MACE A YAU COMPLETE
"Abu daya zan fada miki shi ne yanzu kin girma kin mallaki hankalin kanki, Kinsan daidai da wanda ba daidai ba, Kinsan idan akace *budurci* ko virginity Kinsan me hakan yake nufi, nasan Kinsan shi ne Abinda ya zaunar damu gidan mazajenmu har yanzu, idan kika Bari ya kubce miki I'm so sorry to say bana tunanin zakiyi darajar da wadda ta kaishi gidanta zatayi, inason Kiyi tattalin shi don kuwa shi zai fadi tarbiyya da kika samu. Kada wani ya baki abu ki karba Kici, Kada wani ya kaiki alley ko wani isolated area, Kawaye kisan wacece kawarki da kuma wa kike mu'ammula dasu .... Abu na karshe ki kula da addininki sannna kiyi hakuri shi ne rayuwa! "
Se lokacin Mami tayi shiru yayinda Baki daya Sulaim tayi shirun tana sauraren mahaifiyar ta, dago kanta tayi muryar ta Cikeda rauni tace
Inshaaa Allah Mami, bazan Baki kunya ba, zan zame miki abin alfahari!
Kai Mami ta gyada tace
"Allah yayi miki albarka, idan kikayi haka kin gama mana komai"
"Amin" Sulaim ta furta kafin Mami tace
Kije ki shirya da munyi La'asar Zamu fita, make sure kin saka dan kunne da sarka.
Murmushi Sulaim tayi wanda ya fito da dimple dinta hakan yasa tayi kyau sosae dukda maganganun Mami taba ta suke ga kuma kewar gida da ta Fara ji Tun kafin lokacin tafiyar. Mikewa tayi jiki a sanyaye 1 Don komawa dakinta, dakin yana facing wanda ta fito Daga ciki, tura kofar tayi nan take komai na ciki ya bayyana, oil paint ne jikin bangon dakin purple colour wanda yasa dakin yayi dan duhu kadan, gadonta Irin silver poster bed dark purple, se wata resting chair a gefe, Daga Dayan barin akwai study table da kujerar shi sannan walk in closet da kuma toilet, akwai stickers a mammane jikin bangon dakin hakan yasa dakin ya zama very girly.
Tana ta jan kafa ta fada gadon tayi rub da ciki, hakan ya kasance aladar ta duk lokacin da take son tayi tunani ko kuma ta zama emotional haka nan. Ta jima a Wannan yanayin kafin kiran sallar laasar ya tashe ta, mikewa tayi ta shiga toilet wanda komai na ciki yake light blue ta daura Alwala, wani lungu ta isa a dakin ta shimfida sallaya ta Bada farali, Tana idarwa taji ana knocking hakan yasa tace
Yes... Come in please
Yarinya ce wadda shekarunta bazasu wuce sha uku ba ta shigo tace
Anty Mami tace ki shirya.
DOWNLOAD HERE👈