KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 4

 KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 4

    Duk da cewa sun mishi rauni a bayan kunnen sa wanda har jini yana fitowa, amma hakan baisa ya karaya ba, d’aya bayan d’aya yake fad’a dasu harya gama dasu ko kuma ince sukayi guduwan ceton rayukan su.

Shidai babban nasu yak’i guduwa suna ta fama shida Mubinat. Farhan kuwa ya dira a kansa sannan ya janyo shi har zuwa tsakiyar gurin yana tambayar sa “Waya turo ku,me tayi muku da har zaku je gidanta ku d’auketa? Ina kuka kai mata kayanta!”

Shuru yayi ya kasa amsa tambayan Farhan saboda mummunan kamu da Farhan yayi masa.

“Kayi hak’uri wlh kayanta mun riga damun k’ona su,sannan wlh babu wanda ya turo mu,bayani datayi ne ranan akan mata shine muka had’a kai akan mu sato ta domin kowan nen mu ya tab’a yaji…Farhan bai bari ya k’arasa ba,ya had’e hannayen sa guri d’aya ya murd’e su sannan yace “Ku tab’ata kuji me? Lallai zaka san ka tab’o wa kanka wahala a rayuwar ka.” Wayar sa yasa a kunne “Hello Ahmad,ok ina fitowa. Yana gama wayan ya kamoshi, shi kuwa se hak’uri yake baiwa Farhan yanata magiya,amma sam Farhan bai saurare saba ya fita dashi ya damk’a shi agun su Ahmad. Tun daga gun su Ahmad suke cin Ubansa sannan suka sashi a motarsu sukayi gaba dashi bayan sunyi magana da Ahmad a sirrance, sannan Farhan d’in ya koma ciki amma da baya ya shiga, dan baya so ya sake ganin Sis Mubinat a halin da take ciki babu sutura.+

“Ita kuwa Sis Mubee tana kwance babu wani abu da zata iyayi dole se’an taimaka mata.”

“Farhan ya gama bin gurin da kallo amma sam babu alamun kayanta agun,sannan babu komai agun wanda zai rufe mata jikin ta dashi.

Hakan yasa ya cire wandon suite dake jikinsa da kuma shirt d’in cikin farin, yana takowa dabaya-dabaya harya iso inda take sannan ya durk’usa yakai hannun sa dai-dai saitin bakinta ya b’are salatep d’in da suka manna mata sannan yayi k’ok’ari ya kunce mata hannu d’ayan yace “Kiyi hak’uri kisa wad’an nan kayan nawa mutafi gida, saboda babu wani abu anan da zaki saka,wannan shine kawai abinda zan iya baki .”

   “Kukane mai k’arfi yazo mata,amma yanzu ba lokacin kuka bane, hakan yasa tayi k’ok’ari ta kunce d’aya hannun sannan ta kunce k’afafun tayi saurin d’aukan rigan nashi ta rufe k’irjinta,sannan tayi sauri tasa k’afarta cikin wandon nashi,inda shi kuwa yake k’ok’arin mik’ewa yabar gurin sega Atif ya shigo a gigice yana fad’i “Sis Mubee”

“Subhanalillahi,me nake gani haka?”

Da sauri ta mik’e tsaye tare da jan wandon sama sosai dan ya mata tsawo sosai sannan tasa rigan.

Da gudu Atif ya k’araso inda take ya rungume ta, ita kuwa kuka sosai takeyi gashin kanta duk k’asa gashi ta had’a zufa se kuka takeyi sosai.

“I’m sorry Sis Mubi,Meya faru? Me suka miki,ina fatan basu miki komai ba? Yi magana mana,ina kayan ki?” Duk Atif ne yake jero mata tambayoyin nan. Gefe ta hankad’a shi cikin b’acin rai take magana “Su waye wad’annan mutanen Ya Atif,me kuma alak’arka dasu,me yake faruwa a tsakanin ku,dan wlh ban yarda dakai ba kawai ka gayamin gaskiya,me yasa suke son yimin fyad’e Ya Atif ka sanar dani gaskiya!

Cikin rud’ewa Atif yake bayani “Haba Sis Mubi,me yasa kike tuhu mata haka,wlh bansan suba ban kuma san komai game dasu ba wlh…Kamin shuru Ya Atif,wlh ban yarda dakai ba,su waye suke kiranka a waya tunba yauba kake k’in d’auka,yauma kafin ka fita sun kiraka kuma baka d’auka ba,wlh bazan koma gidan kaba harse ka gayamin gaski.” Tana kaiwa nan tasa kuka mai k’arfi tayi waje da gudu.

Farhan dake tsaye agun tun d’azu ya basu baya yana sauraran duk abinda sukeyi,wanda shi kanshi tunanin da yakeyi kenan.

Atif ya juyo se yaga Farhan tsaye daga shi se rigan suite da gajeren wando. Haushi ne ya sake tokararsa a zuciyar sa, kuma ya tuna da yadda yazo ya sami Mubinat ba kaya a jikinta sannan Farhan yana sunkuye a kusa da ita.

Muryan Abba sukaji yace  “Farhan?” Da sauri suka juyo a tare suna kallonshi.

Farhan zaiyi magana kenan Atif yakai mishi duka yana cewa “Dama kaine ka d’auke min mata? Awani dalili kenan, Abba kagani ko,kadai gani da idonka har yunk’urin fyad’e yake da niyan mata,duk shi ya had’a wannan shirin tunda shi kad’ai yazo nan kuma ace ya kasa kama koda mutum d’aya?”

Mubinat dake jikin Abbanta cikin kuka tace “Haba Ya Atif,me kake cewa ne,yanzu kaida kanka kake fad’in hakan akan Ya Farhan?

  Abba ne yace “Dukku dakata,wai me yake faruwa ne Farhan?”

Atif yayi saurin cewa Abba har kana tambayar sa? Babu kaya ajikin Sis Mubee nazo na sameta kuma yana kusa da ita, sannan abba kalli jikinshi dagashi se gajeren wando da rigannan fa,me kayanshi yakeyi a jikinta Abba? Wlh ban yarda da Farhan ba!

“Tasss” kakejin sauk’ar mari da Farhan ya sakewa Atif a fiskar shi.  “Ka gyara kalaman ka Atif, ka gaya min duk abinda kake so amma banda ambatona a matsayin fasik’i domin ni bazan tab’a zamowa kaiba ka gane ko?”

A fusace Atif ya nufo shi yana cewa “Yau kaine ka mareni Farhan? Lallai bakasan me kake yiba,ai take guri ya kaure da fad’an jarumai biyu. Da kyar Abba da Sis Mubee suka raba. Rungume Atif tayi tana cewa dan Allah ka bari Ya Atif kazo mu tafi, “No, sena koya mishi hankali wlh” waya ya ciro ya kira Police cikin ‘yan dak’ik’ai suka iso, ran Farhan ya gama b’aci sosai.

Abba kuwa mamaki yakeyi ya kuma rasa mema zaiyi awannan lokacin,shi kuwa Atif magana yake ba sassauci yace lallai atafi da Farhan. Hannu Farhan ya mik’awa police take suka sashi a gaba.

  Kuka sosai Mubinat takeyi tana cewa “Ya Atif wlh bayi da laifin komai ka saurare ni pls.”

   Bin Farhan takeyi da gudu ta durk’usa a gabansa tana cewa “Pls Ya Farhan kayi bayani,wlh Abba Ya farhan cetona yazo yi…..

Farhan yace “Hakane abinda Atif yafad’a shine dai-dai.

  Ido ta zaro tace “Me nakeji a bakinka Ya Farhan? Dan Allah ka gaya musu gaskiya wlh cetona yazoyi Abba kafi kowa sanin halin Ya Farhan bazai tab’a aikata abinda Ya Atif yake fad’a ba kuskure aka samu.

Farhan yace “Abba kayi hakuri, zuciya ce ta d’ibeni harna biyewa Atif mukayi abinda nake dana sani…”Kai karka raina min hankali fa, tunba yau ba ina ganin duk wani abu da kake yiwa Sis Mubee…Farhan bai bari Atif ya gama magana ba ya bashi amsa cikin b’acin rai da d’aga murya “Kai Atif na aikata hakan se me?!

“Ku tafi dashi nace!”

Inji Atif, take suka wuce dashi, dai-dai k’ofar fita yace “Sis Mubee key d’in mota yana aljihun wandon ki,nabar Shureim da Musa Almajiri a cikin mota karku manta dasu” yana kaiwa nan yaci gaba da tafiya.

  Durk’ushewa Mubeenat tayi a k’asa tana rusa kuka kamar ranta zai fita tana kiran “Ya Farhaaannn, Ya Atif wlh bayi da laifin komai,Abba dan Allah ka dakatar dasu baimin komaiba fa wlh shine wanda ya fara zuwa domin cetona,da bai zoba da sun lalata min rayuwa ta. Abba dubi bayan kunnen sa jini ne yake fitowa sakamakon sanda da suka buga mishi a lokacin da yake fad’a dasu, kuma babu kayana anan saboda k’onawa sukayi hakan yasa Ya Farhan cire kayan jikinsa ya bani domin babu wani abu anan dazan suturce jikina dashi, lokacin daya tsuguna ya bani kayan a lokacin ne Ya Atif ya shigo shine yayi zargin wani abu daban. Wlh bazan koma gidan kaba Ya Atif muddin aka tafi dashi! A guje ta fita waje tana kuka yayin da Atif yabi bayanta da dugu. Abba ne yayiwa Police d’in magana suka sake Ya Farhan inda Abba yaketa bashi hak’uri…k’arar taka birkin mota suka jiyo mai rikitarwa,da gudu Farhan ya wuce Abba zuwa waje. Mubinat ce ke gudu a tsakiyan titi Atif yana biye da ita, k’atuwar mota ce a gaban ta irin masu d’iban yashin nan. Dai-dai nan su Ahmad suka iso kowa “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” yake furtawa, dai-dai inda Atif yayi saurin capke tane shi kuwa Farhan ya gama rud’ewa kawai se yace “Habibty nooo” wanda yayi dai-dai da kamota da Atif yayi suka fad’a gefen titi mai motan yana ta faman zagin su.

Ganin Allah ya kare ne yasa kowa yin hamdala aka maida kallon kuma kan Farhan akan sunan da akaji ya kira Sis Mubee dashi. “Habibty?” Hakan yana nufin memory’nsa ya dawo normal kenan…?

A hankali Farhan ya tuna da kalmar daya furta daga bakinsa,wanda yasan hakan shiyasa kowa dake gun kallonsa.
Cikin sauri da farin ciki Mubinat ta tashi daga jikin Atif tana kallon Farhan ko k’yafta ido batayi,shi kuwa Atif ita da Farhan yake bi da kallo cikin tashi hankali.
“Farhan,Alhamdulillahi memory naka ya dawo” Abba ya fad’a cikin farin ciki.
A hankali Farhan ya rufe idanun sa tare da rik’e kansa yana motsi da leb’en bakinsa,ko ba’a fad’aba kowa yasan addu’a yakeyi.
Dan kar Abba ya zargi wani abune se Ahmad yace “Farhan,kai masha Allah,Alhamdulillah, abokina yanzu ka samu lafiya completely” yana dariya tare da dafa kafad’ar Farhan d’in.
Shureim da aka barsu a cikin mota se faman buga glass d’in mota yakeyi. Hakan yasa Farhan ya maida hankalin sa gun motan,cikin sauri ya kalli Mubinat dake tsaye a gabansa tana murmushin farin ciki. “Akwai key acikin aljihun jikinki kozan samu?” Cewar Farhan.
Hannu tasa ta d’auko sannan ta mik’a mishi,cikin hanzari yaje ya bud’e su.
“Ya Farhan meya sameka naga bayanka da jini?”
“Karka damu Shureim,d’an rauni na samu ba wani ciwo bane sosai”
Da sauri suka fito shida Musa suka k’araso gun, Shureim ya rungume Mubinat yana cewa “Sis Mubee babu abinda ya sameki ko? Ya naga kayan Ya Farhan a jikinki sannan shi na ganshi haka, ina kayanki?”
Farhan ne ya shafi kansa,tare da muntsinin kunnen sa alamun yayi shuri.
Abba yace “Yanzu dai dukku dakata,muje gida gaba d’ayanmu.”
Ba musu Farhan ya kamo hannun Shureim da Musa suka koma motarsu,shi kuma Ahmad yace wa wanda suke tare kaje kawai,nizan kai Abba gida zamuyi waya.
Bayan shima ya tafine,Ahmad yaja motar Abba sukayi gaba. Mubinat tana tsaye tana binsu Farhan da kallo yayin da duk wani b’ak’in cikinta ya sauya zuwa farin ciki. Jin motsin Atif da tayi ne a kusa da ita yasa ta juya suka kalli juna, gaba d’aya jikinsa a mace wucewa tayi zuwa motarsa sannan ya bita a baya.
Shureim se dariya yakeyi wai “Ya Farhan kalli inda Sis Mubee take yawo a cikin kayan ka”
Farhan baisan lokacin dayayi dariya ba hakama Musa almajiri. Seda yaga tafiyar su sannan yabi bayansu zuciyarsa cike da tunani iri daban-daban.
Bayan isarsu gidane Farhan ya kira Ahmad a waya,ba jimawa yazo gun motan,Farhan ya sanar dashi cewa yaje ya kawo mishi shrit da wando a d’aki. Bayan ya kawo mishi ne seya sa a cikin motan, dan bazai iya fita a haka ba ganin taron mutanen dake tsaye a harabar gidan.
Farhan yayi magana da Ahmad a sirrance, kan cewa karya sanar dasu Abba cewan an kama wani, koda Ahmad yaso jin dalilin hakan amma bai samu amsa daga gun Farhan ba.
Umma da Mum d’in Atif da Amal da Aisha, kai kusan duk dangin su Mubinat sun samu labarin abinda ya faru, dan haka suna tsaye a tsakar gida corko-corko.
Suna isa Mubinat taje aguje ta rungume Ummanta tana kuka. Ita kanta Umma seda tayi kwalla. Mum d’in Atif ne tazo kusa da ita tace “Allah sarki Mubinat d’ita Allah ya kiyaye na gaba,Allah ya toni asirinsu,kai Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu,wlh tashin hankali baiyiba.”
Umma tace “Wlh ki bari kawai Allah ya kiyaye kawai su kuma masu irin wannan halin Allah ya shirye su.” Aka amsa da ameen. Cikin jin kunya Mubinat ta kalli su Amal tare dayi musu magana da ido akan su tafi ciki.
Amal ce tace “Sannu Mubee muje ki sauya kayan jikinki” a silale ta wuce suna biye da ita.
Su Abba kuwa parlour suka wuce dukkan ninsu,inda Mahaifin Atif ma ya iso suka wuce a tare.
Dad d’in su Atif ne yace “Aise a tsaura bincike domin baza’abar maganan haka nan ba,dole abi diddigi musan wanda ya turosu. Ahmad yayi magana “Eh dama muma muna kan binciken kenan insha Allahu za’ayi nasara. Atif kuwa yana zaune rai a b’ace zuciyarsa se tafasa takeyi.
Abba yace “To Bayan wannan kuma akwai wani albishir dazan sanar daku a yanzu.”
  Dad d’in Atif ne yace “To muna sauraro”
Abba yace “Alokacin da Mamana take gudu akan titi wanda saura kad’an mota ya bugeta anan Farhan ya samu lafiya,ma’ana wannan had’arin da aka kusa yine ya dawo masa da momory nashi,yanzu lafiyan sa k’alau sedai muyiwa Allah godiya.” Nan parlour ya hargitse da murna anata addu’oi sosai kowa yana nuna farin cikin sa. Abba yaci gaba da cewa “Farhan nasan kana sane da cewa Mamana tayi aure kuma Atif take aure?” Cikin sanyin murya Farhan yace “Eh Abba”
Abba yaci gaba da cewa “To inaso kayi hak’uri kad’au k’addara dama can Mamana ba matarka bace,sannan dan Allah ku cire komai aranku dukkanku biyun musam man kai Atif, gaskiya banji dad’in abinda kukayiba wlh, duk ku d’in d’ayane aguna dan haka ku kula dan Allah.”
“Kayi hak’uri Abba,sharrin zuciya ce insha Allah hakan bazai sake faruwa ba.” Cewar Atif sannan ya kalli Farhan yace “Farhan kayi hak’uri,nayi kuskure.”
“Bakomai wlh ya wuce sannan ya kalli Abba, Abba kayi hak’uri munyi kuskure.” Cewar Farhan
Abba yace “To Alhamdulillahi Allah ya muku albarka” Suka amsa da ameen. Nanma Dad d’in Atif ya sake musu nasiha tare da sake baiwa Farhan hak’uri akan rasa Mubinat dayayi.
“Ka shirya semu je gun Doctor ya dubaka” cewar Abba.
“To” Farhan yace, sannan suka mik’e dukkansu ukun zuwa shashin su.
Mubinat ce zaune suna hira dasu Amal bayan tayi wanka ta canja kaya. Dama da kayanta a gida sunkai kala takwas. Sunci abinci sun k’oshine take basu labarin yadda mutanen nan suka mata. Mamaki sosai sukayi,sannan sukayi musu addu’an shiriya dan bai kamata ayi musu bakiba sedai a nema musu shiriya a gurin Allah.
Mubinat taci gaba da cewa “Ya Farhan ya dawo hayyacinsa yanzu yana sane da komai,inama da ace Abi d’insa yana k’asar, nasan zaifi kowa farin ciki dajin wannan labarin amma fa bazai kainiba.”
Amal da Aisha se binta suke da kallo suna tayata murna. Acikin ransu kuwa cewa suke akwai aiki. Hira sukai sosai, mak’ota se shigo musu sukeyi ana tayasu barkan dawowan Mubinat.
Bayan sallan la’asar Shureim yazo inda suke zaune yace “Sis Mubee wai kifito ku tafi”
Badan taso ba haka ta mik’e suka fito duk kansu,  taso ace sunyi magana ita da Farhan amma hakan baiyu ba. Tayi ta dube-dube ko zata ganshi amma sam babu alaman sa agun, kallon Shureim tayi tare da kiransa da hannunta “Ina Ya Farhan,kodai sun fita ne?” Ta tambaye shi.
“A’a Ya Ahmad ne kawai ya tafi, Ya Farhan yana bacci bayan ya gama k’wallan rasaki dayayi.”
Hankali Mubinat yayi matuk’ar tashi sosai,ji take kamar taje d’akin nashi danta ganshi,amma seta shige cikin mota kamar wanda ruwa ya dake ta. Su Aisha dai basu ce komaiba se ido da suke binta dashi.
Seda Atif ya shigo motar ne su Amal sukace “Zamu zo jibi ki hada mana beta”
“To sekun zo” ta fad’a cikin sanyin murya sannan Atif yaja motarsa suka tafi.
Tun a hanya ya lura da yanayin ta. Tunani yakeyi cikin zuciyarsa “Sis Mubee zata canja min kenan tunda har tasan Farhan ya samu lafiya yanzu, dole inyi saurin yin tarayya da Mubee inaga yin hakan shi zaisa ta saki jiki dani harma ta mance da Farhan muddin d’ana ya shiga jikinta.”
A hankali ya rik’o hannunta tare dayin magana cikin sanyin murya “Sis Mubee, are you alright?”
Shuru tayi bata ce komai ba,ya sake cewa “I’m sorry for what happen,dan Allah ki mance dashi a zuciyarki shaid’an ne da kuma kishin yadda nazo na ganki babu sutura a jikinki.”
Hannunta ta janye daga nashi tace “Ya wuce bakomai.”
Bai sake ce mata komaiba har suka isa gida.
Lokacin baccin su kuwa tana kwance shuru bai shigo ba. Se taji sallamarsa da ledoji cike a hannunsa wanda yasha sayayya iri-iri.
Kayan jikinsa ya cire ya wuce toilet. Babu jimawa ya fito yasa jallabiya yace “Taso muyi sallah”
“Nayi” tace dashi
“Ina nufin muyi nafila”
Mik’ewa tayi tasa himar dama doguwar riga ce a jikin ta.
Bayan sun idar ne yace”Sis Mubee ina fatan yau zan samu had’in kanki a matsayina na mijin ki?”
Mik’ewa tayi ta wuce zuwa d’ayan d’akin da gudu tana kuka.
Tashi yayi ya cire rigan jikinsa ya fesa turare sannan ya bita, k’ofar a bud’e ya jita dan haka ya shige kai tsaye tana kwance akan gadonsa tana kuka.
“Dan Allah karka tab’ani Ya Atif” ta fad’a cikin muryan kuka.
“Me yasa zakice haka Sis Mubee,kin manta yaune alk’awarin mu,me yasa zaki karya min alk’awari bayan na gama sa raina,kinaga kinmin adalci kenan idan kika min hakan?”
Kuka sosai takeyi tana girgiza kanta “Dan Allah kayi hak’uri”
Kanshi ya shafa da hannunsa yayi magana cikin  b’acin rai “Bazai yuba Sis Mubee,yau zaki bani hakkina indai ni Mijinki ne…!
“Me kike nufi danine Sis Mubee,i’m your husband taya zaki dinga guduna haka? For God sake auren mu 3month+ Sis Mubee ahakan kike so muci gaba da zama kenan ina kallonki kina kallona? Wlh bazai yuba na gaji,indai ba wani abu daban kike nufi ba!
Kuka sosai takeyi ganin yadda ranshi ya b’aci sosai. Yaci gaba da cewa
“Kodai kina adana kanki wa Farhan ne?” Cikin sauri ta d’ago da idanun ta wanda yasha kuka tace
“Wannan wani irin magana ne Ya Atif,taya zaka min wannan zargin?”
“Taya bazan yiba Sis Mubee,indai ba haka bane to lallai zaki bani hakkina a yau d’innan! Yana kaiwa nan yayi hanyan fita daga d’akin cikin b’acin rai.
“Wlh bazai yuba Ya Atif,bazan tab’a mallaka maka kainaba sedai in zaka min dole.” Sannan ta rushe da kuka wanda yasa shi tsayawa cak yana mamakin anya Sis Mubee ne tayi wannan maganan?
A fusace ya dawo tare da d’agota daga kwancen da take ya janye hijabin jikinta ya wurgashi gefe sannan ya rik’eta “Me kika ce Sis Mubee?”
Tsoron sane sosai ya kamata dan tun da take bata tab’a mishi gatse kamar na yauba. Cikin jin tsoro ta sake cewa
“Nace sedai kamin dole”
Kallonta yakeyi har cikin ido yace “Kin amince inyi miki dole?” Kai ta d’ago suna kallon juna,da sauri ta shige jikinsa tana magana cikin muryan kuka.
“Dan Allah kayi hak’uri Ya Atif karka min dole wlh…shhhh shikenan,zaki bani had’in kai?”
Kai ta girgiza mishi alaman a’a
Magana yayi cikin sanyin murya “Toya kike so ayi,kina so inje in fara neman matan banza a wajene Sis Mubee?”
Kai ta sake girgizawa da sauri alaman a’a
“Toya kike so inyi ki gaya min,me yasa kike son ki cutar dani Sis Mubee bayan ni kuma bazan tab’a iya cutar dake ba? Please give me this chance Sis Mubee,wlh ina cikin wani hali ina da buk’atarki sosai,please indai ba kina so in shiga cikin wani hali bane toki canja ra’ayinki please?”
Yana gama fad’in haka ya fita ya barta.
Tausayin shi ne ya kamata sosai,toilet ta shiga ta wanke fiskanta sannan tayi zamanta a d’akin nashi.
Kusan awa biyu tana kwance bata sake jin motsin Atif ba, hakan yasa taje d’akin nata,kwance ta ganshi yana juyi akan gado hannayensa suna kan cikin sa
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” ta furta,gaba d’aya ta rikice.
“Ya Atif, subhanalillah Ya Atif me yake damunka? Dan Allah Ya Atif kayi hak’uri ka gafarceni wlh bazan sake hanaka kaina ba, na amince dan Allah ka tashi.” Kuka sosai takeyi.
“Bakomai karki damu,kije ki kwanta kinji?” Yayi maganan cikin wata irin murya mai ban tausayi.
Hankalin Mubinat ya sake tashi sosai “Dan Allah Ya Atif kayi hak’uri wlh bazan sakeba daga yau, na amince maka na mallaka maka kaina amma dan Allah ka tashi.”
“Sis Mubee karki damu kije ki kwanta zan samu sauk’i…lips d’inta yaji cikin nashi tana mishi yadda suka saba,sam yak’i kulata “Sis Mubee stop it please” tare da janye jikinshi daga nata.
“Ya Atif hakan yana nufin kayi fushi dani kenan?”
“Banyi fushi dake ba,kawai dai bana jin dad’i ne zanso ki k’yaleni dan Allah”
Cikin sanyi jiki ta sake matsowa inda yake ta rungume shi tana hawaye.
Babu yadda ya iya da ita a hakan sukayi bacci…
Da asuba shine ya fara tashi ya wuce toilet,bayan ya fito ne seya tasheta tayi alwala sukayi sallah.
“Ya Atif ina kwana”
“Lafiya kin tashi lafiya?”
“Lafiya ya jikinka?”
“Da sauk’i”
“Allah ya sauwak’a,please kayi hak’uri da abinda ya faru jiya”
“Kidena damuwa Sis Mubee,ya riga daya wuce” yana gama fad’in hakan ya wuce zuwa wall drop ya fara shiri.
“Ya Atif ina zakaje da dassafen nan?”
Ba tare daya juyaba yayi magana “Zanje gidan Ya Musty ne,daga can zan wuce hospital”
Cikin sauri ta tashi ta k’araso inda yake ta rungumo shi ta baya “Dan Allah Ya Atif karka kai k’arana gunshi wlh na dena,bazan sakeba domin idan Abba yaji wlh zaimin duka please?”
A hankali ya juyo jin yadda ta rikice,kallon juna sukeyi cikin ido “Sis Mubee,bazai gayawa Abba ba, nasiha kawai zai miki.”
“No Ya Atif wlh na dena Allah,please karkaje please my love.”
Murmushi yayi yace “Ok shikenan,ki dena damuwa bazan jeba ba kuma zan gayawa kowa ba i promise.” Yana shafar furkarta tare da matso da kansa yayi kissing nata.
Ya gama shiri tsaf, se tace dashi “Amma ka tsaya kasha tea mana kafin ka  fitan?”
“Ok had’a min”
Bayan ta kawo mishi ne ta zauna gefensa tace
“Ya Atif ina so in tambayeka ne,kuma inaso ka gayamin gaskiya,meka sani game da mutanen da suka d’aukeni,kuma suwaye suke kiranka a waya baka son d’auka a gabana?”
Ajiyar zuciya yayi sannan ya ajiye kofin tea d’in ya janyota zuwa jikin shi tare da rungumeta ta baya yace “Sis Mubee kina zargina ne?”
“Ba zarginka nake yiba,ina so gaskiya yaci gaba da kasancewa a tsakanin mune tunda kaga yanzu  mu ma’aurata ne na har abada.”
Lips nata ya fara kissing saboda yaji dad’in kalamanta. “Sis Mubee,meyasa bakyamin kamar yadda nake miki?”
“Ai kaga yanzu safiyane shiyasa banci na k’oshi bane.” Ta fad’a tana murmushi.
Zama tayi sosai akan cinyarsa tace “Tell me Ya Atif” hannayenta yana mak’ale a wuyan sa.
“Shikenan zan gaya miki gaskiya,but bazaki gujeniba ba zakiyi komaiba right?”
kai ta d’aga mishi alamun “Eh”
Atif yace “Wlh Sis Mubee bansan komaiba akan wanda suka miki haka,but insha Allah za’a samo su”
“To Allah yasa” cewar Mubinat.
Ya amsa da “Ameen” sannan yaci gaba da cewa. “Wanda suke kirana a waya ba kowa bane illa Mujahid.”
“Waye shi Mujahid d’in?” Ta tambaye shi.
“Wani lokaci munje Kaduna meeting wanda zamuyi 2days acan kafin mu dawo. A Inda mukayi meeting d’inne na yarda ID card d’ina,k’anwar Mujahid ita ta tsinto ta bini har masau kinmu ta bani sannan ta bayyana min irin sona da takeyi tun da tasa idonta akaina. K’in amince mata danayi ne yasa ta nuna min zata iya bani kanta dan irin son da take min.”
“Sis Mubee a wannan ranan shaid’an ya gifta a tsakanin mu har muka aikata zina,kuma tabbas ita yarinyar cikakkiyar budurwa ce na sameta.
“Bayan tawa biyu se Yayanta Mujahid ya kirani yake sanar dani cewa k’anwarsa tana d’auke da cikina na tsawon wata biyu dan haka inzo ko kuma su subiyoni Inda nake.”
“Hankalina ya tashi sosai kuma na tabbatar da ciki nane tunda nine mutum na farko daya fara tarayya da ita.”
“Haka na shirya na tafi kaduna,dama mahaifinsu ya rasu daga ita se Mamanta se Mujahid.”
“Sun nemi da in aureta amma sam nak’i nace azubar da cikin. Su kuwa basu amince da hakanba,naci gaba da tura musu kud’i har cikin ya girma,lokacin aurenmu cikinta yana wata shida.”
“Tunda cikin ya haura wata shida take ta wahala da matsala kala-kala,ni kuma na gaji da kashe kud’i dan haka na fita hanyar su.”
“Kawai se ranan ya kirani wai an kaita asibiti haihuwa kuma suna buk’atan kud’i mai yawa aguna, bayan na tura musu kud’i mai yawane bayan awa biyu ya kirani yake sanar dani cewa ta haihu amma baby’n bata zo da raiba kuma ita  k’anwar nashi tana buk’atan k’arin jini.”
“Haka na sake tura musu da kud’i amma sena gargad’esa da karsu sake kirana akan wani abu tunda baby’n ta koma.”
“Bayan sati biyu ya sake kirana wai suna da buk’atar k’arin kud’i na jinyar k’anwarsa, tun wannan lokacin naci mishi mutunci tare da gargad’insa karya sake kiran wayana, dan asalima ita k’anwar tasa ce ta nemeni bawai nina neme taba.”
“Wannan shine dalilin dayasa kikaga ake kirana bana d’auka saboda bana so ki fahimci halin da ake ciki.”
Hannunta yayi saurin rik’owa yayin da take k’ok’arin tashi daga jikinsa yace “Please forgive me Sis Mubee, ki rufa min asiri kar su Abba suji wannan labarin please I’m sorry Sis Mubee?”
“Yanzu duk kai ka aikata wannan laifin Ya Atif,dama haka kake kenan? Ya Atif d’in dana sani da ba haka halayyar sa sukeba me yasa ka canja daga Atif d’in dah?”
Kuka sosai takeyi yayinda yake binta yana bata hak’uri.
Fad’uwar sa kawai taji a k’asa, da sauri ta juya cikin firgicewa tana girgizashi tana magana “Ya Atif,dan Allah ka tashi me hakan kenan,wlh banyi fushiba ka tashi please…”
Amma sam Atif baya ko motsi, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un please Ya Atif ka tashi dan Allah…”
“Ya Atif please wake up” ruwa taje ta d’ibo a cup tana yayyafa masa sannan ta d’auki wayansa dake gefensa ta kira number’n Abbanta.
Babu b’ata lokaci ya d’auka suna zaune dukkansu a parlour ana gaisawa. “Salamu Alaikum Atif” Abba yayi magana,cikin muryan kuka Mubinat tace “Abba nice,ga Ya Atif nan kwance ya fad’i ko motsi bayayi dan Allah Abba kazo yanzu.”
Cikin rud’ewa Abba yace “Subhanalillah,ganin zuwa” sannan ya katse wayar yace “Farhan tashi muje wai Atif ne ya fad’i ko motsi bayayi”
“Innalillahi” suka furta shida Umma harda Shureim sannan suka fita cikin hanzari suka nufi gidan.
Har lokacin Mubinat tana ta faman kuka gaba d’aya ta gama rud’ewa. Jin k’aran horn d’in mota tare da bud’e gate da akayi ne yasa ta mik’e zuwa bud’e k’ofa dan tasan Abba ne.
Fitowa tayi da gudu ta k’arasa gunsu tana cewa “Muje Abba yana ciki” gaba d’aya idan ka ganta zaka tausaya mata,dan kota kan Farhan ma bata biya.
Abba da Farhan a tare suke duba shi suga ko yana numfashi, tabbas yana numfashi, hakan yasa Abba cewa “Mamana ki kwantar da hankalin ki insha Allah babu komai,Farhan d’agashi muje asibiti.”
Ganin haka yasa Mubinat shigewa d’aki ta sako hijabinta dama k’ananan kayane a jikinta.
Abba ne zaune da Atif a baya,ita kuwa seta shige gaba Farhan ya jasu se hospital.
Suna isa babu b’ata lokaci doctor ya karb’esu dama doctor’n sune. Cikin sauri aka wuce dashi domin gwadashi.
Bayan gwaje-gwajen da doctor yayi ne ya tabbatar da cewa jininsa ne ya haura sosai da kuma fever da yake d’auke dashi.
Mamaki sosai Abba yayi,don tunda Atif ya dawo gidansa da zama bai tab’a yin wani ciwoba,se kuma gashi yau ance jininsa ya hau? “Tome yake damun Atif haka dahar zaisa jininsa yahau har haka?”
Ba Abba kad’ai ba, hatta ita Mubinat d’in da Farhan tunanin da sukeyi kenan a zuciyarsu.
“Kodai k’in amincewa da banyi dashi bane tun farkon aurenmu yasa shi cikin damuwa har ya janyo mishi hakan? Oh no Ya Atif i’m sorry.” Take fad’a a zuciyarta yayinda take ‘yar k’walla a fili.
“Sis Mubee,ki dena damuwa zai samu lafiya insha Allah.” Cewar Farhan
Kunya sosai taji daya fahimci ta shiga damuwa. “Thankyou” tace dashi tare da komawa gefe ta zauna akan farin kujera tana tuna maganar Farhan. Ta lura dashi sam baya so yaganta cikin damuwa,duk da cewa tana auren Atif a yanzu, amma baya iya b’oye damuwarsa muddin ya ganta cikin damuwa.
“Mamana akwai wani abu da yake damun Atif ne a baya?” Abba ya tambaye ta.
“A’a babu komai Abba”
“To nayi mamaki da abinda doctor ya fad’a ne akan Atif.”
Shuru tayi bata ce komai ba.
“Allah ya bashi lafiya” cewar Farhan.
Suka amsa da ameen dukkansu.
Fita Abba yayi waje yana amsa wayan Umma. A hankali Mubinat ta matso inda Atif yake kwance ta zauna a gefen sa.
Shi kuwa Farhan idanunsa suna kanta,baisan me yasa ya kasa d’aga idanunsa daga kanta ba.
  Hannunta takai kan na Atif tana rik’e dasu tare da matso da fuskarta ta tsunbaci gefen fuskarsa tace “Ya Atif please open your eye i’m here”
Farhan baiji komaiba yasan yadda Mubinat takeji da Ya Atif tun farko,dan haka se yayi murmushi tare da cewa “Bari na baku guri ina daga waje” sannan yayi hanyar fita.
Yana dai-dai k’ofa tace “Habibi?”
Ahankali ya tsaya tare da mamakin sunan dayaji ta kirashi dashi. Juyowa yayi suna kallon junansu, fuskarta babu ko  murmushi tace “Thankyou” tare dayin k’walla.
Murmushi ya sakar mata sannan yace da ita “It’s nothing Sis Mubee,i will do anything for both of you.”
K’wallanne yaci gaba da gangarowa daga idanunta zuwa jikinta. Farhan bazai iya jure ganin hakan ba,musamman ma daya san dalilin zubowar su,da sauri ya fice daga d’akin.
Jikinta ta manna akan na  Atif tana kuka wanda ita kad’ai tasan dalilin yinsu…
Cikin k’ank’anin lokaci ‘yan gidansu Atif suka hallara a hospital d’in. Mahaifinsa yana Umrah dan haka yayyunsa ne suka zo da kuma Mum nashi da Aisha.
Cikin jin kunya Mubinat ta gaishe su sannan suka fita waje da Aisha.
“Mubee,me yake damun Ya Atif?” aisha ta tambaye ta.
“Doctor yace jinin sane ya hau da kuma fever.”
“Jininsa ya hau,to me dalilin hakan?”
“Wlh nima abinda nake mamaki kenan Aisha, na kasa gane komai.”
“Mubee,nasan dai bakya son Ya Atif a matsayin mijinki,kuma shi Ya Atif yana matuk’ar k’aunarki wanda kema kinsa da hakan,Mubee hakan zai iya sashi cikin damuwa wanda zai iya haifar mishi da hawan jinin tunda yana sonki.”
“Please Mubee ki tausaya mishi,duk yadda k’awancenmu take ko kuma ‘yan’uwan takarmu dake ina so kisan cewa ina matuk’ar k’aunar Ya Atif sosai amatsayin shi na Yayana wanda muka fito ciki d’aya,dan Allah ki sassauta mishi haka tunda kinga ga abinda ya fara janyo mishi wanda nasan kece sila.”
  Aisha tana kaiwa nan ta wuce cikin d’akin tabar Mubinat a tsaye duk jikinta yayi sanyi dajin kalaman Aisha.
Tunda suke hakan bai tab’a faruwa a tsakaninsu ba,sannan ita kanta Mubinat tasan duk abinda Aisha ta fad’a gaskiyane dan bata bin bayan k’arya ko wani son kai.
Cikin sanyi jiki itama tabi bayan Aishan wanda yayi dai-dai da farkawan Atif yana binsu da kallo. Haka suka dinga mishi sannu har idanunsa suka zo kan Mubinat.
Murmushi ya sakar mata tare da mik’a mata hannunshi alamun tazo, cikin jin kunyan su Mum dasu Yaya Musty se tace “Ya jiki?”
“Da sauk’i” ya bata amsa yana mai cigaba da kallonta.
Ganin hakan yasa su Mum fita waje. Daga su se Aisha ne kad’ai a ciki.
“Sis Mubee?”
“Na’am” ta bashi amsa
“Zonan ki zauna kusa dani”
Ba musu taje ta zauna ya rik’o hannunta tare da tsunbatar su sannan ya kalli Aisha.
Murmushi tayi mishi tace “Ya Atif a baka da lafiyan ma?”
“Aisha kinfi kowa sanin yadda Sis Mubee take aguna,shiyasa koda yaushe nake son injita a kusa dani.”
“Murmushi ta sakeyi tare da cewa “To Allah ya barku tare,ya k’ara soyayya.”
“Ameen Sister,thanks for d prayer”
“Mention not,zan je gurin su Mum ina dawowa” sannan ta fice.
Mubinat tanata binta da kallo da kuma tuna abinda ta gaya mata. Atif ne ya katse mata tunani da cewa “Hey,are you okey?” Tare da juyo da fuskarta suna kallon juna.
“Yeah i’m fine” ta fad’a tare da had’e lips nata da nashi suna kissing d’in junansu cikin jin dad’i.
A hankali ta saki lips nashi tace “I love you my hubby” tana kallonshi da murmushi a fuskarta.
“Sis Mubee,kina nufin kin yafemin abinda na aikata?”
“Yes of cause,kama mance ka sanar dani wani labari makaman cin hakan.”
Farin ciki ne fal akan fuskar shi,ya sake rik’o fuskarta da hannayen sa biyu yace “Can i get that sweet again?” Cikin zolaya.
“Nop” ta bashi amsa cikin zolayar itama.
“But why?”
“Because it belongs to some one.”
“Nd who is that?”
“Emmm,i think is…Atif… Muhammad… Bakari right?”
Dariya sosai yayi tare da rungumeta sosai a jikin shi yana ci gaba dayin dariyan.
“I love you Sis Mubee,nd i will always love you.”
Lips nata ta sake sawa a cikin nashi sukaci gaba da tsotsar junan su.
  Bud’e k’ofa sukaji anyi,Shureim ne tsaye yana kallonsu cikin mamaki sannan ya rufe da sauri ya tsaya daga waje.
“Shureim yaka tsaya kuma?” Farhan ya tambaye shi
“Ya Farhan,kiss naga sunayi,bari naje na dakatar da Umma.”
Dariya sosai yabawa Farhan, kansa ya mara a hankali cikin wasa yace “To kai dama haka kashiga babu sallama?”
Murmushi Shureim yayi yace “Na manta ne,amma bari nayi yanzu.”
Koda aka amsa musu sallamar har awannan lokacin dariyan sukeyi shida Farhan d’in.
Ita kuwa Sis Mubee kunya taji sosai dukda dai shi Farhan d’in bai gansu ba.
Umma ce ta biyosu a baya da sallama,bayan an gaisa ne ake d’an tab’a hira, Shureim se kallon Sis Mubee yakeyi yana dariya.
Farhan ya lura dasu,dan haka yace “Shureim lafiyanka kuwa?”
Da gudu Shureim ya fice waje yana dariya,da sauri Mubinat tabi bayanshi.
Umma tace “Shureim da tsiya,Farhan key yana hannun Shureim karfa yaje ya jefar”
“Ai bazai tab’a jefar waba” cewar Atif.
Wayan Farhan ne ta fara ringing, dan haka ya fita waje domin amsa Kiran.
Ita kuwa Mubinat tana ta tambayan Shureim “Wai dariyan me kake tayine?”
Shuru yayi baice komai ba yana k’ok’arin gudu tana tareshi.
Can ya hango Farhan ya gama waya yana tahowa inda suke ba tare da ita Mubinat ta sani ba taci gaba da tambayar Shureim.
“Ka gayawa Ya Farhan ko?”
Shi kuwa Farhan yaji abinda Mubinat take fad’a dan haka yace “Bai gaya min komai ba ki dena damuwa.”
Da Sauri ta juyo bayanta suna kallon juna har cikin ido. Duk kanninsu sun kasa d’auke idanun su akan junansu dayake suna kusa sosai.
Duk wanda ya gansu yasan wani irin kallo suke yiwa junansu. Cikin dauriya Farhan ya sauke idanunsa ya wuce waje ya tsaya a jikin mota,wani sabon son tane yake shigarsa a hankali.
  Tunani ya shigayi lokacin daya gayawa Abba ra’ayinsa akan Mubinat, Abba yace “Bakomai Farhan Indai kun daidaita da ita shikenan Allah ya sanya alkhairi.”
K’walla Farhan ya had’iya yace “Ya Allah ka yaye min k’aunar Mubinat a cikin zuciya ta…”Su Umma sun dad’e sosai kafin suka tafi.
Atif ya d’an samu sauk’i ba laifi,dan haka ya nemi da a sallamesu amma se Doctor yak’i.
Lokacin da Abba yazo ne Atif ya sake dagewa lallai shi bazai kwana a asibitiba sabida yaji sauk’i,haka Doctor ya sallame su.
Ruwan d’umi ta had’a mishi yayi wanka bayan sun dawo gida.
Sun gama komai nasu sukayi shirin bacci kamar dai yadda suka saba,sedai yau Mubinat shiri na musam man tayiwa Atif domin karb’ansa a matsayin mijinta.
Yayi mamakin ganin rigar baccin data sa,tun a lokacin ya shiga wani irin yanayi bare kuma data zo jikin shi.
Mubinat ta dad’e tana tuna kalaman Aisha,dan haka ita da kanta ta fara shige masa tunda dama can sun saba wasan ninsu. Shi kuwa Atif baya jin k’arfi a jikinsa kamar dai yadda yake da,dan haka yace da ita “Sis Mebee”
“Na’am” tace dashi
Cikin siyasa yayi magana “Inaga banda k’arfi sosai a jikina,kuma bana so ki rainani,shiyasa nake ganin gara mu bari ko zuwa gobe indai hakan ba matsala.”
A cikin ranta dad’in maganar sa taji,amma a fili seta ce “Haba Ya Atif yanzu har kana tunanin akwai raini a tsakanina da kai?”
“Ba haka nake nufiba,ina nufin kar in kasa gamsar dake amatsayin ki na amarya ta.” Ya k’arashe maganar cikin zolaya.
“Hhhhhh Ya Atif kenan,to shikenan ai dayau da goben duk d’ayane,Allah ya kaimu Allah kuma ya baka lafiya.”
“Ameen” yace da ita yana shafar kanta kamar wata baby.
“Jikinka yana min kyau sosai Ya Atif,tun ada har ina gayawa Amal tace min kodai sonka nake,nace mata haba ke kuwa babu hali ince wani abu akan ya Atif se ina sonshi? Tace eh mana.”
“Hhh oh Sis Mubee kinban dariya”
“Serious wlh”
“To ai gashi gabad’aya nama na zama mallakinki ba jikina kad’ai ba.”
“Hmm to ai shine nima nake wannan tunanin yanzu.”
Haka dai sukaita hiransu suna soyayya har sukai bacci.
Washe gari bayan sunyi breakfast ne wayan Atif ya fara ringing,d’auka yayi tare da cewa “Hello Doctor,wlh jiki da sauk’i sosai,ameen nagode,ok toba damuwa insha Allah.” Sannan ya katse ya kalli Mubinat tare da janyota yace “Doctor ne ya kira yaji yaya jikin nawa.”
“Ok” tace dashi sannan suka jiyo ana nocking tare da sallama.
Atif ne yaje ya duba,Farhan ne a tsaye yana sanye da farin suite yayi matuk’ar kyau sosai.
“Ah Farhan,sannu da zuwa bisimillah mana.”
“A’a ba jumawa zanyi sosai ba,nazo ganinkane amma bari mu gaisa da Sis Mubee idan yaso semuje daga waje.”
“Ok hope dai lafiya ko?”
“Eh lafiya lau”
Muryan Mubinat ce tana cewa “Ya Atif kaida waye?”
Atare suka shigo,tun daga nesa ta hango Farhan.
“Laa Ya Farhan sannu da zuwa” sannan tayi saurin shigewa d’aki dan riga da wando ne a jikinta babu ko d’ankwali tayi adon safiya tsaf da ita.
Sanye da himar ta fito ta zauna kusa da Atif tace “Ya Farhan ina kwana”
“Lafiya, ya mai jiki?”
“Alhamdulillah jiki yayi sauk’i ko Ya Atif?”
“Kallonta yayi sannan yayi mutmushi yace “Eh alhamdulillahi zamuce”
“To Allah ya k’ara lfy nizan wuce”
“Da sauri haka Ya Farhan,ka tsaya mana koda coffee ne seka sha”
“Thankyou ak’oshe nake” yana murmushi
“To shikenan,mun gode a gaida su Umma da Shureim”
“Zasuji”
Sannan suka fita shida Atif tanata binsu da kallo.
“Atif dama ranan da aka d’auke Sis Mubee akwai wanda na kama na damk’ashi a hannun su Ahmad,sun bincikesa sosai shine yake gaya musu cewa wanine mai suna Mujahid ya turosu tun daga garin kaduna.”
“Dama mun b’oyewa su Abbane dan gudun kar…”Yanzu kana nufin Mujahid ne ya turosu?” Atif ya tambaye shi cikin mamaki
“Yes abinda ya gaya musu kenan,Atif please ina so in nemi wata alfarma agareka,dan Allah ka kiyaye duk wani abu daka san bai halattaba,kodon d’aurewan zaman lafiya tsakaninka da Sis Mubee da kuma su Abba.”
“Yana da kyau ka rik’eta kodon mutunta su Abba please,shine kawai dama abinda ya kawoni,nizan tafi.”
Jikin Atif yayi sanyi dan ya fahimci cewa sunsan komai kenan dan yasan dole mutumin zai gaya musu abinda ya had’ashi da Mujahid harya turosu garin nan,kuma ya fahimci maganga nun Farhan sosai. Dan haka yace “Nagode sosai Farhan,nagode da irin rufamin asiri dakayi wajen b’oyewa su Abba, dan badan hakanba da sunsan abinda na aikata a baya wanda zasuga kamar laifinane d’auke Sis Mubee da akayi.”
“Sannan insha Allah zan kiyaye bazan tab’a cutar da Sis Mubee ba,zan rik’eta da amana insha Allah nagode sosai.”
“To Alhamdulillah nabarku lafiya,yawwa inaga bai daceba ta dinga kiranka da Ya Atif,saboda kai mijintane a yanzu,kaima kuma bai halatta ka kirata da Sis Mubee ba,hakan bai halattaba a musulunce.”
“Ok,zamu gyara mungode.”
Yana tsaye har Farhan yabar cikin gidan sannan ya dawo ciki yace da Mubinat zai fita.
“To amma kafin ka fita,hiran me kukeyi da Ya Farhan?”
“Don’t worry,idan na dawo zan gaya miki”
“To wai ma ina zakaje ne?”
“Kin manta yauni ango mai jiran gado ne,kedai ki jirani bazan dad’eba ai my love.” Ya manna mata kiss sannan ya fice tana binshi da dariya…
Shuru shuru Atif bai dawoba har bayan sallan isha,sannan kota kira number’n shi baya d’auka. Hankalinta ya tashi sosai.
  11:15pm tajiyo horn nashi,da sauri ta fito tsakar gidan tana tsaye zaman jiransa.
Ko daya tsaya da motan amma shuru bai fito daga ciki ba,da sauri ta k’arasa ta bud’e zaune yake kansa bisa siterin motan.
Kansa ta d’ago “Ya Atif lafiya,jikin nakane ya tashi kuma,ina ka shiga haka naketa kiranka baka d’auka,me yake faruwa ne?”
Hawaye ne cab’e-cab’e akan fuskarsa kaman bana miji ba. Hankalin Mubinat ya sake tashi fiye dana dah.
Kan ta sake ce wani abu ya wuceta idanunsa jajawur ya shige ciki batare daya kalleta ba.
Rufe motar tayi ta biyo bayanshi,koda ta shigo d’akin shi kuwa yana wanka a toilet.
Fitowa yayi yana goge jiki,rungumesa tayi tana cewa “Ya Atif me yake faruwa ne,me yake damunka please kayi  magana mana.”
Kallonta kawai yakeyi sega k’walla yana zubowa. Turashi tayi zuwa gado tare da kashe wutan d’akin ta cire kayan jikinta sannan ta janye tawul nashi ta fara nuna mishi irin son da take mishi inma hakan shine matsalar sa.
Tun baya biye mata har suka shagalta sosai dukkansu. Kuka taji Atif yanayi da murya sosai wanda ya d’aga mata hankali,shine daga samanta tana jin yadda hawayen sa suke zuba a fuskarta har zuwa wuyanta.
“I’m sorry Sis Mubee,i’m so sorry,please forgive me.” Shine abinda ya furta sannan ya fice zuwa d’akinsa yasa key.
Binsa tayi tanata magiya amma sam yak’i kulatama bare ya bud’e mata k’ofan.
Mubinat tafi awa uku a tsaye agun tana buga k’ofan amma duk a banza,kukansa kawai takeji tare da surutai da yakeyi wanda bata san mema yake fad’a ba.
A haka ta wuce d’akinta ta kwanta har bacci yayi gaba da ita batare data saniba.
Da asuba ta mik’e ta nufi toilet bayan ta fito ta gabatar da sallah sannan ta nufi d’akin Atif.
Bugawa sau d’aya kawai tayi yazo ya bud’e mata k’ofa tare da saurin rungumeta.
“Sis Mubee i’m sorry for what happen yesterday night,kije ki shirya zamuje wani guri ne yanzu.”
Mamakine fal a fuskarta “Ina zamuje da asuba haka,sannan baka min bayanin abinda ke faruwa ba na jiya.”
“Zan gaya miki komai,but pls kije ki shirya mu tafi.”
Ba musu taje ta shirya ta fito,lokacin yana sa wani farin peper a aljihunsa.
Rungumeta ya sakeyi sosai yana juyi da ita da ‘yar k’walla a idonsa sannan ya rik’o hanunta suka fita hargun mota.
Tafiya sukeyi tanata bin hanyan da kallo,shi kuwa ko kallon gefenta yak’iyi bare yace da ita wani abu,dan haka itama  shuru tayi tana kallon shi sosai yayinda taga yana horn a k’ofar gidan su.
“Ya Atif lafiya kuwa,meya faru a gidan namu ne,me kake b’oyemin Ya Atif?”
“Kiyi hak’uri aimun iso”
Kallon gidan nasu ta shigayi amma bataga  wani abu daban ba.
A tare suka fito suka nufi parlour’n Abba,ana zaune kamar yadda suka saba da an dawo daga masallaci se’a zauna gaba d’aya ayita hira.
Su kansu Abba sunyi mamakin ganin su Atif da asuba haka. Bayan an gaisane Atif ya fara magana kamar haka
“Abba dan Allah kuyi hak’uri dani da kuma abinda nazo dashi.”
Duk sukayi shuru suna sauraronsa da maida hankalinsu zuwa gareshi.
Shi kuwa Farhan ya d’auka Atif zai fad’awa Abba abinda ya farune tsakaninsu da Mujahid.
Atif yaci gaba da cewa “Abba ga Sis mubee nazo da ita,dan Allah kuyi hak’uri,Sis Mubee gashi”
Juyowa tayi tana kallonshi tare da k’arewa abinda yake mik’a mata kallo,farin peper ce dan haka tasa hannu ta karb’a tana kallonshi.
“Sis Mubee,na sakeki saki d’aya,dan Allah kiyi hak’uri ki yafemin.”
Yana kaiwa nan ya mik’e da sauri ya fice,akabar su Abba da Innalillahi,ita kuwa Mubinat da gudu tabi bayanshi tana kuka tana cewa “Ya Atif saki fa kace,mena maka dan Allah da zaka sakami da saki? Please Ya Atif kayi hak’uri ka mai dani wlh ina sonka please kace ka mai dani mu koma gidanmu Ya Atif…….😔

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *