KUNDIN KADDARATA CHAPTER 46 BY HUGUMA

  Tana shirin kwanciya wayarta ta dauki ruri,mukhtar ne sai ta kumahe idanu tana murmushi

“Na kasa bacci my sumy,ganinki nake kusa da ni”.’yar qaramar dariya ya tasa tana fadin
” baban zumudi ka zama ya mukhtar ne?”shiru ya danyi sannan ya saki ajiyar zuciya
“Bakisan me nake ji ba game da ke sumayya”. Hira suka kashe lokaci suna yi,a nan yake gaya mata ran rakota tare da yaya yahanasu za’a zo,har mamaki take idan taji yadda yaya yahasun ta sauya take nuna mata qauna,basu suka rabu ba sai daya na dare,ta dubi agogo tana zaro ido ganin lokacin da suka shafe tare,sai ta fita ta daura alwala tayi sallah raka’a biyu sannan ta kwanta.

** *

 Shirye shiryen tariya sun kankama sosai,tayi gyaran jiki hadi da qunshi da kitso,kayanta baki daya ta kammalesu.


  Ranar alhamis ana ya gobe zata koma,da azahar suna falo ita da halima da zainab suna hira ita kuma tana gugar ragowar kayan abdallah da bata gama shiryawa ba,sai anty salma qanwar mama wadda anam zata kwana,wayarta dake daki ta soma burari,abdallah ne ya miqe da gudunsa ya dauko ya miqa mata,anty salma ta talle masa qeya tana cewa

” kaji dan jakar uba wai yasan kayan uwarsa,sai kace wani yace zai dauki wayar ne”dariya sukayi dukansu halima tace
“Indai Abdallah ne kadan kika gani anty” ita kuwa sumayya miqewa tayi ganin lambar mukhtar ce ta fita ta koma dakinta
“Lafiya abban abdallah naji muryarka can qasa?”murmushi ya saki sannan yace
” lafiya qalau,a yanzu ma ina gida kwance ina hutawa,babu abinda nayi amma wata gajiya nakeji sosai a jikina,kewarki nake sumayya goben nan kamar ba zata zo ba”tamkar yasan abinda take ji jikinta itama kenam,sai ta saki ajiyar zuciya tana masa murmushi
“Au dariya ma kike min?,naji na gode,amma da zaki taimaka min da kinzo na ganki kinji my sumy” sai ta kasa musa masa,dama suna da agender fita karbo dinkunan sumayya gidan wata mata bayan sallar la’asar ita da anty salma
“Babu damuwa ya mukhtar,amma sai bayan la’asar”cikin zumudi yace
“Da gaske sumayya ta?,kada fa ki shirgani”dariya ta qyalqyale masa da ita
” da gaske nake mana abban abdallah,ka jirayeni,amma fa gobe ba za’a rakoni da wuri ba tunda yau ka sake gani na”
“Babu komai,ai goben ta Allah ce,Allah yayi miki albarka sumayya ta” tana jin dadi ya sanya mata albarka don haka da sauri ta amsa da amin.

   A gidan mai dinki ta bar anty salma tace zata je ta dawo,ta riga da tasan inda zata din saboda haka tayi tayi abdallah ya zauna qememe yaqi har da kukansa ammi zai bi tace madallah yayi ta binta din sai sun dawo.


  A qofar gidan mai adaidaita sahu ya sauketa,ji tayi ana malam ga kudinka,tana waiwayowa sai taga mukhtar ne,cikin mamaki take tambayarsa

“Ya akayi kasan na qaraso”
“Jikina ne ya bani” ya bata amsa yana amsar abdallah daga hannunta yana masa cakulkuli suna qyalqyala dariya tana biye da su har zuwa falon gidan,kallon gidan take ya sauya komai kamar wanda zai kawo budurwa,komai fes gwanin sha’awa,zubewa sukayi kan kujera mukhtar na biyewa abdallah suna ta wasanninsu yayin da sumayyan ke zaune gefe guda
“Wai nikam ‘yar kallo kuka maidani ne,nazo amma ba’a tani,bayan nemana akayi” ta fada tana murguda baki,dariya mukhtar din ya saki yana duban abdallah.”lah,abdallah kaga mamanka na kishi da kai”sai ya kada kai kawai yaron don bai fahimci me yace ba,juyawa yayi gunta
“Dama taimaka mana kika yi kika dafa mana wani abun madam”
“Kamar me?” Ta tambayeshi
“Abinci mai sauqi da dadi”
“An gama” ta fada tana miqewa
“Ammm,madam,amma da kin taimaka kin cire wannan hijabin tunda gaban mijinki kike ko?” Dariya ma ya bata yadda yayi maganar a dake,bata ce komai ba ta cire din,sai ta miqawa abdallah hannu
“Muje kayi fitsari sai ka dawo ko?” Lafewa yayi jikin mukhtar din qememe yaqi yarda da ita
“Barmin yaro na ana dole ne,yayi fitsarinsa babu komai cinyar babanshi ce”.don haka ta juya zuwa kitchen ta barsu nan.

  Tana tsaka da girkin mukhtar ya shigo goye da abdallah,saura qiris ta dona hannunta cikin gas garin dariya

” ka ganka kuwa da goyon nan,don Allah tsaya na maka hoto”shi din ma dariya yake,
“To ya zanyi,yaqi yarda na kwantar da shi kwata kwata”hoto ta musu wajen kala biyar ta nuna masa suka dinga sheqa dariya,tex din da ya shigo wayarta ya katseta,anty salma ce ke gaya mata ta wuce gida uta kam sai ta taho,tana niyyar kiranta tace ta jirata tana tahowa mukhtar ya riqe hannunta
” qyaletq ni da kaina zan maidaki”.qarshe tare suka gama girkin wajen sallar magariba sannan ta karbi abdallah da qyar zata kwantar,sai ya farka ya riqe mukhtar gam gam yana sakin kuka,tilas yace ta qyaleshi suka dauro alwala sukayi jam’in sallar magariba tare sannan ta gabatar masa da abincin.

  Tare suke ci baki dayansu,saidai duk daga kan da zatayi idanuwansa na kanta,saidai ya sakar mata murmushi ta maida masa martani,sake hada idanuwa sukayi karo na barkatai,sai ya kauda kallonsa ya maida kan abdallah

“Na godewa Allah da ya sake gwadamin wannan lokaci cikin rayuwata,lokacin da zan zauna ni da matata abar sona da kuma diyan cikina,ina fata Allah ya rayamin kai” ya fada yana shafa kan abdallah,sai yaron ya dago kai yana kallonsa kamar yasan ma’anar abinda yake cewa
“Ina da buri kanka abdallah” ya sakw fadi,sai ya dubi sumayya
“Ki taimaka min wajen tarbiyyar abdallah don Allah” murmushi ta saki zuciyarta na bugawa kadan kadan
“Banda abinka ya mukhtar ai saidai mu taimaki juna tunda tare zamuyi tarbiyyarsa” girarsa daya ya dage
“Haka ne fa,to Allah ya bamu aron rai”
“Amin ya Allah” ta fada tana ci gaba da cin abincin,sai daga bisani ta lura ba wani cin abincin sosai mukhtar din keyi ba sai aukin kallonsu
“Ai bama cin abincin kake ba fa yaya,wannan kallon duka na meye?”
Murmushi ya kuma saki.”kallon so da qauna nake muku”dariya ya bata sosai
“Naga alama sai na maka dura” ta fadi tana debo abincin da spoon tana bashi,qarshe ita ta qarasa basu abincin dukansu sannan ta gyara gun,kayan wasa taga yana ta hadawa abdallah sannan ya janye ta bedroom yace zata tayashi wani aiki,bata fahimci wayo yayi mata ba sai da labari ya soma shan banban.

  Daf da kammaluwar komai sai ta tsinci hawaye na diga idanunsa,tasa hannu ta shafo sai taji itama nata idanun na fidda ruwan qwallar da batasan dalili ba

“Ya mukhtar ko na yi ma laifi ne?” Ta tambayeshi cikin sanyin jiki,sai ya sake qanqameta yana sakin ajiyar zuciya tare da murmushi
“Babu abinda kika yimin,tsakani na da ke sai fatan alheri,Allah ya haskaka rayuwarki,qwallar farinciki nake musamman idan na tuna gobe zamu sake sabon zama sumayya” dariya tayi tana kwantar da kanta a qirjinsa
“Na gode ya mukhtar”
“Nine da godiya sumayya,ina so ki sake yafemin ki dauka tamkar babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu mara dadi” cikin shagwaba tace
“Ni na manta ma fa ya mukhtar,ni babu abinda ya taba faruwa tsakanina da kai,kai fa uban ‘ya’ya na ne”.

 Da qyar ya yarda zai maidata gida,da sdrd yayi tayi zamanta meye marabar yau da goben,ko a motar ma sai da ya gama yawo da su guri guri ya loda uban siyayya sannan ya kaisu gida,riqe hannunta yayi sanda take shirin fita ya sumbaci bayan hannun nata,itama sai ta maida masa martani,ta jima tsaye a soronsu tana leqensa ganin ya tsaya bai tafi ba,sai daga bisani taga ya ja motar ya tafi.


           *JUMA'A*


 Tun mafarkin da taji daren jiya jikinta a mace yake,tana farkawa ta kira mukhtar din ta tabbatar da lafiyarsa,har yana zolayarta kodai ta qagu ne kawai a kawota,shi bacci ma yakw ta tasheshi,dariya tayi cikin jin kunya sukayi sallama,har zuwa wayewar garin juma'ar jikinta a mace yake,tun safe take kwance ta kasa katabus,tana jiyo koke koken abdallah da yau ya tashi da rigima amma ta kasa cewa komao,har ya shigo dakin ya gama kukansa da kawo mata qarar walida 'yar anty salma ya gaji ya fice ba tare da tace masa komai ba.


    Qarfe hudu na yammacin ranar tana tsaye tana shiryawa cikin dinkin atamfa riga da zani anty salma na tsaye kusa da ita tana bata turare wayarta ta dauki kuwwa,sunan mukhtar ne ya bayyana gabanta yayi mummunan faduwar har qafafuwanta taji sunyi sanyi,sai ta koma bakin gado ta zauna tana amsa wayar cikin fargaba

“Assalamu alaiki amarya ta” muryar mukhtar ta ratsa dodon kunannata,sai ta amsa masa tana lumshe idanuwanta,cikim salon soyayya suka gaisa sannan yace
“Ina fatan kin fara shirin tahowa gidanki” dariya ya bata ta murmusa
“Yanzun haka ma shirin nake angom doki”
“Eh naji na yarda ina abdallah”
“Yana waje,yau tun safe yake ji da rigima wallahi” nemo min shi mu gaisa”
“Bai kusa fa ya mukhtar” ta fada a shagwabe,tuburewa yayi tilas ta qwalawa zainab kira ta kawo shi ta hadasu da wayar taci gaba da shiryawa,sai da ta gama sannan ta karbi wayar
“Nima ina gun masu dinki zan karbi dinkuna na,SAI KIN TAHO?”
“To ya mukhtar,ka kularmin da kanka”
“To my sumy”. Ajjiye wayar tayi tana sakim ajiyar zuciya.

   Bayan sallar magariba 'yan rakiyar nata sukayi mata sallama kowa ya kama gabansa,ganin har isha'i tayi shiru sai ta daura alwala tayi sallar isha'inta,sam gidan ba,gabanta ke yawaita faduwa tana ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakil,ga abdallah na tare da mukhtar tare zasu taho da shi,ganin shirun yayi yawa sai ta miqe ta kunna saudi qur'an Allah ya taimaketa ma akwai wutar nepa ta zauna tana ci gaba da saurara zuciyarta na mata wani iri babu dadi.


   Firgigit ta dawo hayyacinta tana duba agogo,goma na dare ta dubi wayarta dake ta faman ruri,sunan malam ta gani kam screen dinta,sai taji gabanta yayi mummunan faduwa har sai da ta furta hasbunallahu wa ni'imal wakil a bayyane sannan ta kara wayar a kunnenta

“sumayya kina ina?” Abinda taji malam ya fadi kenan,sai tambayar ta bata mamaki
“Ina gida na malam”
“Yauwa to maza kashe wayarki ki fito qofar gida abubakar na jiranki,yace yana ta bugu bakiji ba”sai ta amsa da to kawai tare da bin umarnin malam din kawai tana jin wani yanayi nabin fata da tsokar jikinta,hijabin data idar da sallah ta zira ta fito kai tsaye qofar gidan ba tare data rufe gidan ba.

  Ya abbakar ne tsaye jikin adaidaita sahu kansa a kife,qarar bude gidan ya janyo hankalin sa,sai ya kalleta

“ya baki kulle gidan ba,malam ke son ganinki”
“To” kawai ta kuma cewa ta koma ta jajjanyo qofofin,tana fitowa ta miqawa ya abubakar wayar tata don ji tayi ta fara yi mata nauyi a hannu,kallonta kawai yayi ya sanya hannu ya amshi wayar ya sanya a aljihunsa suka shiga adaidaita sahun ya jasu suka bar qofar gidan ba tare da kowa ya sake cewa komai ba.

  Cikin harabar asibitin mai adaidata ya faka ya abbakar ya biyashi suka fito,binsa kawai take a baya ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,tarin tambayoyi ke yawo kan kwanyarta amma ta gaza furta koda guda?,shin waye a asibiti?,me ya faru ko meke faruwa?.gab da zasu haura saman asibitin ta iya tambayarsa

“Ya abbakar,wai me yake faruwa?,waye ba lafiya?”
“Babu komai muje kawai”
Tun daga farkon barandar ta fara cin karo da mutane,yaya yahanasu,malam,kawu mahaifin abdur rahman da hajiya mahaifiyarsa,jamila yarinyar yaya yahanasu,sai mamanta da wasu mutane uku da batasan su waye ba,tunda taga yaya yahanasu mukhtar ko abdallah ne suka fado ranta,jikinta ya fara rawa sai ta fara qoqarin faduwa sanda suka had ido da yaya yahanasu taga ta saki kuka,da sauri hajiyan abdur rahman ta qaraso ta tareta ta zaunar da ita kan kujera tana fadin
“Yi a hankali sumayya,babu komai in sha Allah Allah zai bashi lafiya,kiyi masa addu’a”
“Waye hajiya me ya sameshi” malam ne ya qaraso yayi mata bayani,hatsari mukhtar din ya samu yana hanyar tahowa gida shida abdallah gab da sallar magariba,yanzu haka mukhtar din na tare da likitoci amma sunce yanzu zasu fito da shi saidai ICU zasu kaishi,wani irin tauri taji zuciyarta tayi
“La haula wala quwwata illa billah” ta dinga maimaitawa,jin jikinta take kamar ba nata ba.

   Bata ce komai ba har zuwa sanda aka bude qofar wani daki aka turo gadon,mukhtar ne kwance tamkar gawa,babu abinda ke aiki a jikinsa sai numfashinsa dake fusga duk bayan wasu daqiqu,kansa nannade da bandeji fari wanda jinin da ya ci gaba da ratsowa ke barazanar sauya masa kala,a haka ma sun gyarashi sun dan gogeshi,wani kalar tashin hankali ya ruftowa sumayya,sai ta miqe tsaye har suka wuce da shi intensive care unit din,kukan yaya yahansu na haduwa da nata tashin hankalin yana yamutsa qwaqwalwarta,qunshe bakinta tayi cikin hijabi ta saki wani irin kuka qasa qasa ta soma furtawa

“Ya ubangiji na,na roqeka kada ka sanya wannan ya zama cikin KUNDIN QADDARA ta,Allah na tuba,na tuba ubangiji na” abinda ta dinga maimaitawa kenan qasa qasa,hajiyan abdur rahman ita ta dinga lallashinta,saidai babu abinda ke qara mata sai tashin hankali ahaka sha biyu na dare ya cimmasu dai dai lokacin da likitocin suka fito,bayani suka yi masu kan dakin bai buqatar shigar mutane ciki,haka nan mutum daya suke da buqata wanda zai zauna da mara lafiya
“Don Allah don annabi malam ku qyaleni na kwana,wallahi bazan iya tafiya gida ba” sumayya ta fada tana fashewa da kuka,babu wanda tausayinta bai kama ba anan,ganin babu yadfa za’ayi a barta ita daya kawu da ya abbakar zasu kwana cikin asibitin,ita kuma ta kwana gun mukhtar din.

  A hankali ta dinga takawa har gaban gadon da mukhtar din ke kwance,ko ina na'ura ce ke aiki a jikinsa,baki daya fuskarsa ta sauya kamar ba mukhtar ba,kallo daya zaka masa kasan lallai ya bugu sosai a kansa don tuni har ya kumbura kan nasa,kujera ta ajjiye bakin gadon tana qoqarin danne zuciyarta tare da tuna nasihar da malam yayi kata kafin su tafi 

“Kuka baya maganin komai,addu’a ita ke magani” abinda ya gaya mata na qarshe kenan,kanta ta girgiza tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai ta kama tafin hannunsa ta sanya cikin nata,a hankali murya can qasa mai cike da rauni ta soma karanto ayoyin qur’ani wadanda su suka dinga debe mata kewa tsawon daren,saidai abinda ke daga mata hankali dai dai da second daya babu wani abu da taga ya motsa daga jikinsa,wanda likitocin sunce ta kula ko yaya taga ya motsa ta sanar musu,duk da lokaci bayan lokaci suna shigowa suna sake dubashi.

   Sai da suka saitu sosai kan hanya sannan mama tace

“Ina abdallah” tofa,sai lokacin hankalin kowa ya dawo jikinsa,duk cikinsu babu mai amsar tambayar,don hatta jama’ar da suka ceci mukhtar dim babu wanda yace yaga yaro,take wani sabon tashin hankalin ya samesu,mama kam kasa daurewa tayi saboda tsananin tausayin sumayya sai kawai ta sanya kuka,kai tsaye malam ya nemi alfarmar mai abun hawar ya canja akalarsa zuwa policestation wanda tafi kusa da inda al’amarin ya faru don si shigar da report cike da matsanancin tashin hankali.

  Kiran sallar asubar fari sanyi ya fara busowa,sam bata lura ba tana gyara zamanta,tana daga kai suka hada idanu,ya bude idanuwansa tar yana kallonta,wani farinciki ya dinga zagaya ta,ga mamakinta taji sai taji ya kita sunanta,cikin matsanancin farinciki ta amsa

“Qarfe nawa?”
“An kusa sallar asuba”
“Daura min alwala sumayya banyi sallar magariba da isha ba” girgiza kai tayi
“Ya mukhtar jikinka duka kayan aiki ne,ka bari likita yazo sai ayi maka” tubure mata yayi hakan ya sanya ta lallaba ta shashshafa masa ruwan iya inda zai yiwu,yana daga kwancen ya dinga halarto da sallar yana yi har ya kammala baki daya tana zaune tana kallonsa,yana sallamar qarshe kansa saitinta ne sai ya zuba mata idanu,murmushi tayi tace
“Sannu ya mukhtar” kai ya kada mata sannan yace
“Ina abdallah” abdallah,ta dinga nanatawa,idan kunnuwanta basuyi mata qarya ba ance tare suke da abdallah,to ina yake ina yayi?
“Ina fata lafiya yake babu abinda ya sameshi” tabbas lafiya yake idan da ba lafiya ba da sun gaya mata
“Lafiya yake ya mukhtar” ta fada cikin salon son kwantar da hankalinsa
“Alhamdulillah” taji ya fada sai ya maida kansa,cikin farinciki da tada sallah itama.

 Shaquwa taji ya soma yi wadda kan ta idar da sallar ta qara yawa,tana sallamewa tayi kansa tana masa sannu,da hanzari ta dauko ruwan roba ta bude ta fara bashi a hankali,sosai ya sha ruwan kuwa sannan ta cire roban daga bakinsa ta qulle tana masa sannu,minti biyar tsakani shaquwar ta dawo,ta sake matsawa gunsa tana riqe da hannunsa tana masa sannu cikin tashin hankali ganin yadda qirjinsa ke dagawa wannan karon

“Bari na qara maka ruwan” ta fadi tana shirin juyawa inda gorar ruwan take,sai taji ya damqe hannunta,juyowa tayi tare da tsayawa cak kamar an kafeta,idanuwansa taga sun fara juyewa,jikinta ya hau rawa ta qanqame hannunsa tana fadi a fili
“La’ilaha ilallah,muhammadur rasulullah” abinda ta dinga maimaitawa kenan a fili babu qaqqautawa,a hankali taji ya kama yana maimaitawa,kusan minti biyu yana fada shima cikin fusgar numfashi sai taga idanunsa na lumshewa,riqon da ya yiwa hannunta tsaurinsa ya sassauta
(Abinda ake so ga kowanne majinyaci kenan,mutuwa na da sa gigita da daga hankali,amma gata ake so ka yiwa mamaci wanda shine qarshen qaunar da zaka nuna masa,a yayin daka fuskanci wasu alamu na fitar ruhi daga gangar jikin majinyaci,bakinka ya dinga ambaton la’ilaha ilallahu muhammadur rasulullah ko za’a dace mamaci ya kama,ba cewa ake fadi abinda na fada ba,ko kuma cene la’ilaha ilallah,a’a ka dinga fadi yadda kunnuwansa zasu iya ji,idan Allah ya qaddara bawansa ne na gari sai ya kama ya kuma cika da ita,Allah kasa mu cika da wannan kalma mu da daukacin musulmi baki daya,amin).

  Hannunta ta zare qirjinta na fat fat fat,hawaye ne ke bin kuncinta,wasi wasi ya cika zuciyarta,fata take ba abinda take zato bane,wannan tunani ya sanyata fita da gudu tayi ofishin likitan.