KWAI CIKIN KAYA CHAPTER A BOOK2

 KWAI CIKIN KAYA CHAPTER A

                   BOOK2

Typing📲

              ƘWAI cikin ƘAYA!!

                     Bilyn Abdull ce🤙🏻

Assalamu alaikum, barkanku da wannan lokaci, barkanmu da sake dawowa filin daga, insha ALLAHU zan cigaba da littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA kamar yanda na fara, inafatan haɗin kai daga gareku, haɗin kan kuwa shine tsaftataccen Comments da zai iya zaburar dani akan abinda nake rubutawa, masu ɗaukar littafi su ɗaura a youtobe wlhy wlhy na rantse duk wanda ya ɗauramin ƙwai cikin ƙaya a youtobe kar yay kuka dani akan matakin da zan ɗauka yay kuka da kansa. Masu cewa kuma na maida littafin na kuɗi kudaina yimin ƙarya, inda naso hakan da tun a 1 zance na kuɗine. Masoya kumuje zuwa, yanzu za’a fara wasan😉🤓.

14

BOOK TWO

         (1)9

…………Kowa yana cike da murnar dawowar aunty Shahudah a gidan amma banda ni, ba komai ya jawo hakanba kuwa sai irin tarbar dana samu daga gareta bayan dawowata aiki a randa ta dawo.

     Cikin ɗokin ganinta da kewa na nufeta, amma saita kalleni cikin wani yanayi na wulaƙanci da ƙyama kamar yanda ta sabamin a baya, daga ƙarshe ta koma dariyar aikina. Hakan ba ƙaramin ciwo yayminba, musamman yanda naga harsu Mom sun biye mata suma suna tayata dariyar. Daurewa nai nima na tayasu, dan na ɗaukama kaina alƙawarin insha ALLAHU sun daina ganin raunina a yanzu. Sai da muka gama dariyar sannan na nufi ɗakina nabarsu, su Aunty Aamilah na bata labarin yanda akai nazama dss a yanzu.

      Ina shiga ɗakina na faɗa saman gado na fashe da kuka, tabbas wulaƙanci bashida ƙyau sam a rayuwa, ƙasƙanci ga mutum abune mai muni, amma a wannan duniyar babu abinda mutane suke alfahari dashi kamar ƙasƙanta ɗan uwansu musulmi.

      “Sai kaga mai dukiya yana ƙasƙanta talaka koda da magana ne, mai ilimi na ƙasƙanta marashi, mai mulki na ƙasƙanta mabiyansa, miji na ƙasƙanta iyalansa, ɗan uwa na ƙasƙanta na ƙasa dashi. koyaya mutum yafi wani saikaga yana hura hanci wajen ganin yayi tozarci ga wanda bai kaisaba, kaicon mutane da wannan ɗabi’a, kamanta ALLAHN daya baka shima bai manta da shiba, sannan badan ka fisaba ya baka shi ya hanashi, ikonsane wannan yabama wani ilimi yayi wani jahili, ya bama wani dukiya yayi wani talaka, ya bama wani haihuwa yayi wani babu ɗa, ya bama wani mulki yayi wani mabiyi, ya bama wani lafiya yayi wani mara lafiya, kowa a rayuwa akwai jarabawarsa, kaine wane bashike nuna kafi kowa ba, kai ka samu kaza ko kake da kaza bashike nuna ALLAH yafi sonka ba, nima ALLAH yana sona, kuma ina sake gode masa da yanda yayini aunty Shahudah…….”5

        Tun daga wannan ranar na sake jabaya ga kowa da komai na gidan, Dad dama bai dawoba, hakama Yah Qaseem yayi tafiya tun washe garin dawowar aunty Shahudah gidan. ko a wajen aiki bani da wata walwala, Ummie da wasu abokan aikina sai suka danganta rashin walwalar tawa da kewar Yah Qaseem da bayanan, dan zuwa yanzun mutane da yawa sun san alaƙar dake a tsakanina dashi.

       Ni kuma a ɓangarena ba damuwar rashin yah Qaseem bane da lamarin gidanmu kawai kecin raina, akwai wani abu daban danaketa ƙoƙarin tureshi a raina, dan bana fatan gaskata zancen zuciyata koda da wasa kuwa.

★★★★★★★★

         Yau data kasance juma’a dai-dai da dawowar aunty Shahudah da kwanaki huɗu Dad shima ya dawo, kowa yay murnar dawowarsa tamkar yanda muka saba, ya kuma samu tarba daga matarsa harma da Aunty Shahudah dake ganin wannan dawowar tatace. Nidai ina daga baya-baya dukda jana a jiki da Dad keyi, dan motsi kaɗan ya sako sunana a cikin zancensa, hakan na kula baƙaramin sosa zuciyar Aunty Shahudah ya keyi ba, hakama Mom. Dana kula abin zaiyi tsamari saina zare jikina na gudu ɗaki, dama dai muna zaune ne muna cin abincin dare.

     Ban sake yunƙurin fitowaba kuwa har safiyar washe gari domin nima naji a raina yakamata na basu waje su gana da mahaifansu. duk da kasancewar asabar ce babu aiki ban iya komawa barci ba, dan narigada na saba yanzu da yanayin tashin sassafe. Ina zaune akan abin sallah tun bayan idar da sallar asubahi ban tashiba, na lazimci azkar nai karatun Qur’ani, rashin abunyi ya sakani tashi nahau gyaran ɗakina, hakan sai ya jani tsayin lokaci har kusan tara da wasu mintuna.

       Sama-sama nake jiyo hayaniya kamar na kuka, kukan kuma yaymin kama da muryar Mom. Nai azamar ajiye tawul ɗin dana ɗauka zan shiga wanka na fita. Sosai gabana ya faɗi saboda cin karo da Mom dake kuka iyakar ƙarfinta, Dad na riƙeta, daƙyar na iya haɗa maganganunsu, daga ƙarshe na fahimci ƙanin Mom ɗine ALLAH yayma rasuwa mai suna Usman, tabbas naji suna yawan faɗar sunan Uncle Usman, sai dai ban sanshiba, ban taɓa ganinsaba, dan duk zamana a gidan ban taɓa zuwa gidansu mom ɗinba, bankuma cika ganin ƴan uwanta suna zuwaba, kowa dai yasan halin wasu ƴan bokon nan da aƙidar rashin son takura.

      Nima dai tausayin Mom ya sakani bin sahun masu sharar hawaye, nan dai Dad ya cigaba da lallaɓata, kafin yajata sama, muma yace duk mu shirya domin tafiya can gidan. Hakanne ya saka kowa nufar ɗakinsa mu duka.

STORY CONTINUES BELOW

______________________________

            A daren jiya juma’a misalin ƙarfe sha biyu da wasu mintuna mummunan labari ya iso gidansu Jawaad, cewar Uncle Usman ya samu haɗarin mota a hanyarsa ta dawowa daga tafiyar da yayi ta kwanaki biyu.

        Lallai wannan gida sun fuskanci tashin hankali na bazata, dan bayan mahaifin Jawaad basu ƙara rasa ko ɗaya a cikinsuba, kaf ƴaƴan malam Yusif Abdul-aziz ne kawai ALLAH yayma rasuwa. Saiko shi malam Yusif ɗin da matarsa ɗaya sai mama maryam, idan ka cire waɗanan huɗun sauran duk sunada ransu, saima yaɗuwa da suka sake yi saboda haihuwar jikoki harma da tattaɓa kunne.

         Ruɗanin da mama Atika ta shigane ya sakata yanke jiki ta faɗi, dan abune da tunaninsu bai taɓa kawo musuba anan kusa duk da sunsan mutuwa tabbacice ga duk mai rai, ba Uncle Usman ba ko ita kanta data tsufa sosai bata tuna mutuwar zata iya ɗaukarta a yanzu balle shi da ayanzune ake ƙara shiryama duniyar filin zama.

          Lokacin da gidansu Jawaad ke cikin wannan ruɗanin shi yanacan suna gumurzu da wasu gungun ƴan ta’adda da suke fako tun kusan sati uku da suka shige, sai a yaune ALLAH ya basu nasarar yin fito na fito dasu, sun sami nasarar kama wasu a cikinsu, yayinda wasu suka gudu.

       Kusan ƙarfe huɗu na dare suka iso station ɗinsu da waɗanda suka cafko, sunyi tiɓis da gajiya, ga yunwa dake cin hanjinsu ta bala’i ma kuwa, sai dai jarumtarsu da juriya mai haɗe da trianing ɗin da suka gogu a ciki duk ya ɓoye gazawarsu. Rose cema dai kawai ta kasa juriyar kasancewar ƙarfin zuciyar mace dana namiji ba ɗayaba, dukda itama ta cancanci a kirata jarumar kuwa, Jawaad ma baiso akai aikin da itaba, amma ta matsa akan sai taje, badan yasoba ya barta ta bisu.

          A station ɗin suka ƙarasa kwanan, washe gari safiyar asabar ana idar da sallar asuba Jawaad ya kira gimba akan yazo ya ɗaukesa. Yanda yaji muryan gimban ne ya bashi mamaki, cikin yanayin gizagonsa yake jefa masa tambayar lafiya?.

         Sanin halinsa baya son ɓoye-ɓoye a magana ya saka Gimba faɗa masa gaskiyar tashin hankalin da ake ciki a gidan nasu.

      Dukda halin da yake ciki da matsalolin dangin mahaifin nasa hakan bai hanashi shiga ƙololuwar tashin hankaliba, a take ya birkicema su Jabeer, waɗanda suma jin rasuwar tai bala’in sakasu a ruɗani. Basu wani ɓata lokaciba suka nufi gidansu Jawaad ɗin kai tsaye, duk da halin gajiya da buƙatar hutun da suke a ciki. Sun iso gidan ƙarfe kusan bakwai da wasu ƴan mintuna, hankalin Jawaad ya sake tashi sosai ganin halin da ahalinsa ke a ciki, tuni ya manta da gajiyar dake tattare dashi.

      Bai zaunaba su Uncle Nasir suka jashi zuwa asibitin da gawar Uncle Usman take domin su amso, abinda yasa ba’aje tun jiyaba saboda ba’a nan cikin gari bane, inda ya baro yafi kusa da inda yay haɗarin, shiyyasa aka  maidashi asibitin can garin.

★★★★★★★

       Ƙarfe goma da wasu mintuna muka iso gidansu Mom, katafaren gida na alfarma da ƙawa, dukda cikin tashin hankalin mutuwa mukazo hakan bai hanani mamaki da jinjina dukiya irinta wannan ahaliba, lallai dolene su aunty Shahudah suyi wulaƙanci yanda sukeso, kaga gida tamkar ba hannune ya ginashiba, harabar gidan kawai naganimafa kenan, sai mutanen gidan da zakaima kallo ɗaya ka fahinci ƴan bokone na haƙiƙa tun zamanin da boko keda tsada da daraja kuwa……

      Ina cikin wannan tunanin ne nafara jiyo ƙarfin koke-koke na ƙaruwa, babu shiri na dawo hayyacina, a sannanne na lura ashe an iso da gawar mamacinne.

     Har ciki sosai Ambulance ɗin dake ɗauke da gawar ta shigo, ta tsaya dai-dai sashen danaji wasu na ambata da sashen mama Atika mahaifiyarsu Mom. Zuciyata tai masifar harbawa saboda ganin wanda ya fito daga Ambulance ɗin.

     Cikin tsagwaron mamaki na furta “Boss kuma anan?” akan laɓɓana, kamar yanda nakejin zuciyata aduk sanda ta samu kusanci dashi yanzunma bata canja zaniba, dole na shiga karanto addu’a gudun kar nayi abinda zai jawo hankalin mutane a kaina.

     Nayi nisa a tunanin da har aka fidda gawar ban saniba, saida suna gab da shiga sashin ne nakai idanuna kansu tare da sauraren koke-koken mutane, su biyune kawai ke ɗauke da gawar a mankara, tana lulluɓe da farin ƙyalle da yay face-face da jini, alamar dai mamacin ya bugu sakamakon Accident ɗin da yayi, nantake sai zuciyata tai rauni saboda tunowa da mutuwar nawa mahaifin, sai kawai na durƙushe a wajen na fashe da kuka mai cin rai da zuciya.

STORY CONTINUES BELOW

          Isowar gawarce ta saka gidan ya kuma cika sosai, koke-koken da akeyi ya sake ƙaruwa, ban kuma ganinsaba kuma har aka sake fitowa da gawar kusan sha biyu na safe, da alama dai yanzu an masa sutura za’a miƙashi gidansa na gaskiyane. Wani da nake ƙyautata zaton ɗansane ya rugo da gudu ya riƙe mankarar da aka ɗakko yana kuka da roƙon su ajiye masa Dadynsa, yarone da bazai gaza shekaru sha uku ba a duniya, sai ƴanmata guda biyu da zasu iya kawai 23 da 20 suma sukazo suka riƙe. Hakan ya kuma tada hankalin jama’a, ni kaina sunyi masifar bani tausayi, suma kenan da suke da gatan dangi dana jin daɗin rayuwa, na tuna sanda baba ya tafi ya barni, har aka binnesa ma ni bansan ina nawa hankalin ya keba.

      Na share ƙwallar dake gudu bisa kumatuna, dai-dai isowarsa, wajen da alama yanzune ya fito, shine ya janye yaron ya rungumesa a jikinsa yana bubbuga bayansa, hakan ya saka ƴan matanma sakin mankarar suka durƙushe a wajen suna kuka. Bai saki yaronba har saida aka fita da gawar, ya shafa kansa yana ɗago fuskarsa, babu wanda yasan miya faɗama yaron, amma kowa ya kula magana yay masa kafin ya sakesa ya fice shima zuwa waje inda za’a sallacesa.

          Tashin hankalin da ake cikine yasa ban samu damar tunanin alaƙar gidan da boss ba sam, bankuma sake ganinsaba, sai dai ganin nasa da nayi yana nan daram a zuciyata, dan kwanaki kusan shida kenan ban gansaba ko’a office, tun fitar da sukai ranar sai yaune na ganshi. A mamakina sai naji raina sakayau, bakamar yanda na tsinci kaina cikin ƙunci ba a kwanakinan.

★★★★★★

           Tun bayan zuwanmu gidan ban sake sanya ƴan gidanmu a idonaba, har zuwa yanzu da aketa hada-hadar sallar azhar da cin abinci, garama dad bayan sun dawo daga binne gawar ya shigo cikin gidan shi da wasu manyan mutane sunyi gaisuwa, daga haka ban sake saka ko ɗaya a cikinsu a idanunaba.

        Mutane nata shiga sassan gidan domin gabatar da salla, sai dai ni narasa ina zan dosa koda na tashi, waɗanda nazo dominsu ban sake ganinsuba, ina zan shiga nikan nace zanyi salla? Tunda babu wanda ya sanni babu kuma wanda na sani.

      Ina nan zaune ina saƙa mai fishsheni a zuciya budurwar dake zaune a kusa dani ta miƙomin jakkarta da waya akan na riƙe mata tana zuwa, kamar zanyi magana sai kuma na amsa ina maida mata murtanin murmushin da takemin, ina zaune a wajen ban motsaba nai uban tagumi harta dawo.

        Na miƙa mata kayanta, ta amsa tana min godiya, harta tafi sai kuma ta dawo da baya idonta a kaina.

      “Ƴar uwa kozaki taso muje muyi sallane? Naga kowa na harama amma ke koma motsi bakiyba, ko dai kina hutune?”.

        Murmushin yaƙe naimata, sai dai ban motsaba, nace, “Karki damu zan nema waɗanda mukazo tare sai nayi a wajensu”.

         Tai ɗan shiru tana kallona, kamar bazata tankaba, dan harna fara murnar ta barni, sai na tsinkayi muryarta tana faɗin, “Yanda mutane ke cike a gidannan kafin ki ganosun ai kin wahala, sannan duk inda zakiy salla a gidannan yau bazai kai nutsuwar inda zamujeba, dan sashen yaya ne kawai nasan babu mutane, indai ba kina tsoron karna saidaki bane”.

     Ta bani dariya, amma sai banyiba saboda yanayin da ake ciki, sai kawai na miƙe batare danace komaiba, dan na lura akwaita da surutu.

      

      Tun shigowarmu sashen na yarda da zancenta, dankuwa tsit yake babu wata hayaniya anan, tamjar ba cikin gidan yakeba. Sai wani daddaɗan ƙamshi daya shige mini hanci, batare dana shiryaba na shaƙa na haɗiyeshi cikin maƙoshina, karon farko a rayuwata da naga falon da yafi na gidan Dad ƙyau da tsari, ada tunanina yana bani babu gidan da yakai na Dad haɗuwa da tsaruwar kayan alatu, dan dukkan gidajen iyayen su Ummie basu kai na Dad ba, amma a yau dana tsinci kaina cikin wannan aljannar duniyar duk sai na raina wancan alfaharin nawa, yanda aka ƙawata matattakalar benen dake falon kawai abar kalloce ga mai kallo duk wayewarsa kuwa. Ban gama bama idona abinciba budurwar taja hannuna zuwa wani ɗaki, mun iske mutum uku suna salla, sai ɗaya data fito daga bayi da alama alwalar itama tayo, sai wata kwance a kan gadon dake ɗakin da yara biyu suna kallon waya. Duk suka zubomin ido na rashin sani, wadda ta fito daga bayice tace, “Wai ina kikajene haka Nabeelah? an aika Ammar ya kiraki amma yace bai gankiba”.

        Hannuna ta saki tana saɓule jakkarta dake a kafaɗa, “Babu inda najefa Aunty Hanifah, ina can jikin sashen Uncle Sulaiman zaune, nima yanzu saida na leƙo naga kuna nan sannan ai na taho”.

       Batace mata komaiba, hakanne ya sakani gaisheta dan naga babbace ta girmeni, na juya ga wadda ke a saman gadon tare da yara itama zan gaisheta sai tai saurin gaisheni. Murmushi kawai nayi, dan ita zan iya girmarta, suma yaran sai suka gaidani, na amsa musu da kulawa ina tambayar sunayensu. Namijin yace Ammar, macen kuma Islam. Yaran sun birgeni, gasu masu ƙyau. Wadda muka shigo tare da aka kira da Nabeelah ce tace min na shiga bayin nayo alwala, cikin tsokana take faɗin “Karnayi abin kunya gashi bansan sunan ƙawar tawabama”.

      Ƴar dariya nai babu shiri, ina ƙoƙarin shigewa nace mata sunana Bilkisu. A tare naga duk sun kalleni suna ɗora hannu a bakunansu, hakama biyu a masu sallar da suka idar suma suka juyo suna kallona. Yanda naɗanyi diri-diri na alamar shakkune ya saka ɗaya a cikin waɗanda suka idar da sallar babbar mace tai murmushi da cewa “Mai babban sunace ashe”. Numfashi na sauke a hankali kafin na gaisheta cikin risinawa, ta amsamin tana sake faɗaɗa dara’ar fuskarta, kafin tace naje nai alwalar kar lokaci ya ƙure. Shigewa nayi bayin nima da tunanin ko sunan waye nasu Bilkisun? Daga gani kam dai suna girmama mai sunan sosai.

     Ina fitowa Nabeelah ta shiga, suma duk sun tashi daga abin sallar alamar sun bamu waje, sai wadda muka iske tayo alwala kawaice ke salla a wajen, na gaida sauran biyun da bamu gaisaba suma sannan na kabbara sallata.

        Bayan mun idar da sallar a cikinsu babu wanda ya tambayeni game dani, sai dai sunata ƙoƙarin sakoni cikin hirarsu wadda duk ta karkata ga mai irin sunana danaji manyan na ambata da Yaya Bilki, yaran kuma na kiranta Mah-mah Yanda suke hira akanta cikin damuwa da kewane ya sakani tunanin ko bata da raine? Bani da mai bani wannan amsar, dan haka na haɗiye abina cikin rai ina cigaba da saurarensu….

          Kusan mintuna talatin ina sauraren hirarsu mai cike da birgewar kasancewarsu ahali ɗaya, kafin na miƙe domin tafiya, dan ya kamata naje na binciki inda su Mom suke koda su basu damu da nemanaba.

     Duk kallona sukai cike da alamar tambaya.

      Murmushi nayi, nace, “Zanjene kar abokan tafiyata suyita nemana”.

       Suma duk murmushin sukaimin, Nabeelah ta miƙomin wayarta tana faɗin, “To sakamin Number ki muke zuminci, danni dai nayi ƙawa daga yau”. Ban musaba na amsa wayar tata fuskata har lokacin da murmushi, na saka mata Number ta ina miƙa mata wayar, wadda naji suna kira Aunty Batool tace, “Lallai kin jajubarma kanki kuma Ummien mu, dan shegen surutun Nabeelah takai a guji ƙawance da ita, gaki keman daga gani bakida yawan magana”.

     Sanin dani take yasani faɗin, “Aunty ai sunfi daɗin ƙawance irinsu Nabeelah”.

     Atake kowa ya shiga faɗin a’a-a’a, yayinda Nabeelah keta ƙoƙarin kare kanta, niko ina musu dariya. Godiya na sake musu kafin nai musu sallama.

       Zuciyata tai wani irin harbawa lokacin da akai knocking ƙofar ɗakin tare da sallama cikin wata irin sassanyar murya dake nuna mai ita yana a matuƙar gajiye, tattare da tsagwaron damuwa.  Akusan tare suka amsa, nikuma na janye hannuna dana ɗora akan mariƙin ƙofar cike da fargaba, ban gama tattara fahimtata waje gudaba aka turo ƙofar aka shigo, kaɗan ya rage ya bugeni, nai saurin ja baya kaɗan dan na bashi hanya sosai.

       Idanunane suka fara sauka akan ƙyaƙyƙyawar ƙafar da baƙin wandon jeans ya sake haskawa, jijjigar da zuciyata keyine ya dasamin tsoron yarda da hasashena, dan haka na kasa ɗago idona naga wanene? Dukda ƙamshin turarensa ya nema saka zuciyata faso ƙirjina ta fito……

      Ganin yaƙi shigewa ya bani hanyane ya sakani ɗago idanuna a hankali nakai dubana gareshi, a lokaci ɗaya idanunmu suka shige na juna saboda shima dai-dai ya kalleni. Naɗan sake ja da baya na alamun mamakin sake ganinsa anan, amma shi a mamakina sai naga ya janye nasa idanun babu wani alamar mamakin ganina da ya nuna.

      Yanda naji su Nabeelah na rige-rigen gaishesane ya sakani aro jarumta nima nabi layinsu na gaidashi, sau ɗaya ya amsa mana tare da amsa ta’azziyar da mukai masa ya ƙarasa ga iyayensu Nabeelah, hakanne ni kuma ya bani damar saurin ficewa cike da sassarfa daga ɗakin……….✍🏻

2

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.13

Alhmdllh inama kowa fatan alkairi, nakumaji daɗin wannan tarba, naso ace zan iya jurewa na biku ɗai-ɗai na amsama kowa Comments ɗinsa, sai dai nace kuyi haƙuri, kamar yanda matsalan ido ta dakatar dani da typing dolene yanzuma na ringa lallaɓawa saboda kunada ɗunbin yawa, akwai group insha ALLAHU da aka buɗe a shafin manhajar Telegram, masu amfani da wannan shafi su maza su garzaya idan suna buƙata, domin canne zai zama dandalin tattaunawa akan littfin ƙwai cikin ƙaya da sada zuminci, duk mai karatu yana buƙatar dandali na tattaunawa akan littafi, dan da yawanmu hakan na bamu nishaɗi da sake fahimtar da mu abinda bamu fahimtaba, kuma yana ƙarama writer ƙarfin gwiwar typing koda batai niyyar hakanba, ku maza kar a baku labari. Zakuna samuna koda yaushe a can domin ku tabbatar ina tare daku, masoyan bily kuma na isar da saƙonku gareta akan ta daina tsoron jay😂, masoyan Shahudah tana miƙo muku gaisuwa itama🤓.+

https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g20

Wannan shine link ɗin group namu mai suna MASARAUTAR BILYN ABDULL A manhajar Telegram😘😘.

7
2
…………..Koda na fito daga ɗakin saida na huta a falon saboda yanda zuciyata ke mutsu-mutsu a cikin ƙirjina, ina matuƙar mamakin wannan al’amari dake yawan faruwa tsakanina da mutumin nan, na kuma rasa wazan tunkara da maganar halin da nake tsintar kaina akansa kozan samu fashin baƙin saɓanin wanda zuciyata ke kissima min, nidai nasan ba tsoronsa nakeba, to minene dalili? Wannan amsar nake neman mai bani.
        Gwiwa a sage naja ƙafafuna na fice daga sashen zuwa harabar gidan. Yanzunma dai ban sami ko ɗaya daga cikin su aunty Aamilah ba, gashi banida Number kowa a cikinsu. Dole na sake nemar guri na zauna inda babu yawan hayaniyar mutane, sai jefi-jefi nakan ɗanga sun gittani.1

★★★★★

     Yanda Jawaad ya nuna halin ko in kula da ganin na Bilkisu bazaka taɓa tunanin yama santaba, sai dai harta fice daga ɗakin yana kallontane ta wutsiyar ido, acan ƙasan zuciyarsa na raya masa “Ita kuma miya kawota nan?” sai dai a fili bazaka taɓa fahimtar komaiba.
      Zama yay a saman ƴar dirowar dake farkon shigowa ɗakin, cikin girmamawa ya gaisa da iyayensa, sukai masa gaisuwar ta’aziyyah tare da jero addu’ar neman gafara ga mamacin, har suka cigaba da ɗan tattaunawa akan rasuwar wadda ta jasu tunowa da rasuwar mahaifin Jawaad ɗin shima da ɓatan mahaifiyarsa.
          Haɗiyar zuciya kawai Jawaad yake famanyi, amma bakinsa ya kasa furta komai, daga ƙarshema saiya miƙe yana faɗa musu zaije ya ɗan kwanta, gimba zai kawo musu abincin da zasu ci.
    Basu hanashi tafiyaba, dan yanayinsa ya nuna yana buƙatar hutun sosai.

★..::..★

        Sai kusan ƙarfe biyar na hangi Mom suna gaisawa da wasu gungun baƙi da sukazo musu gaisuwa, da sauri na miƙe na nufeta karta sake ɓacemin, dan matuƙar gajiya na gaji da zaman ni kaɗai, danma naɗanyi cheating dasu Rebecca ne a group ɗin da muka buɗe iya mu biyar kawai na rage kaɗaici. Daga gefe na tsaya harta gama gaisuwa da mutanen suka tafi kafin na ƙaraso gareta, gaidata na farayi a ɗarare, tunda nasan bani da wata fawa a gareta, amma a mamakina sai naji ta amsa harda tambayata ina na shiga tun ɗazun bata ganniba? wani sanyi ya ratsa zuciyata, kasancewata marainiya ina matuƙar buƙatar kulawar mahaifiya koda kaɗanne, rashin samu kuma na sakani a ƙunci sosai, sai dai ina ƙoƙarin shanyewa ba kowa ke fahimtar hakanba. Cikin girmamawa na bata amsar tambayarta, saita bani umarni akan muje ciki naci abinci.
        Ban sake sakashi a idonaba har zuwa dare bayan sallar isha’i da muka fito domin tafiya gida, ƙiri da muzu Aamilah da aunty Shahudah suketa ƙoƙarin zamewa haɗa tafiya dani, duk da basu fito fili sun faɗaba na fahimci haka da kaina, dan kafin nagama kimtsawa harsun fice daga sashen na Mama Atika, sai tare muka fito da Mom, sai muka iske harsun tafi wai tare da Yah Salman.
     Banji haushiba, saima murmushi da nayi kawai, driver ne zai tafi da Mom, dan haka nima su zanbi dole. Mom ta tsaya gaisuwa da wasu mata da suma zasu tafi, ƴan gayune sosai da kallo ɗaya zakai musu ka fahimci naira ta zauna musu, nidai bayan na gaishesu jikin mota na koma na jingina kawai ina kallonsu da mamakin yanda naga Mom ta sake dasu sosai, yanda na santa da wulaƙanci, koda yake masu iya magana kance wata gaban tafi gaban raini ai.
         Zuciyata ta motsa da ƙarfi a cikin ƙirjina, hakan ya saka tsoro ziyartar raina, koban faɗaba nasan hakan na nufin Dodona ya kusanto wajen koma yana wajen, zuwa yanzu nafara sabawa da wannan SABON AL’AMARIN namu.
      Ilai kuwa ina ɗago idanu akansa na sauke, tsaye yake ɗan nesa damu kaɗan, hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ɗayan kuma ya riƙe waya dake kunnensa, wadda ke nuna alamar yana magana da wanine, ɗan taku yake ɗaya biyu cike da nutsuwa da cikar haiba, ba kayan ɗazun bane a jikinsa, daga wando har rigar jikinsa na yanzu duk fararene tas, gefe wando na duka ƙafar biyu akwai ratsin dogon zare jaa daga sama har ƙasa, sai agaban rigar shima anyi rubutu da ja, hasken dake ƙwanyar a tsakar gidanne ya sani ganin abinda aka rubuta, sai silifas fari shima, sosai kayan sukai masa ƙyau, har na iya kasa janye idona a kansa dukda wutsilniyar da zuciyata keyi kuwa.

STORY CONTINUES BELOW

          Haka kawai Jawaad dake waya da Jabeer yaji a jikinsa kallonsa akeyi, kallon kuma irinna wanda keda kaifin gani da baiwar ƙarfin kwarjinin idanu, duk yanda yaso basarwa tamkar yanda ya saba hakan sai ya gagara, dole ya fara wulƙita nasa fararen idanun kozai samu nasarar cafko wannan mayen idon dake neman saukar masa da gajiya. Karaf kuwa idanunsa suka sauka akanta, shima ƙirjinsa ya motsa alamar harbawar zuciyarsa. Tabbas yaji a ransa itace ke kallonsa, amma a mamakinsa sam idanunta da hankalinta basa kansa, karon farko da miskilancin yarinyarnan ya motsa zuciyarsa, tun ganinsa da ita na farko a airport ya fahimci miskilace ta bugawa a jarida, kasancewar ALLAH ya azurtashi da ilimin karantar hallayyar ɗan adam cikin lokaci ƙanƙani, zuwa yanzu mamakin ganinta yabar ransa, dan ya kula akwai alaƙa tsakaninta da Qaseem…….
      “Hello…hello…” Da Jabeer keta ambatane ya sakashi dawowa hayyacinsa, dan tuni ya saki wayar da suke ya kama sabgar bilkisu, abinda bayayi sam a rayuwarsa (wato shiga abinda bai shafesa ba), yaja siririn tsaki yana murza goshinsa da hannunsa daya ciro daga cikin aljihu.
      Dai-dai lokacin da Bilkisu ta buɗe gaban mota ta shiga ta zauna, dan Mom harta shige baya itama.
         Wani irin harɗaɗɗen numfashi ya sauke har Jabeer na tambayarsa “ko lafiya?”.
      Gutun tsaki yaja yana yanke wayar batare daya bashi amsaba, yakuma jan wani tsakin har sau biyu yana takaicin kansa da shiga hurumin da ba nasaba.

_______________________________

      Washe gari ban biyosuba, dan inama barci suka fice, babu wanda yace a tasoni, nima koda na tashi kuku ke sanarmin sun tafi banji komaiba a raina saima daɗi, tunda nasan zuwana bazai ƙara komaiba koya hana, hasalima banason gamuwa da Dodona.
        Bayan na karya ɗaki na koma nai wanka, nai shiri cikin doguwar riga ta atanfa data samu zaunannen ɗinki, bawata kwalliya naiba, nasaka turare sama-sama na fito bayan na yafa ƙarmin gyale.
     Kai tsaye gate na nufa wajen baba maigadi dake zaune shida mai bayin filawar gidan suna hira, suna ganina suka shiga gaisheni cikin girmamawa, sam banason hakan da sukemin, dan kuwa niba kowa bace a gidan face maicin alfarma, sannan duk sun girmeni, baba maigadi ma a haife ya haifeni, shima mai bayin fulawar kobai haifi kamata ba nasan yanada manyan ƴaƴa…..
       “Hajiya fita zakiyine?”.
Baba mai gadi ya katsemin tunanina, kaina na girgiza masa ina murmushi. “A’a baba ba fita zanyiba, hasalima wajenka nazo muyi magana idan ban takura makaba dan ALLAH”.
      Da sauri yace, “Haba wace takura kuma” yay maganar yana miƙewa da sauri, babu jimawa sai gashi da farar kujera, ajiyemin yay gefensu alamar na zauna, mai bayin fulawa kuwa yay mana sallama akan zaije gida yakai cefane.

          Sake gaisawa mukai da baba maigadi, yay min ta’aziyyar rasuwar da akayi, nako amsa masa tare da tambayar lafiyar iyalansa, bayan amsamin da yay muka ɗanyi shiru, tunani nake ta ina zan fara abinda ya kawoni garesa?. Zuwa wasu ƴan mintuna sai dabara ta faɗomin, nai murmushi ina sake maida hankalina gareshi da kunna voice recorder dan na samu damar kwashe dukkan abinda zamu tattauna nayi nazari a tsanake a kansu.
       “Uhm… Baba dan ALLAH niko wata tambayace dani?”.
     Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “ALLAH Yasa na sani hajiya”.
     Murmushi naɗan masa, nace, “Insha ALLAHU inada tabbacin kama sani ɗin”.
       Baice komaiba sai hankalinsa daya maido kaina baki ɗaya, nima sai na sake nutsuwa sosai.
       “Baba dan ALLAH ko zaka iya tuna ranar da abinnan ya faru da Amina a gidannan da wanda ba’asan ko waneneba?”.
          A bazata maganar tazo masa, dan haka kawai saiya hau tari babu shiri. A rikice na shiga masa sannu, na jawo ruwan dana fito dashi daga ciki na miƙa masa da sauri bayan na ɓalle murfin, amsa yay har hannunsa na rawa ya kafa goran a baki ya ɓaɓɓaka, saida yasha kusan rabi kafin ya sauke, idanunsa harsun kaɗa sunyi jajur, sai naji tausayinsa ya kamani, koda ya dawo dai-dai shiru nai ban sake masa tambayarba har tsawon wasu mintuna.
      Na sake jeho masa tambayar a karo na biyu, yanzunkam a mamakinawa shiru yay bai tanka minba, sai dai yanata ƴan kalle-kalle tamkar mai tsoron a ganmu ko wani ya jimu. Jin bashi da niyyar bani amsa ya sakani kallonsa, a karo na uku na sake maimaita masa tambayar da sigar kwantar da kai………
      “Ɗi!! Ɗi!!! Ɗi!!…” mukaji horn ɗin mota daga waje, hakanne ya sakashi tashi da sauri ya nufi gate ɗin, na tabbatar dama hanyar da zai gudu yake nema, sai kawai na samu kaina da ƙura masa idanu ganin yanda har yanzu jikinsa ke mazarin rawa.
        Hancin motar Dad ne ya danno kai cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya ina miƙewa tsaye, saboda tsayawar da driver yayi a saitin da nake zaune, shi kuma Dad ya sauke glass ɗin ɓangarensa yana mani murmushi.
      Nima murmushin nake masa ina miƙewa na nufesa, da hannu yaymin nuni nazo, dole nabi motar da direba yaja zuwa ciki inda zaiyi fakin.1

STORY CONTINUES BELOW

        Tare da Dad muka shige cikin falo yana tambayata miyyasa banbi su Mom ba can gida?, cikin girmamawa na bashi amsa akan sun wucene ina barci lokacin. Nayi zaton zaiyi faɗa, amma sai naji kawai yay ƙaramar dariya. Mun yada zango a falon ƙasa, ya bani Umarnin naje nasa kuku ya haɗa masa abinci mara nauyi yunwa ya keji, ya fita bai karyabane.
      Koda naje kicin ɗin sai ban fitoba na zauna mukayi abu mai sauƙi wa Dad ɗin ni da kuku, dan zuwa yanzunkam Alhmdllh hannuna yay masifar faɗawa akan girki kala-kala na zamani, na gargajiya kuwa dama bani da matsala a kansa, innata tarigada tayi min wannan horon tun ban gama fahimtar muhimmancin girki ga ɗiya mace ba.
      Bayan mun kammala nice da kaina na kawoma Dad, lokacin yana waya, na ɗora tiren bisa tebir ɗin tsakkiyar falon na jasa gabansa, buɗe masa komai nayi tare da tsiyaya masa ruwa a kofi sannan na koma gefe na zauna, a haka ya faracin abincin yana cigaba da wayarsa data jashi tsayin lokaci, sai yazam yanacin abincinne kawai a shiririce. Dan harya kammala wayar baici ko kashi ɗayaba bisa uku, ya ajiye wayar yana maido hankalinsa gareni, “Taso muci mana ɗiyata”.
      “Lah Dad nakane, ni ban daɗema da karyawaba fa”.
    Cike da kulawa yacemin, “Da gaske?”.
      Na langaɓe kai gefe ina ɗagawa alamar eh. Murmushi yayi ya cigaba dacin abincinasa yana mani hirar data bani mamaki, dan kuwa akan kasuwancinsane ya ɗakkomin hira, yana faɗamin alkairi da kullum kamfaninsa ke samu da yanda kuɗaɗe ke shigo masa babu ƙaƙƙautawa. Banda masha ALLAH da ALLAH ya ƙara sanya albarka babu abinda nake iya cewa, danni kam dai ban fahimci dalilin mani labarinba, tunda a ganina ai sirrinsane wannan, ko a cikin ƴaƴa kuwa a ganina sai wanda ka aminta da amanarsa.
    Kamar kuwa ya karanci mike raina, sai cewa yay, “Kinji inata baki labarin abinda bai shafekiba ko?”.
     Murmushin yaƙe naɗanyi ina gyaɗa kaina, shima ya murmusa yana mai kai cokalin romon farfesun daya ɗobo a bakinsa.
        “Karkiji komai a ranki Bilkisu, na yarda da kene kawai shiyyasa, dan na fahimci keɗin yarinyace mai hankali da tarin nutsuwa, sannan sam baki da yawan surutu, waɗanan halayyar taki na ƙaramin ƙaunarki sosai”.
     Murmushi yanzunkam nayi har haƙorana na bayyana, nace, “Nagode Daddy”.
     Ƙaramar dariya yay yana miƙewa bayan ya ajiye kofin da yasha ruwa, “Kinga bara naje naɗan kwanta na huta, zuwa yamma saimu tafi gidan rasuwar muma”.
    Kaina na jinjina masa kawai, dan nima tuni nake buƙatar keɓancewa, inason yin nazari akan halinda mai gadi ya shiga akan tambayar danai masa ɗazun kafin zuwansu Dad daya gaza amsa mani.

         Koda Yammar bamuje ko inaba, dan banga Dad ba sai bayan la’asar lokacin da yah Salim ke dawowa gidan. Harare-hararen da yaketayine ya sakani tashi na barmusu falon na koma ɗaki.

★..★…:::::…★..★

           Washe gari litinin kowa yasan tushen aiki, hakanne ya sakani shiri tun a farar safiya, lokacin dana fito babu wanda ya fito a mutanen gidan, tea kawai nasha driver ya ɗaukeni zuwa station ɗinmu kamar yanda a yanzu da Yah Qaseem bayanan kullum shine ke kaini.

        Nayi mamakin rashin ganinsa yauma a office, bayan nasan ya dawo, daga baya sai nayi tunanin kodan dai rasuwarcan ne da bansan minene alaƙarsa da mamacinba, dan har yanzu ina mamakin ganinsa a gidan su Mom ɗin, dukda wani sashe na zuciyata na rayamin shima ɗan uwansune ƙila sunje gaisuwane.
    Daga haka ban daɗaba ban ragaba har lokacin tashi yayi muka tashi.
         Tare muka tafi a motar Ummie, dan ita Dadyn ta ya bata mota ƴar ƙarama tun fara aikinmu, tun tafiyar Yah Qaseem sai yazam direba na kawoni da safe, ita kuma mutafi tare idan mun tashi sai ta ajiyeni gida ta wuce nasu gidan.
       Kiran da Nazifa tai minne a waya muke amsawa tare da Ummie dake tuƙi, dan a amsa kuwwa (Hans free)na saka wayar yanda itama zataji, munzo dai-dai shataletalen (roundabout) ɗin da zamu ɗauki hanyar gida danja (traffic light) ta tsaidamu, sai kwasar dariyar labarin da Nazifa ke bamu mukeyi.
     Kusan minti goma muna a haka, saina fahimci sam motocin basa motsawa ma, buɗe motar nai na leƙa, hayaniyar mutane sosai ke tashi, dan motocin dake tahowa a dukkannin titinan huɗune suka cure waje guda, watama ta mugun bugama wata, sun saka jami’i mai bada hannu a tsakkiya sunata zabga masa masifa. Mamaki ya sake kamani, nadai dawo na zauna, mun cigaba da hira kusan ta minti ɗaya nadai sake jin abin bai zaunamin a raiba, dan wannan go slow ɗin yafi kama da wanda aka haɗa da gangan, gashi motoci sai sake taruwa sukeyi titin na sake cinkushewa. Ummie na bama Nazifa amsa ni kuma na maida kallona ga mirror ɗin waje, har yanzu dai babu alamar motsin motocin a dukkanin titinan huɗu da suka raba kansu, sai naɗan kalli Ummie ina yamutsa fuska, dan na lura har yanzu ita bama ta fahimci halin da ake cikiba.
       “Ummie akwai matsalafa, tabbas wannan cinkosan  haɗashi akayi akan sani”.
       Da sauri ta katse wayar tana cema Nazifa muna zuwa.
      Kashe motar tai duk muka fita a hanzarce, tabbas an haɗashine da gayya, hakkanne ya sakamu fara ƴan dube-dube muna kutsawa tsakanin motoci domin san isa ainahin wajen da danjar take.
     Gaba ɗaya wajen ya hargitse, sai hayaniya ke sake tashi, duk yanda mai bada hannun keson dai-daita komai hakan ya gagara, ga waɗanda motarsu ta gogi junama sun fara faɗa na shirin danbe. babu yanda za’ai muyi magana muma wani ya sauraremu, dan abin yafi karfinmu.
     Kalle-kalle na maida hankalina wajenyi sosai kozan samo bakin zaren,
Idona ya kasa barin wata baƙar mota mai baƙin gilashi {tinted glass}, na wuceta yafi sau uku ina sake dawowa gareta, dan sai buga azababben horn mai motar yake nason a bashi hanya ya wuce tamkar shi kaɗaine yafi kowa buƙatar titin kosan tafiya.
       Glass ɗin na ƙwanƙwasa, dan na tabbata koma wanene a ciki shi yana kallon na waje ai, ba’a saukeba na sake bugawa, dan haka kawai nakejin wata irin jarumta da ƙarfin zuciya da bansan daga ina tazo minba……..
       A fusace aka bugo mirfin motar ya bugeni, kafin na dawo daga jin zafin da nayi kawai naji ƙarar harbin bindiga har sau biyu.
     Take wajen ya hargitse da ihu, nima na toshe kunnena ina mai duƙewa ƙasa, mutane sai fita suke daga mota suna gudu, masu dabara kuma na kwanciya a ƙasa, tuni jama’ar dasuka taru suna hayaniya kowa ya kama gabansa, wasu sai son jan ababen hawansu baya suke suna komawa da baya-baya domin ƙoƙarin barin wajen.
       Cikin tunanin da yazomin daga UBANGIJINA ya sani fahimtar akwai matsala.
        Murfin motar da bai gama buɗuwaba aka ziro hannu ahaka aka ƙara wani harbin na kalla, da ƙafa na turashi ya bigi motar, hakan yasaka hannun da yay harbin ya matse sosai, ƙara ya saki yana sakin bindigar itama ta faɗi ƙasa.
      Jan motar sukai da wani irin ƙarfi, dukda motsocin dake gabansu bila adadin, tuni wajen ya sake ruɗewa, jikake garraaam!! Kaccaam!! Na haɗewar motoci, wata na bugar wata, gilasai sai fashewa suke famanyi, waɗanda suke a motocin basu fitaba sunata ihu na firgita.
     Saura kaɗan su takemin ƙafa, nai azamar sunkuyawa na ɗauki bindigarsa data faɗi, banyi zato ko tsammanin zan iya abinda nake yunƙuriba, amma cikin amincin UBANGIJI koda na harba sai harsashin ya sauka akan tayar motar ta baya.
     Tangal-tangal motar ta fara, hakan kuma ya sake hargitse wajen da ihun mutane. Kuma harbin ɗayar tayar nayi, hakan ya saka motocin dake gefenta, sukuma suka bigi fitilar dake a tsakkiyar titi ta tsaya cak.
          Gaba ɗayansu suka fito kuma lokaci ɗaya, dukansu sanye cikin baƙaƙen kaya, gaba ɗayansu bindigace a hannayensu, hatta da wanda na bugama hannu da ƙofa na ɗauka tashi yana tare da wata, hannunsa dana buga sai faman jale-jale yake tabbacin na jimasa ciwo…….
         Da ƙarfi naji an fisgi hannuna, dai-dai shigar ihun Ummie cikin kunnena tana faɗin “Bily!!! harsashi!!”………………✍🏻

3
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻9

Page 3

……………Shuuuu yazo ya wuce sai jikin glass ɗin wata motar bus.

      Saurin kallon wanda ke riƙe da hannuna nayi, gabana yay masifar faɗuwa saboda cin karo da nai da fuskar da ban taɓa tunanin gani a wajenba ko tsammani, ya sake fisgar min hannu muka duƙe bayan wata mota saboda tahowar wasu harsasan huɗu kanmu.

     Cikin matuƙar fusata ya girgizamin hannu yana faɗin, “K shashasha ki dawo hankalinki!!”.

    Yanda yay maganar da wata firgitacciyar muryace ta dawo dani duniyar mutane, amma hatta da kunnuwana da sun doɗe baki ɗaya ko ƙarar harbin banaji.

        Ya jefamin wata bindigar a jiki, cikin zafin nama na cafeta.

     Sosai Jawaad yaji mamakin salon na bilkisu, sai dai babu wannan lokacin a garesa yanzun, dan haka ya maida hankalinsa akan abinda ke gabasu.

       Wajen ya sake hargitsewa da musayar wutar harbe-harbe, kowa burinsa ya kare kansa, mutane kam bamuda tabbacin halin da suke ciki a yanzu.

      Bazan iya tantance muku halin dana tsinci kainaba a ciki a wannan lokacin, amma ni kaina nasan na zama jaruma mai ban al’ajabi..+

         Kowa ya jigatu a wajennan. Bagamu jami’an tsaronba baga ƴan ta’addaba, balle kuma jama’ar gari da suka fimu shiga ruɗani da tashin hankali. Sai dai abin farin cikin shine mutum biyune suka haɗu da tsautsayin harbi a farar hula, ɗaya a ƙafa ɗaya a hannu, amma Alhmdllh babu wanda ya rasa ransa sai a cikin ƴan ta’addar da aka harba a ƙirji. Mun sami nasarar cafkesu baki ɗaya, su biyarne, ɗaya ya mutu, ɗaya naji masa ciwo a hannu, sai raunika da sauran suka samu da wasu a cikinmu harda ni da gilashin wata mota ya yanka a hannu.

         Wannan shine karon farko dana taɓajin mummunan rauni makamancin haka a rayuwata, sai dai lokacin dana jisa ruɗani baisa na maida hankaliba dukda inajin wani masifaffen zafi da raɗaɗi na ratsani, a cikin ƴan uwana kuma babu wanda ya lura sai da ƙura ta lafa, zuwa sannan na zubar da jini sosai, harma takai ina ganin jiri a idanuna, dama gashi inajin yunwa sosai. Rose da hankalinta ya fara kaiwa kainace ta iso gareni da hanzari, dan tuni hayaniyar mutane data ababen hawa data cika wajen ta fara yima kunnuwana nisa, duhu ya fara mamaye idanuna, hakama numfashina sai tattarewa yake waje guda yana dunƙulewa a cikin ƙirjina, abinda kawai zan iya tunawa shine taroni da tai na faɗa jikinta, daga haka ban sake fahimtar komaiba daga duniyar mutane.

★★..::..★..::..★..::..★★

         A hankali nake buɗe idanuna da sukaimin masifar nauyi, naɗan motsa kaɗan ina cije leɓe kafin na samu nasarar buɗe ido da ƙyau. ‘Asibiti kuma?’ na ambata a hankali ina waige-waige da kallon ɗakin dana buɗe ido na ganni cikin bazata. A saman hannuna dake naɗe da bandegi na sauke ganina, sai yanzune abinda ya faru yake ƙoƙarin dawomin a zuciya, a hasashena zan iya cewa jiya kenan abin ya faru, dan yanzu dai ranace ƙwanyar na fahimta, idan kuma ban mantaba ƙurar jiya ta tashine da yammaci har zuwa duhun mangariba, kenan a cikin asibiti na kwana?.

           Bani da amsar tambayar tawa, kamar yanda babu alamun akwai mai amsa mani ita a kusa, dan babu kowa a ɗakin sai ni kaɗai.

      Na ɗauki tsawon wasu mintuna da bazan iya ƙididdige yawansuba sallamar Ummie ta riski kunnuwana, nakai dubana gareta yayinda take ajiye madaidaicin kwandon data shigo dashi a hannu,

     “Bily ashe kin tashi ma?”

Tai maganar tana matsowa daf dani. tare da taɓa hannuna da naji ciwon. murmushi nai mata, kafin na buɗe baki a hankali ina bata amsa da “eh”. Zama tai a kujerar gaban gadon, tana murmushi, tace, “Kai Alhmdllh, bily kin bala’in rikitamu jiya, wlhy mun zata bazaki sake buɗe ido ki ganmu ba”. Da tsagwaron mamaki nace, “Miyasa?”. Tai ƙaramar dariya tana miƙewa, “karki damu zan baki labarin komai, yanzu dai bara na kira Doctor danya dubaki, daganan kici abinci ko, dan tun kiran sallar farko na tashi domin na haɗa miki shi”. Kaina kawai na iya rausayarwa gefe ina binta da murmushi, tare da tarin ƙaunar da nake jinmu tamkar jini guda.

        Ba’a ɗauki wani dogon lokaciba Doctor yazo, yaymin tanbayoyi  kafin ya bama Ummie Umarni akan ta taimakamin nayi wanka ga bayi nan, idan na kammala naci abinci nasha magani, zuwa yamma ƙilama su sallameni tunda sunga komai normal.

      Da taimakon Ummie na sakko a gadon, sai yanzune na kuma fahimtar  a ɗaki na musamman nake, kuma ni kaɗaice a ciki, na kalli ledar jini dake rataye a ƙarfe cikin mamaki, Ummie data lura saita bani amsa da faɗin, “Ke aka ƙaramawa, dan sanda muka iso jininki ya zuba da yawa, amma Doctor yace babu wata damuwa a hakan, idan an ƙara miki zai amfaneki, idan kuma ba’a ƙaraba bazaki cutuba, sai dai boss ya dage akan a ƙara miki jinin dole, anbuƙaci gwada su oga Hafiz koza’a samu na ɗaya a cikinsu yay dai-dai da naki, amma sai boss ya hana a gwada kowa, a cewarsa jininsa yana rukunin da zai iya bama kowa, dan haka a ɗeba nashi, kowa yasha mamakin furucinsa, amma bawan ALLAHN nan ya fuske abinsa, babu ma wanda ya samu ƙofar kawo masa wargin tambayar dalilin hakan, daga ƙarshe dai jininsa aka ɗiba aka saka miki…….”

     Lokaci ɗaya nai masifar zabura da zaro idanuna waje, har ina bige hannuna mai ciwo, hakan ya sakani cije lip ɗina na ƙasa kafin nace, “Jininsa fa kikace?”.

     Sosai ta ƙyalƙyale da dariya, “Wlhy karkiji wasa, jinin Boss ne ke gauraye da naki suna aiki a kowacce kafar jijiyarki a halin yanzu”.

         “Na shiga uku ni Bilkisu” nai maganar ciki yanayin ta ƙaremin. Dariya Ummie ta cigaba dayi, dan na lura sam bata fahimci tashin hankalin da nake a cikiba da gaske, ban sake iya maganaba har taimin rakkiya cikin toilet ɗin ɗakin dake tsaf babu datti, ga ruwan ɗumi ta haɗa mani kuma.

      A cikin dabaru nake wankan gudun karna jiƙa hannun dake naɗe da bandeji, sai dai zuciyata sam bata tare da hankalina, sai faman juya maganar sakamin jinin Boss da Ummie tace anyi nakeyi, haka kawai naji hawaye masu ɗumi suna sauka bisa kumatuna, bansan na mineneba, sannan bansan dalilin zubar tasuba, sai dai wani gefe na zuciyata na danganta saukarsu da ganin kamar bankai matsayin da za’ace jinin wannan bawa ya gaurayu da nawaba, da kuma zaka tambayeni dalilin faɗar haka a lokacin bazan iya cewa komaiba balle yin fashin baƙi. Haka dai na kammala na fito, da taimakon Ummie na kimtsa cikin kayan da tazomin dasu, ta shafa min mai harda ƴar hoda fara ta sakamin dan karna zauna fuska na ƙyalli, na zauna a saman gadon jingine da filo ita kuma ta haɗamin tea, tare da zubamin farfesun kan rago daketa ƙamshin kayan yaji.

       “Ummie ƴan gidanmu kuwa sun sani?”.

       Sai da ta miƙamin tea ɗin kafin tace, “Eh, tun jiya da daddare sukazo ai, Daddy, Mom sai Aamilah da Shahudah da Salim, lokacin bakisan inda hankalinki yakeba, anama ƙara miki jinin ne”.

    Kaina na gyaɗa mata sannan na amshi kofin, cikin suɓucewar harshe nace, “Sanda sukazo Boss na nan?”.

     Tsareni tai da kallon tuhuma, ni kuma na basar cikin kauda mata shakkun dake neman yin ƙutse a ranta, fahimtar hakanne ya sakata daidaita yanayinta itama, tace, “A’a sun tafi lokaci harsu Oga Aliyu, ni kaɗaice kawai, saboda nima Daddy ne yace na jirashi shida Mami zasuzo su dubaki saisu tafi dani, tunda Doctor yace basa buƙatar kowa ya zauna dake”.

          Bansan miyasaba sai kawai naji zuciyata tamin daɗi da rashin haɗuwar tasu, na cigaba da shan tea ɗin a hankali, Ummie ce ta kuma maido hankalina gareta da faɗin,

      “Ammafa kin bala’in burgeni jiya wlhy Bily, wai dama baki da tsoro ashe?”.

     Murmushi nayi kaɗan ina lumshe idanuna tare da muskuta zamana yanda zanji daɗi sosai, “Ummie ba tsorone banda shiba, wani lokacin tsoro da kansa yana jin tsoron mai tsoronsa, sai dai ba kowacce ƙwarin gwiwa ke fahimtar da hakanba, a duk lokacin da kikejin tsoron abu to kawai ki tunkareshi koda kina tunanin zaki halaka ne, ina mai tabbatar miki shi wannan abin tsoron shine zai koma tsoronki, da gaske daga jiya na ƙarajin ƙarfin gwiwar yima ƙasata aiki bakin rai bakin fama , alƙawarin danai da izinin ALLAH bazata tashi a banzaba, daga yanzu zan cigaba da tunkarar kowanne irin abin tsoro daka iya tsoratar da al’ummar ƙasata koda zai sakani fuskantar ƙalubale, bani da kowa sai kaina Ummie, akwai irina da yawa a faɗin duniya, waɗanda sukafini shiga gararin rayuwa da buƙatar jin ɗumin duniya a dalilin rashin majingina ta iyaye, wadda mutuwa ta nisantasu, kokuma iyayen na raye ƙaddara ta nisantasu, sai dai ita duniyar ta juya musu nata bayan saboda bata buƙatar nasu ɗumin, waɗanda kuma keda kusanci da duniyar suna hantararsu saboda basu da buƙatar taimakonsu koda da nuna tausayawane, irina da sukasan wannan zafinne kawai yakamata ace suna iya tunawa dasu da waiwayensu a lokacin da suka sami damar ƙutsawa jikin duniya ta ƙarfin tsiya. Na shiga aikinnan ne domin ALLAH, zanyi hidima wa ƙasata domin ita ƙasata ce, zan rungumi marayu irina domin ƴan uwanane, zan kare haƙƙin ƴan ƙasata domin suɗin ahalinane, nabar kallon allon tsoro a gabana a yanzun, allon jajircewa kawai nake burin cinmawa insha ALLAHU, abokan tafiya kawai nake buƙata, waɗanda basai naje farautarsuba, da kansu nakeso suzo gareni, hakkane kawai zaisa na tabbatar da sun cika sharuɗɗan abokan gwagwarmaya dai-dai da yaƙar tsorona, jiya ta wuce, yanzu a yau muke, abi mafi muhimmanci shine mu fiskanci gobanmu idan muna cikin masu rabon gani”.

         Sosai Ummie keta faman jinjina kai da dogon bayanina da bani da tabbacin zai zama abin fahimta ga kowa har ita kanta, wani zai iya kallonsa ta fuskar ƙuruciya, wani yace rashin hankali na mata, wani yace wauta ta mara gata, wani yace zaƙewa ta ƴaƴa mata masu san nuna daidaita kafaɗunsu da maza, hakan bazai dameniba a duk yanda fahimtarka ta baka, abinda na sani kawai zuciya sirrin mai ita kawai takeji, duk bin diddigin ma’abocin kusanci koya kasa kunnuwa bazaiji komaiba sai bugawarta, idan kuwa har mun yarda gaibu sunanta gaibu, to yazama tilas muyi imani da hankali koda bama ganinsa a zahiri saita yaƙini kawai.

        “Maganganunki irin na mutanene masu himma bilkisu, sannan masu duba gabansu mizatazo dashi, bawai yau ɗinsu kawaiba, da jiyansu data shuɗe ta zama tarihi, tun haɗuwata dake ta farko na fahimci kinada wata baiwa ɓoyayya da bakowa ALLAH ya bama ilhamar hasasotaba, daga lokacin kuma da muka kasance ma’abota kusanci na tabbatar da zamu ribantu da junanmu, sai dai taki ribar da zamu samu saita ɗara tamu muhimmanci da amfani a garemu, k…….”

         “Sam ban gamsu da bayanankiba Ummie” na faɗa cikin ɗaga mata hannu saboda yanda ta kwararo zance.

       “Miyasa kikace haka Bily?”.

   “Banason faɗa kice na maida hannun agogo baya, mubar zancen kawai watarana ma ƙarasa, mizai hana kije wajen Doctor kimasa maganar ya sallamemu haka, banason zaman asibiti a rayuwata”.

      kafin Ummie ta samu damar yin magana aka turo ƙofar aka shigo da sallama, Dad ne, hakanne ya sakani faɗaɗa murmushi akan fuskata, saurin tashi tsaye Ummie tayi ta bashi kujerar da take zaune akai, kafin ta gaidashi cikin girmamawa. Nima gaidashi nai, ya tambayeni jikina cike da kulawa. Naji daɗin ganinsa sosai, nakumaji daɗin alhinin daya nuna akan halin dana tsinci kaina, sai dai nayi ƙoƙarin daƙile alwashinsa na buƙatar nabar aikin, danshi kam ya fara tsorata dajin cewa wannan aikin namu da gaske bai dace da ɗiya mace ba, musamman ma irina da nake yarinya ƙarama.

      Cikin murmushi da girmamawa a garesa nace, “Dad addu’arku kawai muke buƙata, idan har zamu cigaba da sakawa a ranmu mata basu dace da irin kowanne aikiba saboda matsalolin cikinsa, to lallai yankinmu bazai daina fuskantar koma bayaba, hakama sauran mata masu tasowa bazasu daina fuskantar ƙalubale na daƙile burinsu akan kansu da ƙasarsuba”.

        Sosai Dad yay murmushi, ya shafa kaina da cewar, “ALLAH yay miki albarka kinji, lallai tunaninki ƙyaƙyƙyawane Bilkisu, ALLAH ya kiyaye gaba to, nabiya ta wajen likita, ya baki sallama yanzu haka, sai dai ya tabbatarmin daga office ɗinku an turo ɗaukarki, ɗan aiken na hanya kuma, dan haka ni zan wuce, dama daga nan airport na dosa”.

       “Dad badai har zaka sake wata tafiyar ba?”.

    Murmushi yaymin mai ƙayatarwa yana jinjina kansa, “Hakane bilkisu, masu iya magana nacewa na kwance baiga gariba, muma addu’arku muke buƙata tamkar yanda kuke buƙatar tamu kinji, wannan karon kuma bazan jimaba, dan sati ɗaya kacal zanyi, idan na wuce hakan kuwa bazan zarta gomaba”.

       “To Dad ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada nasarar abinda za’a fita nema mai albarka”.

     “Amin ɗiyata, nagode sosai”.

Itama Ummie tai masa addu’a, ya amsa mata da kulawa kafin ya ajiye mana kuɗaɗe masu kauri ya fice daga ɗakin”.2

         Koda Dad ya fice fuskarsa ɗauke take da murmushi tare da ɗunbin tausayin yarinyar a ransa, shidai haka kawai ALLAH ya dasa masa ƙaunarta a zuciya, yaɗan juya ya kalli ɗakin yay murmushi kafin ya cigaba da tafiya……..

    Gaff sukaci karo da mutum, Gimba yay saurin fara jero kalamun ban haƙuri a gareshi. Batare da Dad yay masa wani kallon arziƙiba yace babu damuwa, yay wucewarsa. Binsa da kallo Gimba yay cikin wani tsagwaron mamaki da juya abinda ya gani a cikin zuciyarsa, sarai ya gane mahaifin matar Boss ɗinsace ta da, kuma mijin Gwaggonsa, afili yace, “To mikenan? Mi yazo yi nan? Minene ma’anar wannan kallon da yayma ɗakin nan? Minenema haɗinsa da ɗakin?”. Bashi da mai amsa masa wannan tambayoyin, dan haka yaja bakinsa ya tsuke dan bai dace ya shiga abinda babu ruwansaba, Boss na yawan masa nasiha da kiyaye abinda ba huruminsaba koda a inane, kuma koda akan minene.

         A ɗaki kuwa bayan fitar Dad yabo Ummie ta shiga jero masa, yayinda Bilkisu ke tayata tare da ƙara buɗe ƙyawawan halaye na Dad waɗanda Ummie batasan da suba. A haka gimba yay sallama a ƙofar ɗakin, sai da na  suturta jikinna kafin mu bashi damar shigowa, dukda bamusan shiɗin waneneba.

       Mun gaisa da juna cikin girmamawa, sannan ya kora mana bayani akan cewar Boss ɗinsa Jawaad ne ya bada umarnin yazo yakaimu  gida dan an bani sallama.

      Kallon juna mukai ni da Ummie, kowanne baki a hangame, sai dai bamu da damar bin ba’asi akan wannan umarnin, dan kuwa dai yana sama damu, mizaisa mu tuhumesa da abinda bamu da bakin zarensa. Haka muka shiga kimtsawa har Doctor ya shigo, ya ƙara mana bayani akan yanda  zan kula da cuwon saboda gudun karya zarta haka, tare da kwanakin da zan ringa zuwa asibitin domin tabbatar da ingancin kulawar da nake bashi.

           ___________________________

                             JAWAAD

   ___________________________________

             Zaune suke a office ɗinsa su huɗu, aminan juna kenan da sukejin kansu jini guda, sannan abokan amanar juna masu taruwa wajen magance matsalolin juna da ƙarfin zuciya dana aljihu.

     Sunyi nisa cikin tattauna abinda ya faru a yammacin jiya ne, domin dai da gaske Jabeer ne ya haɗa cinkoson jiya da gangan saboda son cimma burin kama tsagerun da suka biyo, amma sai suka ɓace musu, ganin zasu rasa wannan damarne Jawaad ya bama Jabeer umarnin nuna ƙwarewarsa kasancewarsa masani sosai ta ɓangaren na’ura mai ƙwaƙwalwa.

      A take kuwa ya nuna gwarzantakar tashi, ya haɗa cinkoson da su Bilkisu suka riska saboda tabbacin nan kaɗaice hanyar da masu laifin zasubi su tsira da wuri, ita kuma Bilkisu tayi tarar aradu daka akan abinda bata da tabbaci.

       Aliyu ne ya fara faɗin, “Maganar gaskiya na daɗe banga jarumar mace mai ƙarancin shekaru irin yarinyarnanba, a yanda labari ke fitowa da ga bakunan mutane na yanda ta tari motar mutanen da suka fara ganin farkon al’amari da yanda ta tunkari mutanen zai baka tabbacin da gaske tanada kaifin zuciya akan aikinta”.

       Cikin jin jina kai na tabbaci Jabeer yace, “Lallai maganarka tana akan gaskiya wlhy Aliyu, nifa abindama ya sake birgeni da ita shine, dukda mugun ciwon da taji, amma saita dake dan tabbatarma da duniya lallai ita ma’aikaciyar tsaroce ta gaske ba ƴar burgaba”.

       Fuska shimfiɗe da murmushi Hafiz  yace, “Sosaima kuwa Jabeer, dolene ƙaimin yarinyar ya burge kowa, dan kuwa da ƙwaƙwalwa tai amfani wajen fahimtar motar tana da alaƙa da rashin gaskiya, ta kuma nuna himmarta na sadaukarwa koda hakan na nufin zata cutu a wajensu, ta cancanci kowanne irin jinjina ga hukumarnan tamu, musamman idan akai la’akari da shigowarta cikin aiki jiya-jiya kawai, bana tunanin kuma an taɓama fita da ita wani aiki makamancin haka koda sau ɗaya”.

           Duk wannan zance da suke faman zubawa akan yabon Bilkisu da jinjina himmarta Jawaad na zaune shima a cikinsu, yana sanye cikin baƙaƙen suit kamar sauran da a kullum suke ƙara masa kwarjinin kasancewarsa ma’aikaci, sai dai ya cire rigar sama, yana zaune ne kawai da baƙin dogon wandon da rigar ciki mai dogon hannu kalar kore mai haske, maɓallan rigar uku a buɗe, hakanne ya bayyana singlet ɗinsa kaɗan fara tas, yaci zanzaro, ya tsuke ƙugunsa da belt kalar shirt ɗinsa.

       Abinda zai baka mamaki ko tari bai yiba akan maganar, baima nuna ya fahimci mi suke tattaunawarba sam, yana zaune ne ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, kansa sunkuye yanata faman danne-danne a cikin tab… ɗinsa ta kamfanin Apple, sam fuskarsa babu wata walwala, kuma ba’a tsuke take sosaiba.

        Aliyu ne yakai dubansa garesa, tare da faɗin, “Ka fuskanci abinda muke tattaunawa game da yarinyarnan kuwa Jay?”……………✍11

           

      

   

        

          

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.16Page 4

……………Shiru tamkar bazai tankaba, kusan sakanni sha biyar kafin yay magana batare daya bar danne-dannen tab… Ɗinba balle ya kallesu, “Wace yarinya kenan?”. Yay tambayar cikin nuna halin ko’in kula balle su sami ƙwarin gwiwa akan ya jisun.

      Duk kallonsa sukai da mamaki saboda yanda sukasanshi dason mutum mai himma, amma yanda ya amshi maganar ya matuƙar basu mamaki a yanzun.

      Jabeer ne yace, “Yarinyar jiya daka bama jini mana Jay”.

       “Humm” yace kawai ya sharesu bai sake tankawa ba, tsawon mintuna duk sun zura masa idanu suna jiran ƙarin bayani, dan sunyi tsammanin fara jin yabon yarinyar da ga bakinsa ma kafin su su furta, amma ya share kamar ya manta dasu ma a office ɗin.

        “Wai boss lafiya kuwa?” Hafiz yay tambayar a wani yanayi.

    Sai yanzune ya ɗago ya kallesu su duka, kallo irin a taƙaice ɗinan ya janye mayatattun idanunsa masu cikar gashi da haske tamkar madara, ya taɓe baki kaɗan kafin ya miƙe daga wajen ya nufin kujerarsa ta zama, dan da suna zaunene a rukunin kujeru da’aka shirya a office ɗin domin hutawa ko ganawa da baƙi na musamman. 

        Sai da ya zauna sosai ya juya kujerarsa tana fuskantarsu kafin yace, “Abun harinmu a yanzu shine mutuwar jami’inmu da sir Ahmad yamin bayani, minene shawararku akan hakan?”.

          Aliyu ne ya samu damar faɗin, “Bincike akan shi ɗin wanene? Tunkan fara aiki a wannan hukumar har zuwa farawar tashi, tare da sanin masu bashi gudunmawa akan aikin da yazama sanadinsa, da kuma sanin a ƙarƙashin wa ya samu umarnin”.

         “shawara mai ƙyau” Jawaad ya faɗa yana lumshe idanu da kwantar da bayansa jikin kujerar yana lilawa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi, kusan sakanni biyar kafin ya sake ɗagowa yana kallonsu da nazartarsu.  Ya ɗauke idanunsa tare da sake komawa jikin kujerar ya kwanta, “Idan an sallamota daga asibiti zatayi bincike akan dukan bayanan Aliyu”.

        Cikin matuƙar mamaki suka kallesa, cikin harɗewar harshe Jabeer yace, “wai kana nufin yarinyar?”.

     Kallonsa kawai yay ya janye idanu, sai dai baice komaiba. Sun fahimci amsar kenan, dan haka Aliyu yace, “Amma boss baka ganin aikin zai mata girma? Musamman idan mukai dubi akan shine na farko?”.

         Cikin halin ko in kula ya taɓe baki, ba tare daya kallesu ba yaja wasu takardu dake saman tebir ɗin nasa yana faɗin, “Maybe hakan, maybe kuma ba hakan baneba, naga kuma da kanku kun yarda da ƙwazonta, to miye kuma na kokwanto yanzun?”.

      Babu wanda ya sake cewa komai. sai dai a ƙasan ransu duk sai suka kasance cikin nadamar kwarzanta ƙwazon yarinyar da yawa irin haka, dan a ganinsu bata kai ƙwarin da za’a sakata a irin wannan babban aikin hakaba mai haɗari, musamman idan sukai dubi da ko rose data daɗe a cikinsu baya bata irin wannan damar.

      Takardar da ya maida hankali a kanta ya ɗago saitin Hafiz, “Hafiz wanene da wannan bayanan haka?”.

      Tasowa Hafiz yay ya dawo gabansa, ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana mai amsar takardar, nazarin mintuna biyu ya ɗago kai yana kallonsa, “Akan case ɗin yaron nan da aka samu makamai a shagonsu ne, Aliyu ne akan binciken kuma”.

     Jawaad ya maida kallonsa ga Aliyu, hakan ne ya saka Aliyun tasowa ya nufosu shima.2

              __________★★__________

                           BILKEESU

     _________________________________

                 Wani irin mayataccen ƙamshi ya shiga rige-rigen zirarawa cikin ƙofofin hancinanmu yayinda muke shiga motar da boss ya turo ɗaukarmu, batare da kowannenmu ya fargaba muka tsinci kawunanmu da lumshe idanu muna sake buɗe hancunan namu sosai. A haka yaja motar muka bar asibitin, tabbas wannan ƙamshine daya cancanci ajiyeshi a ma’ajin zuciya da ƙwaƙwalwa saboda ya kasance na musamman, bansan miyasa na kirashi na musammanba, sai dai kawai zan iya fassara hakan da kasancewarsa na musamman a duk lokacin da hanci ya shaƙa koda ba namuba. Naji tamkarma kar motar ta tsaya ace na daina shaƙar wannan ƙamshin, sai dai babu yanda zanyi dan hakan tilasne. A wannan yanayin muka isa gida, ya ajiyemu a gate ya juya, mukuma muka shiga ciki bayan mun masa godiya.

      Mun iske gidan babu kowa, suna gidan rasuwa su duka, dan haka mukai zamanmu dagani sai Ummie da tace boss ya bata umarnin ta zauna dani harna warke tun a jiya. Ban tambayeta daliliba, kamar yanda itama bata kawo komai a rantaba game da hakan, sai dan tana ganin ya fahimci bani da wadda nakeda kusanci da shi sama da ita a station ɗin namu.2

STORY CONTINUES BELOW

              __★.:.★__________★.:.★__

                             JAWAAD

        _____★.:.★__________★.:.★_____1

                   Suna tsaka da cigaba da magana shi da su Aliyu kira ya riskesa daga office ɗin B.G, duk da kiran ya bashi mamaki daga shi harsu Jabeer ɗin hakan bai hanashi fita domin cika umarni ba.

        Galala nai da baki ina kallon haɗuwa da tsari na office ɗin da Jawaad ya shiga, komai yaji babu algus. Banma kaina buƙuluba nabi ko’ina daki-daki da kallo a office ɗin, kafin na sauke idanu ga mai ikon faɗa aji na hukumar tasu. Danƙari, na ambata a zuciyata dan kuwa munzo ƙarshen zance, sam babu alamun fara’a balle sassauci tattare dashi, Jay ya miƙa gaisuwa cikin girmamawa kafin ya samu izinin zama daga gareshi.

       “Sir Ance kana kirana” Jawaad ya faɗa cike da girmamawa.

      A cikin maƙoshi ya bashi amsa da cewar, “Uhhm” daga haka yaja bakinsa yay tsit. Gani nai shima Jawaad ɗin ya sake kame kansa ba tare daya sake tankawa ba, kusan mintuna huɗu suna a haka kafin ya ɗago kai tare da juyama Jawaad fuskar lap-top ɗin dake gabansa, hotone mai motsi (video), Bilkisu ta bayyana tana harbi da bindiga har guda biyu a rikicin jiya, gaba ɗaya bidiyon bai wuce na minti ɗaya da wasu sakanni ba, saboda iya itaɗin kawai aka nuna, ƙarewarsa ce ta saka Jawaad kallonsa cikin rashin fahimta.

       Cikin zafin rai da fusata ya zazzaroma Jawaad ɗin idanunsa jajaye, “Wannan yarinyar tanada izinin yin harbi ne kamar haka dama?”.

         Jawaad da ya tsuke fuska shima ya girgiza kansa kawai.

       “Ya akai tayi kuma?”.

Sai da Jay ya furzar da huci kaɗan kafin yace, “Sir bamu da wani zaɓine bayan hakan, domin musayar wutace, idan kuma bata da makamin kare kanta a hannu rayuwarta na cikin haɗari, musamman daya kasance da taimakonta muka riski masu laifin”.

          “Hakan yana nufin shine matakin ƙarshe da kuke da mafita kawai?”.

       Shiru Jawaad yay bai motsaba, sai maƙogwaronsa ne keta kai kawo a cikin wuyansa, yayi kicin-kicin da fuska.

             “Da kai nake magana Captain!”.

       “Sir nasan munyi kuskure, amma a duba uzirinmu muma, musamman na isa wajen a ƙurarren lokaci, sannan a duba irin rawar da yarinyar ta taka, duk da kasancewarta ƙaramar ma’aikaciya, wadda ta shigo jiya-jiya cikin wannan hukumar tamu, ta nuna ƙwazon da ya kamata a jinjinama ƙoƙarinta ba ƙalubalantar taba, domin kuwa ita bata da laifi, nine mai laifi dana bata bindigar”.

         “Uhyim, kana nufin yanzu dai ka kareta?, sannan dukkan hukuncin da zai biyo baya zaka ɗauka kuma?”.

     Shiru tamkar bazai amsaba, sai kuma ya ɗago idanunsa harsun kaɗa da ɓacin rai, a kasaushe yace, “Aimin duk hukuncin da za’ai matan babu damuwa”.

      Shiru B.G yay kawai yana kallon Jawaad ɗin, yasan yaron dama akwai taurin kai, dan tun shigowarsa hukumar ƴan sanda ma da tsaurin ido ya shigo, kasancewar wanene mahaifinsa yasa aka hana kowa nuna masa yatsa, himmarsa da zafin nama ne ya saka aka maidoshi cikin hukuma DSS, shi kuma har cikin ransa yaron bai masaba, sanin dalilin kuwa wannan sirrinsane….

     “Kaje zamu nemeka”  B.G ya faɗa a daƙile.

    Uffan Jawaad baice ba, ya miƙe kawai tare da yin salute nashi ya fice abinsa yana haɗiyar zuciya, duk wanda zai iya ganinsa a wannan lokacin dolene ya fahimci ransa a matuƙar ɓace yake, mai makon ya wuce office ɗinsa sai ya nufi office ɗin L.C, wato sir Ahmad barewa, canne kawai zai kai damuwarsa ya samo mafitar da yake buƙata.

       Bayan yay knocking ƙofar aka bashi izinin shiga, ya riga da yasan ya gansa ta cctv, tunda ya turo ƙofar ya shigo sir Ahmad ya fahimci akwai damuwa, ya kafeshi da idanu kuwa, yayinda shi kuma Jawaad ɗin yaƙi yarda su haɗa idanu.

      Sai da ya miƙa gaisuwa Sir Ahmad yay masa nuni da kujera alamar ya zauna.

        Koda Jay ya zauna sai baice uffanba, sai ajiyar zuciya kawai yake faman yi, sir Ahmad yay murmushi irin nasu na manya masu kaifin tunani, kafin ya miƙe daga mazauninsa ya nufi firij ɗin dake a office ɗin, goran ruwa ya ɗakko ya miƙa masa batare da yayi magana ba, babu musu ya amsa, ya ɓalle murfin yana kai goran bakinsa, sai da ya shanye fin rabi sannan ya ajiye yana sauke numfashi a jajjere.

      Wani murmushin Sir Ahmad ya kumayi, sannan ya zauna a kujerar dake kusa da Jawaad ɗin suna kallon juna “Captain! Lafiya kuwa? Waya zinguro mazajene?”.

       Idanu Jay ya ɗago ya kalli Sir Ahmad, sai kuma ya janye yana shaƙar numfashi da zafi…..

     “Jay!”

Sir Ahmad ya kirayi sunansa yana ɗora hannunsa bisa kafaɗarsa.

     A karo na Biyu Jawaad ya sake kallon Sir Ahmad barewa, ya cije leɓensa da ƙarfi yana faɗin, “Daga office ɗin B.G nake Sir”.

        “Na sani ai” cewar sir Ahmad yana murmushi.

      Cikin sauri da tsagwaron mamaki Jawaad ya kalli Sir Ahmad, kallo irin na tuhuma.

        Ƴar dariya sir Ahmad yayi, ya kuma kai hannu ya bubbuga kafaɗar Jawaad ɗin a hankali, “Kar kai fushi yarona, karkuma ka shiga ruɗani, banason ka manta kanka a cikin mutane masu kaifin basira, za’ai amfani da yarinyarne kawai ai wasa da hankalinka, kaga kenan an samo lagwonka da damar bama maƙiyanka yin wasoso a saman mutuncinka, kar kaga laifin B.G, shima sashi akayi, domin bana tantama umarni ya samu daga sama, sai dai wanene? Akan minene? Shine ban saniba”.

        “Zuutt!” wani abu dake tsaye a maƙoshin Jawaad ya faɗa cikin cikinsa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, saboda dai Sir Ahmad ya dawo dashi a hayyacinsa da wuri…

     Sir Ahmad ya miƙe yana murmushinsa na kamilallun mutane, ainahin kujerar zamansa ya koma ya zauna..

       “Abin bai baka mamakiba ace iya inda take harbin kawai aka kawo masa, sannan kuma ita kaɗai, bayan kuma batakashin da kuka gwabza a wajen ku kusan goma ne”.

           “Sir ai abinda ya matuƙar ɓatamin rai kenan, taya za’ai ace itace kawai za’a ɗauka?….”

       “Saboda ita kaɗai tazo da salon da ya ajiye ruɗani a zukatan masu fargaba akan jajircewarka”.

        “Salo kuma sir?!”.

“Yes! Jawaad, salo mai ƙayatarwama kuwa, andaɗe ba’a samu mai ƙaracin shekaru irinta da wannan ƙwazonba, abin ƙarin mamakin kuma gata mace, yarinyar da alama zata ajiye tarihi a wannan hukumar, dan alamomin hakan sun farane daga jiya”.

       “Sir! to amma su wanene ke ganin hakan matsayin ƙalubale garesu? Miyasa kuma….?”.

        “Nima ban saniba Jay”.

    Shiru Jawaad yay na wasu sakanni kafin yace,  “Saboda mi suka zaɓi hukuntata bayan karramawa ta cancanta dashi sir?”.

      Sir Ahmad yay gajeruwar dariya idonsa akan Jay, yace, “Saboda ƙwazonta abin dubawane ga mai hankali, sannan abin tunani ga irin waɗanda basa buƙatarta, wannan shine aiki na farko da yarinyar tayi, kuma ba sakata akayiba, sai dai ƙwazonta ya girmi matsayinta da gogewarta a aikin, hakanne ya sakasu saka maka alamar tambaya (?), musamman daya kasance tare da kai aka fara ganin baiwar ta ta”.

         Karan farko da Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya harda dukan tebir ɗin gabansu, Sir Ahmad dake kallonsa shima murmushinsa ya faɗaɗa, ya juyo sosai yana fuskantarsa, har yanzu kuma fuskar tasa da sauran dariyarsa irin wadda kafin yayita akan kai ruwa rana,

       “Sir kasan minene kuwa?”.

              “Saika faɗa Jawaad”.

  “Sun bani dariya ALLAH, danni Ko sunanta ban saniba fa”.

      Dariya shima sir Ahmad ya shiga ƙyalƙyalawa, kafin yace, “Cakwakiya kenan, to tabbas kuwa daga masu wannan ƙullin abun ba haka bane ba Jawaad, kallon ƘWAI CIKIN ƘAYA sukema lamarin”.

      “Nima na fahimci hakan a yanzu sir”.

       “Yayi ƙyau. Miya faru jiya?”.

Tun daga farkon zuwansu inda abun ya faru har ƙarshe Jawaad ya bama Sir Ahmad labarin komai bai ɓoye masaba.

     Kai kawai Sir Ahmad yake jinjinawa har Jawaad yakai ƙarshen jawabinsa, ya sauke numfashi kaɗan yana faɗin, “Zamu shiga meeting anjima, kuma nasan akan wannan maganarne, shawara ɗaya dazan baka yanzu shine, kai ƙoƙarin gano wanda ya ɗauki wannan bidiyon, sannan kayi gaggawar samo bidiyon da yafi wannan na wajensu tsaho, ka kumayi saurin rubuta bayanai akan komai ka tura office ɗin L.G tare da bidiyo ɗin daka samo ɗin”.

       Kamar Jawaad zaice wani abu, sai kuma yay shiru yana miƙewa da faɗin, “Okey sir, zanyi ƙoƙari insha ALLAH”.

      

       

        ★★★★1

Gaba ɗaya kan Jawaad ya kulle da wannan lamari, ya rasama ta yaya zai fassara al’amarin, maganganunsa da Sir Ahmad kawai ke masa kai kawo a cikin zuciya, tare da zuwansa office ɗin B.G, ya rasa ina zai kama ma shikam? Yana buƙatar ganin su Jabeer tare dashi yanzunan, sai dai tabbas bazai yuwu a station ɗinanba, dan yanzu dukkanin motsinsa abin bibiyane.

     Ƙaramar wayarsa ya ɗauka ya turama Hafiz saƙo, kafin ya tura wayar aljihu bayan ya kasheta gaba ɗaya ma, wasu takardu ya ɗiba ya fito a hanzarce, hana kowa ya bisa yayi, ya shiga mota shi da Gimba kawai suka fice daga station ɗin.

          Danne-danne yaketa famanyi a lap-top, hakan ya saka gimba kallonsa ta cikin madubi, “Boss! Ina zamuje?”.

    Ba tare da ya ɗagoba yace, “A.Y Street”.

        Cikin girmamawa Gimba ya amsa, tare da juya kan motar suka nufi hanyar gidan Jawaad ɗin dake anguwar A.Y street.

         Sunyi wajen mintuna talatin da zuwa kafin su Aliyu su iso. A falo suka iskeshi har yanzu yanata faman danne-danne a lap-top, a haka ya amsa sallamarsu ko ɗagowa baiyiba ma. Sai da suka zauna da kusan mintuna biyu sannan ya ɗago ya kallesu, kallo ɗaya yayma Rose ya ɗauke kansa, hakan yay bala’in sosa ranta, dan akwai kwallin data shafa, an kuma tabbatar mata idan suka haɗa ido da shi zai haukace mata, yabar kallon kowacce mace da gashin arziƙi sai ita, amma ɗan rainin wayon tun’a station takeson su haɗa ido da shi hakan ya gagara…

         “Boss! Lafiya dai ko?”.

Aliyu da ya kafeshi da idanu ya faɗa.

       Lap-top ɗin ya ajiye yana faɗin, “Da dai sauƙi Aliyu, an yanka ne ta tashi”.

         “Kamar ya?;” suka faɗa cikin haɗa baki su uku, rose ce kawai da bata fahimci hausarba batace komaiba.

        Cikin takaici Jawaad yace, “Ƴan uwana wasan jiya ya koma yaƙi, kukan tsuntsuwa mai zanen kanari ya zame mana abin magana”.

        Sun fahimci zaurancensa, saboda wannan yana ɗaya daga cikin salonsu, musamman akan aikin da suka samu gamayya da waɗanda basa cikinsu, sai dai basu fahimci dalilin zaurancenba a yanzu, saboda duk sune a wajen babu baƙon ido.

         Jabeer yace, “Jay bansan miyasa ka zaɓi ƙin buɗe zancenba, bayan kuma duk mune babu wani bare a cikinmu?”.

       Jawaad yace “Nima bansan miyasa harshena ya zaɓi hakanba Jabeer, sai dai saƙon kamar tun daga zuciyane”.

       “Idan na fahimta, kamar zuciyarka na ɗarsa maka akwai ɗan baya ga dangi kenan a cikin tafiyar?”. Hafiz yay maganar cikin taraddadi.

         Cikin sauke nannauyan numfashi Jawaad yace, “Bani da tabbas, sai dai zuciyata na rayamin akwai idon mikiya a bayanmu”……………✍

13

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻1Page 5

      

        ………….Duk Kasa cewa komai sukai, sai idanu da suka zubama Jawaad tamkar wani bakonsu.

             Rose da zuciyarta ke tafasa akan rashin kallonta da jawaad baiyiba ta kasa daurewa, ta dubesu baki ɗaya a wani yanayi, “Boss wai mike fauwane? tai maganar cikin harshen turanci da tsare Jawaad da idanu tana fatan ta dace yanzun.

       A mamakinta yanzunma dai ƙin kallonta yayi, sai Lap-top ɗinsa ya miƙa mata kawai, ya koma ya zauna tare da ɗaukar tab.. Ɗinsa ya shiga tafa saƙo da hanzari.

      Gani nai Aliyu ya ɗago ya kallesa, yay masa wani salo da ido tare da cije baki, murmushi Aliyu yayi kawai ya maida kansa, kafin ya miƙe yabar falon, hakama Jabeer da Hafiz duk ya tura musu suma, Hafiz shima tashi yay ya fita, Jabeer kuma ya koma kusa da Rose dan kawai ya ɗauke hankalinta da aikin da Jay ya bata itama.

         Bayan fitar su Aliyu da kusan mintuna tara ya miƙe yabar falon ya nufi bedroom ɗinsa. Sai da ya kulle ƙofar kafin ya ciro ƙaramar wayarsa yay kiran Hafiz.

          “Hafiz yaya? An dace kuwa?”.

“Ba’a daceba Boss, amma ga shawara mana?”.

       “Micece shawarar taka?”.

“Mu bincika kowanne manhajar yanar gizo ko zamu dace wani ya ɗauka, kasan yanzu ba’a raba mutane da ƴan ɗauke-ɗauke a waya, maganar gano wanda ya kaima su B.G kuma ba abune mai sauƙiba ace yanzu da gaggawa, sai dai mu canja shawara ta wannan gaɓar”.

       “Na fahimceka Hafiz, yanzu kayi duk yanda ya dace, amma inaji a raina koma wanene yakai wannan bayanan yana da kusanci damu Hafiz, amma banason zargin kowa”.

       “Boss zargi dolene, kuma koma wanene ya daɗe a jikinmu, a sannu zamu cinmasa da ƙarfin ƙudirar UBANGIJI, dan shine ke haska mana hanya a dukkan lamuranmu”.

      “Insha ALLAHU Hafiz, yanzu dai sai na jika”.

      Yana yankewa yay kiran Aliyu shima, sai dai daga ɓangaren Aliyun an dace, dan ya turo masa dukkan bayanai akan Bilkisu da abinda ya shafi shigowarta hukumar tasu, da horon data samu, da ƙwazon data nuna tun a wajen horaswa, alaƙarta da Qaseem,  sai dai babu wani bayani kafin zuwanta gidansu Qaseem ɗin, hakkanne yaɗan tsayama Jawaad a zuciya, har yakejin dolene ya sake binciken, dan karfa nan gaba ta zame masa ƘWAI CIKIN ƘAYA kuma kamar yanda ƴan bayan fage ke hasashe.+

         Daga ɓangaren Hafiz ma an dace daga baya, dan kuwa cikin amincin ALLAH ya samo bidiyon faruwar komai tun daga lokacin da Bilkisu ta kaima motar masu laifin caffa kafin zuwansu, har zuwa sanda abubuwa suka lafa.

        Yaci karo da Bidiyon ne a wani chennal na youtobe, bayan ya shiga manhajar Google yay Searching, sai dai abinda ya bashi mamaki yana kammala sauke video’n akan manhajar ta youtobe wanda ya ɗora ɗin ya saukeshi daga accaunt ɗin, hakan sai yay bala’in ɗarsa mamaki a zuciyar Hafiz, harya kasa haƙuri ya kira Jawaad ya shaida masa.

         Murmushi Jay yayi yana shafa kansa, “Ba abin mamaki bane Jabeer, musamman idan mukai la’akari da babu wata kafar yaɗa labarai da dama ta saki bidiyon mai tsawon hakan, sai wasu ɓangarori da dukansu iya inda muke musayar wutane kawai”.

       Hafiz yace “Hankalina sam bai kaiba sai yanzu kam, koma miye yake a ɓoye ALLAH zai bayyanashi ai, mudai domin ALLAH mukema ƙasarmu aiki, duk mai yunƙurin daƙilemu kuma ALLAH zai mana maganinsa”.

      “Insha ALLAHU kuwa Hafiz” Cewar Jay cike da takaici.1

Kafin dare duk sun haɗa bayanan da ya kamata akan maganar, sun tura iya waɗanda Sir Ahmad ya umarcesu zuwa Office ɗin, L.G, sauran kuma sun adana a wajensu domin ya zame musu hujjar kare kai, hatta da bidiyon suma gutsira sukai suka tura, sauran kuma suka adana a wajensu.

      

    

                ___________★__________

                           SHAHUDAH

     _________________________________

                   Tunda suka fara zuwa gidan rasuwarnan sau ɗaya taga Jawaad, harga ALLAH ita kuma dominsa take zuwa, a tunaninta idan suka haɗu zai matuƙar rikicewa da ganinta, musamman ma yanda ta sake canjawa da ƙyau mai ƙayatarwa, sosai ta gama shirya shika-shikan rama dukkan abubuwan da yay mata kafin ta yarda da buƙatarsa ta komawa gidansa.

     Sai dai abin mamaki da al’ajabi dukkan tunaninta sai bai zama gaskiyaba, dan kuwa ko a randa suka haɗu kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, komai kuma a kan idanun Mom ya faru, dan suna a falon mama Atika ne a washe garin rasuwar ya shigo da baƙi su Sir Ahmad da sukazo gaisuwa. Sarai idanunsa sun gane masa Shahudah, amma sai ya ɗauke idanu cikin nuna halinsa na ko’in kula da abu.

       Abin ya sosa mata rai sosai, amma saita danne da yaƙinin ƙila yayi hakane saboda ganin suna cikin jama’a. Koda suka koma gida sai basuyi maganar da Mom ba, saboda kowa ya dawo a gajiye wajen bacci yafi buƙata. Washe gari kuwa kwalliya tayi ta musamman dan Jawaad nanma babu sa’a, dan har dare da suka baro gidan bata sakashi a cikin idanunta ba, washe gari kuma suna isowa gate ɗin gidanne motar Jawaad ɗin ke fita da alama ya nufi office ne. Waɗanan akasin da akaita samune suka jefata a cikin damuwa har yau ta kasa daurewa.

STORY CONTINUES BELOW

      “Mom kinga abinda Bb ya kemin kuwa? Bayan ya kamata ace ya nuna zalamarsa da kewata na shekarun da muka kwashe bama tare”.

      “Huhm” Mom ta faɗa tana shafa kan Shahudah dake saman cinyarta, dan kuwa suna cikin bedroom ɗin Mama Atika ne ita da Shahudahn kawai, dan ta fahimci ɗiyar tata na tare da damuwa, yau tunda sukazo gidan ta shigo ɗakin Mama Atika bata sake fitaba, shiyyasa ta biyota, sai ta isketa cikin damuwa, hakanne ya sakata zama ta dora kan Shahudah a cinyarta tana shafawa, itakuma take bata labarin ruɗanin data shiga akan tarbar data samu daga wanda batai tsammaniba daga Bb ɗinta (Jawaad).

       Mom ta haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi tana sake yamutsa sumar Shahudah’n, “Kar taurin kan yaron nan ya ɗaga hankalinki fiye da haka Shahudah, ki barsa, ni da kaina zan sauke masa wutar dake ci a kansa, bara dai a gama hidimar rasuwarnan kinji”.

      Kai Shahudah ta ɗaga mata cike da shagwaɓa, har ƙwalla na sakko mata a kan kumatu tace, “Amma Mom wane mataki zaki ɗauka to?”..

    Mom ta share mata hawaye tana murmushi, “Karki damu Shahudah zaki gani, kedai sonake kicigaba da kwantarmin da hankalinki, nan kusa kaɗan zaki dawo ɗakin mijinki”.

        Kai Shahudah ta ɗaga mata tana murmushi da rungume mom. Murmushi mom tayi taci gaba da lallashinta cikin so da ƙauna.

Nikam nace, “Mai uwa a gindin murhu baya cin tuwonsa gaya ai Shahudah😋😜🤸🏼.2

               ..::..★__________★..::..

                          BILKEESU

     ____★..::..★__________★..::..★____

          Kwanaki huɗu cir bana zuwa Office ina gida ina jiyyar hannuna, yayinda kullum Ummie ke tare dani, ƴan gidanmu kuwa basa yini suna gidan rasuwa, barci kawai ke kawosu gidan. A kwana na biyar nai shirin komawa aiki, dan naji sauƙi sosai, a kuma daren ranarne Yah Qaseem ya dawo, nayi farin cikin dawowar tasa, dan nikaina nasan idan nace banason Yah Qaseem na yaudari kaina, a ƴan kwanakinan da bayanan sosai nayi kewarsa.

       Tun a daren yake jeramin tambayoyi akan hannuna, bai samu amsa ko ɗaya ba daga gareni sai murmushi kawai.

      Koda muka tashi da safe ma dai bai fasa sonjin musabbabin ciwonba, da naga ya damu sai kawai nace masa tsautsayine ya gitta mani a wajen aiki, badan ya yardaba ya ƙyaleni kawai, kasancewar yau zan koma aiki nima sai na bisa muka tafi tare kamar yanda muka saba kafin yay tafiyar.

        Yah Qaseem na gama daidaita fakin motarsa wani jami’inmu na isowa wajen, ya isarmin da saƙon kira daga office ɗin B.G, maganar da jami’in yazo da itane ya sakamu kallon juna ni da yah Qaseem ɗin.

        Idanuna na janye daga cikin na Yah Qaseem daya tsatstsareni da kallon tuhuma, da ƙyar na haɗiye yawun da ya tarumin a baki, dan girman office ɗin mai kiran nawa na kalla da kuma tunanin minene dalilin kiran?.

      Yah Qaseem da har yanzu idanusa ke kaina da alamar tambaya na kuma kallo, ya gyara tsaiwarsa yana mai jehomin tambaya,

      “Bilkisu mikike ɓoyemin ne?”.

Da sauri na girgiza masa kaina, “Wlhy Yah Qaseem bana ɓoye maka komai, nima bansan minene dalilin kiranba, amma bara naje najiyo”.

     Ban jira amsarsaba na bar wajen cikin tafiyar sassarfa, zuciyata sai bugu take da sauri-sauri, dan inaji a raina wannan kiran bana lafiya bane ba, musamman idan nai dubi da ƙaramin matsayina a hukumar. 

         Koda na iso sai da na jira aka bani izinin shiga sannan, wannan shine karon farko da zan shiga office ɗin a rayuwata, ba shi kaɗai bane a cikin office ɗin, jinai wani abu ya tsargamin daga saman kaina har zuwa yatsan ƙafata, na aro jarumtar dole na yafama kaina tunda bansan minene dalilin kiranba. Na miƙa musu gaisuwa cikin girmamawa kafin na zauna inda aka nunamin.

      Tambayar farko da aka jefamin ta sakani ɗago idanuna na kallesu badan na shiryama hakanba, ba firgici ne ya sakani kallon nasu ba, nutsuwace ta zomin saɓanin yanda na shigo a rikice, dan kuwa a nawa tunanin inhar akan rikicin daya faru kwanaki biyar da suka wucene banga wani abin kuskure dana aikata a cikiba, zamana na gyara na fara amsa musu tambayarsu da iya gaskiyata dana sani.

       Yanda Bilkisu ke amsa musu kowacce tambaya kanta tsaye babu ko ɗigon firgici ko rawar harshe ya sakasu kafeta da idanu, su kansu iya zallar gaskiyarta suke gani a saman fuskarta da furucinta.

      Sun mata tambayoyi sosai, domin sake tabbatar da gaskiyar tata suka sake maimaito mata dukkan tambayoyin da sukai matan a farko, abinda ta faɗa daga farko shine ta sake maimaitawa saboda hakan shine gaskiyarta.

Kusan awa ɗaya da wasu mintuna suka sallamoni na fito, a raina sai juya wannan al’amari nakeyi…

_________________________________

     

JAWAAD

     

             Zaune yake a office yanata aikin duba wasu tulin takardun dake gabansa yaji knocking ƙofa, siririn tsaki yaja dan baya buƙatar kowa a irin wannan lokacin, izinin shigowa ya bada batare daya ɗago ba balle kallon wanene?.

     Ƙamshin turarenta kawai ya bashi amsar wacece, harta zauna bayan gaisheshi da tayi bai ɗago ɗinba, a haka ya amsa mata.

          “Mi kike buƙata?”

Ya faɗa yana cigaba da aikinsa batare da ya ɗago ɗinba.

         Duk da taji haushi sai ta danne, abinda ta gani kuma ta jiyo game da kiran Bilkisu da akayi office ɗin B.G ta zayyane masa, karon farko da ya ɗago ƙyawawan idanunsa ya sauke akan rose, sai dai baice komaiba. Duk da tsawon kwanaki kenan tana buri da buƙatar irin wannan kallon daga garesa saboda kwallin da take sakawa na jawo hankalinsa kanta sai ta kasa jurewa, dan wani irin kwarjininsane ya kuma cika mata idanu da gangar jikinta, tai azamar janye idanun nata ƙirjinta na wata irin harbawa.

       Har lokacin idon Jawaad na akanta, ya cigaba da ƙare mata kallon nazari har kusan mintuna biyu kafin ya janye ya maida ga aikinsa.

     Ɓoyayyen numfashi rose ta sauke, daga can ƙasan ranta kuma wani daɗi na sake mamayeta, dan kuwa dai tasan ta gama da taurin kan Jay kamar yanda bokanta ya sanar mata, inhar suka haɗa ido wannan kwallin na idonta to lallai tagama da mallakarsa har abada, ba kuma zai sake kallon kowacce maceba bayan itaɗin.

           Sakanni kusan ashirin bai tankaba, bai kuma sake kallonta ba. Takaici ya sake mamaye zuciyar rose, ta buɗe baki da nufin yin magana ya miƙe tsaye, bindigarsa da wayoyinsa dake saman tebir ya ɗauka ya tura cikin aljihun Blue jeans ɗinsa, tare da ɗaukar tab… ɗinsa a hannu. “muje” ya faɗa batare da ya kalleta ba.

     Binsa tai da kallon mamaki, harya buɗe ƙofar office ɗin ya fice, dole itama ta tashi da hanzari ta bisa, a ranta tana ayyana cewar ‘Yau ƴan wulaƙancinne a kansa kenan?’.

      Fitowar Jay daga office yay dai-dai da fitowar Bilkisu daga sashen office’s ɗin su B.G, kaɗan ya rage suyi karo, kasancewar hanyar data haɗa shataletalen office’s ɗin ɗayace kafin su ƙarasa su hau lifter da zata kaisu kasa.

      Da sauri naja baya ƙirjinna na motsawa, cikin dakewar harshe da banyi zaton inada shi ba nace, “Kayi haƙuri dan ALLAH , bansan ka taho bane”.

         Ƙyawawan fararen idanunsa ya zubamin kansa tsaye, kusan sakan biyar tamkar zai cinyeni dasu sannan ya janye batare da yace dani komaiba. ya raɓani zai wuce, hakan yasa na matsa baya na bashi hanya, tafiya ya fara tare da faɗin, “Biyoni”…………..✍ 

6

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻  10😂😂🤣😂🤣😆😆😆Kunsan miyasa nake dariyarnan? Akan yanda kuke ganin kamar bily tsoron Jay takeyi, dukfa halin da take shiga shiba fahimta yakeba, hasalima kallon miskila idan kun lura yake mata, akwai masu samun kansu a irin yanayin bily akan wani ko wata, sai daga baya suke fahimtar dalilin shigarsu irin wannan halin, itama bily lokaci zai warware mata komai har muma mu sami amsa, ina muku fatan alkairi aduk inda kuke, sosai Comments naku na sakani nishadi da sani typing kodama ban niyyaba.

   I love you wujiga-wujiga irin trillions ɗinnan🤸🏼🤸🏼🤸🏼 😍😘😍😘😍😘🤗.

10

 Page 6

              

        

      Ko kaɗan ban fahimci dani yakeba, musamman dana waiga naga rose data fito daga office ɗinsa a bayanna, wani kallo naga ta watsamin mai kama da takaicin tabi bayansa. Numfashi na sauke mai nauyi na shafa ƙirjinna dai-dai saitin zuciyarta dake harbawa da sauri-sauri, duk da na fahimci kallon da rose tai mani sai hakan bai dameni ba, dan bata ita nakeba. Nima fita nai daga wajen, na fito ainahin harabar station ɗin domin nufar sashenmu.

        “Ɗi! Ɗi! Ɗi!!” gimba ya danna mata horn kamar yanda Jay ya bashi umarni.

           Duk da naji horn ɗin hakan baisa na fahimci da ni akeba, saboda idan akai dubi da sauran jami’ai irina daketa kaikawo a harabar wajen, kowa da hidimarsa.

      “K! Wace irin daƙiƙiyace da baƙya fahimtane? A haka kike tunanin zama jami’ar tsaron al’umma!!?”

     Maganar Rose a tsawace ta shiga dodon kunnena ina gab da shiga lungu  da zai sadani da office ɗinmu. Da sauri na juyo, idona ya sauka akan rose dake huci da jifana da kallon takaici mai nunin tsana. Duk da naji zafin kalaman datai amfani dasu a gareni sai na danne saboda tana sama da ni, a ladabce nace, “Kiyi haƙuri maa! Bansan dani kike ba”.

    Tsaki rose ta buga, tare da juyawa tabarni  a wajen, wani jami’i dake tsaye kusa damu ya kalleni da tausayawa, dan shi dai yarinyar tunda tazo station ɗin ɗabi’unta birgesa sukeyi, ganin ban fahimci manufar rose ba sai yay min fassara akan nabi bayanta maybe kirana akeyi.

     Godiya nai masa, kafin nabi bayanta cikin nutsuwata, sam ban iya sauri ko rikita kaina a tafiya ba koda kuwa a tsorace nake, a yanzunma duk da zuciyata na cike da tunani da baƙin cikin abinda tamin ban rikita kainaba a yayin bin bayanta, can na hangota jikin wata farar mota mai ƙyau da ɗaukar hankali, na cigaba da takawa a nutse gareta, ina isa jikin motar ita kuma tana buɗe gaba ta shige, hakan sai ya sakani a duhu, dan bansan kuma wajenwa zanje ba. Saitin inda take na ƙarasa, na ɗan risina yanda zata ganni ina faɗin, “Gani maa!”.

     Kafin ta bani amsa ƙofar murfin baya naga ta buɗe, ita da drivern naga duk sun kalli bayansu, hakanne ya sakani kallon murfin ta waje nima, muryar drivern ta katse min tunani, “Ki shiga” ya faɗa yana nunamin bayan.

      Duk da na shiga ruɗani, ga harbawar da ƙirjina keyi hakan bai hanani bin umarninsaba, koda wasa ban kalli waye a bayanba, na shiga kamar yanda aka umarceni, sai da na zauna ne wani mayen ƙamshi ya samu cikakkiyar damar surɗaɗawa a ƙofofin hancina, da sauri nai ƙoƙarin kallon gefena, gabana ya faɗi dan ganin wanda banyi zatoba, fuskarsa babu alamar wasa kamar yanda na gansa yanzu da mukai karo…..

      “Sai kin gama kallona zaki rufe ƙofar ne?” muryarsa ta daki dodon kunnena babu zato, kaina na girgiza da sauri ina tattaro busashen yawun bakina da ƙyar na haɗiye, tare da jawo murfin motar na rufe. Nama rasa yanda zan fassara wannan al’amarin sam, gashi yanayin dana tsinci kaina ya hana mani damar yin nazarin daya dace da hakan.1

         Ɓangaren Rose da Gimba kuwa mamakine fal a rayukansu, gimba shaidane akan bai taɓa ganin rose ta shiga bayan motaba kusa da boss, baima taɓa bata wannan damarba koda a fuskane, idan har kaga wani ya zauna a kusa da shi to lallai sai dai cikin su Aliyu ne, amma yau abin mamaki sai gashi shi da kansa yasa hannu ya buɗema yarinya ƙarama murfin mota, ya kuma bata lasisin zama a gefensa, ‘Anya kuwa?’ ya ayyana akan laɓɓansa yana mai satar kallonsu ta mirror.

     Ita kanta rose a kume take da mamaki, ita duk zatonta wani abun zai saka yarinyar, bata kawo a ranta wannan abar zuwan jiya hukumarsu har tanada lasisin shiga cikinsu ba, balle harma ta shiga motar da boss yake ciki, a kusa da shima, shi da kansa ma ya bata lasisin zaman, abinda ita bai taɓa bata fuska a kaiba, ko zaman gaban motar da yakema sai ya gadama yake barintayi koda taso hakan kuwa, idan ko bata mantaba wannan itace shekara ta bakwai cif tare da shi tana aiki a ƙarƙashin group ɗinsa, ‘To mi hakan ke nufi?’ tayi tambayar a zuciyarta.

         Shi kansa Jawaad mamakin kan nasa yake, amma da yake shi kogine babu mai gane gabansa balle bayansa sai bai nuna koda a fuskaba, hasalima tunda suka fice daga station ɗin kansa na duƙene yana danna tab.. Da alama wani abun yakeyi, sai dai ƙamshin turaren bilkisu duk ya addabi hancinsa.

        Kowa da abinda yake kissimawa ransa har suka iso inda yake buƙata, gimba ya samu waje yay fakin, babu wanda yay yunƙurin buɗe motar a cikinsu balle ai tunanin fita, duk suna jiran umarni daga garesa. Shiko yay burus tamkar baiji motar ta tsayaba, sai faman danne-dannensa yake cigaba dayi a tab ɗin.

STORY CONTINUES BELOW

         Sosai zaman ya gundureni, ba komai ya jawo hakanba sai matsuwar da zuciyata ta samu saboda kusancin dana samu da shi tare da lokaci mai tsayi da hakan bai taɓa faruwa ba, da gefen ido na saci kallonsa, sanye yake da wandon jeans kalar bulu, sai t-shirt fara, ta kwanta a jikinsa luf, dan yanda ƙirarsa ta bayyana ta cikakken mutum mai motsa jiki kawai ya isa baka amsa, dogon hannu gareta, amma ya tattareshi sama ya koma iyakar gwiwar hannun, sai agogon fata baƙi mai azabar ƙyau a tsintsiyar hannunsa da gashi ke kwance na alamar jin daɗi, na sauke idanuna bisa yatsansa dake cakalar tab ɗin, sanye yake da zoben azurfa mai tambarin stone babba tamkar diamond, da gani kasan zoben zaiyi tsada koda ba’a faɗa makaba……..

       “Gimba ka tabbatar nanne wajen?”.

     Maganarsa ta katse min dogon nazarin dana tafi na babu gaira babu dalili.

        “Eh wlhy boss nanne, kuma wannan shine dai-dai lokacin da a kullum yake zuwa cin abincin safe shi da abokin nashi, a yanzu haka kuma inada tabbacin abokin nasa na cikin wajen, nanda mintuna ƙalilan zai iya fitowa”.

     Uffan bai ceba, ya kuma cigaba da sabgarsa tamkar bashine yay tambayar aka bashi amsaba, a fuska dai baiyi kama da miskiliba, abinda kawai na fassara halayyar wannan mutumin shine Ɗan wulaƙanci ne lamba ɗaya kuwa, babu wanda ya sake magana tsahon wasu mintuna, bansan mi sauran sukeba, ni dai ina takure ne jikin ƙofa idona a waje ina kallon shiga da fitar mutanen dake fitowa a cikin wajen cin abincin (Restaurant), kasantuwar gilashin motar mai duhune nasan babu mai ganinmu, sai dai mu mu gansa, hakan ya sakani baje idanuna nake kallon komai daki-daki.

       “Yauwa boss ga shinan ya fito” gimba ya faɗa da sauri yana nuna ƙofar shiga da fita na gidan abincin. Nidai kallon wajen nayi, shikam ko motsi baiyiba, bai kuma ɗago ya kalli abinda drivern ya nunaba, sai cewa da yay “Rose! Kibi wancan mutumin, duk yanda zakiyi kiyi magana ta shiga tsakaninku, magana kuma irin wadda zata iya zama mai kusanci”.

       “Okey boss” ta amsa da sauri tana buɗe motar ta fice, sai lokacinne naga ya ɗago kansa ya kalli wajen, ba tare da ya sauke gilashin motarba, “Gimba ka tabbatar ka ɗaukesu a hoto mai motsi” yay maganar idonsa a kansu.

     Saurin amsawa drivern yayi, tare da buɗe motar ya fice da sauri. Gabana ya faɗi dan ganin an barni daga ni sai shi a motar, sai dai nayi ƙoƙarin kamewa gudun karna zubda darajata da akasan ɗiya mace mai tarbiyya da ita, kallonsu na cigaba dayi kamar yanda shima na fahimci hankalinsa na kansu.

          Muna kallo rose ta bigi saurayin da ya fito daga wajen cin abincin yana latsa waya, wayar hannunsa ta faɗi, kusan a tare suka duƙa domin ɗauka, bakin rose ɗin na motsawa, sai dai mu bamajin mi take faɗa, saurayinne yay murmushi suka miƙe tare bayan ita ta samu nasarar tattara wayarsa data tarwatse a hannunta, magana yake mata tana bashi amsa da murmushi saman fuskarta, sai dai shima bamajinsa, ta miƙa masa wayar tana faɗaɗa murmushin fuskarta tamkar yanda shima yake faɗaɗa nashi, bai amshi wayarba sundai cigaba da magana, sai kuma mukaga suna ƙyalƙyata dariya a tare, hanya ya nuna mata alamar suje, babu musu kuwa tabi umarninsa, tana gaba yana biye da ita har wajen wata Blue ɗin mota, shine ya buɗe mata ta shiga ta zauna sannan shima ya buɗe ya shiga sashen mai tuƙi, munata kallonsu har suka bar harabar restaurant ɗin……

     Numfashi ya sauke a hankali yana ɗauke idanunsa da ga wajen, hakan ya sakani nima sauke nawa a ɓoye ina gyara zama cikin alamar takura, addu’ata da fatana bai wuce drivern ya dawo cikin motarba kona samu sauƙi, babban fatana kuma yace na koma gaba inda rose ta tashi, sai dai har tsahon mintuna biyar da barin su rose gidan abincin baiko motsaba balle ya kalleni, saima kansa da ya kwantar jikin sit ya lumshe idanu, “Ƙil!-ƙill!!” tab dinsa tai motsi alamar shigowar saƙo, bai motsaba, hakan yasa mamaki ya kamani……

        “Ɗauki ki duba mi tace?” ya faɗa ba tare da ya motsaba. Gabana ya faɗi, dan nadai fahimci dani yake, kuma yana nufin tab.. Ɗin tasa zan ɗauka, ganin bai sake maganaba ne ya sakani kallonsa, a ɗarare nace, “Dani kake sir?”.

       “A’a da kaina nake” ya faɗa a daƙile……

     Kafinma ya rufe baki na kai hannu na ɗauki tab ɗin da ya ajiye a tsakkiyarmu, gabana sai wata irin faɗuwa yake tamkar zan haɗiye zuciyata a cikin bakina, madannin na danna ta kawo haske, wani haɗaɗɗen hotonsa ya bayyana, duk da son kallon hoton da naji ya tsargamin hakan baisa na tsayaba, saima mamakin ganin babu lock a jikin tab din ne ya kamani, naja hoton yay sama kawai, a take apps da yawa suka bayyana, baza ido na shigayi wajen neman messeges app, da ƙyar na tsaida hankalina na ganosa, ina buɗewa kuwa da sunan rose na fara cin karo, na buɗe saƙon nata, abinda ta turo bai shige kalmomi hamsin ba.     “boss ya buƙaci nabisa, duk abinda ake ciki zakaji daga gareni”.

       Cikin ɗan rawar baki nakaranto masa kamar yanda ta rubuto da harshen turanci, bai motsaba, bai kuma tanka mani ba, hakan yasani ajiye tab ɗin ina mai satar kallonsa, sai da ya ɓata lokaci kafin ya jehomin tambaya.

        “Ya sunanki?”.

‘Ikon ALLAH’ na faɗa a raina kafin na bashi amsa da, “Bilkisu Adam makaho”.

       Yanda ya buɗe idanu da sauri a kaina ba ƙaramin firgitani yay ba, mayun idanunsa masu saka tsigar jikina tashi ya dasamin, bansan miya bashi mamakiba, sunan nawane? Kokuwa na babana? Kokuwa makahon dana ambata a ƙarshe?. bansan amsarba, bani da ƙwarin gwiwar tambayarsa kuma. Tsahon minti ɗaya da sakanni yana kallona kafin ya janye idanunsa yana motsa baki tamkar mai son cewa wani abu,ni dai ta wutsiyar ido nake kallonsa shi da jin kansa.

       Baice dani komaiba ya buɗe motar ya fita, ajiyar zuciya na sauke, dan fitar tasa sai naji kamar ya bani wani ƙaton filin cin karena babu babbaka ne…….

        “Ko sai an fiddoki?”. Furucinsa ya daki kunnena, da azama na buɗe murfin na fice nima, gani nai ya wani zubomin idanu, bansan mi yake nazartaba daga gareni, sai jefani a ruɗanin zuciya dana takurar kaifin idanunsa da yayi, hakan yaja nai ƙasa da kaina dan bazan jura kallonba.

         Takunsa kawai naji alamar ya matsa daga kusa dani, na saci kallonsa, sai naga yana ƙokarin ciro abu daga cikin but ɗin motar da ya buɗe, nufonin da yayne ya sani saurin ɗauke idona, ya miƙomin farar coat ta mata da tsayinta zai iya kaiwa gwiwa, ban musaba na amsa, sai dai ina buƙatar ƙarin bayani, “Saka” ya faɗa yana wuceni.

      Sosai naketa mamaki, na warware rigar na saka a jikina saman Uniform ɗin dana sanya, sai ya zam rigar ta ɓoye bayyanar ni wacece, baƙin wandon kawai ake iya gani ta ƙasa, daga sama kuwa farin baby hijjab ɗinane ya bayyana, sai rigar ta fiddamin da wani tsari daban daya bayyanar da sirrintaccen kwarjinina da wasu ke iya ambata da ƙyawu. Bai cemin komaiba yay gaba na bisa a baya, dan zuwa yanzu kam na fara fahimtar hallayarsa da hanyoyin maganin zama da shi.

      Sai da muka gabato shiga ƙofar wajen sannan ya tsaya muka daidaita tafiya, ƙasa-ƙasa na tsinkayi muryarsa yana magana.

        “Ki kula sosai, sannan ki tabbatar da yanayinki ya canja tamkar munada dangantaka, idan kikamin shirmen da aikina ya buɗe lallai sai kinyi nadamar hakan”.

       Sosai maganganunsa suka tsirgamin zuciya, dan kuwa ban gama fahimtar ma’anarsu ba balle manufarsu har muka ƙarasa shiga wajen.

         Wajen yay bala’in haɗuwa, daga gani kasan masu abokan magana a aljihune kawai keda hurumin shigarsa, dan danan akai mana tarba ta mutuntawa, yanda ya ƙawata fuskarsa da murmushi ne ya ɗauren kai, hakan yasani nima aro irin basajar tasa na yafama kaina ina murmushin, ɗaya daga cikin yaran wajenne ya nuna mana wajen zama, bayan mun zauna yake tambayarmu komi muke buƙata.

       Boss ya juyo yana kallona fuskarsa shinfiɗe da wani murmushin da ya kusa zautani, “My princess! Mi kike buƙata?”.

     Wata masifar harbawa zuciyata tayi, kaɗan ya rage ban fallasamu ba, nai azamar haɗiye zuciyata dake niyyar fitowa ta baki saboda salon da yay amfani wajen kiran sunana da yanayin fitar sautin, da ƙyar na iya dai-daita kaina nai wani farin da bansan na iyaba da idanu, ina wani narke murya nace, “Duk abinda ka zaɓa mana yayi my king”.

     Ɗauke idanunsa yay daga kaina, har zuwa yanzun fuskarsa ɗauke da murmushin da ya fidda lotsar dimples ɗinsa masu ɗaukar hankali, ya duba waiter ɗin yana bashi umarnin ya bashi list ɗin abinda suke da shi ya duba.

    Da girmamawa ya amsa yana barin wajen, saurin yin ƙasa nai da idanuna ganin ya maido kallonsa gareni, murya ƙasa-ƙasa yace, “Ina sake gargaɗinki a karo na biyu”.

     Kaina na jijjiga masa ina saurin gyara yanayina. Sallama wata matashiyar budurwa taimana saɓanin wanda yazo ɗazun, sanye take da Uniform ɗin wajen itama, cikin girmamawa ta ajiye goran ruwa biyu da kofuna dake saman tire ƙarami, kafin ta miƙa masa ɗan littafi dake a hannunta. Amsa yay yana dubawa, tare da yin alama da pen ɗin data haɗa masa da shi akan duk abinda muke buƙata, baifi sakan sha biyarba ya miƙomin littafin yana fadin, “Duba yayi?”.

     Amsa nayi ina kuma matse nutsuwata, nai nazarin duk abinda ya zaɓadin kafin na ɗago ina murmushi, cikin salon da bansan nayiba na ɗaga masa gira ɗaya da juya ƙwayar idona kaɗan alamar yayi.

    Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana sakin wani lallausan murmushi da yafi na ɗazu.

    ‘Innalillahi….’ Na iya ambata ina saurin maida fitsarindake neman kufcemin.

         Tana barin wajen ya kalleni da sauri, murya ya rage ƙasa sosai, wanda yake nesa damu zai ɗauka soyayya mukeyi, maganar da ya faɗamince ta sakani jinjina masa kai da sauri, ina kuma murmushi, badan tanada alaƙa da murmushin nawa bane, sai dan kawai barin murmushin akan fuskar tawa ya zama tilas saboda kiyaye gargaɗinsa25

ALLAH ka gafarta iyayenmu😭🙏🏻18Barka da juma’a.

5

  Page 7

……………..Mintuna kaɗan budurwar ta dawo da tire babba a hannu, wanda aka jero abubuwan da muka buƙata a kansa.

            Tana ƙoƙarin ajiyewane Jay ya miƙa hannu zai ɗauki ruwan da aka fara kawo masu, a salon da babu wanda ya isa fahimtasa har bily bata kulaba ya tanƙwaɓi tiren ya suɓuce, jikake “Tarats!!! Tass! Tatass!!” kwanikan da suka zube na fashewa, abinda ke cikinsu gaba ɗaya sun koma jikinsu sun wankesu, duk jikinsu ya ɓaci daga shi har bily da bata san mafari ba, a take duk hankalin mutanen dake kusa dasu ya dawo kansu.

              Na ɓata fuska saboda harga ALLAH banji daɗin yanda jikina ya ɓaciba. Cikin langwaɓe kai na kallesa kamar zanyi kuka.

        Da ƙyar Jay yay ƙoƙarin haɗiye dariyar dake neman kufce masa saboda yanda Bily tayi fuska kamar zata fasa ihu, ga mai da yay tsalle harkan fuskarta sai naso yake.

      A fusace  na miƙe saboda ganinma dariya yake neman yimin, dan da gaske haushi naji har raina, maimakon ya mata faɗa amma kuma tsabar wulaƙanci yake neman yimin dariya a cikin mutane, bamma san sanda na fara zazzaga mata masifa akan tayi hakanne da gangan ba, yanda ta rikice ba ƙaramin tausayi ta baniba, amma kuma uwar mi take kallo da zata wankemu haka?, shima jinake kamar na juya na talle masa ƙeya yasin.

           Jawaad ya tsaya kawai yana kallon bakin Bily dake masifa, babu shiri murmushi ya suɓuce masa, ganin tamkar abin nata da gaskene shima sai ya miƙe, cikin son maidota hayyacinta ya nema riƙo hannunta, amma sam taƙi yarda, dan danan wasu ma’aikatan nasu sukazo, da alama suɗin manyane, haƙuri suketa bamu amma naƙi saurarensu, daga ƙarshema nai ficewata, shikuma yay azamar biyoni yana faɗin, “princess! Princess! Please ki tsaya mana”.

     Ƙo juyowama banyiba na nufi motarmu na buɗe zan shige, saurin riƙe murfin yayi yasha gabana alamar hanani shiga motar, ya wani marairaice yana lallashina, wlhy da kunsan yanda zuciyata ke harbawa sanda muke a wannan yanayin da kun bala’in tausayamin, a haka budurwar da wasu ma’aikatan wajen suka iso suka taddamu, haƙurin suka cigaba da bamu, sai da muka ɗan garasu da kalamun cewar bazamu sake zuwa wajenba tunda basusan kimar Customers ba kafin na nuna na haƙura da ƙyar, dan zuwa yanzu na dawo hankalina akan shirinmu.

     Sun buƙaci mu koma wajen a bamu wani abincin amma na tubure akan bazan koma ba, sai dai a haɗo mana takeaway, ba musu suka amince da bukatata, ganin sunbar wajen ne ya sani sauke ajiyar zuciya ina matsawa baya saboda kusancin da muka samu ni da shi neman karya ƙwarin gwiwa da nake bama kaina ya keyi, gashi yay masifar tsareni da idanunsa.

     Shima matsawa yayi, ya nuna min mota alamar na shiga yana zubamin harara, “saurin shigewar nayi kuwa, ya rufemin murfin ya zagaya ɗayan ɓangaren, da sauri gimba dake bayanmu tsaye yana kallon dramar tamu ya buɗe masa, hanasa rufewa yayi, saima ya zauna ƙafafunsa duka a waje. A haka budurwar ta dawo ɗauke da takeaway ɗin da muka buƙata, gimba ya amsa ledojin, shi kuma ya miƙa mata atm card ɗinsa tare da wata takarda yana magana ƙasa-ƙasa, “Saboda baƙwason ya tona muku asiri kuka kasheshi?”.

     A firgice budurwar ta kalli Jay, sai kuma ta hau waige-waige jikinta sai tsuma yakeyi.

    Ya sake faɗin, “Ki daina ɓatama kanki lokaci, akwai address ɗin inda zaki sameta (ya nuna bily) a jikin takardar nan ranar lahadi, yarage naki kizo ko kiƙi zuwa, sauran bayani mahaifinki zanyimawa”.

     Sake rikicewa tayi, jikinta sai wata masifar tsuma yakeyi. Yanda taketa kallonsa a firgicene ya sakani tabbatar da maganar bamai daɗi ya faɗa mataba, tabar wajen da sassarfa, yayinda gimba ya take mata baya domin amso atm ɗin idan sun cire kuɗinsu.

       Wato dai duk yanda nake tunanin aikin nan namu yafi ƙarfin tunanina, irin wannan makirci haka tamkar wani shirin film.

 

          Gimba bai wani jimaba ya fito da ɗan hanzarinsa, motar shiru tamkar babu mutum mai numfashi, nidai takurace ta hanani yin ƙwaƙwƙwaran motsi, danma ALLAH ya soni yanzu a gaba nake ba kamar yanda muka zoba, shiko bansan mi yakeyiba, dan nakasa kallonsa koda ta mirror ne, abinda ya faru a wajen da wanda nayi keta dawomin a rai, sai naga kamar na zaƙe da yawa, ko a gidan uwarwama na samo ƙwarin gwiwar zuba masifar irin haka?’.

       Sai da gimba ya tada mota sannan yace, “Boss zamu koma station ne?”.

    Shiru bai bashi amsaba har muka fice daga gate ɗin wajen muka hau titi, ni nama ɗauka ko barci yakeyi, sai jinai ya bashi amsa da,

      “A.Y….”

Ban fahimci ma’anar maganarba, amma shi gimban naga kamar ya gane mi yace. Wayata daketa vibration tun ɗazun na kalla, yah Qaseem ne yanzuma, wannan shine kira na kusan bakwai kenan, tun muna cikin wajen cin abinci kiransa keta shigowa, sai dai bansan miyasa nakasa ɗagawa ba, a hankali na sauke ajiyar zuciya jin wayar ta yanke, kasheta nai baki ɗaya ma, dan bansan dalilin kiranba, idan kuma na ɗaga bansan mizance masaba, bankuma saniba ko ɗagawar zai iya zama laifi a wajen wanda muke tare. Isowarmu wani gida mai ƙyau da tsarine ya yanke tunanina, tunda aka buɗe mana gate muka shigo naketa bama idona abinci nidai, gimba ya tsaida mota ya buɗe ya fita, ni dai banyi yunƙurin fitarba harshi aka buɗe masa ya fice, akan idona yabar wajen ya nufi wata ƙofa mai alamar shiga ainahin cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya kaɗan ina lumshe ido, fatana yazam shikenan yace a maidani station………

       Kallon gimba dake bani umarnin shiga nai da sauri, yay murmushi yana sake maimaitamin, “Ki shiga inji boss”.

      Jinai tamkar na fasa ihu, amma bani da ikon cewa ba hakaba, dole na fito ina sake bin harabar gidan da kallo, gimba ne yaymin jagora har ciki, ‘Masha ALLAH’ na faɗa akan laɓɓana saboda haɗuwar da falon yayi, babu kowa a ciki sai ƙamshi mai daɗi dake tashi a cikinsa….

     Gimba yace, “Ki shiga nan saiki gyara jikinki”.

    Murmushi naɗan masa ina jinjina kaina, na nufi ƙofar raina cike da tsoro da mamaki, sai faman tambayar kaina nake ko ina matar gidan? Dan naji gidan tsit. ‘Kika sani ko tare suka shige ciki?’ zuciyata ta ayyana min haka, bakina naɗan taɓe, na tura ƙofar na shiga da sallama. Ɗakine babba, akwai komai na amfani kuma a ciki, sai dana gama ƙare masa kallo kafin na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton bayine, bayan na rufe ƙofar sai kuma nai tsaye ina ƙarema kaina kallo ta cikin madubin dake toilet ɗin, Toni ta inama zan farane? Ni bawasu kayane dani ba, gashi kayana sun ɓaci sosai, na zare rigar saman da ya bani, wadda kasancewarta fara ta ɓaci sosai, hakama wandona, amma da yake baƙine shi ba gani akeba, sai ƙamshin miya da yake da mai dakemin naso a jikine zaisa ka gane ya ɓaci shima sosai, shawarar cirewa na wanke nayi, dan haka na cireshi a ɗarare.

       Ban fahimci kuskurena na jiƙa wandonba sai dana gama wankesa nanfa tunanin inda zanje na shanya, da kuma ta yanda zanma fita shanyawar tunda bawasu kayanne daniba yazomin. jinai hawaye sun cika idona, ‘Ni balki naga takaina’ na faɗa a hankali ina haɗiye kukan dake neman zuwamin. A bayin na shanya wandon na fito ɗaure da sabon tawul dana gani, na zauna a bakin gadon na rabga tagumi ina addu’ar neman mafita.

     Nai firgigit jin an turo ƙofar kamar a fusace, fuskarta a haɗe ta shigo hannunta ɗauke da leda yellow mai tambarin M&N, cike da kallon tsana ta miƙamin ledar, amsa nai nidai cikin girmamawa amma ina mamakin yanda takemin a ƙasan raina. Juyawa tai zata fice na bita da kallo, sai da ta buɗe ƙofar sannan tace, “Ana jiranki” kawai ta fice abinta.

     Numfashi na sauke a hankali, na buɗe ledar na fidda kayan ciki, wandone da riga duk baƙaƙe, sai baby hijjab fari irin waɗanda nake sakawa, tashi nai na saka kayan, sunmin bala’in ƙyau, sai dai inajin kunyar fita a haka sosai, dan sun wani lafe a jikina dukda dai rigar bata matseniba, bani da zaɓin daya wuce daurewa na fita a hakan kawai, danma baby hijjab ɗin ya rufemin ƙirji, na maida kayan dana cire a jikina cikin ledar harda wandon dana jiƙa ɗin, kaina a ƙasa na fito daga ɗakin, zuciiyata sai harbawa take da sauri-sauri.

           Wani iri naji a raina ganin kusan su biyar ne a falon, sai na kumajina a matuƙar takure musamman saboda kayan dake jikina, ƙarasawa nai cike da aro jarumtar dole ganin su hankalinsuma ba’a kaina yakeba, sallama nai duk suka amsa mani, na gaishesu da girmamawa nanma suka amsa, na kula kamar kallon mamaki sukemin irin kamar basuyi tunanina ganina a wajenba, hakan sai ya sakani jin wani iri, na saci kallon dodon nawa, dan tunda na fito baiko ɗaga kai ya kalli sashen da nakeba, yana zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, idonsa na bisa takardun dake hannunsa, shima ya canja kayansa zuwa farin wando da baƙar t-shirt mai gajeren hannu, rigar ta kwanta masa a jiki, hakan yasa ta fidda ainahinsa na ƙaƙƙarfan mutum…….

       “Bismillah zauna mana”

Oga Hafiz ya katse min satar kallon boss dana shagala yi, kaina na jinjina na zauna a inda ya nunamin ɗin a ɗarare.6

      Tun fitowar Bilkisu a idanun Jawaad ne, duk kuma abinda take yana kallonta ta gefen ido, amma babu wanda zai iya fahinta, idan akai dubi da yanda ya maida dukkan hankalinsa ga takardar hannunsa, ɗago idanunsa yay yana kallon Aliyu dake danna lap-top, yace, “Aliy ya buɗe ne?”.

      Girgiza kai Aliyun yayi yana guntun tsaki, ya juya masa fuskar lap-top ɗin da faɗin, “Ni banama zaton yana amfani da accaunt ɗinnan gaskiya, boss wai mizai hana mu aika wani cikinsu kawai, sai naga haka kamar zaifi komai sauƙi da muzauna a bayan fage muna wahal da kanmu, tunda bamu da tabbacin yarinyar zata bamu haɗun kai”.

    Kafin Jawaad ya bashi amsa Rose dake gefensa tanata wani cika da batsewa tai caraf ta amshe zancen, “Boss dabaran Aliyu yayi sosai, kaga sai a aika yarinyarnan kawai cikinsun”.

       Wani mugun kallo da ya bama kowa mamaki a wajen Jawaad ya watsama Rose, sai kuma ya ɗauke kai batare da yace mata komaiba.

         Duk zuba masa ido sukai suji ko zai bama rose amsar maganarta, ni dai kaina a ƙasa ban ɗagoba inata wasa da yatsun hannuna, na ɗan saci kallon nasa nima sai naga ya cigaba da duba takardar hannun nasa ma tamkar baisan mi akeba. Tsawon mintuna bakwai muna a haka kafin muga ya ajiye takardan hannun nasa ya miƙe, wata ƙofa ya nufa, duk suka sake binsa da kallo harni da nakeyi a munafunce. yana shigewa duk suka maido dubansu gareni, inaga ganin yanda na takura kaina ne da ganin kamar bare a cikinsune ya saka oga Jabeer sakarmin murmushi, cikin tsokana yace, “Anya kuwa wannan ƙanwar tamu ba matsoraciya bace?”.

      Karon farko da nai murmushi, na ɗan kallesa na ɗauke idanuna da faɗin, “A’a Sir”.

    Dariya duk sukayi, amma banda Rose da ta ɗauke kai tana taɓe baki.

      Oga Aliyu dake danna lap-top har yanzu yace, “To idan ba matsoraciya bace ki saki jikinki damu, munan duk yayunkine ba surukaiba, minene sunanki?”.

      Naɗan kalli sashen da yake fuskata ɗauke da murmushi nace, “Bilkisu Adam makah..o”.

        Na ƙare maganar a hankali saboda yay dai-dai da fitowarsa daga ɗakin daya shiga, ya ɗoro baƙan jacket saman kayansa, ido muka haɗa, nai saurin janyewa nawa ina haɗiye murmushin kan fuskata saboda maganar da su Hafiz sukeyi na cewar “Ashe mai babban sunace, duk mai wannan sunan kuwa jarumace”.

     Duk dariya sukayi, amma banda rose da shi da muka sake haɗa ido a bazata, saurin janye idanuna nayi zuciyata na wata irin harbawa, hanyar ƙofa ya nufa yana faɗin, “Kumuje” Yana ƙoƙarin gyara baƙar jacket ɗin daya ɗoro saman rigarsa.

     Rose ce farkon miƙewa ta fice, niko ban motsaba sai da suka gama fita sannan na zama ƙarshe.

          Jikin motar da mukazo na hango rose tsaye, ta wani haɗe fuska, shi kuma yana daga gefe waya a kunnensa, hannunsa ɗaya a aljihun farin wandonsa, ido muka haɗa nai saurin janye nawa nidai, dan sam banyi zaton sashen da nake yake kalloba ma, a raina ina mamakin yanda duk sanda zan saci kallonsa nakan kama idanunsa a kaina shima, sai naji haushi na balla masa harara ta gefen ido duk da baisan inaiba.

     Duk tsaye mukai muna jiran ya kammala, kusan mintuna uku kafin ya sauke wayar ya tako wajen motar da rose ke tsaye, muma duk muna kusa, ya kalli Hafiz yana faɗin, “Yanzu yaya za’ai kenan?”.

         Hafiz yace, “Boss inaga ku koma Office, ni da rose da Aliyu zamuje can anguwar mu sake bincikawa, maybe mu samu wani a gidan yanzun”.

     “Okey hakan yayi” yay maganar yana yunƙurin buɗe motar, dole Rose data cika fam da haushi ta matsa, har zai shiga ta katse hanzarinsa da faɗin, “Boss nikam da sun wuce, sai na biku, zan ɗauka wayata dana manta a office, zan bisu a baya tunda nasan anguwar”.

       Ɗagowa yay yana kallonta fuskarsa babu walwala, ya janye idanunsa a kanta batare da ya bata amsaba ya maido kaina dan duk kallonsu mukeyi, “Mimaa! Shiga mota muje, ke kuma ki bisu kubiya ta station ɗin tare sai ku ɗauka wayan ku wuce”.

     Duk da naga idanunsa a kaina suke sai ban fahimci dani yakeba saboda sunan daya ambata, gashi har yayi shigewarsa motar.

      Jabeer dake kusa dani yay murmushi, “Dake yake fa, kije kutafi”.

    Kaina na jinjina masa kawai ina murmushin ƙarfin hali da sake juya sunan a raina, ‘Mimaa;? To wannan sunan kuma daga ina haka?’. Na ƙarasa zan shiga gaba, sai dai rose taƙi matsawa a wajen, na kalleta nace, “Zan shiga ciki maa”.

    Shiru bata motsaba, bakuma ta tanka minba…………..✍

11

Rose yau kinga idi wajen bily team, dama hauhinmu sukeji😥🤐.

90

Asha weekend lafiya😜😑😉🤗🤗.

14

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻17Page 8

………….Jawaad dake kallonsu daga ciki yay murmushi kawai yana girgiza kai, dan ya fahimci wani abu daga Rose ɗin. hannu ya miƙa ya buɗe murfin ɗayan gefensa, Hafiz dake ta wajen tsaye yace, “Kinga mai sunan Momcy zo tanan”.

      Amsa masa nai da “to” na nufi can duk da a raina banso hakanba dai, sai dai haka kawai naji inason bama shegiyar rose ɗinnan haushi yanzun, dan na kula sam bata ƙaunata dai, su mutanen duniya dasun ganka shiru-shiru saisu dinga ɗaukarka sakarai ko bakasan abinda kakeba, indai nice kuwa tasa kanta a ramin damisa wlhy. Ina shiga Hafiz ya rufe murfin, gimba yay ma mota key, bansan yanda aka ƙare da rose ba mukabar gidan bayan oga Jabeer ya shiga gaba bisa umarnin Boss da yay masa magana.

   

           Har muka isa station oga Jabeer da gimba na hira, amma ni dashi kamar mun haɗiyi kwaɗo. Yanda na takurama babu abinda nake buƙata kamar mu iso na sauka nidai. koda gimba ya tsaida motar ban fitaba saida duk suka fita, baiko kalli kowaba a cikinmu yay gaba abinsa zuwa hanyar office ɗinsa, Jabeer ne kawai ya kalleni fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “To mai sunan mom sannu da ƙoƙari, ki ƙara ƙaimi da jarumta dan aiki da boss sai jarumi na gaske”.

       Duk da ban fahimci zancensaba nai murmushi ina ɗaga masa kai, sannan nace, “ngd” a ƙasan raina kuwa ina tunanin wai sunan wa? gareni suketa wani boyen suna.

    Murmushi yay shima, ya nunamin cikin motar yana faɗin, “Karki damu babu godiya a tsakaninmu, ki tattara masa tarkacensa kibisa office dasu, ai kinsan office ɗin ko?”.

          Tamkar na fasa ihu haka naji, amma sai na daure nace, “Ban taɓa shigaba dai, amma na sani”. Yace, “To Alhmdllh saiki kaimasa ni na wuce office ”. Kaina na jinjina masa batare da nace komaiba, shima yay murmushi kawai ya wuce abinsa.

    Duƙawa nai na tattaro wayoyinsa da tab da wasu takardu daya bari sai bindiga da keys da bansan kona miyeba, sai ƙamshi suke tamkar suma turaren ake fesa musu, ledar takeaway ɗinmu gimba ya bani, ban musaba na amsa, dan duk zatona duk shi zan kaimawa, sallama nai masa na nufi hanyar da zata kaini office ɗin da kaya riƙi-riƙi saikace wata ƴar gudun hijira, danma na barma gimba ledata akan idan na fito zan karɓa dukda yacemin gida zaije. Sai da na hau lifter domin office ɗinsa na hawa na uku ne, sai saƙawa da kwancewa nake ina zancen zuci, na iso shataletalen da ya raba hanyoyi uku na offices ɗinsu, ɗaya nasan hanyar dazata sadaka da offices ɗin su B.G ne, wanda suke a hawa na ƙarshe, sai kuma ɗayar hanyar bansan offices ɗin suwayeba a wajen, sai ɗayar hanyar da naga ya fito ɗazun, nan na nufa kai tsaye, dogon corridor ne da ƙofofi jere kusan goma, hakan yasa na fara bi ina karanta rubutun saman gudun kuskure, sai da naje na bakwai sannan naga an rubuta Captain Jawaad A yusif, inada tabbacin nanne, dan tunda aka gayamin cikakken sunansa bantaɓa mantawaba koda a second ɗaya ne kuwa. Sai da na daidaita kaina da sake ƙarfafa zuciyata da ke neman faso ƙirjina ta fito sannan nai knocking har sau uku, amma banji an amsa maniba, nai jim kusan na minti ɗaya kafin na ƙara yin knocking ɗin kamar mai tsoron a jita, nanma shiru, nakai hannu zan sake aka amsa mani. Ajiyar zuciya na sauke a hankali kafin na tura ƙofar da sallama na shiga, office ne da ya amsa sunansa office, dan kuwa yayi ƙyau, babu wasu tarkace komai kuma tsaf, ga mayen turarensa ya kama office ɗin haɗi da freshener mai daɗin ƙamshi, sai suka bada ƙamshi na musamman, kallo ɗaya naima inda yake zaune a kujerarsa ta office na duƙar da kaina, shima kuma bai kalleniba, baikuma cemin komaiba, yanata rubuce-rubucensa hankali kwance tamkarma baisan wani ya shigoba. Jinai tsayuwar ta isheni, dan haka na gyara kaɗan ina yamutse fuska, batare dana ɗago na kallesa ba nace, “Sir gashi inji oga Jabeer”.

      Jay da tun ɗazu ya daina rubutun ya kwantar da bayansa jikin kujerar kawai yana kallonta da jinjina shegen miskilancinta ya lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci ɗaya, sai faman goga ƙasan biron hannunsa yake a jikin laɓɓansa, ko motsi baiyiba ballanta ya amsa mata. Tsabar miskilancin yarinyarne kawai ke bashi mamaki, ya ɗan taɓe baki tare da maida kallonsa ga Computer ɗin dake kan desk ɗinsa, bironsa ya ajiye yana lafe jikin kujerar ya fara sarrafa keyboard ɗin Computer ɗin.

          Ƙaran danna keyboard da najine ya sakani ɗago idanuna nai masa kallon second 2 na janye, karan farko a rayuwata dana sake jinjina wulaƙancin mutuminnan, ‘kenan bazai tanka mani ba komi yake nufi?’ na ambata a zuciyata ina maijin takaicinsa. Satar kallonsa na sake yi sai muka haɗa idanu, da sauri na janye nawa ina tura baki gaba batare dana san nayima hakanba.

     Sautin fitar ƙaramin tsakinsa ya sakani saurin sake kallonsa, yako dallamin harara alamun har yanzu idonsa a kaina suke, “Kin zama bodyguard ɗinane shin?” yay maganar a hankali kamar baison yi.

       Kaina na girgiza masa, duk da bani da tabbacin kallon nawa yake har yanzu, takawa nai zuwa gaban tebir ɗin na ajiye kayan harda ledar abincin, ban kallesaba bai kuma tankaminba na juya zan fita.

      “Zonan”

Na tsinkayi umarninsa. Juyowa nai kaina a ƙasa batare dana kallesa ba, “Zauna” ya sake faɗa a daƙile. ‘Kai nikam na shiga uku da wannan mutumin’ na ambata a zuciyata ina mai jina a matuƙar takure, zuciyata sai faman harbawa take da sauri-sauri. Shiru office ɗin ya sake ɗauka na kusan minti ɗaya, sai ƙarar keyboard da yake dannawa kawai kake ji. Knocking ƙofa akai ya bada izinin shigowa, matashin sauriyi ma’aikacinmune ɗauke da takardu a hannu, kallo ɗaya nai masa na ɗauke idona, duk da shi na lura sai kallon mamakin ganina a nan ɗin ya keyi, har takai boss ya daka masa tsawa.

      “Kallon mutane aka turoka yine!?”.

     Cikin sauri da ladab yace, “Sorry sir”.

      Banji ya tanka masaba, danni kaina a duƙe banma ɗagoba, sai sautin siririn tsakinsa naji kawai, shidai saurayin sai faman nanata kalmar haƙuri ya keyi kusan sau huɗu kafin ya fara masa bayani akan takardun hannunsa, banji ya tankaba, hakan yasani satar kallonsu, gani nai ya miƙa hannu ya amsa takardun yana dubawa, kafin ya ɗago ya kallesa da sake miƙa masa ta kardun yana faɗin, ”Ka kaisu office ɗin Lieut..; Richard, kace ya duba, zuwa anjima sai yazo dasu ina nemansa”. “Okey sir” ya faɗa cike da girmamawa kafin ya amsa ya fita ko sau ɗaya bai sake gigin kallon sashen da nakeba.

        Ɓoyayyen numfashi na sauke bayan ficewarsa, saima naji yaɗan bani tausayi……..+

STORY CONTINUES BELOW

     “Bani malt.. A cikin fridge”. maganarsa ta dawo dani hayyacina, miƙewa nai ina ɗan dube-dube a office ɗin danson gano fridge ɗin, shi kuma yaja ledan abincin ya buɗe, ganin fridge ɗin da nayi bayansa kaɗan ya sakani nufar wajen, kasancewar ƙaramine madaidaici yasa saida na sunkuya, malt ɗin ne kawai a ciki da coc… nidai na ɗakko abinda ya sakani tare da kofin dana gani a saman fridge ɗin kusan guda shidda saƙale jikin wani ƙarfe mai ƙyau, gabansa naje na ajiye ina haɗiye yawu da ƙyar, dai-dai yana buɗe takeaway ɗin gasashen naman kaza daketa ƙamshi, ina ajewa nabar wajen na koma inda na fara zama a ɗaya daga kujeru biyun dake gaban tebir ɗinsa, ganinai kawai ya turo naman gabana, na ɗago na kallesa muka haɗa ido, kuma tamke fuska yay ya nunamin naman. Tamkar zan fasa kuka nace, “Nifa na ƙoshi, azumima nakeyi”. Banza yaymin tamkar baima jiba, ya ɗauki gwangwanin malt ɗinsa ya ɓalle hancin ya kai baki, kafin ya ajiye ya maida hannunsa kan keyboard ɗin Computer ya cigaba da daƙilarsu. Mun kwashi kusan minti uku a haka, bai tankaniba, nikuma banci namanba dukda ƙamshinsa ya addabeni.

     kamar daga sama naji yace, “Karki bari na sake miki magana, kiyi ki fitarmin a office”.

      Batare dana shiryaba bakina ya suɓuce wajen faɗin, “Toni nacefa azumi nake, sokake na karya azumina ne?”.

       Tunda ta fara magana ya dakata daga daƙilar Computer’n ya zubama laɓɓanta idanu da kumatunta da take ɗan kumburawa, sai da takai aya sannan ya janye ya maida ga abinda ya keyi batare da ya nuna yamaji mita faɗaba.

         A matuƙar takure nake gaba ɗaya bugun zuciyata da numfashina sun dawo a maƙoshina, kaɗan nake jira na amayota kowama ya huta, yaƙi kulani, sannan yaƙi cemin na tafi, ganinfa yama manta dani saina miƙe abina na nufi hanyar ƙofa, bai tanka maniba har saida na kama ƙofar zan buɗe sannan yace, “An taɓa karyaki?”. Cak na tsaya, ni ban fitaba, ni ban komaba, bamma iya sakin mariƙin ƙofarba saboda yanda furucinsa ya daki ƙirjina, sai da na shaƙi iska na fesar sannan na juyo a hankali ina kallonsa, kauda kaina nayi saboda ganin shima niɗin yake kallo, ya wani haɗe fuska tamkar hadarin tsakkiyar ogusta.

        “Idan kika bari na sake miki magana ki kuka da kanki”.

      A yanda yay maganar da tsananin kaushi sai tsoro ya sake tsirgamin, dama dai ƙarfin hali nake kawai, dole na dawo na zauna ina sake haɗe fuska dan nikam gaskiya an sakama rayuwata ido, komawa nai kujerar dana tashi na zauna. Ina zama shikuma yana miƙewa ɗauke da wasu takardu ya fice daga office ɗin abinsa batare da yace dani komaiba. Na sauke nannauyan numfashi ina kallon naman, bani da zaɓinda ya wuce nacin kawai kodan ya barni na tafi, na ɗauki cinya nakai bakina ina ambatar bismilla, ɗanɗanon naman da laushinsa ya sakani lumshe idanuna, ko ba’a faɗaba dama namannan zaiyi ɗankaren daɗi ai, ban ankaraba na laƙume cinyar na sake ɗaukar wata tsoka irin ta haƙarƙarinan, (Damafa inaso shegen gulma ne. Lol) ina gab da cinyeta aka turo ƙofar da azabar ƙarfi aka shigo, a tsananin razane da ganin wanda ya shigo ɗinne ya sakani miƙewa babu shiri ina kallonsa. Shima idanunsa ya zubamin tamkar zai cinyeni da su.

         “Ubanmi kikeyi nan Bilkisu?!!”

Idanuna na lumshe saboda tsawar tashi ta rasha kunnuwana, na buɗe a hankali kansa, cike da dakiya na zubasu a kansa nace, “Yah Qaseem miya faru?”.

       Wata malalaciyar harara ya zubamin kamar zai juye idanunsa ƙasa, ya fara takowa inda nake, taku baifi ukuba tsakaninmu ya rage aka buɗe ƙofar office ɗin aka shigo. Ni da shi duk kallon ƙofar mukai, sai dai shi a take ya janye nasa idon yana jan uban tsaki. Nikam numfashi na sauke a ɓoye dan koba komai na samu kuɓuta daga wannan yunƙurin na yah Qaseem da bansan mi zuciyarsa ke kissima masa yaminba.

         Jay da ya shigo kuwa kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa ya taka zuwa ga kujerarsa ya zauna.

       A mamakina sai naga yama cigaba da daƙilar Keyboard ɗin Computer ɗin hankalinsa kwance kamar baisan damuba. Shima yah Qaseem ɗin bai tanka masaba ya kalleni yace, “Wuce muje”.

     Jawaad daketa danne-dannensa batare daya ɗagoba yace, “Kai ka kawotane?”. Dogon tsaki yah Qaseem yaja yana damƙar hannuna da faɗin, “Miye na azarɓaɓi ƙaramin tsagera, ai zan dawo kanka idan na gama da ita”. Ya ƙare maganar da fisgar hannuna muka nufi ƙofa. Jinake tamkar na kurma ihu, ‘Nikuma wannan wace fitinace na shigo ciki haka?’……….

      “Wlhy kika fita daga office ɗinan saina saɓa miki kamanninki!”

      Muka tsinkayo kakkausan furucin boss yayinda yah Qaseem ya murɗa ƙofar zamu fice. Bani kaɗaiba hatta da yah Qaseem ɗinma tsayawa daga yunƙurin fitar yay, ya juya yana kallonsa, nidai kaina a ƙasa na gaza kallon kowa a cikinsu, addu’ar ALLAH ya kuɓtar dani daga tsakaninsu kawai nakeyi a raina, dan bansan wazan bijiremawaba? Wakuma zanma biyayya ba?. Yarfar da hannuna yah Qaseem yay ya nufesa, zafin da najine ya sakani durƙushewa a wajen ina sakin siririyar ƙarar azaba.

      Qaseem daya ƙarisa gaban Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa har wasu abubuwan na faɗuwa, “A matsayinka na ubanwa zaka saɓa mata kamannin?”. Ko motsi Jawaad baiyiba balle ya kalli Qaseem, aikin gabansa kawai ya cigaba dayi hankalinsa kwance. A kausashe Qaseem ya sake maimaita tambayar tamkar zai mari Jay ɗin. Ɗago idanu Jawaad yay ya zubasu akan Qaseem, cike da gadara yace, “Qaseem fitarmin daga office!!”.

     “Anƙi a fita, kayi duk abinda kaga zaka iyayi” Qaseem ya maida masa amsa a zafafe shima.

     Jawaad bai sake magana ba, ya miƙe ya nufi Bilkisu dake durƙushe tana hawaye saboda hannunta dake zugi.

     

        Tsayuwar mutum kawai naji a kaina, cikin bada umarni yace, “Tashi”. Miƙewa nai babu musu, na saci kallonsa, ganin shima kallon nawa yakene yasa na janye nawa ina goge fuska, kafin ya sake wata magana yah Qaseem yazo ya shiga tsakkiyarmu, ”Wuce muje” ya faɗa yana nunamin hanya, haushin murɗamin hannu da yayne yasa naƙi motsawa. Ganin naƙi motsawarne ya sake hasalashi ya ɗaga hannu zai saukemin mari.

         Rufe idona nai da sauri naja baya saboda masifar firgita da nai da ihun da yaymin akai, na ƙanƙame jikina ganin ya ɗaga hannu zai makeni, shirun da naji yasani ɗago kaina kaɗan naga miya hanashi dukan nawa da yay niyya.. Saurin waro idanu nai waje ganin boss riƙe da hannun Yah Qaseem da ya ƙara kumbura sai hura dogon hancinsa yake.

       “kika fita saina karyaki a office ɗinan Miemaa” boss yay magana a dake  kamar yanda na fahimci halittarsace yin magana kai tsaye koda a gaban wa yake. Saurin duƙar da kaina nai saboda tsatstsareni da yay da idanu, nai baya daga kusa dasu cike da tashin hankalin sakani tsakkiya da sukai.

        yah Qaseem ya fisge hannunsa dake cikin na boss ya kai hannu zai damƙoni ina ƙoƙarin matsawa. Cikin matuƙar zafin nama boss ya fisgi yah Qaseem ɗin gefe, hakan sai ya bani damar mannewa a bango na sake musu kuka kawai, dan zuciyata bazata iya ɗauka ba.8

          A cikin tsagwaron fushi Qaseem ya damƙi wuyan rigar Jawaad zai shaƙeshi, “Amma kasan zan iya illataka ko?”.

     Murmushi Jawaad yayi yasa hannu ya ture hannun Qaseem dake damƙe da wuyansa, cikin halin ko in kula yace, “Ka illatanin mana Qaseem, kai wai wace irin banzar zuciyane da kai haka? Mace zaka ɗaga hannu ka daka?”. A matuƙar masife Qaseem yace, “ina ruwanka? Miye matsalarka?” baki Jawaad ya taɓe yana watsa hannayensa da ɗage kafaɗa yace, “Banda” ya ƙare maganar da juyawa zai koma kujerarsa. Saurin maidoshi baya Qaseem yay, hakan ya saka Jawaad tsayawa sai dai bai juyo ya kalli Qaseem ɗinba, ƙoƙarin danne zuciyarsa yake dan bayaso su raba hali gaban yarinyarnan kamar yanda ya kula Qaseem yana buƙata. Cikin nunashi da ɗanyatsa Qaseem yace, “Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da zaka sake saka Bilkisu! cikin lamarinka, itaɗin matar dazan aurace, ya rage naka ka kiyayi ko kaci gaba”.

       Rumtse idanu Jawaad yayi saboda jin yanda Qaseem ya ambaci sunan mahaifiyarsa gatsal, ya juyo a hankali yana kallon Qaseem cikin ido, cikin ƙunar zuciya yace, “Ko wacece ita a wajenka baya gabana, sai dai kai kasani baka isa hanani sakata aikin dana gadamaba tunda har tazo station ɗinnan a ƙasana, kasa a ranka yanzu aka fara wasan kuma, ina gargaɗinka Ka kiyayi  kai hannu kan mace da nufin duka”. ya ƙare maganar a wani irin yanayin rainin wayo. Hakan sai yay masifar sake fusata Qaseem, a tsawace yace, “Matsayinka na ubanwa?”…………..✍

     1

Qaseem team & Jawaad team banda faɗa kuma 🚴🏼🏋🏼🤼🏼😂😖.32

Ina Bil-Qas team nidai😜🤫🤸🏼.20

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻21Page 9

…………A matsayinka na ubanwa?” cewar Qaseem a fusace.

        Cike da rainin wayo Jay yace, “Lokacine zai nuna maka”.8

             Jabeer da ya shigo office ɗin kusan mintuna biyar da suka shuɗe, amma jaraba ta hanasu ganinsa yay gyaran murya.

        Duk kallon ƙofar mukai, Cikin nuna alamun tamkar baima fahimci mike faruwa a office ɗinba ya kalleni tare da miƙamin kwalin dake a hannunsa, “Momcyn mu kikai wannan Office ɗin MM; daga nan ki wuce ƙasa naga ana nemanki”.

     Kaina na ɗaga da sauri, na amsa kwalin na fice ina mai godema ALLAH da zuwan oga Jabeer da yay belina hannun waɗanan zakunan.

      Babu wanda yay magana tsakanin Jawaad da Qaseem ɗin har Bilkisu ta fita, Jabeer ya maida kallonsa kansu yana ɗan murmushi, “Haba basawanmu, ya zaku saka yarinya tsakkiya kuna yaƙi? Ai saiku rikitata, miye nata a ciki tunda batasan miye tsakaninku ba?, yakamata kumata adalci, aiki take kamar yanda kuke aiki, ku sakata abinda zaku sakata matsayinku na waɗanda suke sama da ita, amma bawai ku sakata tsakkiya akan abinda ke zukatanku ba”.

      Juyowa Jay yayi, kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kansa kawai ya juya yana mai ɗaura hannunsa a kafaɗar Qaseem ɗin yaɗan bubbuga kaɗan ya koma mazauninsa. Binsa da kallo Qaseem yay cike da takaici da baƙin ciki, a ransa yana rayama kansa inhar Jawaad yay gigin cigaba da kutse a al’amuran Bilkisu wlhy wannan karon sai ya karta masa rashin mutuncin da bazai taɓa mantawa da shiba har ƙarshen numfashinsa, yaja tsaki tare da harar Jabeer ya fice daga office ɗin..

           Jabeer dake binsa da kallo ya girgiza kai kawai sannan ya juyo ga Jawaad da ya cigaba da harkar gabansa, ƙarasawa yay ya zauna yana ɗora wayarsa a tebirin Jay ɗin, “Boss dan ALLAH son yarinyarnan kakeyi ne?”.

      A bazata maganar ta zoma Jawaad, dan haka babu shiri ya ɗago idanunsa da sukai sirkin jaa da ƙara girma ya watsama Jabeer ɗin wata uwar harara, sai kuma yaja tsaki  ya maida kansa ƙasa.

        Jabeer ya haɗiye dariyarsa yana gyara zamansa, “ALLAH ba wasa nakeba Jay, kuma idan hakan ta kasance wlhy zanyi murna, dan nutsuwar yarinyar na burgeni, g……”

      “Motsoww! Jabeer banason shirme, wace irin banzar maganace wannan, Please banaso karka sake”.

    Hannu Jabeer ya haɗe waje guda alamar ban haƙuri, Jawaad ya kuma hararsa ya ɗauke kai. Shidai Jabeer yay murmushi kawai, cikin son kauda zancen yace, “Yanzu nakeji su Sir Ahmad sun sake shiga meeting akan batunnan”.

         Jawaad da kansa ke durƙushe yana aiki yace, “Basai suyi tayiba tunda basu da tunanin kansu sai abinda aka ɗorasu a kai”. Jabeer yace, “Wlhy Jay ni mamaki suke bani ma, saboda ALLAH maimakon subama yarinya ƙwarin gwiwa akan abinda ta fara sai kawai su ɓige da tsugunne-tsugune, kai yanzu mi kake tunani akan batun?”.

      Kallonsa Jay yayi fuska a taɓe, sai kuma yaja tsaki ya maida kansa ga abinda yakeyi, “Tunanin mizanyi akan wannan shirmen Jabeer, iyakaci suce zasu dakatar da ita na wani lokaci ta huta, ko su canja mata wajen aiki ai dai ko? Tunda basu isa suce ta ajiye aikiba akan hakan”.

      “To ai babu wanda ya kamata kabari ya kasance a ciki” cewar Jabeer yana kafe Jay da idanu.

      Shiru Jawaad yay bai tankaba, tsahon mintuna biyu harma Jabeer ya fidda rai da samun amsa sai yaji yace, “Akanmi zan hana ni kuwa? A matsayina kuma nawa? Dukansu ogannina ne, suna sama dani nesa ba kusa ba, to mizan iya musu kona hanasu?”.

          “Jay! Saboda ina ƙwaɗayin yarinyar ta shigo tawagarmu”.

       “Humm” Jawaad ya faɗa a taƙaice.

Jabeer da ya fahimci amsar kenan sai ya cigaba da faɗin, “Ba ƙaramar nasara bace hakan a garemu Jay, dan inaji a raina zata ƙara kawomana nasarori, amma kadaiyi tunani akan hakan”.

      Ƙin cewa komai Jawaad yayi, hakan yasa Jabeer sakin zancen shima ya ɗakko masa na aikin da suka fara yau kawai, ananne Jay ɗin kuma ya bashi dukkan attention ɗinsa suka shiga tattaunawa.1

       

★★★★★★★

         lna fitowa daga office ɗin MM naci karo da Ummie, bansan miyasa na tsinci kaina da gyara yanayinaba na sakar mata murmushi, hararata tayi ita kuwa tana fusgar hannuna mukai gaba. Masallaci muka nufa dan lokacin sallar zuhur yayi.

     Bayan mun idar da sallane mun fito Ummie ke tambayata akan ina naje? Mi kuma ya sami kana?. Ban wani ja zancenba na bata labarin abinda zan iya, sai dai ban bata labarin miya faru tsakanina da yah Qaseem ba da kuma ceton da boss yay min a hannunsa yanzun.

          Sosai naga mamaki a wajen Ummie tattare da labarin nawa, harna kasa haƙuri nai mata tambaya, tai ƴar dariya kawai da cewar, “Abunne da mamaki ALLAH, wannan mutum mai fuska kamar hadarin tsakkiyar damina ɗin?”.

       “Ba abin mamaki bane Ummie, ni kawai na danganta lamarin da abinda ya farune ranar, ganina yake kamar wata jarumar gaske, baisan lamarin duk buge bane kawai” sosai Ummie ta kwashe da dariya cike da shaƙiyanci, nakai mata duka ta kauce tana cigaba da dariyarta, sai da tai mai isarta sannan ta dawo tana bani haƙuri muka shirya, daga haka muka cigaba da tsokanar junanmu da aikin dake gabanmu kuma.

     Har lokacin tashi yayi ban sake saka boss da yah Qaseem a idanunaba, dama bai zama lallai na gansunba kasancewar bani da hurumin hakan sai idan sune sukaso, haɗuwarmu a inuwa ɗaya dama sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Haka kawai na tsinci kaina da tsoron bin yah Qaseem, sai kawai nabi Ummie ta saukeni a gida

STORY CONTINUES BELOW

   ★★★★★

            Bayan sallar magriba ina zaune a saman abin salla ina azkar aka turo ƙofar ɗakina aka shigo, kaina na ɗaga ina kallonsa, yanda fuskarsa ke a tamke saida naji gabana ya faɗi, amma sai na dake abina nace, “Yah Qaseem ka dawo?”. Baice dani uffanba sai wata uwar harara daya makamin, ɗauke idona nai tamkar ban ganiba,  ya ida shigowa cikin ɗakin yana bin ko ina da kallo, bakin gado ya ƙarasa ya zauna, hakan sai ya sakani jin wani iri, dan kuwa ni kaɗaice a gidan, koda na dawo ban iske kowa ba, su mom basu dawo daga gidan rasuwaba. A daƙile yace, “Waye ya maidoki gida?”.

       Kaina tsaye nace, “Ummie ce, na jiraka naga baka fitoba gashi magrib ya gabato, sai kawai na biyota”.

        Shiru yay tamkar bazaice komaiba, sai numfashi yake saukewa da sauri-sauri, hakan yasani tsira masa ido, “Yayah lafiya kuwa?”.

         Wata harara ya sake danƙaramin kamar idonsa zai faɗo ƙasa, “Uwar miye haɗinki da shi Jawaad ɗin? Da har zaku  fita tare? Ban miki Warning akansa ba?”.

        Zamana na gyara sosai akan abin sallar saboda jin ƙafata ta fara yami, duk da na lura bawai maganar wasa yakeminba inata ƙoƙarin dakewa.

       Bansan yanda zan bashi amsa ya fahimtaba, amma ni banajin kuskure nayi tunda akan aikine ai. “Dake nake magana Bilkisu!!”. Saurin kallonsa nayi danjin yanda yay maganar a kausashe, nace, “Aiki muka fita fa”.

       “Aiki? Duk jami’an dake cikin Station ɗin babu wanda zai ɗauka suje aiki sai ke?”.

         “Yayah ni wlhy ban saniba”.

Saida yasake watsamin harara dayin ƙwafa sannan yace, “Su kuma waɗannan kayan na jikinkifa da nagani ɗazun? Ina kayan da kika fita dasu daga gida da safe?”.

     Kaina tsaye nace, “A wajen aiki da muka fita ne a mistake jikinmu ya ɓaci, to shinefa sai… Sai… Sa………”

      “Sai ubanmi? Bilkisu!!”.

“Sai Rose ta bani wasu kayan na zanja”.

       “Harda ita kuka fita?” yay maganar cikin kakkafeni da idanu. “Eh” na bashi amsa cike da ƙwarin gwiwa.

        Karon farko da yaymin murmushi, ya sakko daga saman gadon ya zauna kusa da ni sosai ya tanƙwashe ƙafafunsa (Dan zuciyarsa tayi sanyi jin basu kaɗai bane, amma hakan ba yana nufin zaiƙi saka musu ido bane ba). Yanda muka samu kusancine ya sakani matsawa baya kaɗan, baice komaiba, saima hannuna daya kamo cikin nashi, nai ƙoƙarin amshewa amma sai ya hanani damar yin hakan, murya a sanyaye yace, “Bilkisu!”.

        Amsawa nai idona na kawo ƙwalla, dan banason kama hannuna da yayi……

       “Kinsan kuwa yanda nake sonki da kishin ganin wani ya raɓeki?”. Shiru nai bance komaiba, shima bai jira amsata ba ya cigaba da faɗin, “Daga yau karna sake ganinki da Jawaad, idan kuma ba hakaba to lallai zan saɓa miki kuwa! Domin koba aurenki zanba yayankine ni, dolene na saka miki ido gudun karki lalace”.

     Yanda ya ƙare maganar sai yaban dariya, a raina nace, ‘Kaima ka samu dama ai lalatanin zakai’, amma a fili sai, nace, “Yayah nifa banice naje wajensaba, bayan na fito daga kiran da akai minne mukai karo dashi a hanya, shi kuma ya fito daga office ɗinsa, shine yace na biyosa, da farko ma bansan dani yake ba sai da ya sake aikowa sannan, amma dan ALLAH kayi haƙuri”.

     Murmushi yay min yana jinjina kai, yace, “Nasan dama ba laifinki bane, amma zan takama al’amarin birki tunkan yay nisa kinji, ina sonkine da yawa shiyyasa bazan juri ganinki da waniba ballema maƙiyina Bilkisu…”

     Ya ƙare maganar a hankali yana matsowa jikina sosai, gabana ne ya shiga faɗuwa, nai ƙoƙarin ja da baya amma sai hakan ya gagara saboda riƙon da yaymin bana wasa bane, sannan ƙarfina da nasa ba ɗaya bane, matsananciyar rawa jikina na fara sabida ƙoƙarin kawo fuskarsa kan tawa da yake, na shiga girgiza masa kai ina hawaye, roƙonsa nakeson yi, bakina sai motsawa yake amma na kasa furta komai, ya riƙe kaina da ƙyau yana ƙoƙarin ɗora bakinsa kan nawa na ƙwalla ƙara.

      Da sauri ya sakeni shima yaja baya saboda tsorata da ƙarata, jikina sai ɓari yake na tashi a guje na shige toilet ɗina na banko ƙofar harda murza key. ‘innalillahi wa inna ilaihirraji’un’ naketa ambata, wace irin masiface kuma wannan ni Bilkisu, kuka na shiga rusawa a bayin sosai, duk da inajin ƙwanƙwasa ƙofar da yaketa famanyi yana kiran sunana da bani haƙuri banko tankashiba, kusan mintuna talatin naji shiru alamar yabar wajen, ban buɗe ƙofarba har sannan sai bayan wani lokacin sannan na buɗe kaɗan na leƙa, babu kowa a ɗakin saima ƙofa dana gani buɗe alamar ya fita, komawa nai toilet ɗin na ɗauro alwala na fito, sai da na sakama ƙofar key kafin na tada sallar isha’i.

         Haka nai kwanciyata da yunwa ban fitaba duk da inajin motsin su mom da suka dawo kusan ƙarfe goma, ina idar da sallar asuba nai shirin barin gidan, dan gwarama na shiga gidansu Amina daga baya sai na wuce wajen aikin, bazanbi yah Qaseem ba. Sauri-sauri na kammala na fito, gabana ya faɗi ganinsa zaune a falo yana shan shayi alamar dai shima harya gama shirinsa, yanda ya tsatstsareni da idanu kuma ya sakani tsayawa cak nai ƙasa da kaina, “Kizo kisha shayi mu wuce, dan sauri nake yau”.

     Bance dashi komaiba na wuce zuwa kicin, kaɗan na haɗa tea a kofi na zauna a kicin ɗin ina sha, dan kuku ma bai kai ga fitowaba, saurin kallon ƙofar nai jin an shigo, nai masa kallo ɗaya na ɗauke kaina gefe, baice komaiba nima banceba, sai ajiye kofin da nai na nufi ƙofa, matsawa yay ya bani hanya, a ɗarare na raɓashi na fita yabi bayana.

      Badan raina yaso ba na shigar motar Yah Qaseem yau ɗinnan, shiru motar babu mai cewa komai ni da shi, ko redio bai kunnaba, tuƙi yake a hankali kamar bayaso, mun ɗanyi nisa da gida ina lafe a jikin kujera da karanto addu’ar neman tsarin ALLAH daga shaiɗanin dake ingiza zuciyar yah Qaseem ga abinda bai daceba gareni naji motar kamar ta tsaya, idanuna dake cike da barci na buɗe, naɗan waigo na kalleshi, ganin ni yake kallo sai na janye idanuna ina sake gyara zama, wlhy bazan ɓoye mukuba a tsorace nake, bani da ƙarfin dazan kare kaina ga murɗaɗɗan namiji irin yah Qaseem koda ace yay shirin cutar da nine, cikin dauriyar dole nace, “Yah Qaseem lafiya muka tsaya?”.

      Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, har lokacin inajin idanunsa na yawo a kaina, sai dai baice komaiba, kusan mintuna biyu suka sake shuɗewa, a bazata na tsinkayi muryarsa, yace, “Kiyi haƙuri Bilkisu akan abinda ya faru jiya, banyi hakan da niyyaba tunda kinsha faɗamin baƙyaso”.

      Ajiyar zuciya na sauke inajin daɗin kalamansa, na share hawayen da suka zubomin, ba tare dana kallesa ba nace, “Na haƙura Yah Qaseem, amma dan ALLAH ka rufamin asiri, kaji tausayin maraicina ka barni da mutuncina, gidanku itace mafakata ta ƙarshe da nake alfahari da ita, idan shaiɗan ya lulluɓe maka ido ka tuzguɗemin ita bansan ina zan dosaba, haramunne a addininmu, sannan cutarwace a garemu, wannan ba shi bane soyayya kamar yanda yake a tunanin yahudu da nasara, ƙoface kawai ta saɓon UBANGIJI, kuma tushen fasiƙanci, daga kama hannuna da kakeson yi a koda yaushe matsala zata fara, tun inaji banason hakan wataran sai kaga shaiɗan ya ƙawatamin nafara jin daɗi, a tafi matakin sumbata, makulin buɗema shaiɗan ƙofa kenan da komai na baɗala zai iya wanzuwa tsakanin namiji da mace, duk takatsantsan ɗinmu wataran kafin mu farga sai akai ga aikata zina, ‘Wa’iyazubillah’. Yah Qaseem namiji da mace duk hukunci ɗaya garesu wajen ALLAH idan suka aikata zina, amma a zahirance ta rayuwar duniya mace itace ke fara ƙasƙanta a idanun al’umma makusantanta dama na nesa da ita, domin itace ke ɗaukar ciki, itace wasu almomi ke fara bayyana a gareta, farko rasa mutunci, ƙasƙanta mutincin gidansu dama ahalinta, tabon da zaita bibiyar rayuwarta har ƙarshen zuri’arta, ita ake fara aibantawa kafin abokin tarayyarta, itace ke rasa mijin aure, ita akafi nunama ƙyama, itace keda rauni. Abin tausayi da tashin hankali ƴa mace na fuskantar waɗanan matsalolin koda ace fyaɗe akai mata. Yah Qaseem indai sona kace da gaske dan ALLAH ka daina min waɗanan abubuwan, wlhy banaso, basa burgeni……”

          Qaseem yaja wani bahagon numfashi saboda tausayi da bily ta bashi, harga ALLAH sonta yake da gaskiya ba yaudaraba, ALLAH ne ya jarabcesa da sonta batare daya shiryama hakanba, yanda take kuka sai ya kumajin tausayinta sosai a ransa, murya a sanyaye yace, “Na fahimceki Bilkisu, insha ALLAH kuma zan kiyaye, idan kin amince zanma Dad magana akan aurenmu”.

      Sauran hawayena na share tare da kallonsa, ganin ni yake kallo sai na ɗaga masa kai alamar na amince. Ya saki wani murmushi najin daɗi yana sake tsatstsareni da idanunsa farare tas, a hankali ya furta, “Inasonki da yawa Bilkisu na, gara dai nayi na mallakeki kusa dani na huta da wa’azinnan”. Murmushi nayi ina ɓoye fuskata, shima yay ƙaramar dariya yana mai tada motar muka cigaba da tafiya. Hira yaytamin har muka ƙarisa station ɗinmu duk da ba amsa nake bashiba sai dai eh ko a’a da murmushi kuma.1

BAYAN KWANA UKU.

       A kwanaki ukunnan Boss bai sake shiga harkataba, harna ɗauka gargaɗin Yah Qaseem ne yasa ya barni, tunda ina ganin dai yana sama dashi. Shima a ɓangaren Yah Qaseem na samu sauƙin yawan kai hannunsa jikina da yakeyi, sai dai wasu take-taken Yah Salman a gidan yanzu suke cazamin kai, ya masifar samin idanu, kowane motsina sai ya tanka magana a kai, Aunty Shahudah cema naga dai tayi sanyi, bansan mike damuntaba, amma saina lura kamar bata cikin nutsuwarta. 

      Ban sake cema baba maigadi komaiba game da zancen Amina saboda saka idon Yah Salman a kaina, amma inata wasu shirye-shirye a gefe nabin matakan da zan gano bakin zaren, dan abinda baba mai gadi yayi ranar yana nan tsaye cak a zuciyata bai gogeba. Da wannan tunaninma yau na fita wajen aiki.

     

          Tunda muka dawo sallar zuhur muna a office ɗinmu da boss ya dunƙulemu, kowa yana hidimar aikin daya dace, yayinda Ni da Ummie muna aikine muna ƴar hirarmu data shafemu, hakama sauran kowa nayi da abokin maganarsa, hakanne yasa ɗakin ɗaukar kananun surutai sama-sama. A bazata naji office ɗin ya ɗauki shiru tamkar ruwa ya cinye kowa, batare dana ɗagoba nai ƙaramar dariya ina faɗin, “Ummie mutuwace ta gitta a office ɗin namu ne?”.

      Shiru naji Ummie batace komaiba, hakanne ya sani ɗagowa a tunanina batajini ba.

            ‘kutumelecy’……………✍1

Assalamu alaikum.2

      Inason naɗanyi bayani da nake fatan a fahimceni, akan maganar aikinsu Jawaad, inason mai karatu ya fahimci wani abu anan, aikin da muka dangantasu dashi bawai yana nufin ainahin abinda ya shafi ma’aikatan zahirin bane, bamusan komai da ya shafesu ba, tayaya zamuce komai nasu sai ya shigo labarinmu, domin ba’akan hakan muke rubutu ba, da yawanmu ma idan za’a tambayemu bazamuce munsan waɗanan ma’aikatanba kai tsaye, domin su aikinsu bawai a bayyane yakeba kamar ƴan-sanda da dai sauransu da suke cikinmu ba, aikine na wanda kai kanka idan ba wani daliliba bazaka taɓa ka gansu suna yawo gama gari ba ko wani aikinsu a bayyane, so na danganta waɗanan jaruman littafine da hakan saboda mutunci da himma da ƙwazo na irin jami’anmu da mu kanmu bamu saniba, matasanmu kuma su zama masu himma dason bama ƙasarsu gudunmawa da zuciya ɗaya a kowace ƙasa suke ba lallai sai tamu ba, tom inaso ku kalli wannan kawai a matsayin labari bawai lallai abinda yake a zahiri ba, ko yake lallai mu bibiya, matsayinsu, misukeyi? Mizasuyi? Duk iyakarsa labari irin na marubuci {ƙirƙira}, bani da hurumin shiga abinda bani da lasisi a kai, domin bamma sani ba, waɗanan jami’an littafine bawai na zahiri dake aiki a ƙasarmu ba, idan kun kula sam babu wani sunan gari dake nunama a ina suke, ko a wane waje suke, musa a ranmu kawai ƙirƙirarren labari muke karantawa, ilimantarwa, nishaɗi, da faɗakarwa, ba akan kowaba, domin ba’akan kowan mukeyi ba, duk abinda zamu iya ganin yaci karo da waccan rayuwar ta zahiri to kawai fiƙira ce irin ta marubuci bawai dan inada ilimin sani ba ko bibiya balle bincika, ina fatan duk wanda ke bibiyar wannan littafi a ko’ina yake zai kasance maiyin ƙyaƙyƙyawan fahimta akan inda muka dosa, sannan abinda kake ganin na karkace ko shiga hurumin da banawaba ina fatan zakuyi gaggawar dawo dani hanya, ALLAH yasa mu dace, ALLAH kuma ya ƙarama dukkan jami’an tsaronmu lafiya da ƙwazo da nagarta a duk duniyar da suke.🙏🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻17

Page 10

    …………‘Kutumelecy’ na faɗa a cikin raina ina saurin janye idanuna dana ware a kansa da tsaida taunar cingam ɗin da nakeyi lokaci ɗaya, ganin yanda ya tsatstsareni da muggan idanunsa.  Zungurin ƙafata dana ɗora saman tebir ɗina Ummie tayi.

     Kallonsa na sake sata sai naga shima idanunsa yanzu akan ƙafar tawa suke harma da sauran ƴan uwana, da sauri na sauke ƙafar ƙasa na nutsu kamar yanda kowa yayi. Bai tankama kowaba ya ida takowa tsakiyyar ɗakin yana binmu da kallo daki-daki, har tsawon mintuna biyu muna a haka tamkar ɗan doka da ƴan gidan kallon ƙwallo ko ɓarayin agwagi, nidai sai faman jan addu’a nake saboda jin yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri tamkar ko yaushe idan na samu kusanci da shi.

     Ganin bazai tankaba sai muka shiga gaisheshi ɗaya bayan ɗaya, hannu kawai yake ɗaga mana amma bai sake kallon kowaba baikuma amsa mana da bakiba. Yaja kujerar dake gaban tebir ɗin Uchie ya zauna, bamusan mi suke tattaunawaba har kusan tsawon mintuna sha biyar kafin ya miƙe ya fice. Yana fita muka shiga sauke a jiyar zuciya, yayinda wasu suka shiga gulmarsa musamman ma matan cikinmu, nidai sabon cingam na ɓare na jefa a baki na cigaba da sabgar gabana.3

____________________________________

               A gidan su Jawaad kam taron meeting Mom ta tara da ƴan uwanta, sunɗau tsahon lokaci suna tattaunawa akan Jawaad da maganarsa da Shahudah, duk da dai da farko Uncle Nasir yaso bijirewa, a cewarsa suma sunada ƴaƴan da zasu bama Jawaad ɗin ai ya aura. Shahudah ta kiya musu hankalin da bai kamata su sake sakata a sabgarsu ba.

       Kuka mama Atika ta fasa musu, tare da ɗakko musu maganar data saka suka nutsu waje guda.

        “Munsan Sabira tayi laifi da tafka kuskure a baya, amma kuyi haƙuri munada tabbacin zuwa yanzu ta magantu za’a samu gyara musamman idan mukai dubi da yanda take son yaron, amma ni na yarda da shawarar Nasiru, mu fara ma Jawaad maganar auren wata a cikin yaran gidannan, idan ya nuna rashin amincewa saimu tirsasashi ya maida Sabira ɗakinta, dan baikamata mu zubamasa ido yana yawo sakaka babu aureba, shekararsu kusan biyar kenan da rabuwa, amma yaƙi aure, inba neman matan banza yaron nan yakeba yaza’ai mutum mai lafiya kamarsa ace yanaƙin aure?, su waɗancan dangin uwar tasa sakarkaru da yake tsoronsa sukeji sun gaza masa magana kuma, tomu bai kamata mu saka masa idoba, dan kuwa mune duniya zata zaga basuba, amma yaya kuka gani? Danni dai shawarace na kawo matsayina na uwa a gareku, da Badiyya nada isashiyar lafiyama tare zamuyi muku, yanzu saiku zauna ku yanke shawara a tsakaninku” ta ƙare maganar da tashi ta fice daga falon.

     Duk binta sukai da kallo harta fita, Uncle Sulaimam ya sauke numfashi yana faɗin, “Nidai ƴan uwana na yarda da maganar mama, dan nidai zaman Jawaad bayamin daɗi a haka, da Abdul-aziz nada rai bazai zubama gudan jininsa ido kamar yanda mu muka kasa riƙe amana mukaiba, duk da bana zargin Jawaad da neman mata, dan mu shaidane akan tarbiyya da sanin yakamata na yaron nan”. Duk shiru sukai basu ce komaiba, wasu na hararsa ta gefen ido wasu na ƙunƙuni a cikin rai, dan suma sunsan ƴaƴan Mama Badiyya sam nasa tare da burinsu a gidan, su kaɗaine masu ƙaunar Jawaad dan ALLAH badan dukiyarsaba. Jin shirun yayi yawane ya saka Mom yin magana. “Nima na aminta da maganar mama, kuma ina goyon bayan ɗan uwana Sulaiman”.

         Daga maganar Mom sai kowama ya fara faɗar abinda ke ransa, daga ƙarshe dai suka ajiye shawara akan zama da Jawaad ɗin idan ya dawo aiki da wuri yau, kokuwa weekend idan ALLAH ya kaimu.4

_____________________________________

             A makare yau Jawaad ya tashi a wajen aiki, saboda fitar da sukai shi da Hafiz zuwa wani waje da yamma, basu dawoba sai bayan magriba, akwai abinda zai ɗauka a office shiyyasa suka dawo, amma da daga inda sukaje gida zai wuce. Bayan ya tattaro abinda zai ɗakko a office ɗin nasa sai yaga lokacin sallar isha’i ma yayi, dan haka suka tsaya sukai a station ɗin.

           Koda suka fito yunwar dake cin cikinsa yasa yace su tsaya wajen wani haɗaɗɗen gashin kaji, gimba ya amsa masa da girmamawa.  gimba ne ya fita domin amsowa, kasancewar wajen ba baƙonsu bane akaima gimba tarba ta sanayya, kamar yanda Jawaad ya bashi umarni takeaway biyu akayi sai fura da yogurt masu sanyi aka saka ɗaɗɗaya a ciki, gimba ya bada kuɗin sannan ya dawo mota suka ƙarasa gida.

         Ganin da sauran mutane da keta shigi da fici a sassan gidan sai ya bashi mamaki, a ganinsa dai tunda anyi addu’an bakwai mikuma mutane keyi tunda ba taron biki bane. Saurin kauda abin yay a zuciyarsa dan a ganinsa hakan ba huruminsa bane, yaso shiga sashen Uncle Usman ya gaida Mama Zainab matarsa kamar yanda yakeyi kullum tunda akai rasuwar, sai dai a matuƙar gajiye yake, ga masifaffiyar yunwa dake cin hanjinsa.

         Tare suka shiga sashensa da gimba dake ɗauke da tarkacensa, bayan ya ajiye masa a falon ƙasa yay masa sallama ya fita, shima bai iya ƙarasawa bedroom ba ya yada zango a falo, sai da ya huta na wasu mintuna sannan ya miƙe ya haura sama, duk da yana buƙatar fara cin abinci haka ya daure, dan shi mutumne mai yawan cin abinci, idan bai samu bane dai yakanyi haƙuri kawai. Ɗakin barcinsa ya ƙarasa ya watsa ruwa, kusan ƙarfe tara ya fito tsaf dashi sai baza ƙamshi yake. Ya shiga kicin ya ɗakko kofi da filet, a falon ƙasa ya zauna ya kunna tv domin kallon labarai, yana kallonne yana cin abinci, lokaci-lokaci kuma yakan amsa waya idan an kirashi, ya daɗe zaune a falon har aka kammala labaran kafin ya miƙe yay ciki dan yana matuƙar buƙatar hutawa.

STORY CONTINUES BELOW

SHAHUDAH

      Saboda son haɗuwa da Jawaad yasa yau taƙi binsu Mom gida, a cewarta nan zata kwana, Mom bata hanata ba, suka tafi ita da Aamilah kawai saboda Salman ne yazo ɗaukarsu dama ba driver ba.

     Wajen ƙarfe goma ta kammala kwalliyarta, tai shiga cikin kayan barci masu taushi da ƙyau, dan sunyi masifar fidda mata surarta, sai ƙamshi take kamar jikar gidan mai turare, a ranta ta ƙudiri aniyar maido hankalin mijinta kanta yau, dan ta gaji da wannan wasan ɓuyan da sukeyi, ta kuma shirya karɓar cikin da yake buƙata. (Karku manta Shahudah batasan Jawaad ya saketa ba fa😥🤦🏻, ɓoye mata shine kuskuren dasu mom suka tafka).

     Hijjab ɗin mama Atika da ya kai mata har ƙasa ta ɗauka ta saka, babu kowa a sashen na mama Atika, itama tayi barci ma tun ɗazun, kai tsaye Shahudah ta nufi sashen Jawaad tanata zuba murmushi, dan ita kaɗai tasan abubuwan data shirya masa, yau ɗinan basai gobeba sai ta zautar da gayen nan, ta sake sakin tattausan murmushi lokacin data murɗa ƙofar taji ta buɗe. Jawaad ya manta shaf bai rufeba ya haye sama, sai da ta gama ƙarema falon kallo, komai tsaf tamkar ba namiji ke zauneba, tasan Jawaad yanada tsafta, sam bayason ƙazanta, duk jin kan nan nasa baya ƙyashin tashi yay shara yay morping wa sashen,, ya samu wannan horonne a zamansa da kakarsa Mama maryam, hatta da girki Jawaad ya iya, kawai rashin isashen lokacin kai ne ke hanashi yi. batasan miyasa bayason masu hidimaba. Ta sake sakin murmushi kafin ta fara taka steps ɗin a hankali tana wani yauƙi saikace tarwaɗa, a falo ta cire hijjab ɗin ta jefa saman kujera, ta kuma gyara rigarta da gashinta sannan ta nufi hanyar ɗakinsa.

       Jawaad kam a gajiye yake matuƙa. hakan yasa yana shigowa bayan yay brush da alwala yay adduar barci ya kwanta, bai wani jima da kwanciyaba barci yay gaba dashi, fitilar gefen gado ce kawai a kunne, itama ta ɓangare ɗaya, hakan yasa ɗakin yay dim babu haske sosai, bai kumayi dunɗum ba. Shahudah data murɗa ƙofar ta shigo a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana mai shaƙar ƙamshin da ɗakin keyi, komai na Bb’n ta daban yake dana kowa, bata ganin fuskarsa, dan ya juya ma ƙofar bayane, sannan ya lulluɓa da bargo saboda uban AC’n daya ƙure ɗakin da shi, ‘ko tsoron murama bayayi’ ta faɗa tana ɗaukar remote ɗin acn ta rage ƙarfinsa.

       Jawaad da baisanma hidimar da akeba barcinsa yake hankali kwance da mafarki mai daɗi, hakan yasa yaketa faman sauke numfashi a hankali. Ya sauke ajiyar zuciya lokacin da Shahudah ta hawo gadon a hankali ta kwanto bayansa bayan ta ɗaga bargon ta shiga, itama ajiyar zuciyar ta sauke ƙwallan kewarsa na taruwar mata a idanu, jitake tamkar ta haɗiyesa ta hutama kawai. Cikin salon data shirya masa a wannan dare ta fara yawo da hannunta a jikinsa, Jawaad dai bai motsaba, amma da alama jikinsa na karɓar saƙwannin Shahudah kamar yanda tai fata. Mafarkin da Jay keyi da saɓanin Shahudah yay dai-dai da abinda take masa a zahiri, hakanne yasa ta samu haɗin kan gangar jikinsa har takai ya gyara kwanciyarsa yana sake rungumeta, hakan yayma Huda daɗi kuwa, ta ƙara ƙaimi kan abinda takeyi, kamar wasa saiga tafiya tayi nisa a tsakaninsu, dan tuni ya fara maida mata murtanin sumbatarsa da takeyi.

          Yanda take sauke numfashi ne da sauri-sauri akan fuskarsa ya sakashi farkawa, dan kuwa tabbas wannan al’amarin ya wuce a mafarki kawai, a matuƙar razane ya hankaɗeta daga jikinsa yana ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihirraji’un. Wace ƴar iska ce haka ta shigomin ɗaki?”. Yay maganar yana ƙoƙarin kunna fitilar ɗakin.

       Shahudah daya jefar gefe duk da taji zafi tai ƙoƙarin tashi zaune tana sauke numfashi a gwame, hasken daya gauraye ɗakin ne ya basu damar ganin juna. Kansa ya dafe yana ƙara ambaton “Innalillahi….” Shahudah ta matso jikinsa tana neman kwantawa a kafaɗarsa ya sake tureta a fusace, “Wai ke wane irin dabbanci ne wannan? shin baki da hankaline Hudah?”. Tabbas maganganunsa sun mata zafi, amma saita daure cikin dakewa da tsiwarta tace, “Dan nazo wajen mijina zakacemin banda hankali?, to ka ɗauka ni da kai duk mun zama mahaukatan”.

      Karon farko Jawaad ya waro idanu waje, yace, “Miji!?, Hudah rashin ilimin addinin naki harya ƙara faɗaɗa haka? Kinga bani da lokacin wannan haukar tashi ki fitarmin daga sashe kafin na saɓa miki kamanni, kuma wlhy wannan yazama na farko na ƙarshe da zaki sake shigomin nan”.

       Kuka Shahudah ta saki, ta nuna kanta tana faɗin, “Yanzu nan tsanar da kaimin bb har ta kai haka? To wlhy babu inda zanje, dan inada haƙƙi a kanka ai, duk ma abinda zakayi sai kaitayi, amma ka sani niba ƴar iska bace, amma wlhy da tuni naje na nema wani namijin a waj…….”

      Mari ya kai mata tai saurin kaucewa, cikin daka tsawa yace, “Tashi ki fita a ɗakinan kafin na raba kanki da wuyanki wawuya kawai!!”. Saurin sauka tay a gadon, dan yanda ya harzuƙo ɗinan zai iya maketa, batasan ma bashi da wannan ƙarfinba a yanzu, dan ta sakashi a kwale-kwale. Da ƙyar Jawaad ya iya sakkowa a gadon saboda tashin hankalin da Shahudah ta sakashi, duk ƙoƙarin kame kansa da dauriyar da yakeyi yau ta kwanto masa liƙi, ya murzama ƙofar key ya dawo saman gadon jiki babu ƙwari. Gaba ɗaya kansa ya toshe, yama gaza yin tunani akan Shahudah.

       Duk yanda Jawaad yaso yayi barci a wannan daren ya kasa, gashi maganin da yake sha ya barsa a office saboda ya ƙare ya sayosu jiya, sai kuma ya manta bai ɗakkoba, ya watsama jikinsa ruwan sanyi yafi sau shidda kafin asuba, sosai mararsa ke masa masifar ciwo, ko sallar asuba bai fitaba a ɗaki yayi, sai bayan ya idarne barci ɓarawo ya sacesa, shima a matuƙar wahale yayisa.

       

         Shahudah kuwa da kuka rurus tabar sashen zuwa sashen mama Atika, a falo ta zube tacigaba da kukanta har barci ɓarawo ya saceta.

  6

___________________________________

                       Yau ma har muka fito Office banga kowa a cikin ƴan gidanba, cikin nishaɗi muke ƴar firarmu da Yah Qaseem har muka iso, saida na rakashi har office da tarkacensa sannan na fito nima zuwa namu.

       Ummie bata isoba, hakan yasa na zauna bayan mun gaisa da waɗanda na tarar, ƴan abubuwan da baza’a rasaba na shiga yi, gefe ɗaya kuma ina amsa hirarsu Dawood sama-sama akan aiki, a hankali mukaita ƙaruwa har kowa ya gama isowa, Ummie ta zauna saman tebirina tana faɗin, “Bily gulma da ɗumi-ɗuminta fa”.

         Kallonta nai ina faɗin, “Ƴar sa ido mikika samo mana?”. Ƙaramar dariya tayi da sauke murya ƙasa tace, “Ankawo kuɗin Nazifa”. “Dan ALLAH da gaske?” nai maganar cikin waro ido waje bakina washe da fara’a. Ummie tace, “Wlhy da gaske nake, kema tace ta kiraki bai shigaba, amma ta tura miki saƙo ai”. Wayata na ɗauka ina faɗin, “Kashewa nai da zan kwanta, tunda na tashi kuma ban buɗe data ba, oh ni su Nazifa an mana wayo, da Al-mustaphan dai?”. “Shi kuwa” cewar Ummie tana dariya.

       Fita mukai zuwa can baya nai kiran Nazifa a waya, bugu biyu ta ɗauka tana faɗin, “Inba gulmaba Bily miye na kirana da farar safiyarnan?”. Dariya mukai ni da Ummie, nace, “Ai gara dai muci gulmar da ɗuminta basai ta huceba, yarinyarnan da gaske dai kin dage aure kikeso?”. “Ban isa bane?” Nazifa ta faɗa tana dariya. “Kin isa kuwa tsaf” Ummie ta bata amsa. Haka muka cigaba da hira cikin so da ƙaunar juna har bamusan lokaci yaja ba.

           Daƙyar muka iya katse hirar muka koma office gudun kar’a nememu.

JAWAAD

     Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai daga kwanciyar da Jawaad yay bayan sallar asuba sai zazzaɓi mai azabar zafi ya rufesa, duk yanda yaso ƙoƙarin tashi yay shirin office lamarin ya gagara. Wani wahalallen barcin nema ya sake awan gaba dashi bayan ya koma saman gado yaja bargo.

       Gimba yay shiri da wuri kamar yanda yasan suna sammakon fita, sai dai yafi tsayuwar awa guda wajensu baba maigadi babu alamar boss ɗin nashi, dama kuma bai gansa a massallaci ba yau da asuba. Bai dai tambayi kowaba ya cigaba da jira har zuwa ƙarfe tara, zuwa lokacin dai kam abin ya fara bashi mamaki, abinda zai riƙe boss har ƙarfe tara bai fita office ba to lallai dole ya saka kokwanto a zuciyar duk wanda yake tare da shi, wayarsa yay kira har sau uku ba’a amsaba, ya sake daurewa dai ya zauna awa ɗaya ta kuma shuɗewa goma tayi. Yanzu kam tilas ya miƙe ya nufi sashen, yay knocking har kusan sau goma baiji motsin kowaba, hakan yasashi murɗa ƙofar, cikin sa’a kuwa ta buɗe, sai dai koda ya shiga babu kowa a falon, babuma alamar wani ya fito cikinsa. Nan kawai yake da hurumin shiga dan haka bai ƙara gaba ba ya juya ya fita. Yabar wayarsa a mota har baisan su Oga Aliyu nata kiransaba suma jin Boss baizo office ba, sun kuma kira wayoyinsa duka babu wacce ya ɗaga, shine suke kiran Gimban suji ko wani waje sukaje? Amma shima kuma bai amsa musu ba.

           Misalin sha ɗaya da wasu mintuna sai ga Nabeelah da Ummansu sunzo gidan domin sake yima mama Zainab gaisuwa, dan rabonsu da gidan tun ranar rasuwar. Bayan sun shiga sashen mama zainab sun fito sai suka shiga wajen mama Badiyya don su gaisheta da jiki, basu jimaba suka fito zuwa sashen mama Atika, ananne suka iske Shahudah babu lafiya, tana kwance cikin doguwar kujera lulluɓe da bargo, sun mata addu’ar samun lafiya suka miƙe zasu tafi amma sai mama Atika ta tsaidasu da zancen auren Jawaad, murmushi Ummah tayi kawai, tabama mama Atika haƙuri akan zasu masa magana, baki kawai mama Atika ta taɓe, su Umma kuma suka fito abinsu Nabeelah nata ƙunƙuni akan ansama yayansu ido. Basuyi zaton samun Jawaad a gidaba, dan haka sukai yunƙurin barin gidan, Gimba daketa dakon jiran fitowarsu yay azamar isowa garesu yana gaida Umma, da mamaki ta amsa masa, “A’a gimba baku fita office bane ko dawowa kayi kai?”.

       “Wlhy mama bamu fitaba, har yanzu boss bai fitoba, bansan ko lafiya ba? Nai knocking na kirashi amma duk babu wani amsa”.

     Shiru Ummah tayi na wasu sakanni, sai kuma ta fasa shiga motar ta nufi sashen Jay, Nabeelah ma data tuƙosu harta shiga mota ta kunna ta kashe ta fito tabi bayan Ummah.1

____________________________________

             kasancewar  juma’a ce yau ɗin bayan an sakko salla mun fito zamu fita neman abinci saboda yunwar da nakeji mukaci karo da Oga Jabeer zai shiga mota, har mun gaishesa munwuce sai kuma yay kirana. Dawowa nai ina amsa masa da girmamawa, yace, “Shigo mota ki rakani wani waje”.

     Duk da banso ba sai ban masa musuba na shiga Ummie kuma ta wuce tana min dariyar mugunta…………✍

“Saura muji wani yace Hudah🙄 ehe😏.

10

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

    9Page 11

         ……………Tafiyar da batafi mintina talatin ba muka iso inda ya bani mamaki, bandai cema oga Jabeer komaiba har aka buɗe mana gate muka shiga. A dai-dai sashen da mukai salla ranar rasuwar Uncle Usman yay fakin, ya kashe motar yana faɗin, “Muje ko”.

          Bance komaiba na buɗe murfin na fita kamar yanda shima yayi, yana gaba ina biye da shi har zuwa ƙofar falon, sai kalle-kalle nake ina ƙara jinjina girman wannan gida, koba’a faɗaba kasan an narkar da dukiya wajen ginashi, Oga jabeer ne yay knocking, babu jimawa akazo aka buɗe ƙofar.

         Cikin murmushi Nabeelah data buɗe ƙofar tace, “Yah Jabeer sannu da zuwa”. “Yauwa Nabeelah” ya amsa yana mata murmushi shima. Sai da ya shige sannan ta ganni, cike da mamaki ta waro idanu alamar ganina a bazata da tai,  kafin ta daka tsalle ta ɗaneni tana dariya, “Lah ƙawata dama rai kanga rai?”. Murmushi nayi ina mai jinjina wautar Nabeelah a raina, cikin surutunta tace, “Dama kinsan Yah Jabeer?”. Amsa na bata da cewar, “Eh, wajen aikinmu ɗaya”. Zata sake jehomin wata tambayar Jabeer ya katseta, “To Akku mai bakin magana kaimu ɗakin da yake”.

          Yanda tayi da fuskane ya sakani yin murmushi, ita a dole taji haushin ance mata Akku, hannuna ta kama tana tuttura baki gaba tai mana jagora har sama, bansan minene ya kawomuba balle tunanin wajen wa mukazo, ni dai kawai inabin Umarnine. ‘Tabɗi’ na faɗa a raina saboda ganin yanda falon saman ya haɗu matuƙa shima, sai sassanyan ƙamshi ke tashi, muryar kamilar mace ta amsa mana sallamar da mukai tare da faɗin, “Jabiru sannunku, ku shigo mana”.

       Oga Jabeer ya amsa da “Yauwa Umma, ashe kema kina nan?”. Tace, “Eh muma bamu jima da zuwaba, nazo na sakema Hajiya Zainab gaisuwane sai Gimba ke cemin basu fita Office ba, yanata jiran Jawaad ya fito bai fitoba, shinefa na shigo na iskesa kwance rijif cikin zazzaɓi”.

        “Ya salam, wlhy muma a office tun ɗazu muke zuba idon ganinsa amma shiru, mun kirasa bai ɗaukaba hakama Gimba, tomu tunaninmu koma wani wajen sukaje tunda munga jiya lafiya lau yabar office, sai daga baya ne gimba ya kira yasanar mana ai baida lafiya, ko sallar juma’a ma da ƙyar in zai iya fita, shinefa nace bara mu sakko massalaci nazo naga jikin nasa, tunda su Hafiz sun fita wani aiki”.

          Sosai gabana ya faɗi da jin sunan Boss a zancensu, harda ƙarin furucin rashin lafiya, banji amsar data bama Jabeer ba saboda tunanin dana tafi…….3

        Hannuna da aka riƙone ya katse mani tunani, na kalli Ummah data riƙonin nai ƙasa da kai ina faɗin, “Ina yini”. Ummah tace, “Lah kece Auntyna? Aini bamma ganekiba da farko wlhy nama zata Maman Areef ce (Matar Jabeer). “A’a Umma nice” na bata amsa kaina a ƙasa, kafin ta samu damar yimin tambaya Jabeer ya bata amsa da cewar, “A’a Umma ba Fannah bace, Mom ɗinmu ce, da alama ma kin santa kenan?”. Ummah tai murmushi tana zaunar dani a kujerar kusa da ita, tace, “Nasanta Jabiru, ƙawar Nabeelah ce ai, ina ka samo mana ita ne haka? Ko dai ta biyu ce?”. Yanzun kam ƙaramar dariya Jabeer yay yana girgiza kansa, “Wai Ummah ta biyu kuma? A wannan marrar ɗayarma ya aka ƙare, sai dai idan zaki nemarwa ɗanki ne, shine gwauro, wajen aikinmu ɗaya da Mom ɗinmu” ya ƙare maganar idonsa a kaina.

         Dariya tayi tana sake riƙo hannuna, cikin sigar tambaya tace, “ɗiyata kina son ɗana?”. Kasa cemata komai nai sai ƙasa dana ƙarayi da kaina, a raina ina faɗin, ‘Ni inada Yah Qaseem ɗina’. Jin bance komaiba ta maida kallonta ga Jabeer,

           Cike da mamaki tace, “Waima tsaya Jabiru, kana nufin itama irin aikin naku takeyi?”. “Sosaima kuwa Ummah” ya bata amsa cike da karsashi. Haɓa ta riƙe tana sake damƙe hannuna, “Oh ni ɗiyata, kekuma abinda ya burgeki kenan? To Nabeelah kinji fa jaruman mata, ba irinki matsoraciya ba” Nabeelah da mamaki ya kashe tace, “Wai dan ALLAH da gaske?”. Hararta Jabeer yay yace, “Da gaske mana”. Nabeelah tace, “Tab, wlhy bari Yah Jay ya warke nima ƴar sanda zan zama”. dariya Umma da Jabeer sukai mata, nidai na murmusa ina kallonta da faɗin, “Dakin burge kuwa, kinga ƙawata ta dawo kusa dani”. Da sauri ta cafe da faɗin, “Karki damu ƙawa ina nan tafe, kam Nabeelah ƴar sanda, ashe zan ragargaji ƙattai”.

       Jabeer yace, “ko kuma ke su ragargajeki ba”. Ɓata fuska tai da tura baki, “A’a wlhy Yah Jabeer kar kai min baki tun yanzu”.

STORY CONTINUES BELOW

       Kafin ya bata amsa Ummah tace, “Kaga Jabiru kubar wannan ba gajiya zataiba, ku shiga yana ciki, amma ban saniba ko idonsa biyu dan Doctor ya saka masa ruwa tun ɗazun”.

       Miƙewa mukai muna faɗin ALLAH ya bashi lafiya.

     Oga Jabeer na gaba ina biye da shi har cikin ɗakin nasa da ya gama haɗuwa, babu wani datti balle tarkace, nayi zaton zamu sami matarsa a cikin ɗakin, amma sai naga shi kaɗaine kwance a kan gado lulluɓe da farin bargo, hannunsa ɗaya liƙe da ruwan da ake saka masa, ya ɗora ɗayan saman cikinsa, fuskarsa tayi wani irin fayau alamar yaɗan rame. Yauce rana ta farko dana iya masa kallon kai tsaye kuma na tsawon mintuna, ƙyaƙyƙyawane, komai nasa dai-dai da fuskarsa………

 

   “Momcy zauna mana” Oga Jabeer ya faɗa cikin katsemin tunani, kaina na jinjina na zauna saman stool ɗin daya ajiyemin kusa da gadon kaɗan, shi kuma ya zauna a bakin gadon kusa da shi, hannu yakai saman kansa yanason jin yanayin jikin nasa, ni dai ɗauke kaina nai na maida wajen kallon ƙaramin hoton dake drawer gefen gadon, da gani tsohon hotone, ƙyawawan mata da miji da suke a ganiyar shekarun ƙuruciya, sunyi ƙyau sosai da dacewa da juna, ga hoton ya ɗauku duk da bana wannan zamanin bane.            

          Jawaad ya buɗe ido a hankali saboda hannu da Jabeer ya ɗaura masa a goshi, akan Bilkisu dake saitinsa ya saukesu, ya ɗan lumshe ya sake buɗewa akan nata, sunɗan kumburo sannan sun sake girma, daga ciki sunyi jaa kaɗa alamar dai bayajin daɗi. Jabeer ya kalla kafin ya sake maida idonsa kan Bilkisu, ya kuma janyewa yabi inda yaga idonta na kallo shima, hankalinta nakan kallon hoton Mamansa da Abbansa daya ajiye a bed side drawer, shima Jabeer kallon wajen yayi, amma a mamakinsa sai yaga Jawaad yakai hannu ya juya hoton. Murmushi Jabeer yay yana girgiza kansa.

         Hankalina na dawo ganin an juya hoton, nai saurin bin hannun daya juyaɗin da kallo har zuwa fuskar mamallakin hannun, idanunsa a kaina suke, dan haka na janye nawa ina ɗan yamutsa fuska, a raina nace, ‘Baida lafiya ma bazai bar shegen kallon mutane ba’.

           Jabeer dake binsu da kallo shidai yay ƴar dariya kawai, kafin yace, “A kacema ka warke mu tashi muje kawai?”. Harara Jawaad ya zuba masa, sai kuma ya miƙa masa hannunsa da aka saka ruwan, yay masa alama da ido akan ya cire masa. Kallon ledar ruwan Jabeer yay, yace, “Ya za’a cire bai ƙareba?, saura kaɗan ai, kaɗan sake haƙuri”. Jawaad da sai yanzune zaiyi magana ya yamutse fuska da motsa laɓɓansa a hankali saboda rashin jin ƙarfin jiki, “To sannu likita, kaga ni ciremin, dama Ummah ce ta takura aka sakan”.

       Kafin Oga Jabeer yace wani abu na katsesu da cewar, “Ina yini, ya jiki”. Ban yarda na kallesa ba. hakan yasan bansan a yanda ya amsa minba.

         Kallonta Jawaad yay ya janye idanunsa, akan laɓaɓansa yace, “Alhmdllh”.

       Sallamar Ummah yasa duk muka kalli ƙofa, tace, “A ya ake cire ruwan bai ƙareba?”. Jabeer yace, “Wlhy Ummah kema ƙya faɗa, cayay a cire wai”. Ummah tace, “Kaci gidanku Jawaad, saurin mikake to? Duk abinka dai bazaka fita aikiba yau, dan a gidannan ma zan yini, dan karna tafi ka saci jiki kace zaka tafi ma agogo sarkin aiki”. Fuska ya ɓata, yace, “Kai Ummah ni nagaji da kwanciyarnan, kumafa naji sauƙi” “Haka mukeso dama ai kasamu sauƙin, amma babu inda zakaje, barama na haɗa maka ruwa kai wanka kaji daɗin jikinka”.

       Yanda ya cuskule fuska ni saima yaban dariya, a raina nace ‘duk girman ɗa a gaban uwa shi yarone’ Har Ummah ta nufi haɗa masa ruwan sai naga kamar bai dace ba ina zaune na barta da aiki, miƙewa nai ina faɗin, “Ummah ki barshi bara na haɗa, inane bayin?”. Murmushi Umma tayi tana kallon Bilkisu da yaba hankalinta, tace, “To ɗiyata kuma Yayata nagode kinji, ga shinan shiga”. Kaina na jinjina mata na nufi inda ta nuna mani.

        Jabeer da yaji daɗin abinda Bilkisun tayi yay murmushi yana kallon Jay, “Jay wlhy yarinyar nan tanada hankali”. Banza Jawaad yay masa tamkar baijiba. Jabeer yace, “Nasanfa kaji minace”. “Malam ka cikani da surutu, zaka fita a ɗakinan fa” dariya Jabeer ya kwashe da ita, dan shikam dai ransa na bashi abubuwa da dama. Idanun Jawaad dake harar Jabeer tamkar zasu faɗo ya nuna masa hanyar fita. Jabeer yace, “ALLAH babu inda zani, dama kasamu mukazo dubaka, bara na kira su Hafiz nace karma suzo ka warke”.2

STORY CONTINUES BELOW

          Koda na shiga toilet ɗin saida na tsaya nagama ƙare masa kallo, ‘Humm’ kawai na iya faɗa, dukda babu wani datti sai naga dacewar fara wankewa kafin na haɗa ruwan, cikin mintuna ƙalilan na gama tsaftace bayin kafin na haɗa masa ruwa mai zafi sosai, a ganina idan yazo bai masa dai-daiba sai ya sake sirkawa, lokacin dana fito iskesa nai zaune a bakin gadon, kayan barcine jikinsa farare, wandon dogo har ƙasa, hakan yasa banji na takuraba, maganar aiki sukeyi yanzunkam, sai dai shi yana dafe da kansa alamar yana masa ciwo ko yay masa nauyi. nace, “An haɗa ruwan”. Jabeer ne kawai yacemin “Sannu da aiki” shiko baima kalleniba ya miƙe ya nufi bayin yana tafiya a hankali.

       Bayan shigewarsa Oga Jabeer ya miƙe yana faɗin, “Bara na sayo masa abu na dawo, kiɗan gyara masa ɗakin”. Kaina kawai na ɗaga masa dukda banso hakanba, sai mita nake a raina akan ‘to ina matarsa da ita bazatazo ta gyaraba, ni kofa haɗa ruwan wankanma dan naga Ummah ce zatayi, a matsayinta na babba kuma bai kamata na bartaba bayan ina zaune a wajen’ haka naita mita ina aiki, na gyara gadon tsaf tare da jera filolin a wani style mai ƙyau, nidai kawai nayine saboda inason gyaran gado dama can, balle irin wannan da yaji kayan shinfiɗa na alfarma, ga filos da yawa. Ina cikin gyaran gadon ne Nabeelah ta shigo da kayan shara. Tace, “Lah ƙawata daga zuwa dubiya sai a sakaki aiki? Ummah tace kije ki huta bara na gyara”. Murmushi na mata nace, “A’a ki barsa kawai, ɗakinma ai babu datti”. ƙasa tai da murya tana kallon toilet tace, “Yayanmu ba’ai masa abin arziƙi ai, kaɗan daga aikinsa ya fito ya sakaki wani aikin kuma”. Tabani dariya yanda takeyi tana kallon bayin, nace, “Dama ya fito ya jiki”. Kafin na rufe baki ta fice a ɗakin da gudu tana faɗin, “Saikin fito, dama girki nake masa”. Kaina na girgiza kawai naci gaba da aikin ina jinjina wautarta, gata dai zamuyi sa’anni, amma nakula Nabeelah autace kodan shiriritarta.

          Har na gama gyara komai tsaf bai fitoba, na kammala morping tsaf kafin na ɗauka turaren ɗaki dana gani saman ƴar dirowar farkon shigowa ɗakin kala-kala, ɗauka nai nahau fesawa jikin labuloli da saman gado dama ɗakin gaba ɗaya, a bazata naji an buɗe ƙofar bayin, hakanne ya sakani kallon wajen babu shiri, ai kallo ɗaya nai masa na juya da sauri na nufi ƙofar fita ɗakin, gwangwanin freshener ɗin na ajiye na ɗauki bokitin danai morping nai waje abuna.

                 Jawaad dai yana tsaye a ƙofar bayin yana binta da kallo harta fice, shima baiyi zaton samun kowa a ɗakinba shiyyasa ya fito kansa tsaye, dukda ma dai sanye yake da rigar wanka a jikinsa ba towel ba, cikin rashin jin ƙarfin jiki ya tako zuwa cikin ɗakin, har yanzu mararsa a ƙulle take, dukda dai bakamar jiya da dare ba, da kuma safiyar yau, danma ƙin faɗama Doctor ɗin ainahin abinda ke damunsa yay, cayay kawai zazzaɓine ke damunsa, shi kaɗai yasan yanda yakejin haushin Shahudah da kuma matakin dazai ɗauka a kanta. Idanunsa suka sauka akan gadon da yanda akaima filolin, kasa ɗauke idanunsa yay har na tsahon mintuna kusan biyu, sosai gadon yay masa ƙyau, sai yaga tamkar ba gadonsa ba.2

         Tunda na fito Ummah keta faman jeramin sannu, ni dai murmushi kawai nake, na gyara falon saman ma duk da babu datti, falon ƙasa dai Nabeelah na iske ta gyara harma tana morping. Kiran da Umma taimin daga kicin na amsa, ta miƙamin ƙaramin tire data ɗaura kofin tea a kai yanata turiri, “Yauwa ɗiyata dan ALLAH miƙama yayanku wannan ya fara sha kafin wannan uwar shiriritar ta kammala girkin, daga nan sai kiji ko yana buƙatar wani abun kuma”. “To” kawai na iya ce mata na amsa na fito. Koda na fito sai na roƙi Nabeelah tazo ta rakani, catai ALLAH naje ni kaɗai, dan inhar mukaje mu biyu cazai anmasa gayya.

     Badan nasoba na nufi saman ni kaɗai, addu’a nake a raina Oga Jabeer yazo mu wuce. Sai da nai knocking ya bani izinin shiga sannan na shiga da sallama, kaina a ƙasa ban yarda na kalli ko inaba sai gabana, saida naje dab da shine sannan na kallesa sau ɗauya na ɗauke idona, har ya saka kaya, baƙin wando da yellow ɗin riga folo, yana zaune ne a bakin gado da waya a hannunsa, hannunsa ɗaya dafe da kansa yanzu ma, nidai na ajiye tiren a gabansa ina faɗin, “Gashi inji Ummah, tace kanason wani abune?”. Banji ya tankaba, bankuma damu da yace ɗinba dama na miƙe zan fita.

       “Zonan” ya faɗa a hankali. Dawowa nai ina jan numfashina da ƙyar, dan duk a takure nake, danma zuwa yanzu kamar naɗan fara sabawa da kasancewarmu tare zuciyata ta sassauta min wajen bugun da takeyi idan har muna tare. Nace, “Gani”. Shiru yaymin kamar ba shine yay kiranaba, sai da yaja wasu sakanni kafin ya nunamin dogon table ɗin dake a gaban gadon ta gaba, “Ɗauka waɗancan keys ɗin, kije Gimba ya kaiki station, zaki ɗakkomin abu a office”.

      Duk yanda naso daurewa sai da gabana ya faɗi, ta yaya zanje na buɗe office ɗinsa nikam? A matsayin wa? Na shiga uku, mutumin nan nason jefani a matsala shidai na lura……

      “Miemaa!” ya faɗa a ɗan tsawace ganin dukma bayanin da yake mata hankalinta baya tare da shi. Firgigit na kawo numfashi tare da kallonsa, yanda ya danƙaramin harara ya sakani saurin duƙar da kaina. “Ina miki magana kina wani banzan tunani”. “Sorry sir” na faɗa da sanyin murya, dan harga ALLAH banji miya faɗaba”. Ƙaramin tsaki yaja, ya miƙomin waya batare da ya ce min komaiba, amsa nai ina jiran ƙarin bayani, amma sai ya shareni yama ɗauki tea ɗinsa ya fara sha.

        “Tashimin a kai kafin na canja miki kalar fuskarki”. Fuska na kumbura na juya na fita ina ƙunƙuni a raina.

       Jawaad dake binta da harara yay ƙaramin tsaki da faɗin, “Miskilar banza kawai”.10

        Banason zuwa ni kaɗai, hakan yasani cema Nabeelah tazo muje ya aikemu, da yake batasan gaskiyar zancenba sai ta bini muka bar Ummah na haɗa masa abinci. A jikin mota muka iske gimba da alamar yasan da tafiyar, zai buɗe mana mota nace ya barsa kawai, murmushi yayi ya shiga mazaunin driver yana tambayarmu “ya jikin boss ɗin” da sauƙi, muka faɗa kusan a tare sannan muka gaidashi.

       Tunda muka tafi Nabeelah ke zuba mana surutu, Gimba nata biye mata, nidai murmushi ne nawa idan sunyi wani abun dariyar, har mamaki nake yanda Nabeelah bata gajiya da zance saikace wata akku. 

       Nidai har Gimba yay fakin addu’a nake ALLAH yasa karna haɗu da Yah Qaseem, gefe kuma ga maganar shiga Office ɗinsa bansan yanda za’a fassarani ba, sauƙinma na taho da Nabeelah ne, tunanin zuwa office ɗin Oga Aliyu ko Hafiz nayi, saisu kaimu office ɗin, a ganina hakan sai yafi, jan Nabeelah nai zuwa Office’s ɗin nasu sai dai munyi rashin sa’a duk a rufe alamar bamasa station ɗin kenan…………….✍

“Team Bil-Qas & Jay-Hud. Saura wani yace sunan baiyiba😏😜😂”

44

Fatan alkairi a gareku baki ɗaya😍😍😘👌🏼

10

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.24

     Page 12

………….Babu yanda na iya dole naja hannun Nabeelah muka nufi office ɗin, sai dai tunma a hawan farko aka dakatar da Nabeelah, ni kaɗai aka bari na wuce, kamar na fasa kuka haka naji, sai dai nayi mamaki a raina yanda babu wanda ya tambayeni mizanje yi?.

Office ɗin na nan tsaf, duk da yau ba’a gyaraba tunda baizoba babu wani datti, yau kam ban cuci kainaba saida nagama ƙare masa kallo gabas da yamma kudu da arewa, hatta da hotunan saman tebir ɗinsa sai da na gama kalleso, tsabar jan magana irin tawa na zauna saman kujerarsa ina gwada yanda yake zama, nakai kusan mintuna huɗu ina shirirtata kafin kira ya shigo wayar da ya bani, ƙurama wayar ido nayi tamkar mai tsoron ɗauka har sai da ta kusa katsewa sannan na ɗauka nasa a kunne batare da nayi maganaba. Daga canma shiru anƙi cewa komai harna tsahon sakanni.

“Baki iya sallama bane?” muryarsa ta daki kunnena a bazata, idanu na zaro waje dan wlhy banyi zaton shi bane, nace, “Sorry Sir” bai amsa minba sai cewa da yay, ki buɗe ƙaraman drawer na jikin table akwai faran leda da kwali a ciki ki ciroshi” na amsa da “to”. Ina ƙoƙarin jawo ledan kwalin ya fita a ciki, hakanne ya sani cirosu ɗai-ɗai shi da ledan, haka kawai na tsinci kaina dason karanta abinda aka rubuta a kwalin, dan da alama na magani ne, shaf na manta da wayar a kunne take bai kasheba, na hau karatun rubutun jikin maganin ina faman zaro idanu saboda fahimtar danai maganin na miye. Daga can Jawaad da yaji a jikinsa akwai abinda ta nutsu takeyi wanda ya ɗaura zarginsa akan maganin cikin sanyin murya yay magana saboda cikinsa dake murɗa masa a lokacin, “Bincike kike mini?” a bazata naji maganar tasa, shiyyasa na saki kwalin ƙasa batare dana shirya ba, cikin rawar baki, nace, “A…a’a sir” shiru Jawaad baice komaiba idanunsa a lumshe yana faman cizon lip ɗinsa na ƙasa, sai da ya lafa masa sannan ya sake maida hankali akan wayar, nikam duk a tsorace nake, gani nake tamkar ya gane mi nakeyi, cigaba yay da lissafo min duk abinda yake buƙata, na sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya jin yabar waccan maganar, na ɗauka kwalin maganin na maida a ledar ina cigaba da ɗaukar duk abinda yace, inda kuma ya faɗa anan nake ganinsa, bayan na haɗasu na zuba a wata leda baƙa na fito.+

A ƙasa na iske Nabeelah ta cika tai fam da haushi, taban dariya, hakan yasa na murmusa ina kamo hannunta, ƙwafa tai tace, “ALLAH yayanmun nan ko, saina rama abinda yay min”. Nace, “Miyay miki?” ta sake yin ƙwafa, “Bakiga yasa a hanani shiga office ɗinsa ba, ALLAH nima duk randa na fara aiki bazan bari yazomin office ba”. Yanzunkam kasa jurewa nai saida na dara, “Oh Nabeelah yaushe ya hanaki shiga Office ɗinsa, jami’anmu dai sun hanaki”.

“Kutt wlhy bakisan halinsaba ne, nasan shine yace karsu barni”. Nace, “To kiyi haƙuri, Yaya yayi laifi”. Tunanin zamu dawo yanzu da oga Jabeer yasa ban shiga ko inaba, Mun isa wajen Gimba ya ɗaukemu muka koma, yanzu kam a falon ƙasa muka iskesu harda su Aliyu, mamaki ƙarara na gani a idanun Rose saboda ganina, a tare na gaishesu gaba ɗayansu na ƙarasa gaban sarakin dake kwance a doguwar kujera, cikin girmamawa na ajiye ledan da keys ɗin da wayar a table ɗin dake gabansa nace, “Gashi”. Idanunsa dake rufe ya buɗe ya zubasu a kaina, “Dama tare da Nabeelah na aikeki?” yay maganar yana hararata. Ƙasa nai da idanuna ina girgiza masa kaina alamar a’a. Ƙwafa yay ya ɗauke kansa, ganin hakan yasani barin wajen da nufin bar musu falon ma.

“Waye zai ɗauke miki kayan nan”. juyowa nayi, kafin na ƙaraso wajensa Rose dake zaune a kujerar dake inda ƙafafunsa suke ta miƙe ta ɗauki ledan da cewar, “Ƙyale shashasha boss ina za’a kai?”. Banza yay bai tanka ba, niko na sake juyawa zan fita. “K! Ina wasa dake ko?”. Nazata da Rose ɗin yake hakan yasa nai yunƙuri cigaba da tafiyata Aliyu ya kirani.

“Momi zoki amsa ki kai masa sama kinji”. “To” nace, na dawo na miƙama rose dake ɗauke da ledan hannu alamar ta bani, wata banzar harara ta zubamin ta dangwarar da ledar ƙasa ta koma ta zauna, bance da ita uffanba na ɗauka ledar da keys ɗin na nufi sama, dama duk abinnan da ake tuni Nabeelah ta haye tunda muka shigo ta gaida su Hafiz ta haye abinta.

Bily na gama hayewa Jawaad ya miƙe cikin dauriya ya ɗauki ɗaya daga ruwan da aka ajiyema su Hafiz yabi bayanta yana tafiya a hankali, dan inhar yace zaiyi hanzari dolene a fahimci matsalarsa, ca yay musu yana zuwa. Rose ta bisa da kallo a wani irin yanayi maisa ƙuna a zuciya, a ƙufule ta kalli su Aliyu tana faɗin, “Wai miye haɗin wannan yarinyar da Boss ne?, shishshiginta yayi yawafa” dukansu da mamaki suka kalleta, duk da sun fahimci tsagwaron kishi tattare da zancenta, Jabeer ya kare bakinsa da hannu yana dariya ƙasa-ƙasa, sai da Hafiz ya hararesa sannan ya haɗiye da ƙyar, ya kalli sama sannan ya maido dubansa ga Rose data sake cika fam. “Wai Rose kina nufin sonta yake?”. Da sauri tace, “Itaɗin banza, kaima kasan Boss ya wuce da ajinta, kawai dai itace ke shishshige masa”.

Hafiz yace, “Humm” Aliyu dake murmushi ne ya bata amsa, “Toke tunda kinsan haka miye na damuwar, dan ya sakata aiki sai ya zama wani abu, sau nawa ke ya sakaki ayyuka da sukafi wannan?”. Baki ta taɓe, cikin hausanta da bawani fita yakeba tace, “Amma tunda muke nama taɓa zuwa nan gidan ne? Itako daga gani tana nan tun ɗazun”. Cike da jin haushi Hafiz yace, “To idan ya sakko saiki masa wannan tambayar kuma ai”. Harar Hafiz tayi, dan tun dama can basa shiri, baya shiga sabgarta sai dole, dama sunfi ɗasawa da Jabeer duk cikinsu, Aliyu kuwa baida yawan hayaniya, dan harma yafi Jawaad rashin son magana. Babu wanda ya sake cewa komai, sai Rose daketa kallon hanyar benen tana cika da batsewa da sauke tagwayen ajiyar zuciya.1

STORY CONTINUES BELOW

A sama kuwa koda na isa Nabeelah na bama kayan akan yace takai masa su ɗaki, har Nabeelah ta amsa zata wuce sai gashi ya hawo, hakan yasani saurin riƙo ledan saboda wata uwar harara daya sauke min, Nabeelah ta juyo zatai magana itama ta samu rabonta na harar, sakarmin ledar tayi da sauri tana barin wajen, ni kam dai ƙasa nai da kai kawai.

Duk abinda sukeyi Ummah na zaune tana kallonsu, sai dai tayi kamar batasan sunayiba.

Jawaad ya wuce ɗaki batare da yace komaiba, dan shikuma baima lura da Ummah ba, bayansa nabi gudun karna sake wani laifin. baice dani komaiba harna ajiye ledan nai hanyar fita. Na sauke numfashi ganin na fito lafiya, a raina ina mitar ‘mutum sai baƙar takura’ matarka dai taga banu yasin, a can ƙasan raina kuma tunani nake yanada mata to miya haɗashi da shan magani irin wannan?, nifa dukma sai naji inajin kunyar abun yasin, nikam bazan sake yarda idona ya shiga cikin nashiba, wannan abun kunya har ina haka. Muna a falon Nabeelah na fama dani akan abinci data zubo ya fito, bai kalli kowaba a cikinmu ya sauka ƙasa.1

Ban sakko ba har saida suka tashi tafiya Jabeer ya ƙwalamin kira, lokacin dana ƙaraso duk sun fice daga shi sai Jabeer ɗin, inda yake Jabeer ya nunamin alamar yana kirana, na ƙarasa gabansa dan yanzu ya tashi zaune, batare da ya kalleni ba yace, “Ranar lahadi ƙarfe goma na safe kije ku haɗu da wannan yarinyar, Jabeer zai baki address ɗin wajen”. nidai nace masa to ina jiran ƙarin bayani, sai dai bai sake cewa komaiba, oga Jabeer yace, “muje to, Boss ALLAH ya ƙara sauƙi”. “Amin” ya faɗa akan laɓɓa, nima nace ALLAH ya ƙara sauƙi nai gaba batare da jiran ya amsaba, dan yaban haushi.

Ni da Jabeer a motarsa muka koma, su Aliyu kuwa suna a motar Hafiz da sukazo a ciki, ina kallon yanda Rose keta bina da baƙar harara nai tamkar ban ganiba.

Munzo fita daga layinne naga motar Mom zasu shiga su kuma, nace, “Lah ga mom can”. Jabeer dake tuƙi yace, “Ƙila itama zataje ganin boss ne ko?”. Kallonsa nai nace, “ganinsa kuma? Wai da gaske Ƴan uwansu ne?” dariya yay yana harba motar kan titi, yace, “Momin mu kemafa na kula akwai shiririta wani sa’in, bakiga gidansu ɗaya bane, ai da mom da Abban Jay babansu ɗaya, sannan Jay shine ya auri Shahudah kafin su rabu”.

Mugun waro idanu nayi baki a hangame, nace, “Wai dan ALLAH oga kana nufin dama shine mijin aunty Shahudah?”. Jabeer dake murmushi yace, “Ƙwarai kuwa, ammafa a da kenan, amma ke yaya kuke dasu Shahudah da har bama kisaniba?”. Daƙyar na iya ce masa kamar yanda Mom suke da Abban Boss, nima da Abbansu Aunty Shahudah da Mamana babansu ɗaya”.

Kai Jabeer ya shiga kaɗawa yana faɗin, “Tab cakwakiya kenan, kice shiyyasa Qaseem beson kowa ya raɓu dake? Kodai ƴar gida zamuyi?”. Murmushin yaƙe kawai nai masa bance komaiba, danni gaba ɗaya kaina ya toshe, koda wasa ban taɓa kawo cewar boss mijin aunty Shahudah bane ba, to yama akai na kasa fahimta? Koda yake bai taɓa zuwa gidanba ina nan, bankuma taɓa ganin koda hotonsa ba a gidan, amma kuma inban mantaba nasha jin sunan Jawaad a bakin ƴan gidan, ‘ya salam, miya toshe min kaina haka?’. Har mukaje station wannan tunani ne keta kaikawo tsakanin ƙwanyata da zuciyata batare da nasan ma’anar hakanba, shima kuma oga Jabeer bai sake cemin komaiba saima redio daya kunna.

Koda muka iso office nabi oga Jabeer kamar yanda ya umarceni, ya bani ƙaramar takarda ta address ɗin wajen da boss yace sannan na fito. Na iske su ummie sunata shirin tashi, dan biyar tayi, ALLAH ma ya soni nayi sallar la’asar yanzu da muka koma gidansu boss, nima ɗaukar tarkacena nai muka fito tare, dan Ummie zanbi, na leƙa office ɗin yah Qaseem bayan na fito daga wajen oga Jabeer na iske bayanan ya fita wai. Daurewa nai na cire alaƙar Aunty Shahudah da boss data tsayan a rai ba gaira ba sabar na biyema Ummie mukaita hirarmu, har gida ta kaini, sai dai bata shigaba iyakarta gate na sauka ita kuma ta juya.

Na iske su a falo aunty Shahudah kwance Doctor na saka mata ƙarin ruwa, ba hurumina bane tambayar abinda ya sameta, na gaishesu tare da mata sannu cikin jimami sannan na wuce ɗaki abina. Bansan miyasa na tsinci kaina cikin rashin jin daɗin komaiba, nai wanka na canja kaya, ganinma magrib tayi saina bari nai salla sannan nai zaman yin azkar har aka kira sallar isha’i, itama tashi nai nayi sannan na fito falon dan sake duba Aunty Shahudah, dan banajin yunwa, tun abincin da naci a gidan boss bai sauka ba, duk da saida Nabeelah ma tai fushi sannan naci bayan ummah ta saka baki.

Na iske aunty Shahudah ta koma ɗaki, sai yah Qaseem kawai a dining yana cin abinci, sannu da dawowa nai masa, yay murmushi yana min alamar nazo. Ban musaba naje garesa, naja kujera nima na zauna, “Kinyi ƙyau” ya faɗa yana kashemin ido ɗaya, murmushi kawai nayi bance komaiba. Haka yayta ɗan jana da hira harya kammala, ya miƙe domin zuwa yay wanka, nima miƙewar nai nace bara na sake duba aunty Shahudah naje na kwanta na gaji.

Zaune na isketa Aunty Aamilah na bata magani, na sake mata sannu da ALLAH ya ƙara sauƙi na fito, ɗaki na koma nai kwanciyata duk da nasan gobe idan ALLAH ya kaimu babu aiki, amma inason na kira Dad da safe idan ya bari sai naje gidan Inna Zainabu na gaishesu, da wannan tunanin barci ya kwasheni.

A ɗakin Shahudah kam bayan fitowar Bilkisu Aamilah ce ta sauke ajiyar zuciya tana mai fuskantar ƴar uwar tata da ƙyau. “Sister ga shawara mana” Shahudah da duk tazama kalar tausayi ta jinjina mata kai alamar tana saurarenta. Aamilah ta sake jan numfashi kafin tace, “Ina ganin yarinyar nan Bilkisu zamu iya sakata tai mana wani abu” murya a dasashe Shahudah tace, “Ban ganeba Aamilah “. “Sister ina magana ne akan Brother Jawaad, da nayi tunanin Broth ne a farko, sai dai daga baya nasan bamai yuwuwa bane, musamman idan mukai dubi da yanda basama shiri tun suna yara, sam jinin Qaseem da Jawaad bai haɗuba, bankuma san lokacin dazai haɗunba, so idan mukace zamu ɗorasa akan ya taimaka mana sai dai ya ɓata komai tunda dama can bason aurenku yakeba, yanzu da yarinyar nan ta shigo, sai naga mizai hana mu amfanu da ita, dan kinsan bata da yawan hayaniya da surutu, sannan mutumin dake da irinki bazai kalletaba da sigar birgewa balle akai ga so, ballantana zuciyarmu tayi tunanin ko zata iya cin amanarmu, ko shi yaji wani abu a kanta”. Shahudah datai shiru tana kallon Aamilah tace, “Maganganunki kawai naji Aamilah, amma ban gane ina suka dosaba sam, wane taimko zamu nema akan Bb?”. “Yauwa, yanzu kikai tambaya mai ƙyau Sisi na, inaji a raina Yarinyar zata taimakemu, sai dai bani da tabbacin wajen aikinsu ɗaya, duk da dai naga kullum tare take fita da Broth, kuma Broth da Brother Jawaad wajen aikinsu ɗaya ne, amma wannan ba wani abu bane, zamu iya tambayarta”. Kai kawai Shahudah ta jinjina alamar gamsuwa, Aamilah tace, “ki kwanta ki huta zamu tattauna zuwa da safe, tunda weekend ne tana gida babu inda take zuwa”. Nanma da kai Shahudah ta amsa mata..

★★★★★

Washe gari da safe na tashi nai ƴan ayyukan dazan iya harda kayana da sukai datti, na gyara ɗakina tsaf nai wanka sannan na fito, babu kowa falon dan har lokacin ma bana tunanin wani ya tashi a jama’ar gidan, kicin na nufa na samawa cikina abinci naci, kafin na sake komawa ɗaki na shiga neman Number dad da ya kirani kwanaki uku da suka shige, kusan duk Numbers nashi na ƙetare inada ita, dan yakan kirani lokaci-lokaci idan yay tafiya tamkar yanda yakema sauran ƴaƴansa, bata shigaba, na sake gwadawa har sau uku saina haƙura, bazan iya zuwa ko inaba bayan wajen aiki saida umarninsa, dan banida wani jagora sama da shi a halin yanzu a duniya, sai ko yaya Qaseem da nake fatan ya zama na biyu a matsayin miji. Na aje maganar zuwa gidan Inna zainabu akan sai idan ALLAH ya kaimu gobe, idan naje inda boss yace na gama abinda nakeyi sai na shiga wajen wanke kai daga nan na wuce can koda ban jimaba sai na gaishesu na taho gida, da wannan tunanin na miƙe da nufin zuwa gidansu Amina.

Harna fice babu motsin kowa, muka gaisa da baba mai-gadi na fice abina. Da sallama na shiga gidan, Amina dake a tsakar gida tana wanke-wanke ta amsa tana kumbura fuska, dariya nayi ganin yanda tayi, dan nasan dalili, ta ɗauke kanta da faɗin, “Munyi fushi, ki koma a binki”. Kafin nace wani abu mama tace, “Kwarai kuwa Amina ina bayanki”. Kunnuwana na kama duka biyu na kneeling alamar dai na tuba, dariya suka sanya daga mama har Amina da yayan Amina daya fito da ga bayi, shine yace, “A ni dai na yafe ma ƴar ƙanuwata, nasan aikine ke mata yawa”. Nace, “Yauwa Yayanmu, shiyyasa nake yayinka a koda yaushe”. yay dariya da haɗe yatsun sa babba da manuniya alamar dai-dai👌🏼 kenan.

“Oh, mu baƙya yayinmu kenan? To kin ƙarama kanki laifi har tsallon ƙwaɗo sai kinyi” Amina ta faɗa tana miƙewa ɗauke da kwandon data saka kwanikan. Mama tace, “A’a auta nimafa na huce, ama mai-gadon lu’u-lu’u haƙuri”. Dariya muka saka gaba ɗayanmu saboda furicin mama, Amina tace, “Shikenan na haƙura tunda mama ta saka baki, amma da yau ɗinan saina tsamar da ƙafafunki”. Harararta nai kafin na zauna a inda ta tashi na gaida Mama da Yaya Sule, daga nan muka hau hirarmu.

Wajen sha biyu Amina na tayani tsifar kai muna hira, mama kuma nata ƙoƙarin ɗaura awara da muka tace da Amina bayan munje munkai markaɗe, nace, “Amina!”.

“Na’am” ta amsamin tana leƙo fuskata. Ɗalli namata a fuska da ɗan yatsa, ta matsar da fuskarta tana ɓata fiska saboda zafi, niko na kwashe da dariya, “Ke ɗince kin wani kawomin fuska saikace maison leƙa ramin gwal”. Dariya itama tayi tana ranƙwashina a kai, “Ai bazakici bulusba kuwa”. “ALLAH da zafi” na faɗa ina harararta” tace, “Nima ai naji zafin shiyyasa na rama”. “Ba komai zaki gane shayi ruwane. Maganarnance dai zamu sake”. Shiru tayi kamar bazatace komaiba, tsifar da takemin ma ta koma min ita a hankali, na zungureta da hannu dan nasan ta faɗa kogin tunanin nata. Numfashi ta kawo a hankali, tace, “Ina saurarenki”.

“Amina, a zaman da kikai gidanmu na tsahon wasu shekaru, nasan zakisan halayyar kowa dake cikin gidan nan”. Tace, “Hakane” “Alhmdllh, mizan iya sani akan Qaseem da Salman?”. Shiru tai na wasu sakanni kafin ta sauke numfashi, “Duk abinda kikeson sani zan iya faɗa miki Bilkisu inhar na sanshi, wanda kuma ban sanshiba zance miki ban saniba, kimin tambaya zanfi fahimtar mikike son sani game dasu?”.

Cike da gamsuwar maganarta nace, “Hakane, Qaseem da Salman suna neman mata?”…………….✍

Asha weekend lafiya🤫🤭😉😍👌🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻17

Page 13

……………..Shiru tai na wasu mintuna kafin tace, “Ban taɓa ganinsu da idanunaba a gado ɗaya da mace, amma tabbas Salman yakansha zuwa da ƴammata gidan idan kamar basa nan, ko kuma suna barcinsu na ƙaddara, dan akwai lokacin farkon dawowarsu da yataɓa zuwa da wata yarinyar ƙabila suka kwana a gidan, da safe ta fito zata tafi ALLAH ya haɗasu da Alhaji a bazata, koda ya tambayeta daga ina? Saita faɗa masa Salman ne ya kawota, wlhy a lokacin nazata Alhaji zaiyi kiran Salman yaymasa tatas a gaban yarinyar, ya kuma gargaɗesa sake kawo wata sai kawai naga ya sallami yarinyar ta tafi, shikuma ya shiga mota abinsa ya fita rai a ɓace, dan ko driver hanawa yay ya tuƙasa da kansa yaja mota ranar. Bilkisu bansan miyasa Alhaji keda sakaci wajen tsawatarma yaransa akan abinda ba daidaiba, ya gwammaci ya shanye ɓacin ran a ransa komin zafin da abun yay masa da kuma illarsa garesu da yazauna ya nuna musu kuskurensu, gaskiya ban taɓa ganin wanda yayma boko da rayuwar yahudu ƙazamin ruƙo irin Uncle ɗinkiba, sai dai ina tausaya masa, dan banyi tunanin waɗannan ƴaƴan nasa zasu masa addu’a ba a lokacin da ƙasa ta rufe idanunsa, sai dai dayake UBANGIJI gafurunne kuma rahimun ba’a shigar masa al’amari, ikonsane ya canjasu kosu ƙare rayuwarsu a haguggunce kamar yanda suka tashi. Qaseem kam dai bazance na taɓa ganin ya kawo mace gidan nanba, sai dai nakanji yana waya, dan kusan sau uku ko biyu inajin yana waya da ambatar sunan hotel, ba sunan hotel daya shigo ciki bane kawai yasa nai tunanin hakan, sunan mata dakan shigo a zancen nasa da salon yanda yake wayarne kawai dai ya ɗarsa mani haka. Sai kuma faɗa da naji wataran Hajiya na masa akan batun aure, take cewa ya zauna yanata shashanci a waje sai ya gama tsufa baiyi aureba, idan soyake wata ta haifa mata jika a waje sai ya bada himma. Kinga a zancenta yana nuna kenan yana yin abinda bai daceba ta kamashi ko aka kawo mata labari. Sai dai shima babu tabbas, tunda ba ido da ido nidai na gansaba. Abu na biyu kuma Qaseem baya shaye-shaye, baida wulaƙanci tamkar Hajiya, dan baya shiga huruminka sai idan kaine ka saka kanka a ciki ko wani dalili ya haɗaku, da wahala kiga yana hantarar masu aiki sai idan sun ƙuresa gaskiya, shiyyasa lokacin da kikazo gidan naga yanata biyema su Hajiya akan abinda suke miki nata mamaki, dan nasan ba halinsa bane, sai daga baya na fahimci soyayyace yake miki batare da shima ya saniba, shiyyasa baya iya yin shiru akan al’amarinki. Salman yana shaye-shaye, dan ɗakinsa ma zaki gansu zube baya shakka balle shayin kowa, sannan ɗan wulaƙancine dason yanƙwana mutum, sai dai shi kuma akwai ƙyauta, dan bashi da rowa, akwai kuma tausayi idan ƴan mutuncin na kansa bai cake ba, dan wani rashin mutuncin nasa abinda yake sha ne ke azashi bisa hanyar aikatawa. Haka rayuwa take, duk inda kika samu mutum da mugun hali zaki samesa da ƙyaƙyƙyawa kuma”.

      “Hakane kam Amina” na faɗa ina sake juya maganganunta a cikin raina.2

         Tunda na dawo gida maganganun Amina ne kawai keta kai kawo a raina, na idar da sallar la’asar ina cikin naɗe abin sallar Aunty Shahudah ta shigo, sosai nayi mamakin ganinta harma fuskata ta kasa ɓoyewa, dan tunda aka bani ɗakinta bata sake shigowaba, hasalima a wancan lokacin catai ƙyanƙyami kayan ciki take tunda na taɓasu.

      Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo sannan ta zauna a bakin gado, fuskarta wasai babu alamin turɓune wa kamar yanda takeyi da, sannan babu kallon banza balle hantara.

        “Oh, sai kallona kike tamkar kin samu tv Bilkisu”. Murmushin da ban shiryaba nayi, dan inaga yaune karan farko dana fara jin sunana a bakinta, nace, “Aunty Shahudah ai mamakin shigowarki nan nake, nasan dai…..” sai kuma nai shiru ban ƙarisa ba. Batace komaiba sai gefenta data nunamin da hannu alamar na zauna. Nima ban musaba na zauna ɗin inata ƙara mamakinta dai. Cikin katsemin tunani tace,

      “Bilkisu aiki nazo kimin, konawa kike buƙata zan biyaki”. Kallonta nai da mamaki, sai kuma na girgiza kaina, “Aunty Shahudah ni yanzu dan zaki sakani abu har sai kin biyani? Bana buƙatar ki dinga kallon haka tsakanina dake, ki sakani kominene kike da buƙata a matsayinki na wacce take sama dani kuma nake ƙanwarki, nikuma nai miki alƙawarin inhar baifi ƙarfin himmata ba zan yimiki shi”. Tai guntun murmushin da ke ƙarama ƙyaƙyƙyawar fuskarta ƙyau tana jinjina kai, Tace, “Bansan haka kike da kirkiba ai, amma duk da haka zan biyaki, domin aikin ya cancanci hakan”.

      “Humm” kawai nace mata.

Ta sake muskuta zamanta da cewar, “Waje ɗaya kuke aiki da Broth ko?”. Nasan Yah Qaseem suke cema haka, dan haka nace mata “Eh”. Tace, “Yauwa, a Station ɗinku, akwai wanda nakeson kimin aikin a kansa, sunansa Jawaad, bai zama lallai ki sanshiba, dan shi mutumne da baya shiga kowane tarkace, yanzu ɗinma sai munyi shawara da dogon nazarin da har zaki iya samun kusancin taimakon nawa a wajenshi, dan nasan bazai kulaki ba kai tsaye”. Ta ɗanso bani dariya a maganganunta, amma sai na danne banyiba, dan nima nasan gaskiya dukta faɗa akan halayyar Boss, to amma yanda take faɗan magana a habaice kuma tanason na mata aikine ya saka abin son bani dariya. Tace, “Abinda yasa na zaɓeki a aikin nan saboda, baki da surutu, sannan kin iya hausa sosai, zaki fimu sanin hanyoyin da zaki fahimtar dashi ya fahimta saboda shi mayen son yaren hausane”. Yanzunkam kasa daurewa nai sai da na murmusa, banda shirme irin nata dasu da suka ɗauki yaren wani wata tsiya, ai sai sakarai ke ƙin yarensa.

     “Tom aunty Shahudah, yanzu mikikeso nayi ni?”. Jim tayi alamar tunani akan abinda ke’a ranta, sai kuma zuwa can ta sauke numfashi, “Zan ringa baki saƙo kina kai masa kulum, wannan shine kawai aikinki, idan kuma ya tambayi wani abu game dani, sai kisan yanda zaki tsarashi da manya-manyan hausarnan naku. Amma dai Aamilah zata sake miki bayani yanda zaki fahimta, danni harma narasa yanda zaki sake ƙara fahimtata”.

       “Karki damu Aunty, ko a yanzunma na fahimceki, matsalar kawai shine yanda zan samu kusancin dashi, da har zan sako masa babbar magana data shafi rayuwarsa ne, dan kinga wannan babbar maganace data kasance sirrinsa da ya shafesa ba zancen aikiba, amma namiki alƙawarin zan gwada ta wasu hanyoyi, saiki dage da addu’a kuma”.  

      “Okey, zuwa anjima zamu fita ni da Aamilah, zamu sayo abinda zakije masa dashi ranar Monday”. Na jinjina mata kaina kawai, dan bansan miyasa take bani tausayiba yanzu, na kula tana sonshi sosai, to ai Boss ya cancanci a soshi, sannan ita kanta ina mamakin yanda ya iya sakaci da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar, ba namiji irinsaba hatta dani mace aunty Shahudah na birgeni, tana cikin mata ƙyawawa ajin farko da ba cikin baƙaƙeba kosu kansu fararen ta shiga cikinsu saisun yabata, sun dace sosai matsayin ma’aurata ita da Boss, ‘sai dai nikam ta yaya zan tunkaresa da maganar nan?’.7

STORY CONTINUES BELOW

JAWAAD

           Tun sanda yasha maganin sai ya dinga samun nutsuwa a hankali harya  farajin ɗan ƙarfi bayan tafiyarsu bilkisu, sai kuma yaƙi da zuciya, sosai maganin na masa aiki, amma yasan wataran zai daina tamkar yanda na bayama sukai yayi suka shuɗe, ko abokinsa Doctor Sooraj ɗin da ya bashi shawarar amfani da wannan maganin ya tabbatar masa na wani ɗan lokacine kawai, babbar mafita shine yay aure, inba hakaba ƙwayoyin da yakesha domin kare kansa daga faɗawa halakar da yake gudu to lallai zasu iya masa illa ma wataran, tunda har ALLAH ya bashi lafiya da muhalli, dukiyar aure mi yakema zaman jira? Idan matarsa yakeso ya dawo da ita mana yabar cutar kansa. A lokacin da Dr Sooraj kema Jay wannan maganar ƙin ce masa uffan yay, daga ƙarshema sai yay masa sallama ya baro office ɗin.

            Da daddare bayan tafiyar su Ummah gida ya samu kira daga Uncle Nasir, duk da bayajin ƙwarin jikinsa haka ya tashi ya fita bayan ya saka dogon wando a jikinsa, dan harma ya riga yay shirin barci shi. Kansa tsaye falon Uncle Nasir ya nufa, bayan yay sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, Uncle Nasir na zaune shida matarsa suna hira da kallon labarai, ya gaishesu da girmamawa. Duk fuskokinsu ɗauke da fara’a suka amsa masa, Uncle Nasir yace ya taso susha Fruit salad ɗin da yake sha, Jawaad ya amsa da, “Alhmdllh Uncle na ƙoshi”.

      “Aiko saika shashi” cewar Hajiya Sumayya matar Uncle Nasir, ta cigaba da faɗin, “kai yanzu Jawaad kenan ka girmi cin abincin kowa a gidan nan?, tunda kai aure shikenan, da ai ba haka kakeyiba, mu yanzu ka yayemu daga iyayenka kenan?, inaga ko shayin wajenan rabon daka shashi tun daren ɗaurin aurenka da Shahudah, to ni dai yanzu kamar yanda na saba a baya kullum zan zubo abinci na aiko dashi sashenka, idan kaso kaita jerenshi kamar ɗakin amarya”.

    Murmushi yayi tare da kai hannu ya shafi kansa, yace, “Nayi laifi Ammi, amma ayi haƙuri, kinsan yanayin aikinmune yasa, wani lokacin bana shigowa da wuri, kuma ina fita da wuri,  amma daga yanzun indai na dawo da wuri zanyi magana a kawo mani”. “To yanzu naji magana, bara na zuba maka fruit salad ɗin”.

     Uncle Nasir dake saurarensu yace, “

Ke nama lura sake ɗaure masa ƙugun zama babu aure kikeyi, yanzu ba zancen adinga kai masa abinci nai zamanyi ba, zancen wadda zata dinga dafa masa kamar kowane magidanci zanyi”. Tace, “Ah Alhaji indai nan ne aini ina bayanka, ga ƙannensa nan su Abdur-rahman za’ai musu haihuwa ta bibbiyu, shiko ya zauna ruwan ido kamar wanda bai ɗanɗana auren yajiba”.

         “Barsa, ai na shirya maganinsa wannan karon, idan har bai shiryaba ni a shirye nake na zaɓi ɗaya daga yaran gidanan na aura masa”. Da sauri Jay ya kalli kawun nasa harda waro idanu. “Kalleni da ƙyau fa, ALLAH inhar baka yunƙuro a cikin shekararnan ba, a yaran gidanan zan aura maka, karkuma ka ɗauka maganar wasa nake maka, gobema insha ALLAH zanje na sami Alhaji babah muyi magana (Kakansa mahaifin Mamansa), idan kuma matarka kakeso ka dawo da ita”. Shiru Jawaad yayi baice komaiba har Uncle Nasir ya gama masa faɗa sannan ya bashi haƙuri akan insha ALLAH zaiyi abinda sukeso, amma su ƙara masa lokaci.

        Uncle Nasir yace, “Ba damuwa, ALLAH ya kawo mafita, amma ranar lahadi idan ALLAH ya kaimu akwai meeting da za’ai ƙarfe huɗu, sai kai ƙoƙari ka halarta, karka bari ayi kuka da kai kamar ko yaushe dan ALLAH”.

        “Insha ALLAHU Uncle zan kiyaye”.

       Ya daɗe a sashen suna hira dan sai kusan ƙarfe ɗaya ya koma sashensa, kasancewar yasha barcin rana sai bai iya yin na darenba da wuri, lap-top ya buɗe ya shiga wasu ayyukan, sai wajen biyu da rabi ya rufe ya tashi, alwala yayo yay nafilfili tare da jero doguwar addu’a akan mahaifinsa da mahaifiyarsa, dama sauran al’umma baki ɗaya.

     

     Sakamakon rashin kwanciya da wuri ya sashi makara sallar asuba, ya tashi a gaggauce ya nufi toilet ya ɗauro alwala, bayan ya gabatar da salla yay wanka ya gyara gadonsa sanan yay shirin fita, Gimba ya tafi gida weekend, dan haka shi da kansa yaja motarsa sai ƙaton gidan gonarsa da ya gada wajen mahaifinsa dake can asalin ƙauyen kakansa Alhaji Yusif, inda sukai rayuwa da kakarsa mama maryam, garin kuma da mahaifinsa yay rayuwar ƙuruciya harma data girma. Sosai an samu cigaba da abubuwa masu dama a cikin ƙauyen wanda duk sanadin mahaifinsane, an musu titi, an kuma kai musu wuta, ga dam ɗinsu da har yanzu suke noman rani, dan garin yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan da ake amfanuwa da nomansu da kiwo a jihar tasu dama maƙwaftanta baki ɗaya. Alkairin mahaifinsa da shi kansa wanda yakeyi yasa a kullum yake mai daraja a wajensu, idan yaje ji suke tamkar su haɗiyeshi, saika rantse wani sarakine.

      Kamar yanda ya saba gidan mai gari ya sauka, dan haka ya keyi a duk lokacin da yaje ƙauyen, hakan na ƙara masa daraja da kwarjini, kamar yanda shima yakejin daɗin abinda suke masa ɗin, dan maigari yana masa abu tamkar uba, kasancewarsa abokine ga mahaifinsa Abdul-aziz tunna ƙuruciya. Ya samu tarba kuwa ta mutuntawa, inda akaita haba-haba dashi da abincin gargajiya masu tsafta kamar yaune aka fara ganinsa matsayin baƙo. Sam Jawaad bashi da girman kan zaɓar cima ko raina cimar ƙauye, hasalima suna masa saɗi fiye dana zamani, idan har yaje ƙauyen nan komi suka bashi cin abinsa yake, saboda yanada yaƙini akan tsaftar iyalan baba maigari, tun yana ƙanƙanin yaro mahaifinsa ke zuwa dashi, hakama mama maryam na kawosa kafin ta rasu, hankalinsa kwance yaci ya ƙoshi, dan dama da yunwarsa yazo, bayan sun gaisa da baba maigari da jama’ar dake fada suka nufi gidan gona shi da Abbati ɗan baba maigarin da zasuyi sa’anni da Jawaad, dan abokinsane na amana, dukkan sirrin gidan gonarsa yana hannun Abbati, shike kula da komai, Abbati dukda yayi karatu har matakin degree na biyu yana zaune ne anan ƙauyen tare da iyayensa, iyakarsa yaje birni wajen aiki ya dawo garinsu ya kwanta, matarsa ɗaya da ƴaƴa huɗu, yayi ɗan gininsa na zamani saboda ƙauyen yanzu yanada dukkan cigaban da ake hangensa a birnin, kuma mafi yawansu sunada aƙidar son zaman gida sai dai waɗanda aiki ya tilastama komawa birnin akan dole, dan a dalilin Abdul-aziz mahaifin Jawaad ƙauyen yanada manyan ƴan boko matasa masu jini a jika dake taka rawar gani sosai a sassan ƙasar.

     Suna tafe suna hirarsu cikin nishaɗi, inda Abbati keta kiran sauran abokansu dake gida ta waya yana sanar musu Jawaad yazo. Jawaad ya fige wayar yana hararar Abbati, “Malam ya isheka haka, sai gayyatomin ƴan iskannan kake salon kuzo ku addabeni da surutu mara ma’ana”. Abbati ya kwashe da dariya, “Oh ashe kana tsoron surutun namu? Ai indai kaga munbar maka surutu kuwa sai kayi abinda mukeso, ka dubemu daga mai yara uku sai masu huɗu amma kai ka zauna ruwan ido Jay, ai kosu Jabeer da kuke tare a birni  sunada iyalansu, wai kodai da kurwanka Shahudah ta tafine bani labari kafin su Isa su zo”.

     Kafin Jay yay magana sukaji ance, “Ai gamu mun iso”. Daƙƙuwa Jay ya watsama abokan nasa huɗu da suka iso wajen yanzu-yanzu, waɗanda suma duk sunyi karatu kowa da abin yinsa, kuma suna bada gudunmawa a gidan gonarsa suma. “Duk kunci ƙaniyarku zomayen banza, uwarwa ya gayyatoku nan?”.

      Dariya suka sanya baki ɗaya, Labaran ya dunƙule hannu ya bigi damtsen hannun Jawaad yana faɗin, “Bar wani mazurai gaye, munfika ƙarfi fa inma hayaƙin kakeji, dan mu kullum matanmu ƙara mana sukeyi” duka shima Jawaad ya kai masa, Labaran yay saurin duƙewa. “Ɗan iska da ka tsaya naima fuskarka damage sai naga ƙarfin da Asiyan ke baka, mara mutunci”. Dariya suka sanya su dukansu, Aminu yace, “Mudai mun gaji da ganinka haka ALLAH kuwa”. “Gaskiyane Aminu, ya kamata ka duba Jay” cewar isa. “Hakane kam lokaci baya jira fa, kullum girma muke ƙarawa ƙuruciyarmu na guduwa” cewar Salisu dake dafe da kafaɗar Jawaad. Murmushi kawai Jawaad yayi, yasan halin abokan nasa, tunkan yay auren farkoma haka sukaita addabarsa, sai da akai bikinsa da shahudane suka sama masa lafiya, yanzunma ko waya yake dasu faɗansu kenan, shi kansa ba auren bane bayaso, gidan jiya yake tsoron komawa…….. Adam ya katse masa tunani da cewar, “Idan kuma a birnin babu wadda tai maka ka duba a garin nan mana, auren nan shine cikar martabar mutum”. Abbati yace, “Maganarku nakan hanya ƴan uwa, ko ɓato maka rai akai daga waje kana shigowa gida kaga iyalanka sai kaji ka huce, musamman idan kayi dace da macen datasan yanda zata tattali dukkanin farin cikinka, koda gajiyarka ka kwaso kanada inda za’a nuna tausayinka a sauke maka ita da kulawa”. Jawaad ya shafa kansa yana sauke numfashi da girgiza kai, “Kudai baku da magana saita aure dai jarababbu, ko hutawa bakwayi, karku damu zanyi, kumin addu’a kudai. a tare suka shiga masa addu’ar kuwa kafin su fara bashi hannu suna gaisuwa.

       Jawaad nason abokansa na ƙauyensu, dan suna bashi nishaɗi da faɗa masa gaskiya komai ɗacinta, shiyyasa ko kansa ɗaukar zafi yay a wajen aiki tuni yake ƙoƙarin ware weekend ɗin da zai shigo, dan yasan zai samu nutsuwa sosai…………..✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.3

Page 14
Guys ɗinan anya kunaso na mutu da idanuna?, kusan words dubu uku nakeyifa a kullum amma sai naji kuna farautar ƙari🤔, aradu inason ƙulla shekara ɗari da idanuna kuyi haƙuri😂🤣😂. Ga zaɓin lokacin posting, 11pm ko kuma 6am. Waɗanda naga sunfi rinjaye sai abi ra’ayinsu. Amma masu cewa dama Jay yana dariya?? nima kun bani dariya wlhy sosai, waye baya ya dariya a duniya, sai dai idan bata kamaba😂. Harda ƙyaƙyƙewa zakuji yayima wataran🚴🏼🚴🏼👌🏼.69
Ina muku fatan alkairi😍😘😍😘😘😘.11
…………….Zagayen gidan gonar suka farayi suna hira mai daɗi da mutunta juna, sashen dabbobin da ake kiwo da sashen da ake noma, sashen kaji, kifi, su talo-talo, zabi, agwagi, kajin gida, zomaye, harda tantabaru, sai sashen itatuwan fruits, komai yana tafiya yanda yake buƙata, sun nufi inda Jawaad ya gyara shima suke fidda yankakkun kaji dasu zabbi da sauran duk nau’in ƙananun dabbobin da ake kiwo a wajen ana packaging nasu a ledoji a shiryasu a wasu robobi manya masu haske domin masu sari dake kaiwa birni, hakama ƙwan kaji da zabi dana talo-talo, sai inda ake tace tsaftatacciyar madarar shanu kuma ana sakawa a galoli shima, kowacce galon da adadin litar da take ci, da inda ake shirya dukkanin nau’in kayan itatuwa suma. Abin dai dolene ya burge mai kallo da ƙayatarwa sosai. Sai da suka shiga lungu da saƙo, ya kuma gamsuwa da yanda komai ke tafiya, yana ta ma ma’aikatan jinjina da sake basu ƙwarin gwiwa, inda yaga kuskure kuwa cikin hikima yake musu gyara ba yanda zasu fahimci gazawarsu ba, yanda yake tafiyar da al’amarinsu na ƙara masa girma a idonsu sosai da daraja. Bayan sun kammala zagayawa suka yada zango ƙarƙashin bukkar bunu da tasha gyara domin hutawa, gefenta kuma anyi ɗan gini mai 2 bedroom kawai, domin idan yazo da shirin kwana nan yake kwana ko gidan baba maigari, hirarsu suka cigaba dayi cikin nishaɗi, lokaci-lokaci Jay yakan amsa waya, wadda ta shafi aiki kuwa yakan tashi ya koma gefe idan ya gama ya dawo. Da rana sai ga abinci lafiyayye daga gidan baba maigari an aiko musu, harda fura mai ƙyau da tasha damu. Yini guda anan suka yisa, Jawaad yaji matsalolin jama’ar garinsa waɗanda zai iya kawo gyara da iya ƙarfin aljihunsa yace zaiyi, dan dama ya daɗe bai zoba kusan wata uku. wanda sukafi ƙarfinsa kuma zasu haɗa hannu domin neman taimakon wanda zai iya musu, Jawaad ya gaji mahaifinsa a abubuwa da dama, komai nashi na al’ummane, dukiyar da mahaifinsa ya bari bata rufe masa ido ya zama asharari ba, sai ya ɗora kyawawan aiyukansa akan wanda mahaifinsa ya fara, tare da nasa da ya ƙirƙira shima, yanda yake rayuwarsa a sauƙaƙe bazaka taɓa tunanin an tara masa irin wannan dukiyarba, dan ko iya gidan gonarnan ai al’amarine babba, balle kuma akwai wanima bayan wannan, bayan sauran abubuwa da shima nasa ƙoƙarin.
       Bayan sunbar gidan gona gidan baba mai-gari suka koma, sun samu zama dashi da manyan gari suka tattauna akan maganar da sukai a gidan gona na abokansa, sai bayan sallar magriba Jawaad ya baro ƙauyen cike da tsaraba daga jama’a, duk da sunsan yanadashi hakan baisa suji ƙyashin ƙyautata masa da ni’imar da suma ALLAH yay musu ba. A hanya ya tsaya yay sallar isha’i kafin ya ƙarisa gidan Umma ƙarama. Tayi murnar ganinsa ita da yaranta, ya sauke mata tsarabarta anan da ɗibar mata wadda mutane suka bashi yay mata sallama ya tafi dan bai jimaba sosai, daga nan sai gidan Ummah babba, gidansu Nabeelah kenan, nanma sunyi murnar ganinsa, inda suka fara faɗansu shi da Batool kamar yanda suka saba, itama dai tsarabar ya ajiye musu ya tafi, a gida ya yada zango, kasancewar kowa ya shige sashensa shima nashi ya shige akan da safe zai fiddama kowa nasa kason, sauran ya kaima kakansa nasa shima, sai nasu Hafiz.+
WASHE GARI LAHADI.
        Washe gari lahadi, na tashi da burin abubuwa da dama, dan da daddare na samu Dad da yah Qassem ya kirashi, na faɗa masa zanje na gaida Inna zainabu yace naje sai driver ya kaini, na sanar masa zanhau napep saboda zan fara zuwa wajen aiki da aka sakani kafin naje canɗin idan na fito wajen saloon. Ina kammala gyaran ɗaki nai wanka, na fita nai breakfast sama-sama na koma ɗaki nai shiri. Doguwar rigace na saka ta Material baƙa da ratsin fari, ta zaunamin ɗas a jiki, gashi ta buɗe daga ƙasa bata wani matseniba sai a ƙirji kamar yanda tsarin ɗinkin yake, maɗaurin da akai mata na kama na ɗaure a bayana, sai ta kuma fita da ƙyau. Gashina dake a tsefe na kuma gyarama zaman ribbon, sanan na saka farar hula mai ƙyau, na kawo ƙaramin gyale baƙi na yana a kaina, tare da kalmashesa a ƙirjina ya rufe ruf na ɗora a kafaɗa ƙasanshi suka sauka bayana, basai an faɗaminba, ni kaina nasan nayi ƙyau, hakan yasa naita kallon kaina a mirror ina murmushi, a gurguje na ƙarasa kimtsawa na fito sagale da ƴar jikkata a kafaɗa ina ƙamshi mai sanyi, sai takalma masu ɗan tudu kaɗan, na riga na faɗama Mom zan fita dama tun da daddare, hakan yasa yanzu nai ficewata kaina tsaye tunda babu wanda ya tashi har Yah Qaseem da baisan zan fitaba, dan banfaɗa masabama gudun matsala.
       Da ƙafa na taka har titi na tari napep na hau zuwa inda Oga Jabeer ya bani.
STORY CONTINUES BELOW
        Bayan fitar Bilkisu daga gidan Mom ta fito daga ɗakinta, tanason tayi magana da Shahudah ne, shiyyasa tun ɗazun taketa dakon fitar bily, tana tsoron halin da Shahudah zata iya shiga da har bily zata sani, dan a ganinta bily ita kaɗaice bare a cikinsu da bai kamata tasan sirrinsu ba. Sam jiya batai barciba akan bayanin da Shahudah tai musu na zuwa ɓangaren Jawaad da tayi, ta fahimci sunyi kuskuren ƙin sanarma Shahudah gaskiyar lamari akan sakinta da Jawaad yayi tun lokacin da wancan al’amarin ya faru, ba damuwarta abinda Shahudah ta aikataba, damuwarta kar Jawaad ya sake gudun Shahudah akan hakan, dan ita kanta inhar zata faɗi gaskiya bata taɓa kama Jawaad da abun rashin gaskiya ba dangane da fasiƙanci, dan ko lokacin da basa ƙasar ma idan yaje musu hutu duk jarabar Shahudah da naci akan yazo suje club baya zuwa, ita kanta ma faɗa yake mata, shiyyasa da yaje take kame kanta. To tasan akan hakan Jawaad zai iya sake bijire musu ne dangane da maida Shahudah.
     Tashin Shahudah kenan a barci tayo brush da alwala ta fito mom ta shigo, ƙarfe goma saura sai yanzune wai ake alwalar sallar asuba😭🤦🏻.
     “Mom lafiya?” Shahudah dake ƙoƙarin saka gyale ta faɗa tana kallon mom. Mom ta zauna bakin gado tana faɗin, “Magana nazo muyi”. Zama Shahudah tai ta fasa sallan, Mom tace ba salla zakiyiba ne?” “Eh salla zanyi, amma muyi magana sai nayi daga baya”. “Karki damu tashi kiyi sallar zan jiraki”. Shahudah batace komaiba ta miƙe ta kabbara salla, wadda ALLAH kaɗai yasan mima take karantawa, dan a mintuna ƙalilan ta idar da kayarta ta dawo wajen mom dake zaune tai tagumi da juya abinda zai iya biyo baya a ranta. Motsin Shahudah ne ya maidota hayyacinta ta gyara zama, tare da kamo hannayen Shahudah duka cikin nata ta kafeta da idanu, “Shahudah magana zanyi miki, inason ki nutsu ki fahimta, domin muma a yanzu haka hanyar gyara ɓarnar da kikayi muke, munada tabbacin samun nasara kuma, abinda yasa muka yanke hukunci sanar mikin a yanzu dukda mun ɓoye a baya saboda gudun halin da zaki shiga, yanzu kam saboda karki sake ƙara tafka irin kuskuren da kikayi ranar na zuwa wajen Jawaad”.
       “Mom ni dan ALLAH kimin magana kai tsaye, ki daina yimin wannan manya-manyan hausan naki da ba wani fahimtarsu nakeba, minene ya faru”. Yanda tai maganar da kumbura bakin shagwaɓa yasa mon yin ƴar dariya tana shafar kumatunta, “Nifa daɗina dake taɓara maman Dadynta, karki damu ai zan kaiki, kumani sonake ki iya hausar ai tunda yaren mamanki ce”. Shahudah batace komaiba sai ɓata fuska data sake yi. Mom ta ɗauka takardan data shigo dashi ta miƙama Shahudah. Babu musu Shahudah ta amsa tabuɗe takardan batare da tace komaiba.
      Kasancewar Jawaad da turanci ya rubutama Shahudah takardan saki sai ta fahimci komai dallah-dallah. Hannunta na rawa da bakinta ta ɗaga takardar, “Mom kina nufin BB ne ya aiko min da wanan dan naje wajensa?”.
     Kai Mom ta girgiza mata, “Badan kinje wajensa bane, wannan takardar shekararta biyar kenan a gidannan, mune dai bamu bakiba tun lokacin da akai rikicin zubar da cikin nan, munƙi bakine saboda gudun karki sake shiga wani hali akan wanda kika tsinci kanki a wancan lokacin, dan munata ƙoƙarin duk bin hanyar data dace ki koma ɗakinki, sai dai zuwan da kikai wajensa ya ɗakko hanyar ɓata dukkanin shirin namu, shi bazai fahimci bakisan ya sakekiba, zai fassara abinne ta wata siga daban”.
        Matsanancin kuka shahudah ta fashe dashi, ta dafe kanta dake juya mata lokaci ɗaya, yanda tai baya zata faɗine yasa Mom azamar tarota tana kiran sunanta a razane, rungumeta shahudah tayi tana kuma kuka tamkar ranta zai fita, sai dai ƙarancin tunaninta na raya mata cewar tamkar sakin a banzane, dan Jawaad yayi ƙarya ya kwana da yunwa, aurensu baida maraba dana zobe, babu kishiya babu saki, ta daka tsalle ta dire a gaban Mom tare da wawaso rantsuwa ta sake direwa akan baima isaba. Yanda ta birkicema Mom tana kuka da rantsuwar Jawaad bai isabane ya jawo hankalin Aamilah data fito falon ƙasa neman abinci, sai Qaseem dake a d/table zaune yana karyawa shima, a guje Aamilah tay sama, Qaseem ma ya miƙe yabi bayanta. Yanda Shahudah ta rikice Mom na rirriƙeta sai abun ya basu mamaki suka shiga tambayar mom ko lafiya?. Basu samu amsa daga bakin mom ɗinba sai a takardar sakin da Shahudah ta jefar ƙasa, Qaseem yace, “K dalla malama nutsu mana anan” yanda yay maganar a tsawace yasa Shahudah nutsuwa sai dai ta maka masa harara tamkar zata makesa.
      Bai kulata ba ya maida dubansa ga Mom yana kaɗa takardar, “Ita wannan ɗin kuma daga ina Mom? Wata ya sake aikowa?” mom tace, “A’a waccance dai, kasan bata saniba, shinefa ranar Alhamis datasa muka barta can taje………” Mom ta zayyanema Qaseem komai daya faru tsakanin Jay da Shahudah a daren juma’a wato ranar alhamis, wanda shine sanadin ciwonta. Jiyay tamkar ya make Shahudah dan takaici, Aamilah kam da yake Shahudah ta faɗa mata komai sai bataji abun a saboba, ya nuna ta da yatsa yana faɗin, “Kedai wlhy daƙiƙiyace, wai ubanmiye a jikin wannan wawan Jawaad ɗin da sauran maza suka rasa har kika nace masa?”. A fusace Shahudah tace, “Sai dai idan kaine daƙiƙin, kaiɗin ubanmiye a jikin yarinyarnan da sauran mata suka rasa ka nace mata (Bilkisu take nufi) (hakan ba sabon abu bane dan babu wani girmama juna a tsakaninsu). Duka yakai mata yana faɗin, “Idan kinajin iskancinki a gidannan kibar sakkoni, inba hakaba wlhy saina ɓallaki watan Shahudah. “Ka ɓallani ɗin tunda kai ɗin ubanane, saika gayamin banza na kasa maida maka amsa da wofi, uwarwa yama sakaka cikin maganar? Bansan shishshigi”. Dukan ya sake kaimata Mom ta tare. “Wai wane irin iskancine wannan!! Taya zaku sakani tsakkiya da shirme, ku barni naji da abinda ya dameni mana!!”. Duk dakatawa sukai kowa na huci kamar wasu ƴan dambe. Daga ƙarshe Qaseem ya juya zai fita Mom ta dakatar dashi ta hanyar kamo hannunsa, ƙin juyowa yay yadai tsaya, “Kayi haƙuri, ni banason wannan saurin fushin naka Qaseem, kasandai halin rashin kunyar Shahudah a gidanan, yakamata ka cigaba da haƙuri dasu a matsayinka na babba a cikinsu, kaji”. Ajiyar zuciya ya sauke, ya kaɗa kansa kawai. Tace, “To ku zauna muyi magana, Aamilah jeki kira Salman”.3
BILKEESU
           Gurin ya haɗu matuƙa, bawani mugun ƙato baneba, madaidaici ne da akayisa domin masu hutawa kawai, yasha gyara da korayen ciyayi da flowers masu ƙamshi, nidai saima na zama baƙauya, dan duk zamana garin bansan da zamansa ba, koda yake inama nake zuwa, dama yawona dasu Ummie ne idan mun dawo hutu, to ƙafarmu bata taɓa zuwa nanba kuma, sai dai a zahiri na kame kaina ina tafiya cikin nutsuwa, ƙarƙashin ɗaya daga cikin ƙananun bukkokin da aka ƙawata wajen na nufa, naja kujera ɗaya cikin huɗu dake a kowacce ruffa na zauna tare da ɗora jikkata akan tebir ɗin na buɗe na ciro waya. Motsi naji a kaina, dan haka na duba wanda yazo wajen, ɗaya daga ma’aikatansu ne, ya gaisheni yana mai dire tiren hannunsa. Amsa masa nai tare da jeho masa tambaya akan kuɗin abinda ya kawo, duk da bani nace ya kawoba, tunanina tsarinsu kenan. “Karki damu Madam, an rigada an biya” ya faɗa yana barin wajen. Binsa kawai nai da kallo harya shigema ganina, mamakina shine ‘waye ya biya?’. bani da mai bani amsa, hakan yasani kauda abin a raina na duba abinda ya ajiye ɗin. Popcorn ne sai robar ice-creem da Malt ɗaya da ruwa, na ɗauke idona inajan guntun tsaki tare maida hankalina ga wayata na fara tafama Oga Jabeer saƙo. Bayan na tura masa naga ya wuce sai kawai na shiga yin Game batare dana kula abinda aka ajiye min ɗinba dan a ƙoshe nake.
       “Hy Babie!” aka faɗa dai-dai kunnena, a tsorace na ɗago idanuna dan a bazata abin yazomin, banji motsin kowaba. Ƙyaƙyƙyawan saurayi fari tas kuma ɗan gaye ya sakarmin murmushi da ɗage gira ɗaya sama, “Sorry na tsorataki ko?”.
          Janye idanuna nayi daga kansa batare dana tanka masaba ko magana. “Kin cancanta” ya faɗa yana zama kujerar dake facing ɗina. Nanma dai ƙin kulashi nayi, yaja ɗan kwalin da Popcorn ɗin ke ciki ya fara ɗiba yana afawa a bakinsa tare da lumshe ido alamar dai akwai daɗi. Janye idanuna nai daga satar kallonsa na tura wayata a jikka na miƙe zan bar masa wajen. Da sauri shima ya miƙe yazo gabana ya tsaya, baya naja kaɗan ina ɓata fuska. Yace, “ALLAH bazaki tafiba sai kin kulani”. Na dafe kaina ina lumshe idanuna irin na ka kaini bango ɗin nan……
     “Please babie kice wani abu mana”.
Nabuɗe baki zanyi magana kawai naji baƙon ƙamshin turare a wajen tare da motsi, waigawa nai saboda yanda, nakejin bugun zuciyata na sauya salo. Wanda nai tunanin kuwa shine na gani. ‘Boss!’ na ambata a cikin zuciyata, duk da ya rufe fuskarsa sosai da facing cap baƙa datai masa masifar ƙyau hakan bazaisa naƙi ganesa ba, ƙamshinsa ma kawai amsatace dan bana manta ƙamshin turarensa sam, dana jisa nake shaida yazo waje. sake ja baya daga gaban gayen da shima shi yake kallo nayi.
          Jawaad kam yayi tamkarma bai gansu ba, sai ƙoƙarin buɗe gwangwanin Malt.. Ɗin da aka kawoma Bily kawai yake hankalinsa kwance, sai dai fuskarsa a matuƙar ɗaure take babu alamun sassauci, ya zaro wayarsa da ga aljihu tare da gyara zamansa, ya kwantar da bayansa jikin kujerar sosai ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai kace wani saraki, yana sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa masifar ƙyau da fidda cikar haibarsa, sai hula hana salla inji hausawa😂, a samanta an rubuta favourite da ruwan gwal mai ƙyalƙyali, idanunsa toshe da baƙin glasess, hakan yasa babu mai fahimtar ina idanunsa suke kallo kai tsaye. A zuciyata nace, ‘glass nama Boss ƙyau matuƙa idan ya saka, bansaniba koni kaɗai ke iya ganin hakan banda sauran mutane, amm…..
         “Babie!” saurayin ya ambata da ɗan ƙarfi ganin hankalin Bily baya tare da shi. Kallona na maido kansa, nace, “Ba sunana Babie ba” yay murmushi mai ƙayatarwa, “To a faɗamin sunan mana uhum”. “Bana doguwar magana da wanda bai iya sallama ba”. kansa ya dafe alamar ya fahimci kuskurensa, yace, “Sorry Assalamu alaiki”. “Wa’alaikassalam”. Na amsa masa.
       Murmushi ya sake yi, yace, “Na gode da kika tunatar dani abinda na manta, hakan na sake tabbatarmin na samu abokiyar rayuwa ta gari, irin wadda ta cancanci zama uwar ƴaƴana. Sunana Kamaludden shehu Manya, matar tawa fa?”. ni dariyama yaso bani wlhy, wai matarsa, daga ganin sarkin fawa sai miya tai daɗi. kaina na girgiza masa kawai na juya zan bar wajen, amma sai yay azamar sake shan gabana, “Haba babie, naga na gyara kuskuren da yasa aka ƙi kulani tun a farko ai, koda bazaki kulani a nanba ki bani Number mana. Sonake ya barni, shiyyasa na miƙa masa hannu alamar ya bani wayarsa na saka masa. Cike da ɗoki ya ciro wayarsa a aljihu ya miƙomin, sai dai kafin na kai hannu na amsa wani hannun ya amshe wayar…………..✍
17
ALLAH ka gafartama iyayrnmu😭🙏🏻
  
   12Page 15
     To yau page ɗin ƙwai cikin ƙaya na ƙuɗine, duk wanda ya karanta ina roƙonsa dan girman ALLAH ya biya da addu’ar ALLAH ya kawo mana iyakar tashin hankalin dake damun wasu yankuna namu na arewaci, dan ALLAH ina roƙon har ƴaƴanmu ku saka suyi wannan addu’ar a dukkanin sallolinsu biyar na wannan yinin, domin addu’ar yara abuce mai muhimmanci a garemu mubar sakaci da ita, idan baki aureba ki roƙa mana jama’ar gidanku suyi da kanninki, duk da munsan anayi dama, sai dai ina fatan wannan ta zama ta musamman domin ALLAH, dan ALLAH kar’a manta, kar’a manta, kar’a manta.36
      Ya rabbi ka kawo mana ƙarshen waɗanan tashin hankali, ya ALLAH ka ruɓanya rahamarka da rangwame a garemu, ya Rabbi ka yafe mana kurakuranmu, ya Rabbi kaimana maganin abinda bazamu iyaba harma da wanda zamu iya ɗin, ya rabbi ka taimaki bayinka dake cikin gararin rayuwa da hali na buƙatar agaji, ya rabbi ka kawoma muhallansu zaman lafiya, kasaka kwanciyar hankali a zukatansu suma su sami cigaba da rayuwa a yankunansu kamar kowa, ya rabbi ka kawoma ƙasarmu zaman lafiya baki ɗaya da dukkanin duniyar musulunci, ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa kasa ta zama rahama a garemu duniya da lahira🙏🏻😭.31
Idan kasan bazaka biyaba karka karanta, bayin ALLAH na buƙatar tallafin addu’oinmu, dan girman ALLAH karmu wofantar da lamarinsu saboda mu muna barci a gidajenmu da iyalanmu bayan munci mun ƙoshi, ba’a zahiri kawai nakeson ayiba har abaɗi ma ita mukafi buƙata😭.
Masu 6am sunyi winning, wannan shine zaizama lokacin posting ɗinmu kafin na daina fushi da kamfanin masu yellow’n tambari 🙄🙄🙄.
…………….Daga ni har shi kallonsa mukai. Nidai na sauke idanuna da hannuna a hankali ina haɗiyar yawu da ƙyar. Kamal yace, “Haba malam ya haka?” Jawaad bai tanka masaba, sai wayar daya daddana alamar wani abun yayi a ciki ya miƙa masa. A ƙufule Kamal ya amsa yana faɗin, “Wanan rainin wayone ai, ya zakazo ka shiga abinda bai shafeka ba?”.
    Ban jira amsar da boss zai bashiba nabar wajen nidai, saboda wata muguwar harara daya makamin dan ya cire madubin idonsa. 
     Jawaad ya maida kallonsa ga kamal yace, “Karka damu ka kira Number dana saka maka zaka sameta”. Kamal yay ɗan shiru alamar nazari, sai kuma yay saurin taɓa hannun Jawaad dake shirin barin wajen, Jay ya juyo yana kallonsa, sai dai baice komaiba. “Sorry, dan ALLAH ko ƙanwarka ce dai?” wani munafukin murmushi Jawaad yayi tare da ɗagema kamal gira ɗaya sannan ya wani juya kansa da lumshe ido yabar wajen. Sam Kamal bai fahimci komai daga yaren na Jawaad ba, sai dai kuma ya haƙura akan zai nema waje ya zauna harsu tashi tafiya ya bisu a baya, dan shifa yaga matar aure.2
           Tsaye yazo ya sameni ina waya da Zuhrah, baiko kalleni ba yaja kujerar da ya fara zama ɗazun ya sake zaunawa yana maida glasess ɗinsa a ido kamar ma ya manta dani, nima ɗin dai ƙasa-ƙasa nake satar kallonsa yanda nasan bazai fahimtaba ina wayata, a ƙasan raina inata tunanin komi ya cema Kamal? Number wa kuma ya saka masa a waya? Dan nidai nasan baisan tawaba. Zuwan ɗaya daga ma’aikatan wajen ne ya sakani janye idona a kansa, umarnin kwashe kayan wajen ya basa tare da sake kawo wasu, dai-dai lokacin da muka ƙarisa wayar,  sai da yabar wajen ne cikin dauriya nace masa, “Ina kwana sir”.
     Shiru bai tanka minba, saima ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ɗauke kansa, duk a tsorace nake, gani nake zaimin faɗa akan ganina da Kamal, amma har aka sake kawo abinda ya saka ɗin baice dani komaiba.
      Ni kuma har lokacin ina tsaye duk da ƙafafuna sun gaji haka na fuske abina, shiko ya buɗe sabon Popcorn ɗin da aka kawo ya hau ci yanayi yana danna waya, baifi ɗiba uku ba wata mata mai sanye da hijjab har ƙasa da niƙaf ta iso wajen, sallama tai mana, na amsa mata, shiko bangama ya motsaba har sai da taja kujerar gefensa ta zauna, sai da ta ɗage niƙaf ɗin tana gaishesa sannan na fahimci wadda muke jirace.
       Batare da ya amsa mata gaisuwarta ba yace, “Kinsan irin ɓata mana lokacin da kikai?” haƙuri ta bashi. Kallona yay ya ɗauke kansa batare da yace komaiba, hakan ya sakani gyara kujera nima na zauna.
STORY CONTINUES BELOW
          Munja tsahon lokaci tare da ita yana mata tambayoyi kala-kala, wasu ni kaina idan yayi hanjin cikina saisun kaɗa balle ita da akemawa, gaba ɗaya duk ya gama rikitata da gizagonsa, sai dai ina jinjina masa akan yanda ya samu ƙwarewa akan kutse cikin al’amuran mutum yay bincike, har kai da yakemawa ɗin ka kasa saita kanka wajen bashi amsa ta gaskiya, dan lokacin da yarinyar ta iso a take-takenta na farko banga alamun zata bada haɗin kai ba, amma yanda ya fara bi da ita sai naga tuni ta zurma tana faɗin harma wanda bai tambaya ba ɗin. Ina kuma ƙara samun ilimi na aiki nima a wajensa sosai. Lokacin da muka kammala anata kiran sallar zuhur, dan haka mukayi a cikin wajen har shima da wasu mutanen, dan akwai masallaci ƙarami da sukayi, hakan yasa wajen ya sake burgeni da ƙaramin nutsuwa. Koda muka idar tafiya tayi, nima na samu waje na zauna ina jiran ya fito nai masa sallama na wuce.
      Kiran da ya shigomin a waya na ɗaga, Ummie ce, bayan mun gaisa take tambayata ina inane? Dan taje gidanmu akace na fita. Amsa na bata da cewar naje wani wajene, yanzu kuma zanje na wanke kai na wuce gidan inna Zainabu, daga haka mukai sallama akan zata sameni a wajen saloon ɗin ko gidan inna zainabu, na amsa da to na ajiye wayar. Ina ɗagowa muka haɗa ido da boss dake magana da wani da nake ƙyautata zaton sunsan junane. Janye idona nai kamar yanda shima ya ɗauke nasa, basu wani jimaba wancan yay ciki shi kuma ya nufi hanyar fita. Bin bayansa nayi ina ƙunƙuni, danni ɓatamin lokaci aketa famanyi.
           Kusan a tare muka ƙarisa jikin motar da nake ƙyautata zaton da ita yazo, nayi zaton gimba ne ya kawosa, amma sai naga saɓanin hakan, dan mazaunin driver ya buɗe ya shiga, ta gefen nasa naje na tsaya, nace masa zan wuce gida nima.
        Kallona yay ya ɗauke idonsa, sai da yay ma motar key, batare da ya kalleni ba yace, “Kina ɓatan lokaci fa, ko jira kike na ɗaukeki na sakaki ne?”.
        ‘Innalillahi…’ kuji sabon sharri, na faɗa a raina ina kumbura fuska, danni dama abinda nake gudu kenan yace mu tafi tare, to amma yaya zanyi, babu fuskar wargi a garesa, dan haka na zagaya na buɗe gefen mai zaman banza na zauna.
      Baice komaiba yay reverse tare da harba motar saman titi da ɗanbanzan gudu. Idanu na lumshe ina faɗin ‘Ga wanda yafi Yah Qaseem shegen gudu da mota’. Babu mai magana a cikinmu, sai shi da ke murza sitiyarin a hankali tamkar bayaso. Bai tambayeni ina zaniba, nikuma ban sanar masaba inajin shakkar magana dan sai wani shan ƙamshi yakeyi fuskarsa a ɗaure sosai.
     Tafiyar da bata wuce mintuna goma sha biyu ba muka iso wani waje, da mamaki na kalli abinda aka rubuta (LADIES MIRROR) sannan na kallesa shima, ta yaya akai yasan saloon zanzo to?, cikin ƙarfin hali nace, “Nifa ba nan nake zuwa ba”.
       ATM ya miƙomin batare daya kula maganata ba, nai ƙasa da kaina ina sake faɗin, “Ai ambani kuɗin a gida”. Bai tanka minba nanma, sai ajiyemin atm ɗin da yay a kan cinya tare da ƙaramar takarda. Tamkar zan fasa kuka haka naji, na buɗe motar na fice ina sake juya al’amarin mutumin nan a raina, aunty Shahudah tasha wahala yasin, ni saima ta bani tausayi, ƙilama wannan halin nasane ya sakata gudowa gida ‘Mtsoww’. Da wannan tunanin na ƙarasa cikin wajen da ya gama haɗuwa, dan yafi inda nake zuwa nesa ba kusaba. gashi ƙaton gaske. Yanda ma’aikatan wajen suka tarbeni sai abin yaban mamaki, abin akwai birgewa. Sai da na zaunane bayan na sanar musu abinda nake buƙata sannan na sami duba takardar daya haɗomin da ita, sai naga ashe password ɗin Atm ɗin nasane  ya rubuta min, samun kaina nayi dayin murmushi.
       An wanke min kaina tsaf da tafin ƙafa, aka gyaramin ƙumba, wadda ta wanke min kance ta bani shawarar nayi kitso, a cewarta su inhar zasu maka aiki suna duba yanayin gashinka su ɗoraka a ƙyaƙyƙyawan tsarin da bazai karye ba, kuma zai dinga tsaho, daɗin hakan da mutane ke shigane ke sakasu sake dawowa daga nan saisu zama basu da wajen zuwa sai nan. Murmushi na mata, ina cewa “Kodai za’amin daɗin bakin ƴan kasuwa ne?”. Kanta ta girgiza tana murmushi, “Sam ba haka bane auntyna, duk abinda zakiji daga bakina shine gaskiya, Gimbiya tana ajiye ingantattun kayan aiki da nagarta a wajen nan, waɗanda daga kowacce duniya kake zaka yaba”. Kasancewar nasan boss ba jirana zai tsaya yiba sai nace, “Okey babu damuwa amin kaɗan to”.
       Wani sashen daban da inda akai min wankin kai aka kaini, mutum uku kawai akema kitso, muka gaisa sannan na zauna nima, wadda zataimin ce ta iso kusa dani, muna cikinyi idanuna suka sauka akan ƙaton hoton dake sama a wajen, wanda naga wanima a can inda na baro, sai dai nesa da yay danine yasa banga waɗanda ke a jikiba, anan kam ras nake kallonsu kamar nayi magana su amsa, ƙyaƙyƙyawar mace hamshaƙiya ta gaske ce, tasha alƙyabba mai azabar ƙyau dake nuna jinin sarautace ita, gefenta ma ƙyaƙyƙyawan namijine mai tarin kamala da cikar haiba, kai tsaye na ganesa shi, dan kuwa dai sarkinmu ne Muhammad Sameer Saifudden, a raina nace ‘to ko matarsa ce wannan ɗin?’……. Maganar wadda kemin kitso ta katse min tunani da faɗin, “Duk wanda ya zauna nan baya gajiya da kallon hoton nan na sarauniya MUNAYA uwargida ga adalin sarkinmu, ita kanta wani lokacin har kishin hakan takeyi idan ta shigo takan juya hoton ya ɗau tsahon lokaci a kife”. Duk yanda naso shareta saina kasa, nai guntun murmushi, nace, “To miyasa zata barshi tunda ba dokar ƙasace ta tilasta a ajiyeba?”. kafin ta samu damar bani amsa, ƙyawawan ƴammata uku da yara biyu suka shigo wajen, biyu masu tsananin kama da Sarki Sameer, sauran kuma naɗan yanayi dasu sai dai basa tsananin kama, ukun zamu iya sa’anni dasu, biyun kuwa bazasu wuce shekara goma sha uku ba. Cike da girmamawa naga ma’aikatan na gaishesu, sai dai yanda suke amsawa babu wulaƙanci sai suka birgeni, gashi sai murmushi suke mana, nima sai na maida musu murmushin kamar yanda sukeyi, cikin manyan ɗaya ta miƙomin hannu mukai musabaha tana faɗin, “Kitsonki yayi ƙyau”. “Nagode” nace mata a taƙaice. Sauranma duk muka gaisa, suka kuma gaisa da sauran da muke zaune.
      Ɗaya a Ƙaramar tace, “Aunty Amaturrahman nidai irin kitson auntyn nan nakeso” tai maganar tana nunani. Wadda aka kira da Amaturrahman ɗin ta amsa mata da cewar, “Okey Safah sai a miki ai, burina dai ayi kitson kamar yanda Ummu tace”. Ɗayar tai ƴar dariya idonta akan waya, tace, “Mudai dan ALLAH karki cikamana kunnuwa da ihunkin nan Safah, Marwah dai nasan bamai jinta, inba hakaba ALLAH muka koma saina bama kowa labari a masarauta har Momma”. Ɓata fuska yarinyar tayi, tace, “Ai bazanyiba, salon kisa su Jalaludden Su ringa rainani ko Aunty Meenal? Ni wlhy wajen Uncle Sauban zan koma india can babu ruwan mutum da wani kitso ko nabi Aunty Amatullah Niger”. Dariya sukai mata, banda wadda suka kira Marwah shugabar miskilanci da jin kai, daka ganta kaga Sarki Sameer Saifudden sak kamar yay kaki ya ajiye, ni dai ina saurarensu ne sama-sama. Bayan an gama minne na miƙe nai musu sallama na fita, ashe wajen ɗaukko Atm ɗin boss dana saka a jakka gudun basai naje wajen biya naita dube-dube ba na yarda ɗan abinda ID cards ɗina suke ciki da wasu passport ɗina dake a tare.
             Ina cikin biyan kuɗin wayata tai ring, na kalla kamar bazan ɗagaba saboda sabuwar Number ce sai kuma na ɗauka na saka a kunne batare da nayi magana ba, daga canma shiru akayi, hakanne ya sani cewa, “Asslamu alaikum wanene?”. “Kin gama?” muryar wanda banyi zato ko tsammaniba ta daki kunnena a bazata. Da sauri na cire wayar a kunnena na sake kallon Number, gabana sai faɗuwa yakeyi, dan nasan nidai baida Number ta, jin an yanke wayar na amshi atm ɗin da ake miƙomin na fice da sauri domin tabbatarwa.
         Jinai wani abu ya tsirgamin daga saman kai har yatsan ƙafa saboda ganin motarsa fake a inda ya tsaya ɗazun, a fili nace, “Mikenan? Zaunawa yay jirana?’. Azababben horn ɗin daya danna ne ya sani nufar motar tamkar mai tsoron hakan. Nasan duk abinda zan zaunayi bayan shiga motar laifi zai zama kuma, hakan yasa na buɗe na shiga. Baiko kalleniba ya tada motar muka fice. Sai da muka ɗauki hanya nai dauriyar cewa, “Dan ALLAH kayi haƙuri sir, wlhy nazata tafiya kayi ne, shiyyasa da suka ce na zauna sumin kitso na yarda”. harara ya ballamin ya ɗauke kansa ya maida ga titi. Ban sake cewa komaiba, nacigaba da kallon titi, kamar yanda shima yake gudu kamar shi kaɗaine a titin. Wayarsa ce ta shiga ruri, batare da ya kalli waye ba ya ɗaga da hannunsa na haggu yasa a Hans free, daga can akai sallama, ya amsa cikin ladabi tamkar bashiba, “Ya mukai da kai ranar juma’a akan zuwa meeting ɗin nan Jawaad?”.  yay saurin dafe kansa da faɗin, “Oh ALLAH, kayi haƙuri Uncle, naɗan fita wani wajene amma insha ALLAH gani nan zuwa”. “To ALLAH yasa” daga can aka faɗa ana yanke wayar. Huci ya furzar yana ɗan bugar sitiyarin, Na ɗan saci kallonsa na ɗauke kaina, sai kawai naga ya canja hanya saɓanin inda muke. Nidai ban iya cewa komaiba, domin ko wainar dake cikin tanda a yau ta fini samun freedom ɗin kanta. Sai da naga ya shigo layin gidansune na iya kallonsa tamkar zanyi kuka. “Sir wlhy nifa akwai inda zanje”. bai kulaniba, yay fakin a waje batare da mun shiga cikin gidanba, sai da ya kashe motar sannan ya juyo ya kalleni.
         A bazata kawai naji yace, “Inga kitson”. “Uhyim!” na faɗa ina ɗago kai da sauri da waro masa idanu cikin tsagwaron firgicin jin abinda yace. Banga alamun shi ya fuskanci abinda yay ɗin kamar yanada ban al’ajabiba, dan ya wani sake haɗe fuska fiye da da.
        “Karki cinyeni da idanunkin nan malama, ɗaukesu a kaina, zan ganine idan sun iya sai nake kai matata can”.
      Fuska na kumbura cikin suɓutar baki nace, “Aunty Shahudahr da batason kitso ɗince zataje?”. Saukar yatsun hannunsa kawai naji kan laɓɓana ya ɗallamin da ƙarfi, azabar zafin danajine ya sakani saurin dafe bakin idanuna na cika da ƙwalla na kalleshi, ya dallamin uwar harar tamkar zai haɗiyeni da idanun, saurin maida kaina nayi gefe hawayen da suka cikan ido suka sami damar silalomin, dan da gaske naji zafi. kafin nagama fita daga zafinne, naji hannunsa saman kaina ya zame gyalen dana yana da hular, ya saukesu saman kafaɗata, yana faɗin, “Magulmaciya waye ya tambayeki to?”.  Maybe idan nace muku kaɗan ya rage zuciyata ta fito ta baki a wannan lokacin bazaku yardaba, jikina kansa tsuma yake, lokaci ɗaya dukkan ilahirin gashin jikina ya miƙe domin jin ya ja jelar gashina dake ɗaure da ribbon yana faɗin “Ashe ba ƙwaiƙwaido bace?” yay maganar a can ƙasan maƙoshi yana ɗauka hular yana ƙoƙarin maidamin a kai, na rintse idanuna ina fisgar numfashi da ƙyar tamkar mai Asthma, ya ɗauka gyalenma ya naɗamin kamar yanda ya gansa sannan ya kalleni fuska a matuƙar ɗaure, yace, “Kalleni nan”. Daƙyar na iya juriyar ɗagowa na zuba idanuna cikin nashi, yanda ya kafeni da idanu sai na kasa jurewa nai ƙasa da kaina saboda wasu abubuwa danaga suna fitowa a idanunsa waɗanda ban taɓa ganiba, ga idon ya kaɗa da jaa kaɗan tamkar wanda yake cikin fushi. Cikin ɗacin murya da saukemin wata harara mai firgitarwa da ban mamaki yace, “Hankalinki ya kwanta waɗanda kika fitama tallan jikin sun gani harsun tanka, Saina sauyama wannan fuskar taki kamanni idan na sake ganin kin fita ba hijjab”. Yana gama faɗa ya buɗe motar ya fice abinsa batare da ya sake kallona ba.
        Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, shiko ko waiwayena baiyiba har ya isa jikin ƙaton gate ɗin ya tura ƙaramar ƙofar ya shiga. Baya nai luuu na faɗa jikin kujerar na jingina bayana, ina sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu, nace, ‘Na shiga uku ni balkisu’. naja kusan mintuna uku a haka kafin na samu numfashina ya dai-daita. Gaba ɗaya man kaina ya gama tsiyayewa, nama rasa yanda zan fassara abun nasa, nakai hannu na shafa laɓɓana da har yanzu sukemin zafi, sai kuma na buɗe ido na kalli mirror, har laɓɓana sunyi ja, a fili nace, ‘Mugu, aiko Yah Qassem dake dani bai kafan wannan dokarba saishi daga mijin Auntyna’. Sai kuma nai saurin dafe bakin na kalli inda ya tashi sai kace ancemin gashi ya dawo. Da sauri na sake rintse idanu da dafe kai, a fili na sake faɗin, ‘Ya rabbi ka kawomin ɗauki, Mutumin nan zai kasheni’. Sai kuma na harari ƙofar gate ɗin na buɗe motar da sauri na fice abina,
   
★★18
     Jawaad kam Haka kawai ya tsinci kansa dayin murmushi lokacin daya buɗe gate ɗin ya shiga gida, sai kuma ya taɓe baki tare da jan ƙaramin tsaki ya nufi sashen mama Atika yana ƙwafa mai nuna takaicin wani abu da har yanzu yake cimasa rai. yasan dai taron meeting ɗin bai wuce can ɓangaren mama Atika ba saboda shegen fitinar tsohuwar. Da sallama ya shiga, suka amsa kusan su duka alamar shi ake jira, wani iri yaji a ransa saboda ganin harda kakansa dasu Umma, yadai samu waje ya zauna sannan ya gaidasu.
     2
★★★★★★★
            A LADIES MIRROR kuwa lokacin da abinda ID cards ɗin Bily suke ciki ya faɗi akan idon Safah ne, amma sai taƙi magana, sai da ta tabbatar bily ta daɗe da barin wajen sannan ta ɗauka tana faɗin, “Lah Aunty Meenal diba kiga auntyn nan da nace amin irin kitsontace ta yarda”. Duk kallonta sukayi, Amaturrahman ta dalla mata harara da faɗin, “Shine dan iskanci bakiyi maganaba sai yanzun?”. Baki ta tura gaba tana langaɓe kai gefe, “To ai mantawa nayi ko”. Amatullah tai dariya da cewa, “Kai Safah lamarinki sai ke wlhy, saiki bada a ajiye mata dan nasan zata dawo nema”. Da sauri tace, “A’a aunty Ama mu kai mata dai”. Marwah da tun ɗazun bata kula kowaba tanata game a ipad ɗinta ta harari Safah. Ramawa Safah tai, cikin tsiwarta data gada wajen Munaya tace, “Miye kike wani hararana ke kuma malama?”. Lips Marwah ta cije like Sarki Sameer, ta ɗauke kanta batare data tanka mataba.
       Duk yanda sukaso Safah ta bada a ajiyema bily saboda idan ta dawo nema ma’aikatan wajen su bata fir taƙi, daga ƙarshe Amaturrahman tayi kiran Ummu ta sanar mata, Sarauniya Munaya dake kishingiɗe a kilisarta ana tausa mata ƙafa ta girgiza kai kawai da lumshe ido, babu abinda Safah ta bari na halayyarta, ta tabbatar kuma akwai dalilin da yasata yin hakan, a hankali tace, “Kubarta tazo dashi, sai a nema yarinyar”. Amaturrahman tace, “Ummu yanzu nan biye mata zakiyi?” yanke wayar Munaya tayi batare da ta bama Amaturrahman amsaba. Dole badan sun soba akabi abinda Safah keso sukatafi dashi bayan an kammala musu kitso su duka kamar yanda Ummu ta korosu suyi badan sunso hakanba…………..✍8
Maison zuwa gagara badau ya shirya muje gaida Sarki Sameer Saifudden da gimbiya Munaya😉😉lol.15
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.22Page 16
……………Napep na samu na tare nai tafiyata gidan Inna zainabu. Can nai zamana mukasha hira da Lawusa da a yanzu muke ɗasawa har bayan sallar isha’i sannan na nufo gida.
★★★★★
           Bayan an buɗe taro da addu’a Uncle Nasir ya fara jawabi kamar haka. “Kamar yanda kowa ya sani mun fara tattaunawa akan maganar zaman Jawaad babu aure a kwanakin baya, har takai mukai masa tayin cikin yaran gidannan ko akwai wadda ya keso, sai dai ya nuna a lokacin zaiyi tunani, tun daga wancan lokacin ban sakeji daga gareshiba, to magana ta gaskiya mun gaji da ganinsa yana yawo a gari haka ana zaginmu, shi kansa bama girmansa bane, ƙannen-ƙannen bayansa ma gasunan duk da iyalansu har da ƴaƴa, yakamata Jawaad kaima kanka faɗa, dan lokaci bawai zai zauna jiranka baneba, kai kaɗai Abdul-aziz ya haifa, zamuso ganin ƴaƴanka a duniya kamar yanda mukasan da yanada rai zai ɗokantu da haka shima. A wannan karon ba shawara muke bakaba, umarnine, shiyyasama mukazo da Alhaji Baba domin ya zama shaida, tare da iyayenka, dolene a wannan karon kayi aure, ka zaɓi mace ɗaya a cikin ƴaƴan gidannan koma fiye da ɗayar mukuma zamu aura maka”.
     Jawaad da kansa ke ƙasa yay guntun murmushi domin son ɓoye ɓacin ransa, batare da ya ɗagoba yace, “Uncle ku gafarceni, bazan jaku da nisaba, duk cikin yaran gidannan bazan iya auren kowaba, dan kallon ƙannena nake musu tamkar ciki ɗaya…” da sauri Uncle Uwaisu yace, “Ai tamkar kace, bawai hakan bane, tunda babu ta inda ALLAH ya haramta maka, Jawaad bamason shirme, garama ka zaɓa komu mu zaɓa maka, kokuma ka ɗauki zaɓi na biyu, wato ka maida matarka ɗakinta kuje kuyi haƙuru da juna tunda yarinyarnan ta horu kuma tana sonka”. Yanzu kam kasa daurewa yay saida ya ɗago kansa ya kalli Uncle Uwaisu, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru saboda gargaɗi da Alhaji Baba yay masa da ido, kansa ya maida ƙasa yana sauke ajiyar zuciya.
      Uncle Sulaiman yace, “Son!” ɗago kai Jawaad yay ya kalli Uncle ɗin nasa da yake matuƙar so saboda ƙyawun halinsa, yace, “Na’am Uncle”. “Ko Kanada wadda kake sone?”. Ƙasa Jay ya maida kansa yana motsa laɓɓansa, sai dai babu maijin mi yake cewa, Uncle Taheer ya katsesa da faɗin, “Kai muke saurare Jawaad”. Batare daya ɗagoba ya girgiza musu kai alamar a’a. Shiru falon ya ɗauka kowa ya zuba masa idonu, shi kuma yaƙi kallonsu. Mama Zuhurah da bata da yawan magana tace, “To Jawaad ya kakeso ayi kenan? Yanzu kai kafijin daɗin kullum aita zaman meeting akanka akan maganar kaƙi aure, ka rufa mana asiri ka fidda kanka damu iyayenka daga zargi da zunɗen al’umma kaji, ƴar uwarka na sonka, tayi nadamar kuskuren datai a baya, kayi haƙuri a maida aurenku kaji”.
          Ɗagowa yay zaiyi magana fitowar Shahudah ta katse masa hanzari, gabansa taje ta durƙusa tamkar yanda Mama Atika da Mom suka kitsa mata, ta fashe da kuka tare da kama ƙafafunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta da harshen turancin da tafi ƙwarewa ya cinye tace, “Bb dan ALLAH ka gafarceni, wlhy nayi nadamar abinda na aikata, nakumayi alƙawrin bazan sakeba, na yarda zan haihu maka yara komai yawan da kake buƙata yanzun, idan ka barni mutuwa zanyi wlhy, dan ALLAH ka ceci rayuwata Bb…” hannunta ya ture daga saman ƙafarsa yana hararta, “Kima daina ɓata lokacinki, indai haihuwace bana buƙata daga gareki Hudah, karki damu kije kicigaba da cin moriyar ƙuruciyarki kinji, indai nine kima saka a ranki baki taɓa sanin mai kama daniba dan mun rabu kenan”. Fashewa tai da matsanancin kuka yanzunkam fiye da da, dan har ƙasan ranta kalamansa sun masifar sosa mata zuciya, ta dafe kanta dake juya mata, babu zato sai kawai ganinta ƙasa sukai ta yanke jiki ta faɗi. Gaba ɗaya ƴan falon da suka zuba musu ido suka miƙe, shi kansa Jawaad ɗin kallonta yake, dan ya zata salon iskancinta ne, sai daga baya da aketa jijjigata babu alamar rai tattare da itane ya fuskanci babu wasa a lamarinta, gaba ɗaya falon ya rikice, dan iya ƙoƙari anyi Shahudah taƙi farfaɗowa, Mom sai kuka take da sambatu.
       Dole aka kwashi Shahudah zuwa asibiti da gaggawa kuwa, dan wasunsu harsu fidda ran da gaske ta mutu.1
★★★★★★★
          Tun a gate baba maigadi yake sanarmin ai babu kowa a gidan duk suna asibiti aunty Shahudah babu lafiya, hankalina ya tashi sosai, dan haka nai azamar tsayar da mai napep ɗin dake shirin juyawa dan harma ya fara tafiya, shiga nayi na sanar masa asibitin da baba magadi ya sanarmin an kaita. Asibitine mai ƙyau dan na kuɗine, kasancewar bansan ina zan nufaba sai nai kiran aunty Aamilah, saidai bata amsa ba, na sake kira nanma babu amsa, maida kiran nai kan Yah Qaseem, sai da ta kusan tsinkewa sannan ya ɗaga, faɗa masa nai gani a asibitin a ina suke?. Muryarsa a sanyaye yace na jirasa yazo ya shiga dani.
        A yanda na gansa kawai na tabbatar akwai babbar damuwa dangane da aunty Shahudah, kasa daurewa nai na shiga jera masa tambayoyi. Amsa ɗaya na samu daga garesa, shine ta farfaɗo, sai dai sun mata allurar barci, sun kuma hana kowa ganinta sai banzan Jawaad ɗin da taketa sambatun kira. Ta bani tausayi matuƙa, dan na sake fahimtar tsananin son da takema Boss.
           Duk sai da na gaida waɗanda na tarar a wajen, sannan na tambayesu ya mai jiki, sai dai babu Boss babu dalilinsa a wajen, zama nai kamar yanda suke zaune jigum-jigum, kusan mintuna biyar sai naji ƙamshin turarensa. Ɗago kai nai dan tabbatarwa, karaf kuwa muka haɗa ido dashi, ya dalla mani harara sannan ya ɗauke kansa tamkar baiyiba.  Nima janye nawa nai, dan nasan laifina dai bai wuce tafiya bada izininsa ba. Cikin nutsatstsiyar muryarsa dake tattare da alamun gajiya naji yana faɗima Uncles nasa da matansu ya kamata su tafi gida su huta, tunda dai Doctor yace bazasu bari a gantaba har sai zuwa safiya.
          Cike da nazari nake satar kallon yanda wasu suke masa kallon harara dajin haushi a kaikaice, amma a zahiri suna amsashi cike da kulawa, sai al’amarin nasu yay masifar ɗaure min kaina, to amma abinda babu ruwanka ai daɗin kallo garesa, dan haka nai ƙasa da kaina kawai ina sauraren mahawarar da suke akan wanda zai zauna ya kwana, ance Mom taje gida Aamilah ta zauna, sai dai ita aunty Aamilah ta tubure akan tsoro takeji ta kwana asibiti, da sauri Salman yace, “Kedai wawuyace Aamilah, to sai wannan yarinyar tazauna ku kwana ai”. Yay maganar yana nunanu. Da sauri Yah Qaseem yace, “Itakuma aikin tafa? Itadai Aamilah da babu inda take zuwa itace ta cancanci kwana da itan”. Shiru kowa yay, sai kuma daga baya wasu sukai na’am da batun Yah Qaseem ɗin, na saci kallon Boss da uffan baiceba, yama ɗauke kansa daga garemu tamkar baisan mimukeyiba, nikam lamarinsa kan bani mamaki wani lokacin gaskiya.
           Wata mata da nake ƙyautata zaton cikin matan Uncles ɗin nasune ta kawo shawaran haɗa Aunty Aamilah da ɗaya daga cikin yaran gidansu ɗin da wata dattijuwar mai aiki, akan wannan shawarar aka zauna, dan haka duk sai muka fara shirin tafiya. Har mun fito baki ɗaya Mom tace gaskiya bazata iya tafiyaba, itama anan zata kwana, duk kallonta mukai da mamaki, sai kuma naga tsoro akan fuskokin wasu, dan koni naji wani iri saboda ganin Mom na sharar ƙwalla, nasan yanda ƴan gidanmu ke masifar son aunty Shahudah, hakan ya samo asaline saboda so mai tsanani da Dad ke nunamata kasancewar sunan Mahaifiyarsa taci, sai naji a raina kamar zamu iya rasa aunty Shahudah, duk yanda aka lallashi Mom taƙi aminta da hakan, sai kawai aka barta. jinai wani iri, dan tundafa Mom zata zauna nikaɗaice mace zan kwana a gidan, nima da sauri nace to zan zauna a asibitin, da sassafe sai naje gida.
      Harara Yah Qaseem ya dallamin da cewar bazan zaunaba gida zani. Niko na fara roƙonsa akan ya barni, shikuma yaƙi saurarena, kowa kuma yaƙi saka mana baki. Na kalli inda Boss yake tsaye a jikin mota hawaye na gangaromin akan fuska, sarai nasan duk yanajinmu, amma yayi kunnen uwar shegu da kowa, harna yanke ƙauna daga taimakon kowa na tsinkayi muryarsa yana faɗin,
           “Ita Aamilah ta fito ku wuce gidan tare mana, dan sunmayi yawa anan tunda Mom zata zauna, na tabbata sai ma’aikatan asibitin sunyi ƙorafi”.  Harararsa Yah Qaseem yayi, sai dai baiyi maganaba.
      Uncle Nasir ne yay na’am da shawarar Jawaad, dan haka ya aika aka kira Aamilah. Naji daɗin hakan da samun nutsuwa sosai. Daɗin da najine ya sakani matsawa inda yake nace, “Thanks you Sir”. Banza yaymin tamkar bai jiniba, sai daƙilar waya yake abinsa, na ɗaga ƙafafuna zanbar wajen naji yace, “Uhm”. Kallonsa kawai nai sau ɗaya nabar wajen zuwa motar Yah Qaseem daketa antayomin harara tamkar idanunsa zasu zubo ƙasa.
STORY CONTINUES BELOW
             Tunda muka tafi yah Qaseem keta zabga jarabar da babu wanda yasan kanta, daga ni har Aunty Aamilah da Yah Salman babu wanda ya kulashi, yana gama fakin kowa yay ficewarsa, dama nice farkon fitama nai cikin falo dan banaso ya tsaidani, nayi masifar gajiya wajen hutu kawai nake buƙata. Ina shiga ɗakina na murza key, na zaresu na ajiye saman mirror tare da jikkata dana cire a kafaɗa. Idanuna har lumshewa suke saboda gajiya, haka na daure nayo wanka da alwala na fito, daƙyar na iyayin shafa’i da wutiri na faɗa saman gado, sama-sama ma nai addu’a sai barci.
            
                     Cikin barci na ringajin saukar numfashin mutum a jikina, na buɗe idanu a razane ina ambaton ‘Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un’ tabbas a jikin mutum nake, na buɗe baki zan ƙwalla ƙara aka dafe bakin da hannu, cikin wata irin murya da bantaɓa jin mai itaba a gidan ake magana da shafamin jiki, “Bazan iya saduwa dake baƙya cikin hankalinkiba kamar sauran, shiyyasa na zaɓi baki damar farkawa, kiyi haƙuri ki bani haɗinkai cikin sauƙi bilkisu, samunkine kaɗai ya ragema cikar burina yanzun, karki lalatamin tanadina na tsahon shekaru, nai miki alƙawarin zan biki a sannu bazan cutar dakeba kodan son da nake miki, sannan zaki moru da tagomashi mai yawa a gareni saɓanin sauran da basu sami komaiba sai baƙin ciki, tun farko kece tsanin nasarata da na ɗauku dakon jira tsahon lokaci”.
            Tsabar tashin hankalin da nake ciki sai zufa nake kwararwa dukda ac dake aiki a ɗakin, jikina wata irin muguwar rawa yake da ɗaukar azababben zafi lokaci ɗaya, gashi ya rufemin baki, hawayenma sunƙi fita daga idona sai zuciyata ke kukan, duk addu’ar da tazomin bakina yi nake da taimakon UBANGIJI na.22
اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرورِهِمْ .
“Allahumma inna naj’aluka fee nuhoorihim wana’oothu bika min shuroorihim”.1
       Ya ALLAH! Mu mun sanya ka a gabansu, kuma muna neman tsarinka daga sharrace-sharracensu.
اَللَّهُمَّ أَنْتَ عَضُدِي، وَأَنْتَ نَصِيرِي، بِكَ أَجُولُ وَبِكَ أَصُولُ وَبِكَ أُقَاتِلُ.
“Allahumma anta ‘adudee, wa-anta naseeree, bika ajoolu wabika asoolu wabika oqatil”.
        Ya ALLAH kai ne mai karfafa ni, kuma kai ne mataimakina, da karfinka ne nake yin dabarun yaki, kuma da karfinka ne nake kai hari, kuma da karfinka ne nake yin yaki.
حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.
     “Hasbunal-lahu wani’mal-wakeel”.
ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro.
اَللَّهُمَّ رَبِّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ، وَرَبِّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَارًا مِنْ (فُلاَنٍ)، وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلاَئِقِكَ؛ أَنْ يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى، عَزَّ جَارُكَ، وَجَلَّ ثَنَاؤُكَ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ.
    “Allahumma rabba s-mawati s-sab’i wa rabba-l-‘arshi-l-‘azimi. Kun li jaran min  (fulanin) wa ahzabihi min khala’iqika, an yafruta ‘alayya ahadun minhum aw yatgha. ‘Azza jaruka, wa jalla thana’uka, wa la ilaha illa anta”.
       Ya Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al’arshi mai girma, ka kasance mai tsari gare ni daga wane dan wane, da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ketare haddi, kariyarka ta buwaya, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai kai.
اَللهُ أَكْبَرْ، اَللهُ أَعَزُّ مِنْ خَلْقِهِ جَمِيعاً ، اَللهُ أَعَزُّ مِمَّا أَخَافُ وَأَحْذَرُ، أَعُوذُ بِاللهِ الَّذِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ، الْمُمْسِكِ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ أَنْ يَقَعْنَ عَلَى اْلأَرْضِ إِلاَّ بِإِذْنِهِ، مِنْ شَرِّ عَبْدِكَ فُلاَنٌ، وَجُنُودِهِ وَأَتْبَاعِهِ وَأَشْيَاعِهِ، مِنَ الْجِنِّ وَاْلإِنْسِ، اَللَّهُمَّ كُنْ لِي جَاراً مِنْ شَرِّهِمْ، جَلَّ ثَنَاؤُكَ وَعَزَّ جَارُكَ، وَتَبَارَكَ اِسْمُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ ” ثَلاَثَ مَرَّاتٍ.
“ALLAHU akbaru. ALLAHU a’azzu min khalqihi jami’an. ALLAHU a’azzu mimma akhfu wa ahdharu. A’udhu billahi lazee la ilaha illa huwal mumsikis samawatis sab’i an yaqa’na ‘alal-ardi illa bi’izinihi, min sharri ‘abdika  (fulanin) wa junudihi wa atba’ihi wa ashya’ihi minal-jinni wal-insi. Allahumma kun li jaran min sharrihim Jalla thana’uka wa ‘azza jaruka, wa tabaraka smuka, wa la ilaha ghayruka”.
STORY CONTINUES BELOW
    ALLAH shi ne mafi girma, ALLAH shi ne mafi buwaya daga dukkanin halittarsa, shi ne mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin ALLAH, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, mai rike sammai daga su ruguzo a kan kasa sai da izininsa, daga sharrin bawanka  (ya ambai sunansa), Ya ALLAH! Ka zamo mai tsari gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma kaiyarka ta buwaya, kuma alherin sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba”.
            
        Duk da na rigada na sadaƙar tawa ta ƙare ban fasa karanto addu’oinba ina faɗama ALLAH kukana, koda a wani wajen bana haɗa kalmomin dai-dai saboda ruɗani karantowa nake, wata razananniyar ƙara mukaji a dukkanin illahirin gidan, hakan ya saka koma waye sakarmin baki ya miƙe a firgice kamar yanda nima na samu damar ƙwalla tawa ƙarar saboda firgita da nayi, ɗif naji kunnuwana sun daɗe banajin motsin komai, dukda ɗakin a duhu yake dunɗum, jinai an sake rungumeni an fashe da kuka, yanzunkam a tare muka ƙwala ihu da koma wanene duk da naji jikin ya banbanta dana wancan, ɗakin sai naga yana wani irin juyamin tamkar ina cikin hajijiya, rumtse idanuna nai da ƙarfi na sake ƙwalla ƙarar da ni kaina bansan iyakar ina muryata ta tsaya ba a gidan, daga nan ban sake sanin mi duniyar ke cikiba kuma.
           Duk wanda yake a cikin gidan kunnensa saida ya jiye masa ƙara maiban tashin hankali da tsoratarwa da aka ƙwala da farko a wannan dare, wadda taɗauki adadin mintuna biyar kafin ta gushe ihun bilkisu ya biyo bayanta, Aamilah da ɗakinta ke kusa dana Bilkisu ce ta fara fitowa a razane saboda kiɗimar data shiga na tsoro itama, cikin lalube ta afko ɗakin bilkisu batare data saniba itama tana ihun, fitar sautin ihun bilkisu ne ya bata damar isa inda take suka ƙanƙame juna suna kuka maiban tashin hankali. A daidai lokacin da Qaseem da Salman harma da kuku suka shigo sashen suma a razane, dan duk wanda yake gidan yaji ƙarar farko, sannan a yanzu yana jiyo ihun su Aamilah dake nuna alamar tsoratar da sukaice ta gusar musu da hankali suka tsinci kansu a yanayin. Kuku ne ya samu damar kunna fitilar ɗakin haske ya gauraye ko’ina, dukansu kansu Bilkisu sukayi, dan hakan yayi daidai da ɗaukewar numfashinta daga gangar jikinta.
            Babu mai iya musalta tashin hankalin da suke ciki a wannan dare, kan kowa ya kulle daga abinda ya faru, cikin ƙarfin hali Salman ya ɗakko ruwa ya miƙama Qaseem dake taya Aamilah jijjiga Bilkisu, bai tsaya yayyafa mataba ya bulbule matashi kawai a fuska, wani nannauyan numfashi Bily ta kawo, sai dai jikinta babu alamun ƙarfi, ta buɗe idanu a hankali ta kalli kowa sai kuma ta maida ta lumshesu hawayen da bata samu yiba ɗazun suna ziraro mata a kumatu masu ɗumi.
       Sama-sama nake iya jiyo muryar yah Qaseem daketa jeramin sannu shida Aamilah da Kuku, bandaiji muryar Salman ba sai daga baya, tsahon wasu mintuna muna a haka kafin barci yaɗan fara fisgata, addu’a nake buƙatar ko yaya wani ya dinga karantowa yana tofamin kozanji sauƙin abinda nakeji a jikina tamkar ana kunna garwashin wuta, sai dai nasan ba samu zanba, dan duk waɗanda suke a kaina babu mai irin wannan tunanin. nesa-nesa nake jiyo maganar Yah Qaseem dake cewa Aunty Aamilah mutashi muje mu kwanta, da taimakonta na koma saman gado, sai daifa tace itama anan zata kwana bazata koma ɗakintaba, sannan suma dan ALLAH su kwanta anan ɓangaren basai sun koma nasuba. Bansan amsar da suka bataba saboda idona ya rufe ruf da barci.4
★★★
           Kiran sallar farko na asubahi na farka, sai dai abin mamaki da al’ajabi na mance kaso mafi yawa na abinda ya faru jiya a gidan, na tashi zaune ina kallon Aunty Aamilah dake mamuƙe dani alamar a tsorace tai barci, ajiyar zuciya na sauke a hankali inason tuno koda wani abune kaɗan, sai dai sam ƙwaƙwalwata ta gaza aiki, tamkar ansa murfi an toshe bututun dake kai saƙo tsakanin ƙwaƙwalwa da zuciyata, addu’a na shiga karantowa kozan sami sassaucin da nakeji dangane da ƙuncin da zuciyata ta shiga da zafin da nakeji a cikinta.6
اَللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُوفَلا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْن، وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ.
“Allahumma rahmataka arjoo fala takilnee ila nafsee tarfata ‘ayn, wa-aslih lee sha’nee kullah, la ilaha illa ant”.
        Ya ALLAH! Rahamarka nake kauna, don haka kar ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne, kuma ka kyautata mini sha’ainina dukkansa; babu abin bautawa da gaskiya sai kai.
         Sai da aka fara kiran salla ta biyu sannan na samu ƙarfin sakkowa daga gadon, banda ƙuncin zuciya babu abinda nakeji a jikina, sai kaina dake ɗan ciwo kaɗan-kaɗan da marata, ban ɗauki hakan komaiba, dan nasan hakan alamun zuwan period ɗinane, da sam bana ciwon mara idan zanyi al’ada, amma a shekararnan gaba ɗaya haka nake fama dukda bawai yanamin tsanani baneba. Saida na duba na tabbatar babu alamar zuwansa ciwon mararne kawai sannan nai wanka dan na samu ƙwarin jikina, daga nan nayo alwala na fito. Nayi ƙoƙarin tada aunty Aamilah amma sam taƙi koda motsi, haka na haƙura na barta nai sallata ganin nima lokaci na neman ƙwace mani. Bayan nayi azkar karatun alkur’ani nayi har zuwa 7am sannan na tashi, shirin office nayi abina, harna kammala aunty Aamilah batako motsaba har lokacin, nakuma ƙoƙarin tadata salla amma taƙi tashi, ƙyaleta nayi na fita kicin danna samu koɗan tea na sha dukda banajin cin komai.
★★★★★★★
           Tunda suka shigo gidan daga asibiti daƙyar ya iya dauriyar yin wanka saboda barcin da yakeji, ya samu yay shafa’i da wutiri a daddafe ya haye gadonsa, ya fara addu’a, amma bashi da tabbacin ya kammalata barci yay awan gaba dashi. Can tsakkiyar dare ya farka a matuƙar razane saboda mummunan mafarkin da yayi.
         ‘Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un’. 
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ.
“A’oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa’iqabih, washarri ‘ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon”.
      Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin al’amurana).
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a’uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem’. ya faɗa sau uku, yay addu’a ya tofa gefen haggunsa da dama sau uku, sannan ya sauka a gadon, alwala yayo yazo yay salla raka’a biyu saboda idonsa cike yake da barci, yay addu’a sama-sama ya koma saman gadon ya kwanta, sai dai ya canja sashen da yay mafarkin dashi ɗazun. Babu jimawa barcin ya sake awan gaba dashi.
      Ana kiran sallar shiga massalaci ya farka, hakan ya sakashi ɗaura al’wala ya fita massalaci dan har an tada sallah. Koda aka idar bai wuce motsa jikiba yau sai ya shigo gida duk da yana buƙata saboda jikinsa yayi nauyi, gyara ɗakinsa yay ya shiga wanka, bayan ya fito yay shirin office. Ƙarfe bakwai da kwata Gimba ya ɗaukesa suka fice daga gidan…………..✍
37
Gaskiya an fara sakama boss ido a gidannan fa😑, yana koyama yarinya aiki anacewa yayi🤐🙄 nayi nan, karkuma ace na koma team Beejay ne🚴🏼.
7
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.19Page 17
…………….Bayan na kammala shan tea ɗin dana sakama suga kaɗan sai na fito daga kicin ɗin, a falo na iske Yah Qaseem zaune yana waya da Dad, da alama abinda ya faru a daren jiya yake bashi labari, sai dai yanda naji yana faɗama Dad ɗin shima wai ba komai zai iya tunawaba, shidai kawai an bamu tsoro jiya a gidan. Bansan mi Dad ya faɗa masaba, nadaiji ya amsa masa da cewar, “To Dad ALLAH ya kawoka lafiya, itama yanzu zamuje asibitin muji yaya jikin nata”. Yaɗanyi shiru yana sauraren mi Dad ɗin ke faɗa daga can, sai yace, ”Okey gata”. Wayan ya bani, muka gaisa da Dad, daga can yace, “Ɗiyata yaya jikin naki?”. Muryata a sanyaye da har yanzu nakejin jikina wani iri nace, “Alhmdllh Dad, banajin ciwon komai sai na kai, gashima nayi shirin Office ”. “To ALLAH ya kiyaye gaba ya ƙara sauƙi kinji, nima insha ALLAHU ina tafe, anjima kaɗan zan iso”. Nace, “To Dad ALLAH ya kawoka lafiya”. “Amin” ya faɗa mukai sallama, na miƙama Yah Qaseem wayarsa. Miƙewa yay yana faɗin, “Muje dan mu samu mubiya asibitin”. Kaina na jinjina masa, har mun fara tafiya nace, “Yah Qaseem bazakasha ko tea ba?”. Kansa ya girgizamin a sanyaye, haka kawai na samu kaina da tsura masa idanu, gani nai fuskarsa tai jazur kasancewarsa farin mutum, idanunsama haka, duk ya wani fita hayyacinsa, gashi tamkar a firgice yake. Cikin katseni yace, “Bilkisu lafiya?”. Firgigit na dawo hayyacina, saina girgiza masa kai kawai nai gaba ya biyoni a baya.
        Tunda muka fice daga gidan babu mai iya cema ɗan uwansa komai, yau ko redio bai kunnaba, sannan sam baya gudu kamar yanda ya saba, duk yanda naso tuno wani abu na daren jiya na kasa hakan a yanzunma, iyakar firgitar da mukai kadaice ban mantaba da abinda ya biyo bayanta, amma miye musabbabin hakan? Amsar itace ban saniba ba, tamkar anma ƙwaƙwalwarta formatting ɗin komai lokaci ɗaya, haƙura nai dason tunawar na cigaba da maimaita ‘Hasbinallahu wa ni’imal wakil’ a cikin zuciyata.43
            Motar Jawaad na fita daga asibitin bayan yasa gimba ya biyo sun duba Shahudah su Bilkisu na shigowa, shi Qaseem yaga fitarsu Jawaad, amma bily bata luraba dan hankalinta baya tare da duniyar mutane.
       Shiga suma sukai suka duba Shahudah, har yanzu barci take, sundai leƙata ta Window suka fito, gudun karsu makara yasa sukaima Mom sallama suka wuce office.
★★★★★★
            Koda muka iso yau ban samu damar yima Yah Qaseem rakkiyaba, shima bai nema hakanba, da kansa ya kwashi kayansa ya wuce office nima na wuce. Sama-sama nai gaisuwa da kowa na zauna a mazaunina, Ummie kanta yau takula bani da walwala, koda ta dameni da tambaya sai nace mata aunty Shahudah ce bata da lafiya tana asibiti. “ALLAH ya bata lafiya” kawai tace cikin rashin ɗaukar abun da muhimmanci.
       Ban iya cewa da ita komaiba na cigaba da aikin gabana, kusan sha ɗaya akai kiran wayar landline ɗin office ɗin namu, Ada dake kusa ta ɗaga, da hannu taimin nuni nazo. Na ajiye biron hannuna na nufeta, miƙamin kan wayar tayi tabar wajen, na saka a kunne nace, “Hello”. “Ki sameni a office” kawai akace aka yanke. kamar nayi kuka haka naji, da inada dama dana roƙesa ya ɗagan ƙafa zuwa ɗan anjima, dan marata a ƙulle take tamau ga wani azababben ciwon kai dake cina tamkar jijiyoyin kan zasu katse. Mazaunina na koma na ɗauki ATM ɗinsa dana manta jiya ban bashiba na saka a aljihu na fita, ina kallon su Ada na gulmata, na girgiza kai kawai na fice abina dan banida lokacinsu.
        Halin da nake ciki ya sake haddasama tafiyata sanyi, ga fuskata a cinkushe sosai, wadda harni kaina nasan bana cikin yanayin farin ciki gaba ɗaya yau, abinne ya haɗemin da yawa, zuwan period kan sakama mace ɓacin rai na babu gaira babu sabar, tausayin aunty Shahudah da ganinta yau ya sake ɗagan hankali, damuwar abinda ya faru a daren jiya dason tuna koda ƙanƙanin abune amma hakan ya gagara, ciwon kai ga mara dakan saka mutum takura yaji baya buƙatar yin koda magana ma.
        Nai knocking ƙofar a hankali tamkar banaso, shirun da naji ya sakani sake ƙwanƙwasawa, umarnin shigowar da aka bani daga cikine ya sakani tura ƙofar na shiga.
          Ƙamshin dana shaƙa a office ɗin ya sakani jin ɗan sanyi a raina, na ƙarasa inda yake ina mai satar kallonsa, sanye yake da suit yau, sun masa ƙyau sosai kamar koda yaushe, bai ɗagoba tunda na shigo, yanata rubuce-rubuce a takarda. nace, “Ina kwana sir” bai amsa minba, hakanne ya sakani kallonsa da haushi, sai da na kalli abinda ke a kunnensa na fahimci waya yakeyi, yaɗan ɗago ido ya kalleni yana faɗin, “Okey Sir” cikin jinjina kai. Da hannu yaymin nuni da kujera, kaina na gyaɗa masa kawai na zauna, cigaba da abinda yakeyi yayi. Bawani sauraren abinda yake nakeba balle na fahimta saboda halin da nake ciki, kusan mintuna bakwai kafin suyi sallama ya cigaba da rubuce-rubucensa baice dani uffanba.
        Cikin dauriya na kumace masa “Ina kwana”. “Lafiya” kawai yacemin yana cigaba da sabgarsa. Ɓoyayyen numfashi na sauke ina ƙoƙarin son daidaita gudun zuciyata, na ɗora masa ATM ɗinsa saman table ɗin nace, “Gashi nagode, ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”.
        Karon farko da tunda bilkisu ta shigo office ɗin Jawaad ya ɗago ya kalleta.
      Yanda ya zubamin idanun ne ya sakani saurin duƙar da kaina, baiyi maganaba ya maida kansa ga abinda yakeyi yana ɗan lumshe idanu. sai kuma ya ɗago kansa, takardun dake gefen hannun damarsa ya ɗakko, buɗesu ya shigayi na wasu mintuna sannan ya miƙomin yana kafeni da muggan idanunsa, “Ki fara tattare dukanin bayanan wannan case ɗin a file ɗinnan, komai dake aka farashi, ki nutsu kiyi abinda ya dace”. Kaina na jinjina masa, ya sake miƙomin hotuna guda biyu, batare da ya kalleni ba yace, “Ki sakasu a ciki” suma amsar nai na buɗe na saka a farkon takardun ina cije lip saboda wani mugun katsawa da marata tayi. Babu shiri na ajiyesu na kwantar da kaina jikin tebirin ina ambaton sunan ALLAH da ɗaura hannuna na haggu bisa cikina.
         Idanu Jawaad ya zuba mata na wasu sakanni, sai kuma ya ɗauke kansa, duk yanda yaso basarwar sai ya kasa, a hankali yace, “Miemaa” shiru Bilkisu bata amsaba, bakuma ta motsaba, ya zuba mata ido a karo na biyu, ganin taƙi ɗagowa sai ya miƙe ya zagaya inda take. Kujerar dake kallon wadda take zaune yaja baya kaɗan ya zauna, nanma idanunsa a kanta, dan yarasa kuma mizai mata, sunanta ya kuma kira yanzunma a hankali.
        Ƙwallan da suka cikamin ido na share sannan na ɗago kaina ina amsawa da “Na’am” Ganin idonsa a kaina suke ya sakani maida nawa na risinar ƙasa. yace,
      “Lafiya?”
Kaina na jinjina masa alamar eh babu komai, dan ko giyar wake nasha bazan iya cemasa marata ke ciwoba, fatana kawai ya sallameni na koma.
      Ƙaramin tsaki naji yayi, cikin ɗan kausasa murya yace, “K kalleni”. Ɗagowa nai na kallesa danjin babu wasa a furucinsa, yanda ya zuba idanunsa cikin nawa bazan iya jurewaba, naɗan risinar da nawa ina haɗiye busashshen yawun dana tattaro daga bakina da ƙyar.
      “Ni zakima ƙarya?”
Da sauri na girgiza kaina. Ya sake cewa ”Mi akai miki?”. Saboda ya barni nace, “Kaina ke ciwo”. Shiru yay baice komaiba, hakan yasa na ɗago kaina a tunanina bani yake kalloba. Sai dai anyi rashin sa’a idanunsa ƙyam suke a kaina. Ɗauke nawa nai ina kumbura fuska danni banason wannan kallon takuramin yakeyi.
      Huci naji yaɗan fitar kaɗan mai kama da ajiyar zuciya, yace, “Tashi kije ki kwanta”. Kallonsa nai da mamakin maganarsa, ni ina zani na kwanta to?. Doguwar kujerar dake rukunin kujerun office ɗin a gefe ya nunamin fuskarsa a matuƙar ɗaure babu wasa.. Gabana ya faɗi, na kallesa cikin waro idanu da rawar baki dan nakasa cewa komai. Harara ya zubamin, a ɗan tsawace yace, “Na fara wasa da kene?”. Saurin girgiza kaina nayi na miƙe.
         Kasancewar dama kwanciyar nake buƙata saina shiga sauke tagwayen ajiyar zuciya lokacin dana kwanta, na takure waje ɗaya saboda azabar da nakeji, bammasan hawaye nabin kumatunaba, kusan mintuna uku kafin ta lafamin, na buɗe idanuna a hankali na saukesu akan Boss dake zaune saman centre table ɗin rukunin kujerar ya zubamin idanu, saurin maidawa nai na rufe ina ƙoƙarin haɗiye kukana. Baice dani komaiba, amma inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina har yanzun. Yunƙurawa nai zan tashi yace, “Koma ki kwanta”. cikin marairaice fuska nace, “Ya daina ai, zan koma nacigaba da aikina”. Yanda yay kicin-kicin da fuska ya tilasta min komawa na kwanta yanda yake buƙata. “Mike miki ciwo?” ya jehomin tambayar a kausashe.  Bansan sanda na tura baki gaba ba nace, “Nifa kainane kawai sir”. Bai tanka minba yamiƙe yabar wajen, ban sake sanin mi yakeyiba saboda ciwon ya dawo. Saida ya lafamin ne na buɗe ido naga Ummie durƙushe a gabana tanamin sannu, hannunta na kama na riƙe ina hawaye, “Ummie ki taimakeni kiyi masa dabara mubar office ɗin nan dan ALLAH”. Kanta ta jinjinamin tana gogen hawayen, tace, “Mararki ke ciwo ne?” da sauri na ɗaga mata kaina ina cije baki. Nace, “Koda yaushe zai iya fitowa wlhy Ummie”. Cikin ƙara rage murya ƙasa Ummie tace karki damu bara nai masa magana”.
          Jawaad da duk ke saurarensu daga inda yake zaune ya girgiza kai kawai. Mutum ne shi da ALLAH yayma baiwar jii, dukda ahankali suke maganar yana jiyosu batare da sunyi tunanin hakanba. Koda Ummie ta miƙe zuwa inda yake domin ta tsarashi kamar yanda Bilyn ta buƙata sai yace ta tafi. Babu ƙofar yimasa musu, dan haka tabi umarni ta fice tana waigen bilyn. Waya ya ɗauka shikuma ya tura saƙo. Cigaba yay da aikinsa kamar ya manta da Bilkisu a office ɗin, lokaci-lokaci yakan amsa waya koshi ya kira. Kusan mintuna ashirin da tura saƙonsa aka kawo masa abinda ya buƙata, Gimba ne ya shigo ya ajiye ledan hannunsa bayan ya gaishesa.
         Sama-sama nake jin muryar gimba a office ɗin, kafin kuma naji alamar fitarsa. Ƙamshin turaren Boss da naji a akaina ya sakani buɗe idanu, yace, “Tashi zaune” babu musu na tashi, a raina ina murna zai barni na tafi, abinda ke cikin ledar ya fiddo sai naga magunguna ne, batare da ya kalleniba yace, “Kinci abinci?”. A hankali nace, “Nasha tea tun a gida”. Baice komaiba ya miƙe. Naɗan bisa da kallo sai kuma na janye idanuna ganin ba fita zaiyi daga office ɗinba, bansan mi yakeyiba saboda ya juyamin baya, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya juyo ɗauke da kofi, ya zauna a table ɗin tamkar ɗazun yana miƙomin tea ɗin daketa turiri, sai cake, yanda yay da fuskane ya tabbatarmin babu wasa, ya miƙe yana faɗin, “minti biyar na baki kuma”. Bance komaiba nidai sai fuska dana kumbura. Dayake yunwar nakeji kuma tea ɗin ya haɗashi dai-dai yanda zan iyasha gashi babu suga sai gashi na shanye naci cake ɗin, ina ajiye kofin yana dawowa wajen hannunsa ɗauke da ruwa, nidai kaina a ƙasa naƙi kallonsa, dan dauriya kawai nakeyi kar yaga na cika raki, sai haɗiye kukan dake tahomin nakeyi da sauri-sauri, da kansa ya ɓalla maganin ya miƙamin. Amsa nai babu musu na zuba a baki, ya miƙamin ruwan shima, na kammala sha ya amsa yana min nuni dana kwanta. Ban musaba dan babuma damar yin musun na koma na kwanta kamar ɗazun, shikuma ya miƙe zaibar wajen. Bansan lokacin da harshena ya suɓuce nace, “Sir dan ALLAH kai min addu’a a ruwa ka bani nasha, sannan ka tofamin, jinake jikina kamar ana kunna garwashin wuta”. Cak ya tsaya, sai kuma ya juyo a hankali tamkar mai ciwon wuya ya zuba min idanu. Lumshe nawa nai hawayen da nake maƙalewa suka silalo.
         Wani irin bugu ƙirjin Jawaad yake da sauri-sauri, ga wani irin sanyi na ratsashi daga saman kai har yatsan ƙafa tamkar wanda ake tsundumawa cikin ƙanƙara, mafarkinsane na daren jiya yake rige-rigen dawo masa a kwaƙwalwa. Bayan gushewar kuwwar halittu masu ban tsoro da ya samu damar yin addu’a ta koresu, sai furucin ƙarshe na cikin mafarkin daya fito daga bakin wata murya mai amo da baisan daga ina ta ɓulloba ita kuma, yay masa tsaye cak a zuciya yakuma kasa fashin baƙi a kai harya iso office ɗin nan, {Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini ta tabbata, rashin gaggawa zai tabbatar da zubewar jinane, hhhhhhhhh karku manta! Karku manta!! Karku manta!! Hhhhhhhhhhh!!!!}……… “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” ya shiga ambata lokacin da yaji gilmawar abu shuuu ta bayan kunnensa, da dawowar maganar tamkar a yanzu ake mai ambatonta ke faɗinta, hankalinsa ne ya dawo jikinsa. ya kalli inda bilkisu take kwance har barci ya fara fisgarta, samun kansa yay da tsira mata idanu a zahiri, a baɗini kuma taurarin cikin mafarkinsa ne daya koma barci bayan yayi addu’a da nafila ne suke masa kaikawo, yay ƙoƙarin tuno furicin mahaifinsa aka taurari huɗu da sukafi kowaɗanne haske acikin taurarin da ya gani, sai guda ɗaya shima mai tsananin haske amma ya matsa nesa dasu sosai, ya kasa tuna komai da Abba ya faɗa masa akan taurarin, kansa ya shiga yamutsawa cikin wani irin yanayi, a fili ya furta, “Jiya wace irin ranace?”. “Ranar da zata zama cikin ranakun tunawa daga nan har ƙarshen numfashi”. Bily da idanunta ke rufe har tana sauke numfashin tabbatuwar barci ta faɗa cikin motsa labɓanta da sauti mai sanyi, badan ALLAH ya yisa mai jii ba da bazai taɓa fahimta ba. Dukda yaji wani abu a ransa game da amsar tata sai ya tureshi da tunanin ai a fili yay magana shima, tajisane shiyyasa ta bashi wannan amsar, to amma abin tambaya anan miyasa ta bashi amsar a haka?. Ƙirjimsa yay wani irin motsawa, kiran sunata ya shigayi amma ko motsi bataiba alamar barcinta yayi ƙarfi. Ƙwaƙwalwarsa ma saita gaza tunanin komai, samun kansa yay da fara mata addu’ar data buƙata kawai ya shiga tofa mata akan fuska, gani yay ta saki wani lallausan murmushi tana motsa laɓɓanta, yay saurin kai kunnensa amma bayajin komai, ɗagowa yay ya kalleta sai kuma yaga ta yamutsa fusaka ta maida fuskarta ta haɗe. Yay shiru yana kallonta kafin ya miƙe yabar wajen.1
STORY CONTINUES BELOW
      Cikin ƙanƙanin lokaci barcin Bilkisu yay ƙarfi sosai saboda maganin na saka barci, gashi dama bawani isashen barci ta samu a daren jiyaba, Jawaad kam ya cigaba da ayyukansa har akai kiran sallar zuhur. Tashi yay ya shiga toilet yay alwala ya fito, idanunsa suka sauka akan bily dake takure cikin kujera alamar sanyi takeji. Takawa yay a hankali wajen zamansa, rigar suit ɗinsa dake jikin kujerar a rataye ya cire ya nufeta, lulluɓa mata yay dukda bata rufe har ƙafafuba, cikin barci ta sauke ajiyar zuciya jin ɗumi ya ratsata, ya ɗan lumshe ido ya buɗe yana girgiza kai, sai kuma ya kalli agogo ya nufi hanyar fita da hanzari ganin zai makara salla.
         Koda aka fito salla bai dawo office ɗinba ya amsa kiran da Sir Ahmad ke masa a office ɗinsa.
★★-:-:-:-★★★-:-:-:-:-:-★★★-:-:-:-★★
               Ƙarfe biyu da wasu mintuna Dad ya isa asibiti, daga airport bai zarce ko gidaba yasa driver ya wuto dashi dan ya matsu yaga jikin mamansa, zuwa lokacin Shahudah ta farfaɗo, sai dai daka ganta kasan tanajin jiki, tayi zuru-zuru, farar fatarta tai jajur musamman fuskarta ma, Dad ya zauna a bakin gadon kusa da ita yana mai shafa gashin kanta fuskarsa a ƙwaɓe tamkar zaiyi kuka dan tausayinta. “Sannu kinji mamana, ALLAH ya baki lafiya”. Hawayene suka ziraro a kumatun Shahudah, ta kama hannun Dad ta riƙe tana magana a hankali saboda nauyin da ƙirjinta yay mata, “Dad bazan samu lafiyaba, mutuwa zanyi, tunda Bb baya buƙatata gara na mutu, Dad cayayfa mun rabu kenan har abada, ya daina sona Dad, Dad mut……” saurin ɗora hannunsa yay akan bakinta yana girgiza kansa, “Mamana bazaki mutuba, ni da kaina zan roƙesa, ko durƙusa masa ta kama zanyi Mamana danki samu farin ciki, indai ina raye a duniya babu ɗayanku da zai nema abu ya rasashi ko menene shi, danku kawai nake neman arziƙi, nai miki alƙawarin saikin koma wajen Jawaad kinji, zaku sake rayuwarku ta jin daɗi fiyema da da har ki haifamin jikoki, nidai abinda nakeso dake ki kwantarmin da hankalinki ki samu lafiya, namiki alƙawarin daga nan ko gida bazaniba office ɗin Jawaad zanje kinji”. Kanta ta ɗaga tana zubda hawaye, tace, “Kaje dan ALLAH Dad, ka faɗa masa ina sonsa, idan ya barni mutuwa zanyi, wlhy namasa alƙawarin ko a daren yau yakeso yamin ciki na haihu gobe, na kuma samin wani jibi, ko ƴaƴa ɗarine zan haifa masa indai zamu kasance tare har abada”. Wata irin kunya ce ta tsargama Doctor jin furucin Shahudah wai ko yau ai mata ciki ta haihu gobe, a ransa yace anya kuwa wannan ƴa da ubane? ‘to irin wannan manya-manyan zance haka babu risinawa’ yaɗan girgiza kansa yana mamakin yanda tarbiyyar yaran hausa fulani keta ƙara ƙuɓucewa a hannun iyayen wannan zamanin, a ganin ko uwa mace ya dace ƴa taji nauyin buɗe wani lafazin a gabanta inba doleba balle uba namiji, gashi ya kula shi Dad ɗinma ko a jikinsa, saima biyema Shahudah da yake sakeyi yana lallashinta da alƙawarta mata samun duk abinda takeso, anya kuwa wannan hanyar ɓullewace iyaye ke ginama ƴaƴansu?, a yanzu tarbiyya da al’adun kunyar da aka sanmu dashi na tangal-tangal ɗin ɓarewa a hannayenmu tamkar kwale-kwale a ƙaton kogi inaga ƴaƴan dake tasowa waɗanda suke jiran amsar tarbiyya a hannun ƴaƴanmu, anya kuwa zamu girbi abinda iyayenmu suka shuka a garemu na alkairi?……
     Maganar Dad ta katsema Doctor tunaninsa, ya miƙe yana mai ranƙwafawa ya sumbaci koshin Shahudah da kumatunta, sannan ya shafa kanta cikin sigar lallashi da nuna tsagwaron soyayya da ƙaunar da yake mata yace, “Ki kwantar da hankalinki Mamana, yanzun nan zanje na isar ga saƙonki ga bb’n ki kinji, ki cire komai a ranki indai Jawaad ne kamar kin samu”. Kaita gyaɗa masa, murya a sanyaye tace, “I love you so much my Daddyna, duniyata, farincikina”. Cikin jin daɗin kalamanta Dad ya sake shafa kanta yana murmushi, yace, “I love you more mamana sanyin idaniyata, ki bani awa ɗaya kacal zan dawo miki da zance mai daɗin gaske”. Kanta ta ɗaga masa tana lumshe idanu tare da murmushi.
      Dad ya matsa daga gaban gadon tare da kamo hannun Aamilah dake tsaye jikin Window tana kallonsu, “My autana zo mana”. Baki taɗan tura gaba tana ƙoƙarin ƙwace hannunta, tace, “Bayan bakama kulaniba sai mamanka”. Jawota yay jikinsa ya rungume yana murmushi, “Waneni da ƙin kula autar Mom, ayi haƙuri bazan sakeba ihuyim”. Kanta ta jinjina masa kafin ta taso daga jikinsa tana kallon fuskarsa, cikin magana a hankali dankar Shahudah taji tace, “Dad dan ALLAH kasaka mai shegen taurin kan nan yay sanyi, kaga sister tana cikin damuwa, son da take masa yayi yawa tausayi take bani”. Murmushi Dad yayi ya shafa fuskarta, “Karki damu autana, insha ALLAH komai yazo ƙarshe kinji, bara naje na dawo kafin Mom ɗinku ta dawo”. Kanta ta jinjina masa, shikuma ya saketa ya fice.1
★★★★★★
           A station kuwa, bayan an fito salla Rose ce ta nufi Office ɗin Jay domin kai masa wasu takardu, tai knocking dan batai tunanin bai dawoba, jin babu amsa kusan sau uku saita tura ta shiga, dan sarai tasan randa yakejin wulaƙancinsa haka yakeyi, takuma tabbatar yana kallonta ta cctv. Babu kowa a office ɗin sai ƙamshinsa, saita shiga waige-waige, hangen kamar mutum a kwance a kujera ya sata takawa ta nufi wajen, ƙirjinta yay masifar bugawa saboda yin tozali da fuskar bily dake barci tana sauke numfashi a hankali tabbacin lafiya ta samu, ga rigar boss lilliɓe a jikinta. Cikin gurɓataccen hausanta ta lailayi ashariya ta direta tana kaɗa jiki da hura hanci, kafin takai hannu da nufin finciko bilkisu ƙasa, dan ta rantse yau sai tayi maganin shegiyar baƙar yarinyarnan koda boss zaiyi markaɗenta ya murza a turmi jininta ya zama mai, tsokarta da ƙashinta da fatarta su zama tunkuzar ƙuli-ƙuli………….✍42
To baza’ai tankaɗe da rairaya a gabanaba Rose nayi nana🚴🏼. Yau words dubu uku harda ɗari uku da hansin da hida nayi yanda zaku karanta har lahadi🤭🤫🤥🤐.6
Barkanmu da juma’a, kar’a manta da saka bayin ALLAH a addu’ar juma’a😥🙏🏻.8
Musha weekend lafiya😍😘🚴🏼
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
        14Page 18
……………“Wannan shine kuskure mafi girman da zaki aikata a rayuwarki inhar hannunki ya sauka kanta!!”.
         Kakkausan furuci daya karaɗe illahirin office ɗin da kunnuwan Rose kenan a lokacin da hannunta ke gab da kaiwa jikin Bilkisu da batasan Rose ɗin na kantaba ma, dan barci take cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, harma ta manta a inda take kwance.
        A firgice Rose ta janye hannunta tare da ɗago idanunta da juyowa domin tabbatar da abinda take zato, ilai kuwa shine fuska a murtuke babu alamar wasa tattare dashi balle sassauci, ya saki hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa yana cigaba da watsa mata wani mugun kallon daketa tsitstsinke jijiyoyin jikinta da hanjin cikinta, “Mi kike shirin yi da?” ya faɗa muryarsa cike da tsanarta irin wadda bata taɓa ganiba a gareshi. Da ƙyar Rose ta haɗiye ɗan yawun data tattaro a maƙoshinta, tace, “Ni babu abinda zanyi, kawai dai na shigone na ganta anan kwance____” “Shine zaki tada ita saboda a kanki take kwance?”. Yay saurin ƙarasa mata zancen data ɗakko yana tsatstsareta da idanu. Fuska ta sake tsukewa cikin tsananin kishi tace, “Ni wlhy yarinyarnan batai minba”. Wani banzan kallo sama da ƙasa yay mata ya ɗauke kansa yana faɗin, “Saiki kasheta ai”. Kamar zatai kuka tace, “Amma boss wai miye haɗinka da ƙwailar yarinyarnan? dako mace bata gama zamaba ma”. Tsaki yayi ya juya zaibar wajen yana faɗin, “Duk abinda ke ranki shine tsakaninmu, kozaki hana?”. Tamkar rose zata fasa kuka tabishi da kallo, yana zama Su Hafiz na shigowa da sallama, hannun Aliyu ɗauke da leda mai tambarin gidan abinci, duk kallon Rose sukai ganinta tsaye tamkar gunki tana kallon Jawaad da tamkarma baisan da itaba, ga fuskarsa a matuƙar ɗaure alamun zuciyar na kusa, mai tsautsayi ya taɓa a fashe masa ita. Hafiz ne ya fara janye idanunsa daga kan Rose ya sauke akan Bilkisu dake kwance tana barcinta lulluɓe da rigar Jay, har yanzu ko motsi bataiba dukda ihun da yayma Rose ɗazun, kafin suma su Jabeer su lura da ita. Babu wanda yace komai a cikinsu, shi kuma Jay baiko ɗago yama kallesuba balle su saran zai tanka.
       Aliyu ya matsa inda Jay yake ya ajiye ledar yana faɗin, “Ga abinci, kasa munje munata jiranka a wajen ashe kai kanama nan ka manta damu Boss”. Ɗago ido Jay yay fuska a yatsine ya harari Aliyu batare da yace komaiba, shi dai Aliyu zama yay abinsa bai kulashiba, Jabeer ma yaja kujerar kusa da Aliyu ya zauna yana haɗiye dariyarsa, dan ya lura Rose suman tsaye tayi a wajen kokuma ta samu gushewar hankaline na wasu mintoci.
       Hafiz yay guntun tsaki yana harar Rose, “Ke kuma lafiya kika wani tsaya ƙiƙam kamar wata dogariya?”. Numfashi Rose ta kawo cikin dawowa hayyacinta, ta watsama Hafiz harara kafin ta nufi ƙofar fita batare data tankama kowa a cikinsu ba, jikinta sai rawa yakeyi. Tana fita Jabeer ya kwashe da dariya, duka Hafiz yakai masa ya duƙe, Jay ya galla masa harara da faɗin, “Dilla malam miye haka?”. “Me nayi ni?” cewar Jabeer dake rama harar da Jay yay masa, ya cigaba da faɗin, “Kai ka dace da wannan tambayar baniba boss, sai neman haukatar da yaran mutane kake kana wani cijewa, gwara idan son yarinyarnan kake kafito ka sanarma duniya ka kuma shiga cikin ƴan takara ko Rose ta dawo hankalinta, kuma ka kwana da sanin Qaseem son yarinyarnan yake, yasin ka tsaya kallon ruwa ƙwaɗone zaima ƙafa, saboda gida ɗaya suke kwana suna tashi, dan a ruwa kake kusa da kada malam”. A fusace Jay da dama kaɗan yake jira ya miƙe, ƙofa ya nunama Jabeer yana huci, “Tashi ka fita a office ɗinan Jabeer kafin nama rashin mutuncin da bazaka taɓa mantawaba, banason wasan banza kaima ka sani ko”. Miƙewa Jabeer yay yana taɓe baki, yasan fitar tasa shine mafi alkairi dan Jawaad a wuya yake, shikuma idan yay zuciyar da har ɓacinta ya fito a muryarsa kai nesa dashi yafi komai alkairi, idan ya huce da kansa zai nemeka yay maka bayani harma daban haƙuri idan yasan yamaka abinda bai daceba. Ficewa Jabeer yay yana murmushi da girgiza kai. Jawaad ya koma ya zauna yana ƙwafa, sai kuma ya miƙe ya nufi toilet yabar su Hafiz dake binsa da kallo.
       A sanyaye Aliyu yace, “Sonta yake amma kamar shima bai fahimci hakaba Hafiz”. Cikin damuwa Hafiz ya bama Aliyu amsa da cewar, “Na daɗe da fahimtar haka Aliy, ba fahimtace baiyiba kuma shima, sarƙaƙiyar dake cikin al’amarin yarinyarne yake sakashi ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai kuskuren daya kasa tunawa shine, ba kowanne irin SO bane yake haɗiyuwa lokacin da ake buƙata, wani koda ka korashi da ruwan haƙuri dana juriya a maƙoshi yake tsayawa ya tsaida dukkanin muhimman al’amuranka wucewa cikin zuciya da ƙwaƙwalwa,  ni kaina na waiga ta kowacce kusurwa bashi da wani magoyin baya akan al’amarin yarinyarnan sai sashe ɗaya, shi kuma baida wani ƙarfin iko akan hakan”. ajiyar zuciya Aliyu ya sauke mai ƙarfi yana dafe kansa, sai kuma ya ɗago ya kalli Hafiz dake kallon inda Bilkisu take, yace, “Minene mafita yanzu Hafiz? Jay yana buƙatar mace a kusa dashi sosai ta kowanne ɓangarema kuwa, yarinyarnan kuma tanada mafi yawan nagartar data dace ta zame masa abokiyar rayuwa, mizai hana mu bashi shawarar ya sanar mata ABINDA KE RANSA”. Numfashi Hafiz ya sauke yay shiru na wasu sakkani yana nazari da bubbuga yatsansa akan baki, ya kalli Aliyu yana kaɗa kai, “Aliyu ita kanta yarinyarfa bamuda wani ƙwarin gwiwar samun goyon bayanta, dan tayi nisa wajen son ɗan uwanta, sannan bana tunanin zata iya barin Qaseem kodan halaccin mahaifinsa a rayuwarta ta ɗauki waninsa, shiyyasa nace maka akwai sarƙaƙiya takowacce kusurwa, Kasan Jabeer yanada fiƙira akan irin waɗannan al’amuran, sai dai shi matsalarsa saka wasa a dukkan lamarinsa, bansan lokacin da zai dinga kallon abu mai muhimmanci a muhallin daya dace ba, amma mubari zuwa weekend sai muyi zamana musamman akan maganar”. Cikin gamsuwa Aliyu yace, “Shikenan ALLAH ya kaimu”. Fitowar Jay daga bayi fuskarsa jiƙe da ruwa ya sakasu yin shiru, babu wanda yace dashi komai yazo ya zauna a kujerarsa, Hafiz ne ya fara miƙewa yana faɗin, “Bara muje zuwa anjima ma dawo muyi maganar idan ka samu lokaci”. Kai kawai jay ya ɗaga amma baice uffanba.+
STORY CONTINUES BELOW
      Fitar su Aliyu babu jimawa Dad ya iso station ɗin su Jawaad, ba’a bashi damar shigaba saida ya kira Jawaad a waya, tamkarma Jawaad bazai ɗauka wayarba sai wani tunani yazo masa a rai, hakan yasa bayan wayar ta katse yabi bayan kiran Dad shi ya kirashi. Koda ya sanarmasa yana gate sosai mamaki ya kasheshi, amma sai yabama securitys ɗin umarnin a rako Dad office ɗinsa, shaf ya manta da Bilkisu dake kwance tana barci.
        Bai nunama Dad komaiba yay masa tarba ta mutuntawa, bayan sun gaisa ya bashi ruwa Dad ya fara magana cikin karyar da murya. “Jawaad”. Yanda ya kira sunansane ya sakashi ɗaga kai ya kallesa, ya amsa da “Na’am”. “Jawaad wajenka nazo gwiwoyina a ƙasa da tarin magiya da roƙon da idan kamawa tai na duƙa a gabanka zanyi hakan. Dan ALLAH ka tausayama Mamana ka dubi al’amarinta, bazan musamaka ba akan ita mai laifice damu kanmu, sai dai ince dan ALLAH mu manta da baya domin ta shuɗe, wlhy ina mai tabbatar maka duk wautar dake kan Mamana a yanzu babu ita, dan ta gurzu da horonka, ka tausayamin kodan ciwon dake tare da ita na hawan jini da likita ya sanar mana, badan tanada sauran shan ruwaba faɗuwar da tai jiya a gidanku likita ya tabbatar mana da sai ta kamu da paralysis, wlhy yarinyarnan tana sonka fiye da yanda kake zato ko tsammani……..” Jawaad da kansa ke ƙasa yace, “Kayi haƙuri Dad ban katsekaba, da Huda na min irin wannan son da bazata guji haɗa zuri’a daniba, yakamata mu fahimci Hudah ta huce sahun ƙuruciya yanzun, bai kamata ace duk abinda yazo zuciyarta tai tunanin aikatashi shine mafi dai-dai a rayuwarta ba, sannan kuma abinda takeso ace dole saita samesa, dolene duk inda akwai take wataran za’a samu babu. batason haihuwa yanzun miyasa ta yarda tai aure? Bata shirya zama kamar kowacce macen aureba miyasa ta zaɓi muyi aure? A ganina da sai ta bari sai lokacin da duk ta shirya waɗan nan, Dady ni bahaushene, uwata bahaushiyace, mahaifina bahaushene, dukkanin dangina hausawane sai fulani, addinina shine musulunci, addinin iyayena da dangina duk musuluncine, tayaya Hudah take tunanin zan biye mata na ajiye dokokin UBANGIJINA na ɗauki son zuciyarta?, tayaya take tunani zan ajiye al’adun yarena dana tashi cikinsu na ɗauki ra’ayinta data aro a wajen wasu?, ai duk duniyar da zan shiga dady ina alfahari da abubuwannan guda biyu, YARENA ADDININAH, banajin kunyar nuna kaina a gaban kowanne mahaluki da tambari kasancewata musulmi, dan rahamace babba a gareni da wofantar da ita babbar asarace da bata da madadi duniya da lahira, a duk duniyar dana shiga zan kira kaina bahaushe, koda wanda nake tare dashi baitaɓa jin sunan yaren hausa ba ma zan tabbatar masa da yaren ya fara saninsa a lokacin kuma nai masa AlFAHARI dashi saboda yarena ne, shine harshen da UBANGIJINA yafi ganin ya cancanta na fito a ciki ya zama abin maganata, to mizaisa na ƙyamacesa saboda yaren wasu da ko za’a kashesuma basusan nawa ba, wlhy Dady idan ka cire LARABCI daya kasance yaren MANZON ALLAH (S.A.W) to babu wani yare da yakai muhimmancin dazan fifitashi sama da yarena na HAUSA, duk yaren da kaji yafita a harshena saɓanin LARABCI da HAUSA to inayinsane saboda lalurar mu’amulla da mutane badan ina kallonsa a saman nawaba. Kayi haƙuri Dad mubar wannan maganar kawai, ku tayamu addu’ar ALLAH ya bama kowa dai-dai da ra’ayinsa ni da ita, dan nikam Hudah tafi ƙarfina”.
          Jikin Dad duk yayi sanyi da maganganun Jawaad, dan kuwa dukkan abinda ya lissafa matsalace mai tushe da shima yanada kaso mafi yawa wajen ƙirƙirarta ga ahalinsa, to amma yanzu bata wannan akeba, matsalar mamansa itace gaba da komai. Ya nisa cikin girgiza kai da raunana murya fiye da farko yace, “A karo na babu adadi Jawaad zan kuma cewa kayi haƙuri, ina mai tabbatar maka a yanzu zaka sami mamana a yanda kakeso kuma kake buƙata”.
            Shiru Jawaad yay yana mai kallon Dad cike da tausayi, dan yasan shine ginshiƙin ruguza gidansa wajen sakaci, gashi a yanzu abinda ya raina yayi gawurtar da al’amarinsa yafi ƙarfinsa amma shi baima fahimtaba, cike da girmamawa yace, “Kayi haƙuri Dad zanzo gida na sameka idan na tashi aiki insha ALLAH, wannan maganar bata nan baceba, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. Shiru Dad yay ya kasa tashi, dan gani yake tamkar Jay yawo da hankali zai masa, saboda yasan taurin kan yaron da kafiya idan ya juyama abu baya, tun yana yaro ya fahimci wannan shegiyar halayyar tattare dashi, shiko buƙatar ƴaƴansa bai haɗata da komai a wannan duniyar ba. A bazata Jawaad kawai sai yaga Dad tsuggunne gabansa yana faɗin, “Jawaad dan girman ALLAH karka wofantar da maganar n….” da sauri Jawaad ya miƙe jikinsa har rawa yake ya tanƙwaɓe wayarsa dake kan desk ɗinsa ta faɗi ƙasa, baibi takantaba ya kama hannun Dad yana faɗin, “Ya ilahi, Dad dan ALLAH ka tashi, minene kakeyi haka? Wlhy na tabbatar maka zanzo muyi magana a gida” da ƙyar Jawaad ya samu Dad ya tashi tsaye, gaba ɗaya al’amarin yana neman birkita masa ƙwaƙwalwa, wane irin ubane Dad? Wane irin kalar mugun so ne wannan yakema ƴaƴansa? Abin yayi yawa matuƙa, kowanne iyaye nason ƴaƴansu amma na Dad yana neman wuce hankali. Shidai Jawaad sai ya koma lallashin Dad ɗin ya samu suka fita yay masa rakkiya ya tafi, gaba ɗaya kansa a cinkushe yake, harma ya fara masa wani masiffen ciwo tacan ciki.3
STORY CONTINUES BELOW
        Koda ya dawo office da shashshekar kukan Bilkisu ya fara cin karo, tun shigowar Dad ta farka, dukkan maganganun da Dad sukai da Jawaad kaf ta jisu, takuma fahimci kaso mafi yawa na dangane da matsalar data raba aunty Shahudah da mijinta, Dad ya bata tausayi matuƙa gaya yau, babban mutum kamarsa da ya haifi ɗan da yafi Jawaad amma yake tsugunawa a gabansa domin kawai farin cikin ƴarsa, wanne irin makahon so ne haka Uncle ɗin nata kema zuri’arsa?, a ganinta lokaci yayi da zata bada gudunmawarta ga Dad ko ƴar kaɗance……
      Jawaad tsaye yay a ƙofa hannunsa duka biyu cikin aljihun wandonsa ya zuba mata ido, ransa a dagule yake, sannan ita kuma baisan ma’anar kukan nataba balle inda ya dosa, hakanne ya sakashi jan wani shegen tsaki ya cigaba da takowa cikin office ɗin batare daya sake kallonta ba. Har cikin zuciya da ruhi tsakinsa ya taɓa Bily, hakan ya sake jawo gudun ruwan hawayenta babu ƙaƙƙautawa, ta cigaba da kukanta na tsawon wasu mintuna shi kuma yana cigaba da aikinsa tamkarma baisan da zamanta a office ɗinba. Dan kanta taji kukan ya isheta ta share hawayenta ta tashi ɗauke da rigarsa a hannu ta nufesa. A tsorace zuciyarta take, amma wani sashe na bata ƙwarin gwiwa akan abinda take shirin yi. Gaban Jawaad taje ta durƙusa kanta a ƙasa. Jawaad da yaƙi ɗagowa ya kalleta dukda yanajin motsinta ya cigaba da aikinsa.
         Karan farko a rayuwar Bilkisu data shirya ambaton sunan Jay a harshenta harma da ƙarfin halin furtawa a gabansa, sai dai tayi imanin bazata iya ambaton sunansa da kallonsaba a yau, dan haka ta duƙar da kanta tana durƙushe akan gwiwoyinta, rigarsa riƙe a hannunta ajiye akan cinya, tace, “Yah Jawaad!.…….”
     Cak Jay dake rubutu a wasu takardu ya tsaya tamkar wanda aka tsaida da remote, shi bai kalleta ba, kuma bai cigaba da abinda yakeba, saima lumshe idanunsa da yay yana sauraren sarawar da kansa ke masa da harbawar jijiyoyinsa harma da gudun jininsa daya tsinke a lokaci ɗaya. Bilkisu daba kallonsa takeba ta cigaba da faɗin “Dan girman ALLAH Yah Jawaad kayi haƙuri karka wofantar da magiyar Dadynmu, wlhy ni shaidace aunty Shahudah na matuƙar sonka, duk da bansan ainahin matsalarkuba inada yaƙinin zaka iya amfani da son da take maka ka canjata, matsalar da duk kake ganinta da ita ƙirƙirarriyar matsalace dakeda tushe a gareta tun tana tsumman haihuwa, ba laifinta bane ita kaɗai haka ta tashi taga kanta itama, bata isa banbance baƙi ko fariba a buƙatar jin zafi saboda an nuna mata hakan shine dai-dai da rayuwarta kuma nasararta, Mahaifina yasha faɗamin, {Bilkisu, aduk lokacin da zama ya haɗaki da mutane ki fara nutsuwa ki fuskanci halayyarsu da tsarin rayuwar da suka rayu, dan babu wata zuciya dake gogayya da ƴar uwarta akan hallayya iri ɗaya, lokacin da k tarbiyyarki ta baki dai-dai a wajen wani shi kuskurene, abinda yake kuskure a yaƙininki a wajen wani dai-dai ne, idan har kika kasance cikin mutane masu fahimtar ilimin duniya ina mai tabbatar miki zaki zama nasararki sama data kowa koda ace ke kaɗai kike kallon kanki a wannan nasarar,  daga lokacinda ilimin sanin hallayar ɗan adam ya dawo tafin hannunki inada yaƙinin zaki gyara ɓarna da yawa, domin zakibi mutum da halinsa ki ɗorashi akan hanyarki mai nagarta batare dashi yasan ya afkaba ma, munzo zamanin da halin ɗan adam dashi ake cinsa da yaƙi bada takobiba, zauna dame ƙinki da zuciya ɗaya, ƙyautata masa kuma da yaƙinin neman sakamo wajen mai badawa ba ga shiba, koda shi a kullum zai kasance mai bibiyar bayanki da sharri, karki zama mai damuwa da zama gwana a duniya, dan wani lokacin nasarar duniya faɗuwace gamai ita, koda idanun duniya na kallonsa a saman kowa, mai kuma sa’a fiye da kowa}, Yah Jawaad ba soyayyarka kawai aunty Shahudah ke buƙataba, a yanzu tafi buƙatar ka jingina da soyayyar tata ka ɗorata a hanyar tsira domin kaikaɗaine zata iya saurara, saboda girmamaka a matsayin gwaninta, na yarda dakai ta kowanne fanni koda banida ilimin sanin ɓoyayyun halayenka, ina sake roƙonka a matsayin Yaya ba shugabana a wajen aikiba, dan ALLAH ka ceto rayukan bayin da zukatansu suke a rufe ruf akan sanin gaskiya da makomar bin hanyarta, yahudanci da nasaranci duhune, wannan duhun kuma shike mamaye da jama’ar gidanmu, sai dai hasken ruɗani da gushewar banbance mai tsafta ya hana ijiyarsu ganin kowanne tsani sai wanda suka hau, kullum fatana ALLAH ya kawo musu drivern dazai fidda rayukansu a kwale-kwale saboda ni nayi ƙanƙanta ƙarancin matsayin yin wannan jagorancin, kaiko inada yaƙinin zaka iya, domin son da sukema aunty Shahudah gyaruwarta tamkar gyaruwar kaso mafi yawane daga ahalin gidan, ciki kuwa harda Dad da tuni ya fahimci gaskiya, sai dai ƙarfin riƙonta a garesa da tafi ya hanashi nunawa ko a fuska, ya gwammaci ya haɗiyeta a rai yacigaba da rainon ƴaƴansa tamkar ƴaƴan agwagi da basa bin uwa sai dai ita ta bisu” na ɗago kai a karo na farko tunda na fara maganar na kallesa, sai dai a mamakinna shi ba ni yake kalloba, gashi yayi kicin-kicin da fuska irin yanda ban taɓa ganiba a tun sanina dashi, na raya a raina saitna dire abinda na fara, dan haka nace, “Dan ALLAH Yaya Jawaad ka yarda a maida aurenku da aunty Shahudah a karo na b….i…y…u.”
         A yanda ya juyo ya sauke rikitattun idanunsa a kainane yay masifar hargitsani na ƙarasa kalmar ƙarshe da ɗai-ɗai………….✍60
Tab wlhy badaniba nayi nan, idan ya huce na dawo na ƙarasa muku yanda aka ƙare🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼kuma bily addu’ar fitowa lafiya itama, dan inaga ba’a taɓa karyata ba😂🤣.6
Barkanmu da dawowa, inafatan kowa yayi weekend cikin ƙoshin lafiya?.😍😍6
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.19Page 193
…………….Idanunsa sunyi masifar kaɗawa sunyi jajur, batare da yace dani komaiba yaymin nuni da ƙofa alamar in fita, kasa koda motsi nayi, sai hawaye dake cigaba da ambaliya a kumatuna tamkar an buɗe fanfo.
          Cikin matuƙar kaushin murya da tsawa na tsinkayi furucinsa cikin kunnuwana, “Miemaa! niɗin sa’anki ne ko?!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai jikina na rawa saboda harga ALLAH na matuƙar tsorata da yanayinsa. Ya sake faɗin, “Tashi kifita a office ɗinan kafin naimiki duk abinda yazomin kai, Yanzunan har idonki yakai tsaurin kallona ki faɗamin abinda ya dace dani?!, ki fitar min anan kona sauya miki kamanni!!”. Kuka na sake fashewa dashi ina saurin jan jikina nai baya gudun karya makeni, dan harga ALLAH tausayin Dad na tsaga dukkan jijiyoyin jikina harda aunty Shahudah, na tabbatar samun boss ga aunty Shahudah shine farin cikin gidanmu, Hawayen dake ziraromin na share tare da faɗin “Kayi haƙuri dan ALLAH, bazan sakeba”. Cikin faɗan dana rasa abinda ya fusatashi irin haka yace….. “Baki jiniba ko?!” yay maganar a hasale yana tasowa kaina, Baya na shiga jan gwiwoyina batare dana tashiba, matsanancin fushin dana gani akan fuskarsa ya bani tsoro matuƙa, bantaɓa tunanin yanada zafin zuciya irin hakaba, ya nunani da ɗanyatsa yana faɗin, “Badai kece kika buƙata da kanki ba, to duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki ba daniba Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan shashashar banza”. Ya ƙare maganar yana ranƙwafowa kaina ya fisge rigarsa dake hannuna ya fice daga office ɗin”.
          Ɗif naji komai na ya ɗauke wuta yabar aiki, sam narasa awane mizani zan ɗora ruɗaɗɗun kalamansa marasa tushe balle makama, man kaina gaba ɗaya ya tsiyaye, babu wata jijiya dake ɗaukar saƙon ƙwaƙwalwa zuwa zuciya dake aiki a jikina har tsahon wasu mintuna da naji saukar abu mai ɗumi a jikina. Zumbur na miƙe domin samun dawowar hankalina daya gushe na wucin gadi. Ban sami damar gama tattaro abinda ya shuɗeba idona ya sauka akan Oga Jabeer dake bakin ƙofa a tsaye yana kallona. murmushi yaymin kafin ya ƙarasa shigowa office ɗin, “Tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki kinji” Ya faɗa yanamin nuni da hannu. Ban musa masaba na miƙe, dan koba komai ina buƙatar duba halin da nake a ciki.
             Bani da isashen lokacin fashin baƙi akan ruɗaɗɗun kalamansa, dan kaina tsaye ina dangantasune kawai da rufewar ido ga mamallakin furtasu, to danmima zuciyata kesan rikitani da hasashen abinda bazai taɓa zama hakaba, na ƙurama kaina ido a madubin dake cikin toilet ɗin ina mai tariyo kalaman dallah-dallah yanda zasu bani fassarar da nake buƙata, “{Duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki badaniba Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan shashashar banza}”. ‘Kenan yana nufin inhar aunty Shahudah ta sake koma masa da halinta na baya akwai hannuna wajen cutar dashi? Kuma nizai kuhunta ba itaba? To miyasa? Miyasa zan zama laifi akan ƙoƙarin ganin na inganta auren sunna, na haɗa zukata biyu masu ƙaunar junansu, na tabbata shima yana sonta kawai halayyarta yake ƙyamata, to miyasa ni laifin zai tattara a kaina kuma?’ “Saboda kalamanki ne suka tursasashi yarda ta koma” wata zuciya ta ayyanamin daga can ƙasan rai, ‘To miyasa zai amince da abinda bai zama wajibiba? Ni shawara na bashi da nuna masa ƙwaɗayin samun lada ai ba tilasba, sannan na ceto zuciyar Dad daga ɓacin ran tashin hankalin gudan jininsa, kenan hakan yana nufin kuskure nayi?, ni wacece da har zai amshi roƙona ya wajabtama kansa?, nasake tambayar kaina hawaye na silalomin. Nima kaina sai yanzu naga ƙarfin halina da wautata akan taryarsa, banyi tsammanin zan iya hakanba koda a cikin mafarkine kuwa, zan cigaba da roƙon ALLAH ya hana faruwar matsalar da yake hangowar, insha ALLAHU lafiya zasu zauna abinsu. Haƙura nai da tunanin na kimtsa jikina da tissue ɗin dana gani a toilet ɗin dan inada tabbacin zai riƙeni har zuwa a tashi insha ALLAHU, na sake ɗauraye fuskata na fito. Zaune na iske oga Jabeer, yana ganina yay ƙaramar dariya da faɗin, “Anya maman nan tamu ba raguwa baceba?” murmushin da ban niyyaba ya suɓucemin, na girgiza masa kai ina faɗin “a’a sir”. Dariyar ya sakeyi da cewar, “To ALLAH yasa, yanzu daga nan sai ina kuma?”. Nace, “Zan koma Office ne, akwai aikin da boss ma ya sani tun ranar waccan monday ɗin ban kammalaba”. Ya miƙe yana faɗin, “To masha ALLAH, nima bara na koma office, amma daga yau idan kikaga Jay a irin wannan matsanancin fushin ki daina masa naci akan koma wane irin maganace, dan idan yay fushi irin haka akwai matsala, ALLAH ne ya taimakeki ya zaɓi ya fita yabar miki office ɗin, amma dabai fitanba ke kuma kika cigaba da taurinkan kin fita komai zai iya biyo baya, ki kiyaye kinji, boss ya wuce duk yanda kike zatonsa, mutumne murɗaɗɗe mai wahalar sha’ani matuƙa, idan yaso kaji dadinsa baka taɓa fahimtar tsaurinsa, idan baiso hakanba wahala zakasha ta gaske”.
       Nace,  “Insha Allah zan kiyaye nagode sosai”.
      “Hakan shine dai-dai, ALLAH ya kiyaye gaba”.
     Tare muka fita, shi ya nufi office nikuma na sauka ƙasa, harna fara tafiya sai naji ina buƙatar ganin yah Qaseem, dan tunda mukazo yau ban gansaba kuma bai nemeniba, ko a waya.
       Nayi knocking kusan sau uku babu amsa, hakan yasani tura ƙofar office ɗin a hankali na shiga, zaune na sameshi a kujerarsa, ya kwantar da bayansa jikinta idanunsa a lumshe, na sake maimaita sallamar tawa idona kafe a kansa. A hankali ya buɗe idonu yana kallona, sai kuma ya tsashi zaune sosai yana murmushi damin alamar nazo da hannu. Takawa nai a hankali zuwa garesa, na zauna a ɗaya daga kujerar gaban tebirinsa idona har yanzu a kansa. Wani murmushin ya sakemin, kafin ya buɗe baki a hankali cikin sanyin murya yace, “Har yanzu jikin dai bilkisu?”. “A’a Yah Qaseem naji sauƙi, mike damunka? Tunda muka baro gida baka da walwala, gashi har yanzu ina ganinta a saman fuskarka kuma, mike faruwane?”.
       “Humm” ya faɗa yana cije baki, kafin yace, “Babu komai, kawai dai banajin ƙarfin jikinane”. Numfashi na sauke a hankali fuskata na nuna tausayinsa, nace, “To ko zamu tafi gida kaga likita”. Nanma kansa ya girgiza mani, cikin kauda maganar yace, “Kinci abinci ko?”. Kaina kawai na iya ɗaga masa, dan jinai dukna damu da halin da yake a ciki, shiru mukai na wasu mintuna kafin na miƙe nace, “bara na wuce dama leƙoka nayi dan naji shiru”.
      Baice komaiba saida na doshi hanyar fita daga office ɗin, “Ki ƙoƙarin gama abinda kikeyi, da anyi la’asar zamu wuce dan yanzu Mom ta kirani jikin Shahudah ya sake rikicewa”. Sosai naji gabana ya faɗi, na kaɗa masa kai kawai ina haɗiye ƙwallar data cika mani ido, “ALLAH ya bata lafiya” “Amin”. ya amsa mini akan laɓɓa.11
STORY CONTINUES BELOW
★★★★★★★
               A ɓangaren Jay kuwa gaba ɗaya yarasa gane kansa, haka kawai ya tsinci zuciyarsa da fushi mai tsanani, koda ya fita daga station rasa ina zai dosa yayi, yata zagaye gari daga wannan titi zuwa wannan har ƙarfe biyar na yamma, sallar la’asar kawai ya tsaya yayi da lokacinta yayi, ganin yamma tayi saiya juya kan motar Jabeer daya ɗakko daga office ya nufi gidan Alhaji baba kakansa.
       A ƙofar gida ya iske Alhaji baba da tsaaffin anguwar a bishiyar dalbejiyar dake ƙofar gidansa, inda yake zama duk yamma yasha iska koda hantsi, sai yazam tsaffin dake anguwa sukanzo suma su zauna suyita hira, a kusa dasu yay parking, yaja kusan mintuna uku bai fito a motarba, tsoffin nata magana akan wanene? Amma bai tankaba balle ya fita, shiko Alhaji baba bai tankaba, dan yaji a ransa Jawaad ne dukda yasan ba motarsa bace, kuma glass ɗin motar nada duhu ba’a ganin na ciki.
      Sai da ya mula dan kansa ya buɗe ya fito. Alhaji Baba ya bisa da kallo kawai batare da yace komaiba. Jawaad ya rissina ya gaida tsoffin kafin ya miƙe ya nufi hanyar gate ɗin gidan batare da yacema Alhaji baba komaiba. A falo ya zube saman doguwar kujera ko takalmi bai cireba, ya lumshe idanunsa yana maijin kewar iyayensa na tsarga masa da zafi-zafi, a yau babu abinda yake tsananin buƙata sama da ɗumin mahaifiyarsa, burinsa kawai ya ɗora kansa a cinyarta tana shafawa da tambayar damuwarsa, shiko ya juye mata duk abinda ke ransa ta bashi shawara da masa addu’a. Sai dai kuma gashi ƙaddara ta daɗe da hana hakan a jerin farin cikin rayuwarsa, ƙilama tuna tabar masa duniyar bai saniba, kokuma ta fita hayyacinta fiye da yanda zata iya tuna ita wacecema balle abinda shi ta haifa, amma duk yanda take yanason abinsa, zaiyi farin ciki da maraba da ganinta a duk yanda take.
           Buɗe idanunsa yay saboda saukar hannun Alhaji baba a saman fuskarsa yana share masa ƙwalla, Alhaji baba yay murmushi cikin zolaya yace, “Kullum kai saika kwaso ragwantakarka ka kawomin gida, ina namijin dake filin daga ina kuka Muhammadu”. Murmushi Jay yayi tareda lumshe ido yana rungume hannun kakan nasa a cikin wuyansa, baidaice komaiba, hakan yasa Alhaji baba ɗaga kansa ya zauna sannan ya maida kan saman cinyarsa ya ɗora, ahankali ya shiga shafa kan Jay dake cinyar tasa, hannunsa ɗaya kuma na shafa fuskarsa da ƙananun gashin saje da bai askeba ke kwance a jiki. Shiru sukai gaba ɗaya, Jawaad yay lamo a jikin kakansa yana sauke numfashi a hankali, tuni kaso mafi yawa na damuwarsa yaji ya gudu, tsahon lokaci suka ɗauka a haka babu wanda yay magana, ganin lokacin salla ya gabato Alhaji baba ya shafa fuskar Jay yana faɗin, “Muhammadu tashi kaje kai wanka kayo alwala muje masallaci”. Buɗe idanu Jawaad yay a hankali, sun ƙanƙance sosai alamar yanajin barci, tashi yay ya nufi ɗakin kakansa dan baida matsalar kaya tunda yana ajiyewa anan. Cike da tausayawa Alhaji baba ya bisa da kallo, yana tsananin son jikan nasa tilo namiji da tausayinsa matuƙa, a kullum baya gazawa da yimasa addu’ar kariya daga dukkanin abin ƙi da maƙiya.
 
             Ana ƙoƙarin shiga sallah Jawaad ya fito a gaggauce cikin jallabiya ruwan siminti, sai ƙamshin turaren kakansa yake mai sanyin daɗi, tare suka tafi massalaci dan Alhaji Baba yayi alwala a toilet ɗin falo. Koda aka idar sai sukai zamansu acan har isha’i, bayan sun fitone Alhaji baba yay sallama da mutane da neman gafara ga wanda ya ɓatamawa bisaga al’adarsa, dan acewarsa bai zama lallai yana cikin jerin masu tashi suga safiyar gobe ba, shiyyasa duk bayan kowacce sallar isha’i yakanyi sallama da maƙwaftansa da neman gafararsu kafin ya shige gida. Sun iske Nabeelah ta kawo masa abinci kamar kullum, tunda ta gaida Jay sau ɗaya ya amsa yay kwanciyarsa a doguwar kujera, sai hira suke ita da Alhaji Baba, zuwa takwas da rabi tai musu sallama ta tafi dan tare suke da driver dama. Tana fita Jawaad ya sakko ya shiga buɗe kulolin da aka jero cikin kwandon mai ƙyau daga gidan Ummah, tuwone kamar kullum dare da Alhaji baba ya wajabtama kansa, jay ya miƙe zuwa kicin ya ɗakko filet da cokali, tuwon alkamar ya dawo ya ɗiba da miyar ɗanyar kuɓewa, shidai Alhaji baba nata tsokanarsa da gwauro kafi tuzuru. Wani ya tanka wani yay shiru, sai kuma a hankali ya saki jikinsa sukai hira sosai kamar yanda Alhaji baba ya buƙata, cikin hikima kuma yake masa nasiha, sai wajen sha ɗaya suka kwanta, dan Jay yace anan zai kwana yau, da yayi sallar asuba sai ya wuce gida.
STORY CONTINUES BELOW
★★★★★★
             Ƙarfe huɗu da rabi muka bar office, daga nan asibiti muka nufa, mun iske jikin aunty Shahudah kan babu daɗi, dan yanzunma dai saida tasha allurar barci. Anan muka zauna har magriba saboda kowa yana nan sannan muka tafi kamar yanda Dad ya bamu umarni. Har zuwa yanzun dai Yah Qaseem bashi da wata walwala, muna isa gida kuma kowa yay ɗakinsa, naji haushin ganin ɗakina kaca-kaca, yanda Aunty Aamilah ta tashi haka ta barminshi uwa turken jakai, gadon na fara gyarawa nai shara sannan na shiga wanka, dama gaba ɗaya a takure nake, saidai maganin da boss ya bani ya mugun taimaka mani, dan jina nake sakayau babu ciwon marar sai abinda ba’a rasaba. Kamar yanda na saba har alwala saida na ɗaura dukda ina fashin salla, sannan na fito nai shirin barci, gado na haye na buɗe data, dan munada meeting dasu Ummie akan bikin Nazifa, munyi nisa a firarmu sosai Nazifa tai wata maganar data saka zuciyata bugawa lokaci guda, “Sisters wlhy akwai matsala, ko kunsan a daren jiya anyima jikar marka mai aikinmu fyaɗe, kuma kamar dai namu ne itama saida aka bugar da ita”. Ina gama karanta abinda Nazifa ta rubuta na saki wayar a kan gado jikina na wata irin rawa, a wani irin firgici maiban tsoro na tsinci kaina a ciki, na shiga waige-waige a cikin ɗakin tamkar mai tsoron ganin wani abu, a wani irin matsanancin ihu na shiga faɗin, “Ya isa!! Nace ya isa!!! Ya isa haka nan Pleaseeeeeee” na ƙarashe faɗa da sanyin murya ina fashewa da kuka, Aamilah Da Dad ne sukai rige-rigen shigowa ɗakin saboda jiyo sambatun Bilkisu.
      Dad ya riƙo hannunta data tattare bedsheet ta matse a ciki yana faɗin, “Daughter! K daughter miya faru??”. Bilkisu ta kuma fashewa da kuka tana kallon Dad dake riƙe da hannunta, Aamilah a gefensa, “Dad dan ALLAH kuce dasu ya isa haka, su bari hakanan” ta cije baki tana zazzaro idanu cikin ficewar hayyaci ta fisge hannunta ta tashi zaune a kan gadon, ta bubbugashi da ƙarfi na alamun ɗaukar alwashi, kafin tacigaba da magana cikin kaushin murya, “Wlhy wlhy Dad, inhar basu dainaba, ni da hannuna saina kakkashesu, gunduwa-gunduwa zanyi da namansu naba karnukan office ɗinmu su cinye, kamar yanda suke bibiyarmu wlhy nima zan cigaba da bibiyarsu, subar ganina mace, duk mai hannu a ciki sai ya shiga uku a hannuna, wlhy halakashi zanyi Dad, saina halakashi” ta ƙare maganar da fashewa da kuka tana faɗawa jikin Aamilah.
           Sam Dad bai fahimci komai daga zantukan Bilkisu ba dake fita a murɗe, yama fara tunanin yarinyarnan ko aljanune da ita, jiba jiya yanda suka bashi labarin an basu tsoro a gidan, kuma ita tafi kowa firgita da shiga ruɗani, ahankali ya juya ga ƙofa saboda jin motsi, Salman ne da Qaseem, Qaseem ya jiƙe sharkaf da zufa dukda fanka dake aiki a ɗakin, gashi idanunsa sun kaɗa sunyi jazur har ana iya hango yanda jijiyoyin kansa sukai ruɗu-ruɗu.
       “Qaseem kaikuma mike damunka?” Dad ya faɗa da tsagwaron mamaki, Salman da shima dai jikin nasa a sanyaye yake ya kalli Qaseem tare da dafa kafaɗarsa, kallonsa Qaseem yayi shima, sai dai babu wanda ya iya cema ɗan uwansa komai, saima Qaseem ya zame hannun Salman a jikinsa ya juya ya fita daga ɗakin.
          Dad ya sauke nannauyan numfashi, dan shifa al’amarin ƴaƴan nasa ya fara bashi matsanancin tsoro, shin mike faruwane haka wai?. Babu mai bashi amsa dan haka yay shiru kawai ya zubama Bilkisu dake shashshekar kuka a hankali idanu. Ita kanta Aamilah duk iskancin nan nata yau a firgice take, dan tsaf bata manta tsoratasun da akai jiyaba, hakan yasa Bilkisu na fara sambatu itace farkon  jiyota.
      Dad ya kamo hannun Bilkisu yana rabota da jikin Aamilah, “Bilkisu tashi ki faɗamin mike faruwa?”. Babu musu Bily ta tashi zaune, Dad ya sake cewa, “Miya farune? Jiya ance an tsorataku musamma k, yau kuma gashi mun jiyoki kinata sambatu?”. Hawayen daketa faman ziraro mata ta share.
              Naɗan kalli Dad ƙaɗan na maida kaina ƙasa, cikin muryata data dishashe a yinin yau gaba ɗaya nace, “Dad fyaɗe akaima ƴar mai aikin gidansu Nazifa” shiru yay kawai yana kallona har nakusan sakanni ashirin, kafin ya girgiza kansa cikin wani yanayi yace, “To Bilkisu shine kuma kike irin wannan mahaukacin kukan?, ƴar gidan waye a cikin ƙawayen naki abin ya faru a gidansu?”.  “Gidan Alhaji Sufyan magashi”. “To ALLAH ya kiyaye, ki kwantar da hankalinki shima ai zai ɗauki mataki, inake ina shiga irin wannan maganar ƴar ƙaramarki dake, sannan kuma ma k miye naki a ciki? Ai can matsalar family ɗinsuce, muma muji da tamu gatanan kinji”. Kaina kawai na ɗaga masa cikin tsantsar takaicin furucinsa, yaukam na sake girmama al’amarin Dad fiye da tunanina, miyasa shi kansa kawai ya sani sai ƴaƴansa? Yanzu da ace Aamilah ko aunty Shahudah akaimawa ai da bazaice hakaba ko, anya kuwa koda a kaina wannan abun ya faru Dad zai nuna damuwarsa kuwa?. Sosai gabana ya faɗi da zuwan wannan tunanin a cikin raina, nayi nisa sosai a tunanina har bansan lokacin dasu Dad suka bar ɗakinba, kawai juyawa nai na jini kwance a gado har an lulluɓeni da bargoma, aunty Aamila na kwance a gefena da alama ta jima dayin barci ma, nasan badan tsoron da takejiba bazata taɓa zuwa ta raɓeniba.8
         Dad kam koda suka fita a falonsa na sama ya iske Qaseem zaune yana jiransa, da mamaki ya kallesa. “Kana nufin dama ba zuwa kai ka kwantaba?”. Kai Yah Qaseem ya jinjina alamar eh. Dad ya zauna kusa dashi cikin kulawa yace, “Mike faruwa?”. Kallonsa Qaseem yayi, murya a sanyaye yace, “Dad inason a saka ranar aurenmu ni da Bilkisu”. Shiru Dad yay kawai yana kallon Qaseem tamkar yaune ya fara ganinsa, kusan mintuna biyu kafin ya jinjina kansa, yace, “Shikenan za’ayi hakan, to amma ita kaji ra’ayinta akan ta shirya aure yanzun?”. Kai Qaseem ya jinjina, yace, “Munyi magana da ita ranar, dama dawowarka nake jira Dad, banason asa bikin da nisa kuma, karya wuce wata ɗaya”. Dad yay murmushi cike da tsokana yace, “A lallai wannan angon a shirye yake, yanzu dai kaga Ramadan baifi saura kwana goma sha uku ba ya rage mana, lokaci yazo a ƙure kenan, saimu saka bikin bayan salla kenan kamar da sati biyu, zan fara nemar dangin mahaifinta muyi magana dan wannan huruminsune dukda sun wofantar da al’amarinta, kaga sai a haɗa tare dana mamana kawai ayi a huta”. Fuskar Qaseem ɗauke da murmushi yace, “Shikenan Dad nagode sosai, ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana”. “Amin ya rabbi” Dad ya faɗa yana mamaki a ransa yau Qaseem ya masa godiya akan abu, lallai kusanci da Bilkisu ya kawo cigaba a wani ɓangare na rayuwar yaransa, dan shikam bazai iya tuna randa yayma Qaseem abu yaymasa godiyaba balle akai ga addu’a ma baki ɗaya. Sallama Qaseem yay masa ya sakko, sai da ya leƙa ɗakin Bilkisu yaga sunyi barci ita da Aamilah sannan ya wuce sashensu zuciyarsa najin daɗin ya kusa mallakar bilynsa.4
★★★★★★1
           A ɓangaren Jawaad kuwa bayan an idar da sallar asuba yanayin azkar ya fita daga massalacin, motsa jiki yaɗan zagayo ya koma gidan Alhaji baba, a falo ya iske tsohon zaune yana duba wani littafin addini, Jay ya gaidashi da girmamawa kafin su koma tsokanar juna, ganin lokaci yaja ya miƙe yana faɗin, “Bara nai wanka nazo naje gida na shirya daga can na wuce office”. Cikin zolaya Alhaji baba yace, “To agogo sarkin aiki”. Dariya Jay yayi yana miƙewa da faɗin, “Nikam sunayen da kake jeramin sun isa hakanan”. Alhaji baba yace, “To gwauro na daina”. Juyowa Jawaad yay zai bashi amsa hannunsa ya tanƙwaɓi ɗaya daga cikin hotunan da Alhaji baba ya jera saman wata ƙyaƙyƙyawar drawer dake hanyar shiga bedroom. A take hoton ya kifo ƙasa ya shiga bada ƙarar fashewa…………….✍
Gaisuwa da tarin fatan alkairi a gareku ƴan wattpad, wannan page ɗin yau nakune ku kaɗai, kuyi birgima a ciki ku more😂😘😘😘😍😍😍.
75
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
    
            32
Page 20
……………..“Ya salam” Jawaad ya faɗa tare da ranƙwafawa ya ɗaga frame ɗin da hoton ke ciki, a bisa tsautsayi ya ɗaura hannunsa kan glass ɗin da ya maƙale kaɗan bai ida fitaba, yay tsini siriri, “ouch!!” ya faɗa yana yarfe hannunsa saboda shigar zafin bazata. Alhaji baba ya taso da hanzari garesa, hannun da yake yarfewar ya kama, abinka da jiki babu wahala tuni jini sai rige-rigen fita yake, abin mamaki har yana neman wuce girman ciwon da yajin. Daga Alhaji baba har Jawaad sai fitar jinin da yawa ta basu mamaki, dan sosai yake ɗiga a ƙasan tiles ɗin tamkar wanda yay wani uban yanka, Jawaad yay ƙoƙarin ajiye hoton saman drawer batare da ya kallesa ba sai kawai ya sake ɗora ƙafarsa akan glasess ɗin dake zube ƙasa. Da sauri ya ɗaga ƙafar tare da sake damƙe hoton a hannunsa yaja da baya yana faɗin,  “Yah ALLAH”. 
        Alhaji baba yace, “Subahanallahi sake takawa kayi?, to kaga zauna ina zuwa”. Zama Jawaad yayi ya ɗora fasashshen frime ɗin da ya rage katako da katin hoton kawai a cinyarsa yana tarbe ɗigar jinin hannunsa da ɗayan hannun wanda tuni jinin ya ɗiɗɗiga a hoton ma. Sai dai hankalinsa bai kaiba, har Alhaji baba ya dawo ɗauke da ruwan ɗumi a roba mai ɗan faɗi da guntun towel, a hannun kujerar ya ɗora ya kama hannun Jawaad ya saka a robar tare da jiƙo towel ɗin da ruwan zafi ya goge masa hannun tas dukda dai jinin yaƙi tsayawa har yanzu yana ɗiga, kamar yanda sukai hasashen ɗan yankan bawani mai yawa baneba,  tissue ya warwaro ya ɗora masa dai-dai yankan yana mai tsokanarsa da cewar, “Lallai cin kayan daɗinka yay yawa na wajena, kaga ɗan yanka kaɗan amma jini yayi rabin botiki”. Babu shiri Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, “Oh ALLAH, tsohon nan kana hawa kaina da yawa wlhy, idan yakai rabin botiki ai saidai a ɗiba naka a ƙaramin kenan”. Dariyar alhaji baba yake shima, ya durƙusa tare da kamo ƙafar Jawaad ɗin itama dake jinjin ya saka a robar, kwalbar data sokesa anan tana ciki, hakan yasa Alhaji baba shammatarsa ya cirota, “Ouch!!” Jawaad ya faɗa yana rintse ido dan yaji zafi, ciwon ƙafar yanada ɗan girma, Alhaji baba ya ɗaure masa dan su samu jinin ya tsaya.
         Batool ce ta shigo da sallama ɗauke da abincin kakan nasu. A tsorace take kallon jinin da ƙafar Jawaad ɗin, “Ɗan uwa garin yaya haka?”. Fuska yaɗan yamutsa yana kallonta, yace, “Tsautsayi mana”. Sannu ta shiga jero masa, ta ajiye basket ɗin ta ƙaraso ta amshi tsintsiyar hannun Alhaji baba danta share kwalban kamar yanda taga yana niyyaryi. Jawaad ya sake kai hannu zai ɗauke hoton daga cinyarsa dan yanason ya tashi yaje yay wanka, sai idanunsa suka sauka akan waɗanda ke jikin hoton, dukda jininsa dukya ɗan ɗiɗɗiga a jiki, hakan bai hanashi ganin fuskar mahaifiyarsaba ras a jiki, tayi ƙyau sosai tana murmushinta mai birgewa, ya maida idonsa akan ta kusa da ita, autarsuce da suke kira aunty Mammah, itama ALLAH yay mata rasuwa shekaru masu tazara bayan ɓatan mahaifiyarsa, haka kawai ya samu kansa da tsura musu ido harna tsahon lokaci, sai da Batool ta ɗauke hoton daga hannunsane ya dawo hayyacinsa. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke yana miƙewa. Batool dake kallon hoton tai murmushi da share guntayen hawayen da suka cika mata ido saboda tuno da Gwaggonnin nata guda biyu da suka rasa a ƙaddarar mutuwa da ƙaddarar taɓin hankali.
            Koda Jawaad yay wanka ya kimtsa ya fito bai zauna cin abincin da Batool ta kawoba, sai ya ɗauki hoton daya fasa zai tafi dashi akan zai sabunta masa glass, babu yanda Alhaji baba baiyiba amma yaƙi ya ajiye. Cikin tsokana Batool tace, “ALLAH yasa ba sace maka zaiyiba Alhaji baba”. Harararta Jawaad yay ya fice, batare da ya jira amsar da Alhaji baban zaiba Batool ba.
     Maimakon ya nufi gida kamar yanda yay niyya sai kawai ya wuce office, ta waya ya kira Gimba yasanar masa shi yana office anjima yazo ya samesa zasu fita. Cike da girmamawa gimban ya amsa masa sannan suka ajiye wayar.
      Koda Jawaad ya shiga station kai tsaye office ɗin Jabeer ya nufa, shima da alama bai jima da isowarba, ya ɗago yana kallon Jawaad daya shigo office ɗin da sallama, murmushi yay masa, shikuma Jay ya hararesa yana ƙarasowa ya zauna a kujerar dake gaban tebirin ɗin.  Hannu ya miƙa masa sukai musabaha, murɗe hannu  Jay yay har saida Jabeer yay ƴar ƙara, ya fisge yana hararsa da faɗin, “ALLAH kai mugune na bugawa a takarda, ciremin hannun zakayi boss”. Murmushi Jawaad yayi yana miƙa masa key ɗin motarsa da faɗin, “Gobema ka sake yin gulma”,.  Jabeer ya sake hararsa yana juya hannunsa, “Kasan ALLAH Jay, yau da ace ba sunan momine da itaba da akanta zan rama, ALLAH ya ceceta kuwa”. Murmushi Jay yayi yana taɓe baki, yace, “Kaje ka rama mana ina ruwana, Am sorry jiya na maka tsawa, rainane duk a jagule kaikuma kazo zaka sake cazamin kai da naka shiriritan”.
        Murmushi Jabeer yay yana shafa kansa dajin ƙaunar abokin nasa cikin rai, “Ni dama ban ɗaukesa komaiba, nasan wanene Jay ɗinmu idan yay fushi, ina fatandai itama Momin tamu ka bata haƙuri, dan na koma office ɗinka kusan 3:45 na isketa tana kuka”. Haɗe fuska da lumshe idanu Jay yayi yana sauke numfashi, “Ai  yarinyarnan bata da kunya. manta da zancenta, ina fatan su Hafiz sun iso, dan inason muyi magana”. Kamar yanda ya buƙata sai Jabeer ya bar zancen bily, ya amsa masa da, “Okey bara na kirasu to, nasan duk sun iso yanzun”. Gyara zama Jay yay, yayi shiru har Jabeer ya gama kiransu. Babu wani jimawa sai gasu duk sun shigo, saida suka gaggaisa sannan kowa ya nema wajen zama, Aliyu da idonsa ya sauka akan yatsan Jawaad dake naɗe da bandage yace, “Boss miya samu hannun kuma haka?”. Hannun Jawaad ya kalla yana ƙaramin tsaki, “Wlhy Aliy wani ɗan ciwo naji, shinefa Alhaji baba yaymin wannan naɗin”. Dariya duk sukayi, Hafiz yace, “Shi ka kaima fushin jiya kenan?”. Hararsa Jay yayi amma baice komaiba.
          “Kunga ku ajiye shiritarnan taku muyi magana yau inada aiki a office saboda jiya banyi komaiba”. Duk hankalinsu suka maida gareshi, Jabeer ya direma kowa kofin coffee daya haɗo, “Thanks ” Jawaad ya faɗa yana ɗaukar kofin, suma su Hafiz sukai masa godiya, Jawaad yakai kofin bakinsa sanan ya janye idonsa a kansu, sai dai yay matuƙar canja fuska saboda maganar da zaiyi tana zafarsa a cikin rai, “Guys dolene yarinyarnan tabar cikinmu a wannan karon, bazan iya cigaba da zama da itaba ta isheni haka nan”. Kallon juna suka shigayi kowa da tsoro akan fuskarsa, Aliyu yay ƙarfin halin faɗin, “Wa kake nufi a cikinsu boss? Kasan yanzu sun zama su biyu”. Kallon Aliyu yayi tamkar bazaice komaiba, sai kuma cikin takaici yace, “Rose nake nufi”. Shiru sukai duk suna jinjina zancen a ransu, kafin Hafiz yace, “Banƙi ta takaba Boss, sai dai hakan zai iya zama wata matsala daban, duk da bansan ainahin abinda tai makaba na kula tanason takurama rayuwar mami ne, abinda kuma na fahimta itafa gani take son Mami kake gaskiya shiyyasa take duk waɗanan abubuwan”. Tsaki Jawaad yaja yana yamitse fuska cike da takaici amma baice komaiba. Suma shirun sukai basu damu da rashin bada amsarba, dan a ganinsu idan son Bilkisu yake wataran ai dole ta fito fili ko. Jabeer ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Gaskiya boss hakan ba shine mafitaba, na farko Rose tasan sirrikanmu da yawa, yaƙi take akan soyayyarka a yanzu, idan kace ta barmu zaitai amfani da wannan fushin ta koma cin dunduniyarmu, munada muhimman ayyuka a ƙasa waɗanda munyi zurfi sosai na kaiwa ga nasara, sune zata fara harin ɓatawa, karka manta zagaye muke da maƙiya, ƙaramar ƙofar da za’a kutsa cikin mutuncinmu kawai ake nema dama, magana ta ƙarshe kuma Rose zatabi duk hanyar da zuciyarta ta ƙawata mata ta cutar da mai sunan mom batare da munsan tayaya ta shirya hakanba, kaga kuwa tako ina korarta ba mafita zata bamuba, domin iyakar gudunmu dai bai wuce kabi ta ƙasa kasa aimata transfer ba, duk nisan da kake tunanin zatayi damu ALLAH saita dawo koda ta hanyar saka wanine yay mata aiki kuwa”.
      Dukansu sun gamsu da maganar Jabeer. Aliyu yace, “Maganar Jabeer fa gaskiyace Jay, sawa tabar cikinmu ba mafita bace, gara ace muna ganin duk motsinta, sannan ni a ganin idan kanason Mami ɗin miza hana ka fito ka bayyana mata kawai a wuce wajen, da zafi-zafi ake bugun ƙarfefa a wannan zamanin”. Fuska sosai Jawaad ya haɗe, cikin nuna halin ko in kula ya wani taɓe baki yaƙi cewa komai a karo na biyu kan maganar Bilkisu. Duk idanu suka zuba masa na mamaki, sun rasa miyake ɓoyewa. Sai da ya shaƙi iska dan kansa sannan yay magana, “Kuna ɓatamin rai da shirmennan naku, kunefa dalilin shigowar wannan yarinyar cikin tawagarnan, amma miyasa kuke son maida zancenta wani abu daban, to inagama ba rose bace ta cancanci yin nesa damu, Miemaa zansa aima transfer, ince dai shikenan”.
     Da sauri Hafiz yace, “Ba shikenanba, yarinyarnan yanzune ta fara aiki, ƙwazon data fara nunawa yana buƙatar a cigaba da horar da ita akan gaskiya, munji ba sonta kakeba, kuma insha ALLAH babu mai sake maka wannan maganar, inaga kawai mu zauna dasu ita da Rose kajama Rose dogon gargaɗi akan wannan haukar tata mara tushe, domin munutsu mu fuskanci sauran ayyukan dake gabanmu, yanzu aikinan da muke wlhy yanada matuƙar sarƙaƙiya da haɗari, amma gashi muna wasa dashi, sai dau ku yaya kuka gani?”. Jabeer dake wani shegen murmushi yana satar kallon Jay yace, “Hakan yayi nidai a wajena, gara a bar mana Miemaar mu muyita kwasar albarkacin sunanta”. Hafiz da Aliyu sukai dariya, dan sunsan shaƙiyancin Jabeer ne ya motsa, Jawaad kam uffan baiceba, saima miƙewa da yayi yay musu sallama ya fita.
     Yana fita duk sukayi dariya, Aliyu yace, “ALLAH Jabeer kasama boss ido da yawa, nakula son ƙureshi kake kawai,, ka barshi yasha iskar duniya malam”. Nanma dariyar sukayi, Hafiz yace, “kunga nima bara na koma Office, gayenan addu’armu kawai yafi buƙata”. “Hakane kam” cewar Aliyu dake miƙewa shima.1
STORY CONTINUES BELOW
           Fitowar Jay daga office ɗin Jabeer yay dai-dai da fitowar Bilkisu daga motar Qaseem suna murmushi ma juna, dukda a sama yake kuma ta glass yake ganinsu hakan bai hanashi ganin murmushin yamata ƙyauba, dayake ba yawan ganin murmushin nata yakeba sai yazam idan tayi yakan kasance na musamman, ya taɓe bakinsa yana barin wajen.
       Bilkisu kam da batasan yanayiba rakkiya tayoma Qaseem dake bata labarin maganar da sukai akan aurensu jiya da Dad.
      hakan sai yasani jin daɗi da raguwar nauyin da zuciyarta tayi tun a daren shekaran jiya, a ganina garama nai auren na huta, dan na kula zamanmu a haka haɗarine babba a gareni, maganganun Dad na jiya akan fyaɗen mai aikin su Nazifa ya mugun tsaya mani a rai, inada yaƙinin irin wannan ƙaddarar ta afka tsakanin ni da ƴaƴansa to wlhy nikaɗai zanyi kukana, dan tabbas zai goya musu bayane, a yanda kuwa Yah Qaseem ke kaima jikina hari da halayyar Salman da batai minba komai zai iya faruwan, to maganin ayi kar a fara kawai.
         Saida nai masa rakkiya har office ɗinsa sannan na juya na sauka namu, saida na gaisa da kowa sannan na zauna mazaunina, Computer ɗin gabana na kunna domin duba gajeren video da boss ya bani nai sharhi akan abinda na fahimta ciki, gaba ɗaya hankalina na maida akan aikin har Ummie data makara yau ta shigo, gaisuwa tayi da sauran sannan ta matso inda nake ta bani hannu muka gaisa idonmu akan video mu duka. “Bily jiya wai miyasa kika gudu bayan kinsan magana mai muhimmanci muke tattaunawa a group?”. Murmushi nai mata ina cigaba da control ɗin mouse ɗin Computer a hannuna na haggu, na damar kuma ina riƙe da pen ina rubutu a takarda. “Hankalina ne yay masifar tashi Ummie, al’amarinne akwai ruɗani a ciki, dan na fara zargin mai aikata ɓarnarnan ba mutum ɗaya bane sai dai ƙungiya garesu”. Kujera ta jawo ta zauna saɓanin da da take tsaye ta ranƙwafo jikin tebirina, tace, “Miyasa kikai wannan tunanin bily?”. Kallonta naɗanyi na ɗauke kaina ina cigaba da aikin gabana, nace, “Saboda Amina mana, kinga su su Nazifa a gida ɗaya akai musu ita da marigayiyya, sai kuma na yarinyar jiya, amma ita Amina ai a gidanmu akai mata, yanda ake salon fyaɗen duk iri ɗayane, sai an bugar dasu ake cutar dasu, sannan babu wandda ta taɓa ɗaukar ciki a cikinsu, zuwa yanzu ina buƙatar mu haɗu waje ɗaya mu duka biyar ɗin, dan yadace mushiga binciken neman sauran waɗanda hakan ta faru garesu, inaji a jikina Ummie basu kaɗai bane akwai wasu”. Na ƙare maganar da kallonta idanuna cike da ƙwalla. Kanta ta girgizamin a hankali alamar karnai kuka, na ɗauke kaina ina haɗiye abinda ya tokaremin maƙoshi mai nauyi da ƙyar.
        Nuna mata Computer ɗin nayi ina zooming ɗin wani waje cikin video ɗin da faɗin, “Ummie kalla dan ALLAH mikika fahimta a wajen nan?”. Matsowa tayi sosai tana kallon wajen cike da nazari, kafin ta amshi mouse ɗin hannuna ta maida video’n slowly, “Kai bily kilura da ƙyau wani kasuwancin kurame akeyi a wajen nan fa, ki kalli zuwan yarinyarnan wajen da ƙyau, kafin ta ƙarasa wajen shi wannan mai kifin saida suka kalli juna da mai raken can sukaima juna wata inkiya da idonu, sannan bakin mai kifin ya motsa alamar magana yayi”. Kaina na shiga jinjina mata, nace, “Haka nima duk na fahimta Ummie, to amma sam na kasa fahimtar mi mai kifin ya faɗa, na maimaita wajen yafi sau goma wlhy, amma kuma abin lura anan shi wacan mai facin minene ya ɗauka cikin tayoyi ya bama gurgun yaron can almajiri?”. Baya ummie ta dawo da video dai-dai wajen, da alama mai ɗaukar video bai saka da mai facinba a ɗaukar, dan acan gefe yake yana harkokinsa shi kaɗai, hakan yasa ba komai ake iya fahimta dangane da shiba. “Bily kinsan mizakiyi?” nace, “A’a saikin faɗa”.  kije office ɗin boss kimasa bayani, inba hakaba zamu iya rikita komai anan”.
     Gabana ne ya faɗi jin ta ambaci boss, abinda ya faru jiya ya shiga mani kaikawo, gashi yau yanda na lura baije duba aunty Shahudah bama tun jiya da safe kamar yanda naji iyayenmu na tsogumi a asibitin, ALLAH dai yasa ba maganata bace ta jawo hakan, dan yakamata ace ya cika alƙawarin daya ɗaukama Dad na zuwa gidanmu a daren jiya……… “Lafiya kuwa? Ina magana kin tafi tunani”. Numfashi na kawo ina dafe kai, nace, “Babu komai, bara nakai masan”. Nasan yanda nai maganarne a sanyaye ya sakata bina da kallo, ban yarda mun haɗa idoba na cire flash  ɗin daga Computer’n na ɗauki takardun danake rubuta bayanan na tattare cikin file ɗin daya bani jiya na fita. Maimakon na nufi office ɗin nashi saina tafi office ɗin Oga Aliyu. knocking nai aka bani izinin shiga, su biyu na iske a ciki, hakan yasani gaishesu na tsaya gefe su kammala, dan naga magana suke. Basu wani ɗauki lokaciba wancan ya miƙe ya fita, oga Aliyu ya nunamin kujera alamar na zauna, sake gaidashi nayi sannan na zauna ina ɗora takardun hannuna a tebirin gabansa. “Mami ta samune?” yay maganar cikin zolaya. Murmushi nayi nima na bashi amsa da “Sosai ma”. Yay ƙaramar dariya yana amsar takardun, “To ALLAH yasa mai washa-washa ne da zamuci mu more”. Yanzunkam saida naɗan dara kaɗan, dan bansan yana magana mai tsaho hakaba, yaɗan duba takardun sannan ya kalleni, “Mami ban fahimci komaiba anan, na minene?”. Hannuna naɗan matsa kaɗan sukai ƙara, na muskuta zamana, “Oga Aliyu bayanan daga wani video suke” nai maganar ina miƙa masa flash ɗin hannuna da cigaba da faɗin, “Nice na haɗasu anan, to kuma na cije a wani waje shine nazo neman haske”. shiru yay na sakanni batare daya amshi abin hannunaba, kafin yace, “Okey, wanene ya baki aikin a cikinmu?”. Nace, “Boss ne”. Takardun ya miƙomin, “Kinga to kije wajensa, dan bansan case ɗin miye ba, nasan zai miki bayanin duk da zaki fahimta”. Shiru nayi na kasa amsar takardun.
      Aliyu dake kallonta yace, “Da matsalane?”.
     Kaina na ɗago na kallesa, sai kuma na sauke idanuna ƙasa, “ALLAH oga shi ya cika faɗan tsiya, yaytama mutane mazurai”. Dariya sosai Aliyu yayi da wannan magana tawa, saida ya gaji dan kansa yay shiru, sake miƙomin takardun yayi har yanzu fuskarsa da murmushi, “Ai sai an masa ba daidaiba yake mazurai, tunda akan aikine zai fahimceki bazaiyi faɗaba kinji”. Kaina na jinjina masa, badan nasoba na amshi takardun na fita. Jinake kamar karnaje, amma wani sashe na zuciyata na bani shawarar naje dan akan aikine, bai kamata kuma na sanya wasa akan aikinaba, nidai na kiyaye duk wata hanya da zata sake haɗani dashi harnaga fushinsa kamar na jiya kawai. Da wannan ƙwarin gwiwar na nufi office ɗin, knocking nai aka bani izinin shiga, gabana sai faman faɗuwa yake na tura ƙofar da sallama a ƙasan maƙoshi na shiga.
          Tarin aikine jibge a gaban Jawaad, ko buƙatar shigowar wanima babayi office ɗin, hakan yasa koda Bily ta shigo  sallamarta kawai ya amsa amma bai ɗagoba, ƙarasowarta gabansa ƙamshinta ya tabbatar masa itace, sake ɗaure fuska yay sosai fiye da yanda ta shigo ta sameshi.
        Kallo ɗaya naima fuskarsa na ɗauke kaina, a ɗaure take fiye da kullum ma dana sani, gaba ɗaya ƴar jarumtar dana shigo da ita saita gudu itama, gashi yaƙi kallon ko inda nakema dukda inada tabbacin yasan nice na shigo. Da ƙyar na iya daurewa nace, “Ina kwana Sir”. Batare daya kalleniba yanzunma yace, “Lafiya”. Shiru nai nakasa cigaba da magana, dan yanda ya amsa gaisuwar tawa a daƙile ya sake sanyayamin jiki sosai, ganin tsayuwar tawa bata da amfani na daure nace, “Sir dama akan aikin daka bani ranar monday ne”. Harna fidda rai da samun amsa sai naga ya nunamin kujera batare daya ɗagoba. Ɓoyayyen nunfashi na sauke ina ƙara ƙoƙarin ƙarfafa kaina. Na ajiye takardun hannuna a gabansa kafin naje na zauna a kujerar, shiru muka sakeyi na mintuna, saida ya tattare wasu takardun gabansa waje guda ya ajiyesu gefe kafin ya kalleni. Saurin nuna masa takardun dana ajiye nayi. Janye idanunsa yay daga tsatstsarenin da yay dasu ya ɗauki takardun, shiru tsawon wasu mintuna yana dubasu kafin ya ɗago, yace, “Kin gama ne?”.
         Sau ɗaya na kallesa na ɗauke idanuna ganin ni yake kallo, na girgiza kaina, “A’a ban gamaba, akwai wani wajene a video’n to sai nakeson ka gani kafin na shigar da bayanansa” na ƙare maganar da miƙa masa flash drive ɗin, bai amsaba ya ɗauke kansa daga gareni ya maida ga Computer ɗin gabansa, “Taso kisa”. kamar nai kuka haka naji, sai dai bani da wata mafitar daya wuce bin umarninsa, inda yake naje, a mamakina sai naga ya tashi daga kujerar tasa ya nunamin alamar na zauna, batare da yace uffanba…………✍
8
Yau shafin nakune ƴan telegram, kuma ku warwasa da wannan, alkairin ALLAH yakai gareku aduk inda kuke, ammafa babu canji mun ƴan hud-jay team ne😜😂😂😂😍😍😘😘😘.
8
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.10Page 211
……………Kallonsa nai ya zubamin harara, babu shiri na ɗauke idanuna na zauna kamar yanda ya buƙata a lallausar kujerar tasa dariya nazomin a cikin rai, danni mamakin yanda ya iya harara wa mutane nake, sai kace wani mace. Da ƙyar na iya riƙe dariyar daketa son fallasa na saka flash ɗin a jiki, duk abinda nake yana tsayene a kaina harna kunna video ɗin. Har ya kai karshe ya sake komawa baya baice komaiba, ganin mun maimaitashi sau uku yaƙi magana saina juyo dan inga koma dai nikaɗai nake kallon. Mamaki ya kamani ganinsa tsaye a bayana hannayensa duka biyu cikin aljihun wandonsa, idanunsa akan Computer alamar duk yana kallona. “Idan kin gama kallon nawa saiki nuna inda baki ganeba”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa, kamar wani mai tsoron a jisa.
      Fuska na kumbura tare da ɗauke kaina, a raina nace, ‘Kai wama ya kaika iya kallon mutane’. hannuna na ɗaura saman mouse ɗin nai zumin dai-dai wajen mai faci ina faɗin, “Akan mai facin nan ne dama, kamar akwai alamar tambaya dangane da shi, dan……” kasa ƙarasa maganar nai saboda kusancin da muka samu, a dalilin ranƙwafowar da yay har munajin saukar numfashin junanmu, ya ɗaura hannun hanggunsa saman table ɗin, na damar kuwa saman nawa dake kan mouse. Da sauri na rumtse idanuna, tare dayin azamar janye hannuna dake ƙasan nasa, saboda wani mugun harbawa da zuciyata tai. Baice komaiba, shikam ko a jikinsa, saima ƙoƙarin maida video slowly da yay. Nayi matuƙar takura da tsorata da wannan kusancin namu da yay matuƙar yawa, har takai jikina ya fara rawa, idanuna suka ciko da ƙwalla, sam bana fahimtar bayanin da yakemin ma, dan sama-sama nake jin sautin muryarsa.
     Jawaad da duk abinda yake akan sani yayisa ya juyo yana kallonta, ta rumtse idanu zufa dukta tsatstsafo mata a goshi tamkar babu ac a office ɗin. “Hummm” ya faɗa acan ƙasan maƙoshi ya janye jikinsa. A mamakinsa sai yaji ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, hawaye sun silalo saman kumatunta, saurin ɗauke kansa yay tamkar bai ganiba.
         Har bigewa nake da shi wajen rawar jikin miƙewa daga kujerar jin ya matsa, na goge hawayen dake bin kumatuna batare da na bari ya ganiba, gefen tebirin na koma na tsaya kaina a ƙasa nace, “Sir, bara kawai naje can dashi saina ƙarasa tattara bayanan”. Jawaad da har yanzu yake binta da kallo yaɗan lumshe idanu ya buɗe yana ƙoƙarin danne dariyar dake son kufce masa, murya a daƙile yace, “Barshi zan ƙarasa, ɗauka waɗanan files ɗin ki kaima Hafiz, zuwa anjima ki dawo zamu fita”. Bawani fahimtarsa nakeba, kai kawai na ɗaga masa na ɗiba files ɗin na fice cikin sassarfa. A raina banda takaici babu abinda nakeji, miyasa halin mazan wannan zamanin kusan duk ɗayane? Burinsu kawai su taɓa macen da ba muharramarsu ba a matsayin wayewa, ashe shima mutumin nan haka yake ban saniba?, “Aikam na daina sakar masa fuska wlhy” na faɗa a fili cike da takaici.10
★★★★
       Ƙarfe biyu muka fita cin abinci ni da Ummie, sai da muka gama nai ƙoƙarin biya sai nagama kuɗin dake jikkar tawa bazasu isaba, kusan koda yaushe Ummie ke biya mana inhar bada Yah Qaseem mukazo ba, sai naga da kunya hakan tacigaba da faruwa ai, ATM ɗina na shiga lalube dan na basu su cire, amma sai shima ɗin dai ban gansaba, gabanane ya shiga faɗuwa, dan bama shi kaɗaiba duk cards ɗina basa ciki kenan tunda a tare nake ajiyesu waje guda, kuma inada tabbacin itace jikkar danasan na fita da ita daga gida last. “Wai mikiketa lalube hakane kamar wata makauniya?” Ummie dake shan ruwa ta faɗa bayan ta ajiye kofin. Guntun tsaki naja ina mai bata amsa da, “Ai namafi makauniya yau Ummie, wlhy banga duk Cards ɗinaba, kuma inada tabbacin anan ciki suke”. Tasowa tai tana tayani, sai dai kumafa da gaske babu ɗin, hankalina yayi matuƙar tashi, “Ummie na shiga uku, a ina na jefar nikam?”. “Bily bazan saniba, amma nasan baki da mantuwa, yaushene rabonki dasu?”. “Ummie A ranar lahadi fa da hannuna na sakasu cikin nan dazan fita”. Tace, “Ai da sauƙima, ki tuna ranar ina da ina kikaje tunda kin tabbatar a ciki suke?”. Zama nai idona cike da kwalla ina tunano dukkan abinda ya wakana a wannan yinin, da sauri na kalli Ummie, “Ummie idanma har yardawa nai to bazai wuce wajaje biyu ba wlhy”. Ummie tace, “Ina da ina ne?”. “Saloon da wani garden, amma bara na bincika a saloon ɗin dan inada Number ma’aikaciyarsu ɗaya”.
       Ummie ta biya kuɗin muka fito a wajen, sai da muka koma office sannan nai kiran Number danai saving da Ladies mirror, bugu biyu kuwa aka ɗaga, bayan mun gaisa nace, “Dan ALLAH kiyi haƙuri, na kiraki maybe ba’a lokacin daya daceba”. Daga can tai dariya da faɗin, “lah babu komai”. Nace, “Okey ngd, ranar danazo wajen nan naku ina tunanin na yarda wallet ɗina, sam hankalina bai kaiba sai yanzu, ina fatan anan na yardar ɗin?”. tai ɗan jimm na wasu sakanni kafin tace, “Eh tabbas anan kika yarda, amma bata wajenmu, tana masarauta wajen su aunty Amaturrahman, dama sunbar saƙo akan idan kinzo nema a baki card ɗinsu, yanzu yaya za’ai kenan?”. Wani sanyi naji ya ratsani, na sauke numfashi da cewa, “Babu damuwa, idan na tashi aiki zan biyo na amsa, nagode sosai”. ta amsa da “Babu damuwa, sai kinzo”. Bayan mun kashe wayarne na faɗama Ummie duk yanda mukai, daga ni har ita mamaki muketayi na cewar wallet ɗin na masarauta.
          Ban samu kiran boss ba kamar yanda yace zamu fita har lokacin tashi yayi, zuwa nai na sanarma yah Qaseem ya wuce gida ni zamuje nida Ummie wajen wanke kai, yanzunma da damuwa na iskesa, dan haka bai wani jamin zanceba yace mu haɗu a gida. Nidai al’amarin nasa sake ɗauremin kai yay yanzunma, har muka isa Ladies mirror banbar mamakin wannan canjin nasaba. Sosai Ummie ta rikice da haɗuwar wajen, harda ma kanta alƙawarin zuwa wannan weekend ɗin su mata aiki, bamusha wata wahalaba muka samu wadda na kira ɗin, ta bani card ɗin da suka bari. bamu daɗeba muka fito dan magriba ta gabato.
         Ummie ta ajiyeni a gida ta wuce, koda na shiga saina iske an sallamo auntu Shahudah, falon cike da dangin Momy, da sukazo dubata, nidai na gaishesu itama nai mata yaya jiki na wuce, saboda a rayuwata na tsani kallon wilaƙanci, sukuma naga alamar indai ba nasuba to kowa banzane. Wanka na farayi harda wankan tsarki saboda baƙona ya gudu,  na fito na gabatar da sallar magriba nai azkar, ina zaune a wajen har aka kira isha’i, har lokacin inajiyo hayaniyar ƴan gidansu Momy, dukda yunwar da nakeji saina zaɓi haƙura na kwanta a haka, ɗan kayan maƙulashen da yah Qaseem ke yawan siyamin nakan ajiye a ɗaki su nai zamanci, gefe guda kuma ina ƙoƙarin kiran Number jikin card ɗin da aka bani, saida ta kusa tsinkewa aka ɗaga, munyi gaisuwa da wadda ta ɗagaɗin a mutunce dukda bansan wacece ba, kafin na mata bayanin kaina. Nayi mamakin yanda tai saurin ganewa, kai tsaye tace na tura mata address ɗin inda nake kawai, zasuzo su kawomin har gida. Sosai na ƙara mamaki da jinjina ƙyaƙyƙyawar tarbiyyarsu gaskiya, sam basuda girman kai tamkar ba waɗanda suka fito daga babban gidaba. Godiya nai mata mukai sallama, ban zauna ɓata lokaciba na tura mata number dan inada buƙatar cards ɗina su dawo hannuna da gaggawa.
            Jin gidan yayi shiru yasa na miƙe, dan fitar motoci da naji ya bani tabbacin duk sun wuce, ƙaramin hijjab na saka saman wando da rigar kayan barcina kalar ruwan hoda na fito, wata irin muguwar yunwa nakeji wlhy, rabona da abinci tun wanda mukaci da Ummie da rana. Babu kowa a falon duk sun tafi, na wuce kicin hankalina kwance, plates kawai nagani zube wanda sukaci abinci, sai dai babu komai a kulolin duk an cinye, cike da haushi na fara ƙoƙarin ɗora noodles dan bazan iya haƙurin kwanciya banci komai ba, dan danan na kammala dafawa na fito, mamaki ya kamani jin ƙamshin turaren da banyi zatoba, zuciyata sai harbawa take da sauri-sauri, waige-waige na shigayi a falon, saiko idona ya sauka akan wanda zuciyar tawa ke rayamin,  tsaye yake dafe da ƙarfen benen dake falon waya a kan kunnensa, kamar koda yaushe ƙananun kayane a jikinsa, ido cikin ido muka kalli juna, nai azamar janye nawa ina damƙe plate ɗin indomie ɗina daketa tururi, inaji a jikina har yanzu kallona yake, hakan saiya haifarmin da tafiya a hankali kamar wata hawainiya harna shige lungun ɗakinmu ni da aunty Aamilah.
       Jawaad daya kasa ɗauke idanunsa a kanta har saida ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido da cije lip ɗinsa na ƙasa, sannan ya cigaba da wayarsa, bai wani jimaba sukai sallama ya maida wayar aljihu idanunsa akan lungun da bily ta shiga, cike da kasalar data saukar masa yanzun ya haye saman ya koma wajensu Dad da Alhaji baba da Uncle Nasir da sukazo tare suke tattaunawa.7
STORY CONTINUES BELOW
        Ban kawo komai a rainaba dangane da ganin boss gidanmu, tunda ai dama yayma Dad alƙawarin zuwa, sannan kuma ga aunty Shahudah ta dawo gida itama, abincina naci hankali kwance nai brush na kwanta domin na hutama raina.
       
ALLAH YAY DARE.
              Washe gari safiyar alhamis, koda na tashi sai naci karo da abubuwa uku na farin ciki sun samemu, na farko samun sauƙin aunty Shahudah da har aka sallamo daga asibiti a daren jiya, na biyu maganar aurenta da Boss bayan ansha gumurzu ya amince da ƙyar saboda saka baki da kakansa yay a maganar, na uku tsaida maganar aurena da Yah Qaseem bayan Dad yaje wajen dangin mahaifina ya samesu ashe a jiya da rana, an tsaida aurenmu rana ɗaya dasu aunty Shahudah bayan salla ƙarama da sati biyu. Koba komai na samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, dan nikam abubuwan dake faruwa na wannan lokacin suna matuƙar tsoratar dani da sakani firgici.
     Ban ƙara tabbatar da ina son Yah Qaseem ba sai da aka tsaida ranar auren nan namu, shi kansa wani sake lallaɓani yake da ji dani a yau, dukkan abinda zai saka a gidansa kuma sanda muke tafiya wajen aiki ya nema shawarata, hakama kayan lefe saida yace na faɗi duk abinda nake buƙata, nidai kunyace ta kamani nace kawai na bashi zaɓi.
       Sai dai abu mafi bani mamaki sune jama’ar gidanmu, musamman ma Momy, koda wasa ban taɓa tunanin zata goyi bayan aurena da Yah Qaseem ba, amma sai gashi koda a fuska bata nuna komaiba, saima shirye-shiryen gagarumin biki take na nunama sa’a akan babban ɗanta namiji da zata fara aurarwa. Yah Salman ne kawai da aunty Aamilah sun shafema idanunsu toka suna ƙara faɗaɗa hantarata da muguwar tsana akan ban cancanci zama matar ɗan uwansuba, ƙiri-ƙiri suke nuna hakan babu ko kara a wannan safiya, su Dad dai basu tsawatar musu ba, sannan basu goya musu bayansu ba, Yah Qaseem ne daifa da yay kansu da masifa har saida na roƙesa yayi haƙuri kafin yay shiru muka fito.
    Tom nidai lamarinsu bai ɓatan rai, Alhmdllh tunda wanda zan zauna dashi yana sona, sannan iyayensama suna sona, dansu ƙannensa sunce basayi miye a ciki. A dangima dai akwai ƴan adawa, dan harda inna zainabu faɗa taitama Dad akan haɗani aure da ɗansa da yay kamar yanda Aunty Aamilah take faɗamin cikin gori da tsana, wai acewar inna Zainabu duk ƴaƴan manyan mutane masu kuɗi abokan Dad Qaseem ya rasa wadda zaiso saini? Haka taita jaraba tamkar itace ta haifi Dad ko yah Qaseem ɗin.
       
     Duk wanda ya kalleni a office yau yasan banda wata damuwa tattare dani, dan waɗandama suke faɗin basa ganin dariyata yau sun gani harma da haƙorana, sai dai abinda ya ɗaure kaina da mamaki rai a ɓace naga Boss yau, dan koda nakai masa saƙo office baiko amsa gaisuwataba bayan sallama, sannan harna fito baice dani uffanba, idanunsa jajur, hakama jijiyar kansa duk sunyi ruɗu-ruɗu, duk sai naji babu daɗi, dan koba komai nima ranar danai ciwon mara ya bani kulawa da nuna damuwarsa a kaina, da alama kuma yau shima baida lafiyarne. Kasa zama nai waje guda nakoma office ɗinsa wai naji mike damunsa?, ‘kuji ƙarfin halifa irin nawa’ to aiko dai ban jiyota da daɗiba, dan fatattakoni yay tamakr zai gaggallamin marukama, ALLAH dai ya taimakeni na gudo. A ƙofar office ɗin mukaci karo da gimba kamar a rikice yake, nidai na bashi hanya ya shige ko gaisuwa bamuyiba, sauka nai ƙasa abina ina ƙunƙunai, ban sakebi takansaba har aka tashi aiki kuwa, sai a wajen Ummie nakejin gulmar wai taga boss ya fita ɗazun ransa a ɓace kamar zai tashi sama, ban kulataba ita da zancen nata, dan haushinsa nakeji akan abinda yaymin ɗazun..6
        Mamaki yay matuƙar kamani da muka isa gida na iske aunty Shahudahr data kwana biyu a asibiti rai a hannun ALLAH zaune suna hira mai nuni da tsare-tsaren biki, a raina nace, ‘Dama ciwon so ke damunta ashe, ta samu yanzu kunga ta miƙe harda tsara biki kamar wani auren farko mtsoww’ na ƙare zancen cike da takaicin da bansan dalilinsaba nima. koda nai sallama basu amsaminba sai Momy kaɗai, sannunma ita kaɗai taimin hakama amsa gaisuwata, jikina duk sai yay sanyi, na wucesu ƙwalla na cikamin idanu, nasan dolene saina sake ɗaura ɗammarar haƙuri kam, dan matsalolin dama sukafi haka zasu biyo baya akan aurena da Yah Qaseem, har nai wanka na fito hawaye basu daina gudu a idanunaba, bayan sallar isha’i saima naji gidan tsitt, koda na leƙo iskewa nai duk fita sukai, daga ni sai Yah Qaseem dana iske a d/table yanacin abinci aka bari gidan da alama, zama nai mukaci tare muna ƴar hira, bayan mun kammala ya fita sashensu ni kuma na koma ɗaki nai shirin kwanciya dan barci nakeji kuma. Ina kwance har tara na dare barcin bai ɗaukeniba bankumaji motsin dawowar su Momy ba, sai naji wani tsoro na shigata a hankali, addu’a nai na kwanta ina fatan barci ya ɗaukeni mai nauyi kozan samu nutsuwa, UBANGIJI kuwa sai ya amsa roƙona barcin yay gaba dani babu zato.2
          ‘Innalillahi…’ na ambata cikin farkin barci lokacin da abinda ya faru kwanaki huɗun da suka shuɗe dana manta shi gaba ɗaya a raina yake neman maimaita kansa a wannan daren tamkar ranarma a yau, a matuƙar gigice na farka jikina na mazarin rawa haɗe da bugawar zuciya tamkar zata faso ƙirjina ta fito, na fashe da kuka ina mutsu-mutsun fita daga jikinsa, sai dai hakan ta gagara a yau, dan yaymin riƙo bana wasaba, ga bakina an ɗaureshi da yanda bazan iya maganaba . Wata irin siririyar dariya ya saki a cikin kunnena, yauma dai muryar tamkar irin ta wancan ce, “Hhhh sannu Jaruma, yauma na dawo gareki, ranar kinyi nasarar korata ko, to kisa a ranki yau duk gudunki bazaki iya tsereminba, harke wacece da kika isa ruguzani? Nazo miki da lallami ranar amma kikaƙi saurarata, hhhhhh ke baki isa zama matar aureba yarinya saina karɓi abinda yake nawa, gashi kina a cikin yanayin danafi buƙata ma kina haila, kina bani shikenan, dan samunsa bada igiyar aure a kankiba shine yafi komai muhimmanci, bakuma zan sake bibiyarkiba dana samu cikar burina, hhhh bilkisu kece kammaluwar nasarata, kece ƙarashen nasarorina, da dukkan wahalhaluna na tsawon shekaru zan cika nasarata! Hhhh taya kike tunanin zan bari ki kufcemin, ɗaura miki igiyoyin aure tamkar ni aka ɗaure da igiyoyinne, taya zan bari hakan ta kasance ban amshi abinda yake cikamakin nasarorina ba?, abinda naketa bibiya tsahon shekaru kenan, karki yaudari kanki da tunanin ranar kin tsira yauma zaki tsiran, namiki shiri sosai a yau bilkisu, na shiryama wannan ranar, dan tana cikin damammakin da idan na rasasu babbar asarace a gareni, bana asara yarinya sai dai nasara! hhhhhhh!……..”
          Duk wannan maganganun da yakemin a cikin kunne na zama tamkar wata gawace a kwance, gangar jikina ne kawai a duniya amma numfashina da tunanina basa tare da duniyar, ba’a maganar zubar hawaye ma dan waɗanan dama ke sakasu fitowa, wata irin hasala zuciyata keyi da kumburar ɓacinrai irin wanda ban taɓa tunanin inada shiba, haka kawai yau nakejin zuciyata ta bushe dukda inajin tsoron ya samu nasarar da yake fatan kuwa, sai dai ban fasa gayama UBANGIJINA ba, addu’a nake kawai ina ƙiyasta tunanin shaidar dazan iya barma koma wanene wannan shaiɗanin, bazanyi sake irin na wancan darenba a yau insha ALLAHU, koda ace zaici galaba a kaina nima saina ribantu dashi da izinin UBANGIJINA.
       Lokacin da naji ya sassauta min riƙon da yaymin yana shirin hawa kaina saina samu damar bada dukkan ƙarfina da yazomin daga mahaliccina wajen ƙoƙarin son tureshi, sam hakan bamai sauƙine a gareni, dan da alama ba ƙaramin mutum bane, danni sam kusani bana kawoshi a jerin aljanu, inada tabbacin mutum ne tamkar ni da rigar shaiɗanu. Wata sassanyar dariya maicin rai da nuna tsantsar mugunta da bushewar zuciya ya saki, tare da komawa gefena ya kwanta da faɗin, “Bara na baki damarki, kafin nai yaga-yaga dake yanda bazaki taɓa ganuwaba a safiyar gobe, na kula tausayin banza nake miki, tsaurin idonki yayi matuƙar yawa yarinyarnan”. Ya ƙare maganar da cire abinda ya ɗauremin bakina. Kukan zuci nake da babu hawaye ina kai masa duka ta ko ina da masa gargaɗi cikin zafin rai, “Karka cutar dani dan ALLAH, minai maka kake ƙoƙarin ɓatamin rayuwa?, kaji tausayin maraicina dan ALLAH, kobaka tsoron mahaliccinka ne? ina buƙatar zuwa da martabata gidan mijina tamkar kowacce mace mai mutunci, idan ka ketamin haddi wlhy ALLAH bazai barkaba, zan ƙare rayuwata ne wajen jifanka da munanan addu’oin da koka samu cikar burin naka saiya zame maka musiba, mugu azzalumi, ALLAH ya gagauta tona asirinka dama kosu waye kuke aikatama ƴaƴan mutane ɓarna, ALLAH ya ruguzaku sheɗanu, insha ALLAHU wutar jahannamace makomarku inhar baku tuba kun koma ga ALLAH ba tare da neman yafiyar bayin da kuke cutarwa, la’anannu masu ado da rigar musulunci suna cin dunduniyar bayin ALLAH, insha ALLAH bazaka cika burin nan nakaba koda kuwa kasamu nasara a kaina………
       Shiiiiii!!!! Ya faɗa yana dannemin baki tare da birkiceni ƙasa ya fallamin wani gigitaccen marin da komaina yay tsaye cak na wucin gadi kafin na ƙwalla ƙara, yasa hannu ya dannemin baki tare da kaina da azabar ƙarfi, kiciniya na fara dan harda hancina ya haɗa gaba ɗaya, tako ina yakushinsa nake dukda babu farce a hannuna sosai, hannunane ya sauka akan wuyansa, jin wani abu a ɗaure kamar sarƙan bit na samu damar fincikarsa da masifar ƙarfi saboda fita a hayyacina da nayi lokacin da numfashina ke gab da barin jikina…………….✍34
Ƴan WhatsApp kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi gareku baki ɗaya. Saura kuma yau naji wani yacema Yah Qaseem ko Dad kwarto🙄🚴🏼🚴🏼😍😍😍😘😘😘😍😍.22
       
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻23

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *