KWAI CIKIN KAYA CHAPTER B
BOOK1
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce👌🏼
Shafi na goma sha shida.
Babu editing yau kuyi manage😣🙄
………..Wai nikam kukan mi kike Sister? Ni yanzufa lamarinki har mamaki yake bani, akan Brother Jawaad duk kin zama wata lusara.
Hararar Aamila Hajiya Humaira tayi, hakan yasa ta ɓame bakinta.
Ta mai da kallonta ga Shahudah dake kwance a kafaɗarta, “Babie na tashi muyi magana”.
Tashi Shuhudah tayi zaune, Hajiya Humaira tace, “miya sakaki kuka?”.
Cikin tsagwaron taɓara Shahudah ta fara magana da shashshekar kuka, “Momy wai ni yau Bb yake iya cewa na zaɓi ciki koshi? Harni yake iya furtama zai saki akan cikin da bai gama zama mutumba ma, dama ashe baya sona ban saniba….”
Ta rushe da kuka tana faɗawa jikinta.
Hajiya Humaira tai murmushi tana buga bayan Shahudah, “Ba sonkine bayayiba Shahudah, wannan abun daya ambata miki ma shine ya nuna yana tsananin sonki, duk wanda yake son haɗa jini da kai aikuwa yana sonka Shahudah”.
Shahudah ta ɗago da sauri baki a kumbure, “Wlhy Momy baya sona, tunda har bazaiso abinda nake soba, ni gaskiya ban shirya haihuwa yanzuba, salon nazo na tsufa yaje yana kallon wasu a waje ko?”.
Dariya Aamilah ta kwashe dashi tana faɗin, “Tab ashe su wata ta kusa komawa jagwal, na rantse karma ki yarda, toke ta yaya kikai sake ciki ya shiga jikinki ma?”.
“Zanci ubanki Aamila, tashi kibar ɗakinnan” Hajiya Humaira ce tai maganar a zafafe.
Hakan yasa Aamila tashi ta fita tana ƙunƙuni da buga ƙafa na rahin samun isashshiyar tarbiyya.
“Mamana karki biyema Aamila kinji, ki kwantar da hankalinki akan wannan cikin tunda yazo a kuskure, koshi kaɗai kika haifa ya isa haka, zuwa nan gaban idan kinso saiki ƙara ɗin, kinsan dai Jawaad yanada Zuciya idan aka ƙure haƙurinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya faɗa, kuma Abbanku ma yaji faɗa zai miki, insha ALLAH haihuwar wannan cikin sai dai ya ƙara miki daraja a wajen Jawaad badai ya rage mikiba, ALLAH yasa ki haifa mana little Jawaad dai mu shine babban fatanmu”.
Shahudah dai da maganar bata gama shigarta ba tace, “Yanzu kowa dai baya sona a gidannan, ni wlhy barmuku ƙasar zanyi to, dama saboda shi na dawo cikinta, tunda ya fara wulaƙantani gara nai gaba abuna”.
“Kefa wata sa’in baki da man kai Shahudah, lokacin da ake nuna miki Annabi saiki ta ƙoƙarin rimtse idonki haba, banason shashanci mana, to wlhy ki tabbata inhar kika zuba da cikinnan ba Jawaad kaɗaiba hatta ni da Abbanku mantawa zamuyi dake shasha kawai mai girman banza”.
Yanda Hajiya Humaira ta fusata sai abun ya bama Shahudah mamaki, hakane yasaka ta tsura mata ido kawai, miyasa kowa kejin haushinta akan wannan cikin? Tana kallo Hajiya Humaira ta fice ta barta, kwanciya tai ta rushe da kuka, sai da tayi mai isarta sannan dabarar kiran Qaseem tazo mata.
Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, cikin kuka ta sanar masa da duk abinda ke faruwa.
Da farko shima kamar zai mata masifa akan zubda cikin sai kuma yay saurin haɗiyewa ya kwantar da murya.
“Haba Shahudah na, manta kawai da batunsu, koni banso kika ɗauki ciki yanzuba, amma kuma yaya muka iya, ni badan ina tsoron akan ance idan mata sukaje zubda ciki suna mutuwa ba da dakainama zan kaiki a zubar dashi gaskiya”.
“Broth da gaske wai ana mutuwar dan ALLAH?”.
“Da gaskene fa Dear”.
“Tab wlhy banson na mutu, amma kuma ai itama haihuwar wlhy ance ana mutuwa”.
“Eh amma ai kinga bakamar idan za’a zubar da cikiba, ki kwantar da hankalinki kawai kinji Sweetsister, ke dai kawai kina haihuwar wannan ki ɗauki mataki kinji”.
Haka yayta lallaɓata da kalamai masu sanyi harta aminta da zancensa.
Bayan sun ajiye wayar yay ƙwafa, wlhy badan shima yana da buri akan cikinnan na jikin Shahudah ba da sai ya sakata zubdawa koda ya baƙanta ran Jawaad, dan yasan zubda cikinnan ba ƙaramin sukar zuciyarsa zaiyiba, amma babu komai, idan yasha a wannan ai bazai sha ba anan gaba.+
STORY CONTINUES BELOW

Itakam Shahudah shawarar Qaseem ce ta sakata yarda zata bar ciki, amma wlhy saita rama wulaƙancin da duk Jawaad yay mata a gidannan, bazata sake ɗaga masa ƙafaba daga yanzu….
_______________________
BILKEESU
_______________________
Gidan nasu bawani mai ƙyau bane, ginine dai irin na masu ƙaramin ƙarfi, darene shiyyasa bazan iya ƙarar da komai ba dan gane da tsarinsa, gashi anguwar babu wuta.
Mun shiga da sallama bayan ya ajiye napep ɗinsa inda yakan ajiyeta, gidan shiru kamar babu kowa, sai muryar mutum ɗaya da najiyo ta amsa, ta fito tana ƙoƙarin ɗaura zaninta, amma ganinmu sai ta tsay turus tana haɗe fuska.
“Wannan fa?” ta faɗa muryar ta na ɗaukar zafi.
Ina jinsa yay gajeren tsaki, kamar bazai bata amsaba sai kuma naji yace, “Inna tai barcine?”.
“Ni ban saniba” tai maganar tana juyawa fuska a kumbure.
Kansa kawai ya girgiza ya nufi ɗakin dake can wani ɗan lungu yana min nuni dana biyosa.
Munyi sallama amma ba’a amsaba, ya ƙarasa shiga ɗakin nima ina biye dashi a baya.
“Inna harkun kwantane?”
Tsohuwar dake kwance mai tsananin kamanni da Innata ta ɗaga masa hannu cikin yanayin barci tana faɗin, “Uhm, ka dawo da wuri haka?”.
“Eh wlhy inna, amma ina tare da baƙuwane”.
Babu shiri ta tashi zaune, takai hannu ta ƙara hasken fitilar dake ajiye saitin fuskarta ɗakin yay fayau.
“Aibo baƙuwa daga ina kuma a tsohon darenan?”.
Sai da gabana ya faɗi dajin furucinta, amma amsar da naji ɗan nata na bata ce ta sakani sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya.
“Inna zan miki bayani da safe, yanzu dai gata nan bara na samo mata abinci wajen Lawusa”.
Kamar zatai magana sai kuma ta fasa, ta kalleni fuska babu walwala tana min nuni da wajen zama, zama nayi jikina duk a sanyaye, dan banga alamun zan samu karɓuwa ananba kam.
Muna zaune shiru kaina a ƙasa saiga Shu’aibu ya dawo ɗauke kula, a gabana ya ajiye yana faɗin, “ƙanwata maza kici saiki samu ki kwanta kinji”.
Godiya nai masa, na buɗe kular dan yunwa nakeji, Taliya da wakene a ciki, ban cutama kainaba naci na ƙoshi, dan rabon da na samu nutsuwar cin abinci haka tun ranada zan buge Jazuga.
Tabarma Inna ta bani, na shimfiɗa inda nake zaune na kwanta, filoma sai da ledar da Sani ya bani wadda bansan ko minene a cikina nai filo, kafin kace kwabo barci mai nauyi yay awon gaba dani.
Ban sake sanin halin da ake cikiba sai da asuba da inna ta tasheni nayi sallah.
Ina daga inda nai sallar ne na gaisheta.
Ta amsa min cikin halin ko in kula ta fice abinta, lallai nasan akwai matsala, a yanzuma batasan koni wacce ba ban damu karɓa daga gareta ba inaga ta ji wacece ni?.
Haka na zabga tagumi ina komawa duniyar tunanin yanda rayuwa take tamkar juyawar ƙarfunan agogo, wani lokacin sai kaga komanka nata maimaici bisa ga matsalolin rayuwa, idan kai wasa tuni kake aikata saɓo koda afurucine.
Shigowa inna da Shu’aibu ta katse mani tunani, na gaida shi bayan sun zauna.
Cike da fara a ya amsa yana tambaya ta ya baƙunta?.
Nai ɗan murmushi mai sauti ba tare dana iya cewa komaiba.
Hankalinsa ya maida ga inna daketa faman taɓe baki tana kallonmu, “Inna kinsan wacece kuwa wannan?”.
“Yazan sani baka faɗaba Aibo”.
Ƴar dariya yayi yana gyara zama, yace, “Kalleta da ƙyau dawa tai miki kama?”.
Kallona Inna tayi, sai kuma taɗan taɓe baki, “Yo kai banda abinka Aibo ina nake ganin fuskarta, tunda ta shigo gidannan banda sinne kai da take kamar sabuwar amarya mi takeyi”.
Saurin ɗago kaina nai na kalleta, sai dai kuma ban jureba na janye idanuna, amma dai nasan yanzu zataga fuskar tawa kamar yanda take buƙata.
Inajin yanda idanunta ke yawo a jikina, zuwa wasu mintuna kamar biyu tace, “Ina gano kamannin Zubairu da Asiya tare da ita kuwa Aibo”.
Dandanan bakin Shu’aibu ya washe, cike da zumuɗi yace, “Masha ALLAH, ai ɗiyar Inna Asiyar ce kuwa inna”.
“Ɗiyar Asiya? Kai ina ka samota haka?”
Inna ta faɗa cike da mamaki.
Murmushinsa ya faɗaɗa, tas a yanda muka haɗu jiya sai ya sanar mata, sai jinjina kan mamaki takeyi, ta juyo gareni tana tambayata daga ina nake haka har shi Shu’aibu ya ganoni?.
Da farko nayi niyyar faɗa musu gaskiya, amma yanayin Inna da naga har sannan bawani ɗokin ganina taiba saina canja zancena kawai, na faɗa musu iya abinda zasu iya amsata game da nemnsu kawai na fitoyi dan nagaji da zama ni kaɗai.
Kai inna ta jinjina, babu ko jin nauyina tace, “Amma kai Aibo kana ganin riƙon babbar budurwa kamar wannan bazai zamar mana wani tawayaba? Mu dai ba kuɗin aurar da ita ke garemu ba kaima kasan haka, ga ɗan karen kishin matarka da batason ganin wata mace ta raɓeka, inaga mu taimaka mata da wani abun ta koma inda ta fito tai haƙuri kamar yanda kowa keyi a nasa gida.
Murmushi nayi mai ciwo hawaye na taruwa cikin idona, wato sai yanzu na fahimci abinda yasa dangina ke gudun ɗaukata, ashe hidimar aurar danice damuwarsu kawai, to nida banida ko saurayi wane maganar aurena za’ayi kuma?, maganar shu’aibu ta katseni.
“Haba inna, wannan wace irin maganace haka, koba komai ai Bilkisu abar tausayice, ALLAH kuma shine zai buɗa mana mu sauke dukkan nauyinta gwargwadon iko, dan riƙe maraya ba ƙaramin alkairi bane da falala ga bawa, amma yanzu sai kowa ke gudun hakan, kifa tuna mahaifinku ɗaya da inna Asiya, na tabbata kuma da itace a raye zata riƙe naku ƴaƴan ai, sa……”
“Nikam naji gwanin iya magana, tunda kaji ka gani ta zauna ga fili nan, ni dama dai kai nake tausayi, tunda dukkan ƙarfin riƙe gidannan kaine keyi”.
Cikin jin daɗi yace, “Nagode da amincewarki inna, ALLAH ya tayamu riƙo”.
Wannan shine yazama sanadin zqmana a wannan gida, duk da bajin daɗin zaman nakeba hakan ya fiyemin akan naje naita raɓe-raɓe harna cigaba da gamo da irin gidajen su Uwargida masu dulmiyar da imanin bawa zuwa halaka.
Babu mai sakarmin fuska inba Shu’aibu ba, shi kuma ba yini yake a gidanba, a hankali dukkan aikin gidan ya dawo kaina, sam bani da wani hutu inba dareba shima sai kowa ya rigani kwanciya.
Lawusa matar Shu’aibu ta mugun tsanata, ni zan dafa abincin gidan amma idan tazo rabo ɗan kaɗan take zubamin, wani lokacinma saita gama rabon zatace ta manta dani, sai dai ace na kankare ƙanzon.
Duk da agaban Inna ake komai uffan bata ce mana balle ta nunama Lawusa batai dai-daiba, koda yake na lura Inna tsoron Lawusa takeyi, dan haka zatai ta mata rashin kunya amma bata iya cewa batai dai-daiba, sai idan taimata abinda yay mata zafine sosai zakaji ta faɗama Shu’aibu, shiko iyakarsa yace tayi haƙuri ta bar Lawusar da halinta kawai.
Wannan zama nasu na bani mamaki sosai.
Ban fahimci abinda yasa gidan yake hakaba sai da ƙanwar yaya Shu’aibu Sa’a tazo gidan yini a ranar da nake cika wata guda a cikinsa, itakam hannu biyu ta amsheni, sai murna take matsayina na ƴar uwarta.
Akan Lawusa namin masifa nazo na ɗaura abincin rana sukai faɗa da Sa’a, tace ban ɗorawa ita da take aure a gidan ta fito ta ɗaura, da yake Inna batanan sai babu wanda yace Sa’a batai dai-daiba, nicema naita bama sa’a haƙuri akan tabari kawai nayi, amma fir tace bazanyiba.
Nanne ta zauna ta bani labarin ai Yaya Shu’aibu ba son Lawusa yakeba, Inna ce ta haɗa auren saboda Lawusa ƴar ƙawartace, yanada wadda yakeso amma inna tace bazai aureta ba sai Lawusa.
A lokacin babansu na jiyya baida lafiya, shiyyasa aka rasa mai goyama Shu’aibu baya, dole ya auri Lawusa badan ya soba, bayan bikin da sati biyu kuma babansu yarasu, daga nan Lawusa ta fara ma Inna rashin mutunci a gidan, inna ko bata iya ce mata komai, yanzu haka aurensu shekara uku kenan, amma ko ɓari Lawusar bata taɓa yiba sai rashin mutunci, sai dai duk wannan tijara tata tana tsoron Shu’aibu, ita kuma Sa’a bata raga matane.
“ALLAH ya ƙyauta” kawai na iya faɗa naja bakina na tsuke.
Sai yamma lis Inna ta dawo gidan, Lawusa ta kwashe ƙarya da gaskiya ta faɗa mata a kaina, Inna ko ta rufeni da masifa hardasu gori akan daga taimakona da sukai shine zanzo na watsa musu gida.
Ran Sa’a ya ɓaci akan wannan abu, Shu’aibu na dawo ta kwashe komai itama ta sanar masa, shiko ya balbale Lawusa da masifa har takaisu ga marinta.
Kuka da ihu taita kurmawa akan mari guda ɗaya, yayinda bakinta keta danƙarama Shu’aibu zagi ta uwa ta uba, ta haɗa kaya zata tafi Inna taita roƙonta da bata haƙuri, sai da ƙyar Lawusan ta haƙura saboda tana bala’in son Shu’aibu, batason rabuwa dashi sam.
Ni daga baya ma abin nasu dariya ya koma bani dan na lura dama Lawusa bason tafiya takeba, farfaganda ce kawai.
Sam abinda akemin a gidan sai baya damuna sosai, komai kuma suka buƙata ina musu dan a zauna lafiya, ban taɓa ɗaga kai na kalli wulaƙancin da Lawusar kemainba sam, a ganina ba laifinta bane ai, haka ƙaddarar rayuwata take…..
________________________
JAWAAD
_________________________
Yau ma dai Jawaad bai kwana gidanba, koda ya baro wajensu Aliyu Office ya koma, acan ya raba dare yana aiki, daga baya ya fito, amma saima ya rasa ina zai dosa, sam baya buƙatar komawa gida, dan bayason yawan ɓacin rai a yanzu, yana buƙatar nutsuwa ta musamman akan gudanar da wannan aikin da yake fatan nanda kwana biyu ya kammala shi insha ALLAHU.
Gidan dasu Jabeer suke dai ya sake komawa, ya iske har sunyi barci, dan haka ya buɗe wani ɗakin ya shiga ya kwanta, bama wani barci sosai yayiba aka kira asubahi.
Su Hafiz duk sunyi mamakin ganinsa a gidan, sai dai tunda bai basu fuskar da zasu tambayesa komaiba sai basuce ɗinba.
Suna dawowa daga salla duk da barcin dake cin idonsa bai kwantaba.
Zama sukai yana musu bayanin abinda kowa ya kamata yayi a ranar yau.
Coffee da Jabeer ya dafa musu da kansa kowa yake sha, Jawaad ya ajiye kofin hannunsa yana faɗin, “Dolene yau muyi komai da azama, dan guri na sake ƙure mana. Ni zanje gidan Alhaji kokino na gana da matarsa, Jabeer kaikuma filin jirgi ya kamata kaje ka sake mana bincike a cctv ɗinsu, Aliyu da Hafiz ku kamo mana drivern Alhaji Kokino da ƙaninsa wakili, dan hardashi akaje tarbosa filin jirgi, shima inada alamar tambaya a kansa”.
A tare duk suka jinjina masa kai, sai kuma kowa ya miƙe domin zuwa ya shirya……………✍🏻
https://youtu.be/5xN4SGMIzME
ALƘALAMI TV takuce, maza ku garzaya kar ayi babu ku, Please a danna mana subscribing domin nuna mana ƙauna ta musamman🥰🤙🏻.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻2
Shafi na goma sha bakwai
………….A gaggauce yay shirin cikin Suit kalar ruwan goro mai duhu, sai rigar ciki data kasance ruwan bula mai haske, yanada kaya a gidan, saboda duk randa Shahudah ta haɗa masa zafi to nan ne wajen fakewarsa ya samu nutsuwa, shiyyasa yake da abubuwan amfaninsa.
Turare ya fesa kaɗan ya fito yana ƙoƙarin ɗaurama hannunsa a gogo, rigar suit ɗin ta sama rataye a hannunsa dan bai sakaba.
Su Aliyu dake zaune a falo cikin shirin fita suma suna jiransa duk suka miƙe idonsu a kansa.
Jabeer ya kama hannun da Jawaad yake ɗaurama agogon yana ƙarasa ɗaura masa.
Bai musaba ya miƙa masa hannun yana maida hankalinsa ga Hafiz.
“Hafiz ka kulafa sosai, dan ƙaninsa ɗinnan shegen wayone dashi, duk wani motsinsa inda yake zuwa, da wanda yake mu’amula da dai komai nasa ku sani, a koda yaushe yakan nuna yanason yayan nasa fiye da kansa”.
Ya ƙarasa maganar dai-dai Jabeer na gama ɗaura masa agogon, yace, “Thanks”.
Kai kawai Jabeer ya ɗaga masa, sukai ƙoƙarin ficewa.
Jawaad na gaba suna binsa a baya su uku, dolene ka gansa su burgeka sosai, dan kallo ɗaya zakai musu ka tsinkayo tsantsar jarumtar aikinsu a fuskokinsu.
Gimba ya gaishesu cikin girmamawa, sannan ya buɗe ma Jawaad mota ya shiga.
Suma sauran kowa mota ya shiga, Jabeer shi kaɗai, Hafeez ma shi ɗaya.
Sai Aliyu da ya shiga kusa da Jawaad zasuje gidan Alhaji kokino tare.
Shiru Jawaad na kwance a bayan mota, kansa kwance jikin kujera. yayinda idanunsa ke buɗe yana kallon titi.
Dai-dai danja ta tsayar dasu idonsa ya sauka akan wata mahaukaciya dake tsaye bakin titi tanata soshe-soshe, kafeta da idanu yayi ko ƙyaftawa bayayi, Gimba da Aliyu da basusan mike faruwa ba suna ɗan magana jefi-jefi, gimba yaja motar sukai gaba.
Jawaad yasa handkherchief ya tsane hawayen da suka cika masa idanu, yanajin kewar mamansa sosai, irin yanda bakinsa ma bazai iya furtawa ba, ya lumshe idanunsa yana magana a hankali akan laɓɓa wanda inba kusa da shi kakeba bazakajiba.
“Boss mun iso”
Gimba ya sake maitawa Jawaad da yay nisa cikin tunani sam baisan harma sun samu damar shigowa harabar ƙaton gidan Alhaji kokino ba, Aliyu da gimba harsun fita a motar sai shi kaɗai.
Numfashi mai nauyi Jawaad ya sauke yana kallon Gimba da idanunsa dake a rine da damuwa?.
Baice komaiba ya ziro ƙafafunsa ya fito, agogonsa ya ɗan kalla kafin ya maida kallonsa ga dogon ginin benen gidan,
“Ali muna buƙatar ai mana iso fa”.
“Yes Boss, ai mai gadin ya shiga ya sanar musu ma”.
“Ok” Jawaad ya faɗa yana tura hannayensa biyu cikin aljihun wandonsa kamar maijin sanyi.
Kusan mintina uku sai ga mai gadin ya dawo, shine yay musu jagora har ƙaton falon baƙi dake a cikin gidan, sannan yay musu sallama ya fita.
Zamansu baifi na mintina ukuba wata dattijuwa ta shigo ɗauke da ƙaton tire, ta ajiye sannan ta risina ta gaishesu, cikin kulawa Jawaad ya amsa mata.
Tana fita babban yaron Alhaji kokino ya shigo cikin kayan barci, da alama ma tasoshi akayi daga barcin, dan yanayinsa ya nuna hakan.
Hannu ya bama Jawaad suka gaisa tare da Aliyu da Gimba, sannan ya samu waje ya zauna hankalinsa akan Jawaad.
“Yallaɓai ko an samu wani ƙyaƙyƙyawan news ne haka?”.
Jawaad dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ya girgiza masa kai yana gyara zamansa, “Babu wani labari mai nuni da nasara abokina, yanzu ma munzone dan inason ganawa da dukkan jama’ar gidannan idan babu damuwa”.
“Babu damuwa yallaɓai, barama kaga naje na tattarosu”.
Kai Jawaad ya jinjina masa cikin lumshe idanu, ya miƙa hannu ya amshi system ɗinsa dake a hannun Aliyu, saman cinya ya ɗorata yana ƙoƙarin kunnawa. A haka jama’ar gidan suka fara shigowa cikin sallama.
Jawaad bai ɗago ya kalli kowa ba a cikinsu, danne-dannensa kawai yake a lap-top.
Kowannensu mazauni ya samu, budurwar da tunda ta shigo idonta ke a kan Jawaad ta miƙe daga inda ta zauna tana faɗin, “A yallaɓai ko shayi ai kwasha, dan da alama kunyo sammakon barin gida”.
Ɗan murmushi Aliyu yay kawai, Jawaad kam ko motsi baiyiba balle zancen ɗagowa, zata fara ƙoƙarin haɗa shayinne Aliyu ya ɗan kalleta yana girgiza kansa, “No Please barsa kawai”.
Da sauri Uwargidan Alhaji Kokino dake ƙoƙarin zama ta katsesu da faɗin, “A’a haba dai, in kuka ƙi kuwa bazamuji daɗiba sam”.
Murmushi kawai Jawaad da ya kallesu yayi, amma baice komaiba, dan haka shema’u ta cigaba da haɗama su Jawaad shayin, cike da yanga ta kalle Jawaad kamar shi kaɗai kawai take gani a wajen tana faɗin, “Asa shuga da yawa?”.
“Spoon ɗaya ya isa” Jawaad yay magana a taƙaice ba tare daya kalleta ba.
Koda ta kammala tazo miƙa musu sai da fara bama Jawaad, saboda neman magana saida tai yanda hannunsu ya gogi juna, hakanne ya saka Jawaad ɗago idanu ya kalleta, yanda ta kafesa da natane ya sakashi yin luuu da nasa cikin salon isa irin na mazan da suka isa ya janye daga nata yana faɗin, “Thanks” a hankali.
Tai murmushi saboda jin daɗin godiyar da yay mata, wajen zamanta ta koma bayan ta bama Aliyu da Gimba suma, inda take facing ɗin Jawaad da har yanzu bai kai shayin bakinsa ba yana cigaba da danna lap-top ɗinne.
Amaryar Alhaji kokino ce ƙarshen shigowa cikin shiga ta alfarma, ta samu waje nesa da kowa ta zauna.
Sai lokacinne Jawaad ya janye system ɗin daga saman cinyarsa yana maida hankalinsa garesu.
Shayin yakai bakinsa kafin ya basu dukkan nutsuwarsa yanayin gyaran murya.
“Zakuyi mamakin cewar da nai a tattaromin ku duka, so amin afuwa idan na shiga rayuwarku da yawa. Dama dai akan maganar Alhaji ne, maganar gaskiya a koda yaushe lamarin nan sake rikitar damu yakeyi, musamman idan mukai dubi da lafiyar ALLAH suka baro filin jirgin, ku kuma gashi kunce bai shigo gidannan ba, sai labarin rashin ganinsa aka kawo muku”.
“Hakane kam yallaɓai, mu kanmu mun rasa yanda zamu kwatanta al’amarin gaskiya”.
Kai Jawaad ya jinjina yana duban Amaryar Alhaji.
“Hajiya kece kuka dawo da Alhaji daga tafiya ai?”.
Zamanta ta gyara sannan cikin isa tace, “Tabbas tare muka dawo, sai dai shi gida aka wuto da shi, ni ko gidanmu na wuce saboda uzirin san zuwa na duba mahaifiyata da bata da lafiya, mun rabu dashi akan zaije gida ya kimtsa shima sai ya zo yaga jikin nata”.
Jawaad yay murmushin gefen baki a zuciyarsa ya furta “Kamar yanda aka shirya kenan”, a fili kam sai ya jinjina kansa yana maida hankalinsa ga Uwargidan Alhaji da fuskarta kawai ta isa ta nuna maka tsagwaron damuwarta.
“Maganar gaskiya Hajiya a yanda nazarina ya nunamin Alhaji ya shigo cikin gidannan, cikin abu uku kuma tilas ɗaya ya kasance”.
Kusan gaba ɗayansu zuba masa ido sukai cikin wani irin zumuɗi, suka haɗa baki wajen faɗin, “Yana cikin gidannanfa kace yallaɓai?”.
“No, ba ayanzu nake nufiba” Jawaad ya faɗa yana miƙewa riƙe da kofin shayi a hannu, tamkar malami da ɗalibai haka ya tsaya musu ƙikam dan ya samu damar nazarin fuskar kowa a falon.
“Cikin abu uku dana ambata dolene a samu ɗaya kuwa, na farko shine, ko dai an shaƙama Alhaji wani abu an barsa a motar da aka ɗakkosa sannan aka sanar da ɓatansa gareku, da ga baya kuna cikin wannan ruɗanin aka sake fita dashi daga gidan, kokuma ba’a fitan dashiba yana cikin gidannan har yanzun, ko kuma tunma a hanya drivern sa ya bada ƙafar da akai canjin motar da aka ɗaukesa da wata, ina nufin da haɗin bakinsa a ciki, dama duk wanda suke tare a wannan lokacin
Cikin fusata Amaryar Alhaji Kokino tace, “Ban gane mi kake magana akaiba ɗan saurayi, ya zakayi jam’u akan duk wanda yake tare dashi?”.
Jawaad ya rumtse hannunsa da ƙarfi yana feso numfashi mai zafi, dan ya fara hasala da maganar hajiya Amarya, amma kasancewarsa gwanin ƙwarewa akan aikinsa sai yay azamar dai-daita kansa, “Hajiya ke ai babuke a ciki, saboda tun a filin jirgi kuka rabu kikace? To miye haɗinki ma da tawagar wanda sai da suka shigo har gida dashi?”.
“Hakane” ta faɗa aɗan daburce.
Kusan da yawansu lamarinta sai da ya basu mamaki, amma sai basuce komaiba.
Jawaad ne ya katse musu tunani da kiran sunan Gimba.
Gimba dake daga can gefe yana aikin nazarin kowansu yay saurin faɗin, “Yes Boss”.
“Kiramin mai gadin gidannan”.
Da sauri gimba ya fice, Jawaad kuma ya sake kallon budurwar ɗazun Shema’u data haɗa musu shayi yace, “Zan iya ganin ma’aikatan gidannan duka?”.
“Mizai hana boss” tai maganar da salonta na jan hankali.
Idanunsa ya janye yana faɗin, “Wannan ƴar matsalace” a saman laɓɓansa…….
A mamakinsa sai yaji tace, “Mi kace?”.
Kai ya girgiza mata alamar babu komai.+
STORY CONTINUES BELOW

Cikin mintuna ƙalilan kowa ya hallara, Jawaad ya bisu da kallon nazari, kafin yace, “Inason ku bani haɗin kai, duk maganar da wani ya faɗa daga baya na fahimci ƙarya a cikinta sam bazan yafe masa ba”.
Duk suka amsa da cewar zasu fa ɗi gaskiya.
Kansa ya jinjina musu ya koma cikin kujera ya zauna, “Mai gadi da kai zan fara”.
“To yallaɓai”.
“Kaine a gate, kuma dolene komai nisanka da inda mota tai parking a gidannan sai kaga wanda zai fito a cikinta?”.
“Ƙwarai kuwa yallaɓai”.
“A randa Alhaji ya dawo motoci nawane suka shigo gidannan?”.
“Inaga dai kamar biyarne”.
“Kanaga kokuwa ka tabbatar”.
“Ayi haƙuri yallaɓai na tabbatar”.
“Idan Alhaji zai shigo gidannan kafin ranar yana tsayawa gaisuwa da ku? Kokuwa shigewa kawai yakeyi?”.
“Eh idan aka tsaya da mota ya fito daga ciki sai muje muyi masa barka da zuwa kafin ya shige cikin gida”.
“To aranar kunyi hakan?”.
Jimm mai gadi yayi bai tankaba, sai da Aliyu yace, “Ya dai?”.
Firgigit Mai gadi ya dawo hayyacinsa, cikin in ina yace, “Gaskiya bamu gaisa ba, dan na nufi zan gaishesa kenan bayan rufe gate da nayi sai najiyo suna taraddadin baya cikin motar ai”.
“Waye ya fara ambata baya cikin motar?”.
“Bazan iya ganewa ba, saboda ruɗanin dana tsinci kaina a ciki, kuma darene”.
Jawaad yay guntun murmushi yana lumshe idanunsa, da alama akwai ɗan ɓacin rai tattare dashi.
Da sauri ya sake kallon maigadin da har yaji daɗi an gama dashi, “A daren wace motace ta fara fita a gidannan?”.
“Da yake kasan darene yallaɓai, amma mota kusan uku suka fita, sai dai bazan ce gasuwa da suwanene a cikiba, saboda ruwan sama da ya ɓalle………”
Da ƙarfi Jawaad ya daki tebirin gabansa a wata irin fusata yace, “Ƙaryane!! Dolene ma ka sani”.
Babu wanda bai zabura ba a falon.
Ya kallesu da jajayen idanunsa cikin matuƙar tsawa yace, “Tabbas wanda ya aikata garkuwa da Alhaji yana cikinku, a cikin gidannan yake!! Akwai haɗin bakin wanda ya sanshi, Idan kuma har ya bari na kamashi da hannuna kashinsa ya bushe!” ya ƙare maganar yana nunasu da ɗan yatsa su dukansu, ya miƙe a fusace yana fisgar rigar suit ɗinsa ya rataya a kafaɗa ba tare da ya sauke hannunsa ba ya fice abunsa.
Aliyu ya miƙe da sauri yazo ya ɗauki lap-top da wayar Jawaad da ya bari yabi bayansa da sauri shima yana faɗin, “Hajiya ku sa ido wa junanku kamar yanda ya faɗa”.
Aiko kafin kace mi, hayaniya ta ɓarke a tsakanin Jama’ar gidan babu maijin ta wani, duk ɗinsu Jawaad ya saka musu zargin junansu da bayanin Aliyu na ƙarshe.1
Jawaad kam tunda ya fito a harabar gidan yay tsaye yana dube-dube tamkar mai neman wani abu, nanko nazarin komai yake a cikin ƙwarewar aiki.
Gimba da Aliyu suka ƙaraso, a bayansa suka tsaya suna binsa da kallo, ba tare da ya kallesu ba yace, “Aliyu mika fahimta game da kowansu?”.
“Boss abubuwa da yawa ai, wannan mai gadin da alama yasan wani abu, sai dai kamar yanajin tsoron faɗa, hakama amaryar Alhaji ban yarda da itaba, sai ko dattijuwar data kawo abinci kafin kowa……”
Kallonsa sosai Jawaad yayi, ya tsaresa da idanu tamkar a jikinsa ne zaiga gaskiyar abunda yake buƙatar, sai kuma ya saki lallausan murmushi yaɗan kashema Aliyu ido ya juya a hankali yana takawa cikin izza dajin lallai shi ɗinfa ya kai”.
Murmushi gimba da Aliyu sukayi, dan sunsan halin mai gidan nasu akan iya aiki, tabbas fusatar da yay harya fito ba’a banzaba, yana kan sani ya jefa zargi a zukatan jama’ar gidan baki ɗaya……
_________________________
BILKEESU
_________________________
Yau gaba ɗaya tunda na tashi banajin daɗi, da ƙyar ma na iyayin sallar asubahi na koma na sake kwanciya, kowa yasan ba ɗabi’ata bace baccin safe, dan tunma ina gidanmu na haya bansamun hakan, balle yanzu da aikin gidansu inna zainaba kawai ya isheni.
Cikin barci kawai naji saukar ruwa mai azabar sanyi a kaina.
A matuƙar firgice na tashi zaune jikina na wani irin ɓari na razana da sanyin ruwan, ga zazzaɓi dake jikina daman.
Lawusa ce tsaye kaina tana hura hanci tamkar wata guguwar tsakkiyar rani.
“Sannu isassa, waye ɗan iskanki a gidannan da zai tashi ya ɗaura miki abimci ki tashi kici? K bara kiji, bakifa da maraba da ƴar aiki a gidannan, dolene ki bauta mana mu biyaki da abinci da wajen kwana, inko ba hakaba to lallai kuwa sai dai idan gidan zaki bari”.
Yau rana ta farko a rayuwata da nakejin bazan iya ragama Lawusa ba, hakan yasa na miƙe a bazata na zazzaro mata idanuna dake jajur saboda zafin ciwo, nakai hannu na cakumo mata wuya na maƙureta a bango,
“Tunda gidan Ubanki ne dan ALLAH Lawusa karki barni yau na kwana a cikinsa, ke wai shin jakar wane yankin jejice da bakisan darajar ɗan adam ba?! Ko an gaya miki tsoro kesa ɗan adam shiru-shirune?”.
Na ƙare maganar ina hankaɗata ta bugi da buhun masara dake ɗakin.
Ai kafinma na sake cewa wani abu ta fita a guje tana kururuwa wai akawo mata ɗauki zan kasheta.
Tsaki nayi na zube a ƙasa kamar mara laka a jiki, sai kawai naji hawaye masu zafi na saukamin a kumatu, ga wani irin rawa da jikina keyi tamkar mazari.
A haka naji mutum biyu matan maƙwafta sun shigo suna hayaniya, sai sannama na fahimci daga ni sai Lawusa ne a cikin gidan kenan?.
Sunyi maganar duniya nai banza dasu tamkar banajinsu, sai uhu sukemin a kai wai ban ƙyautaba, kalloma basu isheniba.
Lawusa kuwa tana daga bakin ƙofa taƙi shigowa tana kukan munafunci da danƙaramin zagi ta uwa ta uba da gori iri-iri.
A wannan yanayin inna ta shigo ta iskemu, ta tambayi ba’asi, Lawusa ta zauna ta shirya mata ƙarya da gaskiya, hakama matan da suka shigo, tsabar munafunci harda cewa da ƙyar suka ɓanɓare Lawusa a hannuna………✍🏻
9
Maza ku garzaya manhajarmu ta youtobe domin samun daɗaɗan labaran littatafanmu akan tashoshin, ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS a Audio, karka bari a baka labari, dan har sabbin buks ɗin zafafa zaku iya samu a tashar ta ALƘALAMI TV😻🤙🏻.
Karkuma ku manta da ZAFAFAN littatafai da ga marubutanku masu ɗunbin fasaha kamar haka.
Hafsat (miss xoxo)
Safiyya Huguma
Hafsat rano
Mamu gee
Bilyn Abdull
Akan farashi mai sauƙi, dukkansu biyar zaku samesu ne a naira ɗari biyar kacal, karku bari ayi babuku. Dan da gaske ZAFAFAN ne.😋😋😃🤝🏻
zaku iya tuntuɓar wannan number akan ZAFAFA👇🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Shafi na sha takwas
Babu editing dai
………..A mamakin kowa sai mukaji Inna tace, “To kukam ALLAH ya ƙyauta muku, na lura sam jininku bai haɗuba, bara Aibo yazo, ai na samo maganin wannan yawan fitinar taku mara dalili”.
Ba Lawusa kawaiba, koni kaina nayi mamakin maganar inna, danni a zatonama yau saita koreni a gidan saboda na taɓo ƴar mai ɗinta, amma ji yanda ta nunama halin ko in kula akan zancen, sai daimaganarta na ƙarshe akan mafitar data samo ta tsayan a zuciya sosai, komawa nai na kwanta ina rawar sanyina.
Lawusa kam kuka ta sanya rurus wai dama inna bata ƙaunarta ai a gidan, yau sai ta tattara ta barmusu gidansu, sai inna ta aurama Sha’aibu ni a yau da rana danta nuna ma duniya ni ƴar uwartace”.
Duk surutan nata dai inna bata kulaba, matan kuma da sukazo haɗa munafinci sai gasu suna jan ƙafa suna fita ɗai-ɗai da kunya.
Ina jiyo fitar Lawusa tana cigaba da zagin Inna.
Kaina kawai na girgiza ina mamakin irin wannan tarbiyya ta Lawusa, a hakane wannan zata zama uwar wasu, ita kanta tana buƙatar tarbiyyar balle abinda zata haifa.
A haka wahallalen barci ya kwasheni, ban tashi farkawaba sai lokacin sallar zuhur, shima dai inna ce ta tasheni akan naje nai sallah.
A mamakina kuma na fito zanyi alwala sai naga inna tayi abincin rana da kanta bata tasheni ba.
Salla nayi, ina zaune sai ga sallamar Yaya Shu’aibu ya dawo cin abincin rana kamar yanda ya saba, muryar Inna na tsinkayo tana sanar masa bani da lafiya, hakan ya sakashi faɗin “Subahanallahi, miya sameta kuma?” yay maganar yana ɗage labulen ɗakin.
Sannu nai masa sannan na gaishesa, cike da kulawa ya amsa, ya ƙarasa shigowa ɗakin yana tambayata mike damuna?.
“Yaya zazzaɓine kawai, kuma Alhmdllh yama sauka”.
“Wayyo sannu, ai ko sauron gidannan ya isa saka mutum zazzaɓi, kici abinci saina kaiki kamiz ki amshi magani”.
Nace “to” tare da masa godiya.
Nanma nazata Inna zatace a’a sai naji batace komaiba, sai ma amsar tambayarsa akan Lawusa take bashi, duk abinda ya faru tsakanina da Lawusar ta zano masa, ta ɗora da faɗin, “Ni yanzu na samo mafita akan wannan yawan rigimar tasu, fitar danai yau wani gida ƴar kande ta rakani na samowa Bilkisu aikin wanke-wanke da shara, inasha ALLAHU tananma sai kaga ta haɗa kuiɗin kayan ɗakinta har muma mu mora, kaga bama ta yini gidanba balle wannan fitinar ta cigaba da girmama a gidannan”.
Shu’aibu da fuskarsa ta ɗan nuna alamun damuwa, yace, “Amma Inna ni dai da kinyi shawara dani da ba’ayi hakaba, wane kuma aikin wanke-wanke Bilkisu zatajeyi fisabillahi, ni dai duk da sana’ata ba wata mai ƙwari bace zanyi iya bakin ƙoƙari wajen sauke haƙƙin zuminci akan komai na aurenta, indai dan zaman gidane zanma matarcan ta tsallake magana Bilkisun taje ta fara koyon ɗinkin jakka a wajenta, kinga ko aure tayi ai tasamu madogara insha ALLAHU”.
Ran inna a ɓace tace, “Nikam Aibo bansan miyasa kake nina tamkar ina zalintar yarinyarnanba, yanzu shi aikin da zataje bazai taimaketaba ne? Ko aure tayi ai dai ta samu ta iya komai”.
“Hakane Inna, nima banƙi ta takiba, muyi addu’a to ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi a ciki, idan ta samu lafiya sai muyi maganar”.
“Shike nan”
Inna ta faɗa a taƙaice, da alama dai har yanzu ranta babu daɗi akan canja mata tsari da yayi.+
Bayan mun gama cin abincine ya ɗaukeni a napep ɗinsa zuwa ƙyamiz, an bani magani tare da allura muka dawo gida.
Mamaki ya kamamu saboda iske jibga-jibgan motoci guda biyu da mukayi a ƙofar gidan, sai walƙiya suke.
Na kalli Yaya Shu’aibu ina faɗin, “Yaya baƙinmu ne waɗannan kokuwa?”.
Cikin jimami yace, “Wlhy ban saniba Bilkisu, amma inhar hakane to lallai inaga Kawu Ali ne kuwa yazo, dama lokaci-lokaci yakanzo su gaisa da Inna idan ya samu dama?”.
“Kawu Ali? Shikuma wanene shi?”.
Da mamaki sosai akan fuskarsa ya kalleni, “Bilkisu kina nufin wai baki san Kawu Ali ba shima? Yayansu Inna ne fa, ɗakinsu ɗaya da Inna ai”.
“Wlhy ban sanshiba Yaya, kana nufindai shima babansu ɗaya da Innata kenan?”.
“Ƙwarai kuwa Bilkisu”.
“Yaya to ko shine suke cema Ɗan iya?”.
“Ƙwarai kuwa Bilkisu shine, amma nayi mamaki, na lura dai ke babuma wanda kika sani a dangin kenan?”.
Murmushin yaƙe nayi zuciyata na suka, murya na rawa nace, “Ai yaya sanda Innata nada rai babu wani ɗan uwanta dake raɓarta, nasan dai lokacin ina ƙarama takanje dani wasu wajajen gidan dangi, amma sai na lura saboda tana da nakasa kamar kowa gudunta yakeyi, Inna Zainabu ma abinda yasa ban manta da itaba ita da Kawu Manu saboda Innata na yawan ambatarsune”.
Tausayina sosai na gani a fuskar Yaya Shu’aibu, ya girgiza kansa kawai yana sauke numfashin tsantsar takaici, “Karki damu Bilkisu, komai na rayuwa da kika gani akwai ƙalu bale, watarana sai labari, irinku da kuke tashi cikin rashin gata ALLAH yafi ɗaga darajarku da ni’imomi masu yawa da komawa birge wanda suka juya muku bayan a lokacin da kuke buƙatar taimako, mu shiga ciki kinji, ALLAH ya ƙara miki haƙuri da jimirin cinye jarabawar rayuwa”.
Murmushi nayi ina share hawayen da suka zubomin a fuska, kusan a tare muka fita zuwa cikin gidan.
Ashema ba shi kaɗai bane harda iyalinsa, matarsa da ƴaƴansa namiji da mace su biyu, kallo ɗaya nai masa na gano asalin kamanninsa da Inna zainabu, yana kuma yanayi da innata itama, da yake ni sam ban biyo innata komaiba, gaba ɗaya kamannina na babana ne, dan dana biyo Innata da nazama ƙyaƙyƙyawa kuwa, dan su jinin fulanin asaline.
Inna tanata hidima da baƙinta, bakinta kam a washe tamkar gonar audiga.
Duk tsugunnawa mukai ni da Yaya Shu’aibu muka gaishesu, inna daketa faman washe haƙora tace, “To ka gantanan Ali, wannan itace ɗiyar Asiyar da nake faɗa maka”.
Idonsa a kaina yace, “ALLAHU akbar, ashema ta zama budurwa? Koda yake rabona da ganin Asiya tunfa kafin nabar ƙasarnan, lallai sheɗan ya jagoranci zukatanmu wajen raunana zuminci, yanzu ace ɗan uwanka da kuka tashi gida ɗaya dan aure ya ɗaukesa shikenan sai zuminci ya yanke? Manu ne ma wlhy yake sanarmin rasuwa lokacin bana ƙasar shiyyasa banzo ta’aziyya ba, ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata, ke kuma data bari ALLAH ya rayaki kinji”.
Hawaye na share ina amsawa da amin.
Daga nan ya koma kan Shu’aibu yana masa tambayoyi akan yanzu mi yakeyi?.
Matarsa dai da ƴaƴansa basa cewa Uffan, saima faman danne-dannen wayoyi sukeyi.
A cikin tambayoyin da yakema Yaya Shu’aibu ne yakejin ai ya kammala diploma ɗinsa, daga haka karatun ya tsaya, a take yace ya bashi takardun zai nema masa makaranta ya koma, ya juyo gareni yana tambayata nifa?.
Kaina a ƙasa nace, “Ai kawu ni koma Secondary ɗin ban kammala ba”.
Ya ɗan nuna damuwa saman fuskarsa, hakanne ya sakashi maida kallonsa ga Inna yana faɗin, “To nifa inaga wannan itace hanyar dazan gyara kuskurena akan Asiya, Zainabu zan tafi da Bilkisu ta zauna a gidana cikin ƴan uwanta, itama ta samu ilimin da zata taimaki kanta koda anan gaba babumu a raye”.
Take fuskar Inna ta canja launi, hakama matarsa da ƴaƴansa wani kallo na sukemin mai kama da wannan ƙazamar?.
Yaya Shu’aibu ne kawai ya bayyana tsantsar murnarsa a fili, kafinma inna ta bada amsa tuni Yaya Shu’aibun nata godiya.
Hakan ne ya dakatar da ita daga son hawa dokin naƙin datai niyyar yi.
Niko bammasan yazan fasalta muku yanayin dana shigaba, ɗumin hawaye kawai nakeji suna bin kumatuna, duk da naga rashin jin daɗin iyalansa hakan bai hanani ƙwaɗayin binsu ba, koba komai burina nayin karatu mai zurfi ashe zai cika a duniya, insha ALLAHU zanyi haƙuri da kowane irin halin daza fuskanta daga garesu domin samun cikar burina”.1
STORY CONTINUES BELOW

Abu kamar wasa sai ga magana ta zama babba, dan kuwa dai Kawu Ali cayay nai shiri mu wuce, ba kuma saina ɗauki komi ba, ni kaɗi suke buƙata.
Tashi nai nayi wanka kamar yanda Yaya Shu’aibu ya umarceni, sai gani na fito tsaf cikin irin kayan da Sani ɗan gidan Uwargida ya bani kala uku.
Yanda na ɗanyi tsaf na kula ya sakasu mamaki, dan sanda nake ɗazu kam tamkar an kwatonj da ga bakin kura ne.
Kewar Yaya Shu’aibu kawai naji, amma Inna da Lawusa banji komaiba kam, Yaya Shu’aibu ya kwantarmin da hankali akan ai tunda inacan zai dinga zuwa dubani, da dai kam baya zuwa, dan sau ɗaya ma ya taɓa zuwa gidan, tunta kuma matar Kawu Alin tai masa wulaƙanci shi da inna bai sake zuwa ba koda wasa, amma yanzu darajar zan zauna a gidan zaike zuwa insha ALLAHU.
Yamin nasiha yanda zanyi ƙoƙarin zama da kowa lafiya ba tare da anyi kuka da niba, ya sake maimaitamin muhimmancin haƙuri a duk halin da zan tsinci kaina.
Godiya nai masa cikin share hawayena.
Da zamu wuce har mota suka rakomu, Kawu da matarsa suna a mota ɗaya, yaransuma motarsu daban, to nima sai akace na shiga motar yaran nasu.
Ina kallon namijin baiso hakanba, dan harda guntun tsaki yaja, macenma tanata ƙunƙuninta da ba kowa kejiba.
Suna gaba niko ina zaune a baya a maƙure tamkar wadda aka sace, a haka muka bar anguwar su Inna na ɗaga mana hannu, niko ina share hawayen sabo dana farayi dasu…….
3
________________________
JAWAAD
________________________
Koda suka baro gidan Alhaji kokino station Gimba ya nufa dasu, Jawaad kawai ya fita a motar amma banda Aliyu, dan ɓoyensu akeyi ba kowa yasan da dawowar tasuba.
Gimba ya juya da mota domin maida Aliyu gida, yayinda wani ya ƙaraso da sauri ya amshi kayan hannun Jawaad bayan ya gaidashi cikin girmamawa.
Fuskarshi da ɗan murmushi ya amsa masa, yana gab da shiga Office ɗinsa ya hango Qaseem na fitowa daga Office ɗinsa cikin hanzari, da alama dai wani uzirin zaije, baki Jawaad ya taɓe ya shige abinsa.
Aiki garesa danƙam a office ɗinan, harma tunanin ta ina zai fara yakeyi, ya zauna yana sauke numfashi bayan ya rataye rigar suit ɗinsa jikin kujerar.
Yana duba sabbin files ɗin daya iske a saman tabir ɗinsa yana murmushi sai kace wani zararre, shi kaɗai yasan mi yake tufƙawa a zuciyarsa.
★★★★★★
Saboda ayyukan da yayi sosai, ga mitin da suka zauna bai bar office da wuriba, lokacin da suka hau titi gimba ke tambayarsa ina zasuje? Sai kawai ya bashi amsa da suje gida, dan haka kawai yakejin sha’awar zuwa gidan yau kodan yaga ɗan tayin cikinsa yaji sanyi, duk da bashi da tabbacin Shahudah bata aikata abinda tai niyyaba, tunda yasanta da taurin kai.
Gidan gaba ɗaya babu wuta, hakanne ya bashi mamaki, dan koda babu wutar nepa akwai ƙaton janareto da ake kunnawa da daddare.
Ba tare da ya fita a motarba ya cema gimba yaje ya duba mike faruwa da janareton, dan yasandai ba lafiya ba, tunda dama kullum shike hidima akansa, koda baya gari jan… Ɗin ya samu matsala basajin kunyar kiransa su sanar masa duk da kuwa ALLAH ya basu arziƙi gwargwadon ikon da suma zasu gyara matsalar.
Sai dai bazasuyi hakanba, saboda ɗunbin dukiyar da aka barma Jawaad ɗin itace kawai idonsu ke gani.
Gimba da ya dawo yaɗan risino daga waje yana kallon Jawaad dake danna waya harken ya haske kamilalliyar fuskarsa.
“Boss waifa kaji yaƙi tashine, tun ɗazun ojo yake ta fama, yanzu hakama na iskesa yana ƙara dubawane koza’a dace”.
Janye idanunsa yayi daga kan wayar ya maido kan gimba, fuskarsa da ɗan alamun ɓacin rai yace, “Shine kuma dan wulaƙanci bai faɗaba tun ɗazun a ɗauki mataki?”.
“Wlhy Boss nima namasa wannan faɗan, amma sai ya nunamin ya faɗama kawu babba tun wajen 6, amma sai yace masa yaje sashenka idan ka dawo ya sanar maka, shikuma yazo madam tace bakama kwana gidaba”.
Tsaki kawai Jawaad yayi, ya buɗe motar zai fito, hakanne ya saka Gimba matsawa baya ya bashi hanya.
Yay gaba gimba kuma ya ɗauki ƙaramar jakkar dake gefen Jawaad ɗin ya bisa da ita, kafin ya ƙaraso gareshi harya shige falonsu.
Shahudah na kwance a falo tana kallon tasharta da tafi so saboda waƙoƙi da ake sakawa, sai dai yau anyi abin arziƙi sifikun can ƙasa aka sakasu babu ƙara sosai, kallo ɗaya Jawaad yay mata ya janye idonsa yana fara taka steps ɗin benan.
Tamkar sokuwa haka Shahudah ta bisa da ido, idanunta harsun fara tara ƙwalla……
Ƙwanƙwasa ƙofa da akaine ya sakata maida kallonta wajen, kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa da yes.
Jawaad na step ɗin ƙarshe yaji Gimba ya shigo falon yana gaida Shahudah da cewa ga jikkar boss, tsayawa yay cak saboda wani abu daya taso masa a maƙoshi na ɓacin rai, bakomai bane face tsantsar kishi mai gauraye da baƙin ciki, saboda kayan da yagani a jikin Shahudah, amma dan rashin mutunci ta bama Gimba damar shigowa ba tare da yunƙurin suturta jikinta ba.
Kasa jurewa yay sai da ya juyo ya kallesu, gani yay kan gimba a ƙasa ya juya zai fita, yayinda Shahudah ke tsaye zata je ta ɗauka jikkar a inda Gimba ya ajiye saboda yanda ya ganta bazai iya ƙarasawa gabanta ya bata ba.
Sosai idon Jawaad yay jajur, babu tsammani ma yaji ya cika da hawaye saboda tsabar kishi, juyawa yay kawai ya ƙarasa hayewa batare da yayi mata magana ba.
Yana tsaye gaban mirror yana saɓule rigar saman suit ɗinsa Shahudah ta shigo, baiko kalleta ba ya jefa rigar kan sofa ya fara sassauta tia ɗin wuyansa.
Itama bata tanka masanba taje ta ajiye jakkar saman tebir ɗin gaban gadon sannan ta zauna fuska a ɗaure, ita a dole yanzu tabar sakar masa fuska.
Daga inda take take hangosa ta cikin mirror yana ɓalle maɓallan rigar sa ta ciki kalar bulu, harya gama farar best ɗinsa ta bayyana bata iya janye idonta ba, ya kunce belt ɗinba da saɓe dogon wandon ya faɗi ƙasa sannan yajawo stool ɗin mirror ya zauna ya saɓile ƙafarsa daga cikin wandon, yana fara cire takalmi ne Shahudah ta fara magana cike da gadara kamar yanda ƙanuwarta Aamila ta bata shawara, dan tace inba haka takema Jawaad ba bazai dana cin tuwo akanta ba, itama dai ta yarda da hakan ɗari bisa ɗari, shiyyasa farawa tun daga yanzu.
“Ban taɓa tunanin baka ƙaunata ba sai akan wannan ɗan iskan cikin, wai yau harni kake ƙwatanta zaɓa da ciki bb, walhy ka bani tsantsar mamaki, ni son gaskiya nake maka, dan haka bazan danganta martabarka da ciki ba, zan haifesa kamar yanda ka buƙata, sai daifa ka tabbatar tunma daga yanzu wlhy bazan shayar dashiba, dan ƙirjina bazai zube a banza ba, kaima baka samuba balle wani ɗanka, sannan lokacin da ciki yakai haihuwa sai dai amin cs bazanje wajen haihuwa na buɗe a wofi ba ka samu zarrar bin wata, danku mazan hausawa yanda kuka san bunsiraye akan mata haka kuke…..”
Ba ƙaramin sukar Jawaad maganar Shahudah ta ƙarshe tayi ba, da har zaice mata harda ubanki ma bunsurunne kenan saikuma ya haɗiye abunsa kawai yay shiru yana miƙewa bayan ya zame safar ƙafarsa, dolene ya koyama yarinyarnan ɗanyen hankalin da ƙwaƙwalwarta zata dawo aiki tamkar ta kowa, wlhy ya yarda wayewar da babu ilimin addini a ciki ba ƙaramin daƙiƙanci take kawowa mai itaba.
Ƙala bai ce mataba, baima ko kalli sashen da takeba yay shigewarsa bayi domin samu ya watsama jikinsa ruwa………….✍🏻
10
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
4
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Shafi na goma sha tara
……….A wannan tsakanin kam sai abubuwa suka sake rikice musu a gidan, dan salo-salo na rashin mutunci Shahudah ta ƙaro take tsulama Jawaad, shiko sai ya watsar da ita tamkarma bai san da ita a gidanba, yama koma ba kullum yake kwana a gidanba, gara yaje gidansa da su Aliyu suke yay kwanciyarsa acan, idan suka takura masa da tambayar lafiya yace Shahudah bata nan ne.
Tun suna yarda da zancensa har suka fara zargin akwai dai wata a ƙasa, amma tunda bai basu damar saniba sai basu takura ba, sun dai ɗauki aniyar tayasa da Addu’a.
Cikin hikimar UBANGIJI sai yay ma Jawaad maganin Shahudah ta hanyar jarabtarta da laulayi mai azabar tsiya, dan takai yanzu ma sai da taimakon wani take iya wasu abubuwan, shi sai bai duba abinda take masaba, a duk lokacin da ta nema taimako yakan taimaketa inhar yana gidan.
Abu ɗayane har yanzu ta kasa samu a gareshi, shine sakin fuska, gaba ɗaya tabar ganin haƙoransa a waje, baya wata doguwar magana da ita, idanma yanaji da shariyar sai yazo gidan ya fice bai tanka mataba, tun abun baya damunta harya fara yanzu, dan kuwa tana tsananin buƙatarsa a kusa da ita kuma, sai dai dukkan damar hakan ya toshe mata ita.
Inhar a gidan ya kwana da safe zai leƙa ɗakinta yaji yaya jikinta?, zai kuma tambayeta abinda take buƙata, inhar ta faɗa zaisa a sayo mata.
Idan kuma da dare ya dawo koda ya isketa a falone zai tambayeta yaya ta yini? tana buƙatar wani abu? Iya amsar data bashi zai saurara yay wucewarsa ɗaki, yana shiga yake kullowa dan karma ta shigo masa. Ba ƙaramin zafi hakan yake mataba, harma tanaji tamkar taje ta zubar da shegen cikin taga ƙarshen iskancinsa.
Sai dai zuciyarta na tuna mata gargaɗinsa na ranar, yayi rantsuwa da inhar ta zubar ta tsinka igiyar aurensu duka uku, tasan wanenen Jawaad, tasan kuma zai iya tunda har ya hau dokin zuciya akan hakan..
Ita shaida ce akan haƙurinsa, sannan kuma tasanshi inhar yay zuciya da abu akansha fama kafin ya waiwayesa, a zahiri mutane sukaga sauƙinsa yayi yawa, amma saika nutsu dashi zaka fahimci murɗaɗɗen halinsa na ra’ayin riƙau, mahaifiyarta kace mata haka mahaifin Jawaad yake, dan haka dukkan hallayar Jawaad na ubansa ne, ya kuma kwaso wasu daga uwarsa, dan itama lumbu-lumbu take wutar ƙaiƙayi.+
A yau dai kam lamarin nasa ya mata tsanani, dan ko mama Atika tabi duk hanyar da zataga Jawaad yaƙi bama kowa damar hakan hatta da kawun nansa, saima Qaseem ne ya samu damar gaggaya masa magana a kan Shahudah a office, sai kuma Jawaad ya manna masa hauka ya sharesa tamkarma bai san da shiba.
Waɗannan abubuwa suka taru akan Shahudah sukai mata yawa, dan haka ta shirya zuwa gida kozata samu sassauci dan yau tana ɗan jin jikin da sauƙi.
Dama ita babu tambayar fita a tsarinta, shirin ta tayi ba tare data nema izininsa ba, shi dama baya gidan, a office ya kwana yau.
Shirinta tayi cikin wando da riga jeans da top baƙa mai adon stones an runbuta *Beauty* da manyan baƙi da su, tayi ƙyau dan ƙyau, saboda farar fatarta na ɗaukar wankan ƙananun kaya da kalar baƙi, cikin a lafe kamar babu ɗa a cikinsa, yau dai ba’a samu damar zane fuska da kwalliya ba, fauda kawai aka shafa sai lipsgloss, ƴan arziƙin na kusa kuma, aka saka kimono tare da yafa siririn gyale akai, sai dai an saki rigar ba ɗaureba, hakan yasa taketa jan ƙasa a baya, ga glasess baƙi da aka toshe fuska dashi, ta dai fito asalin ƴar gayenta lamba ɗaya kuma shafin farko a jaridar manya.
Da kanta taja motar, yayinda kiɗa mai taushi ke tashi daga sifikun.
_______________________
BILKEESU
_______________________
Tun a harabar gidan nake tsarkake sunan ALLAH, dolene akira dukiya jarabawa ga bawa, yanzu mai wannan muhallinma dan yace ya manta da danginsa ai bakaga laifinsa ba, wani dai saikaga tamkar alƙalamin rubuta ƙaddarar rayuwarsa a hannunsa yazo…….
Zungurata da akaine ya sakani dawowa hayyacina babu shiri, harara ta gallamin da jan tsaki, “K dalla baƙauyar banza ki wuce muje, kin wani zauna kallon gida, halan yau kika fara ganin irinsa?”.
Bance komai ba, sai bin bayanta da nayi kawai.
A falonma dai akwai abin kallo da bakima bazai iya lissafowaba, abinda kawai zan iya faɗa hotunan masu gidan da aka ƙawata adon falon dasu, a yanda naga hotunan da alama yaran nasama sun zarta biyu, dan kuwa bayan waɗan na gani ga mutane uku kuma a hoto, namiji haɗaɗɗen saurayi maiji da kansa, sai ƙyaƙyƙyawar budurwa da tafi dukkan ƴan gidan asalin ƙyawu, saikace wata jinin larabawa, dan nikam bazan ce baturiya ba, dan ba ƙyawunsu nake ganiba, sai dai shigar tatace kam sak ta turawan ce, sai hoton namiji again da bazai wuce shekaru goma sha biyarba, hoton dai da gani tsohon hotone.
Na sake waigawa ko zanga inda yake babba sai dai babu.
Tunda muka shigo kawu saman bene ya haye, hakan ya saka hajiya binsa itama.
Suma duk sai suka shige ɗakunansu aka barni ni kaɗai a falon tamkar mayya, hakan baisa naji rashin daɗiba, koba komai nasamu damar yima falon kallon tsaf ai.
STORY CONTINUES BELOW

Sakkowar hajiya daga saman bene ranta a ɓace ne ya sakani kallonta, sai kuma na duƙar da kaina saboda mugun kallon data jefeni dashi, kafin tace wani abu sai ga Kawu ma ya sakko fuskarsa babu walwala.
Ni dai dama a ƙasa nake zaune, sai na ƙara ladabtuwa domin girmamawa a garesu.
Kawu yace, “Ɗiyata taso muje kiga ɗakinki kinji”.
Cikin girmamawa na amsa da “to” ina miƙewa, yana gaba ina biye har ɗan lungun dake falon, ɗakuna ne a jere guda biyu, muka isa har gaban na ƙarshen ya buɗe ya shiga, nima shigar dai nayi.
Ɗakine babba sosai, akwai komai a ciki na amfani tamkar ɗakin matar aure, matar aurenma ƴar gata ta gaske.
Da ƴar ƙura a cikinsa kaɗan, alamun dai ba amfani ake dashiba, komai na ciki kuwa kalar ja da fari ne…….
“Bilkisu nan ne zai zama ɗakin ki kinji, shi ɗin ɗakin ƴar uwarkice datai aure kusan wata tara kenan, yanzu kinga saiki maye gurbinta, inason ki kwantar da hankalinki a gidan nan, ki ɗauki kanki tamkar kowa na cikinsa, yanzu dai idan kin huta zuwa dare zamu zauna dan ki san kowa da sunansa kinji”.
“To kawu nagode sosai, ALLAH ya ƙara buɗi da haske na alkairi”.
Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “Amin ɗiyata, amma daga yau ba kawu ba, ki kirani Dad kamar yanda ƴan uwanki suke kirana dashi, kema yanzu baki da banbanci dasu a gareni kinji”.
kaina na ɗaga masa nima ina murmushin jin daɗin dajin tsantsar ƙaunarsa a raina, shine mutum na shida da arayuwa bazan manta da suba, domin sunji tausayina a lokacin da nake buƙatar hakan ga kowa, sun ƙyautata mani lokacin da jama’ar duniya suke guduna, na share hawayen da suka ziraromin a fuska.
Jinai kawai an kama hannuna, na ɗago na kallesa aɗan firgice, “Haba ɗiyata, banason na sake ganin waɗannan hawayen a fuskarki dan ALLAH, nasan bazan iya ɗauke miki dukkan matsalarki ba a rayuwa, amma insha ALLAHU zan kamanta kinji, ki daure ki saki jikinki, zanji daɗin hakan”.
Murmushi nai masa, “Insha ALLAHU Dad bazaka sake ganiba”.
“To Alhmdllh ƴar gidan dad” yay maganar yana rungumeni.
Duk saina rikice, miye hakan kuma kawun yay min?, nashiga ukuna.
Shima fuskantar abun yazomin wani iri ya sakashi sakina yana faɗin, “muje na nuna miki yanda zaki amfani da banɗaki”.
Komai sai da ya nuna min shi, yakuma tabbatar na fahimta sannan ya fita ya barni ina ƙara gwada fahimtar komai yanda bazan manta ba.
Daga baya kuma na zage na gyara ɗakin tsaf, sai naga ya sake ƙyau saboda gyara na musamman daya samu sosai.
★★★★★★★★
A daren ranar wajen cin abinci na sake sanin kowa na gidan, dan kuwa duk Dad yaymin bayani a kansu da sunansu.
Duk na fahimta, duk da dai na kula shi kaɗaine ke ra’ayin zamana a gidan, dan ko babban ɗansu da alama ban cikin tsarinsa shima, sai kallon ƙurilla yake bina dashi a yatsine, wanda hakan ya tunomin da Jazuga a zuciyata, koda na koma ɗaki sai da na zubda hawaye saboda tuno firdausi da su inna da nayi, ina kewarsu sosai, inason sanin halin da suke ciki kuma.
Naci kuka a wannan daren har na rasa hawayen tsiyayarwa, dukkannin komaina na baya ya shiga dawomin daki-daki, ganin ina neman cinye daren da tunani sai na tashi na ɗauro alwala nazo naita nafilfilina ina miƙama ALLAH godiya da kukana game da sabuwar rayuwar dana sake shigowa.
Tabbas rayuwar wannan gida tasha banban da duk inda na rayu, ba’a ɓangaren jindaɗiba kawai harda yanayin zamantakewa da tarbiyya.
Gashi dai ina samun komai na buƙata, dan ko sutura kwana na ɗaya a gidan dad ya kawomin masu yawa, sai dai kumafa duk ƙananune, dan babu ko ƙyallen atanfa.
Abincin da kowa zaici nima shi nakeci, babu wani banbanci tanan ɓangarenma.
Sannan bana aikin komai a gidan, kamar yanda yaran gidan suma basa komai sai ƴan aiki, ko gyaran ɗakina ma sai da nai magana mai aikin gidan ta daina min.
Yanayin tarbiyyar gidan ce dai sai addu’a, dan kuwa na kula dai tsantsar rayuwar turaice da ɗabi’unsu ke wanzuwa ga jama’ar gidan.
Duk kayan daga gadama zaka saka babu ruwan wani da kai, babu mai maka faɗan rashin dacewarsu, rungumar juna tsakanin mazan da matan hakan ba komai bane, shima Dad ɗin dazai tsawatar rungumemu yake, rashin girmama na gaba matsayin na yayanka wannan sam babu shi, ɓangaren ibada ba damunsu tayiba idan har ka cire Dad da ba kullum yake zama gidanba, bazan ce maka arana suna cika salla biyar babu tsallake ba har Mommy ɗin, maganar Qur’an ma ban gansa a gidanba tunda na shigo, amma akwai ɗaki na musamman domin karatu, cike yake da kowanne nau’in littafin daya shafi boko harma dana labaran turanci, komai kayi a gidan sunansa ƴanci kawai, babu mai cemaka akwai kuskure a ciki.
STORY CONTINUES BELOW

Duk ɗabi’un nasu sunmin girma, na kasa kwaikwayon ko guda ɗaya a ciki balle na riƙesa matsayin cigaba.
Hakan yasa a kullum suke hantarata da suna baƙauya ko bagidajiya, bana damuwa dan bana samun sakewar fuska daga kowannensu dama idan ka cire Dad, idan baya gida babu maimun magana sai hantara da harara.
Iyakar nan dai tsananin ya tsaya min, shiyyasa bai cika damuna ba sosai.
A ƴan kwanakin dana samu a gidan jikina harya fara nuna alamun canji, dan kuwa fatata ta fara gogewa, sannan jikinma dai da alama ƙiba zai fara, baƙina da kullum suke zagina a kansa ya fara korewa, dan duk sanda Yah Qaseem zai hantareni yakan kirani da suna baƙar banza.
A kwai ranarda Yah Salman ke faɗin wai dama na taimaki kaina nazo ya kaini asibiti anmin allurar da zan koma fara ko nayi ƙyan gani, danshi wlhy har kunya yakeji suzo suyi baƙi aga ɓaƙar fuskata a cikinsu, ni da kwalta ta titi bamu da maraba.
Dariya Aamila da Mummy sukaita tuntsurawa akan wannan zance, harma Mummy ke faɗin, “karka damu, sonake mu fita shopping ai na haɗo mata mayukan da zata kore wannan mugun baƙin, ni kaina baƙin nan nata har tayarmin da tsigar jikina yakeyi, anya Bilkisu nama taɓa ganin mai baƙinki kuwa?”.
Murmushi kawai nayi ina haɗiye kukan da yake shirin taho mani.
Yah Qaseem yaja tsaki shima daga inda yake zaune yana cewa, “Ku baƙin kawai kuke gani, ni wlhy nafi tsanar naniƙaƙƙen hancin yarinyarnan, sai kace tana gudu aka saka mata, wannan ko farin tayi an faɗa muku fasali zatayi? Indama ALLAH ya sota ya bata jiki mai ƙyau, gashi dan jaraba kullum tana fama da wannan hijjabin sai kace akanta aka fara addini, idanma zaki sauƙaƙama kanki ki sauƙaƙa yarinya, larabawanma tushen musuluncin sha’aninsu sukesha balle ke jinin wahala”.
Nan ɗinma dariyar sukayi, hakan ya sakani kasa jurewa sai da yawayen da nake riƙewa dai suka zubo, hijjab na saka na share kawai.
“Tofa, wai kuka kikeyi dan an faɗa miki gaskiya? Tab kinada aiki wlhy” Yah Salman ne mai maganar yana miƙewa zai fice.
Haka suka cigaba da cimin fuska kowa na faɗin albarkacin bakinsa, dawowar Dad ce ta ceceni na samu sukuni, shikuma ganin yanayina ya sakashi tsareni da tambayar lafiya?.
Nace masa babu komai daga barci na tashi
1
★★★★
Ina sati na huɗu a gidan da safe kowa ya fice, daga ni sai Aunty Aamila da mummy ne a gidan, kuma duk suna ɗakunansu suna barci, niko bana iya dogon barcin nan hakan ya sakani fitowa falo na zauna ina kallo a tv, ɗauke wutar da sukaine ya saka ni miƙewa, ga shirin gidan kuma yasaka naji duk kaɗaici ya taso mani, tashi nai na koma ɗaki na kwanta duk da nasan ba barcin zanyiba.
★★★★
Da ƙyar Shahudah ta iya isa gidansu saboda rashin jin ƙarfin jikinta, tai hon mai gadi ya buɗe mata, yana ma gaisheta amma bata sauraresa ba ta shige, koda tai fakin ma kanta ta kwantar a sitiyari tai shiru na wani lokaci, kusan mintunanta biyar sannan ta samu ta fito zuwa cikin gidan.
Yanda gidan yake shiru tasan su mummy basu tashi barciba, gashi tana buƙatar hutawa, tsohon ɗakinta ta wuce danta samu ta hutama ranta, dama inhar tazo gidan takan zauna acannane.
Takun takalman da najine ya sakani kallon ƙofa, har aka buɗe aka shigo.
Idanuna suka saukakan ƙyaƙyƙyawar matashiyar mace cikin ado na ainahin zubin wayewa ta shigo ɗakin babu ko sallama.
Tozali dani ya sakata zare baƙin glasess ɗin idonta da ya rufe kusan rabin fuskarta tana min kallon sama da ƙasa, nason sanin ke kuma wacece haka?.
Nikuma cire glasess ɗin natane ya bani damar ganeta duk da a hoto na taɓa ganinta, ɗiyarsu Dad da aka bani ɗakintace mai suna Shahudah kamar yanda ya sanarmin ce, yauce ranar farko dana ganta a zahiri, dan kuwa tunda nazo gidan bata zoba, dama Dad ya sanarmin batajin daɗin jikintane tana fama da ƙaramin ciki shiyyasa, amma ita bata iya sati ɗayama batazo gidanba.
Takun takalminta ya sakani dawowa hayyacina, ƙoƙarin fita take tana sake bina da kallo, sai yamushe fuska take tamkar taga wani kashi ko abin ƙyanƙyami.
Da ƙyar na iya fusgo magana a harshena nace, “Sannu da zuwa aunty”.
Banyi tunanin ta amsa mani ba, ta dai fice da ɗan gudu kamar cikin fushi ko tunanin takalmin ƙafarta zai iya kadata bataiba kuwa……
2
______________________
JAWAAD
______________________
Ɓangaren Jawaad kuwa yau gidan Alhaji Kokino ya sake kai ziyara, inda ya samu damar ganawa da dattijuwar nan da wancan zuwan ta kawo musu kayan breakfast.
Wannan karon ma itace ta kawo masa ruwan sha, dan shi kaɗai ya zo sai gimba.
Koda ta ajiye ruwan bayan gaisuwa sai tai yunƙurin juyawa zata fice abinta.
“Da alama dai a ranar sha uku ga watan bakwai, dai-dai da washe garin rasa Alhaji wani abu ya faru wanda ganinsa ko jinsa ya jawo Accident ɗin faɗuwa a gareki har kika samu ciwon da har yanzu kike jinsa a jikinki, kuma tabbas wannan abun da kikaji ko kika gani yana da nasaba da Alhajin”.
Cak ta tsaya, ita bata fitaba bakuma ta dawo da baya ba, ba komai ne ya jawo hakanba sai kalaman Jawaad masu saka rikici ga duk mai alaƙa dasu…..
Jawaad dake ƙoƙarin zubama kansa ruwa a kofi ya sake katseta da faɗin, “Abin bana dogon tunani bane mama, abin kawai na sani zan cigaba da riƙe Yazeed har sai nasan dalilin faɗuwarki a wannan ranar, miya tsorataki?, abu na gaba ki taimaki kanki kije asibiti a duba ƙafarki, dan naga har yanzu kina ɗangyasata”.
Ya kai ƙarshen maganar yana takowa inda take a tsaye.
Hakanne ya sakata kallonsa ta kauda kanta da ƙoƙarin haɗiye hawayenta, tace,
“Miyasa zaka sakamin yaro cikin al’amarin da baisaniba?”.
“Mama idan har kina buƙatar na sanar masa komai a yanzu ai bamu makara ba”.
Idanunta jajur ta ɗago ta kallesa, shima kallon nata yake, amma sai ya janye nasa idanun ganin tana neman rikicewa, yay murmushi yana sake matse kofin hannunsa na glass, rashin ƙwarinsa ne ya saka kofin tarwatsewa sauran ruwan ciki ya jiƙe masa hannu ya zuba a ƙasa, guntayen kofin kuma sukai ɗai-ɗai a ƙasan suma.
Dattijuwa ta sauke idonta akan hannun Jawaad har zuwa kofin da yaya kuci-kuci a saman tayis tamkar ba shiba, sake maida kallonta tayi gareshi a wani yanayi mai nuni da tsantsar damuwarta.
Jawaad ya zaro handkherchief a aljihunsa ya goge hannunsa tas sannan ya turasu a aljihu duka biyun yana ja da baya fuskarsa na ƙara tsukewa.
“A duk lokacin da aka zuba ruwa a glasscup yana da matuƙar ƙayatarwa, har kakanji bakason ɗauke idonka wajen kallonsa koda zaka kwana a haka, amma da tsautsayi zaisa wannan kofin fashewa a hannunka zaka iya gamo da haɗarin yanka maisa aji zafi, shi kuma ruwan dake ciki idan har ya zuba a jikinka ƙoƙarinka kawai ka goge, damshin da ya rage iskace kawai ka iya busar maka dashi, wanda yake a ƙasa kuwa sai kaga dukansa ya zama haɗarine, musamman akan abu mai santsi irin tayis. Na tabbata duk wanda zai shigo falon nan a yanzu zaiyi ƙokarin ganin bai taka wannan ruwan da glasess ɗin nanba, yaron da hankali bai gama bin jikinsa bane kawai zai maidashi abun wasa. Mama bansan yaya zaki rarraba zantukana a jujuwan da suka cancantaba, ni dai kawai abinda raina ya bani komai tsanani zansan gaskiyar zancen….”
Ya raɓata ta gefe zai fice, yana saka ƙafarsa ɗaya a waje yajiyo sautin dariyarta.
Dakatawa yay tare da juyowa yana kallonta.
Tace, “Yarona idan kwalba ta fashe a hannun mutum zafinta kawai zaiji saiko fitar jini da zai gani, amma idan zuciya ta samu suka har abadan wannan tabon baya gogewa komi adadin shekarun da aka ɗauka bayan jin wannan ciwon, ruwan da zai zuba a jiki a goge iska ta busar bashi da banbanci da hawayen dake kwarara daga idaniya zuwa fuska a goge iska ta busar da sauran, inda ake samun banbancin kawai shi wannan ruwane, daya zube labarinsa ya shuɗe, suko waɗannan hawayene koda sun bushe ba’a daina iya ƙididdige su a tsarin da sukazo na farin ciki ko akasinsa har ranarda fitar numfashi zata yanke, ka cancanci a kiraka da suna *Ƙwai cikin ƙaya* sannan kuma lallai kai *Yarone ɓata hankalin dare kayi suna*, duk abinda kake buƙata daga gareni zaka samu, amma ba’a nan gidanba, mu haɗu a gidan daka ɗauki yarona Yazeed………….✍🏻
1
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Ashirin ta tabbata💃🏻🕺🏻😜
…………Tunda suka baro gidan Alhaji kokino maganganun tsohuwar ne kawai ke yawo a zuciyar Jawaad, gaba ɗaya ya kasa fahimtar alaƙar ɓatan Alhaji kokino da kalamanta, ya rarrabasu ajujuwa daban-daban amma basa bashi ainahin abinda ya dace, yay guntun tsoki yana cigaba da shafa gemunsa a hankali, yayinda idanunsa ke kallon hada-hadar jama’ar gari.
Daga nan office ya koma, inda ya tarar da baƙuwa zaune tana jiransa.
Rose da tunda Jawaad ya fito a mota ta dasa masa idanu ko ƙyaftawa batayi ta sauke nannauyan numfashi lokacin daji ƙarfin ƙamshin turarensa gab da ita.
Ta bishi da kallo tana sake yabama kwarjininsa da cikar zati da ALLAH yay masa, tasan sarai ya ganta, amma jiba yanda ya basar abinsa.
Murmushi tayi ta miƙe tana gyara zaman wuyan rigarta.
Itama ƙyaƙyƙyawar ce ba laifi, gata doguwa masha ALLAH, yanda take tafiya cikin zafin nama tana juya dukkan illahirin jikinta zai tabbatar maka da tasamu isashen training wanda ya haɗu da ainahin halittar yanga ta ɗiya mace.
Kanta tsaye ta nufi Office ɗin Jawaad, wanda kowa yasan bata da shamaki da hakan.
Yana zaune a kujerarsa yayinda wani ke tsaye a kansa yana masa bayani akan aikin daya sakashi, har Rose ta zauna bai kalleta ba, dan idonsa nakan wasu takardu ne, itama batace komaiba ta dai zauna tana saurarensu.
Sai da wancan yakai aya sannan Jawaad ya ɗago yana kallonsa da rikitattun idanunsa da mafi yawan lokuta ke tsorata duk wani maison kawo masa wargi.
“Aikinka yayi ƙyau, sannan yana tafiya dai-dai, yanzu dai kafin dare a tababbar an kamo min Ɗan Lawan da yaransa baki ɗayansu, sannan itama kanta Kande barikin a kamomin ita tare da wiwi ɗin dasu ɗan lawan ɗin ke kai mata ajiya”.
“Okey sir” ya amsa yana mai sara masa, takardu biyu Jawaad ya miƙa masa, ya amsa yana ƙara sara masa sannan ya fice.
Lokacinne Rose ta miƙe tai salute ɗin Jawaad dake haɗe takardun daya baza bisa tebir ɗin waje ɗaya, fuskarsa ta sake tsukewa alamar babu wasa, a dake yace,
“Ban saniba yanzu ko zaki maida hankalinki ga aikinki, kokuma zaki cigaba da ɓata lokacinki akan farautar soyayya?”.
Ido Rose ta lumshe tana sakin murmushi mai sauti, ta kuma ƙamewa tare da sarama Jawaad a karo na biyu, “Boss duk zaɓin daka bani zan riƙe”.
Ɗago ido Jawaad yay ya kalleta, mikuma ya tuna sai ya saki wani guntun murmushi yana girgiza kansa. Ya jawo drawer ɗin gefensa ya fiddo bindiga ƴar ƙarama mai ƙyau, saman tebir ɗin ya ajiyeta idonsa akan Rose da itama kallonsa take ko ƙyaftawa babu, yaɗan bugi bindigar kaɗan sannan ya turata gabanta cike da salo.
Itama cikin nata salon ta ɗauka ta wurwurata tare da buɗeta. Babu komai a cikinta, hakan ya sakata sake kallon Jawaad daya maida hankalinsa ga latsa Computer ɗin saman tabir ɗin.
Ba tare daya kalleta ba yace, “Riƙe soyayya a wajenki tamkar riƙe bindiga ne babu bullet a cikinta, kinsan kuwa a garemu jami’an tsaro sam bindigar bata da amfani, domin ba bindigar bace ƙarfinmu harsashin cikinta ne, shima kuma yana amfanine idan an samu ƙwarewar iya harbi. Karki yarda a karo na biyu kiyi sakaci da damarki, Jawaad akwai mai shi”.
“Hummm” ta faɗa cikin ƙunar zuciya ba tare data iya cewa komaiba.
Shima bai sake cemata komanba tsawon lokaci kafin ya miƙe zuwa ga wata kanta, yabi tarin files ɗin cikinta da kallo, da alama dai kwanan wata yake dubawa, har idonsa yakai inda yake buƙatar zuwa sannan ya zaro wata takarda, mazauninsa ya dawo fuska a tamke ya miƙa mata, “Ki samu su Jabeer da wannan file ɗin zakuyi magana”.
“Okey Boss” ta faɗa cikin rissinawar girmamawa gareshi tana amsar file ɗin. Sai da ta sake salute nashi sannan tai ƙoƙarin ficewa.
“Ji mana” Jawaad ya faɗa yana bin Rose da kallo.
Juyowa tai ta kallesa, da ido yay mata nuni da harsasai (bullets) kusan goma daya ɗora a tebir ɗin.
Dawowa tai da baya ta kwashe tana faɗin, “Thanks you boss”.
Baice da ita komaiba, saima maida hankalinsa yay ga kallon Computer harta fice.
Aikinsa ya cigaba dayi, duk da zuciyarsa na tunanin halin da yabar Shahudah jiya da dare, tana bashi tausayi saboda wahalar da cikin yake bata, amma bayason nuna mata hakan koda a fuska ne.
Ƙarfe huɗu da wasu mintuna ya fito massalaci ya zarce office ɗin boss ɗinsa domin amsa kiransa.
Bayan nuna girmamawarsa garesa ya zauna kamar yanda ya bashi izini.
“Jay yaya dai? Na jika shiru, ko akwai matsala ne?”.
“A’a Sir, babu wata matsala aiki yana tafiya dai-dai, a yanzu haka zancen da nake maka insha ALLAHU ƙiris yama rage”.
“To Alhmdllh, banason aikinnan ya shige satinnan, dan yanzu hakama wata ta taso kuma”.
Kallonsa Jawaad yayi da son jin ko minene?.
Ya cigaba da faɗin, “Akwai wani mai kayan miya anguwar ƴan kilishi daga can ƙasan layin, majiya mai ƙarfi ta kawo mana alamar tambaya a kansa, saboda gagarumin fashin da akayi satin baya gidan Alhaji Sulaiman, Qaseem aka ɗora akan case ɗin, sai dai naga baiyi wani serious ba sam, yamafi maida hankalinsa akan wannan case ɗin da ayanzu nasan kai kama kusa kammalashi”.
“Okey Sir, yanzu mikakeson nayi ni akai?”.
“Case ɗin nakeso ya dawo hannunka Jawaad, dan waɗannan ƴan fashin bincikenmu ya nuna sunada laifuka masu yawa, amma basu barin kowacce damar da za’a gane sune, sai yanzune muka ɗan samo bakin zaren”.
“Na gane sir, to amma an buɗema case ɗin file ne?”.
“No, nabar komai a hannunka, dan banida shakku akanka sam”.
Kai Jawaad ya jinjina masa, “To amma sir kozan iya sanin wanda ya kawo sirrin?”.
“Mizai hana Jay”.
Murmushi Jawaad yayi, dan har zuciyarsa yana ƙaunar ogan nasa, ALLAH ne ya ɗaga darajarsa a hukumarsu, da kuma ƙoƙarin ogan nasa, dan ƙarancin shekarunsa basukai ace yana a kujerar da yakeba a yanzu, amma saboda manyan ayyukan da sir Ahmad Barewa ke bashi yaketa samun cigaba, har takai yanzu yana cikin jami’an da hukumar ƴan sanda ta DSS ke ji dashi saboda ƙwazonsa, da salon aikinsa, duk da kuwa ta wani ɓangaren yana zagayene da maƙiya masu burin taɗosa ƙasa a kullum.
Ya daɗe a Office ɗin suna tattaunawa kafin ya fito.
+
STORY CONTINUES BELOW

_________________________
“Ke kuwa yaushene zakiyi hankali mamana?”. Hajiya Humaira ta faɗa saboda faɗowa kanta da Shahudah tayi tana barcinta.
Baki Shahudah ta zumɓura tana faɗin, “Ni Mummy inada hankalina, wai wacece a ɗakina kuma?”.
Baki Hajiya Humaira ta taɓe tana sakkowa daga saman gadon tare da jan tsaki, “Ƴar uwarkuce”.
“Ƴar uwarmu fa mommy? Waccan baƙar yarinyar?”.
“Ita ɗinfa, ɗiyar ƙanwar dad ɗinkj Gurguwarnan da kika taɓa ƙonawa da shayi wani zuwa data taɓayi kuna primary lokacin, koda yake dawuya dai ki tuna ma”.
“Tab wlhy mummy ban mantaba, shine Dad ya jajubo mana ƴarta? Itama gurguwarce halan?”.
“Ko ɗaya, lafiyarta ras itakam, mamar tata ta rasune ai, shine ya kawota nan wai tayi karatu”.
Dariya sosai Shahudah take kwasa harda kwanciya, cikin dariya take faɗar tab ɗi, “Wannan mummunar ce za’aima gatan karatu? Irin waɗannan ko a makarantar ma mi suke ganewa yo? Amma kuma shine ama rasa inda zata zauna sai ɗakina” ta ƙare maganar da kumbura baki.
“Uhm, ke bakisan tsiyar da mukasha akan hakanba da shi, yanzu dai karkice komai ki bar mata ɗakin, ke sai a gyara miki na kusa dani, dan idan kikace wani abu akanta komai zai iya faruwa, ya ɗauki son duniya ya aza a kanta waishinan mai riƙon amana”.
Sosai lamarinnan ya zafi zuciyar Shahudah, harda ma dad ɗinsu wani maganar rashin tarbiyya, na zata Hajiya Humaira zata kwaɓeta sai naga kawai tayi dariya.
Tunda ta fita sai nima na kasa daurewa na fito falo na zauna, kusan awa ɗaya ina wajen zaune duk damuwa ya rufeni, dan bansan dalilinta na fita da gudu ba.
Aunty Aamila ta fito daga ɗakinta cikin figigiyar rigarta ta barci, wadda kaɗan ta zarta cinyarta.
Kallo ɗaya taimin taja tsaki ta wuce tebirin cin abinci.
Lamarinta baya damuna nikam, hakan yasa ko sashen da take bamma kallaba.
Ina zaune a wajan Mummy da baƙuwarmu suka fito, na gaida Mummyn cikin girmmawa kamar yanda na saba.
Amsawa tayi itama cikin nuna halin ko in kula, aunty Shahudah kam bamma isheta kalloba, hakan ya tabbatar min itama dai bazan samu karɓuwaba a gareta kenan, ban damuba, dan ba yaune karon farko dana fuskanci hakanba.
Zuwan Aunty Shahudah gidan yaɗan sake takurani, saboda wulaƙancin da takemin yafi na kowa muni, ko abu na taɓa ita bazatayi amfani da shiba, a cewarta karna gogama ɗan cikinta Munina, nakanyi murmushi aduk lokacin da naji furucinta.
Takai inhar tana falo zaune takance bazan zaunaba wlhy, banaja da ita saina tashi na fita kona koma ɗaki, kaida kazo cin arziƙi miye naka na zaƙewa?.
Kwannanta uku a gidan, duk da kuwa tun a daren da tazo naji suna tafka bala’i da mijinta a waya akan kwannan nata, dan naga tanata magana a zafafe akan dan tazo gidansu zata kwana dole saita sanar masa.
Da alama ma yanke mata waya yayi kafin takai zancen ƙarshe, dan kuwa sai faman faɗin, “Hello hello takeyi, daga ƙarshe cikin takaici tai jifa da wayar saman kujera tana masifa iya iyawarta akan ya kashe mata waya.
Itako Aunty Aamila sai zugata take akan wulaƙancin da yake mata yayi yawa, ni dai banji ƙarshen zancenba na shige ɗaki, dama daga kicin nake na zubo abinci, suko suna a tebir zasuci nasu.
________________________
Ran Jawaad ya ɓaci da ya dawo ya iske Shahudah bata gida, hakanne ya sakashi kiranta amma saita sanar masa tana gidansu, ya tambayeta da izininwa? tahau kansa da masifa, shine kawai ya yanke wayar ba tare daya gama saurarenta ba.
Sam bayason jin zafinta da yake ya cigaba da girmama cikin ransa, dan haka ya tashi yay shirin fita dukda kuwa lokacin ƙarfe tara da rabi na dare, kuma dawowarsa gidan kenan ko hutawa baiyiba.
Da kansa yaja motar dan yabama gimba damar zuwa ya kwanta ya huta.
Kansa tsaye gidan dattijuwarnan ya nufa, yanabin address ɗin da su Hafez suka bashi dalla-dalla.
A ƙofar madaidaicin gida ya tsaida motar dajin tabbacin nanne, dankuwa duk abinda aka kwatanta masa a jikin gidan ya gansa, kashe motar yay sannan ya fito cikin nuna alamun tsantsar gajiyar dake tattare dashi.
Ya kulle motar amma sai bai fitoba ya fara ƙoƙarin yin kira cikin ƙaramar wayarsa.
Bugu uku aka ɗaga, “Gani a ƙofar gida” ya faɗa idonsa akan murfin gidan.
Bansan amsar da aka bashiba daga can naga dai ya kashe wayar yana fitowa a motar, bindigarsa ya ɗauka ya tura a aljiyu sannan ya rufe murfin motar yana mai kulleta gaba ɗaya.
Dai-dai nan dattijuwa mai aiki gidan Alhaji kokino ta fito sanye da lulluɓi.
Da hannu tai masa nuni alamar su shiga, babu musu ya bita, bayan yaɗan wawwaiga bayansa yaga babu alamar kowa a wajen, dukda ma anguwar babu wani isashen haske saboda rashin wutar lantarki.
Gidan bawani babba bane ammafa yasha gyara, dan fes yake sannan kuma da gani babu ƙananun yaran da zasu ɓata.
Zama yay a farar kujerar roba dake ajiye a bangon yamma da yake ƙyautata zaton kicinne, itama ta zauna a ƙofar kicin ɗin bayan ta kawo masa tea tamkar tasan yana buƙatarsa a halin yanzu.
Godiya yay mata kuwa ya ɗauka yana sha.
“Bani da tabbas amma inaji a jikina kasan inda Alhaji yake”.
Jawaad dake ƙoƙarin kai kofin shayi bakinsa ya dakata yana kallonta, leɓensa na ƙasa ya tura cikin bakinsa yana tsotsa tare da kafeta da wani kallon nazari na seconds biyar, sai kuma yay murmushi yana ƙara damƙe kofin shayin da hannu biyu yakai bakinsa ya kurɓa.
Itama kallonsa takeyi har yanzu, sai dai bata sake cewa komaiba.
Jawaad ya cigaba da shan shayinsa kawai idonsa na kallon yanda iska ke kaɗa labulen ɗakin matar.
Yasha kusan rabin kofin shayin sannan ya ajiye yana sauke ajiyar zuciya, idonsa akanta.
“Mama shekararki nawa kina mata aiki?”.
Murmushi dattijuwa tayi tana kallonsa, “Yarona ai mai son kama fara sammako yakeyi”
“Hakane” Jawaad ya faɗa yana shafa kansa cikin murmushi.
“Miyasa take ɓoyemin kanta har yanzu?”.
“Bani da wannan amsar a zahiri da baɗini”.
Kansa ya rausayar kawai, idanunsa na sake rikiɗewa zuwa ja sosai, sai haɗiyar numfashi yake da zafi, hakan yasaka zuciyarsa gudu tare da tsitstsinkewa…….
Mama ta katse masa tunani da faɗin, “Ta bani saƙo na baka”.
Ɗago kansa yay ya kalleta, amma baice komaiba.
“Tace ka sadaukar, a cikin hakan akwai alamar tambaya? Idan kabi diddigi zaka fahimta”.
“Zanyi biyayya, sai dai zan cutu kuma”.
“Shiyyasa nazo maka da maganin hakan”.
Miƙewa Jawaad yay yana kallon agogon hannunsa, “Ina saurarenki, dan lokacina ƙararrene”.
“Karka damu nima komai inayinsa da ƙa’ida. iya ruwa fidda kai, amaryar alhajice mafitarka”.
Jawaad ya juyo yana kallon dattijuwa hannuwansa duka a cikin wandon jeans ɗinsa, “Mimene nata burin?”.
“Kisa da mallakar abinda ya tara”.
Kansa ya jinjina yana murmushi, ahankali ya furta “Abin birgewa”.
Kallonsa mama tayi tana murmushi itama.
Takowa yay ya dawo gabanta yana ɗan jingina da bango, yace, “Shine kikaji a ranar da kika faɗi kenan?”.
Cikin sauke numfashi mama tace, “Kusan haka yarona, sai dai tsoron ya gauraya ne da cin amanar aure, kuma da makusancinsa”.
Hannu ɗaya Jawaad ya ciro a aljihu yana mai shafa fuskarsa, “Idan babu kuskure a hasashena auren manufa tayi da haɗinkan ƙaninsa kenan?”.
“Hasashenka yana kan dai-dai, kamar yanda sukuma ka ruguza musu nasu a ranar da Alhaji zai dawo daga tafiya shi da ita”.
“Zan samu dukkannin bayanan?”.
“Ƙwarai kuwa, harma da wanda baka tambaya ba” tai maganar tana kunce ƙullin haɓar zaninta ta ciro wani ɗan abu ta miƙa masa.
Amsa yay yana sauke numfashi, “Nagode ƙwarai da gaske mama. A sanar mata ina buƙata matuƙa, sannan ke kuma yaushe aikinki zai ƙare a gidan?”.
“Eh to, inada zaɓi biyu ne, sannan dama ɗaya kacal, a koda yaushe za’a iya nemana a rasa”.
“Shikenan, ni zan wuce, a daren yau zan ƙulle bakin zaren”.
“Kariyar ALLAH ta tabbata a gareka tareda rahamarsa akowane lokaci”.
“Amin ya rabbi mama, nagode sosai, da safe Yazeed zai dawo gida”.
Murmushi kawai tai masa, shikuma ya fara taku cike da kasala ya fice daga gidan.1
Buɗe motarsa yay ya shiga sannan ya rufe kansa, ya buɗe hannunsa dake rumtse da abinda mama ta bashi, idanu ya tsira masa yana kallo, kusan mintuna uku sannan ya ajiye yana tada motar ya fice daga anguwar.
Tuƙi yake amma hankalinsa kashi sittin baya a wajen, gefen titi ya samu jikin wani ƙyamiz yay fakin motar, ya cire babbar wayarsa a caji ya danna kiran Jabeer, bugu ɗaya ya ɗauka, sai dai yanda yaji muryarsa ya bashi tabbacin ya fara barci ne.
“Barci kake?”.
Jawaad ya faɗa a ƙasan maƙoshi.
Daga can Jabeer yace, “Wlhy kuwa barcine ya figeni a falo ma, yaya kana office ne?”.
“Eh to badai a cikiba, amma ina akan aikine, inasu Aliyu?”.
“Duk gasu muna a tare”.
“Yauwa ku kasance cikin shiri yanzu nima zan iso”.
Bai jira amsar Jabeer ba ya yanke wayar.
Rose ya kira, itama bugu ɗaya ta ɗauka, ko gaisuwarta bai sauraraba ya fara faɗin, “Yanzun nan ki kira number dana baki ranar, ki kirata da wayar dana baki ki sanar mata tazo bayan kamfanin robobi na kwanar gulbi ta sameki, wannan wayar ta ƙawartace wadda da ita suke haɗa komai, dan haka zatazo da sauri”.
“To amma boss kana ganin zatazo a darennan?”.
Tsawa ya daka mata wadda ta sakata firgita har tana neman yadda wayar, ta daiyi nasarar damƙeta da sauri tana faɗin, “Sorry Boss”.
Tsaki mai ƙarfi Jawaad yaja yana katse kiran, dama zuciyarsa a saman maƙoshi take sosai.
Motar ya tayar yaja da uban gudu zuwa gidansa dasu Aliyu ke ciki, shigowarsa falon yasasu miƙewa su duka cikin girmamawa, hannu ya ɗaga musu kawai ya wuce ɗakin da ke cikin falon, mintuna kamar uku sai gashi ya fito da mace da shekarunta ba zasu gaza talatin da biyu ba.
Dukansu sunsan da zamanta, dan haka basu wani damuba, Jawaad ya ciro waya a aljihunsa yay danne-danne yana miƙa mata, karɓa tayi tana kallonsa a yanayin tsoro-tsoro bariki-bariki….
“Ki kira number nan, ki sanar masa kina tare da Alhaji Kokino, yanzunnan tazo bayan kamfanin robobi na kwanar gulbi ta sameki, kuma yanzunnan”.
Bakinta ta taɓe tana kallon Jawaad ɗin, “Yallaɓai to miyasa zanyi hakan? Bayan kasani na sani Alhaji baya tare dani?”.
Bindiga ya ɗora mata a saman kai ba tare daya ce komaiba.
Take jikinta ya fara mazari, ta shiga ƙoƙarin yin abinda yace.
Yace, “Ki tabbatar muryarki ta fita normal babu gargada a cikinta”.
Zufar data fara jiƙa goshinta ta goge tana haɗiye yawu da ƙyar ta saka wayar a kan kunnenta.
Duk yanda Jawaad ya shaida mata haka tayi, su dai su Hafiz suna tsaye suna kallonsu duk da sun kasa gane kan abokin nasu ma, tunda bai musu bayanin komaiba.
Bayan ta kammala wayar Jawaad ya maida bindigarsa a aljihu yana kallon su Hafeez.
“Zan barta tare daku, nanda mintuna ashirin zan iya kiranku, zakuzo bayan kamfanin kuma ku sameni”.
A tare suka jinjina masa kawuna, ya fice da hanzarinsa………….✍🏻
Kutayani da addu’a nabar wannan ragwantakar typing ɗin🤦🏻♀, ni kaina sainaji kamar baniba🙁, sai bayan kwana bibbiyu fa nake iya tafo shafi ɗaya😞🙆🏻ɗaya, koda yake kuma naga maba buƙata kukeba, dan Comments ma wahalaryi yake muku, shi kuma comments yana karama marubuci ƙwarin gwiwa ne, masuyi ina godiya sosai😘😍, kuma masu karantawa ku wuce ngd😆, mu tafi abinmu kawai a haka, randa na samu dama na ringa tafo muku⛹♀🤸🏻♀🤸🏻♀Shafi na ashirin
………..Guri Jawaad ya samu yay fakin nesa da gidan Alhaji kokino, ya ɗauki ƙaramar wayarsa yay kiran Rose, bugu biyu ta ɗaga.
Kafin yace wani abu tai saurin faɗin, “Sir komai ya tafi dai-dai, yanzu haka ina ƙyautata zaton kowane lokaci zata iya tahowa”.
“Yayi, yanzu haka ina ƙofar gidansu, zankira su Aliyu suzo da ƙawar tata, duk yanda za’ai karki bari tazo ta sameki a wajen koda ta rigasu zuwa”.
“Okey sir”
Rose ta faɗa cikin girmamawa.
Wayar ya katse, ya tada motar ya ƙarasa ƙaton gate ɗin gidan Alhaji kokino.
Horn yayi, babu ɓata lokaci baba mai gadi ya buɗe dan yasan da zuwansa, yay fakin motar ya fito, a kuma dai-dai wanna lokacinne Hajiya Usaina ta fito kamar a rikice, motarta da Jawaad ya kare ta nufa, sai da ta zira key zata buɗe ta juyo da nufin yima baba maigadi magana ya buɗe mata gate idonta ya sauka akan motar Jawaad, yanayin da take cikine ya hanata fahimtar motar bata gidan bace ba.
Ranta a ɓace ta shiga kwala kiran “Baba Dauda! Baba dauda!!”
Jikin Baba mai gadi na rawa ya rugo zuwa gareta yana amsawa da “Na’am hajiya, afuwa naɗan zagaya banɗakine wlhy”.
Batako sauraresa ba ta nuna motar Jawaad, “Uban waye yay fakin mota a gurin nan? Bayan ansan ko yaushe zan iya fita tunda inada mara lafiya a asibiti”.
“Kiyi haƙuri hajiya baƙone yanzu kuma ya shigo shima” ‘Baba yay maganar yana nunamata Jawaad dake tsaye jikin motar yana waya hankalinsa kwance tamkar baisan mi sukeyiba, nanko dukkan hankalinsa na kansu’.
Kaɗan ya rage key ɗin motar data zare daga jikin motar ya faɗi, tai saurin damƙesa dan ba ƙaramin razana tai da ganin Jawaad ɗinba, fasa buɗe motar tayi ta nufo inda Jawaad yake tana ma baba maigadi alamar ya tashi da hannu.
Jawaad ya janye wayar daga kunnensa yana maida hankalinsa gareta, cikin harɗewar harshe tace, “Yallaɓai lafiya kuwa a daren nan? Ko anga Alhaji ne?”.
Fuskarsa ya kauda daga gareta tamkar baiji mi taceba, ya tura wayar tasa a aljihu yana komawa jikin motarsa ya jingina, cike da nutsuwa ya maida hankalinsa gareta, “Nazone inason magana da ɗaya a cikinku, ke ko Hajiya babba”.
“To Yallaɓai nidai amin afuwa jikin mamana ne ya motsa, shine aka kirani asibiti”.
“Okey babu damuwa, bara na bari sai da safe na dawo, ALLAH ya bata lafiya”.
“Amin ngd” tai maganar tana barin wajen cike da sauri, dukta rikice, da alama kuma ganin Jawaad ne ya kawo hakan. Cikin gida ta koma ba tare da tasan mizatayo ba kuma.
Murmushi Jay yayi yana ɗauke ido daga kanta, ya maida dubansa ga baba maigadi yana faɗin, “Buɗemin gate, ina fatan komai done?”.
“Komai dai-dai ƴallaɓai, ALLAH ya ƙara nasara”.
Murmushi Jawaad yay masa, ya buɗe motar ya shige ya bar gidan saboda baba ya buɗe masa gate ɗin.
Yana ƙoƙarin harba motar kan titi yana kiran waya, ya ajiyeta a saman cinyarsa bayan ya saka a hansfree.
“Hello Hafiz!, kuyi maza mu haɗu acan ɗin, idan kun rigani zuwa saiku jirani, inaso saina fara ajiyeshi kafin ku sauketa kuma, saboda tsarin yayi dai-dai”.
“Okey Boss” Hafez ya amsa daga can yana gimtse wayar, zuwa yanzu kam ya fahimci mi Jawaad ke shirinyi, dan haka ya kalli su Jabeer da suma sunji komai saboda a hansfree ya saka.
Dariya sukayi gaba ɗaya, dan sun fahimci inda aikin ya dosa yanzu kam.+
“Daga jikin kamfanin ta baya yay fakin motar, ya fito a ɗan hanzarce bayan ya saka baƙar safar hannu a hannunsa, bayan motar ya buɗe bayan ya wawwaiga babu alamar mutun ta ko ina, yakai hannu ya jawo mutum a seat ɗin baya da ƙyar, dan babu laifi yanada jiki, kuma da alama a sume yake ma. Da ƙyar ya iya saukeshi ƙasa, sai hakki yake, ya sake ɗagashi da ƙyar zuwa wani ƙaramar baca ta kwano dake wajen ya ajiye saman kujera, igiya ya saka ya ɗaɗɗauresa kafin ya zaro allura a aljihun wandonsa yay masa a hannu, bai jira komaiba ya zare abinda suka rufe masa fuska ya fice da hanzari yayo waje.
Mota ya koma, da babaya yajata yaɗan koma nesa da wajen sannan ya kashe ya sake fitowa, wayar dake hannunsa ya ɗora a kunne yana fadin, “Zaku iya kaita”.
Bai jira misu Aliyu zasu ceba ya yanke wayar ya koma kiran Rose wadda tana daga can ɗan nesa da kamfanin itama, tana ɗagawa yace, “Kin ajiye wayar da kika kiratane a bacar?”.
“Yes boss, tun ɗazun ma”.
“Okey kizam cikin shiri, dan bayan awa ɗaya kacal zamu far musu kafin suyi tunanin kashesa”.
“Angama boss”.
Katse kiran yay yana lumshe jajayen idanunsa tare da dafe kai, babu abinda yake buƙata sai hutu, dan a matuƙar jigace yake.
A haka Su Jabeer suka ƙaraso inda yake, dan Aliyu ne kawai yakai matar cikin bacar da Jawaad ya ajiye Alhaji kokino.
Fitar Aliyu da kamar mintuna biyu Alhaji Kokino ya farfaɗo saboda Allurar da Jawaad yay masa, mutsu-mutsu ya fara yana ƙoƙarin buɗe idanu da ƙyar, hakan ya saka matar da Aliyu ya kawo miƙewa jiki na rawa ta nufesa, dan itama tunda Aliyun ya jefota kanta a juye yake bata fahimtar komai, ta rasa dalilinsu na aikata hakan.
Da yake kuma akwai duhu sai bata san ita da waye bane a wajen, da lalube ta isa inda yake, tana ɗora hannunsa jikinsa wayarta da Rose ta ajiye a bacar ta hau ring.
Cikin tsananin firgita ta juya ta kalli wajen, inda shima Alhaji Kokino ya sauke wani nannauyan numfashi, wayar ta nufa dan ɗan hasken screen ɗin ya haska bacar kaɗan, mamaki ya kamata ganin wayartacema ashe, kuma Hajiya Usaina ce ma ke kira, kasa ɗagawa tai harta tsinke.
Aka sake kira, cikin rashin sanin abinyi ta ɗaga, daga can Hajiya Usaina amaryar Alhaji kokino tace, “Lamcy gani a wajen kamfanin, ke kina ta inane?”.
Sosai Lamcy ta zaro idanu waje, amma sai cikin rawar baki ta amsa da cewa, “Ki duba akwai baca ta kwanon langa-langa daga gefen gabas, sai dai karkizo da mota Usaina, wannan lamarin akwai lauje cikin naɗi ba shirinmu bane”.
Katse kiran Hajiya Usaina tayi, dan tafi buƙatar su karasa ga Lamcy komaima sayi acan, fita sukai daga motar itada Abdul ƙanin Alhaji kokinon, dan tare sukazo, kuma yaji komai da Lamcy ta faɗa.
A baca kuwa ɗunbin mamaki da al’ajab ne ya kama Alhaji kokino saboda ganin Lamcy aminiyar matarsa Uswina, ga kuma furucin datai a waya, wanda ya tabbatar masa cewar da Usainar tai waya, “To minene shirin nasu?” yay tambayar a zuciyarsa.
Kafin ya samo amsa ne Abdul da Usaina suka shigo cikin bacar.
Gaba ɗaya sai tunanin Alhaji kokino ya sake birkicewa, ya kafe ɗan uwan nasa da kallo yana faɗin, “Abdul!” sai dai muryar tasa bata fita sosai.
Dariya Abdul ya kwashe da ita yana maida hankalinsa kan Lamcy dake ƙokarin musu bayanin wannan fa sam ba shirinsu bane, karsu ce zasuyi wani yunƙuri a zagaye suke.
Saurin dakatar da ita Abdul yayi da faɗin, “K dalla malama a zagayenwa? Kefa kika kiramu kika kuma sanar mana komai, ni yanzu babuma maganar ɓata lokaci anan, mu aikashi kawai, dan yanzu ƙarfe biyu saura, ya kamata ace nanda uku mun kammala komai munbar wajennan” ya ƙare maganar yana buɗe jakkar da sukazo da ita.
Duk yanda Lamcy taso su fahimceta hakan ya gagara, sai ma ƙoƙarin saka Alhaji kokino suke akan dole yana saka musu hannu a takardun dake cikin jakkar, waɗanda duk na kamfanoninsa ne da kaddarorinsa dake ƙasashe daban-daban harda na nan ƙasar.
Haushi ya kume zuciyar Lamcy, dan ta kula gaba ɗaya kawunan su hajiya Usaina a toshe suke, da ƙarfi ta hankaɗe Abdul daya kama hannun yayan nasa yana sakashi saka hannun dolen.
Kallonta yay da mamaki mai haɗe da ɓacin rai, “Wai ke mike damunki ne? Kokinsha wani abu dayafi ƙarfin kankine?…….”
“Ba nice banda hankaliba Abdul, kune baku da hankali, to idanma barci kuke ku farka wannan shirin duk wasune da nima ban saniba suka tsarashi!!!”.
Yanda tai maganar da cikakkaiyar gaskiyane ya sakasu kallonta su duka, amma sai hajiya Usaina tai tsaki kuma, “Lamcy karki kawo mana wani ruɗani anan, indai akan maganar abinda kikace za’a bakinne munji zamu baki, ke ni harma wani kaso zan ƙara miki a cikin nawa, ai burinmu ya gama cika, dan yau dai ta Alhaji ta ƙare, kudin da muketa wahalar gadi tsahon shekara shidda gasu komai ya dawo hannunmu, nanda sati ɗaya sunayenmu zasu fito cikin manya-manyan masu arziƙin duniya, hhhhhhhhh!!, sai ni Usaina ɗiyar malam garba, mace ta farko mai arziƙin da babu kwatankwacinsa a wannan yanki, Abdul ka kawoma duniyata haske dalilin buɗamin hanyar auren ɗan uwanka, wanda toshewar basira ke sakashi kallon sonsa nake, besan ina cikin waɗanda zasu zamo ƙatshen rayuwarsa bane, hhhhhhhhhh!!!!!!”.
Ta sake kwashe da wata mahaukaciyar dariya Abdul na tayata, hannu yasa ya fisgota ta faɗo jikinsa, a gaban idon Alhaji kokino dake ɗaure suka hau sumbatar juna tare da yamutsa kansu.
Hawaye masu zafi ne suka wanke fuskar Alhaji kokino, ya duƙar da kansa domin daina kallonsu, wuƙa Abdul ya zaro a aljihunsa, babu wanda ya lura ya sokama Lamcy dake ƙokarin jan hannun Hajiya Usaina, so take ta sake fahimtar dasu ko zasu fahimta, idan sunƙi ta gudu itadai ko ranta ta tsira dashi idanma babu dukiyar.
Ƙara ta saki mai ƙarfi tana ƙanƙame Hajiya Usaina.
Da sauri Hajiya Usaina ta saki Abdul da maida kallonta ga Lamcy.
Sosai ta zaro ido ganin wuƙar dake gefen cikin Lamcy ga Abdul riƙe da ita ya ciza bakinsa yana ƙara dannama Lamcy…….
“Abdul mikakeyi haka kuma? Kasheta fa kayi?”…..
Dariya ya kwashe da ita yana jan wuƙar ya fitar daga jikin Lamcy, “Bata da wani amfani a yanzu a gareni, ta gamamin aiki mizaisa na barta? Dolene ta wuce kafin ɗan uwana da ke ku bi bayanta, ni kaɗaine na cancanta da wannan dukiyar hhhhhhhhh!!!!!!!……”
Tsagwaron tsorone ya bayyana a zuciyar Hajiya Usaina, ta zabura baya da sauri tana ƙwalalo idanun mamakin Abdul, kanta yay gadan-gadan, ya ɗaga hannu zai daɓa mata wuƙar aka riƙe masa hannu ta baya.
Juyowa yay yana huci dan duk zatonsa Lamcy ce bata mutuba ta riƙesa, amma a mamakinsa sai yaci karo da fuskar jami’in dake bincike akan ɓatar yayansa, Jawaad Abdul-aziz yusuf.
A wani irin razane ya zaro idanu yana sakin wuƙar, zaiyi magana Jabeer ya ɗora yatsansa kan bakinsa yana faɗin, “Shiiiiii!!”.
Sai kuma ya daki ƙafar Abdul ya zube ƙasa jiki na rawa.
Aliyu yay ƙoƙarin kwance Alhaji Kokino da Jawaad ya ɗaure, Hafiz kuwa nakan su Abdul da binduga, sai Rose dake ƙoƙarin bincikar Lamcy wadda da alama da wuyama takai labari.
A take suka tattaresu, ana ƙoƙarin fita dasu, tuni jiniyar motor ƴan sanda da Ambulance dasu Jawaad suka buƙata tunkan su shigo bacar har sun iso.
Alhaji Kokino da Lamcy asibiti aka wuce dasu, yayinda Abdul da hajiya karima aka nufi ofishin su Jawaad dasu.
STORY CONTINUES BELOW

__________________________________
Da daddare duk muna zaune a falo ana hira, duk da ni a takure nake daga can gefe, ina dai saurarensune kawai, na murmushi nayi na mamaki da takaici na girgiza kaina, dukda suna tsangwamata idan na zauna cikinsu hakan bai hanani son zamanba, dan koba komai ina ƙara ilimin sanin duniya daga garesu, sannan ina rage kaɗaici da damuwa.
Aunty Shahudah da dama ita kaɗaice babu a cikinmu ta sakko daga saman bene cikin wando da riga, sai siririn gyale data yano bisa kai, ganin key ɗin mota a hannunta da bag ya saka mummy faɗin, “ke kuma ina zuwa haka mamana?”.
Tana ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai take fadin, “Mummy jirgin su my friend ya kusa sauka, kin sanshi bayason jira”.
“Okey amma ai baƙya fita ke ɗaya ba adaren nan, Salman ya tashi kuje, tun ɗazunma da driver kika tura da bai ɗakkosa ba?”.
“Mum driver kuma? To da wane yaran zai ɗakkosa?”.
Dariya duk suka sanya, banda ni dama na kasa fahimtar zancen, duk da tun ɗazun dama naji tana faɗin zuwan matafiyin dana kasa yarda a raina namijine duk da yanda take alaƙanta komai nasa da suffofin namiji.
Tashi Salman yay yana tuttura baki irin shi baiso zuwanba, ta jefa masa key ɗin hannunta tana harararsa, amma batace komaiba.
Juyawa tai ta kalleni cikin yamutse fuska tana faɗin, “K karna dawo naga wannan baƙar fuskar taki a falon nan, dan jack ya ganki wlhy zaima iya amai, dan bai saba ganin trash irinki ba”.
Murmushi nayi idona na cika da ƙwalla na miƙe na nufi ɗaki ina maimaita kalmar trash data kirani dashi, sai dai kuma abin mamaki abun baimin zafi sosai ba, dan zuwa yanzu a halayyarta kuma kaɗanne bata zubar na ganiba, gado na haye abina, na faɗa duniyar tunanin da yazamar min abokin rayuwa da ɗebe kewa.
Ban sake sanin hidimar da masu gidan keyiba har washe gari, duk da bayan kusan awa biyu da tafiyar su Aunty Shahudah na fara jiyo ƴar hayaniyarsu, sai kuma gidan ya koma tsitt.
★★★★★★
Da safe ƙin fita nai har lokacin da nakeda tabbacin sun kammala yin breakfast, sai da naji gidan yay shiru sosai sannan na fito, babu kowa a falon hakanne ya bani ƙwarin gwiwar nufar kicin, Amina mai aiki nata ƙoƙarin gyara kicin ɗin, gefe kuma kuku na shirin ɗaura abincin rana, gaisawa mukai duk da suna bani girma kamar kowa na gidan, amma hakan baisa na ɗauki kaina sama da suba, Amina maƙwaftan suke da gidan namu, sai dai su ba masu ƙarfi bane, hakan yasa take shigowa aiki a nan duk wata ana biyanta, tacemin da can ita da mamanta sukeyi, da ciwon ƙafane ya takura mata sai ita tacigaba dayi ita kaɗai.
Itace ta nunamin abincina, dan haka saima na zauna a kujerar kicin ɗin kawai nahau karyawa muna hira da ita, inda shima kuku ke ɗan sakko nasa zancen da turanci, sai hausa ɗai-ɗai wadda sam babu daɗin ji daga harshensa.
Wani irin kuka naji a bayan Windown kicin ɗin, hakan ya sakani kallon Amina ina faɗin, “Minene haka ke kuka?”.
Ƴar dariya tayi tana bani amsa da cewar, “Jojon big Aunty ne”.
Nasan Shahudah suke cema hakan, dan haka nace, “Jojo kuma? Waye mai wannan sunan?”.
Yafitoni tai da hannu alamar nazo na gani, na ajiye dankalin dana ɗauka zansa a baki na miƙe zuwa gareta, kaɗan taja labulen Windown ta yanda zan iya leƙa wajen.
Aunty Shahudah na hango zaune cikin korayen ciyayin da aka gyara wajen da wani ɗan ƙaramin kare mai kama da jikin zaki a saman cinyarta tana shafawa, sai wani tsamurarren bature zaune gefenta daf, Aunty Aamila kwance itama a wajen kanta kamar bisa cinyar baturen suna dariya.
Labulen na saki ina sauke ajiyar zuciya, na dubi Amina sosai, “To Amina wanene jojon a ciki? Dan da alama dai wannan shine baƙon da yazo jiya kenan?”.
Tace, “Karen dake cinyarta shine Jojo, baƙon kuma Jack, a farkon fara aikina gidannan nazo na iske Big aunty da wani karenta jojo, sai dai wataran tsautsayi Boss yazo gidannan ya takashi da mota ya mutu, lokacin har a asibiti ta kwanta jiyyar saboda mutuwar karennan kuwa”.
“Tofa, ALLAH ya ƙyauta to, akan karen? wanene Boss ɗin to? Dan nasan kam ba ƙaramin fin ƙarfinta yayba da har bata ɗauki wani matakiba?”.
Dariya Amina da kuku sukayi, Amina tace, “Aikam kamar kin sani yafi ƙarfin nata, dan har yanzu batayi ko tari hakan a gabansa ba saboda mutuwar karen, ballema ayi tsammanin bin ba’asin yanda abun ya faru, ba kowa bane face mijinta”.
Kaina kawai na jinjina, na koma wajen abincina batare dana ce komaiba, nikam harma naji inason ganin wannan miji na aunty Shahudah, dan kuwa lallai yana ganin shashanci tsantsa daga gareta, inhar shima ba irinta baneba.
Ina cigaba dacin abincina ina sauraren hirar Amina da kuku harna kammala na tashi na fita.7
A falo naci karo da Yaya Qaseem daya shigo ransa a matuƙar ɓace, hannu yasa ya wurgani gefe saboda na shigo masa gaba ba tare dana saniba, kaɗan ya rake fuskata bata bugi tebir din gilas dake wajenba.
Na sauke numfashin ambaton Alhmdllh ina binsa da kallon mamaki harya gama haurawa saman benen yana ƙwalama mummy kira tamkar zai tsaga gidan biyu dan azaba.
Tashi nai tsaye jikina har yanzu rawa yake, na shiga murza hannuna daya bugu da kujera yanamin zogi.
Yaya Qaseem ne ya sake sakkowa yana zage-zage da harshen turanci Mummy na biye dashi tana ƙoƙarin riƙesa da masa magana da hausa ita kuma, amma sam yaƙi saurarenta.
Saiga su Shahudah sun shigo suma daga waje da ɗan gudunsu ita da jack da Aamila.
A take falon ya hautsine da hayaniya, nidai ina daga gefe ina kallonsu, sai dai bana fahimtar komai banda wani suna *Jawaad* danaji Qaseem nata ambata, yayinda Shahudah ke masifa tana nunashi, yako kai mata duka sai da jack ya kare shi aka sameshi.
Abu kamar wasa saiga gidan ya harmutse sosai, Mummy sai fama take dasu amma sunƙi suyi shiru, ganin hakanne ya sakata fashe musu da kuka.
Tsitt falon yayi kuma, sukai kanta banda Qaseem da ya fice abinsa rai ɓace, da sauri jack yabi bayansa, Shahudah da Aamila kuma suka zagaye Mummy, Salman baya gidan dai da alama.
Wannan lamari nasu yayi matuƙar bani mamaki, har yamma kuma ban samu jin abinda zai fahimtar daniba, sai abu ɗaya kacal ne kawai na ɗan gane, da alama dai daga wajen aikine aka fusatar da Qaseem, kuma wanda ya sakashi fusatar yanada alaƙa dasu musamman ma Shahudah da haushin Qaseem yaso ƙarewa a kanta……………✍🏻
1
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃💃🏻👌🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻2Shafi na ashirin da biyu
Kuyi manage da wannan babu editing banajin daɗine😥
11
……………Tun shigowar Qaseem hukumar tasune ya tabbatar akwai abinda ya faru, dama kuma ya samu kirane daga sama akan yazo da gaggawa.
Shigarsa wajen da manyansu suke tare dasu Jawaad ya saka zuciyarsa tsitstsinkewa, musamman tozali da ƴan tawagar Jawaad da yay su Hafeez.
Shi Jawaad ma yana zaune ne kansa a ƙasa saboda ciwon da yake masa, baima san da shigowar Qaseem ɗinba.
Bayan shigowar Qaseem an jira mutane biyu da ake jira suma sun shigo, kafin a fara gudanar da yabo da jinjina akan namijin ƙoƙarin da su Jawaad sukai.
An kuma tabbatar da wanke su Aliyu daga laifin da ake zarginsu dashi wanda yay sanadin zamansu cikin jail.
Take wajen ya ɗauki tafi.
Abinfa zai baka mamaki ko motsi Jay baiyiba a wajen, duk da laifin abokansa da aka wankesu baisashi ya ɗago yama kalli kowa ba sam.
Qaseem ya buƙaci yin magana, dan haka aka bashi damar yi.
Duk da son danne fushinsa da yaketa ƙoƙarin yi hakan ya gagara, sai da muryarsa ta fallasashi, a kausashe yake magana akan yanda aka maida aikin ta bayan fage bayan kuma shi aka damƙawa, ya cigaba da maganganun da suke nuna sukar Jawaad kai tsaye tareda muƙarrabansa, harma yana nuna akwai shiri a cikin lamarin, sai dai idan Jawaad ɗin dama yasan inda Alhaji Kokino yake.
Jay da duk yake sauraren komai yaɗan taɓe bakinsa ba tare daya ɗago ba, ɗakin taron kuma yay tsit an rasa mai bama Qaseem amsar tambayoyinsa, kowa ya zubama Jawaad ido ana buƙatar ƙarin bayani daga garesa, amma abin mamaki tamkarma baisan sunaiba.
Hakanne ya saka Aliyu dake kusa dashi taɓashi kaɗan.
Jawaad ya ɗan ɗago ya kalli Aliyun idanunsa sunyi jajur na gajiya da barci,
“Boss kanafa jin mi yake faɗa”.
Guntun murmushi Jay yayi kawai ya maida kansa yanda yake yana lumshe idanu, sai da Qaseem ya gama ɓaɓatunsa har sir Ahmad ya dakatar dashi sannan ya dawo ya zauna yana huci, ba ƙaramin haushin ƙin kulashi da Jawaad yayba yaji.
Sir Ahmad ne yay bayanin da kowa ya gamsu a wajen bisa shakkun da Qaseem yaso jefa musu akan Jay, daga nan sukai abinda ya tarasu aka sallami kowa.
Dan Jawaad yaƙi cewa kowa komai, koda aka buƙaci jin ta bakinsa Jabeer yaba damar yin bayani, acewarsa shi kansa na ciwo, da yake kowa yasan yanada lalurar ciwon kai da sam idan ya motsa masa bayason takura sai akai masa uziri.
Wannan abunne ya sake fusata Qaseem matuƙa, koda suka fito sai ya tare Jawaad ɗin bisa hanya.
Ko kallonsa Jay bai yiba ya raɓa ta gefensa zai wuce, nanma Qaseem ya sake taresa.
A fusace Jawaad ya fisgo bindigar dake jikin Rose ya nuna Qaseem da ita, dan zuciyarsa a maƙoshi take, shiyyasa sam yaƙi kula Qaseem ɗin tun farko.
Babu wanda yay zaton da gaske Jawaad yake saida ya saki harsashin ciki gadan-gadan akan Qaseem, Aliyu ne ya hankaɗa Qaseem ɗin gefe harbin da Jawaad yayi ya sami ƙofar wani Office dake a wajen.
Nan take wajen ya hargitse da ihu, inda shima Qaseem ya fiddo bindiga wai zai harbi Jawaad, da ƙyar aka rirriƙesa.
Cikin huci Jawaad ya nuna Qaseem ɗin yana faɗin, “Wlhy idan baka fita hanyata ba duk abinda nai maka kaine ka jasa, ka kama kanka Qaseem, karkai wasa da ɗaga maka ƙafan da nakeyi…..?”
Jan Hannun Jawaad da sir Ahmad yayine ya sakashi yin shiru, sai da ya kaisa har Office ɗinsa sannan ya sakesa.
Faɗa ya shiga masa akan waya kaisa aikata wannan gangancin? Yafa tuna Qaseem a samansa yake, baya tsoron abinda zai iya biyo baya?, duk da kowa yasan Qaseem yana shiga rayuwarsa hakan bazai hana a juya abun ta wani ɓangarenba, musamman da akasan Jawaad ɗin yana aiki tuƙuru, wanda hakan yana ɓatama wasu a cikinsu rai da ruguzasu ta hanyoyi da dama sosai.
Ganin Jawaad ɗin baice komaiba shima sir Ahmad ɗin sai yay shiru, dan yasan Jay yanada haƙuri, amma tabbas yanada zuciyar jaraba idan ka kaisa maƙura.
Ruwa ya fiddo a firij ya miƙa masa, babu musu Jawaad ya amsa ya hau sha, sai da yasha fin rabi sannan ya ajiye yana sauke numfashi a gwame.
Ya tsani takura a rayuwarsa, shiyyasa shima bai san takurama kowa, amma Qaseem yaƙi ya riƙe girmansa, ya rasa miya tare masa a wannan duniyar?, tun suna ƙanana Qaseem bayason yaga cigabansa ko farin cikinsa, baisan miyasa hakanba?.
Nannauyan numfashi ya kuma saukewa yana maijin kewar mahaifiyarsa, sosai yake bukatar ɗumi irin na uwa a kusa dashi, sai dai shi tashi ta masa nisan kiwo………
Sir Ahmad ya katse masa tunani ya dafashi a kafaɗa, ɗago jajayen idanunsa yay yana kallonsa, cikin sigar lallashi sir Ahmad ɗin yake ma Jawaad nasiha akan yacigaba da haƙuri da lamarin mutane, haka rayuwa take, kai kana harkokinka baka damu da kowa ba amma wani shi idanunsa na bisa kanka gaba ɗaya, kowa a rayuwa da kagani akwai tasa gaddarar, maƙiya kuma sune gishirin zaman duniya.
Jawaad ya gamsu da jawaban ogan nasa, dan haka yay masa godiya sosai.
A waje kam sosai hayaniya ta ɓarke, su dai sauran waɗanda ke wajen sun zama ƴan kallo, dan kuwa dai faɗan na manyane.
Inda su kuma manyan hankalinsu ya tashi, da ƙyar aka saka Qaseem a mota aka bar wajen dashi, amma sai iƙirarin kashe Jawaad yakeyi.
Wannan shine dalilin shigowarsa gida yana banbamin masifa🤦🏻♀.
+
STORY CONTINUES BELOW

_______________________________
Washe gari da yamma Jack da Aunty Shahudah suka fita yawo, basu dawo gidan nanba sai kusan sha ɗaya na dare, tunda yazo gidan kuma ban yarda mun haɗa hanyaba kamar yanda ƙawarsa ta buƙata, duk da ma dai na lura yau bata da walwala, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci ma bata da lafiya, dan tunda suka dawo daga yawo ita da Jack take ƙudundune a cikin kujera a falo, inaji tanama Amina masifa akan ta kashe mata ac.
Washe gari da safe kuma Abba ya dawo, kowa a gidan yayi farin cikin dawowarsa, dan ranar tare akai zaman cin abinci baki ɗaya har Yaya Qaseem da rabon dana gansa tun randa ya dawo a fusace.
Na zata Abba zaima Aunty Shahudah faɗan ganinta a gida tare da zuwan jack, amma sai naga luf, saima taɓara take zuba masa salo-salo wai ita ciki ya dameta, sannan hannu biyu ya amshi jack ɗin da shikuma yakemin kallon mamakin wannan kuma daga ina?.
Ni dai inda yakema ban kallaba, haka kuma ban saki jiki naci abincinba saboda harar da kowa ke jifana da ita a wajen, idan ka cire dad da lokaci-lokaci yakan kalleni yana maganar miyasa banason cin abinci?.
Amsa ta ɗayace kacal, “Dad inaci”.
Yanda Aunty Aamila keta faman takamin ƙafa ta ƙasan tebirin yasa na miƙe badan na ƙoshiba nace ya isheni, dad ne kawai yay min faɗan hakan, amma kowa baice uffanba.
Nidai nabar wajen ina murmushin yaƙe, ina shiga lungun ɗakinmu kuwa hawaye suka fara rige-rigen zubowa, ban sharesuba kuwa, haka na faɗa saman gado inayinsu, ban sake sanin hidimar da sukeba har washe gari da safe, inda Dad ya buƙaci ganina afalonsa.
Albishir ɗin da Dad yamin akan zanje na zana jarabawa duk sai ya mantar dani komai, bakina ya gaza rufuwa saboda tsantsar murna da farin ciki, yinin ranar da wannan abu na yini, shiyyasa duk abinda akaimin baiko ɓata raina ba.
_________________________
Har Jawaad ya baro office ya dawo gida ransa babu daɗi sam, ya kumazo ya iske Shahudah bata dawo ba, tsaki kawai yaja yay shigewarsa ɗakinsa, wanka kawai yay ya kwanta dukda masifar yunwar dake cinsa, amma gajiyar dake tare dashi har bishi-bishi yake ganin gari.
Yana kwanciya kuwa barci mai ɗan karen nauyi yay awon gaba dashi, bai sake sanin wane hali ake cikiba sai gabda sallar magriba.
A rikice ya tashi saboda salloli da suka wucesa, yay azamar yin ramuwarsu yana jero istigifari ga UBANGIJI.
Bayan ya idar yay shirinsa tsaf ya fice zuwa gidan kakansa daya haifi Mamansa, mijin kakarsa mama maryam kenan.
Ya iskesa yana da baƙi, dan haka bayan ya gaishe da baƙin yay wucewarsa cikin falon tsohon, kuloli yaci karo dasu, dan haka ya zauna yana buɗewa, yasan dai bai wuce tuwo ba, kuma daga gidan Ummansa ne ake kawoma baba, dan tunda mama maryam ta rasu bai sake aureba, shi kaɗai yake zaune a bunsa a gidan saisu idan sunzo.
Tuwonsa ya zuba yaci ya ƙoshi yanamai jin nishaɗi, yaushe rabonsa da abinci mai nagarta irin haka? Yanama zaton tun masar da umman ta aika masace.
“Kai ja’iri, tuwon nawa kake cinyewa?”. Baba dake shigowa ya faɗa yana harar Jawaad da wasa.
Dariya Jawaad ɗin yayi idonsa akan kakansa da tsufa ya kama sosai, “Haba mai ran ƙarfe kaimafa tuwon na gidan Umma nane, tunda kaƙi fita a gwaurantaka kayo mana amarya”.
Dariya sosai tsohon yayi, yasa sandarsa ya daki kafaɗar Jawaad da saida ya sosa wajen saboda zafi.
“Dan gidanku, ni da kai munada banbanci ne? Kaima da kake da matar baka da banbanci da tuzurun da baima taɓa aureba”.
Murmushi Jawaad yay yana ɗan taɓe bakinsa, saboda tsoho dai ya taɓo masa inda ke masa ƙaiƙayi, aiko bai bada amsaba ya miƙe yaje ya wanko hannunsa sannan ya dawo ya zauna.
Baba dake binsa da kallo yace, “Daga ina kake a darennan?”.
Jawaad ya zauna kusa da baba yana jingina kansa da kafaɗarsa yace, “Daga gida”.
Shafa kansa baba yayi yana maijin tausayinsa, yace, “Yau an tuna da tsoho kenan?”.
“Nikam dama kana raina, wani aikine kawai ya dabaibayeni sai yau na sauke nauyinsa”.
Murmushi baba yayi, “Naga komai ai a tv Jawaad, shiyyasa a kullum bana haufi a gareka, sai yanzu ne nake sake gaskta maganar mahaifinka da tun bakasan kanka ba yake dangantaka da aikin ƴan sanda, ashe shiya san miya hango mana”
Murmushi kawai Jawaad yay yana haɗiye abu mai ɗaci a maƙoshinsa, daga nan ya cigaba da sauraren yabo da kakansa keta jerawa akan ƙyawawan halayyar mahaifinsa, a haka barci ya sake sacesa.
Baba yakai dubansa ga fuskar Jawaad, ganin yay barci sai yay murmushi yana kai hannunsa ya shafa kumatun Jawaad ɗin.
Ido Jawaad ya buɗe a hankali ya kallesa, baba yace, “Tashi kaje ɗaki ka kwanta”.
Bai musaba ya miƙe ya shige bedroom ɗin baba, lafiyayyen ɗaki dayasha gyara tamkar bana tsohon da rayuwa taima nisa ba, lallausan gadon baba Jawaad ya haye, yaja bargo ya rufe jikinsa yana lumshe idanunsa, kafin kace mi nan nauyan barcin ya sake ɗaukesa kamar wasa.
STORY CONTINUES BELOW

Yau dai kam Jawaad anan ya kwana tare da kakansa, sai da yay sallar asuba ya karya da breakfast ɗin da Faisal ya kawo daga gidan Umma sannan yayma baba sallama ya tafi gida akan yana nan dawowa anjima zasuyi wata magana da baba.
Baba yace “to ALLAH ya kaimu saika dawo, ALLAH ya tsareka akoda yaushe”.
“Amin” Jawaad ya amsa yana fita.
_________________________
BAYAN SATI BIYU
_________________________
Har wannan lokacin Aunty Shahudah da dai na gida, bata komaba kuma mijinta bai zoba, sannan jack na nan bai tafiba sai kace gidan tsohonsa.
Nikam tun ranar da mukaci abinci tare ban sake zama inda yakeba, saboda har ɗaki ta biyoni ta ƙaremin zagi da cin zarafi akan ko Dad ne ya kuma buƙatar na zauna dasu cib abinci nasan yanda zan zame, idan ba hakaba wlhy saita ci mutuncina.
Haƙuri kawai na bata nikam, dan yanzu ni bana ɗaukarta sahun masu isashen tunani.
Tamin wannan abun ma da kwana uku Dad yace na shirya zuwa makarantar da zanje na zana jarabawata, ranar dai kamar anmin gafara naji, har kukan daɗi nayi kuwa.
Kwana biyu na cika na tattara komai na sayayyar da Dad ya yo mani domin tafiya, dan makarantar boarding school ce, sai dai yanda naji su Aunty Aamila na faɗin wai ban dace da makarantar ba nasan babbar makarantace.
Ranar dazan wuce na lura kowama murna yake da tafiyata, dan Salman harda faɗin, “ALLAH raka taki gona, koba komai sa huta da kallon baƙar fuskata abin amai”.
Dariya mummy da aunty Aamila suka sanya, dan mu kaɗaine a wajen, Shahudah da jack suna can baya suna hira.
Har bakin mota Amina da kuku sukai min rakkiya, sai da sukaga na shiga mota mun fice a gidan sannan.
Na share ƙwallar data zubomin ina murmushin kewa da farin ciki.
3
😅👏🏼ALLAH ya bada nasa takwara, sai dai fa ni ƴar team Shahudah ce😆😜, bara na fece kafin naci mazga⛹♀.
4
_________________________
Tunda Jack ya bata shawarar zubar da cikinnan burinta ya dawo sabi fil, dan ya tabbatar mata Jawaad burga kawai yake mata babu wani sakinta da zaiyi tunda yana masifar sonta.
Ta shafa cikinta da ayanzu haka yake mata ciwo, tabbas tana wahala akan wannan cikin da bata shiryama zuwansa ba, gashi harya fara sakata ƙiba, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, duka shekarunta nawa da za’ace ta ɗauki ciki? Kamar yanda Jack ya faɗa, ita kanta tasan dan tayi gaggawar yin aurene kawai, bakomai ya jawo hakanba kuma sai ƙaunar Jawaad data tunzurata, da shawarar Mummynta, anya kuwa bazata zubarba kawai ta huta? Iyakaci dai ayi badakalar da za’ai na ɗan lokaci ta wuce, daga baya komai zai lafa a wuce wajen.
Zama tai a bakin gado ta dafe kanta tare da cije bakinta saboda murɗawar da cikinta ke mata, kusan min tuna uku tana a haka kafin ta samu ya lafa mata, sai wani zazzaɓi da takeji wanda ya zame mata jiki a yanzu kullum yamma saita yisa.
Wayarta ta ɗauka ta kira Aamila, babu jimawa sai gata ta shigo ɗakin.
“Sisi lafiya kike kirana?”.
Miƙewa Shahudah tayi idonta akan Aamila, “Aamila na yarda da shawararku zan zubar da cikinnan kawai”.
Zaro ido Aamila tayi tana ɗan ja baya, “Wai da gaske dan ALLAH?”.
“Na taɓa miki maganar hakan?”.
“A’a, ai abunne da mamaki, keda kike mugun tsoron Brother Jawaad karya rabu dake, amma yanzu lokaci ɗaya kizo da batun amincewa”.
Tsaki Shahudah taɗanyi, “Karki damu, ni nasan barazanace kawai, son da bb kemin bazai taɓa yarda ya rabu daniba wlhy, kawai yanamin burgane dan karna zubar, idan kuma yay haƙuri nan gaba ai zan haihun, amma gaskiya ba yanzu ba”.
“Kinyi ƙyan kai gaskiya, yanzu ke mikike buƙata?”.
“Shawarar da nake buƙata kenan daga gareki, ɗazun jack yace yasan maganin da zaimin aiki ba tare da nasha wahala ba, inaga kije kufita tare kozaku samu a wani pharmacy ɗin, sai dai dan ALLAH karki bar Mummy ta sani”.
“Karki damu, insha ALLAHU babu wanda zaiji”.
Koda Aamila ta fice sai Shahudah ta koma ta zauna, wayarta ta ɗauka ta dannama Jawaad kira, sai dai harta katse bai ɗagaba.
Text massege ta tura masa kamar yanda suka shirya da jack, kodaga baya cikin ya zube wai bazai zargeta akan itace ta zubarba.
Mummy batasan mi suke shiryawa ba, a gabanta Aamila da jack suka fita a gidan.
Sun bazama neman maganai cikin manyan pharmacy’s ɗin garin, amma samunsa ya gagara, saboda ba kowane ke saidawa ba, dabara ce ta faɗoma Aamila a rai ta kira number Munira cikin yaran gidan su Jawaad, dan ta taɓa bata labarin wata ƙawarta da ta raka zubar da ciki.
Sun sanar mata abinda suke buƙata sai dai basu faɗa mata gaskiyar wanda zaiyi amfani da shiba, itace ta kira likitan daya bama ƙawarta wancan maganin ta haɗasu dasu Aamila, shi kuma yay musu kwatancen inda zasu sameshi.
A asibitinsa da ya kasance privet suka samesa, babu ko ɗar suka biya kuɗin daya yanka musu ya basu allurar da za’ai amfani da ita, a cewarsa itace tafi aiki shap-shap kuma bata cutarwa.
Sai da jack ya duba sukkan bayanan allurar ya kuma tabbatar da maganar Doctor sannan ya suka amsa suka nufi gida.
Jack bashi da shamaki da shiga ɗakin Shahudah a duk sanda yaso, dan haka koda suka dawo a gaban idon Mummy ya shiga, Aamila kuma ta zauna a falon dansu ɓadda hankalin Mummy wai.
Ƙudundune ya iske Shahudah zazzaɓi ya rufeta, ya yaye bargon data rufa yana taɓa gefen wuyanta, buɗe idanunta tayi, ganin jack ne yasata miƙewa da ƙyar tana kallonsa, “Kun samo?” tambayar data fara jefa masa kenan cikin harshen turanci.
Kansa ya ɗaga mata, ya ciro allurar daga aljihunsa yana nuna mata.
Amsa tayi ta jujjuya allurar a hannunta, sai kuma ta kallesa da tambayarsa wai miyasa basu sayo maganinba? Yafasan batason allura.
Bayanin duk yanda sukai ya bata, ya kuma tabbatar mata wannan allurar tafi maganin inganci, hakan ya saka ta aminta da batunsa.
Hannu ta bashi yay mata allurar tana matse baki, can ƙasan zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai biyo baya daga Jawaad………….✍🏻
3
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Shafi na ashirin da uku
BARKAN KU DA JUMA’A
4
……….Tunda aka buɗe mana katafaren gate ɗin makarantar muka shigo nake baje idanu da hanci ina kallon wannan tsararren gini da tamkar ba makaranta ba.
Yanzu nan ni Bilkisu ɗiyar malam Ado makahoce cikin wannan makarantar? Abu kamar mafarki kamar kuma almara. Niko tayaya zan manta da Dad a rayuwata.
Ƙwallar data cikamin ido na share ina fitowa daga cikin motar, ɗalibai duk suna cikin aji, hakan yasa security kawai kake iya gani na shawagi sai malamai.
Mun samu tarba ta musamman ga wani malamin da nakeda tabbacin yazo garemune bisa umarnin Dad, na gaishesa cikin girmamawar da naga nuna jin daɗinsa saman fusakarsa.
Bisa jagorancinsa muka isa har Office ɗin shugabar makarantar, bayan an bani wani form na cike aka haɗani da malamai uku sukaimini interview, duk da karatun bai kasance ɗayaba sun yabama ƙoƙarina.
Na sauke nannauyan numfashi da naji cewar komai yayi, duk da dai ba ɗari bisa ɗari na ƙoƙartaba amma sun amsheni, to dayake kuma abun ya haɗa da harkar kuɗi sai babu wata matsala aka kammala komai tsaf.
Malamin nan dai yana tare dani muka fito, sallama mukai da driver ya tafi domin shi ya gama aikinsa, sai kuma naji hawaye sun cikamin ido, a gaban idona ya wuce.
Malamin ya kalleni yana murmushi, “Ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai-dai kinji, alkairin Alhaji a gareni bazaisa na zuba ido kiƙi nasara ba, sai dai idan ALLAH ya ƙaddaro hakan, akwai yarinyata anan makarantar insha ALLAHU zan haɗaki da ita, zata taimaka miki sosai kafin ku fara zana jarabawar, tunda akwai tazarar kusan 5weeks yanzu haka insha ALLAHU”.
Cikin girmamawa nace, “Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi, ya kuma bada ladan zuminci”.
“Amin” ya faɗa yana maijin daɗin addu’ar yarinyar da yaba tarbiyyarta, dan kuwa yakuma tabbatarwa ba’a gidan Alhaji ta tashiba, saboda sanin da yayma yaransa da sam tarbiyya bata gama wadatar da suba.
Security ɗin dake kusa ya kira, shine ya kwasar min kayana muka nufi inda yace min Hostel ɗinmu kenan, dan lokacin an tashi Ɗalibai duk sun shige ciki.
Mun iske hostel ɗin shiru babu wata hayaniya a cikinsa, sannan ɗalibanma ɗai-ɗai muke gani suna shawagi, kowa kuma harkar gabansa yake babu ruwan wani da wani, a ƙofar wani ɗaki mukaja birki, security ɗin ya ƙwankwasa ƙofar, babu bata lokaci aka buɗe.
Budurwa da bazata gaza sa’a taba ce ta fito, sai dai shigarta zai tabbatar maka da wahala ta kasance musulma.
Ganin malamin dake tare danine yasakata juyawa da gudu ciki tana dariya, ko minti biyu bata rufaba sai gata sun fito itada wata mai tsananin kama da malamin.
“Daddy baƙuwar harta iso?” ta faɗa cikin zumuɗi tana ɗan tsalle a gabansa.
Murmushi yayi mata, ya jinjina kansa tare da faɗin “Eh Ummie na ta iso, gata nan ma sunanta Bilkisu Adam”.
Juyowa tai gareni cikin ɗoki tace, “Barka da zuwa Bily cikin makarantarmu”.
Haɗiye hawayen farin cikin da suka cikamin ido nayi ina amsa mata, banyi zaton zanje waje a karbeni lokaci gudaba kamar yanda Ummie tai mini yau, gata dai da gani itama ƴar gatace amma sam babu fuskar wulaƙanci a tare da ita.
Ta kama hannuna cikin nata tana sauraren bayanin da daddynta ke mata a kaina cikin nuna zaƙuwa da ɗoki, ya maida dubansa gareni yana faɗin, “Bilkisu wannan itace ɗiyata kamar yanda na sanar miki, karkiji komai ki saki jikinki da ita, insha ALLAHU zakiji daɗin zama da ita kamar yanda nima nake ƙyautata mata zato a kanki, komai na tsarin makarantar zata fahimtar dake, karkuma ki cutama kanki, duk abinda ya shige miki duhu ki tambayeta kinji”.
Kaina na ɗaga masa ina risinawar girmamawa a garesa, nace, “Insha ALLAHU Daddy, ngd sosai da karamcinka a gareni”.
“Karki damu Bilkisu, Alhaji Aliyu ya wuce hakan ma a gareni, ALLAH ya bada nasara ni bara na wuce”.
Sallama yay mana Ummie nata masa shagwaɓa ya wuce ya barmu.
Itako ta rungumeni tana sake min barka da zuwa, ta shiga ƙwalama wasu kira da nake ƙyautata zaton ƙawayentane, dan kuwa daga cikin ɗakin suka fito harda wadda ta leƙo ɗazun, su uku ne, kuma duk bazasu wuce sa’anni naba.
Biyu a ciki sun amsheni hannu biyu, ɗaya kam dai sai yamutse fuska takeyi, ban damuba dan na saba ganin irinta tun shaiɗan na yawo da ɗan kanfai cikin duniya.
Sune suka kwasar min kaya har cikin ɗakin dake da gado biyar kacal a cikinsa, sannan komai tsaf tamkar ba makaranta ba.
Zaunar dani Ummie tayi a gado na ƙarshen ɗakin tana faɗin, “Wannan shine gadonki, akwai mai shi da, amma ALLAH ya mata rasuwa hutun da mukaje ɗinnan, yaya tace, tanada ciwon sikila ne.
Nace, “ALLAH sarki, ALLAH ya gafarta mata, kukuma ya baku haƙurin rashinta”.
“Amin” Ummi ta faɗa tana sharar hawaye.
Tace, “Sunana Sumayya Sadik, amma anfi sanina da Ummie saboda sunan Momy na aka saka min”.
Murmushi nayi mata, nace, “Nice name, nima zance Ummie ɗin tunda sunan Momynmu ne”.
Ƴar dariya tayi tajin daɗi, ta nuna sauran su ukun, “Waɗanan ƙawayenmu ne, mu biyarne a guruf ɗinmu kafin rasuwar ƴar uwata, mu ƙawayen junane, ajinmu ɗaya, abu ɗaya muke karanta, kuma burinmu ɗaya. Wannan sunanta Nazifa Sulaiman, wannan kuma Rebecca Emanuel, sai Zuhrah Abbas”.
“Masha ALLAH, sunayenku masu daɗi dukan ku”.
Duk Dariya sukai am ma banda Nazifa da tun farko ta Nuna bata ra’ayina, yanzunma dai tana kwance a gadonta sai latse-latsen wayama take.
Nima na faɗa musu sunana Bilkisu Adam.
Rebecca tai saurin faɗin, “Bilkisu muna fata zaki cike mana gurbin guruf ɗinmu da muka rasa a yanzun”.
Murmushi nai bance komaiba, dan bazance zanyi saurin aminta da suba tunda banga halayyarsu ba……..
Zuhrah ta katse tunanina da faɗin, “Please Bily karkice a’a, muna buƙatarki a cikinmu dan mudai kin mana”.
Nanma murmushi nayi dai, a raina ina mamakin ni da kullum su aunty Shahudah ke kushe munina da ƙyamata ce kuma har suke iƙirarin na musu su kuma?.
Magiya suka shiga min da roƙon karnace a’a, dan haka kawai sainace musu su bari zanyi tunani to.
Murna sukaitayi wadda ni taita bani mamaki, sai dai ina jiyo tsakin da Nazifa tayi kaɗan.
Ban damuba, dan amsar da ƴan uwanta kawai sukaimin ta wadatar dani, da taimakonsu na kintsa kayana tsaf, daga nan muka zauna sunamin lissafin abinda makarantar ta ƙunsa.
Zakuyi mamaki idan nace muku harna kwanta barcin dare ban tuno ko ɗaya daga cikin su aunty Aamila ba bayan Dad kawai da tunda muka iso nake jerama addu’a a zuciyata.
3
STORY CONTINUES BELOW

_________________________
Kamar yanda dokar allurar take sai bayan minti arba’in zata fara aiki, dan haka Jack ya fita yabar Shahudah a ɗakin ita kaɗai, kwanciya tai luf a gadon, sai kuma lokacinne wani mashahurin tsoro da fargaba suke shigarta, babu abinda ke mata kaikawo cikin rai sai Jawaad.
Tabbas ita kanta tasan ta taro match na haƙiƙa a filin da bata da ƙarfin buga ƙwallon, fatanta dai ALLAH yasa tsarin da sukai ya tafi dai-dai, shine kawai zai zama mafita a gareta daga buyagin Jawaad mai zuciyar masifa idan aka ƙuresa.
Da wannan tunanin wani barci mai daɗi ya kwasheta.
★★★★★★
Haka kawai gaban Jawaad yaketa faɗuwa, kuma sai Shahudah kezo masa cikin rai baisan dalilin hakanba, zaune suke a Office ɗinsa shi dasu Aliyu suna tsara yanda zasu fuskanci case ɗin da aka basu dangane da ƴan fashin nan a safiyar yau.
Tsayawa yay daga rubutun da yake a blackboard ya matse maker ɗin hannunsa yana dafe ƙirjinsa.
Zuba masa idanu su Hafeez sukai, Jabeer yace, “Boss lafiya kuwa?”.
Numfashi ya sauke a hankali yana musu murmushin yaƙe, yaɗan girgiza kansa sai kuma ya cigaba da abinda yakeyi.
Badan sun yardaba suka barshi, shikuma zuciyarsa na cigaba da tsitstsinkewa.
Lallai yanaji a ransa wani abu zai faru dashi kuwa, to amma minene?
Wannan amsarce baida ita, dan haka ya share abun yana cigaba da karanto addu’a cikin ransa da maida hankali gasu Aliyun…….
★★★★★★
Wani azababben ciwon marane ya farkar da Shahudah daga daddaɗan barcin daya ɗauketa, ba tare data shiryaba ta fasa ƙarar data jawo hankalin su Mummy dake falo, a matuƙar rikice suka shigo ɗakin har suna ƴar rige-rige kuwa.
Dukansu kanta sukai suna tambayar lafiya kuwa?
Cikin kuka take nuna musu cikinta, a razane Mummy tabi santaleliyar farar ƙafar Shahudah da jini kebi da kallo, har taune harshe take wajen ambaton “Jiniii!!?”.
Cikin ruɗewa Aamila itama ta maimaita “Jini kuma Mummy?”.
Shi dai jack baice komaiba, saboda da hausa su Mummy sukai magana baiji mi sukace ba, sai ƙoƙarin ɗaura kan Shahudah ma yake bisa cinyarsa yana jero mata sorry.
Gaba ɗaya Mummy ta rikice, jikinta sai rawa yake tana jerama Shahudah tambaya akan miya sameta? Miya kawo zubar wannan jinin kuma?.
Bata samu amsa ko guda ba, dan haka ta fice kamar zararriya, Dad ta kira a waya tana sanar masa yazo gida babu lafiya.
Dama yana hanya, dan haka yace mata ga shinan zuwa a rikice.
Ba Mummy ba, hatta su Aamila da sukasan tushen komai sun rikice, dan jini bana wasaba ya ɓallema Shahudah, ta jiƙe inda take kwance sharkaf cikin mintunan da basu wuce goma ba, jikinta kam harya fara saki saboda mahaukacin jinin da take ɓararwa.
A wannan halin Salman da Dad sukazo suka samesu, suma rikicewar sukai, wasu suce a kira Doctor wasu suce a tafi asibiti, daga ƙarshe dai sukabi shawarar Salman da yace akira Doctor kawai, dan kafin su isa asibiti Shahudah zata iya rasa rantama gaba ɗaya.
Kowa ya gamsu da hakan, dan haka aka dannama family Doctor ɗinsu kiran gaggawa.
Doctor ya iso akan lokaci, dan haka ya kora kowa a ɗakin ya shiga ƙoƙarin ganin ya shawo kan matsalar sai dai hakan ya faskara cikin sauƙi, dan kuwa tuni Shahudah da dai ta sanƙame masa alamar suma.
Dole Doctor ya nema taimakon wani abokin aikinsa, babu ɓata lokaci shima ya iso tare da ƙaro musu ƙarin kayan aiki.
Su Dad duk sun rasa ina zasu saka kansu, Mummy kam kuka take rurus wanda ya kasance da biyu, damuwar halin da ɗiyarta ta tsinci kanta da ɓoyayyen burinsu akan cikin da suka ƙwallafa rai.
Salman zai kira Jawaad Dad ya hanashi, acewarsa kar a tada masa da hankaki su jira suga abinda zai biyo baya tukinna.
Dole Salman ya haƙura ya ajiye wayar suka cigaba da zagayen falo, inda lokaci-lokaci Dad kan jeho musu tambaya akan miya kawo sanadin matsalar?.
Amsa ɗaya Mummy ke badawa “Ita bata saniba, wai Shahudah tana ɗakine tun ɗazun tana barci”.
Sam Dad bai gamsu da wannan maganarba, amma sai baija zancenba saboda a yanzu damuwarsu a ceto ran Shahudah tukunna.
STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★
Koda su Rose suka fita suka bar Jawaad shi kaɗai a office ɗin sai zuciyarsa ta kuma ƙuntata da zungurinsa da tunanin Shahudah, abin ya ɗaure masa kai sosai, dan kuwa a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya saboda takaicinta da yakeji ko kawota a ransa bayayi ma sam.
Yanzunma dai ƙoƙarin sake ingijeta yay a zuciyarsa ya shiga wani aikin, yanayi yana jan tsaki a duk sanda ta sake faɗo masa cikin rai.
A haka dai har ya samu nasarar janyeta cikin rai baki ɗaya ya cigaba da harkokinsa kawai.
★★★★★★★
Likitocin nan sunsha wahala kafin su sami nasarar shawo kan jinin dake kwarara a jikin Shahudah, daga nan suka koma ƙoƙarin ganin numfashinta ya dawo, bayan ɗaukar kusan awa biyar a kanta suka samu komai ya dai-daita, sai dai sun zangaɗa mata allurar barci tare da ƙarin ruwa.
Suka fito kowa na yarce gumi, tare da sanarma su Dad jini da Shahudah take buƙata saboda nata data kwararar.
A nannefa aka shiga kallon kallo, dan kuwa kaf gidan jinin kowa baima Shahudah sai na Jawaad, ta taɓa samun wata matsala lokacin tana secondary, har takai ana bukatar ƙara mata jini, a time ɗin an gwada na kowa a gidan bai mataba sai Jawaad, lokacin shikuma sunje can tare da kawu Nasiru ne.
Dad yace, “To amma Doctor kafin muje ga wannan yaya maganar cikin jikinta ne?”.
“Alhaji ai muma ajiye batun ciki gefe, yanzu dai jinin muke buƙata da gaggawa domin tana matuƙar bukatarsa gaskiya, daga baya mayi maganar cikin”.
Ajiyar zuciya Dad yayi, ya ciro wayarsa a aljihu yay kiran Jawaad, kusan kira uku bai amsaba, hakanne ya saka Dad tunanin lallai Jawaad yana kan aiki, dan baya taɓa masa kira biyu a ce bai ɗaukaba inhar yana kusa.
Yana cikin yin zancen zucine sai ga kiran Jay ɗin ya shigo, jikin Dad har rawa yake ya ɗaga.
Haƙuri Jawaad ya bashi akan yay masa afuwa suna yin sallar la’asar ne.
Ajiyar zuciya Dad ya sauke, danshi ruɗewar da suka tsinci kansu a ciki bata bari sunji kiran sallarba ma.
“Babu komai My Son, wlhy wata matsalace ta taso shine nace ALLAH yasa bakan aiki kakeba zan katseka”.
Gaban Jawaad ya faɗi, dan muryar Dad kawai ta mugun tsorashi, yay saurin faɗin, “Babu damuwa Dad, kana buƙatar ganinane?”.
“Sosaima kuwa my son”.
“Insha ALLAHU ka bani nanda mintuna talatin zan iso”.
“ALLAH ya kawoka lafiya”.
Dad ya faɗa yana sauke wayar a kunnensa.
Jawaad ya rasa mizaiyi hasashe a wannan wayar da sukai da Dad, jacket ɗinsa sky blue daya ɗoro saman baƙaƙen kayan jikinsa ya ɗauka jikin hanga ya fice cikin matuƙar hanzarinsa.
Gimba na hangosa ya taso da hanzari yazo ya buɗe masa mota ya shiga, ba tare da ya tambayi ina suka dosaba ya tada motar suka fito.
Saida suka hau kan titi Gimba yace, “Boss ina zamuje”.
“Zangina road” kawai ya iya furata masa yaja bakinsa ya tsuƙe.
Gimba daya fahimci ina suka dosa ya ɗauki hanyar da zata sadasu da gidan su Shahudah.
Tunda aka buɗe gate ɗin gidan gaban Aamila da tasan dokar ya shiga faɗuwa, jitake kamar Jawaad zai gane komai da ya faru a kan fuskarta.
Jawaad ya shigo cikin bajintarsa da jin shiɗinfa ya isa, fuskarsa sam babu walwa.
Yanda yaga duk sun nutsu waje guda sun zuba tagumine ya sakashi tsaresu da mayun idanunsa, Ya sauke akan Jack dake zaune kusa da Salman, aransa ya furta “Jack again?”.
Janyewa yay ya maida ga Dad daya miƙe tsaye yana faɗin, “Yauwa My son ka iso?”.
Kai kawai Jawaad ya iya jinjina masa yana haɗiye wani yawu mai kauri saboda ganin Jack.
Mummy ma ta miƙe ta nufoshi kamar yanda Dad yayi.
Kusan a tare suke ƙoƙarin masa bayani, dan haka ya zuba musu idanu ko ƙyaftawa bayayi.
Tunda suka ambaci jini da Shahudah ta zubar yaji tamkar an buga masa guduma a kansa, ya wani lumshe idanunsa da suka fara canja launi yana fidda numfashi da sauri-sauri………
Maganar Dad dake cewa, “My Son yanzu haka sunce tana buƙatar jini da gaggawa, inba hakaba zamu iya rasata” ta katse tunaninsa.
Buɗe idanunsa yayi yana buso numfashinsa, ba tare daya cema su Dad ɗin komaiba ya juya ya kalli likitocin dake tsaye tsuru-tsuru suna kallonsa.
Takawa ya farayi a hankali cikin nuna halin ko in kula zuwa garesu, ya zauna cikin kujerar dake wajen yana harɗe ƙafafu tare da miƙa musu hannunsa kawai, saboda t-sheat ce jikinsa baƙa wadda ta fidda dukkan ainahin surarsa, sai jacket dake samanta itama tsawon hannun iyakarsa gwiwar hannunsa.
Yanda Doctor yaga Jawaad ɗin duk sai ya dabarbarce, a harzuƙe Jawaad ya kallesa, cikin daka tsawa yace, “Jinin zaka ɗiba kokuwa kallona zaka tsayayi malam?!”.
“A’a yallaɓai, ALLAH ya huci zuciyarka” Doctor ya faɗa jiki na ɓari.
Su dai su Dad duk sun zuba musu ido, tsawar da yay ko ai har cikin hanjin cikin Aamila da Salman ta shiga, shi kansa Jack baisan Jawaad bane zaizo gidan da tuni yabar falon ma.
Doctor ya gama shirin ɗibar jini a jikin Jawaad, dan haka a ɗan shakku yace, “Yallaɓai ko zamu samu ɗaki mu shiga ka kwanta, saboda dokace na ɗibar maka jini a haka”.
Wani mugun kallo Jawaad ya watsama Doctor ɗin, ya ja siririn tsaki da faɗin, “Kai dokar ta dama, kana ɓatamin lokaci bayan inada abunyi kuma”.
“Sorry yallaɓai”.
Uffan Jawaad baice dashiba, sannan ko gezau baiyiba dukda allurar da aka surkuɗa masa cikin jijiyar hannu, wayama ya ɗauka yana latse-latse abunsa tamkar baisan mi akeyiba.
Yana a haka har aka kammala ɗibar jinin, Doctor yace, “Yallaɓai kayi haƙuri karka tashi, dan jiri zai iya kwasarka”.
Banza Jawaad yay masa bai tankaba, duk da idanunsa na masa yam-yam sai ya dake bai nunaba.
Dad da yasan kaɗan daga taurin kan Jawaad yace zai tashin yay saurin faɗin, “My son karka tashi kaji, kaɗan dakata ɗin kamar yanda yace”.
Guntun murmushi ya ɗago yayma Dad ɗin amma baice komaiba, sai kansa daya maida jikin kujerar ya kwantar kawai ya lumshe idanunsa.
Mummy tazo kusa dashi ta zauna tana miƙa masa abu a kofi.
“Karɓa kasha wannan”.
Idanunsa ya buɗe yana kallonta, ta kamo hannunsa ta saka masa kofin, hakanne ya sakashi ɗago kansa daya kwantar yana kallon abinda ke ciki.
Kofin ya matse cikin hannunsa yana ƙankance idanu, a bazata yace, “Mummy miya kawo sanadin hakan?”.
Dukda itama Mummy batasan sanadiba sai da gabanta ya faɗi, cikin ɗan in ina tace, “Yaro na santsin ruwane ya kwasheta ta faɗi, kasan Shahudah batajin magana akan saka shegun takalman nan masu tsini”.
Karan farko daya saki wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa lotsawa, yakai kofin da Mummy ta basa kan bakinsa ya shanye abinda ke ciki gaba ɗaya ba tare da ya bama Mummy amsar maganarta ba.
Koda ya miƙa mata kofin sai ya maida kansa ya kwantar jikin kujerar yay shiru tamkar mai barci.
Gaba ɗayansu ido suka zuba masa, gaba ɗaya yanayin da Jawaad yake ya bama Dad mamaki, amma sai bai kawo komai a ransa ba ya danganta hakan da yanayin aikine maybe…………….✍🏻
4
*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_3
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻Shafi na ashirin da huɗu
…………..Tabbas ran Jawaad a ɓace yake, amma baka isa fahimtar hakan a kan fuskarsa ba, kusan mintuna talatin ya ɗauka zaune kafin ya miƙe da shirin tafiya, a cewarsa zaije ya dawo.
Da kallo duk suka bishi, idon Aamila tamkar zai faɗo ƙasa kuwa, gani take tamkar abinda suka aikata zaije ya binciko.
Salman ya sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Wai miya kawo wannan matsalarne?”.
Jack da Aamilah suka kalli juna kawai, kowanne na haɗiyar yawu da sauri, dan basusan amsar da zasu bama Salman ɗinba kuwa.
Dad kam sama ya nufa yace Mummy tazo yana son ganinta.
Koda suka ƙarasa ɗakinsa sai ya turke Mummy da tambayoyi.
“Aysha mi kuke ɓoyewane?”.
“Kamarya Dadynsu?”.
“Ya ina tambayarki kina tambayata? Yanayin yaron nan kawai ya tabbatarmin akwai wani abu dani ban sanshiba, sannan namiki tambayar miya kawo sanadin zubar jinin, kincemin kema baki saniba, tana ɗaki tana barci, amma gashi shi kin sanar masa faduwa tai da takalmi, minene gaskiyar zancen?”.
“Wlhy Dadynsu nima sai da na faɗa ne na fahimci nayi kuskure, amma kamar yanda na sanar maka bansan minene sanadinba, dan tana ɗaki kwance ne”.
Kai Dad ya dafe yana bubbugawa, itama Mummy zama tai ta sake zabga tagumi tana zancen zuci, babban fatanta ace kawai cikin nan bai zubeba.
Sai dai ita kanta zuciyarta na rawa akan kar dai Shahudah bataji ƙwaɓar da sukai mataba sai da ta aikata ƙudirinta kamar yanda take buri tun farko akan cikin?.
‘Innalillahi, kai amma da yarinyarnan ta cucesu wlhy kuwa’.+
Likitocin nan sai da suka samu dai-daituwar komai sannan suka fito, har lokacin Dad da Mummy basu sakkoba.
Aamilah ta matsa kusa da Doctor ɗinsu, catai yazo zasuyi magana dan ALLAH, tashi yay sukai waje, babu wanda yasan mita faɗa masa, kusan dai mintuna goma sai gasu sun dawo falon.
Itace ta haura sama ta kira su Mummy, Doctor yay musu bayani cewar cikin jikin Shahudah da dai ya zube.
Tambayar farko da suka haɗa baki wajen jefo masa shine, “Minene sanadi?”.
Jimm kaɗan yay kafin yaɗan gyara zamansa, ya ce, “Eto Alhaji matsalar dai kamar daga mahaifarta ne, dan bata da ƙwarin riƙe abu mai nauyi, yanzu kuma cikinta ya shiga wata na uku, shiyyasa ya fara nauyi kaga”.
Kai Dad ya jinjina daga shi har Mummy sun gamsu da hakan, sai yanzu yakejin zargin da yake ya bar ransa, ya gamsu da bayanin matar tasa, amma kuma tayi gangancin cema Jawaad ɗin takalmine ya kada Shahudah.
Itako Mummy dai can ƙasan zuciyarta kamar tai hauka takeji, dan gaba ɗaya kalmar zubewar cikin nan ta gama birkita mata lissafi, kallo ɗayama zakai mata ka fahimci bata a cikin nutsuwarta.
Shi dai Doctor yay musu ƙarin bayani akan idan Shahudah ta tashi, tare da cewa zaije asibiti, idan ya taso aiki zai biyo ya kawo mata magunguna.
★★★★★★
Koda Jawaad ya koma Office harkokin gabansa ya cigaba dayi tamkar babu abinda ke damunsa, sai ɗan ciwon kai da yake danganta nasabarsa da jininsa da aka ɗiba, maimakon kuma ya samu nutsuwa ya huta sai hakan ta gagara, dan bayan kamar awa biyuma Asibiti sukaje shi da Hafeez duba Alhaji Kokino da jikinsa yay ƙyau Alhmdllh.
Dukkan iyalansa na wajen, Shema’u ganin Jawaad jikinta har ɓari yake, shiko batasan yanada abinda kecin ransaba, koda ta gaishesa hannu kawai ya ɗaga mata ko kallon arziƙima bata samu daga garesa ba.
Basu wani jimaba suka baro asibitin, kasancewarsu ƴan sandan farin kaya, ba kaki suke sakawa ba sai babu ruwan kowa dasu, babuma wanda ya kawoma ransa ƴan sandane su, sai dai iyalan Alhaji Kokinon da suka sani.
Bai sake waiwayar gidansu Shahudah ba sai da ya tashi aiki, daga nan ma ɗin gida ya wuce, yay wanka ya kimtsa bayan yasha tea daya zame masa amini yanzu, ya fito cikin kayansa masu taushi farare masu tambarin Adidas, ƙamshinsa yake fitarwa a hankali.
Yauma da kansa ya tuƙa motar zai fice, a gate sukai karo da yaron Kawu Saminu Mas’ood, sauke gilas ɗinsa yayi kamar yanda Mas’ood ɗin yay shima, cikin mutuntawa suka bama juna hannu kowanne yana daga mota bai fitoba sukai musabaha, kowa na tambayar iyalan ɗan uwansa.
Daga haka Jawaad ya fice Mas’ood kuma yay ciki.
Redio ya saka yana saurare harya isa anguwar su Shahudah dake shiru babu hayaniya, duk da babu wutar lantarki ko wanne gida zaka samesa da hasken janareto tunda anguwar duk irinsune masu hannu da shuni.
Yanayin Horn mai gadi ya buɗe da hanzari, dan cayake burkutaccen nanne Qaseem.
Salman da jack na zaune a harabar gidan can gefe, Dukansu kowa da sigari a hannunsa yana zuƙa suna fira.
Salman yay saurin jefar da tasa ya take da ƙafa saboda ganin motar Jawaad.
Nesa dasu kaɗan yay fakin, dukda ya gansu ko kallo basu ishesaba ya rufe motar yay ciki abinsa.
Babu kowa a falon gidan, amma tv nata ɓaɓatu, tsaye yay yana bin falon da kallo kamar wani baƙonsa, hannayensa dukansu na cikin aljihun wandonsa.
Aamila ta fito daga kicin hannunta ɗauke da kofin tea da kuku ya haɗama Shahudah ta amso mata.
Sosai ta firgita da ganin Jawaad, yanda tai bayama kaɗan ya rage ta zubda shayin.
Ɗauke idonsa yay daga kanta tamkar baiga halin data shigaba.
Sannu tai masa, bai amsaba sai kansa kawai ya gyaɗa mata, cikin in ina tace ya hawo sama Shahudah nacan.
Duk da yayi ɗan mamakin miya maidata sama bayan yasan ɗakinta a ƙasa yake, amma sai bai ce uffanba yabi bayan Aamilah.
Aamilah ce ta sanarma Mummy da zuwansa, Mummy taɗan ɗaga murya tana faɗin ya shigo mana.
Jawaad dake ƙofar ɗakin tsaye duk yana saurarensu tura ƙofar yay ya shiga da sallama.
Kallo ɗaya yayma Shahudah dake kwance a gadon dan bata daɗe da farkawa ba, ta daiyi wanka dan ɗaure take da tawul fari, daka ganta kasan batada lafiya dan tayi zuru-zuru, ta ƙara haske sosai ga idanuwa sun kuma yo waje.
Gaisar da Mummy data miƙe yayi, ta amsa suna ficewa ita da Aamilah daga ɗakin.
Tunda suka fita saiya shiga bin ɗakin da kallo tamkar ya ajiye wani abu a ciki, hakan ya saka itama Shahudah ta bisa da kallo ƙirjinta na wani bugawa kamar zai fito.
Kusan minti ɗaya yana kalle-kalle kafin ya koma baya. jingina yay da bango hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa, ƙafarsa ɗaya ajiye a ƙasa ya tokara ɗayar jikin bango, ya tsurama jojo karen Shahudah dake kwance kusa da ita ido ko ƙyaftawa bayayi, sai faman cizon leɓensa na ƙasa yakeyi.
Shahudah da duk jikinta babu ƙwari ta miƙe zaune da ƙyar ta jingina da filo, kofin gefenta ta ɗauka tana juya cokali cikin shayin da Aamilah ta kawo mata, ta ɗago idanu ta sake kallonsa, “Bb ka zauna mana” tai maganar a matuƙar sanyaye.
Ƙala baice mataba, sai ƙafarsa daya sauke yana cigaba da kallon jojo.
Ya tako a hankali zuwa gaban gadon ya tsaya a kanta, sai kuma ya ɗora tsaftatacciyar ƙafarsa saman gadon yana zuba mata idanunsa da suka canja launi baki ɗaya.
A bazata tajiyo muryarsa kausashe yana faɗin,
“Wane likitane yay wannan aiki?”.
Dakewa tai cikin nuna halin ko in kula tace “Wane ai kuma Bb? Kainefa ka bani jini, kuma doctor ɗinmu ne ya ɗiba, wane kuma aiki kake buƙatar sanin wanda yay bayan wannan?”
Ƙafarsa ya sauke ƙasa yana sakin wani murmushin daya saka zuciyar Shahudah harbawa da ƙarfi.
Kujera ya jawo ya zauna, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, ya kuma tsuke fuskarsa yana kafa mata rikitattun idanunsa, “Hudah kinsan sunan aikin ɗan sanda kuwa?”.
Kanta ta girgiza masa a hankali, yanayin da fuskarsa take ya sake ruɗata.
Sauke ƙafarsa yay ya ɗan ranƙwafo yanda zasu ƙara samun kusanci, cikin magana ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa ya kaɗa mata yatsun hannunsa biyu yana kuma fiddo idanu waje sosai yace, “Wasa ƙwaƙwalwa. Dan haka ki faɗa min minene gaskiyar zance akan cikina?”.
Babu shiri Shahudah ta saki kofin shayinta a ƙasa, ya zube kofin ya tarwatse, jikinta sai ɓari yake, murya na rawa tace, “Bb wace irin magana ce wannan? Kana zargina nina zubar kenan?”.
Wani murmushi ya sakar mata yana bin kofin dake tarwatse a ƙasa ga shayin ya jiƙe musu ƙafafu da kallo, ya wani wulƙita idanu luuu yana maido dubansa gareta har lokacin fuskarsa da murmushi wanda ita tasan ma’anarsa sam bana farin ciki bane, ya janye ƙafarsa daga laimar ruwan yana miƙewa tsaye.
Key ɗin hannunsa ya shiga kaɗawa yay taku ɗaya biyu kamar zai nufi hanyar fita sai kuma ya juyo gareta yana nunata da key ɗin.
“Hudah nai miki farin sanin da inaga ko iyayenki basu gama nutsuwa sun mikiba, tun muna mu biyu a ɗakin nan ki faɗamin da haɗin kan wa kika aikata?”.
Cikin son kare kanta ta aro jarumtar dole ta fara masa bayanin abinda likitansu ya faɗa.
Uffan baice da itaba ya zaro handkherchief a aljihunsa yana rissinawa ya ɗauki wani abu a ƙasa, takowa yay ya dawo gabanta, ƙafarsa ya maida a saman gadon ya nuna mata syringe ɗin daya ɗaukko.
“Ki bani amsa da gaggawa kafin nakai maƙura, Wane likitane ya bada?”.
Karon farko a rayuwar Shahudah da taso karanto wata addu’a a harshenta saboda tsagwaron tashin hankali da ruɗani, sai dai batama san miya kamata ta karantan ba tunda ba addu’oin ta saniba.
Kanta ta shiga girgiza masa tana hawaye da matsawa baya, “Bb ni bansan komaiba wlhy, wannan abun bansan wanene ya kawosaba, sai dai idan likitocin nan suka yardashi by mistake, ka yarda dani dan ALLAH”.
Cikin halin ko in kula yace, “Ba dolema na yarda dakeba ƴammata” yay maganar yana ɗaukar leda a saman mirror ɗinta ya saka sirinjin, ko kallonta bai sake yiba ya juya ya fice daga ɗakin cike da izzar da ɓacin rai ya haddasa masa.
Da ƙarfi Shahudah tai yunƙurin miƙewa tsaye danta bisa, sai dai rashin ƙwarin jiki yasa jiri ya kwasheta ta koma saman gadon yaraf ta kwanta hawaye na gudu saman fuskarta, ita kanta a yanzu jitai tana buƙatar cikinma, kodan tashin hankali da tsagwaron bala’in data hango cikin idanun Jawaad.
Mummy da Aamilah na falon, sai dai Aamilah ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kaikawo take tsakanin kujeru, gaba ɗaya yanayin Jawaad ya kuma tsoratata.
Duk da ac dake aiki a falon ita zuface ke tsatstsafoma goshinta.
Sarai Mummy ta lura da halin da Aamilah ke a ciki, amma ta kasa tambayarta mike damunta, dan tunda aka shaida musu cikin nan ya faɗi komai ya sukukuce mata, ko mama Atika ta kasa kira ta sanarmawa balle sauran ƴan uwanta……
Sakkowar Jawaad a fusace daga sama ya katse mata tunani, daga ita har Aamilah suka zuba masa idanu kamar yau suka fara ganinsa.
Baiko kallesu ba yay ficewarsa saboda shiyasan shika-shikan rashin mutuncin daya shiryama kowa a gidan akan cikinsa.
Sosai abinda Jawaad yayi ya kuma birkita zuciyar Mummy, hakama Aamilah da tasan dokar.1
STORY CONTINUES BELOW

A bakin ƙofa Jawaad da Qaseem sukaci karo, kallon kallo sukaima juna Jay ya ɗauke idanunsa ya raɓa Qaseem ɗin ya cigaba da tafiya tamkar baisanshi ba.
Shiko Qaseem ya bisa da kallo har sai da Jawaad ya shiga mota yabar gidan sannan ya taɓe bakinsa, cikin falon ya ƙarasa shiga inda ya samu su Mummy yanda Jawaad ya barsu.
“Mummy miya kawo wancan shashashan gidannan kuma a daren nan?”.
Mummy data maido kallonta ga Qaseem tace, “Kamin wannan tambayar bayan kasan matarsa tana a gidan”.
Zama yay yana jan tsaki, “To ba gidansu tazoba, halan zuwa yay yace su tafi taƙi dan naga yana faman haɗiyar baƙar zuciyarsa da wataran zata zama ajalin sa”.
Kai kawai Mummy ta iya girgizawa tana haɗiye yawu da ƙyar, bayanin dukkan abinda ya faru da Shahudah ta bashi.
Qaseem ya miƙe zumbur yana faɗin, “Mummy anya yarinyarnan ba ɓarar da cikin nan taiba kuwa da gangan?”.
“Wace irin magana kake haka Qaseem? Yanzufa na gama maka bayani akan abinda Doctor ya faɗa mana dangane da mahaifarta ce bata da ƙwari……”
Saurin katse Mummy yay da faɗin, “Kai Mummy impossible, a wannan fushin na Jawaad akwai magana, inkuwa har da gaskene abinda Doctor ya faɗa to lallai shi bai yarda ba, kuma zaiyi bincike”.
“Bincike kuma Broth…?”. ‘Aamilah ta faɗa tsigil cikin sarƙewar harshe’.
Kallonta Mummy da Qaseem sukayi, Mummy dai kuma rikitar da ita sukai, shiko Qaseem ya kafe Aamilah da idanu dan yanayinta ya tabbatar masa bata da gaskiya.
Kafin ya samu damar yin wata magana Salman da Jack suka shigo falon.
Wucewa Qaseem yay sama wajen Shahudah, hakan yasa suma su Mummy take masa baya su duka suka bisa.
A yanda duk suka tarar da Shahudah ne ya tabbatar musu akwai matsala, kusan duk a tare suka shiga jera mata tambayoyi, bata amsa na kowaba a cikinsu sai hawaye da take zirararwa.
Mummy ta zauna tare da jawo kan Shahudah ta ɗaura saman cinyarta, kanta ta shiga shafawa a hankali alamar lallashi.
Hakan ya saka Shahudah fara sambatu da roƙon Mummy akan Jawaad, jinfa zata ɓallo musu ruwa Aamilah ta zauna tana riƙe hannun Shahudah da faɗin, “Haba sister kiyi shiru mana, ki kwantar da hankalinki bakida lafiya fa, insha ALLAHU komai zai zama normal indai Brother Jawaad ne zai huce shima, yanzu yana cikin ruɗanin rashin cikinne da halin da take ciki, amma ki bashi kwana biyu zai sakko ya fahimta kamar yanda kowa ya fahimta”.
Ita dai Shahudah kawai tana sauraren ƙanwar tatane, amma ita tasan wanene Jawaad da abinda zai iya, ballema tun farko tariga da ta saka masa shakku akan cikin tun fil azal, tasan yanzu kam sai abinda ALLAH yayi kawai, amma tabbas akwai ƙura bata wasaba.
★★★★★
Jawaad kam koda yabar gidan gida ya koma, amma tunda yay fakin sai ya gaza fitowa daga cikin motar, kifa kansa yay saman sitiyari yay shiru tamkar mai barci.
Tun yana iyajin motsin wasu daga jama’ar gidan da hayaniyar yara har gidan ya koma yay tsit alamar dare yaja sosai, baka iya jiyo komai sai kukan karnika na gidajen makwafta, da yake akwai wuta kuma sai anguwar ta kuma samun nutsuwar yin shiru babu ƙarar Generators dake hana kunnuwansu zama lafiya.
Tashi yay zaune sosai ya kwantar da kujerar da yake ya ƙara yin Balance ɗin samun yin tunanin da ƙyau, sam baya sha’awar shiga sashen nasu saboda ƙunar da zuciyarsa ke masa.
A watannin daya ɗauka na aurensa da Shahudah bai tsinci komaiba sai takaici da ɓacin rai, kullum da salon fitinar da take kawoma rayuwarsa, ga hargitsin aiki gana cikin gidansa.
Ya tuna maganar kakansa daya taɓa faɗa masa lokacin aurensa da Shahudah.
*_“Jawaad naso ka auri irin wadda rayuwarka keda buƙata, amma tunda haka ALLAH ya tsara muna maka fatan alkairi, sai dai ka sanifa shi ubu mai ƙyau abin san kowane, sai dai ba kowanne ƙyaƙyƙyawa bane kake samunsa ciki da waje mai amfani da amfanarwa, dakamar wuya asamu cikakken farin ciki tattare dashi inhar akwai tangarɗa tun fil azal, wani lokacin daga yanayin ginin abunne a zuciya da kuma rayuwa, wani lokacin kuma tun usul akwai rashin nagarta musamman idan anci karo da sakacin iyaye wajen rashin yin ginin da addini ya koyar, bazaka fahimci komai daga zantukana ba Jawaad sai nan gaba kaɗan, irin waɗannan yaran abinda zaku haifane abin tausayi dakai kanka da za’a jefa cikin garari ba suba, amma dai ALLAH ya sanya albarka da alkairi a ciki, ALLAH yasa muce gamma da akayi”._*
Nannauyan numfashi Jawaad ya sauke yana rumtse idanu da ƙarfi, wato irin waɗannan tashin hankalin da jahilcin ne kakansa ya hango masa tattare da auren Shahudah, wanda shi a baya tunaninsa bai kawo kan hakaba, kawai yafi kallon rashin isashshiyar tarbiyyarta zai tsayane ga taɓara kawai, kuma zai iya canjata da wuri tunda tana sonsa.
A irin kima da nagartar Dad ɗinsu bai ƙyautu ace zuri’arsa ce a wannan yanayin yahudancinba da sunan wai ƴancin kai, shikenan dan ƙaddara ta shigar dakai cikin wata rayuwar da ba takaba saika mantar da kanka da zuri’arka tushensu da addininsu da al’adunsu?, ansan a shekarun da suka ɗauka cikinsu dolene a samu raunin al’adunsu, dan yau da gobe ta wuce wasa, ballema ba zuwa gidan sukeba su, to amma bai dace a duk inda ka tsinci kanka ya zam ka manta da addininka da koyarwarsa ba, dan ako ina kake ALLAH ya wajabta maka yinsa da kuma neman ilimin sani a kansa.
Lallai yana ganin anzo gaɓar da zai tunatar da Dad da Mummy abinda suka mantan kokuma son zuciya ya sakasu maidashi baya saboda son ƴaƴa ko sakacinsu.
Haka Jawaad yayta tunani bai fargaba sai kiran sallar asubahi yaji, nannauyan numfashi ya sauke tare da kallon agogon dake a tsintsiyar hannunsa.
Ya ɗan matse idanunsa da sukai masa nauyin buƙatar barci, da ƙyar ya yunƙura ya tashi zaune sosai, ya buɗe motar ya fita ya nufi ciki.
Ji yake tamkar yabar gidannan gaba ɗaya yau ɗinnan.
1
_________________________
BILKEESU
_________________________
Sosai na samu nutsuwar zuciyar zama dasu Ummie, dama can ni a rayuwata inahar zaka nunamin ni mutumce kamar kowa mai daraja tuni nake sakar maka jiki, to yanda su Ummie suka amsheni sai hakan ya dasamin ƙaunarsu.
Nazifa ce dai har yanzu muna sama-sama ne, niko halinta bai dameniba ko kusa, abinda ya kawoni ma nafi son maida hankali kansa ba matsalar wani ba.
Dan na tabbata a halin yanzu wannan ilimin dazan nutsu na samune babbar katangata kuma gatana koda anan gaba idan ALLAH yasa muna a cikin masu tsahon rai.
Su dukansu babu mugunta suke nunamin karatu, hatta da Nazifa da batayina tunda na fahimci mayyar mathematic ce sai nake raɓarta ta koyan abinda ban fahimtaba.
Zakusha mamaki yanda takan zauna ta koyamin dukda anayine ana dizgani.
Ahankali sai na fara fahimtar halin kowanne a cikinsu har ita Nazifar kuwa, tunda na fahimci yanda halin kowannensu yake saina ƙara ɗaura ɗammarar zama dashi a yanda yaken danna ribantu da hakan.
Bani da lokacin hatta tunani a yanzu, na maida dukkan hankalina ga karatun sai ko bautar ALLAH dake a gaban komai, kullum kuwa ina ƙoƙarin miƙama UBANGIJI kukana.
Abinda ya kuma sakamin nutsuwa da Nazifa sam bata wasa da salla, lokuta da dama ma ita kema su Ummie faɗa akan su tashi suyi akan lokaci, idan har zan tashi da daddare da taji motsina itama zakaga ta tashi tayo alwala tazo kusa dani ta shinfiɗa abin salla.
Hakan dasu Ummie sukaga munayi sai suma ya fara tasiri a ransu, sai suka fara cewa suma mu tashesu dan ALLAH.
Daga nan sai muke tashinsu, itama Rebecca sai take tashi taita addu’oinsu, dan bata iya barcin da muma mun tashi, fatanmu dai ALLAH ya tabbatar da nasara a garemu akan wannan jarabawa.
Kusan halin ƙuruciya, a irin wannan shekarun namu dama zakaga daga harkar makaranta saina samari ke tasiri a rayuwarmu, dan idan mun zauna hira su Zuhrah kanta hirar samarinsu, nidai bani da abin faɗa, dan ko’a mafarki ban taɓa saurayiba, na tuna sanda ina gidanmu na haya har habaici akema innata akan banda farin jinine, bata cewa komai, iyakarta murmushi kawai.
Sai zuwa yanzunne nima nake gasgata maganarsu, lallai banida farin jinin, dan nidai ba’a taɓa cewa ana sonaba, ko irin soyayyar nan ta ƙuruciya ban taɓa yiba, sai dai naga ƙawayena nayi harma a bani saƙon musayar wasiƙar soyayya na kai………….✍🏻
4
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻3Shafi na ashirin da biyar
Kuyi manage tau babu editing🤥😒
………….Wanka ya samu yayi da ruwan ɗumi danya rage nauyin jikin, sannan yay alwala ya fito, jallabiya kawai ya saka ya fito zuwa massallacin gidan dake a ƙofar kiga.
Ana idar da salla ya fice abinsa, dama yau a makare yazo, dan haka yay sallar a ƙofa-ƙofa, bai yarda tsayawa gaisuwa da kowa ba har kawunansa, ya gudo gida ya kwanta.
Duk yanda tunanin yaso masa tasiri barcin da ya keji sai yaci ƙarfinsa, kafin kace mi ya fara sauke numfashi a hankali alamar dai yayi nisa cikin barcin.
A makare ya tashi zuwa office, dan haka yayta komai cikin hanzari harya samu ya kimtsa, yayi ƙyau sosai, ya fito yanata baza ƙamshi kamar ko yaushe.
Gimba da tun ɗazun yake gewayensa da tunanin ko lafiya?, yay saurin miƙewa daga wajensu mai gadi ya nufosa.
Sam babu walwala a fuskarsa, ɗaure take tamau babu sauƙi, kusan biyar daga matasan ƴammatan gidan da suka fito zasu wuce makaranta suka shiga gaishesa kowacce zuciyarta a narke da ƙaunarsa.
Hannu kawai ya ɗaga musu dan baijin zaima iya motsa bakin balle aje ga magana, da sauri Gimba ya buɗe masa motar saboda yau dai yasan babu wargi a wajen boss.
Shima sai da ya zagaya mazaunin direba sannan ya fara gaishesa.
Shiru Jawaad ɗin bai amsaba, Gimba ya kallesa ta mirror, yanda ya gansa kwance a jikin kujera idanu a lumshe ya tabbatar masa lallai akwai matsala.
Bai sake cewa komaiba ya tada motar suka fice daga gidan.
Sai lokacinne Jawaad ya amsa masa gaisuwar, tare da faɗa masa inda zasuje kafin Office.
Jin asibiti ya saka gimba tunanin ko baida lafiya ne?.
A ƙofar gida sukaci karo da motar yaran da aka bama Jawaad ɗin yanzu a Office saboda tsaro su huɗu, gilas ɗin motar kawai Gimba ya sauke suka matso suna gaisheda Jawaad ɗin cikin girmamawa.
Idanunsa ya buɗe yana ɗaga musu hannu, bayani ɗaya yay masa akan Sir Ahmad yace yau zasu fara gudanar da aikinsu, daga yanzu duk inda zai saka ƙafa dolene sai da su.
Numfashi kawai ya basu, yay musu nuni su shiga mota kawai.
Umarninsa sukabi, su ka rabu biyu kowacce mota mutum uku, ɗaya a gaba ɗaya a baya, ta Jawaad tana a tsakkiya.
Shi sam baya buƙatar wasu securitys tare dashi, amma Sir Ahmad ya matsa sosai akan yabar barin Jawaad ɗin na yawo haka tun randa abin nan ya faru tsakaninsa da Qaseem.
Shigarsu asibitin suka samu waje sukai fakin, kasa daurewa Gimba yay ya juyo a ɗarare yace, “Boss ko baka da lafiya ne?”.
Idanu Jawaad ya buɗe a hankali kan gimba, sai kuma yay masa guntun murmushi yana girgiza kai alamar (a’a).
Duk da Gimba bai gamsu ba haka ya fito, Security ɗaya kuma ya buɗema Jawaad ɗin motar, yaja kusan seconds ashirin sannan ya zuro ƙafarsa ƙasa ya fito.
Baƙin eyeglasess ɗinsa ya ɗora saman ido alamar dai babu sassauci kenan, yana tafe suna take masa baya cikin bajinta mai nuna alamun fushi tattare dashi.
Ganinsu kawai ya isa ya baka tsoro, gasu duk sunsha baƙaƙen suits da eyeglasses, fuskoki kam ba’a cewa komai saboda ɗaurewa.
Sun samu girmamawar mutane musamman ma’aikatan asibitin, duk da fuskarsa ɓoyayyar fuskace da ba kowa yasan matsayinta ba, amma yanayinsa da kwarijininsa sun saka mutane ganin girmansa a idanunsu, sannan yanayinsa ya tabbatar da ba ƙaramin mutum bane koda a hasashe saboda mazajen dake rufe da bayansa harda masu binduga a hannu su uku.
Sai ƙalilan da ba’a rasaba da zasu iya sanin fuskar, musamman tsananin kamar da yake da mahaifinsa.
Tsaye yay dai-dai saitin matar da ke a reception ɗin, duk sai ta rikice, Jawaad ya kalli gimba dake gefensa a ƙasan maƙoshi yace, “Office ɗin Doctor Tayyeb”.
Gimba ya juya ga matar yana maimaita mata.
Kai ta shiga gyaɗa masa baki na rawa tana faɗin, “Ok ok Sir” tai maganar tana ƙoƙarin kiran wayar ogan nata Doctor Tayyeb.
Basu san mi ake cemata daga canba, tanata dai ƙoƙarin masa bayanin dazai fa himta amma da alama cewa yake bazai samu ganinsu ba….
Tsawa ɗaya daga securitys ɗin Jawaad ɗin wani ya daka mata, hakanne ya sakata sakin wayar jikinta na tsuma, Gimba yace ta haɗasu da wanda zai kaisu Office ɗin ko ita ta fito ta rakasu.
Duk fa wannan dambarwar da ake Jawaad na tsayene yana saurarensu hannayensa duka biyu a cikin aljihu, nazarin asibitin da mutanen dake kaikawo a cikinsa kawai yakeyi, duk da ma tun shigowarsu kowa ya nutsu waje guda dan yanayinsu ya nunama kowa dama ba ababen wasa bane balle a gansu a ɗauke kai.
Wata Nurse ce tai musu rakkiya har Office ɗin, tana ƙoƙarin yin knocking Jawaad ya ɗaga mata hannu alamar kar tayi.
Ja baya tai kanta a rissine alamar girmamawa a garesa.
Gimba ya tura ƙofar Jawaad ya shige kansa tsaye, yayinda yaransa suka jeru a ƙofar kamar waɗanda sukazo kama ɓarawo😂.
Takun takalman Jawaad suka saka Doctor Tayyeb saurin matsawa daga jikin budurwar daya ƙwakume a Office ɗin yana lalubewa, itama Nurse ce, sanye takema da Uniform ɗin asibitin.
Wani wawan tsaki Jawaad yaja yana ɗauke kai daga garesu, Budurwar dukta ruɗe sai duƙar da kai take cikin alamun jin kunya da firgici, shi kansa Doctor Tayyeb ɗin a firgice yake, ganin Jawaad a asibitinsa da kuma abinda yaga yanayi da ƴar mutane.
Sai faman sinne kai yake yazo ya zauna a mazauninsa yanama Jawaad ɗin barka da zuwa.
Jawaad da bai tankashiba ya jeho masa tambaya mai rikitarwa,
“Wannan shine abinda kakeyi da ƴaƴan al’umma shiyyasa ka salwantar min da ciki?!!”.
Yanda Jawaad yay maganar a matuƙar kausashe ya saka jikin Doctor Tayyeb ɓari, bakinsa na rawa yace, “Yal…Yallaɓai wl… Wlhy kaji na rantse ban san komai akan maganar nanba, matarka ba zubar da cikinta taib…..”
Da ƙarfi Jawaad ya buga tebir ɗin gaban Doctor, wasu abubuwan suka zube, wasuko tsalle sukai suka canjama kansu muhallin zama.
“Mara mutunci, zaka cigaba damin wasan kwaikwayone kokuwa zaka sanarmin gaskiyar batu kafin na fasa ƙwalwarka da bindiga?!”.
Doctor Tayyeb daya manne da bayan kujera zufa na karyo masa ya share gumin goshinsa, “Yallaɓai please Calm dawn, wlhy bansan komaiba, yanda na musu bayani shine gaskiyar magana, mahaifartace bata da ƙwarin riƙe ciki…..”
Miƙewa Jawaad yayi yana wata ƴar dariya da tafa hannayensa, ya tako zuwa gaban kujerar da Dr Tayyeb yake, a saman tebir ɗin ya zauna suna fuskantar juna, ya ajiye ƴar ƙaramar bindigarsa daya ciro a aljihu ya ajiye gefrnsa.
Wani mugun yawu Dr Tayeeb ya haɗiya idonsa akan bindigar, Jawaad ya katsesa da faɗin, “Wannan itace tambayar ƙarshe dazan maka, ya rage naka ka bani amsa dai-dai kokuma ka sakemin ƙarya. Miyasa kabi ra’ayinta ka zubarmin da ciki?”.
Doctor dake lafe jikin kujera tamkar magen datai karo da kura a daji ya haɗiye wani yawu mai kauri idonsa akan bindigar Jawaad daya ɗauka yake jujjuyata a hannu, tabbas yasan Jawaad zai iya aikata komai, shiko da baida laifi gara ya fidda kansa a cikin wannan bala’in tunkan kwaɓarsa tai ruwa, saboda kuɗin Aamilah bazai halaka kansa ba a wofi.
“Yallaɓai kayi haƙuri ka ajiye bindugar na rantse duk abinda kake buƙata zan sanar maka shi”.
Cikin wani salo da murmushin mugunta Jawaad yasa ɗanyatsa ya tura eyeglasess ɗinsa sosai yana faɗin, “Good boy, ashe kasan dokar”.
“Sosaima kuwa yallaɓai” Dr Tayyeb ya faɗa yana jinjina kai tamkar ƙadangaren jangwala gwaja yaga shinkafar manja🤪.
Ajiye bindigar Jawaad yay yana ranƙwafowa kaɗan hannayensa harɗe a cinyarsa da yake zaune da ita a tebir ɗin, ɗayar kuwa tana ƙasane a jiye, “Ina saurarenka”.
Nanma kai Doctor ya jinjina masa, “Maganar gaskiya yallaɓai lafiyar mahaifarta ƙalau, zubar da cikin akai, sai dai wlhy kaji na rantse maka bani nai mata aikinba, andai kiranine kawai na ceto rayuwarta”.
Sosai zuciyar Jawaad ke tsitstsinkewa, ya zare glasess din idonsa yana zuba ma Doctor wani hargitsatstsen kalo, “Uhmyim, wato zubarwa akai? Amma miyasa ka zaɓi faɗar abinda ba haka yakeba? Haka aikinka ya koya maka?”.
“Wlhy A’a yallaɓai, kuskurene ka gafarceni”.
Sauka Jawaad yay daga saman tebir ɗin yana taku a hankali yana faɗin, “Maybe na iya yin hakan idan na tabbatar babu saka hannunka a ciki”.
“Wlhy da gaske nake babu hannuna, bankuma san komai a kaiba”.
Komawa Jawaad yay ainahin kujerar daya fara zama ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana aza hannunsa ɗaya a tebir ɗin yace, “Doctor Tayyeb ka sanni na sanka tun lokacin daka fara aiki gidan Alhaji Ali, karka kuskura a wannan karon ka tsinci kanka a harƙallata, dan wlhy bazan maka ragiba, na kamaka da ƙaryar farko ta faɗar sakamakon abinda ba haka yakeba, kasa a ranka ba’a min ƙarya a shani a banza, yanzu zan tafi, a koda yaushe kuma zan iya nemanka a office ɗina, zaɓin kane kazo akan lokaci koka ɓatamin lokacin”.
“Insha ALLAH zanzo yallaɓai, kuma bazan sake kuskuren maka ƙaryaba akan duk abinda zaka tuhumeni a kansa”.
“Good” Jawaad ya faɗa yana miƙewa da ƙoƙarin tura bindigarsa ta baya, bai kuma tankama Doctor Tayyeb ba ya fice a office ɗin.
Bai cema su Gimba komaiba yay gaba suka sake rufa masa baya har inda suka ajiye motocinsu, buɗe masa akai yanzunma ya shiga ya zauna sannan suma duk suka shiga suka bar asibitin a sukwane.
Haɗiyar zuciya kawai Jawaad keta faman yi, shi kaɗai yasan mi yakeji da yanda ƙirjinsa ke zaɓalɓalar azabar kunar zuciya, shi Shahudah ta zubarma ciki dukda gargaɗin ta da yay akan karta aikata hakan?.1
STORY CONTINUES BELOW

Doctor dai tunda Jawaad ya fice saiya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana share gumi, mikewa yay yaɗan leƙa kansa ta ƙofar da Jawaad bai rufe da ƙyauba, sai da ya hango sun fice sannan ya sauke numfashi yana tura ƙofar ya murza key ya koma jikinta ya lafe yana rumtse ido hannunsa dafe da ƙirjinsa.
A ransa yana ayyana tsaurin ido da tsantsar kwarjinin Jawaad, a fili ya furta, “Tabɗi, waɗannan ai sune mazajen gaskiya”.
😂🤣Su Doctor Tayyeb ashe mata mazane bamu da labari😝.
1
★★★★★
Ko a Office ma da suka isa kowa yau a miskile yaga Jawaad, duk da babu wani ɓacin rai a fuskarsa ko nuna damuwa.
Ya shige Office abinsa, kusan mintuna biyar ya aiko ai masa kiran Aliyu.
Babu ɓata lokaci Aliyu ya amsa kiransa da gaggawa, bayan sun gaisa cikin musabaha Jawaad ya miƙama Aliyu ledar daya ɗakko sirinjin jiya a gidansu Shahudah yana faɗin, “Inason nasan hoton yatsun wanene a jikin Syringe ɗinnan Aliyu yanzun nan”.
Cikin girmamawa Aliyu ya amsa yana faɗin, “Okey Boss, ka bani nanda mintuna Arba’in koma ƙasa da haka”.
Hannu kawai Jawaad ya ɗaga masa ba tare da yace komaiba, Aliyu ya fice shikuma ya shiga wata sabgar daban.
Kusan awa ɗaya sai ga Aliyu ya dawo, sai da ya nema afuwar Jawaad na daɗewar da yayi sannan ya zauna yana miƙa masa ledan da syringe ɗin yake ciki da sakamakon binciken, amsa Jawaad ɗin yayi da faɗin, “Thanks my Dude”.
“Babu godiya a tsakaninmu, amma akan case ɗin miye?”.
Murmushi Jawaad yay masa yana cigaba da duba takardun gabansa, yace, “Share kawai Aliy gadanga ƙusar yaƙi, su Hafiz fa?”.
Kaɗa kai kawai Aliyun yayi, bai matsa akan sai yaji ba, yace, “Hafeez da Rose inaga suna kan aikin nan, Jabeer kuma yana Office”.
“Okey, nima kam inaga zuwa yamma zan ziyarci anguwar can, dan yakamata muɗan fara motsi akan case ɗin nan, tunda ALLAH yasa munga ƙarshen wannan, saura shiga Court kawai ya rage”.
“Okey to ALLAH ya bamu nasara shima, amma wannan aikin na lura kamar zai zama na basaja ne shi?”.
Idanu Jawaad ya ɗago yana kallon Aliyu sosai, ya lashi leɓensa na ƙasa daya bushe sannan ya turasa cikin baki sai kuma ya biddosa yana janye idanunsa daga kan Aliyun murmushi kwance a fuskarsa yana faɗin, “Wani zai zama mai sana’ar kifi kenan”.
Dariya Aliyu yayi, “Kai haba boss? Wannan lokacin kuma tanan ka ɓillo?”.
Cikin taɓe baki Jawaad yace, “Mutanen duniyarne sai ka musu duniyanci kuke zama ku mori duniyar tare”.
“Hakane kam boss, kenan yau akwai zama?”.
“Eto bance a’a ba, amma da kamar wuya, dan akwai wani rami na cikin gida da nima nakeson cikewa, maybe zaku bani yau kawai na ƙarasa”.
“Ai ya zama dole Boss, ALLAH ya bada sa’ar cikosa da alkairi to”.
“Amin” kawai Jay ya faɗa yana haɗiye ɗacin daya riƙe masa maƙoshi.
Daga nan Aliyu yay masa sallama ya fita.
Kusan mintuna ashirin da fitarsa Jawaad ya ɗau ƙaramar wayarsa yay kiran Doctor Tayyeb, yana ɗagawa yace yazo ya samesa a Office.
Bai bashi damar faɗar komaiba ya yanke wayar.
Kamar yanda Jawaad yay Warning ɗinsa bai ɓata lokaciba ya iso kuwa, Gimba ne ya kawosa har Office ɗin, Jawaad daketa faman aiki da Computer baiko motsaba balle ya kallesu har Doctor Tayyeb ya zauna.
Sai da kusan mintuna biyu suka shuɗene ya fara magana ba tare da yabar aikin da yakeyiba.
“Kasan wane aiki zakai min?”.
“A’a yallaɓai sai ka faɗa”.
Jawaad yaɗan kallesa sai kuma ya maida kansa ga aikinsa yana cigaba da faɗin, “Yatsun hannun duk jama’ar gidan Alhaji Ali nake buƙata amma banda Qaseem da shi Alhaji Alin, ya rage naka kabi ta hanyar da ya dace ka aikata, kokuma kayi rawar kai ni kuma na ragargaza maka kwanya babu ruwana”.
Cikin haɗiye yawu Doctor yace, “Wannan mai sauƙine mai gida”.
“Na fika sanin sauƙinsa, dan danaso zanje kai tsayene na nema basai nabi ta hanyar kowaba, inada nawa dalilin sakoka cikin aikinne kawai”.
Ba ƙaramin faɗuwar gaba Doctor yajiba, ya hadiye yawu daƙyar yana fiddo idanu kamar kwarton da mai gida ya kama da farar magriba😑.
Jawaad yace, “Karka tsaya kallona, lokacinka ya fara daga yanzun”.
Mikewa Doctor Tayyeb yayi yay masa sallama ya fice……..
STORY CONTINUES BELOW

_______________________________
Idan nace muku ban fara ganin canji a rayuwata ba nayi ƙarya, dan kuwa ilimi tubaline mai ɗaga darajar kowanne mai fafutukar nemansa, idan kaga saɓanin cikagabanka a cikinsa to lallai bakabi hanyar data daceba wajen samunsa.
Kasancewar su Ummie manyan yarane wayayyu, wayewa kuma mai tsafta tuni sun fara dorani bisa layi, musamman salo-salo na tsaftace jiki dana tsara rayuwa inhar kanada ikon ribantar gobenka.
Tabbas ni baƙace, amma na yarda jin daɗi kan saka koda kai bakine baƙin ya kasance na musamman mai ɗaukar hankalin idanun mai kallonka.
A yanayin da nake ciki da sauyin iska dana fara samu tun a gidan Dad sai suka sake tasiri a yanzu a gareni, gashi dai makaranta muke, makarantarma Boarding skull, sai dai ta kasance ta musamman, dan banbancinta da rayuwar gidanma ƙalilance, anan kawai dai baka ganin iyayenka ne bakuma a ganin gari da jama’a, tunda a killace muke.
A hankali aka fara sanina saboda su Ummie ƴan babu sauƙine, guruf ɗinsu sanannen guruf ne ko a cikin ƴan mate ɗinsu, musamman saboda ƙokarinsu da kwazo da ALLAH ya basu, kowanne zakaga gwarzone a wani subject, hakan yasa har malam ma ji suke dasu ainun.
To sai shigata cikinsu nima ta kuma ƙarfafa fahimtata da tun a baya rashin gatan samun gurbin karatu mai ƙyau ya raunanashi.
Ba karatu kaɗai ba, dai-dai da yanda ake tafiya, saka sutura zuwa magana babu abinda su Ummie basa koyamin, ni wani lokacin ma har mamaki sukeba su a ina suka koyo?.
Sam bana nuna wani girmankai a garesu balle turjiya, komai sukace nayi inhar nasan bai saɓa shari’a ba ko taɓa tarbiyyar al’adata nakan amshesa hannu biyu na riƙe na kuma bada himma wajen fahimtarsa.
A hankali komaina ya cigaba da canjawa ga jarabawa nata gabatomu wadda zuwa yanzu ko fargaba banaji akan zuwanta, dan inada yakinin insha ALLAHU nima za’a goga dani a filin dagar.
Turanci kam yanda yake zama min akan harshe zakasha matuƙar mamaki da tunanin tun inada ƙuruciya dashi na tashi a baki, tsoron mutane da kuka sanni dashi zuwa yanzunkam ya fara guduwa, dan jina nake a gaban kowa zan iya fita a dama dani akan abinda ya kamata.
Sai dai kunya dake ƙara martaba kimar mace a koda yaushe tana nan daram a jikina da ayyukana bata fitaba, hatta wani abun idan su Ummie sukai nakanji nauyinsa harma na kasa saka baki ko kaina a ciki, sukan tasani da dariya sosai harsu koma tsokanata.
Bazance har yanzu Nazifa ta saki jiki daniba, amma dai bata ɗaukata da zafi kamar da.
Akwai malami da Dadyn Ummie ya ajiye mana yake zuwa duk yamma ta fannin ilimin addini, hakanne ya sakani fahimtar abinda ya zaunar da tarbiyyar su Ummie akan tsari ba tare da wayewarsu ta zarce ƙa’idar da addini ya shinfiɗaba.
Lallai ako ina inhar kanason ribantar ilimi toka ɗauki duka biyu ka riƙe, inhar da ililin addini to babu yanda za’ai ilimin boko ya dilmiyaka koyi da nasara kamar yanda naga su Aunty Shahudah sun zarma.
Wayewar mai riƙe da ilimin addini dana zamani a duk inda take dolene ta burgeka, dan zaka ganta cike da tsafta da nutsuwa babu shirme ko rawar kai a ciki.
ALLAH ka bamu ikon cin ribar ilimi a duniya da kuma lahira ba mucinye rabonmu anan duniya ba.
Zuwa yanzun kam inajin kewar gida, a duk lokacin kuma da sabbin ƙawayena suke bada labarin ahalinsu nima nakan bada labarin rayuwatane da iyayena ta gidan haya.
Sukanyi mamaki sosai, dansu sam basu taɓa tunanin ana samun makamanciyar wannan rayuwarba.
Nakanyi murmushi dan bana ganin laifinsu sam, a yanda rayuwa da duniya suka rainesu bazama su kawoma kansu tunanin akwai masu bukatar koda kwatankwacin irin tasu rayuwarba.
A koda yaushe sukan shiga damuwa da tsantsar tausayina harma da waɗanda suke da irin tawa rayuwar koma wadda ta fita, har zumuɗi suke na basu labari, sannan suna kuma ɗaukama kansu alƙawarin zamu zama masu taimakon wasunmu muma anan gaba da izinin ALLAH.
Gaskiya rayuwarsu na birgeni, dukda kasancewarsu ƴan gata iyayensu sunyi ƙoƙarin tsayawa tarbiyyarsu, ta waɗanda keda rauni a cikinsu kuma sun hadu sun daidaitata akan ƙyaƙyƙyawan bigire da shima zai amfana tun ba yanzuba, dan sun tabbatarmin tun daga js1 suke tare a makarantar, hakannema ya dasa shaƙuwa mai yawa a tsakaninsu harma da ƙulluwar zumin iyayensu, ƴar uwar Ummie data rasu na maye gurbin data bari sam basa iya mantata, kullum cikin bani labarinta da ƙyawawan dabi’unta suke, hakanne yasani fahimtarma dukta fisu zurfin ilimin addini da ƙulafucin kulawa dashi.
Wannan itace matakin na sara ta farko da ni BILKEESU ADAM MAKAHO na fara tsinta a duniyar da a baya nake kallon bata bukatar bani filin dazan zuƙi iskar cikinta a baya………….🤩✍🏻
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃💃🏻👌🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻4Shafi na ashirin da shida
Yau ma dai babu editing😣😫
…………Shahudah taɗan samu sauƙi, sai dai fargabar Jawaad ta hanata sukuni sam, gashi a yau ko ƙeyarsa basu ganiba a gidan, tanason kiransa a waya tanajin tsoro.
Kusan ƙarfe uku na rana sai ga Doctor Tayyeb yazo gidan, lokacin duk suna falo, Qaseem ne kawai babu a gidan dan yana Office wajen aiki.
Shahudah na kwance ne a kujera doguwa kanta a kan cinyar Mummy, karenta na kwance daga ƙasa kusa da ita, sai Aamilah da Jack da Salma waɗanda shigowarsu gidan kenan.
Sai da Dr Tayyeb ya bama su Salman hannu suka gaisa sannan ya zauna yana gaida Mummy idonsa akan Shahudah da keta ɓata rai, dan tasan allura yazo yay mata ita kuma batason ta.
“My patient yaya jiki?” ‘Ya faɗa yana mata murmushin yaƙe’.
“Fine” kawai tace masa ta ɗauke kanta.
Bai damu ba yace, “Alhmdllh, yanzu dai babu ciwon marar ko?”.
Kanta kawai ta ɗaga masa.
Shima bai sake cewa komaiba ya shiga haɗa allurar da zai mata, ƙasan zuciyarsa yana tunanin ta yanda zai ɓilloma aikin Jawaad.
Da ƙyar Shahudah ta tsaya akai mata wannan allura, saboda tsabar taɓara harda kukanta.
Sai da ta koma dai-dai ne ya gyara zama yana mata bayanin yanda zata kula da kanta, ya fiddo wasu ƴan kwalaben magani, ɗaya ya miƙama Salman dake kusa dashi yana faɗin, “Salman ko kasan wannan maganin?”.
Karɓa Salman yayi yana dubawa, Dr Tayyeb ya sake ɗibar biyu ya mikama Aamilah da Jack suma, “Kuma ku duba kuga ko kun sanshi”.
Suma basu musaba suka amsa, itama Mummy da Shahudah duk ya miƙa musu, da farko dai Shahudah kam taƙi amsa, a cewarta karya isheta.
Mi kuma ta tuna oho mata, sai ta miƙo hannu ta amsa.
Salman da Aamilah suka fara maido masa da kwalaben suna faɗin sudai bama su gane kan maganinba, kwalayen kwalaben ya miƙa musu duk suka saka da kansu sannan ya amsa ya maida ajikka.
Jack ya kalli Dr Tayyeb cikin nuna shiɗin ƙwararrene yace, “Wannan ai maganin hana ɗaukar cikine, macen da bata haihuwama akan bata ta gwada shi kamar na wasu wattani kafin ta dakata”.
Murmushi Dr Tayyeb yayi yana jin jina kai alamar gamsuwa da bayanin jack, ya miƙa masa kwalin shima ya saka yana faɗin, “A lallai kasan magani kam sosai”.
Jack yaji daɗin yabon da ake masa ya miƙama Doctor bayan ya saka a kwalin yana sake bajewa a kujera, suma su Shahudah duk basu yay suka saka ita da Mummy ya amshe abunsa ya maida duka a jaka, ba tare daya yi musu wani ƙarin bayani ba yay musu sallama ya tafi.
Kaf ɗinsu babu wanda ya kawo wani abu a ransa game da maganin da Doctor Tayyeb ya nuna musu, garama Mummy taji haushinsa sosai, dan ita gani take kawai Doctor ɗin nasu yayi hakanne danya nunama Shahudah hanyar ɗaukar mataki a gaba, itako yanda suka tsara yanzu nanda kwanaki kaɗan Shahudah zata koma ɗakinta ko ALLAH zaisa a dace wani cikin ya shiga.
Dan jiya dai ta daure taje gida tama Mama Atika da ƴan uwanta bayani akan matsalar Shahudah ɗin.
Dukansu sun nuna rashin jin daɗinsu da tausayin Shahudah, sai dai kuma hankalinsu ya tashi, dan a ganinsu inhar Shahudah nada wannan matsalar to kenan yaushene ciki zai fara zaman da zasu sami cikar burinsu?.
Uncle Uwaisu daya kasa haƙuri sai cewa yay, “Anya kuwa kuna ganin bazamu ɗauki matakiba? Indai hakanefa zaman Shahudah da Jawaad bazai mana wani amfaniba kenan? Ko dai mu sake dubawa cikin yaran nan saimu aura masa wata?”.
Tsitt falon yayi kowa ya kasa magana, sai dai fuskar Mummy ta nuna alamun ɓacin rai.
Mama Atika ce ta katse shirun nasu dayin gyaran murya, cikin muryarta ta tsufa tace, “Maganar Uwaisu nakan hanya, hakama shawararsa mai ƙyau ce, sai dai akwai ruɗani a cikin hakan musamman akan ku kanku da zumincin ku”.
“Gaskiyane maganarki mama, gashi kuma bamu da damar sako wani cikin ƴan uwanmu, duk da na daɗe daji a raina kowa nada nasa burin wlhy, suna ɓoyewane kawai dan ace sunason yaron sosai, musamman ma Yaya Nasiru da kuke ganinsa nan ko? Humm”.
Nanma duk shiru suka sake yi, sai Mummy ce a hasale tace, “Amma gaskiya idan akai haka ba aima Shahudah adalciba, ai kamata yay mu nema magani ko mafitar da cikin zaike zama ɗin bawai muyi tunanin mata kishiya ba, sannan ku kunama zaton shi yaron kansa zai yarda da wannan kwamacalar? Shahudah ma da yake so da yaya muka ƙulla auren nasu balle kuma yanzu? Mudai sake tunani amma ba wannan ba”.
Kowa ya gamsu da bayaninta, duk da dai ta nuna akwai nuna taya kishin ɗiyarta a ciki.
daga ƙarshe dai sun yanke shawarar nemawa Shahudah magani, sannan su maidota ɗakinta da wuri ko ALLAH zaisa a dace ciki ya shiga da wuri🤫🥴.
4
STORY CONTINUES BELOW

★★★★★
Dr Tayyeb da ya samu abinda yazo nema yana fita ya sauke ajiyar zuciya, mota ya shiga bai zauna wasaba ya koma Office ɗin Jawaad.
Lokacin Jay yana tare da su Jabeer akan tsara aikinsu da zasu dasama ɗanba.
Bayan saƙon zuwan Dr Tayyeb yazo masa ta hanyar Gimba, bai fitoba, sai gimban ya bama damar amsar saƙon a wajen Doctor.
Gimba na tsaye Dr Tayyeb na bashi kwalayen kwalaben da duk yasamo fingers print ɗinsu Shahudah sai ga Qaseem ya fito daga Office, da alama ma dai ya tashi aiki, aiko sai idonsa karaf akan su Gimba.
Ɗunbin mamaki ne ya kamashi ganin Family Doctor ɗinsu anan, yay saurin ciro wayarsa daga aljihu ya ɗauki Dr Tayyeb da Gimba hoto.
_____________________
Lokacin da Qaseem ya shigo gidan duk su Shahudah sun tashi, Aamilah ce kawai a falon itama tana cin abincine a dani.
Yanda Qaseem ɗin ya shigone ya saka Aamilah kallonsa ita da Amina dake gyaran falon.
Cikin tsawa-tsawa yace ma Amina, “K tattaro min kowa na gidannan”.
Da “To” Amina ta amsa cikin girmamawa.
Tasowa Aamilah tai daga falon tana tambayarsa ko lafiya?.
Bai bata amsaba sai ƙokarin danna wayarsa yake domin son nemo hoton su Dr Tayyeb daya ɗauka.
A haka duk suka fito suka samesu har Shahudah dake fama da kanta.
Kowa yazo sai ya masa tambayar lafiya?.
Ganin duk sun hallara ya bisu da kallo yana faɗin, “Jawaad yazo gidannan yau?”.
A tare suka girgiza masa kai, kowanne da mamakin tambayar akan fuskarsa.
Qaseem ya kuma cewa, “Doctor Tayyeb fa?”.
Salman yace, “Yazo har yayma Shahudah allura”.
Dariya sosai Qaseem ya sanya yana tafa hannaye, wadda tasakasu duk zuba masa idanu, Mummy ta katsesa, “Qaseem lafiyarka kuwa? Minene abin dariya to anan?”.
“Mummy bazaki ganeba, ni dama nasan Jawaad bazai taɓa bariba, da Tayyeb yazo gidannan bayan allura mi yayi?”.
Aamilah taja gajeran tsaki, “Iya allurar yayi mana, sai wani shirmensa na nuna mana wai ko maganin hana ɗaukar ciki, ni jakinma harya wuce ban fahimci manufarsa ba….”
Saurin katse Qaseem yayi, “K shashasha, aiku ya maida jakkan, to lallai akwai manufa, dan inada tabbacin aiki Jawaad ya sakashi, dan naga Dr Tayyeb a Office ɗinmu yanzunan yana bama gimba drivern Jawaad wasu kwalaye”.
Dukansu idanu suka zaro waje har Jack, dan da turanci duk suke magana saboda Jack ɗin ya fahimta.
Mummy tace, “Ni ban ganeba, kai mika fahimta to?”.
Cikin taɓe baki da ɗage kafaɗu Qaseem yace, “Cikinsa yake bin ba’asi mana, ki binciki ƴarki Mummy dan akwai abinda take ɓoye miki, kuma duk wanda yasan da hannunsa a ciki wlhy ya kuka da kansa dan Jawaad ya fiku iya birkicewa, aikin banza kawai kun jama mutane asara, ku duba nan ku gani” ya ƙare maganar yana mika musu wayarsa a hasale.
Dukansu jikinsu tsuma yake, musamman Aamilah da jack da Shahudah, ita kanta Mummy zuface ke karyo mata a kowacce ƙofar gashin jikinta, tsabar ɗumi da ƙwalwar kanta ta ɗauka tama rasa abin faɗa.
Dukansu babu wanda baiga abinda Tayyeb ke mikama Gimba ba, kwalaben daya basune fa.
Mummy da jikinta ke mazari ta juya tana kallon Shahudah dake a birkice, kasa ce mata komai tayi.
Ba Mummy da Shahudah ba kowama a birkicen yake, hatta da Salman da baisan komaiba yay wuƙi-wuƙi da idanu.
Daga nan kowa kai kawo ya shigayi a falon.
Shahudah, Aamilah, Jack, kowa yana tunanine akan a ina matsalar take?.
Yaya akai Dr Tayyeb ya je ga Jawaad? Aamilah da tasan yanda sukai da Dr Tayyeb zuciyarta sai tsitstsinkewa take, zargi biyune a ranta, kodai Doctor ya samu Jawaad da gaskiyar batu, kokuma Zaitun ce ta faɗama Jawaad, to amma ai Zaitun batasan wanene zai amfani da allurarba, ita kawai sun nema sanin likitane ta hanyarta, tayaya zata samu Jay da maganar abinda bata sani ba.
“Kenan a ina matsalar ta fito?”.
Aamilah ta faɗa a fili ba tare da ta sani ba.
Duk kallonta sukayi kuwa, Mummy tace, “Aamilah mi kike faɗane?”.
Cikin in ina Aamilah tace, “M… Mummy bance komaiba”.
Qaseem yace, “Humm yarinya zaki magantu ne, ni dama tun randa abun nan ya faru wlhy na fahimci baki da gaskiya”.
Tsaki Aamilah ta ja mai mugun ƙarfi tana harar Qaseem, tace, “To masheranci, ni kaɗai duk faɗin gidannan ka sakama idanu?, sokake ka ƙalamin sheri? Ai bani cikin ke a jikinaba balle kace….”
A harziƙe Qaseem yay kan Aamilah, ta zuba da gudu ta shige ɗaki ta kulle kanta.
Cikin matuƙar fushi Qaseem yace, “Mummy kina gani ko? Ni wannan ƴar iskar yarinyar take faɗama duk abinda yazo bakinta? Ƙanwata ta huɗu?”.
Cikin damuwa Mummy tace, “Qaseem dan ALLAH ku barni naji da abinda ya dameni, Shahudah inhar zubar da cikin nan kikai wlhy kin cutar damu kuwa”.
Sake ɓaci ran Qaseem yayi ganin Mummy ta nuna halin ko in kula da abinda Aamilah tai masa, Shahudah kam bata iya bama Mummy amsaba saboda jirin dake ɗibarta, ganinta kawai sukai zube a ƙasa wanwars.
2
STORY CONTINUES BELOW

______★______★_______★______
Bayan Jay ya koma Office ne Gimba ya je ya kai masa abinda Dr Tayyeb ya kawo.
Jawaad ya amsa yana buɗe ledar da aka zubo su a ciki, ɗaya bayan ɗaya ya fiddosu ya duba, yay guntun murmishi saboda kowanne da alamar da Dr Tayyeb yayma kwalin yanda za’a gane na kowa, maidasu yay duka a ledan ya sake miƙama gimba.
“Ka kaima Aliyu su, yanzu nake buƙatar results ɗinsu”.
“Okey boss” gimba ya faɗa cikin girmamawa yana amsar ledar..
Ba a wani ɗauki lokaci mai tsawo ba Aliyu ya shigo Office ɗin, lokacin Jawaad na tare da Rose suna magana akan wani aiki daya sakata.
Zama Aliyu yayi a kujerar dake kallon ta Rose ɗin ya miƙama Jay takardu na results ɗin, ya kuma ajiye kwalaben dake a ledar.
“Boss Result biyu fa yayi kama da na farko, dan a jikin syringe ɗin jiya yatsun hannun mutum biyu muka samu, amma ɗaya yafi fitane da ƙyau, duk da dai haka mun samu yanda mukeso. Ka duba da Result ɗin jiya da waɗannan na saman na mutane biyune dake jikin syringe ɗin kamar yanda na faɗa maka tun farko”.
Kai Jay ya shiga jinjinawa yana ɗan lila kansa a kujera, tuni idanunsa sun canja launi sai wani munafukin murmushi dake shimfiɗe bisa fuskarsa wanda Aliyu da Rose duk suka kasa fahimta.
Cikin sauke numfashi ya ajiye takardun yana maida kallonsa ga Aliyu.
“Aliyu kiramin Jabeer”.
“Okey Boss” Aliyu ya amsa yana ƙoƙarin kiran Jabeer a waya, koda Jabeer ya ɗaga daga can sai Aliyu ya sanar masa saƙon Jawaad.
Babu jimawa kam saiga Jabeer ɗin.
Jawaad dake rubutu a takarda ya ɗago ido ya kalli Jabeer, kafin ya miƙa masa takardar daya gama rubutun.
“Jabeer wannan Number ɗin nakeson nasan daga shekaran jiya zuwa yau da mutum nawa akai waya, sannan mutane nawa suka kira layin?”.
Amsa Jabeer yayi yana kaɗa kai, ya nufi wasu Computers guda uku dake can gefe a cikin Office ɗin Jawaad.
Hakan ne ya saka Aliyu miƙewa yabi Jabeer dan ya taimaka masa.
Rose ma mikewar tai ta koma wajen su Jabeer ɗin, shiko Jawaad ya cigaba da aikin da yake a Computer gabansa zuciyarsa na masa wani zogi da ƙuna, domin kuwa result ɗin sayin hannun Jack da Shahudah aka samu a jikin syringe ɗin, na Jack shine ya danne na Shahudah alamar shine ƙarshen riƙe sirinjin.
Kusan mintuna goma sha biyar Jabeer ya juyo yana kallon Jawaad daya maida hankalinsa ga aikinsa tamkar babu abinda ke damunsa.
“Boss ga waɗanda sukai kiran da waɗanda aka kira, sai text messages guda uku da akayi, kuma duk a jiyane kamar ma kai akaimawa”.
Miƙewa Jawaad yay zuwa inda su Jabeer suke, Aliyu yay saurin tashi ya bashi kujerar da yake zauna, jawota baya kaɗan Jay yay ya zauna, da kansa duk yabi ya duba, tabbas saƙo biyu shi Shahudah ta turomawa, sai dai babuma wanda ya duba a ciki dukda yaga shigowarsu tun ɗazun da safe, komawa yay duba Numbers uku da Shahudah ta kira randa abun ya faru, ya ƙurama Number ƙarshe ido yana nazarinta.
Kallon Rose dake tsaye yay yay mata nuni data ɗakko masa wayarsa dake tebir ba tare da yay magana ba.
Cikin hanzari taje ta ɗakko ta kawo masa.
Number Aamilah da tunda yake bai taɓa kiraba sai dai ita ta kirashi ya lalubo.
Akan laɓɓansa ya furata, “Aamilah” a hankali, Murmushi ya saki yana cizar leɓensa na ƙasa, “Jabeer bincikamin itama wannan Number ” yay maganar yana nuna masa Number Aamilah.
itama duƙufa Jabeer yay a kanta, ana cikin hakane Hafiz ya shigo hannunsa ɗauke da takardu, ganin sun haɗa kai waje guda ya nufisu yana faɗin, “Wane shagalin ake anan kuma?”.
Duk kallonsa sukayi, banda Jawaad da Jabeer da hankulansu ke bisa Computer ɗin.
Jabeer yace, “Wannan sune ta kira a jiya, waɗan nan suka kirata, ga kuma na yau”.
Shiru Jawaad yay yana kallon Numbers ɗin, ya sauke numfashi yana girgiza kai, “Ina na shekaran jiya?”.
“Gasu nan” cewar Jabeer yanama Jawaad nuni dasu bayan ya kuma zooming ɗinsu yanda Jay zai gani sosai.
Ahankali ya ringa nazarinsu ɗaya bayan ɗaya, “Jabeer inason nasan kowacce number daga ina akai kira da ita, wanda ta kura kuma a ina yake”.
“Amma zamu ɗauki lokaci Boss, magriba kuma ta gabato……..”
Kafin Jawaad yay magana Rose tace, “Bara muyi tanan kawai zaifi mana sauri”.
Duk juyawa sukai suna kallonta har Jay ɗin da yake lafe jikin kujera yana shafa ƙasumbar data ɗan taru mai a fuska kaɗan.
Sun santa mayyace itama a irin waɗannan binciken, shiyyasa suke son zamanta a tafiyarsu sosai.
Tana danne-danne tana kai kawo, hakan yasa suketa binta da kallo, shima Jabeer bai fasaba dubawar yake daga ɓangarensa.
Cikin min tunan da basu gaza biyarba, Rose tace, “Number mai ƙarshe 3434 mai ita tana a anguwar Sunusi Abdullahi stress, layi na biyu gida mai lamab 107, an kiratane da ƙarfe 10:34am, zamu iya kiran kamfanin layin idan kana bukatar jin abinda aka tattauna akanta Boss”.
Cikin kafeta da idanu yace, “Kin tabbatar?”.
“Yes Sir, gashima ka duba da kanka” tai maganar tana miƙa masa.
Amsa yay shima yana dubawa, duk abinda ta faɗa dai-dai ya gansa, wani luuuu yay da idanunsa yana busar da huci mai azabar zafi. Kafin ya samu cewa wani abu Jabeer ya katseshi da faɗin,
“Boss ita kuma wannan daga Asibitin *NASARARMU* yanzu haka ma mai Number yana cikin asibitin, sannan Number da Rose take magana itama ta kirashi mintuna biyar kafin ita wannan ta kirasan, shima kuma ya kira waccan ɗin bayan awa ɗaya da kiran wannan.
Da ƙarfi Jawaad ya bugi tebirɗin da Computers ɗin suke kai, sai faman fidda numfashi yake da sauri-sauri.
Cikin kakkausar murya yace, “Muna idar da salla ku tababbar likitannan ya gurfanu a gabana, sannan mai wannan number itama kuje har gidan ku kamomin ita!!!”.
Ya ƙare maganar a matuƙar tsawace.
Su duka a tsorace syke kallonsa, gashi dama basu san komai game da aikinba, amma sun kula ya ɗaukesa da zafi tun jiya.
A cikin girmamawa duk suka amsa masa.
Uffan bai sake faɗaba, sai da ya ɗauki rigar suit ɗinsa yana nufar ƙofa yace, “Duk ku kaimin su Zangina road ina jiranku a can”.
Bai jira amsarsuba yay ficewarsa……………🤫✍🏻
3
Naji dukkan ƙorafinku akan son posting kullum, sai dai nace kuyi haƙuri kam, dan lokacine banda shi isashe, buks biyu nakeyi a lokaci guda, bazai yuwu kullum nace zan fidda pages biyu ba, na farko typing yana lashe lokutane, ga hidimar gida, sannan idanuna, ko bakwaso na tsufa da idanune😂?, sai kuma ita kanta ƙwalwa ai tana buƙatar hutu, ta hakanne za’a samu rubuta abu mai amfani da nutsuwa, sannu-sannu bata hana zuwa, da zaran mun kammala ZAFAFA komai zai dai-daita da izinin UBANGIJI, ngd da Comments ɗinku dan suna sani nishaɗi matuƙa, hakama addu’oinku ga mahaifina sukan ƙaramin jin kaimin muku typing koban niyyaba😭🙏🏻, I luv u wujiga-wujiga my kankanati fans😻😻🤫😂.
5
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Shafi na shirin da bakwai
4
…………Koda motar Jawaad da ta Security’s nashi suka iso ƙofar gidan nasu Shahudah basu shigaba, cayay suyi fakin a ƙofar gida.
Zamansa yay a mota bai fitaba, hakan yasa securitys nashi fitowa su zagaye motar da yake a ciki.
Yanata danne-dannensa a waya kai kace bashi bane ya fito Office ɗazun a fusace, sai dai shi yanajin zafinne a cikin zuciyarsa, yayinda fuskarsa ta shanye komai tamkar babu komai.
Har aka kira sallar isha’i suna wajen, da kansa ya buɗe ya fito daga motar dan son gabatar da salla.
Masallacin anguwar dake jikin gidan maƙwaftan su Shahudah suka shiga, tare dasu akai jam’i, suka bar waɗanda basayi a wajen.
Bayan fitowarsu daga salla ne sai ga su Hafiz sun iso tare da Zaitun da Dr Jeo, sake shiga mamaki Zaitun tayi ganin ɗan uwanta Jawaad da take mutuwar ƙauna.
Shiko kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa tamkar bai santaba ma.
Shi da rose da Hafiz, kawai suka shiga gidan, aka bar Aliyu da Jabeer a waje tare da securitys da su Zaitun da aka zubo a mota.
Amina data fito tana shirin wucewa gida tai azamar matsawa ta basu hanya jikinta na rawa, ko kallonta basu yiba kuwa, sai knocking ƙofar falon da Rose ta shigayi.
Amina da ta samu waje ta laƙe inda zata kalli komai, tace, “Ai dama tunda naji dambarwar da akeyi ɗazun a gidan nasan yau akwai kura”, dan haka tai azamar komawa ta ƙofar kicin ta baya, dan tayi alƙawarin sai taga komai kodan ta bama Bilkisu labari idan ta dawo.
Tunda labarin zuwan Dr Tayyeb wajen Jawaad yazoma su Shahudah kowa ya kasa zaune ya kasa tsaye, ga Dad baya nan yayi tafiya jiya da yamma.
Aamilah tafi kowa shiga ruɗani dan dama can ita a kwai tsoron masifa, Shahudah kam dama tanada taurin kai tun fil azal, dukda tana a tsorace da sakamakon abinda zai biyo baya wani gefen zuciyarta na nuna mata Jawaad zaiyi buyaginsa naɗan lokacine ya sakko.
Wannan gurgun tunanin natane yasa bayan ta farfaɗo daga sumar da tayi saita ragema kanta fargabar.
Sunata ƙulla mafitar da zasu kare kansu ne a wajen Jay tun bayan farfadowar Shahudah, a wannan yanayin ne motar Jawaad data security’s ɗinsa suka iso gidan.
Takun takalmansu Jawaad ya sakasu Mummy zubama ƙofar falon ido, dama Shahudah da Aamilah da Mummy ne kawai a falon, duk da kiran sallar magriba da akayi Mummy ce kawai taje tayi, maimakon taima Aamilah magana tunda ita Shahudah batayi saboda jinin ɓari sai batai ba, itako Aamilah dayake bata da man kai batai ko niyyar tashinba balle tunanin yi, idanma zaka bibiya ƙila yau daga sallar asubahi bata sake wata sallaba.
Kamar yanda Qaseem ya ɗorasu a kan keken ɓera koda Jawaad yazo kar wanda ya nuna razana hakan duk suka shirya, sai dai da yake a yanzu basuyi tunanin shi bane sai Aamilah ta miƙe domin duba mai knocking ɗin ƙofar.
Sun san dai idan Jawaad ne kansa tsaye zai shigo ciki.
Cike da barbaɗa ta buɗe ƙofar tana wani yatsine-yashine, taima Rose kallon sama da ƙasa tana faɗin, “Madam ke kuma fa?”.
Rose ta nunama Aamilah ID card ɗinta tana faɗa mata suna “Sunana Rose Ayo, ƴar sandar farin kaya”.
Karaf a kunnen Mummy da Shahudah, dan haka duk suka miƙe suma suna nufo ƙofar.
Aamilah data ɗansha jinin jikinta tace, “To lafiya?”.
“Ai mu dakin gammu kinga lafiya hajiya”. ‘cewar Rose tana wani annaminin murmushi.
Ƙoƙarin fita Shahudah da Mummy sukeyi, hakanne ya saka Rose basu hanya, itama Aamilah saita take musu baya.
Dukansu idanunsu akan Jawaad dake jingine da ƙarfen da akai kwalliyar barandar suka sauka, ya harɗe ƙafafu waje guda yana danna waya tamkarma baisan mi akeba.
Mummy da jikinta ke tsumar tsoron ganin yanayin Jawaad tace, “My son lafiya kuwa….?”
Kansa ya ɗago yana wani kaɗa hannunsa ya matse wayarsa tare da miƙewa tsaye sosai, a kausashe yace, “Ba ɗaba, Jami’in tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya *_JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSUF_* ne wannan, munzo ne domin gayyatar mutane uku na gidannan zasu amsa mana wasu ƴan tambayoyi a office Hajiya”.
Idanu sosai Mummy ta zaro, Shahudah kam ai neman faɗuwa ƙasa tayi, Rose kuwa dake mata kallon tsana ta tarota tana fadin, “Madam kulafa”.
Shiko Jawaad ko kallon inda Shahudah take baimayiba dama.
Aamilah cikinta kam ya ɗuru ruwa, harta fara ƙaramin fitsari a pant ɗinta😝.
Dai-dai nan Jack da Salman suka shigo, dan yajene ya gama shirin jirgin da zai tashi a safiyar gobe dashi zuwa ƙasarsa kamar yanda Qaseem ya bashi shawara, sam basuyi zaton zuwan Jawaad gidan a daren yau ba, ko a ƙofar gida da sukaga motoci basu kawoma ransu shineba tunda shi dai Salman yasan Jawaad baida Securitys.
Mummy zata sake magana Jawaad ya daka mata tsawa yana faɗin, “Hajiya nace wannan ba ɗanki bane, jami’in tsarone a gabanki ki kama kanki”.
Ba Mummy ba hatta dasu Hafislz kansu tsawarsa ta firgitasu, dama tunda suka iso gidan mamaki ya kamasu, dan dai a saninsu wannan gidan Gwaggonsa ce, kuma gidan surukansa. Furicinsa sosai ya sakasu a ruɗani, ya kuma basu umarnin tafiya da Shahudah da jack da Aamilah.
Yana gama lissafa da waɗanda za’a tafi ya doshi hanyar barin gidan cikin takun bajinta mai ɗauke da izzar fushi.
Gaba ɗaya ji da ganin Mummy sai ya toshe ɗaf, bibiyu ma takoma ganin mutane saboda ruɗani da mamakin Jawaad.
Kukan da Aamilah ke yine saboda tafiya da za’ai dasu ya maido Mummy a hayyacinta, duk roƙo da magiyar da takema su Hafiz babu wanda ya saurareta, umarnin boss ɗinsu kawai suke ƙokarin cikawa, duk da zukatansu a ƙulle suke da wannan aiki sukam yau.
Lokacinma da suka fito dasu Shahudah tuni Jawaad ya shige mota abinsa, ya lumshe idanunsa da sukai masa nauyi, jijiyoyin kansa sun fito raɗa-raɗa bisa kansa, duk yanda yaso kiyaye irin wannan ranar sai da Shahudah tai ƙoƙarin zuwanta, to lallai kam zai tabbatar musu shi *_ƘWAI cikin ƘAYA_* ne, gashi dai abinso ga kowa, sannan kuma abin haɗari ga kowa, da kayi kuskuren ɗaukarsa kasha sukar ƙaya, ƙilama kana taɓashi ya iya fashe maka.
Tsabar ya manna musu hauka cayay a kaisu a ajiye, shiko yace a wuce gida dashi yana buƙatar hutawa.1
STORY CONTINUES BELOW

★★★★★
Ana fita dasu Shahudah Mummy ta zube ƙasa ta fashe da kuka tana ƙwala kiran sunan Jawaad.
Salman ne yazo ya ɗagata shi kansa jikinsa sai tsuma yake, gaba ɗaya Jay ya rikiɗe masa a idanu tamkar ba shiba, da ƙyar ya iya taimakawa Mummy ta miƙe suka koma cikin falo.
Shine yay ƙoƙarin kiran Dad ya sanar masa, sannan Qaseem daya fita, dan baya gidan komai ya faru.
Ya kira Mama Atika ya sanar mata itama.
Kafin kace mi komai ya hargitse, magana ta fara fitowa a family house ɗin su Jawaad, dama daga can kuma Maman Zaitun ta kira itama ta sanar da kama Zaitun da akazo akayi ba tare da sunsan mita aikata ba.
Lokacin da motar Jawaad ta shigo gaba ɗaya gidan ya ɗauki zafi.
Yasan abindama yafi hakan zai faru dan haka ya shiryama kowa a gidan akan wannan case ɗin, kallon wani baiyiba a cikinsu ya shige sashensa ya kulle kansa.
Sama ya haye abunsa canma ya kulle har Windows yandama bazaiji kiran waniba a cikinsu, ya kuma kashe duk wayoyinsa suma.
********
Ana cikin haka Mummy da Salman suka iso gidan nasu Jawaad.
Yayinda shi kuma Qaseem ya zarce office a tunaninsa Jawaad yana can dasu Aamilah, sai dai ya iske kosu bama akawo canba, kenan wani waje daban yasa aka kaisu?, kuma an tabbatar masa Jawaad bai dawo office ba tun fitar da yay da yamma.
A fusace ya nufo gidansu Jawaad ɗin, inda ya iske hankulan kowa na gidan a tashe, duk da dai wasu na dariya a ƙasan rai da jinjina abinda Jawaad ɗin ya aikata a bazata.
Duk knocking ƙofar da suke masa baiko motsaba balle suyi tunanin zai buɗe su sami yanda suke buƙata, duk da yana jinsu yay kunnen uwar shegu dasu, wankansa ma yayi, yay shirin kwanciya bayan yayi shafa’i da wutiri, duk da yasan barci da wahala ya ɗaukesa.
Ganin Jawaad yaƙi buɗe ƙofa adaren sukaje suka sanarma kakansa abinda ke faruwa, baiyi mamaki ba, dan dama sune suke ɗaukar Jawaad kamar baisan mi yakeba saboda ya zuma ƴarsu ido tana yanda ta gadama, a gabansu shima ya gwada wayar Jawaad ɗin amma switch up.
Numfashi Baba ya sauke a hankali yana faɗin, “Wayarsa a kashe take, gashi nikuma ba ƙafar kirkiba balle nace zanzo gidan a daren nan, muyi haƙuri zuwa safiya za aimasa magana insha ALLAHU zai fidsosu, wauwtace irinta Jawaad kawai”.
Duk yanda dai suka so ganin su Shahudah basu kwanaba dole suka haƙura tunda babu mafita, aiko ranar anan gidan Mummy ta kwana.
Kamar yanda ya saba yauma sai da ya fita sallar asubahi ya sami salla a cikin jam’i, duk yanda su Uncle Uwaisu sukaso ritsashi basu samu wannan damarba, dan yafisu ƙwarewa a wannan fanin.
Cikin nutsuwarsa yay shirin fita tsaf cikin baƙaƙen Suit da rigarsa ta ciki fara, yayi ƙyau dan dama mai ƙyawunne, tun daga falon sama ya hango Suraj cikin samarin gidan yaron Uncle Uwaisu ne,
Sai da ya haɗa tea ya sakko ƙasa riƙe dashi a hannu yanata turiri, tunda ya fara sakkowa daga steps ɗin benen Suraj ya zuba masa idanu, komai na Jawaad abin so ne, kodan tarin nutsuwar da ALLAH yay masa.
Suraj ya mike domin girmama wa ga Jawaad ɗin, sai da Jay ya zauna a kujera maicin mutum ɗaya yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan shima Suraj ɗin ya zauna.
“Yah Jay barka da safiya”.
Jawaad dake juya cokali cikin kofin tea ɗinsa ya amsa a dakensa, “Barka dai Suraj, lafiya dai ko?”.
Murmushi Suraj yay yana risinar da kai ƙasa, “Lafiya lau Yaya, dama su Abbane sukace na kiraka, wai suna jiranka a sashen Mama”.
Shiru Jay bai amsaba, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan yace, “Tom zanzo”.
Daga haka yay gum da bakinsa.
Mikewa Suraj yay yayi masa sallama ya fita.
Jawaad yaja siririn tsaki yana kai kofin shayinsa a baki, sai da ya kammala shan tea ɗin tas cikin nutsuwa kuma sannan ya miƙe ya fita, dama ko basu kirasa ba yayi niyyar zuwa wajensu.
Kamar yanda ya saba dakewa da shanye ɓacin rai yanzunma hakan yake, ya iso sashen Mama Atika a tsumensa alamun babu wasa ko ɗaukar abinda bai masaba ga kowa.
Gayyar Uncle’s ɗinsa ya iske a falon mama Atika, harma dasu Mummy, murmushi yayi wanda ya bayyana loɓar kumatunsa duka biyu, wato taron dangi aka shirya masa kenan?.
“Duk zan iya daku ai” ya faɗa a fili murya ƙasa-ƙasa yana kaiwa zaune a kujerar da yake ƙyautata zaton dama shi aka barwa.
Wata ƴar ƙaramar dariyar muguntar daya tanadar musu yayi a zuciya.
Suko maɗaukakin mamaki duk ya bayyana a fuskokinsu, musamman yanda sukaga shi tashi fuskar babu alamun damuwa, saima wani kwarjini da cikar haiba shinfiɗe a kanta.
Ya zauna yana ajiye wayoyinsa a ƙaramin tebirin dake gefen kujerar da yake zaune.
“ALLAH dai yasa lafiya? Na ganku haka, Barkanku da safiya?”.
Yay maganar cikin nuna halin ko in kula da kallon ƙurillar da suke binsa dashi su duka.
Sosai tambayar rainin hankalinsa ta bugi ƙirazansu, Uncle Nasir yay masa daƙƙuwa yana faɗin, “Kaci gidanku Jawaad, ya kakema nuna kamar bakasan mika aikataba?”.
Wani murmushi Jawaad ya saki yana harɗe ƙafafu ɗaya bisa ɗaya, da kwantar da bayansa a kujerar, “Uncle minayi nikam?”.
Dukansu baki suka saki suna kallonsa.
A harzuƙe Mummy tace, “Kai mara mutunci, bama kasan mi kayiba? Kaje har gida ka kama matarka ta sunna da ƴan uwanka amma kake mana wannan rainin hankalin naka?”.
Jawaad yay wani luuu da idanu da sauke numfashi, ya taɓe baki kaɗan yana ɗaukar wayarsa ɗaya ya shiga latsawa, “Mummy kenan, na dai kama waɗanda suka bada gudun mawar zubarmin ciki da wadda ta aikata zubarwar, ai matar ƙwarai ta sunna data wadatu da tarbiyya koɗan shegene bata zubar dashi balle ɗan halak na sunna. ku sanarmin kawai yanzu ku miya taraku anan?”.
Mummy data nema zaucewa da kalamun Jawaad zatai magana Uncle Nasir ya katse ta.
“Kai Jawaad ka dawo hankalinka kaji, kasan da suwa kake magana bamason takadaranci, kai yanzu kanaga ya dace ace matar aurenkace ta kwana a rufe? koda abinda kake zargi ya faru ai wannan maganace ta cikin gida, miyasa mu bazakazo ka sanar manaba muyima tufƙar hanci?”.
Shiru kamar Jawaad bazai amsaba, sai kuma ya ajiye wayar da yake dannawar ya maida hankalinsa ga Uncle Nasir yana ƙoƙarin ɗaukar takardar daya ajiye tare da wayoyinsa.
“Uncle wannan ba maganar gida bace, yanzu haka badan yinta yasa nazo nanba, dan Office zanje ana jirana, inhar akan maganar yaran canne kuka taru anan to bazaku ji komai daga gareniba, kudai nema lauya kawai, dan sai an biyani cikina, ita kuma da kuke tunanin zan raga mata saboda igiyar auren da bata amfanamin komaiba tunda aka ƙullata to ga shi nan na tsinkata, kucirema zukatanku mutuncina ne zan taɓa saboda ta kwana hannun jami’an tsaro”.
Babu wanda bai zaro ido waje ba saboda mamakin furucinsa babu ko kunyar ambaton cikinsa da yake.
Jikin Uncle Ayuba har ɓari yake wajen ɗaukar takardar da Jawaad ya ajiye ya duba.
Cikin tsagwaron tsoro da firgici yace, “Wlhy yayi sakin”.
Kusan duk a tare suka ce saki kuma?!!!.
Jawaad ya tattare wayoyinsa zai miƙe yana katse musu tunani da fadin,
“Ku gafarceni zan wuce ana jirana, kuna tunanin zan cigaba da zama da jahilar da sam bata da tarbiyyar addinin islama ne?”.
“Jawaad yaushe ka zama haka?”.
Cewar Uncle Sadiqu baki a hangame.
Babu ko gezau kuwa Jay ya bashi amsa da, “Uncle ai indai nine na wuce hakan, dama can ƙaramin sani kukaimin shiyyasa”.
Hannu mama atika da Inno suka saka aka suka fasa kuka, wai Jawaad na musu rashin kunya, ko ubansa Abdul-aziz bazai musu wannan abunba.
Haƙuri sukaita basu, Jawaad kam yay shiru uffan bai ceba.
Sai da falon ya lafane Uncle Nasir ya kalli Jawaad ɗin ransa a ɓace yace, “Wai shin ko ka fara shaye-shayene bamu saniba? Yanzu kai Jawaad duk yabon hakurinka da ake a gidannan ashe hasashen banza mukeyi?”.
Jawaad dake ta ƙoƙarin danne fushinsa yay guntun murmushi yana shafa fuskarsa, “Uncle duk yanda zan maka bayani bazaka fahimceni ba, bansan wane irin haƙuri kukeso nayi akan jahilci da rashin tarbiyyar hudah ba, ankai maƙurar da bazan iya ɗaga ƙafaba kona yafe gaskiya, karku saka kanku a wannan rigimar domin tsakanin ni da itane kawai a cikinta”.
Da yawansu maganganunsa sun shigesu, dan kuwa dai kowa yasan Shahudah kam bata da tarbiyya.
Gwaggo Nafisa mahaifiyar Zaitun tace, “To anji rigimarka ce tsakaninka da Shahudah, ita kuma Zaitun da su Aamilah miya kawosu ciki?”.
Idonsa ya lumshe nanma yana rumtse hannunsa da ƙarfi, ya buɗesu akanta sun kaɗa sunyi jazur, kamar zaiyi magana sai kuma baice komaiba ya miƙe yana kwasar wayoyinsa, dan idan har ya cigaba da zama tabbas zaiyi abinda ba tarbiyyarsa ba.
Kamar ruwa ya cinyesu haka falon yay tsitt suka bishi da kallo kawai harya fice.
Uwargidan Uncle Nasir ce ta miƙe tana faɗin, “Inhar gaskiya kuke bukata a wannan zancen to yaron nan yafiku gaskiya, mai makon wannan titsiyen da lallaɓashi kukayi yafi, tunda da dai dukanku kunsan gargaɗin da yayma Shahudah tun yunƙurin zubar da cikin nan da tayi na farko, yanzu kuma ta aikata aiko dole ku shirya karɓar abinda yamafi haka daga gareshi”.
Tana gama faɗa tabar musu falon, bata saurari yanda suka kacame da maida mata murtani ba, duk da sunsan gaskiya ta faɗa a maganarta.
Koda Jawaad suka isa Office hidimar gabansa ya cigaba dayi baiko bi takan su Shahudah ba, waɗanda shi kaɗai yasan inda yasa aka kaisu saiko su Hafiz da suka kaisun.
Yayi hakane kuma saboda Qaseem, ilai kuwa ranar Qaseem ɗin yini yay fafutukar bincike nason gano inda Jay yakai su Shahudah ɗin, sai dai ko wata alamar da zai iya samu Jawaad bai bariba.
Daga ƙarshe Office ɗin Jawaad ɗin yaje yana masa magana a gadarance.
Jawaad yay masa banza kamar baisan kurar daya kwaso Qaseem ba, sai da ya gaji da hayaniyarsa ne ya miƙe yana kallonsa a wulaƙance, “Ni bani da lokacin yin magana da kowa akan wannan batun, kuje ku nema lauya zuwa gobe zamu shiga kotu”.
Aiko jin haka Qaseem ya kuma haukacewa da surutai, sai Jawaad ɗinne ya bar masa Office ɗin.
Duk yanda sukaso zama da Jawaad akan a sasanta sam yaƙi basu hadin kai, ranarma bai kwana a gidanba, a gidansa yaje ya kwana, da yake yanzu su Aliyu kowa ya koma gidansa wajen iyalinsa.
Su kansu su Hafiz ɗin yaki sanar musu abinda ke faruwa, duk tambayar da suke masa akan kama su Shahudah sai dai yace suyi hakuri subar maganar.
Daga ƙarshe dole suka ƙyalesa saboda basa bukatar shiga haƙƙinsa.
Dai dai da kakansa yaki yarda su haɗu, hakama su Umma sunbi duk hanyar da zasu gansa akan maganar ya tosheta, yaƙi sauraren kowa, yakumaki faɗama kowa ina su Shahudah suke.
Wannan abu ba ƙaramin tada hankalin Mummy yayiba, ga Abba bai dawoba dukda shima acan hankalin nasa a tashe yake, ya gwada kiran Jawaad ɗin amma saiya iske ya sakashi a black list shima.
Kamar wasa saiga su Shahudah na neman rufa sati guda ba’asan inda sukeba, Jawaad yakumayi finfiris yanata aikin gabansa hankali kwance, dan yama cirema kansa damuwar cikin acewarsa ALLAH yasa haka shine yafi alkairi.1
Lokacin da ake wannan dambarwar kam Bilkisu na makaranta abinta hankali kwance suna shirye-shiryen fara zana jarabawa.
_________________________
BILKEESU
_________________________
Komai na fara zana jarabawarmu ya kammala, dan haka muka ajiye duk wani shiririta muka sake maida hankalinmu a wajen karatu.
Musamman ma ni danafi kowa buƙatar ƙarin haske akan komai, sai dai yanda su Zuhrah ke ƙaramin ƙwarin gwiwa yasa bana tare da wani tsoro ko fargaba, da ai banyi tunanin zuwa wannan matsayinba, ALLAH ya kawoni kuma ai bai kamata na sakama kaina tunanin rashin nasara ba.
A wannan yanayin muka fara zana jarabawar mu………..✍🏻
BAYAN SATI UKU
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃💃🏻👌🏻.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Shafi na ashirin da takwas
MANHA HAUSA NOVEL’S👆🏻
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
✍🏻ALƘALAMI TV👆🏻
Please and Please my dear fans, wannan sune chennals namu a taimaka dan ALLAH aje ai mana subscribing, zasu dinga kawo muku daɗaɗan novels namu babu ko sisinku, ga abubuwan gyaran jiki da ƙaruwa ta fannoni da dama, dan ALLAH a daure a nuna hallaci, hakan zai sake ƙaramin ƙwarin gwiwar baku ƙwai cikin ƙaya a kullum, dan zai tabbatar min kuna biye dani, kuma kuna sona har yanzu, dan ALLAH kar ayi sanya, a danna mana subscribe, idan liks ɗin baya nunawa kuyi Searching ɗinsu ta Accaunt ɗin youtobe zasu nuna muku Please & Please😢🙏🏻🥰🥰💃🏻
2
__________________________
*_BAYAN SATI UKU_*
_BILKEESU_
…………Babu abinda zancema Ubangijina sai godiya, domin kuwa jarabawa na tafiya yanda ya kamata, sai dai ƴan ƙalubale da ba’a rasaba, a yanzu haka abinda ya rage mana bai wuce sati ɗaya ba kacal mu kammala, muɗanyi hutun sati biyu daga nan muyi neco.
Gaba ɗayanmu mun maida hankali, sannan muna taimakon juna, musamman ma ni da suke taimakawa ta kowanne fani.
Yau ma mun fito a gajiye, kowa sai yaƙe yake saboda yunwar dake cin hanjin cikinmu, hostel muka nufa kamar waɗanda aka zanema ƙafafu.
Ummie tace, “Ni yanzuma bama kaje ɗakinba, ka rasa abinda zakaci shine matsalar”.
Rebecca tai dariya da faɗin, “Kina nufin yau ma bazakici abincin da akai ba?”.
“Wlhy bazan ciba, nifa badan kun hananiba da tuni na daɗe da kai report ɗin abinda na gani jiyan nan, ai insha ALLAHU daga jiya harna bar skull ɗinnan bazan sake cin abincin da akai a kitchen ba”.
Dariya duk muka saka mata.
Nace, “Haba ta wajena ki ɗan sassuta, daga jiya kin gani sai kuma akace shikenan kullum za’a cigaba da gani, wannan ɗinma nasan by mistake ya shiga ALLAH”.
Nazifa dake gefena tai saurin faɗin, “Barta Bily, kartaci, wlhy yunwar cikintama ta isheta, ita ɗinnan mayyar son cin doya, duk randa akayi zamuga bazataje ta amso ba da gaske?”.
Ummie ta harari Nazifa tana faɗin, “To ƴar sa ido, duk bin ƙwaƙwƙwafinki ƙyayi ki barni, dan zan tabbatar muku da maganata”.
“ALLAH ya bada iko” cewar Zuhrah.
Duk muka amsa da amin muna dariya, da haka muka ƙarasa hostel.
Sheƙawa da gudu Zuhrah tayi ta fara shiga ɗakinmu tana faɗin, “Nizan fara wanka ehe”.
Ƙarasa shiga muma mukai, Nace, “Kai Zuhraty kin sanfa yanda nake, Please ki barni na fara”.
Shigewarta tai da sauri tana min gwalo, “Ai dama saboda ke ne zanyi fes ɗin, karda ki gogamin nima na ɓule yau”.
“Zaki sani ai, insha ALLAHU gobe sai muna tsaka da jarabawa kiji ya zubo….”
“Wlhy ke muguwace Bily” cewar Rebecca dake cire kayanta, Nazifa da Ummie kuma suka saka dariya.
Haka muke a koda yaushe cikin nishaɗi da kulawa, nakanji tamkar na ɗauki wasu shekaru masu yawa tare dasu ne, dan wanda bai saniba ya gammu zaiyi tunanin tun yarinta muke a haka, ba ƙaramin sakin jiki nayi dasuba suma kuma hakan, idan kaga faɗa a tsakaninmu sai dai rashin fahimta, mukan zauna kuma mu warware da wuri kafin abun yay mana tsamari, Nazifa ma tuni ta fara sakin jiki dani, duk da dai ba kamar su Ummie ba hakan bai dameni ba.
Sai da duk mukai wankan sannan mukaje muka amso abinci, amma banda Ummie datai alƙawarin tabarci har ta wuce.
Irin wannan farin cikin dana samu daga garesune ya sake kawoma rayuwata canji da farin ciki, jikina ya murje tamkar ba’a makaranta nakeba, duk da babu wanda ya taɓa busting ɗina hakan baisa naji ɓacin raiba, amma dai ina kewarsu su duka.
A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gashi mun kammala waec, a ɗan hutun da muka samu kafin fara neco ne ya sakamu sake komawa kan karatun rayuwa.
Dan kuwa ƙawayena sun sake buɗe mun wasu shafukan koyan salo-salo dake maida mace mai aji da tsaftatacciyar wayewa, niko na nutsu wajen bin komai daki-daki ina haddacewa……
STORY CONTINUES BELOW

_________________________
BILKEESU
_________________________
Sai da su Shahudah suka cika sati uku cif sannan Jawaad yay ra’ayinma su kansu su ganshi, dan tunda ya saka aka kaisu aka ɓoye bai sake waiwayensu ba, harkokin gabansu kawai yakeyi.
Yau ɗinma dai tun safe yana office, yayi busy matuƙa saboda ayyukan dake kansa jibge.
Knocking akai dan haka ya bada izinin shigowa.
Bai ɗago ya kalli wanda ya shigo ɗinba, amma ya amsa masa gaisuwar da yake masa ta hanyar ɗaga hannu.
Ya jeho masa tambayar, “Lafiya kuwa?”.
“Lafiya lau Boss baƙine dakai”.
Jawaad dake rubutu ya dakata tare da ɗago manyan idanunsa ya zubasu a kansa, “Baƙi kuma? Maza ko mata?”.
“Boss namiji ɗaya ne dattijo sosai, sai kuma mata biyu da kamar dai budurwa”.
Shiru Jawaad bai amsaba, yadai kafeshi da idanu yana jujjuya pen ɗin hannunsa, yaɗan kaɗa hannunsa yana cigaba da rubutunsa yace, “Shigo dasu”.
Da to ya amsa masa ya juya ya fita.
Jay yaɗan tsaya da rubutu yana tunanin su wanene to? Bakinsa yaɗan motsa kaɗan kawai ya cigaba da abinda yakeyi, sai dai muryar da yaji tayi sallama ne ya sakashi ɗagowa babu shiri.
Kakansa ne da ƙannen mahaifiyarsa, ya ajiye biron da yake rubutun fuskarsa ɗauke da mamaki yace, “Baba kune anan?”.
Baba ya zauna da ƙyar yana ma Jawaad daƙƙuwa, “Kaci mai garin garinku, tunda gudunmu kake aini na biyoka har wajen ɓuyar taka ɗan jakar uba”.
Murmushi kawai Jawaad yayi ya koma ya zauna a kujerarsa yanama su Umman Batool sannu da zuwa, ya maida kallonsa ga Nabeelah datai musu rakkiya, “K miƙoma Umma ƙarama waccan kujerar ta zauna”.
Nabeelah ta amsa masa da to tana nufar kujerar dake gaban Computers ɗin office ɗin ta ɗakkoma Umma ƙarama.
Sanin halinsa da tayi ya sakata fita ta basu waje ita bata zauna ba, da kansa ya miƙe ya buɗe firijin dake office ɗin ya ɗakko musu ruwa da lemo ya ajiye yana sake musu barka da zuwa.
Su dai binsa kawai suke da kallo, dan damuwar da sukayi tunanin yana ciki sam basu ganta a tattare dashiba, sai ma ƙiba ƙamar ya ƙara da ƙyau.
Baba ne ya katse musu tunani da faɗin, “Ja’irin kaya, to yau ta gudu ta ƙare gani ga ka”.
Jawaad dake zama yace, “Haba mai ran ƙarfe ka iya rigima kaima, ni damafa ba gudu nakeba, kawai dai aikine yaymin yawa, iyayena kunajin mai ran ƙarfe fa ya sakani gaba”.
Umma babbace tace, “Ai gaskiya ya faɗa Jawaad, ka aikata laifi kuma ka koma guje-guje”.
“To Umma kema harda k? To duk laifin da ake tunanin nayi amin afuwa Please”.
“Ai ko munso yin fushin da kai bama iyawa Jawaad, amma hukuncin daka yanke akan matarka yayi tsauri da yawa duk da bata ƙyautaba” Umma ƙaramace mai maganar.
Jawaad da yay ƙasa da kai yana murmushi yace, “Baiyi tsauriba Ummana, hakan shine ya dace da Hudah tunda ita bata da hankali, lokuta da dama takan nunamin ita mai taurin kai ce, batasan nawa zafin kan ya zarce nataba, ina ɗaga ƙafane kawai bisa wasu dalilaina, bama ga itaba, su kansu waɗanda suka bata taimakon aikatawar zasuji shakkar aikata kwatan kwacin haka anan gaba”.
Baba yace, “Hakane Jawaad, dama wannan shi nake hango maka tun farko, dan Alhaji Ali yayi matuƙar sakaci da jagorancin tarbiyyar iyalansa, iyaye maza da yawa mukanyi irin wannan sakacin, ba komaine yake kawo hakanba sai ɗaukar kasuwancinmu da girma fiye da tarbiyyar yaranmu, mukan sakarma mata, bayan munsan hannu ɗaya baya ɗaukar jinka, bai zama lallai Uwar ƴaƴanka ta kasance yanda ya kamata uwa ta zamaba, saboda yanzu sam bama duba mai addini mu aura, ƙyale-ƙyalen duniya da adon jikin mace da zuri’ar data fito kawai mukafi kallo, sai kaga idan da raunin tarbiyya akan wannan zuri’ar kaima gidanka zai rayune a raunane, idanma ka samu mai addinin ka aura duk ƙoƙarinta sai kaga nauyin ya mata yawa sosai ta kasa kulawa da yaran yanda ya kamata, musamman ma da yanzu abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa, dole tana buƙatar taimakonka, kama gina yaran bisa ƙyaƙyƙyawan tsari yaka ƙare balle ka rainesu bisa al’adun yahudu da nasara, ilimin boko ba haramun bane, ka saka ɗiyarka mace ko namiji suyi zurfi a cikinsa ba ɓarna bace, matsalar kawai ya kasance babu ilimin addini a cikinsa, to lallai kaima ka tabbatar da ɓarna a gidanka bama sai an faɗa makaba. Irin wannan sakacin shine Alhaji Ali yayi tun farko, mutane nawane ke rayuwa a wajen ƙasar nan kaga yaransu kuma a nutse cikin ƙyaƙyƙyawar tarbiyya, amma shi sai yay kuskuren rashin nuna musu hanyar ALLAH da dokokin saninsa, abinda ya sani kawai ya nema musu suci, ya basu ilimin boko saboda shine mutunci a yanzu. Wannan sam ba haka bane, maiyin wannan tunaninma sam bashi da tunani shi kansa. Nasan an cuta maka ƙwarai da gaske Jawaad, amma haƙuri shine magani, sannan banso kayi gaggawar yin sakinba shi kansa, dan hakan baida amfani sam, daka ƙara haƙuri munbi wasu matakai ko zata gyara”.
Jawaad yace, “Humm, baba ban katseka ba, amma ni nasan irinsu Hudah da wahala su zam cikin Masu gyaran, dan sufa gani suke sunfi kowa sanin abinda ya dace, sunema sukeyin mai ƙyau kowa wawane kidahumi a idanunsu, abinda ya bani matuƙar takaici shine wani kafirin banzane fa ya ɗorata bisa layi bayan ta haƙura zata haifi cikin, wanda ni a ganina maybe bayan hauhuwar tata ta ɗan canja wasu abubuwan, amma yazo ya sake rikita komai”.
Umma tace, “To inma banda jahilci tanada aure miye na wani riƙe ƙaton gardi wai abokinta, ba al’adarku ɗaya ba, ba addininku ɗaya ba, ba jinsinku ɗaya ba, sukuma su Hajiya Humairan suka zuba mata idanu tsabar rashin hankali”.
“Wannan ai shine illar sakacin da baba ya faɗa Yaya, dan inba sakaci ba da girmama al’adun yahudu wlhy hakan sam bazai faruba, yanzu dai komai dai ya rigada ya faru, haƙuri shine yafi cancanta ayi, sai kuma a tari gaba, Yarona ALLAH ya azurtaka da mace ta gari darajar haƙurin da kayi”.
Dukansu da amin suka amsa banda Jawaad da ya amsa nashi a zuciya.
Baba yace, “Yanzu dai Jawaad inason kayi haƙuri ka janye maganar zuwa kotun nan, sannan ka fiddosu daga inda ka ɓoye, nasan kai mai nutsuwane bazaka kaisu station ba dama, akwai dai inda ka kaisu”.
Jawaad ya ɗanyi jimm sai kuma yay guntun murmushi yana haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi, “Shikenan baba zanyi yanda kakeso, dan babu wani sharaɗi da zaku gindayamin na tsallakesa, dama suna gidan Qaseem ne”.
A tare sukace “Gidan Qaseem kuma?”.
Murmushi Jawaad yay yana faɗin, “Eh suna can, nasan halinsa baida hankali, tunaninsa kuma bazai taɓa bashi can na kai suba tunda yasan banma san gidanba, shi kansa bama ko yaushe yake zuwaba, idanma yaje ba ko’ina yake shigaba tunda babu kowa a gidan”.
Dukansu babu wanda mamaki da al’ajab bai fito a fuskarsa ba, yanzu nan duk wannan fafutukar da akeyi akan su Shahudah ashe gidan ɗan uwansu yaje ya ajiyesu, lamarin Jawaad sai shi.
Albarka sosai baba dasu Umma suka saka masa, shiko yana amsawa cikin jin daɗi.
Baba yace, “To maganar dawo da ita ɗakinta fa, shima kayi haƙuri kaji Abdull-Jawaad”.
“Ihm-ihm mai ran ƙarfe karka sake rikitomin sabon aiki, ayi haƙuri nayi kenan, nima inason naɗanyi ƙiba kamar kai ko a fuskane”.
Dariya suka ƙyalƙyale da ita, baba ya kamo hannun Jawaad yana faɗin, “Ja’iri yaji wuju-wuju, bazamu maka tilasba, ƙila nangaba idan ka huce ka maido kayarka koda bamu saniba”.
“Ai bama za’ayi hakanba” cewar Jawaad yana dariya su Umma na tayashi.
Har mota ya rakosu baba nata masa tsiyar wai yanzu sun koma ɗaya duk gwaurayene, wannan azumin zaiba yara su kaɗama Jawaad kiɗan gwauro inhar baiyi sauri yayi aureba..
Shi dai Jawaad nasa murmushi ne, dan yasan dai duk wayo akemasa danya tashi yay aure da wuri, shiko a yanzu dai kam yanda yasha wahala wajen Shahudah tamkar kurar wasa bai yi zaton sake kallon wata ɗiya mace da sunan wani abu so ba balle akai ga aure a yanzun, Kai shi a yanzuma haushi mata yakeji.
1
STORY CONTINUES BELOW

“Munga idi Shahudah ta ja mana tsiya a wajen Jay”.🤣🤣😂⛹♀
4
★★★★★★★
Bayan tafiyarsu Jay Office ya koma ya cigaba da aikin gabansa, dan gaskiya badan su bane bama zai iya sauraren kowa a irin lokacin nanba ma, gashi yanason fita wani waje kuma.
Ya sauke numfashi a hankali yana komawa bayan kujerar ya lafe, idanunsa ya lumshe yana maijin kewar mahaifiyarsa, sosai yake buƙatar ganinta a kusa dashi, badan ya rasa kulawa bane, shi dai yana so yaga ɗa a kusa da uwa, shiyyasa idan Qaseem na wani shirman yakan ga gatane kawai yay masa yawa.
Waya ya ɗauka yay kiran Hafiz akan yazo ya sameshi a office.1
Babu jimawa kuwa saiga Hafiz ya shigo, zama yay bayan sunyi musabaha yana faɗin, “Boss ta samu ne?”.
Jawaad yace, “Kanka aka samu ko?”.
Dariya Hafiz yayi sosai, “Ba komai 1-0 kenan, nima lokacina na zuwa”.
“Zaka daɗe baka isoba kuwa, kasan miya farune?”.
“A’a” cewar Hafiz yana nutsuwa.
Jawaad yay guntun tsaki yana gyara zamansa, inason muje wajen yarannan, shima mai jan kunnen can dake a cell ku fiddoshi harma da likitan, sai dai shi likitan zamu dawo dashi dan wannan asibitin nasa sai mun masa bincike”.
“Ok Boss, yanzu naje mu shirya kenan?”.
“Ai da kai kaɗaima zamuje sai rose, tunda ga Securitys ɗinnan da aka mannamin dole”.
Dariya Hafiz yayi sosai, cikin dariyar yake faɗin, “Ni bansan miyasa bakason Securitys ɗinnanba, wlhy kuma suna ƙara maka ƙyau sosai, dan idan suka dafo maka bayannan dolene maƙiyi yaji tsoro, bakaga kwana biyu Qaseem ma ya shafa maka lafiyaba”.
Baki Jawaad ya ɗan taɓe, “Ai shi wannan bashi da cikakken man kai ne kawai”.
★★★★★★
Jack da Doctor suna nan tare da Jawaad a hukumarsu ashe, su Shahudah ne kawai a gidan Qaseem, kallo ɗaya naima su Jack tausayinsu ya kamani shida Doctor, dan daka gansu kasan ba ƙaramin jigatuwa sukaiba.
An fito dasu daga cikin wani cell aka jefasu a moto.
Dai-dai lokacin da Jawaad ke fitowa daga cikin Office nashi, yau ma dai yana cikin baƙaƙen Suit da suka zauna masa a jiki tamkar danshi akayisu, duk da dai rigar saman riƙe take a hannunsa bai sakaba, yakai hannu yana gyara tie ɗin wuyansa yana taku cikin ƙasaita da jin shifa ya kai, fuskarnan sam babu walwala a cikinta, kallo ɗaya yayma su Jack ya ɗauke idonsa.
Motar da aka buɗe masa ya shiga ya zauna suka fice.
Sun isa gidan Qaseem dake a wata anguwa da ban, gidan yayi ƙyau sosai matar aure kawai yake jira tunda maishi ya tsaya ruwan ido.
Jawaad bai shigaba, baima fita a motaba Hafiz ne kawai ya shiga shi da rose, babu jimawa sai gasu sun fito da su Shahudah.
Ba ƙaramin zare idanuba nayi akansu, Shahudah ƴar gayu ƴar ƙwalisa sati Huɗu babu wanka yay kuke tsammanin ganinta🥴? Ga tashin hankalin basusan inda sukeba, ga abubuwan da Jawaad ya shirya musu a gidan na ban tsoro babu duka babu zagi, kullum basa iya barcin kirki saboda tsoro🤣, ba kowane mai wannan aikinba kuma sai securitys nashi, su ya saka kullum dare suzo suyita abubuwan dake matuƙar firgita su Shahudah, wataran tsabar tashin hankali har fitsari sukeyi a wandunansu, ɓangaren abinci kuwa babu zancen mai daɗi, tsabar yasan Shahudah ma ta tsani tuwon dawa miyar kuka shi yake sakawa kullum batool tayo masa kuma bamai daɗiba a kawo musu, safe da rana da dare, daga ruwan Alwala kuma sai nasha kawai ake ajiye musu, hakan yasa babu damar wanka, to dama a tsare suke, duk bayan wasu awoyi kuma Rose na zuwa ta dubasu.
Tun Shahudah tana yunƙurin amai idan taga tuwon dawa har wahala ta sakata rinkaci tana toshe hanci, to taji zata mace a banza da yunwa, mutuniyarku tayi baƙi sosai kamar wadda ta taso a dokar daji, dama wajen kwanciya tabarma ne kawai aka basu, so babu dai marabar gidanma da prison, ƙilama gara jail ɗin, kowa kuma da ɗakinsa babu mai samun abokin hira ko yaji motsin dazai samu nutsuwa, dama can Rose haushin Shahudah takeji, dan a ganinta saboda Shahudah Jawaad yaƙi sonta😆, shiyyasa tafi takura mata sosai.
Har aka sakasu a mota suma baiko kalli sashen da sukeba, tun daga wajen ya sallami Rose da Hafiz akan su koma Office, shi kuma da securitys ɗinsa da motar dasu Shahudah ke a ciki suka nufi family house ɗinsu.2
STORY CONTINUES BELOW

Da yake yammace sun sami Uncle’s ɗin Jawaad ɗin duk sun dawo gida, shigowar motocin Jawaad ɗin ne ya saka mutanen gidan maida hankalinsu a kansu, ballema ya daɗe baizo gidanba.
Bai fitoba a mota ba har aka kammala fiddo su Shahudah kowanne hannusa da ankwa da yasa aka saka musu saboda son ya sake tada hankalin ƴan gidansu, su ɗauka daga wata uwa duniya aka ɗakko su Shahudah.
Aiko dabararsa yayi tasiri, dan ba ƙaramin tashin hankali kowa ya shigaba da ganin su Aamilah a wannan halin, gashi idanunsu duk a rufe.
Bai shiga sashen kowaba, koda ya fito a harabar gidan ya tsaya aka kawo masa kujera ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya su Jack durƙushe a gabansa sai kace zamanin sayen bayi😂.
Duk wanda ya fito daga sashensa ya gansu haka sai zuciyarsa ta hautsina da tsoro da mamakin tsageranci irin na Jawaad, aiko harda masu koke-koke, shiko ko a kwalar rigarsa.
Mama Atika ta nuna Jawaad tana faɗin, “Kai dai ba yaron arziƙi bane, yanzu akan zubar da ciki kawai ka wajiga rayuwar waɗannan yaran haka?”
Ko kallon inda take baiyiba, ya bama gimba Umarnin ya buɗe musu fuska.
Uncle’s nashi babu wanda ya iya cewa komai saboda tsabar mamakinsa.
Mummy kam zaman dirshan kawai tayi dan tama kasa cewa uffan, ta zubama su Aamilah idanu da Jawaad ɗin tamkar ta samu majigi.2
Jawaad ya katsema kowa tunani, idanusa ya kafe Doctor dasu tamkar zai cinyesa.
Kasa jurewa Doctor yayi yay ƙasa da nasa cike da ƙara jin tsoron Jawaad ɗin har cikin ransa.
Murya a kausashe Jawaad yace, “Likita bokan turai ko? To nikuma Jay bokan likita, miyasa ka zubarmin da ciki?”.
Kai likita ya shiga girgizawa, cikin muryar jigatuwa yace, “Wlhy ban zubar maka da ciki ba, hasalima bansan wanene zaiyi amfani da allurarba, ni dai Zitun ce ta kirani ta haɗani dasu, wannan da waccan sukazo na basu allura suka tafi, amma bansan wa akaimawaba a cikinsu”.
“Uhyihmgg yayi ƙyau” cewar Jawaad yana maida hankalinsa ga Zaitun.
“To ke kuma mai nuna likitan dake zubda ciki fa? Kin taɓa zubarwa ne kema kenan? Shiyyasa har kika sanshi kika kai nawa cikin aka salwantar?”.
“Wlhy yaya, wlhy kaji na rantse ban taɓa aikatawaba, sannan bansan Shahudah ce zata zubar da cikiba, nidai kawai Aamilah ce ta kirani tace na faɗa mata inda zasu sayi maganin zubar da ciki, shine na sanar mata sunan Dr Jeo”.
“Kika sanar mata sunan Dr Jeo, to ke ina kika sanshi idan har baki da alaƙa da yin ɓarnar kema?”.
Hawaye na zirara a kumatun Zaitun tace, “Yah Jawaad ku gafarceni, wlhy sanadin ƙawata na sanshi, dan ita na taɓa rakawa aka zubarma ciki, shinema har na bama Aamilah labari, ni nama manta mun taɓa maganar, ashe ita bata mantaba shine a ranar ta kirani na haɗasu”.
Jawaad yaɗan matse idonsa cikin baƙin ciki, ya maida ga Aamilah, “To ke shugabar tawaga mi cikina ya tsare miki dan uwarki?” Yay maganar da ɗauketa da marin daya gigitata matuƙa ta nema jinta da ganinta ta rasa a lokaci ɗaya.
Babu wanda bai kauda fuskarsaba a wajen, Mummy ta fashe da kuka da tasowa zata riƙe Jawaad securitys nashi suka tareta, dan dama sune suka hana kowa ƙarasowa inda Jawaad din yake balle su Aamilah.
Sai da Aamilah taja kusan mintuna uku kafin hankalinta ya dawo jikinta, sai rawar jiki take tana hawaye.
“Ba magana nake dakeba!!!”.
Jawaad yay maganar cikin matuƙar tsawa.
“Brother zan faɗa maka gaskiya wlhy”.
Jawaad ya watsa mata harara yana huci, yace, “Karma ki faɗa, ki bari nakai ƙarshe wlhy dukan mutuwa zan miki”.
Aamilah na kuka da rawar jiki ta zayyane ma Jawaad duk yanda komai ya faru, kansa kawai ya kwantar a jikin kujerar yay shiru yana kallon Shahudah da tai ƙasa da kai tana hawaye, dan harga ALLAH wani masifar son Jawaad take ƙaraji da cikin data salwantar a yanzu, dan sai yanzu ta fahimci muhimmancin zaman cikin a jikinta.
Duk jikin mutanen gidan ya ƙara sanyi, saboda inhar gaskiya za’a faɗa Jawaad ya fisu gaskiya, dama kuma da yawansu suma sunajin haushin Shahudah saboda lalata musu komai da tayi.
Uffan bai sake cewa da kowansu ba, Shahudah da jack kuwa babu wanda yacema komai sai da ya miƙe, takawa yay a hankali zuwa gaban jack, cikin harshen turanci murya a kausashe yace,
“Na baka nanda awa goma sha biyu kacal, kabar ƙasarnan, inba hakaba, saina kaika inda babu wanda zai sake jin labarinka, kuma daga yau karna sake ganin wannan fuskar taka a ƙasata, idan ra’ayin zama take da kai, sai ta bika ƙasarka can ku ƙarata”.
Yana gama faɗaya ya wuce ta gabansu yana bama securitys ɗinsa umarnin su saki su Aamilah shi kuma Doctor su maida masashi mota.
Yanda bai cema Shahudah komaiba haka bai tankama jama’ar gidansuba kaf ya koma mota suka fice a gida.
Wannan al’amari shine ya kuma jijjiga zukatan ahalin Jawaad, daga kuma wannan rana ya ɗauke kansa daga garesu kaf ɗinsu, yazo duk wani abunsa mai muhimmanci a gidan ya ɗauke ya koma gidansa da zama, yamafi zama a headquarters ɗinsu dan dama can yanada gida a wajen, kawai dai bai cika zaman baneba saboda baya ra’ayi.
Duk kuma wata kaddararsa da takardunsa dake hannun Uncle’s nasa ya basu umarnin maido masa, hatta da gidajen gonar mahaifinsa guda biyu duk ya amshe, hakama gonakin dake ƙauyensu suma dukya amsa sun dawo hanunsa.
Wannan al’amari ya matuƙar tada musu hankaki, harma suka fara tunanin kodai yasan manufarsu dama sharesu yayi?……….✍🏻
To amsa dai naga Jawaad, dan yanzune za’a fara wasan tunda maƙiyan ɓoye zasu fito fili wajen farauta🤸🏻♀, ga Jay namu kuma da alama ya shirya musu, dan haka kumuje zuwa my Sweet fans dan muji yaya wasan zai ƙare💃🏻🤫
1
ZAFAFA SABON KAFCE
Sun fara sauka, masoyanmu ku garzaya kar ayi babu ku, guda biyar fa ɗari biyarne (500) tsabar rahusa, duk mai buƙata ya nema wannan number👇🏼
09032345899
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
Masu tambayar ɗayan novel ɗina kuma yana cikin ZAFAFA BIYAR na kuɗi da mukeyi, duk mai bukata ga Number can nasa a sama ita zai yima magana domin neman ƙarin bayani, ngd da Comments naku, suna sakani nishaɗi matuka.🥰🥰
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻6Shabi na ashirin da tara
…………Ɓangaren su Shahudah ma komai ya caɓe, gashi ma tunda suka fito bata da wani isashshen lafiya, su Mummy kuma sun kasa sanar mata maganar sakin da Jay yay mata.
Jack kuwa washe gari jirgin farko dashi ya tashi.
Abu ya tsayama Dad sosai a zuciya, idan ya zauna yakan tafi dogon tunani game da kalaman Jawaad da yace jahilci na rashin ilimin addini ke ɗawainiya da Shahudah.
Maganar nan na matuƙar sukarshi, dan ya tabbata gaskiya Jawaad ya faɗa, sam a tarbiyyar yaransu babu ilimin addini a cikinta, rabon da yaransa suje islamiyya tun suna ƙananu, irin rayuwar da suka buɗa ido da ita kuma saita goge musu komai, musamman ma daba maida hankali akai ba sanda sunada ƙarancin shekarun, amma yanda yaro bai cika manta abuba dasun tsura da wani abu, koda yake masu iya magana kance duk abinda ba’a tuni a cikinsa yakan lalace ko a canja masa manufa ma baki ɗaya.
Maimakon ya ɗauki mataki akai ko ya zaunar da Shahudah harma da Aamilah yay musu faɗa, ya kuma gyara kuskuren da yay tun farko na sakaci da gidansa, sai ya yanke shawarar tura Shahudah wata ƙasa wai ta huta ko hankalinta ya kwanta.
Koda ya samu Mummy da shawarar tura Shahudah sai ta nuna masa hakan shine dai-dai,
“Wannan shawaran tayi Dadynsu, ni kaina fargabar tunkarar Mamana nake da batun sakin nan da yaron nan yayi, amma idan ta tafi ta huta hankalinta ya dawo jikinta koda tasan babu auren bazata saka kanta a damuwaba, duk da dai munama fatan kafin lokacin ya sakko ya maida auren nasu, kokuma kawai ta koma makaranta acan ɗinma”.
Numfashi mai nauyi Dad ya sauke, yay ɗan gyaran murya kaɗan yana faɗin, “Shikenan to, amma k kina ganin yaron nan zai sakko kuwa? Kigafa abinda ya aikata, yama yanke kowacce alaƙa daku ɗin kanku”.
“Humm ai saima kaga yanda ya rufe ido wlhy, ai ban taɓa sanin Jawaad haka yakeba, dukkan halin mahaifinsa shine tattare dashi, kaita musu abu suyi kamar basu damuba, rana ɗaya saisu birkice maka”.
Murmushi Dady yayi kawai bai iya cewa komaiba. 2
Kwana biyu dayin wannan maganar Daddy ya samu Shahudah da kansa yay mata bayanin shawarar da suka yanke, amma sun nuna mata zata tafine ta huta har lokacin da Jawaad zai sakko daga fushin zubar masa da ciki da tayi.
Shahudah batayi musuba, dan a ganinta hakan shine mafita a gareta, a yanzu komi zatayi Jawaad bazai saurareta ba, to garama taje ko makarantar ta koma ma ta ƙara karatun zaifi.
Qaseem shine yay tama Shahudah kiciniyar tafiyar har komai ya kammala, ranar da zata wuce tata kiran Number Jawaad amma bai ɗagaba, ta tura masa text message na ban haƙuri shima babu reply, ranta dai duk a jagule ta wuce, taso su haɗu da Jawaad ɗin Qaseem ya balbaleta da masifa, dole ta haƙura tadai rubuta saƙo ta barma Aamilah akan koda nan gabane ta bama Jawaad ɗin.
Ita dai Aamilah ta amsane kawai, amma bata da tabbacin iya badawar, dan ko’a mafarki yanzu bata fatan sake haɗuwa da Jawaad, itama karatun zata samu ta koma tama bar ƙasar yafi mata kwanciyar hankali.
_________________________________
Duk da Jawaad yaga kiran Shahudah da saƙonta bai kulaba, kuma sarai yasan da shirin barin ƙasar da take, amma sai yay tamkarma baisan anaiba, abinda ke gabansa kawai yakeyi.
*_BAYAN WATANNI BIYU😹🥴_*
Zuwa yanzu komai ya lafa tsakaninsu Jawaad, duk da dai ta ciki na ciki akeyi, bai sake bi takan labarin Shahudah ba balle bibiyar inda take kokuma mi takeyi?.
Sai dai akan barin gida da share kowa a danginsa baba ya gyara wannan alaƙar, dan dakansa yaje gidan yakuma saka Jawaad zuwa dan dole.
Dukansu ya haɗasu yay musu nasiha akan zuminci da muhimmancinsa, tare da nuna musu illar wanda yazama silar rarrabewarsa. Dukansu jikinsu yayi sanyi har Jawaad ɗin, domin kuwa shima yasan hakan, tunda yanada ilimin addini sosai, har a yanzu ma bawai ya bar nema bane, take sani kawai yayi da kuma tauna aya dan tsakkuwa taji tsoro.
Da kansa ya nema gafarar Uncle’s nashi ya kuma basu haƙuri.
Suma suka bashi haƙuri akan kuskuren da yake gani sun masa. Yace shi basu mashi komaiba, dama dai akan maganar cikin Shahudah ne da duk suka kasa fahimtar an cuta masa suka goyi bayanta.
Sunta baza ido da kunne suji kozai maido musu dukiyarsa daya amsa da kuma maida aurensa da Shahudah sai dai baice komaiba, da Uncle Nasir ma ya takalo masa maganar aure akan bai ƙyautu da mutuncinsa ya zauna babu mataba, cayay suyi masa afuwa akan wannan maganar, maybe zuwa nan gaba kaɗan yayi.
Sunso masa tayin ƴaƴansu sai dai bai bada fuskar hakanba, shiyyasa suka ɗaga masa ƙafa akan sai zuwa gaba.
Shi baima san sunaiba, kwana huɗu da yin wannan zaman Baba ya takura masa sai da ya dawo gidan da zama, randa ya samu dama yakanzo nan ya kwana, wataran kuma acan Barrack nasu yake kwana abinsa, kokuma gidansa, ya dai raba hankalinsa uku babu gaira babu sabar.
Sai dai shima hakan yanacin ransa, yasan da mahaifiyarsa na tare dashi wannan rashin tsayayyyen muhallin da bai samesa ba, dan duk inda take shima anan zai kasance dole.
Ga dai Jawaad ya dawo gidansu da zama, amma zaman sai ya banbanta dana fil azal da yayi, ya ɗaukarma kansa duk safiyar daya kwana a gidan zai shiga ya gaida tsoffin gidan biyu da suka rage, wato su mama Atika, idan yaga yanada isashshen time zai shiga duka sashen Uncles nasa suma, idan bai da kuma shikenan.
A ɓangarensu kuma suma duk sun saka yaransu mata farauto zuciyar Jawaad, kowa burinsa ƴarsa ta samu karɓuwa ga Jay a aura masa.
Sai dai kuma an samu matsala, shi Jawaad ma yaran gidan basu ishesa koda kalloba, yanzu hakama bazai iya kawo sunan wasuba kansa tsaye, yawancin sanda suka taso shi kuma baya gidan yana harkokin karatunsa da wasu abubuwan, amma duk waɗanda ya tashi dasu daga ƙuruciya duk ya sansu yasan sunayensu, to duk sunyi aurema matan, hakama mazan, da yawansu kuma yana gaisuwa dasu ta waya time to time idan sun kirashi.
STORY CONTINUES BELOW

_________________________
BILKEESU
_________________________
A yau muka tashi da farin cikin da baki kaɗai bazai iya furtawaba, dan kuwa mun zana jarabawa ta ƙarshe zamu koma gidajen iyayenmu, gashi dai yau ranar farin cikice ga kowacce ɗaliba, amma mu saita zamar mana ranar kuka nida ƙawayena su Ummie.
Mun haɗa kai a waje guda munata rairawa abin tausayi, Dadyn Ummie na daga gefenmu yana lallashi, duk sun bani adireshinsu, nima na basu nawa, su dama duk sun san gidajen juna iyayensuma nata zuminci.
Kowacce anzo ɗaukarta daga gidansu, niko Dad ya cema Dadyn Ummie ya kaini, bayan duk tafiyar sauran muka rage ni da Ummie kawai, sai da Dady ya gama kimtsawa muma ya ɗaukemu muka tafi, lallai zanyi kewar makarantar nan, har mukai nesa da ita ban daina kallonta ina hawaye.
Sun kaini har cikin gidanmu, wato gidan Dad, dan a yanzu shine kawai zan bigi ƙirji wajen kiransa gidanmu, tunda ƙaddara ta mallakaminshi matsayin gidan.
Amina ta fito a guje ta ƙadandaneni tana ihun murna, shima kuku sai washe haƙwara yake shi da baba mai gadi damai kula da flowers ɗin gidan, Su Dady basu shigaba suka juya akan nanda kwana biyu zai kawo mani Ummie.
Sai da naji ƙwalla ta cikan idanu, har suka fice ina ɗaga mata hannu itama tana ɗagomin, su Amina suka kwashi kayana zuwa ciki.
Duk da babu wanda ya fito domin tarbata a cikinsu ni ɗokin ganinsu nakeyi, sai dai kuma falon tsit babu motsin kowa, to yanzu dai kunsan wannan ba Bilkisun da bace da suke ɗauka bagidajiya, nima na sake ilimin rayuwa dana zamantakewa, cikin tsantsar son ganinsu na fara kwala kiran sunansu ɗaya bayan, Aunty Aamilah ce ta fara fitowa tana faɗan wake ƙwala mata kira haka? Cikin yatsine fuska.
Bamma sauraretaba na rungumeta, taso tureni a jikinta, amma sassanyan ƙamshin data shaƙo daga gareni ya sakata fasawa, nace, “Aunty Aamilah i miss you so much, irin mai zafin nan, mai hana barcin nan”.
Babu shiri tai dariya tana ƙaremin kallo sama da ƙasa, “Gaki dai kin canja kamar ba keba, sai dai shirman na nan kaɗan, ashe dama ƙazantace ta ƙara miki muni da rashin ilimi ga ƙauyanci, duk da kina nan a baƙarki ai yanzuko baƙin ya zama mai ƙyau a idon mai kallonki”.
Dariya nai mata kawai, duk da dai akwai cin fuska a zancenta sai ban ɓata rainaba, na haye sama ina dariya da ƙwala kiran sunan Mummy da Dad.
A falo naci karo da Mummy zata sakko, nako ɗareta itama ina jera mata kalaman kewa.
Dariya Dad ya shigayi shima dake bayanta yana kallonmu cike da birgewa.
Ni nasan ganin Dad ya saka Mummy amsata hannu biyu, wai har itama na faɗin tayi kewata.
Na saketa na nufi Dad, ya buɗe min hannayensa alamun nazo na shige jikinsa shima, amma sam bazan iya hakanba, sainai murmushi cikin nuna jin kunya da girmamawa a gareshi na durƙusa har ƙasa ina gaishesa.
Hakan ba ƙaramin daɗi yay masaba, dan tun a zuwana gidan idan na durƙusa gaidashi sai yakanji al’amarin da girma, dan bai saba ganiba ga yaransa.
“A tashi haka nan Yarinyar Dad, ALLAH yay miki albarka kinji, barka da arziƙi kwalin secondary ya samu, ALLAH ya kaimu randa zamuga na University haka”.
Cikin girmamawa nace, “Amin Dad, nagode sosai”.
Ban tambayi Aunty Shahudah ba, dan na zata dai ta koma gidan aurenta, Yaya Salman ko da Qaseem nasan basu dawo aikiba.
Ɗakina na nufa inda na iske Amina ta gyara minshi tsaf, sannan kuma an canjamin wasu kayayyakin cikima, ga sayayyar abubuwa dana tarar kala-kala, wanda nasan duk Dad ne, dan duk abinda ya sayama yaransa yanzu na lura bai iya mantawa dani a ciki.
Nayi wanka nai salla, Amina ta kawomin abinci, zama tai inaci muna hira tana bani labari muna dariya cikin farin ciki, mun daɗe da ita sosai a ɗakin kafin ta fita, ni kuma na kwanta danna huta kamar yanda Dad ya maido Amina ta sanar min.
Umarninsa kuwa nabi bayan nai salla na kwanta, kafin wani dogon lokaci barci yay gaba dani.
★★★★★
Wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar liyafar cin abinci Dad yasa aka shirya a gidan saboda ni, tunda na fito daga ɗakina idanun Yah Qaseem da Yah Salman na kaina, sket da rigane ƴan kanti a jikina, sket din jaa har ƙasa an masa ado da farin filawoyi, ya buɗe sosai hakan yasa sam baya nuna jikina, sai rigar fara itama mai ƙyau, ta zaunamin ɗas a jiki tamkar anyitane danni, na kawo ƙaramin hijjab na saka wanda ya rufemin ƙirjina, ga wani sassanyan ƙamshi ina fitarwa, tafiyata, maganata da komaina ni kaina nasan ya canja, dan karatun su Ummie bai tafi a banza ba.
Fiskata ɗauke da murmushi na gaida yayun nawa biyu waɗanda sai yanzune muka haɗu tun shigowata gidan, nasha mamakin yanda suka karɓamin babu hantara, saima kallon mamaki da ƙurulla da suketa bina da shi ko kunyar iyayensu dake wajen basaji.
Dad ne ya katse su dayin gyaran murya, duk suka kallesa, shiko yay ƙaramar dariya yana faɗin, “Oh kowa yaga ɗiyata ta canja shine ake kallemin ita kamar ido zai faɗo, to ƙwalelen kowa ɗiyata karatu zatayi ko?”..
Yay maganar yana maido dubansa kaina.
Murmushi nayi daya bayyana jerarrun haƙorana farare tas, wanda ko acan baya da ake jifana da kalmar mummuna akan yaba ƙyawunsu sukam, nace, “Insha ALLAHU Dad”.
Baki Salman ya taɓe da faɗin, “Oh su o e dai an fara wayewa, kin canjafa sosai”.
Kallonsa nai ina kuma ƙayata fuskata da murmushi, nace, “To banda abunka Yah Salman ai kamar yanda ake samun cigaba a kwanaki, haka ake samu a rayuwa, kai dama tunaninka zanta zamane yanda nake?”.
Dukansu babu wanda baimin kallon mamaki ba.
Aamilah tace, “Tofa, wannan nan gaba ba ƙaramar ƴar iyayi za’aiba anan, da kinfi haka ƙyau da munsha kallo kam”.
Itama dariya nai mata ina wani juya idanu, “Banda abinki Aunty Aamilah ai ba ƙyawun fuska bane abin buƙata, ƙyawun zuciya shine cikakken ƙyawun da baya dishewa har ƙarshen numfashi, gwargwadon wannan ƙyawun da ALLAH ya bani ji nake da abuna, so abin ba’a ƙyawun fuska bane auntyna”.
Dariya Dad yayi yana cewa, “Yauwa ɗiyata, ai gara ki ringa ramawa kema”.
Nai siririyar dariya nima da nasan ta sake ƙular dasu, dan Mummy sai antayamin harara take, niko nai mirsisi banbi takan ɗunbin mamakina da al’ajab dake shinfiɗe a fuskarsu ba.
Daga nan ban sake magana ba har muka kammala cin abincin, falo muka koma, duk da ba kowacce hira nake saka musu bakiba idan an sakkoni nakan tanka, dama Dad ne ke yawan sakko sunana a cikin firar, niko ban bashi kunyaba nake amsa masa, banayin shirun nan irin na da.
Duk ɗinsu nasan yau da mamakina zasu kwana, dan kuwa nazo musu da sabon salon da basusan ni da shiba a baya🥴😉.1
STORY CONTINUES BELOW

Washe garima komaina kai tsaye nakeyi a gidan babu wani ɗar-ɗar na tsoron kowa kamar yanda nakeyi a da, ina kicin muna hira dasu Amina ina kallon yanda kuku ke girki dan nasa aniyar miƙewa na koya abubuwa aɗan zaman da zanyi kafin fitowar jarabarmu.
Zaune nake akan drawern kicin ɗin, hannuna riƙe da kofin shayi yanata turiri, ina sanye da kayan barci wando da riga kalar ruwan hoda masu haske, sai guntun hijjab a jikina.
Yah Qaseem ne ya shigo cikin shirin fita, dan kuwa sanye yake cikin Suit da suka ƙara fidda ƙyawunsa, dan shima dai ba daga bayaba wajen ƙyawu.
A kaina ya fara sauke idanunsa, babu zato nawa suka shige cikin nasa, janyewa nai cike da basarwa kamar bangansa ba.
Zama yay a ɗaya daga kujeru huɗun da aka ajiye a kicin ɗin da tebir tsakkiyarsu, zam Dani dai, yayma kuku Umarnin ya bashi abinci mai sauƙi.
Nace, “Yah Qaseem barka da safiya”.
Juyowa yay ya kalleni sosai fuskarsa na sake bayyana tsagwaron mamakina, niko na janye idanuna ina cigaba da shan shayina kamar banice nai maganarba.
Ganin yanda naine ya sashi sauke numfashi kaɗan yacemin, “Barkanki”.
Ban tankaba, bankuma sake kallonsa ba, har kuma ya kammala abinda yake ban gama shan nawa tea ɗinba tsabar shiririta, koda zai fice sai da ya sake kallona ina ganinsa.
Amina dake ƙumshe dariya tace, “Ƙawata, kinfa zoma jama’ar gidan nan da sabon salo alƙur’an”.
Murmushi nai mata ina taɓe baki kaɗan, “Nikam minayi Amina? Kune dai kuke ganin nazo da sabon salon kawai, amma ina nan a Bilkisu na”.
“Tab, inji wa? Wlhy kin canja sosai, kamarfa ba makaranta kikajeba yasin”.
Murmushi kawai nai musu ban sake cewa komaiba.
A ranar dai nasha labari wajen Amina, har rikicin da akasha tsakanin Aunty Shahudah da mijinta, da kuma barin ƙasar da tayi, nasha mamaki, naga kuma wautar su Dad a nan gaskiya, dan ni dai a ganina kamata yay su ɗauki hanyar gyara ɗabi’un yaransu musamman ma Shahudah da nake ganin tafi kowa nuna tsagwaron wayewar, amma gashi son zuciya ya sakasu sake dulmiyar da ita kuma,
“ALLAH ya ƙyauta” kawai na iya faɗa naja bakina na tsuke.
Da yamma Dad yace na shirya muje shopping, ban musaba kuwa nai shirina, ni da shi da Aamilah muka tafi.
Koda muka isa sai ta katsatstsare itace zata zaɓamin komai, da farko na bata dama, amma danaga duk abinda ta ɗauka baiyi dai-dai da tsatinaba saina dakatar da ita ina zaɓa, dan ko kayan kwalliya saita dinga ɗaukar mayukan da zasu sakani fari, niko batasan ba farin nake buƙataba, wannan baƙin da basaso ni shine abin sona, fatar dai ta goge tayi laushi kawai ya wadatar, banyi zariba na ɗiba komai dai-dai misali, ko kayama da yace na ɗauka nace masa atanfa nakeso to, dan naga duk kayana na gida yanzu babu suturun malam bahaushe, niko ina zan iya rayuwa babu kayan gado.
Bai hananiba yace na ɗauka, suma na ɗauki dai-dai musali mukaje Aamilah ta biya bayan ya ɗaukar mini waya shima muka fito.
Naji daɗin wayarnan sosai, dan na tsinci kaina amatuƙar farin ciki bana wasaba.
Na kumayitama Dad godiya da nuna masa farin cikina akan ɗauwainiyar da yakeyi dani, aduk sanda nake masa godiya idan ya saya min abu hakan na sakashi jin wani iri daban, yakanji daɗi kuma sosai a ransa, dan baisaba ganiba daga ƴaƴansa, basusan yay musu abuba suce sun gode, basu da laifi, dan tun farko ba’a nuna musu su godema wanda ya ƙyautata musuba koda a ƙanƙanin abune.
Kwanana huɗu da dawo gidan nacema Dad zanje gidan Inna Zainaba, baiko hanaba yace mu shirya ni da Aamilah driver ya kaimu.
Aiko wannan abu ya mata ciwo, dan masifa taitamin da muka tafi, saima tace mu sauketa a wani anguwa idan mun dawo mu biyo mu ɗauketa dan batai niyyar zuwa ko inaba, bazata wannan ƙazamar anguwar tasu Yaya Shu’aibu ba ta dawo ta kasa shan ko ruwa.
Tausayima ta bani nikam, dan kuwa arziƙin da take tunƙaho dashi wanda ya bata bai manta dasu talakawanba da take kallo ba komaiba.
Mun isa har ƙofar gidan, na shiga ciki da ɗokina ina kiran Inna.
A tsakar gida na isketa tana ɓarar gyaɗa, tunda na shigo ta ɗora idonta a kaina sai fuskarta ta canja, dan kuwa na kula bataso ganina hakaba fes, ban damuba naje na rungumeta ina hawayen farin cikin ganinta, Lawisa dake ɗaki ta bankaɗa labule ta fito, daka ganta kasan barci takeyi, “Waye haka yake mana ihu a cikin gid….”
Bata iya ƙarasawaba saboda tozali datai dani, ta wani taɓe baki tana jan tsaki ta koma cikin ɗakin.
Murmushi nayi ina muƙewa daga jikin inna, na durƙusa har ƙasa na gaisheta, sannan naja kujera na zauna ina tayata ɓarar gyaɗar.
Duk da bata sakarmin fuskaba mun ɗanyi hira, ananma ne nakejin ashe Yah Shu’aibu ya wuce ƙasar ghana karatu, na tayasa murna sosai, duk da naso muhaɗu shima yaga cigaban dana samu, amma dai inna ta bani Number sa dan Dad ya saya mata waya saboda suna waya da Yah Shu’aibun.
Banbi takan Lawisa ba har na baro gidan, bakuma ta sake fitowaba itama har na taho.
Biyawa mukai muka ɗauki Aamilah muka wuce gida, bankuma faɗama kowa ba tare mukaje ba.
Amina na tambaya ko akwai islamiyya a anguwar? Tako tabbatarmin akwaita, bazan iya zama hakaba, nako samu Dad da maganar inason shiga islamiyya tunda ta yamma sukeyi, shima bai hananiba, yace tom na binciko yaya abun yake?.
Tare da Amina mukaje, ta haɗani da yayanta da shima anan yake koyarwa, komai yay mana bayani na tsarin islamiyyar, nima nazo na sanarma Dad.
Sai cewa yay to itama Aamilah taje mu shiga tare mana da zaman banzan da takeyi.
Ai tunma Dad bai kai ƙarshen zancenba tai tsalle ta dire akan bataso, ita da zata bar ƙasar ta koma karatu miye na wahal da kanta shiga cikin kucakan yaran nan wai wani karatu kuma, ai dai ta iya na salla (Ita a nata tunaninma na salar kawai ake buƙata ta iya🤦🏻♀, ALLAH ka ganar damu gaskiya😢🙏🏻).
Nayi zaton Dad da Mummy zasu mata faɗa, a kuma tursasata dole ta shiga, amma sai naji babu wandama yace mata uffan, sai ƴar dariya kawai da Mummy tayi.
Nima ban tankaba, naje nai duk abinda ya dace na fara zuwa abuna ba tare dana sake bi takan Aamilah ba.
Da safe zuwa rana nakan nutsu wajen koyan girki a wajen kuku, da yamma na wuce makaranta.
Satina kusan biyu da dawo gidan saiga Nazifa, Ummie, Zuhrah, Rebecca sun kawomin ziyara, nayi matuƙar murnar wannan ziyara, dan kuwa kowama agidan ya fahimci hakan.
Ranar mun yini muna shaftarmu, sai dare suka wuce, ko islamiyya tare dasu mukajeta.
Tun daga sannan muka koma ziyarar juna akai-akai, nima Dad yasa duk aka kaini gidajensu, zuminci mai ƙarfi ya sake ƙulluwa tsakanina dasu da ahalinsu, harma yayan Zuhrah ya maƙalemin wai sona yake, ranar harda kuka nayi, dan nikam ba’a taɓa cewa ana sonaba sai ranar.
Ban dai bashi fuskaba, amma muna gaisawa ta waya lokaci-lokaci.
1
★★★★★★
Ba a wani ja dogon lokaci ba jarabawarmu ta fito, dukanmu mun sami sakamako mai ƙyau, ranar dai murna ai ba’a magana, dan kowa na gidan sai da ya fahimci ina tare da farin ciki kuwa.
Babu wani ɓata lokaci Dad ya fara nema min skull, da yake bakinmu ɗaya da su Zuhrah, yana tambayata zaɓin makarantar da nakeso na sanar masa wadda muka shirya.
To ashema Daddyn Ummie ne zai nema mana skull ɗin.
A gurguje Please😹🥴⛹♀
Makaranta dai ta samu, inda cikin amincin UBANGIJI duk muka dace da cikar burinmu, dan kuwa mun sake tsintar kammu a muhalli ɗaya ni, Zuhrah, Ummie, Nazifa, Rebecca.
Komai dai an gama mana tsaf, hakama shirin tafiya nima an mani na ƴan gata, na bar gida cike da kewarsu musamman Dad da Amina dasu kuku.
Ƙaramin gida aka kama mana kusa da makarantar mu duka biyar ɗin, ɗaki biyune sai falo sai kicin kawai a gidan, duk kuma abinda zamu iya buƙata su Dad sun haɗa hannu wajen saka mana, an kuma haɗamu zama da wata dattijuwa yayar Dadyn Ummie, itace zata zauna damu saboda kula da duk wani motsinmu, kusan yaran yanzu sai ana saka mana idanu, duk ƙoƙarin tsare mutuncinka idan babu mai ƙwaɓa maka a kusa tuni kake kaucewa ko wata ƙawa ko sauriyi su sakaka a hanyar banza, hakanne yasa aka ajiye mana Gwaggo Hari danta zauna damu.
Ni da Ummie ne muka fara isa, sai ga Zuhrah, bayan magriba kuma sai ga su Rebecca, Zuhrah kam sai washe gari ta iso.
Yau kuma ga inda ƙaddara ta kawo bilynku, sai ku tayamu da addu’ar tsare mutunci da maida hankali akan abinda ya jehomu nanɗin😊………..✍🏻
Barkanku da juma’a, a sakani a addu’ar wannan rana mai albarka Please😑😥Shafi na talatin
………….Salon rayuwa ya kuma canjawa, ga Bilkisu a matakin da zuciya bata taɓa hasasowa ba, balle sakashi a jerin burin mallaka, mun tsunduma a cikin karatu gadan-gadan babu kama hannun yaro. Sannan kamewar kai babu kula samari ko ƙawayen banza kamar yanda mukaima kammu alƙawari, inhar jerin ɗalibai masu ƙwazone, dolene ka samu sunan group ɗinmu a sahun farko, cikin lokaci ƙanƙani sunanmu yay kuwwar fita sararin subahana a makarantar.
Bawai a rashin kunyaba, ko nuna rashin tarbiyya, a’a tamu zarran mu a karatu take da kamun kai.
Ɓangaren samari akwai masu bibiyarmu akoda yaushe, sai dai sam basa samun fuska daga garemu, burinmu kawai cika alƙawarin da muka ɗaukama kawunanmu inhar muna cikin masu tsawon rai.
A haka kwanaki sukaita ja babu ko gargada a ciki, wataran a mori yini da kwana da farin ciki, wataran a riskeshi da saɓanin haka.
Kafin wani dogon nazari watanni biyar suka shuɗe mana, mukazo gida hutun sati buyu.
Bazance hutun baimun daɗi ba, sai dai babu wani farin ciki daya bani, dan na iske Mummy tayi tafiya itada Aamilah zuwa wajen aunty Shahudah, hakama Dad baya ƙasar, sai Salman da Qaseem kawai.
Tun saukata gidan na fahimci bazai zaunu a gareniba, dan kuwa ni kaɗaice mace a cikinsa, Amina ma bata zuwa kamar yanda Mummy ta bata umarni, wannan damar data samu ne ya sakata nufar ƙauyen babanta taɗan huta itama.
Ƙananun ƴan akuyancin da Salman ya fara nuna mini ne ya sakani tattara inawa-inawa tunkan abun yay nisa na fece gidan Inna zainabu kamar yanda na nema izini wajen Dad, nakuma taki sa’a babu musu ya bani dama ba tare daya bincikeni dalilina ba.
Ban wani samu gamsashahiyar tarbaba daga wajen Inna, sai dai hakan bai dameniba, dan hakan ya fimin zama cikin ƙattai.
Lawisa kam yanda ta shareni nima hakan na shareta, tadai san bata isa sakani wani aikiba a yanzu, dan wannan ba Bilkisun da bace data raina.
Nai amfani da damata kuwa, wajen ziyartar gidajen dangin mahaifina harma da sauran na mahaifiyata, duk da kuwa a baya sun nuna basa buƙatata.
Wasu a cikinsu sunji kunya sosai ganina a ƙyaƙyƙyawan yanayi, saɓanin abinda sukai mini fata, ni dai ban maida kaiba, koba komai dai na samu ladan zuminci, kuma duk duniya bani da kamarsu.
A haka na cinye nawa hutun, Dad ya turo mini kuɗin sayayyar komawata ta hannun Qaseem.
Dan haka dole na shirya na koma gida ana saura kwana biyu komawarmu, naji daɗin rashin iske Salman, sai dai shima Yaa Qaseem ɗin yawan kallo da yake bina dashi ya fara takurani, abin mamaki da zanje sayayyama shine ya kaini, sai kuma wani takalata yake da hira, ni abunma sai ya ɗaure kaina matuƙa.
Ban dai nuna masa komaiba ko a fuska, na samu muka kammala ya maidoni, tunda na samu na sheƙa ɗakina saina kulle kaina bai sake ganinaba ban sake ganinsa ba.
Sai dai bayan isha’i naji ana ƙwanƙwasa min ƙofa, koda na buɗe sai na ganshi, mamaki ya kamani, amma kafin nace wani abu sai cewa yay nazo na dafa masa shayi.
Ban masa musuba nabi umarninsa, duk da a zuciyata ƙunƙuni naketayi akan hakan, ga kuku amma ni zaizo ya saka aiki.
Abin al’ajab sai ya biyoni kitchen ɗin, yaja kujera ya zauna, ni dai inata neman tsarin ALLAH daga sharrinsa inma dashi yazo, ina gamawa kuma zan wuce ya tsaidani.
“Zauna mana, kina ganin gidan shiru babu wani abokin hira shine zaki barni ni kaɗai”.
Idanu kawai na ɗaga na kallesa, ganin ya kafeni da nasa idanun sai na sauke numfashi kaɗan, nace, “Yah Qaseem kasan ina shirine fa, gashi sammako zanyi idan ALLAH ya kaimu”.
Kamar bazai tanka minba sai kuma ya sake kallona, baice komaiba ya miƙe yana faɗin, “Muje to kina shirya kayan kina tayani hira”.
Tamkar zan fasa ihu haka naji, haka ya tasani gaba har ɗakina, ya zauna a kujerar gaban mirror ni kuma ina daga wajen gado saman kafet ɗin wajen ina kimtsa kaya, gaba ɗaya jina nake a takure, gashi ba wani hirar mukeba, ya zubamin idone kawai yana shan shayi, niko ina aiki.
Sauri-sauri na kammala nai gefe dasu, cikin kwantar da murya yanda zaiji tausayina nace masa barci nakeji.
Murmushi kawai yayi, ya miƙe ba tare da yace min uffanba ya fita.
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi a fili ina faɗin, “Wannan takura har i…n…a…”
Na ƙare maganar da ɗai-ɗai saboda tozali danai dashi ya dawo baya, munafukin ashe ba tafiya yayba.
Kaina na sunkuyar ƙasa jikina na tsuma saboda tsoro.
Sai da ya gama ƙaremin kallo sama da ƙasa sannan ya juya ya fice abunsa.
Ai yanzu ko motsi banyiba sai da naja lokaci mai tsaho sannan, cikin sanɗa naje na rufe ƙofar tare da murza key.+
STORY CONTINUES BELOW

Washe gari da safe, koda na idar da sallar asuba ban kwantaba, nai dukkan shirye-shiryen daya dace na fidda kayana waje, ɗaki na dawo nai wanka sannan na shirya tsaf na fito.
Nasan dai driver zai kaini, dan haka na nufi wajen motar dana kai kayana.
Cikin girmamawa yace, “Ai kayan suna can” yay maganar da nuna motar Qaseem.
Da mamaki nace masa, “Can kuma? Mikuma ya maidasu can ɗin Nura?”.
“Yallaɓai Qaseem ne yace a maida”.
Kafin na bashi amsa takun takalman Qaseem suka katseni, ba tare daya kalleni ba yace, “Malama ki zagaya mota sauri nake inada wajen zuwa”.
Tamkar na zauna naita ƙwaɗa ihu haka naji, dole nabi umarninsa naje na shiga inda ya buɗemin da kansa bayan ya shiga.
Haka muka tafi tamkar kurame, sai lokaci-lokaci yakan jani da hira, wata na amsa da baki, wata nace, “eh ko A’a”.
Da haka muka iso.
Da kansa ya fito ya taimaka min muka shiga da kayan, ba tare daya zaunaba yace zai wuce.
Sake rakosa nayi wajen mota nai masa godiya.
Harya tada motar sai yace na bashi wayata.
Bashi nayi ina ƙunƙuni a zuciyata, duk da bansan miyayi da itaba naji a jikina number ta ya ɗauka, ya haɗo wayar da kuɗi ya miƙomin.
Zan zare wayar ya harareni, dole na haɗa da kudin na amsa nai masa godiya.
1
★★:★★:★★
Tun daga wannan lokacin abubuwa suka fara sauyawa tsakanina da Yah Qaseem, tun yana kirana lokaci-lokaci harya fara komawa kullum.
Banaƙin ɗauka, dan koba komai matsayin yaya yake a gareni, sannan banjin zan iya tozarta zuri’ar Dad, Yah Qaseem kuma namijin da kowace mace zata iya sone, dan akwai ƙyawu, yana aikinsa, tunda nake dashi ban taɓa kamashi da wani abu mara ƙyauba, sai dai idan a ɓoye yake kayansa, wannan kuma ya rage nasa ai, matsalar sa dai rashin ilimin addini, wanda gaba ɗaya ɗiyan dad ya zama babban tawaya wa rayuwarsu, tsagwaron wayewarce kawai da duniya suka sani.
Munja kusan shekara ɗaya da rabi a haka, shi baice yan sonaba, sai dai alamomi, dan duk randa ya bushi iska zaizo busting ɗina da kaya niƙi-niƙi, zanma ce yafi kowa ziyarata a gidan, idan kuma naje hutu yata bani kulawa kenan harna taho, ko wani abu Aamilah ko Salman sukaimin sai yayi magana a yanzu.
Kulawar da Yah Qaseem ke bani a yanzu na kula tana ɓata ran Mummy, duk da dai bata magana ni nakan hasaso ɓacin rai a fuskarta.
Ni kaina take-takensa suna tsoratani, dan ni dai nasan yafi ƙarfina ta kowanne fanni, duk da canjin dana samu a rayuwa bansama raina zan samu koda wanda bai kaisaba matsayin miji, ni dai kullum addu’ata ALLAH ya bani nagari da zai zamarmin mijin marainiya.
Muna shekara ta uku a makaranta Yah Qaseem ya fiddo manufarsa fili a kaina a kaina, dan kuwa ya tabbatar min shifa sona yake.
Na shiga tsantsar ruɗani da wannan furuci, duk da na daɗe ina hasashen haka, dama a lokacin munje gida weekend ne, ALLAH ma ya soni ana gobe zan komane, aiko washe gari baisan na gudu ba.
Koda na sanarma su Ummie sai sukaita zugani akan na karɓa masa, dan Yah Qaseem ya cancanta, idan kuma bana sonshine to, amma sun daɗe su dama suna hasashen akwai wani abu a ransa game dani, sudai suna bani shawara nai amfani da damata gaskiya.
Ni dai kasa cewa komai nayi, dan idan nacema banson Yah Qaseem nayi ƙarya, ya fini komai a rayuwa, sannan ya cancanta a soshi, amma idan harna amsa to na ɗeboma kaina gagarumar rigima daga ahalinsa, musamman Mummy da tunkan ya furtama take ƙyamatar abun, inaga yanzun yace yana so.
Bai sake bi takaina akan sonjin amsar na aminceba koni ina sonsa, ya dai ƙara ninka kulawarsa kaina fiye da ta baya.
Yana cigaba da sakani sakin jiki dashi ba tare dana saniba nima.
Shi dai Dad koda ya fahimta baice komaiba, amma Mummy ƙiri-ƙiri ta nuna bazata saɓuba, hakama Aamilah da Salman.
Wannan soyayya ta Qaseem ce ta kuma ƙirƙirarmin samubawar tsangwama da tsana a gidan, a wajen Dad da yah Qaseem kawai nake samun sassauci, gashi Dad ba mazauni bane.
Cikin wannan yanayin tsangwama muka shiga shekarar ƙarshe a makaranta nida ƴan uwana guda huɗu.1
______________________
JAWAAD
______________________
A ɓangaren Jay kuwa komai yana tafiya dai-dai, sai dai yau da gobe ba’a kiranta da nasara ko farin ciki ɗari bisa ɗari, dolene wataran tazo da daɗi, wataran saɓanin hakan.
Yana shekara ta biyu da rabuwa da Shahudah wani cigaba na musamman ya zomasa shida tawagarsa, dan kuwa wani horaswa ta musamman aka turasu zuwa ƙasar amuruka.
Duk masoyinsu dolene ya tayasu murna, inda ka cire irinsu Qaseem da suka gaza ɓoye hassadarsu akan maganar.
Dan kuwa dai kowa yasan badan matsayin kujerar Jawaad ta kai bane ya samu wannan cigaba, cancantace kawai da ƙwazonsa ya kaisa.
Da yake tafiyar gaggawace sai basu wani zaman ɓata lokaciba suka fara shiri, horarwas zata zama ta shekaru kusan biyu ce, amma bawai lallai su cika biyunba cif-cif, dan a ƙa’ida ma shekara ɗaya da rabine, sauran watannin da zasu biyo baya na wani tsarine daban.
Hakan yasaka su Aliyu duk da iyalinsu zasu wuce, Rose da Jawaad ne kaɗai babu mahaɗi🥴😂.
Ya sanarma Uncles nashi gaba ɗayansu, sun masa fatan alkairi kuma tare da addu’ar samo nasara.
Sai kuma shawarar mizai hana ya zaɓi ɗaya a yaran dangin a ɗaura musu aure ya tafi da ita, dan ba girmansa bane zama babu mace sam gashi har yana a shekara ta biyu da rabuwarsa da Shahudah, musamman a ƙasa irin wadda zaije yanzun akwai damuwa.
Bai wani jasu da nisaba ya nuna musu suyi haƙuri, maybe zuwa nan gaba idan bukatar hakan ta taso koda yana a cannne zaiyi magana.
Aiko wannan furuci nasa ya sakasu rabama ƴaƴansu lambarsa suyo farautar zuciyarsa bayan wucewarsa daya kirasu ya tabbatar musu ya sauka ƙalau.
Ko Baba ma sai da yay masa maganar auren kafin ya wuce, dan dama yana yawan masa shi dasu Umma, amma a koda yaushe yakan basu haƙurine da daɗin bakin su ƙara masa lokaci, bayason a sake tafka kuskuren baya kamar aurensa da Shahudah.
Sun masa fatan alkairi da addu’ar dacewa da mace ta ƙwarai da nasara akan abinda zashi nema…………….✍🏻
1
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻2