KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 11

 KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 11

Mubeenat ce kwance a d’akinta dake gidansu tana sharar baccinta. Wayarta ta jiyo yanata ringing,a daddafe ta d’auki wayar batare data duba mai kiran taba saboda bacci da take ji sosai.

“Hello”

“Sis Mubee kardai ince baki tashi ba har yanzu?”

“Wlh Ya Atif baccin bai isheniba duk laifinka ne ai jiya ka hanani bacci da wuri.”

“Hhh i’m sorry to,kinsan me?”

Cikin muryar bacci tace “No”

“Kiyi hak’uri da baccinnan haka,kin manta yaune zamu koma gun Doctor?”

“Please Ya Atif mu bari sai zuwa anjuma kad’an”

“Ok to shikenan kiyi baccinki” sannan ya katse wayar tare da k’ara gudun motarsa,tana shirin gyara kwanciyarta dan yin sabon bacci sai taji horn d’in motarsa daga waje.

Mik’ewa tayi ta leka ta window, ai kuwa Atif ne dan haka tayi saurin sa key a k’ofar d’akinta tana dariya.

Ko daya shigo Shureim ne da Ya Farhan zaune akan daining,gaisawa sukayi sama-sama sannan ya wuce da niyan shiga kawai yaji k’ofar a rufe.

Nocking ya shigayi a hankali batare dayayi magana ba.

“Waye?” Cewar Mubeenat bayan tasan shine.

Shuru yayi yaci gaba da nocking harta gaji tazo ta bud’e tare da murza idanunta kamar wanda ta tashi daga bacci yanzu.

Murmushi yake mata tare da k’are mata kallo “Ke wato gaki mai wayo ko? Ai nasan yanzu kika rufe k’ofar da kika san na iso”

“Nida nake bacci zaka ce wai na rufe k’ofa? Nifa ko wanka banyiba Ya Atif barema naci wani abu”

“To waya hanaki,ai ganin daman kine,dan haka wuce muje na miki wanka”

“Mene kace? Wlh ka zauna ka jirani yanzu zan fito”

“Ban yarda ba wuce muje” ya d’agata sama se faman dariya take tana cewa “Dan Allah ka bari Ya Atif wlh zanyi da kaina”

“Nak’i d’in muje nizan miki dan zamufi gamawa da wuri.”

Duk abunda sukeyi a kunne Farhan da Shureim,inda Farhan yace “Shureim ka k’oshi?”

“Eh”

“To tashi Muje yau zaka rakani office”

“To amma bari naje na canja kayan jikina”

“To kayi sauri ina jiranka.”

Da gudu Mubeenat ta fito zuwa parlour batare data lura da Farhan na tsaye ba tanata dariya tana cewa “Wlh ni bana so Ya Atif kazo ka jirani a parlour”

Biyota yayi yana cewa “Sis Mubee zaki b’ata mana lokacine ai”

“Wlh yanzu zan fito i promiss” tana kad’a mishi kanta dako d’ankwali babu akai.

Wani irin kallo taga Atif yana aikawa zuwa bayanta,dan haka tayi saurin juyawa dan taga ko dawa yake.

Ido hud’u sukayi da Farhan dake tsaye. “Sis Mubee ya kamata kisan ba ku kad’ai bane a gidan yanzu akwai Shureim”

Kunya taji sosai dajin kalaman Farhan da yake shirin barin parlour’n tayi saurin cewa “I’m sorry Ya Farhan bansan kuna nan bane”

Juyowa yayi tare da mata murmushi “Na san da hakan” sannan ya fice ya barsu a tsaye.

Juyowa tayi tana kallon Atif dake tsaye daga nesa “ka gani ko,ashe duk abunda mukeyi akan kunnensu ne shida Shureim,gaskiya naji kunya Ya Atif”

Murmushi yayi tare da nuna mata hannu alamun tazo ta shige d’aki.

Ba musu ta wuce yana biye da ita,toilet ta wuce tayi saurin sa key.+

Bayan ta fito ne tazo kusa dashi ta zauna,goge mata jiki ya shigayi batare data dakatar dashi ba har ya shiryata suka fito tare dayiwa Umma sallama akan sun tafi ganin Doctor tayi musu Allah ya kare suka amsa da ameen.

Doctor yaja jinin Mubeenat ya fita ya barsu na wasu lokuta sannan ya dawo.

“Atif ga result na biyunma still negative ya nuna mana,dan haka sai muyi fatan Allah yasa na ukunma ya kasance negative,domin idan na uku ya gwada positive to lallai dashi zamuyi amfani.”

Ajiyar zuciya Atif yayi tare da cewa “Mun gode sosai Doctor,insha Allah duk negative ne dan fatanmu kenan.”

“To Allah yasa Atif,zaku iya tafiya yanzu”

“Mun gode Doctor” cewar Mubeenat.

“Bakomai Mubeenat,amma yana shan magungunansa kuwa?”

“Eh Doctor ni shaida ce yana sha,dan kullum ni nake bashi da hannuna”

“To Alhamdulillah,Allah ya yaye”

“Ameen” sannan suka fice suka kama hanya.

Tunda suka kama hanya Atif baice komaiba ko tunanin me yakeyi oho?

“Ya Atif ya kayi shuru?”

“Sis Mubee burina shine Allah yasa baki kamu da wannan cuta ba,amma kuma ina tuna ya rayuwata zata kasance ne idan har babu ke atare dani”

“Please Ya Atif kabar fad’an haka,ina nan tare da kai babu abunda zai rabamu kaji?”

“Kin tabbata Sis Mubee? Idan akayi yunk’urin rabamu fa?”

“Waye kenan zai raba Mata da Miji? Babu ai,dan haka ka dena damuwa please?”

Ita kanta Mubeenat tasan dolene su rabu inhar bata da cutar,amma tasan za’ayi rikici sosai a wannan lokacin dan haka dolene ta nemo mafita tun wuri…

 

Shin meya kamata Sis Mubee tayine masu karatu?

  Can b’angaren Umman Amal kuwa shekaru biyu kenan tana zaune agun Malam Buba kuma har yau babu wani labari akanta.
  Dan haka ya nuna sha’awarsa nason auranta. Ita kuwa ta amince mishi da dukkan zuciyarta saboda har a yanzu bata san ko wacece itaba sakamakon asiri da yayi tasiri akanta.
Sadakinsa ya bayar naira dubu ashirin aka nemo shaidu aka d’aura musu aure. Dama can ya tab’ayin auren yaransa uku sai Allah yayiwa Matarsa rasuwa,tun bayan rasuwarta bai sake wani aurenba sai yanzu.
*Hmmm! Wannan shine ake kira kaddara,dama can Allah ya kaddara sai Malam Buba ya auri Umman Amal,Allah kasa mu dace ameen.*+
Atif bai wuce da Mubeenat gida ba,sai ya wuce dasu can gidansu.
“Ya Atif ya naga ka kawomu nan kuma?”
“Sis Mubee kince min duk lokacin da nake cikin damuwa nason tarayyar aure dake to in sanar dake zakibi ta wata hanyar ki gamsar dani,na kawomu nanne dan bazan iya yin hakan a gun su Umma ba.”
Zuciyarta sai bugawa yakeyi “Amma Ya Atif ni gaskiya ina tsoro,nan fa daga ni sai kai idan kuma ka kasa hak’ura fa?”
Fuskarta ya shafa “Ki dena damuwa Sis Mubee bazan tab’a cutar dake ba,kawai dai nayi kewar kine sosai”
Jiki sanyaye suka shige ciki ta zauna a takure daga kan kujera.
Kamota yayi ya mik’ar da ita tsaye tare da runguneta yana magana cikin wata irin murya mai tab’a zuciya.
“Sis Mubee ki yarda dani wlh bazan cutar dake ba,kawai dai so nake mu kwanta a gado d’aya ina jin numfashinki a kusa dani har muyi bacci koda na awa uku ne sannan mu koma gida,kinsan nayi missing d’in bacci tare dake kinji?”
Cikin rashin yarda dashi tace “To amma su Umma zasu jimu shuru ai”
“Ok toki sanar da ita cewa munbi wani gurin amma zuwa anjuma zamu dawo”
Toh tace dashi sannan ta kira Umma ta sanar da ita.
Wayan nata ya karb’a ya ajiye a gefe tare da sake rik’ota “Shikenan zamu iya kwanciya?”
Murmushi kawai tayi mishi tare da zame jikinta daga nashi ta koma kan gadon da zauna.
Ganin ta kasa sakin jikintane yasa shi cire kayan jikin shi amma dogon wandon shi na jikinsa ya kwanta tare da cewa “Tunda naga kamar baki yadda daniba to kije kiyi kallo ko kuma ki dafa mana abinshi idan kika gama saiki tasheni,kawai so nake yau mu zauna guri d’aya” yana kaiwa nan ya juya tare da kashe wutan d’akin.
Ganin kamar da gaske baccin yakeji yasa itama mik’ewa daga gefensa bayan ta cire doguwar rigan dake jikinta ya rage daga ita sai legis black da kuma farin bra nata.
Koda ta kwanta bargo taja ta rufe jikinta,shi kuwa ko juyowa baiyiba.
Kusan 30minits babu wanda ya sake motsi acikinsu dan haka ta tabbatar da cewa yayi bacci ne,hakan yasata baccin ita ma.
2:20pm Atif ya farka daga bacci tare da juyi sai yaji mutum kusa dashi,nan ya tuna da cewa Mubeenat ce dan haka ya matso dab da ita ya rungumeta tsam a jikinshi tare da kai hannayensa kan k’irjinta.
Hakan yasa ta farka tare dayin mik’a tana salati,muryarsa taji yana magana cikin rud’ewa “I’m sorry for waking you up Mubee”
Hannunta tasa akan nashi “Pls Ya Atif ka bari,karka tayar wa kanka da hankali”
“Please let me Sis Mubee,hakan zaisa naji dad’i a raina”
Shuru tayi bata sake cewa komaiba tana jin yadda yake mata tare da tausaya mishi matuk’a.
Tsawon minti talatin kenan yake abu d’aya dan haka ta juyo ta yadda zasuna fuskantar junansu
“Lokacin sallah harya wuce,kaje kayi alwala nima nayi sai muyi sallah” tana shafar fuskar shi.
“Kije kiyi alwalan,danni kam sai nayi wanka”
Dariya tasa mishi tare da k’wace kanta ta wuce toilet. Koda ta shiga itama wankan tayi sannan ta fito d’aure da towel duk kunya ya kamata.
Tun daga k’asa yake kallonta har gashin kanta daya ganshi a jik’e. Ahankali ya k’araso inda take tsaye yana mata dariyan shima ita kuwa kanta a sunkuye dan kunyansa dataji.
Bakinsa ya kawo kusa da kunnenta yayi maganar a hankali “Dama kema ashe sai kinyi wankan shine har kike min dariya? Kinyi missing d’inane?”
Wucewa tayi da gudu ta rufe jikinta da bargo tana murmushi,sannan ya shige toilet d’in shima.
Cikin sauri ta mik’e ta bud’e hand bag nata tasa pant nata a ciki sannan ta mayar da legis d’inta jikinta tasa kaya tana zaman jiransa tare da cewa “Niba missing d’inka nayiba Ya Atif,acikin bacci nane nayi mafarkin wani abu ya faru tsakanina da Ya Farhan,kuma ko dana tashi sai naga har pant d’ina ya b’aci,wannan shine dalilin dayasa nayi wanka ba yadda kai kake tunani bane.”
_Hmmmm su Sis Mubee keda kike tare da Mijinki meya kaiki mafarkin Farhan kuma? Inji sad-nas._
Bayan sunyi sallah ne tace “Nifa yunwa nake ji dan haka mu tafi gida”
“Baza ki tafi gida da yunwa ba,zomuje muci abinci sannan mu wuce gida”
Ba musu suka wuce,Atif sai farin ciki yakeji acikin ranshi,a nashi wautar gani yake Mubeenat tayi kewarsa ne sosai.
Bayan wata uku kenan da auren Malam Buba da Umman Amal, yau sai ta tashi da rashin lafiya na ciwon mara.
Mota ya nemo suka tafi asibiti,inda aka tabbatar mishi da cewa matarsa tana d’auke da ciki. Nan dai sukaita murna shida ita daga nan suka dawo gida duk wani aiki yace ta dena yinsa yaransa zasu dinga yi tunda dama can sun iya.
Su Mubeenat kuwa yaune ranar komawa gun doctor bayan wata uku kenan,dan haka suka shirya suka tafi…
Hmmm! Koya sakamakon result d’in k’arshen zai kasance oho kuci gaba da biyoni masoyana
   Anyi awo na ukku bayan wata ukku inda suke zaune ana jiran jin saka mako
Daga Atif d’in har Mubeenat duk a tsorace suke dan sunsan wannan shine gwaji na k’arshe,musamman shi Atif da yake tunanin lokacin rabuwarsu da Mubeenat yazo kenan inhar bata dashi.
Doctor ya shigo fuskarsa d’auke da murmushi ya zauna tare da cewa “Alhamdulillah yanzu ma dai negative ya sake nuna mana,dan haka Mubeenat ta tsira.”
Nanne hankalin Atif ya kwanta tare da cewa “Alhamdulillah! Doctor dama ana iya samun haka? Mutum na d’auke da k’wayar cutar k’anjamau yayi amfani da mace kuma ace ita bata d’auka ba?”
“Yes! Hakan yana faruwa amma in rare cases, shima idan dai amfani da macen bai wuce sau d’aya ba kamar dai irin case d’inku.”
Doctor yaci gaba da cewa “Kasan wasu nada *body immunity* ( garkuwan jikin dake yak’i da  hana k’wayoyin cututtuka shiga jikin D’an Adam) idan suna da tasiri da k’arfi suna hana k’wayoyin cututtuka shiga jikin D’an Adam musamman idan ana samun kyakkyawan abinci mai *balance diet*,
Idan cuta tayi cuta ne tana shiga jikin D’an Adam shine har take iya karya garkuwan jiki saboda tun suna iya yak’i da cutar har tazo tafi k’arfinsu ta kashesu murus ta samu wajen zama.”
“Haka kuma *white blood cells (leukocyte)* suma wani b’angare ne na immune system da ke taimakawa wajen yak’i da bak’in cututtuka da duk wani abu bak’o da zai shiga jikin D’an Adam, idan Allah yasa mutum nada body immune mai kyau da kuma wadataccen white blood cells da suke functioning sosai,cuta ko wacce iri ce tana da wahalar shiga jikin D’an Adam sai dai idan cutar ta dade ba’ayi maganinta ba shine har take cinyesu ta lalatasu sai ta samu gurbin zama.”
“A case irin na Mubeenat Allah ya taimaketa sosai saboda body immune system d’inta is verry responsive and white blood cells d’inta lokacin da muka mata *full blood count* munga yana da yawa da lfy gashi kuma yana functioning yadda ya kamata”
“Amma kam da ka cigaba da amfani da ita da babu ablnda zai hanata d’auka, yanzu dai zamu ce Allah ya so Mubeenat da rahamarsa ya tsareta da tsarewarshi sai kasan matakin d’auka kafin ka kashe ‘yar mutane.”
Shuru Atif yayi ya kasa cewa komai sai kallon Mubeenat da yakeyi kamar zaiyi kuka saboda tausayawa kansa da yayi.
Ita ma hawayene cike a idanunta har yana zuba inda yayi saurin kai hannunsa ya share mata tare da mik’ewa yabar office d’in.
Cikin tausayawa ta kalli Doctor “Yanzu miye abinyi Doctor?”
“Mubeenat dah akwai wata hanya dana gaya muku,amma gaskiya babu”
“Mun gode Doctor” sannan ta goge k’wallanta ta wuce gurin Atif dake zaune a cikin mota yanata kuka kamar k’aramin yaro.
“Dan Allah Ya Atif ka dena please?”
“Nasan yadda kakeji a yanzu,nima kuma hakan nakeji har cikin raina dan Allah muje gida.”
“Bazan iya driving ba a halin da nake ciki yanzu Sis Mubee,sai dai ki jamu yau”
Ganin gaskiyane maganarsa yasa ta zauna tare dajan motar batare data sake cewa komaiba ta maida hankalinta akan tuk’in dayake ba sabawa tayi ba.
Sun dad’e da isowa gida amma dukkansu zaune suke kamar wa’inda akayiwa rasuwa.
“Ya Atif kazo mu shiga ciki ka huta zuwa anjuma saika fito”
Shuru yayi baka jin komai sai sautin kukansa. “Dan Allah ka dena kukan nan Ya Atif,ya kake so inyi ne? Bari naje na kira Umma tunda bazaka dena ba”
Ko d’aga kansa baiyiba gaba d’aya ya zama abin tausayi alokaci guda.
Cikin muryan kuka take yiwa Umma magana “Umma dan Allah kizo kiyiwa Ya Atif magana tun a asibiti yaketa kuka har muka iso nan ko magana baya iya yi”
“Tome ya sameshi haka?”
“Umma gwaji ya tabbatar da cewa bana d’auke da irin cutarsa,duk damuwansa a yanzu shine bazai iya rabuwa dani ba,wlh Umma ina tausayawa Ya Atif har cikin zuciyata, tsoro nake kar k’aunar da yake min ya jefa shi cikin wani hali Umma” ta k’arashe maganar tana mai tsananta yin kukan ta.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” Umma ta furta tare da wucewa gun Atif “Atif dan Allah kayi hak’uri,ai ba akanka aka fara hakanba,sannan har a yanzu Mubeenat matar kace ku wuce ciki kuci abinci”
Idanunsa jawur yake kallon Umma tare da cewa “Umma dan Allah karku rabani da Sis Mubee wlh ita ce rayuwa ta bazan iya rayuwa babu ita ba dan Allah Umma”
Tausayin shine ya kama Umma “Atif Auren Mubeenat a hannunka yake ba’a hannunmu ba,kai kake da iko akanta fiye damu,dan haka ku shiga ciki har sai Abban ku ya dawo muji ta bakinsu.”
Mubeenat ce taje kusa dashi ta rik’o hannunsa tana janshi da dukkan k’arfinta yana biye da ita, ita kuwa Umma k’wallan idanunta take gogewa yayin da motar Farhan ta shigo cikin gidan ya d’auko Shureim daga skul.
Tun daga nesa yake hango Umma tana share k’walla yayin da Mubeenat kuwa take jan hannun Atif tana hawaye shi kuwa yana biye da ita.+
“Umma lafiya,me yake faruwa ne?”
“Su Atif ne yau sunje sun karb’o sakamakon gwajin da akayiwa Mubeenat, an tabbatar da bata d’auke da cutar ita”
“Hakan shiya d’aga musu hankali ita da Atif d’in,abun akwai tausayi wlh” tana kaiwa nan ta wuce Shureim yana biye da ita shi kuwa Farhan yana tsaye yama rasa me zaice…
                “Habibty bata d’auke da HIV? Alhamdulillah na tayaki murna Habibty,kai kuma Atif Allah ya baka lafiya” cewar Farhan sannan yaja motarsa ya fice daga gidan.
Atif bai bar gidansu Mubeenat ba har saida ta tabbatar mishi da cewa *tana tare dashi* sunan book d’in *miemie bee*.
Ta tabbatar mishi da cewa bazata tab’a rabuwa dashi ba inhar zai iya zama da ita batare da wani abu ya sake shiga tsakaninsu ba,shi kuwa ya amince mata da hakan.
Bayan sallan isha ne Dad d’in Atif yazo gidan domin susan meya kamata ayi akan maganan su.
Duk ana zaune a parlour ana sauraron Atif inda yaketa magiyan kar’a raba shi da Sis Mubee d’insa yayi alk’awarin zama da ita haka koda wani abu bazai shiga tsakaninsu ba tunda itama ta amince.
Abban Mubeenat dai yama rasa mai zaice gaba d’aya tausayin Atif ya kamasu dukkansu harda Farhan.
Dad d’insa ne yayi gyaran murya ya fara magana “Atif kayi hak’uri ka d’au kaddaran da Allah ya d’ora maka,babu yadda za’ayi abarka da Mubeenat kuci gaba da zama bayan ga halin da kake ciki,dole ne a raba wannan auren koda kuwa kak’i sakinta.”
“Dad wlh muna son junanmu kuma ai ta amince da yadda muka tsara abunmu ko Sis Mubee? Ki gayawa Dad please karki bari a raba mu dan Allah?”
Cikin muryar kuka take magana “Dad,Abba wlh na amince zan zauna dashi ako wani irin hali ne,amma dan Allah karku rabamu.”
“Mubeenat ku dena wannan shirmen daga ke har shi,babu yadda za’ayi ku zauna a haka koda kuwa kin amince saboda akwai zalinci,dan haka Atif karka fara abinda kai kanka kasan bazai yuba kawai ka d’au hak’uri” cewar Ya Musty.
“Haba Ya Musty kai da kanka kake fad’in hakan?”
“K’warai kuwa Atif,kasan dai ina sonka kuma ina so inci gaba da ganinka tare da Mubeenat,amma hakan bamai yuwuwa bane kayi hakuri.”
“Abba dan Allah ku barmu,wlh zan zauna dashi a hakan sai muyita zamanmu kamar yadda muke dah a matsayin Yaya da K’anwa” cewar Mubeenat.
“Mubeenat kin kasa ganewa ne,duk baku fahimci inda maganar take ba babu amfanin zamanku ai tunda babu riba,sannan musulunci ma bata yadda da hakan ba sabida zaki cutu,kaga Atif nafa gaya maka komai tun a gida dan haka karku b’ata mana lokaci.”
“Haba Ya Musty,Hajiya Kaka kiyi wani abu dan Allah?”
“Da akwai abinda zanyi danayi Atif kai kanka kasan da hakan,duk abinda suka gaya maka shine gaskiya,ka d’au hak’uri dama can Mubeenat ba matar da zaka k’are rayuwa tare da ita bane,Allah yasa hakan shine mafi alkhairi kayi hak’uri Atif.”
“Ni a ganina a d’an bashi lokaci dan a yanzu yana cikin wani irin hali ne,a d’an bashi lokaci kar ayi mishi gaggawa” cewar Abba.
“Babu wani lokaci da za’a bashi,dan abinda shaid’an yake jira kenan,bazan so ace an samu wata matsala ba dan haka kayi abinda ya dace inhar kana son  Mubeenat Atif” cewar Ya Musty.
Juyowa yayi suna kallon juna inda suketa hawaye “Sis Mubee?” Ya kira sunan ta.
D’agowa tayi tana kallonsa “Dan Allah karka cemin komai Ya Atif please?”
“Ke kanki kinsan Atif bazai tab’a aikata miki hakan ba, amma ya zama dole Sis Mubee,kaicona da mai hali irin nawa dama duk mai wani mummunan hali to dolene kaga sakayyan Ubangiji ko’a kanka ko’a kan ‘Ya’yanka ko Yayyun ka ko K’annenka ko kuma wani naka na jini, ni gashi sai Allah ya jarabceni da sonki Sis Mubee, na kuma mallakeki a matsayin matata amma kuma ina? Ina ji ina gani dole in rabu dake koda kuwa zan mutu ne”
“Dan Allah kayi shuru Ya Atif ka dena fad’an hakan,ai muna tare”
“Sis Mubee na sauke igiyar aurena dake kanki dan Allah kiyi hak’uri.”
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” duk ‘yan parlour’n suka furta,sannan Atif ya mik’e kamar wani mara lafiya yana tafiya ahankali kamar wanda babu jini a jikinsa yayi waje.
Mubeenat kuwa kuka ta fashe dashi tare da tasowa zata bishi zuwa waje,sai Ya Musty ya dakatar da ita ta hanyar cewa “Koma ki zauna” sannan yabi bayan Atif d’in inda Mubeenat ta fad’a jikin Ummanta tanata kuka mai tsuma zuciya.
“Abba dan Allah kuyi wani abu akai,wlh ni kad’ai nasan waye Ya Atif,ina tsoron irin halin dazai shiga dan Allah Dad kubarmu tare ad’an bashi lokaci Umma kiyi magana dan Allah?”
“Ki dena kuka Mubeenat,ai magana ta riga data k’are kuma yanzu” cewar Hajiya Kaka.
“Wlh bai k’are ba Hajiya Kaka saki biyu kenan har dana dah kinga har yanzu da sauran aurenmu,dan Allah ku taimaka wlh zan zauna dashi a hakan kodan in kula dashan maganinsa imba hakaba bazai shaba wlh nasan halin Ya Atif dan Allah Abbana ka taimaka min ku tausayawa Ya Atif.”
Dukkansu jikinsu ya mutu murus summa rasa abun cewa dan haka Dad d’in Atif yayi magana “Mubeenat kiyi hak’uri mu tayashi da addu’a kawai,Allah ya miki albarka”
Mik’ewa Abba yayi domin ya raka Yayansa inda Mubeenat take ta rusa kuka da gaske,Umma da Hajiya Kakane suke bata hak’uri,shima Farhan yabi bayansu zuwa waje…Kwance Samira take gaba d’aya abun duniya ya dameta,sallamar Sagir taji wanda hakan yasa ta mik’e zaune.
“Samira lafiya na ganki haka?”
“Hmmm kai dai bari,burina shine Umman Amal tabar gidan dan in auri mijinta in samu ciki in haifa masa d’a namiji domin dukkan dukiyar ya dawo gurinmu amma gashi shuru shekaru biyu kenan kusan uku ma amma har yanzu shuru?”
“To ke miye damuwarki tunda yanzuma ga kud’i sai yadda kikaga dama,ai wlh ki kwantar da hankalinki tunda ita wancan d’in ba dawowa zatayi ba.”
“Bazaka gane bane Sagir,idan ina da d’a agidan nan to koda wata rana zata dawo wlh mune da riba,amma idan bani da d’a to gaskiya akwai matsala sosai.”
“To ga sharawa mana,sai dai bansan yadda zaki jishi ba”
“Ina sauraronka”
“Me zai hana kije ki nemi wani mijin a waje ko zaki samu cikin shikenan saiki lank’aya wa Abban Amal d’in kice nashi ne?”
Shuru tayi tana nazarin kalamansa sannan tace “Kaje zanyi tunani akai idan hakan ya kama aise ayi,dan wlh ina son in haihu kota halin yaya ne”
Haka suka yanke shawaran idan tayi tunani zata sanar dashi.+
B’angaren Umman Amal kuwa,bacci take mai d’auke da mafarkin Amal wai sai kuka takeyi tana cewa “Dan Allah ina kika shiga kika barni ne tsawon shekaru babu labarin ki?”
“Haba Amal ina kuma zanje in barki,gani nan gurin aiki fa kawai naje amma shine kike cewa nayi shekaru? Lallai kinyi kewata sosai”
“To dan Allah Umma karki sake tafiya ki barni dan wlh wannan K’awar taki da kika barni da ita azzaluma ce ta k’arshe wlh sai hantarata takeyi da bakya nan”
Nan samira ta shigo ta tsaya akansu tana cewa “Sannu munafuka wato haka kika ceko? To barima in nad’a miki shegen duka agaban Umman taki inga ta tsiya”
Nan samira ta cafko Amal ta fara duka kamar zata kasheta,inda ita kuwa Ummanta tana zaune tana kuka tare da magiya “Dan Allah Samira kiyi hak’uri zaki kashemin ‘yafa ki tausaya mata mana”
Wani irin ihu Amal tasa mai rikitarwa wanda yayi dai-dai da farkawan Umman Amal daga baccin da takeyi ta fara fad’in “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” tare da k’arewa d’akin da take kwance kallo harta hango Malam Buba daya zabura shima tuni ya farka yana tambayarta “Samira lafiya kuwa?”
Mamakine sosai ya kamata dajin sunan daya kirata dashi,ta sauk’a daga gadon a zabure tana kare jikinta da hannayenta “Waye Samira kuma,sannan waye kai,me nake yi anan?”
Nanne hankalin Malam Buba ya tashi sosai,dan ya tabbatar data dawo hayyacinta ne.
“Ni Mijinkine Samira,harma kina d’auke da cikina a jikinki yanzu haka,tsawon shekaru biyu kenan muna tare dake”
Nan dai ya bata labari tun daga farkon had’uwansu har yanzu.
Salati ta dingayi tana k’walla tare da bashi labarin kanta da kuma mafarkin datayi a yanzu.
Hankalin Malam Buba inyayi dubu toya tashi,domin yana tsananin sonta sosai ya d’auki buri sosai akan cikin dake jikinta,sai kuma gashi tace mishi ita matar aure ce harma da ‘yarta budurwa mai suna Amal.
Atif kuwa ya koma gidansa inda suke zaune  shida Sis Mubee ada,kallon gidan yakeyi da kuma rayuwarsu da sukayi da ita.
Kuka yake sosai kamar mace,inda yace lallai bazai iya rabuwa da Mubeenat ba dolene ya dawo da matarsa.
Wayarsa ya ciro ya kira number’n ta,bugu d’aya ta d’auka dama ta dad’e tana neman shi amma bata sameshi ba.
“Hello Ya Atif?”
Cikin muryar kuka yayi mata magana “Sis Mubee pls kizo wlh mutuwa zanyi”
Hankalinta ya tashi sosai ta rikice “Ya Atif meya sameka kuma? Kana ina ne yanzu?”
“Ina gidanmu nida ke,pls kizo da wuri kafin na mutu” yana kaiwa nan ya katse wayar yaci gaba dayin kuka.
Hijabinta ta d’auka tare da waya ta d’auki 1k ko jaka bata d’auka ba tayi d’akin Umma amma tana toilet dan haka tacewa Shureim ya sanar da Umma cewa ta tafi gidanta gun Ya Atif yana cikin wani hali.
A guje tabar gidan inda Farhan ya hangota tana gudu,mamaki yayi tare da tambayar Shureim “Ina Sis Mubee zataje haka?”
“Wai gidansu gurin Ya Atif”
“Gidansu kuma?”
“Eh haka tace min,wai yana cikin wani hali ne”
Sam hankalin Farhan ya kasa kwanciya ji yake kamar ya bita amma kuma saiya zauna shuru yana nazari.
“Slm Ya Atif?” Take ta kiran sunanshi tare da dudduba d’akunan.
Can ta ganshi a d’akinta sai kuka yake ta k’arasa da gudu ta rungume shi “Me yake damunka Ya Atif,dan Allah ka dena kukan”
“Sis Mubee dan Allah kizo ki zauna dani har lokacin da mutuwata zata zo please karki barni?”
“Ka dena fad’in haka pls” nan ta cire hijabin dake jikinta tana share mishi fuska,ai saiya ji kamar ya had’iyeta karma a sake ganinta.
Mai zai faru? Atif ya mik’e tare da kamota ya rungume yana shirin kaita kan gado.
Cikin jin tsoro tace “Ya Atif me haka? Ka bari please bazan tafi in barka ba muna nan a tare kaji?”
“Sis Mubee idan kina sona please ki bari muyi tarayya dan bazan iya rasakiba wlh”
Tsoro ne k’arara akan fuskarta. “Haba Ya Atif me kake cewa ne? Kasan hakan bazai yuba koda zamu zauna tare kasan babu tarayyan auren a tsakaninmu indai kana sona da gaskiya”
  Atif kam sam ya kasa fahimta sai faman afka mata yake son yi,nan ta fara kuka tana tureshi gefe tare da rok’onsa amma ina baya ma sauraron ta.
Wani turare ta hango daga gefen gadon ta buga mishi akai ya koma gefe sannan ta d’auki wayarta ta fita daga d’akin tare da kiran Amal tana gudu yana biyota tana gayawa Amal cikin muryan kuka.
Hankalin Amal a tashe ta shigo gidansu Mubeenat,Farhan ta gani a haraban gida sai kai komo yakeyi.
Cikin rud’ewa tace “Ya Farhan dan Allah kaje ka taimakawa Sis Mubee,Ya Atif yana neman hakkinsa ne wai a kanta da k’arfi yanzu ta kirani take gaya min sai kuka takeyi tana can gidansu da sukayi aure pls kaje da wuri karya cutar min da k’awa Ya Farhan” ta durk’ushe a k’asa tana kuka…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *