KUSKURE NA CHAPTER A
_HALL_ d’in cike yake damk’am da da mutane, ko ina ka kalla al’umma ne zazzaune da alamun ba’a fara gabatar da occasion d’inba.
_Nima a dai_dai lokacin nasamu isowa k’ofar babban d’akin taron, agogon dake hannuna na duba 7:25 am, hakan ya tabbatarmin saura 5 minutes afara gabatar da occasion d’in, wani security ne ya dakatar dani dacewa “madam can i see your get pass ” ? Ina k’ok’arin manna siririn glasses a ido na d’ago na kalli security nace ” I don’t have a get pass but i am from *Muslim Sisters Organization of nigeria (m.s.o)* na k’arasa fad’ar haka ina me nunamasa wata sheda dake manne ajikin mayafin danayi roling kaina dashi , cikin kulawa securityn yace” you highly welcome madam please your name before you enter and your phone number and email address if available” ? okay RAMLERT Y SALIS is my name my no is 081…… , thank you ya fad’a sannan na doshi k’ofar shiga hall d’in kafin na k’arasa k’ofar ta bud’e ina shiga ta koma ta rufe_
Babban d’akin tarone ya tsaru iya tsaruwa hall d’in babbane na gaban kwatance, wannan shine karona na farko dana ta6a halartar _Transcorp Hilton Hotel_ duk iya tunanina baza’a samu wajen taro me kyau da tsari haka a nigeria ba ammah dana tuna _Transcorp Hilton_ shine babban hotel a duk nigeria sai na dena mamaki but the place is interesting is nice place.
Kowa ka gani acikin hall d’in yayi shiga irin ta Alfarma wayancin mutanan danake kallo sunsa too expensive clothes hakan ya tabbatarmin _the occasion is noble and significant_, mutanen dake d’akin taron sun had’a da manya_manya ‘yan siyasa matansu da maza ma aikatan gidan radio da TV ga manyan ‘yan jaridu da sauran manyan mutane , waje nasamu na zauna banfi mintuna 2 da zama ba sautin speaker ya fara tashi.
_AYANZU NE NIKUMA MARUBUCIYARKI ZAN FARA KAWO MUKU RAHOTO, HAR IZUWA K’ARSHEN LITTAFINA NA *KUSKURENA* ASHA KARATU LPY_
Matashi ne baxai wuce shekaru 35 ba sanye yake cikin black court, daganinsa kaga wanda ya gama jika acikin hutu a hankali yake magana cikin speaker d’in.
“Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu, muna k’ara godewa Allah da ni’imarsa har ya kawomu wannan rana me tarin daraja da tarihi, Aminci ya k’ara tabbata ga Annabi (s a w)da dukkan iyalansa da sahabbansa da dukkan wanda ya bada gaskiya da ranar lahira ameen, godiya ta musamman game girma _Governor_ da muk’arrabansa , ‘yan majalissu da mutananu, Abonka aiki da sauran al’ummar dasukaxo dan tayamu murna”.
Sai yayi shuru na d’an wani lokaci sannan ya d’ora dacewa”At the first place _JAFAR MUHD_ is my name I am the best friend of groom _SAFRAZ HASHIM MUHD_, We are waiting for our groom and his bride along side with his _first lady_ keep waiting please.
Rufe bakinsa keda wuya, hayaniya ta d’an fara shigowa hall d’in daga wata k’ofa dake can watakusurwa a hall d’in hakan ya tabbatar ango yasamu isowa tare da amarya da kuma first lady kamar yadda jafar ya fad’a.
Baka ganin komai sai haske cemara dake ta haskawa nanfa masu video suka fara aikinsu da masu hotuna da ‘yan jaridu da sauransu.
Su uku suka jero sun sashi a tsakiya, daka ganshi zaka tabbatar shine angon kallo d’aya zaka masa kace balarabe ne haduwa kam ya gama ya k’are kamar shi yayi kansa dan kyau _SAFRAZ_ yana da tsayi ammah ba can sosai ba ba siriri bane kuma bashi da jiki fari ne tas yana da manyan danuwa da dogon hanci da k’aramin baki, sajensa ya kwanta a fuskarsa tamkar gashin jararin da aka haifa yau se jajayen la6ensa dasuma dace da fuskarsa, let stop describing , nasan me karatu you already visualize, to see him in your eyes mind.
Amarya ce a gefensa na hagu tayi shiga cikin tsadaddun kaya sai walkiya takeyi, siririyace tana da tsaya medium, chocolate colour ce sai dai daganin fatanta ta gaki da hutu da jin dad’i, tana da doguwar fuska da matsakaicin hanci da baki medium eyes fuskarta tasha kwalliya, Sai wacce ke gefensa na dama da alamun matarsa ce domin yana sak’ale da hannunta kallo d’aya zaka mata kaga tayima masifar kyau, kwarjini, da burgewa, mace ce ajin farko ko mace ‘yar ‘uwarta idan ta kalleta sai ta k’ara balle kuma ace namiji , komai nata idan ka kalla zai burgeka farace ammah ba fari irin tas ba dan mijin ta ya fita fari , ba siririya bace kuma bata da k’iba tana da dara_daran idanuwa da dogon hanci bakinta d’an dai_dai le6enta bak’ine sai gashi daya kwanta a gaban goshinta tanada diri sosai.
Inda aka tanada dan zaman ango da amarya nansuka nufa, ammah sai dai kujeru guda buyune awajen na alfarma ganin hk yasa _IZZATU_ ta fara kwace hannunta dg hannun mijin nata dan tasan kujeru biyun data gani nashine shida amaryarsa babu ita a lissafin, shima safraz ya gane abinda matar tasa izzatu take nufi ammah sai yayi kamar be fahimta ba yakuma rik’e hannunta sosai ta yadda bazata iya kwacewa ba.
Sam ranta baiso ta karasa wurin zaman ba ammah hk ta bisu suka isa ga mazaunin nasu, Amarya _KARIMA_ inda aka tanada dan ita tasamu ta zauna zuciyata a cunkushe ranta sai tafasa yakeyi ganin yadda safraz yake wani mannewa matarsa kuma wai agurin shagalin bikinta bata k’ara jin 6acin raiba sai data ga safraz yana tayiwa izzatu magiya dan Allah ta zauna itakuma izzatu ganin yadda ya marairaice mt kuma gashi people duk su suke kallo sai ta zauna ammah ba dan ranta yasoba tana zama kuwa shima ya zauna karima jitayi kamar tasa hannu aka tayi ihu ganin sun zauna a kujera d’aya wanda ango kawai aka tanadarwa.
Ina !anan hall d’in ya d’auka wasu na dariya da shewa wasu kuwa ransu a 6ace suna ganin abinda angon yayi bai daceba.
Jafar da yake shine minister of the occasion yana dg inda yake yana kallonsu ko kad’an abokinnasa bai bashi aushinba saima burgesa da yayi, sai da hall d’in ya lafa sannan jafar ya fara mgn kamar hk” Alhamdulillahi kamar yadda muka riga muka gani ango da amarya sun iso tare da first lady ayanxu ne km zamu fr gabatar da wannan taro namu God willing, so, batare da 6ata lokaci our first presenter itace hajiya km malama izzatu wato first lady uwargida awajen ango, idan me girma uwargida ga ango ta shirya muna sauraronta”
Cikin mamaki izzatu take sauraron abinda jafar yake cewa, safraz ta kalla sannan tace” Besty why do that to me ?ni mezance idan na tashi ?hb besty nasan wannan plan d’in duk naka ne u have nothing to say ni gaskiya” ta karasa maganar kamar zatayi kwalla, murmushi safraz yayi sannan yace” hb reality don’t say that pls kina da abinda fad’amana sosai i am your one and only pa inason kije ki tabbatarwa jama’an dake hall d’innan bawai mijinki ya k’ara aure bane dan by sonki ke har yanxu sabuwace a gurinsa sauran mt suyi koyi dake my queen ” ya k’arasa mgnr yana d’anyin dariya izzatu dataji ya fr irin wad’annan zancen nasa sai ta galla ms harara ta mik’e a hankali ta fara tafiya, karima da tn jin duk abinda suke cewa ta ta6e baki duk haushi ya isheta.
Taku takeyi cikin nutsuwa fuskarta d’auke da fara’a kowa ya maida hankalinsa kanta wasu na mamaki ganin yadda fuskarta ta nuna kamar tana cikin farinciki sosai batayi kama da wacce akeyi kishiya ba.
Tana isa wajen jafar ya bata abin mgn shima yasamu waje ya zauna, sai data dai_dai ta tsayuwarta sannan ta fr mgn kamar hk-
‘Alhamdulillahi ala kulli halin, I am Izzatu Abubakar the wife of safraz hashim muhd groom of today, okay before i begin let me greet you like am suppose to do so may peace be upon you, Ina yiwa dukkan bak’inmu barka da zuwa muna godiya sosai da sosai dan zuwa tayamu murna a wannan rana me,matukar daraja ’ sai tayi shuru na d’an wani lokaci sannan tacigaba da cewa-
” ‘Y ar fad’akarwar da zanyi zuwa ga amarya zanyi, 1 _Kiji tsoron Allah a zamanta kewarku Allah zai sanya miki mafita a dukkan lamuranki._!
2 _Aure ibadane kisani cewa zaki iya ji ko ganin abinda rai baya so, don hk kiyi hakuri sai ki sami aljannarki cikin sauki.!_
3 _Hak’uri da juriya, rayuwar aure bata wata d’aya bace ko shekara d’aya ko goma ba, rayuwace ta har abada sai da hakuri da juriya.!_
4 _Miji shugabane a gareki, dan hk duk abinda yake buk’ata akowane lokaci dole ki aikatashi muddin ba sa6on Allah bane._!
5 _Nisantar abinda miji yake k’i, dukkan abinda mijinki bayaso ki nisanceshi domin yawan sa6awa miji zai jawo miki tsana._!
6 _Yin abinda miji yakeso, ki kula da da dukkan abinda mijinki yakeso, ki aikatashi koda zaki wahala wajen aikatawa domin wannan shi zaisa mijinki ya k’ara sonki da k’aunarki, kuma ki sani aljannarki tn k’ark’ashin duga_dugan mijinki, ma’ana yin biyayya agaresa zai shigar dake aljannah.!_
7 _Yin taka tsan_tsan da shawarwarin k’awaye, ki kula da dukkan shawara da ko wacce k’awa zt baki, ki za6i mace mai ilimi kuma ma’abociya addini a matsayin abokiyar shawararki.!_
8 _Rik’e sirrinki, kada ki dinga yadda wani yana sanin sirrinki tsakaninki da mijinki koda kuwa ‘yan’uwankine.!_
9 _Kyautata zamantakewaki da ‘yan’uwan mijinki kiyi iya k’ok’arinki dan ganin kin kyautatawa iyayensa, yayyensa k’anansa, da sauran danginsa.!_
10 _Gaskiya da rik’on amana , kiyiwa zamantakewarki ado da yin gaskiyaduk abinda zakiyi kiyi gaskiya km ki rik’e amanar mijinki.!_”
_HALL_ d’inne ya d’au tafi wasu kuma suna kabbara, izzatu ta burge mt da sama a wajen harma da mazan gurin shikuma safraz sai murmushi yakeyi ganin yadda jama’a ke jinjinawa matarsa amarya karima kuwa jikinta yayi sanyi sosai ganin babu wanda yata6a yimata nasiha ta gaskiya km me ratsa jiki irin izzatu wai kuma kishiyartace sai taji ta burgeta sosai ammah sai wani 6arin na zuciyarta ya ce mt ay kawai izzatu ty hkne dan kawai ta burge mutane ayi zaton ko dan Allah tayi.
Sai da hall d’in ya d’an saurara sannan izzatu tacigaba dacewa –
” Yake amarya ki bud’e kunnanki sosai ki jini ki kiyaye wad’annan Abubuwan da zan fadamiki su yanxu guda goma domin suna daga cikin _SUNNONIN AURE_ Idan har kika kiyaye su zaki zm ‘yar auta agurin mijinki‘’
_NA D’AYA_………
~Sannu _sannu kwana nesa muje zuwa page na 2 yau da gobe bata bar komai ba~👌🏻NA D’AYA :
Sanya tozali wato (kwalli).
NA BIYU:
Yin kunshi.
NA UKU:
Daina nuna yawan kish i, (domin mabud’in rabuwane).
NA HUD’U :
Daina mita, surutu,zaigi, ko naci.
NA BIYAR :
Yin ta’ammali da ruwa, (wato tsabta).
NA SHIDDA:
Gano abinda zai faranta ran mijinki a yayin dayake cikin fushi.
NA BAKWAI:
Kawar da kai akan laifin da yayi miki.
NA TAKWAS:
Barin yin mgn lokacin da miji yake cikin fishi.
NA TARA :
Ban da dukan miji, ki zama mai biyayya a garesa.
NA GOMA:
Kamewa dg kai koke_koke zuwaga iyaye ko k’awaye tare da barin d’aga murya sama da tashi.
D’akin taron rud’ewa yayi da hayaniya kowa yana fad’in albarkacin bakinsa, sai da komai ya lafa sannan izzatu tacigaba da cewa:
“Rayuwar aure tana buk’atar abubuwa da dama wanda ko rabi ban lissapa ba, ammah komai yana samuwane a lokacin da matar gd ta zama mai ilimi da wayewa domin ilimi shine jigon komai a rayuwa” . shuru tayi nad’an wani lokaci sannan tacigaba da cewa:
Ilimi shine darajar mace
Shine asalin ‘ya ko wace
Don shike hanata ta lalace
Kuma ilimi shike d’aukaka ‘ya mace.
Ba sanya tufafi tsadaddu ba
Ba d’aura atamfa super ba
Ba zinari dasu fashion ba
Ba shak’e kabot da kiristal ba
Rozis ba alfahari ne ba.
Faharin ‘ya mace kyawun tarbiyarta
Da kula da kiyaye mutuncinta
Da biyan dokar addininta
Haka nan kyawunta d’abi’arta
Ta kwarai ba kyawun fuskaba
Sanin addinine wayewa
Badan kin girma a birni ba.
Wannan karon ma wasu na kabbara wasu na tafi, kowa ka gani fuskarsa d’auke da murmushi musamman safraz da sai washe hak’ora yakeyi.
Izzatu tacigaba da cewa, ” Bari na tak’aita jawabina anan, ina,fata amarya ta fa’idantu,da dukkan abubuwan dana fad’amata,dama dukkan sauran mata baki d’aya, Alhamdullilah Allah yasa abinda na fad’a yazama hujja agareni ba hujja a kainaba , subhanakallamu ashhadu Allah ilaha illah anta astagfuka wa’atubu alaik”. Cikin nutsuwa ta fara takunta dan ta bar gurin.
Safraz cikin hanzari ya taso ya iso inda izzatu take suka jera suna taku d’aya bayan d’aya, Nan da nanhall d’in ya d’au tafi izzatu ta burge,kusan ko wacce mace har mazan dake gurin ammah sai dai wasu matan suna matuk’ar mamakinta gnin ko ajikinta bata damu da auren da mijinta zaiyiba, wasu mazan km na al’ajabi suna raya cewa idan dasu keda izzatu babu wt mace da zata burgesu balle suyi tunanin k’arin aure.
To, haka aka ringa d’auki ba dad’i, muhawara ta barke a tsakanin people dake hall d’in, Nima dai RAMLERT kaina yaso ya d’aure ammah burina kawai ng antashi dg event d’in dan nasamu na isa ga first lady izzatu dan zanso inji labarin ta dan yadda nake gani har tafi mijin nt farinciki a bikin.
An gabatar da manya malamai sunyi fad’akar mai matuk’ar amfani taron yayi gwanin ban sha’awa ya burgewa kowa, Anci ansha delicious food dan save yourself ne kowa yaci abubuwan dayake so an raba gift masu kyau da tsada , sannan taro ya tashi lpy+1, kowa yafi da farinciki da annishawa.
Ina tsaye a premises hotel d’in ina jiran ng fitowar su izzatu sai da kusan kowa ya watse sannan na hango fitowar su kusan su biyar.
Ta gabana suka zo zasu wuce sai alokacin na kula ashe amarya ce kawai da ita da tawagarta dagani abinne bai musu dad’iba shiyasa suka taso amaryasu agaba.
Ba’ada’au wani lokaci ba ng safraz da izzatu tare da jafar da wata mata tana d’auke da baby dagani kasan iyalan jafar ne dukkan su sun nufa inda nake dayake ina tsaye a wajen parking lot ne, sai da sukazo dai_dai dani zasu wuce sannan namu sallama.
Wa’alaikassalam, izzatu ta amsamin.
‘yar’uwa idan babu damuwa inasonyin mgn dake, na fad’a ina kallon izzatu.
Tana murmushi ta cemin, babu wt damuwa ina sauraronki.
A dai_dai lokacin jafar da matarsa suka iso gurin muna gaisawa suka wuce shima safraz yabi bayansu yarage dagani sai izzatu.
Izzatu ce ta fr cemin, ni kuwa sis like i realize your face, kamar RAMLERT Y SALIS ko?
Cikin mamaki nake kallon izzatu ganin ta kira sunana, nace eh! but how come ?
Dariya ta saki sosai tace wonderful ashe idona ba k’arya yayi ba, lallai Ramlert wato har kin manta IZZATU A .A ko?
Wai meke faruwa ne ?na ware ido ina k’ara kallon izzatu sai alokacin na gane dawa nake mgn my lovely friend since at secondary shchooling.
Am i dreaming or are my eyes deceiving me this face look like that of IZZAT A.A Na fad’a ina matuk’ar farinciki mukayi hugging juna.
Yes it’s me , RAMLERT Y SALIS izzatu ta fad’a.
Munyi matuk’ar farinciki sosai domin izzatu classmate d’inace a secondry school munyi abota da aminci tun bayan graduated bamu k’ara ganin juna ba domin ni ina kano itakuma tana Abuja, sai gashi yau cikin ikon Allah mun had’u.
Izzatu tace, Ramlert nayi farincikin had’uwarmu gaskiya, ya bayan rabuwa shekaru da dama.
Nace, i am glad to see you too!komai Alhamdullilah but you vanished without a trice.
Izzatu tace, ba hk bane sis kinsan lokacin da mukayi graduated from secondary acikin mu babu wacce ake bari ta rik’e waya duk shine matsalan ba number gashi bama gari d’aya ammah yanxu we will start !, ta k’arasa mgnr tana dariya.
Nace maganarki gaskiya ne A .A but akwai abubuwan danake son sani sosai ammah baxaiyiwu now ba.
Y salis zaki fara tambayoyin naki kenan ko a school hk kike kamar wata journalist. cewar izzatu.
Dukkan mu mukayi dariya.
Izzatu tace, gobene d’aurin auren mijina kinga yau akayi banquet (waleema)ko?
Nace, Eh! ai shine tambayen nawa sis ina mamaki na duk da cewa ba abun mamaki bane.
Izzatu tace, a gobe za’a d’aura auren sannan agobe amaryar zata wuce england domin cigaba da karatunta ammah one week zt dawo tana yin jarabawar k’arshene domin ta kammala degree d’inta.
To!ikon Allah, ammah meyasa baza’a jira ta kammala ba before ayi bikin?
Dariya izzatu tayi sannan tacemin kiban address d’inki sis zamuyi mgn.
Munyi exchanged na phone number da address sannan mukayi sallama akan cewa duk wanda ya samu dama zai ziyarci d’an’uwansa.
******
*****
****
***
**
**
*
AFTER 6 DAYS
Sis Ramlert dan Allah muje ki kammala cin abincin sai na baki labarin dalla2, cewar izzatu tana k’kok’arin jan hannuna zuwa deining table.
Nace, izzatu wallahi ni na k’agune ba lallai in iya cin wani abuba dama bari kikayi sai mungama, na k’arasa maganar ina marairaice fuskar.
Dole izzatu ta hakura muka koma falo muka zauna.
Izzatu na kallah nace sis ina saurarenki, kuma dan Allah karkiji kunyar fayyacemin komai ba wai ina nufin ki fad’amin sirrinki bane a’a, kamar yadda mukayi a school hk nake son yanxu karki 6oye min.
Izzatu ta nisa sannan tace, Hb Ramlert koda bama tare kina zuciyana banajin zan 6oyemiki wani abu daya danganceni a yanzu sabida ina da tabbacin ke k’awace me gaskiya da rok’on amana, wallahi ina cikin damuwa igiyar aure tana rawa takeyi kodai tayi rauni ko ta tsinke cikin biyu d’aya zai iya faruwa, mijina yana sona fiye da tunanin me tunani ammah anyi mana katanga ni dashi watanmu biyu da Aure ni da shi a yanzu hk ya d’au son duniya ya d’oramin har zuwa yanxu babu wt mace da zata kaini a zuciyarsa ammah jin dad’in rayuwar aure babu shi acikin rayuwar mu nidashi kuma dukkan abubuwan dake faruwa KUSKURENA, izzatu ta k’arasa fad’ar hk hawaye nabin fuskarta.
Jikina ne yayi sanyi jin kalaman izzatu, maganganunta sun d’auremin kai, tears rolling down in her checks har zuwa lokacin, cikin sanyin jiki na kalleta nace, sis pls come down wipe your eyes pls bansan me kikeji a rankiba ammah ki d’aure kidena zubar da hawayenki BAYAN WUYA SAI DAD’I dukkan tsanani yana tare da sauk’i.
Murmushin k’arfin hali tayi sannan tace, thank for your encourage this is my friend tamin alamar jinjinawa, dukkan mu mukayi murmushi.
Izzatu tacigaba dacewa, idan bakayi aure ba ace bakayiba idan km kayi sai matsala!alokacin daka dad’e agidanku bakayi aureba sai anayima kallon d’an isaka bayan kayi aure yadace ayima wani kallo ?ki dubw mijina namijine ra’ayin ko wace ‘ya mace bashi da matsalar komai me zaisa wani namiji ya burgeni ya wadatani da komai na more rayuwa ammah sis mijina ya d’aukeni mazinaciya fasik’a mecin amanar aure.
Sannu_sannu kwana nesa muje zuwa page 3 yau da gobe batabar komai ba👌🏻Wani shocked jikina yayi na ware ido ina kallo izzatu wacce itama ni take kallo, na razana da jin abinda ta fad’a taya hkn zata faru bayan yadda safraz ke nuna son izzatu a gaban kowa.
Izzatu tace, kamar yadda kika sani munyi graduated on 2008, na fr university on 2009 ina shekaran k’arshe befi saura two month na kammala degree ba muka had’u da safraz , Aranar naje _B U K_old side, naje domin wani program da za’a gabatar a ranar domin ni a _B U K_ new side, nake attending lecture department d’inmu na Islamic studies a _B U K_new side yake idan kinga na shiga old side to ko zanje wani program da za’a gabatar a can, to aranar ma hkne domin najene wani program _GLOBAL MONEY WEEK_ wato satin kud’i na duniya, a ranar Allah yayi had’uwata da safraz.
Byan an kammala program ina cikin,tafiya tun kafin na fito dg _B U K_ sai mota ta talalace nayi duk iya k’ok’arina motan yak’i tashi ga yamma tana k’arayi ga babu me gyaran mota akusa da waje mutane kad’an kad’anne ma suke wucewa ta gurin, Ina cikin tunanin yadda zanyi sai ga wata mota tazo ta wuce har tayi nisa sai kuma ta dawo da by, Jafar ne ya bud’e motan ya fito ya iso inda nake yana murmushi, sallama yamin na amsa sannan yace, Can i help you ng kamar your car has broke down,
Nace, hkne zan samu me gyara kuwa a nan ciki?
jafar yace, bazaki samu me gyara ba sai dai idan kin ft waje but you will suffer before you get, if there’s no problem kuzo mu rage miki hanya idan yaso gobe sai kizo da me gyaran sabida yanxu dare yayi i am sure ba wanda zai ta6a miki motanki ko?ya k’arasa maganar yana d’aga mata giransa.
Hk akayi izzatu motan su jafar ta shiga ta bar tata monta a nan, koda ta shiga safraz ta gani a zaune a matuk’in driver sai da suka fita get sannan jafar ya juyo ya kalli izzatu yace, hajiya wace unguwa ce ?
Izzatu tace, a’a babu komai ku sauk’eni a nan tunda kunkawoni main road zan samu abin hawa sai na k’arasa.
jafar yace, no madam baxa’ayi hk ba kibarmu mu k’arasa ladanmu ki taimaka wane unguwa?
izzatu tace, kar na shiga lokacinku maybe you have something important to do.
jafar yace, karki ji komai inane?
izzatu tace, sharad’a pes 1, nagode sosai.
jafar yace, okay mune da godiya.
Tun lokacin da izzatu ta fara mgn safraz ya tsinci kansa a wani yanayi na jin dad’in muryanta hakan yasa ya d’aga ido ya kalleta ta glass itama a dai_dai lokacin ta kalli glass gaban mutar caraf suka had’a ido, safraz ya sakar mt murmushi itama ta maida masa da martini sai kuma gabanta ya shiga fad’uwa duf!duf magar gaskiya tsabar kyawun safraz sai daya firgita izzatu shikuwa har da gyara glass d’in sosai ta yadda zai dinga kallonta da kyau, izzatu kuwa sunkuyar da kanta ty k’asa domin ta gane kallonta yake tayi. 6angaren jafar kuwa duk yaga abinda safraz yakeyi dariya taso ta kwace masa awani 6angaren km murna yakeyi dan yaga alamun yarinyar zata samu shiga agurinsafraz dan yafi kowa farinciki idan hk ta faru domin babbar burinsa shine yaga safraz yasamu yarinyar da tayi masa yayi aure domin yammata sudena kawo masa hari ga safraz kuma baya kula yammata ammah yau dayaga sun wuce izzatu yaga safraz harda juyawa ya kalleta shiyasa yace masa su d’anyi baya.
A dai_dai k’ofar gida suka sauk’e izzatu, tayi musu godiya ta shifa gida.
Haushine ya cika jafar ganin,har sukayi sallama da izzatu safraz baiyi mt mgn ba balle ya k’ar6i number ta. hk suka tafi hanya jafar yana tayiwa safraz masifa shikuwa safraz kallon jafar yayi yana marairaice fuska yace, Ay kasan ni bansan ya akeyiba shiyasa na d’auka zakace mt wani abune shiyasa, jafar da haushi ya isheshi sai yayiwa safraz babza kamar be jisaba.
Abu kamar wasa safraz kwance kan gado ammah sam yakasa bacci, daya rufe ido izzatu yake gani hk kawai sai maganganunta su dinga dawo masa _kar na shiga lokacinku maybe you have something important to do_. A daren dai bai samu bacci ba hk ya kwana yana tinaninta, koda yagari ya waye suna breakfast cokali kawai yake juyawa a flat ba abinda yake ci, ba wanda ya fahimci halin dayake ciki sai mahaifiyar bayan kowa ya kammala Abbansu yayi sallama dasu ya fita, ya rage daga safraz sai maminsu da k’annansa shahida da shahida.
Mami tace, twins maza a tafi school karku zama late comers.
A tare suka mik’e, shahid ne yace, mami and big bro sai mun dawo.
mami tace, yauwa yaran kirki adawo lpy Allah ya taimaka.
safraz yace, pls try to study hard banda wasa sannan ku kulamin da kanku sosai and don’t forget the azkar.
shahida tace, big bro shahid is too much play with his friends by karatu yanxu.
safraz yace, lah! shahid kaifa d’an albarkane gaka yaron kirki why too much playing ?
shahid ya 6ata fuska sannan yace, big bro yarinyar nan fa joking takeyima.
shahida ta kwashe da dariya sannan tayi waje shima shahid yabi bayanta already driver yana jiransu a parking lot.
Mami ta kalli safraz tace, safraz what’s happening ne ng yau duk baka da walwala?
safraz yace, mami nothing gajiya ce kawsi.
mami tace, hym ay ba hk kakeyiba ko gajiyar ce to ma wai me kayi da zaka gaji ?
safraz yace, weather ce kawai mami ammah normal nake.
mami tace, baza dai kawai ka fad’amin ba if don’t share your problem with me whom you share with ?i am your mother your worries is my wworries
Or telling me your worries will not help matters ?
safraz yayi saurin kallon mami yace, nop mami ba hk bene .
mami tace, to menene.
safraz ya tattara nutsuwarsa ya kalli mami sannan yace, dama jiyane … ya kwashe duk yadda had’uwarsu da izzatu ya kasance ya fad’wa mami sannan yacigaba da cewa, mami shine fa too much thinking about her since yesterday i don’t know ?
dariya mami ta dingayi sannan ta kalli safraz tace, wallahi safraz kacika d’an fari yanxu baxaka iya yiwa budurwa mgn ba?
safraz sosa k’eya yayi yace, yace mami to me zance.
Dariya ta kuma yi sannan tace, to ni yanxu koyama zanyi ko ya?
safraz yace, ehmana mami.
Mami tace to tunda kaga gidansu yanxu abinda za’ayi shine kaje kayi wanka ka sanya manyan kaya ba wai court ba, kaje gidansu idan kaje bawai ita zaka k’iranaba a’a da mahaifinta zakayi sallama idan kuka gaisa sai kace masa kaxone idan baiyiwa ‘yarsa mijin ba kanason ya baka izini ka fara zuwa gurinta, to anan zai iya yiwuwa ba ita d’aya bace ‘yarsa budurwa idan yace wacce sai ka kwatanta masa ita, daga nan sai kaji me me zai cema idan ba’ayi mt mijinba to shikenan, daga baya sai ka fr binciken halayenta dama nagarta gidansu ammah idan anyimata to sai kayi hakuri domin haramne neman aure acikin neman aure. Idan kasamu ganin yarinyar bawai ka tsaya kana yimata wannan murmushinaka ba, idan kun gaisa sai kacemata dama tun dana gankine jiya sai naga kin burgeni Allah yasa kema hkne agurinki, sai kayi shuru kaji me zata ce idan kuma tayi murmushi kawai to kaima ka burgeta, sai ka fad’amata kai manufarka akanta itace aure bawai asha soyayyah ba. To my son sauran aykin saika k’arasa inamaka fatan nasara kuma na haneka da k’arya, sannan ka kiyaye kayi tsabtatacciyar soyayyah banda romantic kaji tsoron Allah watarana kaima ubane km baxaka so ayiwa taka ‘yar ba to saika kiyaye domin Annabi yace abinda kayi shi za’aymaka.
Safraz da murnansa yace, mami nagode this my mom da sauri ya matsa inda take yayi mata kiss a check d’inta duk farinciki ya cikashi ya rasa me zaiyiwa mami ya burgeta, sai kuma ya tashi kamar wanda aka tsikara da Allura ya nufi 6angarensa d’insa.
Sai daya shirya tsaf sannan ya fito a falon yakuma samun mami ammah duk sai yaji kunya ta kama sa, safraz yace, mami na tafi need your prayer.
mami tace, my son wish all the best !
mami bayansa tabi da kallo tana,murmushi, itama ta tsincin kanta acikin farinciki tana son taga safraz yayi aure sabida yana buk’tar kulawar mace ayanxu.
Kamar yadda mami ta fad’awa safraz hk yayi, mahaifin izzatu yayi matuk’ar farinciki km ya k’ar6esa hannu biyu domin izzatu ita kad’ai ya haifa baya barin kowa zuwa wajenta sai akan safraz yaji ya aminta dashi bai 6ata lokaci ba ya bashi izinin zuwa wajenta har cikin gidan yashiga ya gaida mahaifiyarta dukkansu sun amshesa da mutunci.
Mahaifin izzatu prof, Abdullah Abubakar professor ne, d’an salin jahar kano ne matarsa d’aya itace hajiya Rukayya, wato mahaifiyar izzatu, ‘yarsu d’aya itace izzatu mahaifinta yana da ra’ayin ‘yarsa tayi karatu akan yasa ko samari izzatu bata kulawa sai abin yaxama abin munafurci a unguwa ammah duk da hk hakan bai dami izzatu ba da iyayenta sunajin zagi iri_iri ammah sun toshe kunansu.
Prof Abdullahi, mutumne kamili kuma salihi bashi da abokin fad’a ammah mutane sun samishi ido, itama hajiya rukayya bata da shige_shige irin na mata hk ma izzatu dan ko k’awa bata shi a unguwar sai dai a shchool ammah suna zaune da mak’otansu lpy, izzatu yarinya ce me nagarta sai dai akwai sa idon mutane a kanata.
Safraz da izzatu soyayyah ce ta shiga tsakaninsu me tsananin k’arfi, zakayi tunanin sun dad’e a tare jafar kusan yafi safraz son kasancewarsa da izzatu.
Ba’a d’au wani lokaci ba aka saka ranar aurensu, sai alokacin ‘yan’uwa da abokan arziki suka san,da zancen.
Safraz d’ane ga Alhaji Hashim Muhammad, Alhaji hashim babban kusane a gwamnati ya rik’e matakai iri_iri wanda a yanxu yana d’aua dg cikin masu nemsn takarar gwammna a kano, Mahaifiyarsa safraz Hajiya maryam muktar babbar mace ce mai ilimi da dattko, safraz shine d’ansu na farko sai twins shahid da shahida,
Hajiya maryam tana da yayarta wacce itace ta rik’eta tun rasuwar iyayensu kuma su biyu kawai suka haifa sunanta momy Adama suna matuk’ar kama da hajiya maryam daka gansu kaga asalin fulani kyawawan asali.
momy adama tana da ‘yaranta mata guda biyu karima itace babban sai sailuba.
*************************************
Momy Adama ce zaune a falon hajiya maryam dagani ranta a 6ace yake ta had’e girar sama da k’asa,
Hajiya maryam ta kalleta tace, Aunty adama nima sai da akayi komai mahaifinsa yake sanarmin sunsa ranar auren safraz wata biyu wallahi bansaniba.
Maryam tunda d’ankinne ai dole kice hk kin nunamin bani da iko akan ‘ya’yanki, tun yaushe nake cemiki karima tana son safraz km na hanata kula ko wanne saurayi idan ta dawo sai su dai_daita kansu ammah kawai sai inji kwatsam wai safraz yana neman wata a can.
~Sannu_sannu kwana nesa muje zuwa page 4 yau da gobe batabar komai ba~👌🏻Hajiya maryam tace, Aunty adama shi yaga yarinyar yace yanaso kinsan mahaifinsa besan da zacen ba shi kanshi safraz kwanaki dana fara yimasa zancen yaje ya nemi karima cemin yayi shifa bayason ayimasa tallar mace yafison idan ya ganta da idonsa intayi masa to, ammah Aunty bawai bawai naki karima da auren safraz bane bugu da k’ari naga karima ta fita waje karatu shiyasa da safraz yazomin da zacen yaga wata yarinya ban hanashi domin maybe alokacin yake buk’atar auren.
Cikin 6acin rai momy adama tace, Au yanzu kariman ce anyi masa talla?yarinyar da maxa ke tururuwar zuwa wajenta ammah na hana nace ni d’ana zan bawa domin zumunci ya k’ara dank’o ammah ni safraz yayiwa hk ? wallahi tallahi indai safraz yak’i amince da za6ina to kuwa zumuncinmu yana daf da rushewa ko ke maryam na isa na fad’amiki kiji balle d’anki ko kin manta ni wace agareki ?
Hajiya maryam cikin raunanniyar murya tace, Aunty adama dan Allah karkice hk yara bazasu ta6a sawa zumuncinmu ya rushe karki manta mu biyune fa tak iyayen mu suka haifa bamu da kowa sai Allah yanxu me zaisa wani k’aramin dalili ya rabamu, In dai nice na haifi safraz to wallahi insha Allah sai ya auri karima ammah inason kimin afuwa kar a rusa wannan zancen neman auren nasa kiyi hakuri yayi auren bayan karima ta kammala karatun ta sai ayi musu aure alokacin.
Wani murmushi momy adama tayi tace, Hb ai sai yanxu naji mgn ammah nasan karima batason kishiya sai dai tayi hakuri, taya zanyi na d’auki ‘yata d’aya na bawa bare ammah idan safraz ne ko na mutu bani da wata matsala nasan zai rik’eta amana sabida ‘yar’uwarsace.
Hajiya maryam tace hk Aunty nima bani da burin daya wuce ng zumuncinmu ya d’ore har abada.
Daga nan suka cigaba da hirarsu, ammah zuciyar hajiya maryam a cunkushe take tunani takeyi kala_kala tasan,cewa karima sam ba irin matan da safraz ke so bane bugu da k’ari bata da wata tarbiya, wannan tunanin shike damu hajiya maryam.
******************************************
A 6angaren iyayen izzatu kuwa sunata shirye_shiryen biki, bikin ‘ya d’aya tilo awajensu komai na bikin na musamman ne har zuwa kayan da suka yiwa d’iyar tasu oder wajece masu kyau da tsada.
A yau takasance ana saura sati d’aya biki, safraz ne zaune shida hajiya maryam.
Safraz yace, mami meyasa zakimin hk ? ni bana santa bai dace na aureta ba mami ya aza’ayi ace bayan aurena da wata biyu kuma ace sai na k’ara yin wani auren, me zancewa izzatu ?auren soyayyah zamuyi da ita fa mami banyi mata adalci ba da munyu aure wata biyu na k’ara aure zansata a zargin mutane dole mutane zasu tsammanin wata matsalace da ita shiyasa zan k’ara aure , mami ki taimakeni kujanye wannan zancen bazan iya yiwa izzatu kishiya ba.
Mami itama da ranta yake k’una tace, safraz nice na haifeka na isa na saka abu kuma kayi wallahi nima ba’a son raina,hk zata kasance ba, umarni momynku ta bani kuma wallahi safraz baxan iya tsallake umarninta ba koda zan 6atawa kowa ita zan faranta mata sabida tamin halacci a rayuwa wanda ko da uwata tana da rai iya abinda zatamin kenan, naji kuma na yarda baka son karima ammah kayi hakuri ka sharemin hawayen dan Allah ba danni ba, ta k’arasa maganar tana matse kwallar dg idonta.
Da sauri safraz yasa hannunsa yana wiping d’in tears dg checks d’inta, shima duk hawaye ya cika idonsa yana cewa, hb mami meyasa zaki 6ata hawayenki mami duk abinda zaisaki farinciki a duniya zanyisa kinji, nothing is more painful to me then tears in your checks my mom, mami in kince na hakuri da izzatu ma zan hakuri sai na auri karima, insha Allah zanyi dukkan abinda kika ce.
Mami murmushin k’arfin hali tayi sannan tace, thank you so much my son, your are my pride i love you so much because you love me too, Allah ya maka albarka safraz ya yayima jagoranci, bance ka hakura da izzatu ba innayi hk ban damu da farincikinka ba Allah ya bk ikon rik’esu su biyu ameen.
Koda safraz ya koma d’akinsa komai dagule masa yayi izzatu kawai yakeji taya zai sanar da ita, besan sa’adda hawaye suka dinga bin idanuwansa ba duniya yaji duka tayimasa zafi, wani tunanine yazomasa, fita yayi ya nufi gidansu izzatu.
Yayi sa’a kuwa ya tadda baban izzatu a gida, bayan sun gaisa baban izzatu da kansa ya isar da safraz zuwa falon bak’i.
Safraz yace, Abbu ina so muyi wt mgn ne dama.
Abbu dayake niyar fita dg d’akin sai ya dawo ya zauna.
Abbu yace, safraz ina sauraronka, Dm tun daga wannan bakin naka nasan akwai mgn, ya k’arasa maganar yana dariya.
Anan safraz ta kwashe duk yadda dukayi da mami ya fad’awa Abbu dukda yadda yake matuk’ar jin kunyarsa.
Dogon numfashi Abbu yaja sannan yace, hak’ik’a safraz ka cika d’a km ka burgeni matuk’a, ka k’ara shiga raina na k’ara yin farinciki sosai sabida nasan wa nabawa auren ‘ya ta, umarnin iyaye abune me girma da km nauyin gaske ba kowa yake iya binsa ba, Ina maka addua Allah ya tayaka rik’onsu duka biyu, ina k’ara yima nisiha akan bin iyaye, sannan kuma karka fad’awa izzatu wannan mgn ko mahaifiyarta ka bari sai bayan biki domin mata akwai ‘yan zuga zasu iya lalata lamarin.
Safraz yy farinciki sosai hk ya tafi yana yabawa da hali irin na mahaifin izzatu, sai alokacin hankalinsa ya kwanta sannan har zuwa time d’in yanajin a ransa bazai iya zaman aure da karima ba sai dai kawai bayason mami ta shiga damuwa.
Karima dake can k’asar England tana,karatu sam bata da labarin safraz zaiyi aure tunanin ya k’are akan da ta kammala karatu ita zai aure kamar ance ta d’auki wayarta tayi connect d’in data ta duba twitter daga nan tayi facebook sai ta koma whatsAp kuma Hankalin karima ne ya tashi alokacin ta ta fara karanta wanu posting cewa _SAFRAZ HASHIM MUHD_ d’a ga Minister ilimi na jahar kano zaiyi aure ranar sunday wanda alokacin ya rage kwana biyune kacal, hankalinta ne ta tashi sosai ganin ko tantama babu safraz d’intane saima dataga hotunan safraz da izzatu dasuka biyo bayan sak’on alokacin numfashinta ya fr sama_sama kamar zai d’auke, cilli tayi da wayar ta fr farfasa abubuwan dake d’akin hardasu bedshit duk tabi ta yayyaga alokacin dai ta zama tamkar mahaukaciya sai data gaji dan kanta sannan ta fad’i gefe guda tana maida numpashi daga nan ta fashe da dukaka mai ban tausayi , wayan ta d’auko ta har had’a sannan ta fara neman number mahaifiyarta wato momy adama.
~Sunnu_sannu kwana nesa muje zuwa page 5 yau da gobe batabar komaiba~👌🏻
Kanta a sunkuye kunya ta kamata, “Da tasan zata shigo ta sameshi hk da bata shigoba” sai taji kamar ta koma da baya.
Shima safraz mamaki yakeyi ganin izzatu a d’akinsa ammah duk da hk yaji dad’in biyoshi da tayi dan sau da dama yana son zuwa d’akinta ammah sai ya kasa musamman idan ya tuna ganinta da yayi da wani najimin ammah ko kad’an har yanzu baiji zai iya hakura da izzatu saboda abinda ta aikata masa ba saima matsanancin sonta da kullum yake k’ara shiga zuciyarsa awani 6angaren kuma yana feeling d’inta kamar ya mutu ya rasa taya zai tinkareta bayan tayi mu’amala da wani bashiba idan ya tuna bazai sameta a budurwa saiji duk duniya tayi masa zafi.
A hankali ya zauna a gefen gadon yana binta da kallo har zuwa lokacin kanta yana k’asa a sunkuye. wani 6arin na zuciyarsa yana cemasa” anya bana cutar da izzatu ?laifin da tayimin ya kai na k’aurace mata hk inason izzatu a raina kamar ny hauka ammah daren aurenmu na farko na kama izzatu da k’warto a gida meyasa baxanyi hakuri na rungumi matata muyu rayuwar farinciki ba sai dai na kasa mantawa da abinda idanuwana suka gani”
Katse tunaninsa yayi da cewa, Izzatu !
A sanyaye ta d’ago kanta tace, na’am.
Sai ya rasa me zaice mata kawai sai yace, kina buk’atar wani abune ?
Izzatu tace, a’a um um inason muyi mgn ne dama ammah bari naje falo kafin ka gama.
Tana gm fad’in hk tayi sauri ta juya zata fita.
K’irjinsa ne ya fara dukan uku_uku a ransa yana tunanin “maganar me izzatu zata fad’amasa kodai zatace ta gaji da zama da shine hk’? hk kawai yaji ya damu kuma yaji zaman da sukeyi kamar lefinsa ne bata da wani laifi.
Cikin hanzari ya bita ya rok’o hannunta alokacin har ta murd’a hannun k’ofar zata fita.
Muryansa a k’asa_k’asa yace, muje ki tayani saka kaya mana Reality dm ko bakizoba yau zanzo gurinki in baki……
Sai kuma yayi shuru ya kasa k’arasawa.
Izzatu kuwa har cikin ranta taji dad’in abinda yace ammah tana cike da kunyarsa ji takeyi kamar tayi hugging d’insa ko zata rage kewar dad’ad’an kalamansa da tayi tun kafin suyi aure.
Kasa yimasa musu tayi hannunta yaja har gaban sif d’in kayansa sannan ya kalleta yace, za6amin kayan da zansa reality.
Sai data gama k’arewa sif d’in kallo sannan ta d’auko wata bak’ar T_shirt da breeches wato k’aramin wandon daya wuce gwuiwa kad’an shima bak’i.
Kallonta yayi yay murmushi yace, Nice colour reality, muje ki gyaramin gashin kaina ki shafamin mai sannan kisamin k……
Sai yayi shuru bai k’arasaba yana kallonta ta gefen ido.
Mamakine ya cika ran izzatu sosai gani takeyi kamar ba safraz bane a gabanta yake wannan maganar, ga kunyarsa da takeji musamman idan ta tuna abinda ya faro a first night d’insu.
gefen gadon ya zauna bayan ya kwaso mata abubuwan da zatayi masa amfani dasu.
mayukan ta d’auka tana dubawa tana karanta batare data tambayesa ba.
A hankalin take shafa masa mai ajikinsa tamkar wacce bata jini ajikinta, shikuwa safraz rufe idonsa yayi sun masa nauyi sam ya kasa bud’ewa har ta gama, sannan ta fara gyara gashin kansa dake kwance tamkar na jinjiri tana shafa masa mai d’aya bayan d’aya.
Na gama izzatu ta fad’a sai alokacin ya bud’e idonsa dasuka sauya dg fari zuwa ja, da ido ya nuna mata kayan,
Ringar ta d’auka ta fr k’ok’arin saka masa har ta gama sannan ta d’au wandon ta rik’e a hannunta kawai ta rasa yaya zatayi, zuwa can safraz yaji shuru sai ya bud’e idonsa yana kallonta, yanayinta daya gani ne yasa ya gane kunya takeji sai yasa hannu ya kar6a yasa da kanshi.
Mik’ewa tsaye yayi sannanya rik’e hannunta yace, zo muje in rakaki d’aki kiyi wanka ko zakaiyi a nan ?ya d’afa mt girarsa.
Murya k’asa_k’asa tace, Ban dad’e dayin wanka ba.
Safraz yace, Okay muje falo sai ki fad’amin maganar.
tare suka jera har zuwa babban falon, daf da daf suka zauna.
Zuciyar safraz tana cike da tsoron jin abinda izzatu zata fad’amasa sai zulumi yakeyi, tsoronsa d’aya kar ta furta abinda yake zargi.
Dan ya shashantar da maganar sai ya kalleta yace, madam nifa yunwa nakeji zo muje muci abicci sai muyi maganar dg baya kou?
Bata masa musuba ta tashi ta bishi tajin dad’in yadda suke a tare yau, tanaji a ranta “koma kawai ta fasa yimasa zancen da zata yimasa ammah wata zuciyar tana cewa a’a kiyimasa kikasani kou ya koma kamar da d’in” da hk suka isa deining itace tayi saved d’insa bata zubawa kantaba, Abinda yakuma faranta ranta a baki safraz yadinga bata har ya tabbatar ta k’oshi.
Bayan sun kammala safraz ya kalleta ammah duk da hk yanajin fargaba a ransa shi yanajin a ransa “zai manta da komai kamar ba’ayiba ya nunawa matarsa irin sonta dayakeyi” safraz yace, Reality ina saurarenki.
Izzatu da fuskarta ta nuna alamun damuwa tace, Dama inason in bk hakuri ne akan abinda ya faru, zaman da mukeyi ni dai hkn yana damuna kayi hakuri dan Allah.
Sai alokacin safraz yayi ajiyar zuciya daya tabbatar ba abinda yake tsammani zt fad’aba, yace, izzatu koni naso na danne namanta dashi ammah na kasa babu abinda yafi 6atamin rai da kikak’i yarda kin aikata kikace sharri ne, ammah yanxu kinyarda ?
Kwallace ta cika idanuwanta zuciyarta na bugawa da k’arfi tanajin rad’ad’i me zafi a ranta “Allah ya isa tsanina da duk wanda ya kullamin wannan sharrin, ya Allah ka bani mafita” izzatu ta fad’a a ranta.
Safraz yace, izzatu ina saurarenki ni wallahi idan kika fad’amin gaskiya babu wanda zan fad’awa idan kinajin tsoron ko zan fad’a i will keep your secret.
Wani 6arin na zuciyar izzatu yace mt” gara ki amince kinyi laifin akan ku ringa irin wannan zaman tunda yace bawanda zai fad’awa”
A hankalin ta d’aga idonta da suke cike da kwalla tace, am!kayi hakuri na yarda, sai ta fashe da kuka me ban tausayi.
A firgice ya d’aga idonsa ya kalleta nan da nan yaji jikinsa ya d’au rawa kanshi yana juyawa.
Itama kuka yaci k’arfinta atake taji kuma nadama tazo mata tafara dana sanin amsa laifin da batayiba.
_IZZATU DA TAKE BANI LABARIN HAWAYE NABIN IDONTA TA KALLENI TACE, RAMLERT AMSA LAIFIN DA BANYIBA WANNAN SHINE BABBAN *KUSKURENA* NAYI DANASANI MARA AMFANI.TACIGABA DA BANI LABARIN KAMAR HK……_
Idonsa sunyi jajajir fuskarshi a d’aure yace, meye amfanin hkn da kika aikata?dama kin kasance kinayi meyasa da kikayi aure bazaki hakura ba?izzatu ko dm bakya sonane?
Batace masa komaiba tacigaba da kuka tana takaicin amsa laifin da tayi.
Sai kuma taji zuciyarta ta dake kwata_kwata rayuwar auren ta fita a ranta.
Muryanta a dake tace, safraz bani da banki da zancema komai ammah dan Allah inason ka sauwak’emin na koma gaban iyayena hkn zaifi.
A afirgice ya kalleta ransa yayi matuk’ar 6aci cikin 6acin rai yace, harni zaki kalla kice na sauwak’e miki ?ke da yin laifi ammah ni da kika yiwa laifin bance zan sauwak’e miki ba sai ke?dama kinsan bakya sona why zaki yarda ki aureni ko kina nufin kin aureni ne dan ki dinga kawomin kwartayanki gidana ?Impossible wallahi, Kinason in sakeki kou?kibari zanyi tunani idan na,yankw hukunci zakigani *fasik’a* kawai. Yaja tsaki tare da buga table dake gabansa.
Hawaye nabin fiskarta tace, safraz nice fasik’a?karka k’ara cemin fasik’a niba fasik’a bace. Cikin sanyin murya ta fad’a tana kallonsa ido cikin ido.
A harxuk’e yace, nafad’a fasik’a kuma mazinaciya idan banda fasik’acin kafin kiyi aure kina aikata zina bayan kinyi aure mezaisa kiyi?wallahi izzatu kin cuceni idan badan darajar mahaifinki ba dana hakura dake idan yaso ciwon sanki ya kasheni ammah ina duba halin da iyayenki zasu shiga idan suka sani ‘yarsu dy tilo abinda takeyi, kin bani kunya sun d’au son duniya sun d’oramiki ammah kinci amarsu tir dame hali irin naki izzatu.
Yana gm fad’an hk ya tashi ya bar gurin ya wuce d’akinsa.
Kasan tile izzatu ta zube tana kuka me d’aga hankali da ban tausayi, ta dad’e tana kuka har kanta ya fr ciwo dan kar masu aiki su shigo kwashe kayan dasukaci abinci su ganta yasa ta tashi da k’yar tawuce d’akinta.
Safraz yana shiga d’akinsa ya fad’a gado shima kuka yayi sosai har ya gode Allah, sai da kukan nashi ya lafa sannan ya tashi zaune, sai kuma alokacin ya fr danasanin abinda yayi mata tausayinta ya kamashi kamar yaje ya bt hakuri sai km yaji bazai iyaba.
Izzatu meyasa zakimin hk?inasonki kamar na mutu why do that to me?dm bakicemin kinyarda ba dama kinkuma cemin sharri akayi miki, Yazanyi da raina Allah hk kaso ka ganni, hk safraz yadinga sambatu shi kad’e har bacci ya fr d’aukarsa.
Karima ce dg can england rik’e da waya a hannunta tana magana:
haba momy ni wallahi na gaji da gafara sa banga k’ahoba yanzu fa harsunyi wata d’aya dayin aure ammah shuru babu wani labari.
momy tace, nima dai abun ya d’auremin kai sosai ammah da masu aikin sun sanarmin kamar basa zaman lafiya dan tun safe yake fita by dawowa sai yamma kinga babu wani zaman lpy a tsaninsu ni a tunanima yarinyar nan ba hk ta barsaba ta asircesa ammah idan banda hk ya kamata da k’warto ammah har yanxu suna tare.
karima tace, momy yanxu to yaya za’ayi?saura baifi wata dy ba na kammala karatuna yanzu hk saura 5 days musamu hutu na 3 weeks sannan mu dawi muyi final exam. yanxu zanzo nayi hutu ns 3 weeks a nigeria inason kafin na dawo ayi waje da ita gaskiya.
Momy tace, ki kwantar da hankalinki koda bata ft ba idan kika shiga zan fad’amiki yadda zakiyi ki fidda ita, nizanfi so idanma kinzo hutun kawai a d’aura auren idan yaso sai ki koma kiyi exam d’inki idan kin dawo saiki tare kou?
karima tace, Wow!wallahi hkne momy shiyasa nakesonki sosai fa!momy sai naxo kawai.
A dai_dai lokacin sakina tashigo falon momy hkne yasa momy ta kashe wayar dan kar taji mesuke cewa.
sakina ta kalli momy tace, momy nasa da aunty kuke waya kou?wai momu haryanxu baku hakura da zancen safraz bane?ni dai har kullum ina k’ara fad”a muku kuji tsoron Allah. yanxu idan akayiwa big bro dole ya auri aunty kina tinanin za’ayi zaman lpy kuwa?wallahi matarsa me mutunci bata da fitina ammah aunty fa masifa tayi mt yawa zata dinga kawo rigima iri_iri.
Momy cikin tsawa tace, ke!zancimiki wallahi sakarya kawai sha_shar banza, karna k’arajin wannan zancen a bakinki kona 6atamiki rai wallahi.
Sakina tace, Allah ya baki hakuri momy ban fad’a danna 6atamiki raiba.
Momy taja tsaki sannan tace, tafi can kibani waje sai iya ladabi kamar gaske, nawa kika samu ciromin ?
Momy bank d’in da layi saosai shiyasa na dad’e ammah abin yaban mamaki sosai me akayi da million d’aya momy ?yaushe aka cire?
momy tace, babu ruwanki bani sakona.
Kud’in ta mik’amata sannan tace, yauwa momy yau na had’u da kawu a banki yace na gaisheku, yana tacemin sailuba!sailuba ammah sam bangane da ni yakeba sai da wasu sukamin mgn.
momy tace, hym!muna amsawa.
sakina takuma cewa, yauwa momy meyass akadena k’irana da sailuba aka kuma sakina?
Momy tace, Dangin ubankune da wannan kinibibin da tsohon cikinki babanku yarasu bayan na haife sukace wai asamiki sunan ‘yar autarsu sailuba nikuma naga bsbu wanda yamin rainon cikinki balle rainon goyo shiyasa nake k’iranki da sunan da na za6a bawai za6insuba.
Sakina tayi murmushi tace, kai momy ai da kin barsu da ba’a rabamin sunaba.
momy tace to uwata. tare da harararna, ni tashi ki d’aukomin jakana driver ya kaini gidansu shahida.
***
**
*
Karima dake zaune ita da wata k’awarta aminiyarta fauzan, alokacin da karima ta gm waya sai fauzan ta kalleta tace,
wai ya ake cikine ?
karima ta kwashe duk sharrin da suka lak’anawa izzatu ta fad’awa fauzan, sannan ta k’ara da ceea, ammah kinsan me?haryanxu bai saketa ba tanan a gidan munafuka.
fauzan tayi dariya tayi shewa tace, lallai ke wawuya ce waya fad’amiki hk ta barshi ai tini ta gm dashi da asiri, idan zakice zaki jira sai ta ft sannan zaki shiga to ai kin tabka babban *KUSKUREN* ai kawai malama tunda har kinsamu za’asashi ya aure dole to ki shiga kawai inyaso k’yasan yadda zakiyi dh baya ammah idan kika tsaya kallon ruwa to kwad’o zai miki k’afa.
Karima tace, hkne fa kou?sis
**************************
Rayuwar izzatu abin tausayi komai yakuma jagulewa babu abinda yake had’ata da safraz
Momy tace, Dangin ubankune da wannan kinibibin da tsohon cikinki babanku yarasu bayan na haife sukace wai asamiki sunan ‘yar autarsu sailuba nikuma naga bsbu wanda yamin rainon cikinki balle rainon goyo shiyasa nake k’iranki da sunan da na za6a bawai za6insuba.
Sakina tayi murmushi tace, kai momy ai da kin barsu da ba’a rabamin sunaba.
momy tace to uwata. tare da harararna, ni tashi ki d’aukomin jakana driver ya kaini gidansu shahida.
***
**
*
Karima dake zaune ita da wata k’awarta aminiyarta fauzan, alokacin da karima ta gm waya sai fauzan ta kalleta tace,
wai ya ake cikine ?
karima ta kwashe duk sharrin da suka lak’anawa izzatu ta fad’awa fauzan, sannan ta k’ara da ceea, ammah kinsan me?haryanxu bai saketa ba tanan a gidan munafuka.
fauzan tayi dariya tayi shewa tace, lallai ke wawuya ce waya fad’amiki hk ta barshi ai tini ta gm dashi da asiri, idan zakice zaki jira sai ta ft sannan zaki shiga to ai kin tabka babban *KUSKUREN* ai kawai malama tunda har kinsamu za’asashi ya aure dole to ki shiga kawai inyaso k’yasan yadda zakiyi dh baya ammah idan kika tsaya kallon ruwa to kwad’o zai miki k’afa.
Karima tace, hkne fa kou?sis
fauzan tace, ni na d’auka ke wayis ace dod’isce mtsss
Hk suka dinga hirarrakinsu du akan izzatu.
**************************
Rayuwar izzatu abin tausayi komai yakuma jagulewa babu abinda yake had’ata da safraz ko giftawarsa ma yanxu tadena gani sai dai wani lokacin taji motsacinsa hk sukeciki har tsawon sati d’aya, kusan kullum sai tayi waya da iyayenta ammah bata bari sun fahimci tana wt matsalaba, sakina da shahida suna zuea mata sosai sun shak’u da ita sosai wani lokacin harda shahid, yanxu harta saba da rayuwarta a hk ta rage damuwa wani lokacin tayi kallo ko cht hkm k’awayenta suna kawo mt ziyara duk da ba wasu k’awayene da itaba dg sumayyah, Aisha sai firdausee k’awayenta ne na university.
Izzatu tana zaune a falo tana kallon tashar TV ta Arew24 sai jin sallamar mami tayi, zuwa tayi ta tarota cikin farinciki da jin dad’i,
Bayan sun gaisa ta kawowa mami kayan motsa baki, sun dad’e suna hira sannan mami ta kalli izzatu tace,
izzatu nazone inason muyi wata magana.
Dub!k’irjin izzatu ya buga, “kar dai safraz ya fad’awa maminsa abinda ya faru”? izzatu ta fad’a a rabta.