KUNDIN KADDARATA CHAPTER 33 BY HUGUMA

Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.

Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya karba ya fice.

Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa share share.

Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.

Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.

Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
“Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa” ya fada yana gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.

A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d’anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan
“Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake”
“Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki ko” maman ta fadi
“Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi” tausayinta ya kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
“Kin gani ai,sai kije ku gaisa” ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.

Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace
“Ina yini” ba tare data daga kai ta dubeshi ba
“Lafiya lau,ya jikin naki”
“Alhamdulillah” ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta
“Ga guri zauna” bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
“Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba”ya furta wani daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.

Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata abinda zaya fadi ba yace
” idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan dawo na karba in sha Allah”
“Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya” ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi.

Babu kowa cikin tsakar gidan nasu kai tsaye ta fada dakin tana jan numfashinta tana jin zuciyarta na mata nauyi,qwalle ke layi kan kuncinta daya na bin daya,a addafe ta nemi gefan katifa ta zauna tana jujjuya kanta cikin zuciyarta tana addu’a wadda bata tantance mai take roqa ba,abu daya zuwa biyu zata iya tantancewa shine haushi da tsanar mukhtar dake mata yawo cikin zuciya,sai kuma zainab wadda take jin ba zata iya yafewa karan tsayen da ta tiwa rayuwarsu ba musamman ita din,wanda gangar jikinta da zuciyarta bata saba da kowa ba sai mukhtar din tun zamanin quruciya zuwa girma.

Ta dauki a qalla mintuna talatin a haka kafin sautin qarar wayarta dake yashe gefe ta katse mata yanayin da take ciki,sunan anty dije ke yawo bisa screen din,tamkar an kwance qullin dake zuciyarta taji zuciyar ta karye hawaye ya sake balle mata tun kafin ta kai ga daga wayar.

Muryarta kawai anty dije taji jikinta ya bata akwai damuwa,fada ta shiga yi tun kafin taji matsalarta akan kan mene ne za’a dinga bata ranta,ta gaya mata me aka mata waye ya bata mata,ganin ta gaza bata amsa yasa ta katse kiran ta nemi layin maman,tana daga daki ta juyo muryar maman da alamu anty dijen ta sameta,jikinta ta komar ta jinginar a bango ta lumshe idanunta tana matse hawaye.

Batasan ya sukayi da mama ba daga bisani ta kirata ta gaya mata idan har taga ba zata iya ba tayi tahowarta abuja gurinta ta zauna ta haihu a nan,godiya ta mata tare da ce mata to ba don tana jin tafiya can din ba,maida kanta tayi ta kwanta sosai saman katifar tana maida ajiyar zuciya

****     ****    ****   ****

La’asar ce sosai misalin qarfe biyar na yammacin,tana zaune saman kujera ‘yar tsuguno tana tsinke danyan zogale,halima na bakin kurfeti wanda take kwashe tuwon dare,mama na saman tabarma daga gefen sumayya tana daka gyada da daddawa,sai zainab wadda ke wankin kayan sumayyan wanda basu wuce kala hudu ba,hira suke irin wadda ta shafesu,sosai hirar kewa sumayya dadi don har qyaqyata dariya take.

Sallamar yaro ce ta katse musu hirar wanda ya sanar musu mukhtar na gaidasu,mama ce ta fadawa yaron yace ya shigo wanda hakan ya sanya sumayya sakin zogalen hannunta ta dafa qasa tare da yunqurawa ta miqe,bat fara’ar dake fuskarta ta bace,a hankali ta juya ta shige dakin yayin da maman ta bita da kallo lokacin da take qoqarin zura hijab a jikinta.

Yara ne suka fara shigo da kaya,akwatu ne har seti uku matsakaita masu kalar ruwan hoda da ruwan toka(ash and pink)masu azabar kyau,sai da suka ajjiyewa suka fice sannan mukhtar din ya shigo.

Sanye yake da shadda ruwan madara(milk)dinkin tazarce wadda tayi masifar masa kyau,sosai ta dace da shi duk da irin ramar da yayi,kamar ko yaushe ya gaisa da maman cikin kunya da nutsuwa kafin shiru ya biyo baya na ‘yan daqiqu sannan yace
“Kaya ne mama gasu nan,idan akwai abinda babu ciki sai a sanarmin don Allah mama” addu’ar fatan alkhairi tayi sannan daga bisani ya miqe bayan ya ajjiye wasu kudi gaban maman ya fice yana kiran halima.

Kusan duk cikin kunnenta komai ya faru,idanunta na a rufe har ya fice daga gidan,wani gudu gudu zuciyarta ke mata tare da wani zafi,duk sanda ta tunashi kota jishi ko ta ganshi wani miki ke motsawa cikin zuciyarta,har yanzu cikin jin haushinsa da zarginsa babu abinda ya ragu cikin zuciyarta,a ko yaushe zuciyarta na gaya mata tunda mukhtar ya zargeta aduniya waye zai gasgata ta?,waye zai yarda da gaskiyarta,a haka ta zame ta kwanta ko zata samu sauqin zugin da zuciyarta ke mata.

Bayan sallar isha’i mama ta nunawa mallam akwatunan,bai buda ba yayi addu’a dai kawai,cikin sauri halima da zainab da suka qagu suga meye a ciki suka matso gaban akwatim suka soma budewa,sumayya na daga saman kujera wadda tunda ta yiwa malam sannu da zuwa bata sake cewa komai ba,sanye take da hijabi hannunta riqe da qaramin alqur’ani tana karantawa qasa qasa,sam idanunta bai kansu karatunta kawai take kamar batasan meke faruwa ba.

Ba qaramin tafiya da su halima kayan sukayi ba,kallo daya zaka musu ka tabbatar mukhtar yayi rawar gani,kaya ne masu dan uban kyau da tsada unisex,takalma huluna,riguna fidoji,tarkace dai kala kala wami abun ma basu san sunanshi ba,akwati biyun duka na jarirai ne,yayin da ta qarshen atamfofi ne super biyu,lace daya shadda daya,sai materials masu kyau guda biyu jaka takalmi da mayafi sai sarqa da awarwaro,kana kallonsu kasan na uwar yaro ne na fitar suna
“Masha Allah,wannan yaro ko yarinya anyi dan gata,don Allah anty sumayya dago ki gani” zainab ta kasa shiru ta fadi haka. A hankali ta daga idanunta ta watsawq zainab din wanda ya sata dawowa hayyacinta,sai tayi shiru ta sadda kai yayin da sumayyan taci gaba da karatunta ba tare data sake tofawa ko dubansu ba.

Qememe taqi yarda a ajjiye kayan a dakinta kusa da ita,tun yaya abubakar na tsokanarta suna dauka wasa ne har suka gane bil haqqi da gaske take,don kuka ta fashe musu da shi,tilas ya abubakar ya karbi kayan ya musu ma’ajiya a dakinsa.

****   ****   ****   ****

Tunda ta idar da sallar isha’i ta kwanta bayan taci tuwon dare,wani mugun ci tayi masa har halima na mata dariya tana tsokanarta duk da yadda take jinta a takure saboda yadda baya da mararta ke ciwo kadan kadan. Bacci taso ya dauketa saidai yaqi zuwa juyi take lokaci bayan lokaci saboda yadda kwanciyar taqi mata dadi duk da cewa idan da sabo ta saba tunda cikinta ya fara nauyi,a haka har su halima suka gama bidirinsu suka shigo suka kwanta bacci ya kwasheta idanunta biyu.

Sannu a hankali taji ciwon yana ci gaba da qaruwar mata daga mararta zuwa baya,sai ta miqe a hankali jin motsin mama da tayi a tsakar gida tana rufe kitchen da alama bata kwanta ba,tana qoqarin shiga daki sumayyan ta kira sunanta,waiwayowa tayi cikin mamaki ta amsa don a tunaninta ta jima da yin bacci tunda ta riga kowa kwanciya.
“Mama marata da baya ne kemin wani irin ciwo,gashi na kasa bacci” idanu ra zuba mata tana nazarinta sannan tace
“Tun yaushe ne?”
“Tun dazu” ta fada tana cije lebe saboda yadda aka mintsineta,kai ta gyada sannan ta juya ta bude dakinta maimakom dakin malam da take niyyar shiga tace da ita
“Shiga ki kwanta anan ina zuwa” ta fadi tana sake juyawa zuwa dakin malam din.

Koda maman ta dawo bakin gado ta sameta zaune saboda kwanciyar ta gagareta,ji take kamar ana tsaga mararta ana karya gadon bayanta,tuni gumi ya fara yi mata sallama,yarfa hannu take tana kiran sunnayan Allah tare da mirgina kai hagu da dama,kofin hannunta maman ta miqa mata cike da tausayi tace ta shanye,kallo daya tayi mata ta tabbatar naquda take,daga kai tayi ta shanye baki daya sannan ta dire kofin a wahalce,cikin mintina qananu ciwon ya sake yin gaba.

Awa daya ta wuce shiru biyu shiru hakan ya sanya mama ta sake komawa gun malam ta kuma karbo mata wani rubutun ta sake shanyewa,tun tana daurewa har hawaye suka qwace mata ba tare data shirya ba,ba shakka zamantowa uwa ba qaramin abu bane haka ta dinga rayawa cikin zuciyarta.

Qarfe biyar saura na asubahin ranar talatar ya zamanto mata ranar tarihi a gurinta,dai dai lokacin da yaron cikinta ya shaqi iskar duniya,kukansa ya karade ilahirin gidan wanda ya sanyawa ilahirin wanda ke gidan yana bacci farkawa,malam kuma dake zaune dungurgur yayi hamdala ga ubangiji yana qarawa.

Ware idanunta tayi sosai sanda iskar sanyin asuba ke busata,tana son tabbatarwa kanta da gaske ne abinda ke cikinta ne ya iso duniya yake cala kuka haka?,da gaske ne a yau itama ta zama uwa?,ta shiga sahun iyaye?,da gaske yau itama zata riqe ta kalla ta kuma raini danta na cikinta?,ta fita daga sahun juya?,wannan kalma ta zama tarihi cikin rayuwarta?,a yau ta haifawa mukhtar da wanda yake buri gareta buri gareshi,sai dai kash,ba zaya samu irin tanadin da suka yiwa rainon da zasu bashi ba,wata qaqqarfar QADDARA ta shigo ta farraqa kasancewarsu tare,a yau zasu raineshi ne a mabanbantan gurare,sai ta saki kuka a fili wanda cikin zuciyarta tana tasbihi ne ga ubangiji,cikin mamaki mama ke dubanta
“Lafiya ko wani guri ke miki ciwo kuma?” Ta tambaya sanda take tsaka da qoqarin dauke yaron da gyara gurin,kai ta girgiza tana ci gaba da kuka,tuni maman ta gano kukan me take saboda haka taci gaba da aikinta tana cewa
“Godiya ya kamata ki yiwa ubangiji ai”.

Kafin gari ya waye tuni komai yayi tsaf daga uwar har dan har gurin da akayi naqudar,maman ce ta shigo da yaron dake nannade cikin shawul ruwan sararin samaniya bayan sunqufe shi da akayi cikin lallausan kayan sanyi suma ruwan bula din,malam ta kaiwa shi bayan ya dawo sallar asubahi ya ganshi,ya sha addu’a kuwa bayan wasu sirrika da ya hada ya dangwala masa a baki,sumayyan na gefan gadon mamam riqe da kofin shayi mai kauri da maman ta hada mata kan ta fita da yaron,har yanzu ta gaza shanyeshi saboda bacci dake dibarta
” karbeshi ki ganshi sumayya ki masa addu’a”maman ta fada tana dora mata shi saman cinyarta bayan ta karbo kofin shayin data samu ta shanye.

A hankali kamar mai tsoron tabashi ta sanya hannu ta tallabeshi,take idanunta suka cika taf da qwalla,a sanyaye ta sanya hannu ta yaye rufin fuskarsa idanunta suka sauka kan fuskar tasa wadda idanunsa ke rufe ruf yana ta sheqar bacci cikin lumana da kwanciyar hankali,kallo daya tayi masa ta hango kamanni na kai tsaye da yaje da babansa duk da ba idanunsa biyu ba,a kallon farko taji wata iriyar qauna da soyayyar yaron ta mamayeta,irin qauna ta da da mahaifi,tausayinta kuma ya samu gurbi cikin zuciyarta karon farko data tuna irin siradin da rayuwarsa ta tsallake kafin ya kai ga isowa zuwa ga wannan fili da muke kira da duniya,sai gashi Allah ya nuna ikonsa,yaro qato kyakkyawa mai cike da qoshin lafiya,wanda ko cikin mafarkinta bata taba tunanin zata haifi kamarsa ba
“Bawan Allah” ta furta ba tare da tasan a fili ta ambaci hakan ba qwalla na kwaranyo mata,daga shi tayi zuwa fuskarta ta karkata kunnensa na dama ta karanta masa kiran sallah ta karkata na hagu ta karanta masa iqama sannan ta ambata masa sunansa *ABDALLAH* bawan Allah.

Murmushi mama tayi ta dubeta
“Amma kya jira babansa yazo ya zaba masa suna ko?” Kai ta girgiza
“Kiyi haquri mama,ni yafi kamata mama na sa masa suna,ni kadai nasan wahalar da nasha,daga ni sai ubangiji na ma…….” Sai ta kasa qarasawa saboda karyewa da zuciyarta tayi
“Kukan ya isa haka,yau ranar murna ce,ajjiyeshi kusa da ke,maza so nake ki kwanta kiyi bacci sosai” bata musa ba din tayi yadda maman tace,tun tunaninnika na bijiro mata har wani nannauyan bacci mai dadi yayi gaba da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *