KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 9
Taro ne na manyan mutane dan haka gurin ya k’ayatu sosai,gashi cike yake da sojoji da police sakamakon manyan mutane da suka halarci taron.
Farhan shine wanda ya bud’e wannan taro da addu’a sannan aka fara gabatar da program cikin harcen turanci inda kowa yake sanya albarkacin bakinsa d’aya bayan d’aya.
Harda yaya Atif se dayayi jawabi dan bai samu tafiya wasan k’wallon da zasu jeba.
Anci ansha aka raba sadaka sosai wa mutane bayin Allah,tare da tabbatar wa jama’a cewa duk wasu masu neman aiki daga wanda suka gama degree harda ‘yan secondary da basu samun daman cigaba da karatun suba da suzo wannan company zai taimaka musu su samu abinyi.
Nan fa iyayen yara sukaita murna ana sake sanya albarka a wannan company.
Mubeenat ce ta kira Ya Atif tace “Please Ya Atif ka gayawa Ya Farhan ayi neman taimakon addu’oi agun jama’a kan Umman Amal asata a addu’a.”
“Ok Sis Mubee”
Tana ganinshi ya sanar da Ya Farhan lokacin Abban Mubeenat ne ke magana kawai se sukaji yana magana akan b’atar Umman Amal tare da neman taimakon addu’a agun ‘yan’uwa.
Nan take Amal ta fara k’walla Mubeenat dake zaune kusa da ita ne take rarrashinta daga nan aka rufe taro da addu’a aka fara watsewa.
Mubeenat Amal da Aisha ne kad’ai a motar Ya Atif shi kuwa Shureim yabi su Farhan,su Umma kuwa suna can motar su Abba.+
Bayan an dawo gidane aka sake zama inda Abbi yake sanar da Abba cewa zuwa wani sati zasu koma,amma Farhan ya dawo nan da zama kenan sannan zaici gaba da zamane anan gidan tunda can shi kad’ai ne idan sun tafi.
Dad’in hakan sosai Abba yaji tare da nuna farin cikinsa akan hakan.
Da gudu Shureim ya mik’e yaje inda Farhan yake zaune yace “Ya Farhan shikenan ka zama d’an gidanmu zamu dinga zuwa yawo ko?”
Hhhh akasa dariya yayinda shi Farhan kuwa yayi mishi murmushi tare da shafar kansa yace “Yeah”
Ummin shi kuwa cewa tayi “Habibty kin samu Yayyu biyu kenan”
Cikin jin kunya Mubeenat ta kai idonta gun Farhan wanda shima ita yake kallo har cikin ido gashi ko k’yafta idon bayayi. Hakan yasa taji kunya tare da saurin maida idanunta kan Ya Atif wanda ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa.
Dad d’in Atif ne yayi musu godiya tare da sallama sannan suka wuce da Ya Musty da kuma Hajiyansu se mom d’in Atif.
Dama Aisha kam tace se dare Ya Atif zai maidata gida.
Amal kam tunda suka dawo ta kwanta a d’akin Mubeenat baccinta kawai take sha.
Mahaifiyarta kuwa bata tsaya ko inaba se’a zanfara,inda ta fad’a hannun wani mutumin kirki mai suna Buba. Mutum ne mai kirki sosai,koda suka had’u yana ganinta yasan dai akwai wani abu tattare da ita,gashi duk abinda aka tambayeta se tace bata sani ba,sunanta ne kawai idan aka tambayeta se tace Samira.
Bayan sallan isha Aisha da Mubeenat suka raka Amal har gida inda suka sami Samira da Sagir zaune a parlour suna hiransu cikin raha da kwanciyar hankali.
Cikin b’acin rai Aisha tace “Hmmm d’an adam butulu,kowa yayi mai kyau dai kansa yayiwa mutane babu tsoron Allah ko kad’an azuciyarsu?”
“Kedai yi shurunki Aisha,bakiji hausa sunce *komai nisan jifa k’asa zata dawo ba*,muna nan muna addu’a Allah ya toni asirin duk wani mai hannu akan b’atan Umman Amal ameen” cewar Mubeenat.
Cikin fushi Sagir ya nufosu “Ku kuma wani mahaukacin karene ya cijeku kukazo nan kuna mana haushi?”
Cikin gatse Aisha ta bashi amsa “Mahaukaciyar Uwarka ce ta cijemu kaga ko dolene muyi haushi dan a cikin karnukanma ita rik’ak’k’iyace sosai.”
Dosota yayi da niyan zai mareta se Amal ta shiga tsakaninsu yayinda itama Samiran ta kamo hannunsa tana cewa “Bana son neman magana Sagir ka k’yalesu”
“Idan bai k’yalemuba ma ya zaiyi damu,nan gani nan bari” cewar Aisha.
“Wlh koda wasa Sagir karka kuskura kace zaka tab’a d’aya daga cikinsu dan wlh wahala zaka sha” cewar Amal.
“Kubar ganin iyayenku masu kud’i ni babu abinda ya dameni wlh maganinku zanyi marasa kunya”
“Kaga nan babban mara kunya golai-golai daku kunzo zama a gidan matar aure daga kai har sakariyar ‘yar taka kunzo kunyi butulci to munsan komai wlh ku jira kamuwar Allah butulai kawai.”
“Ke Aisha kike ko wa wlh ki kame kanki kina jina ko?” Cewar Samira.
“Idan nak’i kuma fa? Zaki tayani kamewane munafukai kawai duk cikinku babu wanda ya isa ya dakatar dani daga abinda nayi niyan fad’a sedai in gaji inyi shuru shashashai kawai.”
Jiki sanyaye suka tsaya suna kallonta yayinda Mubeenat tayi dariya tace “Amma kinmin dai-dai Aisha,barsu da wannan ma kin basu na bacci wuce muje Amal” nan suka wuce suka kaita har d’akinta sannan suka fito suna musu kallon banza tare da cewa “Wlh ta Allah ba takuba,koma menene kukayi zamu gano komai cikin sauk’i makirai kawai” sannan suka fice daga gidan suka barsu a tsaye.
Cikin sanyin jiki Samira tace “Kai Sagiru anya kuwa ba zarginmu jama’a suka farayi ba?”
“To kema dai seme idan sun zargemu,ai babu wani bai shaida a kanmu dan haka yau kiyita kuka kice mishi zamu bar gidan tunda gashi abinda yarama suke fad’a” nan dai ya kitsa mata komai sannan ya fice.
Atif ne ke driving zai mayar da Aisha gida shida Mubeenat.
Magana suketayi akan b’atan Umman Amal inda suke cewa “Wlh Ya Atif duk yadda akayi suna da hannu akai”
“Shhhh bana ce muku karna sakejin hakan daga gareku ba,zato kuke yifa kuma zato zunubine koda kuwa gaskiya ce dan haka karna sake ji kudai kucigaba dayin addu’a Allah ya bayyanata.”
“Ameeen” suka furta sannan suka kama yin wani hiran har suka isa gida.
Gum Mom Atif ya wuce,Aisha da Mubeenat kuwa d’aki suka wuce inda Aisha ta fito mata da kayayyakin da angonta Fahad ya kawo mata.
Nandai suka tab’a hiransu sannan ta d’ibawa Mubeenat nata kason harda bra guda uku masu kyau.
Gun Mom ta wuce da Hajiyan su Ya Musty ta musu sallama sannan suka tafi.
Suna shiga cikin gida ta hango motar su Ya Farhan.
“Ya Atif naga kamar motar su Ya Farhan,me kuma ya dawo dasu oho”
“Ko sunyi mantuwa ne may be.”
Atif yana gaba tana binshi a baya har suka k’arasa parlour’n Abba.
“Yawwa to gasu nanma sun dawo,Mamana dama Ummin Farhan ne tace lallai se’a d’aukoki wai zakici gaba da zama a gidansu harse bayan sun tafi kafin ki dawo gida.”
Cikin jin kunya ta kalli Atif dake zaune ta gefenta yayi mata murmushi itama haka sannan ta kalli Farhan da Abdullahi tace “To Abba duk yadda kace”
“Kije ki had’a kayanki kizo ku tafi kar dare yayi ko?” Cewar Umma.
“To” sannan ta wuce ta had’o kayanta a k’aramin kit ta fito da ledan da Aisha ta bata a hannu.
Atif da Shureim ne suka rakosu hargun mota sannan suka koma, Farhan yaja mota se gida batare da sunce da ita komaiba hiransu suke su biyu tana sauraronsu amma baji takeyiba dayake larabci ne.
Suna isa ta d’auki kit nata da leda batare data lura cewa bra nata guda d’aya ya fita daga ledan ba,zata wuce se Farhan yace da ita “Let me help you” tare da mik’o mata hannun shi. Ba musu ta mik’a mishi kit d’in sannan ta wuce da ledan tare dayin sallama ba kowa a parlour duk suna ciki dan haka ta wuce d’akin Ummi inda ta saba zama.
Ledan ta ajiye a walldrop sannan ta zauna daga gefen gado tana jiran isowar kit nata.
“Slm”
“Wslm tasa hannu ta karb’a tare da cewa thanks”
Murmushi kawai yayi mata sannan ya tafi ta wuce ta ajiye kit d’in tare da bud’ewa ta d’auki rigar baccinta sannan ta rufe ta mayar.
Seda ta wasta ruwa ajikinta sannan tasa kayan bacci ta haye gado.
Ummin Farhan ce ta shigo da sallama ita da Farhan,amsa sallamar tayi tare da tashi ta zauna. Kusa da ita ta zauna “Habibty kin gaji da zama damu ne yasa kika gudu?”
Murmushi tayi tare da cewa “A’a”
“To meyasa kika tafi da kit naki,kodai dan bakya tare da Atif ne anan naga idan kina kusa dashi kinfi sakewa”
“Ba haka bane Ummi kawai dai danmun saba ne dashi sosai,Ya Farhan bai fiye son magana ba shiyasa.”
Murmushi yayi tare da kallon wayar hannunsa yace “A hakan shine bana magana?”
“Eh ba kaman Ya Atif ba gaskiya”
“Karki damu Habibty a hankali zai sake dake asalinsa haka yake inba dani da Abbi nashiba se kuma Abdullahi,amma ko ‘yan’uwanshi nacan Madina haka yake dasu.”
Kallonsa tayi shima kuma ita yake kallo yayi murmushi. “Kin gani ko Ummi shifa sedai yayi murmushi ya danna wayarsa amma baya magana dake da Abbi kawai muke hira shiyasa naji ina kewan su Ya Atif da Shureim”
“Habibi”
“Yes Ummi”
“Kaji abinda tace ko,dan haka ka sake kana mata hira kamar yadda kakeyi da Abdullahi”
“Ok Ummi” ya fad’a sannan ya wuce walldrop nata ya bud’e ya ciro bra nata daya gani a mota ya b’oye acikin suite nashi shine yanzu ya ajiye mata akan kit nata.
“Habibi me kakeyi agun?”
Juyowa yayi yace “Na d’auki ajiya nane dana mance aciki” sannan ya fice yabar d’akin.
Hira sosai sukayi sannan Ummi ta fita,cikin sauri Mubeenat ta mik’e taje inda Farhan ya bud’e cikin mamaki taga bra nata akan kit d’in kuma tasan babu komai akan kit nata dukta kimtsasu acikin kit.
Hannu tasa ta rufe bakinta “Kardai a motarsu na mance shine ya gani ya kawo min,ohh wannan abun kunya har yaushe ni Mubeenat?” Ta fad’a kan gado tana mai jin kunya..Tana kwance taji wayarta ya fara k’ara,koda ta duba bak’uwar number ta gani,ta d’auka tare da cewa “Hello”
Wani daddad’ar murya taji yayi magana a hankali “Habibty”
Cikin mamaki taji muryan Farhan,to a ina ya samu number na kuma? Katse mata tunanin yayi da cewa “Kince bana miki hira kamar Atif?”
“Eh mana Ya Farhan”
“Uhum me kike so ince miki to?”
“Babu kawai dai ka saki jiki dani tunda nima k’anwarka ce”
“Ok zanyi k’ok’arin hakan”
“Gaskiya ya kamata kagafa tare zamu zauna yanzu idan su Ummi suka tafi”
“You know what Habibty?”
Cikin sonji me zai fad’a tace “Seka fad’a”
“I will gonna miss them Habibty,i love my parent so much and i don’t wanna miss them serioursly.”
“Eyyah dama haka rayuwa take Ya Farhan,yau ina Umman Amal? Koda wasa bamu tab’a kawo hakan zai faruba,amma dayake rayuwace kowa da yadda Allah ya tsara mishi yau an nemeta an sara…”
Jin shuru da Mubeenat tayi ta kasa k’arasa maganar saboda k’walla daya zo mata yasa Farhan yayi saurin gane cewa kuka takeyi,hankalinsa a tashe yayi magana cikin rarrashi “Habibty are you craying? Pls stop it i don wanna see you craying and i don’t know why”
“Habibty,please ans me okay?”
Cikin jin dad’in yadda ya nuna kulawarsa a gareta ta share k’wallan tare da cewa “It’s okay i’m fine now”
“Are you sure?”
“Umhum” ta bashi ansa.
“You know what Habibty? When ever i’m talking to you i’m just so happy and kuma bansan dalili ba?”
Murmushi tayi mai d’an sauti “Yaya Farhan kenan,wato dai kana so in dena kuka shiyasa ka gayamin haka ko?”
“Uhum,is not like that Habibty i’m serious”
Bata san me zatace dashi ba dan haka tayi shuru tana murmushi a b’oye.
“Habibty are you there?”
“Yeah”
“Then meyasa kikayi shuru,kodai kin fara jin bacci ne?”
“A’a kawai dai bansan me zance maka bane”
“To shikenan,kince bana magana sosai shiyasa na kiraki dan in miki hira,ina fatan kinji dad’in hiran namu duk dadai nasan ban iya kamar Atif ba but i try ai ko?”
“Hhhhh sosai ma kuwa ai gara hakan”
Murmushi yayi mai sauti sannan yace “Alright Habibty,na miki hira nizan kwanta ma’assalam”
“To nagode sosai bissalam”
“Kinji Abdullahi ko? Wai dawa nake hira haka?”
“Hhh ina jinshi”
“Bari in bashi seki bashi amsa”
“Ok” ta fad’a tana dariya.
“Habibty?” Dariya Mubeenat tasa tare dayin magana cikin harcen turanci “Ya Abdullahi harda kai?”
“Ok kina nufin shi kad’ai ne zai kiraki da Habibty?”
“Rufa min asiri ba haka nake nufiba,shima ai a bakin Ummi yaji”
“To indai hakane shi meyasa baki mishi tambayar da kika min ba?”
“Hahhh haba Ya Abdullahi karka min wata fassara daban please” tana dariya.
“Ai nama yi miki…” karb’an wayar Farhan yayi yasa a kunne a lokacin Mubeenat tanata dariya tare da cewa “A’a kayi hak’uri kaima ka kirani da Habibty’n shikenan?”
Murmushi Farhan yayi tare da cewa “Nidai ban amince maka da hakanba ka kirata da sunanta koba haka bane Habibty?”
Dariya Mubeenat tasakeyi “Ya Farhan karka had’ani da shi fa nidai ba ruwana”
Shima dariyan yayi tare da cewa “Ok Habibty good night”
“Good night” sannan ta ajiye wayar tana dariya.+
Washe gari da safe kuwa ana zaune ana breakfast gabad’aya hankalin Farhan akan Mubeenat yake,ita kuwa abincinta kawai takeci.
“Habibi yaya dai,bangane makaba kwana biyunnan fa” Cewar Abbi.
Dukkanninsu suka maida dubansu kan Farhan,murmushi kawai tayi tare da cewa “I’m fine Abbi”
Kallonsa kawai Mubeenat tayi sannan tace “Abbi duk damuwarsa shine zaku tafi ku barshi anan shi kad’ai right Ya Farhan?”
Kallonta yayi tare da cewa “Yeah it’s true” yana mata murmushi itama haka. Kallonta ta mayar dashi gun Ummi tare da cewa “Amma ai Abbana ma a matsayin Abban shi yake hakama kuma Ummana ko Ummi?”
“Kinyi gaskiya Habibty,sannan gashi da aboki Atif ga kuma k’anne har biyu Ke da Shureim”
“Ehen Ummi gaya mishi dai,harma da Amal kinga mu ukku ma kenan” ta k’arashe maganar cikin zolaya.
“Keba K’anwarsa bace kawai Mubeenat,burina shine in had’a zuriya da Aminina wato Mahaifinki”
Kunya sosai mubeenat taji da maganar Abbi dan haka d’aki ta nufa cikin jin kunyarsu.
Farhan ya kalli Abbi nashi sannan ya kalli Ummi se yayi murmushi.
Kakansu kuwa magana yayi cikin zolaya “Idan kuma Farhan d’in baya so se’a bawa Abdullahi kafin mu koma se’a tsayar da maganan aure kawai.”
Cikin zolaya Abdullahi yace shikenan kuwa Abbi dama yace min baya sonta.”
Da sauri Farhan ya juyo yana kallon Abdullahi,su Ummi kuwa se dariya suke mishi.
Mik’ewa yayi tare da jan kunne Abdullahi yace “I lost my apatite” sannan ya koma parlour ya zauna sunata dariyan shi.
Abbin Farhan da Abban Mubeenat ne zaune suna hira inda Abbin Farhan yake gaya mishi burinsa shine ya had’a Farhan da Mubeenat aure inhar hakan zai yuwu.
“Nayiwa Farhan magana akan hakan,amma dai baice komaiba tukunna inaga mud’an bashi lokaci kafinnan sun sake shak’uwa da ita Mubeenat d’in nasan wata rana da kanshi zaizo min da zancen.”
“Ba komai Aminina Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma had’a kawunansu” cewar Abban Mubeenat.
“Ameen” sannan sukaci gaba dayin hirarsu.
Gidansu Amal kuwa bayan Samira ta d’aga hankalinta ne ta nuna lallai da gaske zasu tafi shine Abban Amal yace da ita ta zauna zai aureta domin ya maye gurbin Umman Amal da ita.
Murna agun Samira ba’a cewa komai,nan Abban Amal yajewa Abban Mubeenat da zancen aurensa da Samira.
Abban Mubeenat baiyi mamakiba saboda maganganu da suke yawo a gari kan cewa da hannunsu Samira akan b’atan Umman Amal,sannan ga maganar da Amininsa wato Abbin Farhan ya sanar dashi kamar dai yadda Kakan Farhan ya gaya mishi cewa akwai asiri a tattare da Abban Amal dan haka a dage mishi da addu’oi.
Tun daga lokacin Abban Amal yana iyakan k’ok’arinsa na mishi addu’oi da kuma karya sihiri na ganyen magarya da akeyi,wanda ko an mishi aka bashi ruwan a gora indai yakai gida tozai gayawa Samira komai da aka gaya mishi a waje,ita kuwa seta ce to Abban Amal aise a gwada.
Amma yana barin gurin zata zubar da wannan maganin da aka bashi setayi dabara ta d’ura wani ruwan maganin da Malam na gura ya basu.
Shiyasa abun nashi yaketa gaba2 har’i zuwa yanzu dayazo musu da maganar auren Samira.
Babu yadda suka iya dashi tunda baya d’aukan shawaran kowa sena Samiran,dan haka aka zuba mishi ido ana tayashi da addu’a.
Yaune su Ummi suka koma k’asar Madina,inda suka bar Farhan cikin kewa sosai.
Kafin su tafi sunje Company sau biyu suna ganin yadda ayyuka suke gudana.
Abbi nashi yace lallai yaba Mubeenat babban matsayi ata gunshi dukda dai secondary skul kawai ta gama a yanzu. Haka kuwa akayi yace ba damuwa amma har yau bata fara zuwaba kuma ta nemi alfarma agun Abbanta daya nemawa Amal ma sesu dinga tafiya tare kota d’an samu sauk’in b’acin rai da take fama dashi a gida.
Yau ne Farhan ya dawo gidansu Mubeenat da zama gaba d’aya,dan seda yayi kwana biyu acan kafin yau ya dawo.
Mubeenat da Shureim ne suka k’arasa gun motar da murnansu “Ya Farhan sannu da dawowa”
“Thankyou Habibty” sannan ya kalli Shureim tare da d’aukan shi sama “Atif ya tafi ko?”
“Eh sun tafi tunda sassafe” cewar Shureim.
“To Allah ya kaisu lafiya”
“Ameen” suka amsa dukkansu sannan Mubeenat ta kamo kit nashi tana ja.
“Habibty stop please” cak ta tsaya tana jiran mezai ce. Sauk’e Shureim yayi yaje ya karb’i kit d’in a hannunta “Is too heavy Habibty take this” ya bata k’aramin kit d’in sannan Shureim ma ya d’auki wani kayan suna tafiya can side d’in su Ya Atif d’in.
Dama Mubeenat ta gyara komai a d’akin yayi tas gashi se k’amshine kawai yake tashi. Shiya karb’i kayan ya kai har zuwa ma’ajiyarsa wato walldrop dake d’akin babbane sosai gashi fari tas.
Mik’ewa tayi tare da cewa “Bari naje na kawo maka abinci”
“No Habibty i’m okay”
“A ina kaci abincin kenan?”
“Mun fita da Ahmad d’azu munci abinci”
“Waye kuma Ahmad Ya Farhan,har kayi abokai kenan?”
“Hhhh Habibty wanda kikace muje mu sayi mota agunsu ne,mun d’an saba dashi Ahmad d’in shine dai abokina a yanzu”
Murmushi tayi tare da cewa “A hankali zaka zama d’an gari,toni zan koma ciki me za’a dafa maka zuwa anjuma?”
“Anything Habibty” ya fad’a yana mata murmushi.
“Ok kad’an huta yanzu to,Shureim muje ko?”
“Kibarmun shi mana yamin hira”
“To shikenan,se anjuma” sannan ta fice yana binta da kallo dan kayan da Ummin shi ta kawo mata ne a jikinta yayi mata kyau sosai doguwar rigar…