KYAUTAR KODA COMPLETE BY NOOR

LAGOS*
Victoria island

“RSVP restaurant” shine sunan dak’e rubuce baro baro a had’add’en restaurant di’n, duk da k’asancewa babban wuri ne, amma talaka kan iya zuwa suma su kashe d’aid’ai aljihun su.

Yammanci ne da misali karfe biyar, mai cike da ni’ima da sanyin d’ad’i daga rabbul samawwati, wata K’yak’yyawar matashiyar buɗurwa ce mai k’imanin shekaru22 zaune kan d’aya daga cikin kujerun wajen, fara ce sosai, mai zagayayyen fuska, mai dauk’e da dogon hancin, fararen oily eyes, da karamin baki, tana da cikar gira haka zalika gashi idanunta masu yalwa ne, bata da jiki ko kadan domin kai tsaye za’a kira ta da siririya, saidai structure din jikinta mai kyau da tsari ne….

A hankali take sipping smoothie din dake gaban ta, yayinda hankalin ta gaba daya ke kan tsadaddiyar wayar hannunta kirar iphone 3G Kings button Wanda kudin shi zai kai $2.5 million, ba ma wayar ƙaɗai ba, komai na jikinta daga sama har zuwa kasa tsad’add’en ne….

Dan bata fuska tayi ganin kusan rabin awa tana zaune amma har yanzu Mr Daniel Paul, bai karaso ba wanda ya k’asance business partner dinsu, kuma sun yi kan cewa anan zasu hadu domin su tattauna wata muhimmiyar magana wanda na cigaban companies din su ne….
Number mr Daniel ta kira yana daga wa ta fara yi masa magana kan rashin zuwan sa da wuri….

Yayinda wani k’yak’yawan saurayi daya bata baya ya yi saurin juyowa jin wata zazzak’ar muryar tamk’ar busar sarewa, take zuciyar sa ta bugu domin ta, kana wani mugun sonta ya tsoki kirjin sa a lokaci daya, zai iya rantsuwa bai taba ganin mai dadin murya hadi da kyawun fuska kamar wanna matashiyar ba, take ya zaro wani babban cardboard paper irin na masu zanen mutum wato (artist)daga cikin katuwar jakar sa ta goyo, cikin kwarewa yake zana wanna matashiyar budurwa idanun sa kafe kan fuskar ta, a ransa yana d’ad’a yaba sihirtaccen kyawunta, yayin da cute bakin ta dake magana ya fi komai tafiya da shi…

D’aidai loƙacin daya gama zanen, wani waiter or nace ma’aikacin restaurant din yazo wujewa, ciƙin muryan sa mai sanyi yace “hey! can you please give this to that young lady over there”
Ya fada yana nuna d’aidai inda budurwar ke zaune.

“yes! Sure” waiter’n ya fada yana amsar cardboard paper d’in daga hannun sa, hannu wanna saurayin ya bashi suƙa yi musabaha ƙana ya furta “Thanks” murmushi waiter yayi kawai yana barin wajen…

D’aidai inda taƙe zaune waiter ya nufa, cikin girmamawa yace “ma’am waccen saurayi yace na baki wanna” ya fada yana nuna sautin inda saurayin ke zaune, dago idanunta tayi ta bi inda ya nuna da k’allo, Sai dai wayam babu wanna saurayin babu alamar sa….

Dan zaro ido waiter nan yayi yana mamakin ta yaya ya bar wajen ba tare da ya ko lura ba, cikin dan rudewa yace “sorry please, yana zaune yanzu nan, kafin na karaso, shi yace na kawo miki”…. Ya fada still cikin girmamawa…

Murmushi ta saki wanda ya loɓar da wani dimple daƙe tsaƙiyar habar ta
“okay no problem” tace tana karban cardboard paper’n a hannun shi, shi ma waiter din murmushi yayi ya bar wajen yana yaba kirkin ta a ransa…

A hankali ta fara warware takardan cardboard paper’n tana tunanin ko waye wanna? Wani zaro ido tayi cikin zallan mamaki, ganin tamkar photo copy dinta ne a jikin paper’n “who is he?” ta fada tana kallon zanen, wani mugun kyau zanen yayi mata , rungume paper’n tayi domin zanen ya burgeta matuk’ar burgewa…

Take ta k’wadaitu da son ganin wanda ya iya zane ta tsaf haka, babu ko digon k’usk’ure, tana cikin wanna zurfin tunanin ne mr Daniel Paul ya karaso hadi da bata uzurin abun da ya rikeshi, “babu damuwa” ta ce kawai suka tattauna abinda ya kawo su duk da rabi da rabin hankalin ta baya wajen…


Ɓayan sun yi sallama da Mr Paul ta fito daga cikin wajen, sosai tafiyar ta ke da daukar hanƙali, duk da bata da kiba amma jikinta har wani girgizan ɓirgewa yake daya yi matukar amsar ta ainun, za a iya tunanin da gangan take yin hak’an, Sai dai sam ba haka bane, halittar ta ce a hak’an…
wasu motoci ne ke fake Masu kyau da tsari har guda shida jera reras, motar dake tsak’iyan sauran motocin shidan ta nufa, wanda ya k’asance kirar Ferrari Monza red color, take wani bodyguard dinta mai sanye cikin suit baki kamar yanda sauran suma kalar shigar su kenan, yayinda wani bak’in glass ke manne kan fuskar ko wannensu, sam babu alamun fara’a a fuskar su, hannu ya mika domin karban cardboard paper’n hannun ta, daga masa hannu tayi alamun ya barshi, take ya bata hanya cikin girmamawa, wani daga cikin bodyguard dinta ne ya bud’e mata motar ta shige kana cikin k’warewa suka bawa motocin wuta….

A nutse suke tafiya kan shimfud’ad’iyyar kwalta reras gwanin sha’awa, yayinda wasu mutanen ki bin had’add’u kuma tsad’add’un motocin da kallo…. yayinda budurwar nan take kallon titi ta cikin glass din motar, amma a zahiri ba kallon motocin dake ta wucewa a kan titi take ba, tunani mai zurfi take, tana tunanin waye wanna daya iya zana fusk’ar ta haka tsaf, abin ya kasa barin zuciyar ta da ma k’wak’walwar ta….

★ Unguwar ikoyi suka nufa, unguwa ne masu hannu da shuni domin babu gidan marasa hali a unguwar, domin talaka bazai iya siyan ko hayan muhalli a unguwar ba.

Babban estate din motoci ke ta shiga, duk yanda baki zai kwantata estate din abin zai faskara, sai dai wanda ya ganewa idanun sa kawai. Domin girman estate din zai iya yin girman wani karamin unguwa, Had’add’en gine ne tamk’ar a turai, domin a turan ma ba ko ina bane za’a samu irin wanna estate din…

Bayan sun gama d’aidaita parking motocin kana dukkanin su suka fito, daya daga ciki ya buɗe mata mota cikin girmamawa,… har kofar da zai sada ta da bangaren mahaifiyar ta suka rakota kana suka juya cikin girmamawa suka koma.

Shigar ta cikin had’add’en falon, yayi d’aidai da tahowar wata K’yak’yyawar mata da zata yi shekaru arba’in da biyar a duniya, wanda idan ka ganta zaka dauka cewa bata fi shekaru talatin da biyar ba saboda kyawun jikinta, tana matsakaicin jiki, yayinda take da tsayi babu laifi, kallo daya zaka yiwa matar ka hango jindadi, Hutu, hadi da kwanciyar hankali a tare da ita.

Murmushi matar ta sakar mata kana tace “welcome back sweetheart, ya gajiya?”

Martani murmushi ta mayar wa matar kana tace “Thank you Mommah na” hadi da bata kisses a kumatun ta biyun.

Riko ta matar ta yi tamk’ar wata yarinya karama ta zaunar da ita kan daya daga Cikin had’add’un royal chair kana tace “bari na zuba miki juice ki sha” murmushi kawai tayi tana bin Mommah’n ta da kallo, bayan Mommah ta dawo ta zauna ta sanya mata juice din a baki bata wani sha da yawa ba ta janye bak’inta, “sweetheart!” Mummy ta kira ta, dago kanta tayi ta kafe su kan Mommah ba tare da ta amsa ba.

Cikin serious tune tace “fadeelah meye damuwar ki, you re not looking okay?”

Budurwar nan mai suna fadeelah tace “ba komai Mommah, ina son hutawa ne kawai” ta fad’a tana sakar wa Mommah murmushin k’arfin hali.

Ita ma Mommah murmushin tayi ta riko hannunta, har part dinta ta rakata sai da ta tabbatar ta kwanta kana ta fito, tana ganin fitar Mommah ta sake bud’e cardboard paper’n nan, take zanen ya bayyana, kurawa zanen hoton ido tayi, tunani masu yawa na zuwar mata, ta gyara kwanciyar yafi sau ba adadi, domin babban burinta a yanzu ta ga waye wanna daya iya zane fusk’ar ta tar tar babu ko mistake, ta duba ta ga ko akwai sunan sa ko number’n sa a kasan zanen kamar yadda masu zanen kan saka, amma babu…

*** *** *** ***

Kwance matashin nan mai zane yake kan cinyar wata mata mai kimanin shekaru hamsin a duniya, sosai take da k’yau domin bazaka yi tunanin ita ce mahaifiyar wanna saurayin ba, saboda bambamcin kalar fatar su, domin baki ne shi irin black beauty din nan yayinda matar ta k’asance fara sosai duk da cewa kalar fatar ta ta dan dishashe sak’amak’on halin babu da suke fama dashi, domin kallo daya zaka yiwa gidan ka tabbatar da hak’an…

“Fadeel my son, lafiyar ka kuwa tun jiya na kasa gane kanka, na kuma tambayeka kace babu komai, shin kana da kowa a duniyar nan da zaka iya raba damuwar ka da shi baya ga ni ummin ka?”
Ta tambayeshi cikin tsananin kulawa yayind’a hannun ke kan gashin sa tana shafawa har yanzu.

Cikin son mahaifiyar sa yace “Mahmah… na fada soyaayyar wata yarinyar” ya karasa yana sauk’e numfashin idanu sa a lumshe yana tuno kyakyyawar fusk’ar ta, murmushin ta, tsarin jikinta da ma dukkanin wani abu daya dangance ta.

“Oohh ya rabb! Fadeel da gaske kake? Yau da kanka kace kana son wata? Gaya min ka sanar da ita? A wani unguwa take?” Mahmah ta yi masa tambayar cikin zallan farinciki da zumudi.

“Ooh Mahmah relax, shiyasa bana son baki labari sometimes fa” ya karasa yana murmushi.

“Bazaka gane ba son, tun yaushe nake cewa ka samo budurwar ka ki, yau kuma ka sanar dani kace bazan yi farinciki ba?” sai k’uma yanayin ta ya sauya a take
Cikin damuwa yace

“lafiya Mahmah?”

Hawaye ne suka ciko idanun ta tace “ina son ganin kayi aure ka tara zuri’a, inason ganin jikokina daga tsatson ka, kai kadai na haifa, kuma ina alfahari da kai, domin daya kake tamkar da dubu, damuwa ta shine idan ma auren ya taso ina muka ga kudin da za a yi hidimomin biki? Ni da kai mun sani cewa kullum cikin babu muke sai godiyar Allah”

Jikinsa ne yayi sanyi d’omin baya kaunar ganin Mahmah cikin damuwa sam, da yana da iko daya cire wanna damuwar, sai dai babu yanda zai yi, ƙaddarar su ce hakan, cikin sanyin muryar sa yace “Mahmah wanna dalilin ne yasa na kasa kowa miki suruka d’omin bazan iya tukarar kowacce mace a haka ta saurare ni ba, d’omin yawancin yanmmatan yanzu are after Money not Love, sannan ita wanna yarinyar ban ma san sunan ta ba, balle gidan”….

DOWNLOAD COMPLETE BELOW ⬇️