KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 10

 KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 10

Washe gari Umma ta zaunar da Mubeenat tana gaya mata ra’ayin Farhan a kanta. “Dan yayi wa Abbanku magana,yanzu ke dama akwai wanda kike sone kodai babu?”

Cikin jin kunya tace “Babu Umma,amma dai ina so ad’an bani koda kwana biyu ne.”

“Ba damuwa kije kiyi tunani,amma ni senake ganin kamar kinyi babbar sa’a idan kika zab’i Farhan a matsayin miji dan Yaron akwai nitsuwa ga addini bayi da matsala sam gashi kuma na gida an san kowa nashi.”

“To Umma nagode” sannan ta mik’e ta fice.

  Atif ne zaune a parlour Umma shida

Mubeenat “Ina jinki Sis Mubee gayamun”

“Ya Atif dama Ya Farhan ne yazo min da wani batu wai yana sona kuma da aure.”

Hannunta ya rik’o “Da gaske kikeyi? Indai gaskiyane to lallai na tayaki murna sis Mubeen,Farhan cikakken mutum ne wanda yasan yakamata gaskiya kinyi dace dan haka na amince dashi 100% kema kice kin amince kinji?”

Dad’i taji sosai “Da gaske kake Ya Atif?”

“Yes, i’m serious wlh ai samun miji irin Farhan abune mai wahala a rayuwarmu ta yau.”

Nan Atif ya fara tunanin wata rana daya cewa Farhan suje yawo mana danshi yana da wata budurwa duk randa buk’atarsa ya tashi to gurinta yake zuwa ta biya mishi buk’ata kaima idan kana so sena nema maka d’aya. Amma sam Farhan seya nuna mishi shifa ba irin wannan samarin yake ba,tun daga lokacinne alak’arsu tad’an ja baya sosai,yafi jin dad’in alak’arsa da Ahmad dan shima baya irin wannan harkar banzan wanda a zamanin yanzu da k’yar ne mace ta samu saurayi wanda kwata-kwata a rayuwarsa bai tab’a yin zinaba gaskiya yana wahala sosai,dan acikin kashi d’ari toda k’yar ne a samu kashi d’aya yana matuk’ar wuya sedai muci gaba da Addu’a Allah ya k’ara shiryar mana da Mazajenmu,Yayyunmu da kuma k’annemmu ameen.

Bayan Atif ya gama wannan tunaninne yayi ta yabawa Mubeenat Farhan sosai,dan haka taji dad’i tare dayi masa godiya.+

A islamiyya Farhan yana yiwa matan aure darasi acikin littafin *ZADUZ-ZAUZAINI* inda yake musu bayani akan ana auren mace dan abubuwa guda hud’u ne.

_Limaliha: dan dukiyarta_

_Walhasabiha: dan nasabarta_

_Wal jamaliha: dan kyanta_

_Wal diniha: dan addininta_

_Fasfar bizatitdeen: kurabauta da ma’abociyar addini._

Karatu yake musu dalla-dalla ta yadda zasu gane. Bayan ya gamane yake tambayarsu “Menene aure?”

Nan dai kowa ya fara bada amsa da cewa kafin ayi aure ana buk’atar abu hud’u

-Mata da miji

-Waliyai

-Sadaki

-Shaidu

Idan aka samu wa’innan to aure yayi Malam.

Shuru Farhan yayi kamar maiyin wani nazari sannan yace dasu “Eh to wannan ai kunmin bayanine akan d’aurin aure,amma me ake nufi da ita AURE?”

Nan kowa yake bada amsar shi da cewa Malam aure dai shine Sadaki don idan babu sadaki toba aure.

Murmushi Farhan yayi tare da cewa “Dukfa ajin nan zallan matan aure ne,amma ace babu wacce tasan ma’anar kalmar aure? Na yadda da amsoshinku,amma ba ita bace Kalmar aure ina zuwa.”

Nan ya fita ya shigo ajin su Mubeenat yace “A cikinku wacece zata gaya min me kalmar aure yake nufi?”

Kowa yanata bada irin amsar da ajin matan aure suka bayar. Farhan yace sam ba haka bane, dama Amal da Mubeenat basuyi magana ba,dan haka Amal ta mik’e tsaye tace “Malam na sani”

“Kin tabbata Amal?”

“Eh”

“To shikenan kibiyoni muje,idan kika dawo seki gayawa ‘yan ajin naku ma’anarsa”

“To Malam” sannan ya fice tana biye dashi a baya har suka shiga ajin matan auren.

Farhan ya kalli aji yace “To Amal,inaso ki gaya mana me ake nufi da aure?”

Kunya sosai taji,amma tasan babu kunya a wurin neman ilimi kuma na addini dan haka tayi magana ta yadda kowa zaiji.

“Aure yana nufin saduwar Mace dana Miji.”

Farhan ya tambayeta “Kin tabbata?”

“Eh Malam wannan itace kalmar aure a wana fahimtar.”

“Nagode Amal zaki iya komawa aji”

Bayan ta fitane ya kalli Aji “Wannan fa budurwa ce batama yi aurenba,amma ta fiku sanin menene aure,idan kuma kun sani kunyace ta hanaku fad’a inaga wannan ba hujja bace,dan babu kunya a wurin koyar addininka” nan dai yayita musu bayani har suka fahimta.

Bayan an tashine Farhan da Shureim suka wuce mota suna zaman jiran Mubeenat da Amal sakamakon wani Malami dake ajinsu.

Can ya hangosu suna fitowa dan haka yace da Shureim ya koma baya ya zauna.

Mubeenat ce ta zauna a gaba su Amal kuwa a baya.

“Ya Farhan kayi hak’uri Malamin Tauhid ne bai barmu mun fitoba wai se kowaccenmu tayi mishi bayani akan Sallah.”

“Kuma mun gaya mishi cewa Sallah Addu’a ce amma yace sam ba haka bane muje munemo mishi ma’anar sallah dan gobe kowacce seta bashi amsa daga waje kafin ta shigo aji.”

Murmushi yayi yana kallonta “Habibty bakisan me sallah ta k’unsa ba?”

Shuru tayi tare da sake kallonshi “Abinda Sallah ta k’unsa kuma?”

“Ahan,abinda sallah ta k’unsa shine ma’anar sallah ai”

Amal dake zaune a baya tace “Ya Farhan kayi mana bayani ta yadda zamu gane please?”

“Ok”

_Sallah wata ibada ce data k’unshi Karatu,Ruku’u da kuma Sujjada,ana farata da Kabbaran harama sannan a k’arasheta da Sallama”_

“Idan kuka gaya mishi haka zai barku ku shiga aji,wannan ita ce Sallah a nawa fahimtar.”

Murmushi sukayi tare da cewa “Mungode” sannan suka wuce gida.

  Bayan isha ya kira wayar Mubeenat bugu d’aya ta d’auka “Hello”

“Habibty nasha gaya miki sallama ya kamata kiyi ba hello ba.”

Murmushi tayi “Sorry Ya Farhan slm”

“Wa’alaiku mus salam,ya kike to?”

“Lafiya lau,kaifa?”

“Ni?”

“Eh ina nufin kaima ya kake?”

“Hhh lfy ta k’alau amma sed’an wata damuwa da take damuna.”

Cikin d’aukin son jin damuwar shi tayi magana “Me kuma yake damunka Ya Farhan?”

“K’aunarki ne Habibty,zuciyata ta kasa samun sukuni dan rashin jin amsarki da bata yiba.”

Murmushi tayi “Ka sanar da zuciyarka data samu salama domin zuciyar Mubeenat takace kai d’aya tak”

Farhan baisan me zaice da itaba dan wani ni’ima ce yaji yana shigarsa ahankali.

“Alhamdulillah,Allah na gode maka daka sa Mubeenat ta amince dashi,Allah ka tabbatar mana da alkhairi Nida Ita”

“Ameen” suka amsa tare sannan yace “Habibty nagode sosai da amincewa dani da kikayi.”

Cikin jin kunya tayi magana a hankali “Nima na gode daka zab’eni a matsayin wanda kake so ta zama abokiyar rayuwarka,domin aganina nama fika sa’a a rayuwa.”

“Ana Hubbuki Habibty”

“Me kenan Ya Farhan?”

“I mean I love you”

Kunya taji dan batasan me zata ceba.

“Ke kuma seki ce min Ana Hubbuka Habibi”

Dariya sosai Mubeenat tayi “Hhhh ashe dai zan koyi larabci?”

“Sosaima daga yau indai ni dake ne toki kirani da Habibi zan iya jin wannan sunan a bakinki?”

“Habibi?” Ta tambaye shi cikin wata irin murya.

Murmushi yayi tare da cewa “Yeah gashi kinfi kowa iya kiran sunan kuwa.”

Hmmm! Wannan daren dai shine dare mai dad’i acikin rayuwarsu domin sunfi awa biyu suna hirarsu tare da farantawa junansu rai dukda dai ita Mubeenat tana jin kunyarsa idan ya mata wani maganar.

Haka sukaita zuba soyayyarsu tsawon wata uku ne kacal amma kowa yasan da batun soyayyarsu,dan a company da store duk Farhan ya sanar da mutane har gidan TV anyi hira dashi akan Company nasu daga k’arshen hiranne yake sanar da al’umma cewa ya samu matar aure dan haka a tayashi da addu’a. Suma ‘yan jaridan sunzo suji wacece haka,amma seya ce musu nan gaba kad’an zai gabatar musu da ita.

Iyayen suma Farin ciki sukayi sosai dangi gaba d’aya kowa yana murna da san barka amma banda Hajiya Kaka wanda ita burinta a duniya bai wuce taga Atif da Mubeenat sunyi aure ba. Hakan yasa sam bata farin cikin soyayyar Farhan da Mubeenat.

Tsawon wata bakwai kenan da fara soyayyar Farhan da Mubeenat wanda a yanzu kamar son da Mubeenat takeyiwa Farhan yayi yawa amma fa a nawa ganin. A ganin Farhan d’in kuwa soyayyarsa tafi na Mubeenat.

Wata rana Hajiya Kaka ta kirawo Atif tana gaya mishi burinta a duniya bai wuce taga ya auri Mubeenat ba “Taya ka bari Farhan ya wuce maka gaba bayan itama Mubeenat d’in tana sonka?”

Murmushi Atif yayi “Hajiya Kaka babu soyayya kamar yadda kuke tunani a tsakanina da Sis Mubee,shak’uwa ce kawai wlh niba sonta nake ba.”

“To idan ma ba sonta kakeba kaki gaggawan dasa soyayyarta a cikin zuciyarka Atif,ai idan kaine zaka aureta abin zaifi burgewa tunda kai yayantane kuma bazata k’ika ba dan ni wlh nasan tana k’aunarka.”

Atif yayi shuru yana nazarin maganar Hajiya Kaka da kuma wanda abokansa ‘yan k’wallo suka mishi akan ya akayi ya bari Farhan ya baiyanawa Mubeenat soyayyarsa?

“Atif kai kafi dacewa da auren mubeenat ba wani bare ba wlh,da nasan ba sonta kakeyiba wlh da tuntuni na shiga danna dad’e ina k’aunar Mubeenat amma yadda naga kun shak’u se nayi tunanin ko soyayyace a tsakaninku Atif kayi missing wlh…”

“Wai tunanin me kakeyine Atif?” Cewar Hajiya kaka.

Ajiyar zuciya yayi yace kaka bake kad’ai kika min wannan maganarba abokaina da dama sunmin wannan maganar amma lokaci ya k’ure Hajiya kaka kuma ina ganin Farhan shi yafi dacewa da auren Sis Mubee nasan zai kula min da Sweet sis fiye da yadda zan kula da itama dan gaskiya Hajiya Kaka Farhan ya fini da komai dan haka ina taya Sis Mubee murnan samun Farhan.”

Lokaci bai k’ureba inhar kana sonta kabar komai a hannuna kaji?”

“Me zaki iyayi akai Hajiya kaka,Abba ya riga daya basu kuma kinsan yadda yake da Abbin Farhan babu yadda za’ayi yace ya fasa sannan ita Sis Mubee tana matuk’ar k’aunar Farhan ta yadda bata jin kiran kowa a yanzu.”

“Tashi kaje Atif,kaidai kad’an ja baya da ita yanzu nasan ta yadda zan b’ullo mata.”

Shuru kawai Atif yayi tare da barin Hajiya kaka ya wuce gida inda yaga Farhan da Mubeenat suna hira a parlour’n Umma.

Cikin murna tace “Ya Atif sannu da dawowa”

“Yawwa” kawai ya furta tare da barin gurin.

Daga Mubeenat har Farhan sunga canji a gareshi dan haka jikinta yayi sanyi tace “Yau lfy naga Ya Atif haka?”

“Kodai akwai abunda yake damunsa ne ko kuma k’ila wanine ya b’ata mishi rai daga waje?” Cewar Farhan.

“Habibi idan bazaka damuba ina so inje muyi magana dashi”

“Bakomai Habibty dama nace miki fita zanyi,kije nima na fita sena dawo.”

“To Allah ya kare min kai” ta fad’a tana murmushi.

“Ameen” sannan ya fice tana biye dashi a baya har seda ya fice a gidan sannan ta wuce gun Atif ta shiga da sallama…”

Slm”
“Wslm please Sis Mubee ina buk’atan kasancewa ni kad’ai.”
Zama tayi akan kujerar dake d’akinsa tana kallon fuskarsa “Kasan dai bazan bar d’akinnan ba tunda na ganka haka.”
“Sis Mubee pls…
“Haba Ya Atif nice fa,me yake damunka ko kuma waya b’ata maka rai ka gayamin zanje in rama maka nefa?”
Bai san lokacin da dariya ya kubce mishi ba.
“Hhhh wlh kinban dariya amma kije da gaske nake Sis Mubee i’m not in the mode pls?”
“Shikenan tunda kace haka,amma dai ina fata bani bace dan naga kamar laifin ya shafeni nima?”
“Kije mana pls leave me along Sis Mubee”
Cikin rashin jin dad’i ta fito ta koma d’akinta tana daga kwance tana tunani akan abinda Atif yayi mata.+
Tun daga wannan ranan Atif baya sakewa duk ‘yan gida garama Abba da Umma wanda su kansu sun lura kan cewa akwai wani abu da yake damun sa.
Koda Abba ya tambayeshi sai yace babu komai haka aka k’yale shi.
Tabbas Atif sai a yanzu yake tunanin maganganun mutane da aketa mishi akan Mubeenat wanda a yanzu gaba d’aya zuciyarsa ta karkata a gareta amma shi kanshi yasan bazaima yuwuba dan sunyi nisa ita da Farhan ta yadda babu mai iya rabasu cikin sauk’i.
Hakan yasa ya fara neman hanya amma duk ta inda yayi yunk’urin farawa se kuma ya bari.
Ganin hakanne yasa abokai suka dinga bashi mugayen shawara wanda shi baizai iya aminta dashi ba,dan yana ganin idan aka raba Mubeenat da Farhan to lallai zata shiga cikin wani hali wanda bazai so ya ganta a cikin damuwa ba.
Kusan sati biyu kenan Mubeenat ta kasa gane kanshi dan haka ranan taje yini a gidansu inda take gayawa Aisha abinda yake faruwa nan Aisha tayi ajiyar zuciya ta fara magana kamar haka.
“Agaskiya Mubee inaga mubar wannan maganar kawai,kema kuma kid’an ja baya dashi kamar yadda ya miki.”
Cikin rashin fahimta ta kalli Aisha sosai tace “Me yasa kika ce min haka Aisha? Shin akwai wani abune da kema zaki b’oye min a yadda muke dake?”
“Ba haka bane Mubee wlh rashin sanar dake shiyafi komai dacewa dan bansan ya zakiji ba wlh”
“Dan Allah ki sanar dani Aisha babu wata b’oye-b’oye fa a tsakanina dake please?”
Muryar Hajiya Kaka sukaji tana cewa “Ba komai bane yake damun Atif sai k’aunarki da yakeyi a cikin zuciyar shi tunda jimawa wanda kafin ya bayyana miki har Farhan ya riga shi.”
Cikin rud’ewa Mubeenat ta kalli Aisha wanda ta sunkuyar da kanta sannan ta sake duban Hajiya Kaka tace “K’aunata fa kika ce Hajiya Kaka? Meyasa bai sanar daniba to? Ke Aisha kinsan da haka me yasa lokacin dana nemi shawarar ki akan amincewa da Ya Farhan kika bani goyon bayanki akai batare dakin gayamin k’udirin Ya Atif a gareni ba? Haba Aisha agaskiya banji dad’in abinda kika min ba wlh,yanzu ya kike so inyi kenan? Dama wannan shine dalilin dayasa Ya Atif ya sauya min gaba d’aya kenan? Allah sarki Ya Atif me yasa kayi zurfin cikin sanar dani akan lokaci,yanzu yaya zanyi kenan ni Mubeenat? Dan Allah ku bani sharawa Hajiya Kaka?” Ta k’arashe maganar tana k’awlla.
Hajiya Kaka ta matso kusa da ita “Mubeenat shawara a gareki take,ke kika san yadda zakiyi ai”
“Wlh bansan meya kamata inyiba Hajiya Kaka,saboda zuciyata tayi nisa da soyayyar Ya Farhan wlh bansan ya zanyiba”
“Dan Allah Mubee ki dena kuka” cewar Aisha.
“Dole ne inyi kuka Aisha,gaba d’aya yanzu k’wak’walwata ta toshe ta dena aiki akan kowa Ya Farhan kad’ai take ganewa,to taya bazan yi kukaba bayan Ya Atif yana cikin irin wannan yanayin a yanzu?”
“Mubee Ya Atif fa ya riga daya hak’ura tunda Ya Farhan ya riga shi,kawai dai inaga har yanzu abun bai gama fita a ranshi bane.”
“Taya zai fita a ranshi bayan gida d’aya suke dukkansu kuma yana ganinsu a tare ai dole zai dinga jin wani abu” cewar Hajiya kaka.
“Innalillahi wa inna’ilaihir raji’un yanzu miye abinyi Hajiya Kaka?”
“Babu wani abinyi ai yanzu sai dai kawai yabar gidan ya dawo nan da zama,dan hausawa sunce k’azantar da baka ganiba tsafta ce.”
“Haba Hajiya Kaka,wlh Ya Atif ba zai bar gidammu ba”
“Ai kuwa dole yabar gidan dan bazan yadda ciwo ya kashemin jika ba.”
“Dan Allah Hajiya Kaka kibar wannan maganan… “Idan ma nabar maganar ai aure zakiyi ki tafi ke ki barshi ina? Dan haka gara yabar gidan tunda wuri” tana kaiwa nan ta fice daga d’akin rai b’ace.
“Subhanalillah Aisha please ki bani shawara pls?”
Shuru Aisha tayi dan bata san me zata ceba,hasalima ita bata san da zancenba seda Kaka take gaya mata dan sam hiran bai had’asu da Atif ba,kuma koda ta tambayeshi randa yazo gidan ce mata yayi acikin ‘yan watanni uku ne yaji  sonta yana shigarsa,kafin ya ankara kuma yaji har Farhan ya riga shi.
“Aisha kinyi shuru kina jina kice dani wani abu mana?”
“Mubeenat please karma maganar ta dameki dan shi fa yama janye a ranshi,ki auri Ya Farhan ai duk d’ayane kuma gaskiya Ya Farhan mutum ne na gari sosai kowa fa murna yake miki wlh harta Daddy ma.”
“Nagode Aisha ni gaskiya bazan iya wannan wunin dana zoba,dan haka zan koma gida kawai.”
“To yanzu wa zai mai dake?”
“Zan hau nape karki damu dama Ya Farhanne ya kawoni akan idan yazo d’aukana seya gaisa dasu Mum dan sauri yakeyi sosai yanzun kinsan jibi ne Iyayensa zasu zo.”
“Mubee ki kirashi kawai yazo ya d’aukeki”
Badan ta soba ta kirashi ringing d’aya ya d’auka “Slm Habibty?”
“Wslm nace idan babu abinda kakeyi dama ina so in komane yanzu”
“Ok kin fasa wunin kenan?”
“Hmmm nidai idan kana wani abunne kawai in hau nape karna tsai da kai?”
“Hhhh Habibty ina kan hanya zuwa nan bada jimawa ba”
“Ok seka k’araso to” sannan ta katse wayar.
Daga ita har Aisha babu wanda ya sake cewa komai har Farhan ya iso,ita Aishan ce ta mishi jagora ya gaida su Mum da Hajiyan su Ya Musty da kuma Hajiya Kaka sannan Mubeenat ta musu sallama cikin sanyin jiki ta shige mota suka tafi.
Shi kanshi Farhan yaga canji a tattare da ita dan haka yayi magana cikin nutsuwa “Habibty yana ganki haka,akwai wani abu ne?”
“Ba komai”
“Ban yarda ba,please tell me kodai nayi laifi ne banzo akan kari ba?”
Murmushi tayi “Ai baka laifi Habibi,kawai dai bana jin dad’in jikina ne shiyasama na fasa wunin”
“Oh no Habibty bari muje muga doc”
Cikin sauri tace “Please Habibi muje gida kawai nasan gajiyane da zaran na d’anyi bacci shikenan wlh”
“Are you sure?”
“Enhen kasan bazan maka k’arya ba ai,i’m okay Habibi” tana kallon shi cike da so.
Shima ita yake kallo yana mata murmushi “Kinsan me Habibty?”
“Seka fad’a”
“Burina a duniya yanzu shine inga an d’aura mana aure,daga wannan rananne zan samu sukuni acikin heart d’ina”
“Ke kuma fa?”
“Ya Farhan bank’i ace yaune d’aurin aurena da kai ba,dan haka yanzuma please ka sanar da Abbi cewa kana son auren nan kusa,dan gani nake kamar mutuwa zanyi wannan buri namu bazata cikaba ni da kai.”
Kallonta yayi sosai danya tuna da mafarkin daya yi na cewa anyi auren Mubeenat da wani wanda bashi bane.
“Habibty please ki dena fad’i hakan bana so,yanzu haka kin tayar min da hankali sosai wlh,bana fatan rasaki a rayuwata Habibty Allah ma ya kare.”
Ganin yadda hankalinsa ya tashine yasata cewa “Ameen Habibina,kayi hak’uri naga bakaji dad’in kalaman nawa ba.”
Murmushi yayi mata tare da cewa “It’s okay Habibty, INNOBY”
“Me kenan?”
“I Need No One But You”
“Hhhh OLKUT Habibi”
Kallonta yayi da alaman tambaya akan fuskar shi,dan haka tayi murmushi tare da cewa “One Love Keep Us Together Habibi”
  Dad’i sosai yaji yace “Ki bari haka kar kisa in b’ata hanyar komawa gida.
Haka sukaita sanyayawa junansu rai da kalamai masu dad’i har suka iso gida,yana sauketa ya juya ya koma.
Atif ne a parlour’n Abba yana kallon ball shida Shureim.
“Ya Atif ina so inyi magana da kai ne”
“Ok Sis Mubee ki bari se anjuma kinsan bana so wannan wasan ya wuce ni”
“Shureim kad’an bamu guri kaji?” Cewar Mubeenat.
Bayan fitar Shureim ne taje ta kashe TV tare da tsayawa a gaban shi tana k’walla.
Kallonta Atif ya tsayayi tare da mik’ewa yaje inda take tsaye “Sis Mubee me haka kuma?”
Cikin muryar kuka tayi magana “Kayi hak’uri da kashe TV danayi kana kallo,Ya Atif ina so ka gaya min gaskiya akan abinda Hajiya Kaka ta fad’a min”
“Wai da gaskene kana sona?”
Tambayar a bazata yaji tazo mishi,dan haka yayi murmushi tare da cewa “Haba Sis Mubee ke dama baki san ina sonki ba harse na gaya miki?”
“Ya Atif ba wannan son nake nufi ba,ina nufin wai kana sona da AURE?”
“Hhh haba Sis Mubee wani irin aure kuma? Kin manta da abinda na gaya muku ne ke da Aisha,bana ra’ayin aure a k’asarnan kema shaida ce taya za’ayi ki yadda da maganar Hajiya Kaka?”
“Ya Atif kabar wasa wlh da gaske nake maka,Hajiya Kaka ta gaya min komai yanzu dana je gida.”
Murmushi Atif yayi tare da kamo hannayenta biyu “Sis Mubee burin Hajiya Kaka shine taga munyi aure ni da ke,a tunaninta soyayyace a tsakanina da ke kuma kema shaida ce kusan kowa wannan tunanin yakeyi akammu,lokacin da maganar nemanki da Farhan ya baza ko ina shine take tambayata na sanar da ita cewa babu soyayya tsakanina dake shak’uwa ce kawai.”
“Sis Mubee Hajiya Kaka tak’i amincewa da maganata dan har cewa tayi to lallai in dasa soyayyarki acikin zuciyata dan ita burinta kenan a duniya taga munyi aure.”
Atif ya saki hannun Mubeenat tare da juya mata baya yaci gaba da bayani.
“Sis Mubee duk lokacin danaje gida sai Hajiya Kaka ta tareni da zancen ki,saina sanar da ita cewa to yanzu ai kin zab’i mijin aurenki kuma mutum ne nagari gashi ansan juna,amma sai Hajiya Kaka ta nuna babu ruwanta ita dai tana nan akan bakanta,tun abun baya damuna har yazo yana damuna Sis Mubee shiyasa kikaga kwanaki na canja miki bakya ganemin duk dan Hajiya kaka ta samu labari nayi,ashe ita kuma yadda ta fassara abun daban ne.”
“Sis Mubee koda bakya tare da Farhan maganar gaskiya shine bawai so nake miki na kizama matata ba,sone na k’anwa da Yaya da fatan kin fahimta Hajiya Kaka so take ta b’ata komai.”
Shuru Mubeenat tayi tana nazarin kalamansa “Ka tabbata Ya Atif?”
“Come on Habibty,kinsan fa Habibi ya kusa dawowa gara ki goge hawayenki kar kisa yazo yayi pornishing d’ina.”
Dariya Mubeenat tayi yayinda ya sake matsowa inda take yace “Share hawayenki Sweet Sis,bana so ki sake sa maganar Hajiya Kaka acikin ranki,verry soon ma zan kawo muku matar da zan aura ta fiki had’uwa sosai fa” ya k’arasa maganar cikin zolaya.
Nan take Mubeenat ta sake se dariya takeyi ita dai taji dad’i tunda sun shirya da Yaya Atif nata.
Shi kuwa se sata dariya yake yana zolayarta amma acikin zuciyarsa shiya san me yake ji akan soyayyarta daya dabaibaye shi…Yau ne su Abbi suka iso k’asar Nigeria bayan an tarosu kai tsaye suka wuce gidansu acan aka yada zango da dukkan ‘yan gidan su Mubeenat dama an musu girki dan haka aka tafi musu dashi amma banda ita Mubeenat tana gidan su Amal suna kallo a d’akin Amal d’in inda Sagir yaketa iya shegensa daga parlour amma ko kulashi basu yiba kamar yadda Abba ya gargad’e su.
  Ummin Farhan ta damu tana son ganin Habibty,inda Ummanta tace “Ai tana can gidansu Amal wai ita kunyar ki takeji amma gobe zan turo miki ita.”
“Hhh Mubeenat dama can akwai kunya ai bare kuma yanzu” cewar Abbin Farhan.
Haka suka yini musu sai bayan la’asar sannan suka koma gida.
Cikin sauri Mubeenat ta dawo gida tana cewa “Umma ya kuka sami su Ummin da Abbi?”
“Lafiyansu k’alau sai tambayar ki sukeyi,dan haka saiki shirya gobe da safe kije ki gaishe su”
“To amma wlh Umma kunya nake ji fa”
“Kunji min iyayi kuma,to kuma shikenan dan kina kunya baza kije ki musu sannu da zuwa ba? Idan baki jeba aisu sa biyoki dan tana son ganinki sosai.”
Dad’i sosai Mubeenat taji har cikin ranta,dan haka tasa a ranta zataje goben.+
  Kanta a sunkuye tana zaune a k’asa “Ina kwana Ummi kun iso lafiya”
“Habibty wannan duk kunya ce haka? Nidai bana son irin wannan jin kunya haka ki d’aukeni kamar Ummanki nima, tashi ki zauna a sama”
“A’a Ummi nan d’inma yayi”
“To bari in d’agata tunda tak’i Ummi” cewar Farhan.
Cikin sauri ta mik’e ta zauna kusa da Ummin suna mata dariya yayin da Ummi ta shafi kanta tace “Habibty tun jiya nake son ganinki dan naga Habibina yayi k’iba nasan kuma kece sila me kike dafa mishine haka?”
Murmushi Mubeenat tayi tare da kwantar da kanta a jikin Ummi tana murmushi.
Shima Farhan d’in kwantar da kanshi yayi ta d’ayan gefen jikin Ummin nashi ta yadda suke fuskantar juna shida Mubeenat.
Murmushi kawai suke yiwa junansu sai Ummi ta katse su da cewa “Habibi ka tashi a jikina karka sa in fara kishi fa”
“Kishi kuma Ummi,me yasa zakiyi kishi?”
“Saboda gaba d’aya naga kamar yanzu kafi son Habibty akai na”
Dariya sosai sukayi dukkansu sannan Farhan ya d’ago da kai yana kallon ta “Ummi taya zaki had’a soyayyarki dana  Habibty? Ai koda wasa bata ma zo kusa dake ba Ummina,domin k’aunar da nake miki daban ne bana tab’a had’aki da kowa” ya k’arashe maganar yana tsunbatar hannunta.
Dad’i taji sosai tace “Ka sake fad’a dai saboda Habibty taji da kyau”
Mubeenat dai sai dariya takeyi, Farhan ya sake cewa “Ummi idan har ina tare da ke to sam bana tuna Habibty kwata-kwata,amma idan ina tare da ita dolene saina tuna dake wannan shine son da nake miki Umminah.”
Tsunbatar sa tayi a goshi tace “Shiyasa a koda yaushe nake godewa Allah daya bani D’a d’an albarka irinka Habibi,ana hubbuka Habibi.”
Dad’i yaji shima ya kalli Mubeenat yace “Ana hubbuki Habibty”
Cikin sauri Umminsa tace “Waye?”
Yayi saurin cewa “I mean ana hubbuki Ummi”
Dariya suka sake sawa dukkansu sannan sukaci gaba da hiransu cikin so da k’auna suna kwance a jikin Ummi tana musu nasiha.
Satin su guda kenan a Nigeria sai Abbin Farhan ya d’ibesu sukaje gurin danginsa suka kwana biyu sannan suka dawo gaba d’aya da Family nashi dan ayi tambayar auren Mubeenat.
An cika sosai inda ake zaune da Dad d’in su Atif da kuma Abban Amal da dai ‘yan’uwa akayi tambaya akan Mubeenat, nan akace dasu an basu tare da tsaida rana nan da wata Uku za’ayi bikin.
Murna agurin wad’annan masoya baya misaltuwa tunba shi Farhan d’inba da yake ganin kamar lokacin bazai zoba.
Kayan tambayan kawai abin kallo ne wanda suka taho dashi daga Madina wane kayan aure,a hakan kuma wai idan auren ya matso zasu zo da kayan aure.
Kowa sai san barka yakeyi akan bikin nasu tare da fatan Allah ya nuna mana.
Watan su d’aya suka koma inda suka cewa Farhan zaije Madina nan da sati biyu domin k’arasa shirinsa na can sannan ya dawo.
Shi kuwa Atif baisan yana son Mubeenat ba sai a yanzu dayaga dai da gaske bikin yazo.
Hankalinsa a tashe sosai yaje gurin Hajiya Kaka yana magiya “Dan Allah Hajiya Kaka kiyi wani abu akai wlh bazan iya rasa Sis Mubee ba”
“Atif nayi iya k’ok’arina amma dukka b’ata min shiri dan haka zan gwada ta wata hanyar in hakan zaiyu to”
“To Hajiya Kaka nagode”
Hajiya kaka ta nasar da Dad d’in Atif abinda ke faruwa,amma sai yace mata ai lokaci ya k’ure Hajiya ni kaina naso ace munyi wannan zumunci amma Allah bai yiba dan haka yayi hak’uri.
Babu yadda Atif ya iya haka ya d’au hak’uri badan yaso ba.
Idan ka ganshi kasan yana cikin wani hali dan haka abokansa sukace bazasu bari abokinsu ya shiga wani hali ba,karma daga baya ya kasa yin wasan k’wallon gashi kusan shine ma mai k’ok’arin cikinsu dan haka suka shiryawa Farhan gadan zare ba tare da sanin shi Atif d’in ba.
Mubeenat tayi shiga mai kyau inda Farhan yana jiran fitowarta zasuje ya gaida Mahaifiyar Aisha Kabir k’awarta mai rasuwa ta sanadiyar amfani da wasu magungunan mata wanda bamu san dame ake had’a suba.
Kallonta ya tsaya yi dan yadda yaga tayi kyau sosai. “Ya Farhan zan bika nima” cewar Shureim.
“To shiga baya muje” cikin murna ya shige sannan Mubeenat ta zauna a gaba Umma tana musu Allah ya kiyaye hanya.
Tunda motar Farhan yabar gida Abokan Atif suka samu labari ta hanyar wani da sukasa yana bibiyarsa.
“Habibty irin wannan wanka haka har kinsa na fara kishi fa,kar wani ya kalle min ke?”
“Ka kwantar da hankalinka ango to be,domin Mubeenat taka ce kai d’aya tak”
Juyowa yayi ya kalli Shureim dake kwance a baya kamar wanda ya samu gado. Murmushi yayi tare da cewa “Dan dai yau muna da yawane amma dana ce wani abu”
Murmushi tayi tare da cewa “Habibi bana ganin yawan mutane indai ina tare da kai,sannan bana shakkar fad’in abinda zuciyata ta gaya min domin wanda na ajiyeta a cikinsa Mutumin kirki ne kuma abin alfaharina”
Dad’i mara misaltuwa ne ya kama Farhan wanda har yana ganin gara yayi shuru dan idan sukaci gaba to lallai Habibty zata cinye shi da kalaman soyayyarta masu sanyaya mishi zuciya.
“Ya naji kayi shurune my Star? Kodai ka bar min gurine domin inyita baje maka kolina? Indai kuwa hakane to lallai ka sake kakkab’e kunnuwanka sannan ka bud’e min zuciyarka domin in shige ciki nasan duk abinda zai faru a ciki to lallai zaka jishi a kunnuwanka yayin da zansa zuciyarka yin bacci da sassanyar kalamaina wanda dankai kad’ai nayisu.”
Hmmm ba Farhan kad’ai ba,harni sadnas gyara zama nayi ina sauraron wad’annan kalaman na Mubeenat harma nayi jorting cikin shafi akai.
Har suka iso inda zasu Farhan maiba san an iso ba saida ta taimaka mishi gurin dakatawa da baitikanta tace “Haba Habibinah munfa wuce gidan”
“Nasan baza kiga laifina ba sabida kece kika mantar dani a cikin zuciyarki ko kuwa ince kika makantar dani.”
“Hhh tona gode,zuwa bayan azahar seka dawo mu koma”
“Yes Mah” ya fad’a yana tsosar lips nashi.
Idonta takai baya taga Shureim kam har yayi bacci abinshi dama baccin yakeji tun a gida amma dayake yana son yawo sai daya biyo su.
Murmushi sukayi a tare sannan Farhan ya fito sukaje suka gaisa sannan ta sake rakoshi gun mota inda ya d’ago shureim ya dawo dashi gaba duk yana bacci.
  Kallonta yake cike da so da k’auna “Habibty sena dawo”
“To Allah ya kare min kai”
“Ameen nagode” sannan ya tafi yana hangota daga mirro inda take tsaye tana binsa da byeee.
Farhan yana cikin tafiya amma se kewar Mubeenat yakeyi kamar wanda suka dad’e basu had’u ba.
Nan ya tuna da kalamanta inda take ce mishi _”Habibi aduk lokacin dakaji kana kewata sosai toka bud’e wannan choculate d’in kasha,acikin d’and’anonsa zakaji tana had’e da soyayyata zuwa gareka”_
Murmushi Farhan yayi tare da ambaton sunanta kamar tana jinsa “Habibty” sannan ya b’are wannan choculate d’in yana gutsuransa a hankali kamar bazai sha ba.
  Wata babbar mota ce ta nufo kansu,hon Farhan yake musu dan yaga sunata nufowa kansa,amma duk da haka baisa sun kauce ba gashi dama titin ba wani motoci sosai su biyunne kawai akan hanyan.
Cikin rud’ewa Farhan ya fara fad’in _”Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”_ wanda hakan yasa Shureim farkawa daga bacci, take yasa ihu mai k’arfin gaske a lokacin da yaga Farhan ya kaucewa k’atuwar motar sun nufi gun wani k’aton dutse mai girma sosai har a lokacin Farhan salati yakeyi yayin da shi kuwa Shureim ya tsume dan tsorata dayayi.
Cikin rud’ewa Farhan ya kira sunan Shureim ganin ya suma,kan ya sake kaucewa dutsen tuni suka bugi wannan dutsen da karfi wanda seda motar tayita juyi kusan sau biyu kafin ta fad’o a k’asa ji kake chaaas.
Cikin sauri mutanen da  Abokan Atif suka basu wannan aikin suka k’araso gurin nan sukaga jini yana zuba daga gefen kan Farhan jikinsa babu kyan gani Shureim kuwa ya fad’a can gefe.
Da wuri suka fito da Farhan tare da d’auko Shureim suka ajiyesu a gefe,shi kuwa mai tuk’a babbar motar seya wuce kamar ma baisan anyi hatsariba.
Nan suka kama ihu suna cewa “Jama’a ku taimaka mana dan Allah” kan ace kwabo mutane sun taru agun bila adadin kowa cewa yake “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” mutane dewa daga cikinsu sun gane Farhan dayake akwai wanda suke aiki a Company nashi dan haka aka d’aukesu cikin gaggawa se Hospital yayinda wani daga cikinsu yace yana da No Abban Mubeenat nan aka kira wayarsa yanata ringing…😥
Abban Mubeenat yana zaune a office yaga bak’uwar number kamar bazai d’auka ba se kuma ya d’aga.
“Slm”
“Wslm sannu Alhaji,d’aya daga cikin ma’aikatan TAIMOOR COMPANY ne a hanyar wucewata ne naga motar Sir Farhan tayi hatsari shi da wani k’aramin yaro yanzu haka suna asibiti”
Cikin kid’imewa Abba yake furta “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un wace asibitin kenan? To ganinan zuwa amma dai suna lafiya ko?”
“Eh to muma bamu saniba gaskiya domin doctors suna kansu,amma muna fatan suna halin lafiya dukda dai shi Farhan d’in yaji raunuka sosai ajikin shi.”
Salati Abba yaketayi tare da wucewa asibitin kai tsaye bayan ya sanar da wansa wato Dad d’in Atif.
Bayan sun iso asibitin ne yake tambayar doctors “Ya masu jiki?”
“Kayi hak’uri Alhaji kad’an jiramu please muna kan aiki ne” yana kaiwa nan ya wuce ciki yabar Abba tsaye yanata addu’a a kid’ime.
Numbar Umma ya kira “Yaushe Farhan ya fita ne? Kuma shi da wa suka fita?”
“Lafiya Abban Mubeenat? Shida Mubeenat ne da kuma Shureim sunje gaida Maman Aisha”
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”
“Abban Mubeenat lafiya kuwa?”
“Hatsari sukayi a hanya,amma kuma ni Farhan da Shureim ne aka cemin an kawo asibitin ai,ina ita Mamana d’in take to?”
Bai jira me Umma zata ceba ya katse wayar tare da kiran Mubeenat,tana ganin Abbanta ne ta d’aga da sauri “Assalam Abba”
“Mamana kina ina ne?”
“Abba ina gun Maman Aisha ban dad’e da zuwa ba”
“Ke da wa?”
“Ya Farhan da Shureim ne suka kawoni,amma sun koma inaga ma basu k’arasa gida ba dan basu dad’e da tafiya ba”
“Shikenan to” sannan ya katse wayar.
Mubeenat tayi mamakin meyasa Abba ya kirata,dan haka ta kira wayan Farhan yanata ringing ba’a d’agawa,can sai taji an d’auka “Hello baiwar Allah kina magana da Mahmud ne”
“Mahmud kuma? Dan Allah mai wayar fa?”
“Kiyi hak’uri bazaki iya magana da mai wayarba a yanzu” yana fad’a mata saiya swiching off na wayan gaba d’aya ya mik’awa wani police d’in da dai sauran abubuwan da suka samu a motar.+
Hankali tashe Mubeenat ta sake kiran wayan amma sai taji a kashe. Mamakine ya bayyana k’ak’ara a fuskarta dan haka ta kira Atif “Hello Ya Atif kana gida ne?”
Cikin wata irin murya yace “Muna hanyar zuwa asibiti”
“Asibiti kuma? Kai da wa?”
“Nida Dad”
“Dad kuma lafiya?”
Nanne Atif ya fahimci cewa batama san me yake faruwa ba,dan haka yace ke kina ina ne?”
“Ina gidan su Aisha Kabir yanzu Ya Farhan da Shureim suka saukeni kuma na kira wayanshi yanzu naji wanine ya d’aga sannan ya kuma kashe wayar”
Cikin jin tausayinta yace “Bari nakai Dad hospital zanzo na d’aukeki”
“Karka damu nasan Ya Farhan yana sane da cewa bayan azahar zaizo ya d’aukeni”
“Sis Mubee Ya Farhan bazai zo ya d’aukekiba domin akwai abinda yakeyi ya gayamin zanzo in d’aukoki”
Cikin rashin fahimta tace “To” sannan ya katse wayar dai-dai lokacin suka iso asibitin.
Abbane ya k’arasa gunsu inda Dad d’in Atif yake tambaya “Yasu Farhan d’in suke?”
“Har yanzu dai babu wani abu da suka ce tukunna sai sun fito.”
Haka suka tsaya shorko-shorko suna ta salati can sega doctors sunata fitowa daga d’akin.
Cikin sauri suka k’araso “Doctor ya masu jikin?”
“Jiki da sauk’i,shi k’aramin yaron ya karye a hannunsa na dama da kuma k’afar hagu amma insha Allah zai samu lafiya danmun mishi d’auri baima saniba sakamakon suman dayayi.”
Shi kuma Farhan Taimoor gaskiya yaji raunuka sosai dan gefen kanshima tad’an bugu yanzu dai saiya farka kafin musan menene yake damunshi amma dai ku tayamu da addu’a.”
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” shine dukkansu suke iya furtawa cike da tausayawa akan fuskarsu.
Atif yace “Abba bari naje na d’auko Sis Mubee dan bata ma san meya faruba dan tace tana jiran Farhan zaije ya d’auko ta”
“To Atif Allah ya kare”
“Ameen” sannan ya fita jiki a sanyaye tare da tunanin mema zai fara gayawa Mubeenat.
Mubeenat kuwa harma tayiwa Maman Aisha kitso ta gama tayi sallah tare da d’an cin abinci sannan taji wayarta na ringing “Hello Ya Atif”
“Sis Mubee gani a waje ki fito mu tafi”
“To ina zuwa” sannan tayiwa Maman Aisha sallama ta rakota har waje nan suka gaisa da Atif sannan ta shige mota suka tafi.
Tunda ta shiga taga Atif yayi shuru kamar bashiba,duk da dai dama ya sauya sosai tunda akayi maganar aurenta da Farhan,amma dai yau d’in ko hirama taga baiyi mata ba dan haka tayi magana.
“Waini Ya Atif bak’i Ya Farhan d’in yayi ne? Imma bak’ine to meyasa shi Mahmud d’in ya d’auki wayarsa kuma harda kashewa?”
K’wallan da Atif yake b’oyewa ne ya d’igo kan cinyarsa inda Mubeenat take bin k’wallan da kallo cikin mamaki.
“Ya Atif lafiya kake k’walla?”
“Lafiya Sis Mubee”
“Kamar ya lafiya bayan ga k’walla har yana d’iga daga idanunka?”
“Sis Mubee… nan wayarsa ta fara ringing ganin Ya Musty ne yasa ya d’auka tare da cewa “Hello Ya Musty”
“Atif wai su Farhan sunyi hatsari? A wani asibiti suke?”
Dan baya so Mubeenat ta fahimci hiran nasu dan haka yace mishi “Namu”
“Ok nima ganinan zuwa to”
“To seka zo” sannan ya katse wayar tare da k’ara gudun motarsa bai sake kallon inda takeba haka kuma koda ta sake tambayarsa ce mata yayi dan Allah ta barshi,badan tasoba taja bakinta tayi shuru har suka iso gida.
Cikin sauri Umma ta fito tana magana “Atif meyasa idan an kira bakwa d’agawa ne? Yasu Farhan d’in basu dai ji ciwo ba ko?” Nan ta maida dubanta gun Mubeenat da take tsaye tana kallon Umma cikin rashin fahimtar abinda taji “Mubeenat ke babu abinda ya sameki ne?”
“Kamar ya Umma meyake faruwa ne? Meya samu su Ya Farhan d’in?”
Se a yanzu ne Umma ta gane cewa Mubeenat batama san komai ba. Atif ne ya matso kusa da Mubeenat yayi magana cikin nutsuwa “Sis Mubee na b’oye miki ne dama nafi so mu dawo gida, Farhan da Shureim sunyi hatsari akan hanyarsu ta dawowa gida yanzu duk suna asibiti”
Take hawaye suka cicciko a idanunta tana fad’in “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un,ina fata dai basu ji ciwoba Ya Atif?”
“Doctor yace Shureim ya karye a k’afa da hannu” Mubeenat bata bari ya k’arasa ba tasa kuka tana cewa “Bacci mafa yakeyi dama Umma wlh har muka isa gidan bacci yakeyi Allah sarki Shureim,bana so in rasahi Umma na rasa Ummata ina k’arama bazanso in sake rasa Shureim ba Umma” ta k’arasa maganar cikin kuka yayinda Atif yake bata hak’uri “Please ki dena kuka Sis Mubee babu abinda zai sameshi nizan koma asibitin”
Cikin sauri Umma tace “Shi kuma Farhan d’in fa?” Se’a yanzu Mubeenat ta tuna dan haka ta juyo tana kallon Atif da jajayen idonta danjin amsar da zai bayar akan Farhan.
“Umma tukunna dai shikam,dan baima san inda yakeba har yanzu,amma dai baiji ciwo sosai ba” yana kaiwa nan ya shige motarsa ya fice ya barsu a tsaye Mubeenat sai rusa kuka takeyi tana “Umma dan Allah muje asibinti muma in gansu”
“Mubeenat ki dena wannan kuka domin bashine mafita ba Addu’a zamuyita musu,sannan bazaiyu muje yanzuba dan su Abbanku duk suna can dole sesun dawo zamu je.”
Hmm! Readers bazan iya gaya muku halin da su Abban Mubeenat da sauran ‘yan’uwa suka shigaba musamman ma Iyayensa da suka samu labari.
  Kana jinsu ta waya kasan suna cikin tashi hankali mara misaltuwa tunba ita Ummin nashi ba da Abbdullahi,dan shi Abbi dauriya kawai yayi irin nasu na manya.
Habibty kuwa ta kasa hana idanuwanta zubar da ruwa domin gani take babu wanda ya kaita tashin hankali ga K’ani ga kuma Masoyi.
Umma bata ce da ita tayi komai ba,dan tasanma bayi zatayiba a wannan yanayi da take ciki dan haka tayi musu girki tana jira azo a d’auke su.
Amal ce take ta rarrashin Mubeenat wanda sam ta kasa yin komai se sallah.
 
Can asibiti kuwa yanzu dai Shureim ya fara motsi tare dayin kuka yana cewa “Abba jikina yana min ciwo”
Atif ne yake rik’e da d’ayan hannunsa yana cewa “Sannu Shureim inane yake maka ciwo?”
“K’afana da Hannuna da jikina” ya fad’a a hankali.
Cikin tausayawa Atif yace “Sannu kaji? Bari naje na kira Doctor ya duba ka”
“A’a Ya Atif karka tafi ka barni ina jin tsoro”
“To shikenan ka dena jin tsoro babu inda zanje  sannu ko?”
“Umhum” yace tare da rufe idanunsa,gaba d’aya tusayinsa ya kama Atif.
Abba ne ya shigo bayan ya fito daga gun Farhan “Abba dama yanzu nace zanje in kira Doctor amma Shureim baya so in fita in barshi”
Cikin sauri ya bud’e ido dan yaji ance Abba. “Abba ka d’aukeni mu tafi gida bana so in zauna anan”
“Shureim ai baka da lafiya ne,yanzu ina ne yake maka ciwo?” Nan ya gaya mishi kamar yadda ya gayawa Atif. Ganin Abba ya shigone yasa Atif barin gurin yaje ya sanar da Doctor kan cewa Shureim ya farka.
Doctor ya nufi gun Shureim yayinda Atif kuma ya shiga gun Farhan.
Kwance yake duk ansa mishi bandage a kanshi tare dasa mishi oxcygen a hancinsa,idan ka ganshi baza kace mutum mai rai bane a kwance k’afarsa fari sol da yatsun kafafunsa dana hannaye.
“Farhan Allah ya tashi kafad’unka” cewar Atif yana k’walla,dan idan kaga Farhan dolene kayi masa k’walla.
Umma ce ta kira Abba take cewa dan Allah azo a d’aukosu suma suga majinyatan. Bayan sun gama wayanne Abba yace Atif yaje ya taho dasu.
Ko da yaje Mubeenat ce ta fara tambayarsa “Ya Atif ya masu jikin?”
“Da sauk’i Sis Mubee Shureim kamma ya farka har yana magana”
Har cikin ranta taji dad’i tare da sake tambaya “Ya Farhan kuma fa?”
“Sis Mubee har yanzu dai bai farfad’oba tukunna amma insha Allah shima zai samu lafiya karki damu kinji?”
“Allah ya basu lafiya” cewar Umma da Amal.
“Ameen” Mubeenat da Atif suka amsa.
D’akin da Shureim yake suka fara shiga Mubeenat tana ganinsa ta fashe da kuka tare da k’arasawa har inda yake ta kasa cewa komai se kuka ganin yadda aka d’aure jikinsa.
Shima kukan yakeyi tare da cewa Sis Mubee ina Ya Farhan?”
Nan aka juya ana kallonshi dan tunda ya farka bai tambayi kowa Farhan ba se yanzu da Mubeenat ta shigo.
Cikin muryar kuka tace “Shureim ka damu da kanka tukunna, ya jikinka?”
“Da sauk’i” nandai duk suka mishi sannu sannan Mubeenat tace “Ya Atif ina Ya Farhan yake?”
“Yana can shida Abba muje”
Yana gaba suna binshi a baya ita da Amal har suka k’arasa zuciyar Mubeenat se bugawa yakeyi da sauri-sauri.
Tunda Atif ya bud’e k’ofan suka hangoshi a kwance kamar wani gawa Abba yana zaune a gefensa.
Hawayene cike a fuskar Mubeenat da Amal,yayinda Abba yake shirin fita ne Amal tace “Sannu Abba ya masu jikin?”
“Jiji da sauk’i Amal sannunku” sannan ya fice daga d’akin.
Fitar Abba kenan Mubeenat ta fashe da kuka ganin halin da Habibinta yake ciki,ita kanta Amal hawaye takeyi sosai a idanunta.
“Sis Mubee please kidena kuka shi kanshi Farhan d’in baya son wata hayaniya a yanzu anfi so ya farka da kanshi”
Cikin muryan kuka tayi magana a hankali “Ya Atif ka kalleshi fa,taya bazanyi kuka ba bayan yana cikin irin wannan halin?”
“Sis Mubee dukda haka addu’a ya kamata kiyi mishi ko kuma kiyi kukan amman a hankali ta yadda bazamu tashe shiba.”
Haka suka zauna shuru a d’akin babu wanda ya sake cewa komai acikinsu daga nan Atif ya fita ya basu guri.
Mik’ewa Mubeenat tayi tana k’are mishi kallo tun daga sama har k’asa,ahankali ta matso kusa dashi tare da kai hannunta zuwa nashi tana kiran sunanshi a hankali “Ya Farhan,dan Allah ka tashi gani a kusa dakai kaji Habibina?”
Amal ce ta dafa kafad’arta “Mubee bakiji abinda akace bane,ba’a so a tashesa shiyasama ba’a so a dinga yawan shigowa,nasan halin da kike ciki amma kiyi hak’uri mujira farkawan sa”
“Amal ba laifina bane wlh,zuciyata ce take sani yin hakan dan gani nake kamar mutuwa zaiyi wlh”
“Dan Allah ki dena fad’in hakan insha Allahu zai tashi da izinin Allah bazaki rasashi ba.”
Haka Amal tayita rarrashinta kafin shigowar su Ya Musty hakan yasa su Mubeenat suka fita sannan Abba yace Atif ya mai dasu gida.
Haka suka koma Mubeenat ji take kamar ta b’ace ta ganta a asibitin inda Ya Musty da Atif sukace zasu kwana da Farhan, Umma kuma zata zauna da Shureim…Washe gari da sauri Mubeenat ta gama had’a musu abinci ta shirya tana jiran Abba ya fito su tafi.
“Mamana kin gama komai?”
“Eh na gama Abba”
“To fito mu tafi”
Fitowa tayi ta shige mota suka tafi.
Alokacin Farhan ya farka sunan Shureim kawai yake furtawa cikin razana.
Ya Musty da Atif suna ta mishi sannu amma kallonsu kawai yake kamar hoto,ganin hakanne yasa Atif tafiya kiran Doctor suka hau gwada shi kota ina tare da tambayar shi inane yake mishi ciwo?”
“A ina nake,sannan ku su waye? Dan Allah Shureim fa,ina Shureim yake? Ina fata babu abinda ya same shi ko?”
Mamaki ya kama Ya Musty danji Farhan yana tambayan waye su,cikin nitsuwa yayi magana “Farhan baka ganemu bane?”
“Eh suwa ku?”
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un,Doctor akwai matsala ya za’ayi yace bai ganemu ba?”
Nan Atif ya matso shima yace Farhan amma ni ka ganeni ai ko?”
Kallonsa Farhan yakeyi ya sake cewa “Atif?”
Nanne Atif yaji sanyi a ransa tare da cewa inaga ya kamata a barshi yad’an sake samun hutu tukunna.+
Zuwan su Abba ne duk aka shiga tare dasu Umma dayake Shureim yanata bacci.
Nan dai suketa mishi sannu yana binsu da kallo har yazo kan Mubeenat.
Ita kuwa hawaye ya gama cika a idanunta,Atif ya kamo hannun Mubeenat yace Farhan ka gane wannan?”
Kallon Mubeenat yakeyi itama kuma haka amma sai yace “Ban santa ba,who is she?”
D’ago da fuska tayi tana kallonsa cikin mamakin jin abinda ya fad’a.
Abba yayi magana “Farhan baka gane Mamana ba?”
Atif yayi saurin cewa “Sis Mubee ce Habibty?”
Rufe idanunsa yayi yana juya kansa sannan ya bud’e “Ban gane taba wlh”
Nan Doctor suka fahimci cewa akwai matsala,dan haka akace duksu fito abarshi ya sake hutawa.
Hankalin kowa ya tashi da ganin yanayin Farhan,kowa tunaninsa shine kardai ya samu cutar mantau ne? Dan ba kowa yake ganewa ba.
Bayan awa hud’u kenan dayi mishi alluran bacci sai yanzu ya farka.
Ya Musty ya sake gani agun yana mishi “Sannu Farhan”
Nanma sake kalloshi yayi tare da cewa “Yawwa ina Shureim ne?”
“Shureim lafiyanshi lau yana bacci a d’aya d’akin”
“Baiji ciwo badai ko?”
“Eh ya samu karaya ne a hannu da k’afa”
“Farhan ka gane ni yanzu?”
“A’a waye kai ina Ummi da Abbi?”
Ya Musty yace “Suna hanya basu iso ba tukunna”
“Basu iso ba daga ina?”
Nan dai Ya Musty yasan akwai matsala sosai dan haka yaje ya kira Doctors sukazo suka sashi cikin wata na’ura ta gwada k’wak’walwa,a nanne aka gano cewa akwai wani guri da jini ya shiga acikin kansa wanda hakan shine dalilin dayasa baya iya gane kowa.
Ya Musty yace “Amma Doctor ita Mubeenat fa itace wanda zai aura a ganina tafi kowa zama sosai acikin zuciyarsa taya zai mance da ita?”
“Eh ai basonshi bane hakan,zai dawo dai-dai insha Allah aci gaba da mishi addu’a,sannan ga magunguna zamu bashi yana sha cikin ikon Allah se kuga nanda wata uku ma ya dawo yadda yake adah”
Jikin kowa yayi sanyi dajin halinda Farhan ya samu kansa aciki,wanda haka sukaita jinyarsa kwanansu biyu a asibiti Iyayensa suka iso.
Bazan iya gaya muku halin da suka shigaba da sukaga d’an nasu,Ummi da Abdullahi sai kuka sukeyi. Kuma cikin ikon Allah dukya ganesu, amma anan Nigeria ne ya gane rabi bai gane rabi ba.
Farhan ya kasa gane wacece Mubeenat a rayuwarsa dukda su Umminsa sunyi iya bakin k’ok’arinsu na fahimtar dashi amma ina,bai ganeta ba, bai gane Ya Musty ba, bai kuma gane Dad d’in su Atif ba da kuma Amal,Abba ma daga bayane ya gane shi.
Satin su d’aya aka sallamesu suka koma gida inda akaci gaba da mishi jinya.
Gidan su Ummi Mubeenat ta koma da zama itace take musu abinci koda zai gano ta da wuri, amma sam baya ma shiga harkarta kwata-kwata.
Tun abun baya damunta har ya fara damunta kullum cikin kuka take Abdullahi yayi ta bata hak’uri tare da cewa muci gaba dayi mishi addu’a Mubeenat insha Allah zai samu lafiya dan Allah karki sa komai a ranki?”
“Abdullahi dole ne in damu fa,wai ya mance ni gaba d’aya baima san wacece niba acikin rayuwarsa,sannan ina k’ok’arin fahimtar dashi amma sam bayama bani wannan damar”
Haka sukaita bata hak’uri dashi da dasu Ummi,dan su shaida ne a yadda yake k’aunar Habibty’n shi.
Kakansa kuwa cewa yayi lallai saidai su koma can k’asarsu ayita mishi jinyan acan dan bai gamsu da nan d’inba.
Babu yadda suka iya haka Abbi ya sanar dasu Abba sannan aka shirya tafi.
Mubeenat tayita kuka tana rok’onsu dan Allah karsu d’auke mata Ya Farhan d’inta,amma tafiya ya zama dole haka suka dinga bata hak’uri tana k’i dan haka Abbi yace abarsu su tafi tare da Mubeenat amma Hajiya Kaka tak’i amincewa da hakan.
Mubeenat taje har inda Farhan da Abdullahi suke tsaye tana magana cikin muryar kuka “Ina maka fatan alkhairi Ya Farhan,Allah ya baka lafiya ina nan ina jiranka Habibi”
“Mubeenat stop craying please” cewar Abdullahi.
“Dolene inyi kuka Abdullahi,babu wanda yasan me nakeji a cikin raina shiyasa” ta sake duban Farhan tace “Ya Farhan babu abinda zaka cemin ne?”
Kallonta yayi tare da cewa me kike so na kawo miki inzan dawo?”
Murmushi tayi tare da cewa “Bana buk’atar komai Ya Farhan,soyayyata kawai nake so ka dawo min da ita dan kar k’aunarka ta jefani cikin wani hali.”
Tana kaiwa nan ta juya a guje tana kuka kamar ranta zai fita inda shi kuwa ya tsaya yana binta da kallo cikin tausayawa.
Hajiya kakace tabi bayanta tana rarrashinta bayan an gama sallama ne suka tafi.
_Allah sarki rayuwa_
Tun bayan tafiyar su Ya Farhan Mubeenat ta zama abin tausayi,ganin hakanne yasa Hajiya Kaka ta d’ibo kayanta da sunan tazo yin sati biyu dan ganin halin da Mubeenat ta shiga.
Tun daga lokacin duk wani walwala na Mubeenat ya k’are Islamiyya ne kawai take iya zuwa Company ma sun dena zuwa inda aka bar komai gurin su Abba.
Watan su Farhan uku da sati biyu a Madina inda ya samu sauk’i sosai idan ka ganshima baka ce ya tab’a yin hatsari ba,sai dai har yanzu ya kasa gane wacece Mubeenat a rayuwarsa.
Ganin lokacin aurensu da aka sa harya wuce ne yasa Abbin Farhan kiran Abba ya bashi hak’uri tare da gaya mashi cewa har yanzu Farhan bai dawo yadda yake ba.
Abba yace bakomai zasuci gaba dayin addu’a tare da janye maganar aure har sai lokacin daya samu lafiya.
_*******_
Bayan wata biyar kenan da faruwan hakan amma har yanzu babu wani canji.
Nanne Hajiya kaka tace gaskiya bazaiyu ace Mubeenat ta zauna tayita jiran saba sai kace shine autan maza,dan haka lallai tana so a aurar da Mubeenat dama k’ila ita ba matar Farhan bace.
Suna zaune gaba d’ayan Family inda Dad yace “A’a Hajiya mudai jira tunda suna son junansu”
“Nifa bazan lamunta ba wlh,dama can Atif yana sonta kunya ya hanashi gaya muku har saida Farhan ya fito ya sanar daku k’udirinsa akan Mubeenat d’in sannanne daga baya Atif yake gayamin wanda naga lokaci ya k’ure tunda an riga da’an ba Farhan d’in”
Dan haka yanzu inaga lokaci yayi da za’a had’a auren gida tsakaninsu.”
Duk wanda suke parlour abun bai musu dad’iba,Abba yayi magana “Atif meyasa ka b’oye min bayan kuna zaune a gida d’aya? Ai Mamana K’anwarka ce kuma dukkaninmu zamuyi murna da farin cikin haka fiyema dashi Farhan d’in,to yanzu bansan ya za’ayiba gaskiya me ka gani Babban Yaya?” Ya kalli Dad d’in Atif.
“Hajiya dan Allah kubar wannan maganar domin ni da kaina na amincewa Abbin Farhan cewar na basu auran Mubeenat idan muka canja magana kuma ai kamar bamu kyauta musu ba” cewar Dad d’in Atif.
“Wani irin ba’a kyauta musu ba? Aisu suka sake d’aga auren waise d’ansu ya samu lafiya ita kuma jikar tawa dayake ta rasa manema saita zauna tana jiransa saikace shine auntan maza? To wlh na gaya muku lallai a had’a wannan auren ko kuma ranku ya b’aci.”
Tana shirin barin parlour Mubeenat ta mik’e tsaye tare da saurin rik’o hannunta “Dan Allah Hajiya Kaka karki rabani da Ya Farhan wlh ina K’aunar shi zan jirashi koma yaushe ne amma dan Allah karku rabani da shi?”
“Ki dena wannan zancenma Mubeenat,dubeki fa yanda kika lalace kin d’auki damuwa kinsa a ranki wlh bazan bari wata cuta ta kama min keba, dan haka ki aminta da d’an’uwanki kawai nasan zaki samu farin ciki fiye dama Farhan d’in.”
Kuka sosai Mubeenat takeyi dan taga da gaske Hajiya Kaka takeyi,gashi yaran nata basa son ganin b’acin ranta dan haka take tunanin k’ila hakan zai iya yuwuwa dan haka taketa rusa kuka tare da barin parlour’n itama ta wuce d’aki.
Mubeenat ta zama abin tausayi, ta kira Atif tayita rok’onsa akan karya amince domin ita Farhan take so.
Atif yayi mata alk’awarin insha Allah zata auri Farhan ta kwantar da hankalinta.
Koda yayi k’ok’arin fahimtar da Hajiya kaka,amma sam tak’i bata sauraran kowa a yanzu. Atif yace shifa baya sonta, duk dan a janye zancen auren dan yaga Mubeenat ta shiga damuwa sosai.
Amma duk da haka baisa Hajiya Kaka ta janye maganar ba,sema k’ara hura wuta da takeyiwa Yaran nata wato Dad d’in Atif da kuma Abban Mubeenat.
Babu yadda Abba ya iya haka ya sanar da Abbin Farhan abinda yake faruwa,shi kuwa yace wlh ba komai kawai ya amincewa umarnin Mahaifiyarsa k’ila dama Farhan ba mijinta bane.
Shi kanshi Abbin Farhan baiji dad’i hakan ba,amma yasan ba laifin abokin shi bane abinne yafi k’arfinsu.
Ko daya gayawa Ummin Farhan sai tace sam bata yadda ba dan ita shaida ce akan k’aunar da Farhan yake yiwa Mubeenat wanda idan ya dawo hayyacinsa zai shiga wani hali dan haka tace lallai su koma Nigeria domin ayi auren kawai a haka.
Ummi tayita k’ok’arin fahimtar da Farhan amma sam ya kasa ganewa,dan haka suka shirya zuka Nigeria.
Koda suka zo babu abinda ya canja Hajiya Kaka tana nan akan bakanta.
Mubeenat kuwa tayita gayawa Farhan amma sai yace toki aureshi mana,ai d’an’uwanki ne. Hakan ba k’aramin ciwo yake mata ba,gashi ya gane duk wa’inda ya mance a baya amma ita ce har yanzu ya kasa gane wacece ita a rayuwarsa ta baya.
Atif ne yake sanar da abokan shi abinda yake faruwa, “Aamma sam bazan yadda ayi auren ba dan Sis Mubee tana son shi sosai lallai idan na yadda akayi auren zata shiga wani hali koma ta tsaneni.”
Nan suka gaya mishi cewa “Atif karka bari wannan damar ta wuceka wlh,kai baka ma san mune silar hatsarin Farhan ba?” Nan dai suka bashi labarin komai da suka aikata.
Cikin fushi Atif yake musu fad’a “Yanzu dakun kashesu fa? Kuma harda Shureim fa acikin motar dama kune? To lallai zanyi k’aranku danni babu hannuna a ciki ban saku ba.”
Haka sukaita rarrashin sa tare da bashi shawarwari harya aminta dasu badan yaso ba.
Ahmad Abdullahi Mubeenat harda ma Shureim sunyi iya kan k’ok’arinsu na fahimtar da Farhan akan soyayyarsa da Mubeenat,amma sam baya iya tuna duk wani abu daya faru a tsakaninsu a baya.
Hakan yasa sukace ya aureta a hakan,amma sai yace dasu bazai iya auran taba har sai ya tuna komai danshi a yanzu ba son Mubeenat yakeyi ba hakan yasa yake ganin bazai iya auranta ba.
Amma idan ya ganta cikin tashin hankali tana kuka sai yabi duk wani hanya da zaiga ya sata farin ciki,amma dai baya jinta a cikin ranshi.
Gurin aiki da Islamiyya duk an zagaya dashi amma ya kasa tinawa.
  Watansu biyu Ummi da Abdullahi suka koma,inda akabar Farhan da Abbi nashi.
Lokacin tafiya Umrah na Dad d’in Atif da Hajiya Kaka yayi dan haka tace lallai sai dai ayi bikin kafin su tafi k’ila idan ta tafi ba lallai ne ta dawo ba.
Haka aka sa ranar auren Atif da Mubeenat. Nan da sati uku.
Tun daga wannan ranan mubeenat ta dena kula kowa dake gidan harda Ummanta,Shureim da Amal kawai take kulawa,shima sai dai tayita musu kuka tana cewa suje suyita fahimtar da Ya Farhan kozai gane,dan idan tana zuwa gurinshi to lallai wata rana za’a samu ta rungumeshi koma wani abun daban…
  
Hmmm! Masu karatu wannan shine abinda ya faru a rayuwarsu ta baya har akayi bikin Atif da Mubeenat, wanda a ranar d’aurin aurensune Farhan ya dawo hayyacinsa.
Shin masu karatu sun tsinci wani darasi kuwa anan?
  Anan zan tsaya domin muci gaba da labarinmu,idan baku mantaba mun tsaya ne a idan Atif ya kamu da H I V sanadiyar halin neman mata daya saba yi a baya wanda yanzu haka Mubeenat tana zaune ne a gidansu har sai an gama mata gwaji kafin asan matakin d’auka anan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *