KOWA YA DAKA TA DABO CHAPTER B KARSHE
BABI NA BAKWAI.
Fatima kwana ta yi sake-sake ganin zata ɓata lokaci a iska ta ɗauro alwala ta durfafi kai wa ubangiji kukanta, washegari da wuri ta tashi ta gama komai ta gaida mahaifiyarta a dakile ta amsa. Karfe goma Mama Hasiya ta aiko yaro kan Fatima tazo ta yi mata kitso Mama taso hanawa amma ganin Babansu yana nan ta barta lallaɓawa ta yi ta saka takardunta cikin abaya ta fita dasu. Da fara a ta shiga ta samu tana ɗaurin kunun zaki ta ajiye takardunta a gefe ta hau tayata suna yi tana bata labarin yadda suka da mahaifinta ta ji daɗi kwarai take ta kira kaninta a waya professor ne ta yi masa bayanin kudurinta na son taimakawa Fatima kwarai ya ji daɗi ya yi mata bayanin wajan da zasu kai takardun a college tare da alkawarin zai kawo mata takardar da zasu kai masa su ce in ji shi yadda abin zai zo musu da sauki. Fatima ji ta yi kamar sun sata aljannah ta karɓi wayar sai zubawa Uncle Sulaiman godiya take yana daga can murmushi kawai yake zubawa shi dai yarinyar na burgrshi jinta yake kamar yar sa kuma wani abun armashi ba shi kaɗai ba hata mai ɗakinsa ya fahimci kaunar da take wa yarinyar sabida nutsuwarta. Sallama suka yi ta dubi Mama Hasiya,
“Mama uncle da matarsa badai kirki ba wallahi wasu lokutan har bana so hanya ta bi dani unguwarsu in biya indai naje kaman ta goyani”.
“Gaskiyarki Fatima Maryam badai kirki ba daga ita har maigidanta”.
Uncle Sulaiman kanin Mama Hasiya ne yana da matar aure da yara biyu, mutum ne mai hakuri da kyautattawa haka ma matarsa yasan Fatima ne a sanadiyar zuwa gidan yayarsa haka matarsa indai tazo Fatima ke mata kitso Sadiya kunshi kuma tana bawa Mama Hasiya ɗinkinta Fatiman ta yi mata duk wannan hidimar koda wasa basa karɓar kuɗinta gara ma Sadiya na karɓa wasu lokutan amma Fatima akaɗa a raya koda wasa haka ɗinki sai dai ta gaji ta daina kawo mata ɗinki takan ce idan suka haɗu,
“Fatima kin dai koreni da batun ɗinki”.
Sarkin kunya sai dai ta yi murmushi kawai, da haka suka saba yawanci dangin Mama Hasiya sun san Fatima don kafin su ɓata da Mama takan ɗauketa su je hidimar danginta, Fatima ta saki ajiyar zuciya tana yaba karamcin matar da ahalinta ta dubeta,
“Mama bansan da bakin da zan gode miki ba”.
“Fatima babu godiya tsakaninmu tamkat jinnina haka nake jinki kuma karki manta ke ɗin makwabciya ce gareni makoci kuwa abun a kyautatta masa ne. Makotaka daya ne daga cikin manyan alakokin zaman takewa da Ubangiji ke hadawa. Makoci ko Makotaka wani babban al’amari ne a tsarin koyarwar Annabin rahma Annabi Muhammadu (SAW). Domin Ubangiji mai girma da daukaka ya fada cikin littafin sa mai girma, cikin suratul Nisa’I aya ta 36 cewa:-
“Ga iyayye a kyautatta musu da makusanta da marayu da makwbta na kusa”.
Da kuma fadin Manzon Allah (SAW) cewa:-
“Jibrilu bai gushe ba yana yimin bayani kan makwabta har na zaci za a ce zai gajeni.”
(Buhari da Muslim).
Sannan akwai hadisin da Abu Shuraih ya rawaito – Manzon Allah (SAW) ya ce:-
“Wallahi bai yi imani ba, Wallahi bai yi imani ba, Wallahi bai yi imani ba!!. Aka ce, “Waye shi ya Manzon Allah (SAW)?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “shi ne wanda maqocinsa bai aminta daga sharrinsa ba”.
Bukhari ne ya rawaito.+
Har ila yau, da fadinsa Alaihis-salam cewa:-
“Wanda ya bayar da gaskiya da Allah da ranar lahira to ya gurmama makocinsa”.
(Buhari da Muslim).
Idan muka yi duba ga wannan aya da wadannan hadisai za mu fahimci girman kyautata wa makwabci da girmama shi, domin girmama shi ma yana nuna cewa mutum ya bayar da gaskiya da Allah da ranar Lahira. Hadisan kwabci basu gushe ba akwai wani hadisin daga Abu Hurairata Allah ya yarda da shi ya ce, an bawa Manzon Allah (SAW) labarin wata mace aka ce, “Ya Manzon Allah, wance tana sallar dare, tana yin azumin ramadana, amma tana da kaifin harshe, tana cutar da makotanta” sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu alheri a tare da ita, ‘yar wuta ce”. Aka sake ce masa: “Wance kuma tana sallar farilla ne kadai, tana azumin watan ramadan, tana sadaka da dan abin da take da shi na cukwi, amma ba ta cutar da kowa. A riwayar Imam Ahmad “Ba ta cutar da kowa da harshenta” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Yar Aljannace”. Bukhari ne ya rawaito shi a cikin (Al’adabul Mufrad). Dadi da kari akwai hadisi daga Abu Juhaifa Allah ya yarda da shi ya ce, wani mutum ya kawo wa Manzon Allah (SAW) karar cewa Makocinsa yana cutar da shi, sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Je ka, ka fitar da kayanka, ka zuba su akan hanya”. Da ya je ya zuba, sai mutane suka rika wuce wa, suna tsine wa wannan makoci. Sai wannan makocin ya ruga wajen Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ya Manzon Allah mutane suna tsine min” sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ai Allah ya tsine maka tun gabanin mutane su tsine maka”.
Sai ya ce, “Ya Manzon Allah ba zan kara ba”. Bukhari ne ya rawaito shi a cikin littafin “Al – Adab”.
Fatima hakika sakaci da wannan al’amari mai girma ba karamin hatsari ba ne ga rayuwar musulmi. Duk da cewa Allah ya kawo mu wani loakci da mafi akasarin makota basa kula da irin wadannan hakkoki, suna cutar da makotansu ta hanyar:- A jiye Mota a kofar gida dan takura masa wajen shiga da fita. Barin ruwa mai mummunan wari da doyi yana kwarara a gaban gidan sa. Barin shara a kofar gida, ko ketare iyaka cikin hakkinsa da shiga iyakar gidansa, ko yi masa sata a wurin aiki ko makaranta ko kasuwa. Bibiyar al’amurarsa don gano laifinsa. Babu laifi idan laifukan nasa sun bayyana kuma ka san cewa zai karbi gyara da nasiha sai ka yi masa nasiha a kebe (wato ba cikin mutane ba).Kai maganar sa wurin makiyansa ko leke ta saman gida ko taga. Damun sa da kadede ko kara lokacin da yake bukatar hutu. Aibata iyalinsa zunɗensa da nuna masa so gabansa saɓanin bayan idonsa. Abinda muka kasa fahimta shi ne kyakkyawar makwabtaka ta na da tasiri wajen tabbatar da aminci da jin dadin rayuwar jama’a, kuma ta na kawo albarka mai yawa. Kiyaye hakkin makwabci ya na kara wa mutane kaunar taimakon juna da hadin kai wajen aiki da tunani, kuma wannan shi ne tushen kulawa da wurin zama da amincinsa da kuma tsabtarsa.
Fatima na ɗaukin ɗiyar makwaftana tamkar ɗiyar dana haifa wallahi yadda nake duban Aisha haka nake kallonki, yanzu haka tare za a kai takardunku sabida mijinta ya barta ta karasa makaranta bayan auranta kar ki ji komai duk sanda ki ke da matsala kofa a buɗe take ki tunkare ni”.
Hawaye ta share tana yi mata godiya ta yi mata kitson ta wuce gida, Sadiya ta samu tana dana waya hankalin ya tafi kacokan ta ɗan ɗaka mata duka,
“keda wa? Ina ce chats ɗin ake da Farouk?”.
Ta karasa furucin tana sauke idanunta kan Mardiya dake kashe murya a waya lamarin sai ya bata sha awa zuciya bata da kashi ta dinga jin ina ma ita ce kome ta tuna sai ta yi saurin watsar da tunani tana faɗi”alhamdullilah”. Sadiya ta juyo,
“a a Aunty littafin mutuniyarki nake karantawa Aisha Chuchu a wani group ashe tana rubutu a yanar gizo?”.
Cikin zumuɗi ta hawo kan gadon, jikinta har rawa yake ta ce,
“kodai wata ce take son samun fada take sa sunanta!?”.
“A’a Aunty ita ce wallahi, karɓi ki karanta sunansa DOGARO DA KAI”.
Mamaki ya cikata Fatima sai godiya take zubawa Sadiya kamar ta bata kujerar makka, ita dai Sadiya murmushi take tana mamakin kaunar da yayarta kema Chuchun.
STORY CONTINUES BELOW

Kwanci tashi cikin kwanaki bakwai aka gama komai mahaifinta ne kaɗai yasan Mama Hasiya ce ta yi mata hudimar makaranta, Fatima ta kama karatu gadan-gadan babu wasa sun bata komai zata yi karatunta kan _Diploma english islamic/hausa_. Bakinta har kunne gata ga Aisha karatunsu suke sossai kodayaushe ta taso makaranta takan biya wajan Mama Hasiya yanzu hantarar da Mama ke mata ta kara yawa sabida yadda Mama Hajara take zugata kan masu karatu basa auruwa wasu kuma basa karatun watsewa suke da ɗalibai ko malaman hakan yasa ta kara matsawa Fatima. Fatima bata da abinyi daga addu a sai azumi ta kama sana’arta babu kama hannun yaro car wash ɗinta mai kyau babu ha inci rububinsa ake sossai dasu take rage hidimar biro da handout da sauransu a gefe guda data samu kuɗin ɗinki take rabawa huɗu kaso ɗaya ta kaiwa Mama Hasiya ajiya kaso ɗaya ta yi hidimar kayan shafarsu ɗaya kuma ta bawa mahaifinta da mahaifiyarta. Hankinta ya kwanta sai yar rama da take yi a tsaye sabida yawan tunani.
SHEKARA DAYA
Duk wani surutu da maganganun muyane suna dawowa kunanta wasu su ce sai mai kuɗi zata aura wasu suce karuwar gida ce da sauransu. Babu wanda take duba ta tanka masa daga matasan har tsoffin banzar gori kuwa tana shansa musamman yanzu da akasa ranar su Sadiya biki saura watanni biyu Mama sai hakilon fito da yaran take su kece raini wani abun da gayya ake yinsa donta tanka amma tankawar ne bata yi sai dai ta ɗauke kai ta yi murmushi. Koda wasa bata yadda ta yi kawa a makaranta ba daga ita sai Aisha babbar matsalarta yanzu yadda mijin Mama Hajara ya takura mata tana wucewa zai nunata yana faɗar taki aure ba makaranta take zuwa ba yawan iskanci take zuwa, tasha yin saurayi a makaranta su biyota gida amma washegari data koma ko kwana biyu tsakani sai su bita da bakar magana da zagi a rin hakan wani ya yi suɓul da baka ya ce mata ai makocinsu mutumin kirkine bai ɓoye masa halinta ba da magiya da komai Fatima ta samu ya bayyana mata suffar mutumin tashin farko ta gano Mallam Sale ne. Kanta ya yi matukar ɗaurewa ta rasa maita tsarewa waɗanan bayin Allah tashin hankali bai tashi kamata ba saida ta samu labarin Sani mai tureda zai auri Rahama sa ar Mardiyarsu ai saita karasa sussucewa. Mamansu ma jikinta ya yi sanyi da jin batun harta kasa daurewa ta ɓuntawa yaran Sadiya sarkin gaɓa-gaɓa saita kwashe da dariya tana faɗin,
“yo Mama kya tambayi kaza hanyar rafi? Ai kunfi kusa keda amuniyar taki?”.
Daga haka suka shashantar da batun amma sun lura mahaifiyarsu ta yi sanyi sossai. Kwanci tashi aka yi bikin Sadiya da Mardiya gida ya rage sai Fatima da tagwaye da Gambonsu da kuma Sadis da Ammar da Saubahn. Mama kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha duk in da ta zauna tace ta rabu da kaya ta huta sai karashe. Dake Fatima mai kyan jiki ce ko an faɗi shekarunta wasu ma basa yadda wasu kuma kance,
“nawa Fatin take shekaru ashirin da ɗoriya?”.
Tagwaye sun fara tasawa sossai ajinsu uku-uku a primary tubarkallah kansu ɗaya nan fa surutun Hajara ya fara komawa kansu, tana ta tsorata Maman da cewar aisu waɗannan ukun rigis sai kita faman da sun kai su samu miji tare ki kwashe don su tagwaye ɗaya bata barin ɗaya ta yi aure ta barta. Idan ta ji hakan takan sasu a gaba tana faɗin,
“ni dai ku rufamin asiri karku cutar da junnanku”.
Yaran basu san komai ba wani lokacin ma dariya suke yi, ita kanta Fatiman dariyar take yi tana mamaki Maman kamar wata sakarya haka Hajara ta maida ita, cikin hukuncin Allah Gambo ta fara wata irin rashin ƙlafiya mai zafi kwananta biyu ta amsa kiran mahallicinta babu wanda bai koka ba sun ji mutuwarta matuka duk da kasancewarta yarinya mai tsiya.
BABI NA TAKWAS
Karatu take babu kama hannun yaro gata da naci da tsananin bincike hakan yasa ta yi fice cikin abokan karatunta a kwai da dama masu bukatar kula dangantaka da ita amma kash iyskarta da kowa gaisuwa da kuma girmamawa sun shiga shekara ta biyu aka yi bikin Rahma da Sani mai tureda suka tare da matarsa a unguwar jan bango cikin hakan kuma aka sako Murja saki kwarara guda uku maigidanta ya ce ya gaji da kazantarta ya kwace yaransa ya bawa amaryarsa. Mama Hajara babu irin bala in da bata yi ba amma ko ajikinsa taso ya basu yaran kodan su sami abin ɗora masa hidima amma atabau yaki amincewa. Su Fatima aski yazo gaban goshi sai murna suke kamar wasa gashi zasu kare shekaru uku cikin nasara babu ko carry over daga ita har Aishan. Kwatsam wani H.O.D ɗinsu ya kyala idanu kan Fatiman tun daga lokacin ya ke bin duk wata hanya da zai sami kanta amma kash abun ya ci tura sunata hada-hadar gama jarrabawar karshan zango da suke ciki wanda daga shi ne zasu shiga ajin karshe hakan yasa Fatima koda yaushe tana kan karatu sana’arta kuwa ta bunkasa Malamansu mata da yawa ita take musu ɗinkuna cikin sauki hakan yasa take da costomer da yawa. Takurawar da ƙlacture ɗinsu ya yi mata yasata fargaba kwata-kwata bata da walwala da nutsuwa a gida bata huta ba haka a makaranta wasu lokutan tana karatun Mama zata zo ta ɗauke fitilar ta hanata shiyasa ta sauwakewa kanta ta sayi karamar waya mai touch buɗin data .samu yasa ta kwashe tagwaye daga makarantar gwamnati zuwa _private_ makarantar kuɗi mahaifinta yaji daɗin hakan sossai kullum tsaye yake wajan yi mata addu a. Yana mamakin ɗabi ar Fatima komai ta samu daga mahaifiyarta sai yan uwanta ko su Sadiya da suke a aure basa wahaltawa mahaifiyarsu kamar ita amma komai ta yi a gwasale sai kyara da hancini.
***
Da sassafe ta shirya cikin atamfarta mai saukin kuɗi ta fesa turare kaɗan tasa baya ta saɓi jakarta zuwa makaranta tafe take tana addu ar Allah yasa bata makarba sabida taga takwas da rabi ta yi kuma takwas da rabi ne ka idarsa. Jikinta har rawa yake ta yi sallama ta shiga ajin. Allah ya taimaketa bai shigo ba ta shiga ta zauna bata ga Aisha ba a haka ya shigo ya yi musu lacture ya fita. Bayan ya fita ne tana zaune wata matashiya ta shigo,
“Fatima Aminu”.
Ta ɗago kai tana murmushi ta dubeta kallon data watsa mata ya sagar mata da guiwa a lallace ta furta,
“kije in ji H.O.D Islamic Department”.
Gaba ɗaya idanun yan ajin nasu ya yo kanta har ta sadda kai tana jin kamar ta nutse don tashin hankali, idan ta ki zuwa bata da mafita zargin da ake mata ba dainawa za a yi ba. Idan kuma ta je nan ma haka ne ga hukuncin da zata karɓa shi daga gareshi wanda babu makawa tasan carry over ne kanta ya yi dum ta mike jiki a sanyaye ta wuce suka rakata da idanu ta wuce. Da sallama ta wuce wata ɗaliba ce ta fito tana gyara jikinta murmushi yake ta haɗiyi wani miyau daya tokare mata makogwaro ta sunkuyar da kai tana kokarin ɓoye kwalar data cika mata idanu. Zuciyarta cike da tsanar masu irin ɗabi ar H.O.D ɗinsu bata gama tunanin ba ta riski numfashinsa yana dukan nata da sauri ta yi baya tana faɗin,
“innalillahi…….”.
Wata dariya ƴya saki tare da buga kafa,
“Fatima ki saki jiki muyi rayuwa!”.
Kai ta shiga girgizawa tana toshe bakinta da kuka yake neman kwacewa,
“a a Malam karatu nazo yi, karatu aka turoni. Ban san wannan rayuwar”.1
“Zaɓi ƴya rage gareki get out of my office!”.
Da sauri ta fice hartana tuntuɓe sabida tashin hankali ko aji bata koma ba ta nufo gida, tana tafe tana saka da warwara kanta banda ciwo babu abinda yake yi har wani duhu take gani tana shiga gida ta samu gidan cike gasu Sadiya da Mardiya sun zo Mama sai nan da nan take da Sadiya sabida shigar karamin ciki Mama Hajjara tazo sai washe baki take tana tanɗar kashi wanda da alama anan aka bata. Jiki a sanyayye ta yi sallama ta zauna tana faɗin,
“sannunku da zuwa amare tun da muka koma ban sake zuwa ba”.
Mama Hajjara ce ta yi karaf ta ce,
“hmmm! To banda ke Fatima ina kika ga yaya tana.jelangiyar zuwa gidan kanne? Balle kuma irinki da babu aure ai saiku haifar da fitina”.
“Gamemin hanya Hajja taje ta ɓalo auran ta jamun sallalan tsiya kawai”.
Kanta ne ya sara ta daure ta yi murmushin yake,
“Mama ina abincina ya ke? Na gaji?”.
“Dole ki gaji Aunty kina kokari ai kun kusa ma ko?”.
Cewar Sadiya tana yi mata kallon tausayi,
“mun kusa sister saura watanni”.
“Allah ya dafa Aunty Farouk yana gaisheki”.
“Ina amsawa sarkin masu kirki na rabu da jin kiransa bari in ci abinci mu ɗan tattauna”.
Ta faɗa tana shafa kan Mardiya,
“amarsu sarkin mislilanci ina ce ba ayi wa Bellon haka?”.
Sune kai ta yi ita kam Fatima dauriya take ji take ina ita ce Mama ke wa wannan tarbar numfasawa ta yi ta sake tambayar abincinta karo na biyu.
“Ai ba aikenki na yi makarantar ba! Kije ki nema duk inda ƙkika san zaki same shi na dafa mun cinye ko an bani kuɗin cefan nan ne?”.
Bata tanka ba ta mike ta fita ta bar gidan Mama Hajara ta washe baki, Sadiya ce ta haɗe fuska,
“wai Mama har yanzu baki sauya daga yadda kike ba ni na rasa me yaya Fati ta yi miki yadda take miki biyayya bama yi miki wallahi amma kin tsaneta”.
“Rufemun baki shegiya kawai mai karambani kina tunanin Fati zata taɓa birgeni idan ba miji ta kawo mun ba? Ai wallahi mudun zan buda idona in ɗora kanta ganɗaɗɗan to kuwa tsana da tsangwama yanzu na fara yi mata ita”.
Dai-dai lokacin ta karaso tana murmushi amma yadda Sadiya ta ƙlura kwalla ce cike taf a idanunta ledojine a hannunta ta mikawa Maman guda, “Mama a rabawa yara”. Sai ga Ammar da Sadis ɗauke da kwalin taliya da mai jarka da maggi leda ɗaya suka dire gaban Maman ta kuma cewa” gashi nan Mama an biyani kuɗin ɗimkuna na ne da kuma na car wash shi ne dana siyo kayan aiki ragowan na siyo kayan abincii”. “Allah ya saka”, ta faɗa a takaice Fatima ta wuce ɗaki kirjinta har wani harbawa yake yi ta cire kaya ta watso ruwa jikinta har rawa yake sabida yunwa ga tunani da tashin hankalin H.O.D ɗinsu duk saita yi wani iri tana fitowa ta iske Maman na raba musu doya da kwan da ta basu tata ta shiga ɗaki ta buɗe ta soma ci guda uku ta ci wani wahalallan amai ya taso mata da gudu ta fito ta yi hanyar magudaddar ruwansu wato gulbi amma kafin ta karasa ta kifa bakinta ya fashe saboda jiri. Mardiya ce ta ta so da gudunta ita da Sadiya suka riketa ta karasa amai take kore fatau da shi har wani yolk yake yi ga ɗaci da bakinta ya dume da shi ta dinga numfashi sama-sama kamar zata amayar da kayan cikinta tukuna ya lafa suka kamota zuwa ɗaki ko kallonta Mama bata yi ba sun zauna jigum suna yi mata sannu Mama ta banko ɗakin tana huci kamar zakanya.
“Fatima ke kuwa Allah ya wadaran haihuwarki idan har abinda nake tunani ya tabbata wallahi tsine miki zanyi!”.
Ras! Gabanta ya faɗi ta sunkuyar da kanta dake barazanar rabewa sabida ciwo, wani wawwan damka Maman ta yi wa hannunta ta hau duba tafin hannunta saki ta yi ta kuma duba farcanta nan ma ta saki ta ɗago fuskarta tana duba idanunta da suka yi jajjur da su zuwa lokacin Fatima ta gama fahimtar kudurin mahaifiyarta wani kunci ne ya mammayeta tashin hankalinta ya karu sabida kallon da Mama take mata mai cike da tuhuma mikewa ta yi tana haɗa hanya ko gabanta bata iya gani hanyar waje ta nufa yuu! Kannanta suka biyota, ita kam yau zata bar Mama kota huta da rayuwar data ke son jefata kawai jefa kafarta take harta fito waje tana ji Sadiya na kwala mata kira amma ta kasa koda juyowa ga duhu ya rufe idanunta can nesa da ita ta hango dishi-dishi kamar Uncle Sulaiman ta hango da Aunty Maryam amma kash kafin ta gama tantancewa ta kasa sanin a wace duniya take yif!!!!. Ta faɗi bata ko numfashi.
BABI NA TARA
A hankali ta dinga buɗe idanunta har suka gama buɗewa baki ɗaya, ta kalli gefanta Aunty Maryam ce da Ahmad a hannunta ta buga uban tagumi gefe kuma Sadiya da Mardiya ne da alama kuka suka sha daga hagu kuma Mama Hasiya ce da a hankali ta shiga tunanin mai ya kawota asibiti can kwakwalwarta ta tuna mata mafarin al ammarin ta dafe kanta da ya sara sossai daidai lokacin aka turo kofar ta sauke idanunta kan mahaifinta kuka ya kwace mata mai tsanani tana jin ina ma ta mutu ta huta da kyar suka lallasheta ta yi shiru sai yamma suka tafi Mama Hasiya ce taji da hidimar komai har washegari bata zo ba a iya jiya kawai kimar Mama Hasiya da danginta ta karu a zuciyarta yayin da kaunar mahaifinta da yan uwanta ta kara ninkuwa a ranta. Misalin karfe uku na yammaci suna zaune ta yi nisa wajan tunanin rayuwarta takaicinta kowa ya zo banda Mamanta. Tana ayyana hakan a ranta fashewa da tayi da kuka saita soma mimmikewa kamar zata suma da sauri uncle Sulaiman ya fita ya kira likita Maryam ta karasa tana rike da ita tana aikin zuba mata ruwa da kyar numfashinta ya daidaita amma kirjinta bai daina bugawa ba. Kwanciya ta ƴyi luf a jikinta tana maida numfashi a haka likitan ya shigo duk suka fita sai Maryam dake rike da ita ya soma aunata. Yana cikin aunata Mata ta shigo bayanta ƙkuma Mama Mariye ce tana take mata baya, akwai alamun damuwa a tattare da fuskarta amma kafiya yasa tana kokarin ɓoyeta zuciyarta zafi take gaba ɗaya. A jiya tun fitar Fatiman Mama Hajja ta zauna tana rata ba mata bayani,
“aikin gani Mariye na faɗa miki gashi duk wata alama ta ciki ta tabbata a jikinta shikenan waɗanan tagwayan masu tasowa zata kashe ma kasuwa wa zai so haɗa zuri a daku?”.
Haka ta zauna ta yi ta yi mata huɗuba, gaba ɗaya tunanin Mama Hajja ya tafi ne kan Mallam na gangare ya sami nasarar haikewa Fatiman har shi yasa wani abu ya faru don haka da murna da komai ta koma gidanta ta tara Murja suna tafawa suna dariya a haka ɗanta Musaddik ya shigo yasha bai kai ga buguwarba tsaf ƴyana jinsu ya ce,
“Mama abani na shan sigari wallahi ko in fasa kwan”.
Jikinta har rawa yake, tsoron Musaddik take yanzu in bata yi wasa ba zai zare wuka don haka babu musu ya bashi ɗari biyu ƴya wuce ya basu waje suka cigaba da tattaunawa. Bayan Likitan ya gama ne ya sauke ajiyar zuciya yana duban Maryam,
“ina mijinta?”.
“Bata da miji likita cikine da ita ƙko?”.
Ba Maryam ba da tasan wace ce Fatima tasan mahaifiyarta ce ke wannan furucin ba, hata likitan kanshi sai da ya tsaya jim yana dubanta sannan ya furta,
“wace ce ke a gareta?”.
“Ni mahaifiyarta ce karka ji komai ka bayyanamin gaskiya”.
Kai kawai ya girgiza yana faɗin,
“MAHAIFIYA CE take wannan furucin?”.
Bai jira amsarta ba ya ce,
“ki sameni a office ke da mahaifinta”.
Yana ficewa ta wurgawa Fatima kallon daya hautsina yayan hanjinta, Sadiya ta share hawaye ji take ina ma ita ce Fatima har ga Allah da duniya zata shiga ta huta Mardiya kuwa ji take zaman wajan ya gundureta tare da uncle Sulaiman suka shiga office ɗin likitan ya dubesu,
“wannan fa?”.
Karaf Maman ta ce,
“karka ji komai ai shima na gida ne faɗi a gabansu su ji”.
Shi dai likita mamakin matar da aka kira da mahaifiya ya ke ya cire glass ɗin sa sannan ya furta,
“iya bincikena babu abun da yake damun yarinyar nan sai ciwon gyambon ciki, sai kuma hawan jini da ya ke barazanar kamata wanda in dai ba a kiyayye ba to kuwa zai mata illa mai karfi”.
“Likita olsa fa kace dama ba ciki bane?”.
Daga uncle Sulaiman har mahaifin Fatima ta awizi suka soma furtawa fuskokinsu cike da mamaki a zafaffe Malam Aminu ya yi mata tsawa haɗe da korata waje amma likitan ya dakatar da shi sabida yana san yi mata bayanin ainihim ciwon bayan ta zauna ya dubesu,
“Baba yarinyarki bata da wani abu pregnancy kawai ciwo ne”.
“Amma likita ai ya ɗashe ta yi fari ga kuma ama……”.
“Wannan baya nufin abin da kike nufi Baba kowace cuta da irin yanayinta. Ita dai ulcer ta kasance daya daga cikin manyan cututtukan dake damun mahiyawancin mutanen wannan zamanin. Ulcer takan kama mace ko namiji,yaro ko babba.
Takan faru ne a duk lokacin da sinadiran dake narke abinci waton(hydrocholoric acid)suke yawan zuba akan hanjin mutum watakila ba abinci a ciki(empty stomach)inda daga nanne suke hude hanji(intestinal holes)
ulcer ta kasu kashi kashi. Akoi peptic,akoi gastric,akoi deodonal ulcer. Alamomin ulcer
1.ulcer tana sanya ciwon ciki da zafin jiki da tsuwar hanji,da zafin ciki,da yawan tashin zuciya,da ciwon kirji,da tarin majina da amai kamar wanda ya sha tsamiya(acid reflux)da kumburin ciki,da ciwom baya,da kashin jini,da rikewar wani bangare na jiki.+
STORY CONTINUES BELOW

Jikinta ya yi sanyi nadama duk ta mammayeta, kenan karya Hajjara ta yi mata Fatimanta ba ciki ne da ita ba. Jiki a saɓule suka yi wa Dr salama suka fito uncle Sulaiman ne ya biya komai, lokacin da suka dawo ɗakin kuka take rirris tana buga kanta Maryam na rike da ita abun tausayi Mardiya kuwa sai ajiyar zuciya take, mahaifinsu ne ya karasa ya riketa yana yi mata nasiha ta yi shiru tana shassheka ya dubi su Sadiya,
“kowa ce ta wuce gidan mijinta itama anjima za a sallameta”.
Ganin fuskarsa babu annuri yasa suka wuce ɗakin ya rage daga mahaifinta sai Mama da Mama Hasiya da uncle da Aunty Mama Hajjara kuwa tuni ta ɓace taje unguwa ta baza labarin Fatima ta yo ciki a makaranta.
Misalin karfe biyar na yamma aka sallamesu uncle banda nasiha babu abinda yake mata, haka ma Mama Hasiya ya ɗauki matarsa suka wuce suna zuwa gida Mama Hasiya ta aiko mata da fresh milk mai kyau ta sha ta samu kannanta duk sunyi jigum-jigum tausayinta ya kamasu suna kaunarta ba kamar tagwaye har sun faɗa. Har zuwa lokacin mahaifinta bai kula Mama ba tana lura da yadda yake watsa mata kallon banza saida ya tabbatar bata bukatar komai sannan ya fice still bai tankawa Mamar ba ita ma bata tanka masa ba daga shi har Fatiman amma Fatiman tana lura da yadda Maman duk ta yi sanyi.
Suna nan zaune har aka kira sallahr magarba, ƙlokaci zuwa lokaci sai suga yaran unguwar sun shigo sun fita da gudu bayan sun kali Fatiman tun tana sharewa har ta tanka,
“Mama kin ga yaran nan ko me suke nema?”.
“Hmm! Ina zan sani Fatima?”.
Ba wanda ya sake magana suka mike suka yi alwala suka bi jam’ i suna raka’ar karshe ne wasu mata su uku suka yi sallama. Hassana da Hussaina dake aikin tattar koko suka amsa Ammar ya mike ya shimfiɗa musu tabarma suka zauna ita dai Fatima tana nan zaune tana tahiya gabanta sai faɗuwa yake ga zuciyarta nata tashi tana sallamewa amai ya taso mata da sauri ta mike jiri ya kwasheta ga mamakinta Mama ce ta riketa tana faɗin,
“Fati bi sannu karki faɗi mana”.
Wani sanyi ne ya kwaranya a zuciyarta ita ta riketa har bakin rariyar ta yi ta gama ta wanke mata baki ta kamota ta zaunar da ita matan sai jera mata sanu suke wata mai surutu cikinsu ta ce,
‘sannu Allah ya raba lafiya”.
Wani abu ne ya daki kirjin Fatima ba shiri ta mike suka yi kallon kallo ita da Mama ta sunkuyar da kai. Bata gama tunanin ba taji muryar su suna faɗin,
“Maman Fatima ashe haka abun ya faru Fatima ciki ne da ita ubangijin ya tsayar iya nan?”.
Wata muguwar ashariya Mama ta antayo tana shakar wuyan Maman Sani mai tureta,
“uban wa ya ce miki ɗiya ta ciki gareta?”.
Mama ta shaketa tana wujujjugata tare da bugata a bango, duk yadda taso ta kwaci kanta ta kasa haka sauran matan sun kasa kwatarta sai da tayi mata lillis ɗaya ce ta ce,
“mufa bamu muka kashe zoman ba rataya aka bamu Hajjara ce ta gaya mana”.
Mutuwar tsaye Mama tayi har matan suka fice ta kasa kataɓus kawai saita fashe da kuka mai tsanani. Kamar an mintsineta ta kwasa da gudu sai gidan Mama Hajjara Fatima hankalinta ya tashi ta fito tana dafa bango ta shiga gidan Mama Hasiya ta yi mata bayani da yake mai gidanta yana nan tambayarsa ta yi suka fito tare suna shiga gidan suka samu faɗa ya runcaɓe duki in doka da Mama da Ma ma Hajjara har an cirema Mama Hajara hakori.
Da kyar suka ɓanɓareta daga jikinta Mama Hajara tana kuka tana faɗin,
“Karya na yi ai yar iskar ce dama kowa ya sani ba makaranta take zuwa ba yawan barbaɗarta take tafiya ta rasa miji an fake da karatu ana yawan karuwanci”.
Haka suka ja ta suka fita gidan har ya fara cika da mutane suna shiga gida Mama Hasiya ta dubeta,
“gaskiya Mariya kuna ban mamaki manya daku kuna faɗa”.
“Hasiya baki san me Hajjara ta yi min ba ta cucceni ta gama dani har abada ta dasamun tsana da tsangwamar ɗiyata bani da abun kushewa sai ita iyakar kokarinta tana kyautattamun amma na zallunceta baki san wani abun takaici ba ina shiga gidan na samu tana bawa Murja labari ashe randa na bata Fatima takai gidan Malami baki suka haɗa ta bashi Fatima don ya ɓatamin ɗiya ta gudo ta barta shi ne take faɗin burin Malam bai cika ba gashi Fatima ta yo ciki”.
Tana karashewa ta fashe da kuka mai cin rai daga Fatima har Mama Hasiya babu wanda ya yi mamaki sabida sun san komai. Mama kuka take tana rokon Fatima gafara a haka mahaifinsu ya shigo ya samu labari bayan ya ji komai ya numfasa ya ce,
“Mun gode wa Allah da kika gane gaskiya, amma batun zallunci kin zallunci Fatima kuma dole ki nemi afuwarta ki sani cewa kowane ɗa yana da hakki kan iyayyansa.
STORY CONTINUES BELOW

Saida ya yi musu nasiha mai ratsa jiki take Mama ta nemi afuwar Fatima da makwafciyarta, suka yi musu sallama ta wuce gida. Fatima ba karfin jiki amma kwana ta yi tana nafila don nuna godiya ga Allah daya nuna mata ranar da Allah ya raba mahaifiyarta da Mama Hajjara muguwar makwafciya lallai ta amince idan ka daka ta bado.
Washegari ta tashi idanu a kumbure sabida rashin bacci, Mama ta dinga tambayarta amma amsar ɗaya ce babu komai karfe sha biyu sai ga su Mardiya farin cikin Sadiya yaki ɓoyuwa ganin yadda Mama take nan da nan da Fatima kasa jurewa ta yi har sai da ta tambayi dalilin sauyin babu jinkiri Mama da kanta ta ware mata komai ta dinga basu labarin yadda take zugata a baya ita dai Fatima jinsu take kawai jin zasu zake wajan aibata Maman yasa ta tanka.
***
Kwanan Fatima biyu cikin kulawar mahaifiyarta, ta yi kyau da ita sai dai fargabar H.O.D ya hanata sukuni Mama na ƙƙlura da yanayinta sai ta kawo duk rashin sabo ne da kusanci da ita, a ranar kwana na uku ta fito cikin shirin makaranta sabida ta sami karfin jikinta sossai ga mamakinta Mamace ta bata kuɗi da sunan kuɗin mota bata ki amsa ba duk da tana da wadatar kuɗi a jikinta hasalima tafiya ta yi tana duban kuɗin tamkar wani MADUBI a gareta jinta take cike da nishaɗi tamkar duniyarta ta zama sabuwa. A haka ta karasa makaranta tana zuwa ta samu Aisha ta zo da murna suka rungume juna ta yi mata ya jiki sai lokacin ta lura da wayar Aisha katuwa i pad ta sa hannu ta karɓa tana faɗin,
“mutuniyar kin faso”.
“Hmm! Kedai bari wallahi, Abban yara ya siyamin kema ya kamata ki siyi ko karama ne ki dinga amfani da ita na lura sai yawon cafe da kike zuwa kuma tsaf waya zata miki komi sai abinda ba a rasa ba”.
“Hmm! Aisha kenan zan sai waya amma ba yanzu ba sai wata na gaba idan na ɗauki adashina”.
“Allah ya taimaka!”.
“Wai yau sai wani nishaɗi kike, kamar kin yi saban ango anya kuwa?”.
Duka ta kai mata sannan ta saki dariya,
“kya ji da shi”.
Hango yar aiken H.O.D ta yau da kullum ya dakusar da fara ar fuskarta kafin ta yi wani yunkuri ta karaso kamar kodayaushe tana yatsina kamar taga kashi,
“ki je yana kira”.
Ka kawai ta ɗaga sabida jijjiyoyin jikinta kwata-kwata sun tsaya cak! Kanta har wani juyawa ya ke ta aro juriya ta yafa daga bisani ta mike,
“Aisha bari in dawo”.
Rike hannuwanta ta yi,
“Fatima zuwa zaki? Gaskiya ba zan ɓoye miki ba yadda ake maganarki a depertment kan zuwa wajansa ina jin ciwo kin san fa ba mutumin kirki bane”.
Idanunta ya yi rau ta maida kwallar,
“eh! Zuwa zan yi ina son kawo karshan alakar ne gaba ɗaya ƴubangiji yana tare dani”.
Bata tanka ba ta saki hannunta ta juya cike da karfin guiwa ta tunkari office ɗin, babu kowa kamar yadda ta yi tunani sai ac da kamshin turare da suka haɗu suka sanyaya jikinta ya zuba mata idanu yana jifanta da wani irin kallo, karon farko data samu irin wannan kallon a rayuwarta ta kasa tantance na so ne kona yaudara ko kuwa sha a wa gaɓɓan jikinta sun saki suka dingi aikamata sakwanin data yi imanin tana bukatarsu a shekarunta ta kasa control na komai nata bata yi aune ba har ya iso inda take ya soma aika mata sakwanin data kasa tantance shin meke shirin faruwa da duniyarta yayin da wata zuciyar ke tunasar da ita mutuncinki ko cikar burinki. Gaba kura baya sayaki shin karatun ko mutuncinta.
BABI NA GOMA……..
Zuciyarta ce ta shiga ruɗani, wani abu ya dinga zaga kwanyar kanta, ta dinga jinta a yanayin data tabbatar gejin shekarunta na bukatar hakan wani tsohon mahallicinta ya ziyarci zuciyarta cikin sakan guda wani karfi da bata taɓa tsamani tana da shi ba ya taso mata ta angajeshi ta ɗaga hannu ta kwaɗa masa mari ya sake wawwurarta kamar mayunwacin zaki ta dage ciccin karfinta ta gasa masa cizo a gefan fuskarsa ai kuwa ya ji zafi ya tankaɗata ta faɗi gefan fuskarta ya gurje sai ga jini cikin kuka ta nuna shi,
“kaji tsoron Allah kar ka buɗe abinda ke rufe ba tare da izinin shari a ba!”.
Kuka ya sarketa ko a jikinsa, sai ma ya marairaice yana rokonta,
“Fatima ki taimakamin zan mutu wallahi”.
“Wallahi bazan yi ba Malam ko gaba da carry over zaka bani ina tsoron mahallicina ina kunyar ha intar mahaifana. Zina masifa ce dake tattare da bala ai wanda suke durkusar da kwanciyar hankalin mai aikatata. Allah SWT ya ce a Alkur’ani magirma cewa:
“Kada ku kusanci zina”.
Manzon Allah SAW ya ce,
”Mazinaci bazai kasance lokacin da yake zina yana da imani ba”.
Manzon Allah SAW ya kara cewa:
“Duk wanda ya yi zina, ko yasha giya Allah zai cire masa imani kamar yadda yake cire riga”.
STORY CONTINUES BELOW

Muslim ya kara ciro wani hadisi mai tsoratarwa, wanda Manzon rahama yake cewa:
”Mutane uku Allah ba zai taɓa magana dasu ba a ranar alkiyama, ba zai kallesu da idon rahamaba.Kuma bazai taɓa taimakonsuba kuma agaresu akwai wata irin Azaba mai radaɗi mutanan sune:-tsoho mazinaci, shugaba makaryaci da kuma talaka mai tsananin girman kai”.
Sannan Manzon Allah SAW ya kara nuna mana, tsananin muni na zina inda ya bayyana mana cewa shi kansa Iblis yana alfahari da ‘ya ‘yansa wanda suka yaudari ɗan Adam ya aukawa zina.Inda yake ce wa:-
“Iblis yana watsa rundunarsa a bayan kasa sannan ya ce dasu, shin waye zai batar da musulmi in saka mar hular sarauta ta? Sannan in mayar dashi makusancina abokin shawarata?. Na farkonsu sai yazo ya ce,
“bangushe ba sanda nasa wani ya saki matarsa, sai shaiɗan ya bashi amsa da cewa:-
“ba wani abin kirki ka aikata ba, kana ina zai auri wata? Wani yazo ya ce,
“ban gusheba sanda nahaɗa wasu mutane gaba tsakaninsu, sai ya bashi amsa kamar wanda yaba na farkonsu, sannan ya ce,
“kana ina za a sassantasu?”.
Har sai wani yazo ya ce,
“ban gushe ba sanda nasa wani ya yi zina da matar da ba halalinsa ba. Shaiɗan sai ya ce,
“madalla da abinda ka aikata,sai ya kusanto dashi sannan ya ɗoramai wannan hula ta sarauta.Ribar me zaka ci Malam? Zina fa bashi ce, wallahi duk abinda ka yi sai an ninka maka domin alkawarin Allah baya tashi. Zamanin da muke ciki baka yi ba ma, an maka Malam ina ga ka aikata. Mai katanada na kare kanka wajan mahallicinka yayin gobe kiyama?.Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar :-Raunin Addini. Karancin Imani. Rashin kunya. Rashin kishi. Rashin mutunci. Rashin kwarjini. Rashin hasken fuska. Duhun zuciya. Rashin kima. Rashin Nagarta. Rashin Nutsuwa. Rashin Amana. Fushin Allah Cikawa babu imani. Azabar Allah”.
Ta karasa tana share hawaye ga mamakinta ko gezau bai yi ba, hasalima dariya ya kyalkkyala tare da tafa hannu yana faɗin,
“wonderfull Fatima! Ashe ba a banza kika zaɓi islamic ba, sai dai kisani wa azinki bazai karamin komai ba kafin kije wajan naje na dawo kuma karki manta duk sanda ka tuba Allah zai yafe maka domin mai karɓar tuban bayinsa ne”.
“Karya kake Malam nasan ba kaina ka fara wannan muguwar ɗabi a ba, irarranku ke ɓata cigaban karatu har ku ɓatashi a zukata da idanun iyayyan da kaddarar ta faɗa wa yaransu ko kunya baka ji ba gemai-gemai da kai amma kana tsayawa kana min batun da babu komai cikinsa face son zuciya irin na gafallalun mutane mabiya turbar shaiɗan kaico da gurɓataccan tunanin irin naka. Ka manta ran dake jikinka aronsa aka baka?! Shin ka manta idan za a karɓa ba za ayi shawara da kai ba? Ko kuɗinka ne ya siya maka?”.
Gaba ɗaya Fatiman ta rikice maganganu take gasa masa masu zafi wayarsa da ta yi kara ya ɗauka ta shammace shi ta buɗe office ɗin ta fice da gudu tana nadamar zuwa ta ɗauki alkawarin ba zata sake zuwa ba sai yanzu take ganin wautarta data zaɓi amsa kiran nasa.
Bata yi aune ba ta ƴyi karo da wani Malaminsu, ta gaggauta gyara nutsuwarta tana gyara mayafinta ƴya bita da wani mayen kallo da hanzari ta kara gaba sabida gabanta da ƴyake faɗuwa tana fitowa wayam babu Aisha babu dalilinta.
Yana shigab office ɗin ya samu Hashim ya yi tagumi ya daki bencin,
“ya dai naga wata dankwaleliya ta fita an shiga ne?”.
Sai da ya yi huci mai zafi daga bisani ya numfasa,
“ina fa”.
“Bangane ba anyi yamma da kare”.
Nan ya kwashe yadda suka yi da ita ya faɗa masa sai da ya yi jim daga bisani ya yi masa raɗa a kunne, tafawa suka yi suka dasa wata hirar.
Fatima kam ta rasa sukuni gani take kowa ya san abunda ke faruwa tsakaninta da Malam, ta kasa zama kwata-kwata haka ta jure har aka tashi kafin lokacin zazzaɓi mai zafi ya rufeta ga kanta dake juyawa haka ta dinga jefa kafa ta nufi bakin titi, tana nan tsaye tana son tsallakawa titin amma jiri na neman ɗibarta Allah ya taimaketa ta ya tsaya, ta ɗaga kafa zata tsallaka kenan motar H.O.D ta kwaso a guje ta yo kanta ankara ta yi da motar tayo baya da gudu hakan ya yi sanadiyar da ɗan acaɓa ya kwasheta ta yi sama ta dawo kasa ta baje, takaici ya kama H.O.D burinsa bai cika ba ya yi jim yana tuki a hankali yana son ya gangara bakin titin ya fita ya karɓeta da zumar kaiwa asibiti bai aune ba wata babba mota ta yo kansu abokinsa da ya shirya tsarin ne ya farga kafin yayi wani yunkuri motar tabi ta kansu take H.O.D ya amsa kiran mahallicinsa nan da nan titin ya ɗinke mai mota kuwa ya karawa motarsa wuta ya gudu aka rasa mai tareshi kasancewar babu jami an tsaro.
STORY CONTINUES BELOW

Fatima na daga gefe in da ake faman akai ta asibiti komai akan idanunta ya faru ta runtse idanu, shikenan H.O.D ya tafi ta tambayi kanta kuka ya kwace mata bata gama tunani ba ta hango mutane sun durfafota da wani mutum an rukoshi cikin jinni aka ajiyeshi inda ya nuna kusa da ita da kyar ta ganeshi sabida duk jikinsa jinnine,
“Fatima ki yafemin wallahi sharin shaiɗan ne”.
Duk da ta ganeshi sai ta haɗiye mamakinta ta ce,
“Malam me kayi min?”.
“Ni nasa Hashim ya bugeki don ki faɗi mu ɗaukeki mukaiki asibiti daga nan mu wuce gidana dake sabida mummunar manufarmu don Allah kiƴyi hakuri!”.
Gaba ɗaya wajan ya ɗauki sallallami, masu tausayinsa suka fara zagi da aibatawa abun haushi wasu har sun fara ɗaukar hoto a waya, Fatima kuwa mamakine ya daskarsr da ita ta furta,
“na yafe maka”.
Take ya soma kakkafewa rai ƴya yi hallinsa, ta runtse idanu tsoron Allah ya sake shiga zuciyarta ana haka hukumar makaranta ta karaso aka kwashe su H.O.D kowane aka kaishi wajan danginsa aka wuce da Fatima asibiti bayan ta bada addireshinta an je an taho da mahaifiyarta. Hankali tashe Maman ta karaso ji take kamar Fatiman mutuwa zata yi ba tare da ta yafe mata tausayin ɗiyarta ya shiga zarga zuciyarta, bata tsinke da lamarin ba sai da taji yadda raɗe-raɗin haɗarin ya faru kuka ta dinga yi tana godiya ga ubangiji daya bata nitsattsayar yariya tabbas Fatima na cikin kariyar ubangiji H.O.D shi ne mutum na biyu daya nemi tarwatsa rayuwarta ubangiji na kareta. Maman sai ta soma zargin kanta bisa wasarere da rayuwar nagartaciyar ɗiya kamar Fatima.
Fatima ta sami karaya a kafarta, ta yi kuka ta yi kuka mai ciwo ba makawa ta san ta rasa wannan shekarar kenan sai ta maimaita shekarar shikenan burinta ya ruguje kaddararta kenan ta lumshe idanu tana ayana haka zata dinga rayuwa daga wannan sai wannan?. Haka shafi-shafi zai dinga buɗewa daga cikin shafukan littafin rayuwarta?. Amsar data gaza samu kenan sai kirjinta dake suya kamar ya fashe.
BABI NA SHA DAYA.
Sai da Fatima ta share kwana goma sha takwas a asibiti duk wata hidima Mama Hasiya da maigidanta ne suka yi, lallai Fatima ta amince sun sami makota na gari masu kaunarsu sabida Allah. An yi mata ɗori masha Allah ya yi kyau haka suka dinga zaryar asibiti sabida kwanciya suka bata. Dake lamarin nata _it depends_ ya danganta da da wacce irin karaya ce da kuma a Ina karayar take. Kamar wanda ya karye a kafa daban ne da wanda ya karye a hannu ko fan yatsa ko dai sauran gurare a jikin Mutum. Kuma ya danganta da kashin _that is affected_. On average idan karayar kafa ne _by 3 months_ wata uku Mutum _is expected to be healed._ To itama Fatima a guiwa ne ta hagu ta samu karayar kuma anyi aikin cikin nasara. Amma zaman asibitin _depends on the condition_ din Mutum. Ana musu _”Open reduction and internal fixation”_ shi ne aikin da ake musu a kafar, daga nan sai a sa musu _POP_ a rataye kafar ko kuma dai a ajiye ta a wani _position_ da zai yi _limiting movement._ Ba’a son yawan motsi da kafar. Daga nan sai a dora su akan _antibiotics_ Saboda _infections_ da kuma _pain killers_. To idan Mutum _is stable_, kuma anyi dacen aikin ya yi kyau kuma bai samu wani _infection_ ba to kamar _2 weeks_ za a iya sallamar Mutum ya karasa warke wa a gida. Idan kuma Mutum ya samu complication to file a ajiye shi a asibiti Na wani tsahon lokacin har sai likitocin sunga _is stable_ sannan sunyi _discharging_ dinshi.
Idan za ayi _discharging_ Mutum. Ana _advising_ dinshi akan _diet_…cin abinci me kyau musamman abincin da yake da _protein_ kamar su kaza, nama, kifi, kwai, madara da _fruits and vegetables_. Suna taimakawa ciwon ya warke da wuri. Akwai maganin da ake bayar wa.. _Anti biotics_. Saboda _infection_ zai sa ciwon ya qi warke da wuri. _Pain killers_ saboda ciwo tsafta da kula da mara lafiya. Ba a so a dinga yawan motsa gurin har sai Mutum ya warke. Idan kuma Mutum ya warke ana so yayi “_ambulatung_” ya fara dan takawa kamar da _croaches_” wadannan abin da ake dogarawa ana tafiya. Idan Mutum is stable za a iya ba shi _appointment date_ din ganin likita kamar _1 month_ wata ɗaya Amma kuma za a fada mishi cewa ko Kafin _one month_ ne Idan yayi _experiancing any complication_ ya koma a duba shi.
Kwanci tashi haka Fatima ta share watani uku a asibiti ana dubata tana karɓar magani, zuwa lokacin sunyi sabo da Dr Sakina mace mai kirki da yakana watanta huɗu cif ta fara takawa kafin wata biyar ta warke garau kaf hidimar kwandalar mahaifanta bata shiga ba daga Farouk mijin Sadiya sai Uncle Sulaiman da kuma Mama Hasiya haka suka tattara suka dawo gida zumunci kam ya kullu tsakaninsu da Dr Sakina. Tana takaicin maimata shekara da zata yi tana kallo su Aisha suka wuce suka barta haka ta koma ajin data baro har sunyi nisa a karatu ta ɗaura ɗan ba ta soma karatu babu kama hannun yaro.
STORY CONTINUES BELOW

*SHEKARA DAYA DA RABI*
A kwana a tashi shekara kwana, cikin ikon Allah komai ya yi farko zai karshe sai ga su Fatima sun kammala _Diploma_ zuwa lokacin Sadiya ta haifi ɗanta Namiji Mardiya kuma nada karamin ciki babu wani jinkiri Uncle Sulaiman ya aiko samo mata D.E form _direct entry_ ta zauna jiran sakammako. Mama taso ta sami koyarwa a nan koda Nagwaggo primary ne Fatiman ta nuna ta fi san ta rike sana’arta har sakammakon ya fito. Allah mai yadda ya so wata uku tsakani sakammako ya fito suka bata _islamic stadies and english_ anan ‘yar aduwa aduwa _university_.
Babban burinta yanzu shi ne samun miji nagari amma abun shiru kamar Malam yaci shirwa, a gefe guda kuma tana son tallafawa kannanta Sadis ya kammala karatu mijin Mama Hasiya ya kaishi kasuwa taso shima ya fara karatun amma abun da yawa Ammar da Saubahn suna aji huɗu tagwaye kuma suna _primary five_. Sadiya ce dai tunda ta yi auren ta saki sana ar sai abinda miji ya kawo ƴya bata ta nuna mata amma taki yau da gobe dole ya gaza suka fara samun saɓani ta soma kawowa Mama korafi koda wasa bata goyi bayanta ba hasalima gargaɗi ta yi mata da kakkausar murya tana faɗin kadda ta sake ta kaso auranta tazo ta zaune mata a gida. Mardiya kuwa mijinta baya san karatu jari ya bata take sai da atamfofi. Zumunci tsakaninta da matar Uncle Sulaiman sai abin da ya yi gaba sun zama tamkar dangi ɗaya. Mama Hajjara kam rayuwa ta tasota gaba ga Murja dake zawarci duk ta hayyaceta kullum sai sunyi faɗa kamar wasu sa ani, a gefe guda ga Rahma Sani ya korota sabida kamuwa da ta yi da ciwon yoyon fitsari abu goma da ashirin. Ta rasa yadda zata fuskanci al ammarin amma hakan bai sa ta yi karatun ta nutsu ba.
Fatima karatu take babu kama hannun yaro, duk wani surutu da zunɗe baya damunta tunda tana samun kwarin guiwa daga wajan mahaifiyarta. A wata sallah da ta yi ɗinkuna ta samu kuɗi masu kauri ta sayi waya babba mai tsada kirar tecno naira dubu sha takwas facebook da whasApp kaɗai ta buɗe tana lekawa jefi-jefi kwatsam ta yi karo da sunan mutuniyar tata wato Chuchu ai nan da nan ta tura mata _freind request_ ta yi sa a ta karɓa hakan yasa ta dinga bibbiyar duk wani post nata masha Allah ta sami shawarwari masu inganci ta kuma rike su raɗam. Zuciyarta ta saka cika da kainar baiwar Allah, a hankali ta ke binta private chat suna ɗan gaisawa bata taɓa tsamanin saukin kanta ya kai haka ba. Tun bata bawa hirarsu muhimmanci harta saki jiki in ta hau bata ganta ba sai ta tambayi dalili musamman in karatu ya taso su gaba, ta lura kwarai matashiyar bata post mara amfani bayan ita akwai mutane da dama data dudduba irin su Husnah M Inuwa da kuma Safiyya Ummu Abdoul har ga Allah tana matukar amfanuwa da ɗan rubutun da suke watsawa.
Cikin ikon Allah Mardiya ta haihu lafiya aka sami yarinya mace ranar suna sun shirya liyafa mai kayatarwa sai dai Fatima na ƙƙlura da yanayin Sadiya bata da walwala sossai, tun safe har zuwa yamma hada-hadar ,’yan suna ya hana taba wa Sadiyan hankalinta sai magariba bayan sunyi sallah ta samu ta jata gefe,
“Sadiya lafiyarki kuwa? Naga duk kin sakwarkwace? Kamar ba matashiya ba?”.
Ga mamakinta maimakon ta bata amsa sai kuka data sa mata,
“Aunty ni dai gaskiya na gaji da auran nan wallahi, ni fitowa kawai zanyi in huta ko ce masa aka yi idan na fito zan rasa manema wallahi rubibina ma za ayi”.
Sai da ta kare mata kallo tsaf daga sama har kasa sannan ta ce,
“meya haɗaku?”.
“Aunty kwata-kwata baya kulawa dani kamar baya, da kamar ya haɗiyeni amma yanzu baya nunamin damuwarsa kuma in yi magana ya ce na fiya korafi?”.
Dariya ce ta kusa kwace wa Fatima sai ta kane tana dubanta zuciyarta ta shiga tuna kan hakan Chuchu ta yi magana _last week_ murmushi ta yi a filli ta furta,
“Allah kara basira Chuchuna”.
Turo baki Sadiya ta yi ta ce,
“ina gaya miki matsalata aikin banza kina kiran Chuchu ko Chacho koma Chacha Allah yasa ta san kina yi, marubutan da aka ce ɗan karan wulakanci ne dasu”.
Bata bi ta kanta ba ta gyara zama ta ce,
“ke Sadiya jini nan zaman aure daban soyayyar da kuka yi a waje daban. Bar ganin kunci uwar soyayya a waje wallahi ba ita zaku ci a gidan aure ba sai dai sauwa-sauwa. Domin zaman da zaku yi a nan halin kowa da ya kunshe yake futowa anan ake gane zahirin kauna, soyayyar waje shirme ce wannan yasa ki ke ganin aure nata tantal baɗi dalili ke kin auri namiji a waje kamar zai haɗiyeki kun zo gida hidimarki ta hau kansa wata rana ma ji zaku kamar kun tsani juna yau da goban kenan. Kema yana ganin kina sansa kina tattalinsa lokacin kina gida, amma kinzo gida komi ya ƙlallace dole a samu rashin fahimta sabida dukkanku kun samu kanku a wani _stage_ matsayi ko in ce miki kadami da baku saba da shi ba bakone a wajanku ku duka biyun dole ku koyi hakuri da junnanku ba kamar ke da za a fita a bari cikin gida kijiki tsit ya Allah gidanku da kika baro na jama a ne duk sai kiji kin takura bale kuma a ajiye yaro ɗaya zuwa biyu idan ba a sami mace jajjurtaciya ba hata tsaftar gidan sauya wa take sai faɗa ya soma zama abokinku keda shi Sadiya ki sani zaman aure wani abu ne da ake fatan daga lokacin da aka fara tunaninsa ya zamo wani abu na har abada , domin hakan ne zai tabbatar da cewa an san abin da ake nufi da aure da kuma irin halin da za a shiga, sanin hakkokin da ke kanka a matsayin miji, sanin matsayinki na mata a gidan aure yana da mahimmancin gaske, domin hakan ne zai ba da damar tabbatar da wanzuwar wannan aure. Yana da kyau ma’aurata su sani, aure ba tsari ne na zama zuwa wani dan lokaci kayyadadde ba, wato da an chinye kayan gara an gama zakin amarci a kama masifa a rabu ba, a’a tsari ne da Allah Ya shirya mana shi, sannan Ya tsara mana yadda zamantakewar za ta kasance. Ya dora ma kowannensu; miji da mata wadansu dokoki. Idan muka ji tsoron Allah a cikin zaman auratayyarmu za mu kasance cikin wadancan biyun da na ambata a baya. In shaa Allahu munji muhimmanci na aure, zamu cigaba daga inda muka tsaya a cikin zaman take war auran.
Saki da kike magana akai ka babbar illa ce. Illar mace ta nemi saki ga miji ya kamata ace mace ta lura da duk lokacin da mijin ta ya canza, sai ta fara bin cikar yadda zata warware matsalar ba tare da vacin rai ba, bare har abin ya kaiga magabata. A ’yan watanni a farkon aure har zuwa shekara daya ko biyu Allah kan jarabci ma’aurata, amma duk wadannan abubuwa ba za su zama wani dalili ne na samun sabani a tsakaninku ba idan har kun san dalilin da ya sa kuke zaune a matsayin ma’aurata. A matsayinki na mata, ki kasance mai hakuri a kan duk abin da mijinki zai yi miki ko da kuwa a kan laifin da kike da gaskiya ne, domin maza a mafiya yawan lokuta ba sa son karbar laifi, to ki yi hakuri a irin wannan lokacin idan abin ya yi tsanani ma ki ba da hakuri, idan hakan ne zai zama mafita ko maslaha. Idan rai ya baci a rika kai zuciya nesa, a rika duba abin da yake ginshiki wanzuwar auren.
Yana da kyau ma’aurata su kasance masu tausasa wa junansu. A matsayinka na maigida ka da ka kasance kullum mai ganin laifin matarka, kada kuma ka zamo mai yawan miti ga abin da aka yi maka na laifi. Hausawa na cewa ka gani, kaki gani, ka ji ka kuma ki ji, wannan na nufin ba kowane abu za ka gani ka yi magana ba, sai abin da ka ga ya wuce gona da iri, a tsawata a kan abin da ya dace kuma idan aka yi maka laifi ka yi magana idan aka ba ka hakuri, to ka hakura, kada ka zama mai riko. Ya kasance zaman aure ne wanda a kowane hali kuka sami kanku za ku iya jurewa cikin yanayin jin dadi ko akasin hakan; cikin halin lafiya ko rashinta, domin a halin da muke ciki a yau za ka tarar daga karamin abu yafaru tsakanin miji da mata, wani abin ma bai kamata ko wanda ke bakin kofar dakinku ya sani ba, amma haka za ka ga ana ta yamadidi da maganar har sai ta kai ga rabuwar wannan aure. Idan har za ku iya jure wa wahalhalun da kuka yi ta sha lokacin da kuke samartaka me zai hana ku karfafa aurenku ya zama na har abada ba? Haba “yar uwa duka duniyar nawa take, auren nan ne kadai zamubi domin mu samu mu rabauta Amma abin mamaki biyayyar auran takan zame mana tamkar aiki a garemu duk fa abinda akace ibada ne tofa mu sani dole sai munyi hakuri mun kauda kai, munyi iya bakin qoqarin mu, domin samun tsira ranar gobe qiyama. “yar uwa idan kina biyayyar aure dan mijin ki ne to ki tsaya har sai ya gode, idan kuwa kinayi domin Allah ne to ki cigaba dayi domin yana ganin ki, kuma ba zai tava watsar da dukkan aiyukan ki ba. Duk macen data roqi mijin ta saki haka kurum to qamshin Aljanna ya haramta gareta, Ashe macen kirki takan nemi saki ne yayin da kowa yasan irin cutar war da ake mata, Amma bawai dan ta gaji da zama dashi ko wani abin da yakeyi wanda bata so ba, aure sunnah ce da duk Annabawan Allah sukayi, bai dace wani yake jin matsalolin ki da mijin ki ba, sai in abin yafi karfin ki. Macen kwarai takan zauna da mijin ta a lokacin da aka samu saɓani domin samun gyara atsaka nin su, takan manta da duk wani zalumci na mijin ta, idan ta tuna da dawainiyar da yake akan su ita da “ya” yan ta, san nan ta fahimci saki ba shine mafita ba, sai an rasa yadda za’a yi san nan, Annabi S.A.W yace,
” Mace a kullum mai saka farin ciki ce ba mai jiran a saka ta ba, farin cikin mijin ki shine naki, duk abinda ya baki ki gode bai kamata ace kin zama mai rainuwa ba, idan wani abu ya hada ku “yar uwa kiyi kokarin kauda kai ki sama ma mijin ki farin ciki domin gobe kiyama ki rabauta. Nasan kina hakuri amma ki kara kuma baza ace shi kaɗaine mai laifi ba kema ba zaki rasa aikata masa badaidai ba zama zaki ki tambateshi Farouk mai nayi maka nasan bazai gaza furtawa ba, ko kin taɓa tuntuɓarsa?”.
Kai ta girgiza mata jiki a sanyaye da haka ta dinga nusar da ita harta gamsu harta mike ta ce,
“Aunty ina kike samun irin wannan bayanan?”.
Cikin murmushi ta ce,
“kanwata Chuchuna”.
Zare idanu ta yi tana faɗin,
“da gaske?”.
“Serious Sadiya, in kina so kuma kinsan Farouk bazai faɗa ba in buɗe miki facebook kiyi join da facebook nata zaki karu”.
“Inama yi zan gwada join”.
Ta faɗa cike da zumuɗi, murmushi Fatiman ta yi tabar wajan.
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji, duk wasu shawarwari da Fatima ta bawa Sadiya sun mata amfani matuka a gefe ɗaya kuma tana amfanuwa da shawarwarin mutuniyar Fatiman. Jari mai kauri Farouk ya bata don ya ji daɗin yadda ta sauya take kulawa da shi da lamuransa ba mita ba korafi bale turo baki kamar an bigi kare taka. Sossai ta buɗe harka kayan kicin take siyarwa masu kyau da sauki, Fatima takan zage ta haɗa tagwaye duk Asabar suna koyo ɗinki suna amfani da tsohon kekenta ita kuma sabon. A gefe guda ta siya musu form suna koyan sana’o’in hannu su humra man kitso da na shafawa zannuwan gado da sauransu. Rayuwar iyalin abin sha awa suna son junansu babu kyashi babu hassada, Ammar kuwa daya dawo makaranta yake garzayawa wajan mahaifinsu yana taya shi saida kayan miya dake ya daina facin. Shi kuma Saubahn hutar da Mama ya yi shi ya cigaba da kiwon kifi kuma dama a agric class yake a ilmance yake tafiyar da aikin yadda ya kamata ai kuwa ita kanta Mama ta fi ganin hasken abun girki kuwa ko cangal basa barinta ta yi. Wani lokacin in ta kalli Fatima har kuka take yadda ta tsangwami rayuwar yarinyar abaya ta tabbata badan Allah yana sonta ba da tuni ta lallace, tana yawaita istigifari tare da neman afuwarta. Karatunta kam sai godiyar Allah komai na tafiya daidai har gobe bata fasa yi wa Mama Hasiya addu a makociyar kirki mai yakana da halin dattako. A gefe guda ga uncle Sulaiman tunda nan yake koyarwa komai ya shige mata duhu shi take tunkara, kuma cikin nasara komai yana warwarewa.
Komai ya yi farko to kuwa zai yi karshe, shekarar da su Fatima suka gama makaranta masha Allah ta fito da _4.95 first class_ wata huɗu da gamawarsu suka karɓi result, wata ɗaya tsakanin _mobilasation list_ na ‘yan tafiya bautar kasa ya fito cikin ikon Allah ta karɓi _call up letter_ ɗinta inda aka yi _posting_ ɗinta yadda ta dinga raba dare tana addu ar Allah ya cika mata burinta a ajiyeta a garinta Allah kuwa ya amsa mata tana karɓowa ta ga Katsina State.
Ranar da aka yi _camp_ don yin _orrientation_ a ranar ita ma ta shiga na Bakori. Tun shigarta garin take jin wani irin nishaɗi, ta lumshe idanu tana ayyana ina ma zata ga Chuchunta ita kam data more sassanyar iska ta dinga ratsa baragen jikinta wani abu mai kama da damuwa ya dinga mintsinin zuciyarta take ruwa ya cika kwarmin idanunta tana ji ina ma zata iya da ta aikata, amma kuma kash komai nada lokaci. Da sauri ta kauda wannan sandararran tunanin daga zuciyarta ta hau yin abinda ya kawota amma fa ranta cike da bukatuwar ina ma ta ga Chuchunta. Bayan gama _registration_ ta sami _exit letter_ don bata damar barin _camp_ ta dawo masauki. Sai da ya rage sati uku saura kwana uku ya cika ta koma _camp_ don ayi _passing out_ ɗinta kamar yadda doka ta tanadar. Ranar da aka yi passing out ɗinta aka basu _primary assigment_ lamarin yazo musu da sauki ba kamar ita da tafi kowa murna domin tsamaninta bai bata nan ba (‘Yar Aduwa University Katsina) aka kaita _Depertment of islamic_ a anan zata yi _saving nation_ ɗinta. Babu jinkiri aka bata _level one_ in da zata ɗauki _couse_ ɗin _texual stadies of qur an anda hadith_. Kaanci tashi suka kammala ta yi _passing out parade_ suka amshi *N.Y.S.C CERTIFICATE* ranar babu wanda yake iya kwatanta farin cikin Fatima bisa samun nasararta ta rasa dame zata sakawa Mama Hasiya da Uncle Sulaiman tabbas waɗanan mutane sun zamo abin tunkahonta Allah ne ya haska duniyarta amma sune sila!.+
Satinsu uku da kammalawa matar Uncle Sulaiman ta haihu, Fatima murna har baki ya kasa rufuwa da su aka yi komai yarinya ta ci sunan Hafsat suna kiranta da Mommah sabida sunan marikiyarsa ne, hidima sossai Fatima ta saki jiki ta yi a sunan har sabon ɗinki ta yi jaririya kuwa kala biyar masu kyau da tsada ta yi mata, mai jego kuwa sarka ta ɗaukar mata wajan Sadiya indian desiner mai kyau suma su Sadiya ba a barsu a baya ba turmin atamfa mai matsakaicin kuɗi ta kawo wa maijeggon Mardiya kuwa takalmi da jaka. Mama Hasiya ta yaba kwarai da kokarinsu cikinsu kuwa har Mama babu wanda bai hallaci sunan Hafsat ba. Yarinyar tubarkallah ɓul-ɓul da ita. Sati ɗaya tsakani uncle Sulaiman yazo gaida yayarsa ya samu Fatima tana yi mata kitso cikin zolaya ya ce,
“ɗiyata wato ko result anki a kawomun in gani ko?”.
Cikin jin nauyi ta ce,
“ba haka ba ne ko Mama? Ai naga ana hidimar sunane”.
Mama Hasiya ta ce,
“ba ruwana keda Babanki kunfi kusa”.
“Kai Mama!”.
Ta faɗa a shagwaɓe,
“kyaleta ɗiyata in kin sami lokaci gobe ki shigo ki kawomun makaranta akwai abun da za ayi da shi muna fatan nasara, ko kuma na sami surukine kar in katse maki hanzari?”.
Da sauri ta girgiza kai, murmushi ya yi yana dubanta cike da tausayawa jinta yake tamkar ɗiyar daya haifa a cikinsa,
“ba komai Fatima ki ci gaba da hakuri shi aure ƙlokaci ne da shi kowa ce mace da kika gani da mijinta kuma rabin kwaɗo baya hawa sama”.
“Na gode uncle”.
Bayan ta koma gida bata ɓoyewa Mama komai ba game da yadda suka yi da uncle Sulaiman ta ji daɗi matuka tare da sanya mata albarka, ta sake yi mata nasiha kan hakuri da juriya abisa kaddararta.
STORY CONTINUES BELOW

BABI NA SHA UKU…..
🇦washegari Fatima ta shirya misalin karfe goma bakinta ɗauke da addu ar nasara ta nufi makaranta cikin shiga ta kammala da kamewa, tana zuwa ta samu uncle da takardunta ya karɓa ya duba ya mike ya fita jim kaɗan sai ga shi hannunsa ɗauke da _offer_ ya karɓo wajan H.O.D. ya mika mata yana murmushi. Fatima ta karɓa hannunta har karkarwa yake, zuciyarta ta yi zugum wajan tunanin tarin nasarorin dake dumfaro rayuwarta ita ba wata mai madafun iko ba amma kuma wadatuwar takawar dake zuciyarta ya hanata karyata hakan, kasa furta kanzil ta yi Uncle na lura da hakan kawai saita fashe masa da kuka ya yi jigum yana sauraranta dukkansu zuciyoyinsu biyu sun lulq tunani daban-daban.
Sai da ta gama kukan don kanta daga bisani ya yi mata nasiha tare, yi mata bayani a karshe ya yi mata aƙbishir da sunanta na cikin waɗanda zasu karɓi schoolaship na tafiya karo karatu kasar sudan ai Fatima sai ta zube tana sujjada shukuriya ga ubangijin talikai daya haskaka duniyarta cikin aminci da kariyarsa.
Kai tsaye gida ta wuce tana yi wa Mama albishiri jikinta ya yi sanyi da yanayin Maman ta dubeta,
“Mama naga kaman bakya murna”.
“Fatima ba murna ce ba na yi bs harga Allah nafi son kiyi aure kema hankalinki ya kwanta ki duba kannanki na baya baya kowace da mijinta da yaranta ke ko sha awar hakan ma banga kina yi ba anya lafiyarki kalau?”.
Fatima an sosso mata taɓon da take fama da shi kawai sai ta fashe da kuka,
“Mama ina son in yi aure amma tada hankalin baida wani fa ida, ki duba ban ɗaga hankalina ba akan yin aure amma kiji bi yadda kika damu ina ga na sama kaina damuwa kan hakan? A waɗanan shekarun nawa idan ban kwantar miki da hankaliba Mama ba na ɗaga miki hankali ba nasani komai nada nada ka ida Mama don Allah karki hanani tafiya karatun nan karki dakushemin hoɓɓasata wallahi na yi miki alkawarin kare miki mutuncina ciki kuwa harda fansar rayuwata ga duk wanda ya nufi keta mutuncina”.
Tausayin yarinyar ya tsirga mata, wani abu ya daki zuciyarta ta tsinke sai ta maida kwalarta ta rungume Fatiman suna kukan zuciya.
Cikin kwanciyar hankali ta fara aikinta, watanta biyu da farawa ta ɗauki albashinta mai tsoka albashin farko ta gyara gidansu ya yi tsaf ya sha fenti, na biyu kuwa tagwaye ta yi wa registration na colifine sauran ta siya wa gidan kayan abinci. Watanta biyar _viser_ ɗin su ta fito ta tafiya _Sudan_ karo karotu wato _masters_ babu wanda bai taya ta murna ba surutu kam tasha shi babu kama hannun yaro iya ka ta kali mutum in taga zata iya ta tanka har _airport_ na Kano suka yi mata rakiya suna kuka tana kuka ta ɗaga zuwa Sudan.
Matar uncle tsaraba sossai ta haɗa mata dangin kayan amfaninmu na gida. *UMDURMAN ISLAMIC UNIVERSITY* nan ce makarantar da aka kai Fatima dake suna da yawa rarrabasu aka yi, wasu an kaisu, Khartoum akwai kuma waɗanda aka kai elrazu university, itama akwai yan scholarship, amman waɗanda suke gasar karatun kur ani. Yan Jigawa sunfi yawa da birnin Kebbi. Elrazi a unguwar Azhari take, amma ita private ce.
Tunda aka kai Fatima aka bata masauki ba ruwanta da kowa, kasancewar a hostel ta zauna, bata yadda ta kama wani waje daban ba kuma suna da nisa tsakaninsu da unguwani. Kuma ka idarsu in dai ke ba mazauniya ba ce ma ana yar garin duk wacce take karatu umdurman, ba ta zama khartoum, sai dai can umdurman din a hostel. ‘Yan matan dake karatu a umdurman suna shiga cikin khartoum duk sati siyayyar kayan amfani, sabida umdurman kamar quarters ne ba suda manyan titinu da supermarket sai sun shiga cikin gari.
Fatima rayuwarta take babu ruwanta da kowa sai karatu shi ne abokinta, tunda karshan sati ya kusa taketa shirya yadda zata fita siyayya sabida kayan abincinta duk sun kare bata saba da nasu ba garama shayi tana ɗan sha na cikin kasuwar makaranta amma ranar data fara shansa ma sai da ta yi zawo, har gara-gara gusa.
Gata dai a hannu kamar bazata yi daɗi ba amma a baki daɗi ras, wata gurasa ce haka, sunanta esh, wani zubin suci kisre da miyar ku6ewa. Esh kuma suna haɗawa da miyar dankali, adas, shorba, malafiya. Kuma duk bayan cin abinci sai an sha shayi. Bayan qaada kuma da yamma kenan. Hakan yasa duk ta takura kamar ba ita ba har wasu kuraje ta yi na sauyin ruwa. Kasancewar esh da full ake rabamusu a makaranta, rana daya da taci full din sai da ta dawo dashi tas, gashi dai kamar wake, amman yafi wake rashin dadi a bakinta, gasu bula-bula kai kace gujjiya ne, ta shiga matsi ba kadan ba gata ba gwanar magana ba bare ta tambaya, karshe dai sai ta fara kar6ar esh din kawai ta taho dukkhanin (shop) gefen hostel dinsu ta sai kwai, ta je ta soya ta hada da esh din taci. Daga baya da ta gano indomie kuma sai ta fara nutsuwa, tasan ba za a rasa su shinkafa da sauran kayan abincinmu irin na gida ba, matsala daya dai rashin sanin garin.
A department ɗinsu akwai wata ƴyar kasar Sudan mai suna Nu aimata, tunda ta kyala ido taga Fatima ta ji ta kwanta mata amma kash Fatima duk haba-haba ɗinta da jama a sai ta ji ina yar mitsilar basudaniyyar bata yi mata ba surutun tsiya kamar cakwaikkwaiwa shi yasa duk inda tasan zata ga Nu aimaht guduwa take, ita kuma Nu aimaht tana biye da duk wani motsinta.
Ranar Laraba ta tashi da son shiga kasuwa kuɗi ta rike a hannunta masu kauri wanda tana tunani zasu isheta shigarta da tayi ta kayatar matuka.
Doguwar riga tasa _sky blue_ ta yi _rolling_ da bakin mayafi takalminta mara tudu ta daɗe tana duban kanta a madubi har wata yar Alkahira tana tsokanarta da bazata yi shigar Sudan ba. Girgiza kai kawai ta yi tana murmushi kasan ranta tana ayyana shigar da ta ƙlura sun fi yi wato Budurwa, abaya. In zata yi gayu eskerto da buluza wato (siket da riga) ko wando da riga. Ko gowns haka masu kyau, suyi (tarha) a kansu wato naɗi . Sannan bata lalle ba ta rasma amman zata iya sa jambarce. Akwai su da karin gashi ayi ado.
Ta jima tana tafiya kan babbar hanyar dazata fitar da ita da umdurman harta gaji sabida rashin sanin in da zata nufa kamar an jehota ta faɗo gaban tare da rike hannayanta har wani tsorata ta yi cikin larabci ta furta,
“Fatima Aminu Muhammad ko? Ina zaki? Ko bakisan hanya bane?”.
Wani takaici ya kasheta ji take kamar ta matse ya mitsilar basudaniyar ta huta gata mitsit sai kafirin shishigi da iya zance, fuska a ɗaure ta bata amsa,
“ina son zuwa siyo kayan amfani ne”.
Bata damu ba ta ja hannunta ta bita tamkar rakumi da akala suna tsaye wata mota ta yi parking mai kyau ta buɗe tare da dubanta,
“mu shiga”.
Zatonta ta hayace bata yi musu ba ta faɗa sai da taga ƴyadda Nu aimaht ke hita da balaraban dake tuka motar ta fahimci akwai sanaya, dubanta ta yi,
“ina zamu fara shiga ne?”.
Cikin lafiyayyan larabci ta maida mata martani,
“ban fahimta ba?”.
“Nufina inda zamu je siyayyar akwai, kiyi amdanida. Tasamoh dake kan titin laffaj jubaa. Sai ahlan dake shargi akwai kuma katon mall Afrah sunansa”.
“Muje kowa ne ni dai bukatata siyayya”.
Ta faɗa a takaice, sai basudaniyar ta ƴyi sakarau da ita na rashin jin daɗi itama Fatiman akwai hakan tare da ita amma ta maze. Kai tsaye a Afrah suka yi tsinke a Fatima sai ta zama yar kyauye ta ware idanu tana kalo kamar yar kyauye ta yaba tsarin wajan sossai. Babbane sosai yanda mai karatu bai taɓa tsammani ba babu abinda babu a ciki. Don haka kaf siyayyarsu anan suka yi ita dai Fatima kayan abinci ta siya amma ta lura cakwaikwaiwar tata sutura ta kwasa irin na mutan garinsu sunkai kala ashirin daga kan kaya zuwa jakunkuna da takalma sai kuma turarruka manya guda uku da a gogo guda biyu.
Sun gama suna shirin fita Fatima ta mika kuɗi sai Nu aimata ta maida mata kuɗinta,
“na biya miki”.
Wani mugun kallo Fatiman ta watsa mata tare da fauce hannunta ta nunata da yatsa,
“sa ki nayi? Bana son shishigi da cusa kai ko kin ga nayi miki kalla da fakirai?”.
Bata jira cewarta ba ta cusa kayan a mota tana juyowa wayam babu Fatima babu dalilinta, neman duniya bata ganta ba haka ta hakura ta wuce suka nufi makaranta tunanunta ko can ta koma duk inda take tunaninta ta duba babu ita har hostel hankalinta ya tashi, mukulin motar ta karɓa ta sallami drivern ta banɗama nemanta cikin unguwani amma ina har bayan la asar ta sake dawowa makaranta babu ita zuwa lokacin Nu aimat ta ci kuka ta gode Allah idanunta jajjur.
Fatima kuwa maimakon ta yo baya sai ta nausa cikin kasuwar ɓat hanya ta ɓace mata ta rasata duk wanda ta tambaya da sun kali kayan jikinta sun fahimci ba yar garinsu bace sai su dare, hankalinta ba karamin tashi ya yi ba gashi bata taho da wayarta ba balle ta kira hukumar makaranta ta galabaita matuka ta nemi bakin kantin da suka yi siyayyar ta zauna tana yi wa kanta Allah ya kara alhakin Nu aimaht ne.
Huɗu da rabi Nu aimaht ta koma Afra duk ta jeme tun daga nesa ta hango Fatima da gudunta ta karaso ta rungumeta sai suka fashe da kukan tausayin junnansu,
“kiyafemin Nu aimaht”.
“Ba komai Fatima kin sha wuya ko duk ni naja miki da na yi miki shishigi amma me yasa baki kira hukumar makaranta ba?”.
Ta yi tambayar tana tsareta da idanu, kunya ta kamata na yar mutan Sudan ɗin ta ce,
“na manto wayata kuma kowa na tambaya basa kulani”.
Murmushi ta yi ta ce,
Yan garinmu nada al adar kin bako kiyi hakuri!”.
Gwale idanu Fatima ta yi tana mamaki ta kasa shanyewa wato basa san bako amma ita taji ta gani take binta saita ji kaunar yar mitsilar basudaniyyar ya kamata,
“na gode Nu aimaht”.
“Ki daina yi min godiya taimako abu ne mai kyau ga musulmi ki taso mu tafi ban koma gida ba tun fitowarmu ke nake nema Abbuna yanata nemana kuma na sallami driver zai musu bayanin inda nake”.
Mikewa ta yi suka jera ta jasu a mota suna tafe tana yi wa Fatiman tambayo yi itama tana tambayarta har bakin hostel ta raka Fatiman ta shigar mata da kayan abun da ya bata mamaki rabin siyayyar ita ta shigowa da ita ta buɗa baki zata yi magana ta tareta,
“na miki shishigi karon farko ki ɗaure ki amsa don Allah ba zan kara ba”.
Murmushi ta yi suka yi _exchange_ na numbata ta wuce Fatima ta dinga buɗe kayan tana mamaki, dogayan siket da rigunansu da wanduna masu riga har guiwa duk gasu nan sai kayan abincin gwangwani nau i daban-daban adanasu ta yi ta zauna tare da ɗaukan wayarta ta kira gida suka gaisa da yan uwanta da Aunty Maryam anan aka mata aƙbishir tagwaye sun ci colifine. Ta lumshe idanu tana tunananin sauyin rayuwar da take samu daga wannan sai wannan..
Tun daga ranar Nu aimaht ta cigaba da nannewa Fatima tun tana ya kice ta har suka yi shakuwa mai tsanani, Fatima na mamakin yadda Nu aimaht taki zaman hostel wanda akwai da dama yan area ɗinsu dake zaman hostel sabida nisa tana lura da ita duk yawan surutunta akwai lokacin da take katse shi koda lacture suke ɗauka ta fita ta tafi gida zurfin ciki bai sa Fatima ta taɓa tambayarta dalili ba. Dangin Fatima babu wanda bai san Nu aimaht ba suna gaisawa da yar hausar da take koya wajan Fatima wani lokacin kuma da larabci suke Sadis dake arabic ya yi yana fassara musu.
Tafe suke tana tsokanar Fatiman dai dai lokacin Na’im Rawad Wad ya karaso wajan yana yi ma Fatima magiyar ta tsaya su yi magan ɗan department ɗin su ne balaraban Saudi ne amma ko a jikinta sai ma ta kara gaba ta barshi da cakwaikwaiwar kawarta tana yin gaba ya dubeta,
“ina son kawarki Nu aimaht”.
“Kayi hakuri matar aure ce”.
Wani kallo ya watsa mata daga bisani ya tanka,
“haka matan aure suke a Sudan zaki rainamin hankali ukkty”.
Jinjina kai ta yi kawai ta wuce ta ce tana zuwa ta ɗaka mata duka,
“kina ɗaga hankalin sudanis fa!”.
Murmushi ta yi sannan ta bata ƙlabarin yadda suka yi itama dariya ta yi tace,
“au ya matan auranku suke?”.
“Eh! Shigarsu ta bambanta sossai da mu yan mata, matar aure tana yin shigar, tubee, (lafaya) su shi da karina kalar tuben, da siket, da tarha, su cogala takalmi, suyi rasma,(fulawa) suyi henna(lalle) su kuma yi dukkhan(hayakin dirot) a dane fuska da _make up_ kwaliya , irin _powder_ nan ta _vampires_, ki gansu dau kamar a sace su”.
“Ke yar mitsila kamar kuraye dai”.
Turo baki tare da cewa,
“gama yi musu tsiya ai wallahi kema cikinsu zaki zauna”.
“Wa!?”.
Ta faɗa tana gwalo idanu ta cigaba,
“Allah ya kiyayye wallahi ba zan yi ba, auran basudane taf”.
Nu aimaht ta yi narai-narai da idanu,
“kai Ukkty me yasa?”.
“Haba Nu aimaht kawai sai in rabo da kasata sabida aure?”.
“Kwarai kuwa aure ai yama fi haka ni yanzu banda Mama ai da tuni ina Alkahira”.
Da sauri ta kauda zancan Fatima na lura da yanayinta ta maze,
“mubar wannan batun yar mitsila ban san bakinki ba baya ga haka da kanki kika zauna kika faɗimun al adunku na kin bako ga bauta da akewa dangin mini bazan iya ba”.
+
Murmushi ta yi ta ce,
“kwarai muna da ɗabi ar tsanar ajaneeb (Bako) akwai mu da nuna banbanci, amma ko akaina ya isa misali kisan ba duk aka zama ɗaya ba!”.
“To ai bazan iya bauta ba kince fa komai kai zaka ke yi wa dangin miji na aiki”.
Waima ta yay dama kuna auratayya da yan wani garin daba naku ba? Tsarabarku ta fiya yawa?”.
“Eh ana yi Fatima, sabida komai namu ya bambanta. Al’ada ya danganta. Gaskiya in kinga ‘yar Nijeriya ta auri Sudani kawai tana ma sa so mai yawa ne”.
“Taf to ni kuwa bama wanda ya yi min duk garinku ki kyaleni ni bazan zo in ta bauta ba wallahi”.
Dariya ta kwace mata ta ce,
“waike an gaya miki bauta ake? Eh ana yi mana amma ya danganta, Kinga al adunmu. Kina auren ɗanmu to kuwa aiki zaki sossai. Wanki naki ne, kima suruku, kima kannensa. Sannan da yawansu tsakaninki da Mamansƴ katangace kawai, ma ana gida ɗaya kuke. Guga shara, komi ke zaki yi”.
“Taf kice rama zan yi saura kashi?”.
Dariya ta sake yi da alama hirar na mata daɗi ita kuwa Fatima ta gama kullewa, ta cigaba,
“Kece wankin kannensa kuma yawanci marassa kunya ke hakan, amma in kika tsare gida shikennan. Ana auratayya sosai kam ya danganta da irin gidan da zaki shiga. Idan akwai wadata, zaki ga har washing machine akwai. Ba kuka zaki bautawa uwarsa haka ba, amman wankin tube kam (lifaya) dole ki wanke mata ki mata mak’wa (guga) idan ne sa ma kuke, kullum kikai girki sai kin aikamata. Wannan kuma yafi faruwa a rayuwar k’auye. Amma idan gidan masu wadata ne baki da matsala. Ba ki da wannan hidimar amman fa ke ce da girki da kuma wankin kayan suruka. In kuka basu sa mugunta ba yar aiki ma ake daukar miki”.
“Kice ku ɗin bayi ne?”.
Da gudu ta bita suka faɗa hostel suna dariya su duka ta sake dubanta tace,
“kice in daina kunshi?”.
“Eh! Wallahi ki daina idan budurwa tayi lalle kallon matar aure ake mata, shiyasa in suka ga Nijeriyan sunyi suyi ta mamaki”.
“Ai kuwa shi zanta yi in samu in rabu da mazan garinku haka kawai in zama baiwa”.
STORY CONTINUES BELOW

Sai kuma ta yi jigum, tunda tazo Sudan Na im ne kaɗai ya nuna yana ra ayinta harta ke guje masa ma anya kuwa tana da rabon aure a duniya?.
Ganin ta lula cikin tunani yasa Nu aimaht ta taɓota sai ta yi murmushi kawai, daga nan suka faɗa wata caftar daban.
NU AIMAH MUHAMMAD NAWAS BIN NAWAF.
Diya ce ga Attajirin ɗan kasuwa mai ci da zamani wato Muhammad Nawaf Nawas asalinsa mutumin Sudan ne dattijo mai shekaru sittin da biyar cif a duniya amma hutu da jin daɗi ya aƙkinta hakan . Dunkiyarsa tsaftattaciyar dukiya ce da ake fitar da hakkin ubangiji. Matarsa Faɗima dattijuwa mai shekaru hamsin da takwas ma aikaciyar lafiya ce fanin mata. Suna da yara huɗu mata uku namiji ɗaya. Khausar ita ce babba tana auran ɗan sarkin masar suna can da iyalanta yaranta biyar duk maza. Mai bu mata ita ce Khairaht tana auran wani babban likita yaranta uku suna Uganda sai Muhammad Muhammad Nawaf bin Nawas shi kuma matashin likita ne kan masu taɓin hankali yana nan tare da iyayansa sai Nu aimaht mai shekaru ashirin da huɗu cif. Rayuwar iyalin rayuwa ce abar so ga kowane iyali suna son junnansu matuka amma duk da wannan walwala da farin cikin ɗa suke ciki akwai abu guda ɗaya daya tafi da farin cikin wannan iyali wanda har yas Nu aimaht da Muhammad suka yi furucin baza su yi aure ba har abada sai sun sami mai cika musu wannan buri.
BABI NA SHA BIYAR……..
Shakuwa tsakanin Fatima da yar mutan Sudan sai kara gaba take, a watani takwas da ta yi a garin sun zaga wajajje da dama masu kayatarwa amma Fatima bata taɓa zuwa gidansu ba koda wasa Nu aimaht bata taɓa nuna mata jin zafin hakan ba kaunar Fatiman take bilhaki wasu lokutan takan ce,
“Fatima badan Mama ba wallahi zan dawo hostel sabida ke”.
Takan yi dariya kawai ranar Laraba misalin karfe biyar na yamma agogon Sudan a Nigeria kuma karfe uku ne na yamma Nu aimaht ta sami Fatima tana waya da su Mama har suka gama bata nemi su gaisa ba ita ma Fatima bata tanka ba.
“Fatima ina neman alfarmarki yau kizo muje ki gaida mahaifana”.
Sai Fatiman taji babu daɗi ita ya kamata ta yi wannan hoɓasar ba Nu aimaht ba amma tana gudun ace ta zake, murmushin yake ta yi ta amsa da,
“ba alfarma tsakaninmu sai dai iko da juna Nu aimaht nasan kina jin zafina koda baki furta ba amma kiyi hakuri sanin wacece ke yass nake baya-baya da ke da kusanci dake banasan abin da zai taɓa martabata”.
Kai tsaye suka wuce gidan nasu, tun a harabar gidan ta soma tsorata da mamaki bisa uwar dukiyar dake cikin gidan suna shiga ta hau tsale-tsalen murna ta soma gabatar da ita wajan masu aikin gidan nan suka dunga haba-haba da ita suka cika mata gabanta da nau in kayan marmari daban-daban kasa cin komai ta yi sai ruwan shayi da gurasa. Daga nan Fatiman taja ta suka je suka gaida Mama sai dai yadda Maman ta karɓeta ya fi bata mamaki, bakuma iya shi ba sashin Maman ya fita daban dana kowa don Nu aimah har sashin mahaifinta ta kaita danata kowane cike da kayan alatu amma na Mama sai ɗima-ɗuman takardu da wasu file file badai ta tanka ba suka yi sallama suka yi wa lambun gidan tsunke tana yi mata bayanin ahalinsu. Sai magariba ta maida ita bayan sunje yi wa Mama sallama abin mamaki saita nuna bata san wacece Fatiman ba abun ya mata ciwo.
Bata nuna hakan ba suka yi sallama, Nu aimaht na ƙlura da yanayinta amma ta kane da Abbu suka yi kiciɓus suka gaisa cike da fara a da girmammawa ta sa driver ya kaita har makaranta bayan ta cikata da turarruka masu tsada.
Fatima ta daɗe tana juya lamarin Mommahn Nu aimaht shi yasa take baya-baya wulakanci take gudu amma tana gudun nunawa Nu aimaht ɗin sai dai ta ajiye hakan matsayin ganin farko.
Kwanci tashi Fatima suka share shekara ɗaya suna karatu, bata da matsala mai yawa sabida tana under schoolaship ga kuma Nu aimaht da bata gajiyawa da bukatunta duk da kaucewa hakan da take yi. Sai dai abin da ya ɗaurewa Fatima kai Nu aimah bata sake janta zuwa gaishe da Mommahnta ba amma bata gajiya wajan bata labarin yayanta Muhammad wanda basu taɓa haɗuwa ba. Ganin yadda ta bagarar da abun yasa ta kasa jurewa tana mamakin yadda ta damu da danginta hata kuɗin jarrabawarsu tagwaye Nu aimaht ɗin ce ta tura da kuɗinta baya ga hidimar kayan sawa da take tura musu wani da saninta wani sai dai Sadis ya faɗa mata.
Hakan yasa da kanta ta yakice ta nemi Nu aimaht suka sake zuwa gidansu amma wannan karon tarbar harta fi ta baya muni wajan Mommahn, koda wasa Fatima bata nunawa Nu aimaht damuwa ba daga lokacin ma ta sa duk hutun asabar acan suke yi amma abun mamaki sai su yini bata ga Mama ba, Muhammad kuwa baya dawowa sai dare, in kuma dawowar yamma ce to ka idarsa inya shiga ɗaki ba mai buɗewa sai mahaifansa hakan yasa har Fatimahn tazo ta tafi ba suga juna ba hakan yasa basu san juna ba.
***
Yau kwana uku kenan Fatima bata ga yar mitsilar basudaniyyar ba, ta kira wayarta bata samu taje gidan amma bata sami kowa ba hankalinta ba karamin tashi ya yi ba, har faɗawa ta yi ta yi wani zuru-zuru da ita kamar mai cuta har waya ta yi gida da kukanta ta sanar musu suma hankalinsu ya tashi sossai a ranar yini suka yi yi mata waya sai da ta yi danasanin basu labari karshe ma kashe wayar ta yi. Kwana ta yi bata yi bacci ba tana nafilfili da rokon Allah ya bayyana mata kawarta gari na wayewa ta hau abin hawa daga ita sai dogon sket da riga mai dogon hannu sai madaidaicin hijabi data saka tana sauka a kofar gidan ta hangi fitowar Nu aimaht da Abbu suna rike da Mommah a gefe ga wani matashi bata tantama Muhammad ne da sassarfa ta karasa ko canjinta bata karɓa ba idanunta taf cike da hawaye ko yadda taga Nu aimaht zuru da ita tasan babu ƙlafiya.
Karasawa ta yi ta gaida Abbu ya amsa a gurguje ta bi bayansu suka shiga gidan, wuce wa da ita suka yi ɗaki jim kaɗan suka fito su kun ba tare da ita ba. Fuskokinsu duk babu daɗi Muhammad ya watsa mata wani sassanyan kallo da ya kashe mata gaɓan jikinta baki ɗaya ta yi saurin kauda kai. Da hanzari Nu aimaht ta karaso suka rungume juna, sai suka fashe da kuka daga bisani ta janye,
“Uktty kin wahal dani, me yake faruwa zuwana uku ba kwa nan wayarki a kashe jiya na kasa bacci har su Mama na faɗawa baki ji yadda suka dameni da waya ba karshe kasheta nayi”.
“Kiyi hakuri Fatima Mommahter ce bata da ƙlafiya”.
Zare idanu ta yi tana kaɗa kai,
“baki kyautamumnba ƙkikaki sanar min wannan shi ne zaman tare?”.
“Kiyi hakuri abu ne ya zo a zafaffe shi yasa”.
“Na hakura muje na ganta”.
“Karku shiga ta samu baccine”.
Muhammad ya faɗa yana sauke idanunsa akan Fatiman, wanda tun ganinta a waje ta sagar da duk wani karsashinsa. Da hanzari Fatiman ta ɗauke idanunta haɗuwar idanunsu ya sauya yanayinta gaba ɗaya ta dingajin wani irin ɓurɓushin abu yana nausar kirjinta da kyar ta aro juriya ta yafa ta gaidashi a gayance ya amsa yana kokarin ɓoye abinda ya daki kuzarinsa amma Nu aimaht ta gama fahimtar kowanansu. Wucewa ya yi zuwa sashinsa daga shi har ita a jiyar zuciya suka saki. Fatima bata jima ba ta bar gidan, sabida ta kasa dakewa. Tunda Fatima ta koma bata da wani kuzari sai tunanin Muhammad kwata-ƙkwata ta kasa kataɓus tana san korar yanayin a zuciyarta amma ta kasa, haka ta kasance kamar mara lafiya. Kwana biyu tsakani ta sake zuwa duba Mommah jikin da sauki amma ko gaisuwar Fatiman bata amsa ba taji zafi ta ayyana kawai Mommah ita ɗin ce bata kauna amma sai ta kane hakan da ta yi ba karamin karawa kanta kima ta yi wajan Nu aimat ba zahirin gaskiya ta tsani tambaya.
Tsayin kwanaki Muhammad ƴya kasa tantance a yanayin da yake yau ma yana sashinsa ya kai mari ya kai gwauro a haka Nu aimaht ta iske shi cikin kulawa take dubansa,
“Akie menene yaƙke damunka”.
Ya fisar da hucci mai zafi,
“Ukkty”.
Kome ya tuna? Sai ya yi shiru ta sake matsawa kamar zata yi kuka tana tambayarsa,
“nima na kasa bambancewa amma inajin wani abu daga ganin da na yi mata”.
“Wacece?”.
“Faɗima!’.
Zare idanu ta yi tana dubansa wani abu mai nauyi ya tokare kirjinta ta kasa motsi. Ras! Gabanta ya faɗi suka yi kallon-kallo ta ɗauke kai tana tunani, anya Fatima zata amince da sharaɗinsu kuwa? Shin yaushe Muhammad ya sauko da sharaɗinsu har yake tunanin aure? A gefe guda kuma tana tunanin yadda Fatima ta ke kin auran Sudanis shin babban batunma aya Fatima zata so Muhammad? Akwai tarin nakasa a tare da wannan al amari.
BABI NA SHA SHIDA
NIGERIA KATSINA STATE UNGUWAR SAULAWA.
Misalin karfe biyar na yammaci ta faɗo gidan babu ko sallama, Rahma dake zaune cikin zarnin robar fitsari kudaje sun mammyeta ta buɗe baki tana faɗin,
“Mamanmu yunwa nake ji”.
Wata muguwar harara Mama Hajaran ta watsa mata, kana daga bisani ta soma sababi,
“ki jira ubanku ya kawo tunkuna’.
Murja da tunda ta fara bala in tana jinta, ta yunkura ta tanka,
“Mamarmu kema yau abinda kike sa Mamansu Fatima ta aikata shi kike aikatawa wallahi tun wuri ki sauya sheka domin bazamu yarda da wannan takurar ba bamu taso a cikinta ba gori da hanci ko? Karfa ki fara wallahi”.
Mukus ta yi tana jinsu ta kasa magana, gaba ɗaya yanzu tsoron Murja take kwata-kwata yarinyar bata tsoranta ga wani tashan fita yawo da take babu inda bata sani ba na yawan sheɗanci a gaban kowa ake zuwa a ɗauketa a fita da ita a mota kuma sanda ta ga dama take dawowa amma hakan bai isheta ba yawo take tana faɗin Mama Mariye ta tura Fatima karuwanici.+
SUDAN KHARTOUM
A gajiye likis ta dawo daga lacture yau bata ga kawartata ba amma hakan bai dameta ba kamar yadda tunani Muhammad ya ɗaga mata hankali ya hanata nutsuwa ta lumshe idanu tare da buɗe wayarta ta shiga gallary tana karewa hotansa data lallaɓa ta turo a wayar kanwarsa kallo. Sanye yake cikin riga jallabiya ruwan kasa mai turuwa, ta ɗan kamashi kaɗan yana tsaye kyam a jikin wani kayatacan wajan hutawa wanda yake acikin gidansu wajan a sagaye yake da kananan bululluka ya ɗanyi zurfi sossai sai aka zuba ruwa samansa da wasu irin fure kala-kala suna shawagi. Ta yi murmushi tana kare masa kallo Muhammad sarauyine na nunawa sa’a yana da cikar hallita mai ɗaukar hankali fuskarsa doguwa ce sossai yana da haɓa yar karama mai kyan fasali hancinsa dogo ziyat da shi siriri sossai idanunsa madaidaita sun ɗan shige ciki. Yana da cikar kasumba baka suɗik kwantaciya luf-luf wadda tasha gyara haka yana da ɗan zagayayyan gashin baki girarsa kuma baka ce a ciki ɗuf da gashi mai ban sha awa bakinsa ɗan karami ɗauke da laɓɓa pink. A ƙansa hiramine ya naɗe da shi duk da babu walwala tare da shi a hotan ya yi matukar burgeta ainun. A hankali ta lumshe idanunta ga mamakinta sai ga hawaye sar! Ya biyo kuncinta ta shafa ta kara shawafa kamar taga abin tsoro har wani ja baya ta dingi yi tana girgiza kai bakinta na furta,
“No! No!! No!!! Muhammad kar ka yi min haka!”.
Sai ta fashe da kuka mai cin rai, Allah ya taimaketa babu kowa a hostel ɗin da sauri ta wanke fuskarta a banɗaki ta fito tana tsattsafe ruwan tana sauke idanunta sai kan Nu aimaht.
Cikin azama ta aro juriya ta yafa ta tareta da murna,
“ke yar mitsila yau kin wahal dani”.
“Me kuma na yi?”.
“Nemanki na yi ta yi ban ganki ba wallahi kodai jikin Mommahn ne?”.
“A a yaya Muhammad ne”.
Ras! Gabanta ya faɗi,
“lafiya!?”.
Ta lura da yanayinta sossai yadda ta nuna damuwa zuciyarta ta shiga zargi anya Fatima bata san Muhammad? Wata zuciyar ta tunasar da ita idan tanasansa zata iya karɓar uzurinku? Sai ta yi saurin ɗauke kai.
“Baya jin daɗi ne wani al ammari ke damunsa ko nace ya ke damunmu baki ɗaya wanda adalilinsa nida shi muka ki ƴyin aure”.
Wani rugugi ya saukar mata aka ta ɗago a razane,
“Nu aimah kimin bayani yadda zan gane”.
Mikewa ta yi tayi taku hudu zuwa shida sannan ta share hawaye ta tako ta dafa Fatima.
“Fatima rayuwar iyalinmu rayuwace mai cike da jin daɗi amma abu ɗaya ya dakusar da farin cikinmu ba komai fane face wata lallura dake damun Mommah”.
“Wace lallura ce Nu aimaht?”.
“Fatima lallurar Mommah wata irin cuta ce mai wuyar sha ani”.
“Wace kennan? Shin akwai cutar da bata da magani ukkty?”.
“Fatima cutar Mommah ba a warkewa sai dai samun sauki”.
“Wace cuta ce?”.
“Fatima cutar, mai suna Alzheimer, a turance. Ita ce take damun Mommah wanda hakan ya dakusar da farin cikinmu Muhammad ya ce bazai taɓa aure ba sai macen da zata iya zama da Mommah ta kula masa da ita, haka nima bazan auri wanda bazai ajiye ni a Sudan ba ina tsananin son mahaifiyata, amma kash ban taɓa saurayi ɗan Sudan ba Fatima kuma duk wanda na kawowa uxurine sai su kafe kan baza su ajiyeni a mahaifata ba na fida rai da zan yi aure tunda daga ni har yayana mun rasa cikar burinmu”.
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un”.
Fatima ta furta daga bisani ta lumshe idanunta, wani abu ya ɗaure jijjiyoyin jikinta tamau, ji take anya kuwa tana da sa a a duniya? Buɗe idanunta ta yi ta sauke su kan Nu aimahta.
“Ukkty wanan wace irin cuta ce?”.
STORY CONTINUES BELOW

“Fatima! Ciwon mantuwa _varies_ kaman yadda Akie ya yi min bayani. Akwai wanda yake faruwa sanadiyar tsufa shi ne wanda ake kira _dementia_, akwai wanda kuma larura ta rashi lafiya ke sawa da shaye shaye ita ce _delirium_, itama sometimes tsufa na sawa. Akwai kuma _amnesia_, itama _amnesia_ din akwai wacce ake kira senile amnesia idan Mutum yana da shekaru masu yawa wato tsofaffi sukan kamuwa da ita.
Akwai kuma _amnesia_ da take faruwa sakamakon matsala a kwakwalwa ko idan Mutum yayi hatsari ,ƙo ya samu buguwa a kai
Kuma ita ma _Amnesia_ din iri biyu ce, akwai _retrograde amnesia_ da ƙkuma _anterograde amnesia._
_Retrograde_ shi ne Mutum zai manta abun da ya faru yanzun nan ko a ranar amma kuma abun da suka faru shekara da shekaru zai iya tunawa.
_Anterograde_ kuma shi ne Mutum zai manta komai da ya fara a baya sai dai ya samu _fresh memory_ abun da suke kara faruwa kawai zai tuna.
To ita Mommah naza _alzheimer’s_ ne. Idan kin tuna nace miki da farko akwai _dementia_. To shi _Alzheimer’s_ din _is a type of dementia_.
Yanda yake shi ne Mutum zai samu matsala da _memory_ din shi, da yanda yake _behaving_ gaba daya zai canza, da yanda Mutum yake tunani duk zai canza. Saboda wani _part_din kwakwalwar Mutum da take _controlling_din _memory_ da _behaviour_ ita ce take tabuwa.
Yawan cin _Alzheimer’s_ a tsofaffi ake samu. Yana farawa a hankali kiga tsoho ya dan fara birki ce wa ko ya fara _behaving_ kamar yaro karami, a hankali har duk kiga sun birkice da irin rikicin tsufan nan.
Amma ba tsofaffi kadai ke samu ba Amma mafi yawancin cases din na tsufa ne, about 80-90% na _problem_ din a _old age_ ake samu, yana farawa kamar daga _65yrs_ zuwa sama.
Fatima gaba ɗaya ta gama tsorata da lamarin tunani take wato kowane Mutum ka gani a rayuwa baya rasa jarrabta daga ubangiji, wato su gasu da wadata da rai da lafiyar da masu son nata amma wani dalili daya gindaya cikin rayuwarta ya hanata auran, sai ta hasko Muhammad da irin yadda zuciyarta ke wassafa kyansa take ta soma hango wautarta data bari zuciyarta ta rufta a kaunarsa anya tama kanta adalci? Ta sake tuna hasken fatarsa ta dubi batarta cikakkiyar bahaushiya baka da ita sai goggewa data samu irin na samun nutsuwa murya na rawa ta ce,
“Ukkty ya _symptoms_ na wannan cutar yake?”.
Hawaye ta share ta ce,
” _Signs and symptoms_ din da suke samu shi ne:-Da farko kafin abun ya zama _serious_, suna farawa da dan mantawar abun da akayi a lokacin, ko irin magana ka fada musu sai su musa suce ba ayi hakan ba. Suna kuma samun _confusion_, abu kadan sai ya ruda su, kuma basa iya rike sabon abu a kansu. Kamar sunan wani sai a fada musu, yanzu su manta a lokacin. A hankali idan abun ya zama _severe_ sai su fara manta har sunan yan gidan su da ya’yan da suka haifa fa makota da duk wasu Mutanen da suka dade suna tare da su. Suna samun _disorientation,_ shi ne za ki ga suna manta su kansu da inda suke, basu san lokaci ba, basa iya bambance safiya da rana, ko an kai su wani guri aka tambaye su ina suke basu sa ni ba.
A hankali sai su fara rudewa, ko dariya akayi suyi ta tsarguwa suce da su ake ko su fara zargin Mutanen da suke tare da su da yin wani abun da ba haka bane. Idan abun ya ci gaba ya kara zama _severe_ sai su fara manta komai ma, su fara _behaving_ kamar yara, magana ta fara zama _problem_ garesu da hadiyar abinci ko ruwa shima y fara zama matsala da tafiyar su duk sai ta canza”.
Kuka ne ya kwacewa Fatima ta tsantsar tausayin Mommah da rayuwarta, murya a raunane ta ce,
“Nu aimaht garin ya Mommah ta sami wannan ciwon?”.
“Haɗari ta yi a wata safiya an kirata a waya ta zo an kawo mara lafiya zata yi mata aiki ta fito tana sauri ko driver bata ɗauka ba da kanta ta yi tukin garin sauri sitiyari ya kwace mata motar ta kifa ta faɗa rami kanta ya bugu”.
Dakin ya yi shiru sai sautin kukansu dake tashi, tabbas Mommah ta bata tausayi sai yanzu ta gano dalilin rashin kulata da bata yi sai da suka ci kukansu suka more kwarai sannan suka lallashi kansu.
***
Fatima dai dumu-dumu ta sami kanta a kaunar Muhammad, haka shima amma cikinsu babu wanda ya sanar da ɗaya har gara Muhammad kanwarsa ta sani Fatima kuwa ita kaɗai take kumbiya-kumbiyarta a hankali ta soma ciwan kai mai zafi wani sa in har bata gani ko karatu gaggararta yake ta rasa wanda zata faɗawa. Aunty Maryam ta kira ta faɗawa matsalar ciwan kanta, hankalinta ya tashi matuka sabida ta tuna da bayanin da Dr ya yi musu kan hawan jinni na gab da kamata ta dinga faɗa in da take shiga ba nan take fita ba tun tana saurara saita fashe mata da kuka jikinta ya yi sanyi ta tabbatar Fatin nada damuwa amma zurfin ciki ya hanata faɗa sai ta sassauta murya ta hau yi mata nasiha jikinta ya yi sanyi ta ce,
“Aunty ki taya ni addu’ a amma ina jin kamar bani da rabon aure a duniya”.
“Fatima abin da fa hakuri bai baka ba rashinsa ba zai baka ba, karki yanke tsamani ba a yanke tsamani da rahamar ubangiji ke fa musulma ce!”.
Sun jima suna maganganu masu muhimmanci daga bisani ta datse ƙlayin suka yi sallama.
STORY CONTINUES BELOW

BABI NA SHA BAKWAI
Kwanci tashi soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Fatima da Muhammad hata Sadis da Sadiya da Aunty Maryam sun sani. Mama dai data sami lamari bata bada goyon baya ba amma bata nuna ba koda wasa ta dai bar abin cikin ranta tana yi mata addu ar samun nagari.
Wata irin zazzafar soyayya Muhammad yake mata abun har tsoro yake bata, Muhammad baya wasa da aiki jarumune amma dalilin Fatima har ya soma wasa da aikinsa duk inda tasa kafa zai sa kafa kafar rakumi da akala. Karatu ya taso su gaba watanni shida ya rage su kammala duk ya ɗaga hankalinsa. Kamar yadda suka saba yau ma sun fita bakin ruwa shan iska suna zaune kan faffaɗar dadduma kanta a kasa tana dana wayarta ya kura mata idanu ya kasa ɗaukewa ta ɗago tana dubansa a sanyaye,
“MD!”.
Shiru bai amsa ba ta sake faɗin,
“MD! MD!! MD!!!’.
Saita hau gurgizashi a firgice ya saki gauron numfashi ga mamakinta hawaye ne taf cike a kwarmin idanunsa cikin tashin hankali take dubansa.
“Muhammad! Menene damuwarka?”.
Ya sunkuyar da kai kawai yana shassheka,
“Muhammad menene?”.
“Fatima!”.
Ya kasa cigaba da magana sai ya ruko hannuwanta suka sarke da juna yana murzawa, ta kasa hana shi hakan duk da tana jin zafin abin da ya aikata kome ta tuna saita zame hannun da sauri, ya ɗago yana dubanta,
“Fatima zaki aure ni?”.
“Muhammad ina ga mun wuce wannan batun zan aureka idan na koma mahaifata, mahaifana suka amince da zaɓina”.
“Kina nufin idan basu amince ba ba zaki aure ni ba?”.
“Tabbas ban maka alkawarin hakan ba”.
Tsam ya mike ya bar mata wajan, tsayin minti ashirin tana zaune bata ganshi ba sai ta hau abin hawa ta yi tafiyarta hostel ta rabu dashi. Kwanaki uku tsakani basu yi waya ba kuma bai nemeta koda wasa bata faɗawa Nu aimaht ba rayuwarsu suke har gidan tana zuwa ta tayata kula da Mama yanzu har lokutan shan maganinta ta sani da irin abincin da ake bata da kuma abin da tafi so. Zaune suke a harabar gidan bayan sun gama ba wa Mama magani Fatima ta dubeta ta ce,
“Nu aimaht wai mai irin cutar Mommah basa warkewa ne? Kuma a kan wana irin magani ake ɗorasu?”.
Kamar daga sama ta ji an amsa mata da,
“waya gaya miki ana tambayar yan arabic depertment abin da ya shafi lafiya?. Yanda ake _treating_ din _patients_ masu _alzheimer’s disease_. Babu wani _specific_ maganin da ake rubuta musu ace wai sun warke gaba daya. Sai dai akwai magungunan da suke taimaka wa kwakwalwar tasu da taimakawa gurin _functioning._ Akwai _drugs_ kamar _donepezil_ ko _galantamine_( daya daga cikin waɗannan saboda aikin su daya ne). Sai kuma _memantine_ shi ma maganin yana _relieving sypytoms_ din Idan kuma duna da _depression_ (irin basa son shiga cikin mutane, suna da damuwa da yawa da rashin magana, rashin fara a da sauran su) za a iya basu _clonezepam_ ko _lorazepam_.
Sai abinci me kyau da shan ruwa ishashshe, da samun bacci da hutawa. Kuma tunda suna da mantuwa sai a taimaka musu da ajiye musu abun da suke bukata a kusa, Idan guri zaa nuna musu kamar xuwa toilet sai a samu hanya mafi sauki da zasu gane hanya, a samu dabaru da za a dunga nuna musu mutane ana fada musu abunda ya kamata su sani, a nuna musu yanda zasu dunga gane lokaci ko ta agogo ne ko kuma da faduwar rana yanda dai zasu gane lokutan sallah da sauran su. Suna bukatar kulawa da mutane a kusa da su amma ba a son yawan hayaniya”.
Harara ta mana masa a fakaice ba tare da Nu aimah ta gani ba ta ɗauke kai tare da furta,
“kenan hakan zai taimaka su warke?”.
Ya gani amma ya shanye kamar bai gani ba,
“A a baza su warke gaba daya ba dole wannan mantawar tana nan. Saboda kwakwalwar ta riga ta zama _affected_ maganin dai zai taimaka gurin hana kwakwalwar ta ci gaba da _damaging,_ zai taimaka musu gurin samun dan nutsuwa haka daga wannan rudewar, ya sa su su dunga shiga hayyacin su, yana rage yawan fadace fadace da suke yi zai yi _cooling_ dinsu _down_ kuma zai yi _improving_ _memory_ ɗinsu. Sai kuma yawan motsa jiki kan taimaka kwarai da gaske.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar Lancet ta Burtaniya ya ce mutanen da ke zama daf da titi sun fi shiga hatsarin kamuwa da cutar kidimewa.
Wani bincike masana kiwon lafiya, ya ce kwararun ‘yan wasan kwallon kafa na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwakwalwa da ke haddasa mantuwa, kuma ciwon mantuwa ciwo ne da ke aka fi samu tsakanin ‘yan wasan dambe da kwallon kafa.
Binciken da aka wallafa a wata mujallar kiwon lafiya, ya yi nazari ne kan tsoffin ‘yan wasa kwallon kafa 14 da ke dauke da ciwon mantuwa, wanda kuma suka soma kwallon tun suna da kananan shekaru da kuma yawaita amfani da kai a buga kwallo.
‘Yan wasan da ba a wallafa sunayensu ba, fittatune da akasari suka shafe shekaru 26 suna taka leda. Daga ciki akwai wadanda suka ta ba yi wa Swansea da South Wales wasa a tsakanin 1980-2010.
Bincike ya ce gwajin da aka gudanar kan shida daga cikin ‘yan wasa, ya bayyana cewa hudu na cikin hali mai tsananni na mantuwa, wanda ciwo ne da ake iya samu tsakanin kashi 12 cikin 100 na al’umma kacal.
A cewar shugabar binciken da ke kwallajen London Institute of Neurology, Helen Ling, wannan ya nuna karara alakar da ke akwai tsakanin wasanni kwallon kafa da ciwon mantuwa mafi muni da ake kira ”Chronic Traumatic encephalopathy” a Turance.
Ling ta ce wannan batu ya bijiro da bukatar tuntubar hukumomin kwallon kafa na FA da FIFA don samar da mafita cikin gaggawa.
Ling ta ci gaba da bayyana cewa alamomin ciwon mantuwa na soma bayyana ne daga shekaru 60 tsakanin masu kwallon kafa sabanni shekaru 70 da aka saba gani tsakanin sauran al’umma. Kuma 12 cikin 14 na mutuwa saboda wannan ciwon idan ya yi tsanani.
A karon farko kenan da ake danganta kwallon kafa da ‘yan wasa ke yi da kai a matsayin musababbin ciwon”.
Duk suka saki ajiyar zuciya suna tunanin rayuwa kowa da abin da yake tunani a kasan ransa, Fatima ta tafi kan tinanin yaya zata yi rayuwa da Muhammad hakan yana nufin in ta yarda zata aureshi zata zamo mai kula da Mama ne?. A gefe guda tunanin anya Mama zata barta ta auri Muhammad ya gama sanyayya jikinta kafin ta farga sai jin hucin numfashinsa ta yi kan fuskarta ta yi saurin kaucewa tana kai masa duka a zuciye,
“na faɗa maka bana so!”.
Nu aimah dariya ta yi ta mike zata bar wajan ta dakatar da ita,
“Uktty ki tsaya kimana alkalanci ya daina bana so kar na soma marinsa”.
Yadda ta yi furucin da gwatin guiwa ya bata tabbacin zata aikata sai ta dakata,
“kiyi hakuri zai daina, ya saba da al adar ne”.
“Ukkty ki kyale Faɗima tace in ta bar Sudan ba zata aune ni ba don haka ba zan bari ta bar kasar nan ba wallahi sai da aure na kisa idanu kuma ki gani”.
Kafin su yi wani yunkuri ya bar wajan ɓata, gaba ɗaya ya ɗaureta da jijjiyoyin jikinta tana duban yadda Nu aimaht ke jafa mata kallon tuhuma daga karshe ta mike suka bar wajan suna tafe babu mai magana kamar kurame.
STORY CONTINUES BELOW

Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji, su Fatima an shiga jarrabawar gama makaranta gaba ɗaya Muhammad ya birkice mata gani yake idan Fatima ta koma kasarta ya rasata kenan hakan yasa ya soma shirya wa kansa tafiya Nigeria ba tare da sanin kowa ba, sai kanwarsa daya karɓi number Sadis a wajanta kai tsaye gidan aminin mahaifinsa ya sauka dake Abuja bayan kwana biyu ya huta ya kira Sadis sun jima suna magana daga bisani ya bayyana masa kudurinsa na son auran Fatima da san zuwa ganin danginta. Sadis ya yi mamaki matuka bai kira Fatima ba sai ya kira Nu aimaht ya yi mata bayani, ta nuna masa yayanta ne ta kara da yi masa bayani mai gamsarwa ba karamin daɗi ya ji ba koba komai cigaba ne ga rayuwar Fatiman amma yana tausayinta kadda Mama ta ki amincewa. Kwana biyu tsakani yana bin gidan dangi shawarar kawo Muhamnad gudun tashin hankali sai da ya sami Sadiya da Mardiyya da Mama Hasiya da kuma mahaifinsu ɗaya bayan ɗaya ya yi musu bayanin komai zuwa lokacin ya samu kiran Muhammad yafi sau shurin masaki, bayan dogon nazari dukkansu suka amince da ya kawo shi amma Mama Hasiya ta nuna tunda Fatiman bata sani ba a sanar da ita.
Lokacin da aka sanar ita ba karamin mamaki ta yi ba, tabbas ta amince Muhammad yana kaunarta tunda ya yi takkakiya har mahaifarta sai dai wani abu mai girma yana yi mata nauyi a kirji tana jin anya ita amince ba ta yi wauta ba? Ya zata iya kulawa Muhammad da Mommahansa wadda ya ta alaka rabin rayuwar matar auransa a kanta a gefe kuma soyayyar Muhammad ita ce karfin kuzarinta ganin babu zaɓi yasa ta sallama ta nuna wa Mama Hasiya zahirin abin da take ji game da shi. Ita ma ta jinjina lamarin karshe ta ƴyi mata fatan alkhairi.
A washegari Muhammad ya iso Katsina tare da rakiyar abokinsa ɗan aminin mahaifinsa Abdush-shakur sun sami tarba mai kyau, kwanansu uku suna zaga dangi dake mahaifin Abdul ɗan asalin Katsina ne kowa ya yi murna da mijin da Fatima ta samu lallai jinkiri ya zame mata alkhairi amma da yawa na faɗin Fatima ta yi nisa da mahaifarta.
: Satinsa ɗaya a Katsina ya tattara ya dawo Sudan bai ɓoyewa mahaifinsa komai ba, ya ƴyi jim daga bisani ya nuna masa zai shawarci amininsa ya je ya bincika masa dangin Fatiman. Koda wasa Fatima bata nuna wa Muhammad tasan yaje kasarta ba haka ma Nu aimaht suka cigaba da shimfiɗa tsaftattaciyar soyayyarsu cike da kulawa da juna. Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji Fatima ta kammala karatunta, ta samu kyakkyawan sakammako sati biyu tsakani ta tattaro kayanta ta nufo gida mahaifarta cike da tsaraba mai tarin yawa daga gwarzon maza Muhammad cikinsu babu wanda bai koka ba da zasu rabu Nu aimah kuwa hada kwanciya asibiti.
Fatima ta dawo cikin danginta cike da walwala ga kwalin karatunta ga kuma miji rantsatse na nunawa sa a. Mama tamkar ta goyata don farin ciki su Mama Hajjara kuwa tamkar su haɗiyi zuciya su mace don hassada. Ta yi wani irin kyau fatarta ta gogge ta ƴyi fress ga wata irin nutsuwa da kamala tattare da ita ta zama cikakkiyar mace yar gayu gaba ɗaya shigarta ta koma ta mutan Sudan haka turarrukanta masu daɗi da sanyin kamshi ga kama kaya in ka ganta cikin lafaya saika rantse bakar basudaniya ce.
Hankalin Mama Hajjara ba karamin tashi ya yi ba ga Rahma kullum ciwo kara gaba yake abun babu kyan gani, ga kuma Murja ta kwaso mata cutar kanjamau duk ta lallace ta koma abin tausayi ranar da Fatima ta shiga gaisheta kasa ganeta ta yi sai da yi mata bayani karshe kuka tasa tana rokonta afuwar abin da ta yi mata. Fatima ta tausaya mata matuka a ranar ta haɗata da Dr Sakina mace mai karamci har gida ta rakasu ta karɓesu da faram-faram ta basu shawarwari masu inganci sun ji daɗi kwarai cikin sati biyu suka sauya kamar basu ba ba kamar Rahma da ciwonta ya sami kulawa ta kuma haɗasu da kungiyoyin dake kula da wannan sashi don taimaka musu.
Ai kuwa cikin wata guda Murja ta sami miji cikin masu irin lallurarta, Rahma kuma an mata aiki cikin nasara ta warke Fatima ta maida ita makaranta Mama Hajjara kuka take tana godewa Fatima da neman yafiyarta.
Watan Fatima huɗu da dawowa Muhammad ya matsa tilas ta amince ya turo magabatansa aka gabatar da komai aka saka bikinsu wata ɗaya kacal. Nu aimaht tafi kowa murna ita ma ta sami miji a can Na’im abokin karatunsu zata aura lokacin da Fatima ta ji ta dinga tsokanarta zata bar Sudan zuwa Saudi amma saita ƴyi mata albishir daya sami aiki a nan Sudan.
KOMAI NADA IYAKA
Ranar Asabar duban mutane suka shaida ɗaurin auran, Fatima Aminu Muhammad da ƙkuma Muhammad Nawaf bin Muhammad Nawas a sadaki kalilan lakadan ba ajalan ba. Uncle Sulaiman shi ya ɗaura auran, kwarai ya ji daɗin karar da suka yi masa haka ma Mama Hasiya. Satinsu biyu suka ɗunguma zuwa Sudan tare da rakiyar wasu cikin danginta Mama Hasiya da Aunty Maryam da kuma Sadiya, Muhammad ya dage sai an tafi da tagwaye duk da Mama taso hanawa amma ya dinga naci tilas ta hakura. Satinsu ɗaya a can domin sun hallaci bikin Nu aimah, dangin Fatima suka jiyo gida Nigeria cike da yaba irin mijin da Fatima ta samu amma kuma kash babu tagwaye ata bau Muhammad ya rike su a wajansa yace Mama ta tsufa ta huta kawai.
Lokacin da Mama ta sami labari ba karamin faɗa ta yi ba, ita ko Fatima daɗi taji sossai hakan ya kara mata kaunar Muhammad kwarai da gaske.
Zaman auranta zamane mai cike da kwanciyar hankali fahimtar juna da kyautattawa uwa uba mutunta juna Muhammad na tattalinta matuka haka itama tana kyautatta masa ga kulawa da take da mahaifiyarsa bata gazawa lallurarta bata damunta tausayinta yafi rinjayarta hata aiki daya samamata saida ya yi wuta-wuta sannan ta amince ta soma zuwa kiri-kiri ta nuna masa zata ajiye komai ta ƙƙlura da Mommahnsa. Ta fara aikinta cikin nasara Muhammad ya sa tagwaye makaranta mai tsada Hassanah na fanin kimiya ita kuma Hussaina art take yaran sungi girma sossai duk suna jss one.
Aikinta take cikin nasara Aunty Maryam ce ta bata shawara ta soma turo dogayan riguna ana sai da mata Ammar ta ɗora kan harkar shi da Saubahn da kuma Kamal yaron Mama Hasiya, cikin nasara kayan Allah yasa musu albarka nan da nan ake kwashewa. Duk lokacin da aka sai da kayan ta kan sa a raba ribar gida shida kaso ɗaya mahaifanta take ba kaso biyu kuma su Kamal ɗin su ɗauka kaso ɗaya kuma ayi hidimar karatun Rahma ɗiyar Mama Hajara da kuma Sadis data ya koma makaranta ya sami addimission a Kano F.C.E sai karshan wata yake zuwa gida. Kaso ɗaya kuma na Mama Hasiya ne da Aunty Maryam da Murja tana tausayin Murja ƙkwarai da gaske.
Babu wanda baya farin ciki da cigan Fatima domin mutum ce mai kyautattawa ga makusantanta. Mama kullum cikin sa mata albarka take haka mahaifinta.
Zuwa lokacin an sami sauye-sauye kala-kala masu kyau da akasinsu ciki hada rashin mahaifiyar Muhammad Nu aimahta ta haifi ɗiya mace taci sunan mahaifiyarta, Fatima kuwa tagwaye ta haifa Nawas da Nawaf. Sadis ya kammala karatunsa ya zama cikakken likita su Ammar kuma duk suna makaranta. Tagwaye ma sun gama secondary suna zuwa hutu gida jefi-jefi tuni Muhammad ya sama musu gurbin karatu. Cikin ikon Allah kuma Sadis ya nuna yana ra ayin auran Rahma babu jinkirtawa aka sha biki tare da sharaɗin Fatima ta ce zata cigaba da karatu. Rayuwarsu ta zamo abin sha awa Fatima ta zamo haske ga ahalinta kowa murna yake da ita. Mama kance lallai dana daka ta muguwar kawa da rayuwar Fatina ta gurɓace tabbas IDAN KA DAKA TA BADO RUWA ZAI JA KA. Saubah kuwa ɗiyar uncle Sulaiman ya ke so babu wanda baya faɗawa duk da karancin shekaruna takwas uncle kuwa ya ce bata da miji sai shi koda bayan ransa. Fatima ma ta yi AMMANA da hakan tana kaunar ahalin Mama Hasiya da dukkan zuciyarta zata iya sadaukar musu da komau nata sun taka muhimmiyar rawa a cigabanta ta tabbata ba komai ya kawo hakan ba YARDA CE SILA!.
Kwatankwacin kusancin Sanah da Auntynta.
Ummu Beenah Ce mu tara a wani in muna da rai da lafiyar rubutawa da kuma lokaci.
Fatan alkhairi ga ɗaukacin masu bibbiyata tun daga farko zuwa karshe ubangiji yasa mu amfana da abunda muka ji muka karanta. Mu da muke rubutawar ubangiji kasa mu kyautatta niyya yayin aikin ubangiji ya fida riya a zukatanmu, fatan nasara ga ɗaukacin marubuta online da publish.
Har gobe ina godiya ga,
Ado Ahmad Gidan Dabino MON.
Aishat Chuchu
Dr Sakeenah ɗiyar Mommahter Maijidda.
Mommah Maijiddah
Bingele Mita.
Dr Ummu Sabreenah
*SADAUKARWA*
Tagwayan Mommah Maijiddah Musa Muhammad Maiduguri. Tare da duk wata mace data tsinci rayuwarta a KADDARAR RAYUWA irin ta RAYUWAR FATIMA wato JINKIRIN AURE.
Tammatbihamdullah
Taku a kullum, Has/sanah Sulaiman Isma il Matazu (UMMU BEENAH)