KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 7
ASALIN LABARIN
Alhaji Bakari sanannan mutum ne sosai a garin Gombe,sabida arziki da Allah ya bashi.
Matarsa d’aya ce tak mai suna Hajiya Aisha. Yaransu ukune kacal a duniya,Maza biyu da kuma Mace.
Muhammad shine babban d’ansu na miji,se kuma Abdullahi,sannan Amina itace autarsu.
Haka suka tashi cikin gata da samun kulawa agun iyayensu har suka girma.
Kansu a had’e yake dukkansu,kuma suna son junansu sosai.
Shi Abdullahi ya fisu sakewa sosai da mutane,hakan yasa shiya fisu jama’a inda ya had’u da wani mai irin sunanshi shima Abdullahi har suka k’ulla abota sosai kowa yasan da zaman abotarsu harma aka zama kamar ‘yan’uwa duk familys ansan juna sosai ana zumunci mai k’arfi.
Wata rana aka tashi da rashin mahaifinsu wato Alhaji Bakari. Babu ciwo babu komai kwanane kawai ya k’are.
Matarsa Hajiya Aisha da yaransa ukun sun shiga wani irin hali na rashin Mahaifi sosai.
Bayan anyi arba’inne aka raba musu gadonsu inda suka samu kud’ad’e masu yawan gaske da gidajen mai da manyan filaye.
Dukkanninsu sunyi karatun boko mai zurfi. Haka sukaci gaba da zama tare da mahaifiyarsu har suka kammala karatunsu. Dama shi Abdullahi aboki suna gama secondary school ya samu kyautar karatu wani uncle nashi ya biya mishi acan Madina,inda shine sanadiyan rabuwansu da amininsa Abdullahi Bakari,amma koda yaushe suna manne a waya.+
Lokacin da dukkansu suka gama kararune shi Babban Yayansu Muhammad yayi aure tare da matarsa jamila. Shi kuwa Abdullahi ya auri Maryam duk a cikin garin gomben. Ita kuwa Amina a Yola tayi aure inda take zaune lafiya har Allah ya bata ciki lokacin haihuwa Allah ya karb’i abinsa,daga ita har babyn’ta suka rasu.
Bayan rasuwarta da shekara d’aya Jamila matar Muhamma ta haifi d’anta na miji mai suna Mustapha,ta sake haifan Abdulhamid sannan Mijinta ya sake k’ara aure inda ya auri bafulatana a cikin gomben mai suna Khadija.
Shi kuwa k’aninsa Abdullahi har yanzu shuru Allah bai bashi haihuwa ba,inda abokai suketa bashi shawaran ya k’ara aure amma sam yak’i saboda yana son matarsa sosai suna zaman lafiya.
Abokinsa Abdullahi dake Madina kuwa acan ya samu wata balarabiya suna son junansu matuk’a dan tare suke karatu acan Madinan. Koda yazo mata da magan aure ta sanar da iyayenta amma sam sukak’i amincewa wai bazasuba d’an Nigeria auren ‘yarsu ba.
Salma Taimoor ‘yar wani Attajiri ne sosai a k’asar Madina,dan kaf familynsu ma manyane suke aurensu acan d’inma.
Haka dai akaita fama da iyayen Salma,ita kuwa tace sam babu wanda take k’auna se Abdullahi.
Ganin babu yadda suka iyane yasa akayi musu aure,da yake shima Abdullahi ba laifi suna da hali suma amma an kafa mishi dokoki kan cewa ‘yarsu salma bazatayi nisa dasuba dan haka suka mallaka musu tapkeken gida a garin Madinan acan suke zaune lafiya da matarsa.
Lokacin da khadija matar Muhammad ta haifi d’anta namiji mai suna Ra’is da kwana biyu Salma matar Abdullahi ma ta haifi d’anta mai kama da ita wato Farhan.
Tun daga lokacin shi Abdullahi Bakari ya shiga damuwa ganin har yanzu Allah bai bashi haihuwa,dan haka sukaje gurin Doctor domin a dubasu ko matsalar daga garesune. Bayan an gama dukkan gwaje gwajene sakamako ya fito cewa dukkanninsu lafiyarsu k’alau babu mai matsala a cikin su.
Jin hakanne yasa Abdullahi da matarsa hankalinsu ya kwanta,yayi alk’awarin bazai k’ara aureba tunda dukkansu lafiyarsu k’alau.
Haka dai sukaci gaba da zamansu cikin soyayya,da kusan shekara uku sannan khajida ta sake haifan d’anta namiji mai suna Atif.
Wannan yaro yaga gata kamar shine na fari a gunta,idan ka ganshi bakace d’ansu bane dan daban ya fita da sauran yaran.
Lokacin tafiya Umrah Abdullahi da Matarsa Maryam tare suka tafi daga can suka ziyarci gurin Amininsa Abdullahi Abban Farhan.
Maryam tana ganin Farhan seta fashe da kuka sabida yadda take son haihuwa amma Allah bai basuba har yanzu,satinsu guda agun amininsa sunyi zaman dad’i sosai gashi itama matar tashi akwai fara’a a d’an wannan kwanakin suka saba sosai har suka dawo Nigeria.
Su Farhan suna da shekara goma sha uku shida Ra’is inda Atif kuwa yakeda shekara goma a duniya Maryam matar Abdullahi ta samu ciki.
Murna agunsu baya misaltuwa duk wani son duniya an d’aurawa cikinnan,hakama k’awarta aminiyarta zainab ita se’a lokacin tayi aure dan ta tsaya karatu tana aure ta fara aikinta kud’i sosai take samu dan tama fi mijin nata arziki.
Cikinsu yana da wata hud’u suka gama sayayyan komai da komai da za’a buk’ata sudai kawai haihuwan suke jira yazo.
Ita zainab k’awartan bata fiye shiga harkan mutane ba,amma tana da son jama’a sedai duk cikin k’awayenta tafi son Maryam sun shak’u sosai.
Haka akaita renon ciki,su Atif kuwa sunata karatu har cikin yakai watan haihuwa anan ne Maryam ta haifi ‘yarta mace son kowa k’in wanda ya rasa taci sunan kakarta Hajiya Aisha inda ake kiranta da Mubeenat.
Hmm! Bazan iya bayyana muku irin gata da wannan ‘yar tashaba,saboda kaf dangin babu ‘ya mace se ita kuma dama an dad’e ana fatan Abdullahi ya samu ‘ya ko d’a a duniya se gashi an samo mace.
Hakanne ma yasa Atif ya Fara kiranta da Sis Mubeenat dan yana son yara tun tashinsa. Bayan wata d’aya k’awarta zainab ma ta haifi ‘yarta mace mai suna Amal,itama dai tasha gatan sosai.
Suna da wata takwas Mahaifiyar su Atif ta sake samun ciki inda ta haifi macen itama aka sa mata sunan kakanta Aisha wanda hakan ake kiranta da shi har yanzu.
Tun daga lokacin babu wanda ya sake haihuwa a cikinsu dama ita Mahaifiyar su Ya Musty kam ta gama haihuwar ta,itama kuma Mahaifiyar su Atif ta gama.
Ita dai Maryam Umman Mubeenat tana so ta sake wani haihuwan amma shuru har seda Mubeenat takai shekara sha uku kafin ta sake sanun ciki inda ta haifi d’anta namiji mai suna Shureim.
Tana cikin jegonsane sark’ewar hak’ori ya kamata wanda shine sanadiyarta na barin duniyar. Idan kaga mubeenat dole ka tausaya mata saboda sun shak’u sosai ga soyayya da kulawa da ake nuna mata.
A lokacin ne Amininsa Abdullahi sukazo Nigeria tare da Matarsa Salma Taimoor da kuma d’ansu tilo wato Farhan.
Koda yaga Mubeenat tana kuka seyaje kusa da ita yana mata maganan cikin harcen larabci ko kallonsa bata yiba. Nan ya tuna da abinda Abi nasa ya gaya masa “Idan mukaje k’asarmu hausa zaka dinga yi musu tunda na koya maka kaji?”
Nan yace da ita “Meya faru kike kuka?”
D’agowa tayi tana kallonshi cikin mamaki “Kai waye?”
“Farhan”
“Daga ina kake?”
“Daga Madina muka zo da abi na gaisuwan rasuwa”
Nan ta sake fashewa da kuka inda Farhan ya rud’e tare da rik’o hannunta “Kiyi shuru ki dena kuka zan baki choculate na kawo miki dewa”
“Ka sakeni bana son choculate d’in kanaga Ummana ta rasu ta barni ni yanzu bani da Umma”
Tausayinta ya kama Farhan nan ya rik’o hannunta zo muje in baki kyautan Ummi na kina so?”
Kai ta d’aga mishi alamun eh. “Toki shiga ciki ki dena kuka zakiga wata mai kama dani kice mata Farhanne ya turoki”
“To” sannan ta wuce yana binta da kallo…Koda ta shiga kuwa gurin Salma Taimoor ta wuce “Ina wuni?”
“Lafiya Mubeenat right?”
“Kai Mubeenat ta d’aga mata alamun “Eh”
Nan take Salma ta rungumeta tana rarrashinta cikin harcen turanci hartayi shuru nad’an wannan lokacin ganin Amal da mamanta sun shigone yasa ta mik’e tayi gunsu.
Nanma dai kukan sukai tayi su biyu.
“Mubeenat” muryan Ya Musty taji
“Na’am”
“Ku dena wannan kukan kunji,addu’a Umma take buk’ata agunki ba kuka ba,duk wani mamaci baya buk’atan kuka se addu’a domin kukanki azaba yake k’ara mata kinji?”
“To” tace dashi sannan suka wuce d’akinta ita a Amal sukayi alwala tare dayin sallah sunata mata addu’a.
Haka dai akaci gaba da zaman makoki harna tsawon kwana uku sannan aka watse amma banda ‘yan’uwan Mubeenat.
Dama akwai k’anwar mahaifiyar tasu mai suna Rabi kuma batayi aureba,dan haka Abban Mubeenat ya nemi da abashi aurenta kodan jaririn da aka bari wato Shureim.
Haka kuwa akayi,bayan kwana arba’in aka d’aura musu aure inda ta tare, tare da rik’e ‘ya’yan yarta tamkar nata wanda ita ce dai Umma da kukeji a baya.
Zuciya d’aya ta rik’esu babu wani abu sannan suna zaman lafiya sosai kamar dai yadda suke da mahaifiyar su Mubeenat.
Ita ta rik’e Shureim tayi renonsa tun bai cika wata biyu ba.
Se’a wannan lokacinne Farhan ya damu iyayensa dasu koma can k’asarsu,amma Umminsa tak’i sam wai Nigeria ya mata dad’i dan haka sukaci gaba da zama abinsu inda ya zauna a gidansa na Nigeri.
Farhan dai k’asar ta ishesa badan sun soba haka suka tattara suka koma.+
Gidan su Mubeenat da Amal babu nisa ko kad’an,hakan yasa iyayensu suka sake k’ulla k’awance dama kuma can ita Mahaifiyar Amal d’in tasan Rabin tunda k’anwar k’awarta ce marigayiya.
Haka sukaci gaba da zama wani sabon alak’ane sosai ya k’ullu musamman da ‘ya’yansuma suka sake zama k’awaye Mubeenat da Amal.
Haka ake tare dukka kaman ‘yan’uwa,ko gidan Uncle Muhamma Mubeenat zataje yini toda Amal suke tafiya a hakanne ma suka saba da Aisha k’anwar Atif sosai duk suka zama k’awayen juna kusan kullum a tare zaka gansu.
Makaranta ma dama Mubeenat da Aisha makaranta d’aya suke,dan haka Amal ma tace a sata agunsu Mubeenat,dayake Mahaifiyarta tana da hali shikenan aka had’asu kullum Abba shine mai kaisu ya d’auko su,wata rana kuma idan Atif yaje d’aukan Aisha seya d’aukosu ya sauk’esu a gida sannan su wuce.
Sunada k’awaye sosai acan suka had’u da Aisha Kabir haka zasuyita yawo a school kamar ‘yan hud’u.
Ya Musty ya gama karatu inda yake aikin Banki,shi kuwa Ya Abdulhamid tunda ya samu aiki da wani kampani suketa canja mishi gurin aiki yanzu haka US aka turashi hakan nema yasa Mahaifinsu yace lallai sedai yayi aure kafin ya tafi.
Biki akayi gangariya ya tafi tare da matarsa can.
Ya Ra’is kuwa dama shine miskili a gidan,a fanni Arabic yake karatunsa acan Egypt,se lokaci-lokaci yake zuwa ganin gida,baya barinsu Aisha da Mubeenat su sake sam indai yana gari gashi baya shiga harkan mutane amma ya takura musu sukam.
Ana hakane auren Ya Musty ya tashi shagali sosai akayi su Mubeenat anyi ado ansha kyau amma koda Ya Ra’is ya gansu cewa yayi su koma bazasu jeba,nan take Aisha ta fara kuka ta wuce ta gayawa Mummy’n su,Atif yana jin haka yace “Ku k’yaleshi sedai ya ganku acan,ku zauna ku jirani zanje na dawo semu tafi.”
Harda Amal haka Ya Atif ya dawo bayan ya kai mutane yazo ya kwashesu segun dinner.
Ab’oye suke shagalinsu wai dan kar Ya Ra’is ya gansu,ai kuwa seda ya gansu amma baice dasu komaiba agun haka aka gama shagali sune na farko da Ya Atif ya fara mayarwa gida sannan yace “Sis Mubeenat ku jirani idan na gama kai mutane zanzo sena maidaku gida kinji?”
“To bakomai seka dawo”
Ai kuwa bayan tafiyar sane sega Ya Ra’is da belt nashi lokacin Amal tana toilet nan ya shiga zubawa Aisha da Mubeenat “Wato kun rainani kenan ko,ince bazakujeba shine kukaje dan baku da kunya,na zama sa’anku ko!
Kuka suke suna cewa “Wayyo Ya Ra’is kayi hak’uri wlh bazamu sake ba”
“Kun rainani ko,wlh daga yau bari na sake ganin kunje wani program na biki zaku gamu dani kuna k’ananan yara wai har kunsan kuje wani dinner ko baku jiba?” Ya tambayenu cikin d’aga murya
“Munji wlh bazamu sakeba kayi hak’uri”
Sannan ya dakata da dukan nasu ya kalli Mubeenat “Anan zaki kwana?”
Cikin muryan kuka tace “A’a”
“To muje in kaiki gida”
“Amal ta shiga toilet ita nake jira”
Se’a lokacin Amal ta bud’e k’ofa duk tsoro ya cikata ta fara tafiya a hankali kanta a sunkuye.
Nan Ya Ra’is ya nufota “Harda ke ko,zomin nan.”
Duk cikinsu Amal tafisu tsoro duka dan haka ta kalli Mubeenat tana komawa da baya “Ya Ra’is dan Allah kayi hak’uri wlh banda lafiya”
“Bakida lafiya kikaje biki,kizo nan nace”
Nan Amal tasa kuka tana bashi hak’uri yayinda take kiran Mubeenat sabida tsoron bulala.
Cikin k’arfin hali Mubeenat ta mik’e zuwa gaban Amal ta tareta tana bawa Ya Ra’is hak’uri.
“Dan Allah kayi hak’uri wlh bata da laifi ninace tazo muje kuma da gaskene bata da lafiya wlh”
“Zaki karb’a mata dukan kenan?”
Kanta take girgizawa “A’a Ya Ra’is dan Allah kayi hak’uri mun tuba wlh bazamu sakeba Allah”
“Tausayin Mubeenat yaji dan haka ya juya ya fice tare da cewa “Ku fito in kaiku gida”
Hawaye suka share tare da d’aukan jakansu suka wuce Aisha tana cewa “Mubeenat Amal dan Allah kuyi hak’uri kunji?”
“Bakomai Aisha semunzo gobe” cewar Mubeenat sannan suka wuce gun motar.
Shida abokinsa ne a cikin motan,har zasu shiga seka Ya Atif daga nesa ya hango su.
“Sister Mubeenat,zaku tafi ne?”
“Eh seda safe”
“Wazai kaiku gida?”
“Ya Ra’is ne”
“Ok to shikenan gobe zanzo in d’aukeku a gida kigaida Umma”
“Zataji” sannan suka wuce baya ita da Amal.
Atif yana shiga Aisha ta fashe da kuka tare da rungume shi.
“Aisha meya sameki?”
“Ya Ra’is ne ya zanemu nida Mubeenat wai dan munje gurin dinner,tana ta kuka yanzu suka tafi”
“Ya zane ku?”
“Eh da belt nashi”
Ran Atif in yayi dubu seda ya b’aci nan ya saki Aisha yaje gun Daddy’n su “Daddy kayiwa Ra’is magana wlh karya sake dukan Aisha da Sister Mubeenat,wai kawai dan yace bazasuje gurin dinner ba ni kuma na d’aukesu muka tafi shine wai ya zanesu yanzu harda Mubeenat marainiya cefa ita Daddy kuma ai naga bikin Yayansu ne.”
“Zanesu yayi?” Daddy ya tambaya
“Eh da belt,wlh Daddy kayi mishi magana Allah bazan sake bari ya dakesu ba tunda ba wani laifin azo a gani sukayi mishi ba.”
“Shikenan zan sameshi ina Mubeenat d’in?”
“Ta koma gida”
“Badamuwa kayi hak’uri”
Sannan Atif ya fita rai a b’ace Daddy yana binsa da kallo.
Tun Mubeenat tana k’arama Atif yake ji da ita dan itace kad’ai k’anwarsu mace har goyonta yanayi Ummanta marigayiya tayita dariya shikuwa ko’a jikinsa renonta yake sosai tun bata san kanta ba shiyasa baya son duk wani abu dazai tab’ata.
“Sister Mubeenat bazaku gaida abokina bane?” Cewar Ya Ra’is.
A tare suka had’a baki “Ina wuni?”
“Lafiya ya kuke?”
“Lafiya” sannan duk sukayi shuru inda su kuwa suketa hira har suka isa k’ofar gidan su.
Dukkansu suka fito daga motar inda Ra’is ya kalli Mubeenat “Kema anan zaki sauka?”
“Eh zan rakata cikin gidansu sannan in wuce”
Fitowa yayi daga cikin motar yace “Muje”
Ba musu sukayi gaba yana binsu a baya har suka kai Amal bakin gate nasu sannan suka juyo.
“Sister Mubeenat?” ya kira sunanta
“Na’am”
“Kiyi hak’uri kinji,kuma karki gayawa Abba ko Umma cewar na dakeki pls”
“To” tace dashi suna takowa har bakin gate sannan ya sake cewa “Kin ji?”
“Eh bazan fad’a musu ba”
“Ok zakizo yini gobe ne?”
“Eh zanzo”
“Da yaushe zaki zo sena zo na d’aukeki?”
“Ya Atif yace zaizo ya d’aukemu tare da Umma zamu zo”
“Alright please kiyi hak’uri and idan nayi miki magana ki dinga ji kinji?”
Kai ta d’aga mishi alamun taji batare datayi magana ba.
“Sister Mubeenat are you angry at me?”
“No” ta bashi amsa a hankali
“Are you sure?”
Kallon shi tayi tana murmushi “Yes”
Shima murmushin yayi tare da knocking gate d’in sega maigadi yazo ya bud’e inda Mubeenat ta shige ta barsu suna gaisawa.
D’akin Umma ta wuce kai tsaye,kuma bata gaya mata cewa an dakesu ba.
Bayan ta gamayiwa Shureim wasane sannan ta wuce d’akinta ta watsa ruwa seta kwanta tana tuna yadda sukayi da Ya Ra’is.
“Yau wai Ya Ra’is ne yamin wad’annan maganganun,shida ko gaishesa kayi kamar bazai amsaba dan miskilanci shine har yana bani hak’uri tare da tambayar koyazo gobe ya d’aukeni?”
“Koda yake shima yasan bai kyauta bane ai sabida ba wani laifi mukayi mishi ba dazai dakemu”
“Allah ya kaimu gobe inbawa Aisha labari nasan zatayi mamaki k’ilama ta k’aryata ni…”
Washe gari da safe Umma ta shirya kanta sannan ta shirya Shureim inda Mubeenat ma ta shirya tare da wucewa gidan su Amal dan taga kosun shirya.
Tsaf suka shirya ita da Mahaifiyarta “Umman Amal ina kwana”
“Mubeenat,lafiya k’alau ya Ummanki da Shureim?”
“Lafiyansu k’alau muma mun shirya”
“Amal kinyi kyau”
“Hmm ina kyau d’in,kinaga Umma tace wai kada nayi kwalliya wai nafi kyau a haka”
“Sosai ma kuwa ai shiyasa nace miki kinyi kyau”
“Ba wanin nan”
“Wlh kuwa da gaske ai natural face naki yafi miki kyau.”
Haka sukaita hira sannan suka fito dukkansu suka nufo gidansu Mubeenat.
Bayan d’an gaishe-gaishe da akayine Umma tace kawai mubi su Amal mu tafi in yaso Atif ya dawo damu tunda nasan Umman Amal baza sukai dare ba.
Haka kuwa akayi su Umma ne a gaba su Amal kuwa suna daga baya rik’e da Shureim a hannunsu.+
Isar su ne aka taresu da kunun gyad’a da kuma taliya wanda yaji kayan had’in sosai.
Nan su Mubeenat sukayi d’akin Aisha da Shureim a hannunsu tana basu labarin yadda sukayi da Ya Ra’is a daren jiya.
Mamaki sosai sukayi dajin yadda ta kasance tsakanin Ya Ra’is da Mubeenat.
Jin muryan Yayyun sunne yasa Aisha fita da gudu ta kamo hannun Ya Atif.
“Aisha har kin shirya ne?”
“Eh ina zaka haka?”
“Gidan Uncle Abdullahi zanje in d’anko su Umma ne”
“Ai sun iso,tare da Umman Amal suka zo yanzun suna ciki”
“Haba ina Sis Mubeenat?”
“Tana d’aki na”
Nan ya kamo hannun Aisha suka wuce d’akinta.
“Ya Atif wannan gayu haka,ina kwana?”
Murmushi yayi “Lafiya Sis Mubeenat yanzu kuwa dama zanje d’aukoku se Aisha tace min kun iso”
“Eh wlh kaga shikenan ka huta sedai ka kaimu yawo zuwa anjuma”
“I promise kuwa zan kaiku”
“Ina kwana Ya Atif?”
“Amal kina lafiya ya Umma da Baba”
“Lafiyansu lau”
Shureim ya karb’a a hannun Mubeenat tare da cewa “Ooh fine boy,Sis Mubeenat sorry naji abinda Ra’is ya muku jiya kiyi hak’uri kinji?”
“Haba Ya Atif aiba komai,mai sonka ne zaiyi maka fad’a idan kayi ba dai-dai ba wlh ba komai ya wuce.”
“Hakane,bari naje da Shureim idan ya fara kuka zan dawo dashi”
“To shikenan” sannan ya fita.
“Hmmm Aisha kinji dad’i wlh” cewar Mubeenat inda Atif bai gama barin k’ofar d’akinba seya tsaya domin yaji abinda Mubeenat zata ce.
“Dad’in me Mubeenat?”
“Kina da Yayyu dewa gashi duk suna sonki da kulawa dake yadda ya dace,inama da ace nima ina da Yaya danaji da’i.”
“Haba Mubeenat ai kema Yayyun kine kuma duk suna sonki”
“Aisha baki gane me nake nufiba,ina so ya zamana cewa nima akwai wani Yayana da muke zaune dashi a gidan mu,kullum ya d’aukeni mu fita yawo ya kaini gun friends nawa ya kaini school ya kuma d’aukoni hakan ba k’aramin farin ciki zai sani ba.”
“Indai wannan ne to karki damu zan gayawa Daddy abinda kikace seya bawa Uncle Abdullahi Ya Ra’is ya koma gidanku da zama”
“Ya Ra’is kuma,gaskiya ni tsoron shi nake ji,bayida son dariya da wasa kamar Ya Muhammad Ya Abdulhamid da kuma Ya Atif,gaskiya imma za’a tambayeni toni Ya Atif nake so ya dawo gidanmu da zama don duk cikinsu yafi sona sannan nima duk cikin Yayyuna nafi son shi.”
Atif yana tsaye yana sauraron hiransu daga nan ya wuce yana murmushi tare da tunanin maganan Mubeenat.
Haka akai yinin biki lafiya zuwa bayan la’asar Amal da Ummanta suka koma.
Su Mubeenat kuwa harse bayan isha Abba da kansa yazo d’aukansu.
Suna cikin tafiyane a mota Mubeenat tace “Abba nima ina son Yayana d’aya ya dawo gidanmu da zama nima in zama mai Yaya”
“To Mamana yanzuma ai kina da Yayyu gasu nan dewa se wanda kika zab’a”
“To Abba ka dawo da d’aya cikin gidanmu mana wlh ina son in zauna da Yayana nima kamar Aisha”
Wayan Abba ne ya fara ringing ya d’auka tare da sallama “Mutanen Madina”
“Ya kuke ya hidima da iyalai ina ‘yata da d’ana?”
“Alhamdulullah gamunan muna hanyan komawa gida mun fito yinin bikin kenan,ina nawa d’an Farhan?”
“To Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya ga d’anka nan zaku gaisa”
“Assalam Abba”
“Wa’alaikumus salam Farhan my son,ya kake ina Ummi?”
“Alhamdulillah Abba ya Mubeenat?”
“Mamana tana lafiya dama yanzu kuwa take cewa tana son d’aya daga cikin Yayyunta ya dawo gidanmu da zama wai ita bata da Yaya a gida”
“Really Abba,tell her that I’m coming for her”
“Hhh okay I will,how is Ummi?”
“She’s fine,can I talk to Mubeenat?”
“Sure my Son” sannan ya mik’awa Mubeenat tare da cewa “Toga Yayanki na Madina zaku gaisa”
Murmushi fal akan fuskarta ta karb’i wayan tare da cewa “To Abba” sannan tasa a kunnenta “Hello”
“Assalamu Alaikum Mubeenat”
“Wa’alaikumus salam,how are you Brother?”
“Well I’m good and you?”
“I’m good also how is Ummi?”
“Ummi is fine,she’s always talking about you,I think she Love’s you so much”
“Really?”
“Yeah,when are you coming to Madina?”
“Ooo I don’t know Ya Farhan,but I will ask Abba okay?”
“Okay my regard to Ummi and… Sorry I forget the name”
“Shureim”
“Yeah Shureim,give my love to him okay?”
“I will,thankyou Ya Farhan”
“You’re welcome, ma’assalam”
“I don’t know what to say Ya Farhan,will you teach me how to speak arabic?”
“Sure,you say bissalam”
“Alright,bissalam Ya Farhan”
“Hhhh okay,Mubeenat how old are you?”
“I’m 13years old”
“13,are you sure?”
“Yeah i’m 13”
“Masha Allah”
“And you Ya Farhan?”
“I’m 23 Mubeenat”
“Okay,ma’assalam”
“Bissalam” sannan ta mik’awa Abba waya sukaci gaba dayin hira sannan ya mik’awa Abbi nashi wayan.
“Abokina ina so zamu zo Nigeria mu bud’e wa Farhan wani campani ne saboda munyi magana sosai da kakanan sa sun nemi shawarata a matsayina na Mahaifinsa,shine na basu wannan shawaran inaga za’a samu nasara sosai idan hakan ya kasance amma meka gani kai?”
“Tabbas wannan shawarace mai kyau sosai sedai muyita addu’a Allah ya tabbatar mana da alkhairi akan hakan”
“Ameen ameen nagode sosai zanzo nima insha Allah idan komai ya kammala domin fara shirye-shirye”
“Toba damuwa Allah ya wuce mana gaba,Allah kuma yasa albarka aciki”
“Ameen nagode seka jini”
“To shikenan agaida kowa da kowa” sannan Abba ya katse wayan yana gayawa Umma duk yadda sukayi da amininsa.
Farin ciki sosai Umma ta nuna tare da musu fatan alkhairi.
“To yanzu wa zasu nad’a anan d’in?” Cewar Umma.
“Eh to tukunna dai,seya zo maji yadda abin zai kasance,kinga ai zan samawa mutane da dama aiki a wannan campanin”
“Wlh kuwa,Allah dai ya tabbatar mana”
“Ameen” suka amsa dukkansu sannan sukai ta hiransu har suka iso gida.
Washe gari da safe Atif da Aisha suna breakfast se yake cewa “Aisha naji hiran da kukeyi da Sis Mubeenat jiya”
“Da gaske Ya Atif,tome ka gani akai?”
“Eh Sis Mubeenat taban tausayi gaskiya,dan haka yadda ta fad’a haka za’ayi”
“Ban ganeba Ya Atif,waye zai koma gidan Uncle Abdullahi da zama kenan?” Ta k’arashe maganar tare da ajiye spoon d’in abincin dake hannunta tana jiran amsar shi.
Shi kuwa Atif ya gano k’anwar tasa,dan haka yace “Ra’is mana”
Dariya tayi tare da d’aukan spoon nata taci gaba dacin abinci “Aina d’auka zaka ce kaine da bazan yarda ba,dan bazan yarda kabarni ba”
Atif yasan halin Aisha sosai,dan haka ya b’ullo mata ta nan.
“Ina! Ai muna nan tare babu inda zanje in barki Sweet Sis”
“Hhh amma fa Ya Atif Mubeenat tsoron Ya Ra’is take ji,kasan wai ita tafi son kaika koma gidansu da zama?”
“Haba dai?”
“Wlh haka ta gaya min wai duk cikin Yayyu kafi damuwa da ita sosai sannan itama tafi sonka”
Murmushi yayi Allah sarki Sis Mubeenat,tana bani tausayine tun da Umma ta rasu wlh shiyasa k’aunarta ya sake shiga zuciyata ina sonta matuk’a”
“Kana sonta matuk’a,kana nufin zaka aureta kenan?”
“Hhhhh ba haka nake nufiba small girl,ina sonta kamar yadda nake sonki ai duk ku k’annena ne babu maganar aure a tsakanina daku kinji?”
“Towa zaka aura Ya Atif?”
“Hhhh Aisha tambayar taki tayi yawa,ni gaskiya bani da ra’ayin auran ‘yar Nigeria acan waje zan nemo matar aure”
“Hhhh lallai Ya Atif dama nima nafi so ka auro balarabiya ko ‘yar india dan zakufi dacewa kai kyakkyawa itama haka”
“Hhhhh karki damu haka za’ayi oya kici abinci anjuma semu je yawo ko?”
“To Ya Atif amma zamubi mu d’auki Mubeenat ko?”
“Eh zamubi” ya fad’a yana murmushi tare da barin parlour…