KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 6
Atif ne zaune shida Abokinsa a gaban Doctor yana bayani cikin tashin hankali.
“Doctor i slept with her”
“Haba Atif,yaya zakayi haka bayan na gaya maka abinda kake d’auke dashi?”
“Doctor i’m sorry,wlh ba laifina bane,nayi iya bakin k’ok’arina dan inga na nisanceta amma hakan bai yuba,please Doctor gayamin cewa Sis Mubee bazata kamu da irin abinda nake d’auke dashiba” ya fad’a yana hawaye.
Doctor ya fara yimusu bayani kamar haka.
“Atif gaskiya seka kawota anyi mata gwaji kafin mu sani,sannan idan akayi mata gwajin baza muyi amfani da abunda gwajin ya nuna mana ba har sai an k’ara yin wani after 3 month daga nan sai a kara wani after 3 month,idan result din farko ya bada negative ba zamu d’auka negative d’in bane har sai an ga result na biyu idan ya bada negative still ba zamu d’auka negative bane,idan result na ukku ya bada negative shine zamu yarda cewa negative din ne.”
“Idan final result ya bada positive to tabbas hakan yake positive d’in ne,abinda yasa ake yin awon har kashi ukku ga wanda ake tunanin yana d’auke da cutar shine wasu tashi daya cutar bata bayyana kanta kuma bata karya garkuwar jiki sai ta dad’e tsananin dad’ewarta shine wata shidda zuwa tara,kafin ta karya garkuwar jiki wanda idan aka kai wannan lokacin dukkan sakamakon da aka samu to haka abun yake.”
“Innalillahi wa’inna ilaihurraji’un,ba damuwa Doctor zan kawota insha Allah,fatan da nakeyi shine Allah yasa Sis Mubee bata d’auki wannan cuta ba,idan harta d’auka to lallai na cuceta Doctor.”
“Muma fatan da mukeyi kenan Atif,but ka sani koda wasa karka sake kusantarta saboda yanzu haka bamusan me take ciki ba.”
“Insha Allah doctor,base ka gayamin wannanba nasan abinda zanyi akai.”
“To shikenan Atif,Allah ya sauwak’a,ka kuma tabbata kana shan maganinka.”
“Hmm,Doctor me amfanin shan maganina indai akayi nasara Sis Mubee bata dashi to ai kaga dole zamana da ita yazo k’arshe kenan,amma nasan bazan iya rayuwa babu Sis Mubee a tare dani ba,dan haka babu wani magani dazan sha kawai zan jira mutuwata dan ta fiyemin zamana babu sis Mubee a rayuwata,bazaku tab’a gane irin son da nake yiwa Sis Mubee bane.”
Yana kaiwa nan ya mik’e cikin damuwa,Doctor yanata mishi magana amm sam bai tsaya sauraron saba. “Allah sarki Atif,Allah ya baka lafiya” cewar Doctor.
Mubee kuwa tana kwance a jikin Farhan ta suma. Goran Faro Amal ta d’auko akan wani table ta bud’e tare da mik’awa Farhan yana durk’ushe ya karb’a ya yayyafa mata a fuskarta tare dajan d’ankwalinta ya shafa mata akai.
Acikin zuciyarsa kuwa addu’oi yaketa karanto mata.
Mutane ne a cike akanta,Abba da Ya Musty ne suke tambayar meya faru? Amal ta kalli Ya Farhan se kuma tayi shuru,Farhan yace “Kawai fad’uwa mukaga tayi.”
Ya kalli mutanen gun sannan yace “Amal ku rik’eta” da sauri matan dake gun suka kakkamata shi kuwa Farhan yayi hanyan waje.
“Farhan ina zakaje?” Cewar Abba.
“Zanga wanine awaje Abba” sannan ya fita Abba yana binshi da kallo sam ya kasa gane yanayin da Farhan yake ciki a yanzu kawai.
Yana fita waje yaga babu motar Atif,seya hango Ahmad zaune a cikin mota ya had’a kai da siterin mota.
Cikin sauri ya k’arasa gunshi tare da buga motar da hannunsa,Ahmad ya bud’e “Farhan lafiya?”
“Kai zanma wannan tambayan,me yake faruwa ne,me naji Amal tana gayawa Sis Mubee?”
“Farhan wlh nayi iya k’ok’arin dakatar da Amal amma hankalinta ya tashi sosai kasan yadda take da Mubee,wlh duk abinda kaji ta fad’a gaskiyane Atif ne yake gayawa sayyid batare dasunsan muna gurinba.”
Juyawa Farhan yayi tare da shafar gashin kansa yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”
Shureim ne yazo a guje “Ya Farhan,Sis Mubee ta farfad’o.”
Kamoshi yayi “Shureim kaje ka cewa Sis Mubee karta yadda tace komai agun,kace nina aikoka sannan akunne zaka gaya mata ta yadda babu wanda zaiji kayi sauri.”
Da gudu shureim ya koma ciki ta inda Amal take zaune ya sunkuya “Sis Mubee,Ya Farhan yace in gaya miki karki ce komai agun” sannan ya tashi ya koma waje.
Abinda Shureim ya fad’a kuwa a kunne Aisha taji komai.
Farhan suna tsaye a waje sega su Atif sun dawo,Ahmad ne yaja hannu Farhan “Muje ciki dan Allah karka ce mishi komai tukunna.”
Aisha tana tunanin zata iya yiwa Farhan cin fuskane,amma data ganshi seta kasa,hango Atif datayi daga bayansune yasa ta mik’e da sauri taje ta gaya mishi abinda ya samu Mubee da kuma abinda Farhan ya aiko a gaya mata.
Cikin sauri Atif ya k’araso gurin,yayinda Amal tabar gun dan tasan zata iya gaya mishi maganganu marasa dad’i.
Karb’eta yayi daga hannun mutane yana shafar gashin kanta da yake kame a tsakiyar kanta yana cewa “Sis Mubee what’s rong?”
Kallonsa kawai takeyi sega hawaye zir-zir a fuskarta. D’agota yayi cak ya nufi waje da ita Aisha tana biye dasu ya ajiyeta a cikin motarsa.
“Sis Mubee tell me what’s happen?”
“You tell me Ya Atif,are you hiding something for me?” Ta fad’a tana hawaye
Jikin Atif yayi sanyi “Nothing Sis Mubee,I’m not hiding anything… “You’re such a liar Ya Atif,ka gayamin me kake b’oyemin tun kafin in gano gaskiyar da kaina.”
Yadda yaga ta fita daga cikin motarne tana masifa yasa shima fitowa yana k’ok’arin rik’ota yana bata hak’uri.
A can ciki kuwa wani irin ciwon kaine ya kama Farhan kamar dai yadda ya tab’a mishi acan Madina,an kuma tabbatar mishi da cewa yawan damuwane da yake sawa a ranshi ya jawo mishi hakan. Hakannema yasa ya tara jama’a tare dayi musu godiya sannan aka rufe taro da addu’a kowa ya kama hanya.
Fitowa sukayi yabar komai a hannu wani daga cikin ma’aikatan akan ya jira a watse seya rufe gurin sannan suka fito yana rik’e da Kansa.
“Farhan lfy?” Cewar Abba
“Lfy Abba kainane yake d’an min ciwo”
“Subhanalillah,Ahmad kuje ka kaishi gun Doctor”
“Abba base najeba zanje in kwanta a gida ind’an huta”
“A’a Farhan Mahaifinka ya gayamin komai game da ciwon kanka,dan haka kuje hospital kaga Doctor.”
“To Abba,muje Ahmad” harda Amal suka tafi sannan su Abba ma suka wuce akabar Atif da Mubee da kuma Aisha suna bin motar su Farhan da kallo.
“Ya Atif bafa zan bika gidankaba,harse ka shirya gayamin gaskiya dan haka ni gida zan tafi kuma karkayi k’ok’arin dakatar dani.”
“No Sis mubee,you can’t do this to me we are going home”
“No! No Ya Atif bazan bikaba wlh senaji gaskiyan lamari,idan ka shirya gayamin to ina sauraronka.”
“Aisha kid’an bamu guri dan Allah” cewar Mubinat,ba musu tabar gurin tana mamakin meya had’asu haka?
Ta maida kallonta gun Atif ta sake cewa “Da gaskene abinda naji game dakai?”
“Me kikaji Sis Mubee tell me,nayi alk’awarin zan gayamiki gaskiya wlh bazan b’oye miki komaiba just tell me please?”
Cikin kuka tace “Da gaskene wai you’re H I V positive?”
Mamaki sosai Atif yayi dajin wannan maganan a bakin Mubee,dan shi yasan bai gayawa kowaba bayan sayyid.
Hannunta ya rik’o “Sis Mubee tell me who tell you please?”
“Karka damu da sanin wanda ya gayamin just answer me!
Cikin rud’ewa da ganin yadda take magana cikin tsawa yace “Yes it’s true Sis Mubee,it’s true but pease…tasss ta wankeshi da mari wanda seda Aisha taji,da gudu tazo gurin zata mari Mubee Atif yayi saurin rik’eta. Kud’i ya ciro daga aljihunsa ya mik’a mata “Kije kihau machine ki tafi gida Aisha kinji,and please karki sanar da Mum komai.”
“Ka barni Ya Atif,koma me Ya Atif ya miki ai bai kamata ki mareshiba a matsayinshi na mijinki.”
“Aisha kiyi shuru da bakinki karki shigo cikin maganan da bakisan komai akaiba.”
Janyeta Atif yayi dan sam bata da niyan barin gurin ya samu abin hawa ya d’aurata sannan ya dawo amma seya hango Mubee can tana tafiya zuwa bakin titi.
Da gudu yabita tare da rungumeta a jikinshi yana hawaye “I’m sorry Sis Mubee,please ki saurareni.”
“Let me go Ya Atif,you know that you’re HIV positive and you slept with me! You’re a monster Ya Atif!
“Sis Mubee please forgive me I’m so sorry,nayita k’ok’arin dakatar dake amma kikak’i wannan dalilinne yasa na sakeki dan kar incigaba da zama dake in cutar da rayuwar,amma danaji kin kirani kina gayamin Umma ta dakeki shine naji haushin kaina dan a tunani dukni na janyo miki,hakanne yasa nazo nace musu na mayar dake.”
“Sis Mubee koda wasa bansan a raina zanyi having sex dake ba,kawai na dawo dakene dan bazan iya rayuwa babu keba shiyasa a wannan daren nayita dakatar dake inak’i amma kece kika tunzurani ta yadda bazan iya barin kiba,idan baki mantaba kinga canji sosai aguna wlh wannan shine gaskiyan Sis Mubee please karki barni please?” Yana kuka da hawaye sharb’e-sharb’e.
“Dukda haka Ya Atif laifinka kawai nake gani,dama can kasan kana da wannan cutar sannan ka aureni?”
“No,wlh bani dashi,asalima kece silar dayasa hakan ya sameni Sis Mubee.”
“Ni kuma,kamar yaya zakace ni?”
“Sis Mubee tunda mukayi aure kike k’in in tab’aki kika kafa min dokokinki na kuma amince miki,lokacin da muka tafi Abuja ne kiketa wasu irin shiga sannan ina ganin yadda matan abokaina suke rayuwarsu cikin soyayya,rananne da muka fita da abokina shaid’an ya had’ani da wata yarinya har muka aikata zina da ita ananne na samo wannan cutar.” Ya k’arashe maganar yana mai zuba gwuiwowinsa a k’asa “Please Sis Mubee believe me wannan shine gaskiyar lamarin.”
“Sannan wlh bansan na kamu da wannan cutarba harse lokacin da kuka kaini hospital dasu Abba a wannan treatment d’in da Doctor yaminne bayan an sallamoni yake sanar dani cewa yana son ganina,bayan na fita mun had’une yake gayamin abinda nake d’auke dashi wanda shine ranan kikaga ban dawo gida da wuriba ko dana dawoma kika kasa gane kaina…”
Koba komai Mubee ta tausaya wa Atif sosai,amma se tace “Ka dena cewa laifinane Ya Atif saboda kai kanka kasan bason aurenmu nake yiba dan haka koma me nayi banyi tunanin zaka zargeni ba.”
“Ya Atif kai kanka ka sani ko a musulunce an hana aure dole danni wlh auren dole aka min da kai,yanzu ina amfanin auren dolen? Iyaye da dama suna wannan kuskuren akan ‘ya’yansu wasu dan kwad’ayin abin duniya wasu kuma dan hangen wani abu amma ni ina ganin alhakin Ya Farhan ne ya kamamu sabida sam ba’a mishi adalci ba wlh,nizan tafi gida.” Ta k’arashe maganar tana kuka sosai itama.
“Please Sis Mubee karki min haka please,naji duk abinda kikace kuma hakane amma yanzu kizo muje zan kaiki gida da kaina please Sis Mubee?”
Tausaya mishi tayi dan haka yana r’ike da hannunta ta bishi har gun motan ya bud’e ta shiga sannan shima ya shige suka tafi.
Tambayan shi takeyi “Wai ina zamu jene Ya Atif?”
“Kiyi hak’uri Sis Mubee gun Doctor zamuje domin ya gwadaki,addu’ata shine naki ya kasance negetive idan hakan ya faru zan barki kije ki auri Farhan tunda shine zab’inki.”
Hawayene masu zafi suke bin kumatun sa yayinda yake gogewa da hannunsa yana driving cikin tashin hankali.
Mubinat ta rikice gabad’aya dajin kalamansa,koda wasa bata tab’a tunanin Atif zai fad’a mata hakaba.
Farhan kuwa bayan an dubashi ne aka bashi magani sannan Doctor yace “Ka dena yawan sa damuwa a ranka,dan inba hakaba zai haifar maka da babban matsala na ciwon zuciya.”
Kamar zasuyi tambaya akan Atif dayake Family Doctor’n sune se kuma sukayi shuru suka wuce.
Sun tafi bada jimawaba sega su Atif,kai tsaye suka wuce ciki babu b’ata lokaci Doctor ya d’ibi jinin Mubee ya fita.
Atif ya kasa zama yanata yawo a tsakiyan office tare da shafar sumar kansa.
Ita kuwa Mubee bazata iya daurewaba,dan haka ta tashi taje har inda yake “Ya Atif?” Ta kira sunanshi a hankali
Juyowa yayi yana kallonta batare daya ce mata komaiba. Shigewa jikinsa tayi tana kuka “I’m sorry Ya Atif,kayi hak’uri da abubuwan dana gaya maka d’azu rainane ya b’aci shiyasa.”
Idanunsa ya goge sannan ya kamata da hannayensa biyu “Bakomai Sis Mubee,har abada bazaki tab’a yin laifiba a gurina komai kikayi ni agurina dai-dai ne,ban saniba ko k’aunar da nake mikine ya janyo hakan.”
Kuka sosai kalaman sa suka k’ara sata,dan haka ta kasa cewa komai tana kwance a jikinsa yayinda ya rungumeta sosai yana k’walla.
Farhan ne d’auke da waya ya kira Abdullahi yana cewa “Abdullahi ina so ka nemamin yarinya dai-dai ni ko kuma ince kamar Habibty,hakan shi zaisa tunani ya ragu a zuciyata,dan Doctor ya tabbatar min da cewa ina dab da samun ciwon zuciya wanda nasan k’aunar Habibty ne ya janyomin hakan.”
“Kana nufin ka shirya yin aure kenan?” Cewar Abdaullahi
“Haka nake tunani nima,inaga yin hakanne zai ragemin k’aunar Habibty,sedai ban saniba ko ita yarinyar zata samu hankalina a matsayina na mijin ta?”
“Please camn down Farhan,everything will fine okay?”
“I hope so too,byee.”
Koda farhan ya katse wayan tunani ya shigayi wata rana shida Mubee tana kwance a parlour Umma tana bacci ya shigo da sallamarsa amma seyaji shuru.
Yana shiga ya hango wani abu farin kipe akan k’irjinta,a hankali yasa wayansa ya d’an turo farin abun batare daya tab’a jikintaba abun ya fad’o a k’asa,kodaya duba se yaga hoton sane.
Mamaki sosai yayi da ganin hakan dan a wannan lokacin basu fara soyayya ba. Motsin dayaga tayine yasashi komawa can bakin k’ofa tare da b’oye hoton a bayansa.
Tambayar kansa yakeyi “Ya akayi Sister Mubee ta samo hotona?”
Bud’e ido tayi tare da mik’ewa tsaye tana goge ido “Ya Farhan sannu da zuwa”
“Yawwa Shureim fa?”
“Kafin inyi bacci dai na barshi yana game anan.”
“Ok tose anjuma”
“Yawwa Ya Farhan an bani sak’o daga Islamiyya akace in baka”
“Ok ina sak’on?”
D’aki ta shige sannan ta d’auko wasik’an ta mik’a mishi.
“Base na karb’a ba,ki karanta ina sauraron ki”
Ahankali ta bud’e ta fara kararu kamar haka.
_Assalamu Alaikum Malam Farhan,da fatan kana lfy?_
_Agaskiya Malam Allah ya jarabceni da k’aunarka ta yadda bazan iya misaltashiba,ina fatan zan samu amsa mai dad’i daga gareka._
_Na barka lfy,daga masoyiyarka Khadija Abbas…_
Mubinat tana gamawa ta kalli Farhan,shima kuma ita yake kallo.
“Ya Farhan sak’on kenan.”
“Ok,tona gode amma kibata hak’uri domin yau na samu matar da zan aura”
“To yanzu dai mezan ce mata?”
“Abinda na gaya miki,da sak’onta yazo kafin minti biyar dana amince mata,amma ta makara domin kuwa wata ta rigata” ya k’arasa maganar yana dariya.
“Amma fa Ya Farhan nace mata baka da budurwa anan garin sedai ko’a can Madina shine ban saniba”
“Eh gaskiya kika gaya mata ai,nima bai wuce minti biyar da suka wuce bane na samu matar aure,Iyayenta kawai zan sanar sannan in sanar da ita yarinyar”
“To Allah ya sanya alkhairi na tayaka murna”
“Ameen thankyou.” Sannan ya wuce ya barta a tsaye tana tunanin wace yarinya ce kuma Ya Farhan ya samu? To Allah dai ya sanya alkhairi koma wacece.
Shi kuwa Farhan d’aki ya dawo Shureim yana kwance,ganin shigowar shine ya mik’e
“Ya Farhan kaga hoton ko?”
“Na gani,amma yaushe Sisyer Mubee ta shigo d’akina harta d’auka min hoto?”
“Ai tana gyara muku d’aki inaga anan ta d’auka”
Ajiye hoton yayi sannan ya wuce toilet.
Shureim yayi tsalle yace “Na had’a soyayya, soyayya, soyayyaaa…”
K’walla Farhan ya share daga idanunsa bayan ya dawo daga tunani.
Ahmad ya shafi kafad’arsa yace “Haba Abokina ka daure mana”
“Tunba yauba abinda naketa k’ok’arin yi kenen Ahamad,amma inaga bazan iya bane.”
Amal dai shuru tayi tana saura ronsu batace komaiba har suka iso gida.
Doctor ne ya shigo da peper a hannunsa,kunya sosai Mubee taji dan yadda yazo ya tatdasu rungume da juna.
Shi kuwa Atif ko’a jikinsa yana rik’e da hannunta suka taho gun Doctor.
“Doctor me result d’in Mubee ya nuna?” Cewar Atif hankalinsa a tashe.
“Atif result nata ya nuna negetive ne a yanzu,but na gaya maka baza muyi murnaba harse anyi mata test sau uku kuma duk bayan 3month ne zakuzo ayi,idan result d’in k’arshe ya nuna negetive tose muyi murna kamar dai yadda na maka bayani.”
“Bakomai Doctor mungode sosai,insha Allah sauranma duk negative zai zama,yanzu babu wani magani da zaka bata kenan?”
“Eh gaskiya babu harse munga result munsan me take ciki,amma please kaikam ka tabbatar kana shan naka maganin don yana taimakawa sosai.”
“Hmm,mungode Doctor amma ai nagaya maka cewa shan maganina bayi da amfani,muje Sis Mubee.”
Doctor ya kalli Mubee yace “Ki tabbatar da yana shan maganinsa akan kari,dan yace bazai sha maganiba tunda hakan ya faru dashi,a tunaninsa zaki gujesane dan haka yake ganin cewa rayuwarsa bata da amfani indai baya tare dake.”
K’walla ta farayi tare da cewa “Thankyou Doctor,kuma insha Allah zaisha maganinsa mun gode sosai.” Sannan tayi saurin bin bayan Atif danya dad’e da ficewa waje.
Zaune yake cikin mota ya had’a kai ta siteri duk abin duniya ta dameshi.
Bayan ta shiga ta zauna ne ta kam’o hannunshi “Ya Atif,kayi hak’uri dan Allah,ka manta da alk’awarin dana maka? Ako wace irin haline bazan tab’a rabuwa dakai ba muna nan a tare.”
Murmushi yayi tare da share hawayensa yace “Thanyou Sis Mubee” sannan ya ja mota se gidansu.
Kallonsa takeyi tare da tambayarsa “Meyasa ka kawomu gidan Abba kuma?”
“Sis Mubee yana da kyau in sanar dasu Abba halin da nake ciki kafin mu koma gidanmu.”
Yana kaiwa nan ya fice daga motar Abba yana kallo a parlour tare da Umma.
Bayan yayi sallama sun gaisa ne yace “Abba ga Sis Mubee zataci gaba da zamanta anan har tsawon wata tara kafin insan me nake ciki,Abba karka tambayeni dalilin hakan Ya Musty zaizo yayi muku bayani anjuma.” Yana kaiwa nan ya fice lokacin Mubee tana k’ok’arin shigowa parlour se suka had’u a bakin k’ofa.
“Ina zakaje Ya Atif?”
“Zanje in duba Farhan ne ki shiga ina zuwa.”
Babu musu ta shiga jikinta a sanyaye. Ganin ta shigene yasashi yin sauri ya shige motarsa tare da barin cikin gidan…