LABARIN RAYUWATA CHAPTER 4 BY Ayeshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
Service ya kawo Amal garin Lagos, da farko gidan Friend in shi ya tura ta zama. Sai dai ba ta cika sati daya ba a gidan ta fuskanci akwai takura a al’amarin gidan sosai wanda ba haka ta saba ba a gidan su, she is free to do everything she likes. Hakan yasa ta tattara kayan ta ta koma daya daga cikin apartments in baban ta da ke lagos in. Ko da ya samu labari ya tmby ta ya akayi kawai ce mishi tayi she needs to be comfortable, shknn zancen ya mutu. A lagos mu ka hadu da Amal kasancewar ta mutum mai rauni tana gani na a hali na taimako ta ceto ni, a wannan lokacin nima in bautar kasan na ke a asibitin koyar na jam’iar lagaos a Ikeja. Ta sani a jikin ta sosai ba tare da wani shakku ko fargaba ba. Tare mu ke zama a Abuja a gidansu, ko kuma Lagos a apartment inta.+
Tunda nasan ta nasan Zaid, na kuma san alaka mai karfi da take gudana a tsakanin su. Zan iya cewa suna rayuwa ne kaman na mata da miji duk da ko ba auren tsakanin su. Iyayen ta sun ki bashi auren ta duk da yana da burin hakan amma hakan bai hana ya shigo gidan su freely duk time in da ya ga dama ba a matsayin Friend in ta ko kuma yazo wurin Salim, wanda tare su kayi karatu a UK.
Kusan su in Kwarya tabi kwarya ne saboda shi inma dan masu hannu da shuni ne. Baban shi babban Custom officer ne da yaji kudi har ya gode Allah kafin yayi ritaya. Intrestingly, maman shi kuma na aiki da SSS ne. Business in Telecommunications ya ke yi a Abuja sai kuma Natural drinks da ya ke da shops in su branch branch a cikin Abuja. Shakes, Zobo, Ginger, Smoothies, mocktails, Yoghurt nd ice cream. Ba mu dade da haduwa yayi offering employing ina karkashin Drinks shop in shi duk time in da nake Abuja. Amal ba tayi wani tunani ba sai ma jin dadin da tayi, i get something to lives on. I really enjoy the work, the pay and everything.
Da shigar doguwar play gown na atamfa da Dan karamin veil na fito falon. Zaune su ke akan dinning suna breakfast ko kuma ince brunch, Shabiyu da rabi na rana har ya gota.
“Sis ina zuwa haka?” Amal ce tayi maganan da spoon in da zaid ya sa ma ta a baki, shi ke ba ta abincin.
“Shopping, ina son toiletries and some groceries. Akwai abinda kike bukata ne?”
“Just pomegranate, ina son yin cocktail in shi”
“Yaya na fah” na fada ina kallon Zaid, tun dazu ya ke faman Satan kallon fuskana.
Siririn murmushi yayi Wanda ya tsaya iya labba “Kanwata kenan, ai kin San mai na ke so” nan take na gane abinda ya ke nufi. Harara n shi nayi, amma idon Amal hararan wasa ne “Kaima kasan ba zaka taba samun wannan ba, I can’t never go that far”
Clueless Amal cewa tayi “Jikin abinki Sis kinji, Traffic in Lagos in nan ina mutum zai yi nisa” bansan lokacin da na saki dariya. A wurin Amal Zaid na ke wa dariya, shi kuma a wurin shi ita na kewa dariya. Unknown to them dukkan su na kewa dariyan. Cikin farin ciki na isa store in, bayan na gama dukkan siyayyan da zanyi ne na ja motan sai Unguwar agege.
A bakin wani katon gida nayi parking, sai dai duk girman gidan bai da plasta ko fenti a jikin shi. Tun daga kofan gidan na fara cin karo da matasa, yan mata da Yan dudu. Daga masu shan sigari, tabar wiwi sai ko masu faman caca ga kuma kidan da ke ta faman tashi. Duk inda na wuce shewa za kaji na tashi suna kiran “Ah Yar baiwa manya yau an shigo kenan” daga musu hannu kawai na ke na wuce a haka har na karasa cikin gidan, inda dakuna ke nan birjik.
“Ah ah kawa yau kece a gidan namu” daga baya na naji an fada, saurin juyawa nayi muka hada ido da zeenah. Rungume juna mu kayi cike da farin ciki. “Yau lafiya da kanki a gidan namu?”
“Kawa fa ban son sharri sai kace da in ban zuwa?”
“Yaushe rabon ki? Ke da sai dai a ganki a mashaya” dariya mu ka kwashe dashi irin na yan duniya, hade da tafa hannu. “Yau dai nazo ai, Allah ya sa mutuniyar ta na nan”
“Ai ko kinci saa, Yanzun nan dawowan ta daga Calabar, kin San mutuniyar na ki ba dai yawo ba”
A tare mu ka karasa wurin dakin Muna cigaba da tattaunawa. Sabbin fuskoki dayawa a gidan, Wadanda na sani da kuwa kusan ince hassada ke tsakaninmu dasu, a ganin su na samu cigaba. Sai masu mutuncin ne zaka ji suna fadi “Yar baiwa manya an shigo kenan?”
A dakin ta na iske ta zaune tana fidda kayan da ta dawo dasu tana ta faman hamma “Sarkin tsafta ba ki bari ki farka daga baccin sannan a gyara kayan” na fada bayan na zauna a bakin gadon dakin ta.
“Ke kin San ba zan iya ba ai, na jiyo muryan ki ai kuna magana da uwar tsugudidin can. Allah Allah na ke ma ni kar ki shigo min da ita”
“Ita ma kinsan baza ta shigo ba ai”
“Keni ba wannan ba daga ganin bakin ki nasan akwai magana. Daman tun da jiya aka kira ni ya shigo gari kuma kunyi rawa tare nasan akwai maganan”
“Me kika je yi calabar wai?”
“Abinda kika sani kuma! Sabon saurayi nayi shi na raka” girgiza kai nayi sannan nace “He propose Yesterday fa”
Saurin gyara zama da tayi tare da sakin gyalen da ke hannun ta”Allah mutuniyar? Na mugun yarda da ke ai” a tare mu ka saki dariya “kuma mai kika ce mai”
“Na nuna mishi kin amincewa ta, in ba haka zai zamo ba yarda tsakaninmu. Ina son fada miki ne dai kawai kisan mai ake ciki”
“Mutuniyar a ciba da gashi, mu bi komai a sannu kaman yanda kike yi har mu cin ma nasara”
“Toh shknn mutuniyar bara na tafi, kya sanarwa Anty abinda ake cikin”
“Yaushe zaki Abuja? Ya kamata ki leka ta da kanki. A gaida sweet Amal” harara na watsa ma ta Wanda ya sata dariya. Nace “Kwanan nan za muje da Amal in, dole ma inje.”
Ko da na koma gidan, Amal kadai na iske. Zaid ya fita meeting in da ya kawo shi garin.
Rashin takaimaiman abun yi yasa mu zaman kallon Korean series, The Doctors. Film ne mai ilimantarwa sosai. Musamman, a wurina, da nayi karatun likitancin.
Wurin la’asar, ta ke sanar min tana son yiwa Zaid girki zai yi baki. Jikin ta har wani rawa ya ke, har ga Allah banji matar shi ta sunna ma tana mishi hidiman da baiwar Allahn nan ta ke mai. Sau da dama na kan so bata shawara akan sha’anin Zaid in, sai dai zuciya ta ke garagadi na akan shiga abinda ba ruwa na. Musamman ma dan sanin ba abinda ya shigo dani rayuwar tasu ba ne.
Samari da Alhazawa kala kala da su ka taka Zaid a kudi, matsayi, ilimi harma da wayewar kai kan nemi kulla alaka da Amal in. Mafi yawancin da shedanan su ke nemanta. Sai dai duk da haka akwai masu son ta da auren da gaske. Amma ba wanda ta ke kulawa Sai shi, ta na mishi wani irin zazzafan soyayyan da ita kanta ba zata iya kiyasta wa ba. Mace mai aji, kwalisa, kyau, budewar ido da ilimi amma soyayya ta iya taka ta hade da mata juyin waina a duk lokacin da ya so hakan. Maza dayawa za su so ace su suka samu wannan garabasar.
Bambancin wannan mazan da Zaid Almansur kuwa shine; in ka cire kyau da ke akwai, Zaid mutum ne dan duniya da ya matukar kwarewa wurin aika ta duniyancin. Ya San mata ya San sirrin su, hakan ya bashi daman siye su cikin sauki da kwanciyar hankali. A tsarin shi bai siye mace da kudi ko da wasa illa zalla soyayya, kwantar da kai, iya kalamai da kuma irin tsarin shigar shi. Sai dai in bai ga classy mace ba, in har ranshi ya biya to fa sai ya samu. Upon all matan da yayi harka da su daga matar shi sai Amal ne bai iya rabuwa dasu ba. They were more like friends da Amal Kafin su fara soyayyan, hakan ya sa ba iya rabuwa in da ita, saboda he really needs her as friend. Ita kadai ce har ranshi ya so ta da aure.
Da kanta ta ke labarin abinda ya faru lokacin da aka hana ta auren shi. Tunda ta taso ba taba cin karo da abinda ta ke so kuma ya gagare ta samu kaman shi ba. Alkawari ta daukan wa kanta muddin aka hana ta auren shi to tabbas sai ta bashi kanta; ma’ana ta mishi kyautan budurcin ta. Hakan ko ya faru, a daren ranar ta fita ta bar gidan su direct ta karasa apartment in shi. Cikin rudu ta shiga gidan, a falo ta same shi yana faman kwankwadan barasa. Ba tayi wata wata ba ta nemi ya bata ta sha in har zai yaye mata damuwa. “It can be addictive” yace mata. Ita dai tace taji ta gani. Dalilin fara shashaye shashayen ta kenan a duk wani lokacin da ta tsinci kanta cikin damuwa. Daga baya ma da ya zamo mata jiki ko da ba ta da damuwan komai shan abinta ta ke. Ranar a gidan shi ta kwana rungume a jikin shi, wannan kam ba wani abu bane a wurin su daman, he hug, kiss and feel her body whenever he feel like doing so. A washegarin ranar ne ta sanar mishi. “She don’t want to wait anymore kuma tunda an hana su aure, she want have the sex” ba tare da wani musu ba ya amshi budurcin ta a ranar. Kaman matan shi ta aure haka yayi treating ita. Duk iskancin shi bai iya mata don yanda ya ke boye mata neme nemen matan shi ko Matar shi bai ma haka.
Sai a kwana na uku sannan yayan ta Saleem yazo ya same ta a gidan. Daman tunda aka bincika duk wani yan uwa da kawayen ta ba a ganta ba ya San ta na wurin shi. Kusan dambe su kayi tsakanin Zaid da Saleem, da kyar ta samu su ka rabu sannan saleem in ya Sa ta a gaba su ka dawo gida ba. Bakin cikin duniya kam ba Wanda mahaifiyar ta ba ta shiga ba, ta yi kuka har ta goge Allah. Ita kuma irin tata kaddarar kenan akan yara ya ke. Baban ta kan rantsuwa yayi ba zai taba bada auren ta wa Zaid ba. Kulle aka mata na kusan sati biyu kafin hutun ta ya Kare ta koma inda ta ke makaranta a UK. Sai dai ba UK ba kowani kasa Amal taje a fadin duniya, abu ne mai sauki a wurin Zaid ya hau jirgi zuwa inda ta ke. A ganin shi rabuwa da ita ba karamin asara bane a wurin shi ko bayan hakan ma yana mugun tausaya ma ta, yasan ko wani hali ta shiga shine sila. Tun daga lokacin ta zama ruwa in dai akan zaid ne, clubs, parties, hotels ba inda ba ta taka ba. Ya sha maido ta har cikin gidan su a buge ba ta San idan kanta ya ke ba, kaman jaririya haka zai fidda ta daga mota ya kai ta har dakin baccin ta. Apartment inta na gefe ne, iyayen kuma na cikin gida shiyasa har ya ajiye ta ya tafi ma ba su sani ba.
…
Wurin bakwai da kwata na dare su ka shigo. Zaid ne da bakin shi guda uku. Biyun kam samari ne da ba zasu wuce 26 zuwa 28 ba, dayan kuma babba ne dan zai ma fi zaid in a shekaru.
Abinci kam kala kala haka muka shirya shi tare da Amal da cook inta. Lokacin da su ka shigo na shiga daki, ina jin muryan bakin suna gaisawa da Amal. “My lady here” muryan zaid na ji yana gabatar da Amal. Duk da ban wurin nasan irin murmushin da ya ke kwance kan fuskan ta duk sanda Zaid ya gabatar da ita a matsayin tashi.
“Lady ina Suhaima ta fito ga business partners” ya fada yana kallon kofan daki na. Dai dai lokacin na bude kofan idanuwa na da nashi suka hade. Da idon ya min alaman wai nayi kyau. Harara na watsa mai, ganin duk sun ban baya. da gashi sai bakon shi daya ke facing ina. Siririn murmushi yayi ya dauke kanshi gudun a harbo inda ya nufa.
Dinning in na kara so, ina kokarin jan kujera “sannun Ku da zuwa”
Ban ji amsan su da kyau ba, mikewa na kusa dani yayi ya ciro min kujeran da kyau. “Bismillah ko”
“Thanks” na fada a hankali ba tare da na kalle shi na zauna. Ina dago kaina, na ga wani irin kallon da Zaid ke jefan Wanda ya fiddo min kujera, ko ya gani ko bai gani ba, ohon mai. A hankali kowa ya fara serving kanshi, ana miko serving spoons, bowls da sauran su.
“My sister, Suhaima” Zaid ke pointing ina yayi maganar.”so beautiful” na kusa da ni in ya fada yana jefa min wani irin side look. “Zaid akwai tattauna wa fa”
“Kar muyi haka da kai mana boss.”
“Oga Hafeez da kanka? Kar Amarya ta jiki fa” Amal ke tsokanar shi, dariya yayi yace “kar ki damu lady Amal, da kaina zan fada mata”
“Sis meet my boss and business partner Hafiz sameer” Zaid ya fada, juyawa nayi ina kallon shi, shi in ma ni ya ke kallo.Hannu ya miko min, shaking hannu mu kayi yana fadin “Delicate skin beauty” murmushi kawai nayi, shi in ne nake tunanin zai ma girmi Zaid in.
“Oga hafeez dai ya dage” Amal ta fada, duk akayi dariya.
“El-yas here, shi ma muna aiki tare. He study interior architecture and design, he design all my shops, company building and apartments”
“Wow! So you are the man behind all these unique aesthetics.”
Dariya yayi, Amal tace “Wai friend dan ma ba kije Company in ba, the interior designs were simply beautiful. Bara dai muje Abuja, ko dan ma ashe nan drinks shop za su koma. I can’t wait to see the new designs on the shop”
“Madam kenan ina godiya, Am already working on the shop interiors ai”
“Then meet Faroukh Usman, Lady ke ma ba ki San shi ba. He is computer expertise and guru. Ba mu dade da fara aiki ba, but he is great”
“Nice meeting you Faroukh” a tare mu ka fada ni da Amal, yana murmushi ya amsa. He looks so nice and innocent.
Ana cin abinci ana taba hira, Wanda duk akan business in su Zaid in ne. “Sister na fada miki we are relocating ba, am tired of handling many small shops. Shi ne mu kayi deciding mu yi babba daya a one location kawai though zamu bar na cikin Universities. Location in yana gefen company inmu, An gama komai na gini sauran interiors in. I want you to be the manager there”
“Nice idea” Hafeez yayi saurin fada, ya kara da cewa “Ku yi magana da El-yas akan interiors inma kawai ba sai nayi ba tunda you will be the oga there” jin dai magana gabadaya na business ne, Amal kam ba field inta ba ne. Hakan ya Sa ta tashi ta koma kan couch ta bude macbook inta.
Ba dadewa Zaid ya bita, jawo shi yayi jikin ta ta shige sosai, su ka cigaba da kallon tare.
…
Bayan Barr ya bar wurin Suhaima zuwa yayi ya dinga shiga yana fita har sai da ya gano adadin kudin bailing in da za ayi requiring. Kudi ne masu matukar yawa, dole ya fara shakkun anya za a sami wadannan kudaden a gun su Suhaima kuwa? Har zai kira Dr suyi shawara sai yayi tunanin bara dai ya gwada au ya gani.
A wani restaurant su ka hadu Zeenah da dare. Sai falli ta ke ta faman mishi, shi kam dai bai tanka ya fara fado ma ta bukatun shi. Da ya kira yawan kudin, duk a tunanin shi za ta girgiza. Sai dai maimakon hakan sai ce mishi tayi “i will write the cheque in ba ka kafin na bar Abuja” ba wani alamun mamaki a fuskan ta, sosai ya ke jin yana son tmbyn ta dukiyan na wanene sai dai bakin shi ya kasa furta hakan.
“Zeenah” ya kira ta a hankali yana kokarin tattaro tambayoyin da ya ke son mata. “Ya kuke da Suhaima?”
Sai da tayi wani fari da ido ta saki mugun murmushi mai cike da ma’anoni tace “kawa ta ce fa, kaman na taba gaya maka ai. Ba kaji kawa mu ke ce wa junan mu ba?”
Tabe baki ya danyi, yana ganin kaman ba zai wani samo abin arziki a wurin ta ba yace “nasani, amma za ki iya fada min inda kika san ta har kuka shaku?”
“Gidan magajiya da ke agege” ta fada kai tsaye tana kara sautin karan chewing gum in da ke bakin ta. “Ka gane akwai yarda da aminci a tsakanin mu duk ba wani zauna tare da ita na dogon lokaci ba, ta kan nemi ni bayan ta bar gidan akai akai kuma…”
“Ita kadai ta zo wannan gidan?” Ya bukata, girgiza kai tayi tace “wata Aminiyar ta ta kawo ta”
Gyade kai yayi yana wani nazari yace “tana ina Aminiyar na ta?”
“Ta dade ba ta kasan nan gsky, banji ta ma san abinda ke faru yanzu haka”
“Okay” yace yana kara sa abun a kwakwalwar shi. “Me za ki iya fada min game da halayen ta?”
Murmushi tayi sosai sannan tace “akwai kirki ga wanda ya zauna da ita ya fuskance ta fa amma don har yau akwai ma su ma ta kallon mai girman kai a gidan namu, ba ta cika magana, a fuskan tan da na mata yana daya daga cikin dalililan da ya so ba ta cika shiga harkan mutane ba. She is a good listener, duk shirman da na zo ma ta dashi tana za ta saurare ni har ta bani mafita. Sannan zan iya ce maka bayan wacce ta kawo ta dani kadai ta ke mu’amala bayan ta bar gidan” tsab ya ke sauraran ta yana kokarin sa lissafin sa a duk bayanan da ta mai. A ko ina da ta zauna, ana mata kallon mai girman kai, ko meyesa haka? Amma a kaduna duk da rashin surutun ta, ba mai mata wannan kallon. Is she just acting ne?
Shi tun da ya bar wurin ta ya ke tunanin lbrn da ta fara bashi, in akwai abinda ya fahimta game da lbrn abu daya ne, bayanan Faroukh ne kawai su ke kokarin zama gsky. Amma zai mata Uzuri, kaman yanda ta bukata.
“Meye sa ta barin gidan Yancin?” Ya tmby zeenah, da ta kalalo idanu “ban san dalilin ba saboda ba ta fada min. Sannan ita ba mai son a dinga ma ta yawan shishigi bane shiyasa ban bukaci sanin ba, amma mutane dayawa na cewa wani mai kudi ne da su ka hadu ya tsaya ma ta har ya kai ta da barin gida” hmmm, komai dai kara daure mishi kai ya ke, duk wani da ya ke samu a kulle su ke zuwa mai, kowanne yana bukatan a warware shi sosai, daga haka ya yanke shawaran sauraron lbrn da ta fara bashi, wanda ya ke tunanin ana za a samo mafita gabadaya.
Godiya ya ma zeenah, ya mata alkhairi sannan kafin su rabu ya sanar mata in yana bukatan wani abu daga gare ta, zai nema ta.Dr Fahad ne tsaya gaban Suhaima yana faman kare ma ta kallo domin ya tabbatar idanuwan shi ba gizo su ke mishi ba. Wannan ba Suhaiman da ya sani bace, wannan tayi duhu sosai, ta lalace sabili da wani irin mugun rama da tayi, kana ganin ta kaga wacce ke cikin garari da masifan rayuwa. Gabadaya ta canja mai a idanu, wani irin hawaye masu zafi yaji sun cika mai idanu ayayin da zuciyan shi ke faman wani irin suya na masifa. “Ya Allah” ya furta a hankali, shi kam ko lokacin da ta ke asibiti bai ga tayi irin wannan lalace wan ba.+
“Suhaima, shin miye labarin Rayuwar ki?” Ya furta a hankali, idanuwan shi a kan nata. Sauke na ta idanun tayi kasa yayin da sautin bugawan zuciyan ta ke kara yawa. Da wani irin rikitaciciyar murya tace “Dr lbr ne mai matukar tsawo wanda ya canci a rubuta shi a cikin littatafai domin koyon darasi a cikin shi, zan baku labarin Rayuwata amma sai a hankali” kanta na a kasan har ta gama gabadaya maganan. Tun da ta shigo bakin wurin, wannan ne karo na farko da Dr Fahad ya sani faman ziyartar ta, ba Wai don bai so hakan ba sai dan daman ba ta samu mishi ba. Ko bai jin komai akan Suhaima, yana ma ta kallon kanwa a gare shi hakan ya sa duk wani matsala da damuwa shi ya ke jin shi kaman na shi. “In sha Allahu Za muyi kokarin fidda ki daga wannan wurin, ko baki fada ba ni kam jikina na bani you are innocent” ba tace komai ba saboda ba ta ma San abun da ya dace tace mishin ba, Dr Fahad na da wani mahimmanci na daban a kadadarorin da ke afkuwa a rayuwan ta.
“Nagode” ta fada a hankali, ita kanta ta san rashin abun cewa ne ya sa ta fadin haka saboda Dr Fahad yafi karfin godiyan fatan baki a wurin ta. Girgiza ma ta kai yayi yace “ki daina min irin haka Suhaima ban so” saurin gyade kai tayi, alaman gamsuwa da kalaman na shi.
“Ina Amarya?” Ta tmby cikin siririn muryar ta. Shi mamaki ma ta bashi, a halin nan da ta ke ciki har ta iya tmbyn wani? Share zance yayi da cewa “ki cigaba da addu’a kaman yanda kike yi sannan ki fawallah wa Allah sauran, mu ma muna yi kuma in sha Allahu za a dace” da kai ta amsa shi, dai dai lokacin dan sandan da ke tsaron wurin ya zo sanar mu su lokacin da aka diba musu ya kare. Murmushin yaki ta aika ma Dr Fahad, ba tare da cewa komai ba ta juya domin komawa inda ya zamar ma ta matsugunni a yanzu. Idanuwan shi na kan ta har ta bace, yana mai cikin dimbin tausayi da son ceton ta ya fito daga station in. Already, sun hadu da Barr Mustapha tun shigowan shi Abujan. Gidan Ummin shi ya nufa domin kai gaisuwa a gare ta zuciyan shi fal tsoron wani irin tarba zai samu, tunda su kayi aure da Rufaida ya ke fuskantan matsaloli daga wurin ta. Har yau kafan ta bai taba taka gidan shi ba, kulan shin da ta kan danyi ma saboda sa bakin Daddyn shi ne. Ranar da ya kawo Rufaida wurin ta kuwa sai da yayi kwallan bakin ciki, ko gaisuwan ta a fizge ta amsa daganan ba su kara ganin ta ba sai kanen shi su Zahra da su kayi ta hidima da Rufaidan. Da yayi tunanin yanda Dada ta ke mishi sai da yaji kaman ya nutse don kunya, amma da ke ita Rufaidan ta sa dawan garin sai Ba ta wani sa abun a ka ba.
…
Eden island,
Seychelles.
Zaune ta ke daga gefe guda a open restaurant in da ke kusa da pool in hotel in. Wannan karon ne ziyarar ta na biyu zuwa kasan da ta kira da kasar baiwa, sai dai ta kasa daina kallo da jinjina ni’iman ubangiji da yayi shi cikin tarin ni’imomi. Mafi yawan bakin da ke wurin wandan da su kazo honeymoon ko kuma dai masoyan da su kazo shakatawa. Yeah, the weather is totally good for them, kaman dai abinda ake cema weather for two. Haka kurum ta ke jin wani iri da ya kasance ita daya ne a irin wannan wuri ba tare da kowa nata ba. Wani irin kadaici ta ke jin ya mamaye yayin da ta ke kokarin danne shi da cocktail in da ke gaban ta, a yanda ta ke jin ta she seriously need someone to share those nice moment with her. Har ga Allah, ba za ta tuna when last taji abinda ta ke ji ba, ta dade da cire namiji daga cikin rayuwan ta, ta kulle su daga babin tarihin rayuwar ta gabadaya. Namiji y riga da ya mata illan da ba zata taba iya warke wa ba, shiyasa ta yakice su daga alamuran ta.
Tana cikin tunanin na ta ne ta hango shi yana taho, cikin tafiyan shi mai burgewa. Za ta iya cewa ita kadai ce yar Nigeria ba haushiya a wurin amma kuma duk da hakan tana da tabbacin ba ita kadai bace idanuwan ta ke kanshi. Yau ma sanye ya ke cikin kananan kaya, gabadaya navy blue sai dai rigan yan da touch of white, hoodie ne wanda ta alakan ta hakan da sanyin da ke garin, sai facing cap in da ke kanshi da ke da touch of red. Kayan sun matukar amsan shi sai dai tunani ta ke kaman akwai abunda is omitted a shigan nashi.
“Hello dear, kina ta jira na ko” yana jawo kujeran da ke facing inta yayi maganan, ba tace komai ba sai murmushin da ta dan yi. Sai da y zauna daf da ita sannan ta gane glasses da ba bata gani bane ya sata tunanin he omit something. Fadada murmushin nashi yayi yace “Ya sabon yanayi kuma? Do you cope well?”
“I love the weather” ta amsa shi tana kara sipping in coffee in da ke gaban ta.
“Nice to hear, shi ya sa na ganki da katon jacket kenan da hulan sanyi” dariyan tsokanan tayi tace “It so nice duk da haka kaga da zafi ne mutum rasa in da zai sa kan shi zai yi”
“Kuma da gsky, as a Nigerians we have to appreciate this daman ai, so let talk about the business, are you in” dan shiru tayi kaman tana tunani, sai can tace mishi “wani irin business ne”
Dan dariya yayi hade da girgiza “mata mata dai, har business inma sai an ja wa aji? Don’t tell me you are getting customers a haka” yana maganan hannun shi na kan gemun shi yana wasa dashi, idanuwan shi kar akan ta ya ke maganan. Hakan da yayi ba karamin kara tafiya yayi da ita ba tace “no ai ba maganan jan aji a business, i just want to know what am getting myself into”
“Are you not an event planner? Ai ba zan nemi wani abu out of your field ba. Do you have event center back in Nigeria” gyade kanta tayi tana realizing yanda ya ke maganan shi natsuwa da ma’ana. “Vows a Abuja” ta fada tana ajiye mug in coffee inta da ya kare.
“You own Vows?” Mamaki ne sosai a kwance a fuskan shi, itan ma mamki ne a na tan saboda a zamanin na social media ba tayi tsamman akwai wani matashi da ke cikin Abuja da bai santa ba.
“Dole kika ja min aji, let do this please” ya fada yana dan marairaice fuska “okay” ta fada simply tana jiran me zai ce.
“My Friends are getting married here. Dukkan su biyu University mu kayi tare a Egypt, am more like the middle kingane ta dalili na su ka hadu. Dukkan su Nigerian ne sai dai ita a kasan Oman ta taso tun secondary school days inta. Har gwara ita ma saboda shi a Saudia aka haife shi bai ma taba zuwa Nigeria ba. This is her Dream place, so they decide ana daura aure a oman ranar za su taho nan ayi duk wani events in bikin su. The issue is they want a wedding of their tradition sai dai they have no any idea da zai sa yayi working, shine fa su ka taso ni a gaba na taho a cewarsu in bincika tunda am living a country in sai nazo a fara shirye shirye” murmushi sosai Umaimah tayi, kana kallon ta kasan tana cikin farin ciki. Ba banza ba jikin ta ya dinga bata zata yi missing opportunity in ta share shi, this is a good idea, shi kan shi sai da ya gane ta ji dadin bayanin da ya mata.
“What is the couple name?” Ta bukata
“Rawan nd Adam”
“You are in the right place” ta fada, already har ta bude system inta ta fara danne danne, shi dai bin ta da kallo kawai ya ke, he likes her fierceness, no wonder events in Vows is always unique. He sees determination in her.
“Tana da outfit ne?” Ta fada still tana ta faman danne danne.
“No, we are planning ayi ordering ready to wear”
Girgiza kai tayi saurin yi tace “we are ordering Bespoke, yaushe ne wedding in?”
“In Three weeks time” shi dai amsa ta kawai yake yi yana kallon yanda ta juye lokaci daya ta koma kan aiki.
“We have enough time, ina da Fashion designer in da za ta iya min a takaitaccen lokacin, i want to talk with the bride saboda in san test inta exactly, then she need to come with a makeup nd henna artist, kayan za a mana delivering ta jirgi. Sai caterers, i will guide them by getting the necessary ingredient so your only job now is to find an interior decorator da kuma caterers in but i want to try talking to Nigerians da su ka zo nan for tourism, experience is the best”
Sosai ta burge shi ganin yanda nan da nan ta hau aiki, kuma da alaman kware da mai da hankali a dukkan abinda ta ke yi “we didn’t even talk about the pay”
“This is a great opportunity for my career zamu yi maganan wannan daga baya”
Folding lips in shi yayi yana kare mata kallo “Rawan will be crazy in ta samu labarin ki, she madly wanted her crazy ideas to work sosai don kowa kallon craziness ya ka mata”
Dan ware idanuwan ta tayi tace “ni kuma i like her because she know what she want”
Dan dariya yayi yace ” sai dai she can’t talk in hausa and her English is not clear sosai, Arabic accent inta keeps affecting”
“Ba matsala” ta amsa.
“So let go for the shopping?” Da ido ya ke jiran amsan ta, lumshe idanuwan na ta tayi cike da tsantsan farin ciki ta mike tsaye “let go then”
…
“Tun daga ranar ba mu kara haduwa da su ba Faroukh ba sai Abuja, hatta Zayd ranar ya koma, bai wani kira ni ba ni ma kuma ban bi ta kanshi ba, don har na fara tunanin ko ya hakura da bukatan shi a kaina ne” Suhaima ce tsaye a gefen barrister tana cigaba da bashi lbrn da ta fara, yau duk yanda ya so ta zauna hakan ya faskara, sam ta ki zama. Hannun ta tasa duka biyun ta riko karfen da ke gaban shi
No 5 Maitama, Abuja.
Brown polkadot armless straight gown ne sanye a jikina, light brown Bf jacket na daura a saman gown in sai veil da na daura a kaina. Ko kadan ban damu da rashin yafa babban gyale da Zai rufe min jikina ba. A gate in vows nayi horn, nan da nan aka bude min gate in na kutsa. Bayan nayi parking a lodge, direct na nufi side in da office building in su ke.
Cikin natsuwa na ke tafiya ta, da ke tuntuni daman ni ba ma’abociyar heels bace, kullum ka kafata sanye na ke da flat shoes. Gaf nake da karasawa wurin elevator na hango shi tafe yana karasawo inda nake. Da sauri na budi ban dakin da ke wurin domin rakubewa, Sam Sam na manta cewa ban dakin maza ne a wurin.
Ajiyar zuciya na saki ina mai rokon Allah ya sa ya wuce da sauri “Baiwar Allah lfy?” Muryan Namiji da naji ya sani saurin juyawa cike da tsoro. Daram! Na ji a gabana sanadiyyan Wanda na gani tsaye a jikin zinc yana wanke hannu. Tabbas, wannan shine anyi gudun gara an fada gidan zago. Faroukh Usman ne employer in Zaid Al-mansur. Abinda zai baku dariyan shine El-yas na hango na ke ta ma wannan gudun.
“Sistern oga ko bake bace?”
Nodding kaina yi da sauri “Sorry Faroukh, am pressed ne gabadaya na manta ban dakin maza ne nan” ba tare da wani reaction ba yace “Eyyah, You can use the restroom tunda you are pressed bara in fita.” Bai kara cewa komai ba ya nufo kofa, matsa mishi nayi ya fita. Gabadaya jiki na rawa ya ke tsabagen tsoro, da kyar na iya kara yan mintuna kafin na fita.
A dai dai lokacin su kuma su ke wurin exit in building in. Elevator in na danna domin karasawa office in da ya kawo ni wurin. Umaimah Amin, Director’s Office. Shine a rubuce a jikin office in da na shiga.
“Hello cutee” secretary in ta fada tana gani.
“Mercy merci, the beautiful lady” dariya tayi tace “kwana biyu, my madam just call ko kin iso” cikin hausan ta da bata gama gwanancewa ba tayi maganan.
“Eyyerh, na dan tsaya kasa ne” na fada ina karasa bude office in director in.
Zaune ta ke akan office chair in tana ta fama rubutu. Sallama nayi ba tare da ta dago ba ta amsa. Wurin couch in da ke office in na nufa na zauna. Ba ta taso ba sai da ta kira mercy ta sanar mata ba ta son ganin kowa for 30 to 45 minutes.
Plain black bubu gown ne ke jikin ta, kwata kwata ba a mishi kwalliya ba, Kullum in ka ganta irin shigan ta kenan, ko atamfa ne kuwa in ba ta mishi bubu to play gown ne. Cikin kasaitar ta taso zuwa inda nake da kwantaciyyar murmushi akan fuskan ta, tafiyan ta kadai abun kallo ne. Kafin akai zuwa kyau da kwarjinin ta kuma. Irin dirarrin matan nan ne da komai yaji, jikin ta ya matukar amsan yanayin ta. Irin matan nan ne da ba kasafai ake taran su a musu magana ba. Kullum ka ganta she is always smiling. Umaimah Amin kenan, mace mai kamar maza ko ma ince wacce ta taka mazan kwazo da kokarin neman na kai. Babban Event planner ce da tayi kaurin suna sosai, The Vows, shine sunan event center inta. Event halls uku manya sosai da maidaidai ta guda biyu ke cikin vows. Bayan su akwai fili sosai, wanda ake organing event a open space a wurin har da ma wurin da ake na tent. Ba wedding event kadai ta tsaya ba, duk wani event in da ya taso ana booking a wurin ta. Yana yanda ta ke fidda decoration inta is always unique, she can be traditional ko kuma ta juya modern. Duk irin yanda kake son tsarin ceremony, in dai kama ta bayani to ko zaka sha mamaki. Tana aiki da different photographers, Videographers, MC, DJ, interior decorators and architectures. Banagaren abin ci da sha ma tana aiki da caterers da ma bakers kala kala. Akwai wanda suna karkashin ta ne tayi employing insu akwai kuma wanda suna zaman kan su ne, appointment ta ke signing. Aikin ta dai ta tabbatar event in ka is well organized. Bayan haka kuma influencer a social media, haka ya matukar kara mata suna kuma ya kara ma business inta farin jini. Ga ta akwai taimako, tana sponsoring yan uwanta dayawa.
Gefen kujeran da nake ta zauna, har yanzu dai da shu’umin murmushin a fuskan ta take kallo na. Bude hannayen ta tayi inviting me for friendly hug. “Baby na nayi kewan ki dayawa”
“Anty na kenan, nima nayi kewan naki ai”
“Allah baby?” Ta fada hade da rungumo ni for seconds sannan tayi pecking ina akan forehead.
“Na fa ga El-yas a kasa” ba a wurin Zaid na fara Sanin El-yas ba, shine dai bai sanni ba. Nan na bata labarin abinda ya afku a kasa. Kallo na tayi sannan ta kwashe da dariya “wannan ai ke zaki tona asirin kanki da kanki, Ya San me ya kawo ki nan? Ai da sai ki Fuske”
“Kin sanni akwai rudewa ne”
“El-yas ba mu da matsala dashi na sani amma sai dai Faroukh in, yana da surutu ne”
“Kai anya?” Na fada hade da girgiza kai.
“Faroukh Usman, zan yi bincike akan shi. Kinsan karamin obstacle sai ya zamo maka babba kafin ka ankare”
“Faree ta kira ni” ta cigaba “So ya ake ciki?” Lbrn gabadaya abinda ya faru tsakanina da Zaid na bata.
“Yanzu kun bar Lagos in gabadaya kenan?”
“Offer week POP in Amal, za ta koma Sunday ita kadai daga baya zanje sai mu dawo tare gabadaya”
Jinjina kai tayi tace “Gsky babe in nan tana ji da ke dayawa baby, anya kuwa? Can i trust her?”
“I promise babu komai Anty na”
Mun dade muna magana, wanda duk tana fada min yanda zan bi da lamarin Zaid Al-mansur ne. “Baby ki fa tabbatar tarkon ki ya danu kafin ta dawo Abuja”
Gyara zama nayi na sa kaina akan cinyan ta “ba ki da matsala dani Allah, komai zan iya miki Anty na” hannun ta dora kan kai na, sannan ta zare veil in, kanana kalaba ke kaina ta tusa yatsunta tsakanin su tana wasa da su. “To yaushe zaki zo wuse, dagaske nayi kewan ki fa”
“Zan zo ai amma sai Amal ta koma Lagos”
Al-mansur
Drinks shop.
Tun bayan gamuwar mu da Zaid a Lagos, ranar da Amal ta ke buge ba mu kara wani haduwan ba. Yau zaune na ke a specific office ina da ke cikin Drink shop in, kwanan mu uku kenan da relocating wurin gabadaya. Ban da wani aiki sai supervising in workers in domin tabbatar da komai na tfy dai dai. Sai kuma Satandard recipes da ne ke forming, inyi guiding in su. Sai na kasance kullum cikin browsing to gather more knowledge akan drinks in.
Knocking naji, kafin in amsa an bude kofan. Ban dago ba amma nasan Zaid ne, tsarin shi ne wannan. Balle ma ga sanyayyen kamshin turaren shi na kullum da kullum da ke tashi.
“Baiwar Allah barka da war haka” daya daga cikin kujeran da ke gaba na ya jawo ya zauna.
“Barkan mu dai Yayana” harara ya aika min mai tattare dace wa zaki sani.
“Babe ya maganan mu” tsare ni yayi da idanu sosai yake kare min kallo.
“Ai na dauka mun bar wannan zancen kuma yayana, ba zan iya ma Amal haka ba” murmushin da ke kan fuskan shi ya bayyana cewa yasan za ayi hakan.
“Zan so ki bar batun Amal domin mu fara fuskantan abinda ke gaban mu. Suhaimaa” jin yanda ya kira sunan ya sani dagowa muka hada ido, kaman kullum yau ma nice na yi kokarin janye nawa idon. Ban ni da rashin kunya na amma ina tsoron sharri kallon cikin kwayan idon mutum. idanuwa na dauke da wasu sirri na daban, yana fallasa mutum sau da dama ko da so boye abun da ke zuci.
“Kin ganni nan wlh ban iya sa abu a rai, in har na sa kuwa ina bin duk wani hanya da ya zo min domin samun wannan abun. Matsayina na ke so in sani a wurinki kawai domin shine muradi na a yanzu”
“Dan uwa na” nayi saurin fada, ina kokarin kara karantar yanayin shi. Ba kaman dazu ba yanzu murmushin ma kin fitowa tayi, “i need more than that please Suhaima” bance mai komai ya mike a hankali har ya karaso inda nake, gab dani sosai ya tsaya har ina iya jiyo sautin fitan numfashin. Dan durkuso wa yayi ya sa kan shi kan table in da ke wurin, hannuna da ke da kan table ya kamo da hannun shi ya rike tam yana murza tafin hannun namu a tare “ina so kisan ba wasa na ke miki ba jewel, i so much love you” a saitin kunne na ya ke magana yana kara manne jikin shi kusa dani. Wutan kai na gabadaya dauke wa yayi a lokacin, ina so in ture shi sai dai kuma nasan this is an opportunity. “Stop this please nifa kawar Amal ce” a hankali nayi maganan sounding so vulnerable.
“Kar ki damu nasan da hakan, for now ina son sanin matsayina a wurin ki kinji” a hankali yake magana yana kallon fuskana, idon shi duk ya marairaice, na kasa tantance gskyn shi a wannan lokacin. Basar nayi saboda ba wannan bane matsala a yanzu nace “recently, banjin wani abu da ban san shi ba akan ka” kara marairaice wa yayi jin amsan da na bashi yace “to ai nasani mana jewel, ni chance kawai na ke so ki bani mana”
Girgiza kai nayi nace mishi “but we don’t have to do this”
“We have to when i can’t control it” sai a lokacin ya raba hannu na da nashi, da hannun yasa ya dan shafo fuskana yace “my beautiful babe, we shall talk later”
Tun daga lokacin ya fara kirana a waya. Da farko ko ya kira ni zancen business mu ke yawan yi dashi, a hankali sai ya fara gangarawa gun inda ke mishi kaikayi. Sai ya gama sa na lissafo mishi estimate in customers in da ake samu per day sai yace min “Jewel wlh your voice is sweet” share shi na ke yi a dukkan wadannan lokuttan ina kokarin canja akalan hiran. “Ina jin dadin muryan ki sosai, kefa?” Murmushin kawai zan yi in kashe wayan ina mai girgiza kai da cije lebbe.+
Haka ma ku cigaba da kasance wa duk da Zayd bai samu wani Fuska a guna Ba hakan bai sa ya janye ba, duk in ya kira ni zan dauka amma ban wani biye mishi. Wani zuciyan ya kan ce min in share shi kawai sai dai wani na hana ni sanin abubuwan da za su biyo baya in na share shin. Zuwa lokacin kuma hakurin su Faree ya fara karewa, sau dayawa ta kan kirani tace min “Aminiya ya isa haka please mana, just get to action.” Tun ta nayi kadan kadan har complain inta ya fara yawa, sau da dama ina mamakin yanda damuwan ta akan Abun ya fi na Anty Umaymah yawa sai dai in share.
Ana gobe za mu je Lagos ni da Zayd in wurin Amal, Da yammaci likis waya na ya hau rururi da sunan da na sa mishi kan Screen.
“Kanwata please ki same ni a bakin Telecom company yanzu nan” bai jira nace mishi komai ina daukan wayan ya koro min bayanin.
“Okay ina dan wani aiki ko za ka bani 15 minutes?” Na amsa kawai saboda ina Neman Excuse in da zai gaji ya wuce. Shiru yayi har na dauka ma ya amince sai kuma naji yace “ke dai kin iya rigima, ai yanzu ma zaki dawo zo please kinji” bai jira na amsa wayan ba yayi saurin katse wa. Dole na na tashi na fita, ban ma kowa magana ba ko da na fito wurin shop in duk da sannun da su ke ta faman min. Staff daya ne yace min “madam are you going out”
“Yanzu zan dawo” nayi saurin amsawa na fita daga wurin gabadaya. Ina fita daga building in na hango motar shi a inda ya ce min, karasa wa wurin nayi kokarin yi ina kokarin kiran numban shi “Gani na fito fa” na fada ina kara karewa motan kallo, da ke tint glass ne kwata kwata ban hango shi.
“Ai na ganki” ya amsa sannan katse wayar, siririn tsaki na ja, ni kam har raina na tsani mutum ya kashe min waya ban gama magana ba bayan ni na kira shi.
Tun kan in karaso naga ya bude min kofan, shu’umin murmushi nayi bayan na karasa gun motan, a raina kuwa fadi nake “ko yau wannan da mai yazo?” Ina shirin shiga motan kaman ance in dago kaina, ido hudu mu kayi da Faroukh shi ma ya fito daga cikin Company in yana bi na da wani irin kallo, kallon da na lura tun ranar da mu ka hadu a vows ya ke bina dashi sai dai ko in bamu hadu ba. Tabe baki na dan yi sannan nayi shigewa ta motan na bar shi yana kallon direction ina har na rufo kofan.
Idanuwan Zayd gabadaya a kaina su ka dauka da wani irin kallo da ban cika ganin yanayi sai lokutta irin wannan in mu kadaice mu biyu. “Jewel, ya fama da aiki” ya fada yana kokarin kamo palms ina, ban ce mishi komai ba har ya hade fingers inmu a tare “what do you want to tell me, ina da ai…” Knocking in da naji je wanda ke fitowa daga setin window in shi ya sa ni yin shiru. Idanuwan shi ya juya zuwa wurin glass in, ba tare da sakin hannun mu ba ya sauke glass in. Faroukh ne tsaye a wurin, muna hada ido shi naji gaba na ya bada dam, amma dan karfin hali irin nawa sai naki janye nawa idon. Shine ya dauke idanuwan nashi wannan karon zuwa fingers ina da na Zayd da su ke hade. Sai lokacin na nakara na fara kokarin raba su, dam Zayd ya rike ya ki Baron hakan ya faru “Ya akayi Faroukh?” Naji Zayd ya tmby.
“Sorry Oga na ganka a ciki i want to give you the papers sai dai kafin na dauko na ga ka fito” magana ya ke yana miko papers in. Amsa Zayd yayi ya dan duba “Sannu Faroukh you did very nice, please help me ka ba secretary ina zai shigar min da su” handing papers in yayi back to Faroukh. “Okay, zan bashi” Faroukh in ya fada ba tare da ya kara kallona ba ya bar wurin.
Sai dai Zayd ya daga glass in window in sannan ya juyo ya raba fingers in namu, hannun gabadaya ya maida kan shoulders ina bayan ya dan matso yace “Kunyan Faroukh kike ji? Ba ki so ya ganmu tare a haka ba ko?” Yana maganan ne idanuwan shi na sauko akan nawa, tun da ya lura ban son hada ido da mutane to sai ba mu hadu ba sai yayi kokarin saka idanuwan shi cikin nawa.
“Please mana…” Bai bari na karasa ba ya cigaba da maganan shi “Ni kuma kin ga ina so kowa ya san mu tare, i want to show the world you are mine” yanayin da naga yana kallon cikin idanun ya sa ni na kasa resisting, saurin jan Veil in nayi na rufe rabin Fuska na ta inda zai iya kallo. “Mine, or are you not” yana maganan yana kokarin janye veil in ni kuma ina sa hannuna ina kare rufewa.
“Okay, yanzu kuma kunya ta a keji jewel?” Ban ankara bayana ya saki ni sai ji nayi ya fisgi motan da speed sosai. “Where are you taking me to?”
“Shhhh” ya amsa min daganan ko ban kara ce mai komai sai gudun da ya ke ta faman kwasawa a cikin Abuja. Tafiya yayi sosai don har ya fara barin cikin Abuja sannan naga ya gangara gefe titi ya hau wani da yayi cikin daji, Tafiyan mintuna basu goma sha biyar ba ya kaimu bakin wani katon gate da aka rubuta Degolden Resort na ga anyi carving a bakin gate in. Muna isa, wurin gate in ya fiddo musu wani card kaman gate pass ne suna gani aka yi saurin budewa ya ja motan ciki. Daga nan ma sai da aka kara tafiyan mintunan, daga cikin motan ina hango different Halls, shops sai dai duk a kulle su ke. Ba straight bane ba ma sai anyi ta kwane kwane ga yanayin wurin the more muna tafiya muna kara shiga daji daji. Mun wuce Basketball court, snooker table, Swimming pools, birds cage kala kala. ni kam na mujiyan na zuba ina kallon ikon rabbi a duk inda aka keta, shi dai hankalin shi na kan tukin da yake da kuma cool music da ke ta faman tashi a cikin motan tunda mu ka baro Al-mansur Telecommunication center. Na tafi cikin duniyan tunani naga yayi parking a gefe, kallo na yayi murmushi kaman zai yi magana kuma sai ya fasa, bude motan yayi ya fita nidai bin shi da kallo kawai na ke har ya zagayo ta saitin inda na ke ya bude kofan. “Bismillah gimbiya, ko in dauke ki ne?” Lokaci daya yayi maganan kuma yana miko min hannu shi. Basar dashi nayi na fito daga cikin motan ina kara kallon yanayin wurin da ke ciki da different flower species hade da bishoyoyi da ke ta faman kadawa. “Do you like the place?”
“Sosai ma, it so lovely” irin kallon da na ce yana min in muna mu biyu kadai ya bini dashi “I’ve never bring a lady here, you are the first”
Saurin bata rai nayi ina bin shi da harara “don’t you believe me jewel?” Sautata muryan shi yayi yayin da ya ke magana.
Nace “na yarda fa kawai dai naji ba dadi ne because i know you’ve taken them somewhere better than this” dariya yayi sosai yana kara gyara tsayuwan shi, folding hands in shi yayi yace “Bawan Allah Zayd, am so lucky ana kishi na” yanda yayi da fuskan shi ne ya bani dariya har na dan dara. “Ni banda wurin da yafi wannan a heart ina, tab kinsan matsayin place in nan a wurina kuwa? To Amal ma ban taba kawo ta wurin nan ba” Fara tafiya yayi yana maganan, da hannu ya min alama da mu je.
“What about your wife?” Dan cije lebe yayi yace “Jewel kenan to Amal ma nace ban kawo ta ba balle Amina”
“Don’t you love her?” Girgiza kai yayi yace min “She is my first love” dan zaro idanu nayi ina kallon shi alaman I need more of the story.
“Not now babe story for another day”
Wani wuri daban mu ka kara shiga kaman wani dan lungu don har ga Allah har na fara tunanin wani abun ya ke shirin min ga garin ya fara duhu duhu. Ganin kallon da na ke mai ya gane hakan, dariya ya dinga min nan da nan kuwa na daure, saboda karfin hali irin nawa.
Dan fili kadan ne karshen long lungun, ina ko daga kai na ciki karo da wani karamin hut, green plants ne aka sa aka yi decorating gaban shi da ta dan gefe gefe a jikin ga wani crystal light da ke ta sparkling daga ko ina na jikin hut in. Saurin runtse idanuwa nayi na bude su still na ga wannan hut in a gabana sai kace wani fairy tale because i can’t completely describe yanda wurin ya hadu, ga wani shiru, iska da natsuwa da ya mamaye wurin gabadaya. Shi dai yana tsaye a gefe na hannun shi aljihu yana ta faman smiling yayin da idanuwan shi ke sauke a kaina da dai irin wannan kallon da na ke ganin it specifically for me. “Muje ko” ya fada yana nuna min hannu, da kyar kafafuna su ka iya motsawa ba tare da gazawa ba zuwa gaban hut in. Sai da muka hau matakalan stairs wurin uku tukun mu ka hau gaban hut, nan ma crystal light in ne ta gefen inda mu ke taka wa ga kuma pink and red roses a ta kasan wurin da su ka hadu su ka ba ma wurin gabadaya wani romantic ambience.
Yanayin jikina gabadaya sai da ya canja, ina Jin wani fargaba hade da firgici na ziyarta na, ba Wai na tsoro ba Aa, tsoron abinda na sa kaina naji yana diran min. Hakanan na ciki gaba da bin shi muna tafiya har zuwa hut in shi, cire flat shoe in nayi kaman yanda na ga yayi wa nashi. Grass carpet ne shimfide a kasan wurin sai kuma wasu green pillows da ke zube a wurin gefen indoors Fairy Lights Da small poppy chandelier a saman hut in. Iya haduwa wurin nan yayi, ban karashe mamaki ne ba sai da muka karasa karshen Hut in ta back view. Ruwa ne zaune a wurin kaman wani ocean, Ashe gabadaya baya wurin Ruwana ga haddadun pebbles masu kayatarwa a wurin ruwa. Kaman wata yarinya da gudu na karasa kan stairs in da zai yi leading in ka wurin ruwan, biyo ni yayi yace “daga ganin ki kinyi wasa da ruwa da kina karama” saurin rufe idanuna nayi ina tunani lokacin da ya ke fadan. Share thought in nayi na bude idanu ina fuskantan wurin da ke gabana. “This is just amazing, like are we really in Nigeria” gyade kai sama yi sannan ya dan duko yace “I like seeing this happiness in you” sosai nayi dariya ina jin wani farin ciki na daban na mamaye ni.
“Jewel can you please close ur eyes?” Kallon shi nayi da alamun tmby “trust me” yace, rufe idanun nawa nayi ina tunanin ko dai ruwan ya ke so ya wulla ni ne? Hannu na naji ya jawo ya zira abu. “U can open” hannu nawa na bi da kallo wani irin sparkling bracelet na gani, shi ma hannu nawa ya ke kallo “I know it will look good on you” ban ankara ba naji ya riko hannun ya dan yi pecking kan bracelet in.
“Jewel i want to hear your opinion please kinji” with no idea na kalle shi yace “Wlh ina son ki, soyyayan da ban shirya ma ta ba, ina miki wani irin so ma dabban da ban san kalan ta ba sai akan ki. Da gsky na ke son ki Suhaima Adam Bello, i want you to be mine forever, i want to marry you mu rayu tare cikin aminci” daga cikin. Idanuwan shi na ke hango iya zallan gskyn abinda ya ke ambata min, idanun har sun rikide sun canja kala. Wani tausayin shi na daban na ji yana ratsa ni yayin da zuciya ta ke tafasa knowing i have to do this without feeling anything akan shi.
“What about Amal?” Na tmby ina jin wani zafi na daukan gabadaya jikina duk da ni’iman da ya mamaye wurin.
“In har kin amince dani i will tell her everything, I want her to know ba ita kadai ba ma kowa” yanda sautin maganan ne fita ma zai tabbatar ma ka iya zuciya abinda ya ke nufi kenan.
“Ba ka tunanin yanda zata ji?” Folding lips in shi yayi da hannun shi.
“Kedai ki bar min komai, I know Amal than anyone knows her. Nasan yanda zan bullowa abun” ita ma Amal in wani irin tausayin ta naji ya mamaye ni nan take, tabbas ba ta dauki matsayin Zayd a wurin ta abun wasa ba. “zan dan taba rayuwan ki Amal ina fatan za ki yafe min” a raina nayi maganan sannan na kalli Zayd nace “nasan zai jawo mana matsala kuma zai tsarwatsa abota da ke tsakanin mu na har abada. She won’t take this lightly”
Rike kanshi yayi yace “ina son Amal so na musamman saboda shakuwan da ke tsakanin mu da ita daban ne sai dai yanda na ke ji a kanki jewel in ban same ki ba to wlh zuciya ta za ta iya fashewa” Jan hannu na yayi ya dauka saitin kirjin shi ina jin yanda zuciyan shi ke buga da sauri da sauri. “Zan aure ki in kasance tare da ke cikin kowani hali Suhaima. Tun randa idanuna su ka ganki zuciya na ke dokawa da soyayyan ki tun ina kin abun har na kasa jurewa, it impossible dole na ke jin kasancewan mu tare”
Tausayin shi da yabi jikina nane ya sa shi tunanin zantukkan shi na kai wa inda ya ke so ya kai. Kara matsowa yayi daf dani ta yanda har muna jin hucin juna, goshin shi ya daura kan nawa yana kallona cikin idanu kaman mai son karanta na “Will you accept my proposal?”
Gyade kaina nayi sannan nayi saurin runtse idanuna, a yayin da jikina ke faman daukan rawa. “Thank you” yayi saurin fada hade da min light hug, for the first time in his life ya rungume ni. A duk sanda jikin wani Namiji ya taba ni sai nayi kokarin janye jikina sai wani tunani ya zo min in fasa in basar.
Mun dan jima a wurin har a kayi Sallan magreeb, mu ka tashi mu ka gabatar da Sallan da ke Abaya ke jiki na. Hira mu kayi sosai wanda mostly rayuwan secondary school in shi da University ya dinga bani wanda dukka ba a Nigeria yayi ba.
Sai wurin 8:00 pm mu ka bar wurin, Shopping ya kaini a Shopright, da ya lura ban daukan abubuwa duk abinda ya san ina so dan zaman mu ni dashi da Amal sai da ya daukan min da abinda bai san ina so ba. Kudi sunci Uban su a wannan ranar kam.
Za mu fita daga store mu ka kara cin karo da Faroukh, sai dai wannan karon tare su ke da El-yas. Wannan kallon banzan da ya ke yi min ya kara bina dashi, dauke kaina nayi zuwa El-yas mu ka gaisa faran faran.
Garam! Kake ji, wata yarinya ce ta shigo cikin store in da dan gudun ta kafin ta ankara har sun ci karo da Faroukh. Kallon banzan nan dai na ga itama ya bita dashi yayin da El-yas da Zayd ke faman mata sannu ganin yanda ta zube a kasa. Karasa wa wurin nayi da azma ina kokarin dago ta sai jin kukan yarinya mu kayi a baya tana kiran “Anty jala Anty jala” ganin mutane sun dan fara taruwa a wurin ya sa Faroukh daukan yarinyar yana dan jijigata, dago wacce aka kira da Zahran nayi ina mata sannu, da force murmushin da ke kan Fuskan tace “Nagode” zaunar da ita nayi akan chair in da ke dan gefe ina amsa security in da ke wurin. Kallo Faroukh ya bimu dashi kaman wanda aka sa dole ya je ya kawo ma ta ruwa yana ambatan “Sorry” amsan tayi ta kurbi ruwan da kyau hankalin ta gurin sister inta da tayi wani irin lafkewa jikin Faroukh “tun da kinsan na fadi ai sai muje mu nemo costume in yanzu, Yaruwa ko kinsan inda zan samu Costumes kinsan gobe hallowen a school gabadaya ta birkita min lissafi sai an nemo mata Sophia, the first costume a dole”
“Ba matsala muje ki gani” ce masu Zayd nayi zan nuna mata wurin, da ke ground building in wurin ya ke nan da nan mu ka isa. Luckly an samu costume in sai dai an cika mi shi price in da yafi adadin kudin da ke hannun Zahran.”
“Kin bani wahala a banza ni dai, gashi ma kudin da aka bani ba zai isa” tsaki taja tace “ma koma gidan hakanan ai” bare baki babyn tayi kaman za ta fashe da kuka. Surprisingly, Ciro debit Faroukh yayi ya mika aka cire iya kudin “lah ai da ka bar shi ma” zahran ta fada, murmushin gefen lebe yayi yace “kar ki damu” wani irin kallo na daban naga yana aika ma ta har ta mai godiya za su wuce nayi saurin tsaida ta. “Zahara can i get ur number?” Tsab ta karanto min su gabadaya. Ni ko ina zuwa wurin motan Zayd inda su ke tsaya dukkan su Ukun na mikawa Faroukh waya na “her contact” nace ai ko gabadaya su ka dara.
“Kin kyauta wa mutumina gsky” El-yas ya fada yana daga gira. Kaman ba zai karbi wayan ba sai kuma ya amsa ya dau numban. For the first and last time a rayuwan shi yace min “thanks”
Har cikin gidan su Amal Zayd ya kai ni. Da ya dan yi parking zan fita ya rufe motan yace “sai yaushe kuma za mu kara fita”
“Anytime, amma kar ka kara min bazata daga yanzu za ki dawo. a bude fa na bar office ina da bag ina da abubuwa a ciki” dariya yayi yace “ai kece kin iya daru, yanzu dai zan tafi amma zan kira ki in naje gida”
“Okay” na amsa ina kokarin bude motan sai dai still a kulle ya ke, juyowa nayi na kalle shi yace “won’t you say Good night to your babe?”
Dariya nayi nace “okay Good night bude min In tafi pls ma yi wayan” dariya yayi sosai yace “ke dai na gane so kike ki fita kar a ganmu tare a mota ko” ban ce komai ba dai, peck yayi saurin kai min kan cheeks yace “To Gud night” abinda na ke gudu dai dai lokacin aka fara knocking in glass in. Muryan Salim Yayan Amal ne ke cewa “Don me kake yi a mota tun dazu Wai” kin budewa yayi ya kalle ni a hankali ya miko min hannu Wai “shake me” saboda ban son rigima ya sa na mika mai hannu. Sannan ya bude motan gabadaya mu ka fito. Kallon mu Salim yayi ya basar. A daddafe na gaida Salim in sannan nayi saurin karasa wa apartment in Amal.Daren ranar da kyar na yi bacci ina tunanin ire iren abubuwan da su ke afko min a rayuwa irin tawa ba tare da na shiryawa hakan ba. Wani bakin cikin da duhu naji ya mamaye zuciya ta sanadiyan tunanin da na afka na wacce ta yi sanadiyar zuwa na duniya, Anty na wacce ban san a wani irin halin rayuwa ta ke ba a yanzun. Anya Anty ta min adalci kuwa? Anya ba ta da komasho a cikin irin rayuwan da na ke ciki a yanzu? Ni kam ina ji a jiki na da ta na cikin rayuwata har izuwa yau to ko ba abinda zai in fada cikin mugun rayuwa irin wannan.+
Da wani mugun ciwo kai na tashi washegari, da kyar na samu na hada tea na sawa ciki na kafin na nufi cikin gida domin gaida Mum, mahaifiyar Amal. Baiwar Allah zaune na same ta a dakin ta kan Sallaya tana ta faman azkar. Sai da na jira ta idar sannan mu ka gaisa, faran faran ba ta da wani matsala. “Mum akwai abinda kike so ne in samo miki?” Cikin fara’a tace “toh dan hado min tea sai ki hado min da wheat bread ina please”
Saurin fita nayi domin kawo ma ta abinda ta bukatan, irin matan nan ne da duk da yawan su al’adan shan shayi da asuban fari bai bar ta ba. Ta kan ce shi breakfast da wuri fa ba abinda ya kai shi mahimmanci, kuyi kokarin tashi kusa abu a cikin Ku in yaso kwa koma baccin na Ku da ya zame muku jiki. Ina son matan saboda ba ta da wani matsala illa mugun son yara da na ke tunanin shi ya jawo illa akan yaran na ta. Ba wanda ya wani dauka ta a cikin su, ga ta yanzu ciwuka na sa ta a gaba wanda duk na ke tunanin na matsalan yaran nata da ma wadanda su ke gidan ne ke sa ta a gaba.
“Mum jirgin mu zai tashi by 12:00 pm, zanje zamu dawo tare da Amal in sha Allah” alaman murna ne ya nuna akan fuskan ta sosai tace “to Allah ya dawo daku lfy Suhaima, ni kam kwanan ina mugayen mafarkai akan Amal da ke sa zuciya ta wasi wasi, nikam Amal na azkar kuwa ko karatun Qur’an kaman yanda na ke ga kina yi” shiru nayi kai na a kasa saboda har ga Allah ban so in mata karya, ni kaina na san sakaci da su yasa rayuwata cikin tangarda balle kuma Amal da sallan ma sai lokacin da taga dama.
Girgiza kai tayi tace “ni kam na yaba da halin ki amma yana da kyau ki dinga sa yar’uwarki kan hanya. Fa’idan kawance da mai ilimin kenan ai, a hankali a hankali sai kiga ta dau hanya”
“In sha Allah Mum” na fada kawai amma a raina ina tunanin yanda mu matasan yanzu ba mu iya wannan ba illa kallo da mu ke mishi a matsayin sa ido da shiga rayuwan mutum. If you are matured and responsible, to shine fa ka kasance ba ruwanka da rayuwan dan uwanka, everyone get to do what he likes and kai da kake tare dashi you have to respect his decision, wayewan fa kenan.
Office na fara zuwa nayi abubuwan da ya kamata sanin zan dan kwana biyu ban nan. Na kammala kenan kiran Fari’ah ya shigo waya na. Da ke na riga da na mike kuma nasan wayan nasan wayan da zamu yi da ita na bukatar sirri. Bakin window na karasa ina kallan waje sannan na ba wa kofa baya.
“Hello Aminiya kina jina?” Faree ta fada tana mai kwantar da murya. Bayan mun gama gaisawa ne ta ke tmbyn ya ake ciki da motive inmu.
Tabe baki nayi duk da daman nasan sanadiyyan kiran na ta “Komai ya tafi yanda ake bukata, Zayd Al-mansur is already on our trap sai dai ina son Ya shiga da kyau ne ta yanda ba shi da wani hanyan da zai zame mishi mafita” dariya ta kwashe dashi irin namu na yan duniya tace “Allah Aminiya yaushe za ki shigo ne? Ko kun riga kun lagos in ne?”
“Ehmm yau zamu da shi gogan sai after one week zamu dawo Abuja. In na shigo zan yi kokari in ganki sai kiji details in, Allah ya sa dai kina gari? Ba ki bi wani jirgin ba” yanzu ma shewa tayi tace “Dadi na da ke mutuniyar akwai hango abu, wlh ban Lagos ina Jigawa?”
“Jigawa dai Mutuniyata? Yau kuma nan Shegen garin ya jaki” tsaki taja tace “ai fa ke kuma dai, to ba ma shegen bane sai dai kuma shegiyar don wata hadaddiyar miya idanuwa na su kayi tozali” tabe baki nayi nace “To Allah kyauta, sai nazo”
Ina kashe wayan na juya, wa zan gani? Faroukh ne a tsaye cikin Office in, kallon da ya ke bina dashi ya isa tabbatar min sarai yaji dukkan abinda na fada a wayan. Ni tabbas naji karara kofa amma da naji shiru, sai na dauka an koma ne. Jikina ne gabadaya yayi sanyi domin ko shakka ban yi Faroukh yaji abinda na fada gabadaya, kaman wanda ake turo shi, to in ba haka ba, ni kam na rasa gane dalili.
“Oga yace in kai ki airport” kawai yace sannan ya bude kofa ya fita daga office duk da nasan akwai more to the explanation da Zayd ya mishi, tunda munyi dashi zai zo ya dauke ni ne.
A gajiya nayi da shirun da ke cikin motan, ga kuma wani guilt da ke cina da rashin gsky. “Kunyi magana da Zahra?” Na fadi maganan ko zan samu ya kauda waccan tunanin a ranshi, kar zuciyan shi tayi zafi a gaban zayd.
Kaman bai zai tanka ni ba, can kuma ko me ya tuna sai yace min “Tace meyesa ba ki kirata ba taga numbanki” A dake ya fadi maganan.
“Eyyah i will try calling her” na amsa ba tare da wani damuwa da yanayin shi ba.
“It better if you don’t” da mamaki karara a fuska na na juya ina kallon shi, karantar yanayin fuska na yace “Because i want you to stay away” yana fadin haka yayi shiru, nima ban ce kala ba sai shi in ya kara cewa “i already like Zahra kuma zan so r/ship inmu yafi haka nan gaba kadan so i will prefer if you stay away saboda having somebody like you in her life will be a bad influence to her, ni kuma zai yi tarnishing abinda na ke nema a wurin ta”
Tab! In da akwai sauran kokonton yaji waya na ko bai ji to yanzu gabadaya ya goge, Faroukh yaji conversation ina da Aminiya sai dai duk da haka ina ganin ya zake a maganganun shi. Kuma bazan dauka ba tunda dai ban shigan mishi rayuwa. “Am sorry if i of…” Saurin dakatar dashi nayi da babban murya nace “Ya isa haka Faroukh, ya kamata ka san right words in da za ka fadawa mutum. Ba ka sanni ba baka san manufata ba don haka you have no right ka dinga fada min duk abinda yazo bakin ka” tabe baki yayi yace “am saying the truth” banza nayi dashi saboda yanda na ke jin zuciya na tafasa tabbas in na tanka ba zai mana da kyau ba kwata kwata.
Ya na kaini airport bai tsaya ko jiran Zayd ba ya wuce. Sai waya na sa na kira Zayd in mu ka hadu.
“My jewel” ya fadada fara’an shi yana gani na, murmushin karfin hali kawai nayi mishi ina fadin “shine jiya ko kira bayan kace za ka kira”
“Am sorry babe, ban fa bar wurin Salim bane sai wurin 12, nasan you already sleep kuma” turo baki nayi na juya kaman nayi fushi in nan.
Leko fuska na ya dinga yi yana dariya “to ba nace kiyi hakuri ba? Ai shknn ko babe a min afuwa please ba zan kara ba” kara hade rai nayi “dariya ma na baka ko?” Hakurin dai ya dinga bani har na sake na juyo yana ta tsokana wai ashe na damu dashi, nima ko biye mishi nayi nace “to daman wa ya isa yaki ka, kawai saboda Amal ne daman”
“Kar ki damu soon wannan tunanin zai zama history my jewel” ba mu wani dade a wurin ba jirgin mu ya daga zuwa birnin ikko. Ko a jirgin ma hadaddiyar soyayyan shi ya dinga nuna min, yanda ya ke min sai kace wata kawai. Wlh Zayd ya iya soyayya kaman turawan da ya zauna tare da, lallai dole Amal ta afka dayawa.
Ko da muka isa Apartment in, Amal bata nan. Nace mishi ina jin yunwa tun tea in da na sha da sassafe ban kara cin komai ba “bara in je in nemo miki abinci, what do you wanna eat babe” girgiza kai nayi na dan turo baki “Ni na gida na ke so”
Kallo na yayi kaman ya cinye, yaja ni dakin da na ke sauka “kwanta ki huta to babe bara in sama miki wani abun” ba musu na nemi wuri na kwanta, shi ko ya dau apron yayi kitchen don har bacci ya fara deba na duk da ma fast food ne ya yin.
“Muje in baki a baki ko babe” hararan shi nayi “in Amal ta shigo fa?” Ba tare da wani damuwa ba yace “kinga shknn ma, na huta dogon speech in da zan ba ta tunda ta gani da idanun ta” rufe baki nayi “rufa min asiri” a bakin ya bani kuwa cike da nuna min zallan soyayyan shi, ni kuwa ina kara narke mishi duk da tausayin da na keji na gauraye dukkan jiki na. Domin na san so, na san menene shi. Ban ko shakka irin wannan Soyayyan Zayd ya ke min a lokacin da ni kuma na ke jin zuciya kekeshe kaman wani dutse. Sai dai wani baiwa daya da nake dashi, am so good at pretending fiye da tunanin mutum ma.
Muna zaune a dinning Amal ta shigo, kaman na sani tashi na daga kan chest in shi kenan. Tana ganin mu ta rigo a gujen ta, jikin shi ta fada ta kankame shi sosai “i so miss you love” ta fada tana sumbatar left cheek in shi. Da ke yana facing ina ne ita kuma bayan ta na ke facing, sai nayi using wannan opportunity in na dan hade rai alaman ina kishin abinda ke gudana a tsakanin su. Da idanun shi ya dinga roko na na mai afuwa, sai ma na basar na mike zan bar wurin alaman da gaske na ke.
Ban san lokacin da Amal ta saki Zayd ba, sai dai ji kawai nayi ta riko hannu na “So Sorry Frnd, am so happy seeing him ne” dan bata fuska nayi ina kallon direction in shi nace “shine ni kuma a ka manta dani ko?” Ita kam har ga Allah ta dauka da ita na ke, side hug ta min hakan ya bani daman kara hada ido da Zayd, still ina iya hango neman afuwa a cikin idanun shi, dauke kai na kawai nayi.
Ita kanta Amal sai da ta dan ga canji daga wurin a ranar duk ko da yanda yayi ta kokarin kar ta gane hakan, amma fushina da na ke nuna masa in ba ta kallo yasa kokarin nashi faskara. Ranar, bai kwana a gidan ba yace mata akwai wani abu da yake son covering. yana fita abinda ya fara yi shine siyan sabin sim, ya tura mun mssg dashi nayi saving.
Muna dakin Amal ina taya ta dan tattare tattaren da ta keyi na barin garin, complain ta ke min “Frnd ni kam anya ba wani matsala da Bestie na kuwa?”
“Wani irin matsala fa ke da masoyin na ki kuma?” Mamaki na ara na daura wa fuskan kaman ban san komai akai ba.
“Kaman he is not himself yau in” wani tunani ne ya fado min, nayi saurin cewa “maybe yana da wani damuwa ne, kinga tunda mu ka baro Abuja haka na ganshi” dan runtse ido tayi ta bude “but we tell each other everything”
“Kar ki damu fa maybe kuma bai jin dadi ne, kila da yaji…” Ringing in da ya shigo wayana ya sani yin shiru, sabon numban nan ne dai da Zayd ya siya. Murmushi da na saki sai da ya sa Amal kallona, da sauri na suri wayan nace “ina zuwa Frnd” dakina na shigo sannan na dau wayan nace “kasa yaran mutane a tunani fa My Man”
“Allah ko? Suwa kenan?” Dariya nayi nace “ni da kawata, ina ta tunanin ka manta dani ba ka kirani ba, kawata kuwa tun dazu maganan ka take ta faman min”
“Oh Allah ni Zaidu gimbiya ta min hakuri to mana, tasan yanda Zuciyata ta kwadaitu da nin muryan ta kuwa? Jira kawai take gangar jiki ya kadaici sai ta danno muradin ranta” dariya nayi sosai “tou kai wa ya koya maka wadannan kalam a hausa?”
“Ai ni ban yada yare na ba jewel” daganan hira muka cigaba dayi dashi yana ta kara jaddada min girman soyayyan shi a gare ni. “Ina zuwa please Bestie na kira na bara ince mata bacci na ke saboda headache kinga sai ta kyale ni mu sha love inmu ko?” Ban ce komai ba, bai kuma kashe wayan nawa ba sabida ina jin sanda yace ma ta kan nashi na ciwo tun safe. Baiwar Allah sannu ta shiga mishi duk muryan ta yayi sanyi. Yana kashewa ya saki muryan shi ya cigaba da sako min zancen soyayya.
Bai dade ba Amal in ta shigo daki na “oh ni Frnd saurayi kika yi haka ake ta faman waya haka?” Sauke wayan nayi nace “Eh to kusan haka Frnd, am getting to know him ne ma” tafa hannunuwan ta tayi tace “wow! Finally kinyi admitting wani bf inki ne, i want to hear the voice of this lucky guy gskg” to fah! Ido ya so raina fata domin na san Amal ko kakayin maye ta ke sai ta gane muryan Zayd in “kar ki damu Frnd zaki san shi ma soon, kawai yanzu ina so in san kamun ludayin shi ne, kinsan mazan ba tabbas wlh sai kaje kasa an saba dashi ya maka halin yan duniya”
“Ke dai bari kowa ka gani case in kenan, maza sun zama abinda su ka zama. I feel lucky to have Zayd, he is different” tana fadin haka ta fita daga dakin, am sure zayd gabadaya yaji conversation inmu, maimakon yayi focusing kan abinda tace instead ce min yayi “Wato ni dinne ma baki san kamun ludayin nawa ba ko jewel?” Darawa nayi nace “ai gsky ne gayu ba tabbas”
…
Kusan kwana mu kayi muna waya, hakan ya sani baccin safe sosai washegari. Sai wurin sha biyun rana ya shigo gidan, nima muryan shi naji na fito falon saboda naji yana suna hira da Amal. Kaman yanda mu ka saba a da can haka muka gaisa dashi yana fadin “kanwata kenan sai yanzu garin ya waye miki don ba aiki ko?”
Amal na jin haka tayi caraf tace “Love ai bakasani kanwar ka Soyayya ya maida ta haka, jiya kwana tayi tana waya don haka ka shirya kunyi suruki” kallona yayi muka hada ido ya sakan min murmushi da wannan kallon nashi na daban. “Kanwata wai haka?” Gyada mishi kai nayi, yace “Ma sha Allah kice muna da shagali”
Tun daga ranar ya komo gidan, a boye mu ke duk wani abun mu inta fita kuwa yanda kasan mun samu duniya sabuwa. Sosai ya nuna min damuwan son fadawa Amal tsakanin mu, nina dakatar dashi, nace ya bari mu koma Abuja in yaso a can in, komai ta fanjama a san nayi. Hakan kuwa aka yi, sai dai duk dare zai baza musu kayan mayen su yayin kaman yana sha, sai ya tabbatar ta tafi duniyan ta ta fara bacci mai nauyi zai dauke ta ya kai ta daki ya kwantar sannan ya taho wuri na. Direct kan gado ya ke hawa ya rungume ni muyi ta hiranmu har muyi bacci sai na tashi asuba zai koma dakin ta. Ba abinda ya taba shiga tsakanin mu ba hugging sai kuma hannuna da ya ke yawan rikewa ko kuma ya shafa fuskana ya sumbaci cheeks ina sabanin Amal da na san ba abinda bai shiga tsakanin su ba.
Ranar POP inta da kanshi ya kai ni wurin Faree, da ke a gidan wata mata mu ka hadu da ita ni kuma nace mishi gidan friend ita ce. Ya ajiye ni akan zai je ya dawo.
A kayataccen falon na samu Faree kwance akan cinya wata hamshakiyyar mata tana susa ma ta kai. Tana gani ta dago tana fadin “Mutuniyata kin karaso kenan?” A daddafe na amsa ta sannan na gaisa da matar da ke ta faman kallo na kaman ta ga wani abinci. Lura da hakan Faree tayi ta dage ta daka ma ta duka kaman wata sa’an tace “Baby na kar muyi haka da ke mana” ban ce komai ba, Faree ta jani zuwa wani karamin falon, kaman gidan ta ta fita ta kawo min drinks da fruit. “Ban lbr mana Aminiya kin tsaya kina kallo na” tabe baki nayi nan na kwashi komai da ya faru tsakanin mu da Zayd na fada mata.
“Kin sanar da Anty Umaymah?” Kyabe baki nayi nace “kinfa san ban cika son zuwa wurin ta yanzu nan sai ta nemi ta sani yin wani abun da ban so” dariya tayi tace “kodai ta ji yar dake dadi ba, you are lucky ma abin ya fara fita akan ta irin irin ku ne dai ta kasa iya resisting” tsaki naja nace ba wannan ba “yanzu miye abun yi ne wai kuma?”
“Keep getting his trust da love har sai ya rabu da wannan Amal in koma ma samu muma hankalin ta ya dawo gare mu” girgiza kai nayi nace “Allah shirye ki dai Amina baki ga maza baki ga mata?” Tsaki ta min ta je “ke kika sani”
“Yanzu haka fa tare mu ke da Zayd in yanzu zai dawo ya dauke ni ma” zaro idanu tayi kaman kuma wacce aka tsikara tayi saurin tashi “ni dai ina son ganin zaid in nan Allah yau sai na ganshi face to face kuma naji voice in shi” ban ce mata komai ba sai gashi zayd ya kira ni na bita mu ka fita. Matan nan na dazu ina ce mata “zan tafi sai anjima” amma ina gabadaya hankalin ta na kan kalle min yanayin jiki, sai ji nayi Faree ta dau takalmi ta wulla ma ta, firgita tayi sosai. Faree ta bitada harara tace “wai ba na hana ki ba?” Murmushi tayi kaman wata mai cuta tace ma fari’an “Afuwan dear” ji nayi raina yayi cunkus nace wa faree “ita kuma wannan kaman wata sakara” dariya tayi tace “ba zaki gane bane ai ke Aminiya tun da kin ki hawa network dakyau, she is a sub dole tayi acting haka” share zancen nayi saboda i don’t want to hear more kuma.
Muna fita na ma Zayd knockin “dan fito please honey kawata na son ku gaisa”
Kaman wani sakarai yace “ta san tsakanin mu kenan” na amsa shi da kai, saurin fitowa yayi ya isa inda ta ke. Faran faran su ka gaisa, sai dai kallon da ta ke jifan Zayd in dashi ya sa ita ma ta koma min kaman wata sakaran kuma.
“Take good care of her” faree ta fada, sosai Zayd yaji dadin encouragement inta, makudan kudi ya fiddo a aljihun shi ya mika mata. Tayi saurin amsa tana godiya, ja wani tayi a kunne ta rada min “He is hot” girgiza kai kawai nayi na zagaya na shiga motan mu ka wuce.Washegarin POP in Amal mu ka hada dukkan wani abu mai mahimmaci da niyan tattara zuwa Abuja, domin cewa tayi ita kam zaman Lagos in ya ishe ta. Zayd ne ya lallashe ta mu ka zauna a cewar shi he got a surprise for herda zai faru a daren, hakanan ta hakura ta zauna.+
She is over the moon tana ta tunanin menene Zayd zai mata. Ni kam na riga da nasan menene saboda a wuri na ma ya nemi shawaran duk abinda ya ke bukata. Abinda kawai yace ma ta shine, ta shirya sosai in her best outfit. Nan naja ta mu ka tafi salon, tana da gashin ta baki mai sheki da tsawo sosai, so ma sha Allah. Don haka gyara kawai aka mata yayi wani irin mugun kyau, su kan su yan salon in sai dai su ka yi ta maganan yawan gaahin na ta. Nima ina da gashi na dai dai gwargwado kam, daganan aka tsantsara mana wani shegen unique make up da ban cika ganin irin shi, kudi ne yayi kuka a wurin. Duk yanda ake cewa make up yafi ma bakake kyau, sai dai na ga na Amal ya fita daban fiye da misali, wani mugun kyau ta min da duk yanda ake ta ce min nayi kyau kasa ganin nawa nayi. Da wannan na fara tunanin mai ma Zayd ya gani a wurina ne da ya ja ra’ayin shi har ya taka na Amal in? Maza dai sai a bar su kawai, ni dai nasan ba abinda zan nuna ma wannan baiwar Allahn duk da ko nasan na fita kugu da dan wasu abubuwa na jiki wanda na ke ganin su ba a bakin komai ba.
Sai wani irin murmushin farin ciki da jindadi ta ke, she couldn’t even keep quiet, tana ce min kila fa Zayd proposing inta zai yi sabida the last time da yayi proposing aka hana ta auren shi kusan hakan ya mata. Amma wannan karon alwashi ta daukan ma kanta babu wanda ya isa hana ta auren zayd in ba haka ba ko har suicide ta na iya yi. Sai da na girgiza jin yanda ta ke maganan da dukkan iya gaskiyan ta. “Ke yanzu za ki iya attempting suicide?” Kai tsaye tace min “my life has no meaning without his Frnd” tausayi ta bani, amma sai na daure na ce mata “amma kinsan ba kyau ko?” Tsaki taja tace “abubuwa nawa ne kuma ma rasa kyau mu ke aikatawa” nan take jiki na yayi sanyi, ba shakka irin rayuwan da ta taso ta gani kenan, sabili da cudanya da musulman mu su ke da turawa, yau da gobe dole lifestyle in su ya shiga kan ka. She is so use to abinda ta fada da babu any doubt ma a cikin sa.
Da tunanin abinda na ke aikata wa mu ka tafi mashayan da Zayd ke jiran mu, kokarin yaki da zuciya ta na ke ta faman yi. Hadewa sosai Amal tayi ranar cikin wata arniyar long mermaid armless sequins gown, dark blue ne with glittering silver stripes mai split ta baya, sosai ya fidda shape in jikin ta. Takalmi da jewelries ma gabadaya silver in ne sai ta kama gashin ta in a bun, yanda kasan model haka ta zama a ranar har idanuna sun kasa daukewa daga kallon ta, she looks so ethereal and luscious. Ban yi mamaki ba da tace min throghout her secondary and University life ita take winning beauty contest, sai dai ko in ba tayi signinng ba amma ba ta samun wata a gaban ta. Ga ta fara sal, hakan ke kara sa sau dayawa mutane ba su iya resisting kallon ta. Kyau kam ta sha shi har ta gaji.
Ni kam Sequin palazzo pant na sa da turtle neck top all in silver, kai na kuma na daura mishi sparkling half turban, shi ma silver in ne sai na zubo da gashi na baya kawai. Amal na ganina tace “wow friend kinyi kyau” murmushi kawai nayi, because i wasn’t in the mood balle ma na riga nasan duk kyan da zanyi ba zan kai rabin nata ba.
Ni nake driving motan nata, jefi jefi muna hira can tace min “Frnd wai ina zamu je ne? Bestie fa bai gaya min inda zamu ba”
“Kar ki damu kawai, mun kusa iso wa” na fada concentration ina na kan driving in da nake, dake nan cikin victorian island in ne ma nan da nan mu ka isa club in da a wajen shi aka rubuta Quilox.
“Me zamu yi a quilox? Amal ta bukata, ban ce mata komai ba sai da na bude kofan na juyo wurin, sauran kadan in ce mata “me kike zuwa yi da a wurin?” sai na fuske da kyar nace mata ” let just go and see” ita kanta sai da ta fahimci something is wrong with my mood.
Muna fara taka kafan mu bakin club in wurin ya dauki ihun “Gi-gi Gi-gi Gi-gi” in some very loud voices, lakabin da yawancin friends in Amal ke mata kenan “Gi-gi Amal” murmushi sosai ke kara deepining kan fuskan ta, tana shaking hand da mutanen da ke zuwa wurin ta suna congratulating inta on her NYSC completion, sai lokacin ta fahimci party in da Zayd ya shirya mata kenan, she couldn’t avoid been a little bit disappointed. Mostly, da su gama magana da ita su ke juyowa wurina “Hey dear pulchritude” da fake smile in da ke kan fuskana na ke amsa musu muna shaking hand. As more people are approaching sai ya zama na akawai mutane dayawa a tsakanin mu.
Ban ankara ba sai ji nayi an fisgo hannu na ana kokarin ja na zuwa wani direction, koma wanene nasan dai dai na ke dashi hakan yasa ban wani ji tsoro ba. Da ke dim light ne sai daga baya na fahimci zayd ne ke jana, yana ta kokarin matso da ni jikin shi sosai. Da saurina fisge hannu na saboda wani irin haushin shi da naji yana ratsa ni a wannan lokacin, my first instinct shi ne in kifa mishi mari saboda tunanin shi ya yaja min abinda na ke yi. “In ka kyale ni ai zan bika ko? You don’t have to keep pulling me” cike da tsiwa nayi zancen sannan kuma na karashe da guntun tsaki na.
Bai yi fushi ba ko kadan sai ma dariyan da yayi “jewel yau rigiman ake ji kenan ko?” Ban tanka shi ba sai ma wani kare hada rai da nayi. Rike da hannu na, focus in shi kuwa gabadaya a kaina cikin wani irin raunaniyar murya a hankali yace “shine rigiman har da bawan Allah Zayd za a ma wa koh? Wato dai babe na lura ko tausayi na ma baki ji” duk da naji ba dadi yanda yayi maganan, sai da naji wani tausayin kaina.
“We are in public kuma Amal is here” shrugging shoulders in shi yayi yace “who care? I just want to appreciate and feel your beauty, you look so stunning my babe kin ganki kuwa?” Tabe baki nayi na dan dauke kai, wanda shi a tunanin shi yana ganin am just pretending ne unknown to him har a zuciyana am not feeling well with him very close to me.
“Naji kuma nagode, is better you start looking for ur girlfriend now.”
Basar da zancen yayi da cewa “you are my girlfriend and am with you” kafin in samu daman magana yayi saurin hade jikin shi da nawa holding me so close to his chest “kin min kyau da yawa jewel, i can’t resist ur sight gashi mun yi anko” sai lokacin na kai idanuwa na wurin kayan da ke jikin shi. Shi inma sequins blazer ne navy blue and silver gliters, buttons a bude su ke hakan ya sa ake ganin V neck silver t shirt in shi da ke ciki, sosai ya kame jikin shi har ana iya ganin shattin packs in da ke adane a cikin.
“ka dai yi anko da girl friend in ka Amal” bai tanka ni ba ma sai ma wani hot kiss da naji ya bani a wuya na yana tabo gashi na da ya zubo baya da hannu shi daya dayan kuma yana kara manna ni da jikin shi. “Ina sonki sosai Suhaima despite all your rigima da rikici” duk da wurin da mu ke ba mutane sai da nayi kokarin fisge jikina daga nashi, a bazata abun yazo mishi shiyasa har na ci nasara.
Dariya ya min yana dan sosa wuyan shi yace “ni ko? Lallai babe kin ci tuwo” kaman ance in daga kai naga Amal na approaching in da mu da dan damuwa kwance a fuskan ta “ai sai ka juya ga bestien ka nan tahowa” ya so basar da zancen nawa, sai kuma ya juya. Suna hada ido a tare su ka sakan wa junan su murmushi, bai jira ta karaso ba ya taka inda ta ke.
Kallon juna su ka yi na seconds kafin yace “you look hot as always” wani blushing tayi a hankali ta matsa wurin shi sosai, a kunne ta rada mishi “all for you” wani wawan runguma ta mishi sosai har tana ajiyan zuciya. Hada ido mu kayi dashi, na tabe baki na juya saboda na lura kokarin min magana ya ke son ta idanu, ni ko ban son fahimta.
“Sun burge ki ne?” Naji an fada daga bayana, da sauri na daga kai dan ganin wanene. Oga Hafeez ne, kaman yanda naji Zayd na fadi ke ta faman washe min hakora. Tun haduwan dashi sanda su kazo tare dasu Faroukh ban kara ganin shi.
“Miss delicate skin” yana maganan ne yana kokarin jan hannu na, saurin matsawa nayi saboda duk duniyanci na a wannan lokacin ba kowani sharan na ke bari ya sa hannun shi a jiki na ba.
“Oh sorry” ya fada amma ina iya jiyo tsantsan duniyanci a muryan nashi.
“Ashe kana nan” kawai dai nayi maganan ne saboda ban bukatar wani tunani ya darsu a zuciya nashi.
“Nayi tfy ne shiyasa bamu hadu ba, ya drinks shop komai dai lfy ko?” Assuring in shi lfy nayi sannan ya cigaba da kokarin ja na da hira.
Daga wurin ina hango kallon da Zayd ke ta jifa na dashi, yanxu kam a zaune su ke a gefe kadan, Amal in tayi luf a jikin shi kaman hira su ke dan naga tana ta dariya.
Zayd ganin naki tanka shi, a zuciye ya dago Amal kaman jaririya ya sunkuce ta su ka nufi wurin bar. Hankali na gabadaya ya kama, hakan ya sa rabin abinda Hafeez ke fada ba jin shi nake ba sai ma na fara tafiya zuwa inda na ga sun nufa. Bina yayi yana fadin “can i have the special dance please?” Kaman in ce mishi Aa, sai kuma nayi saurin tunani “Yeah” na amsa ina daga gira.
Muna isa wurin ya dau tsit kaman ba mashayan nan da ke ta faman tashi to the sound of the music ba, a hankali wani cool music ya fara tashi sai ga waiters na kokarin table da ya sha varieties of flowers sai sparkling ya ke ta faman yi. Attention in mutanen wurin gabadaya wurin ya koma har a ka tsaida abun gaban su Amal da Zayd. Wani rantsatsen Huge cake ne a kai mai steps bakwai, cake in ya hadu iya hadu da bazan iya describing in shi cikin sauki ba. Green and white ne dai, da ya sha poundant da mini pictures inta a jiki sai stickers in make up product, ita kam akwai kaunar make up duk da ba wai ta cika zana wa fuskan ta bane. Happy successful NYSC completion, a ka rubuta a jikin cake in. Gafen cake in kuwa wata katuwar bottle in wine ne, girman shi har ya baci, gashi guda daya tak amma kana ganin shi kasan it worth a lot money.
Kallo abubuwan da ke gaban ta tayi sosai kafin ta juya tana kallon Zayd, da sauri ta bashi side hug tana blushing tayi pecking in shi a cheeks. “You are the truly the best one ever my bestie love”
“I love love” naji Hafeez ya fada, juyawa nayi ina kallon shi da tarin kwallan da ya fara cika min idanu, love is just wow if you are lucky to meet the one. “Are you crying” ban ce mishi komai ba na goge kwallan da ke shirin zuban min. Baki Hafeez ya fara bani unknow to him tunanin yanda zan katse wannan alaka ne ya min tsaye a zuci, ba shakka na san dole in sa aya a walwalan su dukkan su biyu kuwa kafin na bar rayuwan su. A lokacin na fara tunanin dalili na na jinkirta manufa ta kawai don ina jin tausayin su ne ba wai don abi komai a sannu kaman yanda na ke fadawa Aminiya ba. Sai dai bature ya ce the earlier the better, dole in ture duk wani emotions in da ke min yawa in fuskanci abinda ke gabana.
A tare su ka yanke cake in, sai da su kayi wasan shafen shafen cream icing in a fuskokin su, they look so happy together. Har inda na ke Amal ta jawo ni ta tura min cake in a baki, wanda da kyar na iya ci saboda yawan shi, tana ta min dariya. Lokacin mu ka hada ido da Zayd, na so karantar shi sai dai na kasa yin hakan saboda gani na ke kaman zai gano manufa ta in dai na cigaba da yarda muna hada idanu. Barin ma kallon da yake min a lokacin was so intense.
A lokacin aka fara rawa, da sauri Amal ta ja hannu Zayd su ka nufi filin rawan tana ta giggling abin ta cikin wani irin farin ciki na daban da ya bayyana a fuskan ta, har tsalle ta ke abin ta tana jin wani daban. Mugun sanyi jikina yayi ganin mood inta, rawa sosai su ke yi da Zayd, ba irin juyin da ba tayi a jikin shi ba. Alkawarin da nayi wa Hafeez ya sa nayi rawan dashi, mutane wurin sun yi mamaki sanin banda Zayd ban taba attempting rawa da wani ba. Ganin yanda su ke tafi suna faman mana kirari ni da Amal ya sa nasa jiki mu ka kwashi rawa da Hafeez, irin special rawan da na saba biyu. Daga ni da Hafeez in sai su Amal a tsakiyan wurin.
“Time for something special” aka fada a mike, attention in wurin gabadaya ya koma gun. Zayd ne ya amsa mike in ya fara magana “sorry everyone i am going yo distract you a little, i have something special for my bestie” yana gama fada ya amshi wani karamin gift box hannun Hafeez, Kallo na yayi sannan ya juya ya wurin Amal. Ni ya miko ma box in “please open it” ba tare da na kalle shi ba na amsa na fara kokarin bude yayin da yasa ta kulle idanu, ihun da wurin ya dauka ne ya sa ta saurin bude idanu tana fuskan tan abinda ke gabanta. Mouawad 1001 Nights Diamond Purse worth 3.8 million dollars ta gani a gaban ta. She was so shocked har ji tayi kaman ba a duniya ta ke ba na yan sakwanni ko motsi kasawa tayi, tafi wurin ya dauka rau rau rau.
Suman tsaye tayi a wurin tana kallon gift in, tasan cewa duk da kudin mahaifin ta ba zai saya mata wannan bag in ba, she watched the show ita da Zayd ranar da aka yi launching pursue, she was over the moon tana ta cewa ba ta san ya zata ji ba in ta wayi gari tana da wannan pursue in, she can do anything ma duk wanda ya bata wannan kyautan. Rasa abinda za ta mishi tayi, da ke kuma kwakwal war ta ya fara tafiya saboda wine in da tayi ta faman kwankwada. Kallon shi ta ke yana zama ma ta blurry blurry kaman zai bace ma ta, ba abinda ya fado kanta sai wani lokaci da yaso kissing inta in public taki. “i will love to take you in front of everyone ya san you are mine Amal” ba ta kara wani tunani ba tayi saurin crashing lips in su together so fiercly ta yanda ba zai iya resisting ba ko yaso haka. Hot french kiss su ke sharing a tsakiyan club in nan. Duk wani guntun doubt na Amal sai da tayi kissing in shi away a wannan moment in, kaman za su hadiye bakin juna, it was so intense da ya sa har su ka fara gogan jikin juna suna sakin numfashi a tare. Sound music aka saki a wurin nan da nan aka kara cuduwa ba irin kalan rawan da ba ayi ba a wurin ba tare da wani damuwa ba a fuskokin su, kowa abinda ke faranta mishi zuci kawai ya ke kallo.
“Can i get another dance?” Hafeez ne ke maganan yana bin dukkan jiki na da kallo. Murmushi dole na ara na daura wa fuskata. Slowly kuma na girgiza mishi kai. Da narkakkun idanun shi wanda su ka kankace saboda influence abinda ya kwankwada yace min “please mana miss gorgeous” folding hannu na kawai nayi ina kallon shi sanin da nayi ba nacin duniyan da zai yi ya sani bin shi a yanzu tunda banyi niya ba. Da karfi ya ke kokarin jan hannu na nima ina janyewa “Kar ki min haka mana? Kin san yan mata nawa ke aon ganin kansa a matsayin da kike” an zo wurin kenan, ban kaunar mutum mai girman kai, immediately nasan ba zamu taba shiryawa dashi ba. Nasan shi in mai kudi ne and he definitely not need to remind me of that.
“Na gaji, am feeling the weight of the world please allow me” duk magiyan da ke fitowa daga sautin murya na bai sa ya fasa sa hannun shi a jikina ba, wani bakin ciki nake ji yanda ya ke taba ni ba tare da wani tantama ba. Nasan cewa yau da a wuri mai mutunci ya ganni da shigan mutunci ba abinda zai bashi lasisin daura hannun shi a jiki na haka kawai.
Da dukkan karfin shi ya jawo ni jikin shi gabadaya yana fadin “it okay girl let us just cuddle to” fisge jiki na nake kokarin yi naji an ja shi gefe instead. “Oga don’t you see bata so? Please allow her mana, you can’t pressurize her ai” murmushin fatan baki yayi hade da cije leben shi na kasa, siririn tsaki yaja sannan yace “na dauka she is wise, exposed and civilized, why is she doing this kind of thing kuma”
A dan fusace zayd da ya fara harzuka yace “Whatever, you don’t have the right ka sa ta abu in bata so, interest always matters” in annoyance Hafeez ya balla mana harara dukkan mu biyun sannan ya wuce yana cewa zayd “we have to attend the meeting kayi postponing tafiyan ka Abuja” zayd bai amsa mishi ba, sai key da ya wullo min ya nufi hanyan waje.
A/N: How are you all? Anya kuwa ba zan canja sheka ba? 🤔 Gsky ban samun karfin guiwan da na ke bukata a wurin ku. Are you not reading the story? Or you are not enjoying it? Ina bukatan jin ra’ayoyin ku. Maganar gsky in ban samu abinda na ke bukata daga wurin ku ba i will stop posting ne kawai gabadaya, like i can’t even keep updating regularly saboda ban ganin comments inku.
Nagode.