KWAI CIKIN KAYA CHAPTER C KARSHE BOOK1

 KWAI CIKIN KAYA  CHAPTER C KARSHE

                    BOOK1

      Shafi na talatin da ɗaya

…………A ɓangaren Shahudah kam taci alwashin sai Jawaad yazo ya nemeta har inda take, dan a nata hasashen gwala rayuwarsa take a haka.

     Tasan ɗunbin son da yake mata dolene ya jigatu da rashinta, shekaru biyar ta ɗiba masa cif, sai ya koma ƙaramin mahaukaci a kanta sannan ta bayyana a garesa.

       A shirmenta ko ganin ta cinye shekaru biyu bai nemetaba baisa taji a ranta akwai matsalaba, a’a a ganinta kawai ya rasa hanyar da zai iya ganintane, tunda Mummy ta tabbatar mata Jawaad baisan inda takeba har yanzu.

       Ita kuma duk motsin Jay Mummy tana sanar mata komai harma Aamilah da Salman, wani lokacinma harda Qaseem, ko dangane da tafiyar Jawaad Qaseem ne ya sanar mata komai.

        A duk sanda akai mata zancensa danne zuciyarta kawai takeyi, amma kewarsa da ɗunbin begensa kullum sake mamaye zuciyarta yakeyi, batason ya kalleta matsayin mafi arha a mata shiyyasa tai dauriyar riƙe ajinta gam tunda ta ƙetaro kasarsu tai kunnen uwar shegu dashi, sai dai a kullum hotonsa shine abin kallonta, hakama duk wata kafar yaɗa zumunta datasan yanada accaunt a wajen tana bibiyarsa da sunan da ba nataba.

       Ta kasa kula kowane saurayi, ta dai yarda kuyi abota amma ba soyayyaba, to kuma dama can dai gaskiya Shahudah bata iskanci, koshi Jay shaidane akan cikakkiyar budurwa ya sameta, dama can iskancinta baya wuce shan minti, amma bata yarda tarayya da waniba, takance wannan mallakin Jay ne tunma a wancan lokacin, to a yanzunma dai da harma yanzu take ɗauka da aurensa kanta tana taka tsantsan, sai dai fa iya shege da duk wani dandali na taruwar wayayyu tana a wajen babu abinda ya dameta, tunda bawai muhimmancin auren ta saniba balle ƙa’idojinsa, a ganinta duk abinda takeyi ƴancinta ya bata damar yin hakan, balle ta dawo inda babu ruwan wani da wani.

+

A gurguje⛹‍♀😏

_________________________

       BILKEESU

_________________________

             Rayuwa tai nisa, sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun zama yini, yini ya rikiɗa dare, kafin wani dogon nazari daren ya haɗa kwanakin da suka bada satittikan da suka dunƙulle wattani, sai gamu da shekara ɗai-ɗai har huɗu cif a makaranta, yanzu haka jarabawa biyu kacal ta rage mana kammala jarabawar ƙarshen zangon karatunmu na.

     Abubuwa da dama sun faru, wasu a iya tunawa, wasu ko zuciya ta manta saboda hidimomin yau da kullum, mun kwankwaɗi madarar ilimi wadda muke addu’a da fatan ta zamewa rayuwarmu dana ƙasa damu alkairi.

     Zakusha mamaki idan kukaji a cikin baƙin al’amuran da suka zoma rayuwata ciki harda soyayyar Yah Qaseem datai ƙarfi a tsakaninmu,

      Hoo duniya makarantar makaho, kai mai idonma ba ɗage masa ƙafa takeba, wai ni Bilkisu ƴar baƙa mummuna ƴan ƙwalisar samari masu ji da ƙyawu da ƴan canji a aljihu irinsu yaya Qaseem keso? To lallai dai abin da mamaki, sannan yana buƙatar alamar tambaya, shin sone na gaskiya? Kokuwa sone na sha’awa?.

      A wannan kaftawar da zamu farane kawai kowa zai iya fahimtar hakan, danni dai har yanzu baiji amsa tayinsa daga bakina ba.

     Dan duk wani salon rayuwa da iya zama da jama’a a yanzu Alhmdllh na san gwargwadon ilimin da UBANGIJI ya bani.

          Maza da yawa surar da ALLAH ya bani ke ɗibarsu zuwa gareni, ba wai ƙyawuba, duk da ƙoƙarin killace jikina da nake ban tsiraba a wajen mayu irinsu Yah Qaseem.

_________________________

             Uzirin gaggawa ya sakani dawowa gida a weekend ɗinnan domin ɗaukar abinda na manta, babu wanda yasan da zuwana, dan motar haya na shigo.

       Tun isowa gidan namu gabana ya faɗi, dan kuwa da motar ƴan sanda naci karo, na tura ƙaramar ƙofar gate na shi da sassarfa, dama dagani sai handbag ɗita.

        Zan shigo ƴan sandan zasu fita, dan haka suka bani hanya saboda na riga na kawo jiki, koda na shigo sukuma sai suka fice, na bisu da kallo kafin na maido kan Amina dake ta faman kuka ga mamanta itama tanayi.

       Sai Dad da Mummy dake tsaye sunata faman faɗa akan maza su Amina su fice musu da ga gida, inba hakaba zasu bama ƴan sandan da suka fice dama su tafi dasu.

      Gaba ɗaya ban fahimci yaren kowa a cikinsuba, na sake maida dubana ga Yah Salman dake kan mota zaune yana wani munafukin murmushi, Aamilah na daga gefensa tana latse-laste a waya.

         Nai saurin ƙoƙarin riƙo hannun Amina da suke ƙoƙarin fita, amma sai ta fisge a fusace harda bigemin hannu ta fice.

          ‘Lallai akwai matsala’ na ambata a zuciyata ina binsu da kallo har suka fice……

     Kiran da Dad ke minne ya katse tunanina, na sauke ajiyar zuciya ina nufarsu hankalina duk a tashe da tunanin mi akaima Aminar?.

          Ina isowa gabansu Dad abinda ya fara faɗamin shine, “Ƴata rabu da waɗancan masherantan mutanen kinji, dan ba mutanen arziƙi bane masheranta, duk ƙyautatawar da mukaima rayuwarsu sai suka ƙare da nemanmu da sharri”.

      Duk da bansan kan al’amarinba sai naji kalamun dad basumin daɗi ba, dan haka nai murmushin yaƙe kawai ina faɗin, “Wani abune ya faru Dad?”.

     Kafin ya bani amsa Mummy ta katsesa da sauri, “Daga shigowarki Bilkisu, ki shiga ki huta mana koma minene zakiji daga baya”.

        Kaina kawai na iya ɗaga mata, suka shiga ni kuma nabi bayansu.

     Dad dake zama a kujera yay min tambayar lafiya nida nake ƙoƙarin zana jarabawa ta ƙarshe nazo gida?.

        Sai da na durƙusa a gabansu na gaishesu sannan nai masa bayanin abinda ya kawoni.

         Ganin ya gamsu da maganatane ya sakani miƙewa na nufi ɗakina, dan duk tunanina a dagule yake da abinda na gani, sam zuciyata ta kasa yarda su Amina ne basu da gaskiya. Akwai dai abinda tabbas shi Dad bai saniba an ɓoye masa.

      Har nai wanka na fito domin cin abinci wannan lamari na sukata, babu kowa a falon na wuce kicin, a can ɗinma ban samu kowa ba, to dama wa zan gani? Amina ce dai da kuku kuma ga ayanda na iske gidan.

         Babu komai a kicin ɗin, amma da alamun dai anyi abinci, fitowa nai dan na san yana Dani, ilai kuwa a can na hangosa, tunani baisa hankalina ya fara kaiwa canba.

       Ɗiba nai na koma ɗaki kawai, duk da uwar yunwar da nakeji sai kuma nama kasa cin abincin, dan laumata ɗaya jal na ajiye cokalin ina sake karanto damuwar dake tattare da Amina.

     Amina ta taka rawar gani a rayuwata ta gidannan, dan ta soni a lokacin da kowa ya tsaneni, ta ƙaunaceni a lokacin da kowa ke ƙyanƙyami na, to ni tayaya yanzu zan sami nutsuwa a halin da take ciki?.

     Bani da ikon fita gidan a yanzu, amma nayi alwashin zuwa anjima ko a sacene sai naje gidansu Amina.

      Da ƙyar naci rabin abincin dana ɗebo, na zuba tagumi ina cigaba da saƙawa da kwancewa.

         Bayan sallar isha’i na fahimci gidan yayi shiru, a hankali na leƙo falon, babu kowa a ciki, yau ko tv ma ba’a kunnaba, cikin sanɗa na nufi kicin, ta ƙofar baya na fita a hanzarce zuwa harabar gidan, nanma sai da na wawwaiga na tabbatar babu mai kallona sannan na nufi gate.

     Baba mai gadi ya taso yana tambayata ina zanje, saurin masa alamar yay shiru nayi, murya ƙasa-ƙasa nace, “Gidansu Amina zanje baba, dan ALLAH ko wani ya tambaya karkace na fita, duk da nasanma da wuya asan bana nan”.

     Kansa ya ɗagamin, ni kuma na fice da sauri……………✍🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Shafi na talatin da biyu

…………..Gidansu Amina yana maƙwaftaka da gidanne, dan duk anguwar kusan shine ginin talakawa, Amina ta taɓa sanarmin Babanta ne ya saidama Dad filinsa kafin ya rasu, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH karya bar wani ya amshe gidan dasu Amina suke ciki danya lura masu hannu da shuni duk sun saye gidajen talakawan wajen sunyi gine-gine saboda ƙyawun anguwar, shiko gidansune na gado bayason yaransa su rasa.

      Wannan alƙawarine da dad ya riƙe ya saka gidansu Amina zama zakka a anguwar duk da kuwa ansha ƙulla musu dan a mallaki gidan hakan bata faruba.

          Da Amina na fara tozali tana kwance a ƙofar ɗakinsu lulluɓe da bargo tana rawar sanyi, na ƙarasa gareta ina ambaton sunanta.

     Dai-dai nan mamansu ta fito tana ɗangyasa ƙafarta dake mata ciwo, saurin dakatar dani tai a zafafe.

     Na tsaya cak ina kallonta da mamaki, dan nasan matar tana sona sosai, tana ɗaya daga cikin waɗanda suka koyamin dabarun rayuwa da mutane.

       “Mi kikazo yi mana a gidan, ki fita dan ALLAH, bana buƙatar sake ganin fuskar kowa daga ahalinku, dan haka fita kona miki abinda baki taɓa tsammaniba….”

        Kaina na duƙar ƙasa gabana na sake tsananta bugu, murya na rawa nace, “Mama dan ALLAH kiyi haƙuri, kimin uziri bansan komaiba dangane da abinda ke faruwa ba, babu kuma a wajen wanda zanji sai ku, nasan tunda naga fushi a fuskarki an miki ba dai-dai bane, dan ALLAH ki lamincemin mu raba wannan damuwar tare ko zanji sassauci a raina, da……”

     Saurin dakatar dani tai da fadin, “Damuwarmu ai tafi ƙarfin mu kasaftata wani ya samu wani yanki a ciki, an rigada an cuta mana, saboda bamu da komai kuma an nuna mana fin ƙarfi, Bilkisu jin abinda ya faru bashi da amfani a gareki sam…..”

      “Yana da amfani Mama, koba komai ƙila inada gudunmawar da zan iya badawa”.

        “Baki da ita Bilkisu, dan haka fitar min daga gida”

     Ko motsi kasawa nai, hawayen da nake riƙewa suka gangaro bisa kumatuna, juyawa nai a hankali zan fice muryar yayan Amina malamin islamiyyarmu na tsinkayo yana ma mamansu magana.

       “Mama karki haka mu saurareta, dan muma munsan bata san komaiba tunda batanan, kuma koda tana nan bata da wani ƙarfin ikon sawa ko hanawa a gidan muma shaidane”.

        Mama ta sauke numfashi da cewa, “Hakane, dawo Bilkisu”.

       Da sassarfa na juyo garesu, na tako inda Amina take na durƙusa ina yaye bargon da take lulluɓe, ƙara ta ƙwalla, hakan ya sakani saurin ja baya a firgice.

     Mama ta ƙaraso kusa damu tana mata magana, sai da ta sami nutsuwa ne maman ke cewa, “Kiyi haƙuri Bilkisu haka takeyi wanu lokacin, abu kaɗan ke sakata firgita yanzu”.

       Sosai mamaki ya kamani, na kalli maman ina tambayar to minene sanadin hakan? Dan ni dai nasan Amina mace ce mai tarin nutsuwa a komanta.

          Mama ta miƙomin kujera ƴar tsigunno, amsa nayi na zauna ina mai ƙarajin tausayin Amina.

      Itama zama tayi daga ƙofar ɗakin, yayan Amina ma ya zauna daga ƙofar ɗakinsa.

         Kallon mama nayi ina ƙara jeho mata tambayar abinda ke faruwa da Aminar.

      Mama ta sauke numfashi mai ciwo tana share hawaye, tace, “Bilkisu fyaɗe akai mata a cikin gidanku, sai dai mun gaza tantance wanene yayi?, saboda abu suka bata tasha batare data saniba”.

        Bansan sanda na koma ƙasa daɓas ba nai zaman ƴan bori, har taune harshena nake wajen faɗin, “Mama fyaɗe fa?”.

         Kasa bani amsa tayi saboda kukan da takeyi, sai yayan Amina ne cikin takaici yace,

        “Abinda ya faru kenan Bilkisu, munje mun faɗama Alhaji amma hajiya ta katsatstsare a kan sharri akaima ƴaƴanta, bayan kuma a idon mai gadi suka fiddo Amina cikin wani yanayi ita da Aamilah, munje mun ɗakko ƴan sanda shine suka basu kuɗi mukuma aka ƙaryatamu, wlhy badan mama ta hananiba da saina kaisu kotun musulinci, amma yanzu mubarsu ALLAH ya tsayar damu a kotunsa, dan yafi kowa sanin gaskiyar abinda ya faru”.

      Kuka nake sosai, wanda har su mama sai da suka koma lallashina, ganin dare yayi suka lallaɓani na komo gida.

        A falo naci karo da Yah Qaseem, da alama dai ɗakinama yaje bai ganniba, na share hawayen dake gudu a fuskata, ba tare dana kallesa ba nace masa “Ina yini”.

        Cikin kafeni da idonun da nakeji suna yawo a kaina ya amsa mani, ya ɗora da faɗin, “Ina kikaje haka? Na leƙa ɗakinki nama zata ko kina bathroom ne?”.

      Kaina kawai na girgiza masa amma na kasa magana, hakan ya sakashi takowa gabana dab, baya na matsa dan banason sunamin irin wannan abun haka.

     Kafin yay magana nai saurin faɗin, “Kaina ke ciwo Yah Qaseem, ina daga baya ina shan iska dan ina tunanin zafine”.

      Kamar bai gamsu ba, sai kuma cayay, “Okey to ALLAH ya ƙara sauƙi, kinsha magani ko?”.

    Kaina na ɗaga masa.. 

Yace, “To kije ki kwanta, dama nazo naji miya dawo dake gida keda ke shirin dawowa gaba ɗaya”.

      Sai da na raɓashi zan wuce sannan nace, “Babu komai, da safema idan ALLAH ya kaimu zan koma, dama abu na manta kuma ana buƙatarsa shine nazo ɗauka”.

      Banji amsar daya baniba, dan tuni na shige, nakuma dannama ƙofata key dan karma yace zai biyoni.

      Jingina nai da ƙofar ina kuma fashewa da sabon kuka saboda tausayin Amina, inhar zasu iya cutar da yarinyar data ɗauki tsahon shekara tara tana musu bauta to ni ta yaya zan tsira a wajensu? Miyasa zasuma Amina haka? Duk taka tsantsan ɗin yarinyarnan da riƙon addininta da martaba, Amina ko zama babu hijjab batayi a gidan, duk zafi ta gwammaci haƙuri ta zauna a hakan duk dan gujema irin wannan ƙaddarar, “Wane tsinannene ya aikata wannan aikin? Sai yaushene ƴan sandar ƙasarmu zasu ajiye kuɗi su ɗauki gaskiya? sai yaushene masu kuɗin ƙasarmu zasu fara yarda da kuskuren ƴaƴansu su ajiye son zuciya!!” na ƙare maganar da zubewa a ƙasa ina mai tauna leɓena alamar jin zafi mai yawa a zuciyata.

     Ni kaina bansan tsahon lokacin dana ɗauka ina kukaba, ban taɓajin takaicin sakacin Dad ba irin yau, dan inaji a jikina koni akaima abinda akayiwa Amina bazai ɗauki matakiba, a halin yanzu kuwa ai nice a halin hau, dan kuwa zasu iya min kwatankwacin yanda sukai mata.

        Kuka dai na yisa harna rasa hawayen zubarwa, rayuwar gidan haya da talauci, maraicin iyaye, matsalar Jazuga, haɗarin tsintar kai a matsayin mai kisan kai, faɗawa hannun su Uwargida, kuncin zama gidan Inna zainaba, duk sun faru, yau kuma ga jin daɗin da cigaban rayuwa amma cike take da ƙalubale kala-kala tare da firgicin rashin tabbas, shin mutanen duniyane a haka? Kokuwa duniyarce a haka?, wanene zai bani amsar wannan tambayar ko zata zamemin hasken fahimtar cuɗaɗɗun al’amuran cikinta?.+

          Yanda naga rana haka naga dare, sai gabannin asuba barci yaɗan saceni, hakan yasa na tashi a makare, ina yin salla nai shiri a gurguje, banama son ganin kowa a gidan har Dad ɗin kansa, dan haka na rubuta masa text message akan na wuce dan yau ina da jarabawa, naji bazan iya kwana biyun da nai niyyaba sam.

          ALLAH ya soni sanda na fito ana wankema Yah Qaseem motane, bai kai ga fitowa ba.

         Gidansu Amina na shiga, mama na tsakar gida tana damun kunu, na duƙa na gaidata, cikin bina da kallo da takeyi tace, “Bilkisu miya sami fuskarki haka ne?”.

      Murmushi nayi ina haɗiye kukan dake shirin zomin, nace, “Babu komai mama, zan koma makarantane, amma insha ALLAHU baifi nanda kwanaki goma zamu dawo gaba ɗaya ba, akwai wani likita zaizo har gida ya sake duba jikin Amina, insha ALLAHU zai bata dukkan taimako, na kuma muku alƙawarin koba yanzuba saina binciko wanda ya aikata wannan ɓarnar kuma an hukuntashi insha ALLAHU”.

      “Ah ah Bilkisu, karki saka rayuwarki a haɗari kinji, koma wanene mun barsa da ALLAH, zai saka mana, mun gode da nuna kulawarki a garemu”.

       “Mama barin wanda ya aikata yaci bulus shine yake nuna na gama saka kaina a haɗari, dan abinda akaima Amina, nima zasumin kwatankwacinsa ai, ke dai kimin addu’a kawai”.

         Addu’oin fatan alkairi mama ta shiga jeramin, kafin tace na zauna na karya, haƙuri na bata akan bazan iya cin komaiba, sannan inason na wucene dan banason wani yace zai kaini a gida.

      Haka na wuce bayan na leƙa na duba Amina dake barci, a motarma lokaci-lokaci haka naita share hawaye, har ALLAH yasa na iso lafiya.

      1

★★★★★

            Shigowata gidan duk sai suka taho da murnar tarata, sai dai kuma duk sai sukai turus suna kallona.

      Zuhrah tace, “Bily lafiya kuwa? Kinga fuskarki a madubi safiyar yau? K……….”

       Kafin takai ƙarshe Rebecca ta amshe da cewa, “Ku wannan kuka ne, Bily miya faru?”.

    Duk sun rikice, Nazifa da Ummie sukazo suka kama hannuna, ni dai ban iya bama kowannensu amsaba, kallonsu kawai nake tamkar wata gunki, hakan ne ya ƙara tada musu hankali.

       Dai-dai Gwaggo hari ta shigo gidan, da gani daga wani waje take, itama da mamaki take kallona, sai dai batace komaiba har muka shige.

      Rufeni sukai da tambayoyi har Gwaggo Hari, sai ma na rasa nawa zan amsa.

      Ganin sun matsa ne nace musu banajin daɗinefa, subar ɗaga hankalinsu.

     Badan sun yardaba suka barni………….✍🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Shafi na talatin da uku

…………….Duk wanda ya sanni zaisan inada damuwa tun dawowata gida, a kwana na uku da dawowata mukai ɗaya a cikin jarabawar data rage mana, ranar ƴan uwana suka nunamin ɓacin rai sosai akan abinda nake ɓoye musu, dan badan taimakon Nazifa dake kusa daniba da babu abinda zan rubuta sai shirme a takardata.

      Ba komai zai jawo hakanba kuma sai halin da nake ciki na ɗunbin tausayin Amina da fargabar tawa rayuwar idan na koma zaman gidan yanzu.

         Ganin sunyi fushi na basu haƙuri, sannan na ɗora da faɗin,

         “Ƴan uwana kuyi haƙuri, zan aikata muku babban laifi na canja burinmu nason zamowa ƴan jarida, yanzu na gane ba wan nan bane abinda nake buƙata, martaba da kare sauran ta ƴan uwana itace abar buƙatata”.

       “Wace magana kikeyi haka bily, mu bamu fahimceki ba” Rebecca ce mai maganar.

       Zama nai da ƙyau na shiga zayyano musu abinda na gani a gida, wanda inaji a raina cewa na manto abinda na koma ɗaukane dan na iske wannan iftila’in, dan ƙila daban ganiba babu mai bani gamsashen labari.

           A take naga duk sunyi murmushi mai ciwo, Nazifa ta miƙe tabar wajen tana kuka.

     Da kallo mamaki na bita, dan bansan manufar kukan nata ba, “Nazifa!”

      Na ambaci sunanta, hakanne ya sakata tsayawa cak sai dai bata juyo garemu ba.

     Miƙewa nai tsaye na taka zuwa gareta na dafa kafaɗarta, “Nazifa miya sakaki kuka a wannan maganar?”.

         Sai da taja wasu sakanni kafin ta juyo gareni, sosai take hawaye wasu nabin wasu, ta dafa tawa kafaɗar tana sake fashewa da kuka mai ciwo. Ban hanata ba, hakama sauran ƴan uwana babu wanda yay mata magana.

       Rebecca dake bayanmu tsaye tace, “Bilkisu, kukan da Nazifa keyi kukane namu mu duka, duk da dai ke mun ɓoye miki dalilin kukan tuni, sai dai maganarki ta yanzu ta sosa mana inda ke mana ƙaiƙayi harma da tuna mana abinda ya shuɗe”.

        Kallonta nayi sannan na maida gasu Ummie, kukan da Ummie take har yamafi na Nazifa, dan numfashinta har sama yake tamkar zai shiɗe ta fusgosa da ƙyar.

         Hankalina ya sake tashi mtuƙa fiyema da da, nace, “Ƴan uwana ku buɗemin abinda kuka rufemin ko zuciyata zata samu sukuni dan ALLAH”.

        Shiru sukai kusan na mintuna biyu, kafin Zuhrah tazo ta kama hannuna dana Nazifa zuwa inda muka taso.

        Duk zama mukai har Rebecca.

         Zuhrah tace, “Bilkisu kinsan dai mun taɓa baki labarin ƴar uwarmu data rasu sanadin sikila ko?”.

        Cikin ɗaga kai nace, “Tabbas anyi haka”.

       Zuhrah ta share hawayenta yana riƙo hannuna, “Bilkisu tabbas ƴar uwarmu nada sikila amma sanadin baƙin cikin fyaɗe ta rasu”.

     Cikin matuƙar razana na zabura, har taune harshe nake wajen ambaton “Fyaɗe fa kikace Zuhrah?”.

        “Tabbas fyaɗe Bilkisu, ni Nazifa nida ita akaima Fyaɗe a cikin gidanmu sunje mini weekend ita da Ummie, amma abin mamaki da al’ajab sai aka rasa wanda ya aikata mana wannan ta’asa, dan kuwa kamar yanda kika bamu labarin nan sai da aka bugar da Amina muma haka akai mana wlhy. Babu kalar binciken da ba’ayiba amma har yanzu babu wani bayani, kwannamu uku a asibiti ƴar uwarmu ta rasu saboda yanayin jikinta bayason wahala, da kuma dai ƙarar kwana. Bilkisu wlhy ba ɗiyan talakawa kawai akema fyaɗe ba, sannan ba mata kawai ba, harma da maza, ƙanin Rebecca an masa fyaɗe ta hanyar luwaɗi shima kuma ya rasu”.

       Kasa magana nai saboda kuka, jikina sai tsuma yake, hakan yasa na miƙe a fusace ina nunasu, “Amma duk da wannan abubuwan da suka faru da rayuwarku kuka ɓata lokacinku wajen tsara burinku akan business kawai? Rayuwa a hannun ALLAH take, amma baka yanke ƙauna daga rahamarsa, shiyyasa a kullum muke zama masu buri, kuyi haƙuri duk da ni ɗiyan talakawace, ban tashi gidanmu naga kuɗiba hakan bazaisa na cigaba da zama a cikin burinku ba gaskiya”.

     Dukansu kallona sukai, bance musu komaiba naja takarda da biro nai rubutu na tura a tsakkiyarsu.

       Dukansu kallon takardar sukayi, kafin su maido kallonsu gareni.

          “Wannan daga yau ni Bilkisu Adam makaho shine burina, ban isa canjawa gaba ɗaya ba, amma ko alwashin dana ɗauka akan Amina da Nazifa da ƙanin Rebecca da ƴar uwarmu data rasu suka cika naci riba”.

         Rebecca ta kamo hannuna ta ɗora nata, itama tace, “Daya yau nima Rebecca ina tare fake Bilkisu”.

       “Nima ina tare daku” cewar Nazifa tana aza hannunta akan na Rebecca, Ummie da Zuhrah ma duk suka ɗora tare da bamu goyon baya.+

STORY CONTINUES BELOW

      Wannan shine sanadin burinmu, a haka muka ƙarasa jarabawar data rage tare da bikin karramawa da aka gudanar.

      Ranar Dad da kansa yazo ɗaukata shi da Yah Qaseem.

     Nayi farin cikin ganinsu, haka suma sun tayani farin ciki.

      A gidanma nayi mamakin tarbar dana samu daga Mummy.

*_RAYUWA SABON TAKU!_*

………….Dole na kira yanayina na yanzu da suna rayuwa sabon taku, dan kuwa nazo da sabbin salon taka tsantsan a gidan, na sake komawa islamiyya, inda a kullum nake samu na leƙa Amina, duk da yanzu dai ta warke a jiki, sai dai ciwo a zuciya da kuma firgita da takeyi musamman idan taga maza kusa da ita dab. Ina tausaya mata, shiyyasa a kullum bana mantawa da ita a cikin addu’ata.

          Ina fuskantar sabuwar tsangwama daga Mummy da Aamilah akan son da Yah Qaseem ke iƙirarin yanamin, wanda ni banma ɗaukesa a komaiba duk da naji zan iya zama dashi matsayin miji inhar da gaske auren nawa zaiyi, kuma bazance bana sonsaba, sai dai ban ƙwallafa rai ba, idan na samu zan amsa, idan saɓanin haka yazo zan zamto mai haƙuri.

       Rashin Amina ya saka ayyuka da yawa na gidan dawowa a kaina, musamman gyaran sama ɗakin Mummy da Dad da falon saman, sai ko ɗakin Yah Qaseem daya wajabta min shima, da farko har Aamilah da Salman suma sun fara sani, amma sai Yah Qaseem yay magana akan karsu ƙara, matarsa ba ƴar aiki bace.

     Harga ALLAH yaban dariyar wannan furuci, yayinda ya ƙona zuciyar Mummy harta yini bata amsa maganata tana fushi dani, Aamilah kam harda cewa wai Mummy ta bincikeni ina niyyar cinye mata kurwar ɗa, dama ta daɗe da zargin ni mayyace.

     Ban damuba, danni yanzu a rayuwa mukuma ya rage ban ganiba? Sai dai zaman takewar aure da nakeji jama’a na kira da zaman haƙuri shima.

       Kamar kullum yauma na tashi da wuri na kimtsa ɗakina nai wanka, na fito cikin doguwar baƙar riga zuwa kicin, kuku ne kawai keta kiciniyar ɗora breakfast, mun gaisa cikin mutuntawa na haɗa tea na fito falo.

       Shi kaɗai nasha saboda sabon makaranta, yanzunma sai ban iya daurewa saina sha ɗin, dan breakfast ma saina ka sha biyu banyiba ko ƙarfe ɗaya.

      Sallamar Yah Qaseem ce ta sakani ɗago idanu na, na kallesa ina amsa shi.

     Yayi ƙyau cikin suit ɗin sosai, duk da baisa rigar saman ba tana riƙene a hannunsa.

       Fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna a gefena dab, hakan ya sakani matsawa nikuma ina gaidashi.

    Bai amsaba, sai tambaya daya jeho mani,

     “K wai yaushe zakibar gidadanci ne? A zahiri dai ba Bilkisun da bace bagidajiya, amma a baɗini babu abinda ya canja na ƙauyancinta”.

     Duk da maganarsa tamin zafi sai nai murmushi kawai, na cigaba da juya cokalin dake a kofin shayin ba tare dana bashi amsaba.

       “Baki jinane?” ya sake min tambaya?.

       Haɗiye takaicin daya tsayan a maƙoshi nayi naɗan kallesa na ɗauke ido lokaci guda saboda tsareni da yay da kallo, “Naji Yaya, sai dai kasani ni abinda nakeyi ba ƙauyanci bane ko gidadanci, hakan koyarwar addininmu ce, niba muharammarka bace, bamuda hurumin haɗuwar jikin juna a halin yanzu, kodan gujema sharrin shaiɗan mai saka wasuwasi a zukatan bayin ALLAH”.

       Jikinsa ya kwantar a kujerar yana ɗan taɓe baki, yace, “Da haka ake cutarku ai dama ku kullum, shiyyasa hausawanmu sunfi kowa rashin wayewar kai, shikenan sai akace dan namiji ya zauna kusa da mace, koya kama hannunta, koya rungumeta wani abu zai faru?”.

         Mamaki ya kamani jin furucinsa, sai bance komaiba na cigaba da juya cokalin a cikin shayina nidai.

    Babu zato naji ya ɗora hannunsa a saman nawa yana faɗin, “Bani nasha ni”.

      Ban sakar masaba, duk da jinake kamar na make hannunsa daya ɗoramin, nace, “Bari na haɗo maka wani to”.

     “No barsa, wannanma ya wadatar, sai dai idan bakiso nashanye miki” Ya faɗa yana sake matsowa jikina.

     Sakar masa kofin nai kawai na miƙe nabar masa kujerar, domin neman hanyar kuɓuta, ya bini da kallo harna shige kicin.

          A ɗan lingun da zai sadani da kicin ɗin na tsaya ina roƙon UBANGIJI akan wannan rayuwar yahudanci, “Ya ALLAH ka kareni ka karemin martabata da mutuncina harna bar gidannan zuwa gidan aure na, ya rabbi ka hananeni saɓa maka bisa ganganci komin farin cikin da hakan zai sakani”.

    Na haɗiye hawayen dake neman zubomin kafin na ida shiga kicin ɗin, na tarar kuku harya shirya masa abinci saboda shi yake fara fita a gidan kafin kowa.

    Ɗauka kawai nai na kawo masa falon, na iske yana wayane yana shan tea ɗin daya amsa a hannuna.

     Yanda yake wayar a zafafe yana ambatar sunan wani Jawaad ya sakani kallonsa, fuskarsa harta koma jaa saboda bala’i kasancewarsa farin mutum sosai.

      Koda ya gama wayar tsaki yayta ja da ambaton sai ya kawo ƙarshen iskancin Jawaad ɗin.

      Nidai bance dashi uffanba, na haɗa masa abincin na canza kujera can nesa dashi.

      Bala’i na cin ransa bai wani ci abincin kirkiba ya tashi zai fice, gabana yazo ya ranƙwafo wai zaimin kiss, nai saurin kaucewa jikina har rawa yakeyi.

     Wata banzar harara ya watsamin yana jan tsaki.

     “K baƙauya karki ƙaramin ɓacin rai mana”.

      Fuska na ɓata nima, nace, “ALLAH ya baka haƙuri Yaya, sai dai ina sake tuna maka bai daceba, kabari sai munyi aure”.

     Bai tanka maniba ya fice abinsa yana sake jan wani wawan tsaki.

       Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina harar bayansa, kai wlhy da sake, dolene nasan maiyuwa da wuri kafin wankin hula ya kaini dare a gidan nan.

       Kayan da yaci abincin na tattare na gyara falon, na hau sama canma na gyara da ɗakin Mummy, dan tana ɗakin Dad tunda yana gari.

     Sai da komai naga yamin fes sannan na fito harabar gidan tacan baya na zauna ina wani bincike ta waya.

      Naja dogon lokaci a wajen kafin na shiga cikin gida saboda kiran Dad daya shigo min a waya.

      A d/table na iskesu su duka, dan haka na fahimci dalilin kiran Dad.

     Sai da na duƙa har ƙasa na gaishesu shi da Mummy sannan na gaida Aamilah da Salman lokacin da nake zama.

        Anacin abincin ana hira, duk da dai babu bakina a ciki sai lokaci-lokaci, shima Dad ke sakoni a maganar na bashi amsa.

     Bayan mun kammala ne Dad yace na sameshi sama zamuyi magana.

        Duk da inata tunani akan wace magana haka na miƙe nabi bayansa.

      Sai da ya zauna a kujera sannan nima na zauna a ƙasa, yace na koma kujera nima, amma saina bashi haƙuri akan nanma ya isa.

     Murmushi kawai yayi yana gyara zamansa, idonsa a kaina yace, “Bilkisu nasan zakita mamakin wannan kira ko?”.

       Kaina na jinjina masa ina bashi amsa da “Eh wlhy Dad, ALLAH dai yasa banyi laifi bane”.

      “A’a bakiyi laifin komaiba mai gadon zinari, akan karatune dama, mizai hana da wannan zaman ki sake komawa makaranta kawai? Kinga saina turaki wajen yayarki Shahudah ko?”.

          A zuciyata mamakin rayuwa irin ta Dad nake, maimakon yamin zancen aure amma kunji zancen cigaban karatu yakemin, duk da a yanzu ina cikin shekara ta ashirin da huɗu ne…….

      Katsemin tunani yay da faɗin, “Karki ce zaki sakama ranki wata sakarar soyayyar Qaseem kinji, ki tsaya kiyi karatun da zaki tallafi rayuwarki koda bana raye, shi kansa zaifi ganin mutunci da kimarki, duka shekararkima nawa da har zaki sakama kanki maganar aure? Bakiga sakamakon da aure ya bama yayarki Shahudah ba, Rayuwar yau data jiya da mu mukai akwai banbanci kinji”.

      Kaina na ɗaga masa ina murmushi, nace, “Dad dama ba aure nakeso ba, sai dai akwai wani buri a raina”.

     Da sauri yace, “Wane burine haka ɗiyata?”…………✍🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Shafi na talatin da huɗu

……………Murmushi na sakeyi saboda yanda yaymin tambayar cikin zumuɗi, duk yanda zaiyi ka sake dashi dad ya sani, shiyyasa akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsa da yaransa, kawai sakacine dai dashi wanda yake kallon hakan matsayin ƴancin kai.

      “Dad bansan yaya zaka ɗauki zancenba, dan mutanenmu da yawa sukan ɗauki aikin matsayin bai dace da mace ba, sai dai ƙabilun nan suna shigasu, mune dai gaskiya akan daɗe babu ɗiyan bahaushe a ciki….”

        “Kinga faɗamin kawai kanki tsaye, wane aikine?”.

      “Dad aikin ƴan sanda, sonake na zama ƴar sanda inhar kana ganin ya dace nayi?”.

       Kansa yaketa kaɗawa cikin murmushi, ya dafa kaina yana faɗin, “ALLAH yay miki albarka Bilkisu, wannan tunanine mai ƙyau kuwa, wanda ya kamata ace yaranmu mata suna irinsa koda cigabanmu, ina goyon bayanki ɗari bisa ɗari, sai dai kibari zan zaɓa miki wanda zaifi dacewa dake kinji ko?”.

         Kaina na ɗaga masa ina jero masa godiya ta musamman,  dan ina ganin fatana na zama ƴar sanda maisa kaki zai cika.

        Ƴan sanda masu saka kaki yafi birgeni, aikin su Yah Qaseem bai cika birgeniba, dukda su ƴan sandane sunfi yin manyan ayyuka ba irin na ƴan sandan dana saniba masu fuskantar kowacce matsala musamman ma irin tamu ta cikin gidaje, to amma babu yanda zanyi, dan kimar Dad ta wuce nai masa musu koda a mafarkine, bazan dai taɓa masa biyayya akan abinda ya kauce shari’a ba, amma duk wanda ya zaɓamin zan amshesa matsayin zaɓin UBANGIJI na.

       Ina dawowa ɗaki Number Ummie na kira na sanar mata yanda mukai da Dad, taji daɗi sosai, dan haka tace zata sanarma Dadyn ta dan yazo ya samu Dad akan batun, dan suma duk sun sanar a gida kuma an barsu, Zuhrah ce kawai aka hana itama tana kan lallaɓawa.

1

*_KANA NAKA ALLAH NA NASHI_*

       

          Tabbas haka wannan batu yake, sanda kake tsara wancan sai kaga ba shine a kundin ƙaddararka ba, tunda tun farko bakai ka rubuta littafinba balle kai tunanin bin tsarin daka shirya ko zuciyarka tafi so.

    Kwanaki uku dayin wannan magana da Dad sai ga Dadyn Ummie yazo gidan, wanda na lura dai yaron Dad ne, dan abubuwa da dama daya shafi karatun yaran gidan shine tsaye a kansa, hatta da aiki ko wani abu shi dad ke ɗorawa akan nemawa wanda duk yaso.

      Bansan mi suka tattaunaba, na dai je mun gaisa, inda kamar yanda ya saba ya sakemin nasiha akan na kula da komai karna bari nai zirmawar da zanyi dana sani anan gaba.

     Na riga na gahimci hannunka mai sandarsa, dan yasha faɗamin karna yarda nai koyi da tarbiyyar gidanmu, ba ƙaramin daɗi nakejiba kuwa da wannan kulawar tasa, shiyyasa a kullum nake sake ganin kimarsa da mutunci.1

     Nayi zaton ko Yah Qaseem zaice shi aure yakeso muyi baison na tafi wannan aikin, amma sai naji tsitt baice komaiba, sai dama akai kusan sati sannan yakemin tambaya akan maganar.

       Koda na bashi amsa murna kawai ya tayani muka cigaba da wata hirar kuma.

      Hakan sai ya bani mamaki, a shekarun Yah Qaseem ya cancanci buƙatar mace a kusa da shi, kumani ban taɓa kamashi da wata maceba ko ganin wani abu daya danganci mace a ɗakinsa balle nace yana neman mata, to minene matsalarsa? Dan a yanda yake nunamin dai ai yana buƙatar jin ɗumin macen.

     Na kauda wannan tunanin a raina dan bashi da wani muhimmin amfanin da zai mini.

     Su Aamilah kam dariya sukaita min, inajinta har aunty Shahudah ta kira ta sanarmawa itama tana tayasu.

      Mummy dai batace komai akan batunba, amma naji wani furuci nata daya tsayamin a ƙahon zuciya, wanda na lura ita gani take kamar dan neman kusanci da yah Qaseem ne ya sakani son aikin.

      Ni dai na tattara dukkan lamarina a hannun mahaliccina, domin yafi kowa sanin mike raina .

      Nakuma cigaba da miƙa kukana a garesa da fatan dacewa idan har aikin alkairine a garemu, idan ba alkairi bane ALLAH ya canjamana da wanda zai zama alkairi.

         kusan wata guda babu wani bayani daga Dad ko dadyn Ummie, dan dad ma har yayi tafiyar sati uku yaje ya dawo.

     Sai ranar kwatsam na dawo islamiyya na iske Dadyn Ummie da Ummien kanta a gidanmu. Muka rungume juna muna farin ciki, sannan naja hannunta muka shige ɗakina.

        Itace ta fara gumtsamin abinda ya kawosu gidan, tuni farin ciki ya mamaye min zuciya, muka sake rungume juna, kiran Dad ya sakani sakinta muka tafi falonsa tare.

      Na gaida Dadyn Ummie bayan mun zauna, Dad ya miƙomin takardun hannunsa dake tabbatar da an ɗaukemu zamuje training, harda ƴar ƙwallata ta murna tamkarma ance mun zama ƴan sandan.

       Su dad nata min dariya, duk da dai ba ɗan sandan danai fatar zama bane wannan ma nayi farin ciki dashi, naji a jikina shine alkairi a gareni shiyyasa ALLAH yay min canji dashi.

      Mun taso zamu fita naji Dadyn Ummie na faɗin, “Wlhy nayi mamakin hakan Alhaji, dan ban taɓa zaton Jawaad zai iya aikatawaba, kamar yanda na faɗa maka shine yayta ƙoƙarin ganin takardun yarannan sun shiga duka wlhy, musamman dayaji nace saƙon nakane…..”

     Banji amsar da Dad ya bashiba muka ida ficewa, ina mamakin wanene wannan Jawaad da ake yawan faɗar sunansa a gidannan? Sai kuma labarin da Amina ta bani akan Aunty Shahudah da mijinta ya faɗomin a rai, to kodai mijin aunty Shahudah ne? To amma miyasa Yah Qaseem ya tsanesa matuƙa? Bani da mai bani amsa dan haka na kauda zancen a raina kawai muka cigaba da hirarmu da Ummie.

*_INDA RAI! DA RABO_*

         Lallaikam inda rai da rabo inji masu iya magana, to nima dai Bilkisu yanzu na shaida hakan, dan kuwa yau gani cikin jerin waɗanda ake horaswa na hukumar ƴan sandan farin kaya a cikin (Training center) ɗinsu, tare da ƙawayena huɗu a karo na  uku.

         Duk yanda zan fasalta abun ba lallai ku fahimta ba, amma al’amarin ɗanba sauƙine, anji jiki kafin ƙashi da tsoka su saba, yayin da ƙarfin jini da karsashin zuciya ke ƙara yawaita, babu babban maicin ribar abu irin maiyinsa da yaƙini ko fushin son maida murtani.

     Nayi imani da hakan ya taimakama ƙwazonmu sosai ni da ƴan uwana, dan kuwa matakin farko na nasara damu aka shallakesa, kamar wasa sai gamu a mataki na biyu, inda mataki na uku ya kasance na masu babbar nasara, dan kuwa a cikin waɗanda muka shigo wajen mu sama da dubu biyu bamu wuce mutum dubu ɗaya da ɗari uku muka shallakeba, a kuma cikin dubun muka kasance mafiya ƙwazo mu ɗari uku da ashirin, cikin 300 ɗinan aka kuma rairayemu mu saba’in, mu goma sha uku ne kawai mata a cikin saba’in ɗinan, sauran duk sun kasance mazane, cikin amincin ALLAH kuma ko ina ina tare da ƙawayena.

         Mu 70 ɗinnan an waremu domin samun horo na musamman fiye da sauran ƴan uwanmu, ƙwazon da muke nunawa da juriya ya samu fita cikin ƴan rukunin farko kenan.

      

        A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa har suka rikiɗe zuwa watanni, inda cikin amincin UBANGIJI muka cika dikkan shariɗɗan zamowa cikakkun ma’aikata abin alfahari.

      Tabbas wannan nasara da muka samu munyi matuƙar farin ciki da ita, ranar kuma nasha kuka saboda tunowa da iyayena da siraɗin rayuwa dana tsallake batare da hasashen kaiwa wannan matsayinba na yanzu.

      Shiyyasa akace babu maraya sai rago, wannan magana tabbas haka take.

★★★★★★

         Ranar data kasance ranar yayemu ta zamto rana mai daraja da zuciya bazata iya mantawaba, dukanmu muna cikin Uniform da suka ƙara mana kwarjini da cikar kamala, inda manyan baƙi da manyan wannan hukuma sukai jawabai masu nuna ƙwarin gwiwa a garemu da fatan alkairi, sai ƙyaututtukan karramawa da suka biyo baya na ɗalibai mafiya ƙwazo a cikinmu inda sunana ya fito a bazata.

       Wannan abu ya sakani ɗunbin mamaki da al’ajabi, dan ban taɓa kawo hakan a rainaba koda a mafarkina, dan ni kaɗaice mace a cikin waɗanda suka samu wannan karramawa.

          Dad yaji daɗi sosai, hakama Yah Qaseem, su Mummy ma dai dayake duk hardasu akazo sun tayani murna koda bata kai har cikin zukatansuba.

         Daga ƙarshe kowannenmu ya samu takardar tabbatuwarsa ma’aikaci tare da inda aka turaka, matakin karatu ya matuƙar taimaka mana wajen tsintar kai ba’a matsayi mafi ƙaranci ba, dan kuwa bamu kasance matakin ƙarsheba.

      Mun rungume juna mu dasu Zuhrah muna kuka, dan kuwa dai an samu matsala wajen rarrabamu bazamu kasance a waje ɗayaba, kowanne da inda aka cillashi, ni da Ummie ne kawai a waje ɗaya.

      Sosai hakan ya taɓa zukatanmu, har sai da iyayenmu suka koma lallashi da nuna mana ai dama aikin kenan, wannan ba makaranta bace balle muce tilas mu kasance a zaɓinmu.

★★★★★★★

         Sati guda cif da gudanar da bikin yayemu muka shiga filin daga, yau sai ga Bilkisu Adam makaho matsayin ƴar sanda ta hukumar DSS, Yah Qaseem shine ya zamemana fitila a komanmu ni da Ummie, duk da kasancewarsa babba a wannan hukuma.

      Aikin farko da muka fita Ummie tayisa cike da tsoro, ni naita ƙarfafa mata Gwiwa har itama ta samu ƙarfin zuciya, a cikin kwanakin da basu gaza sittin ba, waɗanda a jimlace zasu baka wata biyu mun gama gogewa, muma munaji a ranmu mun isa karanmu yakai tsaiko………….✍🏻

Akwai sauran pages 6 a ƙasa, nima sai naga ana zabga mana ruwan subscribing sannan zan sakesu🙄😂, waɗanda sukai mana sub… Muna godiya, ALLAH yabar zuminci, kuma nayi farin ciki dan duk wanda yayi na gashi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

1

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻1Shafi na talatin da biyar

       …………Yau safiyar Laraba muka tashi da labarin dawowar wasu manyan jami’ai na wannan hukuma tamu kamar yanda manyanmu suka sanar.

       Na kasance a cikin tawagar masu zuwa tarbarsu da aka ɗiba a cikin mu ƙananun ma’aikata, akwai kuma manyanma.

     Hakanne ya tabbatar mana lallai waɗanda zamuje tarar sunada muhimmanci a wannan hukuma. Haka kawai na tsinci kaina da faɗuwar gaba, zuciyata sai wani irin zallo take kamar zata faɗo ƙasa.

      Ƙirjina na dafe ina lumshe idanu, dama tun jiya nakejin tamkar wani gagarumin abu na kusanto rayuwata, sai dai bansan minene ɗinba.

       Mun iso airport ɗin akan lokaci, dan jirginma bai kai ga saukaba sai nan da minti arba’in kamar yanda aka sanar damu.

         A yanda mutane suke kallonmu musamman ma mu matan da muka kasance mu biyu kacal yasa duk na takura, sanye muke da Uniform wanda ni kaina nasan sunma surata matuƙar ƙyau, tabbas bani da ƙyawu mai tsanani amma ALLAH ya azurtani da ƙyaƙyƙyawar  surar dake da wahalar samu ko a cikin matanma, wadda itace ke fisgar maza da yawa a gareni, akwai baby hijjab dana saka kafin na ɗora hular Uniform ɗin a saman kaina, hakan ne zai baka amsar kasancewata musulma kai tsaye.

       Addu’a na rinƙayi a zuciyata, saima na saka eyeglasess a idona saboda kallon ya gundunreni.

           Adadin mintuna na cika jirgin da muke tabbacin jira ya iso, saida  ya gama shawagi a sama kafin ya sauka a inda ya dace, wannan shine karon farko da nazo airport a rayuwata, hakan ya sakani tsarkake sunan UBANGIJI daya sanya fasaha ga zukatan waɗanda suka ƙera jirgi, sannan ya bashi ikon tashi sama duk da girman da yake dashi.

        Bugun zuciyata ya sake sauya salon bugawa da sauri-sauri, hakan ya sakani rumtse idanu dukkan jikina na wata irin tsuma, haka kawai sai nakejin kamar na kama kuka.

         Taɓanin da akaine ya sakani buɗe ido da sauri, ɗaya daga cikin ma’aikacinmu ne da yake nema takurama rayuwata, na kallesa ina ɗauke kaina dan haushi yake bani, shi a dole wai sona yake, tun a wajen training ya maƙalemin, sai kuma akai rashin sa’a muka tsinci kanmu a waje guda.

        Ganin ya gyara tsayuwa zai fara magana nai gaba abuna. Dai-dai fasinjojin jirgin sun fara fitowa.

     Duk wanda ya fito a jirgin idonmu a kansane, sai dai ganin babu wanda ya motsa daga jami’anmu ya tabbatarmin namu tawagar basu fitoba har lokacin.

      Sai da kowa ya gama fitowa har babu alamar sauran mutane kafin wata mata da yara biyu ta fito, sai wata kuma a bayanta ita riƙe da hannun yaro namiji, sai wata na biye musu baya itama.

        Suma sai da suka sauka duka sannan sannan fitowar wani sadauki da tai daidai da tsananta bugun ƙirjina ya fito.

     Zaratan mazaje uku da doguwa budurwa na biye dashi a baya.

       Jinai ƙafafuna na neman gaza ɗaukata, hakan yasani saurin jingina da ɗaya a cikin motocinmu gudun karna faɗi.2

       Jawaad dake fitowa ya sauke idanunsa akan sir Ahmad barewa, kafin yaci gaba da bin ma’aikatan tadabbaci ke nuna sunzo tarbarsu ne.

     Kansa tsaye inda su sir Ahmad da wasu manya suke suka nufa, inda shima Sir Ahmad ɗin ya nufesu fuskarsa cike da fara’a da farin cikin ganinsu.

        Gaba ɗaya sauran ma’aikatan sukaja layi alamar girmamawa, miƙewa nai ina sauke numfashi tamkar wadda tai gudun fanfalaƙe.

      Sai da ya gama gaisawa da manyansa kafin su nufomu su dukasu.

      A tare muka buga ƙafafu tare da yin salute nasu cikin nuna tsantsar girmamawa.

    

      Jawaad dake tsaye yana ƙare musu kallo idonsa ya sauka kan matashiyar budurwa mai hijjab.

     Ganin ya tsura mata idanu Jabeer da suke bayansa yay mata umarni data cire glasses ɗin idonta a ɗan kausashe.

         Kawai jinai idanuna sun cika da ƙwallan da bansan dalilinsu ba, na zare eyeglasess ɗin idona kamar yanda aka umarceni tsigar jikina na wani irin tashi tamkar nai gamo da halittar ban tsoro.

      Babu zato idanuna suka shige cikin nashi idanun masu wani sinadarin da baki bazai iya faɗaɗa bayani akaiba.

     Kasa jurewa nai na janye nawa ina rissinar da kaina tamkar zuciyata zata faɗo ƙasa.

       Shima cikin basarwa ya janye nasa idanun cikin wani salo na halin ko in kula.

      Sai da ya gama ƙare mana kallo mu duka kafin yay guntun murmushin daya saka kumatunsa loɓawa.

     Saitin inda nake yay mana nuni da hannu alamar mu bashi hanya, hakan ya sakamu darewa muka rabu biyu ya gittamu ya wuce, mayen ƙamshin turarensa na rige-rigen shiga ƙofofin hancinanmu.

       Da sauri wasu a cikinmu suka nufi motocin suka bubbuɗe musu har manyan mu da mukazo tare wajen, ni dai bamma iya koda motsiba daga inda nake, saboda bani da wani ƙarfi sam balle samun kuzarin yin abinda ya dace.

       Sai dai idona akan motar daya shiga shi kaɗai baya aka maida aka rufe masa, haka kawai naji tamkar ana kallona, kallo kuma irin na ƙurilla, sai dai iya dube-dubena banga alamun kowa da idonsa ke kainaba, saboda mutane sunata hada-hadarsu ne.

    Hannu na ɗora a hankali bisa ƙirjina dai-dai saitin zuciyata ina lumshe idanu, wasu ƙananun hawaye suka silalomin a kan kumatu, saurin jan hulata nai sosai yanda zata hana kowa kallon halin da nake ciki kafin nasa handkherchief na share cikin dabara ina nufar mota nima.

     

       Jawaad da tunda ya shiga mota idonsa ke akanta yana ƙare mata kallon da shima baisan dalilinsa ba ya lumshe idanu yana huro iska ta ƙofofin hancin, kuma buɗewa yay sai yaga wayam babu ita a wajen, cikin halin ko in kula yaɗan taɓe baki yana ɗauke idanunsa daga kallon wajen ma baki ɗaya ya maida ga wayarsa.

STORY CONTINUES BELOW

         Tanda muka fara tafiya nake jerama kaina tambayiyin da bansan amsarsu ba.

       “Miyasa nakejin tsoro? Miyasa yay min kwarjini fiye da kowa? Miya sakani kuka? Minene ma’anar halin dana shiga bayan banida wata alaƙa da wani abu daya taɓa shafar irin wannan yanayin dana tsinci kaina a ciki balle nace na tunashine?”.

      Waɗanan tambayoyi su naita jerama kaina har muka iso, tarbar da muka iske an shirya musu ananma ce ta sakani samun damar zare jiki na koma can gefe na zauna ina maida numfashi da addu’ar samun daidaituwar wannan baƙon yanayi nawa da baida alaƙa da komai.

       Dafanin da akayine ya sakani juyowa, Ummie ce, hakan yasa tana zama sai kawai na fashe mata da kuka.

       Ɗunbin mamaki ya bayyana a fuskar Ummie, tai kasaƙe tana kallona tamkar wata sokuwa,

      “Bily lafiyarki kuwa?”.

Ban bata amsaba, saima ƙarfin kukana dana ƙara, tai shiru kawai ta sakamin ido, saida nayi mai isata nai shiru dan kaina sannan ta sake jefamin tambaya.

       “Bilkisu mike faruwa ne wai? Ko an miki wani abune da kuka tafi?”.

      Kaina na girgiza mata alamar “A’a”.

    Tace, “To minene ya faru? Ko baki da lafiya ne?”.

       “Lafiyata ƙƙalau kawai na tuna su babane” na samu kaina da mata ƙarya batare danasan dalilin hakanba, dan nasan bama ɓoyema juna abu sam.

       Numfashi ta sauke tana dafani, cikin tausasa murya ta shiga lallashina damin nasihar addu’a su baba ke buƙata bawai kukana ba.

      Kaina na ɗaga mata kafin nace, “Nagode Ummie, insha ALLAH bazan sake yiba”.

     Tai murmushi tana canja akalar firar tamu zuwa wata,

       “Kutt Bily basawannan namu da kuka tarofa sunji gishiri da magi, musamman mai green ɗin Suit ɗinnan”.

       Gabana ya sake faɗuwa jin ta ambacesa, amma saina danne cikin ƙaƙaro murmushi nace, “Kingani ban wani tsaya ƙare musu kalloba, yanzu haka babu kamannin wanda zan iya kawowa a cikinsu”.

       Tace, “Tab, amma lallai kinyi gwari dan wlhy anci kasuwar sama babuke Babie, ai har sunan mai green suit ɗinma na riƙe”.

        Kallonta nayi da mamaki, tare da jin zuciyata tai zallo, kamar na tambayeta yaya sunan sai kuma na taɓe baki ina miƙewa, “Kinga dan ALLAH bar wannan shirmen tashi muje, yaushe kika fara lalacewa ne haka Ummie?”.

      Dariya ta tuntsire da ita tana dukan kafaɗata, tace, “K nakai aurefa, sannan dukkan burikanmu sun cika, miya rage mana kuma? Musamu mazajen aure kawai, kodan ke kin samu Yah Qaseem a hannune”.

       Kallonta nayi a wani irin yanayi jin ta ambaci yah Qaseem, sai ban iya furta komaiba nai gaba abina ina murmushin ƙarfin hali.

     Itama bata sake maganaba ta biyoni da hanzari muka dai-daita tafiyarmu.

           Da ɗan aiken Yah Qaseem mukai karo akan naje yanason ganina.

      Haka kawai sai naji kiran yaban haushi, amma bani da damar ƙin zuwa ɗin.

       Na kalli Ummie ina faɗin, “Dan ALLAH ki rakani tawan”.

      Baya tai tana zaro idanu, “Wa? Rufamin asiri hajiyata, wannan fagen na masoyane ai, aidai ƙone ƙaɗan babie kar ai ƙurmus dan ALLAH”.

         Harara na zuba mata kafin na wuce ina zare hular kaina na riƙe a hannu.

       Koda na isa Office ɗin nasa kaina tsaye na shiga, dan ya bada sharaɗin shigata babu shamaki.

         Kallo ɗaya naima fuskarsa na fahimci ransa a ɓace yake, na zauna ina gaidashi cikin girmamawa kamar yanda na saba.

        Bai amsaba sai numfashi daya sauke, ya taso daga kujerarsa ya dawo inda nake shima ya zauna a ɗayar kujerar dake kallon wadda nake kai.

      Idanu ya tsuramin kusan minti ɗaya, niko na gaza kallonsa saima takura da nayi, cikin son katseshi na shiga gaishesa.

      Nanma numfashin ya kuma saukewa yana janye idanunsa a kaina.

      Ba tare dana kallesanba nace, “Yah Qaseem lafiya dai ko?”.

     Siririn tsaki yaja yana haɗawa da ƙaramar ƙwafa, “inafa lafiya wannan banzan ya dawo”.

      Da mamaki nace, “Banza kuma? Wanene banza yah Qaseem?”.

     Tsakin ya kuma ja yana maido kallonsa kaina, “Bazaki taɓa ganewaba, dan haka share, ina kikaje ɗazun na aika kiranki akace kun fita?”.

        Zamana na gyara cikin rashin damuwa nace, “Ba inda naje, kawai tarbar waɗanan jami’an namu da suka dawone………”

      “Kina nufin dama dake akaje?”

   Yay maganar cikin tare numfashina tamkar zai haɗiyi harshensa.

         Da mamakinsa na ɗaga kaina kawai.

      Sosai ɓacin rai ya kuma bayyana a kan fuskarsa, ya furzar da ɗacin da nakeda tabbacin yanaji tare da miƙewa.

     Nidai uffan bance dashiba saima kallo dana bisa dashi kawai.

     Bansan miya tunaba ya juyi yana faɗin in tashi muje muci abinci.

    Tashin kuwa nayi, ya fita ina biye dashi, koda muka fito a Office ɗin sai ya tsaya muna tafiya a tare.

           Bugawar da zuciyata tayine ya sakani komawa tafiya da sassarfa, ɗago idon da zanyi idona suka sauka akan mutumin ɗazun da mukaje tarba.

        Da ƙyar na iya haɗiye yawun daya tsinkemin a cikin baki saboda kallon ido cikin ido da mukaima juna, amma sai ya janye nashi tamkar bani yake kalloba ya shige motar da aka buɗe masa wadda alamomi suke nuna zai tafi gidane maybe.

         Nannauyan numfashi ya kufcemin wanda yay dai-dai da fitar sautin jan tsakin da Yah Qaseem yayi………..✍🏻

Ga shafi na 35 nan, saura biyar a jakata bazan zuge zip ba sai naga ruwan subscribers😎🏃🏃💃🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻6Shafi na talatin da shida

………….Har muka isa wajen da kullum Yah Qaseem ke kaimu cin abinci anan kusa damu fuskarsa babu walwa, bama muba kusan duk anan manyan jami’an kecin abincin, dan wajene haɗaɗɗe da yasha gyara na musamman, sanan ake abinci mai tsafta da daɗi, sai dai kamarmu ƙananu da ƙarfinmu bai kaiba akwai wani gidan abincin daga ɗayan gefen mukanfi yawan zuwa acan muci.

       To nidai bamma taɓa zuwa wancan ɗinba, dan kullum nan Yah Qaseem ke kawoni, idan kuma aiki yay masa yawa yakan saka akai masa office muci acan kamar yanda wasu daga cikin manyan keyi.

        Kallon bawan ALLAHn can da yaymin lokacin dazai shiga mota ya mugun tsayan a ƙahon zuciya, duk yanda naso turesa hakan ya gagara, sai sauke ajiyar zuciya nake ina tsakurar abincin badan yaymin daɗiba.

     Shi kansa Yah Qaseem na lura bawai cin abinci yakeba sosai yau, dan ransa a ɓace yake, na kuma rasa dalilin hakan sam.

      Haka dai muka tsakura sama-sama muka bar wajen, kafin mu wuce na roƙesa muyima Ummie takeaway.

      Atm ɗin nasa ya miƙamin kawai ya fice, na bisa da kallo ni dai kafin na amsar mata abinda nasan tanaso na fito, sai dai zuciyata na mamakin miya fusata yaya Qaseem haka wai ne?.

     Ban iskeshiba hakan yasa na tafi ni kaɗai, dan da alama ya shige abinsa.+

        Yau bamu bar Office ba sai kusan takwas na dare, tare da Yah Qaseem muka tafi gida, sai lokacin ne na bashi ATM card ɗinsa, inason tambayarsa mike damunsa? Amma wani gefen zuciyata na karantamin na sharesa kawai.

       Sharesan kuwa nayi nama maida hankali wajen cheating da Rebecca da taimin magana.

        Har muka isa gida ni da shi bakin juna bai saɓaba, yanata driving ɗinsa, duk da na lura akwai tuƙin ganganci a ciki, wanda na jima da fuskantarsa ya haddace gudu a titi tunba yanzuba.

        Amina ta taɓa bani labarin yanada driver da aka bashi na office da, sai dai rashin haƙurinsa yasa ya sallami direban, ya gwammaci ya tuƙa kansa da kansa.

     

★★★★★

          A gidanma haka yayta tsumewa, nidai koda na gaida su Mummy dake falo ɗakina na shige, dan yanzu ganin batason sakarmin fuska sai na sake janye mata, aikin dake a gabanama ya isheni gayya basai an haɗamin da damuwa mara dalili ba.

        Sai da nai wanka naji daɗin jikina sannan na fito falon domin neman abinci, ganin abinda aka dafa a gidan, ni kuma ba sonshi nakeba sai kawai na haɗa tea.

     Ina daga dani ina shan tea ɗin nake jiyo hirar Mummy da yaranta, harda Yah Qaseem daya zama ginshiƙin hirar, shima da alama yana yin wanka fitowar yayi, jinai yana sanar mata wai Jawaad ya dawo.

          Da yake ban fahimci kan maganar tasuba sai bansan akan wa yake maganaba, ni dai nayima na tashi na shige ɗaki abuna dan na kwanta na hutama rayuwata.

     Dan tunda na fara aikinnan Yah Qaseem ke tafiya dani da dawo dani a motarsa Mummy ke haushi dani, inaji ranar tana masa faɗa akan hakan, harma da gargaɗi akan ya fita harkata, inba hakaba kuma yay kuka da kansa.

     Bandaiji ya tanka mataba, bai kuma fasa ɗaukata a motarba.

     Niko ina ruwana, tunda bani tama gargaɗinba banbi takai ba na cigaba da binsa kamar yanda Dad ya faɗamasa ya ringa tafiya dani da ɗakkoni tunda ALLAH yasa wajen aikin namu ya kasance ɗayane.

_________________________

JAWAAD

_________________________

           Tarba maiban mamaki Jay ya samu ga ahalinsa, dan kuwa hardasu Umma duk sun taru a family house nasu.

      Danne mamakinsa yay shima ya nuna girmamawa ga wannan tarba tasu, bayan gama amsa sannu da zuwa suka bashi damar shiga sashensa domin watsa ruwa.

        Kaya yake cirewa yana jan ƙaramin tsaki shi kaɗai.

     “bansan miya kawo dalilin yawan tsakinba ni kaina, sai dai mucigaba da bibiyar jay ko zamu sami amsa”😉😹⛹‍♀.2

          Yanda aka gyara sashen da ƙamshin da yakeyi ya ƙayatar dashi, sai dai yanaji a ransa aikin nan sai dai idan batool ɗin Umma ko Nabeelah wani yayisa.

     A wajen wankanma ya samu nishaɗi saboda yana son tsafta a rayuwarsa, ya dai gama ƙaƙale-ƙaƙalensa ya fito ɗaure da tawul yana tsane jikinsa da ƙarami.

        Sosai jarumin na Shahudah ya kuma canjawa, dan dai-dai da gaɓoɓin jikinsa sun sake murɗewa, ga wata gogewa da fatarsa ta sakeyi, yanda ruwa ke gudu a jikinta zai tabbatarma da mai kallonsa hakan.

       Komai yana yinsane a yanayin gajiya, inda son samune kwanciya zaiyi ya hutama ransa basai ya sake fita a waccan hayaniyarba.

     Amma yaya ya iya, dolene ya koma kamar yanda suka buƙata tunda sunce danshi suka taru.

      Sama-sama yay ƴan shafe-shafensa ya saka wando da riga ruwan siminti marasa nauyi, kayan sun masa ƙyau tare da fidda ainahin ƙirar da UBANGIJI yay masa, ya fesa turare kaɗan sannan ya fito harabar gidan daga can baya inda dama anyi wajenne domin hutawa, an gyarashi sosai da korayen ciyayi da filawoyi masu ƙamshi.

      Sam Jawaad baya zuwa wajen, saboda ƴammatan gidan sun maidashi lambun shaƙatawarsu ko ajiye samarinsu suyi hira, shi zaima iya rantsewa tun bayan daya mallaki hankalinsa baizo wajen sau ukuba, mantawama yake dashi gaba ɗaya, zuwa ukunma da yake kyautata zaton yayi shima duk mitin ne da Uncle’s nashi suka shirya ya halarci wajen a wancan lokutan..

         Sosai kuwa walimar cin abinci aka shirya, sai dai ya fahimci tamkar da biyu ne, danshi jami’in tsarone mai matuƙar basira da kaifin tunani, hakanne ya taimaka masa wajen gayyato ɗunbin nasarori a cikin rayuwar aikinsa.

     Yanda ƴammatan Family ɗin nasu kowacce taci ado na ƙure wankane ya sashi fahimtar komai a buɗe.

         Yay ƙwafa a zuciyarsa kawai yana sake shan toka, baisan miyasa akeson takurama rayuwarsa da awaɗanan yaranba, dan haka sukai maƙurar takura masa ta waya yanacan, kullum babu fashi sai yaga text messeges nasu ɗaya bayan ɗaya, harda masu masa a shafukansa na yanar gizo.

      Bai taɓa kula koda ɗayarsu ba, danshi a ganinsa hakan rainine.

        Ƙin cin komai yayi a wajen sai kunun aya kawai, wanda Batool ta tabbatar masa itace ta haɗa masa shi, dan dogon tabirne aka ajiye sannan aka zagayesa da kujerun da adadainsu yakai Hamsin koma fin hakan, manya maza da mata na family ɗin kowa ya samu muhallin zama, su kuma yaran an shimfiɗa musu leda mai ƙyau a ƙasa anan suke nasu shagalin bisa kulawar ma’aikatan gidan.

      Sai da ya gaji da harar da Umma ke masa akan cin abinci sannan ya ɗau cokali badan yaso ba ya fara cin abinda yasa aka zuba masa cikin nutsuwarsa.

      Sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska ya saka dukkan ƴammatan dake fama da rawar kai suka nutsu, dan dama sunsan shi baya son wargi, bakuma shiga sabgarsu yakeba tun fil azal.

       Sai dai sai faman satar kallonsa suke ta wutsiyoyin idanu, shiko baima san sunaiba, abincinsa yakeci yana ɗan jefa magana cikin hirar mazan gidan sa’anninsa.

       Dukda shine ƙarshen fara cin abincin shine kuma farkon fara ajiye cokali, babu wanda bai bisa da kallon mamakiba amma sai ya fuske cike da basarwa kamar baisan miya aikataba, sam saima yaƙi kallon sashen Ummah balle ta sake sakashi tilas akan yacin.

           

         Abubuwan da Jay yakeyi ba ƙaramin ɓata ran Uncle’s nashi sukeba, amma duk sai suka danne zukatansu da addu’ar ALLAH yasa karya watsa musu ƙasa a idanunsu yadai zaɓi matar aure kamar yanda manufar taron take.

       Dukanin tunaninsu bai gama tsayawaba sai da Jawaad ya miƙe bayan mintuna biyar da ajiye cokalinsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yay musu sallama tare da miƙa kalamun godiya na wannan tarba daya samu daga garesu, yay addu’ar sake samun haɗin kai na wannan family mai ɗorewa, tare da jaddada musu abinda sukai masa yau din ya ƙayatar dashi kuma ya bashi farin cikin da bazai mantaba har sai ya rubutashi ya ajiye.

        Kowa fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallon Jawaad ɗin, kowa yaji daɗin kalamansa kuwa, dan basuyi zaton jin hakan daga gareba.

       Shikuma yay wani munafikin murmushin da ya kusa zautar da dukkan ƴanmatan wajen,  shikuma shi kaɗai yasan ma’anar kayansa, kafin ya nema alfarmar tafiya domin ya huta saboda ciwo da kansa ke ɗan masa kaɗan-kaɗan na alamar gajiyar tafiya.

           Basu da yanda suka iya dashi, amma dai Uncle Nasir ya dakatar dashi har ya miƙe yay ɗan guntun bayani na sake masa sannu da zuwa, tare da roƙon Jawaad ɗin ya sake jikinsa tare da yafema duk wanda yake ganin ya masa ba dai-dai ba akan abinda ya faru wancan karo har yayma gidan yaji na kusan shekara.

       Nanma dai godiyar Jawaad ya sakeyi sannan ya tabbatar musu shi komai ya wuce a ransa tuni, suma yana fatan hakan daga garesu, daga ƙarshe yay musu sallama ya koma sashensa.

       Murmushi kawai Umma tai tana girgiza kai da bin Jawaad ɗin da kallo harya ɓacema ganinsu.

         Barinsa wajen ya saka taron ya fara watsewa a hankali, mafi yawansu zukatansu babu daɗi a ciki, musamman ma ƴan matan da suka ƙwallafa rai a kansa babu gaira babu sabar.

      Shi dai baimasan sunaiba, dan yana barin gurin ƙwafa yay yana maijin takaicin rainin da ake neman jawo masa wajen yaran gidan, zama yay a falon yana jiran shigowarsu Umma domin su gaisa kafin ya kwanta.

         Zaman nasa kuwa baifi da mintuna goma ba sai ga Umma dasu batool sun shigo.

     Dariya Batool ta fara masa tana tafa hannaye.

     Harara yaketa zabga dan yasan tsokanarsa zatayi, mata amma baice komaiba, dan itace kawai ke iya taɓasa kasancewar sa’anni suke dashi ta kwana lafiya, wani lokacinma har yakan biye mata, batool bata taɓa aureba, munadai tayata fatan samun miji na gari.

       Ɗauke idonsa yay akan Batool ɗin data zauna a kujerar gefensa tana faɗin, “Kaga mai ƴammata buhu-buhu na Shahudah bada kanka a sare kazo gida kace ya faɗi”.

          “Umma ALLAH kicema yarinyarnan ta kama kanta kota fita falonnan da ƙafa guda”. Jay yay maganar cikin matuƙar ɓata fuska.

     Murmushi Ummah dake zama tayi, yayinda Batool ta bushe da dariya, hakama su Nabeelah duk sai gyale sukasa suna kare fuska dan karya gani.

        “Manta da ita kaji My son, yau ba ranar ɓata fuska bace ba, ina fatan dai ka dawo cikin ƙoshin lafiya?”.

       Numfashi yaɗan sauke mai haɗe da ajiyar zuciya yana faɗin, “Alhmdllh Ummana, sai dai kewarku kawai, yaya jikin Baba?”.

       “A jikinsa Alhmdllh, ai yama samu sauƙi dama murace ta canjawar wannan yanayin, sai kuma jikin tsufa da aketa rarrakawa”.

        Jawaad yace, “ALLAH sarki baba, ALLAH ya ƙara tsahon rai”.

     Da amin suka amsa su duka.

     Su Nabeelah suka sake gaidashi cikin girmamawa, yayinda shima yake amsawa da ƴar kulawa.

    Batool kam cayay bazai amsa mata gaisuwaba.

     Tace, “Karka amsa mana Jay, duk dai wani ɗacin ranka kayisa ka gama Aurene sai anyi makashi, danni harma na zaɓa maka waɗanda suka dace dakai a ƴammatan nan da aketa faman maka talla kana wani fuskewa, auren gata zamuyi maka, ƴammata uku zuƙa-zuƙa sai Shahudah uwar gida ran gida”.

        Remote dake center table ya ɗauka ya jefeta dashi, ta tashi ta fice daga falon tana dariya, shi kuma ya kuma haɗe fuska yana ƙwafa.

     Su Nabeelah ma dai ficewa sukai dansu bashi waje ya tattauna da Umma.

           Dariya Umma ma taɗanyi kaɗan tana faɗin, “Da gaskefa Fatima keyi, waɗanan yaran daka gani dansu aka shirya maka wannan tarbar, ni kuma naga bakama nuna wata alamar zaka zaɓa ɗinba”.

       Cikin takaici Jay yace, “Na sani Ummah, amma dan ALLAH karku biyema shirmensu, zan kuma taka musu birkine dan wannan neman jawomin rainine wajen yara kawai, bansan minene matsalarsu da aurena ba ko rashin yinsa? Nace musu ina buƙatar aurene ko yaya? Za’a wani ringa cusamin yara ƙanan kamar wani ɗan iska……”

       Cikin tare masa numfashi Umma tace,  “Dole zaka buƙaci aure Jawaad, dan koba komai ka rigada ka ɗanɗani zama da mace, kuma koba hakaba ma cikar mutuncinka shine auren, babu wanda zaka sanarma kai kamiline ya yarda bayan mu da mukasan kai wanene, ka daure koda ba’a cikin yaran nasuba ka sami matar aure, idan kuma matarka kakeson maidawa ka maidota dan maybe ta canja zuwa yanzu, tunda na fahimci son da kake matane ya hanaka sake kallon wata mace da sigar auren, baba kansa yana damuwa sosai da rashin sake aurenka, shekarafa huɗu kenan da wasu watanni da rabuwarka da matarka, da aurenma kayi ƙila da yanzu ƴan jikokinmu na kai kawo a falonnan, sannan akwai wasu takardun dukiyarka masu matuƙar muhimmanci dake da alamar tambaya, dan sune silar komai da lokacine kawai zai buɗe kowanne sirrin da mu da kai zamu fahimta baki ɗaya….”

          Shiru Jawaad yay yana nazari dason ƙarin bayani akan maganarta ta ƙarshe, sai dai bata bashi wata damar masa tambaya akan hakanba, shiyyasa yay shiru yana kallonta, sai kuma ya sauke numfashi yana faɗin, “Shikenan Ummah, kuyi haƙuri indai aurene zanyi da izinin ALLAH, duk da har yanzu babu wata mace a raina, kuma ba hasashenku bane ya hanani aure na cewar son Hudah ne har yanzu, sai dai kodan farin cikinku zanyi insha ALLAH, amma ku kwantar da hankalinku ku bani lokaci, dan banason a sake komawa ƴar gidan jiya kamar aurena na baya”.

         Umma tace, “To ALLAH ya tabbatar mana da alkairi. ya kuma kawo mana ta gari wadda zata zo mana da alkairai”.

       Bai iya ce mata komaiba, dan gaba ɗaya sun dagula masa lissafi, basu san yanda yakejin haushin mata bane a ransa da sunbar ambatar aurenan da suka damu ransu akan sai ya ƙara…………..✍🏻

4

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

        Shafi na talatin da bakwai

…………Bayan shigewar Qaseem da Bily babu daɗewa Mummy na zaune tana saƙawa da kwancewa ta yanda zasu ɓulloma zaman Shahudah da Jawaad kira ya shigowa wayarta.

      Ɗauka tayi babu ɓata lokaci, dan kuwa kirane mai matuƙar muhimmanci.

      Sama-sama sukai gaisuwa mai kiran ta fara zayyane mata abinda ya faru a family house ɗin su Jay a yau, wato dai walimar cin abincin da aka shirya masa mai taken yaɗa manufar tallar matan aure.

      Ran Mummy ya ɓaci ƙololuwa, dan a ganinta wannan tsagwaron munafurci ne kawai ƴan uwan nata suka shirya, taya zasu nema aikata haka?, bayan sunsan akwai soyayya mai ƙarfi tsakanin Shahudah da Jawaad ɗin, saɓanine kawai da sharrin shaiɗan ya gitta har wancan matsalar ta faru, maimakon su nema hanyar da za’a sulhunta shine zasu haɗa wannan annamimancin? To lallai lokaci yayi da za’ai uwar watsi kuwa ashe, yanzu ace har mahaifiyarsu ta gaza kiranta ta sanar mata balle ƴan uwanta su Uncle Uwaisu, dan bata saka Maimuna ƙanwarta a wannan sabgar, tunda tuni ta nuna musu bata tare dasu ita dama.

      A wannan dare gaba ɗaya barci gagarar idanun Mummy yayi, gashi Dad baya gari, tayi kiran wayarsa yafi sau goma taƙi shiga, ta kuma kira Mama Atika ba’a ɗaukaba, ta kira Shahudah shima bai shigaba.

     Gaba ɗaya sai kanta ya ƙara ɗaukar zafi, sai sauke ajiyar zuciya takeyi a jere a jere.+

        Gari na wayewa duk da uban barcin dake cin idanunta haka tai shiri tunda farar safiya ta fice a gidan, ko jiran driver bata tsaya yiba, dan aganinta kafin yazo an gama ɓata mata lokacinta.

         Tun shigowarta falon mama Atika dake zaune tana lazimi ke kallonta, Mummy sai sake cika take tana batsewa, ganinfa mahaifiyartasu ba ida addu’ar nan tata zataiba ya sata faɗin, “Wai nikam mama wannan addu’ar bata ƙarewa ne?, nifa a ƙage nazo”.

      Mama Atika batace mata komaiba, hakama bata tsaya da addu’arta ba sai da takai aya, ta shafa tana faɗin, “Ke dai Wlhy Ai’sha sam baki da ɗabi’ar ƙwarai, ba ƙaramin lalacewa rayuwarki taiba a garincan na marasa sallah, mike faruwa na ganki da wannan uwar safiyar?”.

         Cikin sake ɓata fuska Mummy tace, “Ba dole ake ganina da farar safiya ba, yanzu mama dan ALLAH munafurcin da ake shirin ƙullawa ya ƙyautu kenan a gidannan?, kowa yasan alaƙar dake tsakanin Shahudah da yaron nan na wajen Abdul-aziz, amma shine za’a shirya wani annamimanci ta bayan fage ba tare da nasaniba ma……..”

      Saurin katseta mama Atika tai da faɗin, “Ke da ALLAH rufama mutane baki, waye zai sake haɗa sabgarsa da wannan shashashar ƴar taku mai kama da wadda aka yaye jiya, idan barci kike to kidawo hankalinki Ai’sha, badan wawiyar yarinyarnanba da yanzu mun gama mallakar fiyema da abinda muke buƙata, amma tazo ta ɓata mana komai saboda ita shashashar yarinyace taɓararriya, ki duba yanzu wulakancin data jawo mana ne ya saka dukkan manufofin mutan gidannan ya gama bayyana, yanzu kowama yima ƴarsa farautar yaron nan yake, dan dama can shakkatane ya sakasu haɗiye ƙwaɗayinsu a fili, dukda wasunsu na taƙamar komai yana hannunsu ne ai, maimakon kuma a shekaru huɗun nan ku nema hanyar gyara komai tunkan abunma yay nisa ta bashi haƙuri amma sai kuka ɗauketa kuka sake turawa cikin yahudawa, kekuma kika ɗauki fushi damu, yanzu har nai ciwona na gama a gidannan Ai’sha baki leƙoniba, saboda ke mai ƴa ko? To mune muka saketa? Kokuwa mune muka sakashi sakinta? Muda ta ɓatama komai mune ya dace muyi fushi ba keba? ai ko…….”

       “Nidai mama naji, ya isa dan ALLAH, sai faɗa kike ko haɗiyar yawu baƙyayi, naji anyi kuskure, amma kuma ai bai ƙyautu a wancan karon kowa yaƙi fahimtar ƙaddarace sanadin komai ba, ALLAH ya rubuta cikinnan bazaizo duniyaba, daga baya kuma dai ai komai ya dawo ya daidaita, amma sai babu wanda ya kirani a cikinku, ta yaya bazan ɗauki fushiba to?”.

        “Kedai kika sani, ai kuma fushin naki bai miki amfaniba, tunda gashi kin dawo da ƙafarki ko?, kuma a lokacin da kuka makara keda ƴar taki, dan kuwa a yanzu filin dagar ya zama na mafarauta da yawa”.

         “Mama ki daina faɗin mun makara, babu wata makara tunda kowa yasan Jawaad nason Shahudah, kuna insha ALLAHU a cikin watannan zata dawo ƙasarnan”.

      Baki mama Atika ta taɓe da yamusashshiyar fatarta ta tsufa, tace, “Kudai kuka jiyo, danni tawa tai ƙyau, dama kune masu amfana baniba, a shekaruna ni yanzu amfanin mi abinda akemawa ɗin zaimin?, komai da kukaga inayi danku nake yinsa”.

      Shiru itadai Mummy tayi bata tankaba, tana nan zaune har su Uncle Uwaisu suka shigo gaishe da mama Atika, annanfa suma Mummy ta balbalesu da masifa, ta inda take shiga ba tanan take fitaba.

      Wasa-wasa rigima ta kaure a tsakaninsu, dan kuwa yanzu suma ba ɗaga mata ƙafa zasuyiba duk da tana babbar yarsu a ɗakin, duk yanda mama Atika taso suyi shiru sunƙi, har sai da ta saka musu kuka sannan suka dawo hankalinsu sukai shiru.

__________________________________

         To nidai sam bansan bikin da akeba a gidan, naji dai Aunty Aamilah na magana akan Aunty Shahudah zata dawo, banji an faɗi rana ba, bakuma a faɗaminba, nima sai banbi takaiba, dan bakowace sabgar gidan nake shigaba musamman ma yanzu danasan ciwon kaina.

        Tsawon kwanakin da suka biyo baya a satin ban sake jin komai na faɗuwar gaba ba, hakama wanda muka taro a ranar nan ban sake ganin koda ɗaya a cikinsuba.

       Duk da abubuwa masu yawa game dashi sunƙi barin raina, duk kuma ƙoƙarin turesun da nakeyi hakan baisa na damu kaina da rashin ganin nasa ba, na cigaba da harkokin gabana har a yau da mukai safiyar fita aiki kasancewarta Monday tushen aiki.

       Kamar kullum nayi tsaf dani, tamkar ka saceni ka gudu, musamman ma data kasance a yau sanye nake da baƙaƙen suit na mata wando da riga, na kawo farin baby hijjab na saka tamkar yanda na saba a kowace rana, kayan sun zaunamin sosai a jiki tamkar dan jikin aka haliccesu, na saka siririn farin eyeglasess ɗina sannan na fito ɗauke da takalmana a hannu.

    Babu kowa a falon, na ajiye takalman na nufi kicin, kuku harya kammala haɗa mana breakfast ni da Yah Qaseem, tea na shiga haɗawa muna gaisawa dashi, ban fitaba na zauna a ɗaya daga kujerun huɗun dake a kicin din, tebir a tsakkiyarsu, ina fara shan shayin Yah Qaseem na shigowa shi da Salman.

      Nayi mamakin ganin Yah Salman da wannan farar safiyar, shi da kullum sai anyi fama dashi ma yake tashi da safen yay shirin zuwa aiki, da yake a kamfanin Dad yake aikin sai yakai goma bai fitaba ma.

       Hannu Yah Qaseem ya miƙomin alamar mu gaisa, amma sai na girgiza masa kai ina murmushi da faɗin, “Yaya ina kwana”.

      Hararata yayi sannan ya zauna, Yah Salman da shima ke zama ya taɓe baki.

      Shima gaishesa nayi ya amsa a ɗage kamar yanda ya saba.

       Ban sake bi takansuba naci gaba da shan tea ɗina nidai, suma kowanne ƙoƙarin karyawan yakeyi.

        Ban wani ci abincin kirkiba na tashi na koma falo na barsu a kicin ɗin, ina ɗaura takalmina sai ga Yah Qaseem ɗin ya fito yana faɗin, “Tashi muwuce mun makara”.

      Miƙewa nayi muka fice.

★★★★★

         Yayin da muka isa office ina fitowa daga mota da shi na fara tozali.

    Hakanne ya saka gabana faɗuwa, ganin bamu yake kalloba na ɗauke kaina daga garesa, sai ta gefen ido nake satar kallonsa, sanye yake da jeans ruwan toka da farar shirt mai gajeren hannu, idanunsa sakaye cikin glasess da yay masa matuƙar ƙyawu.

    Dole inda suke tsaye shi da wani a jikin wata mota itace hanyar da zanbi ta kaini inda zanje, sai kawai na canja hanya saboda yanda nakejin gabana na cigaba da tsananta faɗuwa.

      Nidai nasan ba tsoro bane ba, sai dai yanamin kwarjini da zan iya rantsewa wani ɗa namiji bai taɓamin irinsa ba, bansan miyasa hakanba? Bankuma san minene dalilin hakanba?.

     Hanya na canja, sai dai inajin tamkar ana bina da kallo, juyowa nayi kaɗan dan inga ko zanga mai kallon nawa, sai dai banga kowaba.

     Na cigaba da tafiya ina karanto addu’ar duk da tazomin kan harshe.

      Ikon ALLAH tunda nayi nesa da wajen dana gansa sai na koma normal, harna ƙarasa wajen da nake ƙyautata zaton ganin Ummie.

        Ɓangaren Jawaad kam da a yau suka dawo aiki shi da tawagarsa, ya iske ayyuka da dama, musamman waɗanda suke da matuƙar haɗarin da ake buƙatar mutum mai ƙwazo da jajircewa irinsu, wasu ayyukan kuma an badasu ga wasu jami’an ne amma sunata musu tafiyar hawainiya basu ƙarasaba babuma wani bayani mai gamsarwa, hakan yasa yau aka miƙasu gaban su Jawaad ɗin.

       Kansa yaɗauki zafi da ganin ayyukan dake jibge a gabansu, duk da kuwa a yanzu sun sake samo dabaru na musamman shida abokan aikinsa da suka samu zuwa wannan horo na musamman a ƙasar amuruka, ya kuma dawo ne da karsashin aikin canja wani abu a ƙasarsa dan bai isa canja komaiba shi yasan wannan, irinsu masu son jajircewa ƙalilanne, tayaya kuwa suka isa canja komai? Sai dai suyi nasu ƙoƙari su koma gefe, UBANGIJI shike da sauran hanyoyin maganin sauran tunkafin nasu, rahamarsace ta saka zukatansu suma jin son gyaran.

      Baƙon da yayi wani abokinsa da sukai secondary tare lauya, yazone bincike akan wani case shine ya rakoshi suka tsaya a jikin motarsa suna magana.

     Sarai Jawaad yaga lokacin da Qaseem da Bily suka fito a motar Qaseem ɗin, amma sai ya ɗauke kansa cikin basarwa, duk da a ƙasan zuciyarsa yana tunanin minene alaƙar Qaseem da wannan yarinyar? Saboda a koda yaushe yake ganinsu tare da juna.

     Sai kuma akai rashin Sa’a shima abokin nasa idonsa suka hango su Bilkisun.

   Yace, “Woow, Jay kaga wata ƙyaƙyƙyawar halitta mai tsada da daraja kuwa?”.

      Jawaad da ras ya fahimci inda abokinsa ya dosa tsabar rainin wayo sai yay tamkar bai fahimtaba…………✍🏻

2

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Shafi na talatin da takwas

…………..Bayan wucewar abokinsa office ɗin Sir Ahmad ya wuce domin amsa kiransa, yana ƙoƙarin shiga yaci karo da Qaseem shima ya fito.

       Ƙoƙarin ɗauke kai Qaseem keyi, shima Jawaad ɗin har yayi niyyar hakan, sai kuma yaga rashin ƙyautuwar abun, Murmushi ya saki har kumatunsa na loɓawa, ya miƙama Qaseem hannu yana faɗin, “Assalamu alaika”.

     Ƙin miƙo nasa Qaseem yayi, sai dai ya amsa masa sallamar.

      Jawaad ya kamo hannun Qaseem cikin nasa tare da faɗin, “Haba ɗan uwana, miyay zafi shiba wutaba? Ina fatan na sameku lfy? Ya jama’ar gidan?”.

        Ran Qaseem ya sosu da wannan rainin hankali na Jawaad, danshi matsayin rainin hankali kawai ya kalli abun, dan haka ya kasa daurewa yace, “Da wannna salon kuma ka dawo?”.

       Jawaad ya murmusa yana sakin hannunsa, cikin gyara tsaiwarsa yana shafa gemu da tura hannunsa ɗaya a aljihu yace, “Minene abin salo anan Qaseem? Kaifa ɗan uwanane jinina, sannan ga alaƙar musulinci a tsakanina dakai, kuma kai yarenane, ogana a wajen aiki, shekara biyu rabon da ka ganni na ganka, da akwai ƙaddarar mutuwa tsakaninmu maybe wani zai samu saƙon mutuwar wanine a tsakaninmu, nidai tsakanina da ALLAH na gaisheka, ya rage naka ka ɗauka hakan kaima ko saɓaninsa, na barka lafiya”.. 

       Sagade Qaseem yay yanabin Jawaad da kallo harya shige office ɗin Sir Ahmad, yayi kamar ya bisa cikin office ɗin sai kuma ya fasa, ya nufi office ɗinsa yana juya kalamun Jawaad cikin ransa.

              Jawaad kam koda ya shiga, bayan yayi gaisuwar girmamawa ga sir Ahmad sai ya nuna masa wajen zama.

         Hannu Sir Ahmad ya bashi cikin musabaha suka sake gaisawa, dukda dai Jawaad na nuna jin kunyar haka ɗin.

        “Jay kasan miyasa na kiraka kuwa?”.

       “A’a Sir”. ‘Jawaad ya faɗa cikin kaɗa kai’.

         Zama sosai Sir Ahmad ya gyara, ya fara magana idanunsa akan Jawaad ɗin.

        “Wato zakayi mamaki idan nace maka baƙin abubuwa da yawa sun sake shigoma hukumarnan, masu ban tsoro da mamaki. Akwai cases da yawa dakai kanka ka fara ka tafi kabari to ina mai tabbatar maka da yawansu ba’a ƙarasa suba har zuwa yau da nake maka maganar nan, waɗanda kuma aka ƙarasa ɗin sun canzu ga bisa salon daka barsu gaba ɗaya ma. Gashi wasu cases ɗin sun sake ƙaruwa da yawa, akwai jami’inmu mai matuƙar ƙwazo kamar kai ɗinnan, bayan tafiyarku nagartarsa ta sake fitowa, amma kamar yanda na sanar maka ranar ya fita wani aiki sai dai gawarsa aka kawo mana, kasan wani abun mamaki?”.

        Jawaad da idonsa ya kaɗa yay jazur ya girgiza kansa.

     Murmushi Sir Ahmad yayi na takaici yana cigaba da faɗin, “Abun mamakin da har yanzu yake cizon zuciyata shine bullets guda uku da aka harbi Abdallah dashi a ƙarjinsa da cikinsa dukansu bullets ne na jami’an tsaro, abi mafi al’ajab Bullets ɗin suna cikin bullets guda dubu sittin da shida da aka kawo ƙasarnan shekaru tara da suka wuce, waɗanda a zahirance bayanai sun nuna bullets ɗin sun ƙare gaba ɗaya bayan shekara ɗaya da wata bakwai da kawosu, bullets ne masu matuƙar haɗari, dan inhar akai harbi mutum dasu acikin seconds ashirin dukkanin illahirin jinin mutum ke tsinkewa, idan ba’ai gaggawar kaisa asibiti ba ya samu taimakon gaggawa zai iya rasa ransa a ƙanƙanin lokaci, sannan ba a kowacce bindiga yake aikiba. To abin tambaya anan, yaya akai bullets ɗin da suka ƙare shekara huɗu baya kuma suka kashe mana jami’inmu? Daga ina suka fito? Wasune aka sake shigowa dasu? Koko dai sune ɗin?”.

          Gaba ɗaya jijiyoyin Kan Jawaad sun mimmiƙe ruɗu-ruɗu, maƙoshinsa sai kaikawo yake a wuyansa saboda tsabar haɗiyar busashshen yawu mai ƙona zuciya.

     Ya matse idanunsa tare da rumtse hannu, muryarsa a matuƙar kausashe yace, “Sir akan wane case wannan abun ya faru?”.

         Sir Ahmad yay murmusa idonsa akan Jawaad, mazantakar Jay akan aiki da kishin ƙasarsa yasa ako wane lokaci yafi sha’awar ganinsa akan aiki na musamman, yaɗan ɗage kafaɗa yana buga tebir kaɗan da komawa cikin kujera ya kwanta, har lokacin idonsa akan Jawaad,

       “Jay ƴan bindiga daɗi ne kawai, amma ga dukkan bayanan komai anan”. ‘Ya ƙare maganar da tura masa wani file gabansa’.

        Ɗauka Jay yayi ba tare daya buɗeba, babu abinda zuciyarsa keyi sai tafarfasa kawai, shiru Office ɗin yayi na wasu mintoci, kafin Sir Ahmad ya katse shirun da faɗin, “A yanzu kana buƙatar runduna ta musamman Jay, fiye dasu Jabeer kawai, munada sabbin ma’aikata masu jini a jika da karsashin aiki a ransu saboda yanzune jinin jikinsu ke zagayawa cikin kowacce jijiya dalilin ƙuruciya da zafin rai mai tare da ɗokin aikin, sannan a cikinsu akwai kwararrun maharban da suka samu horo na musamman a ɓangaren harbi, wanda an daɗe ba’a yaye sabbin horaswa da wannan ƙwazonba a hukumarnan tamu, shawara kawai na baka ba umarniba, dan zuciyata ta yarda da kai, yarda irin wadda ko ɗan dana haifa ban yimawaba duk da kasan cewarsa jami’in tsaro shima, ALLAH yayi jagora haziƙi kuma jarumin yarona abin alfaharin ƙasarsa da ƴan ƙasa”.

       Zazzafan numfashi Jawaad ya sauke yana miƙewa idonsa a matuƙar jazur tamkar ya haɗiyi wuta, yay salute din sir Ahmad sannan ya fice tamkar wanda zaije filin daga.

          Koda ya isa office ma gaba ɗaya zuciyarsa a dagule take, yama rasa wane kalar tunani ya dace ace yayi, dan lamarin ƙasarsa a kullum sake bashi tsoro take, tsoro irin mai firgitarwa da ban ta’ajibi, komai anayinsane saboda kuɗi, kuɗi! Dai kuɗi! Dai, sai yaushene mutane zasu ajiye son zuciya da burin mallakar kuɗaɗe su amshi gaskiya? Da wannan rayuwarne kuma kullum muke fatan ganin kayinmu cikin aljanna, a haka mukeso ALLAH yay mana rahama, a haka mukeso MANZON ALLAH yayi alfahari damu?,

    Ya rumtse idanunsa sosai yana cigaba da haɗiyar ɓacin ran daya tokare maƙoshinsa.

      Bai sake fitaba, bai kuma sake barin wani ya gansaba koda a cikin su Aliyu ne, dan kulle kansa yay a Office ɗin yanata saƙawa da kwancewa.

      Har sai da lokacin salla yayine sannan ya fito domin gabatarwa.

+

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★

           Bayan sallar la’asar ya bama Rose damar tattara masa ƙananun jami’ansu sabbin ɗaukar wannan karon.

    Duk da tayi mamakin hakan sai bata tambayesa ba, dan bataga alamun wasa tattare da shi ba, a yandama taga fuskarsa a matuƙar murtuke sai abun ya bata tsoro, dan irin wannan fushin nasa mafi yawan lokuta sukan gansane idan aiki ya ɗauki zafi.

      Bamusan miya faruba mudai an taramu waje guda, inda aka nema mu rabu rukuni-rukuni akan abinda mukafi samun ƙwarewa dashi a wajen horaswa.

      Ina cikin jami’ai masu ƙwazo da suka samu ƙwarewa wajen harbi, dan haka banyi ƙasa a gwiwa ba wajen shiga cikinsu.

      Sai da duk muka gama rarrabuwa sannan wanda ya saka a taramun ya fito.

          Yanda sautin takun takalman ke fidda ƙara haka nake jin sautin bugun zuciyata na fidda ƙarar bugu, zuwa yanzunkam na ɗan fara jin tsoro, ba komai ya kawo tsoron nawa ba kuwa sai fahimtar da nai kasantuwar wannan mutumin a kusa dani ke kawo min wannan yanayin da bansan dalilinsa ba.

      “Miyasa sai a kansa kawai?” naima kaina tambayar da bani da amsarta…..

        Na tafi tunani sam bansan bikin da ake ba, sai da naji ƙarar sautin bugawar ƙafarsune nai firgigit, dai-dai zasu ajiye hannayensu da sukai Salutes nashi.

    Hakan ya sakani saurin kallon inda yake nima ina ƙoƙarin kai hannuna saman goshina.

     Karaf na tsinci idanunsa a kaina yana watsamin wani kallo mai kama da gargaɗi.

      Ƙasa na maida kaina, muka ajiye hannayenmu tare da ƴan uwana.

       Tsayuwarsa ya gyara har yanzu dukkan hannayensa na cikin aljihun jeans ɗinsa ruwan toka, ƙamshin turarensa na cigaba da addabama ƙofofin hancinanmu, ya ɗan furzar da huci kaɗan yana cigaba da tsatstsaremu da idanunsa masu ban tsoro, gasu yau sunyi jazur alamun yana tattare da ɓacin rai.

       Ganin yanda yake mana kallon ɗaɗɗayan ne yasani fahimtar nazartarmu yake ɗaya bayan ɗaya, babu zato muka tsinkayo muryarsa mai tarin nutsuwa wadda yau shine karo na farko da zan jita, sai dai kuma bamu yay ma maganarba, hakan yasa bamuji miya faɗa ɗinba duka bayan kalmomin farko na ambatar suna Rose da yayi.

         Rose dake gefensa ta kallemu tana matsowa kusa damu sosai da mana bayani akan abinda yace.

      A cikin kowane rukuni yana buƙatar mutum biyu, dan haka zai gwada ƙwazon kowa.

     Mun amsa da girmamawa, kafin kowane rukunu a haɗasu da waɗanda zasuyi nusu gwajin.

     Ni dai har muka bar wajen ban sake yarda na kallesa ba, hasalima gaba ɗaya na kasa samun sukuni, na sauke ajiyar zuciya ina dafe kaina, tare da fatan ALLAH ya kawo mani sauƙi akan wannan *Sabon al’amari* dana tsinci kaina a ciki.

         Mun isa wani ɓoyayyen wajen sirri na hukumar mai ban tsoro, dan kuwa yau naga abinda a films kawai nake gani, wato manya-manyan makamai masu ban tashin hankali, yanzu dama a ƙasarmu akwai irin waɗannan manyan mahaukatan makaman irin haka?

     Gaba ɗaya ganinsu ya saka karsashina guduwa, sai binsu muke da kallo tamkar wasu sokaye, mun daɗe munaji a labari babu jami’an da suka kai hukumar DSS mahaukatan bindigu. ban taɓa gasgata hakanba sai yau da idanuna suka ganemin zahiri……

      Jin takun mutum a bayana ya sakani saurin juyawa, nai saurin matsawa gefe ƙirjina yana bugawar da bai taɓa yiba, dan sam bansan sanda ya shigo wajenba balle isowarsa kusa dani irin haka.

        Baiko nuna yasan dani ba a wajen ya zuge glass ɗin da nake dab, hakan ya sakani yin gaba da sauri.

        Jawaad dake hidimarsa cikin halin ko in kula ya ciro wata ƙaramar bindiga mai ƙyau ruwan Silver, sannan ya taka zuwa kujerar dake tare da tebir ya zauna yana ɗora bindigar da harsasai kusan guda takwas.

         Jabeer da suke tare ya ɗauki bindigar da Jay ya ajiye ya ɗura harsasan robar dake tare da bindigar a cikinta suna magana da Jay wadda sam su bily basajinsu.

      Bayan Jabeer ya kammala ya nufi su Bily dake tsaye suna jiransu.

        Umarni ya bamu akan mutum ɗaya yazo, dama dukanmu mu bakwaine, na rasa yanda zanyi na iya samun cikakkiyar nutsuwa a wajennan, nikam a raina nama fara zargin wannan mutumin ko yanada aljanin da baya sonane shiyyasa yake kiɗimani? Kokuma shine aljanin kansa?.

     Ta yaya dukkan mutane ina mu’amula dasu hankalina kwance, sai shine a duk lokacin da muka samu kusanci gabana zai keta faɗuwa? Wannan lamarin da mamaki wlhy………..

         Ƙarar harbin da ɗaya a cikinmu tai bisa allon gwajine ya maidoni a hayyacina babu shiri, danma harsashin robane, amma a hakan ba ƙaramar firgita nayi ba.

       Kallon da sukemin ya sakani yin murmushin yaƙe, shima na saci kallonsa, sai na tsinci idonsa a kaina, amma saiya janye kamar ba haka bane, ya maida ga allon da wancan yay harbin.

        Sai kuma mukaga ya taso zuwa garemu, hakan ya sakani sake aro nutsuwa na azama kaina, ya karɓi bindigar hannun Oga Jabeer ɗin, a wani salon kai tsaye ya harba harsashin saɓanin mu da sai ka tsaya wajen nutsuwar ina zaka harba.

        A tsakkiyar inda ake buƙata harsashin ya shiga anan kuwa ya shige jikin allon, ya juyo yana fuskantarmu sosai,

       “Wannan shine wajen da nake buƙatar kaɗai harsashi ya shiga”.

      Iya abinda yace kenan ya wurgama Oga Jabeer bindigar shiko ya caɓe.

     Na ƙagara yabar wajen, amma sai naga yama gyara tsaiwarsa alamun babu inda zaije.

     Ɗaya bayan ɗaya muke zuwa kowa yana gwada ƙwazonsa, amma ni na kasa tafiya, dan ji nake tamkar bazan iya komaiba a gabansa.

    Wanda daga shi sai ni dana rage ta ƙarshe yayi shima, hakan na nufin dai duk wayon amarya sai ansha manta, dan ta laɓe-laɓe ta ƙare kuma.

    Haka na taka nima na amsa, sai dai hannuna rawa yakeyi, gashi duk sun wani zubamin idanu.

       Cikin karanto addu’a na fara dake raina da maida hankali akan abinda ke gabana.

      Amma sai babu zato naji ƙamshin mayen turarensa mai daɗin shaƙa ya sake kusantoni…………..✍🏻

1

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻1Shafi na talatin da tara

………….“Ki maida hankali akan abinda kikeyi”.

     Muryarsa mai tarin nutsuwa da amo ta daki dodon kunnena, yayinda zuciyata tai wata irin bugawa tamkar zata faɗo ƙasa, idanuna suka cika da ƙwalla.

      Ruɗanin dana shiga na babu zato babu tsammani ya sakani danna kunamar bindigar ba tare dana saniba…..

     Ji nai kawai sautin tafi na tashi, nai azamar kallonsu kafin na maida ga allon harbin, sai naga na harba ainahin inda ake buƙata.

    Bansan murmushi ya suɓuceminba, na saci kallonsa sai naga wayam yabar wajen ma gaba ɗaya, yana daga can gaban kantar da aka zagaye ɗakin da ita aka kuma rufeta da glasess baki ɗaya, wasu bindigu yake zubama harsasai tamkarma baisan mi akeba…..

     Maganar oga Jabeer ta sakani maida kallona garesa, yace, “Lallai kin cancanci a kiraki gwanar harbi”.

     Murmushi nayi da faɗin, “Nagode sir”.

        Dai-dai Jawaad ya dawo wajen kalamar godiya da Bilkisu kema Jabeer ta shiga kunnensa, yay musu kallo ɗaya yana ɗauke ido da ƙara tamke fuska ya miƙama Jabeer bindugun hannunsa.

     Amsa Jabeer yayi ya miƙama kowannenmu a hannunsa, sannan ya nuna mana inda kowa zai harba ba tare da ya mana bayanin dalilin hakanba.

     Duk jeruwa mukai, kowanne ya zam cikin shiri kafin Oga Jabeer ɗin ya irga uku sannan ya bamu umarni.

     Koda muka harba nidai idanuna na lumshe dan nasan dai bai zama lallai na zam cikin masu nasara tamkar ɗazunba,

        “Inhar zakuyi harbi ku rufe idanunku da tunanin rashin nasara to lallai wataran a filin daga wani zai fasa kayinku da nasa harsashin”.

     Maganarsa ta shiga kunnuwan kowannenmu babu zato, saurin buɗe idanuna nayi da mamakin jin furucinsa, musamman ma da naga ba’a kusa dani yakeba, hasalima ya nufi ƙofar fitane zai fice daga wajen.

        Dukanmu da kallo muka bisa harya fice. kafin sauran ƴan uwana su shiga ma juna kallon-kallo, kowa nason fahimtar wanene ya rufe idon a cikinmu?, sai dai babu wanda ya samu amsarsa.

      Jabeer yay murmusa yana girgiza kansa kawai, da maida kallonsa gasu Bilkisu.

      Shima sallamarmu yayi, dan haka duk muka fito kowa yana ƴar maganarsa da wanda halinsa ya saɓa, mu biyune mata a ciki kawai, ita kuma tunma a wajen training bama shiga sabgar juna da ita.

            Koda muka fito sai na shiga neman Ummie, na iske su basu fitoba, komawa nai bakin aiki, sai dai duk yanda naso ture abinda ya faru a raina yaƙi turuwa, sai kai kawo yakemin a zuciya da ƙwaƙwalwa.

       A wannan yanayin Ummie tazo ta sameni, tun tana kallona harta kasa jurewa ta jehomin tambaya,

        “Madam wai yaya dai?”.

      Kallonta nai da mamaki,

      Nace, “Kamarya?”.

Dariya ta ƙyalƙyale da ita tana girgiza kanta, “Kinga bar zaromin idanu tambaya kawai nayi”.

      Ƙwafa nai mata ina ɗauke idanuna daga kanta da faɗin, “Gulmammiya”.

 +

★★★★★

         Kwanaki huɗu kenan da faruwar wancan gwajin wani abu bai sake tasowa ba, hasalima ban sake ganinsa ba.

      A ɓangarena ma nima nayi shiri tsaf na fara binciken wanda ya keta martabar Amina a cikin gidanmu, shiyyasa yau data kasance lahadi banje ko inaba na sameta a gidansu, nayi amfani da lokacin zuwa islamiyyata ne dana maida duk ranar lahadi, yau sai haƙura nayi da zuwa na yada zango a gidansu Amina.

       Da sallama na shiga, Amina dake zaune a ƙofar ɗakinsu tana tsintar shinkafa ta ɗago tana amsamin fuskarta ɗauke da murmushi, sai kuma ta fara tsokanata da faɗin, “Wai! Yau babbar baƙuwa garemu ashe?”.

    Hararta nai ina jan kujera na zauna kusa da ita, na kalli mama dake mana dariya tana ta ƙoƙarin haɗa wutar abinci nace, “Mama kina jinta ko?”.

      Mama tace, “Toni ai wannan faɗan bana shigarsa daga baya azo a matseni”.

     Dariya mukayi gaba ɗaya, sai da muka tsagaita na shiga gaida mama, ta amsa min cikin kulawa tare da tambayata yaya aikina?.

     Nace, “Alhmdllh mama munata gwaji, dan har yanzu ba’a gama sabawa ba”.

       “Karki damu Bilkisu za’a saba, harma ya zama jiki wataran kuzam kune ake ambata a ƙasar mugaye su tsorata”.

    Murmushi nayi kawai. Sai Amina ta amsa da “Insha ALLAHU kuwa mama” muryarta a kausashe na alamun tasowar ɓacin rai.

     Tausayinta ya kamani, na dafa kafaɗarta ina shafawa alamun lallashi agareta.

       Tai murmushi mai ban takaici ba tare data iya cemin komaiba.

      Shiru na mintuna kusan biyu ya biyo tsakaninmu, ita tana cigaba da tsintar shinkafarta ni kuma ina buɗe littafin da nazo dashi gidan, ɗagowa nai na kalleta, itama sai ta kallenin.

        “Amina nazone mu fara magana akan wancan abun da ya faru a waccan ranar, ina fata ban shiga uzirinkiba?”.

     Murmushi tayimin, “Kai Bilkisu, ni wane uziri gareni, kimin duk tambayar da kikeso, ni kuma zan baki amsa inhar na sani”.

    Kaina na jinjina mata, kafin na jeho mata tambaya, “A waccan ranar da abin ya faru, kowa yana gidan?”.

       Shiru Amina tayi na kusan sakanni goma, kafin tace, “Eh to, lokacin dana shiga kowa yana nan, dan kinsan da zaran nayi sallar asuba nake shiga, sai kuma azhar na dawo gida, na koma bayan sallar la’asar sai goma nake dawowa gida, sai idan Alhaji na nanne yakan ce da nayi sallar magriba naje gida na huta, to a waccan ranarma ina idar da salla na shiga gidan, bayan mun gaisa da baba mai gadi ya tsokaneni kamar yanda ya saba, sai na wuce ciki, na fara gamo driver yana wankema Yah Qaseem mota, shima muka gaisa na shige. Ban iske kowa a falonba sai motsin kuku a kicin, na shiga muka gaisa da shi, shima ya tsokaneni tamkar yanda ya saba mukai dariya kafin na fito na fara ƙoƙarin gyaran falo.

      Harma na kammala gyarawar ina morping Yah Qaseem ya shigo, duk da bansan lokacin daya shigoba ma dan jinai kawai tamkar kallona ake, shine na juya na gansa tsaye, a ɗan rikice na gaishesa dan bansan dalilin kallonba, shima ya amsa yana wucewa kicin ba tare da ya sake kallon nawa ba. Nai ajiyar zuciya ina cigaba da aikina, harna kammala na hau sama shima na gyaro, lokacin dana sakko na iske Yah Qaseem ya fita”.

    Ta sauke numfashi tana share hawaye, kafin ta cigaba da faɗin,

      “Kinsan sai sun tsashi nake samun damar ƙarasa aikin? To ranarma saina wuce kicin tamkar yanda na saba na zauna muna hira da kuku ina karyawa, banfi zaman mintuna gomaba Mummy ta ƙwalan kira, na amsa ina ajiye filet ɗin hannuna ina fita. Na isketa cikin shirin fita, na gaisheta cikin risinawa, tana laluben abu a jakka take amsamin, ta bani umarnin zuwa na taso mata Yah Salman. Da to na amsa ina ficewa.

       Nayi sallama a ƙofar ɗakinsa yafi sau biyar, sai dai babu amsa, sanin halinsa ya sani tura ƙofar na shiga kawai, yana kwance ɗai-ɗai a gado da ga shi sai guntun wando, nai ƙasa da kaina ina kiran sunansa. Kamar yanda ya saba ya tashi a fusace yana mai zagina akan ubanmi nazoyi?. Amsa na bashi da cewar Mummy ce tace na tasoshi, wawan tsaki yaja nidai na fice abina naje na sanar mata cewar gashinan”.

       “Bayan na sanar mata ta cemin zata fitane, idan Aunty Aamilah ta tashi na sanar mata taje can ta sameta inda sukai magana jiya, na amsa da to na nufi sama dan ƙarasa aikina”.

     “Bansan fitar Mummy ba, dan inacan ina aiki, bayan na kammala na sako na nufi kicin, ina ƙoƙarin shiga Yah Salman zai fito, dan jaka mukai karo da juna harna faɗa jikinsa, muguwar mamuƙar da yaymin ba ƙaramin tsoro ta baniba, dan bilhaƙƙi da gaskiya ya rungumeni tare da matseni tsam a jikinsa, nai saurin turesa ina hawaye…….”

      Ta kasa ƙarasawa tana sharar hawayen yanzunma, ni kaina idona ya cika da ƙwalla, handkherchief ɗin hannuna na miƙa mata, ta girgiza min kanta da cewar, “Kona goge waɗanda suka fisu zasu zubo, tuni alƙalamin ƙaddara ya fahimtar dani share hawaye a gareni bashi da wani amfani Bilkisu”.

         Da ƙyar na iya haɗiye yawun daya tokare min maƙoshi, nace, “Sai mi ya faru kuma bayan hakan?”.

      Ta ɗan taɓe bakinta tana ajiye tiren shinkafar da take tsinta, tace, “Tsaki yaymin ya fice a binsa, nima sai na samu kaina da jan tsakin ina shigewa, dama da shirin fita aiki na gansa, dan haka muna daga kicin ɗin mukaji fitar motarsa, itama Aamilah bata jimaba ta tashi a barcinta ta karya tabi bayan Mummy, ya rage gidan daga ni sai kuku da baba mai gadi”.

      Can baya na koma nai zamana a wajen ni kaɗai tamkar yanda na saba, da ga baya da naji na takura saima na fita a gidan na dawo gida, sai dai na iske mama bata nan itama, dama kuma ta faɗamin zataje gaisuwa, jinai nan ɗinma babu daɗi, na sake fita na koma can gidan, na kwanta a falo, anan barci ya kwasheni, ban farkaba sai ana kiran sallar zuhur”.

     Bayan na idar da salla ne na shiga kicin na samu abinda zanci, banga kuku ba, bankumaji motsinsa ba sam, abinci na ɗiba na zauna naci, tsautsayi ya sakani ɗaukar lemo nasha, abindama bai cika damunaba, duk da kuwa ba’aimin iyaka da dukkan wani nau’in abinci dake gidanba, duk abinda masu gidan zasuci Dad ya bani umarnin nima na ɗaukesa naci, kuma sam dukda halayar Mummy bata da ƙyau tanan ɓangaren dolene a yaba mata, ko wanene kai bata ƙyashin kaci komi zasuci, dan duk abinda sukaci shine ma’aikatan gidan keci, kuma za’a baka yanda zai isheka kaci  ka ƙoshi”.

        “Wannan lemo shine sanadin komai, daga shansa ban sake sanin ina hankalina yake ba, sai dai tashi nai na ganni a mawuyacin hali a gidannan…..”

       “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”, naketa maimaitawa, na share hawayen dake zubamin a ido ina riƙo hannun Amina.

      “Amma Amina wa kike zargi a cikin gidannan da aikata miki wannan abun?”.

        Hawayenta ta share tana murmushi mai ciwo, “Bilkisu ni bana zargin kowa, sannan kuma duk ina ƙyautata musu zato”.

         “Humm Amina su kuma basa ƙyautata miki zaton, dan da suna miki ƙyaƙyƙyawan zato da basu biyema son ƴaƴansu ba da zuciyarsu wajen kasa fahimtar an cuta miki, tabbas a wannan gaɓar abin yazo mini da ruɗani, dan zuwa yanzu hatta kuku da baba mai gadi suna cikin zargina”.

       Amina ta zaro idanu tana kallona, hakama mama daketa aikinta tana saurarenmu sai da ta kalleni, sai dai babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu.

     Nace, “Karku damu, shi laifi kowama yana iya aikatashi, musamman ma irin wannan”.

     Dukansu kai suka jinjinamin alamar gamsuwa, na miƙe zan tafi mama tace babu inda zanje sai naci abinci, dan yau ɗanwake takeyi.

      Dole nabi Umarninta na koma na zauna ina murmushi, ganin Amina tana tattare da damuwa na fama mata ciwon da nayi sai na shiga bata labarin wajen aikinmu, musamman inda na nuna ragwantaka a wajen trianing, aiko taita kwasar dariya mama na tayata.

    Bansan yaya akaiba har abinda ya faru dani a airport akan mutuminnan sai da na bata labari.

      Aiko taita kwasar dariya harda hawaye, wai mazari sunga mazaje.

       Ganin ta shiga cikin farin ciki nima sai naji sanyi a raina, koda mama ta kammala tare mukaci abinci mu uku a kwano ɗaya munatama mama santin ɗan waken da yaji daddaɗan yaji daketa ƙamshin tafarnuwa da kayan kamshi.

      Ban bar gidanba har sai da kiran yah Qaseem ya shigo wayata, ina tunanin ya dawo gidane, dan shi yau ya fita akan wani aiki da yakeyi.

      Sallama nai musu na tafi ina jera musu godiya suma sunamin tare da addu’ar fata alkairi………..✍🏻

1

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻5FART ONE END

              Shafi na arba’in😌

………….Ina ƙoƙarin shiga gida kiransa ya sake shigo mani, ɗagawa nai da nufin faɗa masa ganinan zuwa gidan, amma sai naji yana magana mai alamar ba’a gidan yakeba..

        Ya bani umarnine akan na duba ɗakinsa akwai wasu takardu ɗaya daga cikin jami’inmu zaizo ya amsa, na amsa masa da to kafin na yanke wayar na ida shiga da hanzari.

       Kamar yanda ya umarta hakan nayi, ina fitowa na iske wanda aka turo ɗin yazo, shima yana sama dani, dan haka nai masa gaisuwar girmamawa kafin bashi takardun na koma ciki.

      Duk da na iske su Mummy a falo ban iya zama ba, gashesu kawai nayi na shige ɗaki abuna, dan ina buƙatar samun filin yin tunani akan abinda muka tattauna da Amina.

        Sosai komai yake neman ɗaure kaina, duk da kuwa Alhmdllh yanzu na samu ilimi sosai game da bincike, dan ko a wajen horaswa da muka samu, nafi maida hankalina anan sosai, alamu sun nuna Qaseem da Salman basa gida, shin akwai wanda ya dawo daga baya kenan s cikinsu? Ko kuwa kuku zan zarga kai tsaye ne? Baba mai gadi tsoho ne, duk da dai tsufansa bai kai ace bazai iya aikata makamancin hakanba, to amma miyasa zan zargesa ne? Lallai ya dace nama fara bincikarsa akan shiga da fitar kowa a wannan ranar.

    Da wannan tunanin naɗan samu nutsuwa, amma koda nai shirin barci na kwanta sai ya gagara, babu abinda nake sai saƙawa da kwancewa tare da tunanin iyayena.+

_______________________________

         Washe gari litinin muka tashi da shirin aiki, tunda na gama shiri naga harna shiga kicin ina shan tea Yah Qaseem bai shigoba nasan bai kwana gidaba jiya kenan?.

         Tea ɗin kawai na iya sha na fito, babu wanda ya tashi har yanzu a mutanen gidan.

    Nai addu’a na fita tamkar yanda na saba. Yau kam sai driver nabi, muna isa tamkar jira na samu saƙon kira.

      Na nufi inda ake kiran namune na haɗu da Yah Qaseem, murmushi mukaima juna, na gaishesa cikin girmamawa tamkar yanda na saba.

     Shima ya amsamin da kulawa yana tambayata yaya gidan?.

     “Alhmdllh Yah Qaseem, yaya aikin naka? Ai ni bansan baka kwana gidaba sai yanzu da safennan?”.

      Yace, “Oh, wannan wace irin matace dani? Ban kwana a gidaba amma sam bama ta saniba”.

    Haka kawai sai maganarsa ta sakani jin kunya, naja baby hijjab ɗina na rufe muskata ina murmushi, matsowa yay kusa dani gab tamkar zai shige mini jiki, ya kai bakinsa dai-dai saitin kunnene yana faɗin, “Baƙauya”.

      Baya na ɗan ja saboda kusancin da muka samu yayi yawa, na janye hijjabin zan bashi amsa karaf idona akan mutumin ga, gabana yay wata masifaffiyar faɗuwa saboda cin karo da wata shegiyar harara daya watsomin, tuni fara’ar fuskata ta ɗauke baki ɗaya saboda bugun da ƙirjina yakeyi.

       “K lafiya?”

Ƴah Qaseem ya faɗa cikin tsareni da idanu.

     Cikin rawar baki da hadiye yawu da ƙyar nace, “B..babu k..omai”.

       Idanunsa ya ɗauke da ga kaina ya maida saitin inda nake kallo, sai dai yana juyawa shi kuma yana shigewa Office.

      Sake juyowa yay gareni, “Wai haushi kikaji dan nace miki baƙauya?”.

      Murmushin ƙarfin hali nai masa ina girgiza kai, nace, “A’a yayana”.

     Ƙaramar dariya yayi ya dungure min kai tare da zagayeni ya wuce abinsa da faɗin, yaje gida sai ya dawo.

     Ko a dawo lafiyar ban iya ce masaba, na kuma kasa ɗaga koda ƙafata a wajen saboda tsabar yanayin dana tsinci kaina.

            “Haba Bilkisu! Ke kin cika matsala wlhy, tsayuwarmi kuma kike anan?”.

     Nannauyan numfashi na sauke jin muryar Ummie a kusa dani, taja hannuna ba tare da ta sake magana ba zuwa inda ake jiranmu.

       Sosai mamaki ya kamani ganin inda ta kawo mu, zan iya kiransa Office kai tsaye, amma mazauna cikinsa da zasuyi amfani da shi aƙalla mutane goma cif.

        Tunda naji zuciyata ta dai-daita nasan baya wajen, dan haka nakai dubana ga kowa, iya dai mune da aka tara ranar, tare da yallaɓai Hafiz.

       Ya gyara tsaiwarsa yana mana bayani yanda zamu fahimta sosai.

     “Wannan Office ne da zai kasance na musamman ga waɗanda boss ya aminta da ƙwazonsu, dan haka sai kowa ya duba, idan kaga sunanka to kana cikin waɗanda ya zaɓa, idan baka ganiba to ba hakan yana nufin bazai iya aiki da kai bane ko bai yabama ƙoƙarin kaba, kawai dai kasan a ranka hakanne mafi alkairi a gareka”.

      Duk cikin girmamawa muka amsa masa.

      Ni kasama dubawar nayi, sai Ummie ce tabi sauran itama tana dubawa, inajin wasunsu suna murna, alamar dai sunga sunayensu.

    Nima a bazata naji Ummie ta rungumeni tana faɗamin ni da ita duk muna ciki.

      Ban san miya saba, banji baƙin cikiba, kuma banji wani murnaba, kawai dai nayi murmushi ne dan karta zargi wani abu..

        A cikin mu goma ɗinan bakwai mazane, mu uku mata, ni Ummie sai ɗayar mai suna Divine.

     Komai na wajen an yisane da tsari, dan an saka mana shingai da kowa bazaiga abinda ɗan uwansa keyi a sashensaba sai idan yaso hakan.

    Naji daɗin yanda aka saka Ummie kusa dani, duk da ba’a layi ɗaya mukeba wajen zamanta yana kallon nawa, sannan mune ƙarshen bangon wajen.

       Duk wanda yake cikin wannan tafiya yayi farinciki, saɓanin ni da bansan manufar zaɓin da zuciyata ta ɗauka ba.

      

         Shigowar Yah Qaseem station ɗin ya samu labari, bansan dalilinsaba naga ya fara faɗa tamkar zai cinyeni ɗanya, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba.

     Tun ina saurarensa da mamaki na koma al’ajab, daga al’ajabi nakoma ban haushi, har takai abin ya bani tsoro, danni bansan minene laifina a cikiba? Kuma ince nan wajen aikine, bamu da dalilin cewar sai inda muke buƙata za’a zaɓamana.

     A cikin masifarsa ta yau ne nakeji cikakken suna mutumin nan, wato *_Jawaad Abdul-aziz yusif_*.

    Ni dai bance ƙalaba har yaci jarabarsa ya tsire, daga ƙarshe yace na fitar masa a office.

     Na fito ina share hawayen da suka ziraromin babu shiri, sai shi kuma naci karo da shi.

    Tafiya yake a fusace tamkar wani ingarman doki, yana ƙoƙarin saka bindiga a aljihun wandonsa na baya, yayinda su yallaɓai Jabeer ke take masa baya suma fuskarsu babu walwala.

       Yana ƙoƙarin shiga motar da aka buɗe masa ne ya ɗago, sai ko idanunmu cikin na juna.

    Saurin janye nawa nayi ina kauda kai, a ƙasan zuciyata ina mamakin miya fusatashi har hakane?.

    Bani da mai bani amsa, dan haka sai ma tashin motarsu na jiyo.

STORY CONTINUES BELOW

        Har na bar Office ban kuma sakashi idona ba, hakan na nufin dai basu dawoba daga fitar da naga sunyi ɗazun kenan.

      Sai kuma har naje gida abin na damuna, haka kawai naji na damu da tsagwaron damuwar dana karanto a fuskarsa, ranar da wannan abun na kwana a raina.

______________________________1

         Washe garin safiyar talata muka tashi da dawowar aunty Shahudah ƙasar haihuwarta tamkar yanda naji a bakin su Aunty Aamilah, danni dai babu wanda ya sanarmin hakan.

    Ban damuba, dan nasan koba’a faɗaba bani da muhimmancin sanin irin waɗanan abubuwan tunda basu ɗaukeni dai-dai da suba har yanzu, Dad ne kawai yakemin kallon na mutum mai muhimmanci a cikinsu, sai ko Ya Qaseem da shima nake ƙyautata masa zato akaina.

         To ni daima aiki nai ficewata abina, dan shine mai muhimmanci a gareni a yanzu, nabar saƙon sannu da zuwa a faɗa mata wajen Aunty Aamilah, dukda dai a ɗage ta amsamin ban damuba nai wucewata driver ma yau ya ɗaukeni, dan Yah Qaseem ma yau bai kwana gidaba.

    Na fiskanci akwai aiki mai mihimmancin gaske da yakeyi a kwanakinnan, musamman ma yanda ya maida kansa busy ko’a Office bai cika zamaba sosai.1

____________________________

             Ƙarfe biyar na yamma jirgin su Shahudah zai sauka, dan haka tun ƙarfe biyu su Mummy suketa shirin tarbarta, ansa kuku ya shirya mata abinci na musamman kala-kala tamkar ba cikinta kaɗai zai ciba.

      Tsabar gata Mummy da kanta ta tisa ƙeyar Aamilah suke gyara ɗakin Shahudah, Aamilah sai tunzura baki take gaba dan bata saba da aikinba.

      Jitake tamkar taje ta kira Amina, dan ta fahimci amfaninta sosai a gidan a yau, hakama Bilkisu, dan tasan badan wannan ƙaddararran aikin da Bilkisun keyiba ai da yanzu itace zatai gyaran.

     Haka dai suka kammala Mummy ce ƙarfin aikinma, dan danan ɗakin ya ɗauki ƙyau da haske tamkar ba shiba, shima yau yasan maishi zata dawo garesa.

       Huɗu nayi Salman ya baro office ya taho gidan domin zuwa tarbar gimbiya Shahudah😝.

         Gudun karma a ɓata mata rai huɗu da rabi suka bar gidan, sun gwammaci su suje su jirata, amma ba ita taita jiransu ba.

          Zaman da baifi mintuna ashirinba kuwa jirgi ya sauka, fasijoji suka fara fita, sosai idanun su Mummy nakai.

        Can sai ga zillaziyya zankaɗaziyya gimbiyoyi mandiyoyin oga Jawaad ta fito cikin takun ƙasaita da gayu.

     Sanye take cikin wandon blue da yay masifar kama jikinta, sai riga ruwan hoda an rubuta Beauty da ado mai ƙyalƙyali a gaba, siririn gyalenta data yana a kai shima ruwan wandon, sai rigar sanyi data ɗaura a ƙugu, ta toshe fuska da eyeglasess mai nuna blue a jiki.

     Tabbas tayi masifar ƙyau, kuma duk wanda ya gani tilas ya ƙyasa dan ta cancanta.

      Aamilah ta tafi da gudu gareta, hakan yasa Shahudah sakin akwatinta da jakkarta ta hannu a ƙasa ta rungume ƴar uwarta, takalman ƙafarta masu masifar tsini badan sunada maɗauri ba babu abinda zai hana su sakata ta faɗi.

     Wasu daga cikin mutane sai kallonsu suke, musamman irinmu ƴan ƙauye da bamu waye ba😒, dan harda bakuna muka hangame lokacin da Salman yazo ya rungumeta shima.

      Yanda suka ƙanƙame juna lamarin zattakaici, ta sakeshi ta nufi Mummy ta rungume itama, sai kuma suka sake rungumeta baki ɗaya, hakan dai na nuna suna cikin tsantsar farin cikin ganinta duk da sukanje su ganta a can musamman ma Mummy da Aamilah.

        A sabuwar motarta da Dad ya saya mata akaje ɗaukarta ita kaɗai, ta kalli Mummy ta kalli motar cikin alamun tambaya.

    Dariya duk sukai mata, Aamilah ta sanar mata ƙyautar Dad ce.

    Wani ihu Shahudah ta saki tana ɗane Mummy, motar da kullum take nafarkin mallakarta, ta ƙiyasta kuɗinta bazasu kai ta sayaba shiyyasa ta haƙura, ashe Dad zai cika mata burinta.

    Yanda take matuƙar murnar ne yasa mutane suka sake maida hankalinsu a kallonsu, wasu zato suke ko daga karatu Shahudah ta dawone akai mata wanna irin tarba da ƙyauta mai tsoka, har dai suka shiga mota zuwa gida idanun mutane na kansu.

       Daɗi ya ishi Shahudah sosai, dan Dad yay mata bazata irin wadda bazata taɓa iya mantawa ba, sayen motarnan yay bala’in kai mata ko ina a cikin ƙoƙon ranta, har tana tunaninma wace kalar murna zatai masa yasan taji daɗi.

     Murnar motama ta hanata nutsuwa taci abincin kirki a cikinta, duk da tarin abincin da aka shirya matan kuwa.

       Wayar Aamilah ta amsa ta kira Dad ɗin, maimakon tai masa godiya da addu’ar fatan alkairi sai kawai taita masa ihun murna da faɗa masa ya cika mata burinta, shi dai yana saurarentane yana murmushi, yanataso yaji ta masa godiya tamkar yanda idan yayma Bilkisu ƙankanin abu take masa amma sai yaji tsit.

    Maimakon hakan ya taɓa ransa sai ya danne kawai, yama cigaba da nuna mata farin cikinsa na dawowarta, ya kuma tabbatar mata a satinnan shima zaizo ƙasar kodan ita.

STORY CONTINUES BELOW

★★★

    Duk yanda Mummy taso tai haƙuri Shahudah ta huta sannan suyi zancen Jawaad ta kasa, haka ta zayyane mata halin da ake ciki yanzu na tallar ƴammata da ake masa a cikin family ɗinsu.

       Ran Shahudah ya matuƙar dugunzuma, ta shiga masifa da faɗin Jawaad natane ita kaɗai, duk yarinyar datai gigin shigar mata rayuwar miji wlhy sai ta halakata.

     Tai shiri akan a daren zataje family house ɗin su Jay, amma sai Mummy ta hanata, ƙin sauraren Mummy tayi, sai da ƙyar, dan ta nuna mata abinfa YAƘIN SUNƘURU yakeso yanzu, dan haka kar tayi gaggawa, ta jira taji abinda suka shirya akan al’amarin…………✍🏻

Alhamdullahi ala kulli halin🙏🏻😢.

Anan na kawo ƙarshen littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA na ɗaya. Abinda na rubuta daidai ya rabbi ka haɗamu a ladan baki ɗaya, wanda nayi kuskure kuma ALLAH ya yafe mani da ku da kuka karanta🙏🏻😭.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *