*GIDAN LUKMAN*
Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita kadai ke rayuwarta cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe kayansu sunyi qaura zuwa bangaren hajiya,tsakaminta da su kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace suyi matuqar bai sabawa addini ko al'ada ba hajiyan na umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da gida,saidai yakan kira wayar hajiya wanda ya siya ya ajjiye musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran ya kuma gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri yake bata,yace sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama yana bata ran hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam karima bata san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta jin is switch off,hakanan a yanzu ba zata iya cewa ga inda lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin buqatunta na yau da kullum,sannu a hankali hankalinta ya fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman din a kusa bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen malaminta.
***
Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin takabarta na raguwa,ta fawwalawa Allah lamarinta baki daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu bibbiyu,saidai ba'a raba zuciya da tuna abubuwa masu d'aci da suka gabatar mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai yawan shiru shiru,sai kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data sake yi sanadiyyar ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don haka addinin musulunci yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da matarsa da suke kira anty sukan leqosu.
Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar mukhtar alhj farouq ya iso kano,cikin falon sumayya suke zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan ya kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq ya soma gabatar da maganar data tarasu
“Bayan dukkan wani bincike da jami’an tsaro suka gabatar ya bayyana cewa zainab ita ta dauki nauyi ta kuma bada umarnin kisan mukhtar” duk sa suna zargin hakan amma sai da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya tana salati da kalmar shahada tare da ambatar sunan zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora
“Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran wulaqancin da mukhtar ya mata ne na saki uku kuma yaqi maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai amma babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin ya maida aurensa da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki ta sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da ita ba,sai taga gwara ayi biyu babu kowa ya rasa,baya ga haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da baya da tayi har ta haifi abdallah”alhj farouq ya saurara yana maida numfashi cike da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun asali shi mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a rayuwarsa
“La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana kenan,ashe kece ajalin muntari?” Yaya yahanasu ta fada tana sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana jin cewa itace da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja jikinta da qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke zaune a kan cinyarta tana dubansh,idanuwanta sun gaji da kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo
“Sumayya,don girman Allah,don darajar ma’aiki da iyayenki ki yafemin,babu shakka ina ji a raina nice sikar ajalin muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga hankalina na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne kadai ke da ikon bawa bawa ba,na yi masa aure na farko suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko masa wata na tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita ce ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na shiga hurumin ubangiji,idan da na haqura ashe akwai rabon mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar idan baki yafemin ba haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa ba…..” Sai ta kasa qarasa abinda take da niyyar cewa muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda kuka.
Dubanta sumayya keyi kawai,ita yanzu a rayuwa me ya rage mata?,me zai bata mata rai?,mene ribar taqi yafewa yaya yahanasun tunda mai afkuwa ta afku,babu mai goge abinda ya faru,idan ta qullaceta mai hakan zai maganta mata?,koba komai taci darajar mutum biyu MUKHTAR da ABDALLAH
“Allah ya yafe mana baki dayanmu” abinda ta fada cikin raunin murya,babu wanda hakan bai burgeshi ba,godiya ta dinga jerawa sumayyan tare da binta da kyawawan addu’o’i sannan ta juya ga malam
“Malam kaima ina neman afuwarka,abinda na yiwa diyarku da kuka bamu ita cikin aminci da amana tun tana shekara sha uku amma naci amana,na bada gudun mawa wajen mutuwar mijint….” Nan ma kasa qarasawar tayi saboda yadda lamarin ke mata ciwo cikin zuciyarta
“Ya isa yahanasu,babu mai rayawa ko kashewa sai ubangiji,komai akwai sanadiyya amma kuma Allah ya riga ya tsara komai,abinda ake so ga bawa dama shine,a duk sanda ya fahimci yayi wani kuskure to ya nemi afuwa ya kuma guji aikata laifin a gaba,Allah ya bamu dacewa baki daya”
“Amin ya Allah,amin” duka suka amsa,sumayya ta miqe don komawa ciki,haka take bata son zama cikin jama’a balle tayi doguwar magana,a nan alhj farouq ya sanar musu cewa ranar litinin za’a miqa zainab da sauran yaran kotu,amma basai sumayyan taje ba insha Allahu tunda sun amsa laifinsu ba wata doguwar shari’a za’ayi ba.
******* ****** ********
Kwana goma ya rage mata ta kammala takabarta aka gama shari'ar wadda ta dauki wata biyu ana yinta,bincike ya nuna zainab na da hannu dumu dumu wajen mutuwar mukhtar,ita ta biyasu suka kunce tayar motar mukhtar a sanda yake shagon dinki zai amso kayan dinkin sa,yayin da yaran data dauka aiki anjima ana nemansu,irin mutanen da ake hayarsu ne suyi kisa,sun kashe mutane da dama hakan ya sanya aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya,zainab kuwa aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai,aka fara wucewa da ita asibiti,sabida a lokacin cuta mai karya garkuwar jikin dake jikinta ta fara mata tasiri,zaman gidan kurkuku da tayi ba tare data fara shan magani ba ya sata bayyana lokaci guda,alamominta duk sun gama bayyana,sannan qafarta da oga ya daka ta karye aka mata dori dorin baiyi kyau ba,don da aka kwance gun har ya fara ruwa yana neman lalacewa......
*
Ranar da ta kammala takabarta a washegari malam yace su dawo gida,kawun abdur rahman shi ya nemi alfarma gun malam din yayi haquri a gama tattara dukiyoyin muntari a raba gado,shikam yace babu komai duk abinda suka zartas dai dai ne amma kawun yace a masa alfarmar dai,cikin qanqanin lokaci aka kammala hada komai na mukhtar din,aka raba gadon kamar yadda ubangiji ya tsara,kusan dukiyar baki daya abdallah ya cinyeta kasancewarsa d'a namiji qwaya daya tal wajen mahaifinsa,kawu ya tattaro dukiyar baki daya ya kawo gaban malam,sam malam yace yaje ya riqe ya kula da ita amma qememe kawun yaqi,daga qarshe suka yanke shawara aka danqawa ya abubakar ya juya masa cikin kasuwancinsa da yake na saida atamfofi,addu'a sosai suka yiwa abubakar din kan Allah ha tayashi riqo
*SABUWAR RAYUWA*
A kullum ta kebe kanta ita daya tunani take yi yaya rayuwa zata kaya mata?,meyw kuma kundin qaddararta na gaba?,wanne shafi kundin zai bude mata kuma?,amma a zahiri ta saki jikinta ko don yadda 'yan uwa da iyayenta suka damu da ita,burin kowannansu ya faranta mata ya sanyata dariya,kowa tausayinta yake,tana ganin bai kyautu ba taci gaba da zama cikin damuwa har ta sanya wasu,mukhtar dai ya riga ya tafi ba kuma zai taba dawowa ba har abada duk kuwa yadda take qaunarsa,qauna daya ce tsakaninsu kada ta manta da yi masa addu'a,hakan yasa ta rungumi rayuwarta ta kuma rungumi danta,a lokacin cikin kudinta na tumunin takaba ya abbakar ya ware mata wani abu yace ta fara sana'a,dama can sumayya ta iya sana'arta,saboda haka babu bata lokaci ta shiga kasuwar kurmi ta saro kayan humta turaren wuta na daki kaya dana tsugunno sai kwalakca ta koma tsohuwar sana'arta,mutum ce ita mai nasibin sana'a,duk abinda ta sanya kanta ta fara saidawa sai Allah ya kama mata,cikin ikon Allah kuwa sai wannan karon abun nata ya sake bunqasa,cikin abokan ya abbakar akwai mutum uku da iyayen gidansh ke da supermarket,suka buqaci ta kawo su gwada cikin shagon,ta samu kwalabe masu kyau da tsari ta zuba,ba'ayi sati ba suka qare suka kawo mata kudinta suja sake nemam wasu,cikin lokaci qanqani abun ya habaka,sai ta sanya halima da zainab ciki sukeyi tare,tunda ta aikama anty dije itama take karba ta amfanin gida,wani lokaci ta saida ko tayi kyauta.
Sana'ar da take yi ta dauke hankalinta sosai,ta rage mata zaman tunani da kuka,saidai duk da haka babu wani abu da ya ragu na tunanin mukhtar cikin ranta,hakanan duk dare kafin bacci ya dauketa sai tayi kuka mai isarta.
*
*_Bayan shekara daya_*
Koda kwana daya ne ya ratsa cikin rayuwar bawa ta iya yiwuwa kaga sauyi tattare da rayuwar nan tasa,walau a sarari ko a boye,hakan ce ta kasance ga rayuwar gidan su sumayya,wanda a wannan shekara guda din an sauya fasalin gidansu san sake musu gini mai kyau da tsari cikin ribar kudin abdallah sumayya tasa aka yi wannan aiki,sun sake samun rufin asiri sosai,babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa,ci da sha da sutura baki daya,don har taimako takanyi cikin ribar sana'arta wanda bai gaza dubu hudu zuwa qasa ba,an kawo kudin auren zainab wanda ba'a sanya rana ba ana jira zuwa wani lokaci kafin na halima ya gama shiryawa kamar yadda yace a bashi lokaci.
* ** ******
Sanye take da dogon hijabi mai hannu wanda har jan qasa yake,qafarta na sanye da safa sai niqabi daure a fuskarta,wannan itace shigar data koma yi tun randa ta taba fita wani ya biyota ta yiwa kanta alqawarin canza shiga,duk da dama can ma'abociyar sanya hijabi ce,daga ranar ta bada kudi aka dinka mata su kaloli masu kyau har kala biyar,ko ina zata su take sanyawa duk tsadar suturar dake jikinta,ko yaushe kar suke a goge cikin tsafta da qamshi,shigar na matuqar yi mata kyau qara mata kwarjini da kuma boye kyawun sufarta baki daya,dawowarsu kenan daga gidan anty salma ita da halima ta kai mata humra da turaren wutar da ta yiwa wata amarya da za'a yiwa aure 'yar maqotanta,daga nan ta tsaya aka musu lalle ita da haliman bayan ta shiga kasuwa ta sayi kayan humra,saboda anty dije tace sati na sama tana nan zuwa kano,har tana tsokanarta da ita zata koma abuja don ta fuskanci bata qaunar zuwa abujan ko kadan,dariya sumayyan ta dinga yi tana tsokanar anty dijen itama da cewa zaman garinku sai wanda ya saba,haka kawai kaje a qunsheka cikin gidan ba motsin yara bana maqota saidai idan kai ka shiga.
Sam bata damu da sabuwar motar da ta gani ajjiye qofar gidansu ba suka wuce zuwa cikin gidan ita da halima suna 'yan hurarrakinsu,tun daga soron gidan su qamshin turare ke dukar hancinsu ba kuma irin turaren humrarta ba da ya kama gidan,daga bakin qofar falonsu ta hangi takalma sau ciki na maza bata kawo komai a ranta ba tadage niqaf dinta tayi sallama cikin falon.
Abdur rahman ne zaune cikin daya daga cikin kujerun falon sanye da shadda ruwan madara wadda ta haska fatarsa,kansa hula ce zanna,hankalinsa na kan mama suna taba hira da alama labari yake bata,sallamar su ce ta maido hankalinsa bakim qofar,baki ya saki yana kallonta cikin mamaki kamar yadda ta saki baki itama tana kallonsa cike sa mamakin yaushe ya diro nijeria
“Kai kam baka da aiki sai zuwan bazata?”
“Kawai kice yaushe a gari inji maqi baqo” ya fada yana murmushi,sai data samu gu ta zauna sannan ta dubi mama
“Wai don Allah mama yaushe yazo?”
“Fitarku ba dadewa” sai tayi murmushi tana gaida shi,amsawa yake shima cikin sakin fusakar suka fara dan tsokanar juna yadda suka saba,halima ce ta shigo wadda sai da ta tsaya ta daura alwala,a ladabce ta gaidashi ya amsa yana dubanta
“Wai shekara daya tal naga duk kum qara girma,halima ke kam ashe ke kika debo kamar sumayya”dariya tayi ta shige daki don tada sallah,mama ta miqe jin zainab na kiranta tazo taga ruwan miyar tuwon daren data tsayar ya isa.
Maida dubansa yayi ga sumayya
“sumayya ya kuma bayan saduwa,bayan tafiyata lamura masu yawa sun wakana,Allah ya jiqan yaya mukhtar,ya gafarta masa ya masa kyakkyawan masauki a aljanna yasa ya huta”
“Amin ya Allah” ta fada wani miki na neman motsuwa a zuciyarta,zuciyar na son karyewa hawaye na neman zuba,shuru ya ratsa dakin yana nazarinta,ya fuskanci ya taba mata mikin dake zuciyarta
“Tunda nazo nake tambaya ina mutumina ashe yana gidan gwaggwo yahanasu,da yake ban leqa gidan ba,jiya na shigo qasar” sai ta murmusa tana cewa
“Ayyah,ai da ya samu hutu sai tazo ta daukeshi da kanta” idanu ya zaro
“Kice abdallah an fara makaranta,lallai an girma”murmushi ta kuma tana bashi amsa sanda mama ke dawowa cikin falon
“eh,ai yana cika shekara ya abbakar ya sanyashi”
“Wacce makaranta ce?”
“New egypt international” kai ya kada
“Masha Allah” hirar sai ta koma gun mama sai ta miqe itama tayi sallar la’asar,bashi ya bar gidan ba sai da yayi magariba suka gaisa da malam sannan ya ajjiye musu tsaraba dangin alawoyi da jallabiya ta maza data mata tasu sumayya zainab da halima,sai tarin qananan kaya na abdallahnsa.