KUDA WURIN KWADAYI🐝 CHAPTER 2 BY FATEEYZAH MBS

KUDA WURIN KWADAYI🐝 CHAPTER 2 BY FATEEYZAH MBS

Www.bankinhausanovels.com.ng 

*ALHERI WRITERS ASSO.* 

          *A.W.A* 

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

https://chat.whatsapp.com/JcwN25cbC4PB0DUkvu7TtY

 *KUDA WURIN KWADAYI🐝*

 *_Na Fateeyzah mbs✍️_*

 _*Marubuciyar*_👇

 *_Gidan nagoggo_* 

 *_Doctor zahrah_*

 _Tukwucine ga ‘yar mallawa(haseena bammali), marubuciyar jarababban namiji🥰_

 *_Bismillahir rahamanir rahim_* 

 *__________________________*

*Page 2*

   Ganin ya nufo ta ya sa ta kuma shiga wani rudani, tare da zazzaro ido, tana cije baki, wanda a dai² wannan lokacin kuma kunnanta ya jiyo mata kwankwasa kofar da ake yi, wanda hakan ya kuma daburtata.

Jin kwankwasa kofar ya sashi maida idonsa wurin kofar, sabanin daa da hankalinshi da idanunsa, suke kan fuskarta, wanda fuskarshi ke dauke da mamaki da kuma al’a jabin ganinta a cikin gidansa, ganin yanda hankalinsa ya koma kan kofar wanda kuma hakan bai hana sa nufo taba wanda har yazo gab da ita, yasa ta yi saurin daukan  iron(dutsen guga) da ta gani gefenta tare da dagosa sama,sannan cikin zakakkiyar muryarta  mai daukan tunani tace ”  kada ka matso kusa dani, don zan kwala ma ka”.

Sai dai barazanarta bata sa ya dakata ba, sai ma kara matsota da yayi, hakan ya sa ta kuma shiga cikin rudu, tare da wani tsoro da ya darsu a zuciyarta, wanda har ya nuna a fuskarta, wanda kuma ta dayan bangaren ana kuma kwankwaso kofar tare da ambatar “Malam! ,Malam!, Assalamu Alaikum Malam”.

Sai dai duk da alamun hankalinsa na kan kofar, amma kuma idonsa na kanta, wanda ko kiftawa ba yayi, a dai² lokacin ya iso  tare da zuba mata idanu, wanda hakan ya sa ta karasa rikicewa, bakinta na rawa, gaba daya ta nemi natsuwarta ta rasa, daga hannunsa yayi tare da mata nuni zuwa kasa, ganin hakan yasa ta maida idonta kasa, tare da tunanin mai yake nufi, ko da ta kalli kasan bata lura da komai ba, hakan yasa ta kuma  dawo da idonta garesa tana jujjuya masa hannu, domin bakinta ma ya kasa furta wata kalma, duk yadda taso tayi magana amma hakan ya gagara saboda rudin da take ciki.

Dai² lokacin ta tsinci maganarshi, kamar mai rada” ki cire takalminki nace, kina taka min dadduma”, da sauri ta cire takalmin tare da wulli dashi zuwa bakin kofa, hakan yasa shi kuma ya nufi kofar da ake  bubbugawa har lokacin.

Ganin hakan ya sata waro ido cike da tsoro, yayin da bakinta yake kakkarwa.

 ……………………………………..

      Horn yake  yi da karfi, a jikin makeken gidan nasa, wanda kallo daya zaka masa kasan an kashe dukiya, yayin da baba mai gadi ya fito daki da gudu, yana kokarin bude gate,  don ya san ba kowa bane sai mak gidan, don shine yake irin wannan horn din especially idan yayi dare sosai, duk da yanxu tara ta buga, amma a wurinsa yayi latti sosai, saboda kasancewa  karfe shidda yake dawowa, in kuwa ya wuce shiddan nan a waje, haka zai yi ta kwarara horn idan ya dawo, duk wannan tunanin baba mai gadi ne yake yinsa yayin da yake bude gate din.

Da² lokacin ya shigo gidan a guje tare da samun wuri yayi parking, ko sauraren baba mai gadi da yake masa sannu da zuwa bai yi ba, saboda tunaninsa gaba daya yana ga gimbiyarsa, farin cikin rayuwarsa haka kuma wani sashin zuciyarsa, wadda farin cikinta ke sashi a cikin walwala, kallonta kawai idan yayi yana saka sa nishadi, wanda a kullun sai yayi ma Allah godiya da ya cika masa burinsa ya basa sarah a matsayin mata kuma uwar ‘ya’yansa masu zuwa nan gaba, da wannan tunanin ya karasa wurin main door din tare da saka hannunsa ya bude kofar, sannan ya kutsa kai tare da cewa “Assalamu Alaikum mai kyau, gimbiyar sa’eed”.

Tana zaune ta hakimce akan 2seater, daya daga cikin royal chairs din dake dakin colour din navy blue and golden, kyakkyawace ta karshe, domin kallo daya zaka mata, kasan Allah yayi ruwan kyau anan, hasalima sai ka dauka balarabiyace, irin matan nan ne da ko a cikin larabawa samun mai kyanta sai an tona, wani dakakken lace ne a jikinta, wanda kudinsa ya isa mai karamin karfi jari, yayin da ta kashe dauri wanda yayi dai² da fuskarta, gashinta ya fito ta kasan dankwallin, yayin da gashin ke kwance a gadon bayanta, wanda tsayinshi ya kai kwankwansanta, kallon agogo tayi tare da juyawa ta sakin masa wani kallo, irin kallon nan da ke nuni da sai yanxu, cikin sauri ya karasa gareta, tare da ajiye mukullun motarsa a saman center table din dake tsakiyar parlourn, durkusawa yayi kan gwiwoyinsa tare da daura tafin hannunsa akan cinyarta, sannan ya bude baki cikin husky voice dinsa tare da lumshe ido yace” tuba nake sarauniyar mata, kaina bisa wuyana, wallahi  biyawa nayi wurin su hajiya, kuma a hanya go slow ya tsayar dani, ami afuwa gani nan na dawo” ya karashe magana yana mai karya wuya kamar karamin yaro.

Cikin yauki hade da shagwabe fuska tace” shine ka barni ni daya, ina ta jin tsoro, kuma ai da sai ka kirani  a waya ka sanar dani, kuma ni ina ta kiran wayarka baka dauka ba”. Ta fadi haka cikin zazzakar muryarta  mai hade da shagwaba.

Jin abunda tace ya sashi lalubar wayarsa dake aljihu tare da cewa”wallahi shap na manta da wayar, da yake yau tun da muka gama waya dake, na saka wayar a DO NOT DISTURB, saboda jin muryarki kawai ya kara min wani karfin gwiwar yin aiki, shi yasa banso a dameni, amma don Allah kiyi hakuri gimbiya ki yafe min, wallahi kina nan cikin zuciya ta, shi yasa nake ta sauri inzo inga lafiyar ki”.

“Ok, shikenan my king, amma kuma yunwa nake ji”ta karashe maganar tare da rausayar da kai tana sakin  hamma.

Saurin rufe mata baki yayi da tafin hannunsa, sannan yace”  sorry gimbiyata, nasan kin tsaya jirana ne, taso muje dinning in baki”ya karashe zancen yana mai shafa shafaffan cikinta.

Turo baki tayi cikin shagwaba tare da cewa” My king ka manta yau Monday ne bana girki, sai weekend”.

Zaro ido yayi tare da cewa”Haba baby na dauka ai mun gama amarcin, shi yasa yau na turo miki da cefane”.

Make kafada tayi tare da cewa” ni dai a’ah, gaskiya bazan ringa girki ba sai weekend, tunda ranar ne ni da kai muke gida, kaga kuma monday to Friday kana office ni kuma ina school”.

Hade rai yayi tare da zame hannunsa a cinyarta, ya mike yana kokarin barin gabanta, yayin da ita kuma ganin haka yasa ta fara matsen kwalla tare da  diddire kafa kamar wata karamar yarinya.

Saurin juyowa yayi hade da cewa…………

 _Tofa, yau ga shagwababbiya._ 🤔

 _Ya gimbiya sarah zasu kaya da her kings_…

 _Wacece jarumarmu ta farko_

 *KUDA WURIN KWADAYI, WAYE/WACECE*?

 *COMMENT*

 *SHARE*

 *LIKE*

 *_Fateeyzah Mbs✍️_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *