KOMA KAN MASHEKIYA CHAPTER C KARSHE

 KOMA KAN MASHEKIYA CHAPTER C KARSHE

Ahmad ganin ta samu sauki ya sa ya mike ya fadawa Ibrahim yanzu zai dawo.

Wajen Dady ya nufa. Dady na gida zaune a falo shi da Mami sai Na’ima.

yana zuwa ya sawa Dady kuka.

Dady ya hau tambayar sa lafiya.

Ya ce,

“Dady Meenal ce ba lafiya.”

Nan ya kwashe komai ya fada masa. Yana fada wa Dady.

Mami kuwa budar bakin ta sai cewa tayi,

“Ba wani ciwo sun je sun kama wata ne, an yi magani abu ya dawo kan ta.”

Na’ima da ke zaune gefen ta, ta ce,

“Kai Mami dan Allah ki bar maganar nan gwara a tsaya ayi bincike aga gaskiyar me yake damun ta in ya so sai ki magana.”

Mami ta ce,

“Ke dallah rufe baki. Wane irin bincike za’ayi bayan kowa yasan su waye su. Da farkon dai tin da akai auren nan ba ko barin wata bare ciki abu fiye da wata bakwai da aure fa. Gashi nan taje ta jawo wa kan ta jaraba ai, in kuwa ta warke shi zata kama.”

Dady dake kallon ta rai a bace ya ce,

“Abinda nake so dake Hajiya shine ki daina zargi akan abinda baki sani ba. Sannan kuma har yanzu kin ‘ki son yarinyar nan bayan kinsan Ahmad ba karamin yaro bane yaro ne mai hankali ya girma kuma yasan abinda yake dai dai. Na tabbata Amina babban rabo ce gare mu kuma sai kinyi alfahari da ita na tabbata.”

Mikewa Mami tayi ta ce,

“Nifa bazan iya cigaba da zama da yarinyar nan ba wata rana a kawon gawar ‘dana ba.”

Na’ima ma mikewa tayi ta ce,

“Haba Mami nifa abin nan yanzu na saduda ya kamata, mu daina sa musu ido mu barsu su shakata dan Allah mu daina takura musu, haba Mami daman ance *duk abinda kayi kaima sai an maka.* domin ni shaida ce,”

“Dallah can yi min shiru shashasha sakarya. Mayun kuke so to kuje sa cinye ku gaba daya.”

Tayi cikin daki.

Zama Na’ima ta yi ta ce,

“Dady to yanzu mene abin yi.”

Dady yace,

“Bari na kira Malam Tanimu.”

Dady ya kira shi sai cewa yai baya gari amman anjima zai dawo zai shigo insha Allahu.

Haka akayi kuwa da magariba sai ga malamin har gida wajen Dady.

Dady da kansa ya dauki mota suka nufi gidan Ahmad a daren.

Amina kuwa tana can ta tashi kamar ba ita tayi ba dan har ta gyara gidan ta musu girki.

Tai wanka tai kwalliya kamar yadda ta saba. Tana zaune a dakin ta Yaa Ahmad ya shiga.

Kallon ta yayi cikin so da kauna ya ce,

“Meenal kizo Dady na kira.”

Da sauri ta mike tana cewa.

“Lah Dady ne ya zo.”

Hijab ta saka, suka fito a tare. Tana ganin wannan malamin taji juwa na dibar ta.

Da kyar ta iya karasawa gefen Dady kafin ta gaishe shi ta zube agun.

Murmushi Malamin yayi,  Ahmad ya kalla ya ce dauko ruwa. Tofi yayi a cikin ruwan ya watsa mata.

Wata kara ta saki. A ruwan ya karayin wani tofin ya kara watsa mata a fuskar ta.

STORY CONTINUES BELOW

Ihu take tana cewa

“ku taimake ni zai kona ni dan Allah ku taimaken, ku taimakan ku daina kona ni.”

Malamin bai tsaya ba har sai da yayi tofin nan sau hudu sannan ya watsa mata ruwan a jikin ta.

Wata kara ta karayi mai gigita kunnen jama’a.

Ahmad ya kalla ya ce,

“Samo mana garwashi.”

Da sauri Ahmad ya fita yaje bakin titin unguwar su inda ake sai da nama da dare.

Garwashin ya amso ya dawo gida. Wani kullin magari ya dauko ya saka.

Take Amina ta fara mimikewa, tana ihu kamar wacce ake kona jikin ta.

Malamin be kyale ta ba ya kuma yin tofi cikin ruwan ya kara wasta mata a fuska.

Ihu take tana neman a gaji. Sai da malamin ya tabbatar da ya ba ta wahala sannan ya ce,

“Me baiwar Allahn tai maka ka shige ta.”

Cikin rawar murya ya ce,

“Wallahi aiko ni aka yi. Dan Allah ku taimakan wallahi zan tafi bazan kara zuwa gare ta ba. Ku rufan asiri.”

Tofin Malamin ya rakarayi ya zuba mata ruwan wata kara ta kuma yi ta ce,

“Wallahi gaskiya na fada maka wallahi aiko ni akayi.”

Malamin ya kuma watsa mata ruwan addu’ar da yayi.

Sosai take kuka tana neman agaji sai da malamin yasan yaiwa aljannin abinda bazai kara kawo shi jikin Amina ba sannan ya bashi damar ya fita.

Wata atishawa tayi wacce tin tana kwance sai da ta dago dan azaba.

Tana yi kuma ta koma ta kwanta kamar wacce ba laka a jikin ta.

Wata kulba malamin ya fito da ita ya mikawa Dady ya ce,

“Tana shafa wannan a jikin ta. Ya mika masa wani kullin magani ya ce tana turare da shi.”

Ahmad, Dady ya mika wa, sannan malamin ya ce,

“Sannan ta rike azhkar na safe da yamma. In zata kwanta bacci tana alwala.”

Kai Ahmad yake gyadawa. Malamin ya cigaba da bayani,

“Ko bandaki zata shiga tana sitirta jikin ta haka nan tana yawan yin nafulfuli da azumi dan duk kariya ne daga shaidanu.”

Godiya Ahmad yai wa Malam Tanimu. Dady ya ce,

“Kai ta daki.”

Daukar ta yayi ya kai ta daki. Sannan ya dawo ya raka su Dady mota yana kara musu godiya.

Bacci Amina ta dinga yi wanda ba ita ta tashi farkawa ba sai asuba.

Ahmad kuwa zama yayi yana gadin ta dan kar wani abu ya same ta.

Kiran sallah da ya ji ne yasa ya tafi massalaci.

Sai bayan ya dawo ya ganta akan sallaya, zama yai akan gado ya ce,

“Meenal kin tashi ya jikin?”

Murmushi tayi ta ce,

“Ya me yake damu na ne? Tin zuwan Dady ban kara sannin komai ba.”

“Kar ki damu. Ki kwantar da hankalin ki.”

Kai ta gyada masa.

Ya ce,

“Me kike ji yanzu?”

“Kai na ne yake ciwo kawai.”

“Sannu to.”

Ya mike ya fita. Kitchen ya shiga ya dafa ruwan zafi sannan ya soya kwai. A daining ya ajiye ya shiga daki ya tadda ta zata fito.

Kallon ta yayi cikin so da kauna ya ce,

“Ina zaki?”

“Break zan hada maka.”

Kai ya girgiza ya ce,

“Yau na hutar dake ki huta kinji.”

“Haba dai Yaya na barka da aiki kuma?”

“To mene dan miji yai wa matar sa aiki.”

“A’ah bari naje dai nayi.”

Kamo ta yayi suka koma ciki.

Zaunar da ita yayi ya ce,

“Na gama hadawa sai dai in wani abu kike so kuma.”

Kai ta girgiza ta ce,

“A’ah ba na bukatar komai. Nagode.”

“To kwanta ki huta.”

Ya fada yana kwantar da ita.

Jijigata ya dinga yi a hankali har ta samu tai bacci.

Ahmad ya jima zaune yana kallon ta yana tunanin wanda yai wa Aminan sa turen Aljjanu.

Can kuma sai abinda Dr ya fada masa ya fado masa.

To shi yanzu tayaya zai fara kusantar ta, shi bai san me yake damun sa ba.

Tabbas yana bukatar Aminan sa amman be san me yasa yake hana zuwa gare ta ba.

Mikewa yayi ya shiga ban daki ya fito ya shirya cikin bakar riga da dogon bakin wando.

Ya feshe jikin sa da turaruka masu dadin kamshi sannan ya koma falo ya share ya goge. Ya saka karatun Al kur’ani.

Ibrahim ya kira ya share sauran dakunan da ban daki. Duk da ba wani datti sukai ba.

Turaren wuta ya juna dakin ya dinga fitar da kamshi me dadi.

Sai karfe goma Amina ta tashi. Wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya cikin wani purple din riga da siket yan kanti.

Hula tasa akan ta bata yi wata kwalliya ba daga hoda sai kwalli da man lebe.

Turare ta fesa, sannan ta fito falo. Tin daga kofar falon ta take jiyo kamshin turare.

Murmushi tayi ta ce,

“Yaa Ahmad kenan.”

Ahmad ta gani zaune akan kujera yana bin karatun Al kur’ani.

Karasawa tayi ahankali ta zauna a gefen sa. Rumgume ta yayi yana saukar da wata irin ajiyar zuciya.

“Ina kwana?”

Ta fada cikin rada.

Tsigar jikin sa yaji tana tashi ido ya lumshe ya amsa da.

“Lafiya lou. Ya kika tashi ya jikin?”

Idon ta a lumshe ta amsa da

“Lafiya lou.”

“Tashi muje muyi break ko?”

“To ina Ibrahim.”

“Ibrahim ya jima da yi har ya tafi makaranta.”

“Allah sarki. Yaya dazu Naima ta kira ni take min ya jiki. Wai me ya faru ne?”

Allah sarki. Yaya dazu Na’ima ta kira tana min ya jiki? Wai me yake damuna ne?”+

Murmushi yayi ya ce,
“Eh ban fada miki bafa ko Na’ima ai tana gida.”

Ido ta zaro ta ce,
“Lafiya dai ko?”

“Ina fa lafiya. Wai Kanwar mijin ce da Maman sa suka mata sharri.”

“Allah sarki kuma shine yace ta taho gida.”
“Eh kinsan ba kowa ke zama yai tunani ba.”

“Allah ya dai dai ta toh.”
“Ameen!”

“Yaya baka fadan me yake damuna ba.”
“Tashi muje muyi break tukkunna.”
Mikewa tayi suka nufi daining sai da suka gama taga ya tashi ya fita.

Can bakin titi yaje neman garwashi sanna ya dawo. Tana dakin ta dan haka can ya nufa.

Turaren da mallam.ya bashi ya saka sannan ya dauko man ya murza a hannun sa ya shafa mata a jikin ta.

Kallon sa ta tsaya yi duk da kamshin abubuwan ba dadi to amman takasa fada masa bare ta tambaye shi.

Sai da ya gama ya dauke kaskon ya dawo sannan ta ce,
“Yaya wannan kuma na mene?”

Murmushi yayi ya zauna agefen ta ya bata labarin duk abinda ya faru.

Kuka ta fashe dashi ta fada jikin Ahmad. Lallai Ahmad me son tane da wani ne da gidan su zai maida ita ai mata magani.

Amman jibi yadda Dady da Ahmad suka tsaya akan ta wanda ko mahaifiyar ta ma bata sani ba.

“Menene na kukan kuma?”
Ahmad ya tambaye ta.

“Dole nayi kuka Yaa Ahmad da Allah bai bani kai ba da ba kowa ne zai dauki lalura ta ba. Maza nawa ne daga matan su sun fara rashin lafiya suke kai su gida amman jibi ni ku kuka tsaya a kai na har na samu sauki. Yaa Ahmad bansan da me zan saka maka kai da Dady ba. Lallai kai da Dady kun zame min uwa da uba ban da bakin godiya a gareku sai dai Allah yai muku fiye da abinda kukai min.”

Ta kuma fashewa da kuka. Dagota yayi yana goge mata ido yana mata murmushi wanda ke kara kwantar mata da hankali.

Ita murmushi tayi duk da hawaye na zubowa a idon ta.

Dariya yayi ya cee,
“Ina da albishir gareki amman ki daina wannan kukan na fada miki.”

Murmushi tayi ta goge idon ta. Ta ce,
“Ina ji?”

Ya ce,
“To albishirin ki.”

Murmushi tayi ta ce,
“Goro!”

Ido yayi waje dasu yace,
“Tab kaji wayoo. Ni Allah vana son goro.”

Dariya tayi ta ce,
“To ka zabi abinda kake so.”

“Yan biyu nake son ki haifar min.”
Ido tayi waje da su ta ce,
“Ta yaya zan samo maka yan biyu.”

Dariya yayi ya ce,
“Kawo kunnen ki kiji.”

Matsawa tai yai mata rada. Da sauri ta mike zata bar wajen.

Kamo ta yayi ya ce,
“Ina kuma zaki bayan ban fada miki abinda zan fada mikin ba.”

Fuskar ta a rufe da tafin hannu ta ce,
“Wallahi na gode ni kam bari na je na daura girki.”

STORY CONTINUES BELOW

Ta fada tana son tashi. Janyo ta yayi ta fada saman kirjin sa.

Wani yanayi suka fada gaba dayan su. Ido ta lumshe.

Hannu ya saka a aljihun sa ya dauko wasu makullai guda biyu ya ce
“Bude idon ki gani.”

Ido ta bude a hankali kan ta a saman kirjin sa.

“Ma kika gani?”
Ya tambaye ta.

“Makullai.”
Kai ya gyada ya ce,
“All are urs.”

Ido ta zaro ta ce,
“Ni!”

Ta fada tana nuna kan ta. Ya ce,
“Yes naki ne. Wannan na motar ki ne, wannan kuma na shagun kine dake kasuwa.”

Ido ta zaro ta rumgume shi tana mai sumbatar sa a a kumatu.

Kamkame shi tayi wanda shi Yaa Ahmad tini nutsuwar sa ta bar jikin sa.
Duk ta rikita shi, ido kawai ya lumshe yana jin wani abu na masa yawo a jikin ssa.

Shima hugging nata yayi ko zai ji saukin abinda yake ji. Amman ina sai daduwa da yayi.

Wani hali ya tsinci kan sa a ciki wanda ya kasa koda kwakwaran mosti.

Bakin ta ya fara laluba wanda yana caf kar sa, ya fara tsotsa sai kace wanda ya samu sweet.

Tini Amina ta sandare ta kasa ko da motsi saboda wani yanayi da taji ta a ciki wanda bata taba tsinyar kanta a cikin sa ba.

Ya jima yana kissing nata kafin ya daura hannun sa kan kirjin ta.

Wani laushi yaji wannan ya bawa hannun nasa damar latsawa a hankali. A hankali a hankali ya dinga latsa wa.

Amina kuwa yana latsawa taji kamar an janye numfashin ta an dawo da shi. Haka ta dinga ji a duk latsawar da zai mata.

Sai da yayi iya yadda yake so sannan ya sake ta. Zamewa tayi ta kwanta a kan kujera dan duk ba laka a jikin ta.

Shima gefen ta ya kwanta. Can kuma ya jata jikin sa ya matse ta kamar zai mayar da ita cikin ta.

Amina kuwa tana jin sa tayi shiru. Jijjiga ta yake yi a hankali, a ransa yana ji wani sanyi na ratsa shi.

Magana ya farayi a hankali ya ce,
“Meenal Ina sonki. ina kaunar ki, ke farin ciki. Meenal.bazan taba iya rayuwa bake ba. Kin zamo jinin jikina ni dake mun zama hanta da jini. Ina kaunar ki. Amman. Meenal ki yafe min nasan ina cutar ki kuma ina danne miki hakkin amman bansan ya akai haka ba. Bansan saboda me ba. Duk lokacin da naso kusantar ki sai naji kamar an cire min sha’awar hakan Meenal ki fahimce ni, ina son ki ina kaunar ki.
Meenal ki yafe min banyi haka dan na bata miki ko na cuceki ba. Dan Allah Baby ki fahimce ni.”

Dago ta yayi dan yaga a wane yanayi take. Sai dai yaga ashe tai bacci dan numfashin ta ne ke sauka a hankali a hankali.

Ya jima yana kallon ta kafin ya maida ta jikin sa ya rumgume ta. Daki ya kai ta ya rumgume ta.

Bacci suka kwanta me cike da mafarkai.masu dadi a xuciyar su.

Karfe daya da kwata ya farka, bandaki ya shiga yai wanka ya dauro alwala sanna ya fito ya tafi massalaci.

Bai dade da fita ba Amina ta farka itama ban dakin ta shiga tai wanka tai alwala ta fito ta canja shiga.

Sallah tayi sannan ta mike ta shiga kitchen.

Miya ta yi sai farar taliya da ta dafa ta soya musu kifi ta danyi farfesun sa.

Wani turaren wutar ta kuma junawa sannan ta koma daki.

Kwanciya ta kuma yi tana tuna abinda ya shiga tsakanin su da Yaa Ahmad dazu.

Da ta tuna yadda yake kissing nata da tabata sai tai saurin lumshe ido dan ji take kamar a lokacin yake mata.

Wata kunyar sa kuma ta kamata. Yaa Ahmad kuwa daga massalaci gida Mama yaje, ya fada mata duk abinda ke damun Amina.

Sosai hankalin Mami ya tashi amman sai ta nuna ba komai dan ya fada mata tin a jiya aka yi maganin matsalar.

Godiya Mama ta dinga yi dan daga nan cewa yayi taxo suje taga Amina ko hankalin ta zai kwanta. Amman Mama ta ce sam baxata je ba.

Addu’a dai zatai mata Allah ya bata lafiya ya kareta.

Haka Ahmad ya gama zaman sa ya tashi ya yafi.

Sai bayan sallar la’asar sanna ya koma gida.

Lokacin Amina na zaune rike da Alkur’ani tana bita.

Yana shiga ta shafa fatiha, har ta mike tayi gun sa kuma sai ta juyo saboda tino da abinda ya faru dazu.

Murmushi shima yayi dan ya gane me yasa hakan.

Juyowa da ita yayi ya shagwabe fuska ya ce,
“Haba Baby na ni dai gaskiya bana son haka.”

Ya matsa kusa da kunnen ta yai mata rada.

Juyowa tayi ta kai masa duka da gudu ya bar wajen bin sa tayi da gudu ita ma.

Sun jima suna zagaye falon dan har sai da ta gaji ta fada kan kujera tana maida numfashi.

Shima zama yai a kusa da ita ya daura kansa akan cinyar ta.

Ibrahim ne ya shigo da sallama. Amsa masa sukai suna masu maida numfashi.

Murmushi yayi ya ce,
“Yaya Gudu kuka yi ne?”

Fulo Yaa Ahmad ya dauka ya jefa masa. Mikewa yayi ya ce,
“Uhmm Allah bada hakuri.”

Yai cikin daki. Amina ta daga murya ta ce,
“Kazo kaci abinci.”

“To Anty bari na watsa ruwa.”
Kan Ahmad ta dauke daga cinyar sa ta. ta dan taba cikin  sa Ta ce,
“Muje kaci abinci.”

Ta mike tana kama hannun sa. Sai da tai serving nashi sannan suka zauna suka ci abinci.

Suna gamawa Ibrahim ya fito. Zama yayi shima ya ci ya koshi sannan suka koma falo gaba daya suna hira abinsu.

Na’ima da duk abin duniya ya isheta yasa duk tayi nadamar abinda tai wa Amina dan ta san har da haka Allah ya tashi kamata.

Yanzu ma ta jima a daki tana tunanin halin da Amina take ciki.

Waya ta dauka ta kira ta. Amina na dauka ta gaishe ta, ta tambayeta ya jiki.

Suna gama wayar, Na’ima ta mike tai dakin Mami.

Mami na zaune tana danne danne a waya ta ce,

“Mami gunki na zo.”

Mami ta kalle ta ta ce,

“Me ya faru?”

Na’ima ta ce,

“Mami daman akan Amina ne da Yaa Ahmad!”

Mami ta ce,

“To me ya faru?”

“A gaskiya a yanzu ne na fahimci irin halin da muka saka Anty Amina a ciki. Dan nima shi na tarar a gidan Naufal, dan duk wulakancin da mukai mata ba irin wanda ban gani ba a gidan Naufal. A gaskiya ban ji dadin abin ba.”

Mami ta ce,

“Toh kina so yanzu kice kina goyawa Amina baya ne ko me?”

Na’ima ta ce,

“Ba haka bane? Nifa a gaskiya ina ganin ya kamata ki rabu dasu su zauna lafiya Mami har yanzu fa ina jin ba abinda ya shiga tsakanin su. Mami Ya Ahmad fa yana daukar hakkin ta duk da ba acikin hankalin sa yake ba. Kinsan hakkin na kan ki fa Mami. Ya kamata ki barsu haka nan su zauna lafiya suyi zaman lafiya mai cike da kaunar juna. Ba yau kaza gobe kaza ba. Tin da sukai aure kullun da abinda kike jefa musu da farko kinsa naje na tare ina neman fadan ta gashi daga baya kin hana su jin dadin aure ga shi yanzu bata da lafiya kuma nasan kece Mamii. Dan Allah Mami kisa musu albarka.”

Mami ta ce,

“Kinga indan har ke baki da abinda zakiyi to ni ina dashi. Dan haka tashi kiban waje kin zo kin cika min kunne da surutu.”

Da taki tashi sai ta daka mata tsawa ta ce,

“Na ce ki tashi ki bace min daga waje.”

Da sauri Na’ima ta bar wajen tana zubar da hawaye.

Amina kuwa tana can ta dauki Number Naufal a wayar Yaa Ahmad.

Bayan Yaa Ahmad ya tafi office ne, ta kira Naufal.

Bayan sun gaisa ta ce, masa Amina ce matar wan Na’ima.

Kara gaisar da ita yake cikin girmamawa.

Amina ta ce,

“Naufal daman ina son ganin ka ne.”

Naufal ya ce,

“To Anty, yanzu zan wuce office zan biyo ta nan sai na tafi.”

“Shikenan nagode.”

Ta kashe wayar.

Batai minti ashirin da gama wayar da Naufal ba sai gashi ya shigo.

Parking motar sa yayi ya kira number ta.

Sitting room ta bude masa kofa ya shiga.

Kara gaisawa sukai, ta kawo masa lemo da ruwa.

Lemon ya sha kadai, ya maida hankalin sa kan Amina.

Amina ta ce,

“Naufal me ya hada ku da matar taka ne?”

Kai yayi kasa da shi. Ya ce,

“Wallahi Anty ina son Na’ima. Ummah ce ta ce sai na sake ta wai yawo take da dai maganganu kala kala.”

Kai Amina ta gyada. Amina ta ce,

“To kai ka yadda?”

STORY CONTINUES BELOW

Kai ya girgiza ya ce,

“Gaskiya ban yadda ba dan nasan Na’ima bata da halin banza.”

“To yanzu ita Na’imar ta fada maka gidan wacce ta je?”

Kai ya girgiza.

Waya ta dauka ta kira Na’ima cikin Girmama wa Naima ta gaishe da Amina.

Amsawa tayi ta ce,

“Na’ima me ya hada ku da mijin kine?”

Kuka Naima ta fashe da shi ta ce,

“Anty wallahi nasan ba komai bane face hakkin ki dake bina. Wallahi Anty, nasan duk abinda hakkin ke bina dan duk abunda nai miki shi na tadda a gun su Ummahn Naufal. Anty ina son Naufal amman bansan me yasa ya yadda da duk abinda aka fada akai na ba.”

Ta kuma fashewa da kuka. Amina da ta saka wayar a speaker, Naufal najin duk abinda take fada yaji duk tausayin Na’ima ya kamashi.

“To ya isa,”

Amina ta fada.

Sai da tayi shiru ta ce,

“A ina kika kwana ranar da abin ya faru.”

Naima ta ce,

“Gidan Maman Manal”

Maman Manal kawar Na’ima ce dan haka Amina ta ce ta turo mata da number ta.

Naufal kuwa tin da ya fara jin batun Na’ima jikin sa yai sanyi.

Dan ya yadda da duk abinda tta fada dan yasan halin iyayen nashi.

Tana turo number Amina ta kira ta. Dauka tayi, sai da Amina tai mata bayanin ko wace sannan suka kara gaisawa.

Tambayar ta tayi kan cewa anan Na’ima ta kwana kwanakin baya.

“Eh! Anty anan ta kwana dan lokacin ma ta zo tana kuka wai an rufe mata gida. Ni na hanata zuwa gida ganin daga aure sai ace taje kai kara gida.”

Nan ta fada musu gaskiya. Wayar Amina ta kashe! ta kalli Naufal ta ce

“To kaji gaskiyar abin ko?”

Kai ya gyada yana share zufar da ta zubo masa.

“Amman Anty nagode gaskiya ke masoyiyar mu ce da kika warware mana wannan abin nagode kawai Allah ya kara girma.”

“Ba komai Naufal. Nasan irin son da Na’ima ke maka ana bani labari shiyasa dduk da nasan Na’ima da rashin kunya amman nasan bata kula samari.”

“Haka ne nima nasan Na’ima da wannan halin.”

“To shikenan abinda nake son fada maka kenan. Nagode da amsa gayyata ta da kayi.”

Mikewa yayi ya ce,

“To Anty sai kinzo kawon kanwar taki.”

Murmushi tayi itama ta mike ta bi bayan sa.

Sai da ya tafi sannan ta koma gida tana me jin dadi.

Naufal kuwa daga nn gida yayi. Yana shiga ya dinga kwallawa Ummah kira.

Ummah ta fito da saurin ta ta ce,

“A’ah Naufal lafiya?”

Zama yayi itama ta zauna a gefen sa. Ya ce,

“Ummah na samu matar da Na’ima ta kwana a gidan ta. Na samu labarin duk abinda kukai mata.”

Ummah ta ce,

“To akan wannan yar iskar yarinyar kazo kana kwala min kira.”

“Ummah wallahi ina son Na’ima bazan taba iya rayuwa ba Na’ima ba ita kadai nake so.”

Halima kanwar sa ta ce,

“Haba Yaya me zakayi da wannan yarinyar ga mata nan masu aji kamata wanda sukafi Na’ima kyau da komai.”

“Rufe min baki.”

Naufal ya fada.

Ya ce,

“Ina ajin yake agunki. Tinda nake ban taba ganin wani yazo gun ki ba.”

Ummah ta ce,

“To goran ta mata akan wata can zaka gorantawa yar uwar ka.”

Kai ya sosa ya ce

“Yanzu dai ba wannan ba. Ummah na sa an gyara dayan gidan nawa yanzu zan dawo da Na’ima zamu zauna a can kawai.”

Ummah ta rike baki ta ce,

“Toh!!

“Ummah sai dai hakuri amman kiyi hakuri. Na’ima nake so ita nake son zama da ita.”

Ya fita ya bar wajen.

Amina kuwa ranar murna da dadi kamar me, dan da nishadi ta tashi ta daura girki.

Tuwon semovita ta tuka masa miyar zogale, wacce ta ji naman kasuwa da gyada.

Lemon zobo ta hada wanda ta saka cucumber a ciki.

Wanka tayi ta shirya cikin wata shaddar ta mai kama da matrrial ba karamin kyau tayi ba dinkin riga da siket ne.

Yaa Ahmad kawai take jiran dawowar sa.

Tin bayan la’asar take zaune tana jiran sa.

Karfe biyar da rabi sai gashi ya shigo. Da sauri ta mike ta taro shi.

Kallon ta ya tsaya yi ya ce,

“Baby wannan kwalliyar fa?”

Ido ta juya ta ce,

“Taka ce.”

Ido ya zaro ya ce

“Dukka.”

Kai ta gyada masa. Daukar ta yayi gaba dayan ta suka shige baangaren sa.

Sai da yai wanka ya shiraya sannan suka dawo falo.

Lemo ta kawo masa ya sha sai ga kiran sallah magariba nan alwala yayi ya mike ya tafi massalaci.

Sai isha’i suka dawo tare da ibrahim. Gaba daya suka zauna suka ci abinci.

Suna gamawa suka koma daki suna hira. Sai karfe goma kowa ya mike yayi bangaren sa.

Washe gari Naufal yana tashi ya fara shirin zuwa gidan su Naima.+

Sai da yai wanka ya shirya cikin wata milk din shadda sannan ya saka brown takalmi da hula.

Wata marsandi ya dauka ash kala ya nufi sahad store ya lodo musu kaya sannan ya wuce gidan su Naima.

Tin daga bakin gate kirjin sa ke bugawa saboda yasan halin Mamin Na’ima da fada.

Ibrahim da zuwan sa gidan kenan ya ganshi. Gaisawa sukai sannan ya ce gun Dady ya zo.

Da sauri Ibrahim ya shiga fadawa Dady. Dady ya ce ya shigo da shi.

Dan haka tare suka shiga. Suna zama ya durkusa ya gaida Dady,
“Ina kwana?”

“Lafiya lou Naufal ya kuke yasu Maman ta ka?”

Kai a kasa ya amsa da
“Suna nan lafiya.”

Ya cigaba da magana ya ce,
“Dady na gano gaskiyar Al amarin, ashe duk abinda aka fada min game da Naima duk shirine, na mahaifiya ta da kuma kanwata shine na zo dan Allah ayi hakuri Na’ima ta koma dakin ta.”

Mami dake zaune ranta a bace, sai harare harare take. Ta ce,
“Au dan haka wato shine kuka ci mata mutunci kuka kado ta gida. Dan rashin mutinci.”

“Kee!”
Dady ya daka mata tsawa. Wannan Yasa tai shiru bata shirya ba. Ya ce,
“Kiyi shiru wannan ba maganar ki bace kada na kuma jin kin saka min baki anan.”

“Haba Alhaji ‘ya ta ce fa ni na haife ta saboda me bazan magana ba.”

“Keep quite!”
Ya fada ransa a bace.

Ya ce,
“Sai me in yar kice ni din ba ‘ya ta bace, kar ki kuskura ki kara sa mana baki a magana.”

Naufal ya ce,
“Dady ayi hakuri duk laifi nane tinda ban tsaya nayi bincike akai ba.”

Dady ya ce,
“Haka yake naji dadi da wannan maganganun naka. Daman kyan mutum in yasan yai laifi yayi nadama kuma ya bada hakuri. Wato hali ne muka tsinci kan mu na iyaye su tursasawa ‘ya’ya ra’ayin su bayan su yaran suna da ra’ayin su. Amman tinda kazo ka ba da hakuri to babu damuwa komai ya wuce yanzu. Allah taimaka.”

Naufal ya amsa da
“Ameem!”

Dady ya ce,
“Yaushe kake so ta koma gidan ta.”

Kai Naufal yai kasa da shi ya ce,
“Dady ko yanzu ne ma zan ji dadi.”

Kallon Na’ima Dady yayi ya ce,
“Na’ima je ki duko mayafin ki ku tashi ku tafi. Allah miki Albarka a cigaba da hakuri kinji.”

“Toh Dady.”
Ta mike da sauri tayi daki.

Cikin minti biyu sai gata da hijab din ta a jikin ta.

Tana fitowa Dady ya mike ya ce,
“Muje ko?”

Mikewa Naufal yayi yana yiwa Mami sai anjima.

Mami banza tai masa shima bai damu ba ya fito.

Sai da Dady ya saka su a mota sannan ya koma ciki.

Naufal sai godiya yake. Mai gadi ya kira yasa su sauke kayan da ya kawo wa Dady.

Addu’a dady ya dinga sanya musu da albarka.

STORY CONTINUES BELOW

Daga nan gidan Amina suka shige tin a hanya Na’ima ta ce,
“Ina zamu?”

“Ki zuba ido ki gani.”
Shiru tayi.

Har suka shiga harabar gidan su Amina tana mamakin me suka zo yi.

Sai da ya fito ya bude motar sannan ya zaga ya bude mata itama.

Fitowa tai kamar wace bata san gidan ba.

“Muje man!”
ya fada yana nuno mata kofar shiga gidan.

Da sallama suka shiga falon ba kowa a falon sai TV dake aiki ita kadai.

Sallama sukai yi wajen sau uku sai gasu nan sun fito daga kitchen.

Amina na ganin su ta saki murmushi ta karaso cikin falon. Ta ce,
“Ah ah Amarya da ango.”

Murmushi sukayi Ahmad ya ce,
“Wa nake gani haka?”

Kasa Naufal yai da kai ya ce,
“Munzo godiya ne gun Anty Amina.”

Amina tai saurin katse shi ta ce,
“A’ah dan Allah ni bana son haka banyi dan ka fada ba in haka ne ya kawo ka na gode ku tashi ku tafi.!

Murmushi yayi ya ce,
“Ayi hakuri anty amman sai fa na fada.”

Ya kalli Ahmad ya ce,
“Yaa Ahmad ai mana godiya gun Anty ita ta shiryamu da Na’ima har na gane gaskiya.”

Fuska Amina ta hade ta ce,
“Ba nace kar ka fada ba.”

Ta mike tayi kitchen dariya Ahmad yayi ya ce,
“Haka Antyn ku take, bata son godiya.”

Sukai dariya. Bayan ta Na’ima ta bi. sai da ta gama juyo abincin sanna ta kai daining hararar su tayi ta ce,
“Ku taso to.”

Suka mike suka nufi daining din. abinci ta zuba musu duk suka zauna suna ci

Suna gamawa suka.koma falo aka zauna ana hira.

Can Na’ima ta ce,
“Anty dan Allah kiyi hakuri da duk abinda nai miki ki yafe min. Nasan na cutar dake amman dan Allah ina neman yafiyar ki “
Mikewa Amina tayi ta matsa kusa da Naima hannun ta, ta kamo ta ce,
“Haba Na’ima wallahi ba komai ni ban rike ki da komai ba ai ke kanwata ce.”

Rumgume juna sukai Amina na lallashin Na’ima dake kuka.

Sai yamma suka tafi, Sai bayan tafiyar su Ahmad ya ke yiwa Amina godiya.

Fuska ta bata ta ce,
“Ina ruwan ka ba kanwata naiwa ba mene na min godiya.”

Ahmad ya ce,
“Kuma fa haka ne.”

Yau ma kamar ko da yaushe da yake juma’a ce, ya biya ta gidan Mama.

Tana zaune tayi kwalliyar juma’a, ya shiga tana ganin sa, ta saki murmushi ta ce,
“Ahmad har an sakko.”

“Eh wallahi Mama. Ya kike ya gidan?”
Ta amsa masa da duk lafiya.

Hira suka dan taba inda cikin wayo da. Dabara ya ribace ta har ta amince zata je taga gidan Amina dai yau.

Amina kuwa tana gida ta gyare gidan ta tsab sai tashin kamshi yake ta gama girkin ta.

Tai kwalliya cikin wani milk din material an mata dinkin doguwar riga
Ba karamin kyau tai mata ba tai kwalliya sosai a fuskar ta.

Karatun Alkur’ani ta saka a TV ta dauki waya tana chat da Yasmeen,

Anan ne Yasmeen ta ke ce mata har ana sa musu rana da Muslim.

Sosai Amina ta taya ta murna da sanya alheri.

Horn din sa ta jiyo wannan yasa tai saurin mikewa ta fita.

Dai dai fitowar sa daga mota kenan hannun sa rike da leda.

Karasawa tayi ta amsa shi kuma yayi dayan bangaren ya budewa Mama kofa.

Amina na ganin ta ta ruga da gudu ta taro ta tana murna kamar me

Cikin suka shiga Amina ta shiga ta kawo musu ruwa da lemo.

Suna gamawa ta kawo musu abinci da snack din da tayi.

Sai da suka ci suka koshi sanna ta samu damar gaishe da Mama.

Mama ta amsa cikin so da kulawa. Mikewa Ahmad yayi ya fita ya  daga nan zai je wajen Dady.

Yana fita Amina ta dinga zaga gidan da Mama. Mama na sanya musu albarka.

Sai da suka gama suka dawo falo, kitchen Amina ta koma ta kawo mata fruit.

Sha Mama tayi duk abinda Amina taci karo dashi a gidan sai ta kawo mata har Mama ta ce Ya isa haka.

Ranar tare suka yini da Mama sun sha hira dan sai bayan isha’I Yaa Ahmad ya dawo.

Duk yadda Mama taso ta koma gida ya hanata. Dole ta hakura zata kwana anan.

Daki Amina ta kai ta ta ajiye mata duk abinda take bukata sanna itama ta haye gado zata kwanta.

Kallon ta Mama tayi ta ce,
“Me zan gani haka dan nazo zaki bar mijin naki shi kadai.  Maza tashi ki je ki kula da mijin ki. Allah muku albarka.”

Ba yadda Amina zata yi haka ta mike ta fita

Bangaren Ahmad ta nufa yana zaune akan kan gado yana aiki a system, tana lekawa suka hada idon ta koma dayan dakin ta kwanta.

Yaa Ahmad kuwa da yasan haka zata faru yasa ya mike ya bi bayan ta.

Ahmad kuwa da yasan haka zata faru yasa ya tashi yabi bayan ta.

Tana shiga ta kashe fitilar dakin ta haye gado tana jan bargo.

Dakin ya shiga ya kunna fitila. Kallo ta yayi a can karshen gado ta kudundune.

Fitilar ya kashe, yabi bayan ta. Bargon ya yaye ya shiga ciki. Ya rufe su.

Da sauri Amina ta mike tana kallon sa. Kai ya gyada mata ya ce,
“Mama tace, ki zo ki kwana a guna sannan kuma ki ‘ki zuwa gareni ki taho nan.”

Shiru tayi kafin ta koma ta kwanta. Gyara kwanciyya tayi ta kara makalewa a can gefe.

A hankali ya matsa kusa da ita. Tana jin sa tayi shiru.

Daga karshe dai sai da ya rumgume ta ya samu bacci.

Washe gari da safe ta tashi ta gyara bangaren Yaa Ahmad sannan ta tafi nata bangaren.

Dakin da Mama ta kwana ta shiga. Mama na zaune rike da Al kur’ani tana karanta. Ahmad na gefen ta yana jan carbi.

Zama tayi daga nesa da Yaa Ahmad sannan ta gaishe shi. Amsa mata yayi sannan ta kalli Mama da ta ajiye Al kura’nin.

Kai tayi kasa da shi ta ce,
“Mama ina kwana?”

“Lafiya lou Amina kun tashi lafiya.”
Mama ta tambaye ta.

Da lafiya ta amsa sannan ta mike ta tafi kitchen.

Doya ta hau ferayewa kasancewar ta san Mama da son doya da kwai.

Tana cikin feraye wa Yaa Ahmad ya shigo. Kallon ta ya tsaya yi hannun sa harde a kirji.
“Me zaki hadawa Mama?”
Ya tambaye ta yana karasowa cikin kitchen din.

Murmushi tayi ta ce,
“Doya zan soya mata.”

“Sai me?”
Ya tambaye ta.

“Kunun gyada zan dama mata.”
“Ok!”

Ya fada yana yin bangaren firijn din nama da kifi.

Naman kai ya debo ya zuba a wata container.

“Kinga zo ki gyara wannan bari na daura doyar na tace miki gyadar.”

Kallon sa tayi ta ce,
“Kai Yaya da ka bari duka zan iya.”

Matsawa kusa da ita yayi ya ce,
“Kar mu bar Maman mu da yunwa gwara na taya ki ko?”

Kai ta gyada masa ta sakar masa wannan ta koma kan naman.

Abinka da Gas nan da nan suka gama duk abinda zasuyi.

Na Mama ta diba ta kai mata daki sannan ta koma tayi wanka.

Kwalliya tayi me kyau a fuskar ta ta saka wata bakar doguwar riga yar dubai.

Ba karamin kyau tayi ba. Ta saka wata jar hula a kanta.

A falo ta samu Yaa Ahmad. Da sauri ta karasa ta dauko musu break din su.

A falo, suka ci suna gamawa suka tafi dakin da Mama take.

A dakin suka juma suna hira dan sai Azahar Yaa Ahmad ya tafi masalaci.

STORY CONTINUES BELOW

Amina ma bayan tayi sallah ta daura abincin rana.
Mami kuwa tana can labari ya iske ta Ahmad ya bawa Amina mota ya kuma bude mata shago.

Mami kamar tayi hauka dan bakin ciki. Wannan yasa ta kuma yadda da an asirce mata ‘dan ta.

Mama kuwa suna gama cin abincin rana tace lallai su tashi su maida ta gida.

Ba dan sun so ba suka mike kowa yayi dakin sa dan ya kimtsa, Kaya Amina ta canja, ta saka Doguwar riga baka.

Ta yafa jan mayafi ta saka jan cover shoe, akwatin ta ta bude ta rasa me zata daukar wa Mama.
Atampopi ta dibar mata da turaruka ta zuba a leda haka ta tafi kitchen nan ma tana ta binciken abinda zata dibar mata

Soyayyun kaji da ta soya ta zuba mata hade da snack da take yawan yi ta ajiye.

A Falo ta Same ta ita da Yaa Ahmad shima ya canja shiga cikin Shadda brown kala. Sai tashin kamshi yake yana hango Amina ya karasa ya amshi kayan hannun ta.

Mama ta mike tayi gaba suka rufa mata baya.

Ibrahim da dawowarsa kenan daga gidan Mami ya dinga mita wai me yasa ba a fada masa Mama tazo yazo su sha hira ba

Dariya Amina keyi Mama kuma tana bashi hakuri. A gida suka barshi suka tafi kai Mama.

A hanya Yaa Ahmad ya tsaya  yai mata siyayya sannan suka tafi gida.

Sun dan zauna dan sai da sukai sallahar la’asar sannan sukai mata sallama suka tafi.

Mama sai addu’a take musu da sa musu albarka.

Suna fita Amina ta amshi key din mota ta ce,
“Ni zan tuka.”

Murmushi yayi ya ce,
“A dai tafi a hankali dan motata ba learner.”

Suka shiga, hanya yaga ta dauke tayi ta can rijiyar zaki, kallon ta yayi ya ce,
“Ina kuma zamu?”

“Ni fa bana son ina tuki ina magana kar hankalina ya dauke.”
Dariya yayi dan yasan dan kar ta fada masa inda zasu ne ta fadi haka.

A hankali a hankli har suka karaso kofar gidan su Yasmeen.

Horn tayi me gadi ya bude suka shiga. Motar ta parka sannan ta kashe ta. Sai a lokacin ta dawo da kallon ta gareshi.

Gira ta dage masa ta ce,
“Muje ko?”

Murmushi yayi ya kamo hannun ta saurin zame hannun ta tayi ta bude ta zaga ta bude masa.

Cikin gidan suka nufa kai tsaye sai da suka karasa baban falon su sannan sukai sallama.

Dadyn Yasmeen ne ya amsa sallama suka shiga.

Yana zaune Maman Yasmeen a gefen sa suka shiga.

Dady na ganin su ya saki murmushi Mama kuma ta ce,
“Ah lallai yau Yasmeen anyi babban bakuwa.”

“Yasmeen! Yasmeen!!”
Ta kwada mata kira.

Daga nesa Yasmeen ta amsa da
“Na’am!”

Sannan Mami ta maida kallon ta gare su.

Dady ya ce,
“Bismillah!”

Suka karasa cikin dakin. a kasa suka zaune Dady ya ce,
“A’ah ku hau kan kujera.”

‘Ki suka yi suka zauna anan suka fara gaishe da Dady sannan Mama.

Duk suka amsa cikin kulawa suna tambayar su ya gidan.

Suna cikin hira Yasmeen ta karaso tana ganin Amina ta karasa gun ta da gudu ta rumgume ta,
” ‘yar uwa kece!”

Murmushi Amina tayi ta nuna mata Yaa Ahmad.

Kasa Yasmeen tayi da kai ta ce,
“Wallahi ban ganka ba ai.”

Yaa Ahmad ya ce,
“Tayaya zaki ganni.”

Mama ta mike ta fita. Sai da suka gaisa sannan  Yasmeen kuma ta ja hannu Amina sukai cikin dakin ta.

Ya rage daga Dady sai Ya Ahmad. Hira suka fara kafin Yasmeen ta kawo masa lemo da snack amsa yayi yana godiya.

A can kuwa hira ta barke tsakanin Amina da Yasmeen dan sai labarin Muslim take bata wanda an saka rana sauran wata biyu bikin.

Shirye shiryen bikin suka fara, akai kiran sallar magariba. mikewa sukai sukayi sallah ssannan suka zauna.

Yasmeen ta kalli Amina ta ce,
“Amman dai nasan kafin bikin cikin ki ya girma ko?”

kallon ta Amina tai da Mamaki ta ce,
“Wane cikin?”

Cikin ta Yasmeen tai nuni da shi.  Dariya Amina tayi ta ce,
“To ban da komai.”

“Wallahi karya kike, kalli yadda kika kara kyau da haske kuma.kice baki da ciki.”

Dariya Amina tayi dan tasan ba yadda zatai ba. Dan haka da Basma tazo shima kin yadda tayi da tace bata da komai.

Mikewa tayi ta gyara nadin mayafin ta ta ce,
“Bari mu tafi.”

Mikewa Yasmeen tayi ta ce,
“To sai nazo karasa shirye shiryen ko?”

“Allah kawo ki.”
Durowa Yasmeen ta bude ta debo mata wasu tarkace ta ce,
“Wannan in kinje gida ke sha.”

Leka ledar tayi, kamshin gubar mata da taji ta ce,
“Allah shirya ki wai har kin fara ciye ciyen kayan nan.”

“Kar na fara ai ance.in kana da kyau to ka kara da wanka.”
murmushi Amina tayi kawai suka fita.

Mama taje yiwa sallama Mama ta hado mata wasu humra masu dadin gaske ta bata.

Godiya tai mata sannan suka nufi Dakin da su Yaa Ahmad suka. Sai hira. suke Da Dady kamar yadda yake da Dadyn sa,

Dady ya kalle su ya ce,
“Har kun fito.”

Kasa Amina tayi da kai ta ce,
“Eh Dady “

“To Allah yayi albarka a cigaba da hakuri da biyayya ga miji kinji Amina.”
Kai Amina ta gyada.
Hannu yasa a aljihu ya zaro kudi masu yawa ya mika mata. Kin amsa tayi sai Yasmeen ce ta amsa suka fito tare dan raka su.

Mukullin ta mikawa Yaaa Ahmad ya ce,
“Ya kuma haka.?”

Fuska ta marairaice tta ce,
“Kasan ban son tukin dare ai.”

Amsa yayi ya shiga ya tada motar sai da ya juyo da ita sannan ta shiga. Lekowa Yasmeen tayi tana mata bankwana bata lura ba Yasmeen ta saka mata kudin a cinyar ta.
Hanya ya dauka suka tafi, a hanya suna tafe suna hira abin sha’awa har suka karasa gida.

Ibrahim na falo yana kallo yai musu sannu da zuwa sannan ta shige kitchen.

Jallop din macaroni tai musu wacce taji kifi sai zubo da ta hado musu.

Sai da sukai Sallah isha’i sanna suka zauna suka ci abinci.
Falo suka koma suna kallo karfe tara Ibrahim ya tashi yai dakin sa ya rage daga Amina sai Yaa Ahmad.

Goma nayi Yaa Ahmad ya mike ya kashe kayan kallon. Kallon sa tayi ta ce,
“Ya dai?”

“Bacci nake ji kizo ki sani nayi.”
Ya fada yana yin bangaren sa.

kallon mamaki tabi shi da shi ta mike tayi dakin ta. Wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya cikin wata farar rigar bacci iya kar ta gwiwa ta bazo da gashin ta gadon bayan ta.

Ta feshe jikin ta da turaruka kala kala. Sannan ta haye gadon ta, taja bargo.

Yaa Ahmad shima yana zuwa dakin wanka yai ya shirya cikin kayan baccin sa.
Zaman jiran ta ya zauna yaji ta shiru mikewa yayi yai bangaren ta.

A gado ya hango ta tana bacci cikin kwanciyyar hankali.

Kai ya girgiza ya ce,
“Meenal kenan ai kam sai kin kwana a bangare na.”

Bargon ya yaye ya dauke ta suka nufi site din shi sai da ya shiga sannan ta farka.

Ganin ta a hannun sa yasa ta kwantar da kanta a kirjin sa.
Sai da ya kwantar da ita sannan shima ya hau gadon ya jata jikin sa wani sanyi da ni’ima yaji yana ratsa shi.

A haka sukai baccin.

*Bismillahir Rahamanir Rahim*
Alhamdulilah nagode
Yan uwa masu cigiyata ina lafiya kuma dukkan ku sakon ku ya iso gare ni. Da wanda ya kira ni da masu text duk naga sakon ki nagode nagoda kulawa dakaunar ku Nagode da addu’ar ku.
Ina yin ku
Bari mu shiga daga ciki muji mai yai saura
Washe gari da safe bayan ta gama hada musu break ta gyare gidan ta turare shi.
Daki ta koma tai wanka ta shirya cikin wata green din super an mata dinkin riga da siket dikin yai mata kyau ya zauna a jikin ta.
Dan kunne da sarka da abin hannu ta saka silver ta feshe jikin ta da turare.
Falo ta koma ta tadda Yaa Ahmad ya fito shima cikin shirin sa. Yana sanye da farar shadda tai masa kyau sai sheki yake fitar wa.
Sai tashin kamshin turare yake. Durkusawa tayi ta ce,
“Ina kwana Yaya nah.”
Janyo ta yayi jikin sa, ya ce,
“Lafiya lou kin tashi lafiya. Wai ke haka ake ki Kwana a wajen mijin ki amman ki fito ba tare da kin kintsa shi ba gaisuwa ma sai a falo bayan kinsan ba mu kadai ne a gidan ba akwai irin gaisuwar da nake so ba irin wannan ba.”
Kai ta dukar ta ce,
“Kai Yaa Ahmad!”
Ta mike zata bar wajen janyo ta yayi ta fada kirjin sa. Matse ta yayi yana kallon kwalliyar ta.
Ido ta lumshe, bakin sa ya kai dai dai nata yai kissing nata.
Kara narkewa tayi a jikin sa, murmushi yayi, ya ce,
“Wannan gaisuwar bata fi ba?”
Kan ta ta kifa a jikin sa. Dago ta yayi ya rada mata abu a kunne da sauri ta mike tayi dakin Ibrahim tana knocking.
Sai da ya amsa sannan ta koma falo daining ta nufa ta fara serving kowa.
Yaa Ahmad taji ta bayan ta, ya rumgume ta.
“Yaaa Ahmadd!”
Ta kira sunan shi a hankali. Take yaji tsigar jikin sa ya tashi.
Kan sa ya kwantar a wuyan ta. Ido ta lumshe.
sunan sa ta kara kira a hankali.
“Baby nah ki barni na ji dumin jikin ki please!”
Shiru tayi kafin ta ce,
“To ka bari mu karya kaga Ibrahim na nan ko?”
Daga ta yayi yai yaja hannun ta ya zaunar a kan cinyar sa.
Fitowar Ibrahim shiyasa, tai saurin mikewa. Shima cikin shirin sa na makaranta ya fito. Sai da ya gaishe su sannan ya zauna ya ce,
“Ni dai yunwa nake ji. Naga yau soyayya kuke ji.”
Hararar sa Amina tayi ta ce,
“Kagan ka ko Ibrahim!”
Dariya yayi suka fara cin abinci.
Sai da suka gama sannan sukai bangaren Yaa Ahmad.
STORY CONTINUES BELOW
Tana zaune Yaa Ahmad na kwance kan sa a saman cinyar ta suka ji knocking.
Kan ta dauke ya ajiye ta mike tayi bangaren ta. Kofa ta bude.
Tana budewa taga Mami rike da akwatin ta wani faduwar gaba taji.
Da sauri ta furta,
“Inna illahi wainna illahir rajiun!”
Ta fada a zuciyar ta. Hanya ta bata ta shige, ta durkusa ta ce,
“Ina yini? Ya hanya?”
Kallon ta ta tsaya yi daga sama zuwa kasa ba tare da ta amsa gaisuwar ba.
“Wallahi bamu san ke bace shiyasa.”
“Ai daman tayaya zaki san nice bayan gidan duk ki kanai naye shi.”
Ibrahim da shima ya fito dan bude kofa ya ce,
“Haba Umma ya daga zuwa, kuma zaki fara abinda ba dai dai ba. Ko zama bakiyi ba.”
Mami ta ce,
“An bani wurin zaman ne? Ai ba a bani gun zama ba.”
Ibrahim ya ce,
“Yi hakuri ki zauna.”
Zama tayi tana kalle kallen dakin dan ba karamar dukiya aka zuba a dakin ba.
Dakin da yafi na ‘yar ta Naa’ima sai wani bakin cikin ya kara tarar mata.
Ibrahim ya ce,
“Mami ya gida?”
“Lafiya. Ina dan nawa yake?”
Amina ta ce,
“Yana ciki yana bacci bari na taso shi,”
“Tsaya tsaya. Ai daman dole ki tason shi dan ni uwar sa ce da zaki ce bacci yake kenan nace kar ki taso shi ko? to ko da kaina ne zan iya zuwa na taso shi. Kije kice mahaifiyarsa ce tazo,”
Hanyar bangaren sa tayi.  Jiki a sanyaye. Ibrahim ya kalle ta ya ce,
“Mami ya gida?”
Kallon sa tayi tai tsaki. Ya ce,
“Mami ya naga kamar bakya cikin farin ciki ne.”
“Ai bazan taba farin ciki ba in har Ahmad na tare da wannan mayar yarinyar.”
Amina kuwa tana karasa daki ta fara kokarin canja fuskar ta.  A inda ta bar shi a haka ta koma ta same shi.
kan ta daura akan kirjin sa a hankali ta dinga shafa sumar kan sa. Tana hura masa iska a kunnen sa.
Mika ya fara yi kafin ya fara bude lumshe shun idanun sa.
Murmushi ta sakar masa, wanda yana tashi yaga tana cikin damuwa.
Janyo ta yai zai zaunar tai saurin zame hannun ta ta ce,
“Mami na falo tana jiran ka.”
Tana fadar haka ya gane Mami ita ta batawa Amina rai.
Janyo ta ya kara kokarin yi tai saurin matsawa ta ce,
“Ka bar Mami fa “
Kai ya jin jina kawai ya mike ya fita. Bayan sa tabi jiki a sanyaye.
Yana zuwa falo ya zube a kasa yana gaishe da ita.
“Mami ina yini?”
“Lafiya!”
Mami ta amsa masa.
“Ya hanya?”
“Lafiya.”
“Yasu Dady!”
“Duk lafiya. Ai na dauka ka manta damu ne. Tinda wannan abar tazo ta kanannade maka rayuwa.”
Ta fada tana nuna Amina. Ahmad ya ce,
“Mami har yanzu baki bar irin wadan nan abubuwan ba.”
Amina ya Kalla ya ce.
“Meenalty dauki jakar Mami ki kai mata daki.”
Ta mike zata dauka kenan Mami ta janye ta ce,
“Barshi zan dauka, muje ka nuna min dakin!”
Kallon ta Ahmad yayi yai girgiza mata kai. Murmushin karfin hali tayi dan ji take kamar zuciyar ta zata fashe.
Gaba yayi Mami tabi bayan sa ya nuna mata dakin da Mama ta zauna da tazo.
Dakin tabi da kallo
“Tab!”
STORY CONTINUES BELOW
Ta fada a ranta dan bata san wanda yai mata wadan nan kayan ba.
Amina kuwa zama tayi a ranta tana rokar Allah ya kawo mata karshen wannan masifar.
Ibrahim ya ce,
“Anty kiyi hakuri.”
Murmushi tayi ta ce,
“Ba komai Ibrahim.”
******
Washe gari da safe bayan ta gama komai ta hada break Ahmad da kansa ya dauka ya kai mata daki.
Sannan ya tafi yai wanka ya shirya cikin bakin wando da sky blue din riga me dagon hannu.
Amina kuma tayi kwalliya cikin wani bakin material da akai .masa ado da jan swiss. Dinkin doguwar riga ce me babban hannu.
Ta saka dan kunne da sarka ja jaye. Sai tashin kamshi take. A haka Ahmad yaleko dakin.
Yana ganin ta ya tsaya kasa koda motsi dan ba karamin tafiya tayi dashi ba.
Ta yi kyau iya kar kyau. Da kyar ya iya takowa yazo inda ttake. Tana ganin sa ta saki murmushi ta fara gyara masa kwalal rigar sa.
Kallon ta kawai yake dan komai nata burge shi yake.
Hannu ya saka ya zagayo kugunta da shi. Wani yarr taji wanda tai saurin dagowa.
Ida nun sa sun canja kala sunyi ja, sai wani lumshewa suke yake.
Take taji kirjin ta ya mata wani mugun bugu.
“Lafiya?”
Ta tambaye shi dan bata taba ganin sa a irin wannan yanayin ba.
Rumgume ta yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya. Tausayin sa ne ya kamata duk da bata san me yake damun sa ba.
A hankali ta daura hannun ta akan sa tana wasa da sumar kan sa.
Ya jima yana sauke ajiyar zuciya kafin ya zame ya kwanta akan gado.
Kwanciyyar rigin gine yayyi wannan yasa ta haye kansa ta daura kanta a kirjin sa.
Matse ta yayi kam a jikin sa sai kace wacce za a kwace masa ita.
Sun jima a haka kafin kuma jikin sa ya saki. dago ta yayi ya ce,
“Je daki ki daukon wasu kayan.”
Mikewa tayi a hankali dan itama jikin nata ya saki tai bangaren sa.
Milk din riga ta dauko masa da brown wando. tayo dakin ta.
Tana fita ya shiga bandaki ya cire kaya ya sakar wa kan sa ruwa.
Ya jima sannan ya fito ya saka kayan da ta kawo masa.
Falo suka yi suka karya tare da Ibrahim kamar yadda suka saba.
Sannan suka mike suka nufi dakin da Mami ke ciki.
Tinda taga Amina ta canja kalar fuskar ta. Amina ta tsaya daga bakin kofa ta durkusa ta ce,
“Mami ina kwana?”
Banza Mami tai mata. Yaa Ahmad ne ya ce,
“Mami tana gaishe ki fa.”
Wata harara ta watsa masa ta ce,
“To da ban kwana ba zata gannin ta zo taga na mutu ko. to kurwa ta. Tafi karfin ki wallahi.”
Murmushi Amina tayi ta mike ta fita. A falo ta zauna har Ibrahim ya zo ya bata hakuri yai mata sallama ya tafi makaranta.
Har bakin kofa ta raka shi ta dawo falo ta zauna. Duniyar tunani ta tafi a ranta tana cewa,
‘Wai har yaushe zata daina fuskantar wannan abin da take ciki ne.’
Hawaye ne suka zubo mata wanda bata san lokacin da suke zuba ba. Ahmad da ya fito yayo gun ta ganin tana hawaye ya dada tada masa da hankali.
Zama yayi a kusa da ita amman bata san ya zauna ba har sai da ya riko hannun ta sannan ta kalle shi.
“Haba Meenalty kiyi hakuri komai na duniya me karewa ne dan Allah ki kara hakuri da halin Mami kinji.”
Murmushi ta kakalo ta ce,
“Wallahi Ya Ahmad ba komai.”
“Yauwah haka nake so. Ki daina sa damuwa a ran ki kinji.”
“Insha Allah!”
Ya mike tabi bayan sa.
Sai da suka nufi gun motar sa sannan ta ce,
“Wai ina zaka?”
Kallon ta yayi da mamaki ya ce,
“Yau yaushe?”
Fuska ta bata ta ce,
“Monday!”
“Kuma kike tambayata inda zani. To zanje office ne.”
Ya bata amsa.
Ta ce,
“Dan Allah ina son ka zauna min a gida ko da na yau ne, wallahi tsoron Mami nake.”
“Haba sai kace, wata karamar yarinya ai zama da Mami zai sa ku fahimci juna. Har ma ta daina zargin ki da abinda take ganin ki dashi. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru kinji.”
“Ya Ahamd kasan fa Mami ba sona take ba. Kaga dan Allah ka taimaka kai min wannan uzurin na yau.”
Wayar sa ce tayi kara yana dubawa yaga Dady ne.
Kallon ta yayi ya ce,
“Kinga ko Dady ne kinsan baya nan kuma yau zai yi baki a company kinga dole naje kiyi hakuri yanzu zan dawo kinji. Babu abinda zai faru insha Allahu kinji ko?”
“Allah ya yadda a dawo lafiya Allah bada sa’a.”
“Ameen Baby na shiyasa nake kara son ki wallahi. Allah bar min Meenal dina.”
Murmushi tayi ta ce
“Ameen!”
Ya shiga mota. Sai da ta daina kallon sa sannan ta koma ciki.
Ya Ahamd ko a office baya minti biyar be kira Amina ba.
Duk da tana daki bata fito ba sai wajen karfe daya sannan ta fito taje kitcchen dan daura abinci.
Ranar dai bata gamu da Mami ba dan bata bi ta falo ba.
Ya Ahmad kuwa yana gama abinda zzai yi ya dawo gida.
Amina najin horn dinsa hankalin ta ya kwanta dan daman tana tunanin ta yadda zata kai mata abincin.
Yana shigowa ta tare shi. Kafin ya zauna ta mike masa ta ce,
“please ka mika mata.”
Amsa yayi ya nufi dakin da take. Bacci take dan haka ya ajiye mata ya fito.
Bangaren sa suka tafi yai wanka ta kawo masa abinci sannan suka zauna hira.
Sai bayan la’asar ya shiga dakin Mami. Nan suka zauna suna hira har magariba.
Da ya zo mata sai da safe ma kin barin sa ya tafi ko ta manta ba tare suke kwana da Amina bane ohoo.

Washe gari Yaa Ahmad tin karfe Bakwai ya fita dan basu gama da bakin Dady ba.
+
Gidan ya rage daga ita sai Ibrahim da Mami.
Kitchen ta shiga ta hada break sannan ta koma dan taso Ibrahim ya kawo wa Mami abinci.

Mami ta gani zaune a falo ta hakimce. Amina na jin tsoro haka ta karasa gefen Mami ta Durkusa.
“Ina kwana?”
Amina ta fada.
Mami ta ce,
“Da ban kwana ba zaki gannin ki kawon abinci kin tsaya sai kace naki ne.”

Mikewa Amina tayi a hankali ta tafi kitchen ta kawo mata ta ajiye.

Dakin ta ta shige tai wanka ta saka bakar doguwar riga ta haye gado.

Ibrahim ne ya fito cikin shirin makaranta ya saka bakin wando da farar riga.

Durkusawa yayi ya ce,
“Mami ina kwana?”

“Lafiya lou.”
ta amsa tana ya mutsa fuska.

“Mami zan tafi makaranta ne?”

Mami ta ce,
“Uhmm kai saboda sakarci da rashin hankali ka zo ka zauna a cikin gidan nan wannan yarinyar da take shahsasha ballagaza ta zauna sai saka aika ce aikace take. Kuma fa ka girme ta fa.”

“Haba Mama ke dai ba’a raba ki da abin fada. Ni dai bari naje sai na dawo. Kina hakuri damu da duniyar ma gaba daya.”

Ya mike.
Ta ce,
“Allah kiyaye Allah bada sa’a a dawo lafiya.”

“Ameen!”
Ya amsa ya fice.

Baki ta rike a ranta ta ce,
“Wallahi bazan taba barin Ahmad da Amina ba. Ai ba kalar sa bace yafi karfin ta ‘yar matsiya ta. Tab Sai na raba ku wallahi. Yarinya duk ta asirce min ya’ya da miji da yan uwa. To wallahi ni na fi karfin ki. Ta Allah ba taki ba.”
Ta daura kafa daya kan daya tana jijigawa.

“Amina Amina!!”
Ta kwada mata kira.

Da sauri Amina ta karaso tana amsawa da
“Na’am!”

Mami ta ce,
“Naci amman ban koshi ba. Kije ki min sakwara miyar agushi ki kawon yanzun nan.”

Kai ta sunkuyar ta ce,
“To Hajiya!”

Ta nufi kitchen. Doya ta feraye ta daura aaka wuta ta dibi kayan miya ta gyara ta blanding sannan ta gyara nama ta daura miyar.

Nan da nan tayi ta gama abinka da gas ga kayan amfanin zamani da akayi

A fulas ta kawo mata shi. Kallon ta ta yi ta ce,
“Allah yasa baki barbada min wani abu a ciki ba.”

Shiru Amina tayi ta bar wajen. Daki ta koma ta dauro alwala ta hau kan sallaya tana rokan Allah ya yaye wa uwar mijin ta wannan tsanar da tai mata.

Ta jima tana kai kukan ta gun Allah kafin ta tashi ta koma kan gado.

Yasmeen ce tai mata waya suka sha hira wannan ne ya rage mata wata damuwar a ranta.

STORY CONTINUES BELOW

Suna gamawa kuma Yaa Ahmad ya kira ya tambaya ko lafiya.

Suna gamawa Na’ima ta kira. Bayan sun gaisa Na’ima ta ce,
“Anty wai da gaske ne Mami na gidan ki.”

Murmushi Amina tayi ta ce,
“Eh tazo mana kwana biyu.”

“Tabbin Amman Dady bai sani ba wallahi sai na fada masa. Nasan Mami ba dan Allah tazo ba tazo ne ta lalata muku zaman ku.”

“A’ah A’ah Na’ima kar ki damu wallahi Mami ba abinda take mana kowa yana harkar sa kar ki sake ki fadawa Dady in kuwa kika fada masa zamu bata kinji ko?”

“Shikenan Amman Allah Anty sai kinyi hakuri dan Nasan halin Mami. Allah baki nasarar cinye jarabawar ki dan nansan wannan jarabawa ce Allah yake miki.”

“Ameen Na’ima. Ya mai gidan.”
“Yana nan kalou insha Allah zan kawo miki ziyara kwanan nan.”

“Allah nuna mana nagode.”
Amina ta kara mata nasiha suka sallama kowa najin dadin hirar da sukayi.

Kitchen ta tashi ta shiga. Fried rice ta daura sai hadin cabeji da ferfsu sai lemon Aya da tai musu.

Ta gama kenan ta koma tai kwalliya, ta saka wani codeless din ta, pink da adon milk.

Ba karamin kyau dinkin riga da siket din yai mata dai dai jikin ta. Tayi yar make up me kyau a fuska.
Tana kwance akan gado tana danne dannen wayar ta.

Ya Ahamad ma yau tin karfe karfe biyu ya gama abinda zai yi dan haka ya taho gida.

A hanya ya biyo ta bakin makarantar su Ibrahim nan Yusuf maitama sule.

Ibrahim ya gani a gefen titi yana kokarin tsaida abin hawa.

Motar sa Yaa Ahmad ya gangara da ita gefen sa. Ibrahim na ganin sa ya ce,
“Ah Yayah.”
“Ina ka fito ina zaka dan yanzu ba lokacin tashi bane.”
Kai ya sosa ya ce,

“Daman zan dan je…”
Ya Ahmad ya ce,
“Zaka je ina?”

Kai ya sosa, Yaa Ahmad ya ce,
“Ina motar taka?”

“Wallahi kasan karfen nasara bai da tabbas. Zan hau ta makale shine na taho.”

“da ka tambayi Antyn ka tata.”
“Bana son na bata mata abar tane.”

“Kuma haka ne. To malam shige mu tafi gida tinda yawo zaka je.”
Shiga yayi.
Amina kuwa zaman daki ya isheta ta mike tayo daining area. Firij ta bude ta dauko robar ice cream tana sha.

Mami ce tazo ta ce,
“Me kika dafa ne?”

“Uhmm fried rice ce.”
Baki Mami ta tabe ta ce,

“Ki soya min dankali.”
mikewa tayi ta tafi kitchen ta bar ice cream din da take sha.

Mami na ganin tabar wajen ta kunce zanin ta ta zaro wata leda. Sai da ta dan dana ice cream din ta ce,
“Kace ma dadi take sha,”

Sannan ta barbada, a ciki ta cakuda shi. Amina kuwa tana can tana ferayewa.

Lokacin su Yaa Ahmad da Ibrahim suka shigo. Daining sukayo dan yunwa suke ji.

Ibrahim ganin ice cream yasa ya zauna ya ce,
“Anty ko dai mun kusa samu ‘da ne, kwana biyu kwadayi take ji.”

Ahmad najin haka sai yaji a duniya ba abinda yake son gani a yanzu irin ‘dan sa.

Zama Ibrahim yayi ya fara sha.
Amina Tana gamawa ferayewa ta soya mata shi. ta zubo a fulas ta fito.

Ibrahim ta gani yana sha Ice cream ta ce,
“To kwadayi shi kadai ne ya rage dan haka sai kaje ka siyo mana anjima.”

Dariya Yaa Ahmad yayi ya ce,
“Kwadayayu dai.”

Falo tayi Yaa Ahamd yabi ta da kallo, ya ce,
“Ina zaki?”

“Ina zuwa in kaiwa Mami yunwa ko?”
Dadi yaji ya ce,
“Sai kin dawo.”

Tana dawowa ta fara gabatar musu da abinci. Ibrahim kuwa da yana can sha ice cream

Yaa Ahmad ya ce,
“In ka gama kazo muci.”

Yaa Ahmad ya fara cin abincin Ibrahim ya fara rike ciki.

Kallon sa Ahmad yayi ya ce,
“Lafiya?”

“Yaya ciki na! Wayoo cikinah.”
Da sauri Amina tayo gun sa tana cewa
“Ciki kuma.”

Farar kumfar da suka fara gani a bakin sa ita ta tsorata su.
Da sauri Yaa Ahmad ya ce ta dauko mota. zai kamo shi su fito.

Hijab ta saka ta dauki key suka tafi asibiti tin a mota ya daina numfashi duk gudun da Amina keyi.

Suna zuwa *MANS ClINIC* aka amshe shi sai dai ina har ya rasu.

Dr na fitowa suka.mike suka ce
“Dr ya dai?”

Ya ce,
“Munyi iya bakin kokarin mu amman abin yafi karfin mu.”

“To ya ake ciki?”
Amina ta tambaya.

“Yanzu dai zuciyar sa ta daina aiki. Ya rasu.”

“Innalilahi wainna illahir rajiun.”
Amina ta fada tana fashewa da kuka Yaa Ahmad shine ke lallashin ta. Duk da shima dauriya kawai yake.

A haka suka tafi gida aka zzo aka dau gawar ta sa.

Mami ko tana jin labarin mutuwar sa ta zube. Itama sai da akayi asibiti da ita.

A gidan Mami akai zaman makoki can Amina suka koma da zama ita da Na’ima dan sai da akai bakwai suka koma gida.

Mama kuwa kullum sai tayo girki ta kawo kowa na son Amina daga dangin Mamin har na Dady. Mami ce kadai bata son ta.

A zaman makokin ma tare suke da Basma da ita ma aka sa musu rana da Dr Usman.

Anty Maman Basma kuwa sai korafi take Amina bata zuwan musu.

Hakuri Amina ta bata ta ce zata zo. Har Yasmeen sai da tazo gaisuwa.

Ranar da akai bakwai da dare bayan su Naima sun tafi Ahmad yazo zasu tafi.

Dakin Mami, Amina taje mata sallama tana shiga Mami ta hade rai ta ce,
“Kinji Dadi kin cinyen ‘da amman wallahi ki sani bazan bar ki, ki a haka ba.”

Mikewa Amina tayi tana sharar kwala ta fita. Mami bata san yadda suke da Ibrahim ba ne da har zata fadi haka.

Bata da ‘kani ko ‘kanwa sai Ibarhim ta dauki Ibrahim kamar wanda suka fito uwa daya uba daya.
Mutuwar Ibrahim kamar ita akayiwa. Tin tana gida Ibrahim zai je su sha hira sun saba sosai.

Sai yanzu ta kara jin mutuwar Ibrahim sabuwa fil, dan ba karamin kewar sa zata yi ba shine mata shara banda debe mata kewa.

Wani lokacin tare suke girki su gyara gidan tare.

Baya taba barin ta da kadai ci ko da Yaa Ahmad na nan.

Itama ai an mata mutuwa. A haka ta janyo akwatin ta tayo waje.

Dady na zaune ta karasa tai masa bankwana da karai masa ta’aziya.

Hakuri ya kara bata sannan suka tashi suka tafi

Ko a mota ba wanda ya ce da dan uwan sa kala har suka isa gida kowa yayi dakin sa.

Wanka tayi ta haye gado kawai a ranta tana jin yanzu shikenan sun rasa Ibrahim.

Kuka sosai tayi kafin bacci ya dauke ta.

Haka gidan ya zzama wani iri ba dadi bama in Yaa Ahmad ya tafi aiki, sai dai ta zauna tai ta tunanin yadda suke da Ibrahim da yadda yake sasu wasa da dariya.

Sai da Ibrahim yai wata sannan ta dan fara sabawa dda zaman kadai ci.

Yau tana zaune bayan ta gama komai Ya Ahmad ya tafi aiki sai ga Yasmeen nan tazo.

Da murna ta tarbo ta suka zzauna suna hira. Yasmeen ta ce,
“Sis wai baza mu fitar da anko ba?”

Murmushi tayi ta ce,
“Kiyi hakuri dame dame kike so a fitar sai nai magana a kawo mu zaba ko?”

“Au ashe fa da hajiya nake tare, kala biyu ko?”
“To shikenan.”

Waya Amina ta dauka ta kira shago kan a kawo atamfofi da material da codeless.

Ai kuwa cikin awa daya sai ga yaron shagon nan da kaya kala kala.

Karba Amina tayi ta shiga ta nunawa Yasmeen.

Wata atamfa suka fitar ta yini sai wani blue code less. Tadaukar wa Amarya wani code less dan duk yadi daya 20k ta sa a kawo mata jaka da takalman su ta ce wannan na fitar dinner ne golding kala.

A lokacin ta sa a kawo mata ita da Na’ima da Basma nasu sannan ta sallami yaron bayan ta nuna masa wadan da za’a ajiye dan zuwa siya bayan ta bada su akan farashi me sauki ga masu son siya.

Yasmeen kuwa sai godiya take mata dan tasan da kasuwa zasu shiga ba lallai ma su samo kamar wadan nan ba.

Sai da suka girki dan sai yamma ta tafi gida da farin ciki.
*Bayan sati biyu*
Su Amina anan ta shirye sshiryen biki dan wannan satin za su fara.

Dan har ta kai wa Na’ima da Basma ankon su sun dinka. Yini da kamu za ayi sai Dinner da kai amarya.

Su Yaa Ahmad sune babban abokin ango, Amina kuma babbar kawar amarya.
Tare sukaje akai musu make up dan in ka kalli Amina sai kayi zaton ita ce amarya dan dai kalar amaren da ban ce.

Yaa Ahamd kuwa da yaga kyan da tayi cewa yayi baza wajen ba.

Sai da ta kusan kuka kuma su Muslim suka saka baki sannan ya barta ya ce,
“Amman tana gefen sa dan baya son wani ya ganta.”

Dan in ka ganta sai kayi tsammanin budurwa ce duk da ta saka babban mayafi.

Anyi dinner ranar Friday inda akai yi ranar asabar aka kai amarya gidan ta ranar lahadi.

Ahmad da Amina su suka dau amaryar zuwa gidan ta.

Anyi biki lafiya an tashi lafiya kowa ya tafi yana farin ciki da murna.

Washe gari duk yadda Yasmeen tayi da Amina taje gidan ‘ki tayi sai da magariba suka leka ita da Ahmad

Suna shigewa daki Yasmeen ta kalli Amina ta ce,
“Sis haka kika ji? Tab sisi indai haka za ai taji wallahi da zafi nasha wahala wallahi,”
Dariya Amina tayi duk da a ranta tsoro take ji amman a fili tace
“Ba kece ba kikai ta sha magun guna kafin aure. Ki kwantar da hankalin ki na farko ne da kin saba shikenan.”

STORY CONTINUES BELOW

“Dan Allah da gaske in za a ‘kara ba zafi.”

“Eh man. daga karshe ma ke zaki ga kina neman in ya zame miki jiki ki kwantar da hankalin ki.”

“Nagode Sis shiyasa tin dazu nake neman ki. Ya ba wani maganin da zan samu ne.”

Murmushi tayi ta ce,
“Baki daddara ba kenan ko?”
Amina ta fada

“Tsokana nake!”
Yasmeen ta bata amsa.

Amina kuwa tsoro ne ya gama kamata dan ita ma yanzu ai ana dirka mata magani su basu san da ba abinda ya shiga tsakanin su ba.
A falo Muslim ne yace,
“Amma aboki kayi mana wayo daman haka ake ji.”

Kallon sa yayi ya ce,
“Wayyo kuma?”

“Eh man.”
ya matso kusa dashi yai masa rada.

Duka Ahmad ya kai masa ya ce,
“Banza”

“Naji Kuma yanzu sai dai muna jin dadin tare dan kaji.”
Murmushi kawai Ahmad yayi.

Muslim ya ce,
“Ya naga baka son maganar ne?”

“Kai ai dan kai sabon shiga ne shiyasa.”
Dariya Mislim yayi ya ce,
“Wallahi yanzu zan zama tsohon hannu.”

“Ai kai daman dan iska ne?”
“Naji da matata dai nake yi ko?”

Sukai dariya gaba dayan su.

Sai bayan isha suka taho. a mota kowa tunanin da yake daban dan kowa kasa magana yayi.

A haka suka karasa gida sukai sallah kowa ya tafi dakin sa da tunani kala.kala.

Amina kuwa cewa
“Tasan ba rashin so ne ya hana Yaa Ahmad kusantar ta ba. Amman bata san mene dalilin ba. Ita taji ta yadda ko ba abin zai shiga tsakanin su, zata iya zama da Yaa Ahmad in ma shine bai da lafiya. Tinda ita in dai bashi zai taba ta ko yai kiss din ta ba bata fiya jin sha’awa ba sai dai in an Bata tarkacen nan taci shine zata ji marar ta ta daure.”

Ahmad cewa yake,
“A gaskiya yana cutar Amina. Lallai Amina baiwar Allah ce me hakuri da tarbiyya bata taba daga kai tai masa magana akan hakkin ta ba. Bayan yasan da wasu matan ne ko tayya zai sun nema. sai ya tina da labarin *(Matan Ali)* lallai ya tabbata da Amina akwai kawaici. Aure shekara daya ba abinda ya taba shiga tsakanin su. Gaskiya zai je gun likita yaji kome ne matsalar shi yasan yana da feeling dan yana yawan mafarkai sannan duk lokacin da yaga surar Amina hankalin sa na tashi. To a ina matsalar take?”

Da wannan tunanin yai bacci.
******
Mami ce zaune ta rasa yadda zatayi ita a lallai sai taga bayan Amina.

Wata dabara ce ta fado mata. Tai saurin mikewa tayi can batan gari inda ta san yan daba na zama.

Wajen ba kowa sai wasu mutum uku kai daga ganin su kasan ba mutanen kirki bane sai busa hayaki suke.

Daya kansa gashine an masa kitso har gadon baya. Dayan kuma duk fuskar sa a dadauje da yanka. Dayan kuma cangala kafa yake.
Kai daga nesa ma sai sun baka tsoro bare kuma.ka karaso kusa dasu.

Amman a haka Mami ta karasa inda suke, dayan ya ce
“Muna sauraron ki hjy fadi damuwar ki.”

Mami ta ce
“Daman wani aiki nake son na saku kuyi min.”

Ta zura hannu a jaka ta dauko bandir din dubu daya guda uku ta mika musu.

Daya a ciki ya ce,
“Kai irin wannan kudin da dukkan nin alama akwai kasada a cikin sa.”

Mami ta girgiza kai ta ce.
“A’ah! Babu wata kasada wata yarinya ce take auren ‘da bata sa aikin yi saidai kawai ta kwashe masa kudi. Gata yawon vanza take, gashi ta raina ni, ta asircen yaro, Shine nace bari nazo na sa a kashe ta kawai a huta kwanan nan taiyi silar mutuwar dana karami.”

Dayan ya ce,
“Hajiya duk labaran nan da kike bamu bazai amfane mu da komai ba. Aikin da kike so kisa to muna bukatar dadin kudi ko dubu dari biyar ne, dan wannan ba karamin aiki bane.”

Mami ra ce,
“Ku kwantar da hankalin ku wannan kudin da kuka nema zan baku fiye da haka in bukata ta biya.”

Dayan ya ce,
“An gama ita wannan mata da kike magana akan ta idan muje gidan tayaya zamu gane ita ce.”

Takarda Mami ta mika musu ta ce,
“Ga address din gidan ita kadai ce a gidan sai shi, duk inda kuka ga mace a cikin gidan ku kashe ta kawai ita ce. Basu da ko yar aiki dan haka duk inda kuka ga mace kawai ku kashe ta.”

“Ba matsala hajiya aikin nan kamar anyi an gama ne.”

Mami ta ce,
“Idan naga kyakywan saka mako kuma zakuga da kyau zan baku kyakyawan ssakamako,”
“Kije zakiji labarin komai.”
“Nagode!”

Ta tafi tana murna zata ga bayan Amina.

*To Mami ai mutuwa sai Allah ya kawo lokacin ta. In Amina lokaci yayi sai kiga ta mutu da a kashe da kar a kashe ta da tana da lafiya da bata sa lafiya. Kai Allah yasa mufi karfin zuciyar mu. Masu hali irin na Mami Allah ya shirya su. Haka kiyayya take Allah kada ka daura mana kiyayar bayin ka a zuciyar mu.*
*Wannan labarin tabbas shigen sa ya faru. Komai kake ji to wata rana zaka gani. Duniya ta baci kiyayyar ma akan abinda be kai ya kawo ba dan kawai basu da hali take mata wannan kiyayyar*
*kiyayya mugun abu ce muna addu’a Akan Allah ya tsarkake mana zuciyar mu. Dan zuciya bata da kashi. In har zuciya ta gyaro to komai zai zamo mai sauki.*
*Allah yasa mu gama lafiya.*
*Ameen*

Washe gari kamar yadda Amina ta saba tin asuba bata koma ba. ta gyara gidan ta turare ta hada musu break.

Wanka ta shiga tayi ta shirya cikin wata blue din doguwar riga.

Sai jan mayafi da tayi rolling dashi. dakin Yaa Ahmad tayi, lokacin ya fito daga wanka dan haka jallabiyya kawai yasa suka wuce daining.

Sai da suka karya sannan suka koma daki.
Yau ba da wuri zai fita ba dan haka suka zauna kallo wajen sha biyu ya mike yayi bangaren sa cikin rabin awa ya fito cikin shirin sa.

Blue balck din suit ya saka ta cikin kuma dark blue.

Amina na ganin sa ta mike ta na gyara masa gaban rigar.

Murmushi yake ya ce,
“Ni dan gatan Meenal.”

Amina ta ce,
“Ai ka wuce haka.”

“Da gaske?”
“Eh man.!”

Rumgume ta yayi yana sinsinar wuyan ta.

“Baby na bana son nayi nesa dake wallahi.”

Murmushi Amina tayi ta ce,
“Haba ai muna tare ka manta da nafi komai kusanci dakai tinda ni ina cikin zuciyar ka tunanin ka da kwakwalwar ka. Kaga kuwa nafi komai kusanci da kai.”

“Haka ne Baby nah. To ni zan tafi.”
Kai ta dago ta kalle shi.

ita ma ba son fitar tasa take ba amman to ya zatayi dole ya fita dan neman musu halal din sa.

“To Love ka kular min da kan ka. Allah bada sa’a a abinda zaka je nema. Allah tsune idon duk macen da zata kallan min kai.”

Dariya yayi ya kara matse ta a jikin sa. Wani dadi yake ji na ratsa shi wanda baya son ya daina ji.

“Ki kwantar da hankalin ki, ni naki ne ke kadai insha Allahu.”
Ya fada yana kissing wuyan ta.

Idon ta a lumshe ta ce,
“Allah ya yadda.”

“Ameen!”
Ya amsa.

Kasa sakin ta yayi sshine daga ya juya ta na sai ya juya ta nan.

Wani so da kaunar ta yaji yana kara shigar sa.

Ita tayi karfin halin ce wa.
“Dady na jira fa.”

“Uhmm ban son na tafi na barki.”
Murmushi tayi ta ce,
“Ai ina nan ina jiran ka zan maka girki da kwalliya me kyau.”

“Da gaske?”
Kai ta daga masa ya ce,
“To muje!”

Ya kamo hannun ta suka fice sai da ta saka sa a mota sannan ta rufe ta matsa gefe tana masa addu’a hadi da daga masa hannu.

Dai dai zai fita s’ai ga mota nan na kunno kai.

“Motar Na’ima ce!”
Ta fada tana nunowa Ya Ahmad ita.

Fitowa yayi daga tasa ya tsaya, sai da ta parking din ta sannan ta fito.

Tana fitowa tayi wajen Amina ta ce,
“My sweet Anty!”
STORY CONTINUES BELOW

Suka rumgume juna. Sai da ta gama gaishe da ita sanna ta juya ga Yaa Ahmad da ya zuba masu ido dan sun burge shi.

Dan durkusawa tayi ta ce,
“Ina yini?”

Harara ta yayi ya ce,
“Ashe kin san da ni a tsaye ki ka tafi gun ta.”

“Haba Yaya Anty nah ce fa.”
“Kaji ka ina ruwan ka da mu.”

Amina ta fada.
“Lah hade mun kukai. Ai shikenan ko na tashi a aiki bazan dawo ba tinda haka ne.”
Ya fada yana yin wajen motar sa.

Na’ima ta ce,
“Sai na kwana.”

“Mijin naki fa?”
Yaa Ahamd ya tambaya.

“Ai yasan Anty Amina zai hakura na kwana.”
“Gidan ku!”

Yayi mata dakuwa. Amina ce tayi gunsa tana karai masa addu’a.

Janyo ta yayi ya ce,
“Ni ko?”
Kai ta girgiza ta. Ce,
“A’ah!”

“To kiss me kafin na tafi.”
Ido ta zaro, tana wai waye wai waye.
Ya ce,
“Na’ima ta shige. Oya kiss me”

Kai ta girgiza, janyo ta yyai ta fada kan sa ta zauna.

Hade bakin su yayi gu daya sai da ya samu nutsuwa sannan ya sake ta.

Da sauri ta mike ta bar gun a guje.  Dariya yayi ya rufe kofar ya fita.

Na’ima ta samu zaune a falo ta cire mayafi ta ajiye jaka.

Tana shiga tayi gun ta jakar ta dauka ta dauko wata leda ta mika mata.

“Ga wannan ko wanne da akwai takarda a ciki in kin tashi amfani dasu.”

Dariya Amina tayi ta ce,
“Nagode!”

“Kai Anty mene abin godiya.”
Murmushi Amina tayi.

Suka zauna suna hira. Can ta mike ta ce,
“Bari naje nai wanka na kawo miki abinci ko?”

“To Anty!”
Amina ta Mike tayi ciki ya rage Naima kadai a falo tana kallo

tayi dai dai da ita sai kace gidan ta. Kamar daga sama taga kartin maza sun shigo mikewa tayi da sauri ta ce,
“Su waye ku?”

Basu bata amsa ba sai bundiga da suka ddauko suka harbe ta.

Harbi uku suka mata kowa waje daban daban.

Sannan suka juya suka fice a guje.
Amina na fitowa taga Na’ima kwance cikin jini ai tini ta rude waya ta dauka ta kira Yaa Ahamd.

Yaa Ahmad da sauri ya karaso gidan waya ya buga asibiti aka turo mota aka dauke ta.

Sai da sukaje asibiti sannan suka wuce gida.

Suna zuwa Suka tadda Mami da Dady a Falo.

Dady ya ce,
“Ahmad lafiya na ganka haka?”
Amina ya kalla yaga itama duk a birkice ya ce,
“Ko jikin ne?”
Kai Ahmad ya girgiza ya ce,
“A’a Dady Na’ima ce.”

Mami tai saurin katse shi ta ce,
“Me ya samu da Na’iman?”

“Dady, Naima ce yan fashi suka shiga suka harbe ta, yanzu haka munje asibiti.”

“To a wane condition take?”
“Dady sai dai hakuri Allah ya amshi a bar sa.”
“Inna lillahi wainna illahir rajiun!”
Dady ya fada.

Mami kuwa kuka ta fashe da shi tana cewa,
“Na shiga uku Naima ta mutu na shiga uku.”

Kuka take sosai Amina ce take lallashin ta amman bata san ma tana yi ba.
Bayan bakwai Mami ta shirya taje gun bokan ta akan Amina dai
Ya ce, ta kwantar da hankalin ta zai san abinda zzai mata.

Anyi zaman makoki inda ana bakwai kowa ya watse yayi gidan sa.

Amina ba karamin kuka tayi a wannan mutuwar ba shima dan har ciwo ta kwanta.

Boka yana zaune sai ga aljanni sa wanda aka aika jikin Amina da farko ya dawo.

Kallon sa boka yayi rai bace ya ce,
“Kai me ka dawo yi ba na aike ka ba?”

Shiru yai masa, bokan ya ce,
“Ka koma nace ko!”

Aljannin ne ya tashi sai jikin bokan a take bokan ya fara hauka.

Yana tsalle yana gudu yayi cikin gari yara na raka shi suna tsokanar sa.

Amina ce kwance ajikin Yaa Ahmad sai jijjiga ta yake dan tai bacci.

Wayar sa ce tayi kara ya duba Dady ne da sauri ya dauka.

Bayan sun gaisa yake tambayar jikin Amina

Da sauki Ahmad ya amsa masa. Dady ya ce,
“Kaga Maman taka itama a kwance va lafiya?”

Da sauri Ahamd ya ce,
“Me yake damun ta?”

“Gata na. Dai ina jin jinin ta ne ya hau ta sa damuwa a ranta.”
“Allah sauwake to gani nan zuwa.”

Da sauri ya mike Yana gyarawa Amina kwanciya.

Mikewa tayi ta ce,
“Ina zaka?”

Ya ce,
“Mami ce ba lafiya?”

Ido ta zaro ta ce,
“Can zaka?”

Kai ya gyada mata.mikewa tayi ta dauko after ta daura akan kayan jikin ta ta ce
“Muje”
Shi yaja motar har suka isa gida. Dady suka sama a falo, Bayan sun gaisa Ahmad ya ce,
“Ya jikin nata?”

“Da sauki ta dai samu bacci,”
Amina ta ce,
“Allah bata lafiya.”

Suna zaune Mami ta fito tana dariya tana tsalle. Dady ya ce,
“Hajiya!”

Kallon sa tayi ta sheke da dariya ta ce,
“Kai!”

Sanna ta kuma saka wata dariyar, ta kalli Dady ta ce,
“Tsaya kaji ni na hana Ahmad kusan tar Amina duk tsawon lokacin nan da sukai aure, ni na tura mata bakin aljanni ni naje gun boka na karbo maganin mutuwa ibrahim ya ci ya mutu, ni na sa a zo a kashe Amina Aka kashen Na’ima! Hahhhahaha!!

Ta kyakyale da dariya. Kallon ta Ahmad yayi ya ce,
“Dady anya ba zafin ciwo bane mu tafi asibiti.”

Dady ya ce ba wani zafin ciwo zata iya yiyuwa hakan ne.
Da gudu ta fice daga dakin tayi waje kafin Ahmad ya bita har ta fice daga gidan.

Da sauri Amina ta bi bayan sa suka shiga mota.

Da kyar suka kamo ta dan gudu take kamar jirgi

Sai da Ahmad ya kulle ta sannan ta lafa asibiti suka tafi.

Daga nan asibiti suka nufa. Gado aka basu dan a zaton su Jinin ta da ya hau shi ya kawo mata kamar hauka haka.

Amina ce ta zauna a gun ta Dady kuwa cewa yayi.

“Ita tasan me tayi ya dawo kan ta. Daman ance *kai kayi koma kan mashekiya* to tinda ta fara wannan maganar da kamshin gaskiya a ciki.”

Yaa Ahmad da Amina su suka tsaya akan ta. Mama kuwa kullum zata dafo abinci ta kawo asibiti.

Yan Uwan Mami da yawa sunje duba ta dan wasu sai Mamakin halin Amina suke duk abinda Mami tai mata amman ita ke xaune a gunta.

Komai ita take mata dan ma yawanci allurar bacci ake mata dan jinin ta ya sauka ko ta daina magangunun da take.

Da allurar ta sake ta zata tashi tai ta surutai da dariya dan ma a daure take. Komai Yaa Ahmad ya dire musu in yazo yaga Amina a zaune Mami na bacci ko tana surutai yai ta tausaya mata.

Shi kan sa yasan samun mace kamar Amina babban dace ne.

Ace duk abinda Mami ke mata ji yadda take dawainiyya da ita.

Yasmeeen ma tazo duba ta sun jima tare sannan suka tafi.

Sai da sukai wata guda a asibiti duk abinda ake mata ba wani sauyi sai gaba da yayi.

Duk gwaje gwajen kwakwalwar da akai mata ba abinda ke damun ta.

Daga nan ne suka bata transper zuwa asibitin mahaukata.

Amina kuka ta dinga yi tana tausaya wa Mami.

Mami mace yar gayu mai ta kama da kudi da mulki ita ta koma haka.

Tai ta surutai da dariya in kuwa ta samu hanya tace zata fita.

Ba yadda sukai haka suka maida ita asibitin mahaukatan acan ma ba sauyi sai gaba da abin yake.

Nan ma wata daya tayi Amina na gidan su Yaa Ahmad suna kara bawa Dady hakuri akan yai hakuri da Halin da Mami ke ciki.

Mama da kan ta tazo ta bashi hakuri shine ya sauko har ranar yaje ya dubo ta.

Mami na ganin dady ta ce,
“Alhaji kaga ko? Kasha fada min naji tsoron Allah amman naki.”

Sai kuma ta saka dariya ta ce,
“Wajen boka na kan hayi naje shi yayi komai Alhaji.”

Sai ta kuma sa dariya ta kalli Mama ta ce,
“Kema sai nayi maganin ki.”

Sai kuma ta fashe da kuka. Amina ita ta dinga lallashin ta duk da Mami ba sanin abinda tayi tai ba.

Sai dai ta tsaya kallon Amina kawai kamar ta samu TV.

Bayan sun koma gida ne Mama ta ce da Dady,
“Alhaji ya kamata a dawo da Hajiya gida haka ai mata na hausa da rokan ubangiji.”

Kai Dady ya jinjina ya ce,
“Nima tunanin da na fara kenan zan fadawa Malam tanimu komai sannan zan je gun Malanta shima Allah yasa a dace.”

“Ameen!”
Mama ta amsa da.

Ai kuwa a satin suka dauko Mami daga asibitin mahauka ta.

Gida suka dawo aka dinga mata sauka da rubuta mata tana sha.

STORY CONTINUES BELOW

Alhamdulilah ba ai sati biyu ana yi ba Mami ta daina cewa zata fita a guje.

Sai da surutai da take yi kamar radio.surutan da basu da kai. in ba bacci take ba bata taba yin shiru.

Haka Amina ita zatai mata wanki, wanka ma sai ta tsaya akan ta.

Abinci ma in ba Amina ba ba mai bata taci.

Komai in ba Amina ce tace tayi ba bata yi.

Haka da dare zata zauna tai tayi mata karatun alkur’ani har tai bacci.

Alhamdulilah cikin sati Mami jiki ya kara sauki da surutun ma ta rage.

Sai dai bata taba yadda da kowa kamar Amina.

Dan ko Ahmad ne yazo yai mata magana sai ta kalli Amina alamar ta kula sshi sanna zata kula shi.

Haka Dady ma, sai ta kalli Amina take kula shi.

Duk inda Amina tayi tana biye da ita ko kitchen tare suke zuwa sai dai karan bani.

Mami ta koma kamar yarinya karama ba abinda take iya yi. Komai sai an mata
Haka Amina ke fama dan ko abcci take zata tashe ta ta raka ta bandaki.

Sai ta sa tayi addu’ar shiga bayi sannan take samu ta shiga.

A hankali Amina ta dinga koyar da ita abubuwa da yawa.

Addu’a kuwa ba a taba daina ta kullum cikin yin ta take.
Haka nan ruwan ta ya zama na addu’a gaba dayan sa.

Amina bata bacci kullum tana kan sallaya tana rokar wa Mami lafiya.
Yau kimanin watan Mami biyu da dawo wa gida kuma tin daga lokacin Amina ta fara fuskan tar canji daga yadda Mami take.

Yanzu duk abin yarintar nan ta daina sai dai ta zubawa Amina ido in ta na abu.

Yau kamar kullum suna zaune a falo Mami na zaune akan kujera Amina ta fito daga kitchen.

Gefen ta Amina ta zauna hannun ta rike da farantin faten dankali da wake da hanta. Sai lemo da ruwa.

Mami ta kalli ta ce,
“Mami na me nai miki ne kwana biyu kin canja ko kitchen din kin daina bina. Kuma ko nai miki magana bakya kula ni. Me nai miki Mami na wallahi gidan ba dadi in bakya min hirar ki kinji.”

Kallon ta Mami kawai ta tsaya yi, Amina ta ce,
“Dan Allah Mami na kimin murmushi.”

Murmushi kuwa tai mata sanna ta debo abinci a cokali tayi hanyar bakin ta da shi.

Kin bude baki tayi. Amina ta ce,
“Yau kuma ke da kika daina cin abincin hannun kowa sai nawa bude kinji abinda kike so na dafa miki.”

Idon Mami akan Amina ta bude bakin. Haka. Amina ta dinga ciyar da Mami har ta koshi ta bata lemo da ruwa.

Zama tayi ta dauko tarihin mazannin tana karanta mata.

Tana gamawa ta dauko alkurani ta dinga karanta mata.

Sai Yamma ta mike ta kalle Mami ta ce,
“Muje muyi sallah mu shiga kitchen ko?”

Mami dai shiru tayi tabi Amina da kallo har Amina ta kama hannun ta suka shuge ciki.

Har bandaki Amina takai Mami ta hada mata ruwan alwala sannan ta fito.

Sai da Mami ta fito ita ma ya shiga ta fita sukai sallah a tare.

Bayan sun idar sunyi addu’a Amina ta kalli Mami ta ce,
“Mami zaki rakani kitchen din ne ko bacci zakiyi.”

Mikewa Mami tayi ta bi bayan Amina. A kitchen suna girki Amina na bata labaran ban dariya.

STORY CONTINUES BELOW

Ta lura da Mami yanzu in anyi abin dariya takanyi murmushi kawai. Ba kamar da ba da zata tsaya kallon mutum ba. Sai kuma lura da ita da tayi ta kallo ta da take yawan yi.

A haka suka gama girki suka koma daki ta hada mata ruwan wanka ta ce taje tayi.

Wankan tayo ta fito mata da kaya ta saka.

Itama wanka tayi ta fito ta shirya cikin wani milk din material mai flower purple da pink.

Milk din fashion ta saka ta feshe jikin ta da kanshi.

Mami na zaune tana kallon ta hannun ta ta kamo suka nufi falo.

suna zama sai ga shigowar su Dady nan. Da fara’a Amina ta mike ta na masa sannu da zuwa.

Zama yayi ya amsa ya ce,
“Ya jikin Mamin taki?”

Amina ta kalli Mami ta ce,
“Alhamdulilah yanzu tana iya komai da kanta kaga sai dai ta daina magana sai kallo kawai.”

“To ga Malam Tanimu baya nan amman zan fada masa sai muga mai ne akwai.”

“To Allah bata lafiya ddai,”
“Ameen Ya Allah. Allah miki albarka kin mana abinda ba kowa zai mana ba.”

“Haba Dady ba komai ai ku iyaye nane in ban muku ba wa zan wa.”

“Amina kinyi kokari abu wajen wata biyar zuwa shida ana fama Allah ya bata lafiya. Allah kema ya baki me yi miki.”

“Ameen!”
Amina ta amsa
sannan ta ce,
“Dady ga abincin ka can ko nna zan kawo maka.”

“A’ah bari na shiga na watsa ruwa. Ahmad ma yaje dubo Maman ki ne yanzu zaki ganshi.”

Ya mike yayi cikin daki. Sai da Ahmad ya dawo sannan suka zauna suka hadu suka ci abincin gaba dayan su.

Falo suka dawo suna hira Ahmad ya kalli Amina ya ce
“Yau kuma lafiya Mami ba magana.”

Murmushi Amina tayi ta ce,
“Wallahi Yaa Ahmad tin safe nima taki kula nim,”

“Toh! bare kuma mu.”
Sukai murmushi.

Wajen karfe goma kowa yayi daki. alwala ta sa Mami tayi tai sa kayan bacci sannan ta kwanta Amina ta shafe mata jiki da maganin ta. Sannan ta tofe ta da addu’a.

Wanka itama tayi tai alwala tasa kayan bacci tazo ta kwanta a gefen Mami.
Can cikin dare Mami ta mike kallon Amina ta tsaya yi kafin ta ce,
“To me yake damun na haka?”

Tana mamakin yadda Amina ke kula da abubuwa to me hakan ke nufi.

Jin Amina na motsi yasa tai saurin kawnciyya. Amman a ranta ta ce zata ga kome yake faruwa.

*Haka rayuwa take in kana tunanin kafu karfin komai wata rana wani abun sai ya gagare ka, mu zauna da kowa lafiya bbamu san mai taimakon mu ba wata rana.*
*To kenan Mami taji sauki ko me?*
Muje zuwa dai.

18/08/2018
🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵
(Back to sender)
*Almost true life story*
Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*
🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐
Page *33*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

Washe gari ma kamar yadda Amina ta saba kula da Mami haka tayi.

STORY CONTINUES BELOW

Sai da ta sallame ta da komai cikin kulawa sannan ta nufi kitchen dan hada musu break

Tana gamawa ta hau yin aikin gidan itace share can goge can.

Tana kitchen Yaa Ahmad ya shiga. Gaishe shi tayi ta cigaba da aikin ta ba tare da ta kalle shi ba.

Ya jima yana kallon ta kafin ya taka a hankali ya isa gare ta.
Rungumota yayi ta baya ya daura kan sa akan wuyan ta.

Wani yarr taji kafin tai saurin janye jikin ta.
Kallon ta yayi idon sa jajir ta sauri kawar da idon ta daga kallon sa.

Matsowa yayi gefen ta ya ce,
“Haba Baby meyasa kike hanani kusan tar ki ne? In ban zo gareki ba wajen wa zanje.”

Kasa tayi da kai. To ya zatayi ai da kunya a gidan surukan ta tana biye masa gaskiya baza ta iya ba,

Kamo ta yayi ya ce,
“Please ko kiss ne ki bari nai miki kinji.”
Ido kawai ta lumshe.

Yana ganin haka ya matso da saurin sa ya cafki bakin ta.

Sosai yake taba ta har tana fitar da wani irin numfashi.

Kujerar dake kitchen din ya janyo ya zauna ya daura ta kan cinyar sa.

Bayan ta ya dinga shafawa a hankli a hankali har ta samu nutsuwar ta.

Tana jin ta dawo dai dai tai sauri mikewa daga jikin sa ta bar kitchen din.

Bata dawo kitchen din ba sai da ta san ya bar shi.

Aikin ta ta karasa, jiki a sanyaye da haka ta gama komai Mami na kallon ta sanna tayi wanka ta hadowa Mami break din ta.

Sai ta gama bata sannan ta ja ta sukai falo.

Su Dady na fito Amina ta gaishe shi sannan ta kara gaida Yaa Ahmad da sai binta da kallo yake.

A gaskiya yana bukatar kusantar matar sa dan kwana biyun nan ba karamin wahala yake sha ba.

A haka ta hada musu break. Sai da suka ci suka tafi aiki sannan taci sauran su.

Ta mike ta wanke kwanu kan ta hada musu abincin rana.

Haka suke yini da Mami ba uhm bare uhm uhmm dan tinda ta samu lafiya bata kara magana ba.

Sai kallon su da take taga me yake faruwa.

A haka Amina ta cigaba da kulawa da ita.

Sai da Mami tayi sati biyu da samun lafiya ta gane Amina jinyar ta take sannan ta fara nadamar irin tsanar da taiwa Amina.

Wani lokaci haka zata raba dare tana kukan tana rokar Allah yayafe mata abinda tta aikata.

Tin daga lokacin Mami ta daina zaman falo kullum tana daki tana kuka da neman yafiyar ubangiji.

Amina kuwa zaman Mami a daki na damun ta wannan yasa Dady yana dawowa yau ta fada masa.

Murmushi yayi ya ce,
“Yau Malam ya ce zai dawo kuma zai zo insha Allahi.”

Wannan ne ya kwantar da hankalin Amina.

Mami kuwa kunyar Amina da su Dady yake hanata fitowa.

Yau da dare suna zaune a falo duk kan su banda Mami dake daki aa kwance

Ba abinda take sai istigifari na neman yafiyar ubangiji sai yanzu ta gane hanyar da tabi da sam ba me kyau ba ce.

Malam tanimu ne ya shigo tare da Dady. Kallon Amina Dady yayi ya ce,
“Amina je ki kira Mamin taki.”

STORY CONTINUES BELOW

Mikewa Amina tayi ta kira ta tare suka fito Mami biye da ita sanye da hhijab har kasa.
Malam na ganin ta ya ga ta canja sosai zama tayi a gefe.

Tofi Malam yai ya bata ta sha sannan ya sa akawo garwashi. Turare aka saka a gidan.

Mami lafiya kalou tana zaune. Sai da Malam ya gama sannan ya kalli Mami ya ce,
“Hajiya!”

Dagowa Mami tayi ta kalle shi. Malam ya ce,
“Ya kike ji yanzu akwai abinda yake damun ki.”

Kai ta girgiza. Ya ce,
“Masha Allah.”

Dady ya kalla ya ce,
“Alhaji, Hajiya ta samu sauki sai dai ga wanann magun gunan ta cigaba da amfani da su.”

Amsa yayi yai masa godiya, sukai bankwana dashi,

Suna dawowa suka tadda Mami na kuka Amina na lallashin ta.

Dady ne ya zauna ya ce,
“Ai ba kuka zakiyi ba sai ki godewa Allah da yasa baki mutu a halin da kike ba a baya godewa Allah lallai Allah yana son ki.”

Kuka Mami ta kuma saki ta ce,
“Alhaji na dade da gane haka. Na jima da fuskantar haka.”

Duk dakin kallon ta sukai suna mamaki. Dady ya ce,
“Haka ake su bawa ya gane gaskiya. Yarinyar da kika tsana kika tsamgwama ita ta zame miki gata daman na fada miki wata rana sai kinyi al fahari da ita gashi nan tin ba aje ko ina ba.”
Kuka Mami ta kuma saki ta ce,
“Alhaji sai yanzu na gane Amina gata ce a tattare da mu. Duk abinda yya faru da Amina da na mutuwar ya’ya na duk ita na jefa dasu. Allah ba azalumin bawan sa bane sai gashi komai ya juye min tabbas wannan ake kira *’kai kayi koma kan mashekiya* na tura mata abu duk sun dawo kai na. Nagode wa Allah da ka ganar da ni.”

Shiru tayi sannan ta cigaba da magana
“sai ranan na fuskanci wace Amina. Amina yarinya ce mai hankali nutsuwa da ilimi ga girmama ma na gaba da ita tinda da na ji sauki amman na tsaya naga me yake faruwa. Yadda take tafiyar dani shi ya ban mamaki duk da ba a hankali na nake ba bata nuna wani kyama ko tsangwama ba wanda nasan ko dan cikina sai haka yadda take son ganin farin ciki na da min addu’a ma kadai abin lura ne banda dawainiyya da tayi dani “

Amina ta kamo ta rumgume ta ta saka kuka.
Jijjiga ta Amina ta dinga yi tana lallashin ta. Ta ce,
“Haba Mami mene abin kukan yanzu fa lokacin farin ciki ne, Allah ya baki lafiya.”

“Dole nayi kuka Amina dole nayi na cutar dake iya kar cutar wa.”

Dady ta kalla ta ce,
“Alhaji ka taya ni neman gafarar Amina dan na kasance a zaluma a gare su, Alhaji tinda Amina ta auri Ahmad nasan bai taba kusan tar ta ba. Alhaji ina zan kai hakkin yaran nan. A lokacin banyi tunanin iri Halin da zasu shiga ba. Har da ‘dana ban sa halin da Ahmad zai shiga ba dan nasan zai iya yin komai dan samun kwanciyyar hankalin sa tinda na hana shi kula Amina zai iya zuwa ga matan waje. Alhaji ina zan kai hakkin su na wannan ina zan kai hakkin Amina na tura mata aljanni da nayi ina zan kai hakkin ‘ya’yana da na kashe.”

Amina ce ta gangara kusa da ita tana zubar da hawaye ta ce,
“Mami ki kwantar da hankalin ki, ni dai na yafe miki duniya da lahira wallahi ban taba rikon ki da komai ba na dauke ki uwa. Nasan komai me karewa ne dan Allah ki daina kuka ki ta Addu’a Allah ya yafe miki amman ni na yafe miki wallahi “

Kallon ta Mami ta tsaya yi ta xe,
“Kin yafe min? Kin yafe min fa kika ce? Dan Allah da gaske? Alhaji kaji wai ta yafe min.”

Ta kalli Dady. Dannan ta kalli Ahmad ta ce,
“Ahmad! Kaji ta yafe min yanzu duk abinda nai miki kin yafe min.”

Kai Amina ta daga tana share hawaye ta ce,
“Na yafe miki Mami wallahi na yafe miki.”

Rumgune juna sukai suna kuka can kuma ta karasa gefen Dady ta ce,
“Alhaji dan Allah….”

Bata karasa magana ba ya dago ta ya ce,
“Ba komai Na yafe miki Allah ya yafe mana vaki daya.”

Hannun Ahmad ta kamo zatai magana ya ce,
“Mami na kada ki nemi yafiyata Mami na baki taba min komai ba ko in kin min komai ma na yafe miki nima ki yafe min.”

“Allah maka albarka Allah maka Albarka Allah baka zuri’a ta gari Allah ya kara muku dankon soyayya tsakanin ka da Amina. Hakika Amina ita tafi cancanta da samun ka sai yanzu na gane wace Amina na tabbata da wata ka auro baza ta kula dani haka nan ba. Allah muku Albarka daga kai har Amina.”

Kuka dukka suke ban da Dady dake murmushin shiriyar Mami.

Sai da sukai sallah raka’a biyu sannan kowa yayi makwancin sa.

Mami sai nan nan take da Amina.
Washe gari tare suka gyara gidan suka hada break duk yadda Amina tazo ta bari ki tayi ta ce
“A’ah in da Na’ima ce baza ta ce ta bari ba.”

Da haka suka gama suka shiga daki sukai wanka suka fito suka shirya.

A falo suka samu su Dady suma sun kimtsa sai da suka gaisa sannan suka wuce suka karya.

Suna gama karyawa suka koma falo gaba dayan su.

Mami ce ta kalli Dady ta ce,
“Alhaji so nake muje umara ni da Amina da Maman ta.”

Murmushi Dady yayi ya ce,
“Hakan ma yayi, Yanzu Ahmad sai yaje yai muku komai kuje kuyi azumi acan ni zan biyo ku daga baya.”

Ahmad ya ce,
“Amman dai dani zaku tafi ko?”

Dady ya ce,
“Ma tafi tare ko?”
Cikin kankanin lokaci aka shirya musu tafiyar su.

Ana fara azumi suka daga. Inda Tinda zuka je Mami da Amina ba abinda suke sai rokar Allah da ibada.

Bama Mami da ta dage da addu’a Allah ya yafe mata, sai da akai azumi sha biyar sannan su Dady suka dira.

Sun sha ibada inda ana sallah suka wuce dubai dan yin siyayya daga can kuma suka yo gida gaba dayan su.

A gidan Mama suka sauka, sai kashe gari Dady da Mami suka tafi gidan su.

Amina kuma ta ce, sai ta huta zata koma gida. Wannan yasa Ahmad kin tafiya shima.

Mama dai ganin za’a ta kurawa Ahmad yasa ta ce, su tattara su tafi su bar mata gida.

Gidan Mami suka je su mata sallama. Mami ta ce ai Amina baza ta koma ba sai ta gyare ta.

Ba dan ya so ba haka ya hakura ya bar ta amman ji yake kamar yai kuka.

A kalla watan su bakwai ba tare ba, sai dai kallo daga nesa duk yadda yake bukatar ta haka ya jure amman yanzu ma a ace sai an gyara ta.

Wane gyara za ai mata shi a bashi a bar sa haka.

Dady na jin sa lokacin da yake mita dan haka murmushi kawai yayi.

Washe gari ya samu Mami ya ce,
“Kiyiwa Amina abinda ya kamata ta koma dakin ta kinji ko?”

“To Dady daman dan gyaran mu ne na mata da su lallai da gyaran kai. Amman nan da Litinin zata koma.”

Dady ya ce,
“Har sai littinin ki daure ta koma ranar juma’a ai abin yai yawa sati kenan,”

“An gama Alhaji yadda kace haka za’ayi.”

Kamar Amarya haka Mami ta maida Amina dan me gyaran jiki ta dauko mata ta zo tai maka gyaran kwana biyar sannan tai mata lalle da kitso me kyau ya zubo bayan ta
Kaya Mami ta dinka mata banda Engliah wears da ta siyo mata akwati guda.

Kafin ranar lahadi Amina ta koma kamar amarya sosai.
Dan jikin ta ya kara kyau sai tsantsi yake. daga nesa ma sai ta baka sha’awa bare kuma tana kusa da kai,
Mami da kan ta tai mata hade hade ta bata da wasu turaruka masu dadi.
Mami da kanta ta dauki Amina ta kai ta gidan ta. Gidan da aka canja mata kayan daki dan sai a lokacin ma ta gani.
Nasiha sosai Mami. Tai mata tare da kara bata hakuri kan abinda ya faru sannan ta tafi da kewar Amina dan ba karamin sabo sukai ba.
Mami na tafiya Amina ta mike ta shiga kara kimtsa gidan.
Turaren wuta ta kuma jona wa ta shige ban daki.
Wanka ta karayi ta fito ta shirya cikin wani dogon wando da ya dame ta sai yar riga pink kala.
Ribom pink ta saka ya kama kanta ta dauko wata golding din doguwar riga ta saka.
Tana cikin fesa turare Yaa Ahmad ya shigo sanye cikin wata golding din shadda sai sheki take ke ka rantse unguwa zai je ko bikin sa ake.
Dakin ya shigo da sallama hannun sa rike da leda. Yana ganin Amina ya bude mata hannun sa ta taho da gudu ta fada jikin sa.
Hannu ya sa ya rufe abar sa, ya ce,
“Alhamdulilah! Alhamdulilah!!”
Ya fada yana ajiyar zuciya. Gefen gado yayi da ita dan ji yai kafar sa na son kasa daukar su.
Sai da ya ji gwarin jikin sa sannan Ya ce,
“Muje muyi alwala muyi sallah ko?”
“Ina da Alwala.”
Amina ta bashi amsa.
Mike wa yayi ya shiga bayi yai alwala ya fito ya shimfida musu sallaya.
Sai da suka gabatar da sallah raka’a biyu sannan ya janyo ledar da ya shigo da ita.
Budewa yayi ya ce,
“Yau ita ce ranar amarcin mu dan haka sai kin kara cin kaza amarci.”
Fuska Amina ta rufe. Dariya Yaa Ahmad yayi ya ce,
“Ah lallai yarinyar na kunya zama ki daina jin ta ne.”
Da kan sa ya ciyar da ita sannan suka shige ban daki sukai brush suka dawo daki.
Da kansa ya cire mata rigar da ta daura.
Kallon ta ya tsaya yi ya birkice da shigar da ya ganta da ita.
Har bai san lokacin da ya janyo ta jikin sa ya fara romancing nata ba.
Lips din ta ya kamo ya fara totsa kamar alawa. Ya jima yana murzar ta……….
***************
***************
***************
***************
Ahmad ba karamin wahalar da Amina yayi ba dan ya maida ita cikakkiyar mace sannnan ya sarara mata. Bai lura da yadda yai mata ba sai bayan ya samu nutsuwa yaga yadda take fitar da numfashi sama sama.
Da kyar ya iya daukar ta ya kaita bayi. Sai da ya tsarkake ta sannan ya dawo ya cire zanin gadon ya canja wani.
Dauko ta yayi ya saka mata kayan bacci sannan ya kwantar da ita bayan ya jata jikin sa yana lalashin ta. Yana sa mata albarka.
STORY CONTINUES BELOW
Cikin kan kanin lokaci bacci ya dauke ta.
Mikewa yayi ya dauro alwala ya dawo ya tada sallah.
Ya jima yana sallahr godiya da Allah da ya mallaka masa Amina.
Sai asuba ya mike ya je dan tashin Amina zafin da yaji jikin ta shi yasa be tashe ta ba.
Sai da ya dawo daga massalaci sannan ya kira Dr ya fada masa abinda ke faruwa.
Dr ya ce, zai shigo anjima ya dubata. Ya kawo mata magani.
Da haka ya koma daki. A hankali ya dinga shafa kanta zuwa bayan ta.
Da kyar ta iya bude ido. Baki ta dan turo tana gyara kwanciyya.
“Sorry Baby nah kinji zaki makara yin sallahh!”
Da sauri ta mike zata sauka.
Zafin da taji ta kasan ta shi ya hana tamikewa ta koma ta kwanta tana matsar kwalla.
Ganin haka yasa ya dauke ta yayi bandaki da ita.
Sai da tai alwala sannan ya dauko ta. A zaune tai sallah inda tana idarwa ta kwanta a wajen.
Da sauri Ahmad ya mike ya dawo da ita gado yana lallashin ta har wani baccin ya kuma dauke ta.
Sai bayan karfe sha biyu ta farka. Yaa Ahmad ta gani ya saka ta a gaba sai kallon ta yake.
Yana ganin tta tashi yayi gun ta yana mata sannu,  hijab ya dauko ya sa mata ya dauke ta sukai falo.
Doctorn dake dubata ta gani, akan kujeta ya zaunar da ita ce,
“Dr kaji jikin har yanzu bai sauka ba. Gashi bata iya tafiya.”
Amina na jin bayanin sa tai kasa da kai a zuciya tace
“Amman Yaa Ahmad bai kyauta min ba. Komai nawa sai Dr ya sani.”
Dr ya ce,
“Kar ka damu zan mata allura daga nan zata samu sauki insha Allahu. Sai wannan ta sha shi sannan tana shiga ruwan dumi.”
Kai ya gyada ya janyo ta jikin sa, Dr ya hada allura ya Ahmad ya dan bude masa gun da zai mata.
Yana mata ta kamkame shi. Mulmula gun yake yana dan jijjiga ta sannan yai wa Dr sallama ya tafi.
Daukar ta yayi ya nufi bandakin ta da ita. Suna shiga ta ce, Ya fita zata iya da kanta.
Fita yayi ba dan yaso ba dan yasan kunya take ji dai kawai.
Sai da ta gasa jikin ta sosai sannan ta samu tai wanka ta fito tana takawa a hankali.
A dakin ta same sshi tana fito wa ya tare ta yana goge mata jiki.
Mai ya dauko ya shafa mata ya dauko wani mini siket ya saka mata ya dauki wata karamar riga ya zura mata
Mikar da ita yayi yana kallon yadda kayan sukai mata.
Ba karamin kyau tayi ba. Rumgume ta yayi ya ce,
“Allah miki albarka Amina. Allah ya saki a gidan aljanna Allah ya biya miki bukatun ki na alheri Allah ya saka miki da alheri”
Murmushi tayi ta amsa da
“Ameen!”
Mikewa yayi ya fita can sai gashi da katon basket.
Kayan abinci ne Mami ta aiko musu dashi.
Farfesun kayan ciki ne da dankali sai ruwan zafi da gashin bread.
Shi ya dinga bata a baki har ta koshi sannan ya dauke ta sukai falo.
Tausa ya dingai mata har tasamu bacci ya dauke ta.
Kallon ta ya tsaya yi gana godewa Allah da ya bashi Amina dan shi kadai yasan me yaji game da ita.
STORY CONTINUES BELOW
Duk motsin da zatai sai ya jijjiga ta kasa tashi yayi ya bar ta.
Da kyar ya mike ya shiga ya gyara dakin da suka kwana sannan ya dawo ya tasata a gaba da kallo.
Karfe biyu saura kwata ta mike,  ta a mika
Yaa Ahmad ta gani yya zuba mata ido sai murmushi yake.
Fuska ta dan bata ta ce,
“Kai kuma me gadi ka zama ne.”
Murmushi yayi ya ce,
“Indai gareki ne zan zama abinda yafi me gadi ma.”
Murmushi tayi ta kalli agogo ta ce,
“Yaa Ahmad lokacin sallah fa yayi.”
Agogo ya kalla ya ce,
“In ina tare dake manta komai nake alwala fa nayo amman na kasa tashi.”
Murmushi tayi ta ce,
“To kaje Kar a idar.”
Mikewa yayi yai mata kiss a kunci sannan ya fice.
Murmushi tayi ta mike a hankali ta wuce daki.
Wanka ta karayi sanna ta fito tai sallah.
Wata doguwar riga ta saka wacce daga sama ta matse daga kasa kuma ta bude.
Bata sa hula ba ta zubo da gashin ta baya ta nufi kitchen.
Kayan miya ta diba tai blanding ta dauko kaza ta tafasa ta soya ta hada miya.
Ruwan tafiya ta daura sai ga Yaa Ahmad nan.
Kallon satayi tai murmushi ya karaso ya ce,
“Wai girki kike yi?”
Kai ta gyada ya ce,
“haba Baby ai kin gaji da kin bari gashi can na karbo gun Mami.”
“Na shiga uku!”
Amina ta fada tana marairai ce fuska.
“Gun Mami fa ka ce, kai Yaa Ahmad me kace mata to?”
Kallon ta ya tsaya yi yadda take magana cikin shagwaba tana bubbuga kafa a kasa.
Murmushi yayi ya ce,
“Ko ban fada ba tasan me ya faru ai.”
Hararar sa tayi tayi waje tana dingisa kafa.
Murmushi yai yabi bayan ta ya dauke ta suka karasa falo.
Abincin ya zuba musu ya janyo ta yana bata a baki.
Har suka gama bata ce kala ba. Sai da ya janyo ta ya fara romancing nata ne ta ce,
“Yaa Ahmad!”
Daina wa yayi ya ce,
“Mene?”
Kukan shagwaba ta farayi ta ce,
“Amman Yaya ai be dace ka fadawa Mami ta baka abinci ba.”
“To ya zanyi?”
Ya fada yana kallon ta.
Kallon sa tayi
“Yaya to ai zan iya.”
Murmushi yayi ya ce,
“To kiyi hakuri bazan kuma ba.”
Horn suka jjiyo.   Amina ta mike ta fara dingisawa tayi cikin daki.
Mayafi ta dauka tayi rolling sannan ta dauko takalmi me tudu ta saka.
A Hankali take tafiya har ta karaso cikin dakin. Wacce ta gani ce yasa ta fara sauri.
Yasmeen ce tare da Muslim da sauri ta karaso gun ta kallo ta Yasmeen ta tsaya yi ta ce,
“Ciwo kika ji ne?”
Ahmad! Amina ta kalla sannan ta ce,
“Wallah!”
Sai da ta rungune ta suka gaisa da Muslim sannan ta kalli Yasmeen tace,
“Amarya ya gida?”
Murmushi Yasmeen tayi ta ce,
“Amarya kuma amarci ai an bar muku. Ya kuka dawo ya hanya?”
“Lafiya Alhamdulilah!”
Mikewa su Muslim sukai zasu fita. Ahmad yayi gefen Amina ya rada mata abu a kunne suka fice.
STORY CONTINUES BELOW
Tinda ya rada mata tai kasa da kai sai da suka fita sannan ta dago.
Kallon ta Yasmeen tayi ta ce,
“Oh kudai har yanzu kuna nan kamar kwa cinye juna kenan.”
Hararar ta Amina tayi ta ce,
“Dallah can ya garin ya naga kina wani haske ne kin kara kyau ko dai?”
Murmushi tayi ta ce,
“Abinda nazo nai miki albishir kenan. Wata uku dan kiji.”
“Masha Allah. Allah ya raba lafiya. mun kusa zama Momy kenan.”
Sukai dariya daga nan sai hira ta barke.
Sai bayan magariba su Yaa Ahmad suka dawo anan suka ci abincin dare sannan suka tafi,
*******—-*******
*6 years later*
Dukkan su suna cikin gidan Mami suna zaune a falo.
Amina ce zaune a one sitter tana waya da Kawar ta Yasmeen, Ahmad kuma na zaune a hannun kujerar daga gani jira yake ta gama wayar yai mata magana.
Sai wasu twins duk mata suna sanye da doguwar riga iya kar gwiwa. Kan su an musu two babies an saka musu ribon kalar rigar su wato pink. suna kan Dady suna ta wasa. Yaran ba su fi shekara uku uku ba kyawawa dasu. Kamar yayan larabawa.
Sai wani Namiji dake gefen Mami yana nuna mata Wani a wata tab dake hannun sa.
Yaron kyakyawa ne, kamar dan labarabawa shekarun yaron bazai fi biyar zuwa shida ba. Yana sanya da brown din dogon wando sai sky blue din riga me gajeren hannu.
Yan tagwaye, kuma kamar su daya da Amina.
Jasmeen da take hassana ta ce,
“Yaa Aadil naga vedio da ka saka.”
Tasleem ta daga Dady da gudu tayi gun sa ta ce,
“Yaa Aadil ni zan fara gani.”
Amina da take waya sun cika mata kunne ta ce,
“Keep quite!”
Da sauri duk sukai shiru, Wayar ta karasa amsawa sannan ta kashe
Juyo da kallon ta tayi wajen ya Ahmad ta ce,
“Yane Love!”
Rada yai mata a kunne, ta dan dago ta kalle shi sannan ta kalli Mami da Dady ta ce,
“Tin yanzu!”
Kai ya daga mata ya ce,
“Ba yau zasu je gidan Mama ba sai mu bar su mu tafi Abujan ko?”
“Toh!”
Ta fada tana kallon su Aadil.
Ta ce,
“Mami zamu tafi.”
Mami ta ce,
“Yan hutu yau sai gidan Mama ko?”
Jasmeen ce ta mike ta ce,
“Yes Ganny.”
Tasleem ta kalli Amina ta ce,
“Momy mu tafi to?”
Aadil kuma ya mike ya shiga dakin su na gidan Mami ya dauko jakar labtop din sa.
Ahmad da ke gefen Amina har yanzu ya mike zai dauko mata mayafi a dakin Mami.
Mami ce ta kalle shi ta ce,
“Ba sai ka dauko ba ina son magana da ita.”
Mami ta mike, Amina ta bi bayan ta tana masa gwalo.
Dady kuwa dariya yayi ya ce,
“Aadil dauko muku ledar ku kayo shopping jiya.”
Daki yayi ya dauko suka dawo.
Mami da Amina suka fito suna dariya. Kallon su Ahmad yayi ya dauke kai wai yayi fushi.
Jasmeen ta ce,
“Lah Momy kinga Abbi na fushi.”
Amina ce ta maida kallon ta ga Ahmad tayi dariya.
Tasleem kuma ta ce,
“Abbi me akai maka?”
Aadil kuwa dariya yayi ya ce,
“Lah Abbi dan Mami ta kira Momy ba a kira kaba shine kake fushi.”
STORY CONTINUES BELOW
Dariya dukka dakin sukai. Murmushi Ahamd yayi ya ce,
“Kun gansu nan haka suke min suyi ta hade min kai.”
Tasleen tayi gun Amina ta ce,
“Nima ina gun su Momy.”
Jasmee kuma tayi gun Dady ta ce,
“Abbi ka kyale su Mami kaji.”
Aadil kuma ya ce,
“Tab ni dai ina gun Ganny papa ko?”
Yayi gun Dadyn su.
Da haka suka debi yaran sukai gidan Mama dasu.
Amina na parking suka bude suka fice a guje.
Ta fito kenan ya kamo hannun ta. Kallon sa tayi ta ce,
“Haba love ka bari mu shiga mu fito, yanzu zamu tafi fa.”
Murmushi yayi ya ce,
“Zan iya jiran kuwa.”
Dariya tayi ta ce,
“To mu tafi?”
Dariya yayi ya ce,
“Lallai ko Maman bamu gaisar ba.”
Suna shiga suka ga duk sun saka Mama a tsakiya kowa sai labari yake bata.
Gaban su kuma ice cream ne da nama a faranti.
Ahmad ya gaishe da Mama haka ma Amina.
Ya ce,
“Mama ga su nan sunzo hutu sati biyu zasuyi zamuje Abuja mu ma.”
Mama tayi murmushi ta ce,
“To nagode kuwa ku kuma Allah kiyaye hanya.”
Mikewa yayi ya ce,
“My kids ba kuyi min addu’a ba I am going.”
Da gudu sukayo gun sa suna cewa,
“Papa Allah kiyaye hanya A dawo lafiya.”
“Ameen Sai na dawo.”
Ya fita.
Gun Momy suka yi suna cewa,
“Momy safe journey.”
Rungume su tayi tace,
“Banda rashin ki. Kuna taya Mama aiki kunji.”
“To Momy!”
Ta mike. Ta yiwa Mama bankwana da ita.
Amina ta fita suna dago mata hannu. Daga nan Airport suka wuce.
Suna zuwa aka kira su suka hau jirgi.
*******
Amina ce kwance a jikin Ahmad tana masa shagwa ta gaira ba dalili shi kuma duk ya rikirkice sai lalalshin ta yake. Daga lallashi kuma suka wuce duniyar ma’aurata.
nace adawo lpy.
*Alhamdulilah!”
Anan na kawo karshen littafina *Koma kan mashekiya*
Allah ina rokan ka kuskuren dake ciki Allah ka yafen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *