KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 13 KARSHE

 KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 13 KARSHE

Mubeenat ce kwance a d’aki duk abin duniya ya dameta. Musamma yadda taga Ya Farhan ya fita harkanta abin na mata ciwo sosai,ita kuwa tayiwa kanta alk’awarin bazata sake kiran shi ba bare ma tayi tambaya akan shi.

Muryam Umma taji tana k’wala mata kira,cikin hanzari ta mik’e zuwa gareta “Gani Umma”

“Kije Abbanki yana kira”

“To” sannan ta wuce parlour’nsa da sallama ta samu guri ta zauna “Gani Abba”

“Mamana na kirakine domin in sanar dake cewa Farhan ya sake neman aurenki a karo na biyu,sai dai wannan karon ban nemi jin ra’ayinki ba na amsa musu cewa nabasu”

“Shin ko dai akwai wani da kike so daban?”

Wani farin cikine taji ya lullub’eta,fuskarta d’auke da murmushi tace “Ba kowa Abba bani da wani zab’i daya wuce wanda ka amsawa ayanzu,nagode Allah daya bani kai a matsayin Mahaifi Abbana Allah ya saka muku da gidan aljanna” tana kaiwa nan ta mik’e tare da barin parlour’n cikin jin kunya

.

Shi kanshi Abban nata murmushi yakeyi dan yadda yaga ‘yarsa ta nuna farin cikinta a fili,yasan duk duniya babu wanda Mubeenat take so sama da Farhan dan haka yayita musu fatan alkhairi a zuciyarsa yana mai jin farin cikin shima.

Mubeenat murna yak’i b’oyuwa,zuwa d’akin Ummanta tayi ta fad’a jikinta tana cewa “Haba Umma keda ya kamata kimin albishir kuma shine kikayi shuru,lallaima Ya Farhan Umma kinsan tunda ya tafi bai kirani ba,tun yana nan d’inma fita harkata fa yayi gabad’aya ya barni cikin damuwa,amma ba komai saina rama abinda ya mun wlh” ta k’arashe maganar tana murmushi.

“Kunji min rashin kunya ko,toke in banda abinki ba idda kike yiba,ko so kike yace yana sonki bayan kina iddan?”

Ai dai amma Umma sai muci gaba da mu’amala kamar yadda muke ada,bawai ya canja min haka ba,wlh zai dawo ya sameni saina rama Umma”

“Ni d’agani karki karya min k’afa mara kunya”

“Hhhhh haba Ummana idan ban gaya mikiba wa zan gaya wa? Allah ya barmun ku Ummana”

“Ameen,kije ki fara shiri kinama zama a cikin ruwan dana had’a miki kuwa?”

“Ina yi wlh ban tab’a fashi ba,Umma wlh ina tausayin Ya Atif idan har yaji zancen aurena”

“Abbanku zaije ya sameshi ai karki damu”

“To” sannan ta mik’e ta koma d’akinta ta kira Amal tana sanar da ita.

Dariya sosai Amal tayi tare da cewa “Sai yanzu kikaji labari? Aini tunkan ya tafi nasan komai,shi yace kar in sanar dake hhhh”

“Wlh Amal da kina kusa dani dakin sha dundu a bayan ki ‘yar rainin hankali kinaga fa yadda na damu amma shine kika k’yaleni ko? Zamu had’u ai”

“Hhhhh our Habibty is back finally…”

“Yaushe zaku dawo?”

“Gaskiya dole sai Umma ta haihu,amma zamu zo  bikin ai”

“Amal kardai har ansa rana?”

“Hhhh Habibty-Habibty ansa mana this week zasu dawo satin sama kuma kuna soyewa wata k’ila ma harmun samu baby” ta k’arashe maganar cikin zolaya tana dariya.

Itama Mubeenat abun dariya ya bata tace “Ke bafa nason wulak’anci pls ki gaya mun”

“To wai ke Habibty nine Habibinki? Ki tambayesa mana jiki komai”

“Aini mun b’ata dashi ne dan wlh saina rama abinda yamin za kuma ki gani”

“Hhhh ana hubbuki Habibtyyy!”

“Zaki gane wlh kema idan kika shiga hannuna”

“Ke dai zaki gane idan kika shiga hannun Ya Farhan hhhh”

Takaici yasa Mubeenat katse wayar tana tunanin inama Amal tana kusa data sha dundu harda cizo.+

Dad d’in Atif da Abban Mubeenat sun yiwa Atif nasiha suka bashi hak’uri akan ya d’au kaddara haka Allah ya tsara mishi.

Nasiha sosai suka mishi amma ya kasa cewa komai in banda k’walla da yake yi,tare dayin maganan zuci yana cewa “Sis Mubee meyasa zaki amince wa Farhan ki barni,ina alk’awarin mu na cewa bazaki barni ba? Da inga aurenki da Farhan gara min mutuwa ta Sis Mubee”

Haka suka gama mishi nasiha baice komai ba sai hawaye da yake bin fuskar sa.

Ayau su Farhan suka iso Nigeria,Ummi Abbi Kakansa shi da kuma Abdullahi sai abokansa guda biyar su goma cip suka iso.

Bayan an taro sune aka iso dasu gidan Abba inda ananne zasu ci abinci sannan su wuce can gidansu.

Wanka Mubeenat tayi tare da kwalliyarta d’an dai-dai tasa wani riga mai dogo hannu gold jikinsa d’auke da wani abubuwa d’igo-d’igo haka a mulmule sannan ta d’auki jan lapaya ta d’aura shi a kwankwasonta tare da wucewa dashi har saman kafad’arta kamar dai shigan indiya,sannan ta nad’a gyale black a kanta daya sha parking hannunta d’auke da black hand bag tayi kyau sosai.

Ta fito tana taku a hankali ga wani k’amshin turare da iska yake ta yawo dashi a harabar gurin.

10

Duk suka zuba mata ido tun daga k’asa har sama suna kallon ta. Gun Ummi ta nufa kai tsaye inda Ummi ta fara cewa “Oh my Habibty come here lemme give you a hug please”

Murmushi cike da fuskarta ta k’arasa tare da rungume Ummi tana cewa “Wlcum Ummi,i’m so happy to see you again”

Farhan dai ya gama bushewa a tsaye ko k’yafta ido bayayi hakama friends nashi.

Bayan wannanne ta d’an rusuna tace “Abbi sannunku da hanya,sannu Kaka”

“Yawwa Mubeenat sannu” suka fad’a a tare sannan ta kalli su Ya Farhan tace “You are all wlcum”

“Thanks our Habibty” sukace da ita sannan ta sake kallonsu tace “Your Habibty? I’m not your Habibty, kar in barku a tsaye bisimillah ku k’arasa ciki nayi bak’one a waje zanje in dawo” ta k’arashe baganar tare da hararan Farhan.

Dariya suka sa suna kallon Farhan inda yayi saurin bin bayanta su kuwa suka wuce inda Ahmad yake musu jagora.

Mamaki sosai ya kama Farhan daya hango Mubeenat zaune a cikin wata mota ga kuma wani yana zaune a ciki.

Gun motar ya k’arasa yana nocking dayake glass d’in tin ne. Fitowa  tayi ba tare data bari ya kalli na cikin motar ba tace “Ya Farhan ina hira ne,amma yanzu zan shigo”

Kallonta yakeyi har cikin ido baisan lokacin daya ce mata “Waye shi?”

Murmushi tayi tace “Kamar ya waye shi kuma?”

“Ina nufin meya zo yi agurin matar da zan aura?”

“Matar da zaka aura? Kaima kace matar da zaka aura ai ba’a riga da an d’aura auren ba tukunna”

Cikin mamaki yake kallonta “Habibty what are you saying?”

“Please Ya Farhan kaje zan shigo yanzu”

“No bazai yuba,fito mu tafi”

“Kamar ya in fito bak’o nayi taya zaka ce in fito mu tafi shi kuma fa? Ko baka san cewa shine zan aura ba?”

“Shine zaki aura?” Da sauri ya zaga ta d’aya gefen ya bud’e motar ai sai yaga k’afar namiji sanye da takalma masu tsadan gaske hakama kayan jikinsa.

Fitowa yayi fuskarsa d’auke da murmushi ya mik’awa Farhan hannu tare dayi masa sallama,cikin rashin fahimta Farhan ya bashi hannu tare da amsa mishi sallama.

“Sunana Anwar wanda zai auri Mubeenat”

“Wanda zai aureta?” Ya maida kallonsa gun Mubeenat tayi saurin cewa “Ya Farhan shine wannan”

Kallonta yakeyi cikin rashin fahimta ita kuwa Anwar take yiwa murmushi.

Amal da Aisha dake zaune a bayan motar sai suka fashe da dariya tare da fitowa daga motar suna kallon Mubeenat.

Haushi ya kama Mubeenat ta tsaya hararansu su kuwa suka nufi gun Ya Farhan suna dariya tare da cewa “Ya Farhan sannunku da isowa,shima Anwar dariya yayi tare da dafa kafad’ar Farhan yace “Haba Ango kardai ace ka karaya ne? Ni dai sunana Anwar wanda zai auri Aisha ne ba Mubeenat ba karka kaimin duka please”

Dariya suka sa dukkansu inda haushi ya kama Mubeenat ta wuce cikin gida tana hararan Amal da Aisha da suka kopsa mata.Bayan sun gaisa ne Farhan yace da Anwar “To bissimillah mana mu k’arasa ciki”

Amal da Aisha suka wuce ciki su Farhan kuwa suna biye dasu a baya.

Mubeenat suka hango ita da Shureim sai fama kai abinci suke yi zuwa side d’in su Ya Farhan,ganin hakanne yasa sukayi saurin k’arasawa gurin ta tare da cewa “Amarsu da kanki? Ayi mana afuwa kije ki huta”

Wani wawan harara ta bisu dasu tare da mik’a musu suna mata dariya.

Juyowar da zatayi danta koma ciki sai taga Farhan da Anwar,dariya yazo mata amma saita wayance tare dasa hannunta ta kare bakin ta.

Ta gefen inda take ya k’araso yana kallonta “I’m sorry Habibty”

Wani irin kallo ta watsa mishi tare da cewa “Sorry? Hmmm!”

Shirin wucewa take yayi saurin tareta tare da cewa “Ooh come on Habibty so kike Anwar yamin dariya?”

Anwar dake tsaya yana jiransa yace “Ai ina kanyin dariya kam”

Kallon Anwar d’in tayi sannan ta sake kallon Farhan tayi magana cikin shagwab’a “I’m happy to see you Habibi”

Dad’i yaji sosai “Thankyou Habibty,kinsa naji dad’i”

“Zan iya wucewa?”

“Sure” sannan ya matsa gefe ta wuce Anwar yana mata dariya.

Tana isa ciki gun Ummi ta wuce sai shagwab’a ta Ummi take,Umma tana musu dariya tare da cewa Mubeenat “Wai ke bakya jin kunya ne god’ai-gid’ai dake a kan  k’afar ta?”

“Kunyan me zata ji kuma,ni bana son irin wannan kunyan gara ta saki jikinta dani ta d’aukeni tamkar ke”

Haka dai sukaita hira bayan su Amal sun magane Mubeenat ta koma d’akinta suma suna nasu bidirin acan.

Bayan magrib su Ummi suka koma gidan su dasu Farhan dukka dama Farhan yabar komai a hannun Ahmad an sake gyara ko ina agidan dukda dai dama bayi da wani matsala.

Side d’in su suka nufa harda Anwar d’in anata hira bayan isha Anwar da Ahmad sukace zasu tafi Farhan yace “Bari in kira Habibty idan tana son ganina saina biku”

Wayarsa ya d’auka ya kirata sunata hira dasu Aisha ganin kiran sane yasa ta dakata tare da d’aukan wayar “Slm”

“Wslm Habibty me kikeyi?”

“Ba komai,hira muke dasu Aisha”

“Kina son ganina ne?”

“Karka damu nasan ka gaji dan haka ka huta kawai”

“Are you sure?”

“Yes”

“Alright i will call you later”

“Okay byee”

“Byee Habibty” sannan ya katse tare da ce musu “Muje in rakaku”

“Yi zamanka ai mu biyu ne” cewar Ahmad.

“To shikenan Anwar mun gode sosai fa”

“Don’t mention Ango” ya fad’a suna dariya suka wuce.

Hiransu kawai sukeyi cikin harcen larabci gwanin ban sha’awa har kusan 10:22pm sannan kowa ya hau net yana damuwar sa,shi kuwa Farhan ya kira Mubeenat suna hira.

“Ni kayiwa haka ko Ya Farhan?”

“Habibty i’m sorry iddah fa kikeyi kuma aduk lokacin dana ganki ji nake kamar in sake furta miki cewa ina sonki,kuma kinga hakan bai daceba a musulunce shiyasa kawai nayi hakan,but ke kinsan ai bazan miki haka ba ko? sai da dalili”

“Hmmm nidai nayi fushi”

“Haba Habibtyna,i’m sorry for the second time,infact zanyi ta baki hak’uri har sai kin hak’ura”

“To ka shirya bani hak’uri dan ba yanzu zan hak’ura ba”

“Haba Habibty kina so ki hanani bacci ne? I’m so sorry please forgive me?”

“Nak’i d’in”

“Okay tell me,me zanyi ki min hak’uri?”

“Wak’a zaka min mai dad’i kuma da hausa”

“What?! Please ki canja Habibty ban iya wak’a ba i swear”

“Hhhh nidai sai kamin kafin in hak’ura”

“Habibty…?”

“Yes”

“Alright then”

         🎼🎼🎼🎼

In ina tafiya inna ganki zan duk’aa… In ina bacci inna jiki zan farka, bani fatan in kalleki kina yin kukaa… mai tab’a min ke nizann yimai duka, ni jarumine ni k’arfina zanyi rik’aa… sam karkiji komai sam karr kiyo shakka, rabuwa bamu yowa alk’awarii rik’ewaa… Yaaa salam Habibtyna karki barni…

“Hhhhhh lallai Ya Farhan a ina kaji wannan wak’ar harka haddace?”

“Habibty you are too much,i can’t believe wai nina miki wak’a fa”

“Hhhh saura uku ma ai”

“No Habibty wannan ma a bakin Ahmad nakeji yana yiwa Amal shine nayi sata”

“Oooh to ban yadda ba copy-copy,nima kamin nawa daban”

“Haba my Habibty banyi k’ok’ariba kenan yanzu?”

“I’m just kidding Habibi wannan d’inma ban zata zaka yiba wlh dan nasan baka iya ba,amma fa kayi k’ok’ari kamar dama can kai kayi wak’an”

“Hhhh Habibty keba? Ina Amal?”

“Tana can parlour suna kallo a zee world”

“Ok but karfa ki gaya mata na miki wak’a”

“Ai harma nayi recording zan kuma sa mata taji”

“Habibty please?”

“Nak’i” ta amsa shi cikin zolaya”

“Ni kike yiwa haka ko? Ba damuwa nagode”

“Yawwa Ya Farhan?”

“Ahaan”

“Please ina neman wani alfarma a gareka”

“Ina jinki”

“Akan Ya Atif ne,gaba d’aya ya fita harka ta baya ma son ganina,sannan ya dena shan magungunansa please Habibi kaje kayi masa nasiha wata k’ila zai d’auka”

Shuru Farhan yayi na d’an wani lokaci sannan yace “I will do that tomorrow insha Allah Habibty ki dena damuwa”

“Thankyou so much”

“Always Habibty,sai kuma me?”

“Shikenan”

“Idan akwai wani buk’atun let me know please?”

“Babu Ya Farhan dama shi d’inne kawai, kuma na gode daka fahimce ni”

“Habibty can i ask you?”

“Yes ina jin ka”

“Kina son Ya Atif ne?”

Mamakin tambayan nashi taji sosai “Haba Ya Farhan,a tunanina kaine mutum na farko wanda ya sanni fiye da kowa ashe dai ba haka yake ba”

“No Habibty bawai dan abinda kika gaya min yanzu bane yasa nace haka,kawai dai tambaya ce,amma idan bakiji dad’in shiba mubar maganar and i’m sorry”

“Ba komai Ya Farhan,ai kana da daman yimin ko wace irin tambaya,gaskiya Ya Farhan ni ban tab’a son Ya Atif a matsayin mijina ba,sai dai a matsayin Yayana wanda na shak’u dashi nafi ji dashi kuma akan sauran Yayyuna,sai dai zaman da mukayi dashi na d’an watanni yasa shak’uwar mu tafi na dah wanda inaga shiyasa kuke min kallo kona fara sonshi ne.”

Mubeenat taci gaba da cewa “Ya Farhan bazan b’oye maka ba,ina matuk’ar ji da Ya Atif yadda baka tunani domin ya kasance kanar soul mate d’ina ne,amma zuciyata mutum d’aya tak take k’aunar ya shige cikinta ya zamo abokin shawararta daga duniya har lahira wanda ba kowa bane wannan mutumin illa Farhan Abdulhali Taimoor,Ina k’aunar ka fiye da yadda nake k’aunar kaina Ya Farhan i love you,i love you so verry much kai kad’ai ne mutumin da zuciyata take son kasan cewa dashi kazamo Uba ga ‘ya’yan da zan haifa,Ya Farhan ka jingine duk wani tunaninka a gefe domin addu’arka ta gama karb’uwa a kaina,ka riga daka gama dani shiyasa duk abinda Ya Atif yayi bana ganin laifinsa domin soyayya babu abinda bata sawa dukda dai akwai nashi kuskuren,dan Allah Ya Farhan ka rik’eni da amana please?”

Shuru Farhan yayi dan tunda Mubeenat ta fara bayani ji yake kamar ana busa masa sarewa mai dad’i wanda hakan yasa duk wani fanni na jikinsa sai daya tashi dan farin cikin jin kalaman ta,ita kuwa k’walla ne yake bin fuskarta wanda itama bata san da fitowar saba.

Farhan baisan sanda muryarsa ta canja ba yace “Habibty zaki kasheni ai irin wannan kalamai naki duk kin rikitani wlh nama rasa abinda zan ce miki”

Itama shuru tayi tana sauraron yadda taji muryarsa ya sauya gaba d’aya. Katseta yayi da cewa “Habibty i love you more than you do,a yanzu Farhan kamar sabon jaririn da aka haife shi yake,yadda kika renesa haka zai kasance miki farin cikina,insha Allah baza kiyi kuka dani ba Habibty ki kwantar da hankalin ki my Habibty”

“Good night” shine kawai abinda ta iya furta mishi sannan ta katse wayar.

Rufe idanu Farhan yayi tare da kwanciya akan gado yana mai jin wani farin ciki a ransa tare da lasan lips nashi yace “Habibty kin kasheni”

Muryar Abdullahi yaji yana cewa “Ta sumar da kai dai,ba kisa ba”

Tashi yayi zaune yace “Gaskiya love yayi Abdullahi,ashe dai da can cutan kaina nake tayi”

“Hhhh Farhan” sukaita hira daga nan suka kwanta bacci.Washe gari Farhan da Ahmad suka je duba Atif har gida,bayan sun gaisa dasu Mummy ne suka wuce d’akin sa kai tsaye.

“Assalam”

Wani zafi yaji zuciyarsa tayi da yaga Farhan,kamar bazai amsa sallamar ba,sai kuma yayi tunanin ladan da zai wuce shi dan haka yace “Wa’alai kumus salam”

Duk da dai baice dasu su zauna ba,sai suka samu guri suka zauna tare da mik’a masa hannun suka gaisa amma baiso ba.

Farhan yace “Atif nazo ne domin na baka hak’uri akan duk wasu abubuwa da suka faru a tsakanin mu,domin yana da kyau musulmi ya zama mai yafiya da kuma mance duk abinda aka mishi a rayuwa”

“Atif nasan kana da ilimi kasan abubuwa da dama mai kyau da mara kyau sai dai wani lokacin muna da mantuwa,idan baka manta ba a zamanin Annabi Muhammad (S A W) yana zaune da Sahabban sa yana musu nasiha,can sai yace “Ku saurara yanzu d’an Aljanna zai shigo”

Sahabbai suka juya suna kallon k’ofar shigowa domin suga waye wannan d’an Aljannan,sai suka ga wani Mutum yana rik’e da takalmansa a hannu gashi babu yadda yake ma’ana ba yadda suke tsammanin ganin sa ba suka gan shi.

Washe gari ma haka Manzon Allah (S A W) yana cikin musu wa’azi sai yace “Ku saurara d’an Aljanna zai shigo” nan suka zuba ido sai suka sake ganin wannan Mutumin jiyan ne. Washe gari ma haka ya sake faruwa gunka sau ukku kenan?

Bayan an gama wa’azin ne sai d’aya daga cikin Sahabban yace lallai ni yau saina bi wannan Mutumin gidan sa domin inga mai yake yi da kullum sai Annabi yace ga d’an Aljanna zai shigo.

Sahabi yabi Mutumin nan har gida suka gaisa sai yace “Bawan Allah laifi nayi wa Mahaifina shine yace inbar masa gida na tsawon kwana ukku baya son ganina dan Allah ka taimaka min in zauna tare da kai na wannan kwana ukkun?”

Mutumin yace “Ba komai ina maka maraba”

Cikin dare suna bacci amma shi Sahabi ba baccin yake ba idonsa biyu amma dai arufe suke kamar mai baccin gaskiya,a tunaninsa zai ji Mutumin nan ya tashi sallan dare ne amma sai gaya baccin sa kawai yake yi,mamaki ya kama Sahabi yace “To k’ila azumi yake yawan yi”

Da safe yaga ya kawo musu abinci sunci tare. Abin ya dad’a bawa Sahabi mamaki,haka dai sukayi wannan kwana ukkun babu abinda ya canja. Ran da ya cika kwana ukun ne sai yace “Bawan Allah maganar gaskiya dai babu abinda ya had’ani da Mahaifina,abin da yasa na biyoka shine kullum idan zaka shigo masallaci sai Annabi yace mana mu saurara ga d’an Aljanna zai shigo har sau uku,shine nace zanzo gidan ka domin inga wasu irin ayyuka  kake yi haka,sai kuma naga baka ma sallan dare bare azumi.”

Shi kanshi Mutumin sai mamaki ya kama shi yace “To gaskiya dai abinda ka kani shine kullum nake yi”

Sahabi ya mishi sallama harya fara tafiya sai Mutumin ya kira shi yace “Idan akwai abinda nakeyi daban to shine tunda nake ban tab’a kwana da haushin waniba a zuciya na,tumma kafin mutum yamin laifi na riga dana yafe masa wannan shine sam bana rik’o.”

Allahu akbar,yaku ‘yan’uwana akwai wanda zai iya yin haka a yanzu kuwa? Inama ace yau ni Sadiya Tahir haka nake? Yau ace na tashi nayi niyan yafewa Mijina,Iyaye na,’Ya’yana,’Yan’uwa na,Mak’wabta na,Malamai na,D’alibai na dama dukkan sauran ‘Yan’uwa musulmai harma da wa’inda ba musulmai ba,Allah ka shaida na yafe musu har abada. Kufa masu karatu?

Dan Allah mu zamanto masu tsarkakakkun zuciya ako wace irin hali muka samu kanmu Allah ka gafarta mana ka k’ara tsarkake mana zuciyoyummu ameen.

Haka Farhan yaci gaba da kawo k’issoshi daban-daban yana musu nasiha gaba d’ayan su wanda jikin Atif sai ya mutu murus,domin dama can akwai ragowar imanin musulunci a zuciyar sa.

Farhan yaci gaba da cewa “Dan Allah Atif kayi hak’uri ka yafe min duk abin da ya faru,ba wai dan Sis Mubee tamin magana bane yasa nazo,wlh dama can akwai wannan niyan a raina sai kuma naga ta damu sosai jiya take  min magana akan ka. Atif Sis Mubee tana sonka so na hak’ik’a kuma babu yadda na iya nima domin ba laifinta bane dama can haka Allah ya tsara sai kuma ya faru babu makawa,dan Allah kayi hak’uri.”

Ba Atif kad’ai ba,shi kansa Ahmad jikinsa ya mutu dama akwai wanda suke gaba dan haka nan take ya yafe masa acikin zuciyar sa,ya kuma yi alk’awarin zaije ya same shi su yafi juna gaba d’aya.

Mik’ewa sukayi dukkan su biyu suka sake mishi sallama tare da fatan Allah ya bashi lafiya.

Har suka fita daga d’akin Atif baice dasu komai ba sai da suka fita ne sannan zafafan k’walla suka fara zubo masa yana cewa “Nagode Farhan,na gode sosai da Allah yasa muka had’a alak’a da kai,na yafe maka har abada wlh komai ya fita a raina da izinin Allah ina fata kuma zaka yafe min ni da Abokai na,Allah sarki Sis Mubee,nayi alk’awarin sanya ki farin ciki insha Allah.”

Shi kansa wani dad’i yaji,ga kuma wata ni’ima da yake ji yana shigar sa a hankali harma baya so ya dena jinsa.

Su Abban Mubeenat kuwa ana ta shirye-shiryen biki,Dad d’in Atif yace aje a kwaso kayan Mubeenat da yake gidan Atif wanda za’ayi amfani dasu sai a barsu furnitures kuwa duk a sayar sai a cika ayi mata sabo.

Haka kuwa akayi,komai dai masha Allah,tana cikin farin ciki mara misaltuwa sai dai wani lokacin hankalinta na gun Ya Atif da yake basu ji komai daga gare saba har yanzu.

Tana zaune sai ga motar Atif dana Friends nashi har guda ukku.

Cikin sauri ta fito ta nufi gurin su fuskarta d’auke da murna “Ya Atif?”

A hankali ya fito da k’arfe d’aya a hannun sa yana d’an d’ingisawa tare dayi mata murmushi “Yes Sis Mubee ina Angon?”

“Yana can parlour’n Abba,ya jiki naga yanzu da k’arfe d’aya kake tafiya masha Allah,Allah ya k’ara lafiya Ya Atif” tana magana murna fal akan fuskar ta.

“Ameen Sis Mubee ina tabbatar miki da cewa kafin bikin ku zan ajiye wannan k’arfen ma domin zansha rawa sosai agurin dinner”

“Hhhh kai Ya Atif kadai bari ka samu lafiya sosai,sannun ku da zuwa bisimillah ku iso”

“Yawwa Sis Mubee mun gode” sannan suka wuce parlour’n Abba tana binsu da kallo har da k’wallan farin ciki.

Bayan sun gaisa da Abba ne sannan suka gaisa da Farhan. Daga nan suka fito dukkan su suka wuce side nasu inda dukkan su suka bawa Farhan hak’uri akan abin da suka mishi shi da Shureim.

“Dan Allah ku bari,ni dama ban yiwa kowa hiran ba,kuma ya wuce har abada Allah ya yafemu gaba d’aya sai dai ina neman alfarma agun ku?”

Atif yace “Name kenan?”

Farhan yace “Naga lokacin auren ka abokanka dewa,ni kuma kaga mu 8 ne har da kai,dan haka nake son kaban aron abokan ka”

“Hhhh” suka sa dariya Atif yace “Wannan ai mai sauk’i ne imma kana son k’ari fiye da haka zaka samu sai dai mud’in ba kamar ku mune b… Farhan ya katse shi da cewa “Damu daku duk d’aya ne,Allah ya shiryar damu baki d’aya”

Suka amsa da “Ameen” sannan suka tambaye shi programs na bikin yana musu bayani dalla-dalla suma kuma suka kawo nasu shawaran ya kuma amince musu…Bikin Farhan da Mubeenat sai k’ara towa yake yi,duk wani shirye-shirye an gama shi dan shi Farhan yace babu abin da za’ayi a bikin,amma sam su Atif sunk’i dan sune ma suka had’a musu dinner.

Mubeenat kuwa Ummin Farhan ne take ta had’a ta irin nasu had’in na larabawa dama kuma can Umma tana bata ruwan lalle da ganyen magarya tana shiga ciki. Ita kanta Mubee tana jin irin aikin da abubuwan keyi a jikin ta,na Ummin Farhan d’in duk dai ba wasu b’oyayyun abubuwa bane *INIBI NE BUSHASHSHE* irin wanda ake samu a makka,hmmm yana saurin sauk’ar da ni’ima babu wasa sam acikin sa dan cikin minti biyar zakiyi mamaki.

Sai kuma *man hulba dana habbatus sauda da zuma* wannan kullum chokali uku-uku take bata safe rana da kuma dare,amma shi man habba d’in chokali d’aya take bata sau uku a rana.

Bayan wannan abubuwan dana lissafa muku babu komai sai fruits,koda yaushe tana shansu sosai musamman ma kankana.+

Yau aka shiga satin biki, Ango dai had’uwa ya gagara tsakaninsa da Amaryan sa,duk da cewa kusan kullum saiya zo amma baya ganin ta.

Ranan laraba tana shirin tafiya saloon saiga wayar shi “Slm Habibty”

Ita kanta tayi kewarsa sosai dan haka tayi magana cikin shagwab’a “Wslm Habibi had’uwa tayi wuya”

“Ban yadda ba kece dai bakya son mu had’u ko?”

“Wlh Habibi hidima ne,amma ai komai ya kusa zuwa k’arshe ka d’an k’ara hak’uri kaji?”

“Nak’i,kina ina?”

“Gani yanzu zamu je wanke kai dasu Amal”

“Wa zai kaiku?”

“Wlh ban sani ba tukun,may be Anwar ne zasu zo da Aisha”

“Ban yarda ba,ki sanar dasu kowa yayi tafiyar sa ni zanzo in kai Wifey na”

“Hhhh to shikenan zan gaya musu,idan kana kusa to ina jiran ka”

“On my way Habibty”

“Ok saika iso” sannan ta sanar dasu Aisha suna ta mata tsiya.

“Sis Mubee zan rakaki,kinga Ya Farhan ya shareni yanzu kamma”

“Hhhh haba Shureim kaima kasan Ya Farhan ba zai tab’a mancewa da kai ba,kama san kuwa kaine babban aboki?”

“Ni kuma,hmm Sis Mubee aini na b’ata da Ya Farhan ni dai muje in raka ki”

“To shikenan muje” suna isa waje yaga motar Ya Farhan ne nan ya juya zai koma Mubee tayi saurin janyo rigar sa tare da buga motar Farhan da d’ayan hannun ta tana cewa “Haba K’anina na kaina,kafi kowa sanin waye Ya Farhan ai dai ka mishi uzuri ko?”

Dai-dai nan Farhan ya iso gurin su sanye yake da suite blcak yayi kyau sosai ya kalli Mubee tare da cewa “Barni dashi Habibty,ba’a shiga tsakaninmu ai koba haka bane?”

Shureim ya zunb’uro baki yace “Ni dai mun b’ata tunda aka fara maganar auren ka da Sis Mubee shikenan ka sani a kwandon shara na d’auka ma nine babban aboki?”

Kamo hannusa yayi dukka biyu yana murmushi “Haba Shureim kar kasa Habibty ta mana dariya mana,na gaya mata fa cewa kai ne babban aboki harta kayan da zamu sa iri d’aya ne,ita kanta Habibty munfi sati bamu ga juna ba kayi hak’uri na karb’i laifina shikenan?”

Nan yayi murmushi “Toh na hak’ura amma fa zan biku”

“Of cause kaine ma a gaba ita sai ta zauna a baya ita kad’ai ko?”

Nan suka tafa itama sai dariya take musu tare da satan kallon Farhan dan yayi mata kyau sosai.

Suna gaba tana baya shi kuwa sai kallonta yake ta mirrow,data gano kallonta yake sai ta saka wayarta a kunne kamar mai yin waya tace “Hello Amal,ki cewa Ahmad idan yana driving ba’a kallon baya musamman ma daya san ke tashi ce har abada dan haka kice ya kalli gaban sa.”

Farhan yasan dashi takeyi dan baiga lokacin data danna wayan taba kawai sawa a kunne tayi bayan ta kalleshi tayi murmushi.

“I love you Habibty” shine abin da ya furta a yayin daya juyo suna kallon junan su.

Kunya sosai taji ganin Shureim yana zaune kuma yasan me hakan yake nufi,sunkuyar da kanta tayi dan kunya daya kama ta shima ya d’auki kiran wayan da Ahmad yake mishi.

Har suka iso shagon saloon d’in waya yake yi,ita kuwa Mubee fitowa tayi daga motar shima yace wa Shureim ya jira shi a ciki sannan ya fito yabi bayan ta,tana shirin shiga shagon yayi saurin kiran sunan ta “Habibty”

Cak ta tsaya tana jiran isowar shi,ganin bai gama wayan bane yasa tace dashi “Karka damu kaje kawai idan na gama zan kira ka”

“Are you sure?”

“Yes thankyou”

“Habibty wait,ina so inji wani abu daga gareki”

Murmushi tayi tare da cewa “I love you too Habibi” sannan tayi saurin shigewa yana murmushi tare da cewa Ahmad “Wlh gaba d’aya ka dameni”

“Hhhh to shikenan bari in jira ku gama soyayyar taku saina sake kira”

“Ai ka koreta dan haka nima gani nan zuwa,kuma kayi sauri ka kawo Amal dan bana so ta zauna cikin kad’aici.”

“An gama ango mai jiran gado”

“Allah ya shirya”

“Hhh ameen,nima dai na kusa in zama ango mai jiran gadon inji yaya kake ji a yanzu”

“Ka isheni Ahmad sai ka iso nama fasa tafiyan ina jiran ka”

“A’a kaje kawai tunda koka jirani ma ba’a mota d’aya zamu tafi ba”

“To shikenan” sannan ya katse wayar ya kalli Shureim “Me kake so in saya maka?”

“Ice cream”

“An gama babban Aboki”

“Hhhh Ya Farhan ka dena zolaya na fa”

“Da gaske nakeyi,kuma zaka gani,ka manta farkon zuwa na garin nan da kai na fara sabawa? Dan haka kaine babban Aboki”

“Ya Abdullahi fa da Ya Ahmad?”

“Duk a bayan ka suke ai kai daban ne aguna Shureim,infact tare ma zamu tafi Madina tunda kunyi JSCE”

Nan dai Shureim yayi ta murna suka ci gaba da hiransu cijin raha.

Bayan Amal da Aisha sun iso ne namma sukai ta tsokanar Mubee har suka gama Ya Atif ne yazo d’aukan su kamar yadda Farhan ya sanar dashi,Mubee ce a gaba nan suka had’e kai da Atif yana tayata rama abin da su Amal sukai mata.

  Yau take ranar sa lallai da dare yayi  sai feshe Mubee ake da turare masu k’amshin gaske har da Ya Atif yana ta zolayarta,nan taji kukan gaske yazo mata tana tayi Aisha da Amal suna mata wak’an *Ke kika ce kina so da bakice kina soba da ba’a baki shiba,ariii ke amaeya.* Atif yace “Ku dinga tafi mana” sannan ya ciro wayarsa yana veiwing nata wai zaije ya nuna wa Farhan yadda ake sa lalle. Umma ta lek’o ta gansu sai dariyan Atif rake yi.

Washe gari friday bayan an dawo daga Masallaci aka garzayo k’ofar gidan Alhaji Abdullahi Bakari aka d’aura auren *Farhan Abdullahi Taimoor tare da Mubeenat Abdullahi Bakari akan sadaki 500k.*

Farin ciki agun wad’an nan masoya bazai misaltu ba,kowannen su da irin farin cikin da yake ji. Ba sai na zai yana muku irin taron mutane da wannan aure ya samu ba,sai dai ince ku anyana a ranku. Daga Angon har Amaryan kun san su,kun san kyawawane musamman ma shi Ango Farhan😘.

Wurin tand’e-tand’e da lashe-lashe aka wuce shima basai nace komai akai ba,amma anyi albazaranci wanda shi dai Farhan bai so hakan ba,duk aikin Atif ne ya kashe naira bana wasa ba.

Haka akai ta pictures ta b’angaren Ango da Amaryan duk kowa farin ciki kawai yake nunawa su Ya Abdul-Hamid da Ra’is ma duk sun halarci wannan aure kowa yana farin ciki fiye ma da aurenta na baya.

Bayan sallan isha aka fara shirin dinner nan ma Ango yayi fita na kece raini dan harya fi Mubeenat kyau,inda yayi shiga irin nasu,itama tayi kyau sosai dan bamma gane taba.

Abdullahi shine yazo d’aukan Amarya shi da Shureim ne a gaban mota Ango Farhan yana zaune a baya har suka iso gidan su Mubeenat.

Su Amal ne ke mara mata baya har gun motar,inda Ya Atif yayi saurin zuwa ya bud’e mata k’ofa tare da feshe ta da spray harta zauna kusa da Habibin ta sannan ya rufe k’ofar tayi saurin sunkuyar da kanta dan wani kunyan sa take ji,gashi taga ya mata k’warjini sosai a ido.

Abdullahi ya juyo yace “Zamu iya tafiya Amarsu,kodai mu jira su?”

Shuru tayi dan kunya Farhan ne yace “Muje” tare da kamo hannunta yasa a cikin nashi ji tayi kamar ta nitse ya dena ganin ta.

Bayan an isa gurin dinner ne Abdullahi da Shureim suka fita a cikin motar suka barsu,Farhan ya tallafo ta zuwa kafad’arsa har zaiyi magana sai Mubee tayi saurin nuna masa yatsan hannunta inda Farhan ya hango *sadnas* ina ta faman rubutu a cikin littafina. Kallona yayi sosai tare da cemin “Sad-nas ko zaki d’an bamu minti goma?”

“Cikin sanyin jiki nace “To” sannan nabar cikin motar nima na tsaya daga waje ina gadin su…

Anyi dinner lfy aka gama sannan aka fara mai da jama’a gida,dan gaskiya ba k’arya sun sami mutane ‘yan company nasu sun nuna farin cikin su k’arara kowa murna yake da san barka.
Farhan da Mubeenat ne zaune a mota inda yake tambayar ta “Kin gama had’a kayan ki na tafiyan mu?”
Tunowa tayi da irin shirin data ga Umma nayi mata hakan yasa tace dashi “Eh Umma ta min”
“Habibty ‘yar gatan Umma shirya kayanma sai da aka miki?”
Kallonsa tayi inda suka jefi junansu da murmushin farin ciki sannan suka wuce gida.+
Samira kuwa tun data bar gidan su Amal ta shiga yawo gurare daban-daban duk ta inda ta kutsa sai ayita nuna ta ana gulmarta akan ita ta yiwa k’awarta asiri tabar gidan ta kuma aure mijinta yanzu kuma asirinta ya tonu gashi tana d’auke da cutar k’anjamau,wani gurimma idan taje duka ake mata ko’a tofa mata yawu.
Shi kuwa Sagir aiki yake ta nema amma sam ya kasa samu dan muguntan da sukayi ya gama baza ko ina an sannu an kuma san halinsu shima dai daga k’arshe wasu ‘yan shaye-shaye yayiwa rashin kunya suka nad’a mishi shegen duka suka mishi rauni sosai ta inda ko taimakawa kansa ba zai iya yiba hakan yasa ya zauna a gefen masu bara shima yana yi.
Ranan dai ajalin Samira ya sauko inda wani mai machine ya bugeta ta fad’i koda aka d’agota gawarta kawai aka kwashe,shi kuwa mai mashi azumi sittin ya kama sa,Sagir ya samu labari haka akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya batare da tayi cikakken tuba ba. Wa’iyazubillah,yaku ‘yan’uwana mu kasance masu neman gafara agun Mahaliccinmu koda yaushe kuma koda muna ganin banuyi wani laifi ba,barema d’an Adam ajizine dole ne akwai kura-kurai da mukeyi a rashin sani ko a sane Allah ka yafemu baki d’aya.
Tun bayan rasuwar ta Sagir ya sake tsintar kanshi da maraici sosai,hakan yasa ya tuba, tuba ta hak’ik’a ya koma ga Allah yana ta istigifari a yanzu haka ya samu aikin kanikanci kuma da zuciya d’aya yake aiki dasu yana d’an samun na kashewa ba laifi.
Mubeenat dai a gidan su take sakamakon ba’a gama k’arasa ginin Farhan ba,kodai ince an gama gini amma akwai sauran aiyukan da ba’a gama ba.
Aurensu da kwana biyu suka wuce Madina har da Shureim kamar yadda Farhan yayi mishi alk’awari duk suka tafi tabar Amal da Aisha cikin kewa harma dasu Umma.
Isarsu aka zo tararsu kowa so yake yaga Mubeenat nan suka rufeta da murna sai yabata suke yi,ita kuwa murmushi kawai take musu tare dayi musu godiya cikin harcen turanci.
Motar su d’aya da Ummi,Shureim kuwa yana can gun su Farhan.
Suna isa Shureim sai kalle-kalle yake yi yazo inda bai tab’a zuwa ba,koda suka k’arasa ciki masu d’iban kayan su suka zo sai shiga da kayan suke suna taya Farhan Murna.
Ummi da kanta takai Mubeenat har gun wani k’ofa tana bud’ewa taga wani k’aton parlour ne tare da d’aki a ciki da komai, irin dai gidajen su na Madina gurin ya burge ta sosai gashi kana gani basai ance komai ba kasan gidan manya ka shigo.
“Habibty nan shine gefen ki kije ki watsa ruwa sai ku fito muci abinci kinji?”
“To Ummi nagode” ta fad’a da murna fal akan fuskarta.
Bayan Ummi ta tafi ne tare da janyo k’ofar Mubee ta tsaya k’arewa d’akin kallo yayi kyau matuk’a,a hankali take tafiya tana bin ko ina da kallo bud’e k’ofa taji anyi tare da cewa “Slm”
Juyowa tayi dan taga waye amma kafin ta k’arasa juyowa sai taji an rufe mata ido ta baya,k’amshin turarensa da taji ne yasa ta gano cewa Farhan ne dan haka ta wayance kamar bata san shi d’in bane ta fara magana a hankali cikin harcen turanci tana cewa “Waye ne,pls ka cire hannunka a fuskata matar aure ce ni sannan nan d’akin Ummi ta tabbatar min da cewa nawa ne ni kad’ai shiyasa ma bana expecting d’in wani”
Murmushi yayi mai sauti tare ta cire hannayensa daga fuskarta yana kallonta yana girgiza kai “Oh hakama kika ce,kina nufin zaki iya kwana ke kad’ai ne anan?”
Har da dagewar ta tace “Tome zai hana?”
“Alright then na barki lafiya” sannan ya juya zai fita tayi saurin janyo rigarsa ta baya tace “Amma ai zaka min hira tukunna zuwa daren sai ka tafi”
“Nak’i kawai kiyi zamanki ga TV sai ya taya ki hira” da shirin barin d’akin yayi runk’urin fita,ta sake janyo shi tare da rungume shi tana dariya “Haba Ya Farhan bayan kasan kai kad’ai na sani anan”
Dariyan yayi shima tare da rik’eta da kyau yace “Na farko dai ki sauke cemin wannan Ya Farhan d’in yanzu ni Mijin kine,bai dace ki kirani da Yayan kiba,shin akwai aure tsakanin Yaya da k’anwa?”
“To amma ai Ya Farhan…Shhhh ki bani amsa na tukun”
“A’a babu”
“Habibty duk matar auren da kika ji tana kiran Mijinta Yaya ko Daddy ko Babby to kiyi saurin dakatar dasu hakan bai halatta ba a musulunce,wannan shine abin da nake nufi”
Murmushi tayi tare da cewa “To ai da haka nayita kiran Ya Atif a baya”
“Na sani ai,na kuma gaya mishi kamar yadda na gaya miki,daga yau na sauk’e Yaya Farhan daga bakinki gara ma ki kirani da Sunana akan kice mun Yaya kinji?”
“Yes Sir! Naji”
“Hhh shima bana so,call me Habibi kamar yadda Ummi take cemun”
“Okay Habibi” ta fad’a cikin zolaya shi kuwa cak ya d’agata sai bed room nasu ya dire ta akan gado suna yiwa junansu dariya.
Bayan sunyi wanka sun shirya ne,ya rik’o hannunta har Babban parlour inda kowa ya hallaru su kad’ai ake jira dama.
Kunya sosai Mubeenat taji dan ganin su Ummi da Abbi a zaune gashi Farhan yak’i ya saki hannunta har suka k’arasa ya janyo kujera ta zauna sannan shima ya zauna kusa da ita yace da Abbi “Kuyi hak’uri Abbi”
Ummi ce tayi magana “Ba komai Habibi bisimillah” Mubeenat dai kanta a sunkuye dan kunya, bata jin zata ma iya cin abincin.
Ummi ce ta zuba musu Farhan ya fara ci ita kuwa kanta a sunkuye har yanzu,gashi ta b’ata musu lokaci kuma so take ta mik’e ta gudu d’aki amma kunya bazai barta ba,haka ta daure sai da Abbi yayi magana “Mubeenat ki saki jikinki kamar a gida kike kinji?”
“To” kawai shine abinda ta furta sai Farhan yace “Abbi kunya takeji dan kar su Abdullahi suga loman ta”
“Hhhh ita dai ba haka bane aita saba cin abinci damu har da Abdullahin ma sai dai ko sauran Abokanka da mutanen gidan ne” cewar Ummi.
Farhan ya sunkuyo da kansa kamar yadda tayi yana mata magana a hankali “Habibty kunya kike ji?” Saita d’aga mishi kai alaman “Eh”
“Please Habibty karki min haka,ki daure ko kad’an ne kici kinga fa duk mu suka zauna jira basu fara ciba”
K’afansa ta taka da k’arfi dan baza ta iya magana ba gani take kamar su Ummi zasu jita”
Farhan ya fahimce ta dan haka ya sake cewa “Idan baki d’aga kanki kinci ba zan d’aukeki in ajiyeki akan cinyana sannan na baki a baki”
Muryar Abdullahi sukaji yana cewa “Kodai zaku shiga k’asan daining d’inne in mik’a muku?”
Haba nan aka sa musu dariya harda Shureim inda Farhan yace “Kin gani ko,bari na d’agoki to” ba shiri ta d’ago da kai tana murmushi sannan Farhan d’inma ya d’ago yace wa Abdullahi “Wato Ahmad ya koya maka ko?”
“Wlh kamar kasan nayi missing d’in sa da yana nan daya tayani,amma tunda ga Shureim ai shikenan ko Shureim?”
Shureim ya d’aga kai alaman “Eh” yana yiwa Mubeenat dariya.
Farhan ya kalli Shureim yace “Ai haka zamuyi da kai ko Shureim?”
“Ya Farhan nifa bance komai ba,tambayata yayi kawai na bashi amsa”
Su Abbi suka sa dariya har da Mubeenat ma tayi murmushi tare da fara cin abincin a hankaki.
Abbi ya lura da cewa Mubeenat kunyarsu take ji a yanzu,dan haka da suka gama sai suka bar gurin shida Ummi,nan kuwa ta d’an sake duk da dai tana jin nauyin sauran ma amma dai ya ragu. A baki Farhan yake bata tana amsa daga baya tace ta k’oshi haka ya k’yale ta sannan yace da ita “Muje na kaiki d’aki to” ai kuwa da sauri ta mik’e yana rik’e da ita har d’aki,wani ajiyar zuciya ta sauke tare da ce mishi “Ni dai bazan sake fita cin abinci ba”
“Hhhh ban yarda ba Habibty,a haka zaki saba ai,dan tare muke cin abinci mu”
“Allah kuwa kunyan su Abbi nake ji,gashi kuma sai ka rik’eni kamar na zama Shureim?”
“To ai baki da maraba da Shureim d’in a yanzu” nan ta hau b’ata rai tana cewa “Wlh na fishi nifa babba ce gani har nayi aure”
Shi kuwa cewa yake “Baki girma ba sai randa kika haifa mun baby  amma yanzu kam you are just a kid to me” yayi maganar cikin zolaya, tanata fushi tare dayin shagwab’a tana rik’e da fuskarsa da hannayenta biyu tana girgiza mishi fuskar “Wlh bana so fa?”
“To ai ni ina so Habibty baby girl nawa” ya fad’a da zolaya suna dariya…Basu sake fitowa ba har bacci ya d’ebe su sai bayan la’asar suka tashi sukayi sallah sannan ya fita ita kuwa tana zaune tana kallo.
Bayan fitar sa da 1hour sai gashi ya dawo ya mik’e kusa da ita yana mata magana “Habibty ki shirya mu fita gurin taron da aka had’a mana”
“Taro kuma? Na me kenan?”
“Na tayamu murnan biki,dama gobe ya kamata ayi,amma Abbi yace ayi komai yau kawai muma a barmu mu huta gaba d’aya”
“Amma Habibi shine baka gaya mun ba sai yanzu?”
“To i’m sorry,idan kin watsa ruwa Nani na zata zo ta shirya ki”
“Ta shiryani kuma,ni dai zan shirya kaina”
“To ai baki san wani irin shiga zakiyi ba that why nace tazo ta shirya ki”
Shuru tayi sannan tayi murmushi “Okay then bari naje”
“Ok nima bari na shirya”
Bayan fitowar su ne ya shirya cikin wata farar kaya irin dai na pakistan,kallonsa ta tsaya yi domin ita dai kayan basu mata kyau ba ko kad’an.
“Habibi dasu zaka je taron?”
“Yes Habibty,kema kar kiyi make up haka nan zaki fita babu ado”
Mubeenat ta tsaya yin mamaki shi kuwa dariya yake mata tare da manna mata kiss ya fita ya kira Nanin sa.
Ai kuwa wasu kayane a hannunta kamar dai irin na jikin Farhan d’in,ba musu ta saka sannan ta yafa mata wani gyale wanda baima dace da kayan ba. Farhan dai dariya yake ta mata ganin dai shigar bai mata ba amma kuma sai tasa a ranta cewa may be haka sukeyi a al’adar su Amarya ta fita gaban taro da natural face d’in ta.
Nani tayi ta yaba ta haka dai suka fita bikin nasu gwanin sha’awa inda akai ta kid’a Farhan da ‘yan’uwan sa sunata rawa Mubeenat dai dariya take tayi ita da Shureim.
Bayan an gama ne suka zauna daga kan kujera yana kwance akan cinyarta sai hotuna ake watsa musu+
4
daga nan magrib yayi kowa ya watse aka had’owa Mubeenat goma na arziki kaya kala-kala ga gwalagwalai kyauta dai sosai tana ta mamaki.
Bayan anci abinci dare shima dai tana d’an kunya amma ta d’an sake ba kamar na rana ba,sannan kowa yayi musu ma’assalam suka wuce.
Tunda Mubee taji yace taje tayi alwala suyi sallah raka’a biyu tasan cewa yau akwai aiki dan tana da tsoro sosai gashi kuma suna tare dasu Ummi. Sumui-sumui ta wuce tayi alwala sukayi sallah tare da addu’oi Allah ya kare duk wata fitana da zata kunno ya had’asu da alkhairi dake cikin auren ya basu zuriya d’aiyiba ameen.
K’in tashi daga kan sallayan tayi ya lura da ita duk ta sauya ko had’a ido bata so suyi dan nauyin sa take ji sosai.
Zuwa yayi har inda take ya d’agota tsaye tare da rungumeta a jikin sa “Habibty me yake faruwa ne,ki saki jikinki muje mu kwanta kinji?”
Kanta kawai ta d’aga mishi sannan ta cire hijabin jikinta ta haura ta kwanta. Shima jallabiyan ya cire yabi bayanta tare da kashe wutar d’akin ya kuma yimin kashedi da cewa “Sad-Nas karki sake dawowa sai gobe da safe zan nemeki”
“To” nace dashi kawai,amma banji dad’i ba dan naso inga wannan daren yadda zata kasan ce.😉
Washe gari shuru Farhan bai nemoni ba har sai lokacin cin abinci naga ya fito,gaishe sa nayi ya amsa mun fuskarsa d’auke da wata irin murna dana dad’e ban gani ba. “Sad-Nas zaki iya biyoni yanzu” cikin sauri nabi bayan shi inda ya wuce gurin Nani yana gaya mata cewa “Nani kije gun Habibty please sannan ki kai mata abincin ta dan bazata fito ba”
“Ok Habibi i will do it right now” sannan ta had’a komai Farhan yana tsaye yana murmushi shi kad’ai harta gama bai ma sani ba sai data d’an tab’a hannunsa “Habibi i have been talking to you,are you okay?”
Murmushi yayi tare da shafar fuskarsa yace “Nani yau ina cikin farin ciki ne da ban tab’a tsintar kaina a ciki ba, i love Habibty so much Nani” ya fad’a tare da barin kichine d’in ya nufi gurin Ummin shi. Ita kanta Nani farin cikin takeyi saboda D’an d’akinta yana cikin farin ciki hakan yayi mata dad’i sosai da haka ta wuce Mubeenat na kwance ganin Nani sai ta d’an sunkuyar da kanta tare da gaishe ta,muryar Ummi suka jiyo itama gaisawa tazo suyi tare da ajiye wa Mubeenat wani girkin daban sannan ta fice,dan ko d’aga kai Mubeenat ta kasa yi dan kunyansu data ji.
Farhan kuwa zuwa yayi ya tallafo ta agaban Nani yake ta tarairayar ta tun tana jin kunya harta d’an sake dan Nanin bata da damuwa sam.
Bayan fitan Nani ne ta kalli Farhar tare da dukansa a k’irji cikin wasa tace “Kai baka jin kunyan su Ummi ne, wlh kamar in nitse nake ji”
“Hhh Habibty kici abincin sai ki kwanta ki huta dan naga kamar har yanzu a gajiye kike”
“Hmm zaka sani ai,na koreka yau ka barni in kwana ni d’aya tunda haka kake”
Dariya yakeyi sosai tare da cewa “Ai bazan iya ba kuma sai dai amin afuwa tunda ba laifi na bane”
Haka sukaita hira kuma rayuwarsu taci gaba da tafiya kulawa sosai yake bata shi da Iyayensa da kuma kowa nashi duk basu da matsala ko kad’an tarairayarta suke sosai harta saba dasu,dan yanzu tare suke cin abinci koda yaushe kuma bata aikin komai sai dai tayi wanka ta kwanta shima kuma yanzu Farhan duk ya d’auke mata ta zama kamar jaririya a gidan,Shureim ma yana jin dad’in hakan sosai dan cewa Mubeenat yayi shi kam a nema masa makaranta anan dan bazai koma Nigeria ba tana ta mishi dariya.
Watan su biyu a Madina soyayya sai dai muce masha Allah ga wani k’aunarta da Abbi da Ummi suke hakama Nani sun shak’u sosai,tana bata shawarwari akan wasu abubuwan daya shige mata duhu.
Wani rana suna cin abinci kamar yadda suka saba sai Mubee taji amai yazo mata take tasa hannunta a baki tana tari a hankali,Ummi da Farhan suka furta a tare “Sorry Habibty, are you okay?”
Cikin shak’ewa tace “I don’t know” sannan ta mik’e da sauri ta wuce d’aki dan amai data ji yazo mata,haka tayita yinsa a toilet Ummi da Farhan suka biyo ta suna mata sannu. Ganin aman yayi yawa ne yasa Ummi tace wa Farhan ya kira Family Doctor nasu,babu b’ata lokaci yazo Ummi tana rik’e da ita har parlour Doctor ya gama gwaje-gwaje tare da tambayar ta Farhan yana bashi amsa jininta ya d’iba a take ya gama komai yace a mai da ita d’aki ta huta,nan Ummi ta kaita d’aki ta rufe ta sannan ta fito inda Abbi yake tambayar Doctor miye matsalar,sai Doctor yake tabbatar musu da cewa karsu d’aga hankalin su Mubeenat tana d’auke da k’aramin ciki ne yana kuma taya su murna bayan wannan babu wata matsala.
Murna sosai sukayi musamman Ummi,Farhan ya raka Doctor har waje yana mishi tambayoyi akan cikin dan zumud’i.
Tun daga lokacin Ummi tace Mubeenat tayi zamanta a d’aki sannan duk abinda take so shi ake mata ko parlour sun hanata zuwa,wata rana harta gaji da zaman d’akin idan ta nemi Farhan ya kaita cikin gari domin suyi yawo,sam sai yak’i Ummi ma hanawa take wai jaririyarta batayi k’wariba Mubeenat dai ta zama sarauniya hankalinta kwance.
Amal da Aisha kullum cikin tsokanar ta suke tunda ta sanar dasu,Umma tayi murna sosai ganin ta kusa ta zama Kaka dan haka ta fara shirin tarar jikanta Abba ma murna yayi sosai dan Mubeenat tana gaya masa irin kulawa dasu da akeyi ita da Shureim.
   Wasa-wasa Watansu hud’u a madina cikin Mubeenat kuwa wata uku kenan,tana so suje Nigeri amma Abbi yak’i yace sai cikin yayi 4month haka kuwa akayi watansu biyar sannan suka dawo Nigeria,gida suka wuce duk da dai an gama musu gidan su tun tuni,Atif da Ahmad ne suka taro su inda yake ta tsokanar Mubeenat tana jin kunya.
Murna sosai Umma da Abba sukayi ganin yaransu sun dawo gashi sun canja sunyi kyau sunyi fresh,Aisha Amal dai ranan har dare kafin suka koma.
Washe gari Mubee suka koma gidan su yayi kyau sosai,Umma tace Farhan ya dinga zuwa kullum yana karb’a musu abinci. Nan Mubeenat ta sake zama ‘yar gata bata komai domin tana da mai aiki girki kuma Umma ce ke aiko musu ko Farhan d’in yaje ya d’auko.
Cikin mubee yana wata biyar Umman Amal ta haifi D’a Namiji murna sosai itama tayi dan bata da d’a Namiji,Malam Buba ma yayi murna,inda Abban Amal yace ya d’auke mishi nauyin komai kawai ya fad’i sunan yaron nan yayita godiya tare da sawa yaro sunan ABDULLAHI akayi suna masha Allah shima Malam Buban yazo inda aka tsaida magana idan ta yaye shi zaizo ya d’auki d’an amma zai dinga kawosa hutu,itama kuma zasu iya zuwa ganin sa. Tana yin arba’in aka d’aura auren Amal da Ahamad hidima sosai akayi,Abdullahi ma yazo daga Madina da wata uku aka sake d’aura na Aisha da Anwar lokacin Mubeenat da k’yar take iya komai sabo da yadda cikin ya girma dan har ta wuce watannin ta.
Ranan Alhamis ta tashi da ciwon baya,hakan yasa ta sanar da Umma da wuri suka wuce hospital cikin ikon Allah ta haifi ‘yarta mace. Dama ranan kuwa su Ummin Farhan suke hanya.
2
Bazan iya gaya muku farin cikin da ake ciki ba har da Atif,duk da dai a cikin ransa yana tuna yanzu fa da shine Mahaifin wannan kyakkyawar yarinyar da Sis Mubee ta haifa, “Allah kasa mufi k’arfin zuciyoyimmu ka shiryar da masu hali irin nawa” ya k’arasa maganar harda hawaye.
Anyi suna lafiya inda yarinya taci sunan Ummin Farhan ana kiran ta da Nihal.
Bayan sunyi arba’in ne Mubeenat ta karb’i girki suna wata biyu suka sake komawa Madina domin sauran ‘yan’uwa suga NIHAL.
Acan ma sabuwar soyayya suka sake sha dan Ummi ce ke lura da Nihal wai Mubeenat ta huta.
Suna madina sukaji labarin an mai da Auren Umman Amal da Abban Amal daga can suka suna farin cikin su inda Malam Buba yaje ya karb’i D’an sa ya tafi dashi.
Atif kuwa kullum a dana sanin abubuwan daya aikata yake,su Ahmad sun bashi shawaran ya nemi mace mai irin cutarsa suyi aure amma sam yak’i domin har gobe Sis Mubeenat ce a cikin ranshi dan haka bazai iya auran wata ba yana ga gara ya zauna a hakan kawai.
Watansu Mubee Uku suka dawo Nigeria Nihal ta girma masha Allah.
Mubeenat tama Ya Farhan Magana da aje a nemo wannan yarinyar data sawa Ya Atif cuta watak’ila zai aure ta,cikin ikon Allah kuwa sukaje su uku dashi Atif d’in da Ahmad,da yake sana’a sukeyi kuwa sai aka sameta amma tana tsananin ciwo dan abun yaci jikinta sosai basuma baro Abujan ba Allah yayi mata rasuwa da rabon dai zata nemi gafaran Atif d’in.
  Allahu Akbar dama idan Allah yaso bawansa da rahamarsa haka abun yake kasancewa Allah ka gafarta mana zunubbammu ameen.
Haka suka dawo tunani ya dawowa Atif sabo yana ta istinfari,Doctor da kansa ya had’a shi da wata yarinya k’arama itama wanine ya aureta ba tare daya sanar da ita yana da cuta ba,iyayen suka amince masa dayake sunga kud’i har sai bayan auren da wata biyar mijin ya rasu nanne aka gano yana da cutar kuma itama ta kamu,Atif bai soba amma dayake shi d’in mabuk’acin mata ne sai ya amince gudun karya koma rayuwarsa ta baya aka d’aura musu aure suna zaune lafiya gashi yarinyar tana k’aunar shi sosai shi kuwa bata gaban sa amma babu wulak’anci suna zaune k’alau.
Amal da Aisha ma cikine dasu suna fama da laulayi nanne Mubeenat take rama irin zolayar da suka mata.
Shureim kuwa ya girma ya gama secondary skul inda ake nema masa ci gaban karatun sa anan cikin Gomben,haka ratuwa taci gaba da tafiya musu da kuma ‘ya’yan su…
3
 
ALLAHMDULILLAH ANAN NA KAWO K’ASHEN WANNAN LITTAFIN NA #KNJ  KUSKUREN DANAYI ALLAH KA YAFE MUN.  ‘YAN’UWANA ALLAH YASA MUYI AIKI DA DARUSAN DAKE CIKIN LITTAFIN AMEEN…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *