KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 2
Murmushi atif ya tsayayi yayinda mubinat taketa faman juyi akan gado.
“Barkanki da farkawa gimbiyan mata”
Kunya sosai taji,dan gabad’aya tamance cewa ba’agidansu takeba yanzu. D’an murmushi tayi batare datace komaiba ta mik’e zuwa toilet. Byan fitowartane shima ya shiga yayi alwala yazo sukai sallah.
Abincin da umma takai musu hospital shiya d’auko musu yakawo sukaci tare sannan ya bata magungunanta tasha.
“Sis mubinat” yakira sunanta. “Na’am” ta furta tana kallonsa.
“Kizo ki zauna muyi magana” babu musu taje kusa dashi ta zauna tare da zuba mishi ido.
Fiskarsa cike da fara’a yace “inaso kigayamin abinda kike so da kuma wanda bakya so domin in kiyayesu musami zaman lfy atsakaninmu”
Ajiyar zuciya tayi sannan tace “indai kamin alk’awarin cewa bazaka nemi wani abu daga gareniba bayan wanda ka nema d’azu toshikenan babu wata matsala”
“Kina nufin babu tarayyan aure tsakanina dake kenan”?
Shuru tayi ta kasa amsamishi. “Sis mubi,idan dai kinaga hakan daidaine toba komai,nayi alk’awari bazan kusancekiba harse randa kika fara ganina amatsayin mijinki”
Manyan idanunta ta d’ago tana kallonsa cikin tausayi dajin kunya tace ” dan Allah kayi hak’uri ya atif,kad’anmin hak’uri har zuwa… shiii kidena damuwa sis mubi nafahimceki,kuma zan jira harse lokacin da kika fara sona amatsayin miji ba yaya ba. Janyota yayi zuwa jikinshi ya rungumeta yana shafar bayanta tare da rad’a mata cewa “ina so wannan maganar yazama sirri atsakanina dake,sannan inaso kisaki jikinki dani kidena kunyana sannan bazaki hanani hugging nakiba hakama kuma kiss,kin amince da wannan”? Kai ta d’aga masa alaman eh ta amince tare da murmushi a fiskanta.
Shima murmushin ya mayar mata tare da tsunbatan goshinta yana jin dad’in ganin yadda ta sake dashi ayanzu. Cikin zuciyarsa kuwa cewa yake “ya Allah ka karkato da zuciyar mubinat zuwa gareni,Allah ka bani ikon cikamata wannan alk’awari dana d’auka mata ameen”
Bayan sallan isha atif ya tafi gidansu domin karb’a musu abinci,bai jimaba dan dama ya sanar da mum nashi cewa tayi musu abinci.
Mubinat ta gama shirin bacci dan rigar bacci ne ajikinta amma bamai fitar da siffan jikintaba.
Jin k’aran motar atif ne yatabbatar mata da cewa ya dawo. Sallamarsa taji tare da shigowa ya bud’e mata hannayensa,cikin jin kunya ta mik’e taje ta shige jikinsa,shikuwa d’agata yayi sama tanata faman dariya tana cewa “pls ka saukeni ya atif nifa ba shureim bace” hhhh to ai da kad’an kika fishi,bazan saukekiba harse na kaiki kan daining. Dariya takeyi harya direta akan kujera,ita ta zuba musu abincin sukaci sannan tasha maganinta suka wuce d’akinta. Dama sunyi wanka dan haka brush kawai sukayi sannan suka kwanta cikin bargo d’aya kowa da tunanin da yakeyi cikin ransa.
Babu wani abu daya faru atsakaninsu illa kissing nata dayayi tare da mannata ajikinshi da haka sukai bacci.
Atif yana son kissing arayuwarsa,amma kuwa wannan alk’awari yada d’auka zai iya cikawa kenan?… hmmmm muje dai
Gari ya waye sukai sallah sannan suka koma bacci,cikin ikon Allah jikin mubinat yayi sauk’i sosai sedai muce Alhamdulillah…
Farhan kuwa yana can sararin samaniya inda jirginsu ta d’auki hanyarzuwa madina. Tafiya akeyi amma gabad’aya seyaji dama baiyi tfyanba,ya gwammaci yana nigeria koda lbrntane yadinga ji.
Koda suka isa bro nashi mai suna Abdullahi da kuma sauran ‘yan’uwansa maza biyu sukaje tararsa a airpot. Sunyi farincikin ganisa matuk’a tare da murnan memorinsa ya dawo normal yanzu babu wata matsala atattare dashi.
Cikin harshen larabci suketa magana sun rugumesa,murmushi yakeyi dan shima yayi kewarsu sosai. Haka suka d’au hanyar gida yayinda abdullahi yake jan motar.
Wata balarabiya ce kyakkyawar gaske ta fito sanye da doguwar riga irin tasu,ga wani murmushi na farin ciki da takeyi. Farhan naji ya furta “Ummi” tare da wani kalamai dayayi cikin harshe larabci suka rungume junansu tana kwalla tare da cewa “Alhamdulillah habibi” sauran kalaman nata dai cikin yarensune wato larabci,amma zaka iya fahimtar abinda take cewa dan yadda take kuka tare da furta sunan mubinat abakinta.
Hannunsa ta rik’o yana kwalla suka shige cikin gida wanda base na gayamuku irin tsarinsaba.
D’akinsa ya nufa ya watsa ruwa sannan ya fito aka zauna jera masa abinci kala kala amma kad’an yaci sannan aka shiga hira.
Dukdai hirar tasu akan mubinat ce,dan mahaifiyar tasa se hawaye takeyi tana rarrashinsa kamar sabon jariri. Koda yake dama larabawa akwai iya nunawa yaransu k’auna fiye da mazajensuma.
Fararen matane biyu suka shigo tare da rungume farhan suna magana cikin harcensu na larabci. Shi kuwa farhan murmushi yad’anyi ba laifi sannan suka zauna kusa dashi anata faman hira…
Mubinat ne zaune da amal da aisha se kuma shureim a palo suna hira. Amal tace “seku tashi mutafi ai tunda naga jikin nata da sauk’i”
“Nidai ba yanzu zan komaba” cewar shureim.
Amal tace “to aisha tashi mutafi dan wlh banso ya atif yadawo ya samemu” mik’ewa aisha tayi tace “to mubinat Allah ya sauwak’a se kuma kin sake ganinmu”
“Dan Allah kudinga zuwa kullum muna hira pls”
Amal tace “to shikenan semunzo gobe amarya mai magarnar sugar”. Tafawa sukayi ita da aisha suna mata dariya sannan aisha tace “yanzu shikenan mukuma semuyita yawon zuwa gidanki dan bamu da gurin zuwa,ai wlh kafin ki sake ganin k’afarmu agidannan zai dad’e”
Kallonsu mubinat ta tsayayi tare da harara “hakama zakucemin ko”?
“Mayar da wuk’an aminiyata,kinsan koda aisha zatak’i zuwa tofa nikam zaki ganni wlh” murmushi mubinat tayi tace tona gode kugaidasu umma. “Tashi mutafi shureim” cewar aisha.
“A’a wlh kubarshi idan ya atif yazo zaimaidashi” inji mubinat. To ai shikenan suka had’a baki,tare da zuwa gun motarsu inda driver’n su aisha yake jiransu.
Bayan tfyarsune shureim yakeyiwa sis mubinat hira yana cewa “sis mubi ya farhan ma bayida lfy d’azu abbansa yakegayawa abba wai ciwon kai yakeyi sosai”Kuma dama yace min in kawo masa hotunanki,guda biyar ya d’auka acikin kits nashi yacemin idan kina kuka indinga share miki hawaye sannan ince miki ki zauna da ya atif da zuciya d’aya kuma kiyi masa biyayya dan bayaso kizama d’aya daga cikin wanda ake azabtarwa ranan gobe.”
Tunda shureim ya fara magana mubinat take zubar da kwalla harya gama. Hannunsa ta kamo tace “yaushe ya gaya maka wad’annan maganganun?”
“Jiya da dare daya kira wayar umma shine yace abani mugaisa”
Ajiyar zuciya tayi tace “nagode shureim,kace mishi naji sak’onshi” hon d’in motar atif suka jiyo,da sauri ta goge kwallanta dan bata so yasan tayi kuka. Shureim ya fita da sauri yace “dama kainake jira kamaidani gida”
“Amma ai zaka bari inshiga in sanar da sis mubinat tunda bataga shigowanaba”
“To barina tayaka shigar da kayan kafin ka fito”
Kansa atif ya shafa yace “yawwa tona gode” sannan ya wuce da ledan hannunsa ciki.
Sayayyan drinks ne sosai atif yayi dakuma abinda basu dashi. Tas shureim ya shigar zuwa store sannan ya dawo palo ya zauna yana jiran atif.
Rungume yake da ita yace”bari in maida shureim kar dare yayi kina son wani abune”?
“A’a seka dawo”
“Are you sure”?
“Uhm”
“Ok tose na dawo” tare da manna mata kiss a lips nata sunayiwa juna murmushi yafita.
Bayan ta tabbatar da sun tafine ta bud’e wayanta da suka taho mata dashi tana kallon hotunan ya farhan habibinta. Musaman wanda yake bata hak’uri lokacin da shureim ya goge mata komai na wayanta tace seta dakeshi,hakan yasan farhan had’a hannayensa guri d’aya yana bata hak’uri akan karta dasheshi sanye da bak’in shets ajikinsa. Ganin yayi mata kyaune alokacin yasa tayi mishi wannan hoton.
Koda ta dawo daga duniyar tunani seta sake fashewa da kuka tana cewa “Allah yabaka lfy ya farhan…”Bayan Atif ya dawone yake gayawa Mubinat cewa ta shirya dan gobe zasu wuce abuja. Marairaicewa tayi tace “gobe kuma,mezamuje muyi acan d’in?”
“Hutawa mana sis mubinat,kinsan fa ni angone ina so muje yawone kinji?”
Kallonsa tayi cikin shagwab’a “pls mubari se wani sati kagafa ko gurinsu mum bamujeba kuma ina so ind’an k’ara samun lfy kafin muyi tfy pls Ya atif.”
Ganin yadda take mishi shagwab’ane yasa ya amince da cewa “Ok naji,but wani satin bazan sake k’arb’an wani escuse nakiba agree?”
“Yes no”
“Hhhh” yayi dariya tare da rungumeta yace you don’t stard ba?”
“Hahah nop I’m just kidding you” tare da rungumesa tana tuna farhan…
Haka dai rayuwarsu taci gaba da kasancewa babu wani damuwa. Alk’awarinsu yananan kamar dai yadda suka amincewa junansu.
Ta hakanne mubinat take moransa sosai,ga wani sabon k’aunarta dayake shigansa fiye dana da.
Aduk lokacin data buk’aci yin magana da Ya farhan Sam baya Janata,hakan yasa tasake dashi sosai dama kuma can akwai k’auna atsakaninsu.
Duk cikin yayyunta tafi son Ya atif kodon gida d’aya suke zama oho.
Yanzu kam da kanta take musu girki kala kala masu dad’i,daga ita harshi sun fara kyan gani dan hankalinsu akwance yake.
Ta b’angaren farhan kuwa sauk’in shine mahaifiyarsa,yana matuk’ar son mahaifiyar saboda k’auna da take nuna masa. Cikin ikon Allah ya fara samun sauk’i,amma k’aunar da yakeyiwa Sis mubinat yananan acikin zuciyarsa wanda shikam se’a hankali zai fita.
Ganin kamar ya fara mancewa da itane yasa wan mahaifiyarsa yayi masa magana akan wata yarinya acan d’in kozai aureta.
“Farhan baya iya b’oye abu kokuma wani nuk’u-nuk’u,dan haka ya gayawa uncle nasa cewa gaskya hakan bazaiyuba amishi hak’uri.”
Tun daga wannan rana babu wanda yasake mishi magana akan aure…
Can gida Nigeria kuwa su Atif yau suke hangar tafiya abuja.
Dake flight sukabi basu sha wahalan hanyaba. Abokansa dake canne d’aya daga cikinsu wato Nazir,shiyaje ya d’aukosu yakaisu d’aya daga cikin gidajensa da babu kowa aciki yakaisu.
Shidai Nazir sana’an gidaje yakeyi da kuma bada haya,dan shinema ya hana Atif sauka a hotel.
Gidane flat hud’u acikinsa,ukun da mutane aciki,d’ayan kuma babu kowa dama sabbin gidajene. Atif yace tofa guy ka kama k’asafa,murmushi yayi tare da cewa “aiban kaikaba ango suna dariya tare da shigewa ciki.
Komai dai Sabone aciki, kuma awadace 2bedroom ne se parlour da raining dakuma kichine.
Nazir bai zaunaba yace”barinaje gida zamu taho da sweetheart dan girki na musamman tayi muku wlh.”
Bayan tafiyarsane Atif ya shiga musu da kayansu sannan ya rik’o hannunta tare da fiskantarta yace “gurin ya miki,kodai mutafi hotel?”
Murmushi cike da fiskanta tace “yayi,kuma kaga ga mutane agidan zan samu k’awayen hira.”
“Are you sure’bana so kitakura jus tell me the truth” yana shafar firkarta
“I’m serious wlh nan d’in yayi thankyou, ta rungumesa”
Dad’in hakan yaji ya d’agata sama zuwa d’akinsu tana dariya. Akan gado ya direta sannan tace bari nayi wanka,murmushi yayi yace to idan kin fito Nima sena shiga.
Nazir ne da matarsa da kuma ‘yarsu d’aya mai suna Kismat. Idan ka gansu atare dole su burgeka,ga kyakkyawar babynsu kismat ‘yar kimanin shekaru biyar.
Hira sosai sukayi cikin hara dajin dad’i har 3:00pm kafin sukai sallama suka tafi.
Bayan isha Nazir da abokinsa sukazo da Mota biyu,d’ayan sun kawowa Atif ne dan zaga gari shida Mubinat sannan suka koma a d’ayan.
Haka sukaci gabada zama a abuja har tsawon sati d’aya,sunyi yawo sosai ga kuma matan abokan Atif Sunada kirki sosai. Hakan yasa suka shak’u kamar sunyi shekaru tare.
Suma matan da suke zaune a gida d’aya da mubinat d’in suna da kirki sosai ba laifi,Soyayya sosai sukeyi da mazajensu Dan dukkansu amarene.
Hakan yasa wani lokaci Atif yake sa damuwa aransa. Dan wani soyayyanma agabansu akeyi akan idanunsu wanda hakan baisa ya karya alk’awarin dayayiwa mubinat ba,sedai wani lokaci yana tsintar kanshi cikin tunani ko kuma ince damuwa.
Wata rana mubinat tayi wanka cikin english wears riga da wando,rigar hannu d’ayane kawai gata ja. Kyau sosai tayi yayinda tayi parking gashinta a tsakiyar kai.
Tunda Atif yadawo idanunsa na kanta ya kasa d’auke kai,ahankali yabita kichine inda take yanka musu fruit tana wak’an *Umar m sharif* abakinta.
West nata ya rik’o yayinda ta razana sosai dan batasan yashigo kichine d’inba. Bayan ya juyo da itane suna kallon junansu wanda hakan yasa taji tsoronsa dan duk kamanninsa ya sauya idanunsa sun k’ank’ance
Magana yake cikin murya mai kashe jiki yanacewa
“You look beautiful in this dress”
Cikin rawan murya tace “thanks”
“What’s is going on sis mubinat,I won’t do anything I promise okay”
“Silent”
“Why are you quite, say something”
“Please stop it Ya atif” ta furta daidai lokacin da yake neman wuce gona da iri.
Mubinat bataga alaman zai bariba dan haka ta tureshi gefe da k’arfi tana hawaye “pls stop it”
Ajiyar zuciya ya sauk’e amma sam baiji dad’in hakanba acikin ranshi, baice da ita komaiba yabar kichine d’in. Da Sauri ta biyo bayanshi danta lura da yanayinsa na rashin jin dad’in abinda tayi mishi. Yana zaune a parlour rufe da idanunsa ta k’arasa gurin ta zauna kusa dashi tare da sunkuyar da kanta k’asa tace “i’m sorry”
“Silent”
Kanta ta d’ago tana kallonsa cikin nadama ta sake cewa “Ya atif i’m sorry please”tare da rik’o yatsun hannunsa tana wasa dasu.
Hannunsa ya janye tare da mik’ewa ya wuce d’aki batare dayace mata komaiba. Jiki sanyaye tabi bayanshi tana zubar da kwalla.
Kayan jikinsa yake cirewa,gabansa taje ta tsaya tana share kwalla sannan ta sake cewa “Ya atif i’m sorry tsorone ya kamani shiyasa nayi haka…”Tsoro fa kikace,wani irin tsoro kenan sis mubunat,i am your husband yakama kisa hakan aranki kidena guduna pls it’s really hurt can’t you understand!”
“And ki duba irin shigar da kikayi yanzu,kuma kina expecting inyi ignoring d’inki?”
“Kina ganin kinmin adallaci kenan sis mubinat?”
“Nifa mutum ne d’an Adam mai lafiya ajikinshi kika kafa min dokanki nakuma amince miki amma kuma shine zaki tayarmin da hankali kuma kice zan iya jurewa kinaga bakiso kanki sosaiba sis mubinat?”
Tunda ya fara magana take kuka dan yadda taga ranshi ya b’aci yana magana cikin fushi harse daya gama sannan tace “kayi hak’uri dan Allah bazan sakeba” kota kanta baibiba ya wuce d’ayan d’akin ya kwanta abinsa rai ab’ace.
Koda mubinat tabi bayansa amma setaji k’ofar arufe. Bugawa take tana cewa “pls open the door Ya atif I don’t mean to hurt you wlh bazan sakeba pls karkayi fushi dani.”
“Ya atif please open the door”
“Just leave me along sis mubi”
“Please stop saying that, hakan yana nufin kayi fushi danine kenan?”
“Banyi fushiba kawai ina son kasancewa ni kad’aine”
“Dan Allah karkamin haka Ya atif kazo muje mu kwanta,kasan kariga daka sabar min yin bacci tare dakai i’m sorry please…
Atif yana jiyo kukanta da kuma kalamanta amma sam yak’i bud’ewa saboda abinda tamishi yamishi zafi sosai. Yana matsayin mijinta amma babu hali yayi wani abu,atunaninsa Mubinat ta fara sakewa dashi ya d’auka zai sami damar kusantarta ayanzu amma ashe sam ba yadda yake tunanibane.
“Me take nufi kenan wai,mema nayi mata ayanzun dahar zatace ta tsorata dani?”
Shikad’i yake zancen zuci batare daya furta komai afili ba. Muryarta ya jiyo tana cewa “Haba ya Atif dan Allah ka bud’emin”
“Sis Mubinat kije ki kwanta ina buk’atan kad’aicewa ni d’ayane a halin yanzu”
“Please Ya Atif kayi hak’uri kaji?”
“Naji kije kicire kayan jikinki kisa wani ina zuwa”
Bamusu ta wuce taje tasa kayan bacci wanda baya nuna komai na jikinta sannan ta zauna akan gado tana jiran zuwansa. Wayantane ya soma ringing,tana share k’walla ta d’auka da sauri ganin Ya Farhanne ke kiranta.
“Assalamu alaikum” ta furta cikin muryan kukan.
“Wa’alaikumus salam sis Mubinat lfy naji muryanki wani iri haka?”
Dai-daita kanta tayi sannan tace “lafiya k’alau yasu Ummi da Abdullahi?”
“They are all fine,how is Atif?”
Nanne ta fashe da kuka ta kasa cewa komai se kuka. Hankalin Farhan ya tashi yayi magana cikin sanyin murya “Sis Mubinat are you okay?”
“Yes i’m fine”
“Then why are you craying?”
“Ya Atif ne” dai-dai nan Atif ya bud’e kofar ya nufo k’ofarta,jin abinda Mubinat take cewane yasa ya tsaya sauraro. Taci gabada cewa Farhan “Ya atif ne yake fushi dani dan Allah kabashi hak’uri Ya Farhan banaso Allah yayi fushi dani acikin wannan daren.”
Shuru Farhan yayi yana nazarin kalamanta sannan yace “Shikenan kishare hawayenki kidena kuka pls,i will talk to him kinji?”
“Thankyou Ya Farhan,i’m missing you so much…”
“Shhhhh,komai zai dai-daita kidena damuwa please.”
Koda Farhan ya ajiye wayan seyaji ba dad’i aransa yadda yaji tana kuka sannan ya tuna da kalamanta na k’arshe datake cewa “i’m missing you so much Ya Farhan.”
Tashi yayi zaune ya rasa meke mishi dad’i, wayansa ya d’auka ya kira number’n Atif amma akashe. Runtse idanunsa yayi yana zancen zuci
“Tome yake faruwa tsakaninsu,duk yadda akayi akwai wani abu” number’n Atif ya sake kira karo na biyu kuwa seya shiga, “Alhamdulillah” ya furta tare da jiran Atif ya d’auka.
Shikuwa Atif tuni ya koma can d’akin ya kunna wayansa,ganin kiran Farhan ne seya d’auka,dan yasan idan ya sanar da Farhan abinda yake faruwa tofa lallai zaiyiwa Mubina nasiha akan hakan sosai,dan haka ya d’auka tare da cewa “hello”
Bayan sun gaisane Farhan yake tambayarsa meke faruwa tsakaninka da Sis Mubinat dantacemin kana fushi da ita pls inyi maka magana kayi hak’uri.”
“Karka damu komai ya wuce insha Allah,mund’an samu sab’anine but komai ya dai-daita nagode.”
Farhan yayi shuru nad’an wani lokaci sannan yace “toshikenan Allah yabaku zaman lafiya da kuma hak’uri da juna”
“Ameen” cewar Atif sannan sukai sallama.
Komeyasa Atif ya fasa gayawa Farhan abinda ke faruwa oho…
Tana kwance yayi sallama,zunb’ur ta tashi zaune tana kallonsa. Kusa da ita ya zauna tare da janyota jikinsa yace”Wato shine kika fad’awa Farhan ko?”
“Hakan shikad’aine mafita agareni Ya Atif,amma kayi hak’uri bazan sakeba”
“Hakan ya nuna duk lokacin da muka samu sab’ani zaki gaya mishi kenan?”
“Bazan sakeba” ta fad’a kanta asunkuye.
Hannunsa yasa yarik’o fiskarta sannan yace “Please karki sake gayamishi komai a zamantakewarmu dake kinji?”
“Ban tab’a gayamishi komaiba se yau,insha Allah bazan sakeba”
Murmushi yayi yace “promise?”
Kai ta d’aga mishi tana murmushi tace “yes”
Rungumeta yayi yace “i’m sorry dasaki kuka danayi yanzu”
Yatsanta tasa akan lips nashi “shhh, kadena bani kak’uri aikai zanba hak’uri nima bazan sakeba”
Dad’i yaji sosai dan sam Mubinat bata da girmankai indai wajen baiwa mutum hak’urine. Bakaman wasu matanba,dasuke ganin baiwa miji hak’uri asarace atasu fahimtar na jahilci dan wannan jahilcine babba wlh,Allah ya shiryar damu yasa mu gyara ameen…
Haka sukaci gaba da zamansu babu wani matsala dasuke samu. Sedai har yau babu wani abu na auratayya daya shiga tsakaninsu. Kuma ayanzu ita kanta Mubinat tana son tasan menene dad’in auren amma kuma tsorone cike aranta, domin suna hira sosai da mak’waptanta akan mazajensu.
Hakan yasa tabawa Atif daman wasada jikinta koda zata dena jin tsoronsa. Dad’in hakan yaji sosai tun wani rana datace mishi k’irjinta yana ciwo, tambayarta yayi ta ina kikejin ciwon?
Hannunsa takai dai-dai tsakiyar bubs nata tana yawo dashi tare da cemishi “kaga daga nan har nan har tananma duk ciwo yakemin” yayinda take yawo da hannayensa akan bubs nata.
Gogan naku aise ya rikice yana lumshe idanu tare da cewa “sorry” yana matsesu ahankali.
Ita kanta taji dad’in hakan sosai dan lumshe idanunta tayi tana jin yadda yake mata.
Tunfa wannan ranan yasamu daman wasa da k’irjinta cikin sauk’i,azuciyarsa kuwa cewa yayi “saura can…”
_Hmmmm! Mekuke hangowane readers? Muje zuwa dai_
Wasa-wasa su Atif watansu guda kenan a abuja,aurensu kuwa wata d’aya da sati d’aya kenan.
Dukkansu sunji dad’in zamansu a abuja sosai,amma Mubinat tana kewar gida sosai. Gashi Atif yace sesun k’ara sati biyu kafin su koma,hakan yasa ta hak’ura ta amince masa.
Ana sauran sati d’aya su koma Atif suka fita da wani abokinsa mai suna Hamza wanda bayi da aure.
Bayan sun gama zaga garine yace da Atif muje club mana. Atif yace “wato kai har yanzu baka shiryuba ko? Nidai nabar muku gaskiya kuyita fama.”
“Hhhh muje to ka rakani ba jimawa zanyiba wlh” cewar Hamza. Atif baice komaiba suka d’auki hanyan club,tunkafin su isa ‘yanmata suke layi akan titi kowacce da irin adonta. Daga nesa kake hango surarsu mai d’auke hankali dan akwai kyawawa sosai gasu farare tas.
Atif se binsu da kallo yake d’aya bayan d’aya,yana k’yallara idonsa akan wata yace “kai kaga wata anan” hhhh hamza yayi dariya “komu tsayane?”
Tsaki Atif yayi yace “wannan aiseku dabaku da mata.”
Parking hamza yayi yace “toka jirani acikin mota ango,bazan wuce 30minit ba shap-shap zanyi infito dan already tana jirana acikine.”
Kai Atif ya d’aga mishi sannan ya wuce ciki,shikuwa Atif yana zaune acikin mota.
Kyakkyawar yarinyace fara k’irjinnan nata abud’e gasu aciccike tana tsaye ajikin motan tana bugawa ahankali.
Atif ya sauke glass tare da cewa “ya dai?”
Marairaicewa tayi tace “kud’inane sukai short kuma gashi dare yayi please can you help me?”
Hannu yasa a aljihunsa yaciro 2k yamik’a mata batare dayace komaiba.
Ganin bayida niyan kulatane yasa ta sake matsowa dab da motar sannan ta k’arb’i kud’in da hannunta biyu tareda rik’e hannusa ta shafashi akan bubs nata.
Atake Atif ya rikice yakai idonsa gunda hannunsa yake aiseya lumshe ido. Ita kuwa ganin halinda yake cikine yasa ta zura hannunta tacikin glass d’in zuwa kan wandosa…
😔Allah ya dad’a karemana mazajenmu ameen…..