan har zuwa yadda tayi tazo gida yau sai dai bata ce ma Maama wani Abu ya shiga tsakanin ta da Hydar har tayi ciki ba..ta karashe maganar tana hawaye..don Maama tayi comforting nata sai tace,

“Hak’uri zaki yi Hafsat haka kowa ke hak’uri Wata ran sai labari”.

Amma kasan zuciyar ta tana tausayin ‘Yar ta..

Nan ta ringa lallashin ta har ta Fara mantawa da damuwar ta sannan Maama tace Saudat tazo su zaga anguwa ko Hafsat zata ji sauki haka ko aka yi Bayan sun dawo sai ta nemi duk Wata damuwar ta ta rasa nan take cewa tana missing na Hamma Naseer da Sis Faty wato sun zama ‘yan katsina..

**

Hydar ko yanzu shigowar sa gida Umma na ganin yayi parking sai tace Hakeela ta kai masa abinci nan ta d’auka jikin ta har rawa yake yi..

Da sallama ta shiga Amma baya falon da alaman ya shiga wanka nan tayi ta jiran sa har ya gama ya fito sannan cikin kissa tace,

” ya Hydar ga abinci “.

Da kai ya amsa sannan ya je dining d’in ya zauna nan ta Fara serving nashi a hankali tana goga hannun ta da nashi da wuri yaja hannun sa a zuciyar sa yace,

” Wai ina Hafsat ce ta barni da yarinyar nan “.

A zahiri sai yayi gyaran murya sannan yace,

” Hafsat !”

STORY CONTINUES BELOW

“Ai Hafsat tunda ka fita ita ma ta fita har yanzu bata dawo ba”.

A fusace ya d’auki waya ya Kira Saif yana fad’in,

” ina ka bar Hafsat? “

“Sir na kawo ta har gida”.

” ka tabbata? “

“Ehh”.

Daga haka ya kashe wayar sannan ya Kira gate man yana fad’in,

” tunda Hafsat ta fita da Saif ta dawo gidan nan?”

“Gaskiya bata dawo ba”.

Katse wayar yayi sannan ya jefa wayar a aljihu wato bai Isa da ita ba kenan..

” ga abinci “.

” zubar da abincin yayi sanda Hakeela ta tsorata sannan ya wuce d’aki ya d’auko key’n motar sa ya fice ransa a matukar ‘bace.
“To me yasa yake d’aga hankalin sa a kan ta ne?”

Hafsat na tsaye a k’ofar gida suna sallama da Maama da Saudat sai ga motar Hydar da gudu kamar zai d’ebe yaran anguwa kura sai bin motar yake.. Tana ganin motar sa zuciyar ta ya hau bugawa a hankali ta furta Hydar time da yayi parking..

Juyawa tayi zuciyar ta na bugawa ta shiga motar nan ya sake figar motar Maama ko sai kuka ta nufi cikin gida don ta tabbata yau  Allah ne kad’ai zai iya kwatar Hafsat a hannun Hydar..

Yana parking ya fita tare da rufe k’ofar da k’arfi sannan ya juya ‘bangaren ta ya Fara janta har suka wuce parlour su Umma na ganin haka suka Fara murmushi..suna Isa apartment nasu ya jefa ta kan kujera da wuri ta Mike sannan ya d’aga hannun zai mare ta ta rike hannun sa tana fad’in,

“Wallahi in ka mare ni sai na Rama”.

Da mamaki ya kalle ta sannan ya wuce bedroom sai sai Gashi ya dawo da belt a hannun sa nan ko tsoro ya bayyana a fuskar ta don ta San dukan fa zai yi kila ma ya zubar mata da cikin da take tattali..kan ya iso wajen ta su Umma da Hakeela sun shigo nan suka Fara basa hak’uri cikin kissa amma kuma sai hakan yayi tasiri sai ya fasa dukan ta nan Umma tace,

” Hafsat me Kika masa da har zai buge ki?”

“Umma ya wuce wajen karuwanci ya kama ta”.

Jin wannan Kalmar ba k’aramin bata masa rai yayi ba nan yace,

” me ya kawo Ku apartment na tsakanina da ita ne don haka zaku iya tafiya “.

Ta’be baki suka yi suna jin haushin rashin dukan ta yayi a haka suka fice Hafsat ko d’aki ta wuce ta fad’a gado ta Fara kuka ita fa abun Hydar tsoro yake bata a kan me zai ce zai buge ta?me yasa Tun farkon zuwan ta gidan bai nuna mata wannan Kiyayyar ba sai yanzu da suke shirin Fara Tara yara..

Sosai take kuka don yanzu ba abunda ke mata dad’i a duniya..

Hydar ko yana d’akin sa sai yaji nyunwa ta Fara damunsa don haka sai ya wuce cikin gida da niyar yace ma Umma a sama mishi abunda zai ci yana dab da knocking k’ofar ta yaji dariya na fitowa daga d’akin,

” Ai k’awa ta Tun Randa na kar’bo maganin nan nayi ma Hafsat sharri daga ranar Hydar ya daina d’aga mata kafa yanzu haka ma dukar ta zai yi muka Hana”.

Ba k’aramin fadiwa gaban sa yayi ba  ya Fara komawa da baya-baya har ya buge Aisha da ke rike da glass of drink Amma bai ce komai ba ya juya ya fita..bin k’ofar da kallo Aisha tayi sannan tace yanzu kuma me Umma tayi nan ta karisa k’ofar aiko ita ma ji tayi Umma na fad’in,

“Gaskiya maganin na aiki don kowa a gidan ya tsane ta”.

Hakan ne ya tabbatar mata Umma is behind duk abunda ya faru..

STORY CONTINUES BELOW

Hydar na shiga apartment nasu ya zauna a kan kujera yana mai lumshe ido da kuma tsanar kan sa na rashin yarda da kuma fahimtar Hafsat.. Daga falon yana jin yadda take kuka nan yaji zuciyar sa na tafasa a hankali ya mik’e ya nufi d’akin yana tura k’ofar ta mik’e tana kallon sa idanun ta sunyi jaa

” ka biyo ni har d’aki domin ka duke ni ne?Bismillah Ai dama ni d’in baiwa ce a gidan Ku zo ka duke ni kawai”.

Sosai kansa yayi nauyi yana kallon ta cike da tausayi har ya Isa gaban ta tana jiran saukar Mari a fuskar ta sai taji ya janyo ta jikin sa a hankali ta Fara ture sa tana fad’in,

“Kada kace mini bukatar ka ce ta kawo ka in haka ne wallahi sai dai Wata Amma ba ni Hafsat ba”.

Kara hugging nata yayi yana petting Bayan ta a hankali yana fad’in,

” shhhh”.

Kwantar da kanta yayi a kirjin sa  haka ko tayi shiru har sai da ta Fara ajiyar Zuciya sannan yayi breaking hug d’in yace,

“I’m sorry Babie”.

Ido ta zaro jin yau kuma sunan da ya Kira ta kenan sai tace,

” ohhh yau kuma wani Abu aka fad’a maka a kaina?”

“Neva!daga yau duk abunda naji a kan ki bazan sake yarda ba”.

Daga haka ya kwanta a kan gadon yana kallon ceiling ita ko tana tsaye sai kallon sa da mamaki take nan yace,

” ban San me Umma zata samu ba in ta raba ni da ke,bana shiga harkar ta na rasa dalilin da yasa take shiga nawa harkar “.

Ita dai shiru ta masa sai ma zama a bakin gadon da tayi yana ganin haka ya janyo ta jikin sa cikin d’an d’aga murya tace,

” Hydar ka Bari ina azumi “.

” azumin me?”

“Kawo karshen wannan auren”.

” wannan kuma baki Isa ba”.

Jan jikin ta tayi don tana ji a jikin ta baza ta ta’ba yafe ma Hydar ba..

“To a samo mini abunda zanci”.

Mik’ewa tayi ba tare da ta sake kallon sa ba ta wuce kitchen don yanzu ta San irin zaman da zata yi da shi,sai dai suyi zaman ‘Yar aiki da ogan ta da shi tunda dama don su musguna mata suka Aure ta..indomie ta dafa masa sannan ta ajiye a kan dining yana jin ta gama ya fito nan ko ya k’arasa dining d’in zata tafi ya riko hannun ta gaba d’aya tularen sa wari yake mata..

” Hydar nace maka ina azumi fa”.

“Karya kike yi”.

” to naji ka sake ni”.

“Meyasa?”

Tana toshe hanci tace,

“Tularen ka na mini wari”.

” what?naga in na saya ke kike fesa rabi”.

Gudun kar ya d’ago ta sai tace,

“Na gaji da shine ka sake ni”.

Da mamaki yake kallon ta nan ta fusge hannun ta ta wuce tiolet da gudu yana jin tana kwarara amai..

Aisha ko tana shiga d’akin su Abdool ya Kira ta sosai taji dad’i har ta manta da abunda Umma tayi nan ta amsa tana fad’in,

” hello sweetheart “.

” Hy Baby na ya kike”.

Jin yace Baby’n shi ba k’aramin dad’i taji ba nan tace,

“Ina lafiya sai yau ka tuna da ni?”

“Na Isa na manta da princess na”.

” ba Gashi ka manta da ni ba”.

STORY CONTINUES BELOW

“Kaina bisa wuya tuba nake”.

” na yafe maka amma in ka kuma bazan yafe ba”.

“Na yarda ina labari?”

“Yana wajen Ku Ai”.

” Baby na Kira ne don nace miki anjima akwai party’n aboki na k’arfe 10 na dare”.

“Party kuma sannan k’arfe goma?”

“Ehh”.

” gaskiya bana zuwa party Amma kuma Zan je don kai sai dai gidan mu ba’a fita da dare”.

“Ya kina Abu kamar baki Waye bane”.

” Zan kokarta but I can’t promise “.

” yauwa beb sannan mini skirt zaki sa da top”.

“Have you gone crazy Abdool? Don ina son ka hakan baya na nufin Zan tsabawa addini na ba gaskiya ba Zan iya ba”.

Yana jin haka ya katse kirar..

Umma kam tsam bata yi tunanin wani yaji ta ba..

Hafsat na fitowa daga toilet ta zauna tana ajiyar Zuciya daga dining d’in yace,

” baki da lafiya ne?”

“Ni lafiya ta kalau”.

Aman fa”.

” tularen ka”.

Shiru yayi bai ce mata komai ba ya cigaba da cin abincin sa..
Hakeela ko cikin takaici ta koma d’akin ta gaba d’aya haushin Hafsat ya ishe ta kuma ta fahimci Wanda tazo gidan don shi ba samun sa za tayi ba tana cikin haka Khaleel ya shigo ya rungume tadon haushi sai ta mare sa aiko cikin bacin rai ya cire belt d’in jikin sa ya Fara dukan ta sai ihu take nan su Umma da Hydar suka nufi apartment din Hafsat zata shiga sai ta tuna Hydar yace bai yafe ba don haka sai tayi stepping back..

“Khaleel Wai me kuka sha ne yau?d’azun Hydar ya gama dukar matar sa Kaima ka Fara”.

” excuse me ni ban d’aki mata ta ba kuma banga dalilin da zai sa na dake ta ba don ina son ta”.

“So?”

“Ehh so”.

Hakeela da zafin ciwo amma bai Hana wannan Kalmar shiga kunnen ta ba..

” Allah na gode maka da Hydar ya fad’a a gaban kowa wallahi kamar a kunnen Daddy’n Ku”.

“Kina fad’a nima Zan tona miki asiri na abunda Kika yi ma Hafsat kuma kin San Daddy zai yarda sannan kuma Kija musu kunne kada Wanda ya fad’a”.

Yana gama fad’ar haka ya fice abun sa a k’ofar apartment d’in yaga Hafsat nan yaja hannun ta tana fad’in,

” Meya same ta?”

“Ya wuci mijin ta ya shawu ne ya kama jibgarta”.

” shine ka barta da shi”.

“To me Zan mishi sun fi kusa Ai”.

” Amma….”

“Ya ishe ni haka”.
Yana fita Umma tace wallahi ko da wasa wani ya sake ya sanarma Daddy’n Ku cewa Hydar yace yana son Hafsat zai gamu da fushi na,Ku bar sa yaje can shi ya sani..
Watsewa suka yi suka bar Hakeela da Khaleel inda ya kalle ta yace,

” in baki da hankali gobe Kice zaki mare ni wannan ma ba abunda na miki”.

Ita dai tsoro ya bata kuma yanzu ta tabbatar da d’an giya bashi da hankali..

Hydar ko magrib nayi ya wuce masallaci ya bar Hafsat a gida…
Haidar bai dawo gida sai around 8:00pm Yana dawa gida kuma ya wuce bedroom nasa…. Wanka yayi sannan ya kwanta, yana tunanin irin rayuwar gidansu, gefe daya kuma tausayin Hafsat ne a ransa Yana cikin tunanin neh kumaa yaji karar shigowar text message a wayarsa, yana dubawa yaga ma ashe mtn neh, nan kuma yaga ashe tym ya tafi har 10:00pm tayi… Mikewa yayi cikin hanzari ya wuce dakin
Hafsat
Yana shiga ya tarar tayi baccinta,  tsayuwa yayi a kanta kusan 5-6mins sannan ya raba ya kwanta a gefenta tare da janyo ta jikinsa.. A hankili ya kurawa fuskarta ido, yaga ta rame harta fuskartata, ga kuma hawaye sirara na gangara harta kunnenta,  take kuma tausayinta ya kara shiga zuciyarsa A hankali ya mika hannunsa ya kashe light na dakin yayi saura bed side lamp Sannan ya kai harshensaa a hankali yana leaking hawayen nata A hankali kuma ya fara yawo da hannunsa a sassan jikinta, d’ayan hannunsa kuma ya kai yana zagaye lips dinta dashi.. Ita kuwa Hafsat bata ma san yana yi bah, baccinta take sha, harda matsowa tayi cikin jikinsa bata sani ba cikin bacci Shi kuwa zame mata dankwali yayi sannan yakai bakin shi cikin nata, yana sucking tongue nata kamar wanda ya samu sweet A haka kuma ya fara shafa sama kirjinta Ganin duk budurin nan da yakeyi bata farka bah, sai ya zame mata rigaar a hankali, take surar jiknta suka bayyana, kasa dauke idanunsa yayi daga kallon hallitar kirjinta don gani yake sun Kara cika sannan daga bisani ya kai hannunsa yana shafasu a hankali…
Hafsat kuwa jin abin ya fara wuce mafarkii sai tayi mika amma bata bude idanunta ba A dai dai lokacin kuwa haidar ya kai bakinsa kan nipples nata.. Ganin da gaske ne abinda takeji sai ta fara bud’e idanunta a hankali…..
Ganin wanda ke kanta Cikin hanzari ta turesa ta ja baya ta ayka masa da wani irin kallo  Cikin in ina Haidar yace,

” h, Hab, aa Hafsat miye haka?  Nifah mijinka neh..”.

Wani irin kallo ta kuna watso masa a karo na biyu mai cike da tsana, tace

” ban gane kai miji nah bah… Da kasan kai mijinah ne kake wulakanta ni kaida ‘yan uwanka?  Kaga malam.. Nifah ba jakarka bace a gidan nan Kun auro ni neh da na zama baiwa,  toh kuma gashi ina yimuku duk abinda kuke so ae… Amma jikina kam daga yau Haidar ka daina morar tah har abada….”
Ganin tana bata masa lokaci a cikin wannan yanayin da yakeji, kuma yasan koda zai tsaya mata bayani ba saurarsa zatayi bah…. A hankali ya faro matsota, itama kuma tana matsawa har tazo bakin gadon Ta mike ke nan Shikuma Haidar cikin zafin nama yasa hannu ya jawota, harta dan saki kara sabida zafin janta da yayi Nan ta shiga k’ok’arin kwace kanta amma ina karfinsu ba daya bah… Dan a wannan Daren haka tanaji tana gani Haidar ya kusance ta da karfiii… Tun tana zaginshi,  har ta soma basa hakuri Tana kuka tana masa magiya amma inaaaaa.. Sanda har ya biya bukatarsa da ita sannan ya sarara mata😭😭😭..

Mik’ewa yayi ya shiga toilet yayi wanka ita ko a wajen ya barta tana kukan takaici kace yau ya Fara sanin ta..

“Wai mutum ne bayi da hakkin kansa sai yadda wani yayi da shi gaskiya Hydar Allah ba zai bar Ku ba kai da ‘yan uwan ka”.

Tana cikin tunani ya fito harara ya watsa mata sannan yace,

” je ki yi wanka kizo akwai maganar da zamu yi “.

Tana hararar sa ta wuce toilet can ta fito d’aure da towel zata nemi kaya ya janyo ta kan gadon..

” jarabebbe kawai”.

Ta fad’a a zuciyar ta..

Manna ta yayi a jikin sa sannan ya Fara magana a hankali,

“Yanzu don nayi kuskure shine ba zaki yafe mini ba?Hafsat ko kece fa zaki d’auka abun nan gaskiya ce”.

Banza ta masa sai ma baccin ta da take k’ok’arin komawa..

” sannan duk Wata misunderstanding da zai shiga tsakanin mu kada Kice zaki juya mini baya,ba Zan lamunci haka ba bugu da Kari mala’ikun Allah na tsinewa duk macen da ta Hana mijin ta hakkin sa”.

“Hakki?kai da can baka San da hakki na akan ka ba kake k’ok’arin duka na,sannan kaje har k’ofar gidan mu ko sannu baka ce da mahaifiya ta ba”.

” See Babie kiyi hak’uri in sha Allah Zan gyara kurakurai na”.

Banza ta mishi ta Fara baccin ta..jin saukar numfashi sai ya dad’a janyo ta jikin sa sosai suka yi baccin tare…*°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 40📑*
*__________*📖washe gari kuma ita ta Fara farkawa da wuri ta zame jikin ta daga n nasa saboda sabulun da yayi wanka da shi wari yake mata..toilet ta wuce tayi wanka tare da d’auro alwala sannan ta dawo bedroom d’in tana hararar sa, so take ta tashe sa amma kuma bata son jin warin sabulun sa don haka ta toshe hancin ta da Hijab nata sannan ta Fara buga shi a hankali..+

“Hydar lokacin sallah na wucewa”.

Mika yayi tare da sauka a kan gadon ya shige tiolet inda yayi wanka sannan yayi alwala kan ya fito ma ta idar da sallah har ta Fara gyaran d’aki yana fitowa ta toshe hancin ta tana ta’be baki kamar zata yi kuka..

” me haka?”

“Sabulun da Kayi wanka da shi wari yake mini”.

” you are not serious, sabulun nan fa na wankan ki ne kuma ba yau muka Fara wanka da shi ba”.

“Ehh wari yake mini”.

” but naga da shi kike wanka”.

Ya fad’a yana sauke hannun jallabiyar sa da yasa yanzu.

“Ni bada shi nake wanka ba”.

Ta fad’a a shogwa’be

” da wanne kike wanka?”

“Morning fresh”.

Cikin tsawa yace
” what?”

“Kayi sallah lokaci ya kure”

Sallah ya tayar ita kuma taci gaba da gyara d’akin yana idarwa ya haye gado ita kuma ta Nade sallayar da yayi sallah da ita..

“In kin gama ba sai kin d’aura breakfast ba tea kawai Zan sha”.

Da kai ta amsa masa sannan taja k’ofar ta fice zuwa falo inda ta gyara sannan ta bud’e k’ofar falon.. Bud’ewar ta ke da wuya Hakeela ta shigo Allah ma yasa ta gama komai.

Da sakin fuska tace,

“Sannu da shigowa ga waje zauna”.

Zama tayi sannan Tasa kai a k’asa tace,

” Hafsat nasan duk abunda zance miki baza ki yarda ba amma nayi da na sanin abubuwan da na miki son Zuciya ne yasa ni aikata hakan”.

“Ayya yayi kyau”.

” pls Hafsat ki gafarce ni”.

“Hakeela fad’i me ya kawo ki don zanyi girki”.

” Hafsat Ai nima zanyi girkin don wallahi tunda aka sauke miki girki baki ga yadda nake wahala ba”.

“Tunda baki da ta cewa Bari na shiga kitchen”.

” No dama jiya naga kin fito daga wajen Baaba Ladi da kuka shiyasa nace a matsayin mu na kawaye Bari nazo naji me ya same ki”.

Hafsat taso ace Hakeela bata sauya ba da ta fad’a mata cewa ciki ne da ita don su San yadda zasu yi amma ta tabbata fadawa Hakeela na d’aya da zubar cikin jikin ta Wanda ko uban shi bai San da shi ba don haka tace,

STORY CONTINUES BELOW

“Ba komai”.

Sannan ta wuce kitchen Hakeela ko takaicin ne ya kamata amma sai taki tafiya sai ma d’aukar remote tayi ta Fara scrolling channels har ta iso Wanda take so..

Hafsat na gamawa tayi toasting bread sannan ta jera a dining bata yi mamakin ganin Hakeela ba saboda tana jin motsin ta daga kitchen d’in..

” Hakeela bismillah “.

” No ki Kira ya Hydar dai sai muyi tare zai fi,cuxx ba yadda za’a yi kici abinci da ni shi kuka yaci shi d’aya “.

” yana bacci kuma ba’a Tashin sa sai dai in lokacin sallah yayi”.

“Ohk to mu jira sa har ya tashi mana”.

Hafsat bata kawo komai ranta ba tace

” fine”.

Sannan ta zauna a falo lokaci zuwa lokaci ta kan sati kallon Hakeela ganin jikin ta da ciwo don dukan da Khaleel ya mata..

“Kin sha magani ne?”

Hafsat ta tambaye ta ko inda take bata kallo.

“A’ah”.

Mik’ewa Hafsat tayi sannan ta nufi bedroom nata taja drower ta Ciro magani sannan ta fice zuwa falon..

Tana fita Hydar na tashi time ya duba sannan ya shige tiolet ya watsa ruwa tare da yin brush sannan ya fito..
Hafsat ko maganin ta ajiye ma Hakeela tana fad’in,

” in kin karya ki sha zasu miki amfani “.

Poster Hakeela tayi ganin Hydar ya nufi dining d’in kab hankalin sa na kan wayar hannun sa ko inda suke bai kalla ba,sanye yake da vest sai boxer.

Bin direction na idon ta Hafsat tayi haka kawai sai taji wani kishi na taso mata bata San sanda tace,

” da baki a gidan fa ka fito haka”.

Sai a sannan ya d’aga ido ya kalle ta da kuma Hakeela da ke gefen ta cikin jin kunyar yadda Hakeela ta gansa ya juya hafsat ko tsayawa tayi a gaban Hakeela ta tare ganin ta..

“Ke baki San ba kyau kallon al’auran wani ba”.

” Hafsat da kaya a jikin sa fa”.

“So what Ai bai San dake a nan ba da ba zai fito haka ba mind you yayan mijin ki ne”.

Tana rufe bakin ta taji ya kwala mata Kira daga d’aki juyawa tayi ta nufi bedroom nasa tana shiga ya Fara fad’in,

” wannan wani irin iskanci ne?ni na baki izinin bud’e mini k’ofar gida duk sanda Kika so? good for you da ta kalle ni haka ko ba komai taga komai na mijin ki”.

Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba..

“Zaki cire mini kaya ne ko zaki tsaya kallo na a haka”.

Murkud’a masa baki tayi sannan ta nufi wardrobe ta d’auko masa jallabiya ta mika masa..hannun ta ya cabke tare da jefa bakin sa cikin nata ya Fara kissing sanda yayi mai Isar sa sannan ya sake ta yana fad’in,

” kada ki Kara murkud’a mini baki”.

Fita tayi ta bar sa a d’akin shi kuma sa kayan yayi sannan ya had’e fuska ya fito falon..

“Ina kwana ya Hydar”.

” lafiya “.

Yace sannan ya zauna a dining Hafsat ko bismillah tayi ma Hakeela sannan tayi serving nasa..mik’ewa Hakeela tayi ta zauna tana facing Hydar d’in inda Hafsat ta tura mata cooler tayi serving kan ta..

” baza ki ci bane?”

Hydar ya tambaye ta ganin tana tsaya a gefen sa..

Kai ta girgiza masa nan kuma ta dafa kafad’ar sa da hannun ta da k’arfi, dago ido yayi ya kalle ta tare da d’aga mata gira alamar tambaya amma sai ta girgiza masa kai tana hura hanci…

STORY CONTINUES BELOW

Kallon ta yayi har cikin ido nan ya fahimci akwai matsala don haka zai Mike ta girgiza masa kai tana nuna masa Hakeela da kai sai ya kalli Hakeela yace,

“Am Hakeela Dan Allah sandwich nake son ci ko zaki mini a cikin gida”.

Jikin na rawa tace

” of course yanzu ma Zan tafi “.

Tana gama fad’ar haka ta fice shi kuma ya bi Bayan ta ya rufe k’ofar ya dawo da wuri
” Hafsat baki da lafiya ko?”

D’aga masa kai tayi sannan yace

“Meke damun ki?”

“Ina da…….”

Sai wani Zuciya yace, kul Hafsat in Kika fad’a masa ko don Daddy’n sa zai ce Ku zubar”.

“Kina me!”

“Hydar jiri nake ji Bayan nan kuma ina jin Tashin Zuciya”.

” ko zamu je hospital ne!”

Da wuri tace,

“A’ah zai Bari help me na zauna a falo”.

D’aga ta yayi ya kaita falo ya kwantar ganin ta Fara dawa normal sai yace,

” kin Kara nauyi sannan jiya a bed too kin canza gaba d’aya me sirrin”.

Na shiga uku wato masu ciki daban suke Hydar zai gane..

“Baki bani amsa ba”

“Babu tace”.

Breakfast nashi ya gama sannan ya dawo inda take.

” Hw are you feeling yanzu?”

“Alhamdulillah”.

Tace.

” Hafsat wannan wani irin kazanta ne zaki mini magana bakin ki duk nyawu,bazan lamunta ba”.

Mik’ewa tayi da wuri sai toilet nan ko ya jita tana amai sanda ta gama ta fito sannan yace
“Zo nan”.

Zuwa tayi sai yaga gaba d’aya ta sake nan ya zaunar da ita a cinyar sa amma sai tace sabulun sa na wari..

” wannan fa ba naki bane”

“Ehh Dan Allah sake ni”.

” Hafsat nasan kina haka ne don na nisance ki amma ba wani warin da sabulu na ke yi,shin baza ki yafe mini bane?”

“Kayi gaskiya Hydar, meyasa da aka mini sharri baza Kayi amfani da brain naka ba,karshen fita na a gidan nan da kai na fita,sannan kasan ba Bari na ake ina fita ba a ina Zan samo maganin?”

“Sorry”.

Yace yana k’ok’arin shinshina ta da wuri tace,

” wallahi Zan iya maka amai a jiki”.

Wayar sa ya d’auka sannan yayi dialing number’n doctor Wanda ba family doctor’n su bane..

“Hello Doctor Hydar ke magana”.

Ido ta zare don ta San nata yazo karshe yau..

” Ohh Hydar it’s you ya kake?”

Da yake yasa wayar a hands free sai Hydar ya kalle ta sannan yace,

“Ina lafiya, pls mace ce komai sai tace yana mata wari sannan ta daina cin abinci kuma tana Tara nyawu a bakin ga amai wani irin ciwo ne”.

” hmmm doctor yace sannan yace,

“Matar ka ce?”

Kallon Hafsat yayi wacce don yadda zuciyar ta ke bugawa har hannun ta Tasa a kirjin ta.

STORY CONTINUES BELOW

“Ehh mata ta ce”.

” well ka tambaye ta zata fad’a maka don ita tasan meke damunta”.

“Ohk tnx doctor sai anjima”.

” yauwa”.

Tana jin haka ta sauke ajiyar Zuciya shi ko cewa yayi

“Bani ruwa a fridge”.

D’auko masa tayi tana zuwa tsakiyar falon ya kalle ta yace,

” Madam are you pregnant? “

Bata San sanda ta sake ruwan a k’asa ba jikin ta har rawa yake tace,

“Pregnant never”.

” haka kike tsoron ciki daga ambatawa Kika razana”.

Shiru tayi tana kallon sa shi ko hannu ya mika ya kar’bi ruwan sa don tasan aje-aje sai Hydar ya gane tunda shi d’in ba yaro bane don haka sai tace,

“Kana son nayi cikin ne?”

Cike da mamaki yake kallon ta kan yace,

“A’ah ban shirya Tara yara ba don haka ki bi a hankali kada ki sake Kice zaki yi ciki”.

” meyasa “.

” ba yara bane bana so,haihuwa da ke ne bana so don ba mai son Yaron”.

Ranta in yayi dubu ya baci sai tace,

“Jiki na kam Ai kana so ko da an gargad’e ka kada ka kusance ni amma abunda ya fito daga jiki na kam baka so”.

” nifa Bari na fad’a miki gaskiya ina son ki sai dai matsalar bana son yara shine kawai”.

“In Allah ya baka fa?”

“Ya kina magana kamar cikin gare ki,Ai nace miki bana so don haka kada kiyi”.

” Ni kuma ina so”.

“Cabb sai dai in zaki jira nan da wasu shekaru amma yanzu kam ba’a shirye nake ba”.

” fine tunda baka son nayi ciki in other muyi avoiding hakan daga yau jiki na ta haramta a gare ka”.

“Wannan kuma baki Isa ba,Ai akwai wasu hanyoyi”.

Mik’ewa tayi ta bar sa a wajen duk da ta San cewa bata Isa ta Hana sa ba don ita ma tana da bukatar sa amma kuma tayi gangancin d’aukar ciki da wuri kada ma yace cikin ba nasa ba ta shiga uku…kuka ta Fara yi don ita da abun cikin ta suna cikin hatsari Wanda ya kamata ya tsaya by their side shima yace baya so
**
Bangaren su Abdool kuma ba wani Improvement ga Aisha sai lalacewa take kullum in ta Kira sa sai dai yace su had’u a hotel hakan ya tabbatar mata Abdool ba mutumin kirki bane kuma tayi alkawarin koma mene  ne ita zata shirya shi in sha Allah..

Umma kanta ta San Aisha ta canza amma ko ta tambaye ta sai tace ba komai,ita Aisha kuma dama Hafsat ce abokiyar shawarar ta Gashi yanzu sun samu matsala.. Shiryawa tayi sab domin tuna address na Abdool da ya ta’ba fad’a mata ba tare da ta tambayi kowa ba ta kama hanyar gidan su..

Kwatance take ma driver suna tafiya dai-dai wani shago taga masalisan samari kuma Abdool na cikin su,Ciro wayar ta tayi ta Kira sa yana ganin ita ce sai ya mayar da wayar aljihu duk tana kallon sa,sake Kira tayi a karo na biyu inda yaja tsaki sannan ya mik’e yana receiving ya Fara magana kamar Wanda ya bugu mamaki ne karara a fuskar ta kenan intentionally yake hakan to me ribar sa,sauke glasses na motar tayi sannan tace,

“Baby ina gaisuwa”.

Sosai yaji kunya har ya rasa yadda zai yi ganin haka sai tace,

” shigo ciki”.

Shiga yayi driver kuma ya fice inda yake kallon ramar da tayi  sosai.

“Meyasa Abdool? Meyasa ka yaudare ni”.

STORY CONTINUES BELOW

” saboda bana son ki”.

Ya fad’a kai tsaye

“Wallahi karya ne ta fad’a tana Kuma”.

“Aisha ki daina kukar nan saboda Aure tsakanin mu ba zai yiwu ba”.

” meyasa? “

“Aisha sunana Abdullahi Musa Kamale Wanda na tabbata banda bukatar Kara ko kalma d’aya ce kin fahimci Waye uba na”.

Tunda ya ambaci Musa kamale wani duhu ya rufe mata ido take zuciyar ta ya Fara duka kamar zai ballo waje kenan Abdool yayan Hafsat ne  nan ko yaci gaba

” Aisha wallahi dai-dai da Rana d’aya ban ta’ba son ki ba kawai ina son d’aukar ma Hafsat fansa ne”.

Ita ba abunda take fahimta yanzu tunda yace mata asalin sa kuka sosai tabarke  da shi don ta tabbata ba Aure tsakanin su,duk da A.c’n da ke motar ita gumi take had’awa nan shi ma idon sa ya kada yayi zahir ba don shi na miji bane da kukan zai yi..kallon sa tayi sannan ta fahimci lallai shima yana son ta don haka da kyar ta iya cewa

“Zan tafi”.

Da kyar ya fita daga motar inda direct gida ya nufa abokanayen sa na mazalisa na kallon sa ganin take ya canza yana shiga ya Fara ball da duk wani abunda ya samu da wuri Lawal ya tare sa amma ina sai ma k’ok’arin dukan Lawal da yake ganin abun yafi k’arfin sa sai ya Kira Maama Abdool gaba d’aya idon sa a rufe yake haka ya ringa hauka don zafin barin Aisha dole Maama ta bar sa zuciyar ta ba dad’i gaba d’aya hankalin suya tashi..

Lawal ne ya fita waje nan ko abokanayen sa suka ce Wata mota ce tazo wajen sa ya fi minti talatin a ciki Bayan ya fito ne nan ya Fara hauka..

” Aisha ce”.

Lawal ya fad’a a zuciyar sa”.

‘Bangaren Aisha kuma driver na driving amma ji take kamar kanta zai balle kenan dama Abdool Tun farko ba son ta yake ba sannan don Hafsat ya yaudare ta..

Suna Isa gida ta jefar da bag nata a falon Umma da Khadija ne a falon da gudu ta haura upstairs tana goge hawaye cikin Tashin hankali suka rufa mata baya amma kan su iso ta buga k’ofar ta sa key,knocking Umma take tana fad’in,

“Aisha na Me ya same ki fito ki fad’a mini”.

Cikin tsawa tace

” I just want to be alone”.

“Aisha ki bud’e mana k’ofar kada ki illata kan ki”.

” dama kun damu da nine?I said you guys should leave me alone”.

Dole suka tafi Umma na tunanin Meya sa Mi Aisha yarinyar da bata da damuwa.. Ita ko Aisha kuka take da iya k’arfin ta tana
“Why Abdool? Yanzu don Kiyayyar dake tsakanin mu zamu rabu?”

Kuka take sosai Ana cikin haka Hydar ya shigo falon da wuri Umma ta mik’e tare da had’a hannun ta biyu alamar pleading tace,

“Hydar na roke ka ka tambayi Aisha meke damun ta don naga kunfi shakuwa”.

Da alamar tambaya  fuskar sa ya kalle ta

” Ehh Hydar this day’s gaba d’aya ta sauya yanzu  ta shigo gida tana kuka”.

Upstairs ya nufa direct d’akin su Aisha ya wuce inda yayi knocking k’ofar

“Khadija nace Ku bar ni ko”.

Aisha ta fad’a cikin tsawa

” how dare you Aisha ni Kika yi ma tsawa?”

Da Wuri ta mik’e daga zaunen da take ta bud’e k’ofar nan ta fad’a jikin sa tana kuka,ture ta yayi gami da maida k’ofar ya rufe sannan yace,

STORY CONTINUES BELOW

“Me yasa me ki?”

Shiru tayi sai ma goge hawayen ta take

“Kar ki yarda na maimaita tambaya ta”.

” ya Abdool ka tuna Wanda Hafsat ta maka maganar sa kwanaki har tace ina son sa?”

“Ehh Meya faru”.

” ya Hydar ka fahimci abunda Zan fad’a kada Kayi reacting pls”.

Cikin tsawa yace,

“Will you go to the point straight?”

“Dama Abdool yayan ta ne”.

Ba k’aramin bugawa zuciyar sa tayi ba nan take ya tuna gargad’in da Abdool ya masa na cewa muddin ya kusanci Hafsat to shima sai ya lalata kanwar sa.

Aisha na k’ok’arin fahimtar da shi Amma ina idon sa ya rufe baya gani

” Aisha me ya miki?”

“Babu”.

Mari ya d’ebe ta da shi a karo na biyu ya maimaita

” nace me ya miki?”

“Ya Abdool is not what you are thinking kawai yace muyi break up ne”.

” wato ni Hafsat da yayan ta zasu ci Wa Amana lallai kuwa bazan bar shi ba”.

“No ya Hydar kada ka masa komai”.

Ita Aisha tana k’ok’arin dakatar da shi ne saboda tasan muddin Hydar yayi wani Abu Abdool ba zai bata second Chance ba amma kan ta Ankara ya fice daga d’akin su Umma na falo ya wuce su..

” Wai meke faruwa ne?”
Cewar Umma.
Abdool da yanzu ya fito daga d’aki ba tare da ya kalli kowa ba ya nufi hanyar waje ko zai samu saukin abunda ke damun sa,fitar sa ke da wuya motar Hydar yayi parking a k’ofar gidan cike da izza Hydar ya nufo Abdool kamar mayunwacin zaki hannun sa rike da yoghurt yana iso sa ya juye masa a jiki ya Abdool na duba mai ya watsa masa nan kuma ya d’ebe sa da Mari..

Abdool na ganin Hydar ya Fara fad’in

“Wait Hydar I will explain my self”.

Amma ina yayi nisa baya jin Kira haka ya ringa kai mishi punch,Abdool ko ganin da gaske Hydar ke yi ga yan anguwa na kallon su sai ya Zuciya sha’anin ka da mai zuya nan ya kai ma Hydar punch ya kuma kai masa take fad’a ya kaure a tsakanin su sai kai ma juna duka suke yi nan yan anguwa suka taru domin raba su Amma ina….

Da gudu Saudat ta shige gida tana fad’in

” Maama zo Kiga ya Abdool na fad’a a waje “.

” Abdool kuma da fad’a? Duk zuciyar sa Ai baya fad’a “.

Nan ko ta d’auki Hijab ta nufi waje Ai sai ganin Hydar da Abdool tayi da wuri ta nufe su tana fad’in

” Abdool don Allah ka rabu da shi”.

Har Abdool ya sake shi sai ya sake kai masa punch nan Abdool ya koma suka cigaba da fad’a yin duniyar Allah sun ki rabuwa hankalin Maama ya matukar tashi don tasan dole a karshe zasu ji ma junan su ciwo Ana cikin haka Allah ya turo keyar Abba shi ma sun ki rabuwa sanda Abba yace,

“Abdool in baka sake shi ba Allah ya Isa”.

Nan ya sake shi Amma Hydar sai dukan sa yake a haka Abdool ya wuce gida Hydar ko mota ya nufa ya bud’e zai shiga Abba yace,

Aliyu”.

Cak Hydar ya tsaya don tunawa da Ammie ce kad’ai take kiran sa da Aliyu Amma bai juya ba..

” Dan Allah ba don ni ba ka shigo ciki muyi magana “.

Nan ma kin juyawa yayi don gani yake kamar Abdool ya kusanci Aisha

STORY CONTINUES BELOW

” Dan Allah “.

Abba ya kuma maimaitawa nan ya nufi gidan yana shiga yaga an shimfida tabarma Maama da Abdool suna zaune Abba ma zama yayi sannan yace,

” Bismillah zauna mana”.

“Gaskiya ba Zan iya ba don rabon da na zauna a tabarma Tun ina yaro”.

Tabbas akwai karanci tarbiya a tare da Hydar, ko da yake duk yan masu kud’i haka suke.

Abba ya fad’a a zuciyar sa sannan aka basa plastic chair nan ya zauna, yana sama duk suna k’asa deep down inside him yana feeling guilty Amma kuma girman kai ya Hana sa sauka k’asa..

” Hydar kai ne Babba mai ya had’a ka da Abdool”

“Abba ka tambaye sa shi ya San me suka mini shi da Hafsat”.

” Abdool me ya had’a Ku?”

“Abba ina fita kawai ya hau ni da fad’a”.

Malam nasan mai ya had’a su”.
Cewar Maama

” ohh Ashe abun daga iyaye ne”.
Cewar Hydar nan ko Abdool ya kama sa da fad’a akan me zai ci ma iyayen sa mutunci da kyar Abba ya raba su sannan Maama ta masa bayanin komai ta karashe da fad’in

“Hafsat bata San komai ba ranar da ta roke ka alfarmar Abdool ya auri Aisha bata San d’an uwanta bane ranar da ta sani kuma ta nuna masa rashin dacewar abunda ya aikata don ita ce ma tace su rabu”.

Abba na gama ji ya d’ebe Abdool da Mari yana fad’in,

” Abdool ni zaka yi ma haka?in sun wulakan ta Hafsat ma su da Allah don ba zai barsu ba kai waya aike ka rama Shatrrin da sharri?”

“Abba don Allah Kayi hak’uri Wallahi tausayin hafsat ne ya sani yin haka kuma duk yan gidan naga kamar Aisha tafi shakuwa da Hydar shiyasa nayi hakan”.

” rufe mini baki”.

A hankali Hydar ya mik’e ba tare da yace da kowa komai ba ya fice ya Dade a motar kan ya tashar ya nufi gida..a hanya yake fad’in

“Hydar me ka aikata yanzu abunda Kayi ya dace? Har gidan in law’s naka kaje Kayi fad’a?”
Buga staring motar yayi sannan ya kuma cewa

“Da wani ido Zan kalli Hafsat”.

a haka har ya iso gida yana parking ya zauna a mota don ya tabbatar yanzu kam labari ya Isa gare ta zama yayi a motar yau ne gobe ne har ya Fara bacci gate man kuma ganin motar a kunne duk da cewa wani lokacin Hydar kan tsaya a mota in ya dawo yana receiving call Amma na yau ya dad’e sai yayi knocking sau biyu nan Hydar ya sauke glass d’in

” naji ka shiru ne nace bar naga ko lafiya “.

Ajiyar Zuciya yayi gami da shafa fuskar sa da hannu biyu sannan ya kashe motar gami da d’aukar phones nashi ya fito, kallon sa daga sama har kasa gate man ke yi ganin yadda farar jumper’n sa tayi Dotti da squeezing.

” Alhaji fad’a Kayi ne?”

Kallon kansa yayi daga sama har k’asa nan yaga yadda jikin sa ya dawo.

“Alhaji dubi hular ka”.

Hular kamar a bakin kura aka kwashe sa.

Had’a rai yayi sannan yace,

” zaka iya tafiya “.

Tafiya gate man yayi Hydar ko ya nufi apartment nasa zuciyar sa na bugawa Aisha da take balcony nan ta gansa da gudu tazo

” ya Hydar ka masa magana?ya yarda zai Aure ni?”

Shi don fargabar da yake ciki sai yace,

“Aisha ki manta da shi don in nace Zan taimake ki zaki sa ni a matsala”.

STORY CONTINUES BELOW

” what do you mean?”

“You are on your own”.

Jin haka sai tace
” ohk”
Sannan ta tafi a zuciyar ta kuma cewa tayi zata nuna masa she is on her own..

“Wai Hafsat d’in kam wace ce da nake tsoron ta?”

Kai tsaye yasa kansa cikin falon ganin bata nan sai yayi ajiyar Zuciya ya Fara nufar bedroom nan ko ta fito daga kitchen carab suka had’a ido sai ya tsaya kamar wani Yaron ta, so mai mayar da namji bawa😅

“Daga ina haka?”

Yadda take kallon sa ya tabbatar ta gama jin komai sai yace,

“Wait Zan yi miki explaining”.

” me kuma zaka mini explaining Bayan ka dawo kamar yaro dubi jikin ka  fa sai kace dambe Kayi”.

Ajiyar Zuciya yayi sannan yace,

“Wasu ke fad’a naje raba su sai aka had’a da ni”.

Kai ta girgiza tana fad’in,

” ina ruwan ka da su?kuma kada ka shigo mini falo a haka ka tsaya a wurin “.

” Haba Baby Allah bazan sake ba”.

“Ni dai na fad’a maka”.

Tayi bedroom shi ko ta’be baki yayi don ya San dama basu koma normal ba sai can ta fito d’auke da Slipper’s a hannun ta ta ajiye masa nan ya cire Snicker’s nashi yasa Slipper’s d’in sannan yace,

” Baby na shigo?”

“Ehh “
Tace sannan ta nufi kitchen domin duba d’an waken ta tana fad’in,

“Na had’a maka ruwan wanka kaje Kayi in ka fito sai na matse maka punch na fuskar ka da ice”.

Kamar wawa haka ya shige yana magana shi d’aya har a toilet d’in, ta shiga kenan taji yana magana shi d’aya nan tayi knocking tana fad’in,

” kai da Waye? “

“Babu”.

Daga haka ta fice shi kuma yayi wanka ya fito falo nan ta matse masa sannan ta bashi d’an wake yace ba zai ci ba ya d’aura da

” Wai meyasa Kika daina dafa abinci mai ma’ana ne?

“Ciki”
Tace a zuciyar ta amma a zahiri sai tace,

“gani nayi a cikin gida kuke cin abinci”.

” ina wayar ki?”

Tana kashe na sa a chargi don so nake na karanta wani novel da daddare”.

Ta basa amsa tana cin Dan Wake da ta labta masa burkono,kallon ta yayi sannan yace

“Nifa bana son borkono ki Bari haka”.

” ina dai baki nane”.

“Nace ki Bari ko?”

“Meyasa”.

Yana scrolling remote yace,

” nasan zai jima bai bar lips d’in ki ba kuma kin San dai zanyi kissing naki ko?”

Kallon sa tayi sai taga baya kallon ta kai kawai ta girgiza a haka har ta gama ganin ta mik’e sai yace,

“Kizo mini da wayar ki akwai abunda zanyi da shi”.

Kawo masa wayar tayi nan yace ya tafi masallaci ita ko ta gyara gida bashi ya dawo ba sai Bayan i’sha ganin bai dawo da wayar ta ba sai tace,

” ya naga baka dawo da waya ta ba?”

“Laaa Kinga na manta a masallaci Bari na duba”.

Fita yayi a zuciyar sa yana fad’in ke da waya kam ba yanzu ba don nasan dole za’a fad’a miki abunda nayi da farko nasa number’n yan gidan Ku a black jist Amma nasan dole zaki kirasu don haka na karya Sim waya kuma nayi sadaka da shi”.

STORY CONTINUES BELOW

Ya d’an tsaya kan ya koma ciki sai yace mata wayar ta bata sosai taji haushi zata Fara mita yace jikin sa na ciwo dole ta masa massage..
Aisha ko a ranar yin duniyar Allah taki cin abinci..

Washe gari ma rufe kanta tayi a d’aki sanda Daddy ya tura a Kira ta nan ta fito..

” Aisha meke damun ki?”

“Daddy Aure nake so”.

Murmushi yayi sannan yace,

” banda abunki Aisha Ai kin kai ko don Kinga yan uwan ki basu yi bane?suma rashin mazajen ne”.

Daga Fareeda,Asma’u, Khadija duk haushi ne ya kama su.

“Daddy Wanda nake son ba zaka aura mini shi ba”.

” Aisha ko talaka ne Zan aura miki shi don I can make him to your standard “.

” Daddy Abdool Dan Musa Kamale nake so”.

Daddy zai kai spoon bakin sa sai ya jefar a k’asa nan kowa was shock tsantsan bakin ciki Daddy bai ce komai ba ya wuce bedroom Khadija ko cewa tayi

“Yarinya you are in pepper soup”.

Umma kam komai nata tsayawa yayi gwara da ace Fareeda ce ko Asma’u sai tace suje Kawai Amma Yar cikin ta ce Gashi tayi buri akan auren Aisha Ai ba ji ba gani ta hau dukan Aisha har taji mata ciwo nan ta zama kamar mahaukaciya sai cewa take

” Aisha ni zaki kashe da bakin ciki ni zaki tonawa asiri to Wallahi baki Isa ba”.

Haka take ta safa da marwa take nan aka sanar ma Daddy sai yasa aka Kira motar asibiti tana ganin su tace,

“Yauwa gwara da kuka zo Wallahi Aisha ta hauka ce”.

” Zulai ke zasu d’auka ba Aisha ba”.

“Wallahi Alhaji lafiya ta kalau Yar kace ta hauka ce”.

Nan ko ta ringa hauka Hafsat ko jin hayaniya sai ta shigo tana ganin yadda Umma ke yi ta ringa dariya a Bayan kujera har za’a tafi da ita Aisha ta fito tana ganin za’a tafi da Umma ta fad’i ta suma da gudu suka yi kanta nan aka gane Umma da hankalin ta sai Daddy yace a mata allura Amma taki sai yace su d’auke ta nan ta yarda aka mata allurar bacci Aisha kuma aka kaita d’aki..
Few hours later!!

Bayan Aisha ta farfado sai Daddy yaje wajen ta domin rarrashin ta amma taki a Daren ya tura a kashe Abdool Amma ya gudu..
Washe gari Daddy na zaune a falo ta fito da akwatin ta tana ja

” Aisha ina zaki je? “

“Zan shiga duniya tunda ba zaka aura mini Abdool ba”.

” in Kika fita a gidan nan sai na kashe ki”.

“Dama nasan za’a yi haka Bari na sauwaka maka”.

Nan ta fitar da poison zata sha da wuri yace,

“Dakata Aisha kada ki sha”.

“Sai Kayi alkawarin zaka aura mini Abdool”.

” ba Zan aura miki shi ba”.

Zata sha yace,

“Zan aura miki shi on one condition”.

Kowa was surprise Harda Hydar da yanzu ya shigo su Aunty Zainab da Maryam duk sunzo..

” Aisha nayi disowning naki daga cikin yara na ki manta da kina da uba”.

“Dad’in abun ba a kaina ka Fara ba Kayi ma ya Hydar”.

” Aisha….. “

Hydar ya d’aga hannu zai mare ta

“Not anymore ya Hydar don ni yanzu ba Yar gidan nan bane Zan iya ramawa in ka buge ni”.

STORY CONTINUES BELOW

Daga haka ta juya zata shiga upstairs Daddy yace,

” baki da komai a gidan nan don haka ki tafi kawai”.

“Abunda Zan d’auka bada kud’in ka aka saya ba”.

Tana shiga ta d’ebi bangles nata da necklace masu tsada sannan ta jefa ta window sai ta d’auki Qur’an ta fito kallon ta Daddy yayi yace,

” bani nan Ai shima ni na kawo miki daga Umra”.

Mika masa tayi sannan taja akwatin ta dai-dai lokacin Umma ta tashi sai kuka take..
Jan akwatin ta tayi hankali kwance ta fice a gidan inda kowa cikin takaici da bakin ciki suka haura upstairs saura Umma da Daddy kallon ta yayi sannan yace,

“Wai me Musa yake nema da ni ne?yara na duk sai bijire mini suke yi a kan sa,da farko Hydar akan Hafsat yanzu kuma Aisha da d’an sa”.

” hmmm nifa lamarin nan ya Fara bani tsoro alhaji”.
Aisha na fita direct gidan su Abdool ta nufa…

Maama da Lawal suna zaune sai jimamin Daren jiya suke na tura mutani su kashe Abdool Aisha tayi sallama da trolley’n ta,kallon ta Maama tayi inda ta amsa da sakin fuska duk da bata San wace ce bane Lawal ko cewa yayi
“Aisha”.

Murmushi ta masa Abdool dake kwance a d’aki jin an ambaci sunan Aisha ya fito.. Tana ganin sa ta nufe sa shi ko cewa yayi

” Aisha me ya kawo ki gidan mu?”

“Abdool na bar gidan mu mahaifi na yayi disowning na a kan ka”.

” to nan kam baki da masauki gaskiya gwara ki Kara gaba”.

“Haba Abdool ya zaka ce haka”.

Maama ce tace,

” Aisha bai kamata ki bijirewa iyayen ki akan Abdool ba,ki koma ki nemi gafarar su”.

Kuka ta fashe da shi Abdool kuma ya shige d’aki don su sun zata Hydar ne ya tura a kashe Abdool ba Daddy’n su ba..

Kuka sosai take kowa ya share ta a zuciyar ta tace,

“Kowa ya bar gida gida ya bar sa”.

Ganin Rana ya iso ta sai Maama tace,

” Aisha tashi a Rana”.

Mik’ewa tayi ta shiga inuwa gaba d’aya tausayin ta Maama ke ji Amma kuma ta San bata Isa tace komai ba har sai Abba ya dawo..

Haka Aisha taci gaba da kuka har Abba ya dawo nan aka sanar masa sai ya Kira ta..

“Aisha so kike ki jefa mu cikin matsala Bayan na jiya da yayan ki ya turo a kashe Abdool don Allah kiji tausayin mu ki bar mana gida ke da Abdool Baku dace ba”.

Yana gama fad’ar haka shima ya Mike yana fad’in,

” kan na dawo ta tafi”.

Sannan ya fice nan ko ta sake bud’e sabon babin kuka ganin da gaske take ba tafiya zata yi ba sai Maama tace,

“Saudat kaita d’akin Ku ta huta in ta gama sai ta tafi”.

Ai Ana kaita d’aki ta Fara bacci kamar ba gobe don ta kwana biyu bata yi bacci mai d’ad’i ba hankalin Maama sosai ya tashi ganin Abba ya kusa dawa Hafsat bata tashi ba..tura Saudat aka yi ta tashe ta amma duk tsoro take ji sanda Abdool ya fito yaga takalmin ta sannan ya shige d’akin

Ta’ba ta yayi a hankali ko ta tashi had’a rai yayi yace,

” tashi ki tafi gida”.

Rungumar sa tayi ta Fara kuka da wuri ya bare ta daga jikin sa yana fad’in,

STORY CONTINUES BELOW

“A’uzubillah!!daga yau kada ki Kara kuma maza ki barma na gida kan Abba ya dawo”.

” Abdool a kan ka fa na bijirewa iyaye na kai kuma kace baza ka bijirewa naka ba”.

“Aisha kinyi Babban kuskure a rayuwar ki saboda iyaye ba wasa bane,na yarda ina son ki Amma bazan bijirewa iyaye na a kan ki ba”.

” to wallahi ba inda zanje Ai nima nan gidan mu ne”.

Nan ta koma ta kwanta ba yadda bai yi ba dole ya bar ta a haka har Abba ya dawo kowa tsoro yake nan yace,.
“Aishar ta tafi ne?”

“Ehh”

Saudat tace Aisha ko jin haka sai ta fito tace

“Abba gani”.

“Zauna”.

Zama tayi sai yace,

” kin ci abinci? “
Duk mamaki suke ita ko cewa tayi,

“A’ah”

Nan yace a bata abinci gwate suka yi haka ta zauna taci bata nuna kyamar ta ba sai ma cewa da tayi,

“Wallahi Abba abincin yayi dad’i Hafsat na mana Amma bai kai wannan dad’i ba”.

” to Masha Allah “.

” Abba ya gajiyar aiki?”

“Lafiya kalau Maama na”.

Nan ko yaji yarinyar ta shiga ran sa har ma yace,

” ke Yar wace ce a cikin matar Alhaji Munir “.

Tana murmushi tace,

‘Yar Amaryar sa ce”.

” ahh madallah Saudat kai ta d’akin Ku sai kuke kwana tunda Fateema da Hafsat basu nan”.

To tace sannan suka nufi d’akin komai tsab da yake suna da sabta kallon ta saudat tayi snn tace,

“Ga gadon k’awar ki ki kwanta a can”.

” Thom tace tana murmushi..

Maama da Lawal da kuma Abdool tambayar Abba suka yi dalilin sa na barin Hafsat a gidan sai cewa yayi,

“D’azun ina wajen aiki sai ga Alhaji Amadu Wanda a da yake Dan gidan mu ni da Alhaji Munir, sosai muke aikan sa sai dai yafi shakuwa Dani akan Alhaji Munir to Bayan wannan kaddara ta fad’a mini sai ya koma ga Alhaji Munir ba don komai ba kuma sai don samun na abincin sa,to sai yake fad’a mini Alhaji Munir a office sai masifa yake nan kuma yace ba zai yafe mata ba shine ya roke ni da na rike ta Amana kawai tunda mahaifin ta ya Kore ta”.

” tho Abu yayi kyau”.

Cewar Maama

“Kai kuma Abdool Zan aura maka ita ne in Kayi alkawarin zaka rike ta Amana”.

” in sha Allah Abba “.

A d’aki kuma Aisha WhatsApp ta hau nan taga message na Hydar kan cewa she should think twice abunda take ba dai-dai bane sai taga yana online nan tace wannan shine final decision nata don yan gidan sun karbe ta hannu biyu,kin yarda yayi sai tace ya Kira ta suyi vedio call nan ko ta nuna masa k’ofar gidan da kuma su Abba dake magana a gefe ba tare da sun sani ba sannan ta dawo ta d’auka masa d’akin  da kuma gadon da aka bata..

Tabbas nan gidan su Hafsat ce
Yace a zuciyar sa, Saudat na shiga ta juya wayar cikin dabara ta nuna masa nan ko ya gama tabbatar Wa don akwai kama tsakanin ta da Hafsat duk da ita baka ce..

” ohk Aisha hankali na ya kwanta tunda na San inda kike,but duk sanda kike nemar taimako na kud’i ki tambaye ni cuxx I know how it feels in baka gida”.

“Ohk tnx”.

Sannan suka yi sallama nan Saudat tace ta jera kayan ta cikin wardrobe cuxx yanzu suna samu alhamdulillah..

Around 1:45am khaleel neh zaune a wajen night club… Wine bottles neh a gabansa kala daban daban, sai pressing phone yakeyi yanata jan tsakii… Ya kira line na ‘yanmatansa kap basu picking call nasa. … Sai kida ke tashi masu rawa nayi masu romance da sauransu kowa yana abinda yasha masa kai a wajen.. Can dai khaleel ya hango wata yarinya ‘yar matashiya itama ita kadaice ke zaune a table nata… Cikin azama ya mike yaje ya sameta… Dai dai sa’anda ta mike da nufin fita dan ta amsa call da ke shigowa phone nata… Juyawarta keda wuya taji mutum ya rungumeta… Khaleel kuwa baiyi kasa a guiwa bah ya fara kokarin kissing nata… Ae bai ankara ba yaji saukar maruka hagu da dama a face nashi… Malam ya haka zakazo ka wani kama mutum baka sansa bah… Kai har ka iso kazo inda nake nemah balle ka taba ni cewar yarinyar da khaleel ya kama din… Shi kuwa khaleel tsabar bacin rai da mamakin yarinyar ya kasa magana… Sai taune lips nasa yake tayiii… Ita kuwa taja tsaki tayi ficewarta ta barshi a tsaye,
Ganin ta barshi da abin kunya danma Allah yasa kowa a wajen harkarsa yakeyi babu wanda yasan ma yadda sukai…. Wani dake kan table din ya dauka ya fara sha anyhow… Yaga abin bai masa ba a hakan kawai sai ya fita ya shiga motarsa ya kama hanyar zuwa gida…..
Saide muce Allah ne kawai ya iso da khaleel gida lfy… Cikin maye da bacin rai ya shige side nasa, hakeela kuwa tana kwance tana sharar baccinta taji an bankado kofah, kan ta Ankara taji mutum ya fado a kanta da karfiii,  har ta saki karar azaba… Haba khaleel miye haka zaka wani zo min daki cikin dare… Ae bata karasa ba taji saukar mari… sannan ya shiga balbale ta da masifah, ke har kin isa, kina da daki a gidan nn ne mah, ko gidan ubanki ne nn??
Kuma Wlhy dan uwarkii yau dinnan sai kin bani hakkinah… Wlhy babu abinda zan baka, kaje ka wani bugu da giya kazo kana min rashin mutuncii.. To bazan daukii zagar min iyaye da kk kokarinyi bah ehe…. Dan giya kawai…. Cikin tsawa khaleel yace ke ni kk cewa dan giya??  An fada maka din karya nayi neh? Kai ba dan giya ba…. Ae kuwa kafin ta karisa ta fara jin saukar belt ta ko ina a jikinta, ni kk cewa dan giya iyee!! Hakeela tin tana ihu har ta daina tsabar ta dakuu,
Khaleel kuwa yana ajiye belt din… Ya bita kan gadon ya shiga yage kayan jikinta da karfii.. Take kukanta ya karu gashi batada karfin kwatar kanta… Yana gamawa shima ya tuba kayansa.. Ya shiga romancing nata karfi karfi, da mugunta… Cikin dasashiyar murya hakeela ta shiga bashi hkr.. Amma ina baima san tanayi bahh… A haka dai khaleel yayita azabtar da ita…. Yayin da yazo shiga main point of reaction neh hakeela taji wata iriyar azabar da bata taba ji ba a rayuwar ta, take ta tattaro iya karfin da ya saura mata, ta shiga turesa a kanta… Khaleel kuwa da yaga haka ya sake kai mata mari a fuska,  yanacewa watau baki gaji da duka ba koh… Kuma yaushe naga dama dole ki bani hakkinah daga yau, na bar daga miki kafa… A haka dai hakeela tana ji tana gani khaleel ya biya bukatrsa , ya rabata da budurcinta… Haka yayi shigewarsa toilet yayi wanka ya fito..  Inda ya barta haka ya fito ya kuma tarar da ita… Tsaki yaja sannan yace ke dama ba wani taste kike dashi na ‘ya mace bah kikayita jawa mutum raii😬 he banza sha sha sha kawai… Hakeela ji tayi kamar ta hadiya ranta ta mutu dan bakin ciki😭😭😭..

**

Hafsat ce a kitchen Hydar ko ya shirya zuwa office cikin sauri yace,

hafsat ina file da na baki ki ajiye mini?”

“Ka duba d’aki na cikin drower”.

D’akin ta ya wuce inda ya ringa bude bud’e har ransa ya soma baci ya d’aga file d’in kenan PT test ya fado k’asa, bin shi yayi da kallo sannan ya d’aga yaga positive kenan Hafsat Nada ciki ta boye masa..

Ita ko tana kitchen zuciyar ta ya tsinke aiko sai ga Hydar ya fito fuskar sa ko annuri babu ya nufi kitchen d’in sannan yace,

” me wannan? “

Yana nuna mata PT test d’in..

Ba kullum zanje muku posting ba don WhatsApp na na rikici sweety na zata ke muku posting Amma Nike typing naga comments kuma naji dad’i..*°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 41📑*
*__________*📖kallon ta yake cike da bacin rai sannan ya kuma kallon PT test d’in a karo na biyu gaba d’aya jikin ta rawa yake kan yace wani Abu wayar sa yayi ringing nan ya mika mata PT test din hannun ta har rawa yake ta kar’ba shi ko ya fice don call d’in important ne..+

“Hello Sir,Aisha na gidan malam Musa”.

” ohk na gode “.

Dama Hydar yasa a bincika masa inda Aisha take to shine yanzu ya fita domin jin abunda zai ce..

Yana fita Hafsat ta durkushe a wajen tana kuka inda take shafa cikin ta don yau ta San cikin yazo karshe yadda taga Hydar ya bata rai tana cikin kuka ta bud’e fuskar ta don dama ta rufe da hannun ta nan taga kafar mutum kuma ta tabbata na Hydar ne,d’aga idonta tayi ta kalle sa fuskar sa tsam ba annuri da wuri ta mik’e sai riko hannun ta yayi da k’arfi yace,

” Hafsat da gaske ne abunda na gani?”

Tana kuka ta d’aga masa kai sai gani tayi ya d’auki wuka da aka ajiye fruit’s akan center table da shi ido ta zaro ta Fara komawa da baya-baya tana fad’in,

“Wait I will explain my self”.

” explain what?”

Ya tambaya cikin d’aga murya
“Hydar kisan kai fa ba kyau kuma fa cikin nan naka ne ba na wani ba”.

” and so?”

Ya fad’a sanda ya karaso gare ta,rufe idon ta tayi don ta tabbata yanka ta zai yi amma sai taji ya sake wukan a kasa duk da haka bata bud’e ido ba sai da taji yayi hugging nata nan ta bud’e ido cikin kunnen ta yace,

“I Love you”.

Ture sa tayi tana kallon sa cike da mamaki sai ya had’a rai yace,

” why Hafsat? Me na ta’ba miki Wanda Kika ji zafin sa da har zaki yi ciki baza ki fad’a mini ba,do you think zaki iya separating child from his father? “

Tana kuka tace,

“Hydar kace baka so kuma by then already ina da ciki shiyasa na boye maka”.

” but kin San duk dad’ewa Zan gane tunda you can’t pregnant your self by the way Wa zai samu wannan kyautar yaki?”

“But ranar kace……”

“Wait abunda na fad’a ba har Zuciya na bane kuma by then ina zargin kina da ciki ne shiyasa na fad’i haka don na San in akwai zaki fad’a mini”.

” you mean ka amince da unborn child namu?”

Yana murmushi yace,

“Kema Kika amince bare ni”.

Da gudu ta fad’a jikin sa tana murmushi lokaci guda kuma tana share hawayen ta..

” look yanzu lokacin farin ciki ne ko so kike unborn child nawa yace na duki Mum nasa?”

Kai ta girgiza masa nan yayi hugging nata tight yana kissing nata ta ko ina,  ita harga Allah bata zata Hydar zai amince ba..zama suka yi a kujera sai yace,

STORY CONTINUES BELOW

“Wata nawa ne?”

“Biyu”.

Ta ba shi amsa tana kwance a jikin sa.

” amma me ya Hana ki fad’a mini? “

“Hydar Tun time da ka juya mini baya na fahimci ina da ciki to duba da gargadin da Daddy ya maka sai nake tsoron fad’a maka kada kace a zubar”.

” ya ilahi!!Wallahi na manta da Daddy Baby ya zamu yi da cikin nan?”

“Nifa koma me za’a yi Wallahi ba za’a cire ba don Ina son Abu na”.

” Ai dole kiso tunda nawa ne “.

Murmushi tayi tana shafa sajen sa..

” to ya zamu yi? “

“For now kada ki fad’a Wa kowa ya tsaya tsakanin mu kan mu samu mafita don Daddy zai ce a cire”.

” ohk hakan zamu yi,yauwa me ya had’a Aisha da Daddy ta bar gidan nan?”

Gaban sa ne ya fad’i sai kawai ya yanke shawarar fad’a mata gaskiya amma yasan allura ne zai tono garma don haka yace,

“Wai Aure take so Daddy kuma yace ba zai mata ba shine suka bata har yayi disowning nata”.

“Allah kyauta”.

ta fad’a a zahiri amma kasan zuciyar ta kuma tana tunanin kaddai don Abdool Aisha ta bar gidan..

Bangaren Hakeela ko wanka tayi tana kuka don ba mai taimakon ta lokaci d’aya kuma tana da na sanin shiga gidan su Hydar don gaba d’aya jaka Khaleel yake son maida ta kuma ta fahimci uwar sa ba Hana sa zata yi ba..

Tana fitowa wanka tayi sallah sannan ta cigaba da kuka tana tunanin Wai yau ita Hakeela wani gardi ke duka ita da iyayen ta lalla’ba ta suke don ita kadai ce gare su..

**
Gidan su Hafsat kuma komai normal don kowa ya saki jiki da Aisha..

Zaune suke a tsakar gida Maama na kitchen Saudat ko tana wanke-wanke Aisha ta fito ta gaida su sai ta wuce kitchen domin taya Maama duk da ba abunda ta iya sosai..

” Maama Bari Zan miki”.

“A’ah Aisha je ki huta”.

” kenan baki d’auke ni a matsayin Daughter ba ko?”

“Na Isa?zauna muyi”.

Suna cikin yi Abdool ya fito yaga Aisha sai ya shiga kitchen domin taya su gaba d’aya sun takura Maama sai ta fice ta bar musu kitchen d’in..

” Baby kin yi kyau fa”.

“Sai yanzu zaka mini magana fushi nake da kai”.

” kada ki mini haka Wallahi duk wani hukunci Abba ke yankewa a gidan nan”.

“Naji kuma ya wuce”.

Taya ta aikin yake a haka Abba ya fito ya Gan su cikin kitchen ya jima yana kallon su sannan ya wuce su basu sani bama..

Bayan sun gama sai suka sa ma kowa nasa kallon ta yayi yace,

” Aisha ki kawo mini nawa d’aki sai muci tare”.

“Nikam ina tsoron Abba”.

Tafiya yayi  yana murmushi nan ko kowa yaci abinci..

Bayan wasu hours Abdool ya fito Aisha na zaune a tabarma nan ya fito rata kad’an ne a tsakanin su suna kallo a wayar ta..

Nan ma Abba ya Gan su da wuri Abdool ya mik’e ya fita..

Bayan Abba ya dawo sai ya Tara su banda Saudat da Aisha nan yace,

” Abdool ba Zan lamunta abunda kake a gidan nan ba don haka cikin Wata d’aya Zan aura maka ita amma matsalar baka da gidan kan ka da kuma sana’ar da zaka ciyar da ita”.

STORY CONTINUES BELOW

Kansa kawai ya tsunkuyar sai Lawal yace,

“Abba in har gida da aiki ne baka da matsala da wannan a masa auren kawai”.

” hmmm Lawal kenan kana nufin zaku zage damtse wajen Neman kud’i ne?”

“Ko kad’an Abba ina da gida na Zan basa”.

” gaskiya ba zamu k’arbi Abu a wajen ka ba don bamu San daga ina kake ba”.

“Wallahi Abba da kud’in halak na saya gidan kuma tsakanina da Allah Zan basa saboda ba Zan cutar da Ku ba”.

” Lawal karantawa fa kake har yaushe zaka sake samun kud’in da zaka saya wani gida”.

“Dan Allah Abba ka bar zancen nan”.

**

Hafsat ko tsam yanzu bata samun sakin fuska a wajen yan gidan duk da cewa har yanzu tsanar ta suke na abunda tayi ma Daddy amma kuma tsanar yanzu yafi na da saboda bata Isa ta fita waje ba bakaken magana iri-iri wajen Hydar ne kadai take samun sauki gaba d’aya hankalin ta ya tashi nan kuma ta Dad’a zargin kowa ya gane meke tafiya tsakanin Abdool da Aisha Gashi duk sanda tayi ma Hydar maganar sai ya canza topic, wayar ta kuma da tayi magana sai yace zai sayo mata sabuwa don haka ta yanke shawarar zuwa gida ko bai sani ba..

Umma ko gaba d’aya duniya ba abunda ke mata dad’i gidan in ka shiga kace mutuwa aka yi don uwar bakin ta nitsu..
Aboki na zo ka raka ni”.

Taxi suka shiga basu tsaya ko ina ba sai wani sabon anguwa duk da gidajen ba na masu kud’i bane nan Lawal ya biya kud’i sannan suka fito bud’e gidan yayi yana fad’in,

” shigo Abdool “.

Shiga yayi gida ne madaidaici falo d’aya sai 3 bedrooms da kitchen ta waje sai toilets a ciki,gidan yayi kyau ba laifi Gashi akwai fili sosai,bud’e hannun Abdool Lawal yayi sannan yasa masa key yana fad’in,

” Aboki na gidan ka ne halak malak”.

“No Lawal ba Zan iya karban gidan nan ba yafi k’arfi na”.

” mtsww nasan dai tsoron ka kada da kud’in haram na saya to wallahi kud’in halak ne “.

Hugging na lawal yayi suka zaga gidan dukka sannan suka fito a hanyar su na komawa Lawal yace ma Abdool ya basa account number’n sa nan ya basa..

Shigar su gida ke da wuya Lawal ya shiga tiolet Abdool kuma yaga alert,baki da hanci ya bud’e domin ya kasa yarda da abunda idon sa ke gani..

” Two million? Kaii ba gaskiya bace”.

Irga figures d’in yayi yaga dai 6 zero’s ne nan yace ma Saudat
“Ke duba mini”.

Tana dubawa yaga kamar zata bata masa lokaci sai yace,

” Maama duba mini nawa ne”.

Sai kuma yace,

“Baza ki gane ba ma Aisha”.

Nan ta fito sai ya mika mata wayar yace,

” nawa ne wannan? “

Kallo tayi sannan tace,

“2 millions mana”.

” what?Wallahi Lawal zai fito ya same ni”.

Nan ya nuna musu gidan da Lawal ya basa duk baki suka bud’e Lawal na fitowa Abdool yace,

“Lawal yankan kai ka Fara?”

“A’uzubillah,wallahi kud’in halal ne”.

Yana gama fad’ar haka ya fice Abdool ko cewa yayi
STORY CONTINUES BELOW

” Wallahi  Bari Abba ya dawo shi zai raba mu”.

Duk Lawal ya daure musu kai Abba na dawa Abdool ya nuna masa sai ya Kira Lawal d’in,

“Lawal a ina ka samu kud’in nan?”

“Abba na halak ne kuma Ai bazan cutar da Ku ba”.

” Lawal har yau fa kana zaune a gidan mu amma bamu San asalin ka ba”.

“Abba Zan fad’a maka in lokaci yayi amma ba yanzu ba”.

” Allah kai mu”.

“Yauwa Abba in anyi sallar i’sha ina son zamu yi Wata magana”.

Yana gama fad’ar haka ya fice Abba ko masallaci ya wuce inda yayi magrib yana i’sha ya dawo gida da wuri

” Abdool ina Lawal d’in? “

Bai shigo ba tukun”.

Safa da marwa Abba ke yi har Lawal ya shigo nan Abba yace,

“Gani zo muyi maganar”.

Zama suka yi inda Abdool ma ya zauna sai Abba yace,

” bamu waje “.

” A’ah Abba bar shi kawai”.

“To ina jin ka”.

” Abba  dama Wata alfarma nake nema a wajen ka”.

“Wace irin alfarma kenan?”

“Abba Saudat nake so ka bani na aura”.

” Lawal Aure fa shi ba wasa bane ba yadda za’a yi ban San asalin ka ba na baka ‘yata ka aura”.

“Don Allah dai Abba Wallahi zuwa na gidan nan na Santa kuma har na Fara son ta”.

” Lawal anzo wurin da dole na San asalin ka “.

” to shikenan yau Zan fad’a maka asali na”.
Kamar yadda ka sani suna na Lawal mahaifi na kuma Abubakar shamaki”.

Baki Abba ya bud’e yace,

“Kana nufin kai d’an Shamaki ne?”

“Ehh Abba.
TUNANI!!!

Abba da mahaifi na da kai da kuma mahaifin Hydar Ku abokanaye ne guda uku Wanda kowa ya San ku..

Mahaifi na d’an riko ne a wajen  wani Bappan sa a Nigeria,so ba jimawa Bappan nasa ya rasu by then kuma sun shaku sosai kuna business amma Allah bai buda muku ba..mahaifi na na business da Ku kuma kuna son junan Ku sosai Ana cikin haka sai Allah yayiwa Baban sa rasuwa kuma dama asalin su ‘yan Egypt ne nan aka Kira sa yaje yayi claiming gadon sa sai kawai ya had’a dukiyar sa ya koma can gaba d’aya Bayan an bashi gadon sa sai ya had’a da dukiyar sa yaci gaba da business wannan dalilin yasa kuka ji sa shiru bai dawo ba..

Bayan komawar sa da shekara ya auri  Mahaifiya ta inda ta haifi Sisters na guda biyu time d’in Alhaji Munir ma yana da yara uku,Maryam Zainab sai kuma Hydar yana yaro, kai kuma lokacin baka yi Aure ba sai daga baya ka auri Maama ba jimawa ta haifi Abdool Wanda nima a lokacin aka haife ni don tsakanin mu ba nisa…

Allah ya bud’ewa mahaifi na sosai don duk yafi Ku dukiya saboda a can ma Ana ji da shi..duba da gatan da nake samu sai na sangarce na kuma lalace amma kuma bana sata,zina,shan giya kawai dai bana jin maganar kowa ji nake Mun gama Tara komai ba Wanda ya kai mu..

Mahaifi na kuma hakan na masa ciwo sosai ya kuma rasa yadda zai yi da ni don ko karatu bana so Ana cikin haka na gama degree na sai yace zai turo ni Nigeria service nace Allah sauwaka..

To bincike yasa ake masa a Nigeria na skull dai zai turo ni service nan ko ya gane ka gama talaucewa Alhaji Munir kuma sai abunda ya karo a arzikin sa yayi mamaki sosai sai ya turo ni ba tare da ya ajiye masu kula da ni ba…

STORY CONTINUES BELOW

Farkon zuwa na na wahala sosai don ko abinci Nike ciyar da kaina da na fahimci kuskure na sai na Kira Baba na na nemi yafiya da kuma masa alkawarin Zan zama responsible in future nan yaji dad’i yace zai had’a ni da Ku..

Abu na farko da yayi shine yasa aka nema masa inda Abdool ke Neman kud’i sai ya Kira ni naje wajen sai yasa body guard’s nasa suka cire wallet na suka Yar nan Abdool ya bani na masa godiya na biyu kuma body guard’s nasa suka tare Abdool zasu daka na taimaka masa duk ban San shi  ke tura su ba haka muka ringa haduwa da Abdool har muka Saba nan ya fahimci banda wajen zama sai ya kawo ni nan..

Mahaifi na ya turo ni gidan Ku ne don  na bincika masa meke tafiya a rayuwar Ku kuma duk abunda ya faru ina sanar da shi har son Saudat “.

  Back to story!!
Shiru Abba yayi sannan yace,

” had’a ni da mahaifin ka”.

Kiran Baban sa yayi sannan yace,

“Ga Abba”.

Mik’ewa Abba yayi yana fad’in,

” Alhaji shamaki kai ne?”

“Ehh Alhaji Kamale ya Bayan rabuwa?”

“Alhamdulillah kaji batun da da yaro yazo da shi a gaskiya ba Zan iya Hana d’an ka ‘yata ba”.

” na gode sosai Amma so nake a had’a auren “.

” gaskiya bazan boye maka ba dawainiya zai mini yawa”.

“Kar ka damu Ai nima Saudat ‘yace a gare ni”.

” A’ah kasan bana son taimako “.

” Ai Lawal shi zai mata komai tunda shi ke son ta kuma in sha Allah a auren zanzo sai muyi magana don ina son ganin ka”.

“To sai kazo”.

Daga haka suka yi sallama..

” Lawal kaje na baka auren Saudat munyi magana da mahaifin ta “.

” na gode sosai Abba “.

” Allah maka albarka “.

” Ameen”.
A yau d’in ne Hafsat ta shirya domin zuwa gidan su don tasan tabbas Abdool ya San komai don haka yana fita Tasa driver ya kaita da d’ayan motar sa..

Isar ta gida ke da wuya taga Aisha nan ko ta dad’a tsarguwa sai ta zauna tana cewa,

“Maama Wai me ke faruwa ne kowa yaki fad’a mini?”

“Hafsat Aure Abdool zai yi nan da sati hudu”.

” Aure kuma Maama shi da Wa?”

“Da Aisha”.

” garin yaya?”

Kan Maama tayi magana Hydar yayi sallama a gidan,durkusawa yayi kad’an ya gaida Maama sannan ya kalli Hafsat yace,

“Akwai matsala muje gida”.

” butt….”

“Muje kawai”.

Bin sa tayi nan ko Maama ta fahimci Hydar baya son Hafsat ta San komai sai kawai suka barta a mota yace,

” da izinin Wa Kika fita?”

“Sorry Wallahi na kasa fahimtar komai shiyasa naje gida”.

Ta fad’a tana kwanciya a jikin sa..

” tho me Kika ji a gidan?”

“Babu kafun naji ma kazo kawai ance auren ya Abdool da Aisha nan da Wata d’aya”.

Murmushi yayi a zuciyar sa yace,

STORY CONTINUES BELOW

” gwara da baki ji ba”.

Jikin Ammie kam har yau ba wani improvement..
Abba ne yasa aka Kira  masa Saudat tana zuwa ta zauna a k’asa sai yace,

“Saudat ba don komai na Kira ki ba sai don na shaida miki na bada auren ki ga Lawal”.

Da wuri ta d’ago ido ta kalli Abba zuciyar ta na bugawa sai kuma ta sauke k’asa tace,

” Abba Aure kuma?”

“Ehh Aure nan da Wata d’aya ko baki so ne?”

Shiru tayi don su a gidan su yaro baya ja da Babba sai Abba yace,

“In har baki so fa gwara ki fad’a don bazan miki auren dole ba”.

Nan ma shiru tayi sai Abba yace,

” to je ki na baki lokaci in kinyi shawara sai ki fad’a ma Maaman Ku”.

Mik’ewa tayi inda Maama tabi ta d’aki tana fad’in,

“Saudat a zaman da Lawal yayi a gidan nan Mun yaba da halin sa amma kiyi tunani”.

” Maama kun San asalin sa ne da kuke ce mini zaku bani shi “.

” Ehh Saudat d’an abokin Abba’n Ku ne”.

“To zanyi tunani a kai”.

Maama ko fita tayi don bata ga ta zama ba..

Aisha tace zata musu girki  Amma Maama na fita suka kafa shafin soyayya ita da Abdool a hanyar k’ofar gida har Rana yayi Saudat ko cewa tayi
” Aisha shine  kikace zaki yi girki?”

“Barsu kawai Zan ta yaki”.
Cewar Lawal.

Kitchen ta wuce sai tayata yake Amma sai share sa take yi don haushi yake bata ganin baza ta sake da shi ba  sai yace,

” Abba bai Isar miki sako na bane?”

“Ya Isa mana tunda kunyi yadda kuke son da ni”.

” ba wani in har baki so ba za’a miki dole ba”.

Shiru ta masa ta cigaba da aikin tayana tayata sai yace,

“Me amsar ki?”

“Zanyi tunani”

Murmushi yayi don duk abunda aka ce za’a yi tunani to akwai interest nan ya ringa mata hira har ta saki jiki da shi sai hira suke suna dariya don dama friends ne..

Maama na dawa taga dandali har biyu sai ta Kira Saudat tace,

“Ke da Kika ce sai kinyi tunani ne nagan ki da shi”.

” inda-inda ta Fara sai tace,

“Jeki kawai”.

Abba na dawa Maama tace ba sai an jira ta Saudat ba a cigaba da shiri kawai..
    Bayan sati Uku!!!

A yau ne ake kyautata zaton za’a kawo lefen Saudat don yanzu Aure saura sati d’aya amare ko Ana gyara su dai dai gwargwado ba  wani bambamcin da ake nuna ma Aisha inda a gidan su ko ba’a San auren ta saura sati d’aya ba..

Shiri sosai aka yi na tarbar ‘yan gidan su Lawal don shima ya koma sai dai kullum suna   lik’e a waya.

Maama ce ta kalli Aisha tace,

” bani number’n Hydar “.

Bata number’n tayi sai Tasa a wayar ta ta Kira sa yana picking tace,

” an wuni lafiya Maamar Hafsat ke magana “.

” lafiya kalau Maama ya mutani gidan “.

” suna lafiya dama na Kira ne domin sanar da kai auren Abdool wani sati kuma ina da bukatar Hafsat a gida don auren yayan ta da kanwar ta”.

Jim yayi sai can yace,

“Zan tura ta in sha Allah”.

” to a gaida gida”.

Yauwa na gode Maama..

“Maama Wai zai turo ta?”

“Ehh Saudat”.

” Kice gobe akwai shagali ga Su Sis Faty da Hamma Naseer zasu dawo ga kuma Aunty Balkee da Murjanatu zasu zo”.

Aisha dai kallon su kawai take don ta tabbata da iyayen ta na son auren da haka zasu yi ta yi ita da ‘yan uwan ta amma yanzu shiru kake ji..

‘Bangaren Hakeela ko gaba d’aya Khaleel ya sa mata pressure kullum duka kuma duk sanda ya nuna yana bukatar ta dole ta basa had’in kai Gashi ta lalace tayi baki kuma ta rame kai babbar matsalar ta ma rashin lafiyar da take fama da shi ko abinci bata iya ci…ga aikin da ya mata yawa don har yau Hafsat bata dawo girki ba sai dai kuma tana cin uban ‘yan aikin don duk wani aiki suke yi ita dai tana zaune sai zagin su take..

Yau ma kamar kullum tana zaune a kitchen tana chart a wayar ta sai instruction take basu a haka har ta gama girkin nan ko suka jera a dining tazo ta Fara serving nasu..

Zata yi serving Umma kenan Tashin Zuciya yazo mata ba yadda bata yi ba amma ta k’asa controlling da gudu ta nufi waje kan ta fita ma har amai d’in ya fito..

Tana gamawa ta dawo falo nan Umma Tasa aka goge sannan tace,

“Hakeela me ke damun ki?”

“Umma Wallahi this day’s duk bana jin dad’i Gashi amai ya dame ni kuma na rasa meke damuna”.

Da yake ‘Yar ido ce nan Umma ta Kira family doctor yazo the fist thing da Hakeela ta Fara complain a kai shine ciwon kai nan yaga jikin ta duk ciwo  kuma ya tabbata Khaleel ne yake dukan ta tunda shi d’an giya ne sai yayi tunanin hawan jini ne don haka ya d’ebi jinin ta ya tafi..

Bayan magrib ya Kira Umma yace,

Hakeela nada ciki da kuma hawan jini don haka ake kula da ita”.

Godiya ta masa bakin ta kamar gonar auduga don murna a lallai Hakeela tayi ciki Hafsat kuma shiru..

Kuyi hak’uri da wannan kuma Ku mini uzuri ina da abun yi..*°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 42📑*

*__________*📖numfashi yaja gani da mik’ewa ya d’auki key’n mota ya fita a office nashi ma’aikata sai gaisuwa suke d’aga masa Amma ko inda suke bai kalla ba.ko da ya shiga motar ma ya dad’e kan ya tayar sannan ya nufi gida gaba d’aya bai ganewa kan sa ba..

Parking yayi inda ya kuma sauke numfashi sannan ya rufe motar ya nufi apartment nasa a falo ya tarar da Hafsat zata shige kitchen da wuri ya rungume ta gami da rufe ido,ita ko Hafsat tana jin yadda zuciyar sa ke bugawa da wuri tayi breaking hug d’in tana fad’in,

“Baka da lafiya ne?”

Komawa jikin ta yayi a karo na biyu ya kuma lumshe idanun sa ita ko gaba d’aya hankalin ta ya tashi ganin yadda duk yayi sanyi..+

“Pls Hydar say something shirun ka na bani tsoro”.

Breaking hug d’in yayi yana mata murmushin da iya baki ya tsaya a razane tace,

” jikin Ammie ne?”

Kai ya girgiza mata sannan ya kama hannun ta suka zauna a kujera yasa hannun sa kan cikin ta yace,

“Baby I will miss you”.

” na shiga uku kenan tafiya zai yi”.

Ta fad’a a zuciyar ta amma a zahiri sai tace,

“Tafiya zaka yi ne?”

“A’ah d’azun Maama ta Kira ni Wai na tura mata ke”.

Dariya tayi tana nuna sa a karo na farko da tayi irin dariyar har tana dukan sa tace,

” shine ka zama kamar Mara lafiya “.

” I will miss my unborn child”.

“Ni fa dama yau in ka dawo Zan tambaye ka Amma tunda Maama ta sauwaka mini Bari na Fara shiri”.

Cikin gaskiya da gaskiya ya kalle ta yace,

” ba zaki yi missing na ba?”

“Akan me?gidan mu fa zanje kwata-kwata yaushe na San ka”.

Kenan yarinyar nan tana nufin bata so na ne ko me?”
ya tambayi kansa ita ko d’aki ta wuce inda ta d’auko trolley ta ajiye a falon nan ta jido kayan ta ta Fara shiryawa shi dai kallon ta kawai yake..

Tana cikin shiri yace,

“Yau kam ba za’a bani abinci bane?”

“Sorry Daddy’n…”.

” karasa mana Daddy’n Waye”.

Kai ta girgiza tana fad’in

“Manta kawai”.

Sannan ta kawo masa abinci tana fad’in,

” yaushe ma Kayi breakfast “.

Bud’e cooler’s d’in yayi sai yace,

” nifa ba Zan ci wannan abincin ki na masu ciki ba gaskiya “.

” to ya kake so nayi?”

Anzo wajen yarinya ba inda zaki

STORY CONTINUES BELOW

A zahiri sai yace,

“Kin tuna d’an waken da Kika yi ranar irin ta nake so”.

” an gama oga”.
Ita gaba d’aya murna take zata gida da wuri ta shiga kitchen ta had’a masa ta kawo..

Cigaba da shirin ta tayi tana gamawa ta rufe zip d’in sannan tace,

“Bari na shiga wanka”.

” no stew zaki had’a mini Wanda Zan ke ci in kin tafi”.

“To”.

Tace shi kuma ya mik’e yana fad’in,

” Bari naje masallaci azahar yayi”.

Yana fita ta Kira Baaba Ladi a waya tana fad’in,

“Don Allah Baaba stew nake so ki had’a mini,Zan je gida Hydar Wai sai na had’a masa kan na tafi”.

” in dai stew ne akwai Wanda na gama bada jimawa ba yana cikin fridge “.

” yauwa don Allah ki dumama sai ki bayar a kawo mini “.

” to shikenan “.

Wanka ta shiga tana fitowa taga stew nata a dining da wuri ta juye a pot nata sannan ta sa a fridge ta koma tayi sallah daga bisani Tasa kaya..

A dai-dai lokacin Hydar ya shigo don ya tabbatar bata gama ba da mugunta a fuskar sa yace,

” ke da kike had’a stew ne Kika zauna a nan?”

“Ai na gama”.

” what?”

“Relax”.

Ta fad’a tana dafa kafad’ar shi sannan ta cigaba

” ina da tattasai na a soye ga kuma nama a soye so bai yi taking long ba tunda gas ne”.

“Gaskiya ni bana son soyeyyen tattase ki zubar da stew d’in kawai ki mini wani”.

Kallon sa da kyau tayi nan tayi sensing Hydar baya so ta tafi ne sai ta had’a rai tace,

” me zai Hana ka fito fili kawai kace ba Zan je ba ka bar making excuses “.

” Nifa ban ce haka ba”.

Ranta sosai ya baci sai tayi parking kanta yana kallon ta don hijab zata sa sai ya rike hannun ta yace,

“Zan fad’a miki reason da yasa bana son kije gidan Ku”.

Shiru ta masa nan ya Fara fad’a mata Tun zuwa d’akin Aisha da yayi har fadan sa da Abdool da kuma yadda yayi da iyayen ta..

Yana d’ago ido ya d’aura kanta nan yaga idon ta jazir kamar wuta a wajen ta durkushe tana fadin,

” Hydar fad’a da yaya na sannan kaci mutuncin iyaye na ko hak’uri baka basu ba ka tafi”.

“Dan Allah Baby kiyi hak’uri Wallahi nasan nayi kuskure”.

” a gidan nan me Baku mini ba,iyayen ka har duka sun mini Amma dai-dai da Rana d’aya ban ta’ba tamka musu ba Kai kuma har gidan mu….”.

Sai kuka yaci k’arfin ta

“Baby Wallahi har Zan koma na basu hak’uri amma….”.

” Amma baka son ka zubda ajin ka ko?”na gode sosai”.

Tana gama fad’ar haka ta mik’e tare da d’aukar hijab nata ta Saka ba tare da ta sake kallon sa ba ta ja akwatin ta ta bar apartment d’in tana goge hawaye Hydar ko yasan bayi da bakin dakatar da ita..

Falon gidan ta shige domin sallamar Baaba nan taga Hakeela kwance a cinyar Umma sai zuba shogo’ba take yi ita ko kitchen ta shige nan ma Baaba bata nan sai ta fito..

STORY CONTINUES BELOW

“Wasu dai a gidan nan sai cinye mana abinci suke waya sani ma ko juya ce”.

Dariya Hakeela tayi tana fadin,

” Umma Ai in tayi ciki ma sai dai a tambaye ta inda ta samu don mijin ta yafi k’arfin ta “.

Ita dai Hafsat tana share hawaye taja akwatin ta nan Umma tace,

” Wallahi bakin ciki yanzu Kika Fara gani gidan nan dai baza ki bar sa ba”.

Ko a jikin ta fita tayi nan Umma tace gate man kada ya bud’e mata k’ofa..

Hydar na kallon ta daga apartment nasa nan ya Kira gate man yace a bud’e mata Ana bud’ewa ta fice abunda..

Sanda ta tabbatar fuskar ta ba alamun damuwa sannan tayi sallama a gidan su nan taga gidan akwai mutani d’aya d’aya..

Jikin Maama ta fad’a tana murmushi sai Saudat da ke gefe tace,

“Arrogant husband nakin ya barki ne”.

Batar da maganar tayi da fadin,

” shirye-shiryen me kuke yi haka?”

Saudat ba kunya tace

“Lefe na za’a kawo”.

” bangane lefen ki ba ina ce auren ya Abdool ne?”

“Dallah bani waje Mara kunya kawai”.

Mik’ewa Saudat tayi tana fadin,

” Bari naje wajen Aisha “.

Hafsat ko kallon Maama tayi tana fad’in,

” Maama Wai meke faruwa ne Wa Saudat zata aura?”

“Lawal”.

” Haba Maama mutumin da Baku San asalin sa ba “.

” kwantar da hankalin ki”.

Nan Maama ta fad’a mata komai sosai tayi murna sai ta shige d’aki a kan gado taga Aisha kwance tana chatting sai tayi kamar bata ganta ba ta fita ita Aishar ma hakan yafi mata don bata San da wani ido zata kalli Hafsat ba..

Fitar ta ke da wuya Aunty Balkee(favorite Aunty)da Murjanatu da SiS Faty da kuma Hamma Naseer sai Sisters na Abba guda biyu suka shigo gidan Ai Hafsat da gudu ta shige jikin Aunty Balkee..

Maama kam mamaki ne sosai ya kamata tace,

“Kuda kuka ce gobe ne zaku taso sai gaku yau”.

” baza ta nake son yima Hafsat “.

Aiko Saudat ma da gudu ta fito suka rungumi juna da Sis Faty da kuma Hamma Naseer Hafsat d’in ma hakan ce ta kasance..

” Hamma Naseer sai yau”.

“Ehh Wallahi Hafsat kewar Ku ne ya dawo da ni”.

” ke kuma Sis Faty tafiya ko sallama “.

” Hafsat Ai gidan kun ne sai Ku,ko mutum yaje sai a sare sa da tambayoyi”.

“Ke kuma Murja kin kyauta ko Kira Babu”.

” yaushe layin ki yake shiga Ai ke ya kamata ki Kira ni”.

“Wai ina Amaryar Abdool d’in ne?”

“Bari na Kira miki ita Aunty”.

Cewar Saudat nan ta shiga d’akin su ta fito da Aisha kanta a k’asa sister’s na Abba suka ce,

” Ahh Amarya kam kyakyawa”.

“Hafsat Amma tayi kama da mijin ki”.

Cewar Murja.

” Ku huta zaku ji komai “.

Bayan sun huta sai Maama ta fad’a musu komai Harda turowa da aka yi a kashe Abdool nan ko Saudat ta d’aura da rashin mutunci da Hydar yayi Hafsat was not shocked tunda ya fad’a mata komai..

STORY CONTINUES BELOW

” to Allah kiyaye gaba yaushe ‘yan kawo lefen zasu iso?”

Aunty Balkee ta tambaya

“Yanzu dai sai Mun gansu don Wai Bayan zuwan Lawal Nigeria sun koma Dubai da zama so daga wajen zasu zo”.

” Allah kawo su lafiya “.

Duk da Ameen suka amsa Hafsat ko d’akin su ta shiga nan Aunty Balkee ta bita..

” Aunty kin shigo kenan? “

Cikin zargi Aunty Balkee tace,

“Hafsat me nake gani a jikin ki”.

Ba k’aramin bugawa zuciyar ta yayi ba sai ta batsar tace,

” a ita ina?”

“Hafsat nifa ba yarinya bace kin San me nake nufi”.

” Aunty ban fahimce ki ba”.

“Cikin da yake jikin ki nake magana a kai”.

” ciki kuma? “

“Kinga kada ki raina mini wayo kowa ya kalle ki da kyau yaga mai ciki don alamu sun bayyana”.

Kuka ta Fara tana fad’in,

” Dan Allah Aunty ki rufa mini asiri kada kowa yaji”.

“Ashe har yau baki da hankali na rufa miki asiri fa garin yaya haka ya faru?”

Cikin kuka tace,

“Tsautsayi”.

” tsautsayi  shine kike ce na rufa miki asiri, Yaron nan fa har gida yazo ya nuna fitsarar sa amma ke kina can Harda barin sa ya dirka miki ciki upon all warning da na miki”.

“Dan Allah Aunty kada ki fadawa kowa”.

” Ai har Abban ki sai yaji”.

Kuka sosai take nan Aunty ta sassauto tace,,

“K’arfi ya nuna miki ne?”

Kuka ta sake fashewa da shi don bata da bakin cewa ita ta basa kanta don bai nuna mata k’arfi ba..

Aunty ko ganin haka sai ta ayyana a ranta k’arfi ya nunawa Hafsat sai tace,

“Ba Zan fadawa kowa ba amma yadda na gane haka kowa zai gane”.

” Ehh na yarda su gane da kan su”.

K’arfe 5 ‘yan Dubai suka iso gidan su Hafsat nan Aisha da Saudat suka shige d’aki Aunty Balkee Murja da Sis Faty sai Hafsat suka tarbe su Bayan sun gaisa an basu refreshments sai aka Fara shigo da kaya akwatin guda biyar set uku masu kyau pink,purple, sai milk colour sai kuma mai uku guda d’aya..

Albarka ake ta sawa nan ko aka shigar da wani irin wancan set uku da kuma mai uku guda d’aya.

Saudat da Aisha suna d’aki Saudat tace,

“Aisha muje mu lek’a guda nawa ne”.

” Saudat ina tsoron kada Maama ta Gan mu”.

“Dallah ta window ne ba mai ganin mu”.

Nan ko suka Fara lek’a.

Da yake a al’adar su Ana bud’ewa a wajen suka bud’e komai yayi kyau ba abunda babu nan aka ringa sa albarka Bayan sun gama sai suka bud’e na mai guda uku na iyaye da dangi ne sai Aunty Balkee tace,

” Abu yayi kyau zamu iya bud’e wancan? “

Tana nuna d’aya mai biyar set uku..

“Wancan ba namu bane na Abdool ne Wanda za’a Kaima Amaryar sa Lawal yace a bashi kuma komai da ke nan akwai a can”.

STORY CONTINUES BELOW

Godiya sosai suka musu nan suka tafi Hafsat kam gaba d’aya tana takure gudun kar a gano ta..

” Saudat ko rungume Aisha tayi tana fad’in,

“Congrats Aisha”.

” tnx “.

Tace a zuciyar ta ko cewa tayi Saudat kam bata da kunya ba irin Hafsat ba..

Ko da Abba ya dawo nuna masa akayi sai yace,

” Wallahi nima 2million Shamaki ya turo mini Wai gudumawa don Abdool ma d’an sa ne”.

Kowa murna nan Abdool ya Kira Aisha a waya yace tunda akwai mutani dayawa a gidan ta same sa a bangaren su suyi hira ba Wanda zai gane haka ko taje..

“Aisha saura kiris fa”.

Murmushi tayi tace,

” ikon Allah kenan”.

“Kayan sun miki?”

“Ehh Ai kowa Zan aura iya abunda za’a yi kenan”.

” to fad’a mini me kike so ayi a auren don ni bana son bidi’a”.

“Baby naji Saudat tace zata yi kamu so shi kadai zamu yi sai walima don na tabbata Abba ma ba zai Bari ayi bidi’a ba”.

” gaskiya ne kin San wani Abu?”

“A’ah sai ka fad’a”.

” Allah ranar bazan d’aga miki kafa ba”.

“Baby kai ne da maganar nan”.

” Ehh gwara Kice ma Hafsat ta miki shiri na musamman “.

Tsoro ne ya kamata sai ta mik’e tace,

” Bari na tafi kada a neme ni da wuri ta fice shi ko murmushi yayi..

Tana fita taga Aunty Balkee da wuri ta wuce..ko da ta shiga d’aki kuma Hafsat kadai ta tarar nan kunya ya kamata da Hafsat d’in ta fahimci haka sai ta bar mata d’akin nan tayi feeling comfortable..

Washe gari kuma Abdool yace ma Hafsat ta shirya suje taga gidan da Lawal ya basa Ai nan ta shirya don a can gidan bata zuwa yawo kullum tana gida..

Kan ta gama shiri Lawal ya Kira Abdool nan yake fad’a masa wani zai zo ya d’auke sa akwai abunda zai nuna masa ya amsa da to..

Bayan Hafsat ta gama shiri sai ta sallami kowa nan ko Wata Prado baka tayi parking a k’ofar gidan dama Abdool ya fad’a mata komai sai suka shiga basu tsaya ko ina ba sai wani anguwa mai kyau nan driver ya shigar da su wani katafaren gida Wanda gate d’in ma kadai abun kallo ne..

Abdool dai baki ya bud’e Amma Hafsat normal take gani don gidan su Hydar in bai fi wannan ba to sai dai suyi dai-dai..

Bayan sun shiga nan kallo ya sauya don tsaya tsara muku gidan ma bata lokaci ne Gashi yaji furniture’s masu kyau da tsada abun dai Masha Allah don Saudat ta gama samun gida..

“Hafsat gidan Saudat yayi kyau sosai”.

” Ehh wallahi ba k’aramin kud’i Lawal ya kashe ba”.

“Excuse me”.

Wanda ya kawo su yace
Juyawa Abdool yayi sai yace,

” gidan fa naka ne ba na wani ba”.

“Ban gane ba”

“Zai maka bayani”.

Nan aka had’a sa da Lawal a waya sai yace,

” Aboki na gidan naka ne ba na kowa ba Tun farko nayi niyar baka Amma nasan baza ka kar’ba ba,Abdool gaba d’aya frnds na suna abota da nine don kud’in Baba na Kaine mutum na farko da ka taimake ni sanda nake Neman taimako ba tare da kasan uba na ne ke sa haduwar mu ba nima haka kuma na tabbata koda ban San ka ba zaka iya taimako na don haka ka rike gidan ka ne Kai da Aisha na Saudat kuma na gefe don a Jere suke”.

STORY CONTINUES BELOW

“Lawal ban San da wani baki Zan maka godiya ba….”.

” Adana godiyar ka ran Daren farkon Ku Kayi ma Aisha “.

Murmushi yayi yana fad’in,

” yarinyar da tsoro na take ji”.

Lawal d’in ma dariya yayi sai Abdool yaga Hafsat na kallon sa sai ya had’a rai suka yi sallama ita ko cewa tayi,

“Kai yanzu kake dauki meye ban sani ba”😂🤭

Bayan sun fita sai suka shiga na Saudat komai iri d’aya colour ne ya raba nan suka yi ta snapping a waya suna komawa Hafsat tace,

” Aisha zo Kiga gidan ki”.

Nan ko Aisha tazo ta gani Saudat ko cewa tayi,

“Nawa fa”.

Hararar ta Hafsat tayi sannan ta nuna mata..

Hafsat na shiga d’aki Aisha ta bita ganin ba ta rike ta da wani Zuciya ba sai ta ringa bata hak’uri kan abunda ya faru tana kuka,

” don Allah Hafsat ki yafe mini Wallahi Tun ba yau ba nasan sharri aka miki Amma kunya ta Hana ni fuskantar ki”.

“Ba komai Aisha Amma kinyi Babban kuskure da Kika bar gidan Ku”.

” Mrs Hydar ke kan ki shaida ce gidan can ba abunda suke so sai kud’i kuma ni Abdool nake so”.

“Yanzu kina ganin zaki iya rayuwar da Abdool ke yi ne?”

“Ehh duk wuya duk rintsi ina tare da shi tunda shi nake so,a gani na ba abunda yafi haka dad’i ka auri Wanda kake so”.

” tabbas kinyi gaskiya Aisha “.

Sai kuma taji duk ba dad’i don ita bata San wani irin Aure suke ita da Hydar ba tunda har ya iya ciwa iyayen ta mutunci…

ganin yanayin ta ya sauya sai Aisha tace,

” Dan Allah be open to ya Hydar Wallahi zaki sha mamaki saboda bayi da matsala kuma I grantee you yana son ki pls ki basa dama ya nuna miki son da yake miki”.

“Aisha nifa Hydar baya gaba na matsala ta cikin da ke jiki na ya zanyi duk Randa ‘yan gidan Ku suka San da shi”.

” you mean kina da ciki?”

Kai ta d’aga mata da wuri ta rungume ta tana fad’in,

“Dole na Kira ya Hydar nayi congratulating nashi,but Hafsat kada ki Bari a San da cikin yanzu sai ya wuce zubarwa in ba haka ba Daddy da Umma ga munafukar nan Hakeela zasu cire”.

” Ehh for now banda ke da kuma Aunty Balkee ba Wanda ya sani”.

“Kina nufin ya Hydar ma bai sani ba?”

“Na Isa Ai don maita sanda ya gane”.

“To Allah raba lafiya”.

” Ameen amma Dan Allah ko Saudat kada ki fadawa”.

“But why?ya kamata ‘yan gidan Ku su sani”.

” Aisha ‘yan gidan Ku cirewa zasu yi gidan mu kuma ni za’a yanka musamman ya Abdool har banda na sai yayi”.

“Ohh Allah cikin da ya kamata ayi murna Amma boye sa ake wannan Kiyayyar bata yi ba”.

” Kinga bacci nake ji Zan shiga “.

” Dan Allah mu kwana a gadon ki tare”.

“Shikenan”.

Nan Hafsat ta kwanta Aisha ko chat take yi Saudat ma yanzu ta shigo tana call da Lawal ta kwanta sai Murja suka kwanta tare Sis Faty ce karshen shiga..

STORY CONTINUES BELOW

Aisha na cikin chart sai taga message na Hydar don sati biyu da suka wuce yace ta mishi list d’in abubuwan da take so zai saya mata kuma tayi ta tura masa shine ganin Aure saura sati d’aya sai ya tuntube ta..

Bud’e message d’in tayi nan yace ta turo account number ya tura mata kud’in furniture’s da komai sai a saya mata a nan take sanar da shi an mata komai har ta tura masa hoton gidan da yake Abdool ya tura mata ta WhatsApp da kuma hoton kayan auren ta nan yace,

” ina Abdool ya samu gida kamar haka da kayan auren nan?”

“Gida bashi aka yi”.

” Waye?”

“Ya Hydar ka tambayi Hafsat zata fad’a maka”.

Shiru yayi sai can yayi replying

” naga akwai furniture’s ko?”

“Ehh”.

” yanzu me kike da bukata?”

“Ya Hydar kayan da yake a Dubai aka had’a so gowns sun fi yawa kuma na fi son English wears so Zan saya sai kud’in kayan fitan biki”.

” Dubai fa?”

“Ehh nace ka tambayi Hafsat zata maka bayani”.

“Ohk yanzu Zan tura miki 3million sai ki raba ke da Kanwar Hafsat zai yi ko?”

“Ehh tanx”.

Shiru yayi sai can yace,

” ina Hafsat? “

“Tayi bacci Ai”.

Cikin rashin jin dad’i yace,

” tana cin abinci kuwa? “

“Ehh tana ci na manta congrats”.

” tnx ta fad’a ma ‘yan gidan su ne?”

“No tana tsoro call me vedio call Yanzu ayya”.

Calling nata yayi Bayan ta gaishe sa sai Tasa wayar a fuskar Hafsat nan take yaji jikin sa ya mutu bacci take peacefully nan ba kunya yace Aisha ta d’aga masa rigar ta haka ko tayi kallon shafeffen cikin ta yayi yace

“I miss the both of you”.

Sannan ya kashe wayar don ji yake kamar yayi tsunso yaje ya d’auko ta..

I am sorry Hafsat tabbas nayi kuskure Amma in sha Allah bazan Kara ba buri na ki yafe mini ni kuma na miki alkawarin nuna ma duniya son da nake miki ko da daddy zai kashe ni tunda Aisha ma ta iya fighting ma love nata”.

Wayar sa ya d’auka ya ringa kallon pics nata na auren Hakeela Wanda Aisha ta tura masa Tun a lokacin yana jin kewar ta..

‘Bangaren Saudat ma sunyi magana da Lawal ya kuma tura mata 2 millions su saya kayan fitar biki ita da Aisha..

So Washe gari Saudat ta fad’a ma Aisha nan ita ma tace Ai yayan ta ya tura mata sai suka fad’a ma Aunty Balkee nan tace zata roki Abba gobe suje Kaduna in yaso sai suyi sayayyar don Gombe ba zasu samu masu kyau sosai ba..

Da kyar Abba ya yarda ya kuma ce kada Sufi kwana biyu nan ko suka yi godiya sannan suka Fara shiri da Hafsat za’a je don Abuja suka so zuwa Amma Abba yace ba Wanda ya sani a can kuma ba zasu zauna a hotel ba don haka suje Kaduna tunda akwai Addar sa kuma dama zata zo auren sai su dawo tare..

Suna gama shiri Hydar ya Kira Aisha yace ta bama Hafsat waya Amma sai Hafsat taki kar’ba nan Aisha tace mishi zasu je Kaduna da Hafsat sayayya..

Aisha in ita kadai ce a d’akin sa a hands free sai ki bar mata d’akin “.

Haka ko Aisha tayi sai yace,

” Maman Baby har yau fushi ake da ni?”

Kallon wayar tayi Amma bata ce masa komai ba sai ya cigaba

STORY CONTINUES BELOW

“Naji zaku yi tafiya kije na baki izini but ki kula mini da kan ki da kuma abunda ke cikin ki”.

Kallon wayar kadai take yi don bata jin zata iya magana

” I love you bye tunda kin ki magana “.

Yana gama fad’ar haka ya katse kirar sai kawai taji hawaye da wuri ta share sannan ta d’auki wayar Aisha ta fito nan ko suka salami kowa suka kama hanya..

Basu Isa ba har dare amma da yake an San da zuwan su sai aka je aka d’auko su direct gida aka Kai su Bayan sunyi wanka sunci abinci sai suka ta’ba hira Hafsat kam bacci tayi daga nan suka kwanta..

Washe gari Tun safe suka shirya fita inda suka bar Aunty Balkee na bacci don gajiya ita da gajiyar zuwan ta bai fita ba an Kara mata wani..

Da yake Aisha ta iya driving sai ba’a had’a su da driver ba suka tafi don lawal ne ya zaba musu plaza da zasu je yana had’e da boutique..

Bayan sunyi parking sun shiga nan suka Fara sayayya Hafsat na ta ya su..

Bayan shigar su da kamar 50mins motar Aunty Maryam tayi parking a bakin plaza’n da yake mijin ta ya dawo Kaduna da zama kuma basu fi 2months da dawa ba..

Cikin Isa da kasaita ta shiga ta Fara shopping securities na plaza’n har uku suke bin ta a baya da yake ita customer ce na daban duk sati sai tazo kuma ta kan kashe fiye da 1.5 million duk zuwan ta..

Tana cikin zagaye kawai ta hangi Aisha gefen ta kuma Saudat ce cikin Isa ta nufe su tana Isa tace,

” shashasha wato mu zaki batawa gida suna dube ki da Yar matsiya ta kike yawo”.

Ita dai Aisha shiru tayi sai Saudat da ta girgiza kai nan Hafsat ko ta bullo rike da wani takalmin da ya mata kyau tana k’ok’arin nuna musu taga Aunty Maryam..

“Munafuka wato kin wargaza kan gidan mu hankalin ki ya kwanta ko?barauniya kin sati kud’in kani na kin kawo ta sayayya”.

Jin hayaniya ya Fara yawa sai securities suka zo da yake an san mijin ta Nada kud’i haka ma uban ta sai aka Fara korin su Hafsat a plaza’n Aisha ko da yake she is not notice me ba Wanda ya San ita yar Alhaji Munir ne..

Ko da suka zo fita sai manager’n yaga sunyi shopping sosai kuma ba zai iya loosing kud’in ba sai ya d’an sauki yace suje su biya kud’i..

Kayan suka bayar nan aka ce balance nasu 5million karab a kunnen Aunty Maryam sai tace,

” yau zanga yadda zasu yi su biya”.

Transfer Saudat tayi sai ji tayi sunce,

“Ya shigo”.

Ai bata ‘bata  lokaci ba ta shake Saudat tana fad’in,

” Wallahi yau sai kun fitar da sauran kud’in nan”.

“Ki sake ni”.

” bazan Sake ba”.

Da kyar aka sa Aunty Maryam ta sake Saudat sai aka ce su tafi Saudat tace baza ta tafi ba sai ta nuna mata matsayin ta ba hakurin da Hafsat bata bata ba taki nan ta Kira Lawal tace,

“Wato dama kasan wulakan ta mu za’a yi yasa kace muje wajen Gashi Harda korin mu ake”.

” sorry dear bama security d’aya wayar”.

Bama security tayi Amma sai yaki kar’ba nan ta nemi mai saukin kai ta basa sai kawai ya Fara cewa,

“Sorry Sir,yes sir Gashi nan”.

Sai ya Kaima manager da farko yaki kar’ba sanda security ya masa magana a kunne da wuri ya kar’ba yana fad’in,

” Sorry Sir yanzu na fito domin muyi tackling abun”.
Sai kuma yayi shiru da alama fad’a ake masa sai yace,

STORY CONTINUES BELOW

“Ohk Sir”.

Sannan ya bama Saudat waya nan ya dubi Aunty Maryam yace,

” madam zaki iya tafiya kuma daga yau kada ki Kara zuwa plaza’n nan”.

“Akan wad’an nan matsiya ta kake fad’a mini haka ka manta Waye uba na kuma Waye miji na,kullum ina sayan kaya fiya da million”.

” look madam  ki fita kafun muyi disgracing naki”.

Hanyar fita ta kama Saudat ko kujera ta zauna a kai tace,

“Next time ki tsaya iya matsayin ki malama”.

Ita dai fita tayi tana mamaki one phone call yasa aka Kore ta kuma Ai Saudat bata yi kama da yaran masu kud’i ba to Wa suka Kira..

A plaza’n kuma hak’uri aka bama su Saudat nan suka tafi…

Plaza dai na uban Lawal ne Wanda Bayan yaga Lawal yayi hankali sai ya mallaka masa duk wani business nasa da yake Nigeria..

Aunty Maryam ko tana komawa gida ta Kira Daddy tana tambayar sa plaza’n can nasa ne yace A’ah tace kuma bayi da hannun jari a bud’ewa yace ehh nan ta kashe don ita duk zaton ta Hydar ne yaci mata mutunci..

Su Hafsat kuma ba Wanda suka fad’a ma abunda ya faru  a Washe garin kuma suka be flight sai Nigeria don Lawal ya tura musu kud’i..

A ranar da suka koma suka bawa kowa tsarabar sa don Harda Maama da Aunty Balkee suka saya ma kayan fitar biki kuma a ranar ne aka Fara musu dilka da kuma gyare-gyare Aunty Balkee ta kan had’a da Hafsat tunda Hydar yabi hanyar sa Ai gwara a gyara ta kada ya raina ta ba tare da sanin Maama ba..

‘Bangaren Aisha da Abdool kuma Tun ranar da Aunty Balkee ta Gan ta  da Abdool aka sa musu ido haka zai zo ya gama kame kamen sa yayi gaba..

Yau ma zaune yake a bakin k’ofar shi da Aunty Balkee sai lek’a  d’akin yake ko zai hangi Aisha amma shiru sai yace,

” Aisha kam ta fita ne?”

Oho tashi ka bani waje “.

Nan ya tashi yana mita don wayar ma in sun jima kwace na Aisha Aunty Balkee take yi..

A gidan Daddy ko gata sosai Hakeela ke samu don Umma ji take kamar ta maida ta ciki..

Gobe ne kamu ga amare yanzu kam sunyi kyau sosai baran ma Aisha da take Fara haka ma Hafsat tayi kyau sosai sai dai duk tsiya bata zama kusa da Maama gudun kada ta gane abunda ke cikin ta kuma ko anyi abunda bata so haka zata daure taci…

Mai make up musamman aka kawo musu inda Saudat kam ko aiki aka sata tana makale da waya a kunnen ta suna waya da Lawal Maama ko duk sanda ta ganta sai tace,

” Saudat ba kin ce a baki lokaci ba har yau fa bamu ji amsar ki ba”.

Ita dai shiru kawai take yi..

Wanka suka yi inda suka zauna aka Fara musu make up wow💋 abun sai Wanda ya gani don totally kamannin su ya sauya nan suka fito da kayan su mai tsada kowa da colour’n nasa suka sa kowa sai yaba kyan su yake yi Gashi gidan ba laifi ya cika sosai..

Hafsat da yanzu ta fito wanka tana Neman kaya Aunty Balkee tace,

“Zo mana kema a miki”.

” A’ah Aunty ki bar sa kawai”.

Kusa da ita Aunty Balkee taje sannan ta rad’a mata

“Ke ki daina sakewa haka kowa zai gane ciki ne gare ki,ki ringa Abu kamar su Aisha”.

Yake tayi sannan ta zauna aka Fara mata nan take duk tafi su kyau kowa sai madallah yake fad’i Aisha zata mata Hoto tace,

” A’ah bar shi kawai don na San inda zaki kai”.

STORY CONTINUES BELOW

Dole Aisha ta hakura nan Hafsat Tasa kayan ta in ka ganta kace Wata budurwa ce ba matar Aure ba..

Da yake Abba is discipline ya Hana suyi a hotel don haka wani fili da ke Bayan gidan su aka yi decorating nashi sai ya zama kamar wani hotel da yake yaji kud’i so ba ‘bata lokaci aka Ringa tafiya wajen bikin amare kuma mota ce tazo ta d’auke su..

A gidan Daddy ko a social media suka ga invitation card na auren ta ko ina da shi ke Lawal na da shi nan Aunty Maryam ta Kira Aunty Zainab ta sanar mata sannan ta d’aura da abunda aka mata a plaza ta kuma fada mata kayan nawa suka saya nan ko suka shirya tsab tare da sa kayan da yafi na su Saudat tsada sannan suka zo gidan Daddy nan suka sanar ma Umma Amma sai cewa tayi,

“Ku barta taje duniya ce”.

Daga haka Asma’u, Fareeda, Khadija suka shirya suka bi su…

Ita Aisha kuma ta San komin yaya sai yan uwanta sunzo cin mutunci Amma har aka kusa tashi bata Gan su ba sai taji ba dad’i kenan ita ba Wanda yazo auren ta..

Kirar ta aka yi domin tayi rawa nan ta hau stage sai kawai ta hangi su suna zuwa Isar su keda wuya suka Fara Harbin ta da bandir na duba daya Aunty Zainab na fad’i,

” ba dai Aure bane kije zaki gani Wai ki rasa Wanda zaki aura sai talaka “.

” Aunty Zainab bar ta karshe a titi zata ke kwana “.

Cewar Khadija Aunty Balkee zata yi magana waje ya dau hayaniya saboda wasu kidnapper’s da suka shigo wajen nan kowa ya hargitse sai ihu da gudu ake yi  nan securities da ke wajen  wanda lawal yasa suka bud’e musu wuta haka a ka yi ta fama da kyar aka kama d’aya sauran kuma suka gudu Bayan an masa duka sai yace an turo su su kashe Saudat sannan suyi kidnapping Aisha.

Haka kamu ya kargitse su Aunty Balkee duk sun gudu gida Hydar na jin abunda ya faru ya Kira Aisha nan tace lafiyar ta kalau bata San shi problem nasa Hafsat bace sai tace ba abunda ya same ta ajiyar Zuciya ya sauke..

Washe gari a cikin gida suka yi walima nan ma sanda Lawal ya Kara securities don tsaro Wanda aka kama jiya kuma yana wajen su Ana investigating Wanda ya tura su..

Cikin kwanciyar hankali suka yi walimar su don yanzu kowa a tsorace yake..

Ran Jumma’a ko ita ce ranar daurin Aure Baban Murja ne waliyin Saudat Aisha ko sun rasa Wa zai zama waliyin ta suna zaune kawai aka yi parking venza jaa sannan aka bud’e k’ofar Hydar ne sanye cikin farar jumper Harda gare ga hular sa ba k’aramin kyau yayi ba Gashi sajen sa ya sha gyara sai ma yafi angwayen kyau..

Mika ma Abba hannu yayi Bayan sun gaisa sai yace,

“Zan zama waliyin Aisha”.

” nan ko aka basa sadakin ta  gudu Dari kamar yadda ya biya na Hafsat nan ko aka d’aura Aure..

Bayan an gama daurin Aure sai ya tsaya a jikin motar sa nan yaga Abdool sai hira da dariya suke shi da abokanaye sa nan ya nufe su duk hannu ya basu sannan yace,

“Ina son magana da kai”.

Kamar yadda shima Abdool ya masa ran daurin auren sa sai yayi banza da shi sanda Lawal ya Mi shi alama da kai kan cewa yaje nan suka kebe sai Hydar yace,

” Abdool abunda nayi ranar na San ba dai-dai bane don haka Kayi hak’uri”.

Mamaki ne ya kama Abdool d’in nan Hydar yaci gaba

“Ga amanar Aisha kuma na baka Dan Allah ka rike ta hannu biyu kamar yadda na rike maka kanwa”.

Duk zuciyar Abdool dai nace muku in an basa hak’uri shikenan sai yayi murmushi yace,

” ba komai ya wuce Aisha kuma in sha Allah Zan rike ta da Amana”.

“Na gode”.

Hydar ya fada yana murmushi don shi yanzu a shirye yake ya bama kowa hak’uri in har Hafsat zata yafe masa..

Ya juya zai tafi sai Abdool yace,

” ba zaka mini warning kada naje kusa da kanwar ka bane kamar yadda na maka ba?”

“Ni Ai ba irin ka bane na baka ita kyauta”.

” ka dai fad’i gaskiya”.

“Gaskiyar kenan”.

” to kaje nima na baka tawa kanwar”.

Murmushi kawai Hydar yayi yana girgiza kai nan suka yi hugging na juna sannan ya masa fatar alkhairi ya tafi direct wajen Abba ya nufa yana zuwa ya durkusa yana fad’in,

“Abba an Tashi lafiya”.

” lafiya kalau ya gidan naku?”

“Duk suna lafiya dama nazo ne na baka hak’uri kan abunda na aikata ranar”.

” kar kaji komai ni ban rike ka a rai ba jeka na yafe maka”.

“Na gode sosai Abba Maama fa?”

“Ka Kira Hafsat sai ta maka iso”.

Da wuri yace,

” na manta waya ta a gida “.

Da Hamma Naseer Abba ya had’a su don gidan da yake safiya ce ba mutani sosai sai suka nufi cikin gidan shigar sa ke da wuya kuma idon sa ya fada kan Hafsat tayi tagumi tana zaune a bakin k’ofa..

” meke damun Hafsat kuma?”

Ya tambayi kansa har zai nufe ta sai Naseer yace,

“Ga Maaman tazo”.

Durkusawa yayi ya gaishe ta nan ya fada mata abunda ya kawo sa sai tace ta yafe masa ya mata godiya Amma kab idon sa na kan Hafsat..

” muje ko?”

“Dan Allah ka mini magana da kanwar ka”.

Shiru kawai Hamma Naseer yayi sai kuma ya nufi wajen ta a kunne ya mata magana tana d’aga ido taga Hydar sai ta mik’e da wuri taja Vail a k’ofa sai ta nufe sa tana zuwa taja hannun sa sai d’akin su ya Abdool

” me kake yi a nan? “

Kallon ta yake gaba d’aya ta sauya tayi kyau da haske a cikin sati dayan nan.

“Ka tafi ko dai kazo ka sake ci ma iyaye na mutunci ne?”

Hugging nata yayi sai tayi ajiyar Zuciya bai yi breaking hug d’in ba yace,

“Auren Aisha nazo kuma na nemi gafarar kowa”.

Taji dad’i Amma sai bata nuna masa ba yace,

” tunanin me kike yi ko dai baki da lafiya ne?”

“Hydar cikin nan na bani wahala kuma dole na boye kada kowa ya sani”.

” ki Kara hak’uri yana Kara 2 month’s dai shikenan kuma Ai kin kusa komawa Kinga a can ba sai kin yi pretending lafiyar ki kalau ba”.

Shiru dai ta masa tana kwance a jikin sa sai yace,

“Ni Zan tafi kada Abba yazo ya same ni”.

Breaking hug d’in tayi sai ya kalle ta nan ko yasa bakin sa cikin nata ya Fara kissing ita ma Harda mayar masa martani don tunda aka gyara ta ita kadai ta San abunda take ji daurewa kawai take yi..

Suna cikin haka Lawal da Abdool suka sa kan su cikin d’akin ba ko sallama da wuri suka juya Lawal na cewa,

” sorry Dan Allah “.

Cikin jin kunya Hydar ya sake ta sannan ya mata alama da kai kan cewa ta tafi nan ta fita idon ta a k’asa..

Lawal da Abdool kuma ganin ya fita sai suka shigo Abdool na fad’in,

” Haba malam daga cewa na baka ko kunya babu a cikin gidan mu zaka Fara”.

Murmushi yayi yana mika ma Lawal hannu suka gaisa sannan yace,

“I will take your leave”.

Nan suka raka shi har mota ya tafi..

Da dare kuma aka kai amare gidan su..

Wannan na jiya ne Ku jira na yau zuwa dare in sha Allah zanyi.

Naga yadda kuka matsu jiya Wallahi nayi typing editing ne ya Hana ni tura muku jiya sorry.*°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

Page na yau sadaukarwa ne ga duk masoyin book nan na gode kwarai da soyayyar Ku a gare ni..

+
*SHAFI NA 43📑*
*__________*📖motoci dayawa suka zo daukan amare inda ko wanne kaso shiga kawai zaka yi tunda anguwan d’aya ce..motar amare ne kadai daban inda gudun kada Aisha tace ba’a mata adalci ba sai Aunty Balkee tabi na gidan Aisha da Hafsat sai kuma Gwaggo Saratu..

Saudat ko sister’s na Abba ne guda biyu sai Murja a haka aka nufi gidan amare..

Bayan an gama kallon ko ina sai Murja da kuma Zubaina ‘Yar Gwaggo Saratu suka nufi gidan Aisha tunda ita bata gayyaci frnds nata ba sai suka je domin kwana a gidan..

Hafsat, Murja, Zubaina su suka kwana a gidan Aisha sai wasu relatives da ba za’a rasa ba..

Washe gari kuma Umma ta Kira Aunty Maryam da Zainab domin suje har gidan Aisha su ci mata mutunci ko da suka zo sai Aunty Maryam tace,

“Umma kin San gidan ne?”

“Ehh Tun jiya nasa spy kuma yaga gidan da aka kaita domin yace duka amaren gidan su a Jere yake”.

Shi spy da Umma ta tura time da aka kawo Amarya yana ganin gidan da aka sa Aisha sanda ya tsorata amma bai fada ma Umma ba sai ya mata kwatance…

” ohk Umma Ai ko yanzu zamu je muci mutunci ta don ban manta da abunda suka mini a plaza ba”.

“Me suka miki?”

Nan ta kwashe labari ta bama Umma

“Ahh Wallahi kuje duk shegiyar da ta muku kallon banza kuci uwar ta”.

” Ai kuwa”.

Ita ma Umma kwatance ta musu nan Aunty Zainab taja motar ta Aunty Maryam kuma driver ke driving..

Suna Isa anguwar suka ga number’n gidan da Umma ta fada musu nan Aunty Zainab tace,

“Kinga gidan nan ba sa’an Abdool bane ina ji Mun bata”.

” no Zainab mayb a gidan ne don ba zai wuce a BQ aka ajiye ta ba muje mu gani kin San gidan biki baya ‘bata”.

Da wannan shawarar suka shiga gidan daga tsakiyar gidan suke kallo lallai duk Wanda ya Gina gidan nan ya cancanci a yaba masa..

Wata mata ce ta fito daga falon tana k’ok’arin fita nan suka tsaida ta suna mata kallon wulakanci tare da fad’in,

“Wajen Aisha muka zo mu sister’s nata ne”.

Kallon su tayi da kyau yadda suke ji da kan su tace,

” kuje tana ciki”.

Nufar k’ofar main falo suka yi nan suka ga takalmin mutani sai suka sa kai ba abunda suka Fara cin karo da shi sai Babban enlargement na Abdool da Aisha hakan ya tabbatar musu gidan Aisha ne..kallon furniture’s na falon suke lallai ba karya an kashe kud’i mutani kad’an ne a falon sai suka ce,

“Ina Aisha”.

Da kallon banza aka bi su kan aka ce,

“Tana sama”.

STORY CONTINUES BELOW

A hanyar su na hawa upstairs suka ci karo da hafsat da alama basu dad’e da gama breakfast ba don kwanuka take fitar Wa..

” sannun Ku da zuwa”.

Banza suka mata har da d’an ture ta kan suka ce,

“Aisha fa?”

“Tana sama d’aki na farko”.

Tana gama fad’ar haka ta sauka downstairs su kuma suka nufi d’akin sun ko yi sa’a Aisha ita kadai ce a d’akin nan Aunty Maryam tayi ma k’ofar key sannan ta shake Aisha tana fad’in,

“Shegiya wato kud’in Daddy Kika sata kuka Gina gidan nan ko?”

“Nifa ban sati kud’in kowa ba don da kud’in Daddy na sata da tuni ya gane”.

Kenan Abdool kidnapping yake yi har ya Tara kud’i haka to Allah ya Toni asirin Ku sai Mun sanar ma hukuma”.

‘Yan gidan biki kuma jin hayaniya sai suka hauro nan suka Fara buga k’ofa suna fad’in,

” a sake mana Amaryar mu”.

Jin yadda suke buga k’ofar sai suka bud’e tare da fuskantar yan bikin suna fad’in,

“Wallahi sai Mun tona ma Abdool asiri tunda kidnapper ya zama”.

Abun ka da talakawa sai suka fashe da dariya suna nuna su da hannu su ko da yake masu kud’i ne basu San tsiyar nan ba haka suka ringa holo suna musu dariya ganin an manna musu hauka sai suka tafi..

‘Bangaren gidan Saudat ko relatives na Lawal gidan su Hafsat suka nufa inda suka sake sanar da Maama cewa da Amaryar su zasu tafi duk da tasan da haka don Lawal saura masa sati biyu yayi passing out na bautar kasar sa..

” yanzu su Wa zasu mata rakiya”.

“Ina ji Aunty’n ta d’aya da gwaggon ta sai Hafsat”.

” to Abu yayi kyau, suzo su bata passport nasu mu nema musu Visa don already Amarya kam an mata”.

Kiran Aunty Balkee da Hafsat aka yi a waya nan suka dawo gidan, Aunty Balkee ta bada passport nata sannan aka ce Hafsat ta tambayi Hydar first..

“Aunty ya ‘batar mini da waya fa”.

Mika mata waya aka yi sai tace,

” nasan ba zai hanaba mu tafi kawai”.

“No Hafsat sai kin tambaye sa”.

Kame-kame ta Fara yi nan Aunty Balkee ta tuna kila tsoron sa take ji tunda ga yadda suka yi auren sai tace,

” ki hakura da zuwan kawai kawo mana na Faty”.

Dama ita zuwan bai wani shiga ranta ba sai bata damu ba nan ko suka bada visa’n su..

Su Aunty Maryam na komawa gida Umma tace,

“Kunci mutuncin su ko?”

“Su dai suka ci mutuncin mu”.

” yanzu duk kud’in uban Ku har akwai Wanda ya Isa ya ci muku mutunci? “

“Umma muna ganin Abdool nan ko yankan kai ko kidnapping yake yi?”

“Mi ye?”

Nan suka fada mata yadda gidan yake sai tace,

“D’azun spy da na sa ya Kira ni Wai dayan Amaryar Dubai za’a kai ta”.

Shiru Aunty Maryam tayi sai can tace,

” wannan kanwar Hafsat mai kud’i zata aura ba shakka tunda har aka iya disgracing nawa a plaza ina ji shi yayi ma Abdool gidan can fa”.

“Yah maganar ki zai iya zama gaskiya don ba yadda za’a yi uban sa na gida ko oho shi kuma ya Gina mai kyau”.

STORY CONTINUES BELOW

Safa da marwa Umma ta Fara a falon a zuciyar ta  tace,

” Zulai baki ga ta zama ba lokaci yayi da zaki bayyana wannan Kiyayyar saboda shi kan sa Alhaji Munir amfani da shi kike”.

Shiru tayi can tace,

“Kenan sama da shekara 25 aikin da Kika yi ya zama a banza lokaci d’aya Allah ya tura Wanda zai taimake su ya d’aga su?Ba dai Alhaji Shamaki bane”.

Haka ta ringa ayyana abubuwa a ranta..

**

K’arfe 4, su Saudat suka bar Nigeria inda gidan Aisha ko Ana shirin tafiya budan kai..sosai aka yi ma Aisha kwalliya tayi kyau nan aka nufi gidan Abba da ita..

” Maama dubu hamsin ta bayar sai Aunty Balkee da ta ajiye dubu ashirin na budan kai sauran dangi kuma suka had’a dubu salatin duka-duka kud’in sun tashi hundred thousands Hafsat ta bud’e kai tunda Saudat ta tafi..

Bayan gama budan kai sai Abdool ya Kira Hafsat ta wayar Maama tana picking yace,

“Kada Wanda yabi Aisha gidan ta tunda duk jiya anga gida ke kadai ce na yarda ki mata rakiya”.

Kan tace wani Abu ma ya katse wayar nan ta Fara mamakin dokin da yake me yasa ita Hydar bai yi wannan dokin a  kanta ba Tun farkon auren su da kanta tace,

” saboda ba auren soyayya bane “.

Nan ta samu Maama ta fada mata abunda Abdool yace daga haka mota tazo ta d’auke  su suna Isa gidan direct bedroom suka nufa don already magrib yayi nan suka yi sallah sai Hafsat ta Lura yanayin Aisha ya sauya sai tace,

” ya dai Mrs Abdool? “

Da wuri ta shige jikin Hafsat tana fad’in,

“Wallahi tsoro nake ji ance fa da Zafi”.

Shiru Hafsat tayi sai can tace,

” karya ne”.

Breaking hug d’in tayi tana fad’in,

“Wallahi bada gaske bane nifa daga yadda Aunty Balkee ke mana nasiha nida Saudat na gane in Abdool ya kamani tawa ta kare”.

” ka ji ki”.

“Nifa Wallahi kunyar kin nan bana so ki fada mini gaskiya tunda ga ciki a jikin ki”.

Kama hannun Aisha tayi tace,

” kawai ki basa had’in kai if not zaki wahala “.

Haba Aisha kan sai hawaye har dariya ta bama Hafsat da kyar ta lallashe ta suna i’sha Abdool ya shigo ba kunya kuma tayi hugging nashi a gaban Hafsat sai Hafsat ta mik’e tace,

” ni Zan koma”.

“Naseer na waje zai maida ki don dare yayi”.

Sai da safe ta musu sannan ta fita…

Tana fita Abdool yace,

” finally kin zama mata ta kuma nayi alkawarin ba d’aga kafa don haka zo muje muyi alwala..

Toilet suka shiga inda suka yi alwala suna fitowa kuma sai sallah  Bayan sun idar kuma sai ya mata tambayoyi nan ta amsa masa daga haka ya nufi falo..

Kan ya dawo ma har Tasa sleeping dress yana shigowa ya ajiye ledar sa da kuma plates sai ya zauna a k’asa yace,

“Zo mu ci”.

Banza ta masa kamar bata ji sa ba sai yace,

” duk yadda Kika yi baza ki tsira ba don ni yau d’in nan sai na samama Abba na jika”.

Nan ma ko inda yake bata kalla ba sai ya mik’e ya nufe ta tare da kai hannu zai ta’ba ta da wuri ta mik’e tana fad’in,

“Kada ka yarda ka ta’ba ni Abdool”.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi yayi gami da kai hannu a karo na biyu zai ta’ba ta nan ta Fara ihu tare da fashe-fashe komai da ta samu zata jefe sa da shi ga idanun ta sun koma jaa har ta Fara bashi tsoro don shi farko ya zata bata son ya kusance ta ne amma yanzu abun yafi gaban haka.
” Baby tunda baki so ba Zan miki ba”.

Amma ko jin sa bata yi ba sai fashe-fashe take tana fad’in,

“Na tsane ka Abdool ka fita ka bani wuri”.

Sosai ya tausaya mata nan ya bar d’akin Amma duk da haka yana jin ihun ta..

” to meke damun Aisha ne?”

A haka suka kwana duk basu yi bacci ba asuban fari ya shigo d’akin nan yaga tana bacci a kasa wardrobe ya bud’e ya d’auki hijab nata gami da sa mata ya d’auke ta a hannun sa suka nufi gidan Abba suna Isa suka tarar da Maama ta idar da sallah..

“Abdool lafiya na Gan Ku war haka?”

A dai-dai lokacin Aisha ta farka..

“Maama Wallahi jiya Mun kwana ba mu yi bacci ba sai fashe-fashe take yi tana cewa ta tsane ni”.

” innalillah me ke faruwa? “

“Wallahi ban sani ba shiyasa ma na kawo ta gida”.

Kallon Aisha Maama tayi idon ta duk bacci sai tace,

” je d’aki ki kwanta “.

Mik’ewa tayi ta nufi d’akin su, Abdool kuma tagumi yayi nan Maama tace,

” Bari ta tashi muga yadda Allah zai yi”.

“To Bari na koma gida kan ta tashi”.

” to sai ka juyo”.

Komawa gida yayi zuciyar sa cike da damuwa to meyasa Aisha take cewa ta tsane sa da ya matso kusa da ita..

Hafsat na tashiwa taga Aisha na bacci a gadon su Sis Faty nan mamaki ya kamata da wuri ta fito waje tace,

“Maama me ya kawo Aisha kuma?”

Don ita a zaton ta Abdool ya mata jina-jina ne ya kawo ta gida duk da ta San cewa in hakan ne ma ba zai iya kawo ta gida ba don kunya shiyasa ta tambaya..

“Wallahi Wai jiya sun kwana basu yi bacci ba”.

Nan Maama ta fada mata duk abunda Abdool yace

” na shiga uku mai ya samu ‘Yar mutani? “

“Sai Allah fa”.
Aisha bata tashi ba sai 8am tana tashiwa ta kalli gidan da kyau nan Hafsat tace,

” Maama ta tashi”.

Da wuri Maama da sauran ‘yan gidan biki da basu wuce 4 ba suka shiga d’akin nan Maama tace,

“Sannu Aisha”.

Da kai ta amsa sai ta kalli Hafsat tace,

” Wa kuma ya kawo ni gidan nan?”

Duk kallon juna suka yi sai Hafsat tace,

“Kina nufin baki San kinzo gidan nan ba?”

“Ehh ni dai nasan ina gida….”

Sai kunyar Maama ya hanata karasawa sai tace,

“ina Abdool na ko dai wani Abu ya same sa ne?”

“Shh lafiyar sa kalau Aisha kwantar da hankalin ki”.

” to ki kira mini shi mu koma gida”.

“A’ah Aisha ki karya tukun”.

Cewar Maama.

STORY CONTINUES BELOW

” Maama shi fa zanje na masa girki”.

“Aisha ki ci Zan Kira miki yaa Abdool d’in”.

To tace sannan aka kawo mata abinci taci nan kowa ke mamakin lamarin, Abdool na zuwa aka ce tana d’aki.

Shiga d’akin yayi tana kwance ta gansa da wuri ta sauka a kan gado ta nufe sa tare da fadiwa jikin sa tayi hugging nasa har da kai masa kiss a cheeks nasa shi dai mamaki kawai yake.

Breaking hug d’in yayi yana fad’in,

” ya kike”

Tare da shafa fuskar ta.

“Lafiya ta kalau shine ka kawo ni gidan Abba kai da kace ba d’aga kafa”.

Ta fada tana kwanciya a jikin sa

” ba ke bace Kika ki”.

“Ni kuma?”

Ta tambaya don ita inda ya fita falo iya wajen take iya tunawa bata San abunda ya faru Bayan nan ba.

“Ehh mana ke”.

” Baby nifa tunda ka fita falon daga nan ba Zan iya tuna komai ba sai yanzu da na ganni a gidan Abba “.

Sosai yayi mamakin furucin ta nan yace,

” to ki kwanta ina zuwa”.

“A’ah nikam mu tafi gidan mu”.

” to tsaya Bari na fada ma Maama”.

Kwanciya tayi shi ko ya fita nan yake sanar da Maama abunda yace ita ma tace haka tace musu sai kanta ya kulle kowa ya rasa meke damun ta nan Maama tace,

“Hafsat shirya ki raka su”.

Da to ta amsa sannan ta sa Hijab tare da kama hannun Aisha sai Aisha tace,

” ina zamu je?”

“Gidan ki ya Abdool na jiran mu a waje”.

Da wuri ta sauka sannan ta sallami su Maama suka nemi taxi sai hanyar gidan tana makale a jikin Abdool suna Isa taga gidan sai tace,

” nifa Ku maida ni gidan mu bazan shiga gidan nan ba”.

Rike ta Abdool yayi yana fad’in,

“Baby gidan mu ne fa”.

Ture sa tayi tana fad’in,

” na tsane ka kada ka Kara ta’ba ni nan ta Fara jefan sa da duk abunda ta samu tana ihu Harda buga kanta a gini da kyar Hafsat ta rike ta nan  suka Kira taxi aka shigar da ita sai gidan Abba..

Suna shiga gidan ta dawo hayyacin ta sai tace,

“Hafsat Tun d’azun fa nace a maida ni Amma Kika ki”.

Cike da mamaki Hafsat tace,

” na maida ki Kika ringa hauka kina cewa kin tsani ya Abdool “.

” Wallahi karya ne baki maida ni ba kuma ina son Abdool nikam ki maida ni”.

Kallon juna suke don yanzu lamarin Aisha abun tsoro ne sai Maama tace,

“Kina son komawa?”

“Ehh Maama nasan yana jira na”.

” Hafsat kuje da Gwaggo Saratu Ku kaita “.

Cike da murna tace,

” yauwa Maama na gode”.

Nan ko aka sake kaita suna Isa kuma ta Fara hauka Harda duka nan suka maido ta kamar d’azun tana shiga hankalin ta ya dawo jikin ta sai tace,

“Hafsat mu tafi mana”.

STORY CONTINUES BELOW

Shiru Hafsat ta mata don Abba yaje Neman malami ba jimawa kuwa suka shigo nan malamin ya dube ta yace aljani ke damun ta sai tace,

” Wallahi sharri ne banda komai nikam “.

Sallama malamin ya musu ya tafi sai Hafsat tace,

” Aisha sau uku aka kai ki kina cewa ba za ki zauna ba”.

“Wallahi duk karya kuke yanzu na gane wato dama ba so na kuke yi ba,banda nima taya zanyi tunanin makiyan uba na zasu so ni”.

Tana fada tana kuka Amma dukkan su ba Wanda ya damu don gani suke aljanun ne..

D’aki ta shiga da gudu tana kuka

” ni Aisha na tabka Babban kuskure a rayuwa na na bijirewa iyaye na saboda saurayi, tabbas alhakin iyaye na ke bina saboda da nace a maida ni gida na sai su batar mini da hankali suce Wai an kai ni naki zama dole na koma na nemi gafarar iyaye na Amma ta yaya?”

Kuka sosai take Bayan ta gama ta fito zata yi alwala sai Murja tace,

“Aisha zaki koma ne?”

Ita a ganin ta gaste suke mata sai tayi banza da su can tace,

“Ai dama nasan karshe na kuke son gani to Ku kashe ni ku huta don tunda uwa ta ta haife ni ban ta’ba aljanu ba”.

Daga haka ta shiga d’aki shigar ta ke da wuya Abdool ya shigo sai Gwaggo Saratu tace,

” dama ance kafun mutum yayi Aure yasan asalin yarinya, mutum da iyayen ta ma suka Kore ta Ai kasan da can bata da hankali yanzu da ‘Yar talakawa ko auren dangi Kayi ina zaka fuskan ci wannan matsalar yarinya ta haukacewa mutani “.

Kalaman ta sosai suka yi ma Abdool da Aisha Zafi don ita irin mutanin da zasu fad’i duk abunda yazo bakin su ne ba tare da sun yi tunanin yadda zaka ji ba..

‘Yar ta ce ta d’aura da

” Ai mahaukaciya ya auro “.

Dama Zubaina da ka ganta kaga Mara kunya Abdool dai d’akin da Aisha take ya wuce yana shiga ya ganta sai kuka take da wuri ya d’aga ta yasa ta a jikin sa sai tace,

” Abdool yanzu na gane ‘yan uwan ka basu so na so suke su kashe ni su huta ni ka maida ni gidan mu”.

“Aisha kowa na son ki”.

” A’ah kai kadai kake so na”.

Tana gama fad’ar haka ta sake cigaba da kuka nan ya d’ago ta sai yasa bakin sa cikin nata yana kissing ita ko rike harshen sa tayi tana tsotsa hannun ta kuma na shafa fuskar sa ganin ta Fara sauya masa yanayi sai ya zame bakin sa ita kuma da wuri ta fada jikin sa nan ya gane tana da bukatar sa sai ya zaunar da ita yace,

“I am sorry Baby nan gidan Abba ne kuma fa akwai baki I just can’t”.

Kukan ta sake farawa nan yace in bata Bari ba zai tafi da wuri tayi shiru tare da kwanciya a jikin sa har bacci ya d’auke ta.. Ajiyar Zuciya yayi sannan ya kwantar da ita a gefe ya fita yana fad’in,

” Maama tayi bacci Zan fita kan ta tashi “.

” a dawo lafiya “.

Fita yayi Hafsat ko dukkan su tausayin su take..

Can Bayan Aisha ta tashi sai Wata neighbor’n su Maama wacce bata nan aka yi auren ta shigo sai taga Aisha ta tambaya wace ce aka ce matar Abdool nan Maama ta fada mata abunda ke tafiya sai tace akwai wani malamin da ta sani sai suje..

Shiryawa suka yi nan suka nufi wajen sai yana kallon Aisha yace aljanu ne nan yayi ta karance-karancen sa da rubutu sai Aisha ta suma sai yace,

” matsalar aljanu ne kuma had’a ta da su aka yi”.

STORY CONTINUES BELOW

“Malam waya had’a ta da su?”

“Sunan ta Saratu tana da ‘ya Zubaina kuma burin su Abdool ya auri Zubaina don son da take mishi ganin hakan bai samu ba sai suka had’a ta da aljani Wanda da zaran taga gidan ta da mijin ta zata ji ta tsane su ta ringa hauka”.

” to yanzu malam ba yadda za’a yi a magance matsalar? “

“Akwai Zan had’a muku magani zata ke sha na sati d’aya kuma cikin satin kada kaga mijin ta kuma kar taje gidan”.

Godiya sosai suka masa nan ya wasa ma Aisha ruwa ta farfad’o sai ya basu magani suka biya sai gida..

Suna Isa gida kuma Gwaggo Saratu daga kallon da ake mata tasan an gane komai Abba na dawa aka fada masa nan yace,

” Aure ya kare kowa ya tattara ya bar masa gida”.

Dama Gwaggo Saratu ‘yan uba ne da Abba kuma Zubaina ta dad’e tana son Abdool cikin rashin nasara suka bar gidan daga baya sauran ma suka tafi cikin kuka Aisha tace,

“D’an Allah Maama Abba kuyi hak’uri na fada muku duk abunda yazo baki na”.

” ba komai Aisha Ai baki cikin hankalin ki ne”.

“Abba alhakin iyaye nane ke bina kuma na tabbata ba zai daina bi na ba”.

” Aisha kinyi Babban kuskure da Kika bijirewa iyayen ki Tun wuri ki nemi gafara”.

“In sha Allah Abba”.

**

‘Yan Dubai kuma basu Isa ba har 7 na dare direct gidan Saudat aka ajiye ta inda nan da sati zasu dawo da Lawal d’in, su Aunty Balkee kuma suka nufi gidan Baban Lawal..

Saudat na zaune a kan gado zuciyar ta sai bugawa yake nan Lawal ya shigo da kananan kaya a jikin sa da alama yayi wanka ma,zama yayi a bakin gadon yana hade da rai Saudat ko cewa tayi,

” sannu da shigowa “.

” yauwa blacky je ki yi alwala kizo”

Ganin yadda ya had’a rai sai ta wuce toilet tayi alwala ta fito nan suka tada sallah Bayan sun idar yayi mata tambayoyi ta amsa sai ya d’auko kaza a fridge ya bata nan suka ci tare ita dai had’a rai da yayi yana bata tsoro shi ko yayi hakan ne don kada ta masa gardama..

Yana gamawa ya hau gado Bayan ta gama sai yace,

“Zo ki kwanta”.

Ba musu ta hau bed d’in d’an nesa da shi ta kwanta nan ya janyo ta jikin sa a hankali ya jefa bakin sa cikin nata ya Fara kissing daga haka ya zarce da shafa jikin ta cikin rad’a yace,

” kada ki ji tsoro na miki alkawarin a hankali Zan biki”.

Daga haka yayi addu’ar saduwa da iyali sai…..🤐..

Kamar yadda yayi alkawari kuma hakan ce ta kasance a hankali ya bita yana gamawa ya mata wanka nan suka koma bacci..
Su Aunty Balkee ma sun samu tarba me kyau don Baban Lawal a halin yanzu bayi da mata shi da sister’n Lawal ne a gidan don Allah ya ma mijin ta rasuwa kuma sunyi insisting sai su Aunty Balkee sun yi sati..

**

Hafsat tunda Abban Ku yace kowa ya bar masa gida had’a kayan ki ki koma”.

“Maama Zan ke kula da Aisha”.

” je ki kawai ni da Murja zamu kula da ita”.

To tace gami da mik’ewa tayi d’aki nan ta Fara had’a kayan ta sai ga Aisha ta shiga d’akin, zama tayi a bakin gado sai taji tana cewa,

“Lafiya kalau ya Hydar sai yau ka tuna da ni?”

Jin sunan sa sai taji gaban ta ya fad’i

“A’ ah Aisha aiki ne ya mini yawa”.

STORY CONTINUES BELOW

” ya kake ya kowa da kowa?”

“Kowa lafiya hope dai ba matsala?”

“Wallahi ba matsalar komai”.

” great Hafsat kam ba za ta dawo bane?”

Gata ka tambaye ta”.

Aisha na mika mata phone sai taki kar’ba sai kawai tace,

“Ashe ta fita ban sani ba”.

Tsarai ya gane Hafsat taki karban Wayan ne don haka sai suka yi sallama..

Shifa kewar ta yake sosai kuma ya rasa yadda zai yi wani Zuciya yace yaje ya d’auko ta amma yana jin kunya don haka duk ya canza..

Safa da marwa yake a falon ya rasa yadda zai bullowa lamarin daga bisani ya zauna sai tunani yake har bacci ya d’auke sa..
Hafsat ko tana gama shiri tayi hugging Aisha tana fad’in,

” Allah Kara sauki”.

Sannan tayi hugging na Murja tana fad’in,

“Sai kinzo gida na”.

Daga haka ta sallami Maama Murja ta raka ta shiga taxi sai gidan ta..

Tana sauka a k’ofar gate man ya mata sannu da dawa cikin sakin fuska ta gaishe sa daga nan ta nufi bangaren Baaba Ladi..

” ahh su Hafsat sai yau tafiya ko sallama babu”.

“Baaba kan na tafi nayi ta Neman ki ban Gan ki ba”.

” Au haka na fita ne ya gajiyar biki?”

“Gajiya ya bi jiki”.

” ya mutumiyar ki Amarya?”

“Tana lafiya tace a gaishe Ku”.

” to muna amsawa”.

Bama Babba cim-cim tayi sannan tace,

“Bari na Isa”.

” to na gode sosai”.

Apartment nata ta nufa kan ta Isa ta gamu da Umma ta fito daga apartment na Hakeela sai tace,

“An wuni lafiya Umma?”

Kallon banza ta mata gami da Jan tsaki ita kuma sai ta wuce apartment nata..

Tura k’ofar tayi a hankali gami da maidawa ta rufe sai ta Fara Jan trolley’n ta nan taga Hydar a falo yana kwance bacci ma yake a zaune..

Ajiye trolley’n tayi sannan ta nufi wajen sa a hankali ta dafa sa a kafad’ar shi har ya tsorata yana bud’e idanun sa da suka yi jaa don bacci ya kalle ta tana masa murmushi da wuri ya mik’e idon sa duk bacci yace,

“Baby na ke ce?”

“Ehh”

Ta fada tana murmushi da wuri yayi hugging nata yana kai mata kiss ta ko ina..

“Baby nayi missing naki fa”.

Ya fada a shogwabe ita dai dariya ma ya bata nan ita ma tayi hugging nasa tana fad’in,

” miss you too”.

Daga haka sai tace,

“Lafiya kake gida yanzu ya baka je office ba”.

” nifa ko naje ba abunda nake iya yi don missing naki ya unborn child na?”

Hannun sa ta d’aura a cikin ta tana fad’in,

“Lafiyar ta kalau”.

” lafiyar sa dai”.

“Tho Allah kawo mai albarka”.

STORY CONTINUES BELOW

” Ameen ya gajiyar biki?”

“Lafiya kalau jikin ka da dumi fa”.

” kai na ke ciwo”.

“To koma bacci zai daina”.

” Ai tunda kin dawo na fasa baccin “.

Jin jikin ta yayi laushi Gashi tayi haske sai kamshi take sai ya Fara shafa ta da wuri tace,

” Bari na watsa ruwa na gaji”.

Ta San in ta bar sa gangara zai yi sai yace,

“Ya kamata kam”.

Sannan ta d’auki trolley’n ta ta shigar ciki ko ina tsab kuma ta tabbata Baaba Ladi ke gyarawa..

Bayan ta shiga sai tayi wanka nan Tasa gown Mara nauyi ta fito falon kan ta da hula kitchen ta nufa kallon ta yayi yana fad’in,

” ina zuwa kuma princess na?”

“Kitchen zanyi girki”.

” Ai na sauke miki girki a gidan nan zo ki huta”.

“A’ah nikam girki na nake son ci”.

” really? “

Ya tambaya yana kashe mata ido d’aya gami da mik’ewa ya nufe ta yana Isa yasa hannun sa a kugunta tare da janyo ta ya manna ta da jikin sa a hankali ya kama kunnen ta da lips nasa masu sanyi yarr taji a jikin ta nan ko ya Fara shinshina ta da wuri ta ja jikin ta gami da murmushi tace,

“Ka jira zuwa dare Zan baka tsarabar ka”.

Janta jikin sa yayi gami da shafa keyan sa yace,

” ina jira”.

Nan ko duk suka fashe da dariya..ita ma kashe masa ido d’aya tayi gami da ture sa da dukka hannun ta biyu ta nufi kitchen d’in tana murmushi shi ko Bayan ta yabi da kallo yana fad’in
“Allah kaimu dare”.

Daga nan ya koma falon inda yake kallon channel na ball Amma hankalin sa duk na kan Hafsat dake kitchen ita ma in tayi aiki kad’an sai ta lek’o nan ko zai yi murmushi a haka har ta dafa indomie ta fito rike da shi a hannu ta.

” zo ki ji”.

Nufar sa tayi inda ta zauna a cinyar sa shi ko ya ajiye plate d’in a gefe yana feeding nata har ta koshi sannan ta sauke ajiyar Zuciya gami da kallon sa tace,

“Ya jikin Ammie”.

Shima ajiyar Zuciya yayi sannan yace,

” da sauki “.

Nan yace zai tafi masallaci domin gabatar da sallar Asr ita kuma tace zata je cikin gida Ashe ma bai jita ba nan ya mata blowing kiss ya fita..

Sallar Asr tayi sannan Tasa hijab Babba gudun kada a fahimci tana da ciki nan ta nufi cikin gidan ba kowa a falo sai ta d’an kalli falon ba abunda ya sauya ta juya zata fita kenan sai ta tuna da Ammie don haka ta nufi upstairs sai d’akin Ammie a hankali ta tura k’ofar d’akin gami da shiga Ammie na bacci..

” Allah dai ya baki lafiya Ammie “.

Ta Fada gami da d’an matse mata kafa sannan ta fita..

A hanyar sauka suka ci karo da Umma nan ta mata kallon kaskanci ita Hafsat d’in ko a jikin ta har tayi nisa Umma tace,

” dakata”.

Cak ta tsaya.

“Daga yau an dawar dake girki a gidan nan tunda ke juya ce Hakeela na fama da abunda ke cikin ta don haka ko tsinkiye baza ta sake d’agawa ba”.

” naji”.

Hafsat ta fada ba tare da ta kalle ta ba ta sauka sai apartment nata..

Zama tayi gami da tagumi don ta San ba zata iya jure aikin gidan dukka ba don abunda ke cikin ta ita ma yana da bukatar tattali..

STORY CONTINUES BELOW

Hydar ko bai dawo ba har aka yi magrib nan tayi sallah tana jin kewar ‘yan gidan su yanzu da tana da waya dai da ta Kira Saudat taji yadda take..

Ana kiran i’sha tayi wanka gami da sallah nan ta tsaya a mirror ta kalli kanta tabbas ta sauya cikin ta ta shafa tana jin farin ciki a zuciyar ta nan ta shafa mai da Aunty Balkee ta bata gami da cire wani crazy sleeping dress saboda shi da babu duk daya ne fari tas,under wears ta sa sannan Tasa sleeping dress d’in gami da d’aura igiyar sa sannan ta taje kanta ta sake gashin ta a baya sai wani simple shoe da ta Saka nan ta nufi falo,tana fita Hydar na shiga poster yayi yana kallon ta ita kuma sai ta sauya tafiya zuwa ga na Jan hankali da kuma rigima..

Ai yana ganin haka ya rike kahon zuciyar sa don ji yake yana bugawa da k’arfi a hankali ya Fara nufo ta ba tare da ya San inda yake zuwa ba ita kuma bata fasa tafiyar ta ba..

Yana Isa gare ta ya riko hannun ta yana kallon ta daga yatsun kafar ta har tsakiyar kan ta.

“Baby duk wannan wankan ni Kika yi ma?”

“Baka ga komai ba ma”.

Ta fada tana nufar dining gami da cewa,

” Kayi wanka sai kazo kaci abinci “.

” wanka kawai zanyi abinci kam banda appetite na ci”.

“Allah ko?”

Ta tambaya tana zare ido..

“Ya ilaheey”.

Ya fada sannan ya nufi tiolet har ta gama cin abinci bai fito  ba kashe komai na d’akin tayi gami da nufar bedroom direct d’akin ta ta nufa nan ta feshe jikin ta da tulare dayawa sannan ta nufi bedroom nasa tana shiga tayi ma k’ofar key dai-dai time d’in ya fito daga tiolet d’aure da towel..

Hannun sa ta rike gami da zaunar da shi a bakin bed nasa nan ta shafa masa mai cikin salon yaudara sannan ta zauna a cinyar sa tace,

” sai bacci ko?”

“Ai baki Isa ba sai na gaisa da Baby na tunda Kika mini alkawari”.

” shhh”.

Tace gami da d’aura yatsar sa a lips d’in ta a hankali ta ture sa ya kwanta nan ta kwanta a gefen sa tana sauke ajiyar Zuciya..

Juyowa gare ta yayi gami da janyo ta jikin sa yana fad’in,

“Nayi missing naki fa”.

” I am all yours”.

Ta fada tana shafa sajen sa nan ko bai yi kasa a gwiwa ba ya Fara aika mata da sakonni ita ma sai ta Fara mayar masa nan ko suka rikice ma juna a haka har suka biya bukatar su..

Bayan sunyi wanka Hafsat na kwance a jikin sa yace,

“Baby yau fa daban da kullum naji”.

” aikin Aunty Balkee ita ta gyara ni”.

“To Wallahi ko nawa ne Zan ke biya kullum kije gyara kuma Aunty’n nan taki tana da kyauta na musamman”.

” so kake su kashe ni ko don ita a zaton ta fyade ka mini”.

Dariya duk suke yi can yace,

“Gani mayen mata ko?”

“Waya sani”.

Ta fada tana Jan karan hanchin sa shi ko shafa cikin ta yayi yana fadin,

” nan da wasu month’s Zan samu me ce mini Dad”.

“In sha Allah yauwa ka tuna lokacin da muke gidan can kace zaka nemo silar Kiyayyar nan?”

“Ban manta ba kuma na bincika sai dai kash mutum d’aya ce zata iya fada saboda ita ce ta San mafarin sa”.

STORY CONTINUES BELOW

” wace ce?”

“Ammie”.

Kuma a halin yanzu tana kwance”.

” Allah dai ya bata Lafiya “.

Ameen yace sannan suka koma bacci suna makale ma juna..
Washe gari kuma Bayan sun yi sallah sai Hydar ya koma bacci don yau kam ya samu bacci mai dad’i Hafsat ko shiri tayi ta fita nan yaji rufe k’ofar da wuri ya mik’e har zata fita a falo ya ganta..

” ina zuwa da sassafen nan?”

“Jiya Umma tace ni Zan ringa girki”.

” ba inda zaki je”.

“Amma….”

“Kema Ai cikin gare ki,su suna tattalin nasu ke kuma naki kin bar sa ko oho ko,to Wallahi Tun wuri ki koyi kwatar ma kan ki ‘yan ci a gidan nan”.

” Bayan kai ma tsoron Daddy kake ji”.

Shiru yayi bai sake cewa komai ba sai Jan hannun ta da yayi gami da rufe k’ofar suka nufi bedroom nan ya sata bacci..

Tayi bacci bai fi da 30mins ba yaji Ana knocking na k’ofar nan ya nufa yana bud’ewa yaga Umma ce kai tsaye falon ta shige

“Ina Hafsat?”

“Bata jin dad’i”.

” ta fito tayi girki don ba Wanda zai mata”.

“Gaskiya yanzu kam ba zata iya ba”.

” Au Bayan raina ni da Kayi yanzu kuma matar ka zaka sa ta raina ni “.

” ba batun raini a nan girki dai ba zata iya ba”.

“Kace na bata nan da 5mins ta fito”.

Tana gama fad’ar haka ta fice tana fita taji yadda yake ma k’ofar key kenan da gaske  ba zata je ba..

Bayan ya koma sai yayi shirin fita office nan ya biya ta falo yaga yadda Umma ke cin uban ‘yan aiki yau Abu kadan zasu yi ta zage su ko zani ne basu d’aura da kyau ba sai tayi masifa nan ya gaida Daddy dake falon Hakeela ko na zaune a dining Umma na bata abinci a baki sai wani bata rai take don ita takaicin cikin take ji don duk da cikin dake jikin ta bai Hana Khaleel dukan ta ba tana ganin Hydar ta Fara murmushi don ita tsam bata son ya San tana da ciki sai tace,

” ya Hydar ina kwana?”

Ciki-ciki ya amsa da lafiya sai ta sake cewa

“Ya Hydar Hafsat ta dawo ko labari babu”.

” to Hakeela me gamin ki da juya tunda Allah ya baki,Ai inaga kwanan nan za’a zo yashar suckaway a apartment nasu”.

Shi dai banza ya musu yana gamawa ya je wajen Ammie ya gaishe ta sannan ya wuce..
Hafsat na tashi bacci taga baya nan sai kawai taje tayi brush daga nan tayi breakfast taci sannan ta gyara waje..

Bayan tayi Azahar tana kallo taji an banko k’ofar nan Umma ta shigo tana fad’in,

“Munafuka to Wallahi baki Isa ba don Hydar d’in kan sa a karkashin uban sa yake har ni Zan saki aiki ki ki?”

Shiru tayi bata ce da ita komai ba..

“To Wallahi abincin dare ke zaki yi in ba haka ba….”

Ta karashe maganar tana girgiza kai gami da ficewa Hafsat ko abinci ta sake ci sannan tayi wanka tana yin Asr taja k’ofar ta ta nufi cikin gidan..

Ba kowa a falo sai ma’aikata nan ta wuce kitchen suka Fara girki Baaba Ladi na tayata a haka har 6 yayi..

Hydar na parking ya nufi apartment nasu sai yaga bata nan ya shiga toilets duk bata nan sai yayi wanka sannan ya wuce cikin gida don ya tabbatar tana wajen..

Umma da Hakeela  na falon ya wuce su direct kitchen ya nufa ma’aikata na ganin sa suka fita shi kuma hugging na Hafsat yayi ta baya yana fad’in,

“Baby Ashe kina nan?”

“Ehh Wallahi har ka dawo?”

“Allah yayi ya Baby na?”

“Lafiya kalau kaci abinci kuwa?”

“A’ah nazo na tayaki aiki ne”.

” to d’ebi cooler’s d’in sai mu kai dining haka ko suka ringa aiki sai shige mata yake yi ko a jikin sa Umma da Hakeela takaici kamar su mutu..

Suna gama jerawa yace,

“Baby muje ki rage mini gajiya kan su fito”.

Tana murmushi tace,

” silly you”.

Nan ya ja hannun ta suka tafi suka bar Umma baki bud’e kamar shashasha..

Koda suka dawo serving shi ke mika mata plate tana serving Harda manna mata kiss a forehead ko a jikin sa Hakeela ko kamar ta hadiye ran ta..
3days later!!
Haka kullum Hydar ke makale ma Hafsat ya tayata aiki Hakeela ko ta gaji da ganin bakin ciki don haka yau tace Ana gama breakfast zata nemo mafita..

Hafsat na serving nasu Hydar ya  shigo hugging nata yayi gami da shafa cikin ta Wanda Umma cikin kwana 3 nan ta lura yana yawan yi yace,

“Baby na tafi office ki Lura mini da kan ki”.

” an gama Baban Baby”.

Sannan ya fice..

Hakeela ko suna gama breakfast tace,

“Wallahi Umma ban San meyasa ba duk sanda na kalli Hafsat sai naji na tsani Kai na bana son ganin ta”.

” an gama girkin ma daga yau ta gama kin ji”.

“Yauwa Umma na gode”.

” Hakeela baki Lura da yanayin Hafsat ba ko ta ta’ba fada miki wani Abu ne? “..

” A’ah kamar me kenan? “

“Ina zargin Hafsat Nada ciki don daga yanayin ta da kuma yadda ta Kara haske Hydar kuma kullum sai ya shafa cikin ta”.

” Kai gaskiya bance ba don ko hauka Hydar yayi ba zai bar ta tayi ciki ba don tsoron Daddy “.

” koma yaya ne ke kam Zan San nayi”.
Tana gama fad’ar haka ta yi Kira gami da fad’ar maganin da take so aka kawo mata har gida nan kuma mai kawo musu drinks ya kawo Bayan ya gama shigar da na cikin gida da kuma na Khaleel sai Umma tace ya cire na apartment na Hydar dukka ya bar milk kan yasa sabo don shi kadai Hydar ke sha..

Haka ko akayi nan aka sa milk sai yoghurt sai Pepsi guda d’aya don yanzu duk duniya ba abunda Hafsat ke so sama da Pepsi da farko suna mata ganin Yar talakawa ne bata Saba da drinks mai dad’i ba sai Umma Tasa magani a ciki sannan ta basa yasa a fridge d’in.
Hafsat ko tana tashiwa bacci ta nufi fridges gaba d’aya ta bud’e babu Pepsi sai a falo ne taga guda d’aya nan ta bud’e ba tare da ta duba ba ta Fara sha sanda Tasha rabi taji kamar test nasa daci sai ta kalli Goran da kyau nan taga particles farare a ciki..
Bayan ta sha da irin 10mins taji cikin ta ya Fara ciwo ba dad’e Wa ta Fara bleeding nan ta Fara kukan azaba tana cikin haka hydar ya shigo ya Gan ta cikin jini..

“Hafsat mai ya same ki?”

“Hydar ina ji cikin ji ki na zai zube”.

Wani gumi ya Fara hadawa sai tace,

” pls Kai ni asibiti in cikin nan ya zube Zan mutu”.

D’aga ta yayi da gudu suka fita a apartment d’in nan Umma tagan sa rike da Hafsat tana bleeding sai tace,
“Ashe dai akwai cikin to alhamdulillah na zubar”.

Hydar ko a gigice ya nufi mota ganin halin da suke ciki yasa driver bud’e masa mota suka shiga baya shi kuma yayi driving nasu sai hospital..
Yau dai nayi typing ina jiran ruwan comments don naji k’arfin gwiwa yi gobe duk da waya ta ba lafiya..
*°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
*1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 44📑*
*__________*📖suna Isa hospital ya fito rike da ita da gudu suka shiga ciki nan doctors suka kar’be ta gaba d’aya yanayin Hydar ya sauya sai ya had’a hannun sa waje d’aya alamar pleading yace,+

“Pls doctor na roke ka do something kada cikin nan ya fita I promise duk abunda kake so ko nawa ne Zan maka just save my Baby”.

” calm down “.

Doctor ya fada yana dafa kafad’ar shi sannan ya shige ciki..

Safa da marwa Hydar ya Fara yi baji ba gani yake bankade mutani kuma ko sannu baya ce musu har ya gaji ya zauna nan ko gaba d’aya gumi yake hadawa.

A haka yayi ta zama har tsahon 3hours kan doctors din suka fito nan yace da Hydar yana son ganin sa sai suka nufi office na doctor..

Bayan sun zauna sai ya mika ma Hydar hannu Amma shi yanzu duk wannan bai dame sa ba so yake ace cikin na nan..

” alhmdll we manage to save your Baby sai dai matar ka ta wahala cuxx maganin da ta sha na abortion yana da k’arfi sosai”.

“You mean maganin abortion ta sha?”

“Yah shi ta sha kuma the next time tayi attempting zubarwa zata iya rasa ran ta”.

” thank you doctor “.

Ya fada yana mika masa hannu gami da cewa

” yau za’a yi discharging namu?”

“No zaku kwana sai zuwa gobe da safe”.

” ohk tanx”.

Ya fada sannan ya fita gaba d’aya kan sa ya d’aure wato Hafsat pretending take yi na cewa tana son cikin Ashe bata so..

Room da aka ajiye ta ya nufa yana shiga ya ganta kwance hawaye na bin gefen fuskar ta cikin had’a rai ya zauna a bakin gadon ita kuma da wuri ta d’aura hannun sa kan cikin ta tana fad’in,

“Your Baby is still alive”.

Cikin zafin nama ya fusge hannun sa gami da matse ta yana fad’in,

” me yasa Kika yi attempting abortion? “

“Wallahi Hydar ban….”.

” cikin tsawa yace,

“Yi mini shiru tunda baki son cikin za’a cire miki ki huta”.

Kuka ta Fara tana fad’in,

” wallahi ina son cikin “.

” ko dai a gidan Ku ne aka zuga ki ki zubar?”

Da wuri ta girgiza Kai tana fad’in,

“Ba Wanda na fad’a ma ina da ciki pls ka yarda da ni”.

Ganin yadda idon sa yayi jazir kuma jijiyoyin kan sa sun tashi sai tace,

” a gidan Ku ne aka yi k’ok’arin zubarwa”.

Da wuri ya juyo yana kallon ta ita kuma cikin gaskiya da gaskiya tace,

STORY CONTINUES BELOW

“Pepsi na sha kuma ina zargin an sa wani Abu a ciki”.

Mik’ewa yayi da wuri gami da shafa fuskar ta yace,

” kada kije ko ina yanzu zanje gida na dawo “.

Da Kai ta amsa masa sannan ya fita da wuri..

Direct gida ya wuce a tsakiyar falo kuma yaga Goran Pepsi da sauri ya d’aga yana kallo tabbas akwai particles a ciki don haka sai ya koma hospital d’in da shi nan ya nuna ma doctor sai doctor yace,

” Ehh a ciki aka sa maganin”.

Shiru yayi yana nazarin kenan sun gane ciki ne a jikin ta lallai ko dole ya hanata shan ko ruwan gidan ne..

D’akin da aka ajiye ta ya koma nan ya rungume ta yana fad’in,

“Duk sun gane kina da ciki kuma ba zasu fasa attempting zubarwa ba har sai sun San babu shi”.

” why? Nice mace na farko a duniya da na Fara yin ciki da idon kowa zai koma Kai na?”

“Ba ke bace Amma Ai kin San gidan mu Umma ba zata jura ganin ki da ciki ba tunda matar d’an ta Nada ciki”.

” ni fa abun duniya bai dame ni ba su rike abun su ni su bar mini d’a na”.

“Shh kwanta ki huta”.

Bacci ya sata..

Baaba Ladi na gama aiki ta d’auki duk wani abunda ta San zasu bukata da abinci ta Kai musu asibiti nan Hydar ke tambayar ta yadda akayi sai tace masa Umma ce..

Tare suka kwana a hospital d’in Washe gari kuma suka kama hanyar gida..

Yana parking Baaba Ladi ta fito rike da Hafsat nan suka nufi apartment nasu a hanya Umma ta tare su tana fad’in,

” dama duk abunda aka Gina sa akan rashin gaskiya ba Zak yi tasiri ba,Gashi Ana boye cikin kuma Allah ya fitar da shi,Hakeela da ta nuna nata ba Gashi tattalin sa ake ba”.

Banza suka mata suka tafi apartment d’in, Hydar na zuwa tace,

“Hope dai cikin na nan?”

“Ya aka yi Kika San tana da ciki?”

“Ni yarinya ce da Zan ga bleeding ban fahimci ciki ba ne?”

“Kika San daga ina jinin yake fitowa?”

“Ina tambayar ka hope cikin na nan?”

“Bayan an zubar kuma me ya rage Ai nasan abunda kike son ji kenan to cikin ya zube”.

Yana gama fad’ar haka ya wuce apartment nashi ita kuma sai murna take…
Bayan ya Isa sai ya had’a ma Hafsat tea mai kauri ya bata tana sha ya bata magani Baaba Ladi kuma ta gyara musu gida..

” daga yau ko apartment nan kar ki sake Bari kuma ko sun zo kada ki bud’e musu k’ofa “.

” saboda me?”

“Saboda a zaton su cikin babu”.

” to “

Tace ba dadewa kuma bacci ya d’auke ta..

A ‘bangaren Saudat soyayya suke sha ita da Lawal haka ma ‘yan uwan shi na nuna mata so Gashi ba aikin da yake a gida yake wuni haka zasu yi ta makale juna..
Aisha ko tunda ta Fara shan magani bata sake sa Abdool a ido ba har tayi sati,shima kullum sai yazo haka za’a Hana sa kallon ta..
Yau kam yana shiga gidan yayi sallama sai yaji ita ce ta amsa da alama ba kowa a gidan direct d’akin da take ya wuce tana ganin sa da gudu ta hau jikin sa sai yace,

STORY CONTINUES BELOW

“Ina Maama?”

“Ta fita ita da Murja”.

Shima hugging nata yayi gami da Kai mata kiss ta ko ina nan suka zauna a bakin gado yace,

” baki son komawa gidan ki ne?”

“Ina so mana wallahi nayi missing naka”.

” to in Maama ta dawo Kice mata zaki koma “.

” nikam ina tsoro “.

” shikenan sai mu yi ta zama a haka “.

” No ina son komawa fa”.

“To yanzu zo mu kwanta a nan Kinga in ta dawo ta same mu za’a ce ki koma”.

To tace a haka suka kwanta a wajen har Allah yasa Maama suka dawo suna sallama suka ji shiru nan ta shiga d’akin su Hafsat sai taga Abdool da Aisha kwance a gado d’aya.

Buga kafar sa tayi tana fad’in,

” Abdool yaushe ka zama haka ko bakayi haka ba an San matar kace kuma dama yau zata koma don haka tashi Ku bar mini gida”.

Cikin jin kunya ya mik’e ita Aisha kuma ta gagara ko bud’e idon ta ne don kunya sanda Maama ta fita nan suka rungumi juna suna jin dad’i daga haka ya tayata kwashe kayan ta suka fito kan ta a k’asa suka sallami Maama sai gidan su..

Sanda suka iso k’ofar gidan gaban sa ya Fara fadiwa kada tayi kamar na kullum tace ba zata shiga ba amma sai yaga ta shiga Tun daga falo suka Fara makale ma junan su kan kace me duk sun rude nan ko suka nufi bedroom a lokacin Abdool ya karbi hakkin sa iya kuka da magiya kam ta masa.
‘Bangaren suspect da aka kama wajen kamu har yace an turo sa yayi kidnapping Aisha Saudat kuma ya kashe ta bincike ake yi sosai inda ba dukan da ba’a masa ba yaki fadan Wanda ya turo sa ba, sanda aka masa barazanar kashe sa sannan yace,

“Boss nane ya tura ni kuma ban ta’ba ganin sa ba asalima ba a kasar nan yake ba”.

” bani number’n sa “.

Bada number’n yayi inda aka yi tracing but to their greatest surprise line d’in is not registered..

” ta ya mutum zai yi Kira da line da ba’a yi register ba”.

“Ni dai da shi yake Kira na saboda tura mini kud’i yayi ya kuma fada mini abunda zanyi”.

Sun bar case d’in zuwa gobe sai dai a Washe garin aka kashe shi suspect din ganin haka ne yasa commissioner of police da kan shi yace ba zai bar zancen nan ba don case d’in is complicated kuma duk yadda aka yi akwai fasa gurbi a cikin ‘yan sandan don tabbas d’an sanda ne yayi kisan kai..

Nan fa case ya dawo sabo sai aka samu three suspect cikin wad’an da suke duty jiya..

Na farko shine Wanda yake safa da marwa a wajen cell d’in a Daren jiya..

Na biyu kuma yayi ma suspect d’in magana na lokaci mai tsaho..

Sai na uku Wanda ya bama suspect d’in ruwa ya sha..

Nan aka Fara da suspect na d’aya meye reason nasa da yasa yake safa da marwa a kusa da cell na suspect d’in Bayan cells Nada yawa a wajen.
” Sir dalili na na yin haka ba komai bane illa naga wannan ya nuna suspect na biyu ya jima yana masa magana shiyasa nasa ido a kan su Bayan wannan banda wani reason “.

” Gud Kai kuma wani magana kake yi da shi?”

“Sir cewa yayi na d’an masa waya yayi Kira sai nace ba zai yu ba nan yayi insisting sai na tambaye sa Wa zai Kira sai yace mini oga’n sa nan na Hana shi wannan ne yasa na d’auki lokaci mai tsawo muna magana”.

STORY CONTINUES BELOW

Kallon suspect na ukun commissioner of police yayi sai yace,

” ba shakka Kai Kayi wannan kisa’n don na tabbata poison ka sa masa a ruwan da ya sha”.

Shiru yayi nan aka Fara dukan sa Ana tambayar sa dalilin sa na haka sai yace,

“Asali na ba son aikin d’an sanda nake ba kawai nayi ne domin leken asiri duk abunda ke tafiya a nan ni ke Kai rahoto kuma nima wani ne ya sani kisan nan”.

” waya Saka?”

“Oga Bado”.

Jin sunan duk sun tsare don Bado Babban terrorist ne a garin kuma kama sa Abu ne mai wuya..
Nan fa aka sa police d’in a cell sannan aka Fara bincike domin samun Bado..
Lawal ma jin ance an kashe suspect d’in ya tsorata don lamarin Babba ne.

Torturing police d’in aka ringa yi da kyar yake sanar da su cewa,

” kwana ki biyu da suka wuce ina kwance a gida na sai naji Ana knocking na k’ofar sai na fita..fita na ke da wuya sai naga mota tinted glass kuma ba’a bar ni na karasa wajen motar ba nan suka bani envelope sai suka juya ina bud’ewa naga 5 hundred thousands ne a ciki sai kuma wani wasika na cewa in na amince na rubuta yes a k’ofar gida na..

Ni kuma ganin kud’i dayawa sai na yarda nan ko na rubuta a k’ofar gida na a Washe garin kuma aka sake kawo mini waya sabuwa dal iPhone 11 pro sannan suka ce in na gama aikin da suka sani sai na Yar da wayar..

Bayan na kashe sa sai naga wayar Nada tsada da kuma kyau don haka sai nace ba Zan iya yarwa ba”.

“Yanzu ina wayar?”

“Yana gida na”.

Nan aka d’auke sa har gidan sa nan ya d’auko wayar ya basu ko da suka yi tracing numbers da aka Kira duk baya basu abunda suke so don haka sai suka nufi kasuwan siyar da wayoyi nan kuma waje uku ne ake sayar da waya a garin in dai manyan kasuwan waya ne..

Na farkon sun nuna wayar suka ce basu sayar da waya mai tsada haka.dayan kasuwan waya nan ma suka ce waje d’aya ne ake saida mai tsada haka don haka sai suka nufi na karshen a wajen ne kuma suka ringa shiga shaguna har suka iso shagon nan suka nuna wayar sai aka bi receipt na wayoyin da aka saya a nan har aka iso kan wayar sai suka ga sunan Wanda ya saya har da address nasa nan suka nufi gidan sa suna zuwa kuma suka tambaye sa shi ya saya wayar yace,

” Ehh oga nane ya aike ni don ni d’in d’an aika ne a wajen sa na dad’e ina zuwa aikan sa”.

“Wajen sa Muke son ka Kai mu”.

Nan ya Kai su gidan aka kewaye gidan sannan aka ce yayi surrender nan aka kama Bado..

Ko da aka Kai sa police station a cell aka Saka shi tunda ba’a yanke masa hukunci ba bare a sa shi a prison..

Torturing ba irin Wanda ba’a masa ba Amma yaki fad’in Wanda ya tura sa saboda shi a tunanin sa dole wani zai zo yayi rescuing na shi..

Ganin bayi da niyar fad’in Wanda ya tura sa sai Lawal yayi ma commissioner of police magana tare da basa kud’i nan aka d’auki Bado sai Bayan gari..

Suna Isa suka sake sa nan aka ce ya gudu kuma yana da tabbacin kashe sa zasu yi don haka yace,

” nifa ba ni na tura Kai na ba kamar yadda kuke tunani don son kud’i, tura ni aka yi don haka Ku maida ni cell “.

“Ka gudu kawai”.

Ganin fa ba d’aga kafa sai yace musu,

” a cikin yaran da aka ce ayi kidnapping d’aya daya kuma a kashe Wata mata ce ta bani 4 millions da kuma mota domin nayi haka kuma a cikin kud’in na bawa police can da kuma saya masa waya..

STORY CONTINUES BELOW

Jin haka sai suka d’auke sa suka maida sa police station aka tambaye sa wace ce sai yace,

“Hajiya Zulai mata ga Alhaji Munir”.

” karya kake yi kawai so kake ka mata sharri”.

“Ina da proof dayawa da Zan nuna muku amma sai kun Kai ni gida na”.

Nan suka tafi gidan sa da shi sai ya fitar da envelope da ta bashi kud’i saboda cheque ta basa..

Nuna musu cheque d’in yayi sai yace,

” Bayan ta bani sai yaro na ya yaga yana wasa so da naje Bank sai na basu Amma suka ce ba zasu kar’ba ba sai na Kira ta da asalin layin ta nan ta Kira ‘yan bank d’in ta musu magana sai aka cire kud’i a account nata aka bani..

Jin haka sai suka tafi bank d’in nan aka duba transaction nata sai aka ga kamar yadda ya fad’a a ranar tayi transfer kuma account nasa aka tura..

“Kuma in Baku yarda ba Ku bincika waya na saboda duk time da Zan mata aiki bata Kira na da line nata sai fake line Amma a ranar sai na Kira ta kuma ta d’aga”.

Daga Bank MTN office suka nufa nan aka yi tracing layin aka ga confirm nata ne..

Sai ya Kai su hotel da suka had’u nan ko aka duba CC T.V aka ga hoton ta ras.
Bayan haka sai suka maida shi cell ita kuma aka tafi arresting nata..

A cikin gidan su Hydar ko Umma yanzu bata da burin da ya wuce tayi duk wani abunda zata yi tayi gaba..

Yanzu haka tana zaune a falo ita da Hakeela sai rarrashin Hakeela take nan police suka sa Kai cikin falon suna fad’in,

” you are under arrest”.

Mik’ewa tayi tana fad’in,

“Ni kuma”.

” Ehh “.

Nan Daddy ya sauko daga upstairs yana fad’in,

” Wa ya Baku izinin shiga mini gida Kai tsaye?”

“Matar ka ake zargi da sa a kashe Wata”.

” No kun yi mistake “.

” koma yaya ne ka bimu police station sai kuyi bayani”.

Nan aka yi arresting nata aka tafi da ita daga nan Daddy ya bi su nan aka nuna masa evidence da aka Tara against her sai kawai aka sa ta a cell sai kuka take..

Daddy na tambayar ta ta aika ta ne sai kuka take nan ya tabbatar ta aika ta amma ita kukan rashin nasara take yi.

Kiran commissioner of police Daddy yayi don a samu bail d’in ta amma sai yace,

“Let us do our work”.

Hakan ne ya tabbatarwa Daddy lamarin Babba ne tunda har commissioner of police ya San da shi dole ya hakura ya koma gida..

Umma ko yin duniyar Allah taki fad’in gaskiya don haka aka yi filing case a court..
Ranar da aka yi zama na farko a ranar lawyer’n ta yayi pleading a bar ta ta koma gida nan aka bada bail nata ta koma gida Amma Ana cigaba da hearing in kafun anzo judgment..
*After 6 months!!*
Yanzu cikin Hafsat na 8 months while Hakeela kuma 6 months da some weeks..

Tun Bayan da aka samu bail na Umma sai urgent tafiya ya tashi ma Daddy nan ya d’auki Umma suka tafi tare don harkar office ne Amma basu samu dawa ba sanda suka yi spending 5 months.. Hakeela ko Umma na tafiya ta koma gida don ba zata iya wahalar da take sha ba shiyasa ba ma Wanda ya fad’a ma Umma cikin Hafsat na nan har kuma ya fito..

STORY CONTINUES BELOW

Tattali sosai Hafsat ke samu wajen Hydar inda Lawal da Saudat duk sun dawo Nigeria har yayi passing out sun koma Dubai da zama yanzu haka tana da cikin Wata 2 haka ma Aisha..
Umma na dawa daga tafiya ne wani d’an gidan ta ya Kira ta yace yau fa za’a shiga court kuma ya kamata yau kam ta shigo taga yadda al’amura ke tafiya nan ta sanar da Daddy sai suka tafi tare..

Yau dai case yayi Zafi inda aka kawo evidence lawyer’n ta ya gagara kare ta saboda an kawo evidence da bai San da shi ba don an goge duk wani proof da zai yi leading nasu zuwa ga ita ba amma na yau ya basu tsoro har ita Umma..

Bayan sun gama mika evidence nasu kuma Umma taga sai tona mata asiri ake a gaban Daddy Gashi bata ta’ba tunanin akwai Wanda ya San shi ba sai hankalin ta duk ya tashi nan alkali yace,

“Lawyer’n mai kara kana da abun fad’i?”

“Ya mai girma mai Shari’a so nake a d’aga wannan case don sam ban San da evidence da suka kawo ba kafun na gyara komai”.

” ohk an d’aga zuwa sati in kuma baka yi proving nasu wrong ba za’a yi judgment “.

A haka aka watse inda Umma ta koma gida hankali tashe..

Kwanciya tayi a gado tana kallon ceiling nan ta Fara tuna yadda aka yi tazo gidan Alhaji Munir..
*TUNANI!!*
Zulaihat shine sunan ta wacce ta kasance ‘ya take da uban ta ke da shi,Sunan mahaifin ta honorable Sambo Wanda yake politician kuma Babban business man don business nashi international ne yana importing and exporting..

Alhaji Munir (Daddy’n Hydar) Alhaji Musa(Abban Hafsat) Alhaji Shamaki(Baban lawal)duk sun kasance ‘yan gidan Baban ta ne inda Baban Hafsat shine in charge of accounting Baban Hydar kuka in charge of buying and distributing inda zai saro kaya a abroad sannan ya kawo wire house sai kuma yayi distributing, Baban Lawal kuma is in charge of selling shi yake supervising yadda ake sayar da kaya..
Gaba dayan su suna aiki a duk stores nashi sune overall managers a ko wani stores nashi gaba ki d’aya don yana branches kusan biyar a Nigeria kuma a ko wani state da yake da branch yana da shago Uku zuwa sama wani a kasuwa wani kuma cikin gari..

Sana’a na tafiya dai-dai ko wannen su family’n sa a wadace shima gefen sa bayi da matsala sai dai akwai wani yanayi da yake gudanar da business nashi Wanda Alhaji Munir ne kadai yasan yadda yake yi yana saro kaya a outside country don suna saran kaya a countries guda biyu China da Dubai inda China Ana saran electronics Dubai kuma kayan sawa da furniture’s..

Kuma a business nashi nasa da riba Wanda idan suka saro kayan zasu ninka masa kud’i kuma Baban Hydar yana sane da shi amma bai damu ba ..

Wata Rana Baban Hydar yaje saran kaya sai aka samu strictness a border a canza duk wadan da suke zama a border aka kawo sabbin fuskoki sai yayi mamaki matuka kuma abun ya kwa’ba musu lissafi saboda business nasu biyu ne legal da in legal..

Legal d’in shine su Baban Hydar suke in legal d’in kuma yana shigar da su cocaine da bindigogi..

To already sun Riga da sun saro in legal nasu sai suka rasa yadda za’a yi su shigo da kayan Nigeria don haka sai suka sa a cikin kayan da Baban Hydar ya saro..

To da aka zo Baban Hydar ya Saba da legal business nashi in an kawo kayan a jirgin ruwa sai an dudduba kafun a sauke containers d’in Amma yau sai aka samu akasin haka ba’a duba ba sai ma faman rufa-rufa da ake ma kayan, sai suka ce kayan ya wuce..

Lokacin da aka jido containers d’in za’a Kai wire house duk inda yazo kuma ya Saba bada customs duty sai yaji ance,

“Containers na honorable Sambo ne su bar su su wace”.

STORY CONTINUES BELOW

Nan ko za’a bud’e masa hanya ya wuce a haka har ya Isa wire house..

Bayan an Kai wire house sai aka sauke containers d’in shi kuma ya Saba bud’ewa yayi distributing sai wani yace,

” ka Bari sai sha biyu na dare za’a bud’e “.

Sai abun ya cigaba da d’aure masa Kai sai yace ba zai Bari ba don bai San su ba nan wayar sa ya Fara ringing sai suka ce Wayan ka na ringing..

Baban Umma ke Kira nan yace ya bar kayan sai 12 jin haka sai yaki tafiya ya tsaya nan ya Kira Umma yace mata ba zai samu dawa ba..

Har ya Fara bacci suka tashe sa kan cewa za’a bud’e sai ya tsaya yana jiran a bud’e..

Ana bubbudewa sai yaga duk containers da aka bud’e akwai kwali a tsakiyar sai aka cire su nan aka ware masa kayan a gefe nan aka ce ga kayan sa gobe da safe sai yayi distributing.. Sai suka koma gefe da kwalayen su nan motoci sun Kai goma suka zo da katifa ko wani katifa za’a tsaga sa biyu nan yaga an Fara sa gun’s da cocaine a ciki a haka har suka gama suka tafi abun ya daure mishi Kai sosai nan ya Kira Baban Umma yace,

” Alhaji ina son magana da Kai”.

“Ohk kazo gida ka same ni”.

Asuban fari ya tafi gidan Baban Umma sai ya fad’a masa abunda ya faru jiya sai yace,

” kar ka damu duk business nawa ne”.

“Alhaji Harda in legal?”

“Ehh a tunanin ka a k’aramin business. Namu ne zanyi kud’i haka?”.

Daga haka sai ya wuce gida nan ya fad’a ma Ammie duk abunda ya faru time d’in Hydar Nada 7yrs sai tace,

” Alhaji wannan mutumin bai kamata Ku ringa Barka da shi ba,shawarar da Zan baka shine Ku janye jikin Ku a hankali “.

” wallahi nima abunda nake tunani kenan “.

Bayan yayi breakfast sai ya fita lokacin kuma duk duniya bayi da amini da ya wuce Baban Hafsat don haka sai yake jin ya kamata ya sanar da shi abunda ke tafiya don su ja jikin su a hankali..

Bayan ya sanar ma Baban Hafsat sai yace,

” wallahi sai Mun mika sa ga hukuma ba yadda za’a yi mu bar mutum irin sa a cikin mu”.

Dama duk cikin su Baban Hafsat yafi tsoron Allah nan Daddy’n Hydar yace,

“A’ah in muka yi haka mu ma Ai sai a kama mu”.

” nifa wallahi sai na tona masa asiri “.

Nan dai Daddy’n Hydar ma yaji ya kamata su tona masa asiri sai suka fad’a ma Baban Lawal shima yace haka za’a yi..

Duk business da Baban Umma ke yi family’n sa na can England sai dai yake Kai musu ziyara..

So daga wannan lokacin suka d’aura damarar tona masa asiri a haka har Allah ya basu nasara nan aka yi arresting na honorable Sambo..

Time d’in kuma Daddy’n Hydar ya San wurin ajiyar honorable Sambo Wanda ba Wanda ya sani sai Umma wacce bai San da ita ba nan yaje ya d’ebi kud’i son ransa Amma kuma yana fargaban Fara business shi d’aya Abban Hafsat ya tambaye sa inda ya samu kud’i don haka sai ya Kai masa kud’in yace Wanda yake saving ne..

Da yake Abba ya yarda da shi nan suka Fara business kuma Allah ya d’aga su suna cikin yi ne Allah yayi ma mahaifin Baban Lawal rasuwa sai ya tafi da haka su kuma suka cigaba da business nasu..

Time da Umma taji anyi arresting Baban ta sai tazo Nigeria sai prison da aka ajiye sa don life in prison aka masa.

Tas ya kwashe labarin komai ya fad’a mata tare da fad’in,

” ko Bayan rai na ne Zulai ina so ki tarwasa abokanaye ukun nan,soyayyar dake tsakanin su ki maida ta kiyayya”.

“Dad in har banyi haka ba ni ba ‘Yar ka bace na maka alkawarin kawo karshen abotan nan.

So time da ta Fara bincike a kan su su uku sai ta fahimci cewa Baban lawal ya koma Dubai nan ta cire ido a kan shi tunda abotan Alhaji Munir da Musa yafi k’arfi..

A hankali ta Fara shiga rayuwar Daddy inda shi ko ta kan ta baya yi as time moves on sai suka zama frnds da boka da malami har ta samu ya Aure ta lokacin kuma ciwon Zuciya ya kashe Maamar ta..

Daddy’n Hydar ya Aure ta amma bai San cewa ita ‘Yar honorable Sambo bane..

Wannan kenan shine yadda aka yi Alhaji Munir ya auri Umma..
*Back to story!!!*
Numfashi taja sannan tace,

” sai na d’aukar ma Dad na fansa….
Manage this Wallahi yau aiki ya mini yawa kuma bana son barin Ku without update..
*°🔘°ƘIYAYYAR ZUCIYA°🔘°*
              *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    ”’🎐 G•W•A🎐”’
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_

*NA MARUBUCIYA:-*
*HAFCIEY MUSA✍🏼*•

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAss.~

*SHAFI NA 46📑*
*__________*📖Umma na suma aka d’auke ta sai amenity domin bata kulawa..dama already tunda zasu zo hospital d’in tace ma Khadija suzo amma sai taki zuwa Bayan sun zo ma ta Kira ta a waya sai yanzu da taga dama ne ta kamo hanyar asibiti..+

Tana shiga ko aka nuna mata inda Umma take hankalin ta ba k’aramin tashiwa yayi ba,wacce ta kawo Mara lafiya ace ita ma ta kwanta rashin lafiya..

Lura da ita ta cigaba da yi kan ta farka sai ta Kira Khaleel ta sanar da shi matar sa ta haihu nan ya kama hanyar asibiti tunda ba aiki yake ba bare yace sai ya gama..

Hakeela na kwance baby girl nata na kwance a kusa da ita sai kallon yarinyar hakeela take don ita fa ba zata iya barin ‘Yar ta Kira wanna mugun uba ba..

Yana zuwa ko kallon ta bai yi ba bare yace sannu yasa hannu ya d’auki ‘Yar yana smiling ita ko bacci ma take..

Zama yayi a gefe yana fad’in,

“Ina Umma ta shige ne?”

“Ai bata da lafiya”.

Khadija ta bashi amsa tana fita a d’akin domin dubo Umma ta ko yi sa’a ta farka nan ta zauna gefen ta.

” Khadija da gaske ne Hafsat yara uku ta Haifa kuma dukka maza?”

“I don’t know”.

Ta bata amsa cikin halin ko in kula..

” ni Zulai na shiga uku Hafsat ta kawo karshe na da na yara na a gidan Alhaji Munir, na tabbata hankalin kowa zai koma kan yaran ta..
‘Bangaren Hafsat ko Babies nata ba abunda suka bar ma Alhaji Munir duk da cewa Hydar na kama da shi amma su sun fi kama da kakan nasu don sun fi uban su haske..

Baba Ladi ce ta d’auki waya tare da dialing number’n Hydar yana picking ta fita waje tana mai fad’in,

“” Assalamu alaikum “.

“Wa’alaikisalam”.

” dama na Kira ne na fada maka muna asibiti da Hafsat “.

” labor ko?”

“Ehh Wallahi”.

” waya kaita asibitin?”

“Hajiya ce”.

Ai yana jin haka ya bar meeting da yake ya d’auki key’n mota don ya tabbatar kashe masa mata Umma zata yi..

Sanda ma ya Fara tafiya kan ya Kira ta ya tambaye ta wani asibiti nan ta shaida masa bai saya ya saurare ta ba ya wuce..

Yana Isa hospital d’in direct maternity ya wuce inda ya tambayi matar da aka kawo mai ciki..

Ganin Umma yadda take dar-dar da Hakeela ga kuma Khaleel da Khadija da suka zo wajen ta har ma Mamar ta da yanzu ta iso sai yasa nurse d’in tunanin wajen ta yazo don haka ta raka shi har d’akin da Hakeela take..

Yana shiga ya gansu sai ya gaisa da Mamar Hakeela Umma ko yayi kamar bai ganta ba sai yace,

” kin sauka lafiya,Allah raya”.

STORY CONTINUES BELOW

“Lafiya kalau,Ameen”.

Har ya juya zai fita tace,

” baka kalli ‘Yar Ku ba”.

Manna mata hauka yayi kamar bai ji ta ba ya fita kansa ya Dada kullewa to ina Hafsat..

Sake tambayar nurse yayi sai tace ba Wata Bayan Hakeela har zai Kira a waya sai ta Tuna nan tace,

“Akwai Wata zo muje ka ganta”.

Kamar ba zai je ba don baya son zuwa inda ba Hafsat d’in sai kawai ya bita suna shiga yaga Baaba Ladi da wuri ya k’arasa yana fad’in,

” ya jikin ta”.

“Da sauki”.

Da yake baya ta juya masa sai ya k’arasa bed d’in ya lek’a fuskar ta nan yaga tana bacci sai yace,

“Bacci tayi ne?”

“Kila amma yanzu fa muna hira da ita”.

Hannun sa yasa cikin nata totally bai damu da ta haihu ko bata haihu ba damuwar sa dai ace lafiyar ta kalau..

Jin sanyin hannun sa yasa ta farkawa don dama baccin ba nauyi yayi ba nan ta juyo tana fuskantar shi with a smile a fuskar ta.

Shima murmushi yayi gami da cewa,

” Alhamdulillah ba abunda ya same ki “.

Yana gama fadar haka yayi hugging nata Baaba Ladi kam sai murmushi take yi..

” Kai ni kadai zaka yi hugging ne banda babies naka?”

Sai yanzu ya kalli cikin ta yaga ba komai sai kuma yace,

“Baby ko babies?”

Da ido ta nuna masa inda aka kwantar da babies d’in Ai a tunanin sa daga nesa ne baya gani mai kyau Ai ko yana karasawa wajen yaga triplets ne ga tsananin kama da Daddy’n shi da suka yi..

Juyowa wajen Hafsat yayi yana fad’in,

“Dukka wad’an nan nawa?”

Murmushi tayi gami da d’aga masa Kai nan ya rungume ta sosai yana tsananin farin ciki sai ya rada mata,

“Da kyau Baby Kice mu kam ko sau uku muka haihu ya ishe mu tunda guda uku kike Haifa”.

Dukan wasa ta Kai masa tana murmushi ita ma nan ya koma wajen babies d’in d’aya Bayan d’aya ya d’aga su yana mai jin kaunar su har cikin zuciyar sa.

” Baby kin gama mini komai a rayuwa ban San da wani baki Zan miki godiya ba,ina kaunar ki kuma ba Zan iya rabuwa da ke ba,Bayan parents na banda kamar ki “.

Shiru tayi tana kallon sa don bata ta’ba tunanin zasu yi rayuwa mai sauki haka har su haihu ba..
Umma ce ta fita a d’akin rike da wayar ta da alama Kira take yi Ana receiving tace,

” Alhaji tunda gudu na kake ka bar gida Ai ba zaka guji grand child naka ba”.

“What do you mean?”

“Hakeela ta haihu Allah ya bata ‘ya mace”.

” Allahu Akbar!Allah raya amma Ai cikin ta bai Kai haihuwa ba”.

“Ameen,Ehh bakwaini  ta Haifa amma ba’a sa yarinyar a kwalba ba cuxx she is strong”.

” wani hospital kuke?”

Nan ta shaida masa hospital da suke har cikin zuciyar sa yana jin dadin labarin don da tace grand child nasa ya zata matar Hydar ce ta haihu.

Securities ya d’auka kan ya nufi hospital d’in don shi yanzu totally bai yarda da ita ba gani yake zata iya harming nashi ta ko wani hanya Gashi gani yake kamar zata yi threatening nashi ta hanyar yarinyar..

STORY CONTINUES BELOW

Yana Isa hospital securities na biye da shi a baya ita kuma Tun shigowar shi Umma ta Gan shi don a upstairs take tsaye..

Yazo zai shige kawai Hydar ya bud’e k’ofar d’akin da Hafsat take zai fita..

“Wato Khaleel ba zai ta’ba zama responsible ba komai sai ka masa”.

D’an murmushi kadan Hydar yayi gami da cewa,

” No ni a wajen Hafsat nake ita ma ta sauka”.

“Alhamdulillah shine Zulai bata fad’a mini ba”.

” Ai Kai ma kasan ba za ta ta’ba fad’a maka ba”.

“To muje naga grand child na”.

Shiga d’akin suka yi Hafsat na kwance taji sallamar Daddy nan take gaban ta ya fad’i har kasa tashi tayi Baaba Ladi ce ta gaishe sa..

‘Yaran company’n Hydar da Saif ne a cike a d’akin nan Daddy yaji Saif na cewa,

” Alhaji Ai yaran Kai suka d’auko ba Mahaifin su ba”.

Jin haka sai yaji kaunar yaran har cikin zuciyar sa nan ya k’arasa wajen su Ai ko kamar sa ne tsak sai yace,

“Kun San bana rike yara amma dai Ku bani d’aya na gwada”.

Mika masa aka yi yara kam Masha Allah identical triplets ne nan yayi ma Yaron peck a forehead nasa tare da addu’a yana mai tsananin farin ciki sannan ya ajiye su..

Hafsat ko ta San tabbas in har bata gaishe da Daddy ba zasu iya samun matsala da Hydar don haka a hankali ta mik’e tana fad’in,

Sannu da shigowa Daddy”.

Ba sakin fuska ya amsa kuma ko inda take bai kalla ba nan zuciyar ta ya tsinke don ta tabbata jikokin sa kam yana son su Amma ita ba abunda ya raguwa na tsanar ta kuma ta tabbata kwace yaran zai yi ya bar ta da hawan jini..

Har zai fita sai ya juya yace,
” kin sauka lafiya Allah ya yara”.

Daga man ya fita Hydar na bin Bayan sa ita kuma gaba d’aya mood nata ya canza don a tunanin ta in ta haihu komai zai sauya ne..

Bayan fitar su sai ta d’auki wayar Baaba Ladi ta Kira Sis Faty ta shaida mata ta haihu Amma bata yi murna ba..

Dama cikin watanni 6 da suka wuce taje gida kuma time d’in cikin ya fito ganin ta da ciki ba k’aramin tadama iyayen ta hankali yayi ba har kamar hawan jinin Maama zai tashi sai da aka sanar da Aunty Balkee sai tace su d’aga mata kafa kila dole aka mata nan ko suka yi ta jimami..
Sis Faty na sanar da Maama haka kawai gaban ta ya fad’i sai ta sanar ma Abba sai cewa yayi ta shirya suje hospital d’in..

Nuna ma Daddy d’akin da Hakeela take Hydar yayi sai ya fita.

Yana shiga ya tarar da Maamar Hakeela da Umma sai Khadija nan ya kalli yarinyar da kyau,kyakyawa ce Amma tana kama da Umma kasancewar uban ta da Mahaifiyar sa yake kam Gashi ‘Yar sa shi ta d’auko da yake mace ce sai tafi kama da Umma..

“Kinyi kama da kakar ki Allah sa kada ki hau halin ta”.

Da wuri Umma ta kalli Maamar Hakeela don tsarguwa,daddy ko cewa yayi,

” Hakeela kin sauka lafiya Allah raya”..

“Ameen Ameen Daddy”.

Daga nan ya juya ya fita da wuri Umma ta bishi tana fad’in,

” ya za’a yi da batun suna”.

“Ai sai yadda Kika yi Hajiya tunda dukiyar a hannun ki yake”.

Ya fad’a yana mugun smile sannan ya wuce ita kuma ta koma ciki a zuciyar ta tana fad’in sisi baza ta ba ma Hydar ba..

STORY CONTINUES BELOW

Yazo fita kenan yaci karo da Baban Hafsat da Maamar ta sai Abba ya cire Kai kamar bai Gan shi ba haka ma Maama don duk sanda yaga Abba sai yasa an tozarta shi ga mamakin su sai ya mika ma Abba hannu cikin batsarwa ya amsa zai shiga d’akin sai Daddy yace,

” kazo ganin jikokin mu kenan to muje ka gansu”.

Shi ya musu iso har d’akin Hydar na ganin su ya gaishe su cikin girmamawa nan Hafsat ma ta gaishe su kanta a kasa sai suka wuce wajen  Babies..

Hydar ko ya Lura Hafsat pretending take son yi ta nuna ba komai a tsakanin su don haka sai yace,

“Baby na baki tea ki sha ko?”

Duk Juyowa suka yi suna kallon su yana rike da hannun ta ita ko ji take kamar Tasa ihu..

“Don Kinga su Abba ba za kiyi magana ba ko?to da hannu na Zan baki as usual”.

Ita dai rasa bakin magana tayi Maama ko kunya ce ta rufe ta sai Daddy da ya fahimci haka yace,

” Alhaji Musa kaga yara kam da ni suke kama bada Kai ba”.

Yake kawai yayi Maama ko kallon yaran tayi tana mai tsananin tausayin Hafsat ya zata ji in aka raba ta da yara har uku..
Haka Hydar ya ringa shisshige mata har su Maama suka gaji da kallon sa nan suka mik’e tare da musu sallama gaba d’aya Kansu ya d’aure ganin yadda Hydar ke treating Hafsat da Babies d’in da kuma yadda Daddy ya karbe su..
Shi Daddy ko duk da bai ji yadda aka had’a sanadin Kiyayyar ba amma ya tabbata Umma ce ta had’a shiyasa ya d’an sake da shi..
Suna komawa gida Maama ta Kira Aunty Balkee ta shaida mata cewa ‘Yar ta fa ta haihu nan tace gobe in sha Allah zata taso don dole tayi ma ‘Yar ta jego kuma ba zata koma ba sai Bayan auren Sis Faty don saura sati biyu yanzu..
A ranar aka sallame su gida kam ya cika tab  da ‘yan uwa Hydar ne ya had’a ya biya bill d’in hospital d’in Harda na Hakeela sai dai ita kamar ‘Yar ta bata fiya lafiya ba don bakwaini ce ..
Suna komawa gida Maama ta tura ma Hafsat Sis Faty kan Aunty Balkee tazo aiko Sis Faty da Baaba Ladi suka gyara mata gida ko ina tsab sai kamshin tularen wuta ke tashi Hydar ko sayayya yake bana wasa ba duk da Tun farko sunyi sayayya Amma basu yi tunanin yara uku bane,da ya shigo da wannan yana gama juyewa zai koma ya sayo wani haka sis Faty zata ringa kar’ba Ana ajiye ko wanne a ma’ajiyar sa kuma ko wani shigar sa sai ya lek’a Hafsat da babies nasa..

Hajiya Nenne na jin Hafsat ta haihu ta tattara kayan ta tace dole taje tayi ma matar Hydar jego don ta dad’e tana addu’ar Allah nuna mata yaran Hydar..
Tana ganin yara uku sai kukan Dadi nan ta ajiye kayan ta a d’akin Hafsat ta Fara kula da yaran haka zata wuni musu rawa sai dai yaran akwai rikici da gani haka zata ringa zungure su..

Hakeela ma an tura mata Aunty’n ta kuma sosai ‘yan ta ke zuwa ganin ta Umma ko zuwa tayi ta gaishe da Hajiya Nenne nan ne ma taga yara kam kyawawa..
Hydar waya yayi ma Aunty Zainab yana tambayar ta ina Ammie tace Gata zaune kusa da ita don yanzu alhamdulillah jikin ta ya Kara sauki don ta kan yi magana Amma kamar na yara saboda ta dad’e bata yi magana ba kuma ta kan mik’e ita d’aya da kyar ba sai an d’aga ta ba nan yace Tasa wayar a hands free sai Tasa..

“Ammie Hafsat fa ta haihu kuma ta samu triplets dukka maza”.

Da kyar tace,

” alhamdulillah “.

Aunty Zainab kam ko a jikin ta duk da taji son ‘yan ukun tunda yaran kanin ta ne Amma hakan ba zai sa ta daina tsanar Hafsat ba..
A ‘bangaren gidan su Hydar komai na tafiya normal Gashi yau Aunty Balkee ta iso direct a gidan ta sauka Hydar ne ma ya d’auko ta a Tasha ta kuma yaba da halin sa tana Isa Hafsat tayi hugging nata ita ko duk hankalin ta na kan yaran nan suka had’u da Hajiya Nenne da kuma Baaba Ladi sai jagwalgwale suke ma yaran Amma ba hali tace zata yi magana..

STORY CONTINUES BELOW

A ranar da Aunty Balkee tazo a ranar Sis Faty ta koma don tsam bata son zaman gidan,gida ne kowa ta kansa yake ba Wanda ya damu da d’an uwan sa Gashi Maama ita kadai ce sai Hamma Naseer..
Hakeela ce zaune a kan gado tana breastfeeding yarinyar ta ga relatives nata a gefe sai abinci kala-kala da Umma ta turo mata daga ganda sai kaji da kuma pepper soup ga kayan tea’n nan wadacecce..

Khaleel ne ya shigo ya ganta sai ci take tana had’a gumi sai cewa yayi

” dama Ai ba abunda Kika iya sai ci,naga da su Umma suka tafi gidan Ku Kika koma Amma yanzu da haihuwa ce kin San zaki ci dad’i shine Kika dawo gidan mu don asha ganda”.

Duk relatives nata mamaki suke,d’an giya kuma ko a jikin sa yana fita Aunty’n ta tace,

“Wallahi mijin ki bayi da hankali ba kamar mijin kawar ki ba,Wallahi jiya da na shiga yana makale a d’akin Wai sai taci abinci mai kyau sanda aka Kore sa sannan ya tafi Amma wannan tunda nazo banga ya rike yarinyar nan ba ma”.

Bakin ciki ne sosai ya kama Hakeela..
8pm

Aunty Balkee, Baaba Ladi,Nenne sai kuma babies suna zaune a falo Ana kallo Ana kuma ta’ba hira sama-sama don kallon yafi d’aukar hankalin su saboda kwana casa’in suke kallo ko wacce a cikin su na rike da Baby d’aya Hafsat ko tana wanka cuxx zata kwanta, Hydar ya shigo apartment d’in da sallama da kuma sakin fuska..

Waje ya nema ya zauna a sama abun ka da d’an mai kud’i sai a hankali nan ya gaishe su yana mika musu ledojin kayan makulashe da ya kawo musu tare da fad’in,

” Hajiya bani na hannun ki na rike”.

“A’ah bani bayarwa”.

Kallon Aunty Balkee yayi yana d’an murmushi yace,

” Aunty ke fa?”

Banza tayi da shi sai ya kalli Baaba Ladi murmushi ta Mi shi tare da mika masa tana fad’in,

“Don rikicin su ne ya Hana su baka su saboda suna tashi zasu sa kuka”.

” ayya Ai rikicin Maamar su suka d’auka”.

“Wallahi karya ne yadda ka ganta Tun tana yarinya haka take bata San rikici na”.

Cewar Aunty Balkee sai Nenne ce tace,

” ke ma da biye masa,Ai rikicin ba nasa bane don Wallahi shima dai bai yi rikici ba”.

“To Wallahi ina ji na pendon su Saudat ne”.

Aunty Balkee ta fad’a nan Hafsat ta shigo falon da sallama murmushi ta mishi shima haka Bayan sun gaisa sai ya mika mata Yaron ya musu sai da safe don ya gaji sosai..
Yau kwanan yaran uku a duniya kuma sai yau su Aunty Zainab da Maryam suka zo,iso aka musu zuwa bedroom, nan Hafsat ta gaishe su kamar ba zasu amsa ba Hajiya Nenne tace,

” dole aka muku ne zuwan in Baku so ba sai Ku tafi ba zuwan Ku da babu duk d’aya ne”.

Nan ne suka d’an sake fuska sai wasa suke ma yaran Harda pics ga yaran su sun dame su sai an basu yaran haka suka ringa musu pics sun jima kan suka lek’a Hakeela daga haka suka wuce..
Azurfa Hydar ya saya guda uku nan yasa ma yaran a hannun su  a Daren Daddy ya Kira sa kan cewa ya same sa a gidan da yake haka ko ta kasance..

Yana zuwa suka gaisa sai Daddy yayi gyaran murya yace,

“Hydar da Kai da Khaleel duk ni Zan za’ba ma yaran Ku suna”.

” hakan ma yayi Daddy”.

“Khaleel sunan Umma’n shi zai sa Kai kuma yara biyu zaka sa sunana da na Alhaji Shamaki dayan kuma kasa duk Wanda kake so”.

STORY CONTINUES BELOW

” why not a sa sunan Baban Hafsat?”

“No banda shi ka nemi wani”.

” but why Dad,dukkan su fa funds naka ne”.

“Saboda dalili d’aya shiyasa ba Zan sa sunan sa ba don har yau ban manta abunda ya aikata a gare ni ba”.

” pls Dad Ai duk ya wuce ni dai duk duniya banda sunan da Zan sa da ya wuce nasa”.

“Ni kuma Allah ya Isa in kasa sunan sa”.

Jin haka sai ya mik’e cikin takaici ya fice a kan me zai ce ba zai sa sunan Baban Hafsat ba Bayan yasa na Baban lawal,an yima Hafsat adalci kenan shi Wallahi in so samu ne ma duk yaran zai sa ma sunan mahaifin ta ko don ya faranta mata..
A Daren ranar haka ya kwana bai yi bacci ba don shi gaskiya sai dai a fasa yima Baban Lawal Takwara in yaso yara biyun sai yasa musu suna daban..

Yana tashiwa ya Kira Ammie ya shaida mata abunda ke tafiya kuma taga rashin dacewar haka sai tace ma Zainab,

” Zan baki labarin abunda baki sani ba”.

Labari ta Fara bata tun daga abotan Abba da Daddy har da business da suka yi a karkashin Baban Umma da kuma yadda suka tarwasa shi har ma da yadda suka yi kud’i da Kansu zuwa yadda Umma ta shigo gidan har ta nakasa ta da kuma yadda ta warzaga abota tsakanin Abba da Daddy..

Hawaye Aunty Zainab take da kyar tace Ammie me sanadin Kiyayyar??
Dai-dai lokacin Hydar ya shigo Bayan sa kuma Daddy ne don yace yau kam zai zo yaga inda take..

Ba tare da Ammie ta kalle su ba duk da tasan da zuwan su tace,
SANADIN KIYAYYAR ZUCIYA!!

Wata Rana ina zaune a gida time d’in shekarun ki goma  Maryam kuma 8 sai Hydar da yake 6,time d’in an auri umma’n Ku Amma bata haihu ba sai aka Kira ni cewa muna da meeting don haka sai nace mata ga kunan Zan fita tace mini to..

Bayan fita na ita ma sai ta shirya ta fita Ku kuma aka bar Ku Ku kadai kuna wasa a ciki, da tsoro ya Fara kama Ku duk da akwai ‘yan aiki Amma suna apartment nasu sai kuka tafi wajen gate man nan kuka zauna yana gadi Ku kuma kuna wasa..

Ana cikin haka sai aka Kira sallah shi kuma sai yace kada Ku fita Bari yaje sallah daga haka ya wuce..

Fitar sa ke da wuya Alhaji Musa yazo don Daddy’n Ku ya Kira sa kan cewa zasu yi maganar kasuwancin su Amma yana zuwa kuka ce baya nan sai yace ina muke kuke ce ba kowa nan ya Fara holo an bar Ku a gida Ku kadai..

Haka ya zauna da Ku yana jiran sai Mun dawo ya tafi Amma sai yaga ba zamu dawo da wuri ba Hydar ko bacci yake ji sai ya sallame sa ya wuce ciki shima ya muku sallama ya tafi..

Bayan tafiyar sa bai wuce da 5mins ba wani ya shigo fuskar sa a rufe sai ya shiga time d’in anyi sujjada ba Wanda ya kalle sa nan yace,

“Ina iyayen Ku?”

” waye kai?Ba’a sani ba”.

Cewar Maryam

” ina wasa da ke?”

“Ban sani ba”.

Ganin rashin kunyar ta yayi yawa sai ya danne ta a wajen yayi raping nata ya gudu Amma duk kun zata Alhaji Musa ne alhali  Umman Ku ne ta tura sa gate man na ganin haka hankalin sa ya tashi ina dawa na gani nan na Fara kuka na tambaye Ku Waye yayi sai kuka ce alhaji Musa ne kawai yazo nan ko Daddy’n Ku na dawa ya kama mai gadi sai yace alhaji Musa ne kadai ya shigo haka ma ‘yan anguwa   shaidar da suka bayar kenan, nan aka kaita hospital  aka gyara ta Daddy’n Ku kuma yaje har gida yaci zarafin Alhaji Musa daga wannan lokacin bai bar shi ya sake mallakar biyar na kan sa ba..
STORY CONTINUES BELOW

Ranar da Baban ta ya fad’a mini gaskiya gudun kar na tona mata asiri a ranar ta mini allura”.
Back to story!!
” innalillah hakika Zulai ta cutar Dani ta kuma cutar  da iyalai na Allah ya Isa tsakani na da ita”.

“Gafarar alhaji Musa ya kamata ka nema Tun wuri saboda a kan ka al’umma duk suka guje sa har aka Kore sa a anguwan da yake gudun kada ya lalata musu yara”.

” in sha Allah Zan nemi gafarar sa don na cutar da shi da iyalan sa Tun ba ma ‘Yar sa ba”.

Shiru Hydar da Aunty Zainab suka yi nan Abba ya fita Hydar ko ya kwanta a cinyar Ammie yana jin zuciyar sa na Zafi yanzu don fansa har Umma zata sa ayi raping na sister’n shi sannan ta bata ma Baban Hafsat suna…

Daddy yana fita direct gidan su Hafsat ya nufa inda a k’ofar gida ya tarar da Abba..

Hannu ya mika masa suna gaisawa Abba ya cigaba da tafiya nan daddy ya sha gaban sa yana fad’in,

“Dan Allah ka aramin lokacin ka”.

” gaskiya banda lokacin ka”.

“Dan Allah fa nace”.

” sai dai ka jira in na dawo daga kashere”.

“Allah sa lafiya”.

” lafiya zanje wajen Shamaki ne”.

Yana gama fadar haka ya cigaba da tafiya saboda alhaji Shamaki yazo Nigeria kuma akwai wad’an su ayyukan da yake a kashere yasa shi ce ma Abba su had’u a can..

Mota Daddy ya tayar inda ya sha gaban Abba yace,

“Shiga muje nima wajen sa zani”.

Shiga Abba yayi yana fad’in,

” in ma cutar da ni zaka yi Kai da Allah “.

Shi ko Daddy bai ce komai ba suka dau hanyar kashere..
Sun sha tafiya dai-dai gwargwado kan suka Isa nan Abba ya fad’a masa inda zasu samu alhaji Shamaki..
Ba k’aramin mamaki yayi ba ganin su tare nan ya mika musu hannu yana murmushi suka zauna aka kawo musu kayan tabawa Amma tsam Abba yaki sakin jikin sa ganin Daddy na wajen..

Alhali Shamaki ne ya kalle su gaba d’aya cikin zolaya yace,

” Ashe Kiyayyar ta kare banda labari?”

Da wuri Daddy yace,

“In sha Allah ta kare kuma baza ta kuma faruwa ba”.

” to Ai ya kamata nima naji sanadin Kiyayyar ko?”

Nan Daddy ya kwashe komai ya fad’a masa sosai Abba yayi mamakin jin Daddy yace sharri aka masa wato ya gano gaskiya kenan..

Kallon Abba yayi yace,

“Hakika bani da bakin baka hak’uri ka hakura,nine nan sanadin talautar da Kai saboda daga lokacin da muka raba dukiyar mu kowa ya Fara kasuwancin sa Bayan faruwar haka ni ne nasa barayi suka kona shagunan ka sannan suka shiga gidan ka suka yi fashi sai na ranta maka kud’i shima da ka Fara kasuwanci na wargaza sai na Fara binka akan ka biya ni bashi na Wanda shine  sanadin had’a yaran mu Aure”.

” alhaji Munir wannan wace irin kiyayya ce?”

“Wallahi Shamaki kar kaga laifi na laifin mata ta ce kuma kasan Abu in da mata a ciki sai Allah ya shirya”.

” wannan haka ne”.

“Dan Allah Kayi hak’uri mata ta ce take zuga ni yanzu mu manta komai mu koma kamar da na maka alkawari Zan maido maka duk dukiyar ka”.

STORY CONTINUES BELOW

Abba yi yayi kamar baya jin su sanda Daddy ya durkusa a kasa ya had’a hannun sa yana pleading nan alhaji Shamaki yasa baki sai Abba yace,
” Allah na son masu hak’uri don haka ya yafe maka,kuma Ai dukkan mu tazo ta d’auki fansa a kan mu don haka baka da wani laifi,kuskuren ka d’aya shine ka biyewa mace”.
“Na gode sosai”.

Nan ya rungume shi Ai sai suka koma hira da dariya kamar ba su ba kace basu ta’ba batawa ba nan alhaji Munir yace,
” Kun ga dai Hafsat ‘yan uku ta Haifa don haka sunayen mu za’a sa musu saboda yaran nan rahma ne sanadin su ne komai ya dawo dai-dai “.
” ni dai in har aka yi huduba da sunana na daukewa Hydar sayan komai ni zanyi ma Takwara na har shanun suna”.

Cewar Shamaki.
“Ai ko nima dole nayi ma nawa Takwaran”.

Inji alhaji Munir

Sai Abba ko yace,
” Nikam kaza Zan yankawa Takwara na”.

Nan duk suka kwashe da dariya sai Daddy yace,

“Ai takwaran ka zai fi kowa jin dad’i tunda duk dukiyar ka a hannu na yake”.

Haka suka ringa hira kamar kar su rabu nan alhaji Shamaki ya Kara ma Abba jari sannan suka kama hanyar gombe cikin farin ciki..
Daddy na dawa yace ma Hydar ya musu Takwara su uku sosai Hydar yaji dad’i sai ya wuce wajen Hafsat domin fad’a mata..

Komai da komai ya fad’a mata har sanadin Kiyayyar nan ko tayi hawaye ta ringa jin dad’i har tace Mi shi d’azun Aisha da Abdool suka zo Amma Umma bata nan nan ko ya kalli yaran sa ya fita..
Aisha har gida tazo ta nemi gafarar Daddy nan ya yafe mata don shima ya San ta wani wajen yana da laifi daga nan kullum sai tazo ta rike yara..
Saudat kam kullum vedio call take musu don ta ringa kallon yara saboda ita sai Ana gobe suna zata zo..
Batun case na Umma a court kuma har yanzu Ana cigaba da sauraro..

*Ranar suna yara suka ci sunan su  Musa,Munir da kuma Mahmud inda aka sa ma Munir da Mahmud nickname Rafeeq da Ra’eez Hafsat ko tace ta zaba ma Abban ta sunan da za’a ke kiran sa da shi wato Sultan..
Sosai ake tabka rawar gani a sunan kusan competition ake kowa burin sa nasa yafi yawa iyaye mazan nan abun sai shiru haka ma Ammie sai su Aunty Zainab da Maryam da ran suna suka zama tamka frnds na Hafsat sai zolayar ta suke suna fad’in,

” in Kika Kara haihuwa sau uku dai gidan nan zai cika”.

Ita ko sai dariya ga saudat tazo in ka ganta da Aunty Maryam bara kace sun ta’ba samun matsala ba haka ma Aisha..

Bangaren Hakeela ma ba’a bar ta a baya ba sai dai ba zata had’a kanta da yara uku ba sosai iyayen ta suka mata kaya don ita d’aya gare su haka ma Daddy da Hydar sun mata sosai da su Aunty Maryam..
Hidima sosai suka yi abun ba’a fad’i komai dai Masha Allah Amma ranar kowa ta kansa yake don jama’a Ammie ce kadai bata zo ba gudun halin Umma kada ta ganta..
Daga yadda aka yi ma Hafsat kaya Umma sai suma take kamar zata hadiye ranta…
Bayan suna kuma ‘Yar Hakeela ta Fara zazzabi sai aka ce kada ta fita da ita ta Bari sai taji sauki sai ta tafi goyon gida sai Hajiya Nenne tace Hafsat ta jira ta su tafi Rana d’aya..
Daddy ya nemi gafarar Hajiya Nenne abun ka da uwa nan da nan ta yafe masa..
***************

STORY CONTINUES BELOW

Hafsat ce zaune a falo tana breastfeeding na Sultan Aunty Balkee ko na kitchen sai Saudat ce rike da Rafeeq Ra’eez kuma na kwance gate man yayi sallama suka amsa..

“Maman ‘yan uku an wuni lafiya?”

“Lafiya kalau Baaba ya aiki”.

” aiki da godiya ga wannan Wai a kawo miki”.

“Ohk na gode”.

Daga haka ya sallame su ya fice..

Gift’s ne na gani na fad’a masu kyau sosai ko wanne guda uku kenan kowa da nasa sai frames na love iri-iri.

A jikin gifts d’in an rubuta

” from father of your children to his babies”.

Sosai tayi murmushi ga flowers dayawa iri-iri a zuciyar ta tace,

“Wato har yau ba zai daina tura musu gifts ba ko”.

Saudat ko cewa tayi,

” sai kace a kansa aka Fara haihuwa “.

Su Aunty Balkee kam sun Saba..

Bayan Hydar ya dawo gida yayi wanka sai Hafsat ta nufi d’akin sa da Sultan a hannu tana shiga shi kuma yana share jikin sa sai yace,

” na Lura fa kin fi son Sultan nan Bari su girma zance Wa su Rafeeq ba ke bace mum nasu ke Step mum ce “.

Murmushi tayi tana fad’in,

” Ai dole nafi son shi,uba wasa ne?”

“To nawa uban fa?”

“Kaga nifa duk ina so tunda yaran naka ne”.

” ko ke fa?”

“Ashe dama haka ka iya kalaman so shine baka ta’ba fad’a mini face to face ba?”

“A ina Kika ji?”

Ya tambaya yana karban Sultan

“Wad’an da ka tura d’azun, wani I can’t live without you you are my life my everlasting blah blah”.

” ni kuma?”

Cike da mamaki tace,

“Ehh mana Kai ka Saba tura mana gift’s Ai”.

” je ki kawo na gani”.

Mik’ewa tayi tare da d’auko masa yana ganin kalaman soyayyar da aka rubuta kishi ya rufe sa nan take ya Fara had’a zufa..

“Hafsat bani na turo ba”.

” who could it be?”

“I don’t know”.

Nan ya Kira gate man ya tambaye sa waya basa sai yace wani ne ya tsaya a k’ofar gidan ya sauke glass na motar sa amma bai gansa ba sai ya bayar Wai a bama Hafsat..

Bin komai yake cikin nitsuwa nan yaga an rubuta phone number da kuma if you care call me nan take ya d’auki wayar ta da ya saya mata time da ta haihu yasa number’n sai tace,

“Pls kar ka Kira”.

Cikin bacin rai yace,

” Ashe dai kin San Wanda ya tura Miki tunda baki son na Kira”.

“Ai da na sani bazan kawo maka ba,fyn call Him or her”.

Dialing number’n yayi Ana receiving yaji ance,

” hello”.

Sai ya kashe ya dube ta yace,

“Ashe fa Sulaiman ne yake mana wasan nan cuxx muryar shi naji”.

Jin ya ambaci sunan Sulaiman sai gaban ta ya fad’i,

” kin San baya Nigeria shiyasa ya turo ma babies nashi gifts “.

STORY CONTINUES BELOW

Ita dai yake kawai tayi don tasan dole akwai abunda Sulaiman yake nufi sai ta yanke shawarar fad’a ma Hydar abunda ke tsakanin ta da Sulaiman nan Kira ya shigo wayar kuma number’n Sulaiman ne sai Hydar yasa a hands free Sulaiman ko cewa yayi,

” hello baby na kina tunanin Zan manta da ke ne Bayan yadda na so ki amma don butulci Kika auri aboki na,da naso na manta da ke but ba Zan iya barin yara na a wajen ki ba”.

Da wuri tace,

“Yara, wani yara?”

“Kin San me nake nufi kin manta sanda Kika zo waje na muka shashe Hydar kuma Kika ce masa kidnapping naki aka yi,ina fatan kin tuna mai ya faru a tsakanin mu”.

Cikin takaici tace,

” Allah ya Isa mugu azzalumi”.

“Koma mene ne ki fad’a yara dai zanzo na d’auka don ba Zan bar ma Hydar ba gwara ma in d’aya ne”.

Fusge wayar a hannun Hydar tayi nan ta kashe wayar shi kuma wawan Mari ya debe ta da shi har uku yana fad’in,

” ni zaki ci Amana,muguwa azzaluma ya wuce ke,kin sani rainon cikin da ba nawa ba”.

Ciki tsantsan bacin rai tace,

“Hydar kar ka kuma furta wannan Kalmar a bakin ka na cewa yara ba naka bane”.

” na fad’a ba nawa bane shegu ne”.

Rintse idanun ta tayi tace,

“Kai ne na miji da ya Fara sani na a matsayin ‘ya mace a duniya kuma Kai kan ka kasan da haka”.

” karya kike nasan me Kika sha”.

“Hydar ka daina jifa na da mugayen kalamai”.

” an jefe ki waya San maza nawa Kika yi amfani da su da Aure na a kan ki,kila shi da yace yaran sa ma ba nasa bane na wani ne,yaran shegu”.

“Enough tace gami da debe sa da Mari tana hawaye ta nuna sa da yatsa tace,

” idan ka kuma sheganta mini yara sai na maka Wanda yafi wannan “.

” ahh Kika mare ni yau ko Zan kusan kashe ki”.

Nan ya ringa kwala mata Mari har ta fad’i a kasa sultan kuma sai kuka yake haka Hydar ya fice ya barta a kasa komai na duniya ya mata nauyi…
Hydar ji yake kamar dutse aka sa masa a kirjin sa gaba d’aya ya tsani kansa nan ya tuna time da suke gidan can yaga wasika a bag nata kuma akwai Randa wani ya Kira ta wato duk Sulaiman ne..abokin sa na cin amanar sa tare da matar sa har ciki suka yi tare..

Sallah magrib yayi inda yana dawa gida yaga Sulaiman a tsakiyar gidan tare da Umma yana rike da yarinyar Hakeela wacce ake kiran ta da  Ashfat..

“Ah tabarkallah yarinya ta girma a bani yara na kuma na gansu”.

” Haba Sulaiman Ai yaran Hydar da na Khaleel duk d’aya ne akan me zaka bambanta su?”

“Nifa biological yara na nake nufi, Ai yaran Hafsat bana Hydar bane”.

Wani irin fadiwar gaba Umma taji lallai abunda basu yi tunani ba luck zai yi favoring nasu.

” yaran ka?”

“Ehh ga Hakeela tambaye ta Ai ni Hafsat take so Tun farko”.

Murmushi Umma tayi gami da karban Ashfat tace,

” jeka suna wajen uwar su Ashe yara kam shegu ne an tsaya Ana nuna musu Gata”.

Aiko apartment na Hydar ya nufa da wuri Hydar ya rufa masa baya haka ma su Umma yana shiga yaga Rafeeq kwance a kujera sai yasa hannu ya d’auka sannan ya nufi fita da wuri Hajiya Nenne ta sha gaban sa tana rike da Ra’eez tace,

STORY CONTINUES BELOW

“Malam ya dai?”

“Yara na ne Ai”.

Hafsat na kuka a d’aki ta d’auki sultan ta fito ta sha gaban sa tace,

” ajiye mini da na”.

“Dan mu dai”.

Aunty Balkee ce ta wanka masa Mari tana fad’in,

” you will never mind your ways ko?”

Ko a jikin sa sai ma k’ok’arin fita da yaran da yayi nan Daddy ya shigo sai ya iske mummunar labari nan yace a zauna ayi magana..

Bayan sun zauna ne ya dubi Hafsat yace,

“Waya buge ki a fuska?”

“Hydar”.

Girgiza Kai Daddy yayi don ya San Dole Hydar ya mata haka tunda ance yara ba nasa bane..

” Sulaiman for how long ka San Hafsat? “

“Shekaru da dama,kuma nine nan na Kai goro a kanta don son abun duniya aka bama Hydar”.

” Hafsat abunda ya fad’a gaskiya ne?”

Kai ta d’aga alamar ehh sai Daddy yace,

“Randa aka yi kidnapping nashi shi ya d’auke ki ne?”

“Ehh amma…”
“Daddy meyasa kake tambaya, yaran sa ne shegu ita kuma Yar iska”.

Cikin tsawa Daddy yace

” ka Kara magana Hydar Allah ya Isa”.

Kowa a wurin jikin sa mutuwa yayi jin tace shi ya d’auke ta Gashi ta kwana tabbas zai yi wu yaran sa ne.
“Yanzu Sulaiman abunda nake so da Kai kaje gida gobe sai ka dawo tunda dare yayi”.

” nifa ba inda zanje sai da yara na,don Zan Kai ma mahaifiya ta jikan ta”.

Kowa gidan ya rasa meke masa dad’i Hydar kam tsanar Hafsat yayi kamar ya kashe ta da kyar Daddy ya lalla’ba shi ya tafi Hafsat kuma ta kwana kuka Hajiya Nenne da Aunty Balkee na rarrashin ta Hydar ma bai yi bacci ba.
Asuban fari Sulaiman ya dawo gidan ganin da gaske yake Gashi son yaran ya shiga zuciyar Daddy sai yace da Sulaiman ya Kira iyayen sa nan ko suka zo aka had’u a main falo Bayan sun gaisa sai Daddy yace,

“Shin ko kun San abunda ke tsakanin Sulaiman da Hafsat?”

“Budurwar sa ce da ita zai aura amma ba rabon sa bane,Bayan tayi Aure sai muka zaba masa mata muka tura sa can Amma da yaje ba abunda yayi sai fitsaranci ta hanyar nuna ma yarinya da iyayen ta shi mutumin banza ne don haka suka ce ba zasu bashi Yar su ba sai ya dawo Nigeria sati biyu da suka wuce,maganar da nake maka yanzu haka munyi disowning nashi Amma da yace mana yana da d’a sai muka zo don jika abun so ne”.

” shin har Bayan auren ta suna tare?”

“Gaskiya bamu sani ba amma Randa zai tafi ya shigo a rikice ba Wanda ya sallama ya tafi”.

Shiru Daddy yayi kowa a wurin na zuba ido sai Baban Sulaiman yace,

” in kuma bata bamu jikokin mu ba ko court ne sai Mun Kai ta”.
Ganin abun ba wasa bane yasa dole Daddy ya yanke shawarar kiran Abba ya fad’a masa don su San nayi aiko Abba naji saura kadan ya mutu sai ya kalli Sulaiman yace,

“‘Yata ba Yar iska bace bata ta’ba zina ba kuma ba zata ta’ba ba,alhaji ka dubi kama da yaran nan suke da Kai mana in ba jinin Hydar bane zasu yi kama da Kai ne?”
“Ba wani don sunyi kama da shi ba yana nufin jikokin sa bane ko wani mutum a duniya yana da mai kamannin sa kuma Wallahi zuwa gobe in ba’a bani jikoki na ba Zan buga Ku a court”.

STORY CONTINUES BELOW

Cewan Baban Sulaiman Hafsat ko a wajen ta durkushe tana fad’in,

” Wallahi Abba ba yaran sa bane na Hydar ne “.

” kada na Kara jin suna na a bakin ki in ba haka ba…”

“Hydar ban hana ka ba?”

Daddy yace nan yayi shiru..

A Washe garin kuma aka maka su a court nan cikin Tashin hankali Abba ya Kira alhaji Shamaki ya fad’a masa ba k’aramin bakin ciki yayi ba don shima yana son yaran tunda akwai takwaran sa kuma Ai bayi da jika sai yace ma Abba Gashi nan zuwa Nigeria a ranar..
Hafsat ko ta daina cin abinci gaba d’aya ta lalace yaran ma basu samun ruwan nono sosai haka ma Hydar baya ci duk yayi baki..
Kamar yadda Alhaji Shamaki ya fad’a haka ko ya diro shi da Lawal nan suka ga Sulaiman kam da k’arfin su shi da iyayen sa sai alhaji Shamaki yayi gyaran murya yace,

“Dukkan Ku ya ishe Ku haka, yara dai in ma naku ne za’a gane saboda nazo da doctor kuma za’a yi DNA test a gani..
” Alhamdulillah “.

Sulaiman yace jin haka sai duk jikin su ya mutu nan aka d’ebi jinin yaran da na Hydar da kuma Sulaiman duk suka tafi hospital..
Dukkan su suka shiga lap din don kowa ya gani da idon sa,Bayan result ya fita sai doctor’n yace,

” wane ne ya raini cikin har ya girma? “

“Hydar”

“Waya sa musu suna?”

“Hydar”.
” innalillah Abu ya baci ma

Sulaiman  saboda jinin Hydar ne positive na Sulaiman negative “.

Kowa alhamdulillah yake fad’i Hydar bai San sanda yayi murmushi ba Sulaiman ko cewa yayi,

” Wallahi karya ne kun had’a baki da doctor ne”.

“Fine Mun baka nan da 1 hour ka kawo doctor”.

A jin haka sai ya Fara Neman doctor ido a rufe ya ringa zaga hospital da kyar ya samu wani Christian ya had’a baki da shi suka zo..

Shima godawa yayi nan yace,

” Hydar ne Baban yaran sannan yace da Sulaiman

“Bana irin wannan harkan aiki nake ba  business “.

Nan ya tafi Hydar ko ya shake Sulaiman yana fad’in,

” wani irin Mara imani ne Kai,Kayi koyi da Hakeela mana nasan tana so na Tun ban auri Hafsat ba amma da na Aure ta sai ta hakura “.

” ka bar sa ya Hydar rashin tawakkali ne”.

Cewar Hakeela

Nan yace

“Ai bakin mu d’aya ita ce ma ta fad’a mini yadda zanyi saboda ka sake Hafsat na Aure ta”.

Duka Hydar ya ringa Kai masa a karshe yayi handling nasa ma police suka nufi gida Hakeela na jin kunya da kuma da na sanin abunda ta aikata..
**jama’a so fa ba hauka bane,in kaga ko Kika ga baki auri mutum ba to da can you are not destined to be together*

Suna komawa gida Hafsat tace,

” Aunty had’a mana kaya na Bari na had’a nasu sultan sai mu tafi gida..
Kayan su suka had’a tsab Saudat kuma ta Kira driver’n ta yazo ya kaisu gida Hajiya Nenne sai hak’uri take bata Amma taki..
STORY CONTINUES BELOW

Ganin haka sai Hajiya Nenne tace Hakeela ce munafuka ta tattara ta bar gidan tunda mai gaskiya ma zata tafi nan ta tattara ta tafi Hafsat ko ta sallami Baaba Ladi suka tafi..
Suna tafiya police suka shigo nan akayi arresting Umma za’a yi jailing nata for 6yrs ba tare da bail ba..

Ana arresting nata Daddy ya bata takardan saki sai tayi murmushi tace,

Dukiya dai nawa ne”.

Nan ya Kira Hydar sai taga komai da sunan Hydar ne sai ya fad’a mata yadda aka yi hakan ta faru sannan aka tafi da ita..

*Kunga dai yadda karshen Umma ya kasance a duniya,ita ba miji ba ba dukiya ba ba yara ba,don Allah mu rage son abun duniyar*

Bayan tafiyar su da 2days sai Hydar ya gama gathering courage ya nufi gidan su domin bata hak’uri Amma a k’ofar gida yaci karo da Sis Faty Bayan sun gaisa sai yace,

“Hafsat fa?”

“Bata gida tana asibiti yau kwanan su biyu”.

” innalillah kenan Tun Randa suka dawo Waye ba lafiya? “

“Ita”

Nan ya tambaye ta sunan hospital d’in sai ta fad’a mishi cikin Tashin hankali ya nufi hospital din har room da take ya Isa sai yaji irin doctors masu mita kuma they don’t care tana cewa,

“Patient nan fa suna wasting time nasu ne kawai cuxx she will not survive”.

Wani irin tsara kansa yayi sai ga Saudat ta fito daga d’akin tana kuka kamar ranta zai fita nan ya lek’a room d’in sai yaga Hafsat jini ta baki da hanci har ma da kunne sannan Ana Danna mata irin abunda ake sawa mutum a kirjin sa when he is fighting for his life sai ya mik’e ya koma sai kawai yaji hawaye na zuba masa Ana cikin haka sai ta daina motsi nan ko suka barta da wuri ya tare su yana fad’in,

” doctor please help Wallahi ko nawa ne Zan bayar”.

“We are sorry sai dai mu jira time na cikawar ta don heart nata yana barazanar daina bugawa shiyasa kaga ta gagara controlling har kaga jinin na fita ta ko ina she just can’t make it don zuciyar ta kadan kadan yake bugawa “.

Hannu yasa a Kai sai ga hawaye a idon sa ya share yace,

” pls just help her”.

“Sorry Sir wannan fa she can’t make it hall da yake heart nata ne yaja mata”.

Daga haka ta wuce shi kuka Saudat kuka Aunty Balkee duk hawaye suke Ana cikin haka sai ga wani Babban doctor ya shigo Wanda sai Bayan 6 months yake zuwa don a abroad yake da zama da wuri doctors din suka nufe sa suna fad’in,

” sir akwai Wata patient wacce shi can’t make it but her husband keep pleading “.

” lemme see her”.

Nan ko suka je yana ganin ta ya dafa kafad’ar Hydar yace,

“Sorry sir she can’t make it saboda heart nata yana reading saura 3hours ya daina aiki”.

Zare ido yayi yace,

” pls you should help her within this 3hours”.

“A gaskiya bamu da equipment na treating nata a nan”.

” sai a ina?”

“Abroad ne kuma daga nan zuwa wajen 6hours ne kaga before mu Isa ma she is no more”.

” na yarda pls doctor muje Zan nemi private jet na Baba na”.

“Zaku yi asarar kud’in Ku ne fa”.

” yah I don’t care “.

Nan aka Fara shirye-shiryen tafiya ba abunda suka d’auka inda aka tafi da aunty Balkee da kuma Saudat sai Hydar wad’an da suke hospital d’in dai nan aka bar ma Maama da Sis Faty yara..
Kamar yadda doctor ya fad’a suna cikin tafiya suka ji oxygen nata yayi Kara nan doctor’n yace,

” I told you, she is no more “.

Da gudu Hydar yaje wajen ta sai yaga idon ta a rufe da alama ta ido ranta ya fita ya d’aga hannun ta sai yaga ya sake ga oxygen d’in straight line ya nuna alama bata numfashi nan ya sake kuka mai cin rai doctor’n kuma ya rufe ta yana fad’in,

” in munyi landing sai Ku koma don a mata sallah da wuri may jannatul Firdaus be her final destination “.

Kuka sosai duk suke yi.

*Innalillah😭😭😭kullu nafsin za’ikaatul maaut,Wannan ita ce karshen Hafsat kuma Dan Allah kada kuji haushi na don ko wace rai dole ta dandani mutuwa Allah ya jikan ta da rahma Ku sata a addu’ar Ku pls*😓…

Suna landing aka Kira doctor daga Nigeria kan cewa akwai patient ya shiga jirgi yazo ko nawa ne za’a biya sai yake nuna musu zai yi wuya ya juyo cikin 30mins nan suka ringa jayayya..

Hydar ko tunawa da bakin cikin sa ta mutu sai ya Kara kuka da wani ido zai kalli yaranta..

Ganin su Hydar zasu koma sai ya yanke shawarar bin su yana shiga jirgi sai yaga kamar hannun ta na motsi nan yaji tana numfashi a hankali sai ya Kira ambulance aka nufi private hospital nashi da ita Hydar da Aunty Balkee kowa sai goge juna yake basu damu da cewa su surkai bane..
Kiran Nigeria doctor yayi yace musu ba zai samu dawa ba nan aka Fara ma Hafsat aiki successful ta dawo kan rayuwar ta..
*Kada wacce taji haushi na don nace ta mutu🤨nima a tunani na mutuwar tayi*..
Bata farfad’o ba sai Bayan 2 day’s tana farfad’o Wa kuma ta Fara kiran sunan yaran ta duk da taga Hydar kusa da ita amma ko kallon sa sau biyu bata yi ba sai yace,

“Suna gida”.

” ba Kai na tambaya ba kuma Aunty ban yafe ba Hydar ya ta’ba mini yara ko Bayan rai na ne”.

“Hafsat”.

” Aunty na tabbata Allah ya tashe ni ne don na fad’i wannan wasiyar”.

Sabon Tashin hankali ya shiga jin furucin ta a haka ya daina shiga d’akin har suka yi 2weeks suka koma Nigeria..

Ido biyu Hafsat ta Hana Hydar ganin yara kullum sai yazo Amma baya ganin su sai dai in ta shiga wanka ne sai a Kai masa su ya gansu kan ta fito a haka har yara suka yi 4 months taki komawa ganin da gaske take sai yasa iyaye shiga lamarin Amma tace Aure tsakanin ta da Hydar ya kare yara kuma nata ne ita kadai  jin haka sai yasa Ammie da kanta ta shirya taje har gidan don yanzu ta koma gidan Daddy nan ta ringa rokon Hafsat da kyar ta yarda ta koma..

Randa ta koma bakin Hydar har kunne haka ya wuni wasa da yara don yanzu sun girma ita ko aiki take sai dai yayi ta satar kallon ta ganin ba zata sake fuska ba sai ya rike hannun ta yace,

“I am sorry baby wallahi kishin ki ne ya sani haka”.

” Zan yafe maka Amma ya zama karo na karshe “.

” in sha Allah “.

Murmushi tayi sai yace,

” I love you “.

” I love you to”.

Daga wannan ranar suka koma rayuwa cikin farin ciki Abba ma ya saya gida mai kyau Sis Faty kuma tayi Aure har Aunty Balkee ta koma Ammie kuma ta gama warkewa gidan Ana farin ciki sosai inda Khadija ma tayi hankali Khaleel kuma ya shiryu don wa’azin da Ammie ke masa tunda mai barin sa ko oho bata nan da kyar ya yarda ya dawo da Hakeela inda ta nemi gafarar Hafsat suka koma normal….

Gidan dai yanzu sai abunda Hafsat tace don kaunar ta da Ammie take..

Su Saudat ma sun haihu Saudat mace ta Haifa Aisha ma haka..

*ALHAMDULILLAH*!!

*Duka-duka nan na kawo karshen wannan littafi na Kiyayyar Zuciya Kuskuren da nayi Allah yafe mini,na gyara kuma Allah sa wasu su dauka su gyara halin su*..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *