Tana bayansa har suka qarasa inda yaya yahanasu taje zaune tana kallon ikon Allah,a mutunce sumayyan tace
“Yaya ina kwana?”
“Lafiya” ta amsa babu yabo ba fallasa,tana son ganin kyawun kyautatawar data mata idan da hali ta mata godiya amma sai ta kasa,dama sumayyan ba domin ita tayi ba,tayi ne domin girman Allah da kuma girman da zumunci ke da shi a wajen ubangiji,hakanan ko ita ba zata so ace yau yaya abbakar ya auri wata da zata rabashi da su ba,ko ita ta haifa ya auri wadda zata rabasu din,kitchen ta wuce ta soma hadawa kanta dan abinda zata iya ci,ko kafin ta kammala ta fito ma falon babu kowa da alama ta tafi,sai ta zauna ta fara kurbar ruwan shayinta.
Kamar daga sama zainab din ta fito tana banbamin masifa kamar zata ci baki mukhtar na biye da ita yana son shan gabanta amma ya gaza cimmata,qerere tayi a kan sumayya wadda ko mutuncin kallonta bata samu ba
“Uban wa ya saki ki tabamin turaren wuta na?” Sosai abun ya bata mamaki,har tana iya bude baki tayi cigiyar kayan data tabbatar ba na Allah bane?,qare matsota tayi tana huci ta kuma maimaita tambayar tata,ganin zainab din na qoqarin kai hannunta jikinta ya sanya sumayyan dubanta
“Kada ki soma,don fankan fankan bata kilishi wallahi kika dakeni bazan dubi girmanki ba tsaf zan rama” idanu ta zaro tana nuna qirjinta
“Ni zaki daka don ubanki,to dokeni din”
“Wai meye haka ne zainab ba tun cikin daki nake miki magana ba?,ke sumayya tashi ki koma dakinki” wani kallo ta watsa masa sannan ta dakata da shan tea dinta
“Kayi haquri amma bata isa ba wlh don yanzu na fito ban kuma kammala uziri na ba,kana iya janye matarka idan na gama na tafi ita ta fito” ta fada tana ci gaba da kurbar shayinta duk da wata iriyar tafasa da zuciyarta ke mata,jinta take dai~dai sa su baki dayansu,banda daraja da girman sa da take gani babu abinda zai hana ta yayyaba masa baqaqen maganganu masu zafi
“Muje nace zan biyaki kudin ko?” Sai ta sauke ajiyar zuciya,dama abinda yafi damunta kenan,don sake samun wani maganin wannan da sauqi
“Allah ya ceceki” ta fada tana huci sannan ta juya tabi mukhtar din,cak shayin ya tsaya mata a wuya,ambaton sunan Allah ta dinga yi don ya kawo mata dauki,tabbas sai yau ta tabbatar mukhtar dinta ba cikin hayyacinsa yake ba,kayan karin da bata gama ci ba kenan.
**** **** *****
Wani nannauyan bacci ne ya dauketa tun bayan kammala sallar asuba,hakan ya sanya bata tashi ba sai wajen sha daya saura na rana saboda zafin rana da ya fara hudo labule.
Da wata mahaukaciyar yunwa ta farka,saboda haka bandaki kawai ta shiga ta wanko bakinta ta shiga kitchen don samarwa kanta abinda zata ci,don bata sa aka ba tasan ba samun abun kari zata yi ba,haka ne yake faruwa duk ranar girkin zainab din,shi kansa mai gidan wani lokaci sai dai ya fita haka.
Sam bata lura da meke faruwa ba sai data shiga cikin kitchen din sosai,nafi’u ne yaron zainab tsaye dare dare kan stool yana sauke dukkan farantanta na tangaran dake jere cikin glass drower dinta yana sakinsu qasa daya bayab daya suna tarwatsewa.
Da sauri ta qarasa ciki tana kiran sunansa cikin tsawa,ko gezau baiyi ba bare ya fasa aikata abinda yakeyi din,hannunshi ta riqe gam kana ta saukeshi daga kan stool din tana dubansa ransa a bace
“Baka da hankali?,ko bakasan me kake yi ba?,ko bakasan abin amfani kake lalatawa ba?”,cikin rashin kunya yace mata
“na sani mana”abun sai ya bata haushi ta kama kunnansa ba tare da ta murde ba tace
” wato tsabar rashin ji ne kenan ko?”
“Sakarmin kunnena ai kema bake kika siya ba,kuma Allah ya isa na da tabamin kunne da kikayi” sosai yaron ya bata haushi da mamaki,ta sanya tafin hannunta ta buge masa baki,wata qara ya saki kamar wanda aka sanya wuqa aka yanke masa maqogaro yana fadin “wayyo bakina wayyo mama ta fasamin baki”.
A hautsine ta fado kitchen din dama tasan hakan na iya faruwa,don ita ta sanyashi,saboda har yau bata huce takaicin asarara maganinta da sumayyan ta jawo mata ba,duk da mukhtar din sai da ya biya ninkin kudinsa,da sauri ta qarasa inda suke tsaye ta ture sumayya tana fadin
“me kika yi masa?,me tayi maka nafs(da yake haka take kiransa)”
“Bakina ta dakarmin mama duba ki gani”hannunsa ta sauke tana duba bakin,babu wani abu da yayi tunda duka duka dukan data masa ba wani mai zafi bane,waiwayawa tayi ta dubi sumayya dake tsaye rungume da hannu tana dubansu
” dukarmin yaro kikayi saboda bakisan ciwon haihuwa ba ko?,to wallahi sai na rama masa”sai kuwa tayo kan sumayyan gadan gadan.
Ko alama bata motsa ba har ta qaraso inda take,ta daga hannu da niyyar zuba mata mari caraf ta kama hannun nata ta yarfar da shi gefe,sannan cikin bacin rai tace mata
“Bansan ke din wace iriyar uwa bace,ban kuma san irin tarbiyyar da kika bama yaronki ba,amma bari na gaya miki,matuqar irin wannan tarbiyyar ita kika bashi to ba shakka kin cuci kanki,abu na gaba duk iya zaluncin da zaki aikata cikin gidan nan kiyi,Allah na sane da ke,amma kada ki soma gigin daukar hannu kice zaki dake ni,don baki haifeni ba,ba kuma kisan ciwo na ba kamar yadda kika ce bansan ciwon haihuwa ba,kuma kema ba Allah kika yiwa fadanci ba ya baki,ganin……..”.ihun da zainab din ta qwalla gami da dora hannu bisa ka ya dakatar da ita daga maganar da takeyi,sai tayi sororo tana dubanta tare da tunanin ko zainab din nada ciwon hauka ne dake tashi lokaci bayan lokaci?.
Sam bata fahimci tarko bane ta dana mata sai data ga shigowar mukhtar cikin kitchen din a rude,ashe tuni taga giftawar inuwarsa ita zainab din,binsa tayi da kallo sanda ya nufi zainab,ta manta kwana nawa rabon da ta sanyashi cikin idanunta,ranar qarshe kawai zata iya tunawa da bata kuma ganinsa ba sai yau,itace randa ya rufeta da fada tamkar zaya daketa,sabida tayi dan wake abincin dare,ita kuma zainab tace sam bazata ci ba ai dan wake ba abinci bane,ya umarceta ta shiga kitchen ta yiwa zainab din shinkafa da miya qarfe goma na dare,umarnin ya yi mata tsauri saboda haka bata ko tanka ba ta wuce dakinta tayi kwanciyarta bayan ta kulle qofarta,don tana da yaqinin zaya iya biyota,ilai kuwa ya biyo sahun nata,yayi bugun duniya taqi ta bude masa,hakan ya sake harzuqa shi,haka ya koma tare da ci mata alwashin sai ya sabar mata,to tun daga ranar rabon data karbi girki ma cikin gidan,saidai idan sun kammala a barshi a kitchen,idan tana da sha’awarci ta diba,idan bata ga dama ba ma ko kallo bai isheta ba.
“Wato ke kin zama ‘yar iska mara mutunci ko?” Ya fada yana nufota cikin huci bayan zainab ta gama tsara masa qarya kan abinda ya faru,hannu tasa ta toshe bakinta saboda yadda taji kanta ya mata dummm,kalmar ta yiwa qwaqwalwarta tsauri haka nan ta yiwa kanta nauyi,ita mukhtar ke kira da ‘yar iska?,kalmar da babu wani mahaluqi da ya taba jifarta da ita?,da sauri ta juya ta fita daga kitchen din cikin sassarfa saboda kukan dake shirin qwace mata ba wai don mukhtar din dake nufota ba.