LABARIN RAYUWATA CHAPTER 1 BY Ayeshay bee

 LABARIN RAYUWATA CHAPTER 1 BY Ayeshay bee

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kaduna, Nigeria.+

Hadari ne ya mamaye garin gabadaya, daidai lokacin aka fara wani iska Mai karfi kafin kace kabo garin yayi bakikirin alamun ruwa Mai karfi na dab da saukowa. Dole ya sa motocin da ke kan titi su ka fara driving a hankali saboda da kyar su ke ganin gaban su.

Agogon hannun shi ya duba sannan yayi concentrating akan driving in da yake da kyar ma ya ke iya ganin gaban shi.

Roundabout in Oando ya bi ya shiga constitution Road, kaman ance daga kanka ya hango wata budurwa na kokarin tsallaka express in ko duba gaban ta ba tayi kaman ma hankalin ta ba ya jikin ta. Motan da ke gaban shi ma da budurwar ta shigawa gaba gudu yake sosai kaman zai tashi sama kafin ya ankara yaji wani irin kara daya sa shi yin parking ba shiri. Sai hango wanna budurwar yayi tayi sama sannan ta fado akan glass in moton ji kake tas tas glass in motan ya dagar gaje rolling budurwar ta Kara yi sannan ta kife akan kwalta daidai lokacin ruwa Mai karfi ya sauko kam da bakin kwarya, salati ya ke a fili ci ke da shock in abinda ya faru right a gaban shi.

Ko kafin ya je har mutane sun fara taruwa suna wa Wanda ke cikin motan masifa ganin ba a fito ba, Tinted glass ne hakan ya sa ba a gane Wanda ke ciki ba.Ganin karfin ruwan ya na karuwa ya sa dayawa daga cikin mutanen su ka ja baya sai sannan ya samu ganin budurwar da gabadaya jini ya gama bata Mata jiki. Tsaki ya ja da karfi hade da girgiza Kai “ko miye amfanin rufe ta da suka yi suna Kallon ta?” Ya tambayi kanshi. In ma ba karya idanuwan shi su ka mishi ba to tabbas ya hango masu kokarin daukan incident in a waya, girgiza Kai yayi Yana fadin “Allah ya shirya Mana wannan zamani namu” a kasan zuciyan shi.

Sai sannan Wanda ke cikin motan ta samu fitowa abin mamaki Mace itama da ba zata wuce 25 Years ba hade da danta a hannu, Yaron sai kuka ya ke ba ta bi ta kanshi ba Saboda ita ma kanta jikin ta rawa ya ke kaman za ta fadi kasa.

Cinciban yarinyar yayi ya bude bayan motan shi ya sa ta sannan yayi wa motan key, Wanda ke wurin su kayi yo kanshi suna tambayan Ina za shi da ita? Ko Kallon su Bai yi ba ya sa wa motan key ganin haka ya sa su kayi baya.

Komawa motan Matan ta yi ita ma ta bi bayan shi da sauri.

Unguwan rimi ya nufa direct ya dau hanyan nursing home, Barau  dikko yayi parking. Yana isowa nurses su ka fiddo yarinyar su ka daura ta kan gado Emergency aka tura ta zuwa cikin asibitin da sauri.

Da sauri ya bi su cikin asibitin ita ma Matan saurin binshi tayi rike da danta a hannu sai a sannan ya juya ya kalle ta gabadaya ta rude tafiya kawai ta ke ba wai hankalin ta na jikin ta bane.

Wayanta ne ya fara ruri tayi saurin dauka. “Lfy har yanzu ba ki Kara so ba?” A ka fada daga dayan bangaren

Ba ta San lokacin da ta saki kuka ba Jin muryar shi “Lfy me ke faruwa” ya fada a rude.

“Ka zo Barau Dikko ” kawai ta fada sannan ta yi ending call in.

Accident and Emergency room aka nufa da ita da sauri ya je ya canja kayan surgery su ka shiga operation room tare da wasu Yan uwan shi doctors da nurses. Cike da kwarewa su ka fara aikin nasu.

Ta ka sa zaune ta kasa tsaye sai kai wa da kawo wa ta ke zuwa yanzu har yaron nata ya fara kuka. Bayan Yan mintuna Wanda su ka yi wayan ya karaso a rude “Mimi na lafiya me ya faru?” Ya tmby ganin yanda ta rude gabadaya.

Habawa tana ganin shi ta saki kuka Mai karfi “accident nayi na buge wata” ta fada cikin sheshekar kuka “Subhanallah yanzu Ina ta ke?”

“An shiga da ita operation”

“Okay calm down Allah zai rufa asiri and please ki daina kukan nan Kinga dai asibiti mu ke ga jama’a” ya karasa tare da amsan dan da ke hannun ta wanda har ya gaji da kukan ya fara bacin wahala.

Lallashin ta ya dinga yi har sai da ya samu ta yi shiru sai ko ajiyan zuciya da yi karewa, hannun ta ya riko ya na cigaba da bata baki.

Sunfi 3 hours suna jira dole sai da aka Mata dressing hannun ta coz hannun na Kan sitiyari Lokacin da budurwar ta fado glass in ya fashe ya zube Mata a hannu, Dan nata ne ba abinda ya same shi saboda yana Kan kujeran Mai zaman banza a baby suit in shi. Sai gab da magreeb aka fito da ita daga dakin tiyatan aka tura ta zuwa wani dakin na daban.

Suna kokarin Mikewa su bita domin gano halin da ta ke ciki, Dr in da ya kawo ta asibitin ya fito, ganin shi ya sa Namijin tsayawa domin samun bayani daga wurin shi. shi ma dai Kai tsaye wurin su ya nufo, Harara ya fara Kai wa Maryam sannan ya juya ya ba mijin ta hannu.

Zai fara magana likitan ya dakatar dashi “Sorry sir, mu je muyi Sallah please ko”

Ba musu ya bishi bayan ya ce wa matar shi ” ta kwantar da hankalin ta pls kafin su dawo”

Har sun fara tafiya likitan ya juyo “Ki samu Nurses in can su baki ruwan Sallah” ya fadi Kai tsaye ya Mata pointing wasu nurses biyu kafin su ka wuce Masallacin.

Yanayin gari na ruwan sama ya sa a kayi walda a Masallacin. Dalilin da ya sa Maryam ta ga dadewan su kenan duk ta kagu.

Akan hanyar su na dawo wa daga Masallacin Likitan ya farawa Mustapha (Mijin Maryam) bayani “Abokina am sorry to say but your wife is at fault even though ita ma yarinyar da laifin ta Amma ko dan darajan ruwan saman da ke kokarin saukowa a lokacin ya kamata ace ta rage speed inta” shiru Mustapha ya mishi har sai da ya Kai aya sannan.

“Then its my fault not hers, dawo wa na kenan daga tafiya ita Kuma tana school, ba ta son bari na a gida nikadai shiyasa ta ke speeding sosai haka. We accept that is our fault so we are sorry please, ya condition in yarinyar”

Murmushi likitan yayi, yanda Mustapha ke kokarin kare matar shi ya matukar burge shi “let just hope she could make it” Dr Fahad ya fada yana shrugging shoulders in shi sannan ya cigaba “Kanta ya bugu sosai so sai anyi scanning a duba ko da wani matsala sannan Kuma ta samu karaya a kafa da hannu da Kuma karamin Dan yatsan ta na hannu sai Kuma raunuka da taji externally”

Shiru Mustapha yayi gabadaya jikin shi yayi sanyi da kyar ya iya furta.

“Allah ya kara tsarewa, Yanzu ya ake ciki kenan?”

Dan Jim Likitan yayi yana Kallon Mustapha “anyi treating in abinda zai yiwu yanzu the rest sai a hankali she is still unconcious, so an sa mata oxygen. Karayan sai ta farfado za ayi treating in shi. Zuwa gobe dai in sha Allahu za a duba komai”

“To shikenan Allah ya kaimu”

“Ameen” ya amsa

A reception su ka tadda Maryam na jiran su, ta na hango su ta taso. Likitan shigewa yayi ya bar su suna tattaunawa.

Sai can su ka shiga cikin asibitin, a haraba su ka samu likitan fitowan shknn daga dakin patient inta su. “Sorry please Dr za mu iya ganin ta” Mustapha ya bukata.

Kallon su yayi “Of no use, har yanzu ba ta tashi Kuma she will take a while but Bismillah” ya karasa zancen da murda handle in dakin, a tare su ka shiga gabadaya.

Ganin ta a kwance kaman ba ta motsi ya matukar tadawa Maryam hankali, she is feeling guilty sosai, she can’t believe she cause it all.

“Yanzun za a samu Mai kwana da ita ko?”

“No need, Nurses inmu na nan in case inta tashi cikin dare, You can leave now”

“Thank you Dr, may i know your name?”

“Fahad”

“Nice meeting you Dr Fahad” ya fada yana smiling.

Shi ma Dr Fahad in murmushin shi ya mishi “see you tomorrow, am kinda busy now”

“Okay”

Cikin dare ta farka a firgice, jikinta gabadaya rawa da kyar ta samu ta bude idanunta, dakin ta fara bi da kallo a hankali, kaman Kuma wacce ta tuno wani Abu tayi saurin rintsa idon, wani irin uban Kara ta saki tana girgiza kanta.

Ihun na ta ne ya jo hankalin Nurses in da su ke da night duty a lokacin, da sauri mutum uku su ka nufi wurin ta ganin irin warning inda Dr Fahad ya musu kafin ya bar asibitin zuwa gidan shi da ke kusa da asibitin.

Samun ta su kayi tana Fisge Fisge har tayi nasarar cire drip in da ke hannun da ya karye ta jini sai zuba ya ke, kokarin controlling inta su ka shiga yi Amma Ina nema ta ke ta fi karfin su, cikin dabara sister Nabeela ta samu ta Mata alluran bacci sannan jikin ta ya sake su ka samu su ka gyara Mata drip in da ke hannun ta da Kuma kwanciyar ta. Sun so Kiran Dr Fuhad, Nabeela ce ta Hana a cewar ta shi ma ya gaji dayawa, why not a bari sai da safe in ya shigo ya ganta.

Washegari, karfe 8:30 dai dai ta mishi a haraban asibitin, yayi parking kenan ya hango Mustapha ya fito daga motan rike da Dan shi a kafadan sa, Maryam ko tana tsaye a bayan shi.

Hango shin da suka yi ne yasa su ka jire har sai da ya karaso, hannu ya mikawa Mustapha su ka gaisa Maryam Kuma ta gaishe shi, a hankali ya amsa sannan su ka nufi cikin asibitin.

Direct dakin da aka yi admitting inta su ka nufa. Nurses biyu su ka tarar zaune a daki suna hira.

“Good morning Dr” ta fada tana murmushi.

Shi ma murmushin ya maida Mata “morning sister Nabeela, na same ku lfy?”

Amsawa tayi ita ko sister Rufaida tabe baki tayi sannan ta gaida Dr kaman an sa ta dole, Sannan su ka gaisa da su Maryam.

“Ya patient in?” Sister Nabeela yayi ma directing question, shi ma kaman yadda Rufaida ba ta cika son mishi magana ba shi ma bai shiga harkan ta duk da ko ba a asibitin su ka fara sanin juna ba.

“Ta farka cikin dare tana ihu, tayi ta Fisge Fisge har ta cire drip in hannun ta sai da muka Mata alluran bacci’

Shiru yayi alamun tunani kafin can yayi magana “Ya Salam! But meye sa ba ku kira ni ba?”

“Dr Wai Naga kayi aiki ka gaji ne shine nace a bari sai yau kawai tunda za ka shigo da wuri”

“You should have called me Nabeela” ya fadi Yana Kara duban bugun zuciyan ta da sauri ya maida Mata oxygen in da su ka cire ganin numfashin ta na son ya fara seizing. Wasu dube dube ya kara yi.

Wasu zafaffan hawaye ya fara fitowa daga idon Maryam ganin halin da patient in ke ciki har yanzu,  she can’t believe she cause it. Gabadaya jiya kasa rintsawa tayi tana tunani, Mustapha ne ya fara kwantar ma ta da hankali.

Juyawa Dr Fahad yayi ya kalli Mustapha “sorry Dan Allah, akwai abinda Zan Dan yi yanzu sannan zan dan duba patients in da na yi bedridden, I will be back soon”

“Ba matsala” Mustapha ya amsa.

Hankali Rufaida gabadaya ya koma Kan Babyn da ke hannun Maryam, ita haka Allah yayi ta da son yara sosai, burin ta kullum ta ga danta.

Mika mishi hannu ta yi tana smiling, ba musu Yaron ya tafi wurin ta da alamun bai da kiwuya ko bai Kai ya fara kiwiyan ba ne?

“Ya sunan shi?” Ta tambaya

“Haidar” Maryam ta amsa da kyar.

“Wow! Ki ce baba nane, Ma Sha Allah he is cute”

Murmushi karfin hali Maryam tayi saboda yanda Rufaida ta yi complementing Dan ta in a nice way “Thank you” ta fada a hankali.

Nan fa Nabeela ita ma ta fara kokarin amsan Dan, sai da ko su kayi drama da Rufaida saboda da kyar ta yadda ta ba ta shi for some minutes.

“Watan shi nawa?” Nabeela ke tambayan.

“Four months” Maryam ta amsa

“Ma Sha Allah ya na da sauri girma Amma dai gsky”

Da wasa da wasa Hira ya kaure tsakanin Matan ukun, Nurses in na kokarin kwantar mata da hankali suna tabbatar Mata patient za ta tashi domin ko sun Sha samun case in da ya fi haka Kuma su farka sai dai in kwana ya kare. ganin haka ya sa Mustapha ya Mike “Mimi na ga kin samu abokan Hira ba ra na dan leka gidan Anty, jiya da na Kira ta Anisa ta dauka Wai ta kwanta kanta na ciwo”

“To shikenan, ka gaishe ta Pls Zan ma Kira ta”

“Ehmmm sai na dawo”

“Allah ya kiyaye hanya”

“Ameen” ya fadi kafin ya rufo musu kofan dakin.

A kofan gidan yayi parking motan shi sanin ba dadewa zai yi ba sannan ya kutsa Kai cikin gida. Su na Jin Sallaman shi su ka taso da gudu gudu suna “oyoyo ga Uncle” daya bayan daya ya daga su sama, su uku ne Amma kallo Daya xa ka yi wa mazan guda biyu ka gane twins ne sai karamar kanwar su da su ke kama, gabadayan su suna cikin uniform in makarantar Bosede prestige da ke kagoro “Good morning uncle” muhibba ta fada hankalin ta na Kan littafin ta, tabe baki yayi Yana fadin “na ki gaisuwan muhibba ko kallo na ba ayi” da sauri ta Mike tana fadin “sorry uncle, Assignment gare ni in ban yi ba Uncle Victor xai Zane ni”

“Me ya hana ki yi tun jiya? By the way ya baku tafi school ba its already late”

“Uncle its raining Kuma Anty Anisa ma tace teachers inmu ma duk ba su Zo ba” Kulsoom yar 5 years ke bayanin Nan.

Ai ko lokacin Anisa ta fito jiyo muryan Kulsoom na kokarin yi Mata sharri “Kulsoom ke na fada wa haka? Ba momy na ke fadawa ba?” Hararan ta Mustapha yayi “ke Kika ja misu latti ko?”

“No Uncle musty Allah bahaka bane, tun safe ake ruwa Kuma ba su fito ba Ka ga driver ma Bai zo ba. Ina kwana, ya baby haidar? Ya hanya Kuma?”

“Lafiya, Ina Yayanku ne shi ba sai ya Kai ku ba”

“Bacci ya ke yi”

“I will wake him up Ina momy?”

“Typing ta ke a system

“Tell her na zo bara in tada Faroukh ya Kai ku school”

Dakin Faroukh in ya nufa ya ko same shi Yana ta faman minshari “Faroukh! Faroukh!” Ya Kira sunan shi Amma shiru bai farka, bayi ya shigo ya debo ruwa no second thought direct ya watsa mishi Kan fuska, a firgice ya tashi “Anisa wasa da ke ne?”

“Ba Anisa bace bude ido ka ga waye” ba ma sai ya bude idon ba muryar kawai ya ji ya gane Uncle in nasu ke magana.

“Kai Uncle musty” ya fada Yana turo baki can Kuma ya gaishe shi.

“Tashi ka Kai kannen ka schl”

“Uncle mustyyy driver in su bai Zo bane?”

Harara ya bishi dashi “da ya Zo ya na nufin zan tashe ka kena..” Bai jira ya ida zance ba ya tashi da azama, jallabiyan shi da yayi hanging kawai ya dauko ya zira sannan su ka fita dakin.

Ashraf da Arif ne su ka fara rugawa motan sannan sauran su ka bisu bayan an yi ma Mommy da Uncle bye bye.

“Ina kwana Anty” Mustapha ke gaida Antyn ta shi bayan tafiyan yaran.

“Lfy lil”

“Kai Anty da Dana da Mata na Amma ba za ki daina ce min lil ba?”

“You will always be my little brother Musty”

“Ya Kan naki Anisa ta ce min ba ki Jin Dadi Yesterday”

“Wlh Stress, ka San sha’anin business sai a slow”

“Ki dai dinga hutawa Anty, Daman na Kira in fada Miki ne, Mimi got involved in an accident”

Da sauri ta zaro idanu “shine ba ku fada min ba? Tun yaushe? Yanzu Ina ita mimin?”

“Calm down Anty, Ba abinda ya same ta, wata dai ta kade she is still unconscious, ta samu karaye dai abin ma duk ba dadin Jin”

“Oh my God, Ba ga irin ta ba, Fisabillahi Yaushe Mimi za ta daina rough driving…

“Anty ba fa haka bane, na dawo ita Kuma ta je schl sai ta biya wurin kawarta so ba ta dawo da wuri ba har na iso shiyasa ta ke sauri ta dawo gida da wuri, she don’t want to leave me stranded”

Tabe baki Anty tayi “ai daman Kai ba ka taba ganin laifin Mimi shiyasa ta ke komai ta ga dama, wannan wani irin soyayya ne komai mutum yayi daidai ne ba a gyara, Da baban Faroukh Zan hada ku duka biyun, bara na dauko Hijab mu tafi asibitin”

Shiru yayi kawai ba wai Dan ya yarda da abubuwan da Antyn ke fada Kan Matan shi ba, For God sake shi ko kadan bai ganin aibun Maryam.

Sai da ta Kira mijin nata ta sanar dashi sannan su ka tafi bayan ya sanar Mata zasu hadu a asibitin.

Ko da su ka isa har Baban faruk in ya iso Yana jiran su a harabar a asibitin.

Su na shiga dakin da gudu Mimi ta fada jikin baban Faroukh in ta wani irin kuka mai taba zuciya “Subhanallah haba Maryama kaman ba ki San kaddara ba calm down mana” da kyar ya lallashe ta ta fara sakin ajiyan zuciya sai a sannan ta gaida Anty da gabadaya ita ma hankalin ta ya tashi ganin situation in patient in.

Shiru ne ya ratsa dakin kowa da abinda ya ka ayyanawa a zuciyan sa, ajiyan zuciyan Maryam kawai ke tashi kafin Fahad ya shigo dakin.

Sai da su ka gaisa da mutanen dakin kafin ya nufi gun patient in ya na duba yanda ta ke numfashi zuwa yanzu. Drip in hannun ta ya kalla ya ga ya kare.

“Faidah Zo ki cire Mata” sai da ya fada sannan ya yi realizing abinda yayi, me ye sa ya Mata magana? Gashi Kuma sunan da ya Kira ta yayi showing ya Santa personally, cije baki yayi alamun bai so hakan ba.

Ita ma Rufaidan banza ta yi dashi, hakan ba karamin tunzura shi yayi ba “Ku Zo ku cire mata Mana!” A tsawace yayi magana jikin Rufaida na rawa ta yi saurin zuwa ta zare ma ta drip in, ita dai Nabeela har yanzu mamaki ta ke don’t sanin da ta yiwa kawar ta Rufaida ta san a gidan su ne kawai ake ce Mata Faidah.

“Ina ganin za mu kaita scanning room yanzu a duba brain in,  Ya ka mata ace ta farafado gsky”

“Any news about her family?” Engr Usman alkali yayi maganan ya na Kallon dactan.

Girgiza kai Dr Fahad yayi “ba abinda mu ka samu ba komai a hannu ta lokacin da incident in ya faru”

“Then dole ayi contacting police station ayi cigaye a gidajen TV da Radio.”

Hakan ko ya faru Dr Fahad da su Nabeela su ka tafi da ita daki Scanning. Engr da Mustapha Kuma su ka wuce police station yin report, Maryam Kam da kyar ta hakura ta bi Anty gidan ta ba dan ta so ba, a cewarta a barta ta jira in ita ma dole sai da Engr ya sa baki daman in ta murde in ba shi ya sa baki ba to fa baza ta yi ba har gwara ma Anty tana shakkan ta Mustapha ko Daman duk abinda ta ke so to fa shima shi ne farin cikin shi.

Kaman yanda likitan ke zata kan nata ya tabu sosai,  dole sai an mata surgery a gun. Nan da nan aka yi contacting Neurosurgeon. Kan ta ko dole sai da aka Mata aski gabadaya ga gashin ta Mai yawa cika da tsawo duka Allah ya wadata ta dasu, Anyway ta lafiyan ta ake for now.

An shigar da Report, Jaridai, Gidan TV da Radio ba inda ba a dauki hoton an sanar ba Amma shiru kake ji ba Wanda ya fito ya nuna ya Santa, hakan ya sa suka fara doubting Anya Cikin Kaduna ma ta ke kuwa?

Kwana biyu gabadaya ba ta Kara ko motsi tun bayan Wanda tayi daren ranar da aka kawo ta a asibitin, ta ko wani bangare kokarin kulawa da ita ta ke duk da tana cikin halin da ita ba duniya ba ba Kuma lahira ba.

Maryam ko ba karamin rama tayi ba a kwana biyun nan duk ta bi ta susuce ba ta da kuzari, Islamiyyan da ta ke zuwa ma dainawa tayi kullum cikin zulumi da tunani hakan ko ba karamin shafan Haidar yayi ba shi ma in har wani raman yayi saboda rashin kula kullum Yana hannu Mai aikin su. Har Gida Anty ta same ta ta musu tas daga ita har Mustaphan da ya ke biye mata sannan fa aka dan samu sauki, shi Kan shi Mustaphan yaji dadin zuwan Anty yasa ta rage abubuwa da dama.Hankalin Dr Fahad bai kwanta ba sai da ya amsa sakon Dr Usman,  babban Neurologist a jahar Lagos. Haka ma a cikin asibitin ya tsaya kai da kafa domin ganin komai ya zama ready ta yanda likitan na iso wa za a hau aikin. Response patient in nashi kam har yanzu ba a magana.+

Dashi a ka shiga Surgery in yayi assisting. Daki daki haka Dr Usman ke aikin shi a tsanake har ya cima burin abinda ke gaban shi. Wani ajiyan zuciya Dr Fahad ya saki lokacin da Dr Usman ya mishi alaman they are done. He hate losing his patient,  a duk lokacin da abun ya zo da karar kwana ya kan tsinci kanshi cikin tashin hankali. Amma ya za ayi in lokaci yayi? Ba makawa tabbas sai an tafi. Kokarin kulle ta su ka fara. Engr da Mustapha ya ma bayanin yanda aikin ya kasance, Yanayin fuskokin su kadai ya isa tabbatar ma farin cikin da su ke ciki. Balle kuwa Maryam da ta ke ganin itace sillah, da Baban Haidar ya bata lbr har hawaye sai da tayi. Alhmdlh aiki yayi kyau sai kuma jiran farfadowan ta,  nan fa duk su ka dukufa wurin addu’a.

Dr Fahad Jin Suhaima ya ke tamkar wata jinin shi shiyasa bai kyashi Mata komai although su Mustapha na Mata komai but shi in dai ya tsaya akan ta tare da taimakon Nabeela da Rufaida of course.

                Some hours later

A hankali ta fara motsi da idanuwan ta tana kokarin bude su duk da matsanancin zafin da su ke mata haka ta daure tana ta kyaftawa har sai da ta yi nasarar bude idon kadan a haka tana bude tana kullewa har ta bude su gabadaya duk da hasken da ta ke jin ya ma idon yawa bai sa ta kulle ba. Wani irin ta ke Jin jikin ta kaman ba nata ba ga kanta ya mata wani irin nauyi da ba ma zata iya daga shi ba. Mata biyun da ta gani zaune a daki ta kafawa ido tana son tuno anya ta San su kuwa?

Dai dai lokacin Sister Rufaida da Nabeela zaune a dakin suna kallon wani Indian series mai suna Sehr Alasmar a tashar Bollywood da yake da yamma ne around 6:00 pm. Rufaida ce ta fara Jin alamun kaman ana kallon ta da sauri ta juya aiko four eyes su kayi da patient in ta zuba mata idanu ko kyaftawa ba tayi.

Tashi tayi ta nufi wurin ta tana Mata smiling “Sannu ko, are you alright?” Murmushin ta yi kokarin mai da mata ita ma a hankali can kason makoshin ta ta ke kokarin furta “ruwa ruwa” sai a sannan Nabeela ta juyo tana kallon su cike da mamaki. “Wow!! Yaushe ta farka? Let me call Doctor” da sauri ta fita dakin cike da zumudi. Rufaida ko matsawa tayi sosai domin ta ji abinda ta ke kokarin furtawa “Ruwa” ta ji tana furtawa a can kasan makoshi.

“Bara a samo miki” Rufaida ta amsa ba wai dan zata kawo ma ta in ba. Ta san cewa ba ruwa bane abinda ya kamata a fara ba ta bayan ta farka. Kokarin Mikewa patient in ta fara yi amma Kuma ta kasa sai ma wani azababben ciwon da taji bayan nayi.

Fahimtar hakan da Dr Fahad yayi ne ya sa yayi kokarin yi wa Rufaida magana “Faidah help her Mana” cije baki yayi cike da takaici, he can’t believe he is the one messing things not her saurin basarwa yayi gudun ta fahimce takaicin da ya shiga “sa mata pillow ki daga ta she can’t do it” ita Rufaida ba ta ma san ya shigo ba don haka obeying abinda ya ce tayi.

Hannun ta Kan shi nauyi ya ke Mata da kyar ta yi kokarin daga shi sai rawa ya ke ganin haka ya sa Rufaida kwantar mata da hannu duka biyu. Dayan ma kam ta kasa dagawa saboda karayan da ke hannun. Ita dai Nabeela tana baya tana Kallon su, a zuciyan ta tana ayyana yau za ta tmby Rufaida ina ta San Dr Fahad Banda Asibiti coz she can’t take it anymore.

“Sannu Koh” Dr Fahad ke maganan Yana Kallon patient, daga kanta kawai tayi “me kike ji Yana Miki ciwo” ya bukata. Jikinta ta bi da kallo sai a Lokacin ta ankare da bandages in da ke kafan ta da Kuma hannun ta, hannun da ba bandage in ta daga da kyar ta shafa goshin ta nan ma ta Kara Jin wani bandage. Kan nata kaman ba nata ba haka ya mata,  kara shafawa tayi ta tabbatar da da gasken dai ba komai akan. To ina gshin ta ya tafi? Life is full of wonders. Jikin ta nuna mishi gabadaya “sannu ko bara in baki pain reliever, Nabeela samo Mata Tea please, she needs to put something in her stomach” Fita Nabeela tayi ta hado tea in. Waya yayi aka kawo mishi maganin sannan ya Kira Mustapha ya sanar mishi farkawan patient in tasu.

Tea in ma dole Rufaida ce ta yi kokarin bata sannan ta Sha maganin. Sai bayan Magreeb su Mustapha su ka iso, Maryam har kukan murna tayi tana mai godewa Allah da ba ta zamo sanadiyar ajalin ta ba. Sannu su ka dinga Mata tana amsawa da Kai coz maganan nata da kyar ya ke fitowa.

Suna nan a kazo gyara mata karayan da ke jikin ta. Wahala kam ta sha shi har ba a magana sai faman hada zufa ta ke tayi har aka gama.

A Daren Anty na Jin farfadowan ta tazo asibitin tare da Faroukh. Ita dai Suhaima kallo kawai ta ke bin su dashi tana mamakin Ina ta San wadannan mutanen da su ke nan nan da ita haka.

Rufaida ce ta yi suggesting ya kama ta ta yi wanka ko za ta ji dadin jikin. Wheel chair Dr Fahad ya sa aka kawo su sister Nabeela su ka daura ta akai, Wankan ma su dinne su ka taimaka Mata.

Aikin kwanan da Rufaida ta yi kwana biyu yasa ta taho da kayan shafan ta asibitin. Su ta kawo wa patient in ta yi amfani da wani silk material gown inta. Daman all these while uniform insu na asibitin da patient ke using ke jikin ta, aiko cib cib ya mata kaman tun can daman na ta ne. Ko da yake yanayin jikin su daya da Rufaidan. Rayuwa kenan mai abubuwan ban mamaki mutum da ranshi amma sai dai a daga a tayar.

Rufaidan ce ta kwana da ita tana taimaka Mata duk da ba aikin dare gare ta ba ranar. Ta tsaya ne bi sa ga Umurnin Dr Fahad, Nabeela ma dole ya sa ta tafi gida .

8:00 am dai dai Dr Fahad yayi Knocking a dakin Rufaida ta tashi ta bude. “Ina kwana” ta fadi tana yamutsa fuska kaman an sata dole, hararan ta yayi ba tare da ya tanka ba ya nufi gun patient in tashi da ke kwance tana Kallon sama da alamun ta yi zurfi a tunani. “Good morning” ya ce Mata.

A hankali ta juya ta sauke idanun ta cikin nashi “Ina kwana” ta fadi da hausan ta da bai fita sosai “Kin tashi lfy” ya fadi Yana nazarin shin wani yare ce ita don yana da tabbacin ba bahaushiya bace.

Tambayan ta yayi ko da inda ke Mata ciwo sosai, girgiza kanta kawai tayi ta tabbatar mishi da bbu sai dai abinda ba a rasa ba wanda a hankali zai warke.

“Dr what happen to me?” A hankali tayi maganan muryan ta na rawa tana Kallon bandage in da ke hannun ta.

“Sorry, you got involved in an accident” ya bata amsa

Shiru tayi tana nazari tana son tuno abinda ya faru, ganin haka ya sa ya jawo kujeran da ke gaban ta ya zauna, idanu ya zuba Mata yana Mai wani nazari akan shi.

“Ehmm Ina so in tafi gida” Rufaida ke mishi maganan. Banza yayi da ita, ita ma shiru tayi ba tare da ta Kara maimaitawa. “Allah ya kiyaye hanya” ya fada after kusan 3 minutes.

Sai da ta hada koman ta sannan ta yiwa patient in sallama tare da Mata fatan samun sauki.

“Zaki dawo?” Patient in ta tambaya.

Murmushi Rufaida ta Mata sannan ta yi nodding kanta “okay later” patient in ta Kara fadi.

mamakin Sabon da su kayi just in a day Dr Fahad yake. Yasan Rufaidan ba mutum bace mai saurin sabo.

“She is nice” ya ji Suhaiman ta fada bayan fitan Rufaida. Ko ba a fada mishi ba ya San ta fada mai hakan ne Saboda kin amsa gaisuwa Rufaida da yayi instead ma sai ya bita da harara.

Murmushi ya mata har sai da hakoran shi su ka bayyana sannan ya ce “I Know”

“How long have i been here?”

“Three days” ya bata amsa.

Wani ajiyan zuciya ta saki tana wasa da yatsun hannun ta.

“Sorry I have to go, Ina son duba patient in da nayi bedridden. Hope you won’t mind been alone for some time”

“No problem” ta fada da alamun hankalin ta ma ba kan shi ya ke ba.

“Zan sa a kawo Miki breakfast, may I know the name please”

“Suhaima” ta fadi tana lumshe ido cike da tunanin wani yanayi da ya shude a rayuwarta.

Bude kofan da aka yi ne ya katsewa Dr Fahad abinda ya ke Shirin fadi.

Anty da Faroukh ne sai Mustapha rike da basket a hannun su da Kuma Flask sai carton in faro. Sai da su ka gaisa da Dr Fahad sannan ya bar dakin. Kai tsaye Anty ta gabatar mata da abincin, ba musu ta amsa ta fara kokarin ci bayan ta kuskure bakin ta. Faten acca ne da ya Sha kayan lambu da nama da ya dafu lugub, taji dadin abincin sosai saboda ya matukar Kara ma ta appetite saboda haka ta ci abincin da dan dama, da alamun Antyn ta San Kan abincin mara lfy.

Tea ne dai Sha kawai tayi ba dan tana marmari ba, Aa su din ne ba ta so su ga taki sha su ji wani iri ganin yanda su ke kokarin kyautata Mata.

Daga baya Maryam ta zo tare da Anisa da alamun daga kasuwa su ke saboda ledojin da ke hannun su harda trolley. Fruit, brush, Soap, sponge da Kuma cosmetic da dai kayan bukata gabadaya Maryam sai da ta tabbatar ta siyowa patient inta sannan ta baro kasuwan nan. Ita dai Suhaima mamaki ne ya cika ta, shin wannan wasu irin mutane ne haka masu zuciyar taimako? Har rasa bakin gode musu tayi, dama tayi attempting hade rai Maryam tayi ta nuna mata ba ta son hakan. A Nan su ka tambaye ta sunan ta ta sanar musu, ita Kam ba sai ta tambayi nasu ba Saboda gabadaya ta ji an fada.

Suna Shirin tafiya Rufaida ta shigo da Flask in kunu a hannun ta. Daman ita za ta kawo breakfast in da Dr Fahad ya ce za a aiko da Kuma ya ga sun zo dashi ya sa a bari. sanin za ta so kunun ya sa Rufaida taho mata dashi. Aiko sosai ta Sha kunun, ko da Anty ta aiko su Anisa da abincin rana ma ba wani na kirki ta ci ba sai da yamma. Abincin dare ma cewa tayi su barshi kawai za ta Sha fruit.

Hakan ya kasance yawanci Rufaida ke jinyan ta duk wani Abu ita ke taimaka mata ko da ko bata da aiki time in hakan ya sa sabo ya shiga tsakanin su sosai though dai ba wani hira su ke ba saboda gabadayan su mara sa son magana ne. Maryam da su Anisa su kan zauna da ita at times sai kuma Dr Fahad in bai da aiki. Haka kurum ta fi sakewa dashi kodan shi Likita ne? Nabeela ko ta Kan dan shigo in Rufaida na nan Amma mostly ta fi zuwa in Dr Fahad zai shiga dakin in ko tazo ta Dade baya nan to fa tabbas a bisa umurnin shi ne.

  5:30 pm ya gama aikin shi gabadaya, Kai tsaye ya fara Shirin tafiya gida saboda wani irin sarawa da kanshi ya ke yi. He needs to rest. Har ya Zo fita daga asibitin ya tuno da ita, kaman zai wuce sai Kuma yaji ya kasa. He needs to check on her, Yarinyar na matukar bashi tausayi.

Sallama yayi a kofan daki amma shiru bata amsa ba don haka Kai tsaye ya karasa cikin dakin. Zaune ta ke akan gadon a bisa taimakon pillows in da aka jera mata a bayanta ta sunkuyar da Kai sai ko hawaye da ke gangarowa da ga cikin idanun nata.

“Barka da warhaka” ya fada amma still kwata kwata hankalin ta ya tafi wani gun.

Karfen gadon ya buga da karfi, da sauri ta dago kanta a firgice tana Kallon shi. Murmushi ya sakar mata, idanuwan ta da ta zaro ya bi da kallo wani irin kyau ya gama ta mishi fiye da misali. “Astagfrillah” yayi saurin fada a zuciyan shi.

“An barki ke kadi ko?”

“Yanzu maman haidar ta fita” ta amsa kanta a sunkuye.

“Suhaima!” Wani yar taji sakamakon yanayin da ya Kira sunan kaman yanda mahaifin ta ya Kan Kira tane.

“Me ke damun ki?” Girgiza mishi Kai tayi.

“Ehm ehm talk to me an Miki wani Abu ne?”

“Aa” ta fada a hankali Amma dai dai yanda shi in zai iya juyo ta.

“To ki daina kukan nan kinji, ko da irin ta sa kaddarar in muka karbe ta hannu biyu sai Allah ya saka mana da abu mafi alkhairi” shiru tayi tana sauraron shi, da zai san cewa tafi appreciating rayuwar ta a yanzu kan wanda ta baro da bai mata wannan wa’azin ba sam.

“Me kike so in kawo Miki?”

“Bbu” ta fada a takaice

“Ehm ehm Suhaima be free with me fa, duk abinda kike so ki sanar dani kinji” nodding kanta kawai tayi don haka shima yayi shirun ya sa mu wurin ya zauna yana Satan Kallon ta. Mutum ce ita wacce ba ta cika son hayaniya ba coz magana ba ko yaushe ta ke son yi ba. Ganin hakan yasa ya ke yawan barin ta da Rufaida domin ko duk halin daya ne. Kuma ya lura tafi son zaman kuramen da Rufaidan akan kowa. Daga farko ya dauka Rashin sabo da boredom ke sata yawan tunani sai daga baya ya gane akwai abun da ke damun tane which he thought ciwon ta ne ke affecting inta. Saboda hakan ya sa yake mugun tausayin gashi tun da aka rike ta ba Wanda ya fito a matsayin Dan uwanta Yana neman duk da Report in da suka shigar a police station dama gidan jaridu gabadaya.

Da sallama Rufaida ta shigo dakin bayan gama round inta, four eyes su ka yi da Dr Fahad ta yi saurin dauke idon ta. “Sannu ku” kawai tace ta nemi wuri ta zauna.

“Allah ya kara sauki” ya fada sannan ya tashi ya bar dakin sakamakon kanshi da ya ke ji kaman zai fashe.

Ko da ya koma gida tunanin ta kawai ya ke ta fado mai. conversation insu da Mustapha ya tuno inda Mustaphan ke sanar mishi ya kamata a tambaye ta dangin ta domin su nemo su. Ko da ya gwada mata maganan ce mishi tayi kawai in ta warke zata tafi ba sai an nemi kowa ba.

Hakan ya kasance a gun Dr Fahad kusan kullum yana Mai matukar tausaya mata ganin yanda a karancin shekarun ta wannan kaddarar ya afka mata. kuma tabbas akwai wani abu a kasa tsakanin ta yan’uwan ta, yanda ma ba ta so a mata maganan da ya dangance su kwata kwata. In zai shiga dakin sau goma to tabbas ko wani shiga da abinda zai kai mata kullum yana cikin mata hidima. Har magani ma shi yake lallaba ta ta sha in ba haka ba, ta dinga tabe baki kenan koma ta amayo shi in har ba wani abu mai kauri ta Kora ba bayan maganin. Da ya gane kullum cikin siyo mata yoghurt ya ke ko Kuma ya sa Rufaida ta hado Mata kunu. Ita ma Kuma duk ta fi sabawa dashi haka Kuma tafi sakewa dashi don yanzu har magana ta ke maida mishi sosai sabanin sauran da sai dai tayi ta bin su da murmushi har gara Rufaida ita ana mata sama sama.

Ta ji sauki sosai, duk wani ciwo da ke jikin ta ya fara warkewa sai dai karayen da saura sai ko kirjin ta da ke yawan ciwo kaman zai fita daga jikin nata.

“Please Ina son Qur’ani da husnul Muslim” Dr Fahad yaji Patient in tashi na fadi bayan ya gama duba ta zai bar dakin.

“Okay, I will send Nabeela. Ki tabbatar dai kin ci Abinci kin Sha magungunan ki please in time yayi Kinga Ina da Surgery in da zan shiga in 10 minutes”

Turo bakin tayi kaman wata karamar yarinya “Wai yaushe drugs in nan za su kare?”

“Soon” ya bata amsa yana dariya ganin yanda ta turo bakin kaman za ta yi kuka “Don’t cry kinji wata Rana sai lbr za ma kiga kaman baki taba zaman asibitin nan ba” ya karasa zance can kasan ran shi ya na jin wani tausayin ta har cikin jikin shi. Suhaima ko shiru tayi tana wasa da yan yatsun ta. Har ga Allah ba ta burin zuwan wannan ranar da Dr ke fada mata zai zo. Bata ma ki ta kare rayuwar ta a asibitin ba gabadaya.

“Promise me za ki Sha”

“Okay for you”

“For me?” Ya fada with a shock expression all over his face.

“Why?”

“Because kana so in Sha and you are nice” shiru ta danyi kafin ta karasa “just like your sister”

“She told you?”

Girgiza Kai tayi sannan tace “I’ve noticed”

“Zan turo Nabeela In Sha Allah” kawai ya fada kafin ya fita daga dakin.

  Wani tsaki Nabeela ta ja Wanda ya jawo hankalin patient in da ta ke dubawa gabadaya har ko da Rufaida da ke kusa da ita.

“Lafiya sister Nabeela” cike da kulawa Rufaida ke maganan.

“Wannan Dr in Mana, Dr Fahad Wai in Kai wa wannan yarinyar Qur’ani da husnul muslim sai kace wata tubabbiya. Yayi ta samu aiki sai kace wasu bayin shi”

Sakin baki Rufaidan tayi tana Kallon ta, she is very sure da Nabeela ta nuna bata so ba abinda zai sa Dr in ya sa ta, infact ma ita ke zakewa ko bai sa ta ba tayi.

“Kice mishi ba ki so mana I think ba zai sa ki dole ba”

“Don’t tell me ba ki gaji da ganin yarinyar nan ba” Murmushi Rufaida ta yi don ko ta fahimci kwanan zancen.

“Aa wlh, she is innocent” cike da manufofi Rufaida ta fada sai dai Nabeelan ba ta dago ba.

“Ni sai in ga kaman da wani abu tsakanin su. Ko ke baki fuskanci hakan ba? Nasan Dr na damuwa da patient insa amman wannan is daban ne” murmushi Rufaida ta yi ganin zargin ta ya zama dai dai.

Shiru tayi bata Kara magana ba ganin haka yasa Nabeelan ma yin shiru cike da zargi kala kala a ranta. Daga karshe dai dole Sister Nabeela ta je ta dauko qur’anin a office in shi ta Kai wa Suhaiman, fuska a daure tana hararan ta mika mata. Baiwar Allah ba ta ma San me ake ciki ba har godiya ta Mata tana murmushi.

Yau tunda safe da Rufaida ta fito ta ke tunanin Suhaima, hakanan kawai ta ke jin Yarinyar ta mata. Ta na bata tausayi don ta san ba karamin abu zai sa mutum ya samu raunuka irin wannan amma yaki fadi yan uwanshi ba. Yanke shawara tayi tana zuwa asibitin ita za ta fara zuwa ta duba, kwana biyu ba ta leka ta ba ba don komai ba sai dan Dr Fahad, tana kokarin ganin ko yaushe haduwar su yayi karanci. Da wannan tunanin ta samu karasawa asibitin, tana rubuta suna a registern asibitin na ma’aikata gabadaya ta nufi wurin Suhaiman. Kaman ko yaushe kwance ta ke akan gado sai da wannan karon ko ina na jikin ta rawa ya ke, alamun sanyi na damun ta. Fankan da ke aiki a dakin Rufaida ta duba taga a kashe hakan yasa ta nufi wurin Suhaima domin sanin me ke faruwa. Bargon kadai da Sister Rufaida ta kai hannun ta ya dau zafi, ganin haka ya sa fa fara kokarin budewa. Sai faman karkarwa take hakoran ta har hadewa su ke. “Subhanallah! Lfy Suhaima?” Ta furta tana kokarin kai hannun ta wuyan ta, aiko nan in ma radau ta ji shi. Da alamun dai kwana tayi da zazzabin. Rufaida ba ta son lokacin da ta fiddo wayan ta ba ta fara neman numban Dr Fahad. Shigowan shi asibiti kenan yayi parking yaga kiran Rufaidan na shigowa wayan shi. Mamaki ne yaji mamaye sanin da yayi yanzun guje mishi mq ta ke. Daukan wayan yana tunanin ko dai patient in shi ne.+

“Suhaima is…” Iya abinda ya ji ta fada kenan yayi saurin nufan dakin ba tare da ya damu da kashe wayan ba.

“What is the matter?” Kusan a tare ya fada da bude kofan dakin.

“Fever” Rufaidan ta bashi amsa tana kokarin dannawa Suhaima towel in da ta jika da ruwa akan goshin ta.

“Is it that high?” Da Kai ta mishi alamun eh kafin ta matsa ya fara duba ta da stethoscope.

Siririn tsaki ya ja ya juya wurin Rufaida “pls taimaka min da Sphygmomanometer daga ward wurin Vitals” bata ce komai ba ta fita. Mai da hankalin shi yayi kan Suhaimaj da har yanzu ta ke rawan sanyi, ta lullube da bargo fuskan ta ne kawai a waje sai ko kafa da hannun da ke da karayan. Idanuwan ta sunyi ja alamun hada ciwon kai. Hannun shi akan goshin ta, duk da towel in da yazo ya tarar Rufaida na sa mata amma radau yaji shi. Shi daman ya san yawan zaman asibiti ma na sa wa mutum ciwo. A yanda ya kamata, tunda ta fara warke wa ta tafi gida in yaso a dinga kawo ta check up har zuwa lokacin da za a kunce karayan. Sai dai bai jin za iya barin hakan duk da Brr Mustapha ya nuna son tfy da ita in, yana jin cewa ba yan uwan ta bane duk yanda su ka kai da tausayi ba lallai su kula da ita yanda ya kamata domin ko ba su san ciwon ta ba. Komai da ya faru da ita a gaban idon shi ne, yana tunanin ba mamaki hakan yana da alaka da tausayin ta da yake ji na ratsa ko ina na jikin shi. Da komai na rayuwan shi ya ke jin he needs to protect her. Kasa dauke hannun shi a saman goshin ta yayi, bai ko da yi tunanin zai iya kara mata nauyi ba. Addu’a ya fara kokarin mata, bai sanda idanun shi ya sauka akan na ta. Ba wani irin abu ya hango a cikin su da ya sa shi saurin dauke nashi idon, in bq gizo ba ne tabbas shi kam wani haske ya hango mai kashe wa mutum idanu cikin na ta idon. Bai san shigowan Rufaida ba, shi ko takun ta ma bai ji ba sai dai kawai ya ga ta ajiye mishi abinda ya bukata kan table in da ke kusa dashi. Sai a lokacin ya iya daga hannun shi daga kan goshin ta, a hannun da ba karaya ya sa mata abun domin gwada BP inta. Pulse rate inta is high sannan Kuma Bp ma is very high. Ba shakka duk yanda ya so kin yarda da abinda idanun shi ke gaya mishin, Suhaima na fama da hawan jini. Duk sanda ya gwada ba wani canji. Ya kan rasa dalilin da ke sa Yan mata hawan jini sosai a zamanin nan, gabadaya shi kam ji ya ke duk ya fara karaya. A rayuwan shi na likita ya ga abubuwa da dama masu matukar ban tsoro da girgiza, mutum da ranshi amma sai abubuwa da dama su hana shi jin dadin rayuwan. Hakika duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya shiga Uku. “Ki kira lab su turo akwai da tests in da nake so a mata”. Wayan da ke dakin Rufaida ta daga ta kira lab in, su ka tabbatar mata za su zo yanzu. Kara sa ta tayi ta hado alluran da yq ke ganinnza su saukar da zazzabin. Rufaida har ta zo tana tunanin yanda za ta fara yi mata. Fahimtan hakan da yayi ne yace ” kawo kawai ki ban tourniquet a hannun zan mata. Sai ki rubuta min lab request foam in, za ayi Mp, FBC, widal test, Lipid profile, E/U/cr, Screening na hepatitis da Fasting na sugar. Ai ba ta ci komai ba ko?”

“Na dai same ta tana rawan sanyin ne” Rufaida ta fada bayan ta ja wa request foam in tana kokarin filling.

“Have you eaten?” Suhaima ya tmby, girgiza kan ta kawai tayi dan yanda ta ke jin kanta ba za ta iya magana ba, she is feeling out of the world kawai.

Daura tourniquet in yayi a hannun ta ya fara mata allura bayan ya samo jijiyan ya gogo spirit. Allura ne kusan guda uku hakan ya sa shi Using babban Syringe saboda ya mata duka a lokaci daya kawai. Sai dai me? Yana zare alluran sai ga amai ya zo mata ba shiri. Saurin tallabo ta yayi ai ko gabadaya aman ya bata mishi jiki. kokari ta ke ta janye jikin ta amma ya ki bata daman hakan, jikin na ta ba karfi haka nan ta kyale shi. Rufaida sai sannu ta ke mata tana kokarin karasa filling foam in. Dai dai lokacin Mr Edward ya shigo tare da wata IT student a bayan shi. Sannu ya ma patient da shi kan shi Dr in jaje ganin yanda jikin shi ya baci. “Mr Edward kawo kawai na debi jinin”

“Anya Dr ba za kaje ka gyara jikin ka ba kuwa?” Murmushi ya mai yace “bakomai ai in na je sai in gyaran” bashi syringe in yayi, vacoutiner needle ne ma, da yawa ake son jinin saboda yawan tests in. Sai da Dr Fahad ya mata sannu sannan ya kara daura mata tourniquet in amma ba inda yayi alluran ba. Bottle kusan Four ne yayi kokarin ganin kowanne an samu, gudu samun matsala a result in. Rintse idanu Suhaima kawai tayi, har ranta ta ke jin zafin alluran da ke cikin jikin ta, ita kam da lfy lau ma ba zata taba bari ayi da saukin kai ba. Gane hakan da Dr Fahad yayi ne yasa yace mata “sorry ko” bayan ya gama jan jinin, Mr Edward ma sannun ya mata yana amsan bottles in “Please Mr Edward ina son tests in as soon as possible”

“In Sha Allah za ayi kokari likita” ya fada yana amsan bottles in, Mika wa IT student in request foams in Rufaira tayi sannan su ka wuce.

Kokarin magana Suhaiman ta ke yi tana son bashi hakuri yayi saurin girgiza ma ta kai. Kallon Rufaida kawai yayi ta tashi ta kawo mishi ruwa ya dan dauraye jikin shi sannan ta amsa ta taimaka wa Suhaiman, Sai da ya fita dakin ya Kira cleaners domin su gyara wurin shi kuma ya tafi gida domin gyara jikin shi.

Sai bayan 2 hours ya dawo dakin ya samu Maryam, Barr da Anisa sun Zo duba ta ita ko ma bacci take. Sun gaisa ya musu bayanin zazzabin da ta tashi dashi Wanda yafi danganta shi da yawan tunani ne hade da sa damuwa a rai. Ba ta dade ba ta farka, Dr na ganin yanayin ta ya san an samu canji sosai ba kaman dazun da yazo ba. Yanzu kam murmushi ne ma ke kan fuskan ta wanda dai tana yi ne kawai ba don ya kai zuci ba. Kokarin zama ta ke son ganin haka Anisa ta je taimaka mata. Kallon Anisan ta ke sosai tna tunanin akwai inda ta san Fuskan, Dr ne ya lura da hakan yayi mamaki saboda a yan kwanakin da tayi a asibitin ya sa kurawa mutum ido bai daya daga cikin halayen ta. Ita kanta Anisa sai da ta tsargu amma kuma sai tayi kokarin basarwa. Sun dan taba hira kadan har zuwa lokacin da result in lab ya iso sannan su ka mata sallama su ka wuce.

“Am sorry Dr abo…” Ba

p. ta karasa ba yayi saurin katse ta da hannu.

“Shhhh Dr ma ai ya San lalura right?”

Nodding kanta tayi in affirmative

“To a bar zancen ban so” Kan nata dai ta Kara Nodding still.

Duba result in Dr Fahad yayi, ya jin dadin ganin sugar level inta is normal haka kuma ba hepatitis.

“Suhaima” ya kira, dago kanta tayi tana kallon shi. Four eyes su kayi dashi ba ko shakka wannan karon ya tabbatar da abinda ya ke zargin ya gani dazun a cikin idanuwan nata. Dauke na shi yayi.

“Meyesa kike yawan tunani da sa damuwa a rai”

Dagowa tayi tana kallon shi, ta bude baki tana shirin musa wa ya girgiza mata kai “i know you are doing it fa”

Shiru tayi don ba ta ma san me za tace mishi ba, to ta ina ma zata fara? Ita kam ba ta jin za ta iya fadin komai akanta. Nothing is worth saying out ma.

Karkada Kan shi yayi alaman gamsuwan ba maganan za ta mai ba “Whatever, ki yi kokarin rage damuwa coz Yana affecting health inki negatively” Kallon shi ta ke yanda ya ke Mata magana cike da nuna kulawa sai kace wani dan uwanta na jini, Most of the times ya na tuna Mata Wanda ta sani. Halayen su da maganganun su kan mata shige. Wannan dalilin ya na daga cikin

abinda yasa ta yi saurin sakewa dashi, tana ganin kaman wancan inne a gaban ta.

He makes sure ta Sha magungunan ta sannan ya bar asibitin bayan ya kafawa Nurses in dokon kula da ita, ba Wanda ya gani a cikin Nabeela da Rufaida Bai Kuma tambaya ba ya Kama hanyar gaban shi.

Sosai ta fara gajiya da kwanciya ko yaushe akan gado fuskan tan hakan da Rufaida tayi yasa ta kan taimaka mata ta sauko kan wheelchair inta ta dan huta, duk ma har yanzun ba wani hira su ke ba amma Suhaiman na jin dadin zama da ita, ta san cewa Rufaida na daya daga cikin wadanda su ke taimaka mata sosai a yanzun, ta na kuma mahimman ta hakan. Musamman ranar sai ga Maman Rufaidan da kanwar ta sun zo duba ta, matar na da kirki sosai kana ganin ta kaga bafulatana, ai ko fulatancin ta ji suna yi dukkan su. Wani abu da su ka fada ne yasa ta dariya, ba ta ma san sanda tayi shi ba. “Haba ashe yar tawa bafulatana ce daman na zargi hakan” Dada, kaman yanda taji su Rufaidan na kiranta ta fada, dariya kawai ta sa ke yi. A nan Dr Fahad ya zo ya same su, da fara’an shi ya durkusa yana gaida Dadan kanwan Rufaidan ta gaishe shi tan fadin “Hamma Fahad”

“Kai kan asibiti ya boye mana kai kwana biyu ko fahad”

Da sauri yace “yi hakuri Dada ai yau ma dole in zo gida, Aliyu ya dawo ko?” Tun lokacin sau da dama Rufaida na kawo mata abubuwa tace Dada ta bada a kawo mata. Zaman ta a asibitin nan ya sauya tunanin da dama akan yanda ta dauki mutane da zaman takewan rayuwa.

Ita kadai ke zaune a dakin, a zahiri TV ta ke kallo sai dai Kuma hankalin ta bai Kan film in kwata kwata. Ganin haka ya sa ta fiddo Qur’anin da Dr Fahad ya bata ta fara muraja’a cike gwanance tare da ba ma kowani lafazi hakinsa. Ta kai minti arbin tana karatun kafin ta rufe Qur’anin ta fara addu’ointa tana me tuno mutumin da ya bada gudun mowa babba wurin karatun nata.

Wasu zazzafan hawaye ke fita daga cikin idanunta domin tunanin makoman ratuwar ta bayan ta warke. Shin Ina za ta? Baya za ta koma ko Kuma gaba za ta ci. Dr Fahad ne ya katse mata tunanin nata, tana ganin shi ta yi kokarin goge hawayen da ke idanun ta gudun ya fahimci kuka ta ke yi. Sarai ya ga hawayen amma sai ya basar ganin ba ta so ya ganin. Ya na matukar son sanin damuwan, yana son ko akwai gudumuwar da zai iya bata komin kankantan shi amma still bai son takura mata.

“Sorry an barki ke kadai ko?” Murmushi ta Mai kafin ta amsa da bakomai.

“Kin gaji da Asibitin namu ko?”

Wannan karon ma ba tayi magana ba sai shine ya Kara fadin “sai hakuri, Allah dai ya baki lfy” sai a sannan ta amsa mai da Ameen. A ranta faduwan gaba na ya ziyarce ta, a yanzu ta san zaman asibitin ke rufa mata asiri ba ta san me kaddara zai yi da rayuwan ta ba kuma.

“Mu fita waje ki Sha iska” da sauri ta daga mishi Kai yayi murmushin da sai da har dimples insa su ka lotsa.

“Gsky Suhaima kin gaji” ya fadi yana tura wheel chair in nata waje. Wani ajiyan zuciya ta saki bayan fitan ta su daga dakin after kusan 1 month she is finally out.

Za a iya kiran wurin da ya kaita Garden saboda shuke shuken da ke wurin ya karawa mishi Ni’ima, wani iska Mai Dadi Ke hurowa hade da kukan tsuntsaye in kana wurin ba za kaso ka bari ba. Wurin wasu beautiful adorned flowers ya Kai ta, kamshin su sai blowing ya ke. Lavender, lilac and pink lilies ne gabadaya a wurin cikin pot in su making the place purple and pink, she likes the combination. Pink was her favorite color but as she grow up she changed to purple kaman yanda life in ta ke canjawa eventually haka ma likes and dislikes inta dama komai na ta gabadaya inka cire abu daya, she can’t never move on if it comes to that.

Kura Mata idanu Dr Fahad yayi Yana smiling ganin mode in da ta shiga sai dariya ta ke tana smiling as she is touching the flowers tana scenting fragrance insu, kwalla ke zubo daga idon ta tana goge da handkerchief in da Dr in ya bata. Abun mamakin shi ba yanda ya kasa lallashin ta illa bin ta da idanu da yayi cike da sha’awa. abubuwa dayawa ke running a mind in shi, wani irin tausayin ta da Kuma tausayin Kan shi ya ji Yana ratsa shi. Bai San me ke damun ta amma zaman da yayi da ita na yan kwanakin bayan ta yi regaining concious ya tabbatar mishi da ta na cikin wani hali wanda Addu’a ne kadai zai cire ta daga ciki. he is very sure ba health condition inta bane saboda ba ta ta da hankalin ta akan shi ba kwata kwata. Deep down inside him Yana son sanin labarin ta but yasan she can’t open up to him hakanan.

Ita ko Suhaima moment in wani moment ya ke tuno mata wanda ya shude a rayuwarta, she misses and fansy that moment sanin ya riga ya wuce har abada ke sa ta kwalla. If only wishes were horses…

“Earth to Suhaima” clapping hannun shi yayi saitin fuskan ta ganin yanda tayi zurfi sosai cikin tunani.

Kanta ta yi saurin ja baya a firgice kafin ta dago ta kalle shi yana mata dariya.

“Shine ka tsoratani Koh?” Ta fadi kaman ta yi kuka.

“In tambayeki” nodding kanta tayi in affirmative.

“Ke Yar wani gari ne”

Zaro idanu tayi “me ye sa kake tambayana?”

“Isn’t it obvious? Hausanki is not clear”

“Yobe state” yanayin fuskan ta gabadaya canja wa yayi, she looks pale and pathetic.

“Wani gari infact ma wani yare yarukan yobe ai suna dayawa”

Za ta yi magana kenan wayan shi ya dau ruri, da hannu ya nuna mata alamun Yana zuwa, saurin daukan wayan yayi sannan ya sadda Kan shi kasa alamun da Babban mutum zai yi maganan.

“Hello Ummi Nyalli jam?” Ya fadi leaving Suhaima tongue tied, she can’t believe Dr Fahad bafulatani ne ko tace ya iya yaren ganin ranar da Dada ta zo shi Hausa su kayi. Ba wai bai yi Kama dasu bane No ba tayi zaton zai iya speaking fluently haka ba sai gashi ko har ya gama waya da Mahaifiyar shi fulatancin su ke yi.

Sai da ya gama ya juyo ya kalle ta

“Ãn a fullo na?” Ta tambaya leaving him tongue tied, he is beyond shocked, For sure yasan ba bahaushiya bace Amma ko da tace Yobe he expects some tribe like Bolawa ko Kuma badawa, for sure yasan ba kanuri bace.

“Which of the fulani local government are you from in Yobe”

“Damaturu”

“Ummi na Yar Kolere ce”

Runtse idanu tayi cike da takaici jin sunan garin da ya fada bayan hakan ma yanda ya kira mahaifiyar tashi ya sata shiga wani yanayi, a can kasan zuciya ta ke jin ai she is already over this kuma. Da kyar ta furta “Ummi na ma haka”

“Baffa mada no fullo?” Ta tmby shi, nodding Kan shi ya Mata “From jalingo”

Sun Jima suna hira a wurin inda kowannen su ya ke jin dadin hira da dan uwanshi, gabadaya ma juye harshe su ka yi zuwa fulatancin. Da wannan daman yayi Using a siyasance ya mata fadan kuka da tunanin da ta ke yawan yi. “Hawan Jin kawai xai Kara miki Suhaima Allah ne kawai zai miki magani” Nodding kan ta tayi a zahiri Amma fa deep inside tasan cewa she have face a lot… So abu ne mai matukar wuya ta daina tunani wannan tunanin.

Nabeela ce ta Kira shi tana tambayan ko ya tafi gida ne, Eh kawai ya sanar Mata. Tsab ya fahimci Karatun da Nabeelan ke son ya gane shiyasa ma kwana biyu ya ke kauce Mata domin matsalan da ke gaban shi ma ya ishe shi.

“Me kike so in na koma gida insa Rufaida ta taho Miki dashi in za ta zo, gidan zan wuce kawai direct” ya fadi Yana duba agogo.

“Wala dume ma” ta fada kafin ta Kara mishi wani tambayan.

“Are you cousins?”

“And fiance”

Kallo ta bishi dashi with a wider eyes.

“Really? I can’t believe this” shaking kanta tayi cike da shakku “You guys hardly talks”

Murmushi yayi dimples in shi ya shige cike sosai “Suhaima kenan, Can’t you see kawar ta ki miskila ce? And its kind of arranged marriage kin San Fulani”

“But she is nice and you look good together”

Murmushin na shi ya Kara yi Wanda ke tuna Mata da mutumin da kullum Yana ranta “I may not be interested fa Kuma ma I think I’ve just find my girl”

“Ku dai kun cika ruwan ido Allah, yanzu miye laifin Rufaida? ba abinda ta rasa” cike da fada tayi maganan wanda ya sa shi dagowa yana kallon ta.

“Na sani Kuma ba ruwan Ido bane”

“Shine mana”

“Bazaki gane bane” ya fadi Yana kokarin turo wheel chair in nata.

A bakin dakin su ka hadu da Maryam tare dasu Anisa da muhibba don haka kawai ya Mata sallama ya wuce.

Sun dan taba hira sama sama da ke ita in ba mai yawan surutu bane, sai dai yau ma kara Kallon Anisa ta ke da kyau ganin dai da kyar in zargin ta bai zama gsky ba. Ganin dai Anisa ta fara tsarguwa ya sa ta dauke idon ta. A nan Rufaida ta zo ta same su, sai da ko Dr Fahad ya aiko mata da abhbuwa duk da bata fada. Ta kan jinjina irin sabon da tayi da Dr, ko dan ya damu da lamarin ta ne?

Nyalli jam? : an wuni lafiya?

An a fullo na?: Daman Kai bafulatani ne?

Baffa mada no fullo?: Babanka ma bafulatani ne?Bayan kwana biyu+

Sukuku Dr Fahad ya shiga dakin Suhaiman domin ya duba ta. Kallo Daya ta mishi ta fahimci akwai abinda ke damun shi. Gaisuwa su kayi sai Kuma maganan da ba a rasa ba. Suhaima ba taji dadin hakan ba domin ko ance sabo turken Wawa, ka sa daure wa tayi da zai fita ta tmby shi.

“Dr me ke damun ka?”

Kaman jiran tmby ya ke ya samu wuri ya zaune bayan ya dafe Kan shi.

“Ansa min rana” yanda yayi maganan kadai zai tabbatar maka da yanda ya ke Jin zafin abinda ya furtan.

Ba ta San Lokacin da ta saki murmushi ba “Kai Dr wannan ai abin murna ne domin ne, she is a nice girl.”

“Hmm ba daga nan ta ke ba Suhaima, In dan ita ne Rigimar mai sauki ce” girgiza kanshi yayi cike da takaici.

“Ummi na ba ta son auren” Da sauri ta juyo ta kalle shi cike da mamakin abinda ya fadan. Nodding kan shi ya kara yi domin tabbatar mata da abinda ya fada in.

“Any reason?”

“A long story”

Shiru ne ya mamaye dakin na yan sakanni, tunda taji ya fada haka sai tayi tunanin personal issue ne don haka na ta kara mishi maganan. “Kin sha magani kuwa?” Girgiza kai tayi,  wani kallo ya mata alamun ba kya ji ko? Murmushin rashin gsky tayi shi ko ya nufi fridge in dakin.

  Zaune ta ke ita kadai a dakin su na Nurses da ke cikin hospital in. Ita kadai ce a dakin sauran either suna gida ko Kuma sun fita wurin patient.

“Keh lafiya?” Nabeela ta fadi game da girgiza ta. Firgigit ta dawo cikin hayyacin ta tana Kallon ta.

“Kinsan dai ba kyau tagumi ko?” Nodding kanta tayi sannan ta cire tagumin.

“Rufaida lfy me ke damun ki?”

“Bakomai kaina ke ciwo” sannu Nabeela ta mata ba dan ta yadda ba sai dan ko ta so Jin ba lallai Rufaidan ta fada mata.

“Dr Najib fa ya iso kina nan”

“Subhanallah mu je ko?” Rufaida ta fada da mamakin lokacin da ta dauka tana faman tunane tunane.

A dai dai kofan da aka yi admitting Suhaima Rufaida ta tsaya “bara na dubo Suhaima”

Hararan ta Nabeela tayi “so kike muyi latti ko? Ki ja Mana magana”

Murmushi ta mata “haba dai ai Ina tare da Sister Nabeela ba fa so banda matsala” cike da tsokana Rufaidan ta fada haka,  kusan duk ma’aikatan su ba wanda bai dago Dr Najib yana son Nabilan ba,  itan ce dai ba ta bada fuska ba.

Tsaki Nabeela ta ja, a tare su ka shiga dakin. Turus su kayi ganin Dr Fahad a dakin, cike da tashin hankali kowaccen su ke bin hannun da Dr Fahad ke ba Suhaima yoghurt dashi da kallo. They were so much lost in their own world da ba su San da shigowan su ba ma, turo baki Suhaima tayi cike da shagwaba tana mitan ta koshi shi kuma sai insisting ya ke yi.

Nabeela ce tayi karfin halin gyaran murya. Sai ko a sannan su ka juyo “Dr da Kan ka ai da ka Kira nima sai na bata”

“No na hutashe ki” ya fadi yana Sosa Kai.

Glance daya Rufaida ba ta Kara sparing in shi ba, direct wurin Suhaima tayi tana tambayan ta jikin nata, suna gama gaisawa ta bude dakin ta fita ba tare da tawa Nabeela da ke ta faman jan Dr Fahad da Hira magana ba.

Shida dai dai su ka gama round da Dr Najib. Su na daki suna Shirin tafiya gida Kiran Dr Fahad ya shigo wayan Nabeela, da murmushin ta ta dauka tana kokarin gyara murya. Shi ko Dr Fahad Kai tsaye ya tambayeta dalilin Kiran nashi “Ehmm please can i speak to sister Rufaida? Her phone is not going through” clearly za ka iya ganin yanda murmushin da ke Kan fuskan ta yayi vanishing. “Okay” ta fadi da kyar sannan ta mikawa Rufaidan wayan “Dr wants to talk to you”

Kasa kasa tayi sallama ya amsa Mata.

“Stay with Suhaima naje garkuwa hospital” Kai tsaye ya fada in a commanding way.

“Dada na nema na” ta amsa kaman za ta yi kuka.

“I will call her” katse wayan kawai yayi ba tare da ya jira amsan ta ba.

“Lafiya?” Nabeela ta bukata.

“Wai in tsaya da Suhaima”

“Ha’a ke baki gajiya ne wai ki ce mishi yayi assigning wasu Nurses in mana dole sai ke” cike da masifa Nabeela ke magana with an evidence of jealousy a voice in nata.

“I can’t Nabeela”

“Rufaida me ke tsakanin ki da Dr Fahad?” Nabeela ta fada da sauri cike da mamakin amsan Rufaida.

“Me kika gani?”

“Abubuwa dayawa”

Murmushi Kawai Rufaida tayi ta nufi bakin kofan sai da ta turo kofan sannan ta juya tana kallon Nabilan “ban san dalilin ki nakin Dr Najib but he truly likes you. I wanted telling you an sa min rana da Dr Fahad” sake ba ki tayi tana kallon ta, ita ko Rufaida tana gama magana ta bar wurin. Ta fada mata ne don kar tazo taji tace ta munafunce ta alhalin ana tare.

Da ta isa dakin ta samu su Maryam, Anisa na kokarin lallashin Haidar da ke ta faman tsala ihu saboda cerelac in da ta ke Shirin bashi, da azama Rufaida ta amshe shi sai da ta lallashe shi kafin ta bashi cerelac in ya Sha. Zuwa yanzu sun yi sabo sosai da su Maryam in sai hira su ke abin su suna Kallon film in hausa. Sai bayan isha’i su ka tafi har mota Rufaida ta raka su kafin ta dawo.

“Ina Taya ki murna” Suhaima ta fada tana wasa da yatsun hannun ta.

“Na me fa?” Rufaida ta bukata.

“Dr yace min ansa ranar auren ku shine ko lbr bbu ko”

“I can see you guys are that close”

“Don’t be jealous, he is just being nice” shrugging shoulders inta Rufaida ta yi “ba ki Sha magani ba fa, me zakici?”

“Ko me Kika bani Amaryan mu” murmushi Rufaida ta yi kafin ta hada mata abincin. Sai 9:00 clock ya shigo dakin ya samu Rufaida har tayi bacci Suhaima dai bin dakin kawai ta ke da kallo cike da tunanin makoman rayuwar ta.

“To haka ake yi mai jinya tayi bacci ta bar Mara lafiya”

“Dr please ka mai da ta gida mana, I will be fine she is exhausted”

Nodding kan shi kawai yayi sannan ya tashi Rufaida, ba musu ta dauki jakan ta tawa Suhaima sai da safe.

Yana parking a lodge in cikin gidan ta yi saurin bude kofan motan ta nufi cikin gidan, shima part insu na gidan ya nufa ko tsayawa hira da su Aliyu bai yi ba ya nufi dakin shi na da. Tsintar kanshi da tunanin Suhaima yayi, ya na matukar tausayin yarinyar. Jira kawai ya ke ta warke ya samu information a wurin ta domin ya nemo Mata dangin ta duk da alamu ba ta bukatar hakan.

Da su Baffah za su barshi to tabbas ba zai auri Rufaida ba ba wai don baya son ta ba sai don gudun samun matsala nan gaba ko don Kuma kaucewa fushin Ummin sa amma Kuma Dada fa? Halaccin ta a gareshi ya fi karfin ya saka Mata da haka.

Watan Suhaima Daya da sati uku a asibitin, in da sabo yanzu Kam ta gama sabawa da asibitin musamman dakin ta. Amma Kuma ko kadan ba ta Jin asibitin ya gundure ta, maimakon ma haka sai ya kasance ta na fargaban ranar da za a sallameta. This the first time a rayuwarta da kowa da ke tare da ita ya ke nuna Mata soyayya tsakani da Allah. Maryam har tausayi ta ke bata yanda ta ke nan nan da ita domin kuwa a cewarta duk ita taja mata. Sai dai Suhaima har godewa Maryam ta ke domin kuwa da ba ita to tabbas ba ta San me zai same ta ba a wannan bakar ranar.

Washegari, Sauri sauri gudu gudu Dr Fahad ya shiga dakin “sorry pls ban Zo da wuri” murmushi kawai Suhaima tayi tana fadin “bakomai angon Rufaida” hararanta yayi sannan ya ja wheel chair in nata “shall we?” Nodding Kai kawai ta mishi. Section section na asibitin ya dinga yawa da ita kafin daga karshe suka yada zango a garden in da yake yawan Kai ta.

“Sannu Dr” nodding kanshi kawai ya yi.

“You can’t even ask me yasa ban zo da wuri ba ko”

“No need tunda dai kazo ai shknn”

“Kawar kice bata da lfy”

Zaro ido Suhaiman tayi cike da mamaki “subhanallah me ke damun ta?”

“I can’t believe it Wai hawan jini ke son kama Faidah hawan jini fa” cize leben shi yayi cike da takaici, idon shi yayi jawur kallo daya za ka mishi ka fahimci tashin hankalin da ya ke ciki.

Salati ta fara yi ita ma cike da nuna kulawa ko ba komai alkhairin Rufaida gare ta abu ne da zai yi wuyan mantuwa, Gashi ma tana burge ta sosai.

“Is she admitted?”

Girgiza Kan shi yayi “I checked her at home, nayi dripping inta yanzu haka”

“Then why are you here? Kamata yayi ace ka tsaya a kanta Koh?”

“Bazan iya ba Suhaima, I need some air”

Shiru ne ya ratsa wurin for some minutes sai motsin flowers da Shawagin tsuntsaye kawai kake ji yayin da zuciyoyin su ke raya musu abu dayawa.

“Ita ma ba ta son auren ne?” Yaji ta fada a hankali. Nodding kan shi kawai yayi. Qur’anin da ke hannun ta ya kai duba.

“Kin sauke ne?” Murmushi ta yi hade da girgiza Kai.

“Na gama Kahfi Zan shiga Maryam”

“In Kara Miki?”

   “In ba Zan takura maka ba”

  “Karki damu muga Qur’anin”  amsa yayi sannan ya fara flipping through the pages.

Karar shigowar message ya ji a wayar shi har zai share sai Kuma yayi tunanin Kar Ciwon Rufaida ya sa ake neman shi a Gida, gudun a samu matsala yasa yayi saurin ciro Wayar daga Aljihun shi ya bude ta.

Da mamaki ya ke bin screen in wayan da kallo ganin sunan Sister Nabeela baro baro, abin nufi shine itan ce ta turo mishi sms in kenan. Lafiya? Ya tambayi kanshi.

“Am sorry bara dan duba SMS in nan ko” Yayi saurin fadawa Suhaima sannan ya bude message in, in order to clear his doubt.

“Aslm Dr, nasan za kayi mamakin ganin na rubuto maka text. Let me just get straight to the point, Dr a gsky na dauka cewa akwai alaka Mai karfi tsakanin mu da Kai da su ke adane a cikin zuciyoyin mu not until some month back da aka yi admitting Suhaima a asibitin, at first na dauka kulawa ce normally na Dr da patient insa sai daga baya nagane abin ya wuce nan am so envious but more upset time in da Rufaida ta fada min wai ansa muku Rana, I still couldn’t believe it. Abin tambayan a Nan shine playing Ina kake? Coz i can’t even believe kace min you never had a thing for me after all the caring, possession and concern.”

Murmushi yayi bayan ya gama karanta sakon nata, tsab ya fahimci inda ta sa gaba tuntuni sai dai bai son ya nuna mata ba Haka ya ke nufi ba ba tare da itan ta nuna Mai ba yazo ya zubar Mata da pride inta. Nabeela mace Mai pride sosai coz ko a asibitin ba kowa take wa magana ba gabadaya ma tafi sakewa da shi Doctor Fahad in sai Kuma Rufaida. Wani bangaren na zuciyan shi Yana jin kaman bai kyauta ba don shi yayi abunda har ya jawo attention inta kanshi. Ba macen da ya ke tsayawa suyi fira da ita a cikin asibitin kaman ita Nabeelan, komai in Yana bukata ita yake sawa ta mishi shi ko ba komai yasa yake satan ba sai don ba wacce ke mishi abu dai dai ya mai ba in ba ita ba.

Kauda tunanin yayi bayan ya maido wayan shi cikin aljihu. Suratul Maryam ya budo ya mika Mata Qur’anin sannan ya fara rero kira’an sa Mai dadin sauraro Yana biya Mata. Mai da hankali Suhaima tayi ga karatun a zuciyan ta tana Mai rokon Allah ya Bata damar haddar Al-qur’anin kaman yanda Dr Fahad in ya samu just like sanda shi tun Yana karamin shi ma ya haddace. Sau Uku ya biya, sannan ya karanta ta amsa, a na biyar zam zam ta biyo rubu’in da ya kara ma ta gabadayan. Nan Dr Fahad ya gano ita in yar Adam ce Mai saurin fahimta Da daukan karatu.

Sun Kai 1 hour suna karar

Tu. Sannan ya maida ta daki ya Mata sallama bayan ya sa wata ta dinga duba ta.

Kai tsaye ya ciro wayan sa yayi dialling numban Nabeela, kaman ba zata dauka sai da ya kusan tsinke ta dauka.

“Kina Ina?”

“Gida”

“Okay ganinan zuwa”

Dam!! Gaban Nabeela ya buga bayan Dr fahad yayi ending call in. She didn’t expect zai dauki action a Kan SMS in da ta turo Mai, not even immediately. Honestly, she didn’t plan for that, tunda Rufaida ta sanar Mata abinda ke tsakanin su ta shiga wani irin hali matsananci, Ko ita ba zata ce ga iyakan adadin hawayen da ta zubda ba don duk ita a nata tunanin Rufaida da Dr amanan ta su ka ci su ka kulla soyayya a boye. Bata kasance daga cikin Mata masu zurfin ciki ba to top it ma kwata kwata ba ta iya boye abu ba, in har abu na damunta toh it can’t be subtle but its opposite shiyasa ta yanke Shawaran tura mishi mssg in Kai tsaye.

Kiran shi da ya shigo wayan ta ya tabbatar Mata isowan shi, ya Sha sauke ta a gidan nasu shiyasa ya San gidan. Hijabin ta ta dauko har kasa ta nufi side in Anty ta (matar brother inta) bayan ta wanke idanuwan ta da har kumburo wa suka yi tsagagen kukan da ta Sha.

  “Sannu Anty” ta fada hade da dan rusunawa.

Kallon ta Anty ta yi for some moment sannan ta girgiza Kai “Yauwa Nabeela, ba zai dai ki fada min abinda ke damun ki ba ko?”

Murmushin yake tayi sannan tace “Anty Allah bakomai, Su Khalipha har sun tafi islamiyya ne”

“Ehmm ya gama rigiman ke zaki shirya shi har ya gaji ya wuce”

“Allah sarki I’ll make up to him_

“Ya dai fi miki”

“Ehmmm na dan yi bako ne”

“Siriki nane yazo?”

Yake Nabeela tayi kawai har Antyn ta bata key in guest parlor insu domin ta tarbe shi a wurin.

Da tray in Refreshments ta tarbe shi a Falon bayan sun gaisa. Shiru sukayi for some second Yana nazarin ta “kuka ki kayi?” Ya tambaya. Shiru tayi because ba za tace mishi ba Hakan bane bayan is so obvious har fuskanta ya nuna gata fara dama so shirun shine solution.

“Am sorry” taji ya fada da Sauri ta dago manyan idanun ta tana Kallon sa, Nodding Kan shi ya Kara Mata in affirmative. “I like you Nabila but not that way, Am sorry I’ve have gave you the wrong impression” ba ta ce komai ba ya cigaba da magana “Nabeela I couldn’t lie, am really enjoying your company, you are nice, friendly and accommodating. Amma kinsan me? Frankly speaking i’ve never sees you as someone beyond that Friend zone and that’s why am apologizing. Maybe my actions towards you ya sa Kika yi wannan tunanin har Kika yarda da shi. Maganan Suhaima Kuma am just been caring,  u already know her situation sai Kuma Rufaida i thought you are that close”

Girgiza kanta tayi “we are good but she is so secretive bayan haka ma she hardly talks”

Murmushi yayi “we are cousins” da sauri ta dago Kai tana Kallon shi.

“You know, I’ve always suspect things between you two but I’ve never thought of a family”

“Yayanta ne ni and we are engaged since tun kafin in Zama doctor ma” ya karasa zancen da dariya. Nabeela ko neman zafin da take ji tayi ta rasa.

“Arranged marriage?”

  “Something like that”

“I wish you two the best”

“Hope kin dai hakuri and Kuma kin tabbatar da ba yaudaran naki nayi ba” dariya tayi cike da kunyan abinda ta tura mishi a mssg in.

“You are beautiful, just like you said I’ve had something for you but please give my friend a chance” nodding kanta kawai tayi in affirmative sannan su kayi sallama bayan ya sanar Mata rashin lafiyan Rufaidan.

Straight gida ya tafi domin ya ga yanayin jikin Rufaidan.

A falo ya same su Dada da Aliyu yayan Rufaidan. “Yauwa Fahad ai gwara ma da kazo yanzu, kanwar ka fa taki  cin komai sai kuka ta ke anyi rarrashin Amma ina” Dada ta fada bayan sun gaisa “Amma ai ba Amman Koh?” Ya tambaya aka tabbatar mishi da babu. Kai tsaye ya nufi dakin ta. Sai da yayi Knocking kofan sannan Faizah kanwar ta tazo ta bude mishi kofan ta bar dakin. Tana kwance kanta na Kallon sama, drip in ya dade da karewa har an cire Mata.

“Sannu Faidah” ya fadi a hankali his gaze directly on her face. Da Kai ta amsa mishi. “Umma joda” yace bayan ya zauna akan kujera in da ke gab da gadon nata yanda  zai iya fuskantan ta sosai. Ba musu ta tashi ta jingina jikin pillow. “Meye sa baki ci abinci ba? Ko baki so kisha magani ne?” Tabe baki ta yi Jin ambatan maganin da tayi, shi Kam yana matukar mamakin abin a matsayin ta na nurse. “Ko dai sai mun je asibitin ne?” Saurin girgiza kai tayi har sai da ya dan dara ganin reaction inta.

  “Banda appetite, kunu nakeso” ta fada ta Kallon shi.

   “Okay bari in sa Fa’iza ta Miki then”

Turo baki tayi kaman za tayi kuka “Kai ya fad! na ka fa ya fi dadi” da shagwaba tayi maganar, shi Kam mamaki ma ta bashi. Why the sudden interest? Kuma ita ma kishi ta ke akan Suhaima just like Nabeela.

“Okay bara na Miki” kitchen ya nufa direct ya hado Mata kunun gyadan da ta ke matukar kauna. Ga mamakin shi ko ta Sha kunun sosai kafin da kyar ta Sha maganin kaman za tayi amai tana tabe baki.

Sallama ya Mata zai fita ta yi saurin dakar dashi “Dr I can talk to you?”

“Why not”

“Ehmm am sorry Amma you need to talk to Sister Nabeela, it seems like she misunderstood your Feelings towards her”

“And what bothers you akan hakan”

“Kaman Yar uwa ta ke a guna, I don’t want her to get hurt”

“Ko yaushe Kika fara damuwa da matsalar wani? Anyhow, mun riga mun gama magana da ita” Bai jira amsan da zata bashi ba ya bar dakin. kofan ta bi da kallo tana Jin wani zafi a ranta kafin ta lumshe ido cike da tunani kala kala, how she wish he will understand and give her another chance.

Rufaida ba ta gaskata abinda Dr Fahad ya ce Mata ba sai da taga Washegari Nabeela ta kawo Mata ziyara bayan ta tashi daga asibiti, har fatan alkhairi ta Mata hade da bata hakuri akan komai da tayi rashin sani ne. Daman tun can Rufaidan ba ta kullace ta ba, sakewa su kayi abin su suna ta hira kaman ba wani abu tsakanin su, sai bayan magreeba Nabeelan ta shirya tafiya gida. Ai ko har gida Dada ta sa Yaya Aliyu ya kaita.

A/N shin me kuka fuskanta akan littafin? Please do comment and let me know, jin ra’ayoyin ku na da matukar amfani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *