MA’AIKATA CHAPTER A
Jakarta ta dauka ta shiga kitchen dinta wanda yake dan madaidai ci bashi da wani fadi sosai.+
kitchen cabinets dinta ta bude tana bincike ,da Alama wani abu take nema.
Nutela naga ta dauko her favorite, ta dan yi tsaki mtseww, kwalbar ta duba taga saura kadan.
Tana gama breakfast key din motar ta ta dauka , ta feshe jikinta da turare. ta kashe wutar kitchen da palor, ta rufe kofar Apartment dinta ta fita tana yar wakar ta tana juya hips dinta.
Sanye take da gown ta atamfa wada tasha stone work,, ta dan yafa gelen ta ,da purse dinta a hannu.
Na’ima kenan diyace ga wani Attajiri Alhaji ibrahim Giwa .
Ita kadai mahaifinta ya haifa, hakan yasa ita ce diyar da yake so fiye da kowa a duniya.
Na’ima yar asalin kasar Nigeria ce, mahaifiyar ta kuwa yar kasar Niger ce.
Mahaifinta bafulatanin yola ne.
Kyakyauwa ce ,ma’abociyar son turare , tana da jiki irin na models, black beauty ce, akwaita da yawan fara’a. Da girmama na gaba da ita.
Na’ima diyace mai son neman na kanta, kudi da gata da mahaifinta ya bata basu sa ta sangarce ba.
Tayi wa mahaifinta alkawarin sai ta nema na kanta, hakan yasa ta bar gida.
A yanxu dai Na’ima ta dawo garin Abuja ,ta nema apartment tana zaune ita kadai.
Amma lokaci-lokaci mahaifinta na zuwa dubata,Tare da mahaifiyar ta.
Na’ima yarinyace yar shekara 25 ta gama university din ta a kasar uk.
Ta karanta law.
Ta kuma samu aiki anan abuja, Wanda a yanzu dai, cikakeyar lawyer ce.
Tana da son karatu wanda hakan ne yasa babanta ke son ta sosai.
************************************
Tana fita wajan motarta ta nufa direct ta shiga.
Favorite song dinta ta kunna tana bin wakar, har takai gaban GTbank .
Shiga tayi da sauri don tana so tayi deposit na kudi a account dinta.
Tsayawa tayi tana jiran layi ya zo kanta.
Wani taji ya rungumeta ta baya, ta juya zatayi masa masifa taji yace shishssssh! Wato tayi shiru.
Kalon sa ta yi ,sai dai taji gaban ta na faduwa.
MashaAllah ta furta a cikin zuciyar ta, fari ne kyakyawan gaske, yana da pink lips, dugun hanci da manyan idanuwa wanda ya sauke su a kanta.
A hankali taji yace, don’t panic, ki bari na fitar da ke.
Kallon sa tayi cikin firgice, lumshe mata idanun sa yayi yace, muje kin ga mutane na kallon mu.
Shiru tayi bata ce masa komai ba har suka fita.
Bata San lokacin da ta kwantar da kanta a gefen ka fadarsa ba tana shakar kamshin turaren sa mai suna( Boss)
Tsintar kanta tayi da son qamshin.
Mutar sa ya bude yace mata ta zauna a ciki.
Ta bude baki tana shirin yi masa masifa yace shishsh !!
yasa dan yatsan sa kusa da lips din ta.
Shiga tayi ranta a bace ,tace halan kai din kidnapping dina kake son yi?
Marwan najin ta fadi haka ya bushe da dariya, yace mutanan duniya sun kare ne da zanyi kidnapping din ki?
Turo bakin ta tayi, tace what ever, tana yarfar da yatsonta, irin yadda yaran turawa suke yi.
Paper ya samu ya rubuta wani abu ya mika mata.
Murguda masa baki tayi.. Kafin ta karba budewa tayi ta karanta.
(Am sorry, I touch you, but I did wat I did to safe you from embarrassment, you have stain on your cloth)
Ya salam Na’ima ji tayi kamar ta nutse don kunya.
Kallon ta yayi, yaga she’s uncomfortable.
Zan kai ki gida ya fada yana kallon ta,idan ba zaki damu ba.
No thanks, Na’ima ta fada Tana kawar da kanta.
Murmushi ya mata har dimple dinsa ya fito.
I came with my car, Na’ima ta fada cikin sauri.
Dan kwalin kanta ta cire ta daura a waist dinta ta kara daga gelenta ta fito tace thanks for your help.
Kallon kanta yayi,.
Ya salam! MashaAllah ya furta. A duniya yayi yawan kasashe da dama, yaga mata masu dugun gashi, amma sai ya tsinci kanshi da son gashin ta.
Na’ima ta kalle sa lafiya?
Murmushi ya mata yace, ki rufe …
A lokacin Na’ima ta gane gashin kanta yake kallo, wanda ya zubo har gadon bayan ta.
Sauri tayi ta rufe da gelen ta tace sai anjima.
Aisha! Marwan ya fada.
Juyowa tayi ta na kallon lips din sa wanda tun lokacin da ta fara ganin sa suke tempting dinta.
Astagfurullah ta fada a zuciyarta.
Na’ima, yusuf! sunana Na’ima, ta fada tana murmushi.
Dariya yayi yace.
Marwan, sunana marwan not yusuf
Your phone number pls?
Kada kanta tayi tana duba agogon hannunta, kana so nayi latti ne?
Ta fada cike da shagwaba tana langwabar da kanta.
Cike da yanga da jan aji ta zo gaban sa.
Biro ta dauko daga jakar ta, hanun sa ta rike ta rubuta masa number din ta a tafin hannun sa tayi tafiyar ta
Kallon ta ya shiga yi har ta bace masa.
Karar wayar sa ce ta dawo masa da tunanin sa.
Hello mami, ya fada yana yar shagwaba.
Toh mami ina tashi daga aiki zan zo inshaAllah.
Toh ki gaida baba, yana fadar haka ya kashe wayar yana murmushi.
Agogon hanun sa ya kalla ya dan yi tsaki mtswe, for the first time yayi latti zuwa wajan aiki.
Shiga motar yayi, wani sanyi yaji lokacin da ya shaki qamshinta, Wanda yana nan har a lokacin.
Shakar qamshin yayi ya lumshi ido.
Ji yayi ya tsinci kansa da son kamshin ta.
Favorite song dinsa ya kunna ya tada motar sa mai kirar jeep, ya tafi wajan aikin sa.
Pls vote and comments!!Marwan ne rike da lab coat din sa a hannu yana sauri ya bar harabar asibitin da yake aiki.
Wata Nurse na gani da gudu ta kawo masa wayar sa, Doctor!
Ta fada tana maida lumfashin ta da kyar saboda gudun da tayi.
Ka manta wayar ka Dr. ta fada ta mika masa wayar .
Thank you ya fada, ya karbi wayar.
Yana duba wayar yaga misscall din Mami har biyu.
Murmushi yayi ya mayar da wayar aljihun sa.
Ajiye lap coat din sa yayi a bayan mota,
Yana shiga motar,
yaji kamshin Na’ima murmushi yayi yana jin ina ma ace tana gefen sa suna fira.
Daga kansa yayi sama zuciyar sa ta shiga tuna masa pretty face din Na’ima.
He so much like her personality, her smile, and every thing about her.
What is wrong with me?
Ya fada a zuciyar sa, ni ke tunanin mace?
What is trying to happen to me?
Tun lokacin da ya dawo Nigeria bai taba ganin macen da tayi masa ba irin Na’ima
Itace irin matar da yake burin ya mallaka
Shes his dream girl,
tafin hannun sa ya bude yana tuna lokacin da take rubuta masa lambar wayar ta
Murmushi yayi kadan har dimples din sa suka lotsa
Key din motar yasa ya tayar da motar
ya kunna Qira’ar sudais
yana jin favorite surah din sa.
*suratul bakarah*
*******************************
Marwan umar, shine asalin sunan sa.
Marwan dane ga governor na jahar katsina .
Mahaifiyar sa hajia fatima wadda yar asalin garin Adamawa ce.
Marwan yaro ne mai kyauwon gaske, handsome I most say.
Yana da kanwa mace Amal.
Amal yarinyace yar shekara 23 a duniya, tana karanta pharmacy a kasar cairo.
Alhaji umar ,wato mahiafin marwan
mutum ne mai son jama’a kudin sa basu sa shi yaki yan uwan sa ba.
Mutum ne mai yawon taimakon talakawa, wadan da basu dashi.
Maihaifin marwan bashi da wani buri da yawuce ya aurar da Marwan,
amma marwan hakan baya masa dadi, har sukan samu rashin jituwa da mahaifin nasa dalilin hakan.
Marwan yaro ne wanda ya tashi cikin gata, bai taba neman abu ya rasa ba,
domin kuwa mahaifiyar sa da mahaifin sa na kokarin cika masa kowane buri nasa a rayuwa.
Tunda Marwan yake karami mahaifinsa na da babban buri akan sa na ganin ya gaje shi ta fanni siyasa
amma kash!
Alokacin da Marwan ya taso sai ya nuna wa iyayan nasa baya da wannan ra’ayin.
Bashi da wani buri ila ya zama babban likitan mata.
A lokacin da mahaifinsa ya fahimci haka, bai ji dadi ba amma ya yi kokarin cika masa burin sa.
Marwan mutum ne wanda baifiye magana sosai ba,
STORY CONTINUES BELOW

bashi da hayaniya ko kadan.
Yana da son karatu da mai da hankali wajan aikin sa.
Hakan ne yasa bashi da wasu friends sosai ,his books are his friends.
Marwan bai taba having relationship ba saboda bashi da time,
baya ma tunanin having any relationship.
To him relationships are complicated .
To him relationship wani abu ne wanda yake dauke wa mutum hankali from a achieving his goals in life.
Baya wasa da aikin sa kokadan hakan yasa baya son yin aure yanzu.
Wani restaurant naga ya shiga ya saya take away na fried rice da drinks.
Yana saya ya nufi gidan sa dake gwarinpa.
Yana shiga ya shiga kitchen ya ci abincin sa,
ya koma daki ya yi wanka, ya saka white vest da 3quarter baki.
Wayar sa ya dauko daga desk din dakin sa ya kira Mami, gaishe ta yayi suka danyi fira,
daga karshe dai take fada masa mahaifin sa na son ganin sa.
Toh mami kawai ya iya fada mata, ya kashe wayar.
Laptop din sa ya dauko ya cigaba da yin wani research.
Yana gamawa ya sauka kitchen din sa ya hada coffee, ya shiga library din sa yana duba wani book.
Yana gama karatun ,komawa yayi dakin sa ya canja kayan jikin sa zuwa farar shadda, kaftan tayi masa kyau sosai.
Turaran sa ya dauko ya feshe jikin sa ya saka medicated eye glass din sa.
Key din motar sa ya dauka daga saman center table din dakin sa.
Karfe 7:00pm daidai yana gaban gate din gidan su wanda yake maitama.
Yana isa mai gadi ya bude masa gate ya shigo yayi parking motar sa.
Yana fitowa daga mota, baba mai gadi ya gaishe shi, ya mika masa kudi kamar yar da ya saba.
Na gode dan nan, Allah ya maka Albarka, ya baka mata ta gari
Amin baba, Marwan ya fada cikin girmamawa.
Marwan na Shiga cikin gida,
Alhaji Umar ne a zaune a palor tare da matar sa hajiya Fatima,wadda me cike da farin cikin ganin dan ta.
Suna gari daya Amma Marwan yakan yi sati biyu bai zo gidan su ba, saboda yana yin aikin sa baya samun lokaci sosai.
Amma yana waya da su sosai, kusan kullun sai yayi waya da Mamin sa.
Zama yayi kasa gefen mahaifiyar sa
Ya gaishe da iyayan sa cikin girmamawa da ladabi.
Suka Amsa masa cikin fara’a.
Marwan!
Maifinsa ya kira sa.
A duk lokacin da marwan yaji mahaifin sa ya masa irin wannan kiran yasan maganar da zai masa mai mahinmanci ce.
Gyara zama marwan yayi yana sauraron mahaifinsa .
Bari na bako wuri kuyi magana, cewar mami.
Hannun ta tasa ta shafa kan dan na ta kafin ta bar masu wajan.
Na’am Abba!
Marwan ya fada.
Gyara murya Alhaji umar yayi kafin ya kalli dan nasa.
Marwan waye mahaifin ka?
Marwan ya kalli Abban sa yace kai ne Abba, yana fadar haka ya sunkuyar da kan sa.
Alhaji umar ya gyara zama, ya kalli dan nasa yace toh ina baka umarni ba da ka fito da matar aure cikin wannan shekarar.
Abb…
Marwan ya bude baki zaiyi magana Abban sa ya dakatar da shi..
Bana son jin wani excuses din ka yau,
Ba tun yau ba ina maka maganar aure kana jan ye jikin ka da maganar.
Ace mutum balagagge kamar ka yana zaune ba mata?
Shekarunka karuwa suke yi.
Amma kullun aka yi maka maganar aure sai ka ce aiki.
Ba kan ka aka fara aiki ba marwan, kuma aure baya hana aiki.
Bani da wani da wanda ya wuce ka, daga kai sai kanwar ka Allah ya bani.
Ina son ganin jikokina kafin na bar duniya.
Kana jina kuwa?
Ina jinka Abba
Marwan ya fada cikin ladabi.
Kana da wata budurwa ne, wadda kuka sasanta kan ku?
Kada kansa yayi, ya mike tsayi inshaAllah Abba na kusa kawo maku matar da zan aura nan ba da dadewa ba.
To mashaAllah, cewar Abba, Allah ya maka Albarka.
Shiga yayi dakin mahaifiyasa ya same ta kan dadduma tana jan carbi.
Zama yayi gefen ta ya mata sallama kafin ya tafi gidan sa.
Pls vote and commentsZaune take saman gadon ta, tana faman research akan case din da zata yi a kutu nan da kwana biyu.
Sanye take da half vest kalar baki da tight jeans baki.
Don’t be surprise Na’ima loves black color.😉
I don’t blame her shes a lawyer.
Gefen ta na kalla wani kwalin holandia milk ta aje da wani cookies.
Da alama yanzu take breakfast.
Na’ima kenan, she’s really a workaholic bata da time na yin girki.
Though she loves cooking and sports.+
Aiki ta ke amma kwakwalwar ta ta kasa fahimtar abun da take karantawa
Zuciyar ta na tunanu mata
Saurayin da ta hadu da shi.
For the first time a rayuwar ta, taji tana son wani da namiji har take tunanin sa
Sunyi sati biyu kenan da haduwa, amma bai kirata ba.
Wayar ta ce tayi kara, alamar kira ya shigo.
Sauri tayi ta duba number din screen din, tana addu’a Allah yasa Marwan ne.
Murmushi tayi ta sa wayar hands free.
Bestyna taga ni a screen din.
Aisha – haba barrister!
Meye duniya?
Wato don wulakan ci ina ta kiranki wayar ki ma a kashe ta ke.
Na’ima – haba besty kinsan fa yanayin aiki na, ina wani case ne wallahi,
Gaba daya bani da lokacin answer calls.
Aisha – sannu agogo sarkin aiki, ai ke wallahi kiyi a hankali kar ki kashe kan ki, aiki ko ja raba?
Kullun mutum baida lokaci sai kace injin.
Na’ima – dariya Na’ima tayi har tana daga kafar ta, tace kai besty na,
Sowie!
Ya kike ne ,ya gida yasu ummah?
Aisha – lafiya lau, su ummah suna umarah.
Wallahi kawata ki rage wannan aiki kulun mutum bashi da hutu.
Wanan rashin hutun ne fa yake hada ki da samarin ki.
Gaki kyakyawa ,sai farin jini amma wannan aikin naki yana hana samarin ki hakuri.
Na’ima – tsaki na’ima taja mtsww, tace nifa duk wanda ba zai soni a haka ba sai dai fa ya kara gaba.
Ai besty ba ki ma sani ba, aikin nan shine abunda nafi so bayan iyaye na,
bazan iya bari ba saboda wani kato .
Aisha – dariya Aisha tayi tace, idan kin aure sa ai dole ki bi miji,
Ko a shiga wuta.
Kin San aure ba’a wasa dashi.
Na’ima 😁dariya sosai tayi.
zamuyi magana besty yanzu ina wani aiki ne, zan kiraki.
Aisha – toh shikenan, bye.
Na’ima na kashe call din .
Tashi tayi ta cire half vest din da jeans ta daura towel ta shiga wanka.
Tana fitowa ta zauna saman dressing mirror din ta,
Powder ta shafa, sai lip gloss.
Tashi tayi ta dauko black suit din ta da grey shirt ta saka.
Turaran ta ta dauko ta feshe jikin ta.
STORY CONTINUES BELOW

Handbag dinta ta dauka ta sauka.
Tana sauka palor ta shiga duba important documents dinta, wanda zata yi amfani da su wajan case din.
Key din motarta ta dauka, ta kashe wutar gidan kafin ta rufe apartment dinta.
Direct police station taje don yi wa client dinta interview.
Bata bar police station din nan ba har sai karfe 5:pm na yamma.
Tana shiga gida ta ajiye handbag dinta ta zaune ta kunna tv din ta
Seriously? Ta fada tana shafa cikinta
Ji tayi cikin ta na kukan yunwa
Shafa cikinta tayi ta tuna rabun ta da abinci tun safe.
Ta shiga kitchen tayi don’t neman abun da zata ci.
Tana shiga ta bude drawer da kitchen cabinets dinta.
OMG!
Ta furta, ganin ba kayan abinci a gida.
Tunawa tayi rabun ta da yin shopping tun last month.
Dole kayan abincin su kare.
Tsaki tayi mtsww, ta fito kitchen din.
Daki ta koma ta cire kayan jikin ta ,ta shiga wanka.
Tana fitowa ta ji karar wayar ta.
Zama tayi a gefen gadon ta kafin ta daga wayar.
Na’ima!
Murmushi tayi, har wushiryar ta ta bayyana.
Wani sanyi taji cikin ranta saboda, ta dade ta na jiran jin muryar.
Kidnapper!
Ta fada cike da zulaya.
Dariya yayi daga nasa gefen .
Kin gane ni kenan?
Fari tayi da idanun ta, kai kace shine a gaban ta.
Lawyer fa ce ni, ka taba ganin lawyer mai mantuwa.
Murmushi yayi, Ashe barrister ce da kanta.
yace sorry fa kinji ban kira kiba ko?
Walahi aiki ne yayi min yawa, kin San ni din kullun busy nike.
Ba komai Marwan ta fada cikin sanyin murya.
Bayan sun gaisa yake tambayar ta family din ta.
Ya dai naji ki kamar ba lafiya?.
Ajiyar zuciya tayi, ta rike cikin ta wanda tun dazu yake kukan yunwa.
Ba kai bane…
Ta fada a shagwabe.
Dariya sosai Marwan yayi ,haka nan sai yaji yana jin dadin firar su.
Koda bai fiye son magana ba, idan yana tare da Na’ima sai yaji, yana surutu kamar ba shiba
Me nayi maki ne?
Ya fada cike da zolaya.
Yunwa fa nike ji kuma ka ki bari naci abinci.
Murmushi yayi yace.
Ni na hana ki cin abinci?
Banda sharri barrister ya fada yana dariya.
Dare yayi da nazo na kai ki kinci abinci.
Murmushi tayi tace fita ma zanyi yanzu,
Cikin daran nan?
Marwan ya fada cike da mamaki
zanyi shopping ne wallahi akwai kayan abincin da nike so na saya ne.
Ajiyar zuciya Marwan yayi yace toh na gane.
Ko na zo na raka ki ne?
Ya fada yana jiran amsar ta.
Shiru yaji tayi na dan lokaci
Kafin ta ce masa,
No need Marwan
I can take care of my self.
Eyye!
Marwan ya fada cike da zolaya.
Yaushe zan zo ne.
I have something important to say to you,
Yaushe kenan kike free, sai muyi maganar?
Shiru tayi na dan lokaci kafin tace on sunday ina zuwa sport.
Idan kana free sai ka kira ni.
And oops
Na manta, kazo da shirin ka, hop ka iya basket ball?
Dariya sosai Marwan yayi yace sai ki koya mun.
Murmushi Na’ima tayi tace kar ka damu.
Bari na barki kici abinci, take care
Yana fadar haka ya kashe wayar.
Na’ima na aje wayar tayi murmushi tana smiling.
What is happing to her?
Ita mace ce wadda bata fiye bata lokacin ta ba wajan yin waya da samarinta.
Amma sai gashi yau tana waya da stranger har tana jin kamar kar ya kashe wayar bata gaji da jin muryar sa ba.
Tashi tayi ta dauko wata simple gown din ta, tayi rolling gelen ta ta fita shopping.
Pls votes and comments.Yau Na’ima ta tashi cike da farin cikin ganin tayi winning case din da ta dade tana wahala kan shi.
Yau safiyar juma’a ,kamar kulun idan ta tashi tana shiga gym din ta tayi exercise.
Tana gamawa wanka ta shiga tayi arranging kayan ta.
Misalin karfe 10:00am ne jirgin ta zai tashi zuwa yola.
Kitchen ta shiga ta hada tea ta dauko bread da Nutela ta zauna saman dining table din ta.
Tana gama breakfast, ta wanke cup din da tayi using da plates.
Karamin towel ta dauko ta goge hannun ta.
Daki ta koma ta dauko a kwatin ta da gele ta yafa saman kanta.
Karfe 9:00am daidai tana airport.+
Misalin karfe 11:00am na safe tana yola, jirgin ta na sauka ta kira Ammin ta.
Nan da nan aka zo daukar ta.
Tana isa cikin makeken gidan su
Wani hadadan mansion ne, kai kace ba za’a mutum ba.
Fitowa tayi daga motar cike da isa.
Wasu body guard su ka tarbe ta da gaisuwa.
Amsa masu tayi, ta yi masu umarni da su dauko mata akwatin ta daga mota, su kai mata cikin gida.
Tana shiga harabar gidan taga wasu motoci dayawa an parker.
Da alamar akwai baki a gidan.
Addu’a tayi kafin ta shiga, tana tsoron haduwa da baffa Nasir, wato yayan Baban ta.
A kullun yazo gidan sai ya mata maganar aure, hakan yasa bata son haduwar su.
Direct babban palor ta shiga, wanda aka kawata shi da Royal chairs.
Tana shiga taga su Abban ta , da gudu ta je ta rungume shi.
Dariya yayi ya ce Na’ima kin dawo lafiya?
Lafiya lau Abba na ta fada tana smiling.
Abba ka tayi ni murna nayi winning case din, na gode da addu’ar ku.
MashaAllah! Abba ya fada yana murmushi.
Allah ya kara bada sa’a.
Amin Abbana.
Bata lura da mutanen da ke palorn ba sai dai taji ance.
Yau ga shiririta, yarinya ta girma bata san ta girma ba .
Gaban ta ne ya fadi jin muryar baffa Nasir.
Tsugunawa tayi har kasa ta gaishesu, ta gaishe da Ammin ta.
Fada baffa Nasir ya shiga yi mata kamar dai yanda ya saba.
Tashi tayi ranta bace zata bar palorn.
Ina zuwa Na’ima?
Abban ta ya fada yana kallon ta.
Abba zanje nayi wanka ne na ce Abinci.
Toh madallah!
Fitowa tayi ta nufi dakin ta gam!
Taji tayi karo da mutum.
Daga kanta tayi Adnan ta gani tsaye, wato cousin din ta.
Gabanta ne ya shiga faduwa, ta dukar da kanta kasa zata wuce
Kee wai bakye gani ne?
Ya fada yana wani hade rai.
Kallon sa tayi ta ce bana gani ko baka gani?
STORY CONTINUES BELOW

For ur information, sunana Na’ima not kee!
Tsaki taja masa tayi gaba.
Ranta dama a bace yake wannan kuma zai wani kara bata mata rai, masifaffe kawai.
Tana shiga daki ta kwanta, kanta na kallon silin.
Hawaye taji suna zuba daga idanun ta.
Tunda ta ke duniya mahaifin ta bai taba yi mata fada ba.
Amma kullun baffa Nasir yazo sai yayi mata fada.
Banko kufar dakin ta taji anyi da karfi, cikin firgici ta mike ta na kallon wanda ya shigo.
Adnan ne tsayi yana huci, kai kace wani zaki ne.
kee ! Ya fada cikin daga murya
wai ni zaki kalla dan baki da kunya kiyi min tsaki?
Naga alama iyayan ki sun baki lasisin yi wa naga ba dake ranshin kunya ko?
Adnan!
Kai fa musulmi ne, kana ganin kayi daidai kenan?
Ka shigo dakin mace wadda ba muharramar ka ba, kai tsaye ba sallama?
Yanzu da ina cikin yanayin da bai kamata ka ganni bafa?
And !
ta fada tana nuna sa da yatsanta
Don’t ever call my parents!
Na’ima ta fada cikin daga murya, don’t you dare !
Kar ka sake sako iyaye na, idan kana haukanka.
It will be better idan fadan ya tsaya tsakanin mu.
ka tafi ka barmani dakina bana son jin wani shirmen ka ok?
Kallon ta yayi idanun sa sunyi ja saboda bacin rai.
Matsowa yayi dab da fuskar ta hannun sa ya sa ya matse mata baki.
Wani irin kara Na’ima ta saki, ta ture sa, kasan cewar gidan su babba ne, ba wanda yaji karar.
Mugu kawai ta fada tana shirin guduwa jawo ta yayi yace ki bari na baki amsar tambayanyar ki kafin na fita,
Naga alamar kan ki haryanzu rawa yake, zan sassaita maki notin kan ki tukunna.
Dole ki saurare ni, koda yake kin ce ba kyason jin haukana ko?
Zaki ga hauka lokacin da jikin ki ya gaya maki.
Naji kina fadin shigowa dakin ki ba tare da sallama ba ko?
Toh bari kiji, ni har yau kallon yar goye nike maki,
Ur still a kid, me da kika girma a gabana,
banga abunda zai bani sha’awar jikin ki ba.
So ina so kiyi wa bakin ki linzami don kin san halina ba tun yau ba.
I don’t tolerate shit!
You should better be careful next time! Ya fada yana nuna ta da dan yatsan sa.
last warning ya fada yana kallon kwayar idon ta, wanda sun kada sunyi jajar don kuka.
fita yayi fuu.
Fadawa tayi kan gado, meyasa Adnan yake mata haka?
Meyasa tun tana karamar ta baya son ta shida mahaifin sa?
Aure ne ta fada masa ita ba yanzu zata yi ba, amma a kulun baffa Nasir yazo sai ya mata fada.
Tasan bashi da wani buri ila na ta aure dan sa Adnan .
Ita kuma bata ra’ayin haka, saboda Adnan baya cikin mazan da take so,
Ya fiye ji da kai da nuna mulki da sarauta.
Adnan Nasir sarki, shine asalin sunan sa.
Adnan mutum ne wanda baya son raini ko kadan, yana da son mulki da sarauta.
Mahaifin sa Baffan Na’ima ne, mutum ne mai zafin rai, shima Attajirin gaske ne.
Alhaji Nasir sarki shine sarkin yola.
Dan sa daya Adnan, wanda bai dade da dawowa daga Riyad ba.
Adnan kwararran pilot ne.
Yana da yawan tafiye tafiye.
Hakan yasa bashi da burin yin aure.
Baya shiri da na’ima saboda itace mahaifin sa yake burin aura masa.
taci kukan ta, har bacci ya kwashe ta.
Ammi ce ta shigo dakin .
Na’ima!
Tashi tayi ta goge fuskar ta da sauri tayi murmushi.
Na’ima lafiya?
Nagan ki wani iri ne,
Lafiya lau Ammi na, akwai abinci?
Yunwa nake ji.
Murmushi Ammi tayi tace ki tashi akwai abinci a dining table, ke kadai ake jira.
To Ammi!
Ta fada a shagwabe.
Bari na dan yi shower,
Kiyi sauri dai, jiran ki ake, Ammi na fadar haka ta fita daga side din Na’ima.
Ammi na fita Na’ima ta rufe dakin ta daura towel din ta tayi ta shaga wanka.
Tana gamawa tayi light make up, ta saka riga da wando jeans.
Turare ta dauko ta feshe jikin ta kafin ta sauka .
Pls vote and comment.Marwan naga ya fito daga dakin theater.
Yana fita office din sa ya shiga, wani mutum ne naga ya shiga office din sa.
Ka zauna mana, marwan ya fada yana nuna masa kujera.
Dr. Da fatan an dace?
Murmushi Marwan yayi, yace gaskiya ban taba aikin theater da ya tsorata ni ba kamar na matar ka.
Don sai da kyar muka gano man matsalar.
Amma dai Alhamdulilah, mun samu ceto ranta.
Na gode sosai Dr. Allah ya baka mata ta gari..+
Amin na gode, cewar marwan.
Zan iya ganin ta kuwa?
Zaka iya amma sai nan da minti talatin idan ta farfado.
Ok thans.
Yana fadar haka ya fita.
Marwan na ganin yamma yayi ya shirya komawa gida, kasan cewar yau ya wuni ganin patient.
A gajiye yake sosai.
Wata nurse ce naga ta biyo bayan sa da sauri.
Doctor!
Lafiya? Ya fada yana kallon ta,
Murmushi ta masa, tace haba Marwan yanzu ace kullun baka taba fahimtar halin da nike ciki?
Daga idona nayi naga fuskar nurse din,
Sanye take da kaya farare irin wanda nurses ke sakawa, hannun ta rike yake da hand bag din ta,
Da alama itama ta tashi aiki.
Kyakyawa ce bata da tsayi sosai.
I thought we hav already talk about this zarah?
Ya fada yana kallon ta.
Marwan!
Ta kirasa cikin sanyin murya, kasan fa ina son ka Amma kana wulakan ta ni.
Shiru yayi yana kallon ta tausayin ta yaji.
Gefen sa ya kalla, yaga mutane na kallon su
Yace zarah shigo, motar sa ya bude ta shiga.
Tunda suka shiga motar ba wanda yayi magana da wani
Wani restaurant ya kai su.
Suna zama aka kawo masu abinci da drink.
Sai da yayi one spoon kafin ya kalle ta, ina jinki zarah.
Murmushi tayi tace, doctor matsayina na ya mace na zubar da aji na,
na fada maka abun da yake zuciyata ae yaci ace ka saurare ni.
Aje cup din hannun sa yayi, yace ba wai bana son ki bane zarah, amma kiyi hakuri bana jin zan iya aure a halin yanzu.
Kin san ni, kin san halina, bana having relationship da wata, kawai ni mutum ne wanda yafi mai da hankalinsa wajan aikin sa.
Zarah kin fi kowa sannin nena doctor na daya wanda ya kware a aikin sa, a wannan hospital.
Bani da lokacin kaina bare, na mata ta.
Akwai hakki na aure wanda bani da lokacin sauke su.
Zarah ina so ki daina bata lokacin ki a kaina kiyi auren ki.
Kallon fuskar ta yayi ,hawaye yaga na zuba daga idanun ta.
Doctor, ban san yarda zan yi aure da son ka cikin zuciya ta ba.
STORY CONTINUES BELOW

Don nasan ba zan zama mace ta gari ba wajan kula da hakkin mijina.
Kai ne kadai namiji da nike burin zaman aure dashi.
Doctor, nafi kowa dacewa da na aure ka, saboda nasan dole nayi hakuri da kai saboda ina son ka.
Ba zan damu da rashin lokacin ka a kaina ba doctor, asalima hospital daya muke aiki da kai.
Wasu hawayan ne suka kara zubuwa daga idon ta.
Hannu marwan yasa cikin aljihun sa, hankici ya dauko ya mika mata.
Daga kanta tayi ta karba, ta goge fuskarta.
Zarah haka kike da arhar hawaye?
Ya fada cike da zolaya, murmushi tayi har saida fararan hakoranta soka baiyana.
Kallon ta yayi cike da tausayi, yace ko ke fa?
Kici abincin ki sai mu tafi na kai ki gida ok?
Kallon sa zarah tayi tana jin mamakin irin yarda ya saki jiki da ita .
Kallon abincin tayi ,ta dan ya motsa fuska,
Menene?
Marwan ya fada yana kallon ta.
Na koshi, ba zan iya ci ba, ta fada cikin sanyin murya.
Murmushi marwan yayi ,plate din abincin sa ya rufe, mikewa yayi tsayi
Kudi ya aje a gefen table din, ya kalle ta, zo mutafi.
Har gida ya kaita kafin ya koma gidan sa, cike da mamakin hali irin na zarah,
Hakika zarah na son sa fiye da tsamanin sa.
Amma shi a gaskiya baya jin son ta, shiyasa ma yake kauci was maganar ta.
Yasan tun ba yau ba ta me son sa.
Dakin sa ya shiga ,ya cire kayan jikin sa.
Wanka ya shiga, tsayawa yayi 🚿 na sauka a kansa.
Tuna was yayi da Na’ima, wadda zuciyar shi ke matukar son ta ganta.
Murmushi yayi, lokacin da ya tuna harduwa su ta farko.
Mamakin kansa yake, yanda yake tunanin mace, haka kawai.
This is not me, ya fada a cikin ransa.
Alwala yayi ya Kashe shower din yayi, ya daura towel ya fito.
Jallabiya ya saka ya fita sallah isha a masallaci.
Yana dawowa ya saka pj dinsa ya laptop din sa ya dauko, ya fara research din sa.
Wayar sa ce tayi kara, yana dubawa yaga Abba.
Daga wayar yayi ya gaishe da mahaifin sa cike da girmamawa.
Marwan!
Abba ya fada, ina so kazo gida nxt week Saturday. akwai daurin auren, dan abokina da za’a yi.
Toh abba, inshaAllah zan zo.
Sallama suka yi ya kashe wayar.
Yana duba lokaci yaga time din shifting din sa na aikin dare yayi.
Tashi yayi ya canza kayan jikin sa ya koma hospital.
Sai bayan sallar asuba ya dawo gida.
Kitchen ya shiga ya hada coffee, ya sha, kafin yayi wanka.
Garden din sa ya koma yana shan iska har bacci ya kwashe shi.
Sai around 2pm ya tashi yayi sallah, wanka yayi, kafin yaje zone two gidan wani friend din sa Sufyan.
Yana zuwa daidai gidan ya parker mota.
Shiga yayi cikin sallama, wata naga ta fito da alama ita ce matar gidan,
Sanye take da atampa, ta rufe jikin ta da babban gele.
Wani yaro dan shekara uku naga ni yana wasa a palor.
A’a’a yau babban bako mukayi a gidan kenan, ta fada cike da zolaya .
Murmushi marwan yayi, kafin ya zauna.
Wata sabon gani!
Joyowa nayi naga wani magidanci ya fito, shekarunsa ba zasu wuce na marwan ba.
Shege abokina sai yau ake ganin ka?
Agogo sarkin aiki.
Murmushi marwan yayi yace abokina, wai Amir ne yayi girma haka?
Dariya sadiq yayi, yace ka tsaya can har sai mun fara aurar da yara, kai baka yi.
Ya fada yana nuni da yaron da ke wasa a kusa dashi.
Hafsah naga ta kawo drnks da ruwa ta ajiye .
Kafin ta bar palorn.
Zama sadiq yayi kusa da marwan suna firar yaushe rabo.
Sadiq ya kalle Marwan, daga akwai damuwa a tare dashi.
Abokina yadai, naga ina magana kwata kwata hankalin ka na wani wajan.
Sipping drink din da ke hannun sa Marwan yayi kafin yace.
Wallahi sadiq, Abba ne ya matsa sai nayi aure,
Kai kuma kasan, aure bashi ne abun da ke gabana ba yanzu.
Ina so nan da wata daya zan je wani course a England,
Course din kuma na shekara hudu ne.
Nasan abba, ba zai banni na tafi babu mata ba.
Dafa kafadar sa sadiq yayi ya kalle sa,
Marwan ni banga laifin Abba ba don yace kayi aure,
Kalla fa ka gani duk friends din mu sun yi aure, kai ka dai ka rage.
Aure sunnah Anabice
Ya kamata ka fahimci hakan.
Ka duba kaga fa shekara ta 4da aure gashi muna zaune lafiya,
Hafsah bata da matsala ko kadan, takan bani wasu shawarwari akan aiki na.
Ba zaka ka gane ba sadiq, cewar marwan.
Mata, sun kan dauke hankalin mutum daga achieving goal din sa, idan baka yi dace ba.
Nasan kai kam ka more mace don hafsah mace ta gari ce.
my worse fear in life, Mata!
Dariya sosai sadiq yayi.
Suna gama fira, marwan yayi masa sallama kafin ya bar gidan.
Vote and comments.Zama naga tayi idanun ta na zubar da wasu zafafan hawaye.
Dubawa nayi, naga Abban Na’ima, da Ammin ta, sai daga gefe kuma Adnan ne zaune a kasa gefen mahaifin sa.
Baffa Nasir kuma yana zaune ne a babbar kujerar palor, bayan sa wasu dogarai ne guda biyu.
Baffa Nasir, dan Allah ka taimaka mun, ba zan iya barin aiki na ba wallahi.
Da kata!
Baffa Nasir ya fada cikin daga murya, kina mace zamu barki ki kama gida ke kadai.
Ke ba miji ba?
Toh saurara kiji, ko mahaifin ki idan na yanke hukunci bashi da tacewa.+
Bare ke yar sa!
Nan da kwana uku!
Kina jina!
Ya fada yana kallon ta,
Ina so ki bar aikin ki, kin sani sare, dangin mu, basa barin mace yin aiki
Ga iyayan ki nan, sune ma, masu laifin da suka bari, kika tafi har wani gari ba tare da miji ba.
Baffa dan Allah kayi hakuri!
Ta fada cikin rawar murya tana zubar da hawaye.
Tashi ki bani waje! Ya fada cikin daga murya .
Tashi tayi da sauri,tafin hannun ta tasa ta rufe bakin ta dashi ta bar wajan.
Dakinta ta shiga da sauri ta kwanta kifa kanta tayi, ta fara kuka mai tsuma rai.
Tana jin an bude kofa ta mike tsaye,
Why are you here?
Ta fada idanun ta na zubar da hawaye dukar da kanta tayi.
Adnan ka taimaka ma rayuwata, ka barni naji da abun da ke damuna.
Shiru taji yayi,tana daga idanunta ga mamakinta sai taga hawaye a idon sa.
Kallon ta yayi, Na’ima!
Ya fada, cikin sanyin murya.
Kin fi kowa sanin bana son wannan hadin, da sarki ya hada.
Idan kika bari aka daura auran nan,
Hmmn.
Ina guje maki bacin rai.
Ki tana ji maganin hawan jini, don ina maki tambacin ,jinin ki sai ya hau.
I will make sure ,I make ur life as hell as position.
Kina jina ko?
Goge hawayanta tayi, ta kalle sa,
Ubangijina ba zai bari ba.
Allah ya fi karfin ka..!
Meyasa kai ba zaka je ka fadawa sarki baka sona ba?
Oh! Sai ni gani marar kunya ko?
To baka isa ba.
Ba inda zani, tana fadar haka ta shiga toilet, ta fara kuka.
Fita yayi fuu ya bar dakin rashin a bace.
kayan jikin ta ta cire, ta sa ma kanta ruwa 🚿.
Zama tayi, tayi shiru har sai da taji, zuciyar ta tayi sanyi.
Tana gama wankan ta daura farin towel dinta,
Wani karamin towel naga ta dauko, tana goge gashin kanta.
Zama naga tayi kan wata karamar kujera kirar royal.
Light make up naga tayi, ta saka wata doguwar riga kalar white and black.
STORY CONTINUES BELOW

Parking din gashin kanta tayi, ta saka turban cap.
Library dinta ta shiga ta dauko, wani katun littafi.
Fita tayi garden da littafi hannun ta, zama naga tayi.
Bello!
Naji ta kira ,yana zuwa ya gaishe ta cikin girmamawa.
Kaje cikin gida ka dauko mani holandia yoghurt.
Yana tafiya ta shiga karatun littafin ta, kai kace bata da wani damuwa.
Fuskar ta a sake take ba kamar dazu ba.
Hajia!
Bello ne ya kirata, ka ajiye a nan ta fada ba tare da ta bar kallon book din da take karantawa ba.
Tana gama karantawa ta tashi ta koma cikin gida.
Aunty Na’ima!
Sauri nayi na juya don naga wane yaro ne ke kiranta.
Cike da farin ciki ya rungume ta.
I miss you Aunty Na’ima, naji ya fada.
Yaro ne karami bai wuce shekara uku ba, kyakyawa dashi.
Haidar!
Baka ji ko?
Bana ce ka bar gudu ba?
Wata kyakyawan mace ce naji tana magana, da alama ita ce mahaifiyar Haidar.
Boyewa yayi bayan Na’ima, yace Aunty Na’ima ki boye ni, mommy zata yi fada.
Dariya Na’ima tayi, tace, Ayi masa hakuri Aunty zaynab plssss!
Na’ima ta fada tana rike kunnan ta.
Murmushi zaynab tayi, tace wlh Na’ima kina bata yaron nan.
Zama tayi tace wash! Duk na gaji walahi.
Na’ima ce ta dawo gefenta ta zauna, tace ,
Ae dole ki gaji, aunty zaynab, china wasa ne, akwai nisa sosai.
Ina su Ammi?
Zaynab ta fada tana kallon Na’ima.
Sun fita, suna gidan sarki.
Ok dear!
Let me take my bath.
Aunty zaynab akwai gist,
Na’ima ta fada tana murmushi.
Like Seriously?
Aunty zaynab ta fada, tana kashe mata ido.
Aunty Na’ima zan sha chocolate, haidar ya fada a shagwabe.
Chuchu na zai sha chocolate!
Na’ima ta fada tana jan kumatun haidar cikin wasa .
Hannun sa ta rike ta kaishi wajan da take ajeyi chocolate.
Wow aunty Na’ima ki bani dairy milk, ya fada ya tsalle irin na yara.
Dauko masa tayi ta mika masa.
Ki bude mu!
Ya fada a shagwabe, bude masa tayi ta bashi a baki.
Suna shiga babban palor ta ga baban haidar a tsaye.
Barrister, da kanta, ya fada cike da zolaya.
Ya nagan ki a gida ne yaufa Monday.
Ai dogun zance ne ya sadiq.
Kasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki.
Ya zaynab zata fada maka, halin da ake cike.
Ki ci gaba da addu’a, Allah zai kawo mafita.
Amin ya sadiq,
Bari na sa a kawo maka abinci ,tana fada ta bar wajan.
Daddy!
Haidar ya rike baban sa. Aunty Na’ima gave me chocolate, ya fada cike da murna.
Kace mata thank you?
Sadiq ya fada yana kallon dan nasa.
Lets me go an tell her, yana fada ya tafi da gudu.
Zaynab na gani ya shigo palorn, zama tayi kusa da mijin ta,
Wata na gani ta shigo da food flakes da plates,
Tana ajiyewa ta fita.
Zaynab ta zauna, tayi serving mijin ta, tare suka ci abinci.
Na’ima na shigowa ta gansu, eye!
Kaga Romeo and Juliet, ta fada cike da tsokana.
Dariya, sadiq yayi, yace kanwata lokaci ne.
Rabu da ita cewar aunty zaynab, ita mun san irin soyewar da zatayi da nata mijin,
Tana fada ta kashe mata ido.
Wallahi ko aunty zaynab, soyayyar ku na burgi ni,
Tana fadar haka ta bar wajan, wasu hawaye taji suna zuba daga idanunta.
Zaynab mansur sarki!
Diyace ga marigayi sarki masur.
Tun tana karama mahaifanta suka rasu, yayanta Baffa Nasir shine ya bada ita riko wajan kanin sa Abban Na’ima.
Kasan cewar bai samu haihuwa da wuri ba.
Abban Na’ima shine wanda ya rike ta, ya bata ilimi, ya kuma aurar da ita.
Ya aura mata dan abokin sa wato sadiq.
Sadiq dan kasuwa ne,
Na’ima ta dauke ta matsayin sister din ta, kasan cewar sun taso tare a gida daya.
Tana kuma kula da Na’ima sosai, a matsayin karamar kanwar ta.
Pls vote and commentsMarwan na gani sanye yake da manyan kaya.
Abban sa ne gefen sa suna gaisawa
Marwan!
Abban sa ya kirasa.. Da fatan ka nema hutu wajan aikin ka don yau zamuje daurin aure yola.
Murmushi Marwan yayi abba na dauka Hutu na kwana daya.
Toh madallah!
Shiga yayi cikin gida yayi wa mahaifiyar sa bankwana.
Airport suka tafi direct.
Zama yayi bayan sunyi boarding suna jiran lokacin shiga jirgi.
Tunanin Na’ima ya shiga yi, gaba daya kwana biyun nan ya rasa me ke damun sa.
Sunyi da ita zasu hadu basketball field yaje kuma bai same ta ba.+
Ya kira wayar ta, gaba daya a kashe take.
Marwan! Tunanin me kake ne?
Abba ya fada yana dafa kafadar marwan.
Ba komai Abba!
Tashi yayi suka shiga tare da Abban sa.
Sai karfe 12:00 suka isa yola.
Suna shiga garin yola sarki yasa aka je daukan su .
Manyan mutane ,sarakunan arewa na gani ta ko ina .
Dubawa nayi ina neman marwan,ganin shi nayi ya fito cikin mota yayi kyau kai kace yau ne daurin auran sa.
Cikin fada suka shiga shida mahaifin sa .
Mai martaba sarki yayi matukar farin cikin ganin abokinsa wato Abban Marwan.
Kamo hannun sa yayi ya shiga dashi har cikin gida.
Suna zama Abban marwan ya gaishe shi ,bayan sun gaisa ne yake masa murnar daurin auren Dan sa .
Alhaji ina cikin matsala babba,sarki ya fada idanunsa na zubar da hawaye.
Inalilahi wa ina ilaihi ra’ji’un, Abban marwan ya fada hankalin sa a tashe.
Me ke faruwa ne ?
Ka taimaka ka mani Alhaji ! Sarki ya fada yana kallon Abban marwan
Sadda kansa yayi kasa wasu hawaye na gani daga idanun sarki.
Ya salam!
Al’amarin babbane na fada cikin raina.
Kamar yarda ka sani sarki ya cigaba ,yau ne ranar daurin auren Dana Adnan, amma tun wayewar garin yau
Mun nema adnan mun rasa,gaba daya wayarsa bata shiga.
Ajiyar zuciya yayi kafin ya cigaba.
Ka duba kaga irin manya mutane da na gaiyata .
Ina da damar daura masa aure koda bayanan amma ina tausayin yarinyar ganin irin biyayyar da tayi man .
Alhaji! Sarki ya fada cikin raunannar murya ,ka taimaka ka fidda ni kunya.
Ina so ka aura wa danka Na’ima . Ina maka tabbacin ba zakayi dana sani ba
Shiru Abban marwan yayi kafin nan ya tashi tsaye.
Ba komai sarki ,zan rufa maka asiri duniya da lahira .
Zanyi magana da Marwan inshaAllah ba matsala.
Abba Marwan na tashi ,waje yaje ya sa aka kira masa Marwan.
Wani palor na ga sun shiga , lekawa nayi naga me ke faruwa.
Marwan na gani zaune kusa DA mahaifin sa,kansa na kallon kasa.
STORY CONTINUES BELOW

Marwan!
Abban sa ya kira sa.
Na’am Abba ,marwan ya fada cikin girmamawa.
Ina so kayi min biyayya akan abun DA zan fada maka.
Ina maka tambacin ba zakayi dana sani ba inshaAllah.
Marwan ya daga kansa yana kallon Abban sa , damuwa sosai ya gani a fuskar Abban NASA.
Ba komai Abba zan maka biyayya inshaAllah.
Ina so yau zan daura maka aure …
Abba..!
Aure kuma ?
Wasu hawaye nagani idanun marwan.
Kansa ne ya fara masa nauyi ..ba tare DA bata lokaci ba Marwan ya sadda kansa kasa idanun sa na zubar DA hawaye ..
na Aminci Abba!
Ya fada yana ji kamar kansa zai tsage .
MashaAllah na gode Marwan
Agogon hannun sa ya cire ,Wanda zai kai kimanin dubu dari ,ya mika wa Abban sa.
Me zanyi DA wanan Marwan?
A bata a matsayi sadaki ,Marwan ya fada kansa na kallon kasa.
Madallah !
Abban Marwan ya fada yana murmushi .
Allah ya maka Albarka .
Amin Abba!
Marwan na fadar haka ya fice fuu..
Waje ya koma ,ya zauna wani garden kallon wajan yayi ..ya burge shi sosai
Flowers ne ta ko ina, dafa kansa yayi yana tunanin yanda rayuwar shi zata kasan ce.
Ko wacece Amaryar?
Shin irin matar da nike so ce ?
Zan iya bata hakkin ta a matsayin mijinta?
Shin zata yarda dani matsayin mijinta?
Tambayoyin da Marwan ya cigaba DA yi wa kansa kenan .
Karar Algaidatar da yaji ne ya dawo da tunanin sa.
Me kenan? Ya tambaya kansa.
Wata zuciya yaji tace aure aka daura maka.
Ya salam , zubur yayi ya tashi tsaye kasan ne ya kara masa nauyi ..wani jiri yaji ya kwashe shi
Zama yayi yana addu’a Allah ya bashi ikon hakuri DA kaddarar da ta fado masa
***********************************
Na’ima na gani kwance taci kuka har ta gaji.
Idanunta sunyi jajar don kuka, aunty zaynab ce ta shigo dakin da Na’ima take.
Na’ima tashi kici abinci kinji ko?
Tashi kiyi wanka, komai na duniya sai hakuri.
Yanzu baga shi an fasa auran ba?
An fasa auran aunty zaynab!
Na’ima ta fada da karfi ..
Hannun ta zaynab ta rike tace eh an fasa auren da Adnan ta fada tana kallon cikin idon Na’ima.
Na shiga uku aunty zaynab da wa aka daura?
Ta fada tana shirin tashi
Aunty..!!
Tana fada jiri ya kwashe ta.. Ta zube kasa .
Zaynab tayi saurin rike ta, kwantar da ita tayi saman gado ta fita da saurin ta .
Sarki ne zaune da mutane suna taya sa murnar aurar da yar kanin sa.
Zaynab na gani ta shigo da gudu gabada hankalin ta baya tare da ita zuwa tayi gaban sarki tace Na’ima!
Me ya same ta?
Gaba daya mutanan da ke fada hankalin su ya tashi.
Tana can a kwance ta suma.. Zaynab ta fada tana zubar da hawaye.
Wani bafade ya kalla DA ke gefen sa Kira Marwan.. Abban Marwan ya fada.
Marwan na shigowa Abban sa ya basa umarni da yaje ya duba lafiyar matarsa.
Zaynab kuje tare sarki ya fada.
Yana kaiwa bakin kofar dakin..
Ya salam ya furta.. This is not true
Kamshin Na’ima yaji..
Yana shiga dakin gaba daya sai yaji damuwar sa ta sake shi.
Ina take ya fada yana kallon zaynab
Cire bargon zaynab tayi daga fuskar Na’ima.
Na’ima!
marwan ya fada cikin daga murya.
Na’ima ce matata?
Ya fada yana kallon zaynab.
Itace ce wadda aka daura maku aure yau din nan.
Murmushi Marwan yayi,
Kasan ta ne?
Zaynab ta tambaya
Eh nasan ta.
Bari na duba ta ya fada fuskar sa cike da farin ciki.
Akwai abun da kake bukata?
No don’t worry cewar Marwan.
Yanzu dai ki dan bamu waje ya fada cike da kunya.
Murmushi zaynab tayi, tace toh shikenan.
Tana fita marwan ya janye bargon da Na’ima take ciki.
Kallon tsaf ya mata yaga duk ta rame.
Fukar ta ya kalla idanun ta duk sun kunbura. Da alama ta dade tana kuka.
Hannun sa ya yana shafar fuskar ta, bude idanunta tayi a hankali.
Tana kallon sa ta mike..
Marwan!
Me kake anan?
Kuka ta shiga yi.
Shishsh don’t worry ok?
Ya fada yana shafar bayan ta.
Am your husband Na’ima, ya rada mata a kunne.
No!
Ban yarda da ba how is that possible?
Zan fada maki ,calm down.Ki saurare ni Na’ima, kuma ina fata zaki fahimci ni da kyau.
Hannun ta ya rike ya kalli jajayan idanun ta.
Yatsan sa yasa ya goge hawayen da ke zuba daga idanunta.
Look at me Na’ima, kallon sa tayi cikin ido tana sauraran sa.
Kamar yadda kika sani yau ne ranan auran ki da Adnan Sarki.
Amma Allah ya canza maki kaddara, na zama mijin ki .
Na’ima!
A yau ne dunbin mutane dama suka shaida daurin aurena da ke.
Wanda daga ni har ki ba wanda yayi zaton hakan zata faro.+
Marwan Umar!
Na’ima ta kirasa.
Ina so ka dubi girman Allah ka sake ni!
Kuka ta shiga yi iya karfin ta.
Marwan ya dube ta cike da mamaki, hakika Na’ima na yi zaton ke din mai ilimi ce
Banyi tunanin wannan kalmar zata fito daga bakin ki ba.
A matsayin ki na yar boko kuma wadda take da ilimi na addinin musulunci.
Zaki furta wa mijin ki kalmar saki! A ranar auran mu Na’ima!
Kada kansa yayi, yace kaico!
Har a zuciyar sa yasan yana son Na’ima kuma yayi farin ciki matuka da yasan itace matar da aka aura masa.
Amma kash!
Zuciyar shi ta shiga bugawa da karfi jin kalmar da Na’ima ta ambato masa na saki!
Ya salam !
Matsowa yayi dab da ita yana kallon kyakyawan fuskar ta, wadda a halin yanzo tayi ja saboda kuka.
Na’ima yau ce ranar farko da mahaifina ya taba neman wani alfarma daga gare ni
A matsayina na Dan sa wanda ya Haifa.
kuma na yi masa biyayya akan hakan ba tare da bata lokaci ba, don na san zabin sa shine mafi alkhairi a gare ni.
wannan auren kaddara ne ko shakka babu.
kuma ni da ke ba wanda ya san da faruwar hakan, amma Allah ya hada mu.
Na’ima!
Ki sani tun kafin naga matar da Abbana ya ce zai aura min na ammince, koda ban taba ganin taba zan zauna da ita matsayi mata.
Saboda haka ina so ki sa a ranki wannan auren anyi shi ne, na har abada ba saki ba yaji inshaAllah.
Yana fadar haka ya fita fuu.. Ransa a bace.
Marwan! Marwan!
Na’ima ta ki rashi iya karfin ta amma bai ko saurareta ba..
Zuciyaar ta na farin cikin ganin Marwan matsayin mijinta Amma, ita ba aure ne gaban ta ba a halin yanzu
Saboda baffa Nasir yayi mata auran ne saboda ta bar aikin ta kwatakwata shine babban sharadin sa.
Kuka ta shiga yi sosai har bata San lokacin da zaynab da Ammin ta suka shigo dakinta ba.
Lafiya!
What happen Na’ima?
Aunty zaynab ce ta shigo rike da food flask na abinci .
Ammi Dan Allah ki taimaka min Na’ima ta fada tana kuka.
Ajiye food flask din aunty zaynab tayi tace Meke damun kine Na’ima?
Kifa kanta tayi saman cinyan aunty zaynab tace Aunty bana son Auran!
STORY CONTINUES BELOW

I don’t want to get married now!
Subhanallahi! Cewar Ammi
Kar na saki jin kin fada haka kin ji ko? Kanki aka fara aure da zaki tayi wa mutane kuka?
Ammi na fadar haka ta fita daga dakin
Aunty zaynab su Abba basa sona!
Meyasa basu hana baffa Nasir ba, tunda Adnan ya gudu?
Meyasa suka daura mun aure da wani?
Shafa kanta zaynab tayi, tace kiyi hakuri kinji ko?
Haka Allah ya kaddara maku keda shi.
Kinga shi yana da hankali sosai Na’ima ina ganin zai rike ki dakyau, kuma his a nice person.
No! Aunty ni ba na so..
Aunty zaynab kice masa ya sake ni!
Calm down Na’ima meye matsalan ki ne ?
yaron nan yana da kyau, ga aji gashi mai natsuwa amma kice bakya son sa?
Kuma ni kinsan sarki ba jin magana ta zaiyi ba.
Ki shirya ma yanzu yace zamu kaiki Abuja, kuma yace ki basa key din gidan ki na abuja.
Ya salam!
Aunty to ya zanyi da aikina?
Ban sani ba Na’ima ki tashi ana jiran mu.
Kinga ko abincin baki ci ba ma,
Ni ba zan iya cin komai ba aunty, Na’ima ta fada tana turo cute 👄 dita.
************************************
Misalin karfe biyar na yamma aka kawo Amarya dakinta.
Apartment din Marwan aka kaita wanda yake a maitama.
Bashi da wani girma sosai 1 bedroom ne ,sai kitchen da toilet sai palor.
Bayan yan kawo Amarya sun tafi, Na’ima ta fito palor tana neman wayar ta.
Tana daukar wayar ta koma daki, toilet ta shiga tayi alwala .
Tana fitowa taga mutum a tsaye yana kallon ta.
Jikin shi ta kalla, sanye yake da farar shirt da bakin wando, ya saka turare da alama fita zaiyi.
Hav you finish watching me out?
Ya fada yana kallon fararan idanunta
Kauda kan ta tayi gefe tace baka iya sallama bane?
Ta fada tana kallon sa.
Har a zuciyar ta tana son Marwan amma zuciyar ta taki sakin jiki da shi.
Nida dakina za’a yimin sharadi, lokacin da nayi sallaman baki ji bane?
Take!
Wata leda ce ya mika mata, wuce shi tayi cike da yanga ta dauko hijabin ta ta saka.
Ta tsaya gaban sa tace kadan matsa ko? Sallah zanyi.
Murmushin takaici Marwan yayi don ransa ya yi mugun baci.
Ledar ya aje mata saman side drawer ya bar daki.
Na’ima na idar da sallah ta dauko wayar ta, Ammin ta ta kira da aunty zaynab sun Dan taba fira sun yi mata nasiha aka ta zauna lafiya da mijinta kafin ta kashe wayar.
Tashi tayi ta dauko ledar da Marwan ya ajiye mata.
Zama tayi ta bude, gasashiyar kaza ce da ice cream.
Tsaki tayi tace lallai ma Marwan din nan.
Wayace masa ina shan stewbrry ice cream?
Aje wa tayi ta ci kazar.
Tana gamawa ta shiga toilet tayi brush tayi wanka .
Tana fituwa ta saka kayan bacci ta hau gado, zuciyarta cike da tunanin yarda zaman nasu zai kasan ce
Daga bisani tayi addu’a bacci mai nauyi ya kwashe ta.
Bata tashi ba har sai da taji kiran sallah asuba.
Dubawa tayi taga ba alamun Marwan, wani dadi taji ganin bashi a dakin.
May be yana night duty ne ta fada a ranta.
Alwala tayi, ta yi sallah. Tana idar wa tayi azkhar ta koma baccin ta.
Sai 8:00am taji kamar akwai mutum a toilet.
Yana fitowa suka hada ido, ba riga jikin sa ya daura towel a kugunsa.
Kauda kanta tayi ta kalla wani wajan, good morning ya fada ya bar mata dakin.
Bayan sa ta tsura wa ido, har ya bace mata.
Bayan minti talatin taga ya sake shigowa da tray na abinci a hannun sa ,ya aje mata a kasa yace bismillah.
Kallon sa Na’ima tayi, har ya shirya ya saka kafta yayi kyau ya fito ango sosai sai baza kamshi yake.
Zama tayi kasa bude flasks din abincin yayi ya zuba mata.
Kallon plate din tayi taga pepper soup ne da soyayyan dankali.
Kallonta Marwan yayi sanye take da rigar bacci jikin rigar an rubata sleeping beauty karama ci iya kwiwarta.
Sorry jiya ban dawo da wuri ba, Marwan ya fada kai tsaye.
Naje asibiti ne.
Kallon sa Na’ima tayi ta fara cin abincinta bata ce masa komai ba
Na’ima!
You should say something mana, ya fada yana kallon ta.
Tashi Na’ima tayi ta bar abincin tace ni ina ruwana idan baka dawo ba, kasan fa auran nan ba wani dadewa zaiyi ba.
Tana fadar haka ta zauna saman gado .tsayi yayi yace ni kam ba na fada maki ba, ba zan sake ki ba Na’ima don haka ki ma saki jikin ki da gidan nan.
Yana gama fadar haka ya fita ya bar mata dakin.
Tsaki tayi ta kwanta abunta.
Pls vote .Marwan na fita daga dakin su, kitchen ya shiga ya wanke hannun sa.
Yana gama wanke wa ya dauko karamin towel ya goge hannun sa da shi .
Dakin sa ya koma, ops dakin su!
Yana shiga ya bude walldrop din sa ya dauko English wears dinsa riga da wando.+
Duba gefen sa yayi yaga Na’ima a wance tana bacci,
Duban kayan jikin ta yayi da alama tayi wanka, ta saka wata karamar shirt wada ta kai iya cinyar ta.
Bin bayan ta yayi da kallo kafin ya maida duban sa zuwa ga kafet din ya kalla yaga bata kara cin abincin ba.
Yanda ya barshi dazu haka ta barshi a nan.
Daga kafadar sa yayi, irin ko a jikina hannu yasa ya dauka tray din ya fita da shi kitchen.
Yana ajewa ya shiga palor ya sake kayan jikin shi ya koma daki ya feshe jikin shi da turare.
Kallon ta yayi, zuciyar shi na cike da tausayin ta.
Hannun sa yasa zai taba ta amma sai wata zuciyar tashi ta gargadesa da yin hakan.
Zama yayi gefen gadon yana kallon kyakyawar fuskarta.
Kallon kanta yayi yaga gashin kanta har gadon bayan ta.
MashaAllah! Ya furta a hankali.
Hannun sa yasa yana shafar kan nata a hankali.
Tana fara motsi ya bari, tashi yayi ya dauko wayar sa text ya tura mata kafin ya fita ya koma aiki.
Na’ima na tashi daga bacci, toilet ta shiga tayi brush.
Ta dauko wayar ta zata shiga instagram sai taga text message ta gaban screen din wayar ta.
Tana dubawa taga sunan Marwan ne, budewa tayi ta karanta.
Hey wifey, Akwai emergency aikin da zan yi yanzu
take care of your self, akwai abinci a kitchen idan kinji yuwa sai kice.
Tsaki Na’ima ta yi, tace lallai ma wannan mutumnin!
Me yake nufi da bari na a gida ?
Number din sa tayi dailing, yana picking .
Ta fara masifa, Marwan me kake nufi ne?
Ya zaka barni a gida sai kace wata mai gadin ka.
I have already told you ba zan iya zama da kai ba, ka sake ni Marwan idan har kana neman zaman lafiya.
I hate you! Ka sake ni ina so na koma aiki na ba zan zauna zaman gadin gidan ka ba ka ji ko!
Hey woman!
Watch your mouth ok! Marwan ya fada cikin dacin rai, ransa ya baci sosai.
Tun da yake duniya ba’a taba masa irin wanan ba.
Shi mata ke binsa suna son sa, amma yau wai mace ke fada masa bata son sa kai tsaye!
Ya rasa meyasa ya kasa tsanar Na’ima koda yayi kokarin yin hakan ya kasa,
Hakurin sa ne ya kare jin ta kara ambato masa kalmar saki.
Ba zaiyu ina mijinki ba ki rika fada mun irin wannan maganan ba .
Ki sani hakkin ki ne ki kulla da gida na, koda baki sauke sauran hakkina ba, ina ganin ya dace ki sauke wannan.
Maganan aiki kuma ina ce, tun a gida kinsan iyayenki sune suka hana ki aiki bani ba,
STORY CONTINUES BELOW

So don’t put blame on me ok?
Iyayenki sun aura mun ke ne Allah ya sani ina kokarin sauke nawa hakkin a kanki.
Amma ki sani Na’ima ni mace bata isa ta raina ni ba don kawai tana sunan matata.
Ba zan yi tolerating wannan Attitude din ba.
Am a peace man, bana son ana mun hayaniya kin gane ko?
Yanzu ka fara ganin hayaniya Marwan idan baka mun abun da nake so ba.
Na’ima ta fada cike da tsiwa.
Ba zaki daina ba kika ce?
Cewar Marwan
Abun da kaji shi na fada mtsww ta kashe wayar.
Tana aje wayar ta canza kayan jikin ta riga da wando ta saka sai ta daura 👘kimono ta sama.
Sun 👓glasses dinta ta saka ta feshe jikin ta da turare.
Side bag dinta ta naga ta dauka da wayarta.
Tana fita gate client dinta ta kira ta bashi adrees din wajan da zai same ta.
Tana gama wayar ta, taxi tahau zuwa wajan da zata hadu da client dinta.
*******†*******-********************
Marwan ne zaune a office dinsa ya zuba tagumi .
Doctor! Doctor!
Zara ce ta shigo da wani file a hannun ta tana kiran marwan amma hankalin sa yana wani wajan daban.
Hannu tasa ta dan buga desk din.
Kallon ta Marwan yayi cikin razana, yaushe kika shigo ne?
Cike da mamaki zarah tace Dr. Marwan lafiya?
Meke damun ka ne?
Tunda nike ban taba ganin ka cikin yanayi irin wannan ba.
Murmushin takaici Marwan yayi ya kalli zarah yace, ba komai zarah.
Karban file din yayi daga hannun ta yace ki tafi kawai ba damuwa am fine.
Matsowa zarah tayi kusa dashi cike da yanga ta rike hannun sa tace Dr. Am here if you need some one to talk to.
Tana gama fadar haka tabar office din.
Tana fita Marwan yayi ajiyar zuciya, yabi bayan ta da kallo.
Tashi yayi ya bar office din male ward ya shiga ya duba patient dinsa .
Misalin karfe 6:00pm ya tashi daga aiki.
Direct restaurant yaje ya saya masu abinci kafin ya koma gida.
Yana shiga gidan yayi parking motarsa.
Yana shiga cikin gidan yayi sallama yaji shiru ba’a amsa masa daki ya shiga ya bata nan aje abincin da ya sawo yayi a kitchen .
Gaban sa ne ya shiga faduwa, ya duba ko’ina bai ganta ba.
Wayar sa ya dauko yana shirin kiranta kenan sai gata ta shigo palorn.
ina kika shiga Na’ima?
Ina matsayin mijin ki ki fita ba tare da na sani ba?
Idan wani abu ya faru dake fa?
What will i tell your parents?
Answer me Na’ima!
Tambayan ki nake!
Don’t shout Marwan ta fada tana kallon sa.
Cike da yanga ta shiga takunta zuwa dinning table Aje side bag dinta tayi saman dinning table.
Ta cire kimono dinta, ta tsaya daga ita sai black and white top da jeans din da ta saka.
Matsowa tayi dab da fuskarsa, kyakyawar fuskar sa ta kalla ta shafa gefen fuskarsa.
Hakika ba karamin yaki take yi da zuciyarta ba don kuwa tana jin son Marwan amma her pride won’t let her show him that love.
She looks in to his brown eyes, ba abun da ta gani sai zallan sonta da taga ni.
Marwan!
Ta furta cikin sanyi murya, matsawa tayi kusa da kunnan sa tace don’t worry about me ok?
Am grown up woman, I can take care of myself.
Tana gama fadar haka ta shiga kitchen ta barshi nan tsaye.
Daki ya shiga ya cire kayan jikin sa ya shiga wanka.
Hakika Na’ima na neman rikitar dashi don yanzu kam ya yarda sonta ya kamashi.
Idanunsa ya rufe amma yana ganin surarta, salon tafiyarta da muryarta.
Yana fitowa wanka ya ganta ta shigo dakin da plate a hanunta.
Akwai abinci a saman dressing mirror yana fada ya bar dakin don baya son yin wani fada yanzu.
Pls vote bellowZarah ce zaune suna fira da wata kawarta, kasan cewar yau sunday bata je aiki Ba.
Zarah! Zarah!
Safna ce ta kirata amma gaba daya hankalin zarah baya tare da ita.
Lafiya!
Safna ta fada tana kallon Zarah cike da mamaki, what is wrong with you kawata?
Ajiyar zuciya zarah tayi tace wallahi safna ina ganin ciwon son Dr. Marwan ne zai kashe ni.
Safna na jin haka ta kalli zarah cike da mamaki, wane Dr. Marwan din kike nufi?+
Don’t tell me that arrogant man na hospital din ku?
Shifa zarah ta fada cikin sayin murya.
Toh ke baki fada masa ba?
Murmushin takaici zarah tayi
tace Safna a matsayina na mace na zubar da aji na na fada masa,
amma gayan nan yace shi ba soyayya bace a gaban sa hasali ma ba yanzu zaiyi aure ba.
Sai daga baya kuma naji ance yayi aure Safna ba dole raina yayi baki ba.
Ina cin rudun son sa na rasa yanda zanyi da raina safna.
Kin san kuma halin da nike ciki yanzu safna Abba bashi da wani buri a yanzu tun bayan rasuwar mahaifiyata,
sai ganin ya aurar da ni kasan ciwar yana da yawan shekaru a yanzu kuma nice diyar sa kwaya daya tal a duniya.
Amma ya zanyi ba wanda nike son ya mallakeni sai Marwan Safna.
Ajiyar zuciya Safna tayi tace karki damu kawata akwai mafita.
Ina mai tabbatar maki sai kin mallaki Marwan.
Yanzu abun da zakiyi shine mu fara da satar zuciyar tasa.
Kina da kyau Zarah tun muna yara zarah kike dauke hankali samari,
ga diri mai kyau ga ki da iya kalamai masu dadi,
Kamar dai ba mace ba!
Kamar ba Zarah kawata da Na sani ba!
Kece fa mai kwara kan maza, har mazan larabawa sun so ki kika ki,
Haba kawas!
Gashi yau Dan Nigeria bakin fata na raina maki wayo.
Kin bani kunya,
Haba zarah, ina wayewar taki ta tafi ne?
Gaki da ilimi diyar manyan mutane, harki tsaya soyayyar da namiji na baki wahala?
Ina so ki fara da wannan mu gani, kin san fa maza sai ana masu haka.
Shegiya kawata!
InshaAllah kawata zan yi amfani da shawarar ki, cewar zarah.
Idan kuma yaki mu bulo masa ta bayan gida muga tsiyar girman kai,
Kuma kawata karki wani damu da cewar yana da aure, karki sa wannan a ranki sam!
Kiyi dai kokarin dawo da hankalinsa wajan ki.
Dariya sukayi suka tafa hannayansu.
************************************
Marwan na tashi gefen sa ya duba yaga ba Na’ima wato ta bar masa gadon kenan ta koma saman kujera.
Kallon ta yayi, fuskar ta tas mashaAllah sleeping beauty ya fada a ransa.
Matsowa yayi wajan da take kwance ya shafi pink lips dinta Wanda sun dade suna tempting dinsa.
Yana ganin ta fara motsi ya tashi da sauri ya bar wajan.
STORY CONTINUES BELOW

kasan ciwar yau ba aiki kitchen ya shiga ya dafa indomie noodles .
Yana gamawa ya zauna yaci abincinsa yasha tea .
Wow kamshin wani turare naji na tashi juyawa nayi naga ko waye yake shigowa kitchen din.
Daga ni har marwan mun kago muga shigowar ta.
Na’ima ce ta shigo tayi kyau sosai kasan cewar ta natural beauty bata yi wata kwaliya sosai ba amma kana ganinta kasan Allah yayi halitta anan mashaAllah.
Sayan take dawata bakar gown irin na larabawa ta daura dankwalin kayan sai zuba kamshi take yi.
Fridge naga ta bude nutela ta dauko da bread ta shafa ta hada tea.
Tun da ta shigo bata lura da Marwan zaune a kitchen din ba, hakan ya bata damar kunna wakar (star boy) mai taken (soko)tana bi tana rawar wakar.
Dariya ce ta kubci wa Marwan, cikin sauri ta juyo ta kalle sa ta bata rai .
Good morning My Queen!
Ya fada yana kokarin hugging dinta, ture sa tayi dasauri
Kallonta yayi cikin mamaki.
Na’ima! Meye haka?
Dont ever touch me Marwan! Ta fada cikin daga murya.
Am your husband remember? Ya fada yana kallon cikin idanunta.
Wa kike so na taba idan ba ke ba, I hav right over you Na’ima .
Amma na maki alkawari daga yau ba zan sake taba ki ba Na’ima.
Yana gama fadar haka ya fita fuu ransa a bace.
Tsaki Na’ima ta yi tace
Whatever !
oho dai kai ka sani.
Tana gama breakfast din ta, ta dauki wasu document din ta, tabar gidan.
Yana ganin ta fita ya girgiza kansa ba abun da yace mata.
Zama yayi a garden yana tunanin yanda Rayuwar auran nan naso zai kasance.
Shi yana matukar son ta ita kuma tana gudun sa.
Dafe kansa yayi don ji yayi yana sara masa sosai.
Karar message ne ya shigo wayar sa.
Yana dubawa yaga Zarah ce, bude message din yayi.
Salam Dr. I hope you are doing fine?
Wayar ya dauka ya shiga rubuta mata reply ga mamakin sa sai yaji zuciyar sa gaba daya ta rage zafin da take masa.
Gaba daya zarah ta wanke masa bakin cikin da ya shiga dazo.
Zarah kina ina ne?
Yana tura mata nan da nan tayi reply
Ina gidana da ke gwarinba.
Ta tura masa.
Yana gani yayi mata reply.
I want to meet you.
Tura mata.
I hop am not dreaming Dr.?
Ta tura masa.
I will see you in the next few hours .
Ya tura mata.
Sosai zarah tayi farin cikin jin Dr. Marwan zai zo ganin ta.
Tashi tayi da sauri ta shiga kitchen ta fara hada masa varieties na abinci.
Tana gamawa ta gyara kitchen din .
Wayarta naga ta dauko, safna ta kira ta fada mata zuwan marwan din.
Ki tambatar kin ja hankalin sa, cewar safna.
Suna gama wayar ta shiga wanka.
Tana fitowa ta shafa mai da turaruka kala kala.
Zama tayi ta fara makeup kai kace yau ne bikin ta.
Riga da skirt na atampa ta saka wanda suka fito da surar jikinta gaba daya.
Fitowa tayi parlo ta saka turaren wuta da shin fida kafet ta jera kulolin abinci da ta hada masa.
Zama tayi tana jiran isowar sa.
Bayan wasu dan mintuna taji wayarta tayi ringing.
Tana dagawa taji muryarsa, ajiyar zuciya tayi.
Zuwa tayi ta bude masa gate din gidan ya shigo da motar sa.
You are welcome Dr.
Ta fada tana murmushi har fararen hakuranta suka bayyana.
Thank you zarah, ya fada yana kallon idanunta.
Shiga tayi ta gaban sa ta fara takunta kai kace dawisu ce.
Marwan na shiga gida yaji kamshi ya doki hancin sa.
Zama yayi sayin Ac na shigar sa yana shakar kamshin gidan.
Wani farin ciki yaji har cikin ransa.
Ina ma ace Na’ima ce ke masa irin wannan.
Iska yaji an hura masa a idanun sa, yana budewa yaga zarah tana masa murmushi zo muci abinci ta fada tana cire masa hular kansa.
Zama yayi saman kafet din ita ma ta zauna ta zuba masa abincin ta mika masa.
Karba yayi inda yabi hannun ta da kallo.
Tasha zanin lalle.
Kinyi kyau ya furta ba tare da ya san lokacin da ya fada hakan ba.
Murmushi Zarah tayi tace kai ma kayi kyau sosai.
Spoon ya dauko ya fara cin abinci.
Zarah dama kin iya girki haka?
Marwan ya fada yana kai wani spoon din bakinsa.
Murmushi kawai zarah tayi .
Bayan sun gama cin abinci, taya ta yayi suka kai plates din kitchen.
Suna komawa parlo ya zauna yana latsa wayar sa,
Zama zarah tayi tana kallon ikon Allah dama haka Marwan yake?
Mutum ne mai saukin kai?
Haka yake rayuwar auran sa?
Tunawa da yana da aure da tayi sai taji gaba daya ranta ya baci.
Bayan mintina kadan marwan yaBayan mintuna kadan marwan ya bar gidan zarah cike da farin ciki.
Har waje ta rako shi, Dr. Na gode sosai da wannan ziyara
I really appreciate thank you so much.
Kallon ta yayi cikin ido yace thank you soo much Zarah nike da godia.
Murmushi zarah tayi tace Dr. Kenan ba komai wallahi ta fada cike da shagwaba.
Kallonta yayi yaga ta burgi shi, irin yanda take kallon sa ,DA yanda take masa magana .
Wai meke damuna ne?
Ya fada cikin ransa.
Dr.!
Zarah ta kira shi .
Sai a lokacin hankalinsa ya dawo kansa.
Shiga yayi cikin motar sa, ya daga mata hannu kafin ya bar gidan.
************************************
Yana fitowa gidan sa ya koma direct, yana shiga cikin gidan yaga Na’ima a parlo zaune gefenta cup din coffee ne.
Sanye take da wata half vest baka da wani wando iya gwiwarta kalar fari DA ratsin baki kanta ta daure shi da ribbon bata .
Idanunta cikin wani farin glass irin wanda masu ciwan ido suke amfani dashi wajan karatu.
Gabanta kuwa wasu takardu ne tana dubawa.
Kallon tsaf yayi mata, ya lura ko shigowar sa bata jiba, tana faman karatun ta.
Tunawa yayi da yanda dazo zarah ta tarbi shi cike da kulawa, ina ma Na’ima ce ke masa haka, DA yayi farin ciki sosai.
Sallama yayi be jira amsar ta ba kawai ya nufi daki,yana shiga wasu littafan yaga ni ta barsu ako’ina har sai da ya taka wasu kafin ya shiga dakin.
Kada kansa kawai yayi kafin ya cire kayan jiginsa wanka yayi ya sake wasu kayan..
Ya fito parlo yana baza kamshi, kallon sa naga Na’ima nayi ta gefen ido, da alama tasan da shigowar sa.
Gyaran murya yayi, yace I need to talk to you Na’ima, ta kalle sa
What do you what?
Ta fada tana kallon kwayar idon sa, kazo ka tsaya mun a ka
Gabanta ne ya fadi ganin ya kara mata kyau haka nan dai ta daure ta fara masa magana.
Baka ga abun da nike yi bane?
Wai malam me yake damun kane ?
Pls don’t disturb me ina da zaman kotu gobe, tana fadar haka ta cigaba da abun da take
Kallon ta yayi, yaga ta kara masa kyau, Ya salam yarinyar nan fa na rikitar masa da lissafi.
Na’ima dakina ba library din da zaki na ajiye mun littafan ki bane kin jiko?
Ya zaki rika ajiye mun littatafanki ta ko’ina babu ma hanyar da mutum zai shiga daki.
Matsawa yayi kusa da kujerar da take yace.
I don’t want anything from you ok!
Zuwa yayi dab da ita ya kalleta sosai yace Sunana MArwan Umar!
Not malam kin gane ko?
So don’t shout at me like that ever again! Ya fada yana kara jaddada mata kalmar “again “
Yana gama fadar haka ya fita fuu..!! Ransa a bace.
Binsa Na’ima tayi da kallo tace, kai kaso ranka ya baci ae mtsww tsaki tayi tace gaba da karatun ta.
Har yau bata gane meyasa take wa? Marwan rashin kunya ba.
She know deeply inside her heart she loves him more than she can say.
STORY CONTINUES BELOW

Amma kuma her pride won’t let her show him.
Ringing din wayarta taji zubur ta mike ta dauko wayar, tana dubawa Number din aunty zaynab ce.
Murmushi tayi kafin ta dauka,
Nayi fushi aunty zaynab gabadaya kin manta dani ko?
Ya mai gidan naki ? Cewar aunty zaynab .
Haba aunty baki tambaye ni ya nike ba sai shi?
Haba Na’ima kardai har yau baki hakura da abun da ya faru ba kin bi mijinki?
Meke damun kine Na’ima Ibrahim Giwa!
Aunty zaynab ta fada cikin daga murya.
Hmmn aunty kenan, kin manta ni ne? Ba abunda nafi so irin aiki na neman na kai na shine buri na na farko a rayuwa.
Is my first priority in life!!
Kuma kin fi kowa sanin sana diyar auran Marwan iyayena suka hanani aiki gabadaya.
Yaushe kuma zan iya wani farin ciki dashi bayan harda shi cikin matsalar da na shiga.
MARWAN UMAR!
aunty shine wanda ya shigo rayuwata a lokacin da ban shirya ba.
Ba zan boye mike ba aunty ina matukar son sa fiye da yanda kike tsammani .
Amma kuma ba zan iya nuna masa wannan son ba hasali ma, sana diyar abun da ya faru na tsane shi a halin yanzu.
Kawai burina ya sake ni aunty !
Kul! Na’ima ina mai baki shawara da kibi mijinki tun kafin kiyi dana sani
Ni banga dalilin da zai sa ki tsane sa ba, saboda shima aura masa ke akayi ba tare da yasan kowacece ba.
Kiji tsoron Allah kibi mijinki Na’ima kina jina ko?
Tun kafin wata ta karbe maki shi kina ji kina gani.
Ki guji ranar Dana sani Na’ima!!
Na’ima na jin haka ta fara kuka, aunty ba zan iya ba tana fadar haka ta kashe wayar. Dib
Kwashe takardun tayi ta koma daki tana mamakin yanda aunty ta ke fada mata irin wannan kalaman
Shin kamar bata San burin ta a rayuwa shi want nothing but fame and power.
Duniya ta San ta, kuma ta zama mai fada aji .
A haka dai bacci me nauyi ne ya kwashe ta.
************************************
Marwan na fita daga gidan sa, gidan su ya nufa .
Ya gaisar DA baba mai gadi cike da girmamawa.
Babban parlo ya shiga ya tarar da mahaifinsa a kishingide yana waya.
Zama yayi har mahaifin nasa ya gama wayar.
Dukar da kansa yayi ya gaishe da mahaifin nasa cike da girmamawa .
Suna gama gaisawa mahaifin sa ya kalle sa .
Ya matar taka?
Lafiya lau Abba ya fada .
Toh mashaAllah,
Da wani matsala ne ?
Gyara zama Marwan yayi kafi yace Abba dama ina so zan yi tafiya ne na wani course da zanyi a London.
Toh madalla, da matar taka zaku tafi kenan? Cewar Abba
Shiru marwan yayi na dan lokaci kafin yace Abba munyi magana da ita tace ita zata zauna a Nigeria har na dawo..
Toh toh madallah, course din shekara nawa ne?
Shekara uku ne Abba.
Kallon marwan Abba yayi yace ka tabbatar haka tace ba matsala?
Eh Abba haka tace.
Toh mashaAllah.
Yaushe kenan zaka tafi?
Zuwa next week inshaAllah.
Toh shikenan Allah ya kaimu lafiya.
Amin Abba.
Marwan na gama magana da mahaifinsa ya shiga dakin mahaifiyarsa.
A zaune ya same ta tana lazimi, zama yayi gefenta har ta idar.
Suna gama gaisawa tayi masa maganar Na’ima.
Shiry marwan yayi yace tana nan lafiya lau.
Ko da wani matsala ne marwan? Mami ta fada tana kallon dan nata.
Shiru yayi na dan lokaci yace babu mami, toh mashaAllah
Allah ya hada kanku ya baku zaman lafiya.
Amin mami kawai ya fada.
Mikewa yayi yace Mami zan koma gida naga dare ya fara yi
Baza ka jira a gama abincin ba, murmushi yayi yace na koshi Mami.
Har ya tuna dazu girkin da zarah tayi masa, har ya manta rabonda ya ci abinci dayawa irin na ranan.
Toh shikenan a gaida Na’ima,
toh mami ya fadar haka ya fita.
Zuciyar shi cike da tunani, don be San yanda Na’ima zata dauki maganar ba.
Pls vote and comment belowZaune yake gaban sa wani cup din tea ne.
Idanun sa sanye da farin glass ,wata takarda na gani a hannun sa yana dubawa.
Gaba daya hankalinsa baya tare dashi tunani yake yi ta ya zai tunkaro wa Na’ima DA wannan maganar?
Shin ya zata dauki maganar tasa?
Zata yarda ta zauna har yaje ya dawo kuwa?
Yasan Na’ima sarai. ba zata bishi zuwa wani gari ba, balle wata kasa, har tsawon shekara uku kuma.+
Kuma yasan da kyal ta zauna gidan sa har ya dawo sai ta ambato masa kalmar da yafi tsana a duniya
Wato kalmar saki!
Hakika son Na’ima na shirin zautar dashi gaba daya .
Gaba daya Na’ima ta canza masa tunani bashi da wani tunani a yanzu kamar nata.
Yana neman cire ta a ransa don ya lura bata damu da shi ba, wato shi kadai ke kidansa yana rawar sa.
Sonta! Sha’awarta sun dame sa a hanlin yanzu amma yayi alkawarin shi da taba ta har abada, har sai ita da kanta ta bukata hakan.
Assalamu Alaikum Dr.
Wata nurse ce ta shigo da wani file a hannun ta.
A lokacin ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga dazu.
Ajiye shi anan ya fada ba tare da ya kalli fuskarta ba
Har ta fita naga ya sake kiranta.
Nurse!
Juyowa tayi tace
Yes sir!
Call the next patient ya fada kurba tea dake gaban sa.
Wani matashi ne ya shigo zai kai kimanin shekara 20.
Bismillah zauna, cewar Marwan kare masa kallo yayi yaga ba alamar ciwo a jikin sa .
How may i help you?
Marwan ya fada yana kallon yaron.
Shiru yaron yayi.
DA alama bai gane abun da aka tambaye sa ba.
Me ce ce matsalar ka Marwan ya fada yana kara kallon yaron
Sayen yake da wata riga duk ta kode ,wandon sa kuma a yayyage
Tsugunnawa yayi har kasa ya kalle Marwan idanunsa nazubar da hawaye yace
Dr. Ina so ka taimaka mun dan Allah mu talakawa be, akwai yar uwata bata da lafiya ka taimaka ka cito mana ranta Dr.
Zuba masa ido marwan yayi, hawaye na zuba saga idanun sa.
Gaba daya tausayin yaron ya kamashi,
Ina yarinyar take?
Kuma mai ya sameta?
Tana kwayan mu, jiya na zo birni bansan kowa ba.
Wasu ne suka yi mata fyade Dr. Ka taimaka mana, mu marayu ne.
Akwai wata mata da muka hadu DA ita jiya a police station tace mu zo mu same ka zaka taimaka mata kuma ita ma zata taimaka mana wajan kwato wa yar uwata yancen ta..
Ga wannnan takardar tace na baka.
Kallon tsaf Marwan yayi wa yaron
Innalilahi was inna’ilaihi raji’un
Fyade!
Kuma su nawa?
Kuka sosai yaron ya fara yi, yace Dr. Su biyar ne amma sun gudu an rasa inda suke Dr.
STORY CONTINUES BELOW

Kuma baki ne daga birni, bamu san ko yan wane gari bane.
Shiru marwan yayi na Dan lokaci yace ya sunan ka?
Bello sunan na ya fada da sauri.
Karbar takardar Marwan yayi ,yace ina ne kauyan naku?
Wani kauye ne likita hanyar kaduna.
Kallon sa marwan yayi vikie DA tausayi yace Toh shikenan .
Sai kayi kokarin kawo ta gobe don a duba lafiyar ta.
Tsugunawa bello yayi har kasa yana zuba godiya har sai da Marwan yace masa ya tafi kawai ba komai.
Yaron na fita Marwan ya bude takardar.
Assalamu Alaikum
Dr. If I will ask for any favour from you it will be the last favour
” safe the girl life!! “
You don’t need to know who I am,
but I know you are a kind person.
Have a good day!
Zuba wa takardar ido yayi yana mamakin wacece wannan matar?
Kuma meyasa sai asibitin shi ?
Shin ina ma ta San shi ne?
Yayi Alkawarin taimaka masu, ba tare da ya karbi ko sisi ba .
Yana gama fadar haka yaji an kwankwasa kofar office din sa yana dubawa yaga Zarah ce.
Ganin ta yayi ta kara masa kyau, sayen take cikin uniform din ta na nurse rike take da wata karamar paper.
Tana shigowa tayi mashi murmushi tana takunta daya daya har zuwa wajan da Marwan yake zaune.
Kallon ta naga marwan yana yi gabadaya hankalin sa yana kanta.
Hura mass iska tayi a idanunsa tace Dr. Kana lafiya?
Ta fada cike da shagwaba.
Cup din da ke hannun sa ta karba ta Dan kurba kadan, tace Dr. Yunwa nake ji
Pls kazo muje muci abinci, ta fada tana langwabar da kanta irin yanda yara keyi.
Data kansa tayi taji yayi zafi, ta kalle sa day sauri Dr. Lafiya?
Baka da lafiya ne?
Gaba daya zarah ta rude, kallon ta Marwan ya tsaya yi ganin gabadaya ta shiga damuwa.
Shafa gefen fuskarta yayi yace zarah kinga wani yaro da yafita yanzun nan?
Eh na ganshi, meya faru?
Ajiyar zuciya naga marwan yayi ,kafin ya sake daga ido ya kalle ta.
Yace zarah fyade aka yi wa kanwar sa a kauyen su, har mutum goma!
Innalilahi wa inna’ilaihi raji’un!
Ya salam, Dr. Mutane basu da tsoron Allah ,yanzu zasu so ayi wa kanwar su haka?
Allah ya tsare mu, ya kuma ba yarinyar lafiya.
Amin, cewar marwan.
Zanyi kokarin ganin na taimaka masu ba tare da sun biya ko sisi ba inshaAllah.
Murmushi zarah tayi tace Allah ya baka lada, naji dadi sosai Dr da zaka taimaka masu.
Ba komai ai yiwa kai ne.
Rike hannun sa naga zarah tayi, tana dan murmushi lets go and eat Dr.
Akwai aiki sosai a gabana zarah, me je kawai.
No Dr. Ta fada tana turo lips din ta,
Marwan bai san lokacin da yayi locking lips din sa da na Zarah ba.
Sauri yayi ya matsa yace sorry pls.
Kallon sa Zarah tayi, ta matsa kusa dashi tace.
Karka yi nadamar abun da kayi yanzu, na yafe maka ta fada tana murmushi.
Har zata fita, Marwan ya tashi da sauri ya rike mata hannu, janta yayi ta fada kirjin sa.
Gaban zarah ya shiga fadawa da sauri, kallon idanun sa tayi sunyi ja sosai.
Meyake faruwa Dr.?
I need you yana fada haka ya shiga 💏 din ta saida yaga ya samu had in kanta tukunnna ya matsa.
Rike hannun ta yayi yace zo muje
Kallon sa zarah tayi cikin sauri tace doctor ina zamu je?
Juyowa yayi ya kalleta yace zarah kina so na?
Daga kanta tayi alamar eh
Do you trust me?
Tace eh, I trust you doctor.
Then let’s go!
Har zata kara yin magana ya sa dan yatsansa shsish ya rufe mata baki alamar tayi shiru
Rufe file din da ke table din sa yayi ya cire lab coat din sa ya rike mata hannu yace let go!1
Murmushi tayi masa suka fita.
Pls vote and comments
Kai masu karatu karfa marwan ya juya akalar sa…
Ya kuke gani zarah zata cimma burin ?
Shin Na’ima tayi daidai wajan maida hankalin ta wajan aikin ta?
Ko kuna ganin abun da ta yi kuskore ne?.Na’ima na gani ta fito daga kotu sanye take da wata bakar jallabiya irin ta larabawa kanta kuma hula ce fara irin turban din nan.
Hannun ta rike da file,
Barrister!+
Juyowa naga tayi, tana neman me kiranta.
Barristers Na’ima!
Taji an kara fada, tana kara juyowa taga wani saurayi tsaye a gaban ta.
Do I know you?
Ta fada tana kallon sa cikin rashin sani.
Murmushi yayi yace Na’ima Ibrahim Giwa right?
How do you know my name?
Ta fada tana kallon sa cikin ido.
Murmushi yayi har fararin hakoransa suka bayyana.
Kallon ta yayi yace ina so ki janye wannan case din saboda iyayen yaran nan zasu iya baki ko nawa kika bukata don kar wannan magana ta fito barrister.
Kallon sa tayi cikin mamaki tace who that hell are you to tell me that?
Matsawa tayi kusa dashi tana Nuna sa da yatsan ta tace
I don’t know who you are and I don’t bloody care!
but you don’t have any right whatsoever to tell me any rubbish that comes out of your mouth ok!
Kasani koda yan gidan mu ne suka aikata wannan mumunan laifi ba zan taba janyi wannan case din ba.
Kasan cewar su yayan gwamnoni ,ba zai hana a hukunta su ba wallahi.
Murmushi naga Na’ima tayi, kafin tace Kai dan sako ne ina so ka fadawa wanda ya aiko ka.. BAZAN JANYE WANNAN SHARI’A BA!
And I don’t care what the out come will be.
Enough woman!
Saurayin naga ya fada cikin daga murya.
Mind your words!
Yana fadar haka ya fice fuu..!
Cikin motar ta naga ta shiga ta bar harabar koto.
Ajiyar zuciya ta saki.
Ya Allah ka bani sa’a akan mutanan nan ta fada cikin ranta.
Har zuciyar ta bata da wani buri ila na taimakon wadan nan yara da aka zalunta, tayi alkawarin kwato wa yarinyar yancin ta.
Wato don su yayan masu kudi ne shine suke so case din ya mutu?
Tir da irin wannan zalunci, yarinya karama an cuci rayuwar ta gabadaya.
Sai dare likis ta dawo gida, tana shiga kitchen ta shiga ta dafa indomie da kwai .
Tana gama ci ta koma daki, ga mamakinta sai ta ga ba marwan a dakin,
Koda bata damu da shi ba tasan Marwan duk ranan monday gida yake kwana hasalima yana dawowa gida da wuri kafin magrib gashi yanzu har 11:30pm na dare .
Wayarta ta dauko zata kira shi, Tsaki ta danyi tace ko meyasa ma na damu?
Kayan jikinta ta cire ta daura towel dinta ta shiga wanka.
Tana fitowa ta saka kayan baccin ta ta feshe jikin ta da wani Arabian turare kafin ta yi addu’ar bacci.
Ta rufe idon ta amma bacci ya gagara zama tayi tsakiyar gadon tana tunanin wanan irin lamari
Meyasa ta damu da shi haka?
Tsaki ta karayi, tace shi yasa ni ae.
Sai da ta gama harhada takardun da take bukata ta yi nazari a kansu tukunnna
STORY CONTINUES BELOW

Sai bacci barawo ne ya kwasheta.
************************************
Marwan ne kwanci a gado shi da zarah, hankalin sa kwanci yana sharar bacci.
Doctor!
Zarah ta kirashi tana shafa fuskar sa, bude idanun sa yayi ya maida su kan ta.
Zarah ya kirata
Bude idanun sa yayi ya zuba su a kanta
Tana kwance a kirjin sa,
Innalilahi was innailaihi raji’un!
Doctor lafiya?
Zarah ta fada cikin sauri.
Runtse idanun sa yayi, yace zarah wallahi tunda nike ban taba aikata zinah ba, amma yau shedan yaci nasara a kaina.
Kallon sa zarah tayi cike da mamaki gaba daya hankalinsa a tashe yake.
Tabe baki tayi tace doctor toh ni meye nawa aciki?
Kaine fa ka bukaci hakan daga gare ni, kuma na aminci maka without giving a second thought!
Hakika son da nike maka shi yasa na yarje maka da biya maka bukatar ka.
Kasani doctor a budurwa ka same ni, ban taba ma’amula da wani da namiji ba sai kai,
Wannan kuma alkawarine nayi wa zuciyata, kai ka daine namijin da zan iya mallakawa kaina.
Shiyasa bani da wani buri sai na auran ka Marwan umar!
Tana fadar haka ta rufe idanun ta na minti daya.
Wallahi zarah ba laifina bane .
Na’ima ce!
Doctor! Zarah ta kara kirin sa.
Wacece kuma Na’ima?
Kallon zarah yayi cikin ido, itama shi take kallo, tana jiran amsar sa.
Shiru yayi yace, I don’t want to talk about it.
Tashi yayi ya shiga toilet, wanka yayi ya fito ya kalli zarah yace ki boye wannan sirrin tsakanin ni dake,
Kallonta yayi yaga jikinta yayi sanyi, matsawa yayi kusa da ita murmushi yayi mata har sai da dimple dinsa ya lotsa.
Shafa fuskar ta yayi yace menene um? Shiru tayi masa ta Dan turo baki
Wayar sa ce tayi kara, alamar kira ya shigo.
Yana gama ansawar yace, I have to go now.
Kallon sa zarah tayi cike da kissa tace haba doctor ka jira mu tafi tare mana. Sorry zarah emergency ne.
Ina yarinyar da nayi maki maganar ta wadda aka yiwa fyade?
Eh na gane ta, cewar zarah.
Itace aka kawo yanzu, shiyasa zan tafi.
Matsawa tayi kusa dashi cike da yanga hips dinta ya kalla gaba daya tana neman rikita masa lissafi.
Kusa dashi naga ta je tayi masa peck a lips din sa tace ok.
Take good care of your safe.
Har zata matsa Marwan ya kamo hannun ta, fadawa tayi saman chest din sa har tana yar kara.
Take care of your self for me too zarah ya rada mata a kunne.
Murmushi tayi tace i will doctor.
Sai mun hadu anjima ,yana fadar haka ya kashe mata ido.
Dariya tayi sosai tana daga masa hannu, alamar bye.
I love doctor, ta fada tana kallon bayansa.
***********************************
Bayan ya dawo daga Hospital cikin sa’a ya samu ceto rayuwar yarinyar.
Marwan na shiga gida ya tarar da Na’ima na shirin fita itama.
Kallon tsaf yayi mata, English wears ta saka sai ta dura bakar kimono ta yafa karamin gyele.
Hannunta wasu files ne sai baza kamshi take.
Har zata wuce shi ya kira sunan ta.
Amsa masa tayi ba tare da ta juyo ta kallesa ba.
Ina zaki je?
Wane irin tambaya ce wannan Marwan? Cewar Naima
Juyowa tayi tana kallon sa cike da mamaki
Tambaya ce nayi maki a matsayina na mijin ki, ina kuma bukatar amsa yanzu, cewar marwan.
Zama marwan yayi a kujera yana kallonta.
Aiki zan je mana, ta fada tana kauda kanta gefe.
Murmushin takaici yayi yace Na’ima ina son magana dake ne.
Zaro manyan brown eyes dinta tayi tace not now
Kallon agogonta tayi tace, ina da abunyi yanzu, nan da 49minutes zan shiga kotu.
Idan kana da magana gaskiya sai dai ka jira zuwa next week.. Satin nan gaba daya ,zan zama busy ne.
Kallonta yayi cike da mamaki, Na’ima yanzu ni mijin ki bani da right na magana da ke alokacin da nike buka ta, har sai kin fida rana?
Ke wace irin mace ce wai!
Baki tsoron Allah zai tambaye ki?
✋Wait, dakata Marwan!
Ta fada tana daga hannunta.
Ba lecture nike bukata ba yanzu, ina da abunyi.
Idan kana ganin ban dace da kai ba, ka sake ni mana!
Kowa ya huta, tana fadar haka ta ja tsaki tayi gaba.
Bayanta Marwan yabi da ido, zuciyarsa cike da bakin ciki.
Inama zaya iya sakin Na’ima, amma ba zai iya ba don zuciyar sa na matukar son ta .
Tashi yayi ya koma daki, toilet ya shiga ya sakar wa kansa ruwa.
Pls vote and commentsMisalin karfe biyu na rana, marwan na gani a wani haddadin resturant, fuskar sa sake yana murmushi
Kai kace bashi da wata damuwa.
Kallon gefen sa nayi, zarah ce zaune tana kokarin bashi ice cream da hanun ta.+
Kallon tsaf nayi masu sunyi kyau sosai kamar wasu mata da miji.
Zarah!
Marwan ya kirata.
Yes sweet, ta amsa masa tana murmushi har fararen hakoranta suka bayyana.
Ina so zanyi tafiya ne for my PHD, and I really want to tell you something important kafin na tafi.
Hmmn !
Ajiyar zuciya zarah tayi kafin tace, ina jin ka doctor.
Kallon ta naga marwan yana yi cikin ido ,ya shafa gefen fuskar ta.
Hannun ta ya rike gam, kamar wani zai kwace masa ita.
I love you Zarah!
Ya furta a hankali, har bata ji abun da ya fada ba.
Doctor!
Shish !
Dan yatsan sa yasa ya rufe mata baki.
Matsowa yayi kusa da kunnanta ya ce
Believe me, I really do!
I am in love with you Zarah!
Murmushi tayi, sai hawaye suka fara zuba daga idonta.
No Zarah, Marwan ya fada ya girgiza mata kansa ,
Yatsan sa yasa ya goge mata hawayen ta yace..
Kar kiye min asarar hawayen ki ok yana murmushi.
I love you too doctor, ta fada tana kallon idon sa.
************************************
Na’ima na gani rike da file a hannun ta, tare da wasu mutane suna taya ta farin ciki sakamakon case din da tayi winning.
Fuskar ta na kalla, cike take da farin ciki.
Matsawa naga tayi daga wajan da mutane suke,
Wayar ta naga ta dauko daga jaka,
Hello Aunty zaynab!
Na’ima ina kike muna gaban gidan ki tare muke da Abba.
Ya salam!
Na’ima na jin haka hannun ta ya fara kyarma, bata San lokacin da ta saki iPhone dinta ba..
Na shiga uku ta furta bakin ta na rawa.
Na’ima! Hello!
Aunty zaynab ta cigaba da kiran ta, tana ji amma baki ya mutu.
Dauko wayar tayi ta kara a kunnanta hello aunty zaynab ,yanzu zan zo na dan shiga gidan makota ne.
Zama Na’ima tayi cikin mota gaban ta sai faduwa yake yi.
Hannunta tasa ta kunna wakar umar M sharif. Mai taken (kin shiga raina)
Dafe kanta tayi tana neman mafita, kallon kayan jikin ta tayi
Gaba daya hankalinta ya kara tashi.
************************************
Zarah ce na gani tare day malamin ta,
Yanzu me kike so ayi mata ?
Haukatar da ita kike so ayi ?
Gyara zama zarah tayi tace a’a bana bukatar hakan malam
STORY CONTINUES BELOW

Ai ka gama min komai tunda hankalin sa ya dawo waje na gabadaya.
Yanzu abun da nike so shine ka sa su tsani junan su fiye da yanzu.
Ina so ya zama na ni kadai ce matar da zata zama yar gaban goshi malam.
Toh madallah, cewar malam
Za kiga canji kwarai kar ki damu.
Toh malam na gode
Zarah na fita daga gidan malam, motarta ta shiga mai kirar Honda accord.
Tana zama ta lalubo wayar ta daga cikin Gucci bag din ta.
Layin kausar ta nema, ringing daya tayi ta dauka.
Nan ta kwashe komai ta fada mata gabadaya.
Shegiya kawata kina wuta!
Dariya sosai zarah tayi tace, ki bari kawai kawata
Kinsan mutunin nawa sai da haka.
Shekara kusan nawa ina faman neman sosayyayar sa abu ya gagara.
Yanzu kam sai yanda nayi dashi wallahi.
Da gaske kawata?
Cewar kausar
Kina ganin wasa bari dai sai kinzo zamuyi magana sosai.
Toh kawata, cewar kausar.
Sallama naga suyi, zarah ta kashe wayar.
Ac ta kunna kafin ta saka wakar Ali jita. Mai taken (love)
Wakar ta shigabi ahankali.
************************************
Na’ima na parking motar ta a parking lot, motar mahaifin ta ta gani anyi parking dinta. ta bude motar ta jakar ta da files din ta naga ta dauko.
Gaban ta sai faduwa yake yi.
Ya Allah! Ta fada tana ajiyar zuciya.
Tana zuwa balcony din gida taga aunty zaynab da Abbanta a zaune suna jiranta.
Assalamu Alaikum.
Ta fada tana murmushi.
Wslm, suka amsa mata gabadaya.
Da saurin ta tayi hugging Abbanta tana gashe shi.
Ture ta yayi da sauri.
Cike da mamaki ta ja baya tana hawaye, Abba!
Ta fada bakin ta na rawa.
Na’ima wato mun hana kiyi aiki shine kika tsallake. Umarnin mu kika kama naki ko!
Kin bar gidan mijin ki kin tafi kotu,
Ina son tun kafin rai ya bace ki bar wannan aikin,
Don idan sarki yaji abun sai yafi haka, kina jina ko?
Kayi hakuri abba, da sanin sa nike yi kuma bai taba hana ni ba Abba.
Kina nufin Marwan yasan kina zuwa aiki shine ya barki bai fada mana ba?
Eh Abba, Na’ima ta fada cikin sauri.
Toh shikenan bari yazu, din shima wato rufawa matar sa asiri yake yi ko?
Zan masa magana don gaskiya banji dadi ba.
Kayi hakuri Abba, cewar aunty zaynab.
Mu shiga ciki, suna shiga palor.
Na’ima ta shiga kitchen tayi girki mai rai da lafiya.
Tana gamawa tayi wanka ta sake kayan jikin ta.
Ta dauko abincin tayi serving din su.
Suna gama cin abinci ta kwashe plates din ta kai kitchen suka koma daki ita da aunty zaynab.
Suka bar Abba a palor.
Suna shiga aunty zaynab ta kalle ta tace ya naga ta kin wani Kara kiba ko dai kin ci wake ne?
Dariya sosai Na’ima tayi tace hmmn aunty kenan.
Tabe baki aunty zaynab tayi ta mika mata magani a ruba tace gashi oya shanye.
Meye wannan aunty zaynab?
Maganin mata ta fada kai tsaye
Kallonta Na’ima tayi tace bazan sha ba.
Haba aunty wai meye haka ne?
Nifa ba fa mu hada shin fida dashi .
What! Na’ima
Kina nufin baki bashi hakkin sa kenan?
Subhanallah! Kina son Rahmar Allah kuwa Na’ima?
Kunyi shekara da aure amma shiru! Muna ta saran ganin baby shiru.
Allah ya shirye ki Na’ima, kidai ji tsoron Allah ki canza hali, tun kafin na fada a gida wallahi.
Ina mai tabbatar miki idan naji zuwa nan da wasu watan ni baki fada mun good news ba toh fah sai na fada masu Abba.
Haba Naima!
Wane hali kike son jefa mijin ki?
Kina so ya fara neman mata ne?
Plus vote bellow.
Sorry guys for the late postMisalin karfe 6:00pm na yamma Marwan na gani ya bude gate din gidan sa, direct parking lot naga ya nufa.
Bude idanun sa yayi sosai, alamar mamaki ganin motar sirikin sa .
Wata ajiyar zuciya naga ya saki mai karfi.+
Bude motar sa naga yayi kayi ya fito da wata ledar abincin da ya sawo, tare da jakar laptop dinsa,
Kana ganin sa kasan ya kwaso gajiya gabadaya ko tafiya dakyar yakeyi.
Yana bude kofar palor, Abban Na’ima ya gani .
Sallama yayi kafin ya shiga, durkusawa yayi cike da ladabi da girmamawa ya gaisar da sirikin nasa.
Ciki da fara’a Abba ya amsa masa, kaga baki ko ba sanarwa?
Murmushi Marwan yayi yace ba komai ai Abba.
Kayi hakuri kasan yana yin aikin namu ban samu dawuwa da wuri ba.
No, ba komai kar ka damu ina son magana da kaine yanzu, shiyasa kaga ban tafi ba.
Gyara zama Marwan yayi yace Abba lafiya dai ko?
Eh lafiya ba lafiya ba Marwan,
Yanzu ace mun saka doka amma don hali irin na yaran yau, ace kun karya ta?
Kafin sarki ya daura maka aure da Na’ima ya baku sharadin hanata aiki ko?
Haka ne Abba
Toh me yasa ka barta tana yi?
Ina laifin ka bata jari ta fara kasuwanci.
Sadda kansa kasa naga yayi, zuciyar sa gabadaya ta rasa me yasa baya son ana masa zancen Na’ima.
Abba kayi hakuri!
Ya furta kai tsaye
Munyi kuskure sosai amma ba zamu sake ba Abba.
Toh madallah Allah yayi maku Albarka.
Amin Abba.
Idan ka shiga ka turo mun zaynab tazo mu tafi
Cewar Abba.
Toh Abba, yana fada ya mike tsaye, daki ya nufa rike da jakar laptop din sa.
Yana sallama ya shiga.
Cike da girmamawa ya gaisar da aunty zaynab, ta amsa masa cike da fara’a.
Suna gamawa ya fada mata Abba na jiran ta.
Tashi tayi tace toh
Tana ganin Marwan ya shiga toilet ta matso kusa da Na’ima tace wallahi da gaske nike
Idan baki gyara ba toh sai na fada kinji na rantse.
Har waje Na’ima ta raka su kafin su kayi sallama da Marwan
Suna tafiya Marwan yayi mata wani mugun kallo har sai gabanta ya fada.. Rass!
Inalilahi, naji ta fada.
Shi kuma wannan me akayi masa?
Ta fada tana bin bayan sa da kallo.
Marwan na shiga cikin palor, dinning table ya nufa.
Yana zama ya bude rubar abincin sa ya fara ci.
Yana ganin Na’ima ta matso shi ya fara fada meye haka kuma!
Kallon sa Na’ima tayi cike da mamaki, hararar sa tayi kafin ta sakar masa wani dogon tsaki.
Wayar ta, naga ta dauka daga saman table din.
Kallon sa tayi tace masifaffe kawai, tana fadar haka ta kara gaba.
Kada kansa Marwan yayi, yana gama cin abincin sa ya koma daki ya yana shirya kayan sa cikin akwati.
Yana gamawa ya dauko wayar sa, yana kallon Na’ima da gefen ido.
Zaune take saman gado tana karanta wani file dake hannun ta.
Zama yayi bakin gadon yace ga wannan .
Kallon hannun sa Na’ima tayi tace wannan fah?
Murmushi Marwan yayi yace key din sabon gida na ne.
Zaki koma da zama gobe, cike da mamaki ta kalle sa kamar ya?
Kana nufin ni kadai?
Eh kamar yadda kika bukata, bazan sake ki ba Na’ima amma ina so zan bar ki kiyi aikin ki kamar yadda kika bukata.
Zaki koma Sabon gida na da ke wuse 2.
Kallon sa Na’ima ta shiga yi baki bude tana jira taji karshen zancen
Na’ima gobe da asuba jirgina zai tashi, so you should take care of both houses kafin na dawo.
Kyafta idon ta tayi, ta ce Marwan ni bazan iya gadi ba ka gane ko!
Don’t! Don’t start Na’ima Marwan ya fada cikin daga murya, yana daga mata hannu.
But nifa..
Shiiish matsawa yayi kusa da ita dan yatsan sa yasa mata alamar tayi shiru.
Don’t say a word!
Ya fada yana kallon kwayan idonta.
Tashi yayi ,yana huci ya bar dakin.
Kuka Na’ima ta saka cike take da tsoransa, bata taba ganin bacin ransa ba irin na yau.
Ya salam!
Kallon kwayar idon sa kadai tayi amma bata ga komai ba sai tsantsar tsanar ta dake idanunsa.
A baya takan ga tsantsar sonta a idanun sa amma yau kam hmmmnn abun ba’a magana.
Kwantawa tayi a gefen gado idanunta na kallon silin.
Kwakwalwar ta gabadaya ta rasa me ke damunta.
Gabanta ne ya cigaba da faduwa lokacin da ta tuna maganar aunty zaynab.
Wayarta naga ta dauko ta kira kawarta Aisha.
************************************
Zarah ce zaune da kawayan ta biyu kausar da safna .
Kausar ce ta tashi ta dauko 🍸da 🍰 tace kawata wannan partyn fah?
Naga ki hada mana wasu delicious dinner na san dai yau ba birthday din ki bane, koma ba nawa ba, ba kuma na safna ba hummn? Ta daga mata gira 😉
Matsowa safna tayi, ta dafa kausar tace zarah meye labari mutuniyar?
Kodai zamu sha biki ne?
Dariya kausar tayi tace gaskiya kam ki fada mana kawata don mu fara shiri, tana fadar haka suka tafa hannu.
Zarah na gani ta tashi tsaye cike da isa ta matso daf da su.
Cake din hannun kausar ta ci kadan tace me kuke ci na baka na zuba ne !
Murmushi tayi tace nan ba da dadewa ba zaku sha kallo.
Dariya sosai sukayi kafin suka tafa hannun su.
Kausar ce ta matso kusa da zarah tace ina yinki mutuniyata!
Shiyasa kike burgeni wallahi.
Dariya Zarah tayi tace ai ku bari, da ya dawo zan matsa masa da maganar auren mu nan da 3years.
Zaro ido safna tayi tace tabdi jam har sai ya dawo?
Eh mana baya nan ae a halin yanzu, baya Nigeria.
Kash kawata, cewar kausar kinyi shirme.
Ya zaki bari har ya bar Nigeria baku yi aure ba?
Idan kuma ya tafi ya manta da ke fah?
Murmushi zarah tayi tace yama isa.
Bari kuji malami na ya juyar da tunanin sa gare ni don haka..
Wani fargaba don ya tafi..
After all zamu na waya kullum.