KWASAR GANIMA CHAPTER 7 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
NA fito daga gida na cikin tashin hankali saboda halin da diya taMairo ta shiga na jinya. A bakin Titin IBB mu ka yi kicibis da wani
tanKwararren tsoho. Ya kalle ni da tausayi, ya ce, “Baiwar Allah, da ganin ki ki na cikin tashin hankali, amman babu mamaki saboda maKiya na kewaye da ke. Zan ba ki wani garin magani ki yi tirare, za ki sha mamakin makiyan ki da za su bayyana.”
Ban musa zancen sa ba, domin da ma na jima ina zargin Habi facala ta da sanya hannu a ciwon Mairo, ganin ta na da farin jini. Don haka na ce, “Kai amma na ji dadi, Malam! Yanzu haka abin da ya fito da ni kenan. Me zan ba ka, Malam?”
Ya gyara tsayuwa, ya ce, “Ba zan amshi kudin ki ba, sai dai ki ba da sadaka kawai a yi gumba a hada da magani a yi sadaka. Hakan ne zai sanya aikin ya yikyau.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Na zaro dubu daya na ba shi ina godiya. Nan da nan na juya gida don buKata ta biya.
Amma tabbas yau Habi ta shiga uku, don sai na sanya auren ta ya mutu na huta da jarabar saka ta a ido na.
* Bayan na dawo gida na yi wa Mairo turaren, na kulle ta a daki. Na dawo na zauna ina jiyo ta tana ta ihu da tari har ta fara sambatu.
Habi ta ce mani, “Yaya, kamar kukan Mairo na ke ji ko?”
Ban kula ta ba, na koma dakin na tarar da Mairo ta na buge-buge, tana fadin, “Wayyo Habi ki sake ni! Wayyo Habi za ta kashe ni! Ta je gurin wani boka ya ba ta asiri ita da babar ta sun binne a bayan tukuba. Ki taimake ni ki cire, Habi!”
A gigice na fito. ;
Na nufi gurin Habi da ke wanke-wanke, na taKarKare na zabga mata mari™ ina tsuma.
Ta daga kai a rude ta ce, “Me na yi miki ki ka mare ni, Yaya?” Www.bankinhausanovels.com.ng
A zucciye, na ce, “Au, tambaya ta ki ke yi? To yau dubun ki ta cika, ga Mairo can ta tada aljanu ta fadi duk abin da ku ka mata ke da uwar ki. Don haka tun mu na mu biyu ki je ki tsallaka ta sannan ki tono layun da ku ka binne.”
Da mamaki, Habi ta ce, “Yaya, sai ka ce wata mayya za ki ce na tsallaka Mariya? Ai tuni aka sanar da ke ciwon ta shafar jinnu ne…” Www.bankinhausanovels.com.ng
Marin da na Kara zabga mata ya sa ta yin shiru da Kara dafe kunci. Da ya ke ni irin masu girma ce kamar Kirar Samudawa ya sanya na finciko ta ina fadin, “Kur’ani sai kin tsallaka ta!”
Ahaka mu ka Karasa har cikin dakin. Habi na tirjewa, nace, “Tsallaka ta!”
Habi ta ce, “Sai dai ki kashe ni, amman ni ba mayya ba ba za a sanya ni tsallaka mutum ba!”
Ganin za ta bata mini lokaci ya sanya na fara shirgar ta. Ta na ihu ta na ba ita ba ce wallahi, ni kuma ina fadin, “Sai kin tsallaka ta!”
Ihun da ta ke yi ne ya janyo hankalin maKota, su ka shigo daidai lokacin da Habi ta suma, jini ta baki ta hanci.
Gaba daya su ka dauki salati. Ni kuwa har lokacin ban hakura ba. Su na rike ni, ina cewa su sake ni.
Aka kwashi Habi da ran ta ke hannun Allah aka yi asibiti. Sai da aka Kara mata ledar ruwa uku ban da dinkin ciwuka da ta sha. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da miji na ya ji abin da ya faru ya fashe da kuka, ya ce ba ruwan sa. Mijin ta kam cewa ya yi ba zai yarda ba. Su kuwa ‘yan’uwan ta, da yake masu hali ne, da ’yan sanda su ka zo. Ganin ’yan sanda ya sanya na fara shiga hayyaci na, na fara zare ido. Haka su ka tasa ni a gaba. Ina sanar da su halin da diya ta ke ciki, amma ba su saurare ni ba. Su ka sanya ni a sel su ka dinga duka na, wai kafin Habi ta farfado. Ina ihu ina sanar da su abin aljanun Habi su ka fada. Sai su ka Kara duka na su na fadin, “Aljanu ko? Za ki yi bayani!”
Da Habi ta farka, ta sanar da ’yan’uwan ta dalilin dukan. Su ka ce sai sun shigar da Kara. A nan ido na ya Kara raina fata, don ba ni da wani gata sai na baban su Mairo wanda ofishin ’yan sandan ma da Kyar ya zo. Sai ga ni ina kuka ina fadin, “Sharrin jinnu ne da dan tsoho.”
Da Kyar su ka yarda aka yi mana sulhu a ofishin alKali. Amma dai na sha wuya har da su targade.
Neman Aiki OKACIN
da na auri miji na ya kammala digirin sa, amma aiki ya &j samuwa Sai dai kame-kame. Daga Karshe dai na sayar da kayan daki na, na ba shi kudin ya sayi babur don yin aca6a, sauran kudin ya samo mini gurbin karatu a Makarantar Kimiyyar Lafiya.
Musa shi ke kai ni makaranta a kullum ya dauko ni, har na kammala karatun. Ganin bangaren lafiya na karanta ya sanya na fara aiki na wucin gadi a wani Karamin asibiti, ana ba ni dubu uku alawus. Wannan kudin su na taimakon mu matuKa, don mu kan auni masara da shinkafa. Ga shi har aikin cutar shan inna na ke tabawa. Saboda dan babur din namu ya tsufa, kusan da wannan aikin mu ke ci da sha.
Rannan mu na cikin aiki sai ga shugaban Sashen Kiwon Lafiya na Karamar hukuma ya kawo ziyara asibitin da na ke. Aka dinga yi masa Www.bankinhausanovels.com.ng
jawabin kowa har aka zo kai na. Ya Kura mini ido cike da mamaki. Ya ce, “Ke yanzu ba ki da ofa amman ba kya zagayawa sakateriya ko kya dace? Ai zaman ba zai haifar da da mai ido ba. Ki dinga zagawa. Ai duk macen da ba ta sami ofa ba ita ta so.”
Jin wannan jawabin ya sanya rannan na shirya na sanar da Musa, na tafi sakateriya. Shugaba ya na gani na ya kama washe baki.
“A’a, madam ce da kan ta? Zauna mana.”
Na sami wuri na zauna, a zuciya ta ina jinjina kyautatawar sa. Ya gyara zama, ya na cewa, “Ai mace mai kyau irin ki ko aike ta yo a ba ta ofa. Abin da dai nake so dake ki amince da soyayya ta, za ki samu ofa cikin sauKi.”
Mamaki ya cika ni don na tabbata ko goyon yaron da ke baya na ya isa ya nuna auren da ke kai na, amma dai gara in Kara tunasar da shi. Na ce, “°Yallabai ina da aure fa.”
Ya yi wata shashashar dariya, ya ce, “Aina sani. Ni ai na fi son mu’amula da masu aure. Ba ni hadin kan riba ce. Idan ki ka bijire kuma har aikin wucin gadin zan kore ki.” Ya dora da cewa: “Za6i ya rage naki. Idan kin amince sai ki tad da ni gidan shaKatawa ta gobe, idan kuma ba haka ba daga jibi na kore ki saia koma kasa gyada kuma.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Har na koma gida hankali na a tashe ya ke. Maigida na duk ya rude yana tambaya ta abin da ke damu na don ya na matuKar so na. Sai na fashe da kuka, don ba zan iya gaya masa ba saboda kishin sa zai iya sanyawa zuciyar sata buga. Da ya matsa da tambaya sai na ce, “‘Ina son zan bar aiki ne!”
Sai ya rude, ya gigice, idon sa ya ciko da Kwalla.
“Ki taimake mu, Nafi, ki janye wannan batu,” inji shi. “Ko kin manta da dimbin taimakon da aikin ke mana? Idan kin bari me za mu ci? Ki yi
h akuri ?
Ya dinga lallashi na da magiya. Tausayin sa ya hana ni rintsawa. K wana na yi ina saKawa da kwancewa.
Ko hakura zan yi na yarda?
ok Har gari ya waye ban rintsa ba, ina ta neman mafita wurin Allah. Har sati ya wuce ina zuwa aiki na lafiya. Sai na yi tunanin ko ya Kyale ni.
Kwatsam, ranar Litinin ina zuwa aiki aka ba ni takardar sallama. Hankali na ya tashi. Abokan aiki na har da masu kuka. Ashe tashin hankali da Musa zai shiga sai ya fi wannan, domin ina nuna masa ya fashe da kuka ya na fadin: ““Nafi, ba ki yarda da abin da na ce ba kenan! Maimakon ki bari ki amshi albashin wannan watan da saura sati ya Kare ma! Ki na gani babur din ma ya lalace; ko a gyare ya ke ma mutane ba sa hawa saboda Karar sa da ratattakewar da ya yi, ga shi nawa aikin ya Ki samuwa, ba ni da kudii balle
nace zan yi kasuwanci. Amman babu komai, na fara dako…!”
Ido na ya ciko da Kwalla. Da ya san dalilin barin aiki na da ya fi kowa muma. Amma na daure na ce, “Ta yaya zan bar aiki ban sami wani ba? Kora *‘ ce aka yi saboda siyasa. Ka san na fi kowa son aikin nan. Amma ka yi hakuri.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ganin na fara kuka ya sanya ya koma lallashi na.
Tun daga wannan lokaci komai ya Kara kwabe mana domin abin da za mu cima gagarar mu ya ke yi.
Wai sai ga mutumin nan ya turo mai sharar asibitin da saKon cewa wai idan na amince har yanzu bai hakura ba.
Darajar dan aiken ce ta fara zubewa. Ban ce masa komai ba, na koma
gida. Wahala ta yi wahala, har ta kai mu na kwana haka ba mu ci ba. Rannan
maigida na ya zo mini da magana mai dadi, domin an ce Ciyaman shi ne kankat gwurin ba da ofa, ga shi direban sa maKocin mu ne. Shi ya yi mana jagora da asuba don a sannan ake samun Ciyaman. Sa’ilin da mu ka je Kofar gidan mun tarar da shi danKam da jama’a. Da yake ni mace ce na sami shiga gidan na bar Musa da direba a waje.
A dakin amarya ake ganin mutane. San da na shiga amarya ta na gefe, ta ¢j kwalliya. Shugaban Karamar Hukumar ya yi mini albishir mai dadi, ya ce kada in damu, aiki na samu na gama. Ya amshi lambar waya ta da ta maigidan, Sai a sannan rai na ya fara sanyi.
Har mu ka je gida mu na sanya masa albarka. Da yamma ina zaune a tsakar gida ina ta addu’ar Allah ya sa Musa ya samo mana ko da na gari da siga ne,
‘yar tsohuwar waya ta baKuwar lamba na gani. Na daga da sallama na ce, “Waye?”
Sai na ji ance, “Ni ne Ciyaman. Na bugo ne na miki ban-gajiya. Kun je gida lafiya?”
Da sanyin jiki na ce, “Lafiya lau, ran ka ya dade.”
Ya dinga soki-burutsun sa har ya gama ban fahimci komai ba. A daren nan da Kyar na rintsa, ga tunanin wayar Ciyaman ga kuma yunwa, don ba mu ci komai ba, don ma na yaye yarinya ta tana gidan mu.
Washegari da yamma, ya Kara kira na, na dauka jiki na ya na rawa, ya na wata shashashar dariya ya ce, “Kin san Nutsuwa Hotel? To ki same ni a can da takardun ki zan rubuta miki ofar.”
Nace, “Ban sani ba, amma bari maigidan ya dawo sai yarako ni…”
Ya katse ni da sauri: “Wane maigida? Ai sam kada ki gaya masa ma, sai dai ya gan ki da takardar ki.”
Ni dai dana samu ya kashe sai na kashe wayar gaba Www.bankinhausanovels.com.ng daya.
Tun daga wannan ranar ya ke damu na da waya. Abin duniya ya ishe ni. Ga shi Musa ya dora duk burin sa a kan samun aikin nan nawa. Da abin ya ishe ni, saboda saKon da yake aiko mini na yabon sura ta, sai na tauna layin na watsar.
Lokacin da aka kafe takardar daukar ma’aikata Musa ya tafi da Kwarin gwiwar sa, amma sai bai ga sun na ba. Ya dawo gida hankalin sa a tashe. Ya kama ni da fada don direban ya ce Ciyaman ya ce laifi na ne don ya ce na kai wa amaryar sa takardu na har sau uku na Ki kaiwa. Ta inda ya shiga ba ta nan
ya ke fita ba, har ya tunzura ni ni mana hau. Na mike a fusace na ce, “Wai kai
ka san abin da ke hana ni samun aiki ne?”
oe Na tuno da halin da Musa ya taba shiga lokacin da mu ka haua mota wani ya matso kusa da ni ya rotsa wa mutumin kai, sai a ofishin ’yan sanda ya kwana. Na kuma san yanzu ma zai iya zuwa ya rotsa wa Ciyaman kai, ga shi ba mu da na abinci ma balle na beli. Hakan ya sanya nace, “An ce dole sai ka na da babban dan siyasa, kuma ka san matsayin direba ba wani ba ne.” Na kwantar da kai na dinga lallashin sa har ya hakura. A satin mu ka ji gwamnatin jiha na sanarwar za a fara daukar ma’aikata har da masu matakin digiri. Nan da nan mu ka daga dan gadon mu, mu ka sayar. Da ma shi kadai ya rage a dakin. Mu ka sayi fom da kudin ni da shi. Duk wata jarabawa da intabiyu mun halarta. Ranar da aka kafe sunaye, Musa yajeya © duba. Ya iso gida ya na murna da godiya ga Allah. Da ya sanar da ni suna na ya fito, na fara tambayar sa, “Kai kuma fa?” Yace, “Ba suna na, amma ai mun gode Allah da sunan ki ya fito ke din.” Bayan sati guda aka yi kiran mu don mu amshi takardun kama aiki. Ina shiga ofishin jami’in da ke rabawa ya zuba mini ido ya na murmushi. Gaba na ya fara faduwa, na gaishe shi. Ya laluba wasu takardu har ya zo kan tawa, ya zaro ta ya ce, “Ga takardar ki kin samu aiki saboda ni, domin ni na dage a saka ki Www.bankinhausanovels.com.ng Tun a gurin intabiyu na ga kin kwanta a rai na. Ina fatan za ki ba ni tukwici?” Gaba na ya na faduwa, na ce, “Sai dai idan na fara daukar albashin, amman yanzu ba ni da komai…” Dariyar da ya sanya ce ta katse ni, na tsaya ina kallon sa. Ya ce, “Ai ba kudi za ki ba ni ba. Ki ba ni hadin kai kawai, don yanda ki ke da kyau ba kowane namiji zai iya kau da kai daga gare ki ba.” Arannan na Kara tsanar kyau na, don shi ke ja mini komai. Na fara yi masa nasiha da roKon sa, amma mutumin ya Ki yarda. Daga Karshe ya ce, “Idan kin Ki yarda, ki je kawai. Da ma daga cikin mutum dubu hamsin na tsamo ki. Ki je, ba ki darabon arziki ne a duniya.” Na fashe da kuka ina saKawa da kwancewa. Tabbas wannan ce damar da tarage mini ta Karshe. Shin idan na bijire me zan ce da Musa? Ganin na yi shiru ya sanya ya yi zaton na amince. Ya taso ya nufo ni, ya kamo hannu na. Wani irin tsoron Allah ya shige ni. Ta yaya zan yarda in rasa
Jahira a kan duniya? Gara kawai in gaya wa Musa abin da duk ya faru da in sabi Allah. Wannan tunanin ya ba ni Karfin gwiwar zabga wa mutumin nan mari da daya hannu na.
Ya sake ni a gigice, ya tsaya yana kallo nacike da mamaki.
Cikin kuka nace, “Gara in rasa komai da in rasa imani na, Allah ya na sane da ni!” Ina kaiwa nan na juya da sauri na fice ina kuka. Www.bankinhausanovels.com.ng
Na durKusa a Kofar ofis din ina ta kuka. Daga saman kai na na jiyo ana magana, na daga kai na a rude don na san Musa ne. Sai dai sabanin haka wani mutum na gani mai cike da kamala.
Ya ce, “Nafisa, lafiya ki ke kuka? Kin amso ofar taki?”
Na tsaya ina kallon sa da mamakin inda ya san ni.
Sai ya ce, “Ai ni ne Shugaban Ma’aikata na jahar nan, kuma abokin marigayi Kanin babar ki. Nina sanya aka sa sunan ki.
Sai na kuma fashewa da kuka.
Da ya dame ni da tambaya sai na sanar da shi abin da ya faru a ofis din da ya fito. Sai na ga gaba daya hankalin sa ya tashi. A fusace, ya ce in bi shi ofis din.
Ganin mu da wannan shugaba ya tada hankalin mai raba takardun kam aikin. Ai kuwa ta inda shugaba ya shiga ba ta nan ya ke fita ba. Ya yi masa kacakaca har da alKawarin kora daga aiki bayan ya tona masa asiri. Sai jami’ in nan ya durkusa ya na ba ni haKuri da kukan sa.
Shugaba ya dauko mini takarda ta.
Na dinga godiya da hamdala ga Allah. Www.bankinhausanovels.com.ng
A waje, inda aka sake kafe kashi na biyu na sababbin ma’aikata sai na hango Musa ya na ta tsalle. Da alama ya ga sunan sa. Ya na hango ni ya tafia sukwane ya riKe ni ya na sanar da ni shi ma ga sunan sa, kuma da matakin digirin sa.
Wannan shi ne ya mayar da rayuwar mu ta farin ciki. Mun mallaki duk wani abin more rayuwa, amma har lokacin ban taba gaya wa Musa halin da na shiga ba. Na sanya a rai na duk wanda ya tsare dokokin Allah, to zai isar masa.