KOWA YA DAKA TA DABO CHAPTER A

 KOWA YA DAKA TA DABO CHAPTER A

(Wani sashi na labarin _is true life story_)+

BABI NA DAYA
“Ke nifa nafara gajiya wallahi da wannan al amari yarinya tabi ta jabemin a gida babu mashishini, ba dole hankalina ya tashi ba Alla alla nake ta tashi in tattara kan kannanta suma su yi gama in huta amma abu yaci tura”.
“Kema dai Mariye dake wallahi zamani fa ya sauya sai kin tashi tsaye ‘yarki zata sami miji, wai waya ce miki ana zama yanzu ne? Ke wallahi in kina wani abun kamar ba haihuwar kwaryar birni ba sai duhun kai kamar me”.
“Hmm! Hajara baki san kafiyar wannan yar ba ne gata dai mai ruwan nutsuwa sai ruwan kafiyar tsiya shegiya kamar bani na haifeta ba ina fa karɓo taimakon nan dai-dai gwargwado amma wallahi bata yi wai sai ta ce komai lokaci ne!….”

Tunda suka fara batun sai yanzu tasa baki tana dubansu,


“gaskiya bakwa kyautawa Mariye da Hajara kusani ba komai na duniya mai wuce wa ne, kuma komai da kuka gani yana da lokaci yarinyar nan kun bi kun tsangwameta dudu shekarunta nawa ne? Ku fita waje cikin gari kuga yan mata tubarkallah tika-tika wata ma ta goya uwarta don ma ke taki tana da kyan jiki amma duk kin bi kin takura mata da hayyatarki ko wannan baya sa ta rame ta kwantsame ba!”.
Kallonta suke tamkar sun ga abin kyama, suka haɗa baki gaba ɗaya,
“dakata Hasiya don ke Allah ya rufa miki asiri yaranki maza ne, wace hidima kika sani ta rayuwar wahalar yara mata baki san siyan ɗan kunne ba bale gyale sai a dakeka a hanaka kuka?”.

Takaici ne ya kasheta ta yi shiru idanunta suka sauka kan matashiyar budurwar dake tilikar wanki akwai alamun gazawa atare da ita duba da yadda take tsattsafo da gumi ta goshinta ta ɗauke kai tare da mikewa,
“ni dai na wuce amma Mariye ki sani idan kika daka ta bado………”.
“Jeki bana bukatar jin komai daga gareki”.
Bata tanka ba ta wuce tana mamaki halin makotan nata cikin ranta. Tana bada baya Hajara ta dube Mariye,
“matar nan ta raina mana hankali ita don tana da miji ya wadatata da komai tilon yar ta ta guda ɗaya sa ar yarki ki duba harta aurar da ita haihuwa biyu ga tawan itama da ɗa ɗaya shi ne take miki fiffika to ki zauna ki mutu a wahala wannan wahalar tasu da ki ke kika samu ɗaya ta kauce ai kin rage wallahi”.
“Bari kedai aminiyata walahi ga uban nasu babu ubanda ƴyake samowa koya fita wata rana ma sai ya dawo yaci abincin a nan ni wannan jaraba dame ta yi kama?”.
“Ki dai zauna garin kallon ruwa kwaɗo ya miki kafa”.

Saida ta tabbatar ta gama yi mata famfo sannan tabar gidan.
Duk abinda suke tana jinsu bata tanka ba lokaci zuwa lokaci takan faki idanunsu ta share hawaye, zuciyarta na yi mata zafi kamar ta faso kirjinta ta fito don takaici. Ba ita ta gama wankin ba sai gefen magariba ya kammala ta shanya tas ta wanke tsakar gidan ta yo wanka tana fitowa ana kiran magariba kaya kawai tasa ta bi masallaci jam’ibayan sun idar ta ɗauko kulin dabinonta ta yi basmala tare da yin addu ar buɗe baki ta ci. Shigowar kanwarta ya katse mata tunanin da take yi,
“aunty barka da shan ruwa ga abincinki nan”.
“Na gode Sa’adiya, ashe kin dawo ina Mardiya? Amma yau kun daɗe a makaranta”.
“Aiki aka bamu kinsan Malam ɗan fari ba wasa”.

“To ai saiku dage da karatu”,
Ta faɗa tana jan kwanon abinta, tana buɗewa ta tsura masa idanu, banda yunwar da ke adabarta da bazata ta ci wannan abincin ba bata gama tunani ba ta jiyo muryar mahaifiyarsu tana faɗin,
“shegun yara yan iska to ku kashe ni bakin cikinku dana ubanku nidai babu wanda zan karawa abinci cikinku matsiyata uban naku da zai fita nawa ya bani?”.
Kwala ce ta taru a gefan idanunta ta mike ta futo hannunta rike da kwanan abincin har jiri take gani tsabar yunwa da take adabarta,
“Ammar, Sauban da Sadis kuzo ku karɓa kuje ku ci wannan, ku kullum sai kunsa Mama ta yi hayaniyya ko bakwa tausayinta?”.
Yaran shiru suka yi kansu a kasa, Ammar sarkin zuciya ya mike,
“Aunty bana ci basu su suci”.
Yana kaiwa karshe ya fice waje yana huci, Sadis ne ya karɓa ta dafa bango tana duban mahaifiyar tasu cikin tausassa harshe,
“Mama ki dinga hakuri damu da al ammuranmu komai mai wucewa ne bada jimawa ba, bana son kina faɗar shegu ko tsinannu da sauransu bakin uwa guba ne mai haɗari ga yaranta kuma hidimar abinci da kike batu in baki mana ba waye zai mana duk faɗin garin nan? Mufa yaranki ne ke kika haifemu da cikinki mahaifinmu kuma dayana da shi da ya yi miki domin ke kika bamu ƙlabarin irin jin daɗin da kika yi abaya menene faɗuwa gareki a cikin ciyar damu? Wannan fa zobe lada ne kike yi…………..”.

STORY CONTINUES BELOW

“Dakata! Fatima ke kika haifeni ko ni na haifeki? Zaki tasani kina mun wa azi kamar wata ‘yarki, sai a dakeni a hanani kuka shin karya nayi? Uban naku ya bani kuɗin ne da zai fita ina ce naira ɗari ya bani kuna kallo matsiyatan yara sai munafurci to kusa ya koreni kunji”. Mardiyya sarkin miskilanci tana gefe ta yi jigum tana kallonsu.
Sa’adiya ce ta ƴyi karaf,
“Mama fa gaskiya muke faɗa miki, ita rayuwa hakuri ake da ita kuma ko mahaifinka ne yake badaidai ba dole hakkine ka nuna masa kuskuransa…..”.
“Sa,adiya Fatima ni kuke gayawa haka? Shikenan kuje zaku haifa zaku gani kuma insha Allahu sai kun gani”.
Fatima ce ta ja hannun Sa’adiya, suka shiga cikin ɗakinsu suna jiyo sautinta tana mita da sababi har dawowar mahaifinsu. Su Sadis kuwa suna gama cin abincinsu suka mike suka yi waje.

****
Fatima Aminu Muhammad shi ne cikakken sunanta, a salin mahaifanta haifaffun kwaryar Kano suna zaune ita da mahaifanta a garin Katsina cikin kwaryar birni a wata unguwa Saulawa. Su bakwai mahaifansu suka haifa dai
-dai gwargwado sun sami tarbiya yadda ya kamata.Mahaifinsu Malam Aminu Muhammad sana arsa ita ce saida kayan kamshi a kasuwar central cikin ikon Allah a rusar ɗin da aka yi aka haɗa da rumfarsa hakan yasa ya durkushe bashi da komai sai ya tattara abinda ya rage masa ya kama sana’ar faci a nan bakin unguwarsu mutumin kirkine sossai babu ruwansa da shiga shara ba shanu. Mahaifiyarsu kuwa mace ce mai faɗa gata da mita kamar matar makaho, a duniya ita tana san a ɗauka a bata tana jin daɗin hakan. Fatima ita ce babba tana da shekaru a shirin da biyar sai Sadiya mai shekaru sha bakwai sai Mardiyya sha biyar kasancewar tana da girman jiki ajinsu ɗaya da Sadiyan sai kuma Sadis mai goma da Ammar mai takwas sai kuma Saubahn  mai shekaru shida, da Hassana da Hussaina da Gambonsu duk mata masu shekaru huɗu daga kansun ta dakatar da haihuwar a cewarta ta gaji da ita haka sabida matsi da yanayin rayuwa. Gidansu gidane mai wadatar ɗakuna biyu Mamarsu ta ɗauki ɗaya ta basu ɗaya su matan sai kuma mazan da aka fitar wa da karamin ɗaki a soro.Fatima ta kammala karatunta tun shekaru biyu da suka wuce na makarantar gaba da primary takardunta sun yi kyau sossai amma rashin kuɗi ya hana ta cigaba da karatu, Sadiya ita ce ke matakin kusan na karshe wato aji huɗu Mardiyya ma aji huɗu Sadis aji biyu sauran yaran kuma duk suna primary ne. Mahaifinsu nada burin su yi karatu matuka amma rashi ya dakushe shi.Burin maifinsu su yi karatu mai zurfi koda sun yi aure amma babu halin hakan. Ganin zaman bazai yi wu haka ba yasa ta mike ta koyi sana o in hannu tana yin ɗinki ta iya sossai tubarkallah kuma tana ɗanyi babu laifi amma na wajenɓunguwarsu domin keta bazata sa a batanba cikin unguwarsu mutum ɗaya ke bata ɗinki Mama Hasiya. Sadiya kuma kunshi take yi da kitso ita ma Fatin na taɓa kitson jefi-jefi amma tafi maida hankali kan ɗinkinta sai kuma karance-karance. Mardiyya kuma ko ina tana taɓawa ɗinkin da kunshin amma ita ɗinkin jakunkuna take yi. Kaf yaran kowane yana da bambancin ɗabi a da hallaya. Fatima bata da hayaniya amma tana da faram-faran da mutane gata da tsafta da son aiki. Sadiya akwai tsiwa da son gayu sai dai tana da son jiki bata da son moriya amma fa bata ɗaukar raini kuma bata da tsokana. Mardiyya miskila ce bata son magana rayuwarta kawai take lokuta da dama banda makaranta sai ta yini a ɗaki akwai ta da son gyaran ɗaki da kawata shi shiya sa ma Fatima ta dage kan art zata yi a makaranta. Ammar duk ya fisu zuciya abu kaɗan yake sashi fushi saɓanin Sadis da sai an taɓoshi, Saubahn kuwa kowa nasane faransai ne su kuwa tagwaye sak Fatima ne Gambo ce duk da kankantarta ta kwaso halin mita da son abata irin na mahaifiyarsu.

A gefansu Fatima akwai gidaje guda biyu wanda sun kasance suna makotaka juna. Gida na farko gidan kawar mahaifiyarsu ce mai suna Mama Hasiya yaranta biyar babbar mai suna Aisha sa ar Fatima ce tare suka yi makaranta  ta yi aure shekaru biyu da suka wuce yaronta ɗaya sauran kuma duk maza ne suna makaranta in sun dawo sukan je kasuwa rumfar mahaifinsu dake kasuwar yan kaba daidai gwargwado suna da rufin asiri.
Gida na biyu gidan aminiyar mahaifiyarsu Fatima ne Mama Hajara matar Malam Sabo. Yaransu Tara babbar ta yi aure tana da yara huɗu sai mai bi mata yaranta uku ta ukun ce bata taɓa haihuwa ba sai ta huɗun   sa ar Fatima ce an mata aure tun suna ss one haihuwarta biyu duk maza mai suna Murja. Sai ɗaya sa ar Sadiya Khadija itama da kuɗinta da aka kawo da saka rana sai kuma sa ar Mardiya mai suna Rahma sai Murtala da Mussaddik da Aliyu. Mama Hajara irin matan nan ne masu masifar surutu da sa ido kan abinda bai shafesu ba, bata da hali ko kaɗan ga gulma da aibata yaran jama a duk unguwar bame hulda da ita inka ɗauke Mama Hasiya da Mama Mariye, iya kokarin Hasiya tana kokarin kwatantawa Hajara rayuwa amma abun ya ci tura. Haka maigidanta duk inda gulma take ya iya ɗaukota, yaranta babu wanda yake karatu matan dasun taso take tsigesu ta yi musu aure acewarta farin jini garesu. Duk iyayan Fatima yan asalin garin Katsinane mahaifinta maraya ne gaba da baya mahaifiyarta ce keda dangi suma ba wani karfine dasu ba wasu ma cikinsu ta fisu karfi amma bata godewa Allah.

Tunda aka yi bikin sa anin Fatima Mama Mariye ta ɗaga hankalinta, babban bakin cikinta kar ace ɗiyarta ta yi kwantai tun tana ɓoyewa kawayan nata tasa ɗiyar a ɗaki tana nuna mata tayi kokarin fida miji har abun yaci tura ta fara faɗawa kawayan nata Hasiya murmushi tare da furta mata komai lokacine, amma Hajara buɗar baki ta yi ta furta,
“yadai kamata ta motsa wallahi ta fitar da gwani musha biki ga saaninta na kusa dana nesa duk da yaransu, kema hidimar ta yi miki sauki ki huta”.

Hakan ya karawa Mama kaimi ta fara azalzalar Fatin ashe ba ita kaɗai ke kallon Fatin a gaba ba suna haɗa kwankwaso kawartama kenan ina ga makiyanta wannan tunani ya hanata sakata tabi ta hayyaci Fatin. Fatima yariya ce mai kazar-kazar da faran faran da jama a ba wata kyakkyawa bace siririya ce takin karawa amma tana da shape wanda rama ta ɓoye ainihin zubinsa. Tana da doguwar fuska da sirisrin hanci idanunta tubarkallah amma bakinta yana da ɗan faɗi ba laifi fatarta kuwa baka ce amma gyaran da take samu yasa ta yi wani irin launi mai matsakaicin haske kuma ba wai man kati bane tsabar kulawa ne tana da cikakken gashin kai wanda ya kasance _natural_ babu shamfo ko ɗaya a jikinsa. Tana da maida kai kan karatu ga tsafta da wuya ka shiga gidansu ka sami datti sai dai idan bata nan tana da  tsananin biyayya da kawaici kaf wankin mahaifiyarta dana kannanta ita take yi tare da Mardiyya haka aikin gidan basa bari mahaifiyarsu tayi sun dai barta tana ji da sana’ata ta kiwon kifi wanda tana samu babu laifi da ita suka dogara ita ce duk wata hidima tasu. Duk wannan ɗabi a ta Fatima  amma tana da saurin fushi da ɗaukar abu da girma matsala karama kan ɗanga mata hankali ta kwantsame, ganin yadda Mama ta takura mata ne yasa ta daina yawan magana ko hira ake batasa baki in ba sata aka yi ciki ba. Babban takaicin Fatima yadda motsi kaɗan mahaifiyarsu kan buɗa baki tayi musu gorin hidimar da take musu ga saurin aibatawa da mugun baki hakan yafi cimata tuwo a kwarya fiye da komai. Matsalar aure bata gabanta tasan komai nada lokaci kuma zai wuce, shiya sa kwata-kwata ta fice sabgar kowa da wuya ka zaga unguwarsu a ɗaga wata ace wannan kawar Fatima Aminu ce sai dai gaisawa shi ma a tsaitsaye.
***

BABI NA BIYU

Tun fitar Hajara Mariye take dogon nazari bisa shawarar da Hajaran ta bata lallai ya kamata ta motsa ta nemawa Fatima taimakon daya dace wajan Malamai ga Saadiya ta kai girma itama ga waɗannann masu tasowa, ta runtse idanu tana wani tunani na daban. Washegari da wuri Saadiya ta gyara gidan suka shirya yaran suka nufi makaranta Fatima na zaune tana duba wani littafi a hannunta mai suna GWANIN WANI rayuwar yarinyar ciki ta bata tausayi matuka yadda akai musu yankan kauna ta runtse idanu tana kwatanta rayuwar as imagine da sauri ta buɗe idanunta tana share kwallar tausayi sallamar Mama Hajara yasa ta yi saurin daidaita tunaninta ta amsa kadaran-kadahan ta ɗauke kai amma ga mamakinta Mamar bata amsa gaisuwarta ba sai tafa hannu data shiga yi tana sallalami tana kiran,

“Mariye! Me zan gani yau? Na shiga aljannah (Beli) kishiya tara rana ɗaya”.

Da gudu Maman ta fito tana tambayar,

“lafiya Hajja? Me kuma ya faru?”.

Ita kuwa Fatima suman zaune tayi tana mamaki,

“ina fa lafiya Mariye gaskiya kin banu mamaki kika bar Fati tana karanta irin wannan batsar karatun littafin hausa taɓ wallahi a banza take kallonki ta gama sanin komai”.

Wata muguwar sarawa kan Fatima ya yi ta shiga furta kalmar,

“innalillahi wa inna illaihirrraji una”.

Mamaki fal cikin ranta da hali irin nan Mama Hajjara ita da ko kwana biyu bata yi ba da ganin Khadija da waya sabuwa dal kirar tecno android tana kallon film na batsa ta yi mata faɗa ƙkarshe Khadijan ta ce saurayinta ne ya turo mata ta kaɗu da jin hakan ta karɓa ta gogge tare da yi mata nasiha ta kuma samu Mamarsu ta faɗa mata bata samarwa ko tata mahaifiyar ba shi ne take mata wannan sharin lallai mutum mugun itace…….Bata gama tunanin ba ta tsinci sautin da ya fi komai fasa mata kwanya,

“kyale yar iska Hajja so take bakin cikinta dana ubansu daya barni da hidima ya kashe ni, ke banda ina sana ar nan basai na yi bara ba wata rana yara kana bakin kokarinka yan iska suna takaitaka zaki wuce ki maidawa mai littafin ko sai na ɓallaki?”.

Fatima ce ta wuce har wani jiri take gani ta nufi ɗakinsu tana tuntuɓe ta ɗauko mayafi ta shuri takalmi da nufin fita kai wa mai littafin littafinta tana gab da fitan kunnuwanta ya jiyo mata sauti mara daɗi,

“ki shirya na samo wani Malami mu kaita ko Allah yasa za a dace”.

“Kai Hajja gaskiya kina kaunata na gode da shawararki”.

Da hanzari ta karasa ficewa tafe take tana haɗa hanya tanani harta maida littafin a hanyarta ta dawowa ta haɗu da ɗiyar Mama Hajara  da yaranta biyu suna ss one aka yi mata aure amma data ganta saida gabanta ya faɗi. Mace zir babu wani kumari duk ta fita hayyacinta kamar ba matashiya ba fuska nata naso na maiko ga yaro ɗaya a hannu ɗaya kuma a baya ga saida ta yi mata dogon bayani sannan ta ganeta ta mika hannu ta karɓi na bayan wani mugun karnin nono ya daki hancinta hanjinta suka hautsuna saita wayance tace,

“barshi a bayan mu karasa gida”.

Suna tafe tana yi wa Fatima tsiya,

“Fatima ke kinki aure ke baga karatun ba kin zauna a gida kin kime ni narasa daɗin me kike ji? Aure fa akwai daɗi”.

Ta faɗa tana washe bakinta da yayi yellow shar da shi, Fatima ta kare mata kallo ta yi murmushi,

“lallai kam Murja ai naga alamun hakan tunda gashi nagani tare dake!”.

Murja sai ta yi gum don tasan magana Fatin ta faɗa mata kuma yanzuma yaji ta dako sabida yaran babu lafiya uban yaki kaisu asibiti, ga ta da karamin ciki kuma aure yake niyyar karawa a cewarsa ita kazama ce bata iya girki. Da haka suka karasa gida saida ta raka Murjan gida sanan ta shigan nasu gidan ta samu da ɗan dama-dama fushin da Maman take yi.1

Tsayin kwana uku Fatima na sa idanu kan Mama a bisa jike-jiken magungunan da suka amso da sunan farin jini gun Malamai, hakan ya kona mata rai matukar gayya amma ta dane abinta ta ci gaba da fawalawa ubangiji ƙlamarinta. Ranar Asabar tun safe ta gama ɗinkunan mutane aka kawo mata kuɗinta dubu shida cif, ta yi murns matuka ta cire dubu ɗaya ta sayi kayan shafa ita da kannanta Hassana da Hussaina da kuma Gambo ta sake musu uniforma taba mahaifiyarta dubu ɗaya mahaifinta ma haka daga nan tayo musu cefane yau burinta ta gwada dahuwar dambun shinkafa data gani mai kayan lambu a littafin UMMA SAMHAT da kuma leman kwakkwamba da AISHA CHUCHU ta yi cikin nata littafin. Kai tsaye kicin ta wuce ta ɗora girki kafin azahar ta gama gidan sai kamshi yake yi Mama ta kasa hakuri ta dubeta,

“Fatima ina kika koyi dambun nan nidai nasan ba ni na koya miki ba?”.

Murmushi kawai ta yi ta dubeta,

“Mamanmu karki mamaki idan nace miki a ƙlittatafan da ake tunani suna ɓata tarbiya na koyo sabida ba iya ɓata tarbiyar da ake faɗa suke koyawa ba har ma da abun karuwa fanin girki da gyaran jiki da sauransu wallahi Mama BAHAGUWAR FAHIMTA akai musu bance babu masu ɓatawa ba akwai su kam amma ba duk aka taru aka zama ɗaya ba kuma duk lallacewar waje ana samun na kirki wani irin duba kawai wasu gidahuman mutane suke ma marubuta amma nidai Mama marubuta sun taka muhimmiyar rawa a fanin iya girkina don a littatafansu duk nake gani nake ɗauka ke kanki shaidace bakya koyamun girki amma kuma duk randa nayi kina yabawa kawai ina nuna miki naki na kwaikwayane sabida yadda kike hanani ɗaukar littafin in karanta ki yafemun na saɓa miki ina yi a ɓoye gaskiya. Mama  wani fittacen maruburi mai suna Ado Ahmad gidan Dabino yana cewa,

STORY CONTINUES BELOW

“*MARUBUCI DAN BAIWA NE*, haihuwarsa ake yi ba yin sa ake ba. Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan kirkiri wani yanayi na gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da abubuwa wadanda yake amfani da su don isar da sako ga al’ummar da ke karatun rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa si]arori da shafuka har zuwa cikakken littafi.

Wani ana haihuwarsa da rubutu wani kuma koyo yake yi, amma duk marubuta za mu kira su. Shi marubuci mutum ne na daban, ba wai ya fi sauran rukunonin bil’adama ba ne, a’a, shi dai daban yake da sauran mutane, wato dan baiwa ne. Marubuci na yin tunani ne iri na daban, yana kuma kallon rayuwa da al’amuran rayuwa da wata irin fahimta tasa ta daban, sannan ya bayyana ta a rubuce. Kamar yadda aka ambata a sama shi marubuci dan baiwa ne, sannan shi kansa rubutun baiwa ne.

Abu ne sananne ga al’umar da take da ilmi cewa marubuci yana da matukar muhimmanci da tasiri. Saboda haka ya wajaba a kan al’ummar da ta sami marubuci a cikinta ta yi kokaririn jawo ra’ayinsa ko yin tasiri a kan tunaninsa don ya yi rubutu na kwarai, in ba haka ba duk abin da ya rubuta zai yi tasiri a kan ita al’ummar.

Marubuci kan yi rubutu saboda dalilai da dama ko wani hali ko yanayi da ya sami kansa ko wani tarihi na kasa ko dadadde ko kuma wata manufa ko ra’ayi. Don haka marubuci na iya yin rubutu don ilmantarwa ko wayar da kai ko kyautatawa ko fadakarwa ko farfaganda ko ta da zaune tsaye ko cin zarafi ko kuwa tsokana. Yana iya yin rubutu don gina wata akida ko rusawa ko kuwa don ru]ar da jama’a ko kawo sauyi ko kuma don tabbatar da wani ra’ayi ko manufa. Saboda haka marubuci na iya zama dan kwarai ko kuma baragurbi, sai dai a koyaushe yana kokariri ne ya ga cewa ya shawo kan makaranta su amince da shi. Domin kuwa zai yi iya kokaririnsa ya nuna musu cewa sakon nan nasa gasgatacce ne, amintacce ne kuma dauwamamme ne mai farin jini.

Yana da kyau mu fahimci cewa marubuci na da matukar muhimmaci ga duk al’ummar da yake zaune a ciki domin kuwa kadara ne ga wannan al’umma kuma yana iya jawo wani ci gaba ko dakushewa da alkalaminsa. In har ba ka fahimci manufar marubuci a rubutunsa ba, to ka dauka cewa ka jahi1ci fahimtarsa. Don haka duk irin abin da marubuci ya rubuta akwai manufa a cikinsa sai dai ko ba a fahimta ba. Amma fa ba dole ne a ce koyaushe marubuci na yin rubutu mai ma’ana ba.

Wani abin lura shi ne, zama marubuci wani al’amari ne babba. Duk lokacin da mutum ya zamo marubuci ko yake son zama marubuci, to yana shiga wani hali ne mai wuyar gaske. Na farko marubuci a kullum cikin tunani da kokaririn fahimtar al’ummarsa yake. Na biyu duk lokacin da yake rubutu dole ne ya rinka sanya tunaninsa da kuma mutuntakarsa. Shi ne zai zama na kwarai yanzu, wani lokacin kuma ya zama mugu. Ya zama yaro ya zama babba ya zama namiji ya zama mace, kuma duk lokacin da yake rubutu yana tunani ne na irin mutumin ko halin da yake rubutu a kansa.

Wani lokaci kuma marubuci tamkar dan-leken asiri ne domin kuwa muddin zai yi rubutu in har marubucin kwararre ne sai ya yi bincike don gano wasu bayanai ko fahimtar su. In da za ku gamu da shi a irin wuraren da yake neman bayanansa sai ka rantse ba wani abu yake yi ba. Alal misali idan marubucin yana yin rubutun da a ciki sai an yi maganar karuwai ko mashaya, kada ka yi mamaki don ka gan shi a mashaya ko yana tattaunawa da karuwa neman bayani ne ya kai shi. Ta haka yakan bi sauran hanyoyi don gudanar da binciken sa.

Babban muhimmancin da marubuta ke da shi ga al’umma shi ne, na yin amfani da alkalaminsu wurin sauya al’umma. Ya zama lallai a fahimci cewa ayyukan marubuta kan yi tasiri ga al’umma kai tsaye ko kuma ta rashin sani.

Don haka ya zama wajibi ga al’umar da take da marubuta a cikinta ta ga ta taimaka musu ta kuma yi tasiri na kwarai ga tunaninsu don rubutunsu ya yi tasiri nagari ga al’uma.

Mama idan zamu tsaya anan zamu kwana ne ban gama faɗa miki ira-iran abunda masu hikima da fasaha irin Gidan dabino ba da suka fito da amfanin marubuci ba cikin al ummah”.

“Gaskiya Fatima in dai haka ne daga yau kita karatun ƙlittafi amma don Allah kidinga yin masu amfani”.

“Na gode Mama kuma na miki alkawari”.

Lumshe idanu Fatima ta yi zuciyarta cike da farin ciki kan yadda ta kauda wannan matsalar cikin ruwan sanyi tana fatan ace matsalarta ma ta zamo hakan amma tana hango da kamar wuya. Mardiya na gefe kasancewar tana da shiru shiru murmushi kawai take yi tana son Fatima sossai.

STORY CONTINUES BELOW

*BABI NA UKU*

Kwana biyar tsakani Fatima na yin girkuna masu daɗi suna kwasar gara ganin walwalar mahaifiyarta ya fi komai faranta mata rai, saidai a ranar kwana huɗu ne komai ƴya suɓuce mata na yar walwalar data yi nasarar tarba a rayuwarta. Misalin karfe tara na safe mahaifinsu zai fita wajan aikinsa ya zaro kuɗi naira ɗari biyar ya mikawa Mamansu a lallace ta karɓa tana juyata,

“ki amsa da hakuri kiba tagwaye ɗari da hamsin su kai kuɗin makaranta sauran kuma kuyi amfani dasu”.

Sai da ta gama yi masa kallon sakarci sannan ta tanka,

“gaskiya fa Malam na fara gajiya da cikon cefane haka ake rayuwa? Kwai ka nakasani da sauran kuruciyata”.

Fatima dake ɗakinsu tana shirin fitowa ta ƴyi saurin komawa da baya tana jan rai kanta ya sara ta dafeshi ta lallaɓa ta jingina da bango tana maida numfashi kamar wadda ta yi gudun tsere. Sautin mahaifinta ta jiyo yana faɗin,

“haba Maman Fatima karfa ki manta ni mijinki ne, koban ci darajar auratayya ba naci ta iyalan da muka haifa ki sassauta mun kuma sauyin rayuwa babu wanda baya samu ke kanki shaida ce na isa da gidana na tsayawa iyalina a baya yanzuma sauyine kuma ina godewa Allah a bisa yadda ya tsaromin rayuwata ko iya yarana na duba nasan ya yi min ni’ima tunda ya bani iyali”.

“Ahaye! Nanaye miji!? Miji? Ashema miji? Kai wai har mijin da za a kira mijine? Meka ke da shi meka ɗaukewa iyalan naka? Nifa har ga Allah zaman hakuri nake a gidan nan sana ar tawa nawa take? Inyi hidimar abincin yaranka suturarsu kuɗin karatunsu duk ni ɗaya idan kuwa ba a godemin ba ba ace min Allah ya tsine ba”. Da sauri Mardiya da bata tafi makaranta ba ta yi waje tana haɗawa da tuntuɓe.

Wani kakkauran abu ne ya tunkare zuciyar Fatima ji take kamar ta rushe da kuka ta rarrafa ta kwanta tana maida numfashi, bata jiyo yadda suka kare ba sai fitarsa da sautin sallamar Mama Hajja tana rangaɗa salama, amsawa ta yi tana cigaba da nannata maganganu masu ɗaci wanda suka kasance sirrinta ne.

“Kawata keda wa kuma?”.

“Barni da takaici ɗan kwarjalena ne ya guma mun”.

“Kema banda abinki ke kike ɗaga masa kafa wallahi, ni zuwa nayi muje ki karɓowa Fatima taimako zanje ne in amsowa Khadija na tsari kinsan yau saura sati biyu su kawo lefanta”.

Wani wawwan dafa ƙkirji ta yi,

“sati biyu kika ce Hajja Khadijan?”.

“Itafa kedai ki zauna kiga zama”.

“Ai wallahi muje Hajja bani ba zama”.

Fuu ta faɗa ɗaki ta ɗauko mayafi, Fatima data gama sheka sai yanzu ta fito ta tanka,

“Mamanmu ina zaki baki tambayi Baba ba?”.

“Gidan uwarki zani munafuka mai bakin hali kawai, shegiya ba ke zanje taimakawa ba ki matsa ki bani waje na huta da hidimarki ba”.

“Mama don Allah don Annabi (S.A.W) idan don tani zaki fita wallahi bana bukata aure lokaci gareshi kuma idan nawa lokacin ya yi wallahi zan yi kamar ban zauna miki a gabanki ba kowace Mace Mamanmu da mijinta don Allah Mama karki fita babu sanin Baba”.

“La ilaha ilalla, wai Mariya yaushe kika bari wannan yarinyar ta rainaki? Shiyasa nace miki duk karatun da take ne yaja hakan amma kin ki yarda tasan komai a banza take kallonki, wallahi wataran…….”.

Bata gama batunba Mariye ta wawashi muciya ta yi kan Fatima,

“Fatima ki karasani kinji shegiya ga bakin cikinki gana ubanki wallahi Fatima kika kara karatun littafi Allah ya isa ban yafe miki ba”.

Das! Das!! Das!!! Gabanta ya tsananta faɗuwa kalaman mahaifiyartata sun fi komai ruguza mata tunani zuciyarta ta tsinke kuka ya kwace mata,

“kimin komai Mama amma kiyiwa Allah karki yimin baki bakin Mahaifiya guba ne wallahi”.

“Ke kika sani”, ta faɗa tana ficewa daga gidan Fatima ta rakasu da idanu ko kuɗin girkin bata barmusu ba share hawayanta ta yi ta mike ta soma gyara gidan. Misalin karfe ɗaya kaf kannanta sun dawo ta yi wa tagwaye da Gambonsu wanka da kuma Saubahn shi kuma Ammar da Sadis ta zuba musu suka yi da kansu. Yaran suka tasata gaba zuru tasan abinci suke nema Sadis ne ya mike,

“Ammar zo muje mu yi aikin kwatar can da ake yi musamu abinci”.

“Sadis ɓata jikinku fa zaku yi”.

“Aunty yunwa muke ji”.

Ya faɗa kamar zai kuka ta yi jim Sadis yaro mai zuciyar tsiya shi ne kaman zai kuka lallai yakai matuka dabara ta faɗo mata,

“ga katin dashi na can kuɗin ciki ɗari uku ne jeka ka amso ka siyo taliya leda ɗaya da mai saina dafa muku akwai yaji”.

Da sauri yayi waje ta saki ajiyar zuciya Saadiya dake gefe ta dubeta,

“ina Maman ne?”.

“Bata nan”.

Ta faɗa a takaice gudun jan zancen, cikin mintuna talatin ta rarraba musu taliyar a hannu a hannu suka wawushe ita kuwa bata samu ba da Saadiya ta matsa sai tace azumin tsakiyar wata take tilas ta rabu da ita. Tana nan zaune tana saka da kwancewa yaran suka fice zuwa islamiyya sai misalin shida ta dawo kafaffu butu butu dasu da murnarta ta tareta,

“Mama sannu da zuwa”.

Ga mamakinta washe baki ta yi,

“yauwa Fatima kunci abinci?”.

“Eh! Mama munci”.

“Haka ake so”.

Takaici ya cikata maimakon ta tsurata ta tambayeta ina ta samu kuɗin amma saita baje kan tabarma tana hama,

“ɗebo garwashi”.

Ba musu ta ɗebo mata ta ajiye wani kulli magani ta kwance ta zuba ta tura gaban Fatiman ita dai ta yi zuru tana ganin ikon Allah hayakin ya fara damunta ta kafeta da idanu,

“kiyi turarre nace munsamo magani da wuya zaki cuccemu muna zaune munafukai zasu kasaramu ni dama nasan Hasiya bata kaunata ashe ita take miki asiri mai bakin hali ɗiyarta ta tashi ta dankwafemun tawa”.

Cikin mamaki tace,

“kaman ya Mamanmu?”.

“Hmm! Ke yar nan tun a hanya Hajja take faɗamun tana zargin Asiya ce take koremiki manema babu mai zuwa ko kuma da sun fara zuwa su ɗauke kafa ni dai ban yadda ba, ilai kuwa ta fini gaskiya muna zuwa Malamin ya kama sunanta”.

“Mama Malamin dama ya sanki?”.

“A a inafa kijimin ja ira Hajjar dai ya sani ita tana zuwa karbowa yaranta taimako”.

“Mama karya yake zato ne kawai ko kuma haɗin baki domin wani bai isa ya hana wani aure ba”.

“Kinci uwarki Fatima shegiya ana ga gabas kuna ga yamma”.

“Wallahi Mama ba haka bane, ina guje miki faɗawa halaka ne zargi babu kyau Allah ya hana,  mu kyautatta zato Mama kyakkyawan zato yana daga imani, babu wani aiki da zai yiwu idan babu imani da kyautata zato. Gwargwadon yadda mutum ya amince da mutane suma kimanin yadda za su amince da shi ke nan, domin yadda kayi haka za a yi maka, a kowace al’umma ne kuwa. Daya daga cikin abubuwan da ke ba da kwanciyar hankali shine fata na gari a rayuwa da kuma yarda da jama’a. Fata na gari da kyakkyawan zato ga mutane suna samar da nutsuwa, sa6anin mummunan fata da mugun zato ga jama’a, wadanda ke dushe tunani su tsimburar da kamalar sa. Fata na gari a rayuwa kamar haske ne a cikin duhu, yana fadada tunani kuma ya qara wa mutum son alheri, ta haka har zai ci gaba a fahimtar sa game da rayuwa da ra’ayinsa game da ita. Sai ya gane kyawun rayuwa da dadin ta kuma ya dinga ganin mutane da daraja yana mutunta su sosai. Sakamakon haka sai damuwar sa ta ragu, tsammanin alherin sa ya qaru, kuma dangantakar sa da jama’a ta kara karfi sosai a zuciya da kuma a zahiri. Addinin musulunci ya umarci Musulmi da su yiwa junan su kyakkyawan zato kuma su yiwa ayyukan mumini kyakkyawar fassara wadda ta dace da shari’a.

Imam Ali (AS) yace:

“Ka dauki al’amarin dan uwanka a matsayi mafi kyawu har sai wani abu da zai sa ka janye ya bayyana a gare ka, kada ka yi mummunan zato ga kalmar da ta fito daga bakin dan uwan ka alhali za ka iya yi mata kyakkyawan zato”.

Ta sake tausasa murya hada ƙkwalla kwance a gefan idanunta,

“Mama Yi wa juna kyakkyawan zato yana kulla ksuna a tsakanin jama’a kuma ya samar da hadin kai a tsakanin su. Shugabannin musulunci sun yi bayanai iri-iri dangane da sakamakon kyakkyawan zato. Imam Ali (AS) yana cewa:

‘Duk wanda ya yi kyakkyawan zato wa mutane to za su so shi. Kuma……”.

Bata ƙkai karshe ba ta mike tabar mata wajan fuu kamar kububuwa.

Gaban Fatima ya faɗi shi kenan Mama Hajja ta yi nasarar raba Mamanta da macen kwarai anya haka zata zuba idanu hakan ya cigaba da gudanaBABI NA HUDU

Washegari haka suka tashi babu walwala cikin gidan kwata-kwata Fatima bata samu sakin fuska daga Maman ba har hakan ya takurata, bata damu ba kasancewar Asabar ce ta shirya ta nufi islamiyarsu Malamunsu na lura da rashin kuzarinta kasancewar ita ce monitor na ajin har magana ya yi mata kan hakan ta nuna masa babu komai. Ana tashi ta haɗa kan kannanta suka nufo gida yadda ta samu tsakar gidan kaca-kaca ya ɓata mata rai ga Sadiya a zaune bata komai Fatima sarkin saurin hannu duka ta kaimata,

“tashi sakaryar kawai kina zaune gida kaca-kaca ke baki je makaranta ba ke baki gyaraba ko kunya bakya ji muyi baki”.

Turo baki ta yi ta buga kafa,

“ke kika ga zaki iya nifa bana son aikin wahala wallahi”.

Shigowar Maman yasa ta yi gum ta wurgamata harara,

“uban me ta yi miki kike dukanta?”.

Mardiya zata yi magana Fatiman ta rigata, cikin taushin murya ta furta,

“Mama ki duba ƴyadda tabar gidan nan babu kyan gani kuma ma mai ya hanata zuwa makaranta?”.

Tsuke fuska ta yi,

“ina ruwanki ne Fatima? Gidanki ko nawa, kedai kita kokari ki tashi kibar musu gidan ki huta kici gashin kanki zaki damarmun yara”.

Gaba ɗaya taji komi ya sure mata saita ajiye abayarta ta shiga gyaran ɗakinsu,tana gamawa ta fice ta haɗa wanki tana tulluka kamar jaka sai da ta yi rabi sannan su Sadis suka shigo ya dubeta,

“Aunty kawo in shanya miki”.

Ba musu ta bashi don ta kaji matuka duk guiwarta sun sage sai gab da la asar ta gama wankin taci abinci ta yi wanka ta yi shirin isalamiyya suka wuce. Tsayin sati guda Fatima na fama da ɗaɗɗaurewa daga Maman nasu amma bata fasa bata rubutu da burnuka hayaki ba zuwa lokacin gaba mai tsanani ta kullu tsakaninta da Mama Hasiya don har gida taje taci mutuncinta wanda hakan yasa mijinta ya zuciya ya tako har gida ya yi wa kowa na gidan iyaka da shiga sabgar matarsa. Mahaifinsu yaji zafin abin da ta yi matuka ya nuna mata kuranta ta hayyayako masa amma dake ta kaishi makura sai gashi ya yi mata wankin babban bargo. A ranar da ya cika kwanaki bakwai da fara bankamata rubutu misalin karfe takwas na dare sai ga yaro ya shigo.

“Assalamu alaikum, wai ana sallama da Fatima”.

Saadiya ta juyo tana dubansa,

“jeka kace in ji wa?”.

Mama ta yi saurin sallame sallahr da take yi,

“kai! Kai! Kai!!!”.

Yaron ya juyo a rikice,

“kace tana zuwa gata nan”.

Takaici ya kashe Saadiya dake zaune ta juyo tana kallonta,

“Mamanmu anji waye ne da za a ce ta fita kila zaune gari banza ne”.

“Kan uban can kijimin yarinya yar bakin ciki, Allah ya kawo mana karshan bala i zaki mana munafunci ke kuma munasura ki tashi kina kallona da idanunki kwala-kwala dasu”.

Babu kuzari ta mike ta zura hijabinta ta fita waje, turus ta tsaya ganin Sani mai tureda amma saita kane ta karasa suka gaisa, shiru na ɗan lokaci ya yi mata bayanin kansa da manufarsa ta daɗe tana jinjina batun amma bata tanka ba sai ta yi masa sallama ta wuce gida da zumar sai ta yi shawara. Tana shiga ta samu mahaifiyarta sai walwala take, ta lumshe idanu wani farin ciki na shigarta tana son wannan walwala da nishaɗin data gani a fuskar mahaifiyarta su ɗore amma ta yaya? Zuciyarta ta bata amsa ki kawo mata mijin aure ta tambayi kanta wazan kawo mata? Ta kuma bata amsa “ki amince da soyayyar Sani maitureda” ras gabanta ya faɗi ta yi saurin buɗe idanunta ta saukesu kan mahaifiyarta sai nishaɗi take ta zauna tana tattara nutsuwarta. A zuciyarta hango sufar Sani take iya hangenta bashi da makusa ko kaɗan kuma mutum ne mai kyawawwan ɗabi u ko ina yabansa ake, barshi dai da rashi magana shiru-shiru ne ga miskilanci baya ga haka shiɗin akwai kyautattawa makwabta ga tsafta amma fa ya shiga irin ta samarin zamani hasalima hata rigunan yadi da shada da ake yayin kanana masu ɗan kama samari ɗas baya tu amali dasu. Sai kuma matsalarsa na karamar sana’a baya ga haka duk nauyin mahaifiyarsa dana kanansa biyar shi yake ɗauka.

“An dace ne Fatima?”. Ta yi firgiggita tare da sakin ajiyar rai.

“Eh Mama”.

Ta samu bakinta da furta hakan murya na rawa, saita sunkuyar da kai tana maida kwallar data taho mata,

“waye”.

“Mama Sani mai tureda ne, yace zai ga Baba ya nemi yardasa zai fara zuwa wajena”.

Washe baki ta yi tana faɗin,

“masha Allah Aikin Malam ya yi kyau gobe zanje in masa godiya”.

Mikewa ta yi ta zari mayafi sai gidan Hajja ta baza mata labari dukansu sai dariya suke abinsu, tana fita Saadiya ta kankance idanu,

“ke ki rasa abun kulawa sai Sani haba Aunty?”.

Tsuke fuska ta yi, ta tattare goshi tana haɗiye numfashi da kyar kamar wadda aka yi wa kamshin mutuwa.

“yana da makusa ne Sadiya?”.

Gum ta yi kawai sabida shigowar Mama, haka takasance cikin farin ciki har Babansu ya dawo ta watsa masa labari shima ya ji nuna jin daɗinsa sabida yadda yaga matarsa na rawar jiki sossai ya yi fatan alkhairi. Fatima kwana ta yi tana sake-sake, washegari sai ga Mama Hajja suka ɗauki hanya sai yamma suka dawo da magunguna him ita dai bata tankaba. Cikin kankanin lokaci Sani ya samu mazauni a zuciyar yaran gidansu sabida in suka je siyayya baya karba kowa murna yake dashi in ka ɗauke Sadiya da babu wanda ta tsana sai shi a cewarta halin munafukai ne dashi ko ido baya yadda ya haɗa da mutane kansa sum-sum a sukunya Mama kuwa inda kika san ta goya shi a cewarta zai rabata da kaya ta huta. Fatima ta rasa in da zata aza zuciyarta ta huta har ga Allah bata kaunar ganin Sani amma idan ta tuna yadda Mamanta ke farin ciki sai taji guiwarta ta sare kwarai. Watansu biyar da fara soyayya yana zuwa jefi-jefi amma babu wani fahimtar juna tsakaninsu kwatsam mahaifansa suka zo da batun kawo kuɗi. Fatima bata san dawan garin ba sai kawai jin batun kawo kuɗinta ta yi hankalinta ba karamin tashi ya yi ba amma ko koɗan bata nuna ba tsoron ma nunawar take mamaki dai ya hanata magana ganin yadda aketa aikawa makota an kawo kuɗin Fatima dubu goma. Sadiya kuwa bata nan bata san wainar da ake toyawa ba sai da ta dawo gidan kanwar mahaifiyarsu da daddare tun a hanya ake mata murna kanta ya ɗaure lallai ta yadda Mama ta bari anga wallansu banda haka kawo kuɗi ne wani abun yayatawa har haka da haka ta karasa gida tana zumuɗin jin gaskiyar lamari. Ilai kuwa tana shiga Mama tatareta da batun duk sai taji zuciyarta a jagule yar murnar data taho da ita na samun nagartacen saurayi Farouk kanin mijin kanwar Maman duk sai ta koma ciki ta ajiye wa Maman kayan da ya siya mata jiki a saɓule,

“Mama ga wannan Uncle Farouk ne ya bani, yace zai zo su ƴyi magana da Baba”.

Fatima ta yi karambanin cewa,

“ke me yasa kika karɓo masa kaya? Ki bari ayi magana tukuna baku tsoron abin magana wallahi”.

Turo baki ta yi,

“ina ruwanki bakin ciki kawai ko dan Sani baya kawo miki to hada ma waya a ciki kuma touch”.

Maman tana jinsu da bata tanka ba, ba kuma ta dakatar da Sadiyan ba sai ma ta juya tana wata sabgar Fatiman taja jiki, sai dai jin Sadiyan zata zake ne yasa ta tanka cikin ɗaurewa kan ma ta kai karshe Fatima ta bar wajan.

Da rawar jiki ta buɗe tana dubawa kaya turum dasu masha Allah sai ta hau washe baki ta manta da batun Fatima aka hau duba kayan arziki. Sadiya kam lamarin ya ɗaga mata hankali tana tausayin yayarta tasan kwarai Sani baya cikin tsarinta amma tana mamakin kawaici da zurfin ciki irin nata da bazata fito ta furta ba, har zuwa washegari abun yana damunta sai da yamma ne ta sameta a ɗaki babu kowa sai ita da Maman nasu wadda itama tana ɗakinta ta dubeta,

“Aunty wai garin ya haka ya faru? Yaushe ma kuka fahimci juna da za aƴyi batun aure?”.

Ta kare mata kallo ta fahimci kudurin Sadiyan mudun tana son cin fuskarta to kuwa batun Sani take taɓowa sai ta yi murmushi,

“yadda kika ji batun haka na tiskeshi babu wanda ya nemi jin ra ayina”.

“Har Baban?”.

Kai ta ɗaga mata tana jinjinawa, sai kuma ta mirgina kan kamar wani marayan yalo ta lumshe idanunta kirjinta na harbawa da sauri da sauri.

“amma Aunty Sani ba tsaranki bane kuma baku fahimci juna ba”.

“Sadiya ke yarinya ce tsayin lokaci ana soyayya ba shi ne fahimtar juna ba, idan kuna da zurfin tunanin a watanni ma zaku iya fahimtar junnanku saidai bambancin ɗabi a kowa da tasa. Kuma batun dacewa Sadiya dama mace na zaɓawa kanta miji ne hakkine kan iyayye su zaɓama mace mijin aure mudun sun amince da ɗabi u da nagartarsa…..”.

“Aunty ki aje wannan batun, zamani ya sauya”.

“Zamani ya sauya tsarin adddinni kenan Sadiya?”.

Ta faɗa murya a cakuɗe tuni Sadiyan ta harzuka tana dubanta.

“Komai yana tabbata idan da soyayya amma…..”.

“Dakata Saadiya Sani yana da makusa ta fanin ɗabi’a ko kuma hallita shi na tambaye ki eye?”.

Cikin ci da zuci ta dallawa Fatiman harara ji take kamar ta shaketa ta mutu ta huta.

“Babu amma bai dace dake ba, babu tsari a haɗin kwata-kwata haba Aunty don kin rasa miji sai kuma ki auri wanda ko kansa bazai iya rikewa ba balle hidimarki? Sabida Allah an miki adalci a wannan tafiyar? Shin koda ki ke batun addinni basai in kina sonsa ne? Kina ji zaki iya rayuwa dashi? Zaki iya kyautatta masa bayan babu ɗigin soyayyarsa a kirjinki? Ko zaki rantse da Allah kina sonsa? Me yake ruɗarki ne? Kema fa ɗiya ce mai ‘yanci ko addinin da kike takama dashi kike koyi bai amince ayi miki auran da baki so ba akan me? Wai meye ne……!?”.

Gaba ɗaya ta ruɗa Fatiman numfashinta sai kaiwa da komowa yake yi maganganun Sadiya sun mata mugun fami na bunannan abunda yake ranta ta dafe kai “ya illahi…..”. Ta cigaba,

“kinsan Allah koda ban samu wanzuwar Farouk ba wallahi wallahi babu mai azamin kwataragin da zai nakasani, bazan jiɓanci irin su Sani ba balle su kasheni mutum sumun muka sau koma guma miki ya yi babu ubanda zai yarda ita Mama kawai burinta aurar dake kibata waje ta rage gurbi to ki barta ta kashe ki tana biye wa Mama Hajara ko ita haka ace mata mama Hajaran tana jawa yaranta mugun alkaba in datake ja maki na lura abu kaɗan saita miki mugun baki bake kaɗai ba harmu amma tafi tsaurara miki shin aure ba lokaci bane? Kan menene Aunty kema fa mutum ce mai yanci kamar kowa yanzu kiri kiri ta rabata da kawar kwarai Mama Hasiya IDAN KA DAKA TA BADO RUWA YAƁJAKAƁhar arasa igiyar zabarinka me ake da kusanci irin na Mama Hajara Aunty a tunanina makocinka yafi ma ɗan uwa amma wallahi Mama Hajara guba ce mai lasisin kai Mama mahalaka……..”.

“Aunty Sa’adiya Yaya Fati fa ba irinki bace ki barta kawai ta yi……”.

“To Mardiya ta zauna a kasheta da ranta”.

Kamar zakanya haka ta ɗaga labulan ɗakin tana huci ta yi kan Saadiyan,

“to munafuka mai bakin hali irin na ubanta, ki faɗamun idan bata auri Sani ba jikata zan insha? Ko so kike mita zama muna haɗa kafaɗu taji daɗin rainani? Ke inbanda butulci ai godema Sani zaki ki kyautatta masa, shi daya ce yana sonta shekararta nawa a zaune? Waya taɓa tayawa? Ko kare ya taɓa shinshina Fatima? Allah ya taimakeni zan rabu da kaya kinamun bukulu zaki zugata shima Sanin daya ya yazo da taimakon Malam na kan gangare ne daya bata rubutu sai shegen nauyin jinnin tsiya, kinsan Allah ki zugata da kyau duk randa na karajin bakinki kan aibata Sani Saadiya Allah ya isa ban yafe ba”.

Sakin labulan ta yi ta bar ɗakin tana huci wani abu dum ya ratsa kawunan yaran, Fatima taja numfashi tana dubanta.

Kingani ko Saadiya abun da nake guje miki kenan fushin Mama, tana da zafi kan al ammarin da take so ke kuma rawar kai ya hanaki fahimta. Ni babban takaicina ma yadda take aibatamu ya fimun ciwo Sa’adiya bakin mahaifiya kaifi gareshi fiye da tunaninki…….”.+

Shigowar mahaifinsu da mahaifin nasu ne ya tsaida su, sai gata ta zauna tana huci. “Gasu nan ka zamo shaida wallahi, mudun ta kara sa baki kan lamarin Sani da Fatima ban yafe mata ba”.

Shiru ya yi yana dubanta, daga bisani ya dubeta.

“Duk abida kuke Mariya bana tankawa sabida bana san tashin hankali na rasa meke damunki kinbi kin tsangwami kanki da yarinyar nan kamar kanta aka fara jinkirin aure ki sani fa komai nada iyaka a rayuwa”.

“Kace haka mana tunda bakai kake ciyar dasu ba sai abinda ka samo ka miko mana…..”.

“Dakata Mariya ki fahimce ni ba wannan batun nake miki magana ba ina jan hankalinkine kan yawaita Allah ya isa da kike rika a matsayin makamin hukunta yayanki ganinki hakan zaisa su tsorata su kaucewa aikata hakan kinkasa fahimtar bakin uwa kaifaffan makamine dake datse farin cikin rayuwar yaya haba Mariya yaya fa amane a hannunmu. Idan yaro ya yi laifi kafin a yi masa fada ko bayan an yi masa, sai ya bayar da uzuri ko ya nuna ya tuba in za a doke shi, ko ana yi masa fada aka ga ya ji tsoro, a nan yana da hakkin karbar uzurinsa, domin kamar yadda muka san babba yana bayar da uzuri a karba haka yaro yake, muna iya cewa nasa ya fi na babba muhimmanci ba kadan ba.

Yana da muni kwarai idan ya bayar da uzuri ko ya ji tsoro ya tuba a ki karba ko a gwale shi, wannan yana daga hanyar rushe tarbiyyarsa, yana da kyau iyaye mu sani cewa yaro abu ne mai santsi da laudi, ya kamata mu sani cewa kamar yadda muke son a karbi tubanmu da uzirinmu, to haka yara suke tsammani daga garemu, saboda haka tsanantawa game da al’amarin yaro yana karya shi ne, yana kuma lalata masa tarbiyya. Kur’ani mai daraja ya koyar da mu wannan darasin a cikin kissar annabi Ya’akub (a.s) yayin da ‘ya’yansa suka nemi afuwa, sai ya amsa musu da cewa zai nema musu gafara wurin Allah.

Tausasa wa yara da zama tare da su yana daga cikin mafi girman hakkinsu mai muhimmanci a cikin abin da yake yi masu tasiri gun tarbiyya; Wani lokaci iyaye ba sa son yaro ya zauna wajansu ne don su kansu ba su kiyaye abin da ya kamata ba, sai ka ga ba abin da suke sai gulmar mutane, don haka ne ma sai su ce da yara: Kai! ku tashi suna nan suna jin duk abin da ake cewa. Iyaye su sani cewa yaro dan koyi ne abin da yake gani shi zai tashi da shi

Don haka ne idan kana so ka yi wa yaro fada kan wani abu to ya fara ganin daidai a aikace daga gare ka, misali kana son yi wa yaro fadan zubar da abinci in yana ci, ko ya yi bismillah in zai ci, ko hamdala idan ya kare, ko wanke hannu kafin ci da bayan ci, ko kula da salla da zuwa masallaci, ko idan wani yana magana ya saurara kada shi ma ya yi magana, ko kada ya yi zagi, to duk irin wannan kafin ya yi masa tasiri yana da bukatar ya gani ne a tare da kai a aikace.

Misali, idan kina so yaronki ya san yadda ya kamata ya kira sunan babansa, sai ki rika kiran uban da wannan sunan, ba kina kiransa da wani suna ba sannan kina son yaron ya rika kiransa da wani sunan daban ba.

Yaro yana da hakkin yin abokai; sai dai yana da kyau a kula da abokan yaro da zaba masa abokai salihai na gari kamar yadda idan za a yi aure ake zaba masa uwa mumina, a sani bayan iyaye ba wanda ya fi yi wa yaro tasiri irin abokai, don haka da iyayen yara zasu yi kokari su hada ‘ya’yansu abota da yara na gari da ya yi kyau, haka nan ma a ba su kissoshi wadanda kan iya taimakawa su nisanci yaran banza”.

Shiru ta yi tana muzurai ya yi musu nasiha mai ratsa jiki dukansu suka amsa laifinsu Sa’ adiya ta tsuguna ta bata hakuri daga nan ya fita zuwa in da zashi.

BABI NA BIYAR
***
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji, al ammura nata tafiya dai-dai gwargwado ranar Laraba aka kawo kayan lefan Khadija akwati huɗu da karamin kit, Mamansu Fatima sai rawar jiki take dasu aka yi komai ita dai Mama Hasiya na gefe tana kallon ikon Allah, fitar Mama Mariya keda wuya wata makociyarsu Ladi dilalliya ta kali Mama Hajja ta ce,
“kedai kin huta kin fita sahun su o o yaranki da sun taso a hannu a hannu ake kwashesu kamar waina”.
“Kedai bari Ladi gadai su Fatiman Mariye ne an samu an ɗan samu mashinshini Sani mai tureda da kyar shima saida aka haɗa da bin Malamai”.
“Malamai?!”.
Wasu mata su huɗu suka haɗa baki wajan faɗar hakan, cikin zakwaɗi ta muskuta tana kwance musu zare da abawa Mama Hasiya tuni ta daskare a wajan jin yadda ta takarkare tana zuba musu kannun labarai ji ta yi bazata iya ba ta mike ranta a ɓace,
“kin bani mamaki Hajara wallahi ko babu mutunci ke mai rufa asirin Mariya da iyalantane kodan darajar makotaka”.
“Ke Hasiya rufamun baki a wane dangin?”.
“A dangin daya fi komai kusanci dake wato MAKWABTAKAƁna rasa mutanan yanzu mai muka ɗauki kusanci makwabci daya fi ɗan uwa. “Hakkin makwabcin ka shi ne ka kare shi a bayan idonsa, ka girmama shi a gaban idonsa, ka taimaka masa idan an zalunce shi. Kada ka yi kwakkwafi domin gano laifukansa, idan kuma ka san wani mummunan abu dangane da shi to ka boye. Idan ka san cewa zai karbi gyara da nasiha sai ka yi masa nasiha a kebe (wato ba cikin mutane ba). Kada ka yi watsi da shi a lokacin da ya shiga tsanani da wahala. Ka kau da kai daga kurakuransa, ka yafe masa idan ya maka laifi. Ka zauna da shi cikin mutunci…” Wannan shi ne bayanin Imam Sajjad (a s).Mai yiwuwa ne wasu mutane su yi sako-sako da hakkokin abokan zama har ma su cutar da su. Wannan kuma ya na iya zama musabbin rashin kwanciyar hankali a gaba. Domin haka ne Imam Sajjad (a s) ya ke horonmu da mu guji gulma da neman sanin asiran makwabta. Gida wuri ne na aminci da natsuwa saboda haka bai kamata a yi wa mutum shisshigi a wannan hurumi na shi ba. Idan mutum ya kiyaye wannan hakki to shi ma kansa zai sami natsuwa saboda kyakkyawan zato da zai yi wa makwabtansa.
Addinin Musulunci ya ba da muhimmanci kan batutuwan kauna da taimakon juna domin rayuwa ta yi dadi. Domin samar da al’ummma mai lafiya da tsabta, koyarwar addinin Musulunci ta na kokarin rage bambamce bambamcen da ke akwai tsakanin bangarorin al’umma, alal misali mai sukuni da wanda bas hi da abin hannu, saboda mutane su zauna lafiya su yi dogaro da juna su natsu da juna. Domin tabbatar da hakan ne addini ya ke umarni da ayyukan da su ke karafafa dankon zumunci kuma ya ke hani da duk abin da ya ke jawo sukurkucewar yarda da juna a tsakanin mutane.A mahangar addinin Musulunci, dole ne alakokin mutane su kasance na gaskiya ba tare da wani makirci ko kisisina ba. Kyakkyawar dangantakar zamantakewa ta na wanzar da natsuwar zuci da aminci a rayuwa, mummunar dangantaka kuwa ta na haifar da sukurkucewar dabi’un kwarai da kuma matsalolin zamantakewa. Masana su na cewa rushewar kyawawan dabi’un a cikin al’umma ta na fara wa ne daga lalacewar daidaikun mutane. Idan mutum daya ya kulla wa wani makirci sannan shi ma dayan ya rama masa da halinsa, wannan dabi’a ta na iya yaduwa kuma da kadan kadan sai ka ga al’umma ta lalace. Allah ya kiyaye.Domin karfafa alakokin mutane addinin Musulunci ya na horo da kyautata alakoki tsakanin bangarori daban daban na mutane, wadannan kuwa sun hada da makwabta.
Kyakkyawar makwabtaka ta na da tasiri wajen tabbatar da aminci da jin dadin rayuwar jama’a, kuma ta na kawo albarka mai yawa. Kiyaye hakkin makwabci ya na kara wa mutane kaunar taimakon juna da hadin kai wajen aiki da tunani, kuma wannan shi ne tushen kulawa da wurin zama da amincinsa da kuma tsabtarsa. Har wala yau, girmama makwabci ya na wanzar da natsuwa irin ta ruhi sannan kuma ya na sa tsawon rai a duniya. Makwabcin kwarai wata ni’ima ce daga ni’imomin Allah Madaukakin Sarki. Allah ya halicci zuciya bisa dabi’ar kaunar mutumin da ya ke kaunarta kuma ya ke kyautata mata, saboda haka ne ma kyautatawa makwabci ya ke sa zamantakewa ta yi kyau, alakokin mutane su yi karfi. Saboda haka ne Imam Ali dan Abu Talib (a.s) ya ke cewa: “Kyakkyawar makwabtaka ta na raya garuruwa, ta na kuma tsawaita rayuka.”Mai yiwuwa ne wasu mutane su yi sako-sako da hakkokin abokan zama har ma su cutar da su. Wannan kuma ya na iya zama musabbin rashin kwanciyar hankali. Domin haka ne Imam Sajjad (a s) ya ke horonmu da mu guji gulma da neman sanin asiran makwabta. Gida wuri ne na aminci da natsuwa saboda haka bai kamata a yi wa mutum shisshigi a wannan hurumi na shi ba. Idan mutum ya kiyaye wannan hakki to shi ma kansa zai sami natsuwa saboda kyakkyawan zato da zai yi wa makwabtansa.Kyakkyawar makwabtaka, taimakon mutane, gaisar da mara lafiya, tallafawa makwabci da dukiya da makamantar wadannan, su na cikin hakkokin makwabtaka kuma alamu ne na mutum mai kaunar dan Adam.+
STORY CONTINUES BELOW

Idan makwabcinka ya sami wani alheri ko wata nasara to ka yi masa murna, ka yi adduar Allah ya sanya masa albarka a ciki. Annabin rahama Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa) ya ce: “Wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira ya kyautatawa makwabcinsa.” Hakkin makwabci lamari ne da ya shafi abubuwa da yawa. Annabi yana cewa ko gini mai tsawo mutum zai yi, ya nemi yardarm makwabtansa. Idan muka dubi wannan umarni na Ma’aki za mu gane girman hakkin makwabci. Daga cikin cutarwar da dogon gini ya ke yi wa makwabtan da gidajensu gajeri ne, akwai tare musu iska da hasken rana da sauransu. Imam Ali dan Abu talib (a s) ya na cewa: “Manzon Allah ya kasance ya na umurtanmu da kiyaye hakkokin makwabci har muka yi tsammanin makwabta za su gaji juna.” Wannan shi irin muhimmancin da addinin Musulunci ya ba wa makwabtaka. A nan ya na da kyau mu sani cewa addinin Musulunci ya na horo da girmama makwabci ko mene ne addininsa. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya zauna lafiya da makwabtansa wadanda ba Musulmi ba, kuma ya ba su hakkokinsu. A wani lokaci ma wasu daga cikinsu su na cutar da shi amma bai taba ramawa ba sai da alheri”.
Kuka ya kwacewa Fatiman da tun fitar mahaifiyarsu ta korosu ida da Sadiya da kuma Mardiya kan su zo suga laife kar ace suna bakin ciki, Sadiya ta shigo tana huci kamar mesa ta nuna Maman da yatsa,
“ke kuwa annamimmiya ce munafuka maketaciya babu komai a tarayyarki da mahaifiyarmu sai nakasa da jagulewar rayuwa ban taɓa ganin mahaifiyarmu na nuna mahaifinmu da yatsa ba sai akan huɗubar da kike mata lallai keɗin ba makwafciyar kwarai bace nan fa waje ya hargitse da drama da kyar Hasiya ta janye Saadiya ta yi waje suna fita ta yi turus ganin Fatima na kuka hannunsa taja suka yi waje suna fita kowa ya watse Hajjara ta yi kwafa ta furta,
“hmm! Dani kuke zance tayaya zan bari ku huta bayan duk fi yarana nagari daga kan diri har ɗabi a? Tunda uwar taku shasshace ai da ita zan kama kafa idan ka daka ta bado ruwa kuwa zai jaka shi ma Sanin wallahi sai sun rasa shi naga ai mijin marainiya ne baida makusa sai karamar sana a amma kuma yana da nagari”.

Mama Hasiya da kyar ta ƙlallashi su Fatima ta kuma ja hankalinsu kan karsu faɗawa mahaifiyarsu, sun gamsu sun cigaba  da zama a hakan amma amintar mahaifiyarsu na cin ransu.
Haka aka yi bikin Khadija da Mamansu ta yi bajinta sossai yadda ya kamata. Bikin Khadija da kwana bakwai Hajara ta shirya ta nufi gidansu Sani ta yi sa a babu kowa ta samu mahaifiyarsa zaune bayan sun gaisa ta zauna ta dubeta,
“Baba kinsan dai ni aminiyar Mariye ce ko?”.
“Kwarai kuwa Hajara”.
“To gaskiya wani abu na gani da zai cucceki nake kokarin baki kariya kan batun Sani ne da Fatima. Fatima dai da kike gani ba mutuniyar kirki bace, bale uwarta kowa yasan yadda uwarta ke tijare mai gidanta akan ɗan tallafamasa da take da hidimar gida kuma rashin wayaune irin nata ai kai da kaya duk mallakar wuyane. Ita kuma Fati da kike gani bata da kunya ta raina ƴuwarta ya kashin tsuliyarta sabida karatun littattafan nan da take na zamani na batsa ba abinda bata sani ba shuyasa kullum kika je tana ɗaki ana cewa shiru-shiru ba wani shiru shiru masifa ce ke cinta da jaraba duk tabi ta kaɗe ta yi baki tasa kwazaba a ranta tana bin maza”.
Ai sai Baba ta shiga tafa hannunwa tana salallami kamar ba ita ba, banda godiya babu abunda take mata haka suka yi sallama aikuwa a daran ta yi wa Sani iyaka da Fatiman dake yarone mai biyayya take ya amince badon ya so ba.
Kwanci tashi saida Sani ya shafe wata biyu bai zo gidansu Fatima ba, tun abun baya damunta harya soma damunta musamman ganin yadda Maman ta ɗaga hankalinta ita kuwa Sadiya murna take tana Allah yasa an tafi kenan ganin babu mafita yasa ta tunkari Hajja ai kuwa a ranar suka nufi wajan Malam na gangare basu dawo ba saida kulin magunguna him Saadiya takaici ya kasheta ko gaishe da Hajaran ma yanzu ta daina in ba gaban Mamansu ba. Haka aka tasa Fatima gaba ana ɗurkamata in taki sha taci zagi wata rana hada tsinuwa abun na damunta sai dai ta kulle tasha kukanta tsayin wata shida babu Sani babu dalilinsa mahaifinta ne ya gaji karshe yaje wajan mahaifinsa da batun saidai guiwa a sage ya dawo sabida sunce sun janye neman auran kuɗin su suke bukata babu jinkiri yana dawowa ya aikaƴmusu kuɗinsu ta hanyar mijin Mama Hajara ai kuwa tasha murna da tsale bai sanar da kowa ba sai bayan kwana uku da faruwar al amarin ya tarasu gaba ɗaya bayan an yi sallahr isha i saida ya dubesu ɗaya bayan ɗaya sanan ya numfasa ya fara magana.

STORY CONTINUES BELOW

“Fatima ina son ki kasance mai hakuri babu ta inda ubangiji baya jarrabtar bawansa ta kowane yanayi, ba kuma rashin so ba ne kaddara ce ya kaddaro mass don gwada imaninsa. A jiya mahaifan Sani sun karɓi kuɗin auransu da zumar sun fara kuma babu wani kwakkwaran dalili na fasawar tasu kawai ra ayi ne”.
Wani duhu-duhu Maman ta hango yana kusantota ta furta,
“Malam me kace!?”.
Ya sake maimaita mata da karfin guiwa ai saita yi kukan kura ta yi kan Fatima da duka,
“wallahi Malam bakin halin wannan ɗiyar ne ya ja Sani ya gujeta amma bawai da wani daliliba ai dama na ƙlura bata kaunarsa bata kaunar batunsa ku hira yazo ta dinga nunkufurci kenan sai kizo ki zauna mu taru mu jaɓe hankalinki ya kwanta nidai da haihuwarki gara ɓarinki…..”.
Cikin masifa ya katseta,
“wato Mariya ba zaki iya bakinki kan yaran nan ba ko? Kina gani tsabar ɓarin zance da kike Sadisu na ƙlura ya yi masifar rainaki ba kaɗan ba ko magana kika ƴyi kunkuni yake miki amma kinki kiyi hankali ko?”.
“Dakatamun kaika haifesu ko ni? Kokai kasha ruwan zafin ina ruwanka? Kaidai kaji da talaucinka daya dabaibayeka ya hanaka ko siyowa yaranka gazal bale akai ga abinci da sutura”.
Kasa cewa komai ya yi ya mike ya bar mata wajan Mardiya sarkin saurin kuka ta rushe da ihu aikuwa ta yi kanta da duka da ita da Fatiman saida ta yi mai isarta. Kwanaki bakwai tsakani masu son Sadiya da Mardiya suka zo tambaya mahaifinsu ya amince kasancewar suna gab da gama makaranta saura watanni tara aikuwa cikin watan aka karɓi kuɗin auransu dubu ashirin ashirin Mama har rawa tayi don murna tana faɗin basu yi bakin nauyin jini ba Fatima ta yi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita ta kaɗe ta yi baki da wata irin rama. Mamansu dai ta rasa abin yi, ta tunkari Hajara da kudurunta na son komawa wajan Malam kamar almara sai Fatima ta fara samari akwai Musbahu nan gaban su yake ɗan kofar kwaya ne akwai kuma Auwal ɗan nan saulawar ne amma abun mamaki zuwansu baifi biyu ba suka ɗauke kafa hakan kuma ya farune dalilin aikin Mama Hajara data sa maigidanta ƴya je ya aibata Fatiman a wajansu a haka a haka saida ta yi samari takwas babu su. Abun yana damun ita kanta Fatiman babu laifin tsaye babu na zaune sai su janye jikinsu kwatsam Mama Hajara ta samu Mama a wani yammaci.
“Gaskiya Mariya aljannine ya aurar miki ya domin dai hakan ba banza ba ki duba yadda tayi samari da yawa amma duk sun gudu”.
“Nima na fara tunanin hakan Hajja amma bana tunkari mahaifinta da wannan batu ba kinsan halinsa”.
“Shiryawa zaki muje wajan Malam na gangare amma ina ga wannan karon da ita zamu je ki bari gobe zanje wajansa idan da itan ne ke basai kin je ba”.
“Shikenan Hajja na gode ubangiji ya bar zumunci”.
BABI NA SHIDA
Washegari da safe Mama Hajara ta shirya sai wajan Malam bayan sun gaisa ta muskuta ta faɗa masa bukatarta, yayi jim daga bisani ya furta bazai iya ba, nan ta zauna ta dinga kawata masa Fatiman hada guzurin hotanta tuni shaiɗan ya tayata yaji ya gamsu da kudurinta ta yi godiya ta nufo gida. Har Alla alla take gari ya waye ta tafi tun Asuba Mama take tashin Fatima tasata ta shirya lallaɓata take,
“Fatima don Allah Hajja tace banda musu aikinkin mai wuya ne cire bakin aljani kar ki yi gaddama”.
Ita dai jinta take da kunnuwanta har goma ta yi Hajjan tazo suka tafi, tafe suke babu mai magana suka dumfari surkukin ƙlungun shiru babu jama a cikinsa suka samu wasu mata su biyu nan da nan ya sallamesu yana washe baki da ganin Fatiman daga bisani yace ita Fatima ta biyoshi Mama Hajjaran ta zauna a wajan tabarma Fatima taja ta toge tana kunkuni zagin duniya Hajaran tai mata taki shida saida ta hankaɗata sannan ta shiga shi kuwa ya dana sakata tsakaninsa da Allah neman haike mata yaƙke gaba ɗaya ya rikice wani kuka ya kwacewa Fatiman tare da nadamar biyo makiyarta ta zahiri da badinin idon mahaifiyarta saida ya rabata da hijabinta da zaninta Allah ya bata sa a ta suri wata kwalba da alama rubutu ne a ciki ta kwaɗa masa a kai ya faɗi da sauri da gyara jikinta ta fito ta duba amma babu Mama Hajjara babu dalilinta sai yanzu wani tunani ya faɗo mata tabbas wannan shirin Maman ne babu ko kwandala hannunta ta tari napep sai kofar gidansu suna tafe tana share hawaye saida ta sauka tace bari ta amso masa kuɗin sai taji ya ce “Fatima Ahmad ki barshi baki ganeni ba Zaidu Barmo ne”. Mamaki ya kamata ya yi girma sossai ga wata kamala irin ta nutsuwa a nan yaƙke mata bayanin ya cigaba da karatu ita dai jinsa take kawai ganin bata da nutsuwa yasa ta yi masa godiya kai tsaye ta faɗa gidan Mama Hasiya da kukanta ta zayyane mata komai yadda abin ya faru Mama Hasiya ta girgiza kwarai da gaske da al amarin ta dinga yi mata nasiha da ta kame kanta.  Ta dubeta tare da furta,
“Fatima niko da zaki bi shawarata da kin koma makaranta tunda result ɗinki ya yi kyau sossai”.
“Aunty wallahi ina maitar karatu amma halin yi ne babu, kuma kuɗin ɗinki dana dogara dasu dasu nake tallafawa Mamanmu”.
“Karki damu ni zan miki registration kije ki nemi yardar mahaifinki yadda kuka yi kizomin da bayani gobe”.
“Shikenan Mama na gode”.
Kai tsaye gida ta wuce tana jinjina ma Mama Hasiya bisa kyautattawarta mace ce makociyar kwarai mai kyan hali da dattako ga saukin kai tabbas da da akai makwafta masu kyautattawa da makwaftaka ta domin Allah to kuwa da an samu zaman lafiya a duniya.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin kaɗuwa da sanɗa ta shiga gidan da Mardiya ta fara cikiɓus ta wuce ta bita da kallon tausayawa gani yadda duk fatin ta zabge, ta na shiga Maman ta tareta da balbalin masifa kamar zata kasheta,
“yanzu ke sabida matsiyaciya ce bakisan arziki ba shi ne kika gudu kika barta ta nemiki ta rasa to wallahi daga yau ba zan sake wahal da kaina wajan nema miki magani ba koda kanki kaɗai za a rasa manema tunda dai su sauran sun samu kita zama”.
Kanta ya yi zafi ta karewa mahaifiyarsu kallo ta takarkare tana aibatata. Fatima rasa bakin magana ta yi kawai ta faɗa ɗaki tana kuka, tabar komai cikin ranta babu wanda ta faɗawa haka ta zauna jigum Saadiya da Mardiya suka tasata gaba suna bata hakuri zuciyarta ta yi zafi kanta ya  dinga ciwo sossai. Mikewa ta yi ta buɗe ma ajiyarta ta nemo result ɗinta ta kakkaɓe tana jin wani nishaɗi a ranta shigowar Sadis taji daɗi sossai ta bashi yaje ya yo mata photo copy ya dawo ta adana. Misalin karfe tara na dare ta mike ta nufi ɗakin mahaifinta ta yi sa a babu kowa sai shi ɗaya da sallama ta shiga bayan gaisa ta dubeshi,
“Baba ina son ka yarjemin zan koma makaranta”.
Yayi jim daga bisani ya furta,
“makaranta Fatima?”.
Ta ɗaga masa kai ya ƴyi dum,.”Fatima ina sonku da karatu amma lallacewar zamani yasa ina tsoronsa ina da burin karatun ɗiya mace a rayuwata domin ilmi haskene musamman ga Mata. Sannan banda karfin ɗaukar nauyin karatunki amma wallahi ina da burin ganin yarana sun yi karatu musamman ɗiya mace. Mata! Mata!! Mata!!!  Mata sune k’ashin bayan kowace al’ummah,domin idan mace d’aya ta samu wadatacan ilmi tamkar an ilmantar da al’umma ne bakid’aya kasancewarta makaranta ta farko ga yaro,a kwana a tashi.Ilmin d’iya mace zai iya kasuwa fanni daban-daban wato boko da addini.Ilmin addini shi ne mafi kyautuwar ilmi awajan kowane mahaluk’i mai neman dacewa ba wai ga d’iya mace kawai ba amma da yake akan d’iya mace nake magana shi yasa zanfi bada muhimmanci akanta. Yayin da kika riski kanki a b’igiran da basa b’ukatar karatun d’iya mace mai tsayi, karki zafaffawa kanki wajan cewa sai kinyi, maida hankali wajan neman ilmin addinni wanda zai zamo miki abin alfahari anan duniya da kuma gobe k’iyama.Dashi ne zakisan yadda zaki bautawa ubangijinki cikin tsarkakewa da nutsuwa,dashi ne zakisan kanki da abinda zai amfaneki.Gwar-gwardon ilmin da kika samu koda iya makarantar gaba da primary ne zai amfaneki ya amfani iyalanki muddun kinyi mai inganci.Ilimin boko bai zama koma baya idan mukai duba da yanayin zamani, saboda a yanzu anci gaba sosai  komai saida ilimi.Ilmi baya zama b’atanci saidai akwai hanyoyin da suka dace abi wajan nemansa.Wasu lamuran da suka shiga cikinsa ne sukai katutu suka haifar da rud’ani a zukatan al’ummah da iyayyanmu Maza da Mata.Amma banda hakan babban abin alfahari ne ace yau mace ta taka wani matsayi na taimakon al’ummah musamman a harkar lafiya.Abin takaici zaka shiga asibitoci da dama kaga bamu da manyan likitoci mata sai maza, wanda wannan babban abun kaicone a garemu ace Namijine zai duba mace sab’anin mace yar’uwarta,kuma hakan ya samo asaline sakammakon k’arancin mata a wannan fannin,wasu  suna so suyi amma babu damar hakan saboda rashin  wadata yayin da wasu kuma da wadatar amma iyayensu basu basu goyon baya akan hakan ba.

Hakika ilmin ‘ya mace nada matukar muhimmanci,saboda muhimmancinsa nema wasu ke ganin a ilmantar da ita yafi a ilmantar da d’a namiji,hujjarsu ita ce:
     “Ita mace Ita ce uwa kuma makarantar farko ga kowanne dan adam,haqqin kula da tarbiyyan yaro yafi yawa ga uwa ko kuma nace gabadaya ma ya ta’allaqa ne akan ita uwa,toh idan bata samu tayi ilmi ya za’ai taba yaronta ingantacciyar tarbiyya?” Wannan shine ra’ayin masu kafa hujjja kan cewa ilimin mace yafi na da namiji.

Annabi(s.a.w) yana cewa”Neman ilimi farilla ne(wajibi) ne akan duk wani musulmi da musulma”
   Idan muka duba anan zamu ga cewa Annabi bai ware maza zalla kan maganar neman ilimi ba,a’a sai yace” Musulmi da Musulma” Sannan ilimin nan ba wai ana nufin na addini bane kawai a’a harda na zaminin,mu duba hadisin nan na Harijata bn Zaid bn Thabith zamu fahimci hakan,Zaid bn Thabith ya koyi yaren Yahudawa ya kuma yi amfani dashi wajen karanta wasiqa yayinda Yahudawa suka aiko ma Manzon Allah(s.a.w) ko kuma rubuta wasiqa yayin aika musu,shin Idan har akwai wani aibu ko abin tir acikin haka Annabi ya tura shi(Zaid) musamman domin yaje ya koyo wannan ilimi a wajen wadanda suka kasance ba musulmai ne ba?

   “Ina tsoron in umarci bayahude ya rubuta min wasiqa yayi qari ko ragi acikina hakanan kuma ina tsoron in wasiqa tazo daga yahudawa ace bayahude ne zai karanta sai yayi qari ko ragi” Inji Ma’aiki(s.a.w)
(Tuhufatul Ahwazee)
    Duba da wannan hadisin ya kamata iyaaye su riqa barin ‘ya’yansu suna shiga wannan fage na ilimin zamani ana damawa dasu domin ta haka zamu iya ciyar da addininmu gaba, idan kuwa bamu hankalta ba lallai watarana zamu wayi gari muga kafirai sun zamo jagaba akan komai na al’amuran rayuwarmu( Allah ya sawwaqa). Ya ishi mai ilimi daraja saboda fadinsa madaukakin sarki”Allah ya shaida cewa lallai ne babu abin bautawa da gaskiya face Shi,kuma mala’iku da ma’abota ILIMI sun shaida”
    Kuma dai da ilimi ne zaki sauke abinda ke kankk na bauta ko ibada,da shine zaki zama ‘ya mai tsari kuma abar yabo,da ilimi ne zaki kubutar da kanki daga rayuwa ta kaskanci izuwa ga rayuwa mai yanci.

Ma’abota Hikima na cewa “Shi ilimi haske ne,shi yake maida bawa d’a sannan ya maida d’an da bashi dashi bawa” Sannan wasu ma’abota hikiman suka kara da cewa”Ilimi yafi dukiya,domin kuwa shi ilimi shi yake tsaron mai shi kuma duk inda yaje tare yake tafiya da abinsa acikin kansa,acikin qwaqwalwarsa yayinda dukiya kuma mai ita ne ke bata tsaro,idan yayi tafiya ba tare da ita ba toh fa bashi da bambanci da wanda bashi da ita”

Sannan idan mukai nazari da kyau zamu ga babu wani mai ilimi daya tab’a mutuwa da aka rabawa magada iliminsa amma mai dukiya kuwa munji mun kuma gani sau ba adadi,Don haka yan’uwa mu tashi mu nemi ilimin addini dana zamani(boko) don gujewa kunci da kuma dana sanin da kan riski marasa su”
Wani sanyi ne yake kwaranya a ranta tabbas yau ta tabbatar mahaifinsu nada kuduri mai kyau a kansu fiye da tsamaninta muskutawa ta yi ta ce,
“Baba ai hidimar makaranta ba matsala da zarar na shiga zan dinga yin car wash da turare su man kitso dana shafawa ina kaiwa ana siya kuma ga ɗinkuna yanzu ba laifi ana kawowa sai im dinga hidimar dasu”.
“Shikenan Fatima Allah ya taimaka yasa albarka”.
Mama na gefe tana ji bata ce komai ba sai tsaki da ta yi tare da magana kasa-kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *