KWARYA TABI KWARYA COMPLETE

[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
1&2
Lokacin dana shiga masarautar sai da nasha jinin jikina dan ganin yanda tarin bayin dake karkashin masarautar suka nutsu gabas yamma kudu Arewa dukkaninsu suna tsaye sunja layi mazansu da matansu da ‘ya’yansu suna sanye da uniform wanda ke dauke da tambarin masarautar gaba da baya, kowanne kansa a sunkuye ‘kwakkwaran motsi babu wanda yake iya yi…….Can wata rumfa na hango iyayen masarautar zaune kan kujeru na alfarma sun jeru su uku wanda yake tsakiyarsu shine nafi tunanin shine shugaban masarautar wato (Sarki Maimartaba) abinda yasa nake tunanin shine Sarkin sabida ganin yanda wasu mutane gudu biyu masu dauke da jajayen kaya suke tsaye a gefe da gefensa suna masa firfita da wani irin mafici mai baza gwanin birgewa……..Shiru masarautar babu hayaniyar mutane busar algaita gami da sarewa ne kawai take tashi a gurin.
Cikin nutsuwa wasu lafiyayyun motaci guda guda su shigo cikin masarautar, Maimartaba ya fara yun’kurin miqewa tsaye fuskarsa dauke da wani qayattacan mirmushi, Ganin zai miqe yasa fadawan dake gurfane a gabansa suka miqe da sauri suna baza manya manyan rigunan jikinsu……Waziri Galadima Ciroma suma suka miqe tsaye sabida ganin maimartabar ya miqe, dan ganin iyayen masarautar sun miqe ya sanya dukkanin wa’inda suke zaune suma suka miqe tsaye domin girmamawa…….masu busar sarewar suka rud’e tare da sanja salo….gabadayansu suka nufi inda motocin nan sukayi parking suna ta aikin busa algaita gami da sarewa, Wani bafadane yayi saurin bude motar ya fito da sauri ya bud’e daya hannun ya matsa gefe guda tare da dun’kule hannunsa alamun jinjina ga wanda ke cikin motar “Barkan ka da dawowa masarautar gado Aliyu Haidar namijin zaki Sarki mai jiran gado fari kake mai farar aniya Ali baka fito ba sai da ka shirya hakika masarauta da duk wanda ke karkashinta yana murna da dawowarka lafiya.” Wannan kirarin daga bakin bafadan yake fitowa….shuru gurin yayi na minti biyar kafin ya zuro qafarsa d’aya kafar dake dauke da takalmin sarautar na tsirawa ido cikin socond guda na gane cewar mamalakin kafar mugun d’an izzah! ne a qalla ya kai minti biyar da zuro kafa daya ya gagara fito da dayar ko me yake a cikin motar oho! gabadaya idanun kowa a gurin yake mutane da dama sun ‘kagauta suyi tozali dashi mussaman na qasa wa’inda basu sanshi ba sai dai labarin sa, cikinsu har da Sumayya wacce ta kasance d’aya daga cikin ‘ya’yan bayin masarautar itama idonta kur! a gurin tana jira ya fito daga motar ta ganshi tun kafin ya fito ta gazgata abinda jama’ar masarautar ke fada a kansa wato shi d’in mugun d’an izzah! ne mugun d’an d’agawa ne! mugun d’an gadara ne! Mugun muskili ne wanda babu wanda yake gane al’kibularsa sai mutum d’aya itace mamanshi amma hatta da mahaifinsa maimartaba baya gane inda ya dosa.

Cikin nutsuwa ya rankwafo ya fito daga cikin motar tare da zura bak’in gilashin dake hannunsa dan saboda gujewa had’a ido da jama’ar da sukayi masa caaa! da idanunsu ya tsani kallo a rayuwarsa shiyasa sam baya sakarwa mutane fuska mussaman mata dan ya fahimci kamar kallo a jininsu yake be sai ba ko shi suka raina suke k’ure shi da kallon ‘kurrula.
Wasu matasan samari ne wa’inda sukayi sa’anni dashi naga sun fito daga d’aya motar su biyu suna sanye da kayan sarauta a jikinsu amma shi uban gayyar suit ne a jikinsa Shatima da Moddibo sune suka tilasta masa d’aura alkyabba a jikinsa saboda da ita sukaje airport din suka kuma sheda masa cewar maimartaba ne yace lallai su bashi yasa ya shigo da ita cikin masarautar.
Da sauri naga wasu bayi su hudu sun shimfid’a wani farin abu mai tsayi a dadai kafafunsa sai da abin ya dangane har inda iyayen masarautar suke Cikin nutsuwa yasa kafarsa akan abin ya fara tafiya.
Tafiya yake abokansa kuma ‘yan uwansa na gefe da gefensa, yayin da masu busa algaitu suka cigaba da aikinsu tare da rufa musu baya….Lokacin masu camera man vedio camera suka fara aikinsu suma ‘yan Jarida ba’a barsu a baya ba aikin daukar hotonsa kawai sukeyi shi kuma yana d’agawa jama’ar dake gefe da gefan sa hannu ammafa babu walwala ko ta kwabo a fuskarsa wanda ya kamata ace ya saki fuskarsa ya tar’bi dubbanin mutanan dake murnar dawowarsa gida ko a jikinsa daga karshe ma daya ga yana damun kansa sauke hannunsa yayi sai kawai ya sunkuyar da kansa ya cigaba da tafiya babu um! babu umum!! Sukuwa jama’ar masarautar sai kirari suke masa gami dayi masa fatan alkairi a rayuwarsa amma gogan bai d’ago kansa ba ballantana yasan sunayi……….”Wani irin takaici ne ya rufe ni naja tsaki tare da kauda kaina daga kallonsa tabbas na gazagata maganganun da jama’a sukeyi a kansa na rashin kirkinsa yanzu ina laifi ga wanda ke murna da zuwanka gami dayi maka addua idan da mutunci yaci ace ya d’ago kansa ya nuna jin dadinsa amma saboda tsabar izzah! ya gagara kallon inuwar inda mutanan ke tsaitsaye.
Silalewa nayi daga cikin iyayena na kama hanya domin tafiya can shashenmu na bayi, zuwa zanyi na huta dan bazan iya jurar tsayuwa ba rana sai duka na take gashi wanda akeyi dominsa baya gani, mahaifina kawai nake tausayawa dan ba wata cikakkiyar lafiya gareshi ba amma saboda tsabar bin dokar masarauta yasa ya lalla’ba ya fito ya tsaya a matsayinsa…………..
BINTA UMAR ABBALE

Kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa Dashan Allah✊🏻)
5&6
Bayan mun koma gurin tsayuwar mu mun nutsu sai maimartaba ya umarci yaron nasa daya fito ya nunawa jama’a farin cikinsa na dawowarsa masarauta lafiya….A lokacin idanun jamaa yayi caaa! a kansa kowa kokarinsa yayi tozali dashi, ni dai sunkuyar da kaina qasa nayi saboda jin yanda gabana yake faduwa haka kurrum naji bana bukatar kallonsa ba dan komai ba sai dan mugun halinsa na rashin ganin darajar mutane……..Wani bafade ne yay gaggawar gyara masa abin magana ya saita masa daidai bakinsa, kamar wanda akayi wa dole yay gyara sai da yaja lokaci tukkuna cikin rashin walwala a fuskarsa da maganarsa yace.”Alhamdullilah Allah kaine abin godiya. hakika nayi farin ciki mutuka daga dawo dani gida cikin koshin lafiya gami da tarin nasarori masu yawa.” shiru yayi tare da sunkuyar da kansa qasa. Jin yayi shiru yasa nayi saurin dago kaina ina kallon gurin da yake, gani nayi kansa a sunkuye yana kallon ‘kasan gurun tamkar me neman wani abu……Tsaki naja a cikin zuciyata nace”Wannan anyi d’an wulaqanci ya sani sarai jama’a shi suke sauraro amma ya fara magana yayi shiru, kaina na d’auke ina jin takaicin abinda yake……Gyaran murya ya kuma yi kafin ya cigaba da magana…”Sannan kuma nayi farin cikin samun iyayena da ‘yan uwana da dukkanin wanda ke k’ark’ashin masarautar nan lafiya hakika naji dadi sosai da ganin yanda kuka fito ‘ya’yanku da jikokin ku kuka nuna farin cikin ku dangane da dawowa ta gida Nagode sosai inayi muku fatan alkairi.” yana k’are maganarsa ya janye bakinsa daga gurin abin maganar can kusa da Waziri ya koma ya tsaya har yanzu babu fara’a a fuskarsa.
Hayaniya da kace kace ne ya cika gurin, Wani bafade yayi tsawa tare da umartar kowa yay shuru kafin minti biyu gurin yayi tsit! Maimartaba ya miqe a nutse ya karasa gurin da abin magana yake, kafin ya fara magana sai da ya d’aga hannuwan sa sama alamar gaisuwa ga tarin jama’ar dake gurin…..Gurin ya sake rikicewa da hayaniya kowa sai fadin albarkacin bakinsa yake akan maimartaba. Da kyar aka samu sukayi shuru suka bar maimartabar yayi jawabi gami da miqa godiyarsa ga Allah ya kuma miqa godiyarsa ga tarin manyan mutanan da suka samu hallatar gurin suma bayin dake karkashin masarautarsa sai da ya miqa godiyarsa a gurinsu sannan ya koma ya zauna gurin zamansa, Baba Waziri yazo yay nasa jawabin Galadima da Ciroma suma sukayi nasu daidai gwargwado sannan maimartaba ya rufe taron da addua, ya miqe da niyyar shiga cikin gida fadawa ne suka kewaye shi suna ta gyara kintsi dai.”!! Gurin ya karad’e da bushebushe gami da tashin muryoyin maro’ka da hayaniyar jama’a, sai da Sarki da muqarrabansa suka shiga gida tukkuna aka samu lafiya, jama’ar gurin suka watse kowa ya nufi ‘bangaran da yake a cikin gidan………Nida iyayena Cikin yanayi na ciwo muka shiga gurin mu, da sauri muka zaunar dashi, Tambaya ta ri’ke kafadarsa ni kuma hankali a tashe naje na d’ebo masa ruwa jiki na kyarma nazo na tallafo kansa ina kokarin bashi ruwan, bakinsa ya bud’e ina sa masa ruwan yana dawowa, lokaci guda zuciyoyinmu suka karye nida mahaifiyata hawaye muka fara, cikin karfin hali gami da kokarin janyo maganar yace.”Ku daina kuka bashi ne abinda nake bukata ba.”!
Zama nayi kusa dashi na rike hannunsa har yanzu hawaye bai da zubo min ba nace”Baba wai dan Allah me yake damunka kwana biyu ka’ki lafiya kullum cikin rashin kuzari da karfin jiki gashi kuma ka’ki ka bari a kira mai kula da lafiya yazo ya duba ka.”
A hankali yace.”Sumayya ba wani ciwo mai tsanani bane yake damuna zazza’bi ne mai zafi sai hajijiya gami da rashin kuzari to ni dik a tunani na ko shawara ce shiyasa na mayar da hankalina gurin shan maganinta amma yanzu ina ganin dole kije ki kira d’aya daga cikin masu kula da lafiya yazo ya dubani dan ni kadai nasan abinda nakeji a cikin jikina.
Tambaya hawaye ta share a sanyaye ta kalleni da fadin”Kiji can bangaran masu kula da lafiyar ki kirawo daya daga cikinsu yazo ya dubashi ni kaina jikina yay sanyi da wannan rashin lafiyar tasa a tsaitsaye fa ya kai sati hudu yanayi duk da yana shan maganin shawarar babu sauki kullum jikin rikicewa keyi.”
Miqewa nayi da sauri nace “Bari naje can gurinsu na samesu.” takalma na zura da saurin gaske na kama hanyar sashen masu kula da lafiyar gabad’aya bana cikin hayyacina ina tsananin kaunar mahaifina shiyasa rashin lafiyarsa ta d’aga min hankali mutuka.

“Sumayya.” Sunana naji an kira da sauri na tsaya ina waigen bayana.

babu walwala a fuskarsa ya karaso inda nake tsaye kai tsaye yace.”Ina Lawi yake ya bar aikinsa kamata yayi ace kafin mu fita gurin taro ya zubawa dokuna abinci yanda zai ishesu yanzu yanzu na shiga gurin na tarar da gabad’aya babu abinci a gabansu idan fa maimartaba ya samu labarin abinda yake zai fuskanci hukunci.”

A marairace nace”Buba dan Allah kayi hakuri kada ka kai ‘korafi wallahi babana bashi da lafiya tsayin sati hudu yake ciwo a tsaitsaye dukkanin abinda yake dauriya kawai yake dan Allah ka taimaka masa kana bawa dawakan abincin kafin yaji sauqi.

“Ke! saurara da wannan maganar.” Nayi saurin kallonsa kwalla na kokarin zobomin, Ya cigaba da cewa”Kowa da kika gani akawai aikinsa a masarautar nan nawa aikin ma yafi nasa wahala tinda ni kwana nake a tsaye ina zirga zirga banga dalilin da zai sanya na d’auki nauyin wani na d’orawa kaina ba, ke aikin me kike da ba zaki d’auki nauyin mahaifinki ba kafin ya samu lafiya.

Hannu nasa na goge hawayen da suka zubo min nace” Shikkenan zanyi kokari ganin na dauki ragamar kula da dawakan kamar yanda babana yake yi amma ka san dai muna zaman karatu ranaku uku a sati ko kuma idan mun zauna tin safe sai yamma muke tashi.
D’aga kafad’a yay yace.”Ke zaki tsarawa kanki yanda al’amura zasu tafi ni dai na fad’a miki ku kula da aikin ku kada maimartaba yaji wata magana.

Ajiyar zuciya na sauke mai zafi! nace”Shikkenan Buba nagode sosai insha Allahu zan iyakacin bakin kokarina.” Gyda kansa yayi ya bar gurin, nima da sauri na wuce domin nufar inda nayi niyya.

Na jima a tsaye a bakin kofar d’akin nasu ina sallama kafin naji an amsa da fadin”Ko wacece ta shigo.” Jim nayi ina tunanin shiga dan gabad’ayansu maza ne a ciki ina ganin kamar hakan bai dace ba.

Sallama na sakeyi, naji anyi min tsawa! da fad’in “Wai wacece take sallama ne ki shigo ki fadi uzirinki.” Shahada nayi na tura kaina dakin….wasu na kwance kan katifunsu wasu kuma na zazzaune daga su sai gajerun wanduna.
Daga bakin kofa na tsaya nace”Dan Allah d’aya yazo ya duba babana Lawi bashi da lafiya.”

Shuru sukayi min kowa ya cigaba da sabgarsa, raina ya ‘baci! nace”Magana fa nakeyi muku kuna jina.” ‘Dantala ya zaburo min da hayaniya yace.”Ke! babu wanda zai katse abinda yake a cikinmu yaje ya duba babanki idan kina so ayi miki abinda kike so ki shigo ciki muna bukatarki.”

Cike da mamaki nake kallonsu nace”aikin ku ne fa mai zai sanya kuce sai nayi muku wani abu sannan zakuyi to ni ba ‘yar iska bace idan kun saba latsa ‘yan matan dake masarautar to ni ba’ irinsu bace kuma wallahi idan bakuyi wasa ba yanzu zanje fadar sarki na sheda masa abinda kuke aikatawa……….A fusace! naga ya miqe yayo kaina zai mareni na kauce da sauri ina kare fuskata….wanda yake da sauqin halin cikinsu ne ya miqe tare da zira rigarsa ya kalleni da fadin” Shige muje na duba jikin mahaifin naki.” Da sauri na fita daga dakin gabana sai faduwa yake……Tafiya nake zugwi zugwi ina mamakin al’amarin, kawai naji ana ta’ba min mazaunai! Da sauri na juyo ina kallonsa, murmushi yayi ya sosa kansa ido jawur yace.”A gaskiya Sumayya Allah yayi miki baiwa mai mutukar daukar hankali, kina da duk abinda d’a namiji ke bukata a jikin mace kirjinki a cike yake dam-dam uwa uba mazaunai masu masifar rikimin lissafi wallahi tunda kika shiga dakinmu sha’awata ta tashi dan Allah ki bani damar mallakar wannan jikin naki wanda yake kokarin fitar dani hayyacina.

Kallonsa kawai nake wani ‘katoton abu ya tokare min a ma’koshi nace”Yanzu Usman ashe kaima halinku d’aya dasu Dantala a zahiri inayi maka kallon salihi ashe kaima baka da d’abi’a mai kyau Usuman dan Allah meye amfanin lalata da kukeyi da ‘ya’yan mutane idan fa masarauta ta samu labarin abinda kukeyi ba zakuji dad’i ba.

A sanyaye ya sosa kansa cikin jin kunya yace.”Sumayya dan Allah kiyi hakuri wallahi ni ban fiya haikewa ‘yan matan masarautar nan ba su Dantala ne masuyi kema yanzu hankalina ne ya tashi sosai shiyasa na gaza hakuri na kai hannuna mazaunanki amma kiyi hakuri dan Allah kada naji maganar a bakin kowa.
Cikin takaici na girgiza kaina tare da juyawa na cigaba da tafiya raina a masifar ‘kuntacce.

To koda Usuman ya duba babana nan ya gano cewa hawan jini ne ke damunsa hankalinmu ya tashi nida tambaya muka dinga kuka dan mun riga mun san ciwon hawan jini babban ciwo ne gani muke kamar mun kusa muyi bankwana dashi shiyasa gabadaya hankalinmu ya tashi….Usuman ganin duk muna hawaye yasa ya rarrashe mu tare da bamu shawarwarin yanda zamu kula dashi da lafiyarsa yace “Insha Allahu mutukar aka bi dokar da ake bukata masu dauke lalurar suka bi to zai samu lafiya, Ya miqe tare da fad’in ” Zaije yanzu ya kawo masa magungunan da zasu taimaka masa…godiya mukayi masa muna zubar da hawayen tausayi……
BINTA UMAR ABBALE
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
3&4
Yarima Aliyu a nutse ya ‘karasa rumfar da iyayen nasa suke zazzaune ya cire rufaffun takalmansa a nutse yaje ya gurfana a gabansu tare da ‘kaskantar da kansa sosai yace”Allah shi taimake ka ina fatan na same ku lafiya.”? Maimartaba ya d’ora hannunsa a saman kansa cikin farin ciki yace.”Lafiya lau alhamdullilahi Aliyu ina fatan ka dawo gida cike da samun nasarorin da muke bukata.” Ali! Yayi murmushi tare da sake sunkuyar da kanshi qasa, Waziri ne ya karaso gurin a nutse yasa hannunsa ya d’agoshi ya miqe tsaye! wani qayataccen murmushi yayi wanda yay masifar yi masa kyau tabbas da yasan dariya nayi masa kyau to da ya mayar da hankali gurin yi…….Rungume ‘Kanin mahaifin nasa yay a daidai kunnansa ya furta “Baba Waziri ina fatan duk na same ku lafiya.” Waziri cike da walwala da farin ciki yace.”Lafiya lau ka same mu Aliyu haki’ka muna farin cikin dawowarka masarauta lafiya.” Idanunsa dake lumshe ya bud’e! still da ragowar murmushin a fuskarsa yana kokarin yin magana suka hada ido da Galadima shida Ciroma suna tsaitsaye a inda suke fuskarsu babu wata cikakkiyar walwala.

Gyara fuskarsa yayi dan saboda yasan halinsu da rainin hankali suna iya tsinkashi a gaban mutane a kullum burinsu suga sun ‘bata masa rai tun yana yaro suke nuna masa qiyayya tamkar wani abokin gabarsu.

Inda suke ya nufa ya d’an risina cikin nutsuwa yace.”Ina fatan na same ku lafiya.”? Galadima ya gyara yanayin sa yana kokarin danne ‘bacin ran dake ransa yace.”Lafiya lau Alhamdullilahi ina fatan ka dawo gida tare da nasara.”
“Alhamdulillahi.” Shine a binda ya fada tare da yin kasa da kansa gami da goya hannuwansa a baya…………….Daf da zan shiga kofar mu d’aya daga cikin matsu tsaron ‘kofa ya dakatar dani, tsayuwa nayi ina kallonsa har ya qaraso inda nake, Yace.”Waye ya baki ikon barin gurin taro bayan ba’a tashi ba.” Kai tsaye nace”Kaina ne yake ciwo sannan rana na takura min shiyasa na dawo gida.
Shar’be’biyar bulalar hannunsa ya labta min a qafafuna yace.”Kina a matsayin baiwa maqasqanciya kike wannan maganar, baki san abinda kikayi ya sa’bawa dokokin masarauta ba to bari kiji har iyayenki sai an hukunta sabida abinda kika janyo musu.” Wani irin gumi! nake ina kallonsa bakina sai rawa yake yi ga wani irin zafi da kafafuna sukeyi min.
Bulalar ya sake d’agawa zai shaud’a min nayi saurin riqe hannunsa hawaye suka ‘kwace min nace”Bafa ni da lafiya na fad’a maka kaina ke ciwo sannan ga rana a gurin laifi ne dan na dawo gida na huta.”!

Finkice bulalar yayi daga hannuna ya daga da karfin gaske ya shaud’a min a bayana ban san sanda na k’wallara k’ara ba, wannan ‘karar da Sumayya tayi har can gurin taron babu wanda beji ba.
Maimartaba ya tashi fadawa da sauri yace suje su duba cikin gidan………..”Wuce mu koma gurin taro ki fuskanci hukunci ko su waye iyayenki a cikin gidan nan kin janyo musu fushin masarauta.” Abinda yake fada min kenan tare da inginza ni wai lallai sai mun koma gurin taron, ni kuma tsabar taurin kaina sai turjiyewa na keyi hawaye na zuraro min.
Fadawan da Sarki ya turo suka karaso gurin suna tambayar abinda ke faruwa, a take Sarkin kofa yayi musu bayani, Naga babban cikinsu ya zare min ido hade da buga min razananniyar tsawa! ya bani umarnin shigewa mu tafi. Turjewa nayi ina kallonsa da busassun idanuna a fusace! ya tattare babbar rigarsa ya d’auki ni ya sa’ba a kafad’arsa kai tsaye gurin taron ya nufa dani ina kuka da dukansa da zille zille haka ya dinga ratsa mutane dani bai dure ni a ‘ko’ina ba sai gaban maimartaba. gurfana nayi nayi qasa da kaina hawaye na karakaina a fuskata…….Lawi da matarsa hankalinsu ya tashi dan ganin ‘yarsu a gaban maimartaba da alama ta janyo musu fushin masarauta sai duk jikinsu yay sanyi cikin kaskantar da kai suka sunkuyar da kansu gabansu na faduwa, Gabad’aya gurin shuru yay kowa na jiran sarki yayi magana…..wanda har lokacin Yarima Ali! na tsaye goye da hannu kamar wani soja! Maimartaba ya kalli bafaden yana bukatar karin bayani.
Da sauri ya sunkuyar da kansa kasa yace.”Ranka ya dade wannan yarinyar can cikin gida muka sameta tare da d’aya daga cikin masu tsaron kofar bangaran bayi suna jayayya da juna kan umarnin daka bayar.” Mai tsaron kofa yace.”Allah ya taimake ka na ganta zata shiga gida sai na dakatar da ita tare da tambayarta wanda ya bata izinin baro gurin taro bayan ba’a tashi ba shine take fadin maganar da bata cancanta ta fito daga bakinta ba a matsayinta na makaskanciya bai kamata ta nuna gazarwata gurin jimirin tsayuwa a cikin rana domin tar’bar Yarima Ali ba, yarinyar tayi min bayani cewar ita ba zata iya tsayuwa a cikin rana ba.”
Gurin yay tsit kowa na mamakin furucin da ‘yar gidan Lawi bawa! tayi shin da me take taqama dashi ko kuma dame tafi sauran bayin dake masarautar da har take fadar wannan maganar…….Yarima Ali kansa a kasa kamar mai kallon kasan gurin amma yarinyar kawai yake kallo takasan idanunsa bakin gilashin dake idonsa shi ya hana a gane ita din yake kallo, mamaki maigirma yake akan furucin yarinyar ba zata iya tsayuwar a rana ba saboda bata daukeshi da mahimanci a cikin masarautar ba, murtuke fuskarsa yayi ya kauda kansa daga gefan da take gurfane wani irin tsanar yarinyar yaji a cikin zuciyarsa…….Maimartaba yay gyara murya a nutse yace.”Yarinya meye sunanki.”? Murya na rawa tace”Ranka ya dade sunana Sumayya Lawi mahaifina shine ke kula da ‘bangaran dokuna.” Sarki yay shuru na minti biyu kafin yace.”Sumayya me yasa kika karya dokar masarauta bayan kin san dacewa qa’ida ne idan na kira taro kowa ya hallara kuma masarauta bata bawa kowa damar tafiya ba sai na tashi shin kin san muhimmacin wannan ranar a gurina da masarautar gabad’aya.”? Kanta a ‘kasa ta girgiza kai da fad’in “A gafarce ni a ranka ya dad’e nima ba’a son raina ba wallahi kaina ne keyi min ciwo.” Jin abinda tace yasa Yarima Ali harar gefan da take yaja tsaki ‘kasa-‘kasa d’auke kansa yay yana sake ‘bata rai.

Sarki! yace.”Naji uzirin ki Sumayya mai yasa da zaki tafi baki nemi izini a gurin wakilai ba.” Shuru tayi tare da kaskantar da kanta kasa….Maimartaba yace.”Wannan rana nada mutukar mahimanci a gurina da masarautarmu rana ce wacce ya kamata mu sata a cikin kudin tarihin masarauta, tsayin shekaru goma sha biyar masarauta tayi ba tare da d’an cikinta ba wato Yarima Aliyu mai jiran gado…..Tun yana da shakaru goma sha biyu a duniya ya sauke al’kur’ani maigirma tare da sauran littafan addini sai na turashi can kasar amuruka domin neman ilimin zamani Aliyu ya za’bi karatun likitanci wanda ya tabbatar min dashi ne ra’ayinsa ni kuma na goya masa baya domin ya samu ingantaccan sani ta kowane ‘bangare..Alhamdulillahi ya sama dukkanin abinda ake bukatar a samu muna sanya ran dawowarsa gida sai ‘kasar ta b’ukaci daya zauna da ita domin ya taimaka musu da abinda Allah yayi masa, ina zaune a fada sa’ko ya isa gareni akan wannan magana, ba’a son raina na amince da zamansa a kasar ba sai dan ganin shi ya nuna yana bukatar ya zauna ya taimaka musu yasa na amince masa, anan yake tabbatar min da cewa shekara bakwai kacal zaiyi dasu ya ajiye aiki ya dawo ‘kasar sa domin suci moriyarsa wannan dalilin ya sanya na amince da bukatarsa…..A Yau ne Allah yayi nufin dawo dashi gida gabad’aya kamar yanda yayi min al’kawari, wannan dalilin yasa na bada umarni kan cewa dukkanin wanda yake karkashin masarautar nan ya fito domin ya nuna farin cikinsa akan dawowarsa gida lafiya, sai gashi ke! da baki san shi ba kin kasa tsayuwa ki tantance shi ki kama hanya kin tafi koda yake kema kin kawo uzirinki ciwo ya wuce komai! saboda haka anyi miki afuwa abisa karya doka da kikayi amma kada ki sake kwatanta abinda kikayi a yanzu dai masarauta ta yafe miki laifin da kika kaita.”

Kaina a ‘kasa nace”Godiya nake ranka ya dad’e ubangiji Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana insha Allahu ba zan kara ba.” Lawi da Tambaya iyayena sune suka karaso gurin suka gurfana gaban maimartaba suna godiya gami da sake neman afuwa.” Maimartaba ya girgiza kansa a nutse yace.”Babu damuwa kuna iya tashi.” Da sauri muka miqe a tare muka koma muka tsaitsaya cikin ‘yan uwanmu bayi…….
BINTA UMAR ABBALE
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)

7&8
Tamkar mai tausayin taka k’asa haka yake cire qafa yana tafiya kanshi a ‘kasa hannuwansa a goye a baya, Shatima da Moddibo suna gefe da gefansa sai hira sukeyi masa yana dai jinsu da kunne amma ya gagara cewa uffan sai dai idan sun fadi maganar da ta bashi dariya yayi murmushi had’e da girgiza kansa, Yarima Ali mugun miskili ne wanda magana ke masa wuya shiyasa mafi akasari mutane ke ganin kamar dan wulakanci ne ‘Dabi’arsa ce ta rashin son magana da hayaniya gami da rashin fara’a ‘yan uwansa da iyayensa sun san wannan halin nasa tun yana yaro dashi ya taso, tun kafin su qarasa bakin kofar masu tsaron gurin suka zube gwiwowinsu a kasa sunkuyar da kansu sukayi hade da d’unkule hannuwansu alamun gaisuwa.
Shatima da Moddibo ne kawai suka d’aga musu hannu shi kuwa gefan da suke ma bai kallaba ballantana yasan sunayi…….Shatima ne yasa hannu ya bude narkekiyar kofar da zata sada su da falon Fulani wato mahaifiyarsa, A nutse yasa kafarsa cikin falon tare da sauke ajiyar zuciya, lumshe idonsa yayi yana jin wani irin sanyi na ziyartar zuciyarsa yau dai Allah ya dawo dashi gida gaban iyayensa hakika babu wanda ya kaishi farin cikin wannan rana……Bude lumsassun idanunsa yayi ya sauke su a kanta tana gishingide kan kilishi jakadiyarta na gefanta a zaune tana mata firfita da wani irin mafice, Mama fulani kyataccan murmushi ne a fuskarta ta zuba masa ido tana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyarta.

Da sassarfa ya k’arasa kusa da ita yayi zaman raquma a gabanta tare da sunkuyar da kansa yace.”Mammah hakik’a yau ni dake ban san wanda yafi wani farin ciki ba nasan zuciyarki tana cike da farin cikin dawowata gida wannan dalilin ne ya sanya na kasa shiga sashena nace lallai sai nazo nayi tozali dake uwa tagari nayi farin ciki dana dawo gida na sameku cikin koshin lafiya keda maimartaba da duk wani makusancina.”

Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara zamanta hannu ta dora a saman kansa a nutse tace”Allah yayi maka albarka babana nayi mutukar farin cikin dawowarka masarauta lafiya tabbas farin cikin da nake ciki a yau ba zai yafi gaban a kwatanta shi zuciyata tas take da ganinka cikin koshin lafiya babana ka kara girma kayi lafiya ka kara nutsuwa ka cika mutum ta kowane ‘bangare babu shakka dole nagodewa ubangiji a bisa wannan karamaci da yayi mana ina rokon Allah ya raya min kai ya albarkaci rayuwarka da zuriar da zaka samu.”

Hannunta dake saman kansa ya r’iko yasa a bakinsa ya sumbuta lumshe idonsa yay yana murmushi yace.”Mammah nagode sosai da adduarki akoda yaushe ina alfaharin kasantuwarki a matsayin mahaifiyata.”

Murmushi tayi tare da girgiza kanta ta mayar da hankalinta kansu Shatima dake zaune a gefe da gefansa, murmushi ta sakeyi tana kokarin magana suka fara gaisheta, hannunta ta d’ora a saman kansu tace”Ubangiji Allah yayi muku albarka ya had’e kanku kuyi zumunci dan Allah tabbas nasan kuma yau kuna cikin farin cikin dawowar d’an uwanku lafiya.” Shatima yace.”Hakane Mammah hakika muna cikin farin ciki mara mislatuwa muna yiwa Allah godiya daya dawo mana dashi gida lafiya.

Har yanzu da murmushi a fuskarta tace”Yana da kyau ku rakashi ko wane ‘bangare na gidan nan ya gaisa da iyayensa kamar yanda yazo ya gaisa dani.”
Moddibo yace.”Insha Allahu Mammah.” Kallonsa tayi har yanzu yana durkushe a gabanta tace”Babana zakuje sauran sashen iyayenka ku gaisa kafin ka shiga gurinka ka huta nasa hadimai sun shirya maka komai da komai.” Hannunta ya sumbata cike da bin umarni yace.”Mammah abinda kikace shi za’ayi insha Allah.”! Miqewa yayi a nutse ya kalli ‘yan uwan nasa da fad’in ” ku Tashi muje.” Shatima da Moddibo suka miqe kai a kasa suka ce “Mammah a tashi lafiya.” Hannu ta d’aga musu fuskarta yalwace da fara’a idonta a tsaye a kansu har sai da suka fita daga falon ta girgixa kanta gami da sunkuyar da kanta kasa addua take a cikin zuciyarta kan Allah ya cigaba da had’a kawunansu suyi zumunci tsakani da Allah.

Tushen Labari
Maimartaba Sarki Adamu Abdullahi dattijon mutum ne wanda ya iya mulki gami da jagoranci akan komai maimartaba Adamu Abdullah mutum ne mai tsananin tausayi da jin’kai, baya ta’ba yarda talaka ya kaskanta kuma bai yarda da cuta gami da zalinci ba, al’ummar garin suna mutukar jin dadin mulkinsa gami da yanda yake gudanar da hukunci akan wanda yayi zalinci, Sarki Adamu yana da ‘Ya’ya amma dukkaninsu matane d’aya ne Namiji a cikinsu, sai dai ‘yan uwansa suna da yawan ‘ya’ya maza shi kadai Allah yayiwa albarkar ‘ya’ya mata sai ya bashi guda d’aya namiji wanda yake mutukar alfahari dashi kasancewarsa mai tsananin biyayya a gareshi…..Mahaifin Waziri da galadima ya rasu dama a hannunsa suka taso tare da ‘ya’yansa tare kuma duk suka gudanar da harkokin karatunsu………Sulaimanu Dan uwan Sarki Adamu ne ciki daya suka fito shine ya kasance mafi kusa dashi a fada sarki Adamo baya zartar da kowane irin hukunci sai yayi shawara da d’an uwansa wato Waziri Sulaimanu, duk da wannan karamcin da maimartaba keyi masa hakan bai sa ya janye muguwar kiyayyar da yake masa ba da shida zuriarsa kullum burin Waziri Sulaimanu yaga bayan d’an uwansa dan ya tsani ya wayi gari ya ganshi kan karagar mulki…….Shi a yanzu baya sha’awar mulkin tunda shekaru sunja masa yafi sha’awar d’ansa Ciroma ya hau kan kujarar badan komai ba sai dan kada bayan babu ransu a duniya mulki ya cigaba da tabbata a hannun zuriar dan uwan nasa wato Sarki Adamu, shiyasa kullum cikin damuwa yake gami da tunanin ya za’ayi ya ruguza karagar mulkin d’an uwan nasa, Kullum cikin shirya manakisa suke shida d’ansa Ciroma maimartaba sarki Adamu Allah na kareshi daga sharrinsu, Waziri Salmanu ganin ya kwanta ciwo sai jikinsa yay sanyi yana ganin kwanansa ya kare bukatarsa bata biya a kan dan uwansa ba, tabbas jikinsa na bashi mutuwa zaiyi sai kawai ya kira d’ansa ya zaunar dashi suka yanke shawarar karshe a tsakaninsu…….Ciroma mutum ne mara tsoron Allah da tunanin makomarsa, Kai tsaye ya shiga biye biyen malaman tsubbu bai bari ba har sai da bukatarsa ta biya ganin ya durkusar da maimartaba, mugwayen aljannu sun shafe jinsa da ganinsa kana sun kumbura masa jiki yana kwance sai sai komai ayi masa…..Wannan al’amari yayi wa Waziri Sulaimanu dadi mutuka yana kwance rai a hannun Allah amma ‘kara tsarawa d’an nasa sharri yake yi.
Hankalin iyalan Mairataba ya tashi mutuka gaya jama’ar gari suka shiga tsananin tashin hankali da damuwar rashin lafiyar data samu shugaba nagari malamai suka dinga bada taimakonsu iyakacin bakin kokarinsu…….Waziri Sulaimanu ya tara su kaf a guri daya yace”Tunda al’amarin ya kasance a haka to shi a matsayinsa na mai zartar da hukunci da yawun d’an uwansa wato maimartaba Sarki Adamu ya wakilta AbdulJabbar wato Ciroma ya zauna kan karagar mulki kafin aga abinda Allah zai zartar…..Da yawa daga cikinsu babu wanda yay na’am da wannan hukuncin to amma saboda gudun tashin hankali da gutsiri tsoma yasa sukayi fatan alkairi ga hukuncin da ya yanke……..ba’a wani ja dogon lokaci ba Ciroma ya soma zama a fada ya cigaba da gudanar da mulki cikin rashin iyawa gami da tsantsar mugunta da zalinci………A take jama’ar gari suka gane inda ya dosa gabad’aya yafi bada muhimanci akan harkar zalinci ko sharia aka kawo gabansa baya iya yanke hukuncin da sharia ta tanadar shi a ganinsa duk abinda yake daidai ne, Jama’a suka dinga k’orafi gami da surutai har labari ya isa kunan gomnati, a lokacin ta shigo cikin al’amarin bata kuma ja wani dogon lokaci ba ta sauke Ciroma daga kan kujerar mulkin, sannan kafin gomnati ta d’ora wani a matsayin sabon sarki sai da ta duba cancanta tukkuna ta za’bi Abdul-aziz ya maye gurbin mahaifinsa tunda shi cuta ta kwantar dashi…….Komai na saurata gomnati ta damqawa Abdul-aziz jama’ar gari suka dinga farin cikin samun sa a matsayin shugaba…….Wannan al’amari yayi wa Waziri Sulaimanu da d’ansa ciwo dan Ciroma kulle kansa yayi a daki ya dinga bankar giya yana tam’bele shi kadai sai zage zage yake yana surutai………..Waziri Sulaimanu kuwa sai muce tsabar bacin rai ne yasa ya had’iyi zuciya ya mutu sai shiga akayi aka ga gawarsa…..Hankalin iyalansa yayi tsananin tashi suka dinga kuka suna tofin alatsine ga zuriar Adamu suna ganin kamar sune sukayi sanadiyar mutuwar mahaifinsu…….Tun daga mutuwar Waziri Sulaimanu gaba mai tsanani ta shiga tsakanin zuria guda biyu har yanzu kuma itace akeyi ‘ya’ya da jikoki sai dai kowa na kokarin ‘boye bakin cikinsa akan dan uwansa amma daidai da kwayar zarra babu mai kaunar d’an uwansa……….bayan rasuwar Waziri Sulaimanu da sati uku Ciroma yabi dare da rana yaje ya sanyawa Sarki Adamu fillo ya toshe masa hanci murus! ya kashe shi har lahira ya fito daga dakin ba tare da kowa ya ganshi ba…..Shima iyalinsa shiga sukayi suka ga gawarsa al’amarin da yayi masifar tashin hankalinsu, Mutuwar Sarki Adamu ta girgiza zukatan al’ummar gari dayawa yawansu suka dinga kokawa suna fad’ar kyawawan halayensa…………
BINTA UMAR ABBALE
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
9&10
Sarki Abdul-aziz yayi gadon halin mahaifinsa marigayi Maimartaba sarki Adamu gurin kyawawan halaye sosai al’ummar gari ke jin dadin mulkinsa gabadaya ‘yan uwansa sunyi masa mubaya ma’ana sun bashi hadin kai sosai amma banda Ciroma muguwar hassada yake masa da kasantuwarsa a kan karagar mulki Ciroma babu irin qulunboton da ba yayi akan ya ruguza mulkin sarki Abdul-aziz Allah bai bashi nasara ba daga karshe sai ya hakura da biye biyen bokayen ya dawo yana shirya mana’kisa ta karkashin qasa….Sarki Abdul-aziz na da mata biyu Gimbiya Huwaila itace uwar gida ana kiranta da mai babban da’ki haihuwar su bakwai tare amma duk mata ne…..Gimbiya Hawwa ‘yar sarkin Agadaz itace matarsa ta biyu ana kiranta da Fulani sai da suka shekara shida da aure ta samu ciki maimartaba ya tsananta addua akan cikin yana addua akan Allah ya azurtashi da samun d’a namiji ya zama magajinsa………..Allah maji rokon bawansa sai ya amsa masa adduarsa a daidai lokacin da mutane ke tsammanin Fulani zata haifi mace sai Allah ya nuna musu ikonsa Aliyu ya diro duniya cikin koshin lafiya da kuzari…..Haihuwa wannan yaro tayi masifar tashin hankalin Ciroma ya rasa inda zai saka kansa yaji dadi, shi duk a tunaninsa Abdul-aziz ba zai ta’ba haihuwar da namiji ba saboda yana ganin duk ‘ya’yansa mata ne kamar dai yanda mahaifinsa ya dinga haifar ‘ya’ya mata kafin ya rasu…….Mai d’akinsa rasa gane kansa tayi a lokacin dan kulle kansa yake a daki yayi ta surkulle lallai sai yaga karshen jinjirin daka a haifa, wanda tunda ya dira a duniya mahaifiyarsa ta d,daura masa wata ‘yar sar’ka a wuyansa mai dauke da ayatulkursiyu a jiki, wannan dalilin yasa duk tsaface tsafacen da yake yi baya tasiri.

‘Bangaran Mai babban daki kuwa itama ita da yaranta rasa nutsuwa sukayi dan gabad’ayansu basu tsammanin Fulani zata haife cikin jikinta lafiya ba saboda irin fadi tashin da sukeyi a cewar ‘ya’yan wai su ba zasu had’a uba da kowa ba shiyasa tun sanda mahaifin nasu ya auro Fulani Hawwa suka tashi a tsaye dasu da mahaifiyarsu suka dinga jifanta da asiri iri iri wanda ya janyo mata matsala dik lokacin data samu ciki daga zarar yayi kwari sai ya zube hankalinta ya tashi sosai ta dage da azkar gami da rokon Allah ya kareta dan tayi imani cewar al’janu ne ke ra’bar jikinta tunda wani lokacin idan ta kwanta bacci suna zuwa suyi ta tsorata ta…….tunda ta samu cikin Aliyu ta dage da adduar har Allah yasa yayi k’wari gashi cikin ikon Allah ta haifeshi lafiya dalilin daya sa kenan tana haihuwarsa ta daura masa wannan laya mai dauke da ayatulkursiyu saboda tasan tilas ita da yaron su fuskaci kalubale mai girma a masarauta………..Yarima Ali ya taso cikin kauna da so da kulawar iyayensa duk wanda ya kwana ya tashi a cikin gidan yana kaunarsa, Ita kanta mai babban daki ganin kamar maimartaba naso ya gane manufarta akan yaron yasa ta zauna da ‘ya’yanta ta umarce su akan kada su sake su nunawa yaron ‘kiyayyarsu a fili komai za’ayi ta karkashin kasa za’ayi masa, wannan dalilin yasa suke danne hassadarsu a kansa suke nuna masa kauna ammfa Allah ne kadai yasan abinda ke zuciyoyinsu……….’Bangaran ‘yan uwan mahaifinsa kuwa babu wanda ke nuna masa kauna da kulawa sama da Waziri shike jansa a jikinsa sosai yana nuna masa so hakan yana yiwa maimartaba dadi a cikin ransa yana kuma yiwa dan uwan sa addua akan Allah shima ya azurtashi da ‘ya’ya masu albarka, Waziri Abdul-raham matansa uku amma duk cikinsu babu wacce ta ta’ba haihuwa sai da ya auri matarsa ta uku da yake bazawarace tana da ‘ya’ya a wani a gidan sannan aka gane cewa rashin haihuwa daga gurinsa ne shiyasa yake masifar kaunar ‘ya’yan ‘yan uwansa…….wannan dalilin yasa Ciroma da Galadima suke jin haushinsa dan ganin kamar yana fifita Yarima Ali akan ‘ya’yansu Galadima shine mahaifin Shatima shi kuma Ciroma shine mahafin Moddibbo wanda yaci sunan mahaifinsa shine suke kiransa da suna Moddibo, Ciroma Abdul-Jabbar nada ‘ya’ya goma dan duk yafi ‘yan uwansa yawan ‘ya’ya shiyasa har kullum yake fatan sarauta ta dawo hannunsa, mata shida maza hud’u, cikin ‘ya’yanshi akwai mai izzah da taqama tamkar ubanta ne a sarki a cikin masarautar haka take rashin mutunci tare da cin mutuncin duk wanda tayi ra’ayi, Gimbiya Lawisa kyakkyawa ce ta karshe sai dai ko kusa ko alama bata da kyawun hali tana da d’abiar izigilanci da wulakanta mutane mutum komai girmansa bai wuce cin mutunci a gurinta ba……..Gimbiya Lawisa tun kafin tayi wayo tayi hankali Allah ya d’ora mata masifar son Yarima Ali a cikin ranta duk da tana yarinya k’ank’anuwa ya tafi karatu hakan besa ta mance kammanin sa ba. shiyasa yanzu take ta murna da farin cikin dawowarsa masarauta sai shirye shiryen walima takeyi domin nuna masa farin cikin dawowarsa lafiya……..Da kanta ta shirya tsaf cikin shiga ta alfarma tare da bayin dake take mata baya ta nufi ‘bangaransa domin sheda masa abinda ta shirya masa na taya murna……….
BINTA UMAR ABBALE
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah)
11&12
Tun bayan fitar su Satima daga ‘bangaransa yake zaune shi kadai a guri guda ya gaza ta’buka komai kallon kasan d’akin kawai yake yana mamakin abinda ke faruwa a masarautar a lokacin da ya tafi karatu yana da kuruciya shiyasa baya saurin gane wasu abubuwan amma yanzu shigarsa sauran ‘bangarorin gidan domin gaisawa dasu ya fahimci cewar har yanzu bata sauya zani ba a tsakanin iyalan mutane uku da suke da muhimmacin a masarauta ba’a ga maciji kowanne da akwai mugun abu a zuciyarsa dangane da d’an uwansa, Lokacin da suka shiga bangaran mai babban daki gabad’aya sun hallara a falo ita da ‘ya’yanta sun kewaye ta babu wanda yasan abinda suke qullawa sai Allah…….Ganin shigowarsu ne yasa suka daidata nutsuwarsu suna masa barka da zuwa dukkaninsu sai ya’ke sukeyi da kokarin nuna masa kulawa, shi ba yaro bane ballantana ya kasa gane yanayin fuskokinsu dan wasu daga cikinsu sai satar kallonsa suke ta’kasan ido, dalilin daya sa kenan ya kasa zama ya miqe da niyyar tafiya……..Uwargida na fara’a kamar gaske tace”Magajin Sarki ka tsaya kaci abincin ma tun safe ‘Yan uwanka suka baro gidajan mazajensu suka yini suna shirya maka abun tar’ba.”
Ba tare da ya kalleta ba yace.”Nagode Gwaggo ina ganin za’a iya kai min abincin sashena idan na samu nutsuwa sai na zauna naci.” Ta washe bakinta cike da jin dadi tace”To shikkenan yanzu zansa a kai maka kamar yanda ka bukata.”
A nutse ya juya domin yiwa ‘yan uwan nasa godiya sai kawai yaga sunyi masa caaa! da ido da sauri ya sunkuyar da kansa yana mamakin kallon da suke masa tamkar basu taba ganinsa ba, babu cikakkiyar walwala a maganarsa yace.” My Aunt’s ina godiya da hidima.” Da farin ciki a fuskokinsu suka shiga amsawa, rufaffun takalmasa yasa ya fita daga falon, a tsaye a samu su Shatima na jiransa ya fito, kai tsaye suka wuce side din Baba Waziri nan ya samu cikakkiyar karba da kulawa gurin matayensa kamar yanda yake tsammani cike da jin kaunarsu yay musu sallama, Bangaran Ciroma da Galadima kuwa bai samu wata cikakkiyar kulawa ba dan kafatanin su adawa suke dashi Shatima da Moddibo ne kawai suke d’an nuna masa kauna da kulawa suma d’in Allah ne kad’ai yasan abinda ke zuciyarsu…….Wannan dalilin ne yasa tunda ya zauna yake tunanin al’amarin a rayuwarsa ya tsani rabuwar kai da lalacewar zumunci! ya fahimci suna masa hassada sosai saboda mahaifinsa ne ke kan mulki dukkaninsu suna zargin kamar shine zai maye gurbin mahaifinsa bayan Allah ya dauki ransa wanda shi kuma basu san mulki da wani abinda ya shafeshi baya daga cikin tsarin rayuwarsa, a wannan zamanin jan ragamar al’umma na da wahala mutuka shiyasa gabadaya baya da ra’ayi maye gurbin mahaifinsa.
Ya jima zaune a gefen katafaran gadonsa daya sha shimfid’u na alfarma irin na saurata kafin ya miqe a nutse ya nufi toilet din wanda shi kansa abin kallo ne duk abinda mutum ke bukata a kwai a cikin toilet d’in, tsaf yayi wanka ya fito daure da towel a k’ugunsa, a bakin k’ofa ya samu wani bawa hannunsa ringume da kayan sawa irin na sarauta.
Gefan gado ya samu ya zauna ba tare da yace komai ba, bawan ya karaso tare da durkusawa a gabanshi yace.”Ranka ya dade ni sunana Haruna ni zan dinga yi maka hidima da duk abinda kake bukata na shigo naji kana wanka sai na dau’ko maka tufafin da suka dace.”

A nutse ya d’ago kansa yana kallon kayan dake hannun bawan, manyan kaya ne irin na saurata har da nad’i da katuwar alkyabba sam ba zai iya sanya kayan nauyi a jikinsa ba.

Girgiza masa kansa yayi a nutse yace.”Mayar da wa’innan kayan ka dauko min masu sauki.” Da saurin ya miqe da kayan a hannunsa ya bud’e shirgegiyar wardorobe din dake kafe a bangon dakin ya ajiye kayan tare da nemo masa irin kayan da yake bukata……Farin yadi filtex mai taushin gaske ya dauko mashi ya jiye kusa dashi kana ya sake komawa wardorbe din ya dauko wani dan madaidaicin akwati shima yazo ya ajiye masa a kusa dashi……..Wata iriyar hula naga ya dauko mai tafe da takalminta yazo ya tsuguna tare da cire ledar data lullube hular da takalmin ya d’ora kan kayan ya miqe tsaye da sauri tare da matsawa gefe guda kansa a kasa yace.”Ranka ya dad’e na dauko maka dukkanin abin bukata ka duba ka gani idan da akwai wani abinda kake bukata.

Gefan da kayan suke a ajiye ya duba minti biyu yana kallon gurin kafin yace.”Jeka nagode.” Da sauri ya sunkuyar da kansa kasa gami da fadin”Godiya nake Magajin sarki.” yana gama maganarsa ya bude kofar dakin ya fita da saurin gaske……..A nutse ya miqe ya nufi gaban mirror din dake cike da kayan shafe shafe da turaruka na mussaman irin na masu sarauta, Cream kawai ya shafa a jikinsa ya shafawa jikinsa turare mai kamshi, kana ya bar gurin, tsaf ya shirya jikinsa cikin farin yadin wanda akayi masa d’inki mai yankakken hannu irin na zaman gida gaban rigar da bayanta anyi aiki da farin zare wanda yake nuni da tambarin masarautar, a nutse ya bude akwatin nan naga tarin agoguna da manya manyan zubonan azurfa kala kala sai sheqi sukeyi, agogo mai sarqa yasa a hannunshi na dama kana ya zura wasu zubonan azurfa a tsayunsa guda biyu na hagu da dama, zubonan suyi masa kyau sosai da sosai. ya mayar da a kwatin ya rufe ya dauki hular yana gyarata hula ce aka d’inkata da wani irin yadi mafi akasari ma masu saurata suke amfani da ita tsayin hular ne ya bashi dariya ya dinga duba hular yana tunanin ajiyeta ya bar kansa a haka sai dai yayi dubarar lankafe saman ta ya rage mata tsayi yasa a kansa kana ya zura takalman dake gabanshi masu kalar hular …..Gaban mirror ya tsaya yana sake duba kansa, murmushi ya dinga yi yana shafa siririn sajen fuskarsa lallai malam bahaushe yayi gaskiya da yake fad’in kowa ya bar gida to gida ya barshi, yaushe rabonsa da sanya manyan kaya a jikinsa, sai yaga shi kansa ya k’arayiwa kansa kyau da kwarjini wannan zungureriyar hular da yake wa dariya yaga tayi masa kyau sosai ta sake fito masa da kewayayyar fuskarsa mai dauke da k’ayataccen sajensa, ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya bar gurin mirror kai tsaye hanyar fita daga dakin ya nufa………..Yana fitowa Haruna dake tsaye kamar gunki a kofar dakin yayi kasa da kansa tare da fadin”Barka da fitowa.” Ba tare da yace masa komai ba ya wuce cikin falon…..Nan ya ganta a hakimce a kan kujera k’afarta d’aya kan ‘daya tana sakar masa kyakkyawan murmushi………..Idonsa a tsaye a kanta ya samu guri ya zauna cikin d’aya daga cikin k’ayattatun kujerun dake kewaye da falon Wani irin zama yayi irin na masu mulki yasa mata idonsa yana kallo fuskarsa babu d’igon annuri.
Gimbiya Lawisa cikin iyayi da iyawa ta ma’kale murya tare da fadin “Barka da fitowa magajin sarki inayi maka barka da dawowa masarauta lafiya.”
falon shuru yayi bayan gama maganarta tana jiran amsarsa taji shuru bece komai ba, dago kai tayi tana kallonsa taga yana ta kallon jikinta…….Yarima Ali na da muguwar d’abi’ar san mata dan ko acan amurukan ma shagalinsa ya sha da matan turawa da bakaken fata amma duk kulafucinsa bai ta’ba zina ba sai dai romancing nan yake biyawa kansa bukata, yana da bala’in san mata masu kyau da k’irar jiki, Gimbiya Lawisa nada kyau da lafiyayyan jiki shiyasa ya gaza dauke idonsa daga kanta sha’awarta ce ta d’arsu a zuciyarsa. Ganin tana kallonsa tana murmushi yasa yayi gyaran murya da kyar yace.”Daga wane ‘bangare kike.”? ‘Yar dariya tayi tana kallonsa tace”Yanzu dan Allah baka gane ni ba ? nice fa Lawisa ta gurin Baba Ciroma ‘kanwar Moddibo.”‘
Sajensa ya shafa har yanzu babu fara’a a fuskarsa yace.”Ya za’ayi na gane ki bayan rabona daku sama da shekara goma lokacin dana bar gida ina tsammanin baki kai shekaru bakwai a duniya ba.”
Tace”Eh hakane kam shekaruna takwas a lokacin daka tafi karatu amma kuma ni kaga ban mance da kai ba.”! Shuru yay yana kallonta, Ta cigaba da cewa”Wannan dalilin ne yasa ma na shirya gagarimar walima domin taya ka murnar dawowa gida lafiya.” Murmushi yayi yana kallonta yace.”Nagode ‘Kanwata inaso naga ana nuna kulawa akaina nayi farin ciki sosai da wannan karamcin yaushe ne kika tsayar da taron.

Cikin farin ciki da jin dadi tace”Naji dadi sosai daka kar’bi magana ta da mahimanci nagode sosai sannan kuma ranar jumaa ne ranar dana tsayar domin taron walimar.” Da ragowar murmushi a fuskarsa yace.”To shikkenan Allah ya kaimu ranar lafiya.”
Falon yayi shuru Lawisa sai sa’ke-sa’ke take a cikin ranta tana tunanin ko kawai ta fad’a masa tana sonsa tunda taga nan da nan ya kar’bi maganar da ta kawo masa da muhimanci…..tana kokarin tayi magana……Aunty Safiyya d’aya daga cikin yayyunsa ta shigo falon bayanta wasu bayi ne mata guda biyu suna dauke da tire din abinci kai tsaye can gurin daining suka……….Aunty Safiyya ganin Lawisa a zaune tana murmushi yasa tayi saurin kallonta ta kalli ‘kanin nata sai kawai taji farin cikin ganinsu a tare lallai babu shakka Lawisa zata taimaka musu gurin ganin bukatarsu ta biya a kansa…..Cike da farin ciki gami da nuna jin dad’i tace”A’a k’anina soyayya akeyi ne.” Kansa ya sunkuyar qasa bece uffan ba.
Ita kuwa Lawisa sai murmushi takeyi na jin dadi tana kallon aunty Saffiyan tana sunkuyar da kanta.
Kusa dashi taje ta zauna kamar gaske ta dafa kafad’arsa da fadin” A gaskiya nayi farin cikin ganin ku a tare dama babban burinmu a yanzu kayi aure ka sake zama babban mutum to alhamdullilahi tunda ma ‘yar gida za’ayi towo na mai na ne abun yayi dad’i nasan kuma iyayenmu zasuyi farin ciki mutuka, kuma inaso na tabbatar maka da cewar kayi sa’ar matar aure domin dai Lawisa babu abinda ta nema ta rasa na bangaran kyawun hali ga uwa uba kyawun sura.”

Ya d’ago kanshi a nutse yana kallonta “Aunty Safiyya waye yace miki soyayya muke? fitowa ta kenan daga daki na sameta a zaune dan sai da ta gabatar min da kanta na gane cewar famliy nace, tazo tana sheda min walimar da ta shirya domin murnar dawowata gida wannan shine dalilin daya saka kika gan mu a tare.”
BINTA UMAR ABBALE

Shearing 👏🏻👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah)
13&14
Aunty Safiyya a nutse take kallonsa kafin tace”Kai kuwa Magajin sarki meye laifin Lawisa dan Allah kada kaje ka dauko mana ta waje gwanda ka duba a cikin gida ina ganin kamar haka zaifi alkairi.” Shuru yayi mata tare da sunkuyar da kansa. Tace”Idan ka auri ‘yar uwarka a ganina sai kafi samun cikakkiyar kulawa kuma tabbas hakan zai faranta ran iyayenmu dan Allah ka duba maganata da kyau kaji ko.”! har yanzu kansa na sunkuye a kasa ya’ki kallonta ballantana ya bata amsa. mirmushi tayi tare da mikewa da fadin”Miskili kenan to kai dan Allah da irin wannan halin naka wacece zata iya zama da kai idan ba ‘yar uwarka ba? babu macan da zata juri wannan wulakancin naka.”
‘Dago kansa yay yana kallonta cikin rashin walwala yace.”Aunt Safiyya mai yasa kuke yi min irin wannan kallon ne? wallahi ban san ya ake wulakanci ba a rayuwa ku lura da kyau da’bia tace rashin son doguwar magana shiyasa nayi shuru na kyale ki amma duk irin maganganun da kikeyi ina jinki.”

Murmushi tayi tana kallonsa tace”Eh ni zan fadawa kowa hakan d’abi’ar kace shiyasa ma ai nace bama so ka auri bare gwara ka auri ta gida domin sai tafi jurar zama da halayen ka.” murmushi yay wanda ya tsaya iya lab’bansa yace.”Aunt Safiyya ki bar wannan maganar dan Allah.” Jin abinda yace yasa Lawisa saurin kallonsa gabanta na faduwa lallai wallahi tasa rai ganin aunty Safiyya ta shiga maganar yasa take jin tamkar ma ta aure shi ta gama.

Aunty Safiyya ta kalleta tare da fad’in “Lawisa kina sonsa ko.”? babu kunya tace” Eh aunty. ” murmushi tayi tare da kama hanyar fita tana fadin”Ba zan tafi gida ba har sai na bari an tashi daga fada na fadawa maimartaba halin da ake ciki.
Da sauri ya dago kansa yana kallon bayanta cike da mamakin jin abinda ta fad’a……Fuska a kirne ya kalleta da fad’in “Tashi ki fitar min a daki wato dama abinda ya shigo dake kenan? waye ya fad’a miki ina sha’awar auran zumunci dake.”?

Lawisa gabanta ya dinga faduwa tana so tayi magana amma ta kasa saboda tsabar kwarjin da yayi mata gashi ya tsareta da idanunsa masu girman da furgita mara gaskiya.

A sanyaye ta miqe tana gyara alkyabbarta hanyar fita ta kama ranta sai tafarfasa yake yi lallai wai duk wannan kyawun nata da kyawun surar jikinta bata burgeshi ba hakika taji takaicin tsawar da yayi mata meye laifinta da zaice baya sha’awar auran zumunci da ita…….masu take mata baya ganin ta fito fusace yasa suka shiga hankalinsu da sauri suka rufa mata baya suna sunkuyar da kansu ‘kasa………….


Cikin saurin na fito daga gurin mu domin zuwa duba dawakan da babana ke hidimarsu tun safe dana zuba musu abinci ban sake zuwa duba su ba saboda yini mukayi wankin kayanmu nida mahaifiyata wannan dalilin ne yasa ban je gurin da wuri ba…………Ina daf da shiga kofar dawakan na hangeta ita da masu take mata baya, sanin halinta naso a girmamata yasa na sunkuyar da kaina qasa har suka karaso gurin nace” Barka da yamma ranki shi dad’e.” banza tayi min bata amsa ba sai hararata take ni kam ban san me yasa ta tsaneni ba tsakanina da ita harara ne da kallon banza. Ganin taki amsawa yasa da sauri nayi nufin shiga kofar……Naji ta daka min tsawa da fad’in “Ke! mahaukaciya dawo ki tsaya a inda kike ko nace ki tafi ne.”? Cike da mamaki nake kallonta kafin nace” Ranki ya dad’e na gaishe ki kin’ki amsawa me kike so nayi miki a yanzu ina da uziri zan zubawa dawakai abinci.”
Kallona naga tanayi tana girgiza kanta, ni kaina sai da na gama maganar nazo ina nadama sabida nasan na tarowa kaina jaraba, ni haka nake bana barin magana a cikina idan mutum ya gaya min biyar sai na fada masa goma gashi bani da tsoro ko kad’an cikin dubbanin mutane aka ajiye ni zan iya kwatar kaina saboda ina da baki.

Inda nake tazo ta tsaya tana yi min wani irin kallon raini! kafin na ankara naji yawun bakinta a fuskata, da sauri na dago kaina ina kallonta……..Tana wani irin huci! tace”Yanzu Sumayya a matsayinki na makaskanciyar baiwa a gidan nan har kina da damar tsallake umarnina nace miki ga abinda nake bukata kice kina da uziri.”?

Hannu nasa na goge yawun data tofa min nace”Ranki ya dade ki gafarce iya bakin kokarina nayi miki na baki girmanki na risina na gaishe shin to dan Allah dan annabi me kike so nayi miki .”
Mari! ta kwad’a min a kumatuna kafin na dawo daidai ta sake waska min wani a d’aya gefan! Ido jawur nake kallonta ina jin tamkar nima na fitar da hannu na rama! marin……hannu ta daga kawai tana nuna ni tsabar b’acin ran dana kuntunka mata ya hanata magana, a rayuwar Gimbiya Lawisa tun tasowarta a gidan sarautar babu wanda ya ta’ba yi mata gardama akan umarninta sai Sumayya……Juyawa nayi zan shiga kofar dawakai ta janyo faffad’an wuyan rigata aikuwa a take rigar ta yage da yake rigar ta yadi ce mai dogon hannu zanin kuma na shadda kamfala shine uniform din mu a cikin gidan mata zani maza wando amma dai duk ranar jumaa muna sanya tufafi masu kyau domin girmama ranar haka ma ranar sallar ‘karama da babba sarki nayi mana d’inkuna na atamfofi muyi ado domin murna da zuwan ranar………Hannu nasa da sauri na dafe wuyan rigar ganin yana kokarin sab’ulewa. Tsira mata ido nayi rai a ‘bace! nace tsirara zakiyi min ne? kada fa ki manta kema macace idan kinyi min tsirara a idanun jama’a kamar kin tonawa kanki asiri ne.”
Wani marin ta sake bani tana huci! ni kuma mirmushin takaici nayi hannuna dafe da kuncina ina kallon ikon Allah……..Jama’a ne suka taru a gurin sai bata hakuri suke harda masu durkusa mata, Buba ta kalla dake riqe da shar’be’biyar bulala tace”Bani bulalar nan.” Da sauri ya mika mata yana fadin “Tuba take ranki ya d’ad’e.”……..Ganin ta d’aga bulalar zata shaud’a min yasa nayi saurin fizgewa na nannad’eta a hannuna sai kawai muka tsirawa juna ido nida ita jama’ar dake gurin da ita kanta mamakin karfin halina suke………Ta girgiza kanta tana kallon Buba tace” Inaso ka samo igiya mai kauri ka daure mata hannuwa da kafafu yau nayi al’kawarin sai naga karshen taurin kanki.”…………..Kallonta kawai nake tsabar takaici da bakin ciki yasa nake jin kamar na zazzabga mata bulalar dake hannuna, ina kallon Buba ya tawo da murtukekiyar igiya gabana ya yanke ya fad’i ganin ya nufo inda nake………………..yasa na juya baya ina neman mafaka babu dan duk ko ina mutane ne sun kewaye mu, tsugunawa nayi a kusurwa hawaye ya kwace min, Buba babu tausayi yazo ya shiga kici kicin daure min hannuwa da kafafuna sai tirje tirje nake ina haurinsa amma sai da ya samu nasarar daure ni tamau! gwiwowina a kasa kaina a sunkuye na soma jin saukar bulala a gadon bayana…….tsabar taurin kaina yasa na kasa motsi ina dai jin radad’in bulalar na ratsa min jiki amma saboda na nuna mata a banza takeyi yasa na daure………Gimbiya Lawisa sai da jikinta yay sanyi ganin ko gezau na ‘kiyi ballanatana na nuna mata ina jin zafin bulalar, tunani tayi ko itace ba ta iya bulalar ba rai a ‘bace tace”Buba zo kayi mata ka tabbatar da cewa ta ratsa jikinta shegiya basamudiya yanda take da wannan gansameman jikin dama ai duka ba zai ratsa ta ba.” Gefe ta koma tana haki! dan ba karamin galabaita tayi ba.” Buba cike da bin umarni ya daga bulalar zai shaud’a mata, muryarsa ta katse masa hanzari…..Kafatanin jama’ar dake gurin suka juya suna kallonsa ganin ya nufo gurin ne yasa kowa yayi k’asa da kansa har ita Lawisan sunkuyar da kanta tayi……Cikin nutsuwa ya ‘karaso gurin aka bud’a masa hanya ya shiga har inda nake durkushe! ta ‘kasan idona nake kallonsa yana tsaye hannuwansa duk biyun a baya sai kalle kalle yake a gurin kafin naga ya kalleta babu fara’a a tare dashi yace.”Yace.”Meke faruwa ina zaune Haruna ke sheda min ga jama’a sun taru kuma kina gurin saboda haka inaso nasan abinda ke faruwa.”
BINTA UMAR ABBALE

Shearing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA”ATU S YARI
(Kainuwa dasha Allah✊🏻)
15&16
Ganin yanda ya tsira mata idanunsa gami da sake tamke fuskarsa ya sanya jikinta yay sanyi tana jin tsoron ya tozarta a gaban wa’inda suke ganin kima da mutuncinta………Cikin kokarin aro jarumta tace”Tunda nake a cikin gidan nan babu wanda ya ta’ba yi min musu akan umarnin da zan bashi sai wannan ba’kar yarinyar mai fuska irinta ba’kar akuya ta raina ni sosai sai kace ni din abokiyar adawarta ce, gabad’aya mutane suna gaisheni suna bani girma da mutuncina amma ita kokarin ratse ni take ta wuce ina ganin ko wane irin hukunci nasa ayi mata ya dace da ita sabida ta kasa mutunta ni.”

Wani irin kallo yake min tamkar yana kallon abu mai muni! koda yake ban sani ba ko shima ya hango munin nawa da mutane suke fad’arsa wannan dalilin yasa da sauri na sunkuyar da kaina kasa zuciyata tana wani irin zafi! ta k’asan idona nake kallonsa sai ya mutsa fuska yake yana kare min kallo.

A dan sace na dago kaina muka had’a ido dashi! da sauri na kalli inda ya k’urawa ido a jikina…..Cikakken kirjina dake cike dana shanu naga yana satar kallon inda rigata ta yage, nasa hannuna da sauri na sake rufe gurin ina jin wani mugun haushinsa ni ban san meye a jikina ba da maza suke lalacewa gurin kallona, ni dai nasan bani da wani cikakken kyau ga shegen baqi sai kace me? ban sani ba ko nonowa na da suka rinjayi kirjina ne ke d’aukar hankalinsu ko kuma mazaunai na wanda suka cika bayana tamkar suyi magana ni kaina na san a fiska ban cika kyau ba amma na amince da cewar a jiki na cika cikakkiyar macan da kowane namiji yake bukata.

Da sauri na dago kaina ina kallonsa jin kamar yana magana cikin ‘bacin rai! Aikuwa fad’a sosai yakewa Gimbiya Lawisa gami da nuna mata muhimancin mutun komai lalacewar dan adam tunda Allah ya karramashi to kaima sai ka mutuntashi.” Gimbiya Lawisa cikin takaici take kallonsa sam bata dauka zai goyi da bayan yarinyar ba, ranta a ‘bace ta bar gurin yaranta suka bi bayanta da sauri…….A nutse yace.”Kowa ya koma bakin akinsa.” Minti uku gurin ya watse kowa ya nufi inda yake….Hannuwansa na goye a baya ya tsirawa kasa ido yana kallo, cikin zuciyata nace”Anya kuwa wannan guy yana da lafiya gaskiya da matsala a tare dashi duba da yanda yake nacin kallon ‘kasa sai kace wani makaho.
Rigata na dafe na yunk’ura da kyar na mike tsaye. nayi nufin shiga kofar dawakai naji maganarsa.
“Koma ki tsuguna inaso nayi magana dake.” Da sauri na tsuguna tare da sunkuyar da kaina kasa…….sai da yaja dogon lokaci sannan yace.”Me yasa bakya mutunta Lawisa ko mahaifinki nada rawani a masarauta shiyasa kike gani tamkar daidai kike da kowa.”

Maganar tayi min ciwo sosai amma sai na daure wa zuciyata dan saboda nasan bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane…..”Ranka ya dad’e wallahi ina mutunta ta ina gaisheta a duk sanda zamu hadu itace dai ta tsane ni ban san me yasa ba kuma ko yanzu kafin al’amarin nan ya faru sai da na gaisheta tukkuna, maganar rawani kuwa mahaifina ba kowa bane a cikin masarautar nan fyace bawa mai d’aukar d’awainiyar dawakan dake cikin masarauta, sunana Sumayya sunan mahafina Lawi.”

Shuru yayi yana kallonta yana tuno ranar daya dawo ranar da take cewa ba zata tsaya a rana ba .” Babu annuri yace.”Okey kece ranar dana dawo kika nuna gazawarki akan tsayuwa a cikin rana ko.”?
sunkuyar da kaina nayi gabana na faduwa…..Ya ‘bata fuska sosai yace.”Ke da bakin ki kin fad’i cewar babanki bawa ne wanda nasan a cikin bauta aka haifi iyayensa, sannan aka haifeshi shi kuma ya haife ki to me zai sanya ke! kike nunawa masarauta gadara gami da rashin girmama dik wanda yake sama dake.”

Shuru nayi mishi dan banga rashin kyautawar da nayi ba, iyakacin bakin kokarina ina girmama duk wanda ya dace na girmama a masarautar to ban san kuma wane girma zan bata ba.

Tsaki yaja yace.”Tashi kije amma kada ki sake kwatanta abinda kikayi a wannan masarautar wanda keda muqami ko kuma ya gaji sarauta shine zai nuna iko akan komai amma banda ke da kike a matsayin baiwa ‘kasa da sama to wane gadara da izzah zaki nunawa mutane? kinyi sau biyu kada kiyi na uku idan kika sake da kaina zan hukunta ki.”

Cike da mamaki nake kallonsa nace”Ranka ya dad’e a gafarce ni watakila maganar da zan fad’a ba za tayi maka dadi ba, sai nake ganin ita izzar da kake magana akanta ai ba abu ne mai kyau ba izzah! da buwaya gami da iko duk na Allah da Annabi ne, wani Sarki ko mai wani mulki dashi da muqarabbansa duk aro Allah ya basu kuma idan suka kauce hanya akan mulkin da Allah ya basu dole a lahira Ubangiji ya hukuntasu saboda haka ni banga ma’anar wannan maganar da kayi ba dan izzah! na d’aya daga cikin munanan ayyuka.”

Kawai naga ya tsira min ido yana kallona fuskarsa tamkar hadarin dake dab da zubar da ruwa! sunkuyar da kaina kasa nayi na dafe a kasan gurin da hannuna nace”A gafarce ni idan maganar da nayi ta ‘bata maka rai.”
Mikewa nayi na shige kofar dawakan wanda ko ban juya ba nasan bina yake da kallo.

Ya jima tsaye a gurin yana kallon kasa! mugun mamakin yarinyar yake da kalaman da tayi wato tana nuna masa ba zata bi umarninsa ba, tana nuna masa shi din jahili ne be san abinda yake ba tunda gashinan a cikin maganarta har tana kawo masa hadisai! tunda yake ba’a ta’ba katse masa hanzari ba idan yana magana sai yarinyar yana da kyau ya nuna mata muhimancinsa a cikin masarautar.

Koda na gama abinda nake a ciki na fito samunsa nayi a tsaye a inda yake sai kace wani dogari yana tsaye hannu a goye a baya sai kallon kasan gurin yake yi, na girgixa kaina tare da kokarin ratse shi na wuce.

Gyaran murya yay kafin yace.”Tsaya nan gurin.” Da sauri na tsaya nayi kasa da kaina, karasowa yay ya tsaya daf dani har ina jiyo wucin numfashinsa, gabana ya shiga faduwa fuskata na dago na kallesa, naga sai kallona yake da tamkakkiyar fuskarsa, tsoro ne ya shiga jikina nace”Dan Allah kayi hakuri ranka ya dade wallahi ban fada maka magana ba dan na bata maka rai nayi nufin tunasar da kai ne akan abinda ka manta.

Cikin fushi yace.”Kina nufin ni jahili ne kome.”? Na girgixa kaina da sauri nace”A’a ba haka nake nufi ba.” numfashi ya fesar mai zafin gaske yace.”Kada na sake fad’in wata magana ki kawo min hadisai gami da fad’ar Allah yace annabi yace na fiki sanin munin abinda kike magana akai ni inayi miki magana ne akan girmama na sama dake a matsayin ki na baiwar dake karkashin masarauta yasa nace miki lallai ki girmama wanda yake saman ki amma tunda taurin kai zakiyi akan umarnina duk ranar da Lawisa ta sake daukar hukunci akanki zan bari tunda haka kike so.

A sanyaye nace”Yanzu na fahimci maganarka insha Allah zan kiyaye zan kuma cigaba da girmama wanda ke sama dani.

Ba tare da yace komai ba ya janye daga kusa dani ya koma gefe guda ya cigaba da kallona. ajiyar zuciya na sauke gabana na fad’uwa na kallesa, naga sai kallona yake ikon Allah mutumin wai kallon k’urrular me yake min ni ba kwalliya nayi ba ba komai ba amma ya dame ni da kallo……yagaggen wuyan rigana na riqe da sauri na bar gurin tafiyata na hard’ewa nasan idanunsa ne ya janyo min hakan.

Har sai data ‘bace daga gurin sannan ya dauke idanunsa daga hanyar da tabi, yarinyar bata da wani cikakken kyau a fuska amma kuma Allah yayi mata kyawun sura tamkar ita tayi kanta, dugowa mai garin jiki gami da cikakken kirji da fad’in qugu wuyanta a cike dam!dam da wani irin guru-guru ba’kar fatarta lafiyayya lukwi lukwi sai she’ki takeyi abin sha’awa, shi kam tunda yake ganin ba’ka’ken fata bai ta’ba cin karo da fatar data burgeshi ba irin nata…..mirmushi yay gami da shafa siririn sajensa, hakika yarinyar da a waje take to babu abinda zai hanashi romancing da ita dan yayi masifar sha’awarta matsalar kawai yarinyar bata kai matsayin da zai had’a jiki da ita ba, makaskanciyar baiwa ce wacce take ci da sha a k’ar’kashinsa, daba dan haka ba da duk yanda zaiyi sai ya yaudareta ya mori albarkatun jikinta……Fitowa yayi daga gurin cikin sanyin jiki gami da rashin kuzari yake tafiya, kai tsaye sashen mahaifiyarsa ya nufa yana tafiya jama’ar dake shige da fice a gurin na gaishe shi Haruna ne yake take masa baya har ya isa kofar sashen mahaifiyarsa Haruna ya bude masa kofar falon, yayi saurin matsawa gefe shi kuma a nutse ya shiga falon da sallama a bakinsa…..
BINTA UMAR ABBALE
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740
SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)

17&18
Tana kishingid’e a killace a guri guda da cazbaha a hannunta tana lazimi yau ita kadai ce a zaune a falon babu hadimai a kusa da ita ta bukaci zama ita kad’ai ne domin ta kad’aita kanta da mahallicinta shine da dalilin da yasa ta sallami bayin dake kusa da ita.

Tunda ya shigo take sakin murmushi idanunta a kansa har ya k’asara kan kilishin da take kishingide zaman raquma yay a gabanta tare da sunkuyar da kansa cikin tsantsar ladabi yace.”Mamma barka da yamma.” hannunta guda ta dora a saman kanshi tana shafawa gyaran murya tayi tana nuna masa cewar akwai abunda takeyi….Kansa ya dago yana kallonta sai ta nuna masa carbin dake hannunta tana murmushi had’e dayi masa nuni dacewar ya jira ta kammala.

Murmushi yay a nutse yasa hannu kan tire din dake gabanta wanda ke cike da kayan marmari.. tufa(apple) ya d’auka yasa a bakinsa ya gutsira yana sake gyara zamansa a gurin.

Kallonsa take tana murmushi mai ma’ana wanda kai kana ganin yanayin fuskarta zaka gane cewar tana cikin farin ciki kuma akwai soyayya da shaquwa mai yawa a tsakaninta da yaron nata.

Magajin sarki sai da ya cinye tufa(apple) uku tukkuna ta kammala lazimin a nutse tace”Babana barka da yamma.” Ya dago kansa da sauri yace.”Mammah barka dai ina fatan kin wuni cikin koshin lafiya.” Yafadi maganar a sanda yake kokarin riko hannuwanta.

Tace.”Lafiya lau na wuni ina fatan baka da matsala dan tun safe nake jiran shigowarka yau ba kayi shigowar safe ba ina fatan lafiya.”

Zamansa ya gyara har yanzu kuma hannuwansa na rike da nata yace.”Wallahi Mammah yau bacci na yini ina yi sai gefin la’asar na tashi nayi wanka wannan shine dalilin da yasa ban shigo mun gaisa ba.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace”To alhamdulillahi tunda lafiyarka lau dama akwai muhimiyyar maganar da nake so mu tattauna da kai.”

Ya sake gyara zamansa cikin kulawa yace.”Ina sauraran maganar Mammah.” Da farin ciki ta tare da ita tace”Ashe bayan dawowarka gida kun shirya tsakaninku kai da Lawisa ‘yar gurin Kawun ka Ciroma d’azu da safe maimartaba yake sheda min yanda al’amura suka kasance hakika naji dadi sosai daka za’bi matar aure acikin dangi ina ganin hakan sai yafi mana kwanciyar hankali da kai baki daya.”

Shiru yayi kansa a kasa ya rasa abinda zaice. ashe sai da aunt Safiyya taje ta fad’i maganar wallahi shi ya dauka da wasa takeyi! tunda yake bai ta’ba sha’awar auran zumunci ba saboda gudun lalacewarsa yafi so ya fita waje yaje can ya auro saboda baya so ya auri ‘yar dangi zumunci ya sake lalacewa dama a lalace yake shiyasa kwata-kwata baiyi na’am da maganar ba ashe sai da taje ta fadi maganar.

Fulani ganin yayi shuru tace.”Babana ko akwai matsala ne? naga kayi shuru kana tunani kayi min bayani dan ba naso ayi al’amarin nan rayuka su ‘baci idan ba kai ke son al’amarin ba to tun kafin tafiya tayi nisa a warwareshi.”

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yana kokarin ‘boye damuwar dake fuskarsa yace.”Mammah ba wani abu bane yasa kika nayi shuru ina tunanin abinda aunty Safiyya ta aikata bayan nayi mata bayani cewar babu wata alaqa ta soyayya a tsakanina da Lawisa kawai tazo ta ganta ne a ranar dana dawo tazo tana sheda min cewa ta shirya walima domin murnar dawowata gida lafiya to ita kuma aunt Safiyyan shine take tunanin soyayya ce a tsakanina da ita.

Fulani shuru tayi tana mamakin al’amarin ta kalleshi a nutse tace”To yanzu wace shawara ka yanke dan gaskiya al’amarin yayiwa Maimartaba dadi bashi kadai ba har sauran ‘yan uwansa sunyi farin ciki nima kuma naji dadin hakan idan kace ka janye maganar baza suji dadi ba.

Murmushi yay wanda ya tsaya iya le’bansa yace.”Mammah bana fatan ranar da zata zo na ‘bata muku rai dake da maimartaba tunda dai maganar nan ta fita har iyaye sunji to ina ganin babu damuwa zan auri yarinyar amma a gaba dole na ‘kara aure mutukar Allah ya had’ani da wacce nake so.”

Fulani murmushi tayi tana girgiza kanta cike da tsantsar farin ciki a maganarta tace”Ubana ina alfahari dakai mutuka ina jin dadin yanda kake kula dani da gudun ‘bacin raina ina rokon Allah ya azurtaka da zuria masu albarka kamar yanda kake mana ladabi da biyayya kai ma ubangiji Allah yasa ‘ya’yanka suyi maka.

Cikin sakin fuska ya amsa da ameen Mammana.! dama nace ina bukatar masu hidima a sashena domin wani sa’in hidima nayi wa Haruna yawa.”

Cikin kulawa tace”Ayya ai wannan mai sauki ne ubana dama saboda nasan baka san hayaniya yasa na tura maka Haruna saboda nasan yana da nutsuwa amma insha Allahu zan sake turo maka mutum uku sun isa ko.”? Yace.”Yace mutum biyu ma sun isa sai su zauna su uku ina ganin hakan yafi” Tace.”To shikkenan Ubana kada ka damu insha za’a turo masu hankali da nutsuwa.


Washe garin ranar bayan mun fito daga gurin karatu ni da Lahira muna tafe muna magana, Haruna yasha gabanmu yace.”Sumayya Lahira kuje can b’angaran Fulani ana bukatar’ku.”

Kallonsa nayi nace”Haruna ina fata dai lafiya ba wani laifin mukayi ba.” Yace.”Babu komai ku kwantar da hankalinku sannan ba ku kad’ai aka nema ba har da sauran ‘yan uwa.” Ajiyar zuciya na sauke nace”Haruna dan Allah zan duba jikin babana kuje kawai na biyo bayanku daga baya.”

Da sauri yace.”Wai sumayya mai yasa kike gardama da umarnin masarauta akwai ‘ya’ya da yawa da iyayensu suke halin rashin lafiya amma basa irin abinda kikeyi.

Hannu na d’aga masa nace”Haruna abinda yasa kaji nace haka sabida nike bashi magani yanzu haka Tambaya mahafiyata suna d’akin dahuwa(dakin girka abinci) suna aiki girka abinci kuma nasan idan naje bai zama dole a sallame mu da wuri ba shiyasa nace zan fara dubashi na bashi magani tukkuna.

Haruna yace.”Ba za’a wani dad’e ba insha Allah kedai kawai ki shige muje.” Girgiza kaina nayi na kalli Lahira dake rungume da jaka nace”Muje.” Haruna gaba yayi da sauri muka rufa masa ba zuwa b’angaran Fulani.
A jere muka samu ‘yan uwanmu bayi maza da mata sunja layi a bakin k’ofa kai tsaye ‘bangaran mata muka nufa nida Lahira muka tsaya shi kuma Haruna da sauri ya bude kofar falon ya shiga ciku…..Surutai ne suka shiga tashi a gurin bayan shigar haruna falon dukkanin mu muna mamakin tara mu da Mammah fulani tayi sabida mun san da cewar ita din macace mai mutunci da karamci bata fiye tara mu taci mana mutunci ba kamar sauran ‘bangarorin dake gidan, dukkanin mu dai addua mukeyi akan Allah yasa alkairi ne.

Haruna na fitowa muka bishi da kallo ya kalli ‘bangaran maza da sauri yace.”Ku shigo a nutse.” Suka dinga shiga falon a nutse har suka qare, kusan mintina goma sha biyar da shigarsu suka fito kowa ya kama gabansa banda mutum biyu da suka ja gefe suka tsaya.

Haruna ya kallemu da fadin”Ku shigo a nutse.” Da sauri muka tu’be takalman mu muka fara shiga daya bayan daya.

Zubewa mukayi a gabanta muna gaisheta…..Amsawa ta dinga yi cikin walwala tana kallonmu fuska a sake babu nuna ‘kyama

A nutse ta dinga tambayar sunayenmu muna fad’a mata, ta d’ora idanunta a kaina fuskarta a sake tace”Sumayya ina tsammanin zaki fi ‘yan uwanki kuzari da kazar kazar saboda haka ke kad’ai zan dauka a cikin ku zaki kasance daya daga cikin hadiman Magajin Sarki zaki dinga kulawa dashi da duk abunda yake bukata keda sauran ‘yan uwanki amma su din maza ne Haruna da Isa da Hamza ke kad’ai ce mace a cikinsu.”

Tunda take maganar gabana ke fad’uwa sam banyi farin ciki dajin wannan al’amarin ba ba dan komai ba sai dan sanin da nayi cewar bani da lokacin kaina na farko ina d’awaniyya da mahaifina na biyu ina kula da aikinsa dake cikin gidan ina nufin d’awainiya da dawakai, na uku kuma karatun dana k’wallafawa raina a kansa wanda ba kowane yake da ra’ayin yinsa a cikin masarautar ba, dama Maimartaba ya bude sashen karatu a gidan sabida mu, wanda yake da ra’ayi yaje ya dauki darasi na boko dana arabic wanda kuma baya da ra’ayi yayi zamansa to nida iyayena muna da ra’ayin karatu shiyasa suka goya min baya domun na samu ilimi yanzu haka mun kai izifi talatin a cikin al’kur’ani maigirma, sauran littafan addini kuwa nan ma mun sauke wasu ‘bangaran boko ma ina fahinta sosai dan ina jin turanci amma ba sosai ba wannan dalilin ya sanya naji gabad’aya banji dadin a’lamarin ba

Cikin kokarin danne damuwata na kaskantar da kaina cike da ladabi nace”Godiya nake ranki ya dade hakika naji dadi mutuka da kika za’be ni a matsayin wacce zata kula da sashen Yarima ina rokon ubangiji Allah ya bani ikon daukar amanar da kika bani.”

Cikin farin ciki Fulani tace.”Babu damuwa Sumayya kuna iya tashi ku tafiya Haruna zai jagorance ku zuwa sashen nasa sai ku gabatar masa da kanku a matsayin wanda na turo ku.

A nutse muka mike mukayi mata sallama cike da ladabi muka fita daga falon, Haruna dasu Isa suna tsaye suna magana na kallesu fuskata babu walwala nace”Ku muje ko.”? Haruna yace.”Ke aka za’ba.”? Daga masa kaina nayi na kalli Lahira nace”Dan Allah kafin ki shiga gurin ku ki duba babana ki bashi magani idan kuma Tambaya ta dawo shikkenan.” Lahira tace”Kada ki damu insha Allah zan dubashi sai kin shigo.

Lokacin da muka isa b’angaran nasa a kishingid’e muka same shi cikin furanni yana sanye da ‘kananun kaya gabansa kayan marmari ne cikin tire wayarsa yake dubawa fuskar nan a had’e! cikin zuciyata nace “Naga sanda zan ga dariyar guy nan kullum fuska babu rahama Allah dai ya kyauta.”

Gabansa muka zube gwiwoyinmu a k’asa had’a baki mukayi gurin fad’in “Barka da hutawa Magajin sarki muna fatan mun same ka lafiya.”! K’asa mukayi da kanmu bayan mun gama maganar…..

Shuru yayi mana kamar bai san damu a gurin ba, raina ya ‘baci sosai aqallah mun kai minti goma a gurfane a gabansa kamar wasu masu neman gafara wannan wace irin rayuwa ce.

Kallonsa nayi a lokacin da yake kokarin gyara zama karaf! muka had’a ido kwarjini yayi min wanda yasa na ma’kale maganar dake raina nayi kasa da kaina gabana na fad’uwa guy ya tara duk abubuwan da ake bukata yana da kyau sosai gashi dogo abinda yafi birgeni a tare dashi manyan idanunsa wanda suke a lumshe k’wayoyin idanunsa basu cika fari ba sun d’an sirka da ja banta’ba ganin kwayar idanunsa tayi haske ba.
muryarsa ce ta katse min nazarin da nake…..
BINTA UMAR ABBALE

Shearing 👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
19&20
“Haruna wa’innan fa.”? ya fad’a yana nuna mu da bakinsa.Haruna ya sunkuyar da kansa kasa cikin taushin murya yace.” Ranka ya dad’e Mama Fulani itace tace nazo dasu domin su gabatar maka da kansu a a matsayinsu na wa’inda zasu taimaka min da d’awainiyarka.”

Kansa ya sunkuyar ‘kasa yana nazari kafin ya dago yana yi min wani irin kallo babu walwala a tare dashi yace.”Mutum biyu nace kuma banda mace a ciki nafi bukatar maza sabida haka ke kina iya tafiya.” Yana kallona ya ‘kare maganar.

Dad’i naji ya rufeni jin abinda yace yasa da sauri na k’askantar da kaina da fadin”Godiya nake ranka ya dade.” na yun’kura na mike tsaye risinawa nayi da fadin”A tashi lafiya.” Da sauri nayi nufin barin gurin naji yace.”Dakata.” Nayi saurin juyowa ina kallonsa addua nakeyi a zuciyata kada yace ya fasa.

Gani nayi ya sunkuyar da kansa raina ya ‘baci! nida su Haruna kasa’ke mukayi muna jiran muji abinda zece………B’angaransa kuwa tunani yay kan cewar zamanta a sashen nasa zai iya taimaka masa ta wani bangaran shine dalilin daya sa ya dakatar da ita daga tafiya.

Kallona yayi a ya mutse yace.”Meye sunanki ma.”? Babu walwala a tare dani nace”Sunana Sumayya Lawi.” Ya shiga girgiza kansa minti biyu ya kalli Haruna da fad’in ” ka shiga dasu ciki ka nuna musu abinda ya dace akwai d’akuna a falo kuyi amfani da d’aya kai da ‘yan uwanka ita kuma sai ta dauki daya inaso ku dawo sashena da zama har abadah kune hadimai na koda nayi aure.”

Gabana ya dinga bugawa ina kallonsa kwalla na taruwa a idona nace”Ranka ya dad’e inada magana.” Ya kalleni yana ya mutsa fuska. Saurin sunkuyar da kaina kasa nayi bakina na rawa nace”Ranka ya dade naji kana maganar mu dawo sashenka har abada ni ina da mara lafiya mahaifina bashi da lafiya kuma ni nake jinyarsa.”

Kaina a kasa nake maganar ina kokarin mayar da hawayen dake kokarin zubowa…..shuru gurin yayi na kusan minti biyar kafin ya dago kansa ya kalli su Haruna da fad’in”Ku tashi kuje.” Da sauri suka mike suna mika godiyarsu a gurinsa

Bayan barin su Haruna daga gurin na kai minti goma a tsaye be kula ni ba, sai duba wayarsa yake yi fuskarsa a murtuke. gabadaya naji gwiwowina sun sage na kalleshi inaso nayi magana ido muka hada dashi gwarjinsa ya hana ni cewa komai.

“Kina nufin kina tsaye ‘kerere a kaina zanyi magana dake.”? Ciki ciki ya fadi maganar, zubewa nayi gwiwa a kasa nace” Ranka ya dade a gafarce ni wallahi hankalina ne gabad’aya yana kan mahaifina.”

Ajiyar zuciya yayi ya mike zaune had’e dayin wani irin zama na saurata hannunsa ya d’ora kan gwiwarsa, na kalli hannun yatsunsa guda uku na sanye da zubonan azirfa masu kyau sake sunkuyar da kaina nayi ina jiran jin ta bakinsa. kallona yayi a ya mutse yace.”Mai yake damun mahaifin naki.”? Da sauri nace” Daya daga cikin masu duba lafiya ya tabbatar mana da cewar hawan jini ke damunsa tsayin wata daya yana fama amma dai yanzu da sauki tunda an d’orashi akan magani.

Shuru gurin yay bayan na gama maganata, ya dinga kallon ‘kasan kafet din da yake zaune kamar ba zaice komai ba daga bisani ya d’ago kansa tare da fad’in “Inaso kiyi min jagora ‘bangaran naku domin na duba mahaifin naki.”

Kallonsa nayi ina mamakin maganarsa, girarsa dake cike da gashi ya d’aga min domin so ya tabbarar min da maganarsa.

Nace”Babu damuwa ranka ya dad’e idan ka shirya zuwa yanzu sai nayi maka jagora.” Ina d’urkushe a gabansa ya mi’ke a nutse yasa takalminsa yace.”Tashi muje.” Da sauri na mike ina karkad’e jikina.

Tsayawa nayi ina jira yayi gaba nabi bayansa ya nuna min hanya da hannunsa ba tare da yace komai ba na fahimci abinda yake nufi da sauri nayi gaba ya rufa min baya.

Yanayin tafiya ta da tashi ba daya bane koda na waiwaya sai naga nayi masa nisa sosai d’an tsayawa nayi ina jiran zuwanshi…..Bangaran shi kuwa tafiya kawai yake amma hankalinsa tuntuni ya tashi sakamakon yanayin tafiyar da takeyi sassan jikinta na motsawa mazaunanta ba ‘karamin tayar masa da hankali yayi ba hakan ya sake sanya masa rashin kuzari da karfin jiki ya dinga tafiya tamkar wanda ‘kwai ya fashewa a ciki gabad’aya sha’awarshi ta tashi yana so ya samu yarinyar da zata d’ebe masa kewa.

Sai da ya kusa zuwa dab dani sannan na juya na cigaba da tafiya…..Yarima Ali ajiyar zuciya ya sauke ya tsirawa faffad’an qugunta ido wanda yake juyawa cikin zanin kamfalar dake jikinta……..ajiyar zuciya ya dinga saukewa yana kokarin danne abinda ke taso masa.

Koda muka shiga gurin namu Tambaya dake bakin rijiya tana wanke kwanuka mikewa tayi da sauri ganina tare dashi yasa hankalinta ya tashi tana tsoro ko wani abu ne ya faru, ganin ta razana yasa nace”Ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru Yarima zai duba jikin babana ne.”

Zubewa tayi gabansa tana gaisheshi gami dayi masa godiya. Cikin sanyin murya ya amsa tare da bata umarnin mi’kewa.
Na kalleshi a nutse nace”Ranka ya dade bisimillah ka shigo.” Takalmansa ya cire a nutse ya rankwafa domin shiga dakin dake gajeriyar kofa ce shi kuma ya kasance mutum mai tsayi shine dalilin da yasa ya risina domun shiga dakin.

Guri na shiga karkad’ewa wai ko zai zauna, sai naga yaja ya tsaya yana kallon babana dake kwance yana bacci…..Cikin rawar baki nace”Ka ganshi ko wallahi yana jin ji……! hannu ya daga min alamanun baya bukatar maganata, nayi shuru ina kallonsa sai kallon babana yake kafin ya kalleni yace”Ina maganin da kuke bashi.”?
Da sauri na dauko na mika masa, ya jima yana duba magungunan kafin ya miko min da fadin”Kada ku sake bashi maganin ku ajeshi zamuje yanzu nasa Haruna ya samo masa wasu insha Allah zasuyi masa.”
Da sauri nace”To mungode shima na hausan da muke bashi mu daina.”? Kallona yayi da sauri yace.”Bayan wannan maganin akwai wanda kuke bashi.”? nace.”Eh akwai na hausa wanda na kar’bo gurin masu maganin gargajiya.”

Tsaki! yaja da fad’in”Jeki dauko min maganin nagani.” Na mike da sauri na fita tsakar gida na samu Tambaya ta gama wanke kwanuka tana tsaye jikin bango (garu)ta rungume hannuwanta a kirji.
“Tambaya ina maganin da ki’ka jiqawa babana.” Da sauri ta shiga wani daki dake tsakar gidan ta dauko maganin cikin bokitin roba madaidaici karba nayi da sauri na shiga dakin, na mika masa .

“Ajiye ki bud’e nagani.” Ajiyewa nayi a kasan guri nayi yanda yace. Ni dashi gabad’aya tsirawa maganin ido mukayi ganin yanda yake wata irin kumfa ga wari na tashi a cikinsa.
Dauke kansa yay rai a b’ace yace.”Rufe.” Jiki a sanyaye na rufe ina kallonsa, Yace.”Wannan maganin kwanansa nawa a jiqe.”? a sanyaye nace”Zai kai sati biyu.” Cike da taikaci yace.” Waye ya fad’a miki ana had’a maganin hausa dana bature a tare? shuru nayi kaina a kasa…..Ya cigaba da cewa”Magani kun jiqa shi tsayin sati biyu yana kumfa wari na tashi a cikinsa amma kuna d’irka masa so kuke ku kasheshi.”? Nayi saurin kallonsa ina girgiza kaina. Yace.”To ko dan gaba ba’a hada maganin hausa dana bature a tare sannan kuma idan kun jiqa maganin hausa to kuyi amfani dashi a lokacin idan ya kwana daya biyu ku zubar dashi domin ya tashi a aiki amma magani tsayin sati biyu a jiqe kuna bashi dole ku kasa gane kansa.

Nace”Kayi hakuri zamu gyara insha Allah.” Shiru yayi ya sunkuyar kansa ‘kasa, na dinga satar kallonsa ina mamakin wannan d’abia tashi bini bini kallon ‘kasa sai kace makaho……..”Anjima bayan isha’i ki shigo ki kar’bar masa wasu maganin insha Allahu zai samu lafiya.” Murya na rawa nace”To mungode ranka ya dade.”
Ba tare da yace wani abuba ya rankwafa da niyyar fita daga dakin……..Bayansa nabi naga suna sallama da tambaya, har soro na rakashi ina godiya uffan bece min ba har ya fita daga zauran namu…..na koma cikin gidan da sauri na shiga yiwa Tambaya bayani da yayi akan maganin gargajiyar da muka jiqa.
BINTA UMAR ABBALE

Kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
21&22
Sai bayan dana idar da sallar isha’i tukkuna na shedawa Tambaya maganar komawa ta ‘bangaransa da aiki. shuru tayi tana nazarin al’amarin tace”Sumayya dole ne mubi umarnin masarauta bamu da za’bi sai abinda suka ce damu saboda haka na umarce ki kije ki kula da Yarima bisa amana ki kyautata masa kamar yanda zaki kyautatawa iyayenki.” Nace”Tambaya babu wanda nake ji sai babana ki duba kiga halin da yake ciki gashi kema bakya zama sosai kullum kuna gurin girkin abinci bana so a barshi shi kadai a gidan shiyasa wallahi tunda naji maganar hankalina ya tashi.”

“Sumayya duk abinda Allah yayi nufun zartarwa akan mahaifinki to ko muna nan ko bama nan bamu isa mu hana Allah ikonsa ba, saboda haka ki nutsu ki kwantar da hankalin ki cuta ba mutuwa bace insha Allah Allah zai tashi kafad’unsa.”

Shuru nayi ina sa’ke-sa’ke a cikin raina.
Tace”Tunda kinyi sallah sai kici abinci ki tafi kada ki ‘bata lokaci a samu matsala.
A sanyaye naje na ‘Dauko kula ta abincin na had’o da plate na zauna inda na tashi abincin na zuba a plate nayi bisimillah a nutse na fara ci, Tambaya miqewa tayi ta nufi inda mijinta yake kwance, a hankali ta shiga kiran sunansa, bude idonsa yayi ya kalleta a hankali ya mayar da idon ya rufe, tace”Malam kaji maganar da muke tattaunawa ko.” ? idanunsa ya bude ya kalli gefan da nake zaune ina cin abinci.
A sar’ke yace”Sumayya kibi umarnin masarauta ko bayan babu raina bance ki bijirewa masarauta ba domin baki da wani tushe sai ita iyayenmu da kakannimu duk a k’arkashin masarauta suka rayu a haka duk aka haife mu saboda haka nake umartar ki da cewar kiyi biyayya kamar yanda kika ga munayi a matsayin mu na iyayenki.”

Muryata na rawa nace”Baba dan Allah ka daina maganar mutuwa insha Allahu zaka tashi ka cigaba da sabgogin ka cuta ba mutuwa bace.” Murmushi yay yace.”Sumayya kenan to ina rokon ubangiji Allah ya tashi kafad’una na cigaba da rayuwa a tare daku.'”
murya na rawa nace”ameen baba Allah ya baka lafiya.” amsawa sukayi da “ameen” na mike na fita domin wanke hannuna.

Lokacin dana shiga dakin Tambaya na kokarin mikar dashi zaune domin ta d’aura masa alwala taimaka mata nayi mukayi masa alwalar ta gyara shi sosai yanda zaiji dadin sallah ya tayar da iqama a nutse! kallona tayi tace”Kiyi maza ka tafi mana.” Sai Naji zuciyata ta karye tunda na taso ban ta’ba zuwa ko’ina na kwana ba kullum ina tare da iyayena
A sanyaye na juya ina goge hawaye da hannuna nace”Na tafi.” Itama tambayan cikin alhini tace”Sai da safe.” Jin kuka naso ya kufce min yasa nayi gaggawar fita daga dakin, takalmana dake bakin kofar dakin na zura na fita daga gidan.

Haruna da su Isa na samu a falon suna aikace aikace, gaisawa mukayi na nemi kan kujera na zauna ina rarraba idona a katafaran falon nashi daya gaji da had’uwa, ko wace kusurwa hotonshi ne a manne wani da manyan kaya na sarauta wani kuma da ‘kananun kaya cikin hotonan nasa babu wanda yayi dariya a ciki fuska a murtuke tamkar wanda akayiwa dole gurin daukar hoton, muryar Haruna ce ta katse min tunanin da nake, na kalleshi inaso ya sake maimaita min abinda yake fad’a, Yace.”Sumayya ba zama zakiyi ba zaki hau sama ne ki bubbuga idan ya bude sai ki sheda masa isowarki idan da akwai abinda yake bukata kiyi masa sai kiyi mu dai mun gama aikin mu zamuje mu huta sai ya b’ukace mu.” Na kalleshi da fadin”Ina ne d’akin nasa.”
Wata matattakalar bene ya nuna min da fadin”Kina kaiwa karshen benan za kiga wata kofa mai biyu nan ne d’akinsa sai ki danna wani abu a jikin kofar zai yi magana.

Nayi shuru ina sa’ke-sa’ke mi’kewa nayi na kama hanyar benan, da k’yar nake hawa benan sabida santsin ties d’in ina hawa ina ri’ke sandar benan gabana na fad’uwa! ajiyar zuciya na ajiye bayan na gani a kofar dakin
Sai da na daidaita nutsuwa ta tukkuna na danna abinda zai isar masa da isowata. shuru ba’ayi magana ba, nasa hannu akan abun na latsa da kar’fi! Naji muryarsa yana fad’in “Wanene.” “Nice Sumayya.” Murya a hard’e na fadi maganar. shuru har tsayin mintina goma bai bude ba jikina yayi sanyi kamar nayi tafiya ta sai dai na daure na cigaba da tsayuwa, motsin bude kofar naji nayi saurin ja gefe tare dayin kasa da kaina, koda ya bude kofar ban kalleshi ba nace” Barka da dare ranka ya dade.”

“Barka dai shigo ciki.” Yafada tare da juyawa cikin dakin. Dago kaina nayi da sauri na mayar dashi qasa sakamakon ganinsa da nayi d’aure da towel gabana ya dinga bugawa kasa shiga dakin nai nayi tsaye a bakin kofar ina tararrabi.”

Zama yay gefan bed dinshi yana kallon bakin kofar, “Ke! ki shigo nace dake.”! A tsawace ya fad’i maganar, shahada nayi na shiga yace.” Kulle kofar.” hannu nasa na tura kofar dakin ta rufe, tsayuwa nayi jikin kofar kaina a qasa nace”Ranka ya dade gani nazo.” Shareni yayi ya cigaba da murza vasilin a jikinsa, duk da kaina a qasa yake sai da naga cinyoyinsa d’an towel din ya dinga turewa daga jikinsa yana shafa vasilin din, ganin kamar yana so yayi tsirara yasa na juya masa baya.

“Ke! dodo ne ni da zaki juya min ba okey zan saki yanzu ki shafa min vasillin din tunda abin hakane.” Ji nayi yawun bakina ya bushe, nace”Dan Allah kasa kayanka baligin mutum kamar ka bai kamata ana ganin tsaraicinsa ba.

“Wa’azi za kiyi min kome.”? Shuru nayi masa, yace.” Malama Zo nan ki shafa min vasilin din a bayana.” Kasa juyawa nayi ballantana naje nabi umarninsa. “Ko bakya ji ne.” Hanci na shaqa kunyar duniya ta isheni nace”Dan Allah kayi hakuri ba zan iya ba.” Tsaki naji yaja daga hakan be sake cewa komai ba ya cigaba da shafa mai a jikinsa.

“To na gama sai ki juyo.” A hankali na juya kaina a ‘kasa ban yarda na kalleshi ba, yace” Zo ki kar’bi maganin nasa Haruna yaje gurin seda magani ya siyo zo in nuna miki yanda zaku dinga bashi.
Zuwa nayi na durkusa gabansa a nutse ya fito da magungunan daga ciki leda ya shiga nuna min yanda qa’idarsu take, muryata na rawa nace”Allah ya saka da alkairi mungode.” Yace.”Ki koma yanzu ki bashi maganin kamar yanda nace amma ki tabbatar kafin ki bashi yaci abinci ya koshi.” Ina kokarin miqewa tsaye nace”Insha Allahu yanda kace haka za’ayi.” da ledar maganin a hannuna na kama hanyar fita daga dakin.
Ka shingid’a yayi tare da bin bayanta da shu’umin kallo, sajensa ya shafa yana lumshe idonsa gabad’aya yarinyar ta rikitashi duk wani abu da yake daurewa yake yi amma yana bukatar wacce zata d’ebe masa kewa.

Sai da na tabbatar da yaci ya k’oshi tukkuna na bashi maganin kamar yanda ya umarce ni, mahaifiyata na kalla dake kokarin gyara masa shimfida nace”koda da safe ban shigo da wuri ba ai kinga yanda na bashi maganin ko.”? Tace”Eh na gani insha Allahu zan kwatanta.” Miqewa nayi na sakeyi mata sallama a karo na biyu, tace”To Allah ya tashemu lafiya.” da ”ameen na amsa cikin sauri na fita daga dakin.

Yana kishingid’e kasan kafet din dake ‘kasan bed dinshi na same shi da romot a hannunsa yana kallon wa’ko’kin turawan america, kauda kaina nayi daga kan tv dan ganin yanda turawa ke bad’ala sai rungume rungume suke suna tsotsar bakin junansu.

A sar’ke nace”Ranka ya dade na dawo na bashi maganin kamar yanda kace idan da akwai abinda kake bukata kayi magana sai nayi maka.”

Uffan bece min ba hankalinsa na kan tv yana kallon raye rayen turawa.
Na sunkuyar da kaina k’asa, hakika raina yana ‘baci idan yana min wannan wulakacin a rayuwata na tsani nayi magana a watsar dani.

Sai da ya mula tukkuna ya kalleni tare da fad’in “Ina bukatar kiyi min matsar jiki kwana biyu sabida rashin motsa jikina da banyi ba yana min ciwo insha Allah gobe zan fita da doki cikin gari na wasa jinina.”

Duk da na fahimci abinda yake nufi sai nace”Ban gane abinda kake nufi ba.” Gyara zamansa yayi yana fuskantata yace”Ina bukatar tausa shine abinda nake nufi.”

Jarumta na aro nace”Amma ina ganin kamar hakan be dace ba idan tausa kake bukata maza ‘yan uwanka su yafi cancanta suyi maka bani ba da nake a matsayin mace ba.”

Gani nayi ya sha kunu! kaina na sunkuyar gabana na faduwa…”Kina a matsayin mace sai akayi yaya.”? shuru nayi bance komai ba, ya cigaba da cewa”Na fahimci kina da taurin kai babu abinda za’a umarce ki dashi kiyi kai tsaye sai kinyi musu, kada ki manta fa kina karkashin masarauta duk abinda aka umarce ki dashi naki to ne.”

Hanci na shaqa na sake risinar da kaina qasa nace”A gafarce ni ranka ya dad’e ba wai ina jayayya da umarninka bane A’a inaso na nuna maka illar abinda kake so na aikata bai kamata na ra’bi jikinka ba a matsayinka na baligi nima haka.”

D’akin ne yayi shuru bayan gama maganata, dago kaina nayi na kalleshi naga ya tsirawa tv ido fuskar nan kamar wanda aka aikowa da sak’on mutuwa.

Tv din na d’an kalla a sace naga abinda ake aikatawa ya zarce tunani na, mace da namiji ne tsirara sun dage suna sex sai nishi sukeyi……gabana ya dinga bugawa da sauri na miqe na kama hanya zan fita.
“Kada ki kuskura ki fita a d’akin nan.” Ja nayi na tsaya ba tare dana juyowa ba gabana na faduwa still ina jiyo nishin ‘yan iskan.”
BINTA UMAR ABBALE

Shearing👏🏻👏🏻

Dan Allah idan ba siyan book din nan zakiyi ba kada ki kira waya ta, masu flashing kuyi wa Allah da Annabi ku bari bana jin dadin abinda kukeyi🤨
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740
[12/29, 12:33 PM] 💜: SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
23&24
“Ki dawo kiyi aikin dana saki.” Maganarsa ce ta doki dodon kunnena, juyowa nayi fuskata a had’e nace”Allah ya kiyashe ni aikata haramci Ranka ya dade bana jin zan iya bin umarnin ka tunda ya sa’bawa addinin musulunci.” Ina gama maganata na kama handle domin bude kofa na fita muryar mahaifina naji a kunnena lokacin da yake min gargadin akan bin umarnin masarauta, hawaye ne ya ciko a idona ina jin tsoro kada garin bin umarni wani mummunan abu ya faru a tsakani na dashi tunda Annabi S.a.w yace.” Duk inda mace da namiji suka had’u to na ukun su shed’an ne babban tashin hankalin kuma shine ya kunna iskanci a d’akin shiyasa gabad’aya na kasa samun nustuwa…….Saukar hannunsa naji akan nawa dake jin kofar dakin, na dinga jin hucin numfashinsa na sauka a daidai wuyana, cikin faduwar gaba na juyo sai na ganshi dab dani saura kadan kirjinsa ya gogi nawa, saurin jingina nayi a jikin bango(garu) numfashina na fita da sauri da sauri, sunkuyar da kaina kasa nayi bakina na rawa magana nake so nayi amma tsabar fargaba da tashin hankali ya hanani cewa komai.
“Ba zakiyi min ba ko.” cikin wata ‘yar iskar murya ya fadi maganar, cike da jarumta na kalleshi nace”Kaji tsoron Allah a duk inda kake nasan kasan kallon tsaraici haramun ne yanzu dan Allah meye amfanin kallon blue film da kake yi kuma menene na cewa lallai sai nayi maka tausa idan baka da wata manufa akaina.”

Shuru yayi bece min komai ba kuma be daina kallona ba, hannunsa dake dogare a jikin kofar na ture ina kokarin fita daga tsakaninsa ya mayar dani jikin bangon ya matse da kirjinsa, kafin nayi aune naji saukar hannunsa akan mazaunai na yana shafa su, karfi ne yazo min da wani tunkude shi ina haki! na nuna shi da hannu da fad’in “Kada ka sake yunkurin kai hannunka jikina ni ba ‘yar iska bace irin wanda ka saba nema a turai, yanzu na gane munufar ka a kaina dama badan nayi maka aiki ka bukaci zamana a sashenka ba na gane sabida ka cimma wata munufa ne to ta Allah zai kare ni daga sharrin ka.”
Cikin tsanani ‘bacin rai na kare maganar a fusace na bude kofa zan fita ya finciko ni kafin nayi wani yunkuri naji saukar mari a kumatuna, ido na tsirawa masa ina kallonsa yana huci yace.”Ni kike kira d’an iska.”? Muryata na rawa nace”Ni ban ce maka dan iska ba amma nace kaji tsoron Allah akan abinda kake aikatawa wanda kasan haramun ne.” Wani kallon banza yayi min da fadin “Saboda kin samu nayi sha’awarki shine kika samu damar fad’a min dukkanin maganar da kike so ko an fada miki ni sa’anki ne da zaki tsaya a gabana kina kokarin zagina.”‘

Risinar da kaina qasa nayi nace” Allah ya baka hakuri idan akwai maganar data bata maka rai a cikin maganganuna to ina neman afuwa.” Da hannu ya nuna min kofa cikin tsawa yace.”Fice min a daki banza mummuna kawai.” Da sauri na bude ‘kofar dakin na fita gabana sai dukan uku uku yake…….Tamkar wani zautacce ya juya jikinsa na kyarma bed ya kwanta ruf da ciki yana murk’ususu mararsa ta cika tayi fam sai ciwo take masa.

Dakin da Haruna ya nuna min na shiga na rufo kofa na samu gefan gado na zauna har yanzu ban dawo nutsuwata ba, sosai nake mamakin al’amarin, a haka idan ka kalleshi zaka dauka mutumin kirki ne sabida a zahiri yana da fuskar salihai ashe ba anan take ba shi d’in mugun shaid’ani ne mane min mata wato yana da manufa a kanta shiyasa ya bukaci zamanta a gurinsa, to kuwa idan hakane dole tayi takatsantsan dashi da dabi’unsa.
Da kyar bacci ya d’auketa saboda tsabar damuwa da tashin hankali.

B’angaransa kuwa yanda yaga rana haka yaga dare ya dinga matagugu yana riqe ciki sai gefin asubahi ya samu sassauci abinda ke damunsa cikin tsanani damuwa yayi wanka da alwala ya shirya shiga massalaci haka ya sakko tamkar wanda yayi shekara akwance tare suka tafi masjid din dasu Haruna domun gabatar da sallar asubahi.

Bayan na idar da sallah na jima hannuna a sama ina rokon Allah ya kareni daga sharrinsa na shafa adduar na mike a nutse na fita falon na jima a tsaye ina sak’e sa’ke kafin na nufi kofar kicin domin shirya abin kari………..Tsaf na shirya kayan karin kummalo na fito dasu ina jerawa kan daning….Shine a gaba su Haruna na bayanshi, ‘kasa nayi da kaina tare da risinawa nace” Ranka ya dade Barka da asubah.” Banza yayi mun ya wuce benansa, a sanyaye na dago kaina muka hada ido da Haruna ya’ke nayi nace”Haruna kun tashi lafiya.”? Yace.”Lafiya lau Sumayya ina fata kema kin tashi lafiya.”? na amsa da lafiya lau alhmdullhi.” Har zai bar gurin sai kuma ya tsaya yace.”Sumayya baki karanci damuwa a fuskar Yarima ba.”?
Girgiza kaina nayi ba tare da na kalleshi ba nace”Banga komai ba ai ka san shi ba’a gane farin cikin sa da ‘bacin ransa tunda kullum fuskarsa a murtuke take da rashin fara’a.”
Yace.”Hakane to amma yana da kyau mu had’u gabadayanmu muje mu sameshi mu tambayeshi ko munyi masa laifi sai mu bashi hakuri.” Shuru nayi ba tare da nace komai ba na cigaba da ayyukana.
Yace.”Kinyi shuru bakice komai ba.” Nace”To hakan yayi muje.” Haruna ya kalli Isa da Hamza yace.”Shawarata tayi ko.” ? duk sukace tayi muje mu sameshi mu tambayeshi ko munyi masa laifi sai mu bashi hakuri.
Jirana sukayi na gama gyara daning sannan muka hau saman nashi.

Yana kwance cikin bargo yace.”Kowaye ya turo kofar, a bude take.” Haruna ya bude kofar dakin muka shiga gabad’ayan mu kanmu a kasa muka ajiye gwiwowin mu a kasa gaishe shi muka farayi kafin mu fara neman afuwarsa duk da bamu san laifin da mukayi ba.

Shuru dakin yayi bayan mun gama magana uffan bece mana ba yana kwance cikin bargo fuskarsa na kallon rufin dakin.
Haruna yace”Ranka ya dade a gafarce mu.”! Gyaran mirya yayi ya juyo yana fuskantar mu, sunkuyar da kaina kasa nayi ganin fuskarsa a hade gashi kwayoyin idanunsa sun sakeyin jawur! “Babu wani abu da kukayi bana jin dadi ne shiyasa kuka ganni haka da rashin kuzari.”
Haruna dasu Isa suka shiga damuwa dajin furucinsa ni kuwa ko gezau banyi ba tunda nasan karya yake kawai ya fadi hakane domin kare kansa, sannu suke masa tamkar bakinsu yayi tsayi, nima sai nabi ayarinsu na dinga yi masa hannu ina rokon Allah ya bashi lafiya.

Gyaran murya yay a karo na biyu yace.”Kuna iya tafiya.” Haruna yace.”Ranka ya dade sai zuwa anjima za kayi wanka ko kuma yanzu na hada maka ruwan wankan.” ? girgiza kansa yay yace.”Bari anjima ka shigo ka had’a min inaso nayi bacci yanzu.” Yace.”To godiya nake ranka ya dade a tashi lafiya.” Mik’ewa sukayi da niyyar fita, nayi kasa da idanuna ba tare da na kalleshi ba nace”Ranka ya dad’e yana qarko na shirya danning ina nufin gurin cin abinci komai ya kammala idan baka bukatar zama a daning din sai kayi magana na kawo maka nan.”
Shuru yayi min, jikina ya bani kallona yake, aikuwa ina dago kai muka had’a ido, a maimakon ya ji kunya na kamashi yana kallona sai ma ya sake k’ureni da jajayen idanunsa dake bani tsoro.
Yun’kurawa nayi zan tashi naji maganarsa a dashe “Ki kawo min nan.” na risina da fadin”angama ranka ya dade.” da sauri na juya domun fita daga dakin……kallo ya bita dashi yana jin yanda gabansa ke miqewa hannu yasa ya danne jijiyar tashi yana jan tsaki a fili yace.”Sabida rashin adalci ki rasa a inda zaki nuna kwad’ayin ki sai a inda be dace ba mtwww! tsaki yaja mai k’arfi yana danneta ita kuma sai miqewa take.

Ina sauka qasa na samu ‘Yan uwanshi Shatima da Maddibo har’kasa na durkusa na gaishe su, suka amsa min a sake mussaman Shatima sai murmushi yake min, wuce su nayi da sauri na nufi kicin na dauko wani tire na silver mai fad’i dainng din na nufa na shirya kayan break fast din akai na dauka a nutse na nufi saman da tire din a hannuna

Abin mamaki! samunsa nayi a zaune shida ‘yan uwan nashi suna hira, a nutse na ajiye tire din a gabanshi, kai a sunkuye nace”Dan Allah ina neman alfarama.”
“Wace irin alfarma.” yafada ba tare da ya kalleta ni ba.” naji dadi sosai da bai shareni ba nace”Zanje in duba dawakai kasancewar aikin babana kenan to tunda ya kwanta rashin lafiya na dawo da dawaniyyar hannuna bayan nan inaso zan zauna a gurin karatu.”

Jim yayi na minti biyu yace.”Kije.” cikin jin dadi nace”Nagode ranka ya dade.” yunkurawa nayi na mike tsaye da fadin”A tashi lafiya.” babu wanda ya amsa min a cikinsu. da sauri na kama hanyar fita daga dakin.
Shatima ya kalli Moddibo da fad’in “Wannan yarinyar tana da dirin jiki mai kyau amma kuma bata da wani kyau gata ‘baka.”
Moddibo dariya yay yace.”Kai ina ruwanka da muninta idan biyan bukata nake nema ni bana duba muni ina duba abinda zai gamsar dani.” Dariya sukayi tare da tafawa a tsakaninsu, Haushin abinda suke yasa ya mike ya nufi toilet yana jin wani irin d’aci! a cikin ranshi, ashe dai bashi kadai ke ganin kyawun jikin yarinyar ba, har da sauran mutane yaji takaicin yanda Shatima ke kwarzanta kyawun dirin jikinta, brush yay ya fito da fuska a had’e.
kan kafet din ya zauna gami da tankwashe kafafunsa, a nutse ya tsiyaya bak’in tea a cup ya shiga kur’ba a hankali a hankali yana sauraran hirarrakin dasu Shatima keyi mafi akasari hiran ta ‘yan mata ne, cup din tea ya ajiye a nutse ya bude wata silver farfesun zallan naman rago da dankali ne a ciki yayi kyau sosai sai ‘kamshi yake Yaji yana sha’awar shan farfesun ya hada da bread a nutse ya zuba a plate ya kallesu da fadin”Bisimillah.” Moddibo ya girgiza kanshi da fad’in” Ni dai Alhamdullhi ban san Shatima ba.” Shatima dake duba wayarsa yace.”Nima a koshe nake wallahi.” Ba tare da yace komai ba ya fara shan farfesun yana had’ashi da bread….Modibbo ajiyar zuciya ya sauke ganin yana shan farfesun wani farin ciki ya cika masa zuciyarsa, dauke kansa yay suka cigaba da magana da Shatima.

Wani irin tari ne ya sarqe shi ya ajiye bread din hannunsa yana riqe kirjinsa tari yake sosai idanunsa sun cika da ruwa. Shatima ne yay saurin miqa masa ruwa ya kar’ba yana kokarin sawa a bakinsa ruwan na dawowa, sai kawai ya ajiye goran ruwan ya danne kirjinsa yana cigaba da tarin cikin galabaita ya mi’ke tsaye! sai suma suka miqe cikin tashin hankali suna rirri’keshi ya fadi a gurin, jini ne ya biyo bayan tarin da yake…….A gigice suka rufu a kansa suna k’okarin mikar dashi zaune.

Fitowa ta kenan daga gurin Dawakai Haruna ya karaso inda nake hankali a tashe yace.”Sumayya Yarima Ali bashi da lafiya bayan fitarki daga sashen Tari ya sarqeshi ya dinga aman jini.”

Kirjina na dafe cikin tashin hankali nace”Haruna wane irin aman jini kuma.”? Yace.”Aman jini dai da kika sani Sumayya yanzu haka sashen nasa a cike yake da ‘yan uwa dan har maimartaba ma yana gurin ana bunkice akan abincin da yaci wallahi ke kadai nake tausayawa.”

Kallonsa na shiga yi a tsorace nace”Haruna ni kuma meye laifina da kake tausaya min.” Yana kokarin magana Hamza ya karaso gurin yace.”Ke! Sumayya kizo ana neman ki a sashen Yarima.” Naji gabana ya fad’i! Magana nake so nayi amma bakina yayi min nauyi, dakyar na iya furta kalmar innalillahi wa’ina ilaihi raji’un.” nabi bayansu domin zuwa jin kiran da ake min……
BINTA UMAR ABBALE

Kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
25&26
Cikin tararrabi gami da fargaba muka shiga falon, gimbiya Lawisa ce a zaune akan kujera muna shiga ta mike tsaye da sauri tana watsa min mugun kallo! sunkuyar da kaina qasa nayi nace”Ranki ya dade barka da safiya.” Hannu ta daga min cikin tuhuma tace”Me kika zubawa Yarima acikin farfesu wanda ya janyo masa aman jini.”?
Gabana na faduwa nace”Ban zuba masa komai ba ranki ya dade.” Marina tayi tana huci! tace”Zaki fad’a ko sai kin fuskanci hukunci mai tsauri.”! Hannu na dafe da kuncina nace”Iya gaskiyata na fada wallahi ban sa masa komai ba.” Za tayi magana Haruna ya katseta da fadin”Sumayya ki hau sama Maimartaba na bukatar ganinki.” naji jinin jikina ya tsinke gabad’aya neman yawu nayi na rasa a bakina, salo salo na nufi saman ina adduar akan Allah ya fitar dani.

Lokacin dana shiga dakin sai naji na sare da al’amarin dan ganin yanda dakin ke ciki da jama’a gabad’ayan su suna tsaye a kansa yana kwance a bed kansa a cinyar mahaifiyarsa bakinsa rufe da wani abu da ya nuna alamun an tare jini likita ne a tsaye a kansa.
Sunkuyar da kaina kasa nayi na zube gwiwata a kasa nace”Barkan ku da wannan lokaci.” Gabad’aya suka juyo suna kallona…….muryar Moddibo naji cikin tsawa yace.”K’araso ciki munufaka.” Na yun’kura da sauri na karasa gabansu na tsuguna! Moddibo zai sake magana maimartaba ya katse shi.
Shuru dakin yayi kafin maimartaba ya fara magana kamar haka.
“Sumayya wace irin guba kika sakawa Yarima a cikin abincinsa inaso ki fada min wanda ya saki zuba masa guba a cikin masarautar nan.”! hawaye suka k’wace min nace” Na rantse da wanda raina ke hannunsa ban zuba masa komai ba, lafiya lau na gama abinci na bashi kafin na tafi gurin mu.”

” ‘Karya kike munufuka akwai abinda kika zuba masa wato kina so ki kashe ki ko.”? Moddibo ne ke wannan maganar kamar zai kai min duka

Waziri ne yayi masa tsawa yayi shuru yana huci……Uwargida wato mai babban daki tace”Wato ba zaki fadi gaskiya ba kenan musu zakiyi akan binkicen da likita yayi akan farfesun da kika bashi yasha, to shikkenan tunda kina gardama ki dauki farfesun kisha mu gani.”

Ina kuka nace”Ranki ya dade wallahi kiyashi ban ta’ba kashewa ballantana mutum, ni kuwa me Yarima yayi min da zan kasheshi dan Allah ku duba maganata kuyi binkice sosai akan al’amarin wallahi ban sa masa guba a acikin abinci ba.”

Ciroma yace.”Zaki rufe mana baki ko kuwa.” Shuru nayi ina kallon qasan gurin nace”Ku gafarce ni na fada muku iya gaskiyata ne.”

Dakin shuru yayi kowa yana jira yaji ta bakin Sarki, wanda yay shuru yana nazari tabbas al’amarin na bukatar bunkice kamar yanda yarinyar ta fada.

Itama Mamma tunanin da take kenan ba zai zama dole ace yarinyar ce ta zuba masa guba ba mybe akwai dai wata mak’arkashiyar shiyasa tayi shuru ba tace komai ba.

Sarki gyaran murya yay yace.”Sumayya kin san girman Allah da Annabin Allah.” Da sauri nace”Eh ranka ya dad’e.” Yace.”To magana ta k’are tunda har kinyi rantsuwa da Allah da annabi baki zubawa Yarima guba ba ki tashi ki tafi.” Da sauri na kaskantar da kaina kasa nace”Godiya nake ranka ya dad’e.
Yunk’urawa nayi na miqe da fadi “Na barku lafiya.” Babu wanda ya tanka min har na fita daga dakin.

Maimartaba ya kallesu a nutse yace.”Ina ganin zamu tsananta binkice akan wannan al’amarin dan alamu sun nuna cewa yarinyar nan bata da alhaki akan wannan al’amarin saboda haka zamu bar maganar tunda Allah ya kiyaye gubar ba tayi tasiri a tare dashi ba ammafa hakan ba zai sa mu kasa d’aukar mataki akan duk wanda muka samu da alhakin faruwan wannan al’amarin ba.” Waziri yace.”Hakane ranka ya dad’e tabbas yanayin yarinyar ya nuna gaskiyarta sai a ‘kara saka matakan tsaro a sashen nasa saboda gujewa faruwar wani abu makamancin wannan.” Galadima da Ciroma shuru sukayi dan al’amarin gabad’aya bai musu dad’i ba sun so ace gubar ta kashe yaron kowa ya huta……. .

Ko kallonta banyi ba na nufi kofa da niyyar fita daga dakin. cikin tsawa tace”Ke! mai baqi kamar bakin tukunya tsaya anan gurin.” kamar kada na tsaya sai dai na yanke shawarar tsayawa amma ban juyo ba.

Kamshin turaranta ne ya tabbatar min da cewa tazo inda nake na dago kaina ina kallonta tana yi min kallon kaskanci tace.” Da izinin wa kike shige da fice a sashen Yarima.” Wani kallo nai mata nace”Da izinin mahaifiyarsa.” Girgiza kanta tayi tace”Itace ta baki guba kisa masa a abinci ko kuma wa.” wani irin kallo nai mata nace” Uwa ta haifi d’anta ta kashe shi anya kina da hankali kuwa.”? Rai a bace ta kalleni tace”Ni kike fadawa wannan maganar.”? Nace”To ai ji nayi maganar taki tayi kama data mahaukata.”
Shuru tayi na minti biyu, kafin tace”Tunda kin zama mai kula dashi ta fannin abinci inaso nayi amfani dake domin cimma munufata.”! Kallonta nayi babu walwala a tare dani nace”Wace irin manufa ce.”?
Murmushi tayi tace”Kije zan neme ki gobe zamu tattauna.” Girgiza kaina nayi na wuce daga gurin ina mamakin maganar ta

Gurinmu na koma a gurguje nayi wanka na sauya kaya kana na zauna domun karyawa hira muke da Tambaya amma koda wasa ban fada mata abinda ya faru ba, Tace”Sumayya babu abinda zamu cewa Yarima Ali kinga maganin nan da kika kawo jiya yana da kyau dan jiya gabad’aya babanki bai kwana da zazzabi ba kinga jikinsa ma gumi yake alamu na nuna lafiya ta samu.” Nace”To Alhamdulilahi idan na koma sashen zanyi masa bayanin yanayin jikin nasa.” Tace”Hakan yana da kyau ki ‘karayi masa godiya.” Nace “Insha Allah.”
A gurguje na kammala karin kummalo na dauki jakar litattafaina sallama nayi mata na nufi gurin karatu.

‘Karfe d’aya da rabi mun fito daga karatu hira muke da Lahira ina tunanin fada mata abinda ya faru, Lantana ta k’araso gurin. “Sumayya kije b’angaran Mamma Fulani tana son ganinki.”
Gabana ya fadi ido na tsirawa Lantana ina so nayi magana amma bakina yayi nauyi ina kallo Lanatana ta bar gurin na garara cewa komai………..”Lahira dan Allah zoki rakani.” A sanyaye nayi mata maganar. Tace”Muje Allah dai yasa ba laifi kikayi ba.” Nace” Bana tsammanin hakan.” Tafiya muke ni da ita kowa na sa’ke sa’ke a ransa. Lahira guri ta samu ta zauna a harabar gurin ni kuma na nufi kofar shiga falon masu gadin kofar ne suka bude min na shiga a nutse sallama nayi cikin nutsuwa na ‘karasa inda suke zaune ita da yaron nata.
Gwiwa a kasa kaina a sunkuye nace”Ranki ya dade barkanku da wannan lokaci.” Amsa min tayi a nutse tana gyara zamanta shi kuwa ko kallona baiye ba kanshi yana dukufe yana kallon kasan kafet kamar yanda ya saba.

“Sumayya.” Sunana data kira yasa na dawo cikin hankalina. a nutse na amsa “Na’am ranki ya dad’e. ” Inaso ki nutsu da kyau zamuyi magana dake.” Ciki da tsantsar ladabi Nace”To ranki ya dade ina sauraranki.”

“Sumayya kiji tsoron Allah kiji tsoron mahallicin ki ki fad’a min gaskiyar lamari shin waye ya saki zubawa Magajin sarki guba a cikin abinci? inaso ki fad’a min gaskiya akan al’amarin nan daya faru babu abinda za’ayi miki idan kin fad’i wanda yasa ki aikata wannan mugun aikin gaskiyar magana nake jira ta fito daga bakin ki.

Zuciyata ce ta karye hawaye na kokarin zubo min ina kokarin mayar dashi sai da ya zuba a raunane nace” Ranki ya dade wallahi tallahi Allah d’aya ne daga shi babu wani, babu wanda ya sani na zubawa Yarima guba a farfesu wallahi ban san yanda al’amarin nan ya faru ba.” ina kuka na kare maganar.

Shuru falon yay na minti biyu kafin tace”Yi shuru ki daina kuka nayi miki wata tambaya.” Hannu nasa na goge hawaye nace”Ranki ya dade ina sauraranki.” tace”Bayan kin kammala aikin ki babu wanda ya shigo gurin.”? Shuru nayi ina tunanin maganar…….
BINTA UMAR ABBALE

Kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
29&30
Tana zaune a kan kujera ya shigo ya sameta, zama yay a gabanta ya dafe kansa kana ganin fuskarsa kasan yana cikin damuwa….Kallon fuskarta nayi itama nan take na gane akwai abinda ke damunta, Uwargida Huwaila mai babban daki ina nufin uwargidan Maimartaba itace tare da Moddibo a zaune abin duniya ya ishe su, Kallonsa tayi cikin tsantsar bacin rai da takaici tace ” Wai shin Moddibo ka tabbata duka maganin ka juye masa a abincin.”? Ajiyar zuciya ya sauke a cizgune yace”Wallahi gabadaya na juye domin ki tabbatar da magana ta ma kinga muzubin maganin.” Hannu ya zira a aljihu ya dauko wata madaidaiciyar kwalba…….Tace”Amma gaskiya abin ya bani mamaki wallahi, wannan maganin karfi ne dashi banyi tsammamin Yarima Ali zai shura a gurin ba.” Yace.”Ni kaina al’amarin ya bani mamaki wallahi a yanda nasan maganin nan da saurin kisa banta’ba tsammanin zaiyi rai ba.” Ajiyar zuciya ta sauke tace”Shegen yaro karfin jini gareshi to tunda ya tsallake wannan zamu barshi ya huta idan an kwana biyu mu cigaba da bibiyarsa dan ba rabuwa Zamuyi dashi ba har sai munga baya motsi sannan zamu hakura.” Muddibo tsaki mai karfi yaja yace.”gaskiya naso ya ya she’ka barzahu amma babu komai kamar yanda kika fada cewa ba zamu rabu dashi ba har sai mun cimma munufarmu a kansa.”
Tace”Ka manta kawai idan an kwana biyu zan sake kiranka mutattauna yanda za’ayi.” Yace.”Shikkenan sai naji daga gareki.” Sallama sukayi da juna kowanne zuciyarsa cike da mugun nufi akan Bawan Allah.

Sai kusan biyar da Rabi na yamma na gama wanki lokacin Tambaya ta dad’e da dawowa ina jin tashin maganarsu a daki suna hira ita da babana na dinga jin wani irin farin ciki da nishadi a cikin zuciyata hakika ina matukar so na ga iyayena na walwala da farin ciki.

A gurguje nayi wanka na fito na kimtsa jikina da sauri na kallesu nace”Ni zanje sashen Yarima domin na dafa masa abinda zaici da daddare.” Cike da nuna kulawa sukayi min fatan alkairi

Da sauri nake tafiya ina kallon rana wacce take ‘kokarin fad’uwa hakan ya nuna min cewa yamma tayi sosai daf ake da kiran sallar magariba tunda safe ban kara komawa sashen ba sai yanzu, addua nake a cikin zuciyata akan kada Allah yasa ya tuhume ni da wata magana.

Su Haruna na samu a harabar gurin muka gaisa a gurguje na wuce su daya daga cikin masu tsaron kofar ne ya bude min na shiga falon……..Can na hangoshi kwance kan doguwar kujera yayi filo da hannuwansa babu wata sutturar arziki a jikinsa vest ce mai duhu sai short nickar a jikinsa, kaina a kasa na ‘karasa inda yake, tsugunawa nayi kamar koda yaushe nace”Ranka ya dade barka da yamma.” Shuru yayi bai tanka min ba. satar kallonsa nayi ta kasan idona naga ya k’urawa rufin dakin ido, ganin yanda kwayoyin idanunsa suka kad’a yasa naji wani iri a jikina. gaishe shi na sakeyi yayi min banza.

Jikina ne yayi sanyi da halin ko’in kular da yake nuna min, a rayuwata na tsani nayi magana a shareni, muryata na rawa nace”Ranka ya dad’e zan shiga kicin yanzu inaso ka fada min abinda kake bukatar ci da daddare.”

“Me ya hana ki shigowa da wuri.”? a dakile yayi maganar, nace” Wallahi na tsaya nayi wanki ne shiyasa ban samu damar shigowa da wuri ba.” Shuru yayi yana sake gyara kwanciyarsa, ta kasan idona nake kallonsa naga yana bin ilahirin jikina da kallo. sunkuyar da kaina kasa nayi ina adduar rinjaye.

“Kin iya tuwo.”? Yafad’i maganar a kasalance. da sauri nace”Ranka ya dade kowane abinci kake bukata na zamani dana gargajiya na iya insha Allah baka da matsala.”

Ji nayi ya sauke wata ajiyar zuciya kamar wanda yaci kuka ya koshi! saurin d’ago kaina nayi ina kallonsa har yanzu ni yake kallo koda muka hada ido bai dauke kansa ba, yace.”Kiyi min tuwo amma bana san wannan abar mai wari a cikin miya. ” na gane daddawa yake nufi nace”To insha Allah ba zan san daddawa ba.” Mikewa nayi da sauri na nufi kicin din….Wani irin kallo ya bita dashi yana lumshe idonsa, a duk sanda zai kalli wani sashe na jikin yarinyar sai yaji kamar ana ‘kara rura masa wutar sha’awarta a cikin jikinsa.
Kullum so yake ya yakice abin daga jikinsa abin yaci tura da yarinyar yake kwana da ita yake tashi, a zahiri da bad’ini yasan yarinyar ba kalarsa bace domin hausawa suna cewa ‘Kwarya tabi ‘kwarya yana ganin ko iskanci zaiyi bai dace yayi da ‘yar bayi ba wacce take ma’kaskanciya a ‘kasan sa, dalilin daya sa kullum yake kokarin cire sha’awarta a cikin ransa abin nacin tura, sam rashin kyawunta da ‘bakar fatar ta basa damunsa abubuwan dake da wahalar samu daya hango a jikinta yake kulafuci yana ganin zai huta sosai a jikin yarinyar, yaso ace tana daidai dashi ne to da babu abinda zai hanashi auranta kodan ya kawar da ‘kulafuncinsa a kanta.

Mi’kewa zaune yayi ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa ya kai mintina goma a haka kafin ya mike yabi bayanta kicin din

Motsin tsayuwarsa naji a bakin kofa nayi saurin juyawa ina kallonsa, tsorata nayi sosai ganin yanda yake kallonsa da idanunsa da sukayi ja gashi sai lumshesu yake……Baki na rawa nace”Ranka ya dade kana bukatar wani abu ne.”? Girgiza kansa yay alamun baya bukatar komai.
Jikina a sanyaye na juya domin cigaba da aikina amma inaa! tsabar yanda idonsa ke tasiri a kaina yasa na kasa ta’buka komai.
‘Kasa – ‘kasa naji yace.” Idan kin gama kizo ki gyara min toilet d’ina.” Na kalleshi inaso nayi magana sai naga ya juya ya tafi.
Tsayuwa nayi ina mamakin maganarsa na dauka ai gyaran gida dasu toilet duk nasu Haruna ne ni bani da hurumin hakan, to kodai yana da wata munufa ne? wani sashe na zuciya ta yake fada min haka.. shuru nayi ina nazari, to ko ma dai wace irin manufa yake da ita a kaina bana fatan ya samu galaba a kaina toilet zan shiga in gyara masa da tsarkakkiyar zuciya. saboda haka ina gama ayyukana na nufin dakin nasa domin aikata aikin daya umarceni.

Zaune na sameshi a kan sofa idanunsa tsaye a kofar shigowa hada ido mukayi nayi gaggawar sauke kaina kasa, cikin tsarguwa na k’arasa kofar toilet din zanin jikina sai hard’eni yake tsabar yanda ya ‘kureni da idanunsa, toilet din na bude na shiga ba tare da nace masa komai ba gaskiya na fara gajiya da wannnan masifaffan kallon da yake min………Girman toilet din da yanda aka ‘kawata shi ya dinga bani mamaki bandaki gurin zubar da najasa an narka masa dukiya kamar baza’a mutu ba, girgiza kaina nayi na tattare zanina cikin sauri na soma aikina so nake nayi saurin gamawa kada magariba tayi…..Undis dinsa na tattara nasa cikin abin wanki ina kokarin kunna washing machine din ya shigo toilet din, ban yarda na kalleshi ba nace”Ranka ya dad’e za kayi wani uzirin ne.”? Inda nake tsaye ya durfafo gabana ya tsananta fad’uwa adduar rinjaye na shigayi a cikin zuciyata.

Daf dani ya tsaya yana fesa min hucin numfashinsa, kasa kallonsa nayi sabida yanda naga ya koma wani iri gabadaya yanayin fuskarsa ya sauya kalar tausayi. babu zato naji ya riko hannuna ya d’ora saman short nickar din dake cikinsa, a zabure! na cire hannuna ina kallon gurin…..gabansa naga ya mike cikin wandon yana sake kokarin kamo hannuna yasa a gurun….bangajeshi nayi da karfin gaske! yayi taga-taga zai fad’i! cikin zafin nama na bude kofar toilet din na fita gabana na dukan uku uku anya kuwa zan iya cigaba da zama da wannan guy kuwa? gabadaya yanda na fahimce shi baya nufina da alkairi.

Bayan fitar ta daga toilet din goshinsa yasa a jikin bango (garu) yana furzar da wani irin huci mai zafi daga bakinsa, ya rasa wace irin masifa ce wannan gabad’aya ya rasa gane kansa da abinda ke damunsa burinsa bukatarsa ta biya da yarinyar ita kuma taki ta bashi had’in kai yarinyar gabadaya ba tsaransa bace har ya ajiye girma da muqamin sa yana biyayyarta tana wula’kantashi yana ganin dole ya nuna mata kuskuranta akan irin abinda take masa, da kyar yay wanka ya daura alwala ya fito fuskar nan babu fara’a ya kintsa jikinsa, k’asa ya sauka, lokacin na kammala komai na shirya gurin cin abincin ina zaune abin duniya ya isheni……tunda naga yanayin fuskarsa nasha jinin jikina, koda ya karaso inda nake sake risinar da kaina nayi da fadin”Barka da fitowa.” Wuce ni yayi ya nufi hanyar fita ba tare da yace komai ba. bayansa nabi da kallo ina ayyana abubuwa da yawa a kansa.
Bayan fitarsa da minti goma nima na bar gurun.

Sai bayan daya gabatar da sallar isha’i ya shigo kai tsaye gurin cin abinci ya nufa ya zauna daya daga cikin kujerun gurin, wayarsa ya d’auko ya shiga ma’adanar hotuna tarin pictures ne na matan turawa da bakake fata wanda ba zasu irgu ba, yawanci kuma duk tsirara suke pictures din yake kallo wai ko zai samu sasaaucin abinda ke damunsa. Cikin wannan halin na fito na sameshi, kai tsaye inda yake na nufa.
Dan risinawa nayi murya k’asa nace”Ranka Ina iya zuba maka abincin.” A watse ya kalleni yace.”haka kawai zan zauna anan gurin babu dalili.”? Da sauri nace”Afuwa ranka ya dade.” Mikewa nayi cikin nutsuwa na bud’e fulas din dana sa tuwon a ciki na dauk’o leda biyu nasa akan plate na mayar da fulas din na rufe miyar na bud’e itama nasa ma a plate na bude daya fulas din dake dauke da jar miya waccan nasa mata naman rago itama nasa masa a plate kana na mayar na rufe ruwa da lemo na ajiye masa gabansa naja gefe na tsaya kaina a kasa nace”Ranka ya dad’e na had’a komai.”
Dago kansa yayi yana bin abincin da wani irin kallo yana ya mutse fuska yace.”Ke! wannan wane irin tuwo ne ba’ki sai kace ke.”!! Naji ciwo cimin fuska da yayi, cikin dauriya nace”Ranka ya dade tuwon dawa ne.” Tsaki yaja mai karfi ya mike a fusace ya d’aga k’yallen da abincin ke kai ya watso min a jikina.! cikin rashin mutunci yace.”Waye zaici wannan ba’kin abun ko an fad’a miki kowa ma jaki ne kamar ki! dallah malama matsa ki bawa mutane guri.”! Cikin hayaniya yake maganar har yana dukan daning d’in da hannunsa….
BINTA UMAR ABBALE

Kuyi sharing please👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
27&28
“Anya Shatima da Moddibo zasu iya cutar da d’an uwansu? tunanin da nakeyi kenan a cikin zuciyata. ni dai nasan babu wani ‘bako daya shigo sashen bayansu sai ni dasu Haruna bana tsammanin Abokanshi kuma shaqiqan ‘yan uwansa zasu iya sa masa abunda zai kashe shi a cikin abinci. shuru nayi kaina a kasa ina tararrabin fad’ar maganar dake bakina.
“Sumayya ke nake saurare.” Muryarta ce ta doki dodon kunnena.

A nutse nace”Ranki ya dade babu wani bako daya shigo sashen sai ‘yan uwanshi wato Shatima da Maddibo sune suka shigo bayan na jera abincin a daning na hau sama domin in sheda masa lokacin dana sakko na samesu su biyu a falon.” na karasa maganar ina sake sunkuyar da kaina……Fulani na shirin magana ya katseta da fad’in “Me kike nufi da wannan maganar kina nufin Maddibo ko Shatima wani na iya samin guba a abinci.”? Shuru nayi gabana na fad’uwa sabida yanayin yanda yay maganar ya nuna min ‘bacin ransa.”

“Sumayya.” naji ta kira sunana, amsawa nayi ina kallonta, tace”Tun ganina dake na farko naji kin kwanta min a raina sosai na yaba da nutsuwarki da hankalinki ina mutukar son mutum mai gaskiya da rikon Amana, inaso ki ri’ke amanar dana dam’ka miki hannu biyu kisa idonki sosai akan masu shige da fice a sashen babana, tunda ka kan ‘yan uwanshi maza da mata da kuma sauran bayin dake cikin gidan nan inaso kisa idonki sosai akan shige da ficen su a sashen sannan ki dinga lura da abincinsa gami da abin shansa ruwa ko lemo ko makamancin haka Ina neman wannan alfarmar a gurin.”

Cikin sanyin jiki nace”Insha Allahu zan kula da amanar da kika bani nayi al’kawarin bin umarninki.” Murmushi tayi a nutse tace”Tashi kije Allah yayi miki albarka.” na amsa da ameen ina jin sanyi a cikin raina. yun’kurawa nayi a nutse nace”A tashi lafiya ranki ya dade.” Hannu ta daga min alamun naje da sauri na bar gurin zuciyata tas tabbas addua bata faduwa ‘kasa banza.

A nutse ta kalleshi gami da fadin”Babana me ka fahimta a maganar yarinyar nan? ni ina ganin wannan al’amarin daya faru da akwai saka hannun ‘yan uwanka ina nufin Shatima da Moddibo.”

Kallonta yayi mamaki tattare a fuskarsa, tace”Ko shakka bana yi akwai saka hannunsa a ciki amma inaso kasa ido sosai a kansu sannan ka kula da kanka ba komai xaka ci a gabansu ba akwai mummunar manufa a zuciyarsu.”

“Mamma bana tsammanin Shatima ko Moddibo wani zai iya cutar dani a cikinsu ni nafi tunanin wani abu yarinyar nan tayi amfani dashi gurin girkin wanda ya janyo hakan bana zargin kowa akan faruwar wannan al’amari.

Murmushi me ciwo tayi tace” Nima bana zargin kowa amma dai tunda nace maka kayi takatsantsan dasu to kayi domin hausawa na cewa makashinka na gindin ka nasan baka manta irin zaman marinar da akeyi a cikin gidan nan ba, kowa ka ganshi ka kalle shi kawai mafi akasarinsu babu kyakkyawar manufa acikin zuciyarsu.”
Shuru yayi yana nazarin maganar mahaifiyar tasa.


Lahira tace”Wai ya naga kin fito jikinki duk a sanyaye.” Ajiyar zuciya na sauke nace”Lahira ina cikin tsaka mai wuya amma na roki Allah ya fitar dani cikin ruwan sanyi.” Tace”me ya faru.” A nutse na warware mata dukkanin abinda ke faruwa.
Lahira a jiyar zuciya ta sauke tace”Gaskiya dole ki shiga tashin hankali amma mungode Allah da ya sanya Maimartaba da amaryarsa masu fahimta ne, daba dan hakaba nasan da tuni kina fuskantar hukunci.”
Nace”Hakane Lahira amma shi Yariman bai yarda da cewa ‘yan uwansa zasu cutar dashi ba ban san abinda ke cikin zuciyarsa ba.” Lahira shuru tayi tana tunani kafin tace”Dama ai bai za ma lallai ya yarda ba saboda ganin sun taso tare abu makamancin wannan bai ta’ba faruwa ba a tsakaninsu dole ya shiga ko kwanton cewa zasu iya cutar dashi.” Nace”nima nayi kokwanto da farko daga bisani da nayi tunani sai na gane hakan zata iya faruwa tunda yanzu gabad’ayansu idanunsu ya rufe babu abinda suke so sai mulki na fahimci cewa suna masa hassada dan ganin kamar shi zai gaji mahaifinsa.” Lahira tace”Dama abinda yake faruwa kenan yanzu duk wani abu da ‘yan uwansa zasuyi masa a kan mulki ne saboda haka shawarar da zan baki itace ki zage damtse ki kula da amanar da kika d’auka kiyi iyakacin bakin kokarin ki gurin ganin kin kareshi daga sharrin masu sharri.”
A sanyaye nace”Insha Allahu zan lura zanyi iyakacin bakin kokarina.”
Da wannan maganar muka rabu da juna.

Sosai nayi farin cikin ganin babana a zaune yana cin abinci da kuzari a tattare dashi, cikin farin ciki na ajiye jakata na zauna kusa dashi ina murmushi nace”Baba nayi farin cikin ganinka a zaune kana cin abinci da hannunka hakika hankalina na tashi a duk sanda zanga Tambaya na baka abinci a baki yau naji dadi sosai dana ganka ka samu lafiya kana ciyar da kanka abinci da hannunka.” Murmushi yayi a nutse ya kalleni yace.”Ai tun bayan fitarku ke da mahaifiyarki naji kwari a jikina da kaina nayi wanka nayi dukk sallolin da ke kaina Sumayya hakika bamu da abinda zamuyi wa Yarima sai dai addua gami da fatan gamawa da duniya lafiya naji dad’in taimakon da yayi min Allah yayi nufin zan samu lafiya ta dalilinsa hakan yasa na yanke shawara kancewa bayan sallar isha’i zaki rakani nayi masa godiya kan alkairin da yayi min.”

Ina murmushi nace”Gaskiya ne baba Yarima ya cancanci godiya daga gurinmu insha Allahu zanyi maka jagora zuwa gurinsa kamar yanda ka bukata.” Yace.”To masha Allah kema ki dauki abinci kici dan naga kamar da akwai yunwa a tare dake.” Cike da walwala nace”Baba lokacin dana shigo ina dauke da yunwa mai tsanani amma ganinka a zaune kana cin abinci da kanka yasa naji cikina ya cika yanzu bana jin yunwa ko kadan.” Yana dariya yace.”Sumayya ban yarda ba dole kici abinci domin bana son ki zauna da yunwa. kwanukan dake gabansa na janyo
Cike da tsokana nace”To bari na fara cinye wanda ka rage saboda na samu albarka idan ban koshi ba sai na karo wani.” Hannunsa na dama ya d’ora a saman kaina fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi yace.”Allah yayi miki albarka Sumayya.” Ina kokarin kai abinci bakina Na amsa da ameeen baba.”

Tsaf na gama cikin abincin na gyara gurin na gyara masa shimfid’arsa kana na shiga tattaro kayan wankin mu kwata kwata bana san zama da daud’a shiyasa kullum gurin mu zaka sameshi a tsaftace babu kazanta ko kad’an.
Wanki na fito dashi tsakar gida na ajiye a guri guda kana na koma cikin dakin, na sameshi yana duba littafin addini nace”Baba bari naje na duba dawakai bana so hankalina ya dauke gurin wanki na manta ban basu abinci ba.”

Ya kalleni yana girgiza kansa nasan abinda yake ji a zuciyarsa game dani,sunkuyar da kaina kasa nayi yace.”Ina alfahari da Allah ya bani ke a matsayin ‘ya kin fiye min haihuwar maza goma Sumayya ina alfaharin samunki kuma ina mai tabbatar miki da cewa yanda kikayi mana biyayya kema da yardar Allah naki ‘ya’yan zasuyi miki.”
Murmushi nayi cikin jin dadin adduar da yayi min nace”Insha Allah baba kada ka damu zan cigaba da kula da aikin ka har sai sanda ka samu kwarin jikin ka.” Murmushi yayi ya zuba mata ido har ta fita daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke yana addua akan Allah ya bashi tsawan rai a duniya yaga auranta da abinda zata haifa………..
BINTA UMAR ABBALE

Kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
33&34
Kwana biyu kyara da hantara ne a Tsakanina dashi komai nayi masa ba nayi masa gwaninta, magana kuwa sai nayi sau biyar bai bani amsa d’aya ba, haka dai na cigaba da hakuri da halinsa ina kokarin ganin na sauke nauyinsa dake kaina, a tsakanin kwanaki biyu zuwa hud’u duk abinda zan girka masa naci ko sha baya ko kallon daning din ballanatana ya zauna yaci, yanda na ajiye haka zan zo na dauke, ganin kamar ‘barnar tayi yawa yasa na yanke shawarar samun sa muyi magana idan baya bukata sai na daina wahalar da kaina da asarar abinci…….. samun sa nayi gurin da yake hutawa na tsuguna gwiwa a ‘kasa kamar koda yaushe nace” Ranka ya dade Barka da yamma.” Kamar da dutse nake magana, kallonsa nayi ina jin wani kunci a cikin zuciyata, a gaskiya na fara gajiya da wannan wulakancin, hankalinsa na kan wayarsa yana latse latse a kai……’bacin ran dake taso min na danne Nace”Dama inaso muyi magana da kai ta fahimta ne.” Ta ‘kasan ido naga yayi min wani kallo, na cigaba da cewa”Naga kamar baka ‘bukatar abincin da nake hidimar girka maka safe da rana da dare me zai hana a daina a sarar abinci idan baka bukata sai na bari akan a dinga zubarwa.”

Zamansa ya gyara yayi wani irin zama irin nasu na saurata hannunsa dake d’auke da zobunan azurfa ya d’ora saman gwiwarsa ya tsira min idanunsa.
Kasa kallonsa nayi a yanayin dan ganin yanda ya ‘kara wani kwarjini da cika ido gashi zaman da yayi yay masa kyau ha’kika ya dace a kirashi da Sarki! ba Yarima ba dan komai nashi cikin mulki da muskilanci yake yi.

“Kece kika ajiye abincin gidan da kike wannan maganar.”? Maganarsa ta bani mamaki sosai nace” A’a bani bace ba, ni a nufina ‘barnar abincin da ake tayi yawa sabida na safe haka yake tarar dana rana sannan na dare ya tarar dana rana, wani zubin lalacewa yake sai dai na bawa dabbobi ko na zubar.”

“Ki cigaba da aikin ki bana bukatar ki huta.” Yafad’a tare da tsira mun ido gami da san ya tabbatar min da maganarsa, “Inaso ka fad’a min dalilin ka na yanke wannan hukuncin ya za’ayi kai ba cin abinci kake ba amma kasa a girka a zubar wannan ai izgilanci ne.” Gaura min mari yay yana huci yace.”Koda yaushe kina yawan fad’ar wannan maganar akai na sabida kin raina ni ko.”? yana nuna ni da hannunsa yake maganar, d’auke kaina nayi daka fuskarsa nayi kasa dashi hannuna dafe da kuncina…..”Wallahi duk sanda na sake jin kin jefe ni da kalmar izgilanci sai na baki mamaki na lura dake kwata-kwata bakya shakka fad’a min kowace kalma kodan kinga na nuna ina sha’awarki ne kike tunanin wani abu.'”

D’agowa nayi raina a ‘bace Nace”Allah ya baka hakuri idan furucina ya ‘bata maka rai ni inaso na tunasar da kai abinda ka sani ka manta ko kuma nace kake takewa saboda giyar mulki ranka ya dad’e kai mutum ne mai girman kai gami da Izigilanci a kan komai alhalin kai d’in ba komai bane a gurin Allah inaso na tunasar da kai cewa wannan d’abi’un da kake yi zasu nesan taka da rahamar Allah.” Hawayen da nake maqalewa ne suka zubo.

“Tashi ki bani guri.”! Kalmar da ya fad’a kenan cikin ‘bacin rai! Mikewa nayi na sunkuya cikin tausasawa nace” A gafarce ni idan maganar da nayi ta ‘bata maka rai.” Ba tare da yace min komai ba ya sunkuyar da Kansa k’asa.
Gurin na bari da sauri na nufi sashen Mahaifiyarsa wato Fulani zuwa zanyi na sheda mata dukkanin abinda ke faruwa, domin kamar ita ta dauke ni aiki ta bani amana yana da kyau duk abinda ke faruwa tasa ni saboda kada wani mummunan abu makamancin wanda ya faru a baya ya faru a tuhume ni da wani abu, a tsakanin kwanaki biyar din da suka gabata bani da masaniyyar inda yake cin abinci na safe rana da dare idan ma a gurinta yake ci to yana da kyau na sani ko hankalina ya kwanta.

Ina gurfane a gabanta na sheda mata dukkanin abinda ke faruwa……a da tana kishingid’e a lokacin da nake maganar sai naga tayi saurin mi’kewa zaune gabad’aya ta mayar da hankalinta kaina tace”Sumayya kika ce yau kwana biyar babana baya cin abincin da kika girka.”? Nace”K’warai kuwa ranki ya d’ade ganin kwanakin suna yawa ne yasa na yanke shawarar zuwa na sheda miki.”

“A’ina babana yake cin abinci.”? Tafad’a tana kallona, Nace” Ranki ya d’ad’e nima wallahi ban sani ba.” Ajiyar zuciya ta sauke da sauri tace”Miko min wayata gata nan.” Da sauri na dauka na mika mata.
Number shi ta kira inaji yana gaisheta bata amsa ba tace”Maza kazo sashena ina nemanka.”
Kashe wayar tayi ta kalleni da fad’in “Sumayya kije ki cigaba da aikin ki kada ki fasa yi masa abinci a duk sanda kika kammala kika sheda masa idan bai ci ba kizo ki sheda min.”

Nace”To insha Allah ranki ya dade zanbi umarninki.”Tace.”Tashi kije Allah yayi miki albarka.” Cikin farin ciki na amsa da “ameen Ranki ya dade ina godiya.”

Raina fari tas na bar sashen gurinmu na nufa domin nayi shirye shiryen shiga gurun karatu……Tsaf na fito cikin hijabi fari tas da jakar littafai a hannuna Babana na kwance a katifa bacci naso ya daukeshi nace”Baba kayi bacci ne.”? Mi’kewa zaune yay yace.” Yana dai so ya dauke ni dama ke nake jira ki shirya mu fita tare yau inaso na shiga gurin Dawakai na dubasu.”

Nace”Baba ka zauna ka sake samun ‘kwari jikin ka dawakai na nan kalau babu abinda ya samesu.” Yace.”Sumayya zaman nan ya isheni wace lafiya kuma akeso na samu bayan wannan inaso na koma bakin aiki.”Nace”To shikkenan baba nida naso ka k’ara watsakewa sosai kafin nan.”

Mi’kewa yay yana dariya yace.”Sumayya zaman gida sai mata idan kinga namiji ya zauna a gida to dole ce kamar dai ni da rashin lafiya ya hanani gudanar da harkokina.” Murmushi nayi nace “Hakane baba, to tunda Tambaya na gurin aikinsu sai mu sawa kofar ‘kwad’o.” Yace.”Eh hakane yi maza ki d’auko kwad’on insha Allahu kafin ta dawo nima na dawo.”

‘Kwadon (key) na dauko muka fito tare muna hira na kulle gidan na bashi key din yasa a aljihun rigar jikinsa, muka fara tafiya…….Daf da zamu rabu kowa yay inda ya nufa Lantana ta tari gabanmu, a duk sanda zanga Lantana sai gabana ya fad’i saboda duk sa’kon da zata fad’a bana alkairi bane.

“Sumayya kije can ‘bangaran Maigirma Ciroma Gimbiya Lawisa ke san ganinki.” Na kalleta da fad’in “Lantana kin dai ga shirin da nayi ko zan shiga gurin karatu ne sai dai idan na fito.”

“Kinga Sumayya bani zaki fad’awa hakaba ita wacce ta aiko ni ita zaki fad’awa ni dai na cika umarnina idan kin’ki zuwa zan tabbatar mata da cewa na sheda miki sa’konta.”

Zanyi magana babana ya katseni Ya kalli Lantana a nutse yace.”Kije kice gatanan zuwa.” Lantana ta bar gurin da sauri…….Cikin kulawa ya kalleni yace.”Sumayya duk wani uziri naki to yabi bayan na masarauta, kiran da Gimbiya Lawisa tayi miki yafi uzirinki wanda zaki gabatar a yanzu, nasha fad’a miki cewar baki da wani gata da abinda zakiyi tun’kaho dashi sai wannan masarautar domin a cikinta aka haifi iyayena da kakanni na gabad’ayan mu tasowa mukayi muka ganmu a cikinta tsohuwar marasauta ce mai d’umbin tarihi, iyayenmu sunbi umarnin masarauta har suka koma ga Allah, Ina fatan ni dake da mahaifiyarki muma mu kamanta abinda magabatan mu sukayi dan haka kibi umarnin masarauta kije kiji kiran da akeyi miki.

Ajiyar zuciya na sauke ina kallonsa a sanyaye nace”Baba naji kana maganar nabi umarni inaso nayi maka wata tambaya.” Yace.”Ina sauraranki.”” Nace”Baba idan ya kasance wani umarnin ya sa’bawa dokokin Ubangiji ba shin har dashi zan bi.”? Girgiza kansa yay yace.”A’a Sumayya ban umarce ki akan sa’bawa Allah ba, duk abinda ya zama na sa’bawa mahallici ne to kiyi kokarin nesanta kanki dashi.
Nace.”Alhamdullihi baba bari nayi sauri naje domin naji kiran da ake min.” Cikin kauna gami da tausayi irin na iyaye yace.”To d’iyar kirki Allah yay miki albarka.” Ameen nace cikin sauri na bar gurin….Lawi bai bar gurin ba har sai da ya daina hango ‘yar tashi.

Lantana ce tayi min jagora har Lambun da take hutawa, tare da hadimanta na sameta. takalmana na cire a nutse nasa gwiwowina a k’asan gurin nace”Barka da hutawa ranki ya dade.” Shuru tayi min bata amsa ba. gurin ya dauki shuru na kusan minti uku kafin ta dago kanta cikin shan qamshi ta kalli hadimanta dake gefe da gefanta tace”Ku tashi kuje zanyi sirri da Sumayya.”
Jiki na rawa suka miqe suna godiya.

Gurin ya sake daukar shuru na ‘yan mintina kafin naga ta gyara zamanta cikin kasaita ta kalleni da fad’in “Zauna sosai muyi magana aini daga yau kin zama qawata aminiyata.” Cike da mamaki nake kallonta ina mamakin furucinta. zamana na gyara sosai a gabanta nace”Ranki ya dade ina sauraranki.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin naji ta kira sunana. a nutse na amsa ina kallonta, Tace”Inaso na saki wani aiki ta ‘bangaran Yarima Ali ina nufin magajin Sarki, tunda ya kasance kin zama mai kula dashi ta fannin abincinsa da abin shansa to zanyi amfani dake gurin ganin bukata ta biya a kansa.
Nasan kin san da maganar auran dake tsakanina dashi ko.”? Kallonta nayi ina mamakin maganarta aure a tsakaninta da Yarima gaskiya ban san da maganar ba.

Girgiza kaina nayi nace”A’a ranki ya dade ban san da maganar ba.” Tace”To yau na sanar dake cewa Iyayanmu zasu daure aurena dashi farkon watan gobe, a zahiri nike sonsa koda yana sona bai kai wanda nake masa ba, wannan dalilin yasa nake so nabi matakan da zasu janyo hankalinsa kaina, inaso kafin zuwan ranar daurin aurena dashi na mallake shi da zuciyarsa gabad’aya.”
Da sauri na kalleta, sai naga tayi murmushi tana d’aga min gira ‘kasa nayi da kaina tare da cigaba da sauraranta.

“A kwai wasu sinadarai da zan baki wanda zaki dinga zuba masa a cikin abincinsa da abin shan sa ya zama na dai duk wani abu da zai ci ko ya sha kina sa masa sinadaran dana baki.” ajiyar zuciya na sauke tare dago kaina na kalleta bayan gama maganarta ta Nace…….
BINTA UMAR ABBALE

Please kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
31&32
Cikin wani irin yanayi na ‘kunar zucci nake kallonsa kafin na kalli jikina gabad’aya gaban rigata ya ‘baci da miya har wajejen wuyana da gefan fuskarta ya samu rabonsa, idona naji yana kawo ruwa wannan irin wulakanci ne dacin mutumci mutumin nan yake min, danne damuwa ta nayi na kalleshi yana zaune sai huci! yake kamar wanda akayiwa gagarimun laifi nace”Ranka ya dad’e kai ne ka bukaci da ayi maka tuwo ni kuma sai nayi tunanin tuqa maka na dawa saboda nasan abun marmari ne zai fi maka dadi akan sauran dan me zaka wulakanta ni ka wulakanta abinci babu kyau abinda ka’aikata domin akwai mutane da yawa da suke neman abinda zasu kai bakinsu kai ka samu kana watsar wa.”
Cike da jarumta nake maganar.

Wani irin kallo naga yanayi min na k’askanci kafin ya tattaro yawun bakinsa ya tofa min a fuska cikin izigalanci yace.”Ki ‘bace min daga gurin nan na daine ganin wannan ba’kar fuskarta ki a idona.”

Takaici kamar ya kasheni nasa hannu na goge yawun daya tofa min, baki na bude zanyi magana ya daga min hannu alamun baya bukatar yaji abinda zance, banyi shuru ba domin na riga na dauki aniya akansa, Nace”Kana yawan kushe hallitar Allah shin wai me bak’in mutum yayi wa mutane ne da suke ‘kyamatarsa kada ka manta yadin da akayiwa d’akin Allah ado ba’ki ne,, da farin mutum da b’akin mutum duka Allah ne ya hallicesu kuma bai fifita wani akan wani ba duk daya suke a gurinsa wanda yafi kyautata masa shine mafi kusanci dashi, amma kun d’auki karan tsana kun d’orawa ‘bakar hallita wannan yana nuni da cewar kuna nunawa Ubangiji cewar bai hallita ba.”

Mi’kewa tsaye yayi ya nuna min kofar fita da hannunsa. Girgiza kaina nayi na bar gurin zuciyata na wani irin tafarfasa gabad’aya halayyar sa bata da kyau girman kai gami da izzah muna nan ayyuka ne wanda Allah baya so yana da ilimin addini daidai gwargwado yasan abubuwan da yake aikatawa basu da kyau amma saboda shed’an ya riga ya gama yi masa fitsari akansa kullum daukar kansa yake wata tsiya alhalin kuma a gurin Allah ba komai bane.

Koda na shiga gurin mu kai tsaye ruwa na zuba a bokiti na shiga band’aki domin wanke jikina nasan idan na shiga daki iyayena suka ga jikina a ‘bace zasu tambayi dalili shiyasa nayi wannan dubarar, bayan nayi wanka zanin kamfalar na d’auro a kirjina na yafa dankwalin na fito, ina tsaka da d’aura alwala Tambaya ta fito daga daki, tace”haba ni tun dazu nake jin motsi ina daki nace bari dai na duba na gani ashe kece.”tana kallon fuskata tafadi maganar, kokarin kawar da abinda ke damuna nayi nace”Ai ina shigowa bandaki na nufa nayi wanka ko jikina ya warware.” Tace”Ai kam wannan uban wanki da kikayi ai dole jikin ki yayi miki tsami amma me yasa baki d’umama ruwan zafi ba? ina ganin da da ruwan zafi kikayi wankan sai kinfi jin dadi.”

Nace”Nima sai da na fara wankan sannan nayi tunanin hakan.” Tambaya kicin ta wuce domin ajiye kwanonin abinci dake hannunta ni kuma bayan na daura alwala dakin na shiga na samu babana zaune a kan dadduma yana lazimi sannu nayi masa na shige cikin kuryar dakin domin na kimtsa jikina.

Irin dai kayan nasa a jikina na fito da hijabin da nake sallah a wuyana, dadduma na hau na tayar da sallah……….Tambaya ta shigo dakin hannunta rike da silba mai murfi a kusa dani ta ajiye silbar tace”Idan kin idar ga abincin ki nan.” kuryar dakin ta shiga domin gabatar da tata sallar, bayan na idar da sallar na jima hannuna a sama ina rokon Allah yasa naci jarabawar daya d’ora min na kuma tsananta addua ta akan ya kareni daga sharrin masu sharri. shafawa nayi a fuskarta na juya ina kokarin cire hijab din wuya na, sai naga babana na shafa fuskarsa da dukkanin hannuwansa hakan ya nuna min cewar adduata yake shafawa a fuskarsa.

Ina murmushi nace”Baba barkan ka da dare.” Shima da murmushin a fuskarsa yace.”Barka dai yarinyar arziki.” silbar abincina na janyo a nutse nace”Naso na dawo da wuri muci abinci a tare domin samun tabarraki.” da yalwatacciyar fara’a a fuskarsa yace.”Na riga naci abinci Sumayya amma kawo na sa miki albarka.”

Da sauri na miqa masa silbar abincin ina murmushi, bisimillah yay yasa hannunsa ya d’ibi dafadukan shinkafar dake cikin silbar a bakinsa yasa yana taunawa yace.”To gashinan nasa albarka.”

Silbar na janye na gyara zamana ina murmushi nace”Godiya nake baba Allah ya kara maka lafiya.” ya amsa da amin yana kallona da murmushi a fuskarsa.

D’akin ne yay shuru na minti biyu kafin na kalleshi a nutse nace”Yanzu idan na kammala cin abincin zamuje can sashen Yariman ko.”? Yace”Af kinga na manta wallahi gwara da kika tuna min maza gama cin abincin muje.”
“To nace” na mayar da hankalina gurin cin abincin…Tsaf na kammala na fita da kwanon ina shiga dakin na tarar dashi a tsaye kuryar dakin na leqa Tambaya na kan dadduma da carbi a hannunta nace”Zamuje sashen Yarima da Baba.” Hannu ta daga min alamun sai mun dawo.” Koda na juyo sai na tarar har ya rigani fita murmushi nayi nabi bayansa da sauri.

Lokacin da muka isa sashen shuru dan su Haruna ma a harabar gurin muka samesu nan yake sheda min ai Yalla’bai din ne yace su fita su bashi guri zuwa anjima sa dawo.” hakan ya nuna mun cewa har yanzu yana cikin ‘bacin ran abinda ya faru tsakani na dashi…..Babana na kalla a tsanake nace”Baba zauna bari na hau sama na sheda masa zuwanka.

Ya samu kujera ya zauna a nutse ni kuma na nufin saman domin sheda masa zuwansa…..Na jima ina nocking kafin naji yace.”Waye.”? A sanyaye nace.”Nice.” shuru na minti biyar naji alamun bud’e k’ofar matsawa gefe nayi kaina a kasa……Wani irin kallon banza ya watsa min da fad’in “Lafiya.”? Kai a kasa nace” Babana nayiwa jagora zuwa gurinka yana so ku gaisa kana yay maka godiya kan alkairin da kayi masa sosai yaji dadin magungunan daka bashi yanzu haka yana ‘kasa jiranka.”

Shuru bece komai ba na d’ago kaina a sace na kalleshi sai naga yana kallon ‘kasan gurin, ajiyar zuciya na sauke cikin raina nace”Abin yazo kenan kallon k’asa kamar makaho.” Mun kai minti biyar nida shi a tsaye a kafin naji yace.” Ni Bana abun alkairi domin a gode min, ba ni na bawa babanki Lafiya ba Allah ne dan haka shi zaiyi wa godiya ba niba.” Yana k’are maganarsa ya bugo min kof’a.

Na jima a tsaye a gurin ina kallon kofar kafin na sauke ajiyar zuciya a sanyaye na sau’ko ‘kasa na sameshi a zaune a inda yake.

Cikin taushin murya na sheda masa abinda yace….bai nuna komai ba yace.”To babu komai Sumayya dama mafi akasari masu taimako basa so a damesu da godiya tabbas hakane Allah ne ya bani lafiya amma kuma shine ya zama sanadi dan haka zan cigaba dayi masa addua har karshen rayuwata.”
A sanyaye nace”Hakane baba Allah ne abin godiya a garemu addua kuma ba zamu daina yi masa ba tunda shi ya zama sanadi.” To Har muka isa gurin mu muna tattauna maganar a tsakanin mu………..
BINTA UMAR ABBALE
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

Sannu da kokari mai babban suna

DR MUHAMMAD MK
Ina mutukar godiya da alkairin ka, na baka kyautar wannan pege d’in🥰

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
35&36
“Ranki ya dad’e wane irin sinadarai ne kike magana akansu inso kiyi min bayani yanda zan fahimci inda maganar ki ta dosa.” Duk da na gane abinda take nufi sai kawai na tsinci kaina dayi mata wannan maganar.

Murmushi tayi tace”Haba Sumayya kamar ba mace ba zaki ce baki fahimci inda na dosa ba, to shikkenan tunda baki gane ba bari na fahimatar dake, Takanas! Mamana ta tura aka kar’bo mata Taimako daga gurun malamanta duk domin na samu nasarar mallakar zuciyarsa kin san hausawa nacewa ko kana da kyau ka qara da wanka to ballanatana ni da ban zauna daram a cikin zuciyarsa ba, kinga kuwa dole na tashi tsaye naga na r’ikeshi a tafin hannuna kafin zuwan ranar daurin auran namu.”

Wani irin kallo nake mata na mara hankali Nace”Ranki ya dade ki gafarce koda maganata zata ‘bata miki rai ni ina ganin wannan sinadaran babu wani abu da zasuyi miki me zai hana ki nemi soyayyarsa ta hanyar Allah duk ga hanyoyi nan a saukake hanyoyin da zaki bi ki mallakeshi da zuciyar sa, a ganina idan kika ce ta wannan hanyar zaki mallake shi to zakiyi ta wahalar da kanki a banza da wof………”Ke! rufe min shegan bakin ki a nan gurin.” A fusace ta katse min magana.
Tsira mata ido nayi kallona take tana huci tace”Ba shawara na nema a gurinki ba umarni na baki zaki aikata abinda na saki ko ba zaki aikata ba.

Har na bude baki zanyi magana sai kuma nayi shuru ina nazari, kai tsaye idan na’ki aminta da umarninta zata bi wata hanyar ne ta cimma k’udirinta, tabbas asiri zaiyi gaggawar tasiri a jikinsa tunda na lura bai wani damu da addini ba wannan tunanin da nayi yasa nayi saurin neman afuwarta nace”Insha Allahu zan zartar da umarnin zaki bani.” Gyara kishingid’ar tayi tana saukar da numfashi, shuru gurin yay kimanin minti goma kafin naji tace”Kalleni nan.” Na dago kaina na zuba mata ido.

Wata leda viva ta miko min da fadin”Bud’e ki fito da kayan dake ciki.” Da sauri nayi abinda tace, magunguna ne a ‘kulle a wani ‘bakin yanki mai ratsin ja da fari dauri uku tace.”Ki duba a tsanake zanyi miki baya ni kada kije kiyiwa mutane baragada.”

Nace”Ina dubawa ranki ya dade.”
“Wannan wanda yake da ratsin baki da fari na abinci ne kina jina ko.”? nace” Eh ina jinki.” Ta cigaba da cewa”Duk wani abinda zaici ya kasance sai kin barbad’e shi da wannan maganin sannan ki bashi.” Nace” na fahimta ranki ya dade.” Ajiyar zuciya ta sauke tace”Shi kuma wannan mai ratsin ja da fari din na lemo ne kina jina ko.”? Nace”Eh.” ta cigaba da cewa”lemo ko wane iri ne kafin yasha ki bude ki barbad’a maganin a ciki.” Nace”To ranki ya dad’e na fahimta insha Allah zanyi miki kokari nima inaso ki mallaki zuciyarsa.”

Dariya tasa tana kallona jin furucin da nayi….tsaki naja cikin zuciyata nace”Dubi shashashar banza.” “Zaki iya tashi ki tafi inaso yau ki fara gudanar da aikin ki idan naga al’amura na tafiya kamar yanda nake so nayi miki alkawarin kyauta mai tsoka.” ‘ka’kalo murmishi nayi na yunkura domin mikewa nace”Godiya nake.” Hannu ta daga alamun ta amsa.
Takalma na zura hannuna ri’ke da ledar maganin nace”A tashi lafiya.” Hanya ta nuna min alamar na tafi. da sauri na bar gurin zuciyata cike da takaici.

Ina tafiya ina mamakin al’amarin gaskiya na raina wayon ta ashe duk ‘kasaitarta ta banza ce tunda gashi ta kasa janyo hankalin namiji sai ta had’a da asiri! a zahiri gimbiya Lawisa nada kyau da kyawun jiki babu namijin da ba zaiyi sha’awar ta zama mallakinsa ba, gaskiya nayi mamaki da ba tayi wa Yarima Ali ba wato yanda na fahimce shi kyau ko yawancin wasu abubuwa basa burgeshi yafi duba nagartar mutum. ajiyar zuciya na sauke tsigar jikina na tashi dana tuna irin masifaffan kallon da yake min a duk lokacin da muka had’u……. cikin ramin bulo nasa ledar magungunan na dauki wani dutse na rufe gurin da sauri na bar gurin kai tsaye gurin karatu na nufa karatu sosai akayi an gabatar da wasu darrusan bana nan haka nayi hakuri na zauna na samu abinda na samu.

‘Karfe d’aya da rabi mun fito kowa sai shiga gurinsu yake ni kuwa Lahira na bawa jakar littatafai na nace ta’aje min a gurinta, kai tsaye sashensa na nufa domin gabatar da aikina.

Samun sa nayi a falo yana d’acin rai! dan tunda na kalli fuskarsa jikina yay sanyi, gaishe shi nayi ya watsar da gaisuwa cikin ‘bacin rai yace.”Wato maganar da nayi miki bata gamsar dake ba sai da kikaje kika had’a ni da mahaifiyata ko.”?
Da sauri na sunkuyar da kaina nace”Ban fad’awa mahaifiyarka maganar da wata manufa sai dan ganin yana da kyau ta san lamarin domin ta binkici a’ina kake cin abinci.”

“Ni yaro k’arami ne da zakiyi min wannan maganar.”? girgiza kaina nayi, ‘kwafa yay da fad’in ” Tun ranar da kikayi min wannan ‘bakin abun nake ‘kyank’yamin ki da dukkanin abinda zai fito daga hannunki, kece wahalalliya kiyi ta girki kina zubarwa ba zanci ba kuma wallahi kika kuskura kika sake zuwa kika fad’a mahaifiyata wata magana sai nayi miki mugun abu.”

Na jima ina kallonsa kallon da banta’ba yi masa ba, gabad’aya mamakinsa ne ya rufe ni ashe abin arziki yana zama tsiya to wane mugun abu zaiyi mata……..”Ki wace ki bani guri kullum kina cikin tufafi d’aya sai kace jaka.”

Na sake kallonsa zuciyata sai zafi take kamar na mayar masa da martani sai dai na daurewa zuciyata da sauri na bar gurin, kicin na nufa, koda na shiga kicin din kasa aikata komai nayi na tsaya jikin drowars ina sa’ke-sa’ke! yanzu dai koda nayi masa abincin baci zaiyi ba tunda ya fad’a min to ina ganin idan nayi abincin na ajiye tamkar nayi albazazzaranci ne. wata dubara ce ta fad’o min ina ganin itace mafita a gareni.
Zama nayi kan wata kujera ta mussaman wacce aka tanade ta domin hutawa, sai da na dauki kimanin mintuna ar’ba’in kana na mi’ke na dauko tire din da nake jera masa abincin sabbi fulas na jera a kai na fita daga kicin din hannuna rike da tiren kai tsaye gurin cin abincin na nufa, na jera tsaf tamkar da abincin a ciki.

Da sauri na baro gurin nesa dashi na tsuguna nace”Yallabai na kammala.” ko kallona beyi ba ballanatana ya amsa min, miqewa nayi da fadin” A tashi lafiya” da sauri na nufi kofar fita.

Kallo ya bita dashi yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, akan idonsa ta fita daga falon, ya tsirawa fuskar wayarsa ido ta nayi masa gizonta a idonsa……Ya’ki yay da zuciyarsa ya miqe ya nufi danning din domin ganin abinda ta girka, dan yayi wa mahaifiyarsa al’kawari akan ya daina cin abincin waje sai na yarinyar tunda da ita ta amince masa, A kwanakin da suka gabata yana aika Haruna restaurant yay masa take a way da safe kuma ruwan tea kawai yake sha da biscuits…… Zama yay kan kujerar daning din a nutse ya fara kici-kicin bud’e fulas din, yana budewa yaga wayam babu komai. da sauri yasa hannunsa kan d’ayan tunkafin ya bud’e ya nuna masa da babu komai a ciki…….Cike da takaici ya daga fulas din yana duba cikinsa tamkar me neman wani abu. Lallai ashe yarinyar bata da mutunci ashe bata girka komai ba amma tazo ta jera fulas a daning sai kace wacce tayi abin arzi’ki! sosai ya shiga mamaki abunda tayi, kafin kuma al’amarin ya shiga bashi dariya.

Ya dinga dariya shi kad’ai ya mi’ke ya nufi ‘kofa da niyyar fita Haruna zai kira yazo ya samo masa abinda zaici dan yunwa yake ji.

Moddibo ne ya shigo falon a lokacin da yake daf da fita, tsayawa yay yana murmushi, shima Muddibon murmushi yay masa ya bashi hannu suka gaisa da juna.

A nutse yace.”Ina zuwa na ganka cikin manyan kaya ina Shatima yake.”? Muddibo yace.” Shatima na gurin aiki ni kuma zanje gurin bikin birthday din wani friend d’ina shine na keso muje tare ko babu komai kaga gari na lura tunda ka dawo kullum kana gida baka san zuwa ko’ina.”

Sajensa ya shafa a nutse yace.”Okey jira ni nayi wanka na kimtsa jikina dama yanzu yanzu nake tunanin kiran Haruna ya samo min abinda zanci babu damuwa yanzu idan mun fita sai mu tsaya a gurin cin abincin.” Muddibo yace.”Okey to babu damuwa muje ka kimtsa a nutse sai mu fita.” Sai suka nufi saman a tare suna maganganun da suka shafe su……
BINTA UMAR ABBALE

Please kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
37&38
Shigar ‘kananun kaya yayi a jikinsa kasancewar ana d’an busa sanyi yasa ya d’ora jacket wacce ta sauko har gwiwarsa hular sanyi yasa ya sunkufe kanshi, ya sakaye idanunsa da bakin galishi, Moddibo sai tsokanarsa yake yana kiransa da bakin bature wai idan ba wanda yayi masa farin sani ba babu wanda zai ce ya had’a jinsi da bakar fata, murmushi kawai yake bai tanka masa ba, suka sauko a tare suna hira Moddibo farin ciki fal a zuciyarsa yana addua Allah yasa bukatarsa ta biya a kansa.

Su Haruna na ganin fitowarsu suka mike suna mika gaisuwa, ya tsaya yana magana dasu shi kuma Moddibo parking area ya nufa direba ya mike tsaye da sauri ya karaso gurin, Moddibo key ya kar’ba daga hannun Direban ya bashi umarnin tafiya….a nutse ya karaso gurin yana kallon Moddibon dake zaune a cikin motar yana sa mata key yace.”Meye Amfanin direba za kayi draving da kanka.

Moddibo na murmushi yace.”Yau d’aya naji ina sha’awar tuqa mota da kaina shigo kawai mu tafi.” Jim yay na minti biyu ya kama murfin motar zai bud’e, da sauri Yakubu direba ya bude masa ya shiga ya mayar da murfin ya rufe da fadin”A sauka lafiya ranka ya dade.” Hannu kawai ya daga masa Moddibo yaja motar suka bar gurin.

Hira suke sosai a tsakaninsu Yarima Ali ya saki jikinsa da Moddibo yana ganin dan uwansa ne dake kaunarsa ba zai ta’ba cutar dashi ba, yayin dashi kuma Muddibon ke Allah Allah su isa gurin birthday din ya cimma manufarsa a kansa, Yanayin Moddibo bai nuna cuta da zalinci ba sosai ya saki fuskarsa sai fara’a yake yana nunawa d’an uwan nashi kauna da kulawa, Magajin sarki ya sake sakin jikinsa dashi yana ganin ba zai ta’ba cutar dashi ba.

Gurin birthday din ya cika da samari da ‘yan mata ‘ya’yan manya masu kudi duk wanda ya hallaci gurin birthday diin
Nura promise to d’an gayu ne kuma ubanshi mai kudi ne kuma mai mu’kami ne

Guri na mussaman aka tanadar musu suka zaune a killace Magajin sarki sai sake tamke fuskarsa yake ganin yanda idanun ‘yan mata yayi caaa a kansa, gaskiya yayi dakacan zuwa gurin a rayuwarsa ya tsani kallo mussaman daga gurin mace………..Cikin k’ayatarwa Nura ya yanka cake kafin a shiga rabon kayan ciye ciye. A nutse ta k’araso gurin da suke zaune hannunta dauke da tire da yake cike da kayan ci da sha, ajiyewa tayi kan tevur din dake gabansu ta zauna kusa da Moddibo suka gaisa tana satar kallon Yarima Ali wanda shi kuma tun zamanta a gurin yayi kici kici da fuska.

“Moddibo ganinku yayi wuya tun bayan kammala karatunmu kowa ya watse ko a waya bama gaisawa yanzu dai kafin taro ya watse inaso ka bani number wayarka.

Muddibo yace.” Wallahi kam Latifa al’amura ne sukayi yawa ina fatan kina lafiya ya mutan gida.” Da murmushi a fuskarta ta amsa kafin tace”Wannan d’an uwanka ne naga kuna yanayin kama da juna.”

Muddibo murmushi yay ya kalli gefan da yake zaune yace.”Kingdom kenan Magajin sarki kenan shi muke sa ran ya gaji sarautarmu.”

Latifa zare ido tayi tana kallonsa tace”Ashe masu ‘kasar ne a gabana Yallabai barka da wannan lokacin.” tafad’a tana kallonsa, Ba tare da ya kalleta ba ya amsa ya mayar da hankalinsa gurin Moddibo da fadin”Yana da kyau mu tafi kamar yanda na fad’a maka inaso na samu abinda zanci..

Moddibo yace.”Okey me zai hana kaci abincin gashi nan Latifa ta ajiye mana ina ganin ba sai munje restaurant ba.” tevur din ya kalla ya dauke kansa daga gurin, yana da kyankyami ba kowane abincin yake iya ci ba.

Latifa ce ta shiga bud’e mishi ledar da aka rufe abincin tana fadin “bisimillah ranka ya dad’e.” Ya sake kallon abincin a karo na biyu…Shinkafa ce akayi mata wata irin dahuwa sai kayi da gaske sannan zaka gane shinkafa ce taji kayan lambu da nama sai kamshi take daya plate din kuma gasheshshen nama ne da akayi mishi had’i da ganyayyaki sai manyan lemuka masu sanyi……A nutse yasa hannu kan cokalin ya d’ebo abincin yasa a bakinsa, yana taunawa yaji tes din abincin be masa ba daurewa yay yaci cokali uku ya ajiye tare da goge bakinsa da tissue.

Moddibo yace.”Ya naga ka ajiye cokalin.” Girgiza kansa yay yana ya mutsa fuska “Alhamdullhi wannan da naci ya isa.” Moddibo na dariya yace.”Ashe ba yunwa kake ji ba dama.” Ta’be bakinsa yayi yace.”Ina jin yunwa sosai dan rabona da wani abincin kirki tun jiya da daddare kawai tes din abincin ne beyi min ba.”
Muddibo murmushi yay a cikin zuciyarsa yace.”Ai tunda dai kaci magana ta ‘kare. A zahiri kuwa cewa yay .”Okey bari ni na gwada na gani ko zan iya ci.” Shiru yay yana kallonsa. Moddibo a maimakon yaci na plate din dake gabansa sai ya janyo sabon plate ya bude ya fara ci a nutse….Lokacin Latifa ta jima da barin gurin..Moddibo abinci yake ci yana satar kallonsa ta kasan idonsa.

Yana zaune yaji kansa na juyawa amai na taso masa, daurewa ya dinga yi yana danne aman sabida jama’ar dake gurin, Moddibo ya kalleshi hade da fadin”Ya dai dan uwa naga sai ya mutsa fuska kake.” Hannu yasa cikin Aljihu ya dauko hankici ya tsane gumin goshinsa a kasalance yace.”Wallahi kaga ina zaune kawai nake jin jiri ga wani amai na taso min.

Cikin kulawa ya ajiye cokalin hannunsa da fadin”Subahanallahi kodai abincin da kaci ne ya janyo maka hakan.” Cikin damuwa yace.Mybe shine amma nafi tunanin yunwar dana tara ce ta janyo hakan kai dai yi sauri ka gama mu tafi gida dan na soma ganin dishi dishi a cikin idanuwana.

Moddibo ya mike tsaye da sauri da fadin”Ina zan ga nutsuwar cin abinci bari na kira Nura yazo ku gaisa mu wuce kawai.” yana gama maganarsa ya kusa cikin mutane domin kiran abokin nasa.

Tare suka dawo gurin da Nura, Magajin Sarki ya danne abinda ke damunsa suka gaisa da Nura yay masa fatan alkairi sosai kana ya mi’ke gaba yay ya barsu suna magana.

Cikin mota Muddibo ya sameshi yay gaggawar bude motar ya shiga ya zauna kunnar motar yay hankalinsa a kansa yace.”Kodai mu tsaya a hospital ne dan naga kana jin jiki sosai.” Girgiza kansa yay yace.”Muje gida kawai a yanzu babu abinda nake so sai kwanciya daga baya sai a kira Family doctor ya duba ni.”
Moddibo yaja motar da fadin”To Allah ya sawwake.

“Ameeen yace yana rintse idanunsa…….sosai Muddibo ke sharara gudu kan kwalta ya kalleshi da fadin” Muddibo tafi a hankali mana.” Muddubo yace.”Ina sauri ne mu isa gida ka kwanta ka huta gabadaya Hankalina ya tashi wallahi bana k’aunar ganinka cikin damuwa.

Murmushi yay yana kallonsa yana sake jin kaunarsa a cikin ransa yace.”Nagode sosai dan uwa amma kayi tu’ki a nutse zamu kai gida da yardar Allah”

Muddibo murmushi yay yace.”Insha Allah.” Rage gudun motar yay motar ta cigaba da tafiya a nutse…..ajiyar zuciya ya sauke ya rintse idanunsa yana jin yanda wani irin mahaukacin amai yake taso masa kansa sai juyawa yake tsigar jikinsa na tashi, sake rintse idonsa yay yana kiran sunan Allah…………….”Innalilihi wa’ina ilaihi raji’un.”!!! kalmar daya ji Muddibo ya furta kenan da sauri ya bud’e idonsa da yake gani dishi-dishi dasu, gani yay motar ta ‘kwace daga hannun Muddibo sun nausa cikin bishiyu motar sai tangal-tangal takeyi tana dukan duwatsu da manya manya bishiyu. kafin yay wani yunkuri yaga Muddibo yay fittt! ya fice a motar murfin ya koma ya rufe gam!
Kansa na juyawa yana kiran sunan Allah yasa hannu kan sitiyarin motar yana kokarin tsayar da ita ai kamar kara ingizata yake motar ta sake nausawa cikin gurin, sai kawai ya shiga kalmar shahada yana ganin kamar lokacin sa ne yayi.

Muddibo mi’kewa yay da sauri ya shiga karkade jikinsa gabadaya bai damu da daddaujewar da yayi ba shi dai tunda Mota ta nausa da Ma’kiyansa cikin daji shikkenan ajiyar zuciya ya sauke yasan ko shakka ba yayi dole yau yayi kwanan barzahu……Wayarsa ya dauko cikin aljihu cikin tashin hankali ya shedawa Waziri abinda ke faruwa….

Gabad’aya masarautar hargitsewa tayi masu koke-koke nayi masu salati nayi, masoyan Yarima Ali irina mune muke cikin tsananin tashin hankali dan ni dana samu labarin al’amarin sai da na d’auki buta na zagaya band’aki(Ummu Siyama kince wai me yasa ba’a sa star din littafi tana kashi😂 to gashinan Sumayya ta zaga bayan gida cikinta ya karta lol)

‘Bangaran iyayensa kuwa gabad’aya Maimartaba rikicewa yay ya dinga salati yana neman fad’uwa, Fulani har ta fishi dauriya da tawakkali dan labarin abinda ya faru yana riskarta “Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un! ta ambata dalilin da yansa kenan ta samu kwarin gwiwar tausar mijin nata.
Gabadaya maimartaba jikinsa saki yay ya zauna kan kujera zufa na karyo masa, a yanda Muddibo ya sheda musu yanda accident din ya kasance basa tsammanin zasu sameshi da rai……..Waziri Galadima da Ciroma tare da fadawa suka shiga mota domin riskar gurin da accident din ya afku.

Fulani kuwa kad’aita kanta tayi da Ubangijinta tana kuka tana yi wa yaron nata adduar samun rahamar ubangiji dan gabad’ayansu sun fitar da rai a kansa suna ganin gawarsa kawai za’a kawo cikin gidan.

Bangaran Uwargida kuwa tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda dadi dan bayan Muddibo ya shedawa Waziri faruwar al’amarin ita ya kira ya tabbatar mata da cewa aiki yay kyau Magajin sarki sai dai wani kuma dan yana da tabbacin wannan ya she’ka barzahu.” Murna da farin ciki kamar ya kasheta. a take ta dinga kiran yaranta tana fada masu abinda ya faru, tace dukkaninsu suzo gidan suna kuka gami da nuna alhininsu amma Allah ne kadai yasan abinda ke zuciyoyinsu. aikuwa hakane ya kasance kowacce da kuka take shigowa gidan harda masu fadin” Magajin Sarki Allah ya jikanka muna murna ka dawo gida xamu zauna da kai ashe ba zaka dade tare damu ba zaka koma ga mahallincin ka, wayyo Allah mutuwa Kinyi mana yank’an kauna……Abinda wasu daga cikinsu ke fada kenan suna kuka da fyatar majina……
BINTA UMAR ABBALE

Please kuyi sharing👏🏻
[1/13, 9:47 PM] 💜: ‘KWARYA TABI ‘KWARYA
NA
BINTA UMAR ABBALE🍒 bintaumarabbale@gmail.com

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️
‘Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi


Littafin na kudi ne….!
#300…..0542382124…Binta Umar gtbank…idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin………. Ga masu bukatar VIP Group 600 ne
Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d’aya 90899076_88137740

SADAUKARWA NE
GA
HAJIYA SHAFA’ATU S YARI
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
LAST FREE PEGE🥰
wannan pege din shine ‘karshe ‘yar uwa kina so ki karanta littafi ki nishad’antu ki fad’akantu amma kuma kike ganin kyashin biyan #300 akan abinda za’ayi tsayin wata biyu ko uku ana baki kina farin ciki kina dariya, dan Allah mu dai nayi wa junanmu ganin ido wallahi rubutun nan akwai wuya meye #300 ko #600 dan kin biya marubuciya kin karanta labarinta, idan kina bukatar ki biya kudinki sai ki duba bayanai na na sama, kada ki zauna sai an sato kin ganshi a gruops ki karanta akwai ‘karanta a ciki da zubar da aji kina karanta littafin da akayi doka akai ke kanki ba zakiji dadin hakan ba #300 ko #600 ta biya miki bukata🥰 masoya na asali sai na ganku😇

39&40
Kiran sunan Allah kawai yake yana kici kici da sitiyarin motar duk a kokarinsa naganin ya tsayar da motar, inaa! motar tuni ta k’wace ita nausawa kawai take cikin sa’ko gami da kwazazzabai tana cin tuntu’be da duwarwatsu gami da manya manyan bishiyun da suke gurin, da sauri ya dauke hannunsa daga kan sitiyarin motar ya fara kici kicin bude motar lokacin wuta har ta soma tashi, motar tayi duhu da haya’ki! tari mai karfi ne ya sar’ke masa shi da sauri ya dafe kirjinsa yana salati…..Motar ce ta daki wata rusheshiyar bishiyar kuka a take ta wuntsila zata kifa cikin ikon Allah ya wuntsilo can gefe ya fad’i kansa ya bugu da wani k’aton dutsan wuta dake dashe a gurin………Kirjinsa ya rike yana janyo numfashi gami da kiran sunan Allah numfashin sa ne ya dauke jikinsa ya saki ya fadi a gurin jini duk ya wanke masa fuska da rigar jikinsa.

‘Karasowar su gurin yayi daidai da tashin wuta motar ta dinga ci da wuta wani irin haya’ki na tashi. a gigice Muddibo ya durfafi gurin yana ihu! gami da kiran sunansa “Magaji sarki?”!!! gurin sai da ya amsa sabida yanda yake wani irin ihu! yana fizgewa dole sai yaje gurin.

Waziri hawaye ya shiga sharewa yana ta ambaton Allah a cikin zuciyarsa, Galadima da Ciroma kuwa Allah ne kadai yasan abinda ke zuciyoyinsu a zahiri dai idan ka kalli fuskarsu zaka ga alamun tashin hankali da damuwa amma mugun dadi da farin ciki sukaji a cikin ransu bukatarsu ta biya wanda suka tsana ya bar duniya.

Jami’an tsaro ne suka iso gurin Tare da Shatima da labari ya sameshi yana gurin aiki kuka sosai yake yi daya iso gurin yaga yanda wuta taci ta cinye motar ko kyallin Dan uwan nasa ba’a gani Shatima shine ya kewa Magajin sarki kauna ta gaskiya shiyasa ya shiga mugun tashin hankali da ya samu labarin faruwar al’amarin..Durkushewa yayi a gurin ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa yana kuka hade da nemawa dan uwan nasa gafara.

Jami’an tsaron ne Suka durfafi gurin suna haska fitilar su, Shatima mi’kewa yay yabi bayansu shima Muddibon sai ya mike da sauri yabi bayansu, Shatima wayarsa ya kunna yana goge hawaye yana dube dube a gurin.

A tsanake jami’an tsaron suka binkita cikin motar dake tashin hayaki kad’an kad’an duk ko ina sun duba basu ga wani abu da ya dangace shi ba, misali koda wutar ta cinyeshi ai bazu rasa ganin koda agogonsa ba hakan zai tabbatar musu da zarginsu.

Babban cikinsu ya kalli Muddibo dake haske haske a gurin yace.”Bana tsammanin fa wutar ta tashi da Yarima a motar nan dan ba muga wani abu wanda zai tabbatar mana da zarginmu ba.”

Moddibo gabansa ya fad’i! da sauri yace.”Ku dai kara dubawa yanda wutar nan ta tashi bana tsammanin zata bar wani abu daya dangance shi amma ku tsananta binkice a gurin sosai.” Yana maganar yana laluben gurin gumi ne kawai ke tsiyaya a jikinsa, shima ya soma shan jinin jikinsa dan ko alama bai ga wani sashe na jikinsa a gurin ba da wuta ta ‘kona shi to da tuni sunga sassan jikinsa a wani gurin.

Binkice sosai sukayi a gurin ba suga komai ba Muddibo ya dinga share zufa yana mamakin al’amarin to ya akayi haka ta faru! ina Magajin sarki ya shiga da wuta bata ‘kone shi ba.

A sanyaye jami’an tsaro suka shedawa su Waziri abinda ke faruwa…..Waziri ya sauke ajiyar zuciya yana godewa Allah yace.”Ko shakka ba nayi jikina na bani yaron nan yana raye dan da wuta ta cinyeshi to da anga sheda saboda haka gurin dai za a tsananta dubawa watakila ko ya gangara wani gurin ne.

Galadima da Ciroma kasa magana sukayi murnarsu gabad’aya ta koma cikinsu sai muzurai suke gurin gabadaya zuciyoyinsu babu kyakkyawan abu…

Shatima cikin gurin ya dinga kutsawa yana haska wayarsa yaji yaci tuntu’be da wani abu da sauri ya Haska gurin, ganinsa a kwance a gurin yasa ya razana wayar ta fadi da sauri ya dauka ya tsuguna a gurin yana tatta’ba jikinsa jinin dake fita daga saman kansa shine ya tsorata shi, hannu ya dora a kirjinsa nan yaji yana harbawa akwai alamun rai a jikinsa, da sauri ya cire rigar jikinsa ya shiga tsane masa jinin ganin kamar wahalar da kansa yake yasa da sauri ya mike ya fita daga gurin yana waiwayensa……Kicibus sukayi da jami’an tsaron suna sake dubawa ……a sarqe yace musu kuzo gashi can bakin gangare da alama akwai sauran rai a tare dashi.” Hankali a tashe suka durfafi gurin suna godewa Allah

Yanda aka fito da Magajin sarki daga gurin zaku dauka ya dad’e da mutuwa dan gabad’aya jikinsa ya sandare ya saki wani police ne ya d’aukoshi daukar jarirai suka fito dashi …….Muddibo tun daga nesa da ya hangosu jinin jikinsa ya tsinke jiki na kyarma ya iskesu yana haska fuskar sa da wayar hannunsa baki na rawa ya kalli Shatima yace.”A ina aka ganshi anya ma kuwa da akwai rai a jikinsa.”!? a kid’ime yake maganar kana ganinsa zaka gane a cikin rud’u yake. Shatima yace.”Can karkashin wani k’aton dutse na ganshi a sume goshinsa na zubar da jini akwai alamar rai a tare dashi.”
Muddibo hular kansa ya cire cikin tsantsar tashin hankali ya shiga firfita da ita. Shatima ya shiga mamaki mai tsanani ganin yanda Muddibon ya rud’e sai fadi yake .”Wannan da alama ya jima da mutuwa Shatima duba fa ka gani yanda jikinsa ya sandare…..Dansandan dake dauke da Magajin sarkin a hannunsa yace.”Akwai rai a jikinsa kawai taimakon gaggawa za’ayi masa.” Muddibo shuru yay da bakinsa dan baya so ya sake wata maganar su zarge shi da wani abun.

Kai tsaye babban asibiti suka nufa dashi, Waziri da Shatima ne kawai ke masa fatan samun lafiya Ciroma da Muddibo Galadima fatan mutuwa kawai suke masa………Kai tsaye emagancy aka nufa dashi manya manya likitoci suka rufu a kansa domin ceto ransa…….Waziri ne ya umarci Shatima ya sanarwa da Maimartaba halin da ake ciki, koda Maimartaba ya samu labarin cewa yaronsa na raye sujjada yayi a gurin ya godewa Allah, a lokacin ya shirya tafiya asibitin domin duba yaron nasa, Fulani kuwa kawaici ta nuna ta zauna a gida tana addua gami da godewa Allah, Bangaran Uwargida kuwa da suka samu labarin abinda ke da akwai sai murnarsu ta koma ciki suka dinga ‘kunci suna zage zage da kyar suka iya danne ‘bacin ransu suka shiga mota suka nufi asibitin suna shirya wata mana’kisar.

Ni kaina dana samu labarin cewar yana raye bai mutu ba sai da nayi sallah raka biyu na godewa Allah sannan kafin na tashi sai da nayi masa addua da fatan samun lafiya ingantacciya.

Sai bayan kwana biyu Ya farfado yasan wanda yake kansa babu wanda ya fara kira sai Muddibo hawaye suka sakko masa a kumatu. Maimartaba yace maza aje a kira Muddibo yazo ya ganshi yana daina zargin ya mutu….Muddibo na shigowa dakin ya sauke ajiyar zuciya, tsirawa juna ido sukayi, kawai sai Muddibo ya fashe da kuka tare da riqe hannunsa yace.”Sannu Yarima ashe tsautsayi da qaddara ne ya fitar damu naji dadi da Allah ya taikaita mana wahala ina kuma rokon Allah ya tsaremu da sharrin karfe.” Kamar wani mutumin arziki yakare maganar.

Rintse hannun Muddibon yayi a cikin nasa yana so yayi magana amma bakinsa yayi masa nauyi wani irin sarawa kansa yake ga wata irin ishirwa na damunsa da kyar ya iya furta maganar dake bakinsa. “Bani ruwa.” Muddibo yayi saurin daukar goran ruwa dake kan drowar ya bude masa zai sa masa a baki ya kar’ba ya sha da kansa, kadan ya rage ya mika masa goran ruwan kana ya shiga bin dakin da kallo. iyayensa ya gani ya tsaitsaye sai yaji zuciyarsa ta karye, ya kamo hannun Waziri ya rike da kyau yace.”Baba ku kwantar da hankalinku insha Allah zan samu lafiya.”

Waziri ya tsira masa ido babu abinda ke tayar masa da hankali sai kat’on bandejin dake nad’e a kansa gabadaya hallitar fuskarsa ta sauya ko’ina a kumbure dalilin daya sa ma kenan Maimartaba ya kasa tsayuwa a dakin ganin hallitun yaron nasa sun sauya yasa ya fita daga dakin hankali a tashe.

Kwana biyar da faruwar al’amarin na samu su Haruna domin mu tattauna yana da kyau muje asibitin mu duba jikinsa dan gabad’aya tunda al’amarin ya faru na rasa gane kaina kullum da damuwa nake kwana ina ganin kamar idan na wayi gari za’a zo a fadi mutuwarsa.

Haruna yace.”Shawara tayi sai mu bari da daddare bayan munyi sallar isha’i sai muje muga yanayin jikin nasa.” Nace”To shikkenan tare ma zamuje da babana shima yana so ya duba shi.” Haruna yace.” To babu damuwa.

Ina k’okarin shiga ‘kofar dawakai Jakadiyar Fulani ta dakatar dani, gaisawa mukayi da juna kafin ta isar da sak’on ta, nace”Fulani na nema na.” Karyar da kaina nayi nace”Dan Allah ta tsaya na zubawa dawakai abinci sai mu tafi tare.”
Da yake tana da saukin kai tace” Muje na taya ki.”

Tare muka shiga gurin, Hira muke sama-sama nake tambayar ta yanayin jikin Yariman sabida nasan ita ba zata rasa sanin abinda ke zuwa ya dawo ba, tace”Jikinsa da sauki wallahi kullum ana ganin cigaba amma zamansa a asibitin nan akwai hadari dan kullum ‘yan uwansa mata cikin zurga zurga suke wai sunje dubashi gabadaya babu tsoron Allah a ransu zasu iya cutar dashi saboda irin kiyayyar da suke masa.

Cikin mamaki nake kallonta nace”Yan uwansa na jini su cutar dashi me yayi musu mai zafi wai shin ma nawa duniyar take.” ? Jakadiya tayi murmushi mai ciwo tace”Yarinya ni nasan abinda baki sani ba a masarautar nan babu wanda ke kaunar dan uwansa dukkaninsu kisan mummu’ke sukewa junansu kowa na samun dama akan dan uwansa cutarsa zaiyi wannan al’amarin ma da ya faru da Yarima muna zargin dasa hannun ma’kiya kin san gabad’aya kowa ya daura masa kiyayya da kyashi da hassada saboda suna ganin kamar shine zai gaji kujerar mahaifinsa.

Na jima ina mamakin maganar kafin na girgiza kaina nace”Jakadiya mutane idan suna wani abu wallahi har mamaki suke bani mutum fa bai ta’ba tsarawa kansa abinda yake so ba face wanda Allah ya tsara masa nasan ba’a kan komai suke wannan abunba akan mulki ne a ganina sai su bari suga abinda Allah zai zartar ba wai su dinga cutar dashi ba watakila ma bashi ne zai hau kujerar ba wani ne babu fa wanda ya san gaibu sai Allah.”

Muna kokarin fita daga gurin Jakadiya tace”Ke da kika san Allah kenan amma su ina mai tabbatar miki da cewar basu san Allah ba, dan da sun sanshi ba zasu dinga aikata munanan ayyuka ba.” Ajiyar zuciya na sauke nace”Allah ya kyauta Allah kuma shiryemu baki d’aya.” Ta amsa Ameeen ya Allah.”

Cikin nutsuwa na gaisheta tare dayi mata jaje akan abinda ya faru. Amsawa tayi kafin ta gyara zamanta tana kallona tare da kiran sunana.
Na amsa ina kallonta, tace”Ina fata baki mance akinki ba ko.”? Nace.”Eh ranki ya dad’e.” Tace.”To Alhamdullhi ina so kije asibiti ki zauna da babana ki cigaba da kula dashi kamar yanda kike kula dashi a gida.” Nace”Dama yau muka yanke shawarar zuwa duba shi nida su Haruna” Tace”To babu damuwa suma suna iya zama asibitin ku hadu ku kula dashi har randa za’a sallamoshi ya dawo gida, alhmdullhi kullum jikin nasa ‘kara sauki yake.
Shuru nayi ina tunani maganarta tace”Nasan kina tunanin gurin kwanciya ko.”? nace”Eh ranki ya dade.” Tace”Kada ki damu babban asibiti ne akwai dakunan da zaku kwanta ku sake babu damuwa ki tafi da ‘yan kayan sawarki bana tsammanin ma zakuyi sati daya da zuwa ba’a bashi sallama ba tunda jikin nasa ya soma warwarewa.” ajiyar zuciya na sauke da fadin”To babu damuwa ranki ya dade bari naje na shirya kayana.” Ta amsa min da to shikkenan. Har na kai kofa ta dakatar dani juyowa nayi ina kallonta tace”Ki kula da kyau ba kowane irin abinci zaki bari yaci ba.” ko ba tayi min bayani ba na gane inda ta dosa sannan kafin shigowata gurinta mun tattauna maganar da Jakadiyarta.

Lokacin da zamu tafi asibitin iyayena fatan alkairi sukayi min, na sake jin kwarin gwiwa ganin yanda babana yake kuzari jinin jikinsa ya dawo yanzu bashi da matsalar komai yana fita yayi sabgoginsa hankalinsa a kwance to wannan dalilin yasa naji bana fargabar tafiya asibitin.

Lokacin da muka shiga dakin yana zaune kan gado da tufa (apple) a hannunsa yana ci Gimbiya Lawisa na gefansa suna magana kan kujera kuma daya daga cikin yayyunsa ne wacce bata dade da zuwa ba, ta kawo masa abinci cikin kwando wai lallai sai yaci a gabanta sannan zata tafi.

A nutse nabi su daya bayan daya na gaishe su sannam muka karasa gadon da yake zaune….Haruna ne ya fara magana “Ranka ya dade barka da dare ya jiki munayi maka fatan alkairi ubangiji Allah ya tsare gabanka da bayanka.” A nutse ya amsa fuskarsa tana nuna alamun yaji dadi da zuwan mu Isa da Hamza suka gaishe shi dayi masa ya jiki nima a nutse na mika gaisuwata ya amsa cikin sakin fuska harda godiya.”
Fita mukayi daga dakin muka zauna a reception muna hira….Kimanin minti ashirin da zaman mu a gurin suka fito daga dakin. Aunty Sakina gaba tayi ita kuma Lawisa tsayawa tayi a kaina tana kallona tace”Ina fata kina gudanar da aikin dana saki.”?
Nace”Sosai kuwa ranki ya dad’e kullum ina yi har nake tunanin tambayarki ko kinga sauyi sai da na ganku a tare ke dashi kuna hira na tabbatar da cewa maganin yana aiki.”

Murmushi tayi tace”Har yanzu na kasa gane inda ya dosa akan soyayyata Ali mugun baud’addan mutum ne wanda ba’a gane gabansa da bayansa, amma tunda muna da zafafan malamai nasan zasuyi min maganinsa.” Nace”Kwarai kuwa ranki ya dade.” Tace” Ki cigaba da gudanar da aikin ki bance ki d’aga kafa ba wai dan ganin bashi da lafiya karki saurara a cikin ko wane yanayi burina aikin da nake a kansa yayi tasiri.” Nace”Kada ki damu ranki ya dade tafe nake da sinadaran da kika bani ko yanzu ya shirya cin abinci zanyi dubarar zuba masa.
Murmushi tayi tare da fadin” Na fada miki idan aiki yay kyau zanyi miki kyauta ta mussaman saboda haka sai ki sake zage damtse.” Ina murmushi nace “Nayi alkawari.” Tana tafiyar takama ta bar Gurin, tsaki naja ‘kasa-kasa nace”Dube ta dan Allah jahilar banza da wofi.

Su Haruna na gani sun mike sun nufi dakin, ido na zubawa kofar ina sauraran fitowarsu basu dade a ciki ba suka fito Hamza ya kalleni da fad’in ”Ki shiga ki bashi abinci yana bukata.” Mik’ewa nayi da sauri na nufi dakin

Yana zaune a inda yake ganin shigowata yasa ya fara yunkurin sauka kasa. da sauri na janye kwandon abincin dake gaban gadon ya zuro kafafunsa a nutse ya mike tsaye bayansa nabi da kallo ganin ya nufi toilet yasa na sauke ajiyar zuciya.

Ina tsaye a gurin ya fito muka hada ido, kaina na sunkuyar kasa ina jin faduwar gaba kada’n kad’an, idan na kalli fuskarsa sai naji zuciyata na karyewa nima yanzu na tabbatar da cewa yana da makiya gaba da baya dalilin daya sa kenan naji zan iya sadaukar da rayuwata a kansa tausayi yake bani.

K’asan kafet ya zauna ba tare daya kalleni ba yace.”Ki zuba min abinci nasha magani na kwanta bacci nakeji.” Nace”to ranka ya dad’e.” Kwandon abincin dake gabana na janyo na fara kokarin fito da fulas din dake ciki……Yace.”Kada ki bude wannan dauko wancan na aunty Sakina shine nake bukata dan nayi mata al’kawarin cin abincinta.”
A nutse na mayar da fulas din hannuna na janye kwandon gefe na dauko wanda ya bukata.

Cikin nutsuwa na fito da komai na kwandon na dauki plate mai dan zurfi na bude fulas din dake dauke da abincin. pride rice ce a ciki taji kayan lambu da nama amma kuma qamshin da take yasha bambam dana lafiyayyan abinci….Tsirawa cikin fulas din ido nayi ina duba abincin ciki. nan na hango taratsatsin magani a ciki dan wani gefan ma har ya rine da kalar maganin, kallonsa nayi gabana na fad’uwa yanzu ya za’ayi na fad’a masa abinda ke da akwai.

Kallona yayi yana yamutsa fuska yace.”Zaman me kike ne ke nake jira fa.” murya na rawa nace”Ranka ya dade abincin ya lalace.” Wani irin kallo ya watsa min da fadin”Kamar yaya ya lalace.”? Nace”Eh duba ka gani wallahi ya lalace gashinan kamshin sa ya sanja.”

Tsaki yaja tare da fadin”Kinga bana son wata magana ki zuba min abinci naci koda tsutsa ke fita a cikinsa to tunda nayi alkawari sai na cika.” shuru nayi ina sake sake a raina.

“Wai ba zakiyi aikin dana saki ba.” Cikin tsawa yay maganar…….Cikin jin tsoro nace”Wallahi abincin bashi da kyau ba zaka ci ba.” Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta, a fusace! yasa hannu zai Dauki fulas din abincin nayi gaggawar daukewa. bayana nasa fulas din ina kallonsa kwallah ta cika kwarmin idona.

A murtuke yace.”Ina wasa dake ko.”? girgiza kaina nayi ina nufin aa. Yace.”To zuba min abinci bani da lafiya bana son hayaniya.” Hannu nasa na dauke kwallar data taru a idona nace”Sai dai na zuba maka wancan dan wannan da kake so kaci bashi da kyau.” Yace.”Wai cikin ki ko nawa ? ina ruwan ki idan naci lalataccan abinci cikina ne ba naki ba sannan nayi wa ‘yar uwata al’kawari zanci abinda ta kawo min.”

Nace”Kayi hakuri ba zan iya baka kaci abinda zai cutar da kai ba dan kai amana ne a hannuna.” Kallona yayi yana mamakin maganata, yace.” Wai Saboda me bakya son naci abincin aunty Sakina ne.”? bakina ne ya su’buce da fad’in “Saboda akwai guba a ciki.”
Gani nayi ya murtuke fuskarsa “me kike nufi? kina nufin anty Sakina zata cutar dani kome.”? kai tsaye na daga kaina ” Zata iya cutar da kai tun ba…….! kafin na karasa ya wanka min mari a kumatuna. cikin gigita nake kallonsa bakina na wani irin rawa so nake na fadi karshen maganar amma na kasa sakamakon marin daya waska min. kallon banzan da yake min yasa nayi gaggawar yin kasa da kaina.
BINTA UMAR ABBALE

LAST FREE PEGE
Kada ki sake ayi wannan tafiyar babu ke ‘Yar uwa kada ki saka ganin kyashi a kan abinda kike so ki kauda kanki ki biya #300 ki karanta littafin nan hankali kwance……..Vip gruop#600 Normal gruop#300 idan kati zaki turo #400 ne.

PAID BOOK
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
BABBAN YARO
MASHAHURI
SADAUKI OMAR
LADIDI KWADAGA
TSANTSAR BUTULCI
DA WATA A KASA
NIDA YAYA SADAM
YAR BANGAR SIYASA
MADADI

Kai tsaye zaki iya samun wa’innan littafan idan kin tuntu’bi wannan numbers
08089965176
07084653262
BINTA UMAR ABBALE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *