“Kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii.”
Shine Karar take birki da driver yayi,motar dai tsohuwa ce da gani kuma an Dade Ana tafiye-tafiye da ita shiyasa tsufa ya kamata yanzu haka bacin ta Na uku kenan a hanyar tasu Wanda hakan ya tilasta musu tafiyar dare.. Take birkin da aka yi har masu bacci a motar sanda suka farka saboda a bazata suka ji shi wasu ko har buga goshin su suka yi jikin seat Na gaba ciki ko har da yarinya Yar budurwar da ba zata wuce shekara sha bakwai ba
“Wayyo Allah na”
Ta fada idanun ta Na cikowa da kwalla tana yarfa hannu saboda sosai taji zafin buguwa da tayi,matar da ke kusa da ita wacce zata Kai 45yrs ne ta harere ta tana cewa
“Wallahi duk da bana ganin fuskar Ki da kyau saboda dare ne kada Ki sake Ki mini kuka da wanne daya zanji da fargabar tafiyar dare koda shegen kukan banzan Ki kamar karamar yarinya maza Ki hadiye kukan ko naci uban Ki”.
Rintse idanun ta tayi da sauri jin Wai ko taci ubanta Amma bata isa tayi magana ba saboda tsananin tsoron matar da take yi kuma a yanzu duk duniya bata da kamar ta tunda tare suke Gashi itama harga Allah tsoron tafiyar Daren take yi haka kawai sai gaban ta yake mugun faduwa wannan dalilin ne ma ya Hana ta bacci a motar duk da dai yau kam Alhamdulillah da alama gab suke da Isa garin da zasu saboda yau kwana 2 kenan tafiyar taki karewa…tsaki taja ganin yarinyar ta hadiye kukan sannan ta dubi driver tana fadin,
” lafiya dai ko malam”.
“Wallahi ina ji taya ce ta yoye dole sai Na canza Wata”.ya fada lokacin da ya juyo yana kallon ta
” subhanallah cikin Daren nan,Gashi a daji muke Dan Allah Ka hanzarta mu bar nan tsoro nake ji “.murmushi Mai sauti yayi gami da fad’in
” kada Ki damu ba komai in sha Allah Ai Mun Saba irin tafiyar “.
Ya karisa zancen shi da bude kofar motar ya fita, ita ko kallon yarinyar tayi sai ganin ta tayi jingine da jikin kujera ta rintse ido Wanda ta tabbatar ba bacci take ba tsoro ne ya sata yin hakan saboda harga Allah dajin abun tsoro ne Gashi su biyu ne kadai passengers da suka rage..
” Dahiru dauko mana taya a boot da sauri”
Driver ya Kira Karen motar sa nan take ya fice domin cika umarnin uban gidan shi yana Kai masa sai ya tayasa suka sauya tayar motar sai yace Bari ya Dan taba Ruwa nan ya shige daji shi ko driver kuma motar ya kunna inda kafar shi daya Na waje daya kuma Na ciki nan suka zauna zaman jiran dawar Dahiru..
kamar daga sama sai jin karan bindigogi suka yi take jikin su ya hau rawa ko wannen su duk addu’ar da tazo bakin sa yake yi Dahiru kuma jin haka sai ya makale a inda yake domin tseratar da tashi rayuwar.. gani suka yi ‘yan fashi sun zagaye su ko wanne fuskar sa rufe da marks sai ido da wajen hanci ne a bude duk da dare ne suna iya gano su Wanda akalla sun Kai mutum bakwai nan suka janyo wuyar driver suka jefa shi waje cikin muryar su Mara dadin sauraro irin ta yan shaye-shaye suka ce
“Duk Ku fito a motar”.
Har kokawa wajen fitowa suke yi suna fitowa kuma suka zube a kasa kamar yadda suka ga driver yayi..shiru shiru ba Wanda ya sake bin ta Kansu sai sigarin su da suke busawa a kan su ita dai yarinyar har fitsari sai da tayi a jikin ta duk son kukan ta kuma yau ba baki,ganin sun koma can gefe sun mance da sune ya sa driver kokarin magana
” Oga”
ga mamakin su sai suka ji an sake bindiga suna juyawa kuma suka ga driver kwance ba rai a jikin sa saitin zuciyar sa suka harba hakan yasa suka sake shiga hankalin su kowacce zufa Na fitowa daga jikin ta cikin su ma ya rude gaba daya..sun Kai kusan 40mins Bayan sun gama shaye-shaye da bushe-bushen su sai suka Kama Mata da yarinyar suka hau tafiya da su sun yi tafiya kusan Na minti goma kan suka hango motar su nan aka jefa su a ciki suka hau tafiyar da tsam ba gane hanya suke yi ba gaba daya lamarin ya daure musu Kai shin In da gaske yan fashi ne Ai kudi zasu tambaya in ko yan kidnapping ne Ai gidaje suke zuwa ba tsayawa cikin dare a hanya ba..
Dahiru ko koda yaji sun tafi bai fito ba sai Bayan 20mins don gani yake kamar buya suka yi nan ya haska touch Na wayar sa jikin sa duk rawa yake yi don yana ga kamar zasu dawo sosai yayi kukan kashe uban gidan shi da suka yi yana jinjina rashin imani irin tasu da kuma tausayawa matar nan da Yar ta da suka dauka..
Tafiya dai taki karewa da kyar ta kare kasan wani katon dutsen nan aka fiddo su waje gaba daya baka hango ko alamar daki a wajen don da gani daji ne sosai..
ita yarinyar addu’ar cikawa da imani take yi saboda yau dai ta San dole rai zai yi halin shi ko kuwa….
Da sauri ta cire tunanin a ranta don in har suka ce lalata Mata rayuwa zasu yi to wallahi gwara kawai su kashe ta din..
Dutse suka Fara hawa Wanda da kyar suke iyawa kasancewar su Mata gwara ma ita yarinya ce Amma matar ba karamin wahala take sha ba don girma ya Fara kamata haka suka riga ture su suna jin ciwo su kuma tashi su cigaba da tafiya da kyar Allah ya basu ikon karasa karshen dutsen inda nan suka ga kangon kidnappers din yake don yanzu kam sun tabbatar kidnappers ne ba yan fashi ba dama sun San Nigeria Na fama dasu….
sun zauna sai dai tsam wurin ba haske ko fuskar su baka iya gani Amma dai wurin ya nuna tabbas an Dade Ana zaune wajen har ya dawo tamkar gida suma zubewa a kasa suka yi kowa da abunda ke damun sa…
Bayan Isar su da kamar hour 1 sai suka hura wuta tare da daura kaskon tuya sai da tayi zafi sannan suka yiwa matar alama da hannu tazo jikin ta na rawa ta nufe su sai suka ce ta zauna a kaskon da suka sauke,tabbas ta san gasa duwawun ta zasu yi za kuma ta sha azaba amma saboda tsoron su mata yadda suka yiwa driver sai ta zauna tare da sakin razanenniyar kara tana kuka tsakanin ta da Allah ganin haka yasa yarinyar ma fashewa da kuka aiko mari suka ringa kai mata a fuska take bakin ta ya kumbura dole ta hadiye sauran kukan don azaba, matar ko har yanzu bata daina jin azaba ba duk da kayan da yake jikin ta ganin haka sai suka koma wajen zamar su suna harkar gaban su Na shaye shaye da hira cikin yaren su Wanda ba Hausa bane.. bayan irin 1 hour lokacin kaskon yayi sanyi sai suka ga duk sun baje sai bacci suke Gashi basu ce da su komai ba kuma basirar daure su bai zo musu ba da yake suna ganin ba iya sauka zasu yi ba kasancewar su Mata..
ganin fa kamar da gaske bacci suke yi yasa matar tura kafar ta gaba ta kuma dawo da shi baya basu farka ba,karfe ta kuma bugawa taga ba Mai motsi cikin su saboda kwaya da suke sha basu ma San tana yi ba Kama hannun yarinyar tayi suka mike a hankali nan suka Fara sauka dutsen Wanda zuwa yanzu cinyoyin su da kafufun su sunyi tsami da kyar suke iya sauka kuma sun tabbata in sun Kama su to mutuwa zasu yi sai dai koma yaya ne ya zama dole su bar wajen kan su farka in har suna son tsira da rayuwar su aikuwa ba karamin azaba suka sha ba kan su gama sauka nan suka Fara jefa kafa duk inda suka samu cikin Daren ba tare da sanin ina suka dosa ba su dai tafiya kawai suke yi haka ko suka kwana tafiya kan gari ya Waye gaba daya sun galabaita Amma ganin tsam ba alamar mutani a kauyen sai suka cigaba da tafiyar har sai wajajen 9 Na safe suka shiga kauyen da akwai mutani nan suka nemi Ruwa suka sha gaba daya sun koma kalar tausayi daga nan suka tambayi inda Tasha yake aka sanar da su Kai tsaye Tasha suka nufa saboda dama ita bata sa kudi a purse a kashe ni Ka dauka take Sawa direct motar Kano suka shiga abinci ma sai a hanya suka ci duk Wanda ya kalli yarinyar ko sai yaji tausayin ta saboda galabaituwa da tayi Gashi idon jazir ya dawo don wahala ga bakin ta har karkashewa yayi ..
Yau din ma dai kusan dare suka yi a hanya Amma sun isa inda suke so da yake an San da zuwan su cikin Daren aka budo musu kofa Ai kuwa sosai aka yi murnar ganin su take aka basu abinci Kala Kala ita dai matar cikin dare taje chemist aka hada Mata magani yarinyar ce dai ba wacce tabi ta kanta nan suka kwanta don ba abunda suke bukatar yi fiye da bacci duk da zuwa yanzu bakin yarinyar ya kumbura sosai..
Koda asuba tayi da kyar suka iya sallah sannan suka koma bacci kan su tashi matar gidan ta fice wajen aikin ta saboda tasan dole suyi hutu sosai..ranar dai yan Gata suka zama don bacci suka wuni yi sallah kawai ke tada su basu wani damu da abinci ba kam duk da bakin ta Na Mata Zafi sosai sai dai tayi ta Zubda kwalla, Bayan baccin ya bar jikin su ne matar ce ta Fara yi wanka kan yarinyar.. Koda ta shiga wanka zama tayi kan dutsen wankan dake bandakin ba tare da ta cire Kayan ta ba, a zahiri bucket Na karfe da Ruwa ke ciki da cup Na wanka ta zubawa ido Amma a badini kuwa tunani take yi
“Ya Rabbi wacece ni daga ina nake gaba daya duniyar ta fice mini a rai komai ma ba son shi nake yi ba,Na rasa dalilin da yasa bana iya tuno komai a rayuwa Na sai suna Na Wanda shi din ma banda tabbacin haka ne,banyi hatsari ba bare ace kwakwalwa ta ta samu matsala Na kamu da ciwon mantau,shin banda iyaye ne ko dai ni din marainiyar ce ?” In ko ina da su meyasa ba Wanda ya taba nema Na, to ko dai shegiya ce ni in ko haka ne ai dole zan tuna baya na..wai ko da uwa ce ta mini baki kamar yadda kowa ke fadi inko haka ne na tabbata tsinenniya shiyasa kullum bala’e da fitina basu da wajen zuwa sai waje na,Gashi yanzu baki Na ciwo yake Amma saboda rashin Gata da asali Na rasa me saya mini magani.
Hawaye ta shareda Bayan hannun ta tana Mai Jan hanci da kuma jinjina wannan lamarin a ranta haka kawai ace mutum bai iya tuna komai sai sunan shi Wanda shima ba tabbas akan ta wannan wace iriyar kaddara ce iya sati biyu da suka wuce a rayuwar ta zata iya tunawa..ganin ba inda tunani zai kaita a hankali ta Fara cire Kayan jikin ta tana makalawa a katangar bandakin sannan ta wanko inner wears nata tare da gasa bakin ta duk da tana jin Zafi haka ta daure daga bisani tayi wanka sanin dama ita din ba kaya ne da ita ba duka duka basu wuce Kala hudu ba Gashi sun Bari a motar inda yan kidnappers suka riske su dole kayan jikin ta ta mayar tana fitowa ne ta karewa gidan kallo madaidaici ne yana nan dai bana masu kudi ba haka zalika bana talakawa ba sai dai da ganin gidan macece ke rike da shi Kai tsaye zata iya cewa gidan ba Na miji..alwala tayi jin an Fara kiraye-kirayen sallah’n magrib nan ta gabatar da sallah’n a brander’n dakin saboda akwai hasken Nepa a wajen sannan ta Nade sallayar tayi ciki saboda gudun kada sauro su gama da ita a waje tunda bata da Mai saya Mata magani.. tana shiga ta takure waje daya ganin matar gidan ta dawo Hala lokacin da take wanka ne kuma ta shigo da alama kuma labarin abunda ya faru da su aka bata saboda taji tana cewa Allah kiyaye gaba
“An wuni lafiya”
Ta fada Wa Mai gidan
“Lafiya kalau”
Ta amsa tana Mai kare Mata kallo sannan ta mayar da kallon ta ga matar da suka zo tare tace,
“Larai ita ce ko?”
“Ehh ita ce ina fatan ta miki?”
Kallon yarinyar ta kuma yi a Karo Na biyu sannan ta sauke numfashi tace
“Eh ba laifi Amma sai nake ganin kamar tayi yarinya”.
” ah Haba shekarun ta 17 fa ba wani yarinya baki ga ma tana da halittar girma ba Ki bata nan da shekara biyu cikekkiyar budurwa zata zama”.
Ita dai tana jin su Amma ta kasa cewa komai sai da ta tsinci muryar matar tana fadin,
“Meye sunan ki”?”
“Laylerh”.
Ta fada kanta a kasa murmushi Mai sauti taji matar tayi Wanda ya sata dago kanta ta kalli matar sai ji tayi tace,
” Larai jira Na dauko miki kudin Ki Na San gobe zaki wuce”.
Washe baki tayi kamar gonar auduga tana fadin “Ai kuwa”..
“Ya ilaheee kenan saida ni aka yi innalillah wannan din kuma wace ce Shikenan haka rayuwa ta zata kare Na zama kamar kwallon kafa duk Mai bukata zai buga”
Larai din ma tsintar ta tayi a hanya sati biyu da suka wuce nan ta ringa rokon Larai da ta taimaka Mata da kyar da dauke ta don duniya ba tabbas Ai kuwa ta gwammace yawo a titi da wahalar da Tasha a gidan saboda wanka ne kadai bata yiwa Larai kuma abinci ma sai ya game ta take bata..
Bangaren Larai din kuma ta kan yi safarar Mata a boye Wanda da yaran talakawa kawai take yi Gashi dama tayiwa Kawar ta alkawarin kawo Mata yarinya shiyasa da Allah ya hada ta da Laylerh ta karbe ta ta kawo ta ba tare da sanin ita Kawar tata nan zata ajiye ta ko gaba ita ma zata saida ta ba…
Fitowa tayi da kudi masu yawa ta mika Mata nan tayi godiya ganin matar ta fice a daki yasa ta kallon Laylerh daga sama har kasa tana fadin,
“Saura kada kiyi biyayya wallahi uban Ki zata ci don ta fini Zafi Anya ma ba uwa bace ta miki baki Kika shiga duniya saboda kullum cikin fitina kike nima Gashi yanzu ya Fara shafana Ai gwara Na bar Ki a nan nayi gaba kan rayuwa ta ta hallaka”.
Ita dai Laylerh ido ta zuba Mata ta kuma fahimci duk duniya ba zagin da Larai ta iya fiye da cewa zata ci uban ta duk da kusan kullum tana fada Mata Kalmar yafi a Irga Amma duk sanda ta fada sai taji Zafi a ranta..
” kallon fa?mayya kawai wallahi kuruwata daci Gare shi yafi karfin Ki don ni wallahi idanuwan kin nan tsoro suke bani”.
Kasa ta sauke idanun ta don Allah ya sani tana tsoron Larai kusan kullum sai ta duke ta tsaki Larai taja gami da diba Mata abinci cikin Wanda aka kawo musu ta tura Mata gaban ta kallon abincin tayi tana jinjina rashin imani irin Na Larai yau ko yaro Dan shekara uku Ai sai ya cinye ya nemi Kari bare ita da tasan da a kauye take tuni tayi Aure Harda yara..cin abincin tayi don ba yadda ta iya sannan ta fitar da kwano tana kallon yadda Larai ke cin abincin gaban ta Wanda mutum biyu zasu ci har su rage..tana dawa tayi i’sha ta kwanta…
Washe gari da sassafe Larai ta gama shirin tafiya Bayan ta sallami kowa sai ta kalli Laylerh tana fad’in,
“Adai yiwa manya biyayya”.
Karon farko kenan a rayuwar ta ta fada jikin Larai ta rungume tana fashewa da kuka saboda ita dai Larai kadai ta Sani a rayuwar ta ture ta Larai tayi tana fad’in,
” munafuka su din ce miki aka yi ba mutani bane?”
Tana gama fadar haka ta Kama hanyar fita cikin kuka Laylerh tace,
“Allah kiyaye hanya”.
” Amin”
Tace saboda sanin wannan addu’ar tafi bukata a yanzu sannan ta fice abun ta..
Durkushewa tayi a wajen tana kuka Mai cin rai ko da matar ta dawo daga daka Larai kallo daya ta Mata Wanda ya sata hadiye kukan ta gami da mikewa..cigaba da tafiya matar tayi ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace,
“Ki shirya yau zaki Fara zuwa wajen aiki”.
” aiki”.
Ta maimaita a ran ta to wani irin aiki ne wannan da ba za’a tausyawa halin da take ciki ba a Bari sai ta warke sanin ba Mai bata amsa ya sata mikewa ta Debi Ruwa a buta ta wanke fuskar ta sannan ta nemi hijab ta saka da Slipper’s tana jiran fitowar ta..bata dauki dogon lokaci ba ta fito rike da handbag nata tana Mikawa Laylerh da wuri ta Karba ita ko Key’s da suke hannun ta ta rufo kofar da shi tayi gaba ba tare da tace da Laylerh ci kan Ki ba ganin haka ne ya sata bin Bayan ta da wuri suna fita ta rufe k’ofar da kwado hakan ne ya Dada tabbatarwa Laylerh cewa su kadai ne a gidan….
adaidaita ta tare tana fad’in Jan bolo suka shiga sai kallon yanayin garin Laylerh take yi Amma bata cewa komai,tafiya Mai Dan nisa suka yi kan taji tace a nan suna fita ta mika mishi kudi tayi gaba Laylerh na biye da ita suka shiga wani guri..
Ganin yadda kowa ke gaishe ta hakan ya tabbatar Mata da ita ce me wajen kenan a hotel zata yi aiki..hararar ta tayi gami da fisge jakar ta tana fadin,
“Mairo ga sabuwar ma’aikaciya a nuna Mata komai da komai”
Cikin girmamawa da tsoro tace,
“An gama ranki ya Dade”.
Sannan ta juya tana kallon Laylerh tana mamakin ina madam nasu ta samo wannan kyakyawar yarinya sai dai hanci ne bata da shi Gata karama sauran ma duk sun kalle ta kowa ya koma bakin aikin sa ita ko bin ko ina take da kallo ganin yadda kowa ke aikin wahala Amma bata ji komai ba saboda ta San ba mummunar hannu ta fada ba duk da bata da tabbacin iya aikin hotel din zata ke yi don tsam madam d’in bata Mata Kama da mutumiyar arziki ba tafi ganin kamar ita ma tana shafarar Mata irin Kawar ta Larai..
DOWNLOAD COMPLETE BELOW