MAEESHA CHAPTER C KARSHE

 MAEESHA CHAPTER C KARSHE

Tana shiga daki taji an rufe kofa tana juyowa sai taji anyi saurin rungumeta tace swt hrt ai saika tsoratani haka+
Yace haba dai ai bansan matata da tsorobah sbd ita jarumace ya tallabeta zuwa gado yace ina bukatarki matata.

Bayan sun gama jin dadinsu sannan suka shiga toilet sukayi wanka sannan ta shiryashi yace  kinga lokaci ya kure bari nayi sauri naje nasan yanxu haka abokina yana jirana.

Allah yakiyaye mun kai mijina saika dawo

Yana saukowa qasa saiga nabila ta fito yana ganinta yayi kamar bai gantabah yafice warsa.

Tace kaidai akeji ta haura sama zuwa part dinshi tana shiga parlon tayi arba da mayiesha tafito sannan tace nabila harkin tashi dazu naje dubaki da muka dawo amma kina bacci

Tace ehh ban dade da tashibah.
Dama abu nakeso kibani
Tace to muzauna koh

Suna zaunawa sai tace dama kudinane sunyi qasa shine nakeso kibani kamar dubu hamsin zanyi wani abu.

Mayiesha tace nabila dubu hamsin fa kikace
Eh duhu hamsin kodai sunyi kadanne

Mayiesha tace a gaskiya banida dubu hamsin a hannuna amma kibari idan mai gidan ya dawo sai natambayeshi

Nabila tace haba taya kina zama a wannan gidan kice wai bakida dubu hamsin

Kinga nabila bazan yimiki qaryabah inada dubu ashirin idan zasu isheki saina baki idan kuma bazasu ishekibah saikibari haryadawo

Tace kidaukomun kawai zanyi maneji.

Mayiesha tatashk zuwa daki tana mamakin kome nabila zatayi da kudi haka.

Tana shiga daki sai nabila ta hango ipad din nabila a kan table tana charge taje kusa ta dauka tace tabdi ipad kuma ta apple amma fa ta burgeni.tana
Jin motsin mayiesha satayi sauri ta zauna

Gashi sai kiyi maneji
Nabila ta karba sannan tace waccan ipad din takice

Mayiesha tace ehh tawace
Nabila tace amma fah kinajin dadinki sosai wlhy amma idan ranki bazai bacibah inason ki aramun.

Mayiesha tace ba damuwa kidauka idan kin qare saiki mayarmun

Nabila ta dauki ipad din tana murmushi tace thanks sis tafice.

Wacece nabila?!

Nabila abdullahi yer uwace  ga mahaifin munawwar wato alhaji abdulhakeem wacce a gidansu aka sake mata da yawa sbd itace auta a dakinsu sannan kuma ummarta ta sake mata sosai hakan yasa takeyin abunda taga dama idan tace zataje makaranta saita biyewa qawayenta suje suyi tayin shaye shayensu hakan yana matukar batawa mahaifinta rai amma ita bata damubah kuma gashi ummanta ta daure mata akan komai bayan sunyi hutun makarantane tace zatazo abuja tayi hutu gun hajiya sbd tasamu damar yin abunda ranta keso wannan kenan.

Cigaban labari:

Da daddare kusan qarfe takwas da rabi nabila tatashi tayi shiga cikin wasu irin matsasun kaya masu bayyana rabin jikinta taci kwalliya sannan ta dauki makullin motanta takira aisha tace muhadu kawai a club.
Tafito parlour bakowa har zata fita sai mayiesha tafito kitchen ta ganta tace nabila ina zakije yanxu da daddare.

Nabila tace gidan qawata zanje

Amma ahaka zaki fita ko mayafi babu kuma ki kalli irin shigarda kikayifah

Kinga dan Allah kada ki matsamun kawai kiyi harkar gabanki saina dawo tafice.
Ana bude mata mota ta taka motar da gudu tafice.

Mayiesha tace ikon Allah wannan kuma wace irin macece haka Allah ya sawwaka ta zauna a parlor tana danne danne a wayanta.

Bayam minti ashirin sai taji horn din motar munawwar tayi saurim fitowa ta tarbeshi yace da fatan na tarar da matata lafiya qalau.

Tace ina cikin koshin lafia mijina suka fice zuwa parlor yace yunwa nakeji sosai muje naci abunci sbd kinsan bazan iya cin abuncin kowa sai naki.

Suna tsakar cin abunci yace ina nabila ko motsinta banaji

Mayiesha tace tafita
Tafita kuma cikin wannan daren ina taje

Wai taje gidan qawarta bazata dadebah zata dawo

Yace amma da daddrennan Allah yasa lafiya

To ameen.

Tana zaune da qawayenta sai masha’arsu sukeyi sunata rawa har kusan qarde goma da rabi aisha tace wannan wayar kuma a ina kika samu

Tace ta matar dan uwanane na karba.

Aisha tace amma fah tabirgeni sosai
Allah koh nima haka shiyasa ma nakeson idan nakoma nace mata kawai ta barmun ita.bari naje toilet nadawo.
Cikin tangadi da maye tashiga toilet ai kuwa tana shiha aisha tasaka hannu ta dauke ipad din ta boye a jakarta sannan tatashi taci gaba da rawa.

Munawwar da mayiesha suna kwance suna labari sai yace wai lafiya har yanxi nabila bata dawobah

Mayiesha tace haba aiba qaramar yarinya bace da zata bata nasan duk inda take yanxu tana hanyar dawowa gida
Kodai zaka kira wayar tane

Noo banda numba dinta fah
Yawwa ki daukomun ipad dinki zan tura hotonta sbd inason akawomun irinta.

Tace ayyan aikuwa na arawa nabila ita dazu sbd tace wai zatayi amfani da ita

Taya zaki dauki abunki kibata kinsan me zatayi da ita

Haba dai ai bazatayi wani abu da bashida kyaubah yanxu dai kayi hakuri idan ta dawo saina karba bazan sake batabah

Yawwa baby na dadina dake idan nayi miki magana baki musamun.

Har kusan sha biyu  na dare sannan aisha tace yakamata fah nabila kije gida kinga nikam sai qarfe uku zankoma nida bashir.

Nabila tace to saida safe ta dauki jakarta cikin maye tashiga mota tana tafiya a hankali dakyar ta iso gida.

Ana bude mata ta shigo a lokacin su munawwar sukaji qarar shigowarta nan yayi saurin lekawa yaga itace sannan cikin fushi yafito zuwa qasa mayiesha ta biyo bayanshi.

Tana shigowa parlo tana tangadi tasamu guri ta zauna a lokacin ya sauko qasa.
Yace nabila daga ina kike

Ta kalleshi sannan tayi shuru batace komaibah

Yace tambayarki nakeyifah

Tace daga gidan qawata nan yayi saurin rufe hanci yace meye wannan kikasha mai wari haka.

Ba komai kawai lemu ne nasha

Yace nabila dama kina shan giya subhanallah

Mayiesha tace giya kuma haba dai taya zakace haka
Gashinan kinajin warinta amma wannan yarinyar kin cika  cikakkiyar yer iska to wlhy daga yau kin dena fita daga gidannan bani makullin motarki.

Meyasa zan baka makulli
Kibani kafin na kwasheki da mari ya dauki jakarta ua bude ya dauki makullin sannan yace ina ipad din mayiesha

Nabila tace tana ciki manah

Bata ciki kibani nace

Tana ciki mana ya wurga mata jakar yace gatanan ki daukomun.

Nan mayiesha tace dan Allah kabita a hankali mana zanyi mata magana gobe kaga yanxu ba’a hayyacinta takebah

Ta rike nabila takaita har daki ta kwantar da ita sannan tafito.

By maryam ashutrah.

Suna shigowa daki yace bantaba ganin yarinya irin wannan bah yer qarama da ita ta lalata rayuwarta haka+

Dan Allah kabar wannan magana sai gobe kayi mata nasiha watakil yadena.

Yace to Allah shirya

Yawwa abunda yakamata kace kenan tun farko kuma dazu kafin tafita tazo ta sameni akan nabata dunu hamsin nace banida dubu hamsin amma na dauki dubi ashirin nabata

Dubu hamsin fah kikace mezatayi da kudi haka
Nima bansanibah amma wlhy danasan giya zataje tasha da bazan batabah.

Da asubah bayan sun gama sallar asubah munawwar yace kije kitada nabila tayo sallah

To Allah yasa tatashi idan taqi tashi kizo kisanardani kuma kikarbo ipad dinki.

Tana shiga dakin nabila taganta sai shakar bacci takeyi tayi saurin rufe hancinta tace wai wannan wani irin warine dakinnan yakeyi haka.taje gunda take ta tasheta dakyar tatashi sannan tace idan kin gama sallah dan Allah kifito parlo saina saka a gyara dakinnan naki wlhy wani wari wari yakeyi.

Aikuwa nabila ta kalleta tace jar ubannan waton kina nufin nice ke wari koh to wlhy banice ke waribah wadda kika bari a gida mai dattin dan kwali itace take wari

Har nabila zata mareta tace wlhy kinci sa’ar ke yer uwar miji nace da wlhy sai kin san dawakike.

Ba abunda zaki iyamun maza kifita daga dakinnan kafin nayi miki tsinannen duka.

Mayiesha ta jujjuya sannan tace kinganni wlhy bana dakuwa ga da namiji ballantama mace kuma macen ma kamar ki wawiya kawai marar tarbiyya tafice warta.

Tana shiga daki munawwar yace Yana ganki haka rai abace mekuma ya faru ai nan take mayiesha ta fashe da kuka.

Hankalin munawwar yatashi sosai yazo gunda take yace haba matata me akayi miki kike kuka dan Allah kidena kada kisa zuciyata ta fashe.

Wlhy nabila yau taci sa’ar ita yer uwarkace da wlhy saina hada mata jini da majina ta sake fashewa da kuka

Me nabilan tayi miki ne

Batace mishi komaibah a fusace yatashi harya isa bakin kofa ta rikeshi da sauri tace ka kyaleta kawai

Wlhy a duniyar nan ba wanda ya isa yasakaki hawaye na kyaleshi ballantana mace ki kyaleni kawai

Nidai nace ka kyaleta kuma ai yawuce bakomai

Wlhu taci alfarmarki kuma idan tasake yi miki wani abunda zai bata miki rai a gidannan sai taji ba dadi.

Da safe suna cikin karin kumallo nabila tafito kawai tashiga kitchen ta dibo abunci a plate ta dauki drinks tafito zata fice daki.

Munawwar yace ke zonan

Ta juyo ta kalleshi sannan tace abunci zanci

Cikin fushi yace idan kika bari na qara yi miki magana wlhy sai ranki yayi mummunan baci
Dataga da gaske yakeyi sannan ta isa inda yake

Yace lokacinda kika fito parlo baki ganmu bane dazaki fice baki iya gaisuwa bane.

Ni bama wannan bah ba wanda yake bukatar gaisuwarki samu guri ki zauna.

Ta zauna sannan yace ki kalleni da kyau daga yau bazaki sake fita daga gidannan bah idan kinga kin fito to hajiyace tazo kuka tafi tare sannan bayan haka idan kika sake batawa matata rai wlhy saikin bar gidannan sbd bazakizo ita da gidanta kihanata zaman lafiyabah.

Kuma yanxu kibata hakuri.

Haba dai mena mana da zan wani bata hakuri

Mayiesha tace bakomai kirike hakurinki bana bukatarsa sbd ba amfaninda zaimun

STORY CONTINUES BELOW

Munawwar yace kuma yanxunnan kitashi kije ki daukomata ipad dinta

Nabila tace naduba bangantabah wata kila ta batane

Munawwar yayi saurin tashi tsaye yaje gunda take yace wlhy kodai kitashi kidauko ipad dinnan kokuma nanuna miki ke qaramar yer iskace.sannan daga yau kidena saka irin wannan kayan a gidana wannan gidan bana shaidanu bane idan kuma bakida kayan arziki saikije ki karba daga mayiesha.

To wai meyasa zaku takura munne sbd kawai ina zama a gidanku kuma ni bawanda ya isa ya chanja mun tsarin rayuwata kafin tarufe baki taji saukan mari a fuskanta kafin ta ankara sai taji wani.

Mayiesha tace dan Allah ka kyaleta mana amma kekuma nabila idan ma sone kike nabaki ai saiki fadamun bawai kizo da wani zance bah.

Munawwar yace ba wanda zai bata wannan ipad din sbd me saboda tana mutumtaki kokuma sbd tana ganin girmanki wlhy nabaki nan da awa biyu kimayar da wannan ipad din

Tafice daki itakuma tafice tana kuka
Mayiesha tace yau naga ikon Allah hmmm Allah ya sawwaka.

Tana shiga daki ta dauki wayarta takira aisha yana dauka tace ke jiyafah a club ansace ipad dim matar dan uwana kuma wlhy idan bamu samo tabah nasan halakani kawai zaiyi a gidannan.

Aisha tace tabb to yanxu taya zamu sameta kawai kije kisameta kibata hakuri kice ta bata.

Ni bazan iya bata hakuribah sbd ko kallo ba ishenibah

Aikuwa saiki samu yadda zaki fidda kanki idan mijinta ya riskeki
Kuma hakane fah wlhy dazu kinsan mari nasha a gunshi kuma yace bazan sake fita daga gidannan bah.

Haba dai lallai wannan mutumin amma ai bai hana nazo nan gidanbah kada kisamu kawai zan dinga zuwa

Shegiya aisha kiyasa nakesonki sbd kina da kwakwalwa

Haba kada kidamu kuma marinki da yayi wlhy saimun dau fansa

Haka yakamata kawai idan kinzo saimu tsara komai
Yawwa ba damuwa saikin ganni.

Bayan sati daya mayiesha ta iya mota ba abunda yake bata wahala sannan gashi zasu fara zuwa makaranta itada mijinta.

Munawwar na zaune a parlon sa tare da mayiesha suna shan farfesu sai wayanshi tayi qara yana dubawa yaga hajiya ce kekira da numbar nigeria yana dauka yace hajiya harkun iso kenan.

Tace wlhy yanxu na shigo gida yakuke
Wlhy lafiya qalau amma hajiya naji dadin dawowarki gobe inshallah zamuzo nan kinga yau saiki dan huta.

To Allah yakawoku lafiya ina nabila
Tana nan qalau nikam ai dama na matsu kidawo chan takons inda kike sbd nikam idan tana zama a gidannan wata rana ballata zanyi sbd sam batada tarbiyya

Hajiya tace banason haka kaji koh ai yer uwarkace kake fadan haka.

Nidai ina ‘yata gatanan

BAYAN sun gaisa da hajiya sai ta kashe.

Munawwar yace kinga gobe zamu fara zuwa school haka so kinga kenan da daddare zamuje gun hajiya to Allah yakaimu.

To Allah ya kaimu.

Nabila tana zaune a dining tana cin abunci mayiesha tafito sannan tace barkadai nabila dama zan fada mikine hajiya tadawo sbd haka gobe da daddare zamuje mu ganta.

Yawwa nagode Allah daya nunamun zanbar wannan gidan
Wannan kuma kanki akeji sbd haka saiki shirya

Ai koda bakice bah shiryawa zanyi nabarmuku gidanku.

Yawwa sannan batun ipad dita idan ma lalacewa tayi ko siyar wa kikayi ko kuma bata tayi chankije kirike nayafe miki.

Ke nihar zaki kallah kiwani cemun wai siyar da iPad dinki nayi to ki kalleni da kyau banyi kama da wacce tafito daga gidan matsiyatabah dahar zakice na siyar da ipad dinki.

Kinga nabila gwara kibari murabu dake cikin kwanciyar hankali idan kuna ba haka bah to wlhy zaki yabawa aya zakinta.

Waike kinzata tsoronki nakeyi kawai ina kyalekine sbd dan uwanki banza kawai marat tarbiyya.

Nabila tace nikike cewa marar tarbiyya ta daga hannu kenan zata mari mayiesha ta rike hannunta ta juyashi nabila tasaki wata irin qara sannan tasaketa tace kisan da wadanda zakiyi fada badainibah sbd nafi qarfinki ta ficewarta.

Nabila tace wlhy daga ke har mijinki sai nayi maganinku tashiga daki tana ta sake sake a zuciyarta ta.

By maryam ashutrah

Da safe bayan sun karya suka shirya sannan suka fice zuwa makaranta.

Nabila na tashi ta fito taji shuru tace daga dukkan alamu bakowa a gidannan larai!larai!!
Larai tace na’am
Wai kunajin ina kiranki kinyi wani banza dani ina mayiesha

Tace sun fita tare da alhaji

Ina sukaje
Wlhy ban sanibah

To zaki iya tafiya.

Yayi kyau takira aisha tace ke kina ina

Tace aikuwa ina kusa da unguwarku nida saurayina.

To kawai ai saiku iso
Haba dai kinsan halin dan uwannan naki fah bakiga irin kallonda yakemun bane

Ke dan Allah kada kidamu basanan sun fita kinga kuwa zamu iya hutawarmu nadan lokaci

To shikenan saimunzo

Taje tacewa mai gadi zanyi baki idan sun iso kabude musu kofa

Yace to
Bayan wani dan lokaci sai gasu a gidan suna shigowa parlor nabila tace ke kisaki ranki nafada miki basanan.

Yawwa haka nakeso to ku zauna

Bayan sun zauna sannan aisha tace mukhtar wannan itace qawata nabila da nake yawan baka labarinta.

Muhktar yace sannunki dai
Tace yawwa bari akawomuku abun sha.

Bayan sun huta nabila tace ke wai kinsan yau zan koma gidan hajiya

Aisha tace ke haba harta dawo
Eh wlhy kinga kuwa yakamata muyi abunda yakamata kafin nafice.

Hakane kamata yayi muhada bari da barayi sushigo gidannan suyi musu tsinannan duka sannan kuma su kwace duk wani abu nasu.

Kinga kawai saimu raba kafin kikoma Kaduna

Gsky wannan shawarar taki tayi to yanxu a ina zamu samu.

Mukhtar yace idan dai nima zan samu wani kason a ciki to zan hada boys dina kawai sai mufaso.

Nabila tace haba kada ka damu da wannan.

Bayan sun gama maganar sannan nabila ta dauko musu sauran kayan shaye shayensu sukayita har karsu.

Nabika tace aisha idan kun gama shirye shiryen saiku sanar dani

Ah idan dai wannan ne kada kidamu

Bayan sun qare sannan suka fice.

Bayan sunje sungama duk abunda yakamata sannan suka fara karatu.bayan mayiesha tagama lectures dinta takira wayar munawwar yana dauka tace nifa mun gama lectures dinmu.

Yace to kijirani gun mota ina zuwa

Tace toh takashe.

Tana tsaye gurin mota saiga wata yen mata su biyu suka nufo inda take.sukayi mata sallama ta amsa sannan ta farkon tace sunana fatima aliyu a wannan makarantar nake karatu sannan wannan qawatace sunanta aminah faisal dama mun ganki ne tundazu da kika shigo makarantar nan kuma daga dukkan alamu ke sabuwar shigowace.

Eh hakane yau nafara zuwa makarantarnan
Dama kawai mun gankine mukaji muna qaunarki idan bazaki damubah zamu iya zama qawayenki.

Mayiesha tace ba damuwa ni sunana ameena alkasim amma ana kirana MAYIESHA.

Fatima tace wow amma suna mai dadi.
Shikenan zaki iya bamu nomba dinki kinga zamu dinga taimaka miki idan akwai lecture kawai kiranki zamuyi.
Tace ba damuwa ta basu numbar.

STORY CONTINUES BELOW

Sukace shikenan sai anjima suka fice itakuma ta shiga mota tana jiran munawwar bayan wasu yen mintina yashigo yace am sorry my dear nabarki kinata jirana wasu yen abubuwa suka tsayar dani

Ba damuwa muje

Suna shigowa parlo munawwar yace waton yarinyarnan damuka fita tayi shaye shaye ta.

Mayiesha tace haba yayana meyasa zakace haka

Bakyajin warin giya ne da sigari
Kuma hakane fah amma ka kyaleta kada kamata magana yanxu abun yazama fada tunda yau zata fice warta.

Hakane kam tafi ruwa gudu

To Allah dai ya kyauta muje muyi wanka musauko cin abunci sbd yunwa nakeji sosai
Yace nima wlhy haka.

Suna zaune akan dinning sunacin abunci sai mayiesha tace yawwa bari nakira umma naji ya jikinta naji dazu tace batajin dadi.

Gsky kam hakan yanada da kyau.
Takirata amma abba ne ya dauka bayan sun gaisa tace ina umma yace gamunan a asibiti jikinne yayi tsanani.amma dai yanxu da sauki tunda harta samu bacci

Mayiesha tace subhanallah to idan ta farka sai abani ita.

Yace to ina gaida mijin naki

To abba zaiji.

Takashe tacewa munawwar wai ummace jikin yayi tsanani har an kwantar da ita.

Subhanallah Allah ya qara sauki

Ameen amma dai yanxu tasamu bacci idan ta farka saiku gaisa.

To badamuwa.

Da daddare bayan sallar isha’i suka shirya zuwa gidan hajiya.

Itakuma nabila ta dauki kayanta zuwa motarta sannan munawwar yace nabila kixo parlor inason magana dake.

Bayan dukansu sun zauna sai yace nabila dan Allah ki sauya yadda kike rayuwarki sbd idan kika cigaba a haka ko mijin aure bazaki samubah sannan kuma ba abunda hakan zai haifar miki sai nadama.

Tace naji kuma nagode da nasihar.

Mayiesha tace nikuma abunda zance miki shine kisan irin mutanen da zakiyi mu’amala dasu ta yau da kullum sannan kuma aduk inda kike ki zauna da mutane lafiya.

Nabila tace waton kina nufin qawata mutuniyar banzace to wlhy ba ruwanki da ita mtswww tatashi zuwa motarta.

Munawwar yace Allah dai yashirya suka nufi motarsu mayiesha taja motar suka fice nabila na binsu abaya.

Bayan yen mintuna suka isa gidan suka tarar da hajiya a parlor suka gaisheta dukansu.

Hajiya tace to kuzauna
Dukansu suka zauna

Hajiya tace nabila yakike ya kuma gidan
Wlhy lafiya qalau kowa da kowa
To masha Allah dama qarshen satinnan zaki koma koh

Eh hakane sbd zamu koma makaranta wanj sati

To Allah yakaimu kishiga ciki koh.

Tatashi ta kwashi kayanta tahaura sama.

Hajiya tace nasameku lafiya

Dukansu sukace lafiya qalau ya hanya

Alhamdulillahi ya hakuri kuma da nabila sbd nasan halinta bataji
Munawwar yace aikam wlhy hajiya sbd kullum  abun nata sai gaba yakeyi.

Yanxu haka ipad dinda kika baiwa mayiesha ita tabatar da ita.

Kai ai nabila bataji Allah dai yashirya
Dukansu sukace ameen
Hajiya tace mayiesha ‘yata kinga yadda kika qara kyau kuwa kinchanja sosai.

Mayiesha ta sunkuyar da kanta qara

Hajiya tace to Allah yayi muku albarka duka sukace ameen.

Har kusam qarfe goma da rabi sannan suka fice gida bayan sunsha tsarabah.

Mayiesha tafito toilet ta zauna gaban madubi tana gyara gashinta munawwar yace kawo natayi baby na.

I hope dai kina fahimtar karatu sosai a makarantar

Mayiesha tace gaskiya ina fahimta sosai ba laifi

Yawwa yayi kyau kiqara kokari
To Allah ya taimakemu duka nan wayanta taji shigowar sako.

Tana dubawa sai taga message kamar haka”hey mayiesha nice fatima dama naga dare yayine shiyasa nace bari nayimiki text gobe bamuda lecture da safe sai qarfe biyu take care”

Tana gama karantawa tace hubby na banida lecture da safe sai qarfe biyu.

Yace to Allah ya kaimu kinga kenan zan fita nabarki amma dan Allah kiyi driving a hankali idan kuma bazaki iyabah saiki saka driver ya kaiki.

Tace to shikenan inshallah.

Sun kwanta chan cikin dare misalin qarfe uku da rabi na dare munawwar yadinga jin hayaniya.
Yafarka sannan ya leka ta window daga sama ya hango yen fashine suke kokarin shigowa gidan.

By Maryam ashutrah

Da sauri yaje ya tada mayiesha taki tatashi yace mayiesha kitashi yen fashi a gidannan.
Da sauri ya bude idonta ta farka tace yen bashi kuma+

Yace zo kigani
Ta leka a window ta hangosu sai kokarin shigowa sukeyi

Tace kakira yen sanda yanxu.

Yace kafin su iso sai sunshigo gidan kawai muje mu samesu

Mayiesha tace kada ka mantafah su bindigane dasu

Yace to ai sai idan mun nuna muna tsoronsune kuma nasan yadda zamuyi musu wayo dukansu kawai kitashi muje.

Barayin na samun nasarar shigowa gidan suka nufi parlo saisuha mayiesha zaune a parlor ta nade kafarta daya akan daya.

Babban su yaje gunda yace waton ke ko tsoro bakijibah mayiesha tace meyasa zanji tsoro bayan nasan da zuwanku.yanxu dai nasan kome yakawoku to idan kaine babba saika biyo ni nabaka duk abunda kakeso.

Yace to wlhy kin nemar wa kanki sauki kuma idan kikayi kuskuren rainamun hankali saina fasa miki kai da bindigannan.

Tace haba yallabai taya za’ayi haka kawai ka biyoni.

Ta haura sama shikuma yayi wa yaransa alamar sujirashi.

Yana shiga dakin tayi yaji anrufe kofa da sauri munawwar ya saka masa  wuka a wuya yace kanayin dogon motsi zan yanka maka wuya.nan mayiesha tayi saurin kwace bindigarshi sannan ta nunashi da ita tace yau zan kasheka kuma nakashe banza.

Muktar yace dan Allah kuyi hakuri.

Munawwar yace waton kana ganin mu wawayene koh kokuma matsorata to yau zaka gane kurenka daga kai had yen uwan naka.
Amma idan kuma kanason nayi maka hakuri to ka sanar dani waya aikoku.

Muhktar jikin rawar jiki yace wlhy nabilace ita da qawar ta aisha.

STORY CONTINUES BELOW

Mayiesha tace wace nabila wacce take a gidannan.

Yace ehh

Munawwar yace idan dai itace to nasan zata iya yanzu abu daya zan maka shine na hadaku da hukuma.

Mukhtar yace kada kayi haka wlhy idan mahaifina yaji wannan labarin nasan bazanji da dadibah.

Munawwar yace ashedai kai qaramin dan iskane nan take ya  kaimishi naushi a fuska yace kafin ma kaje police station saina hada maka jini da majina yazama shaida ga abokanan naka.
Nan kuwa ya saka wukar dake hannunshi ya yanka masa hannu da gefen fuska yayi mishi doguwar tsaga sannan ya barbi bindigan daga hannun mayiesha ya nuna a kansa yace bazamu fita dakai a parlor bah sbd nasan yen uwanka zasuyi kokarin kai mana hari.

Bayan wani dan lokaci wani daga cikin barayin yace naha har yanxu oga baifitobah anya lafiya kuwa.
Wani daga ciki yace kasanshi ai saiya huta da ita sannan zai sauko ba jimawa sukaji qarar motocin yen sanda nan take ko wannensu hankalinshi ya tashi tafim suyi wani yunkurin guduwa yen sandan suka shigo nan suka shiga harbin yen sandan amma dayake sunfisu kwarewa basu samu kodaya daga cikinsubah basusha wuyabah gurin kamasu sannan inspector dinsu yashigo parlon sukuma suna saukowa munawwar ya mikawa dan sandan muktar da bindigar.

Inspector yace lallai kunyi kokari sosai gurin yiwa wadannan barayin wayo sannan kuma kunyi kokarin gurin nuna rashin tsoro Allah ya qara tsarewa dukansu sukace ameen inspector yasaka muktar agaba suka wuce.

Mayiesha tace amma munawwar har yanxu ina tunanin memukayiwa nabila dahar zata mana haka.

Munawwar yace ai wannan komai zata iya sbd shegiyace bari nayi sauri nakira umma sbd ina tsoron kada ace har gidan tasaka barayi suje.

STORY CONTINUES BELOW

Yayi saurin haurawa sama ya dauki wayanshi saidai yakirata kusan sai hudu sannan ta dauka tace lafiya dai munawwar naga kiranka cikin wannan daren

Yace dama kawai kira nayi naji ko lafiya

Tace lafiya qalau wani abunne ya faru yace bakomai amma gobe da safe zamuzo gidan tace to Allah ya kaimu yakashe wayar.

Munawwar yace kinkwantar da hankalinki Allah yana tare damu ba abunda zaifaru.

Suka koma bacci.

Da safe bayan Munawwar yadawo daga lecture dinsa na safe suka wuce zuwa gidan hajiya.

Suka tarar da hajiya da nabila a parlor suna kallo.

Munawwar cikin fushi yaje ya daure nabila da wani wawan mari saida ta sume nan take.
Hajiya tayi saurin rikeshi tace rufamun asiri kada ka kasheta dan Allah

Mayiesha da sauri ta debo ruwa ta yayyafa mata aikuwa tana farfadowa ta fice daki da gudu ta rufe kofa

Hajiya tace wai lafiya meyake faruwane.

Munawwar yace hajiya kinsan me wannan matsiyaciyar yarinyar tayi.wai fa yen fashi ta aika mana a gida jiya da daddare.

Nan take hajiya ta saki salati tace yen fashi fah kace munawwar!

Yace wlhy hajiya Allah yasa damufi qarfinsu da wayo da dubara mukayi galaba akansu yanxu haka suna hannun yen sanda.

Hajia tace haba munawwar wannan yer qaramar yarinyar meta sani dahar zata yi wannan aika aika.

Mayiesha tace umma wlhy da gaskene sbd babban nasu shida kansa ya tabbatarmuna da hakan

Hajiya tace lallai nabila tacika butulu to wlhy yau dinnan zata koma garinsu sannan bazan fadawa kowa abunda tayibah sbd za’ace sharri mukeyi mata.

Da sauri hajiya yaje gun kofar tace kifito munafuka yau dinnan saikin bar gidannan kuma wlhy idan baki fitobah zan saka a balla kofar a fiddo sannan ayi miki dukan tsiya.

Nabila na cikin daki tana ta kuka sannan ta dauki makullinta ta bude kofar.

Hajiya ta janyo ta da qarfi tace amma wlhy kinji kunya dukda irin halaccinda nayi miki keda iyayenki amma abunda zaki sakamun kenan kifitarmun daga gida yanxu.

Cikin sauri zata fita hajiya ta kwace makullin dake hannunta tace ai motar ta gidannan ce badaga gidan iyayenki kikazo da itabah.sannan ta haura sama da sauri ta debo wasu kudade ta damka mata tace kitari mota kiwuce sannan kikwashi kayanki sbd bazakibarmun su anan bah.

Haka dai taje ta dauko akwatinta ta fita.

Hajia ta zauna tace da fatan ba wanda suka yiwa komai a cikinku

Munawwar yace basu taba kowabah

To alhamdulilla anjima zanje police station din saina tabbatar da an hukuntasu.

Nabila kuma gidansu aisha ta nufa tana shiga itakuma aisha tafito kenan zata fita.

Aisha tace lafiya na nabila na ganki a haka

Nabila ta kwashe komai tafada mata sannan Aisha tace shikenan asirinmu ya tonu kenan nima kowane lokaci zan iya ganim yen sanda a gidannan.

Nabila tace yanxu yazamuyi

Aisha tace abu daya zakiyi shine kiwuce tasha kuyi kaduna.

Nabila tace haka ma zakice kinsan wlhy idan nakoma gida yanxu zasu gane akwai matsala.

Aisha tace to nikam ba abunda zan iya yimiki sbd ni yanxu shiga zanyi na kwaso kayana nayi gun yen uwana dake nasarawa.

Nabila tace to ai sai muje tare idan yaso idan hutuna ya qare saina koma kaduna.

Aisha tace kinga ba inda zanje dake wlhy sbd sun sanni mai tarbiyya da natsimuwa idan naje chan yanxu idan na daukeki mukaje tare ai asirina ya tonu.

Nabila tace haka zakicemun aisha

Tace ai dole na fadi haka kawai kije ni kinga tafiyata.

Harta juya suka

Harta juya zata tafi sakuma nabila ta hango ipad din mayiesha a cikin qaramar jakarta+

Tayi saurin taci gabanta tace aisha inaso naga wannan wayar dake a jakarki

Aisha tace sbd me

Sbd naga tayi kamada ta mayiesha ne

to ba ita bace wannan ta wani abokinane

To kinunamun mana

No basai kingani bah

Aikuwa nan nabila tayi sauri ta saka hannunta a cikin jakar aisha ta fiddo ipad din tace jar ubannan kai wato aisha dama kece kika dauki wannan ipad din shine kuka wani fuske.

Aisha tace dalla malama kibani wayana ta kwace iPad din daga hannun nabila.

Nabila tace waton aisha bayan iskanci da lalata abokanai dakuma shaye shaye harda sata kikeyi kuma kirasa wacce zakiyiwa sata saini.

Anyi miki sata din kokinada qarfine ki kwata banza kawai marar hankali kinga kifice daganan kafin na sako miki karnuka wlhy.

Nabila najin anyi maganar kare tace kinyi hasara wlhy shegiya wulakantatta.

Tace ai kece babbar wulakantatta wacce take son halakar da yen uwanta banza marar wayo kawai.

Nabila tafice tana maijin haushin aisha dakuma tunda duk irin abubuwanda tayi mata abaya.

Bayan wata daya:

Suna fitowa daga lectures fatima tace wai wlhy nagaji sosai gashi yau wannan lecturer din ya wahalar damu

Mayiesha tace kedai kawai kibari gashi da kallon mata.
Nidai yanxu zan wuce gida sbd nima a gajiye nake sosai gashi inajin bacci.

Amina tace waike mayiesha anya lafiya kike kuwa naga ko a class muke saiki fara tangadin bacci idan kuma muka fito saikice bacci kikeji sosai kiyi saurin wucewa gida.

STORY CONTINUES BELOW

Mayiesha tace watakil gajiyace tamun yawa wlhy nidai zan fice saimunyi waya.
Sukayi sallama tashiga mota takama hanyar gida.

Ta biya ta Farmers market tasiye guava dakuma agwalima sannan ta fice gida.

Tana shiga part dinta ta tarar da munawwar sai faman latsa laptop dinsa yakeyi tashiga da sallama.
Ya amsa yatashi yace oyoyo my queen kika barni nikadai a gida.

Amma ai kacemun zaku hadu da ahmad abokinka

Eh naje nasameshi harmun gama na dawo.meye wannan a hannunki tace guava ce dakuma agwalima.

Yace kedai kullum siyar kayan kwalama

Tace nadaiji yanxu dai bari naje nayi wanka naci abunci nadan huta.

Yace nikuma kibarni anan koh

A’a idan na shirya zanfito saina tayaka hira har bacci ya daukeni.

To saikin fito.

Tana gama shiryawa tasaka qananan kaya riga da wando tafito.
Ya kalleta sannan yace wlhy swt hrt sai qara fari kikeyi kina wani kyau da sheki

Tace zaka fara wannan zolayar taka koh

Ai gaskiya nafada

Ta zauna kusa dashi suna dan hira ta dauko guava din harta ciza saikuma tayi saurin furzarwa

Lafiya dai naga kin furzar kodai ba dadine

Wlhy haka kawai kuma naji banaso gashi har zuciyata ta fara tashi kamar ma amai nakeji ai kafin ta rufe bakinta kawai tatasho da sauri zuwa toilet din parlo tafara kwara amai

Da sauri munawwar yabi bayanta yace anya baby na lafiya qalau kike kuwa

Lafiya qalau kawai dai bana dan jin qarfin jikinane

To yanxu kije kikwanta

To shikenan.
Taje daki ta kwanta shikuma yaje yaci gaba da abunda yakeyi

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari tana zaune da munawwar suna ta hira yace yakamata yau kam muje muga hajiya.
Tace gsky kam mun dade bamujebah Yawwa wai dan Allah yaushe zamuje katsina nidai inason ganin su umma.s bd har yanxu jikinta yana damunta

Kada kidamu idan mukayi hutun school zamuje har muyi hutu achan.

To Allah yakaimu.bayan sun shirya suka nufi gidan hajiya suna isa suka taddata a garden din gidan tan karatun newspaper.

Tace sannunku da zuwa yaran albarka

Suka gasheta cikin ladabi

Ta amsa tare da murmushi tace to muje parlor kun tadda ni sai karance karance nakeyi.

Suka isa parlor hajiya tasaka mai aiki takawo musu abunci.
Suka dan taba hira sai munawwar yace bari na dibar mana abunci sbd nidai yunwa nakeji

Mayiesha tace ohh so kake kace ban baka abuncibah kafin mufito kenan koh

Yace nidai ba’aji haka daga bakinabah
Yana bude abuncin Mayiesha tayi saurin rufe hancinta tace pls ka rufe banason warinsa yana tadamun zuciya.

Hajiya ta kalli mayiesha tace abuncinda  kikeso nafah jollof din shinkafa da kaji.

Tacs wlhy hajiya nima haka kawai naji banaso.
Munawwar yarufe yace a gaskiya daga nan asibiti zamuje sbd nidai nakasa gane wannan abun daga kice bakyason kanshin wannan sai kice bakison wanchan ga masifar bacci.

Hajiya tace yakamata kam amma tun yaushe kika fadajin haka tace hajiya bai dadebah yanxu sati daya kenan.

Hajiya tace zonan taje hajiya ta kalli hannunta sannan ta kalli idanta da kyai tayi murmushi irin nasu na manya tace yanxu kuje asibiti.

Munawwar yace to hajiya yanxunnan kuwa daga chan zamu dawo sbd yau asabar ba lectures samukai dare anan.

Tace to saikun dawo.

Suna isa asibiti basu wani sha wahalabah sukaga likita bayan sunyi kwaje kwajen jini da sauransu sai suka jira sakamako.
Bayan minti goma sha biyar likitan yafito rike da paper a hannunshi ya baiwa munawwar yace congratulations  matarka tanada juna biyu har wata daya yanxu abunda yakamata shine tafara zuwa awo da wuri daga ranar litinin kuma duk wasu abubuwanda yakamata suna rubuce anan yajuya ya tafi.

STORY CONTINUES BELOW

Munawwar ya kalli paper din sannan yace daga hannu sama yace Allah na gode maka.

Mayiesha tace alhamdullilah nayi farin ciki sosai.

Munawwar yace yanxu kawai saimukoma musanar da hajiya.

Bayan sun isa gida hajiya tayi farin ciki sosai da taji wannan labarin harda yen hawayenta sbd tana farin cikin zata zama kaka.

Tace yanxu kaga yazama dole ka kula da mayiesha sosai fiye da da idan kuma bazaka iyabah to saikuma tadawonan harta haihu.

Munawwar yace haba dai hajiya ai abun baikai chan bah zan qara bata kula ta musamman.

Suna cikin hira sai wayan Mayiesha tayi qara tana dubawa taga abbane ke kiranta haka kawai sai taji gabanta ya fadi ta dauka tare da sallama.

Tajishi yana sheshekar kuka tace abba lafiya dai najika a haka kodai jikin ummana ya qara tsananta.

Yace Mayiesha saidai muyi haquri amma ummanki tarasu!

Dummm gaban Mayiesha yabuga nan take kawai saita suma.

Hajiya da munawwar sukayo kanta da sauri
Munawwar yayi saurin daukar wayar yace abba lafiya

Abba yace munawwar kuyi hakuri amma ummanku tarigamu gidan gaskiya.

Nan take ya saki wayar tare dayin salati
Hajiya tace lafiya munawwar ya kalleta tare dayin hawaye yace umma tarasu.

Hajiya tasaka salati tatashi da sauri ta dauko ruwa ta yayyafawa Mayiesha amma ina taki tatashi hankalinsu duka ya tashi

Hajiya tace maza ka dauketa muwuce asibiti.

Dasukaje asibiti dakyar likitoci suka shafo kanta sannan ta farfado tana cikin kuka tare da kiran sunan ummanta.

Likita yace dan Allah meyasa ku mutane kukeyin hakane taya zaku sanar da ita abunda yayi matukar tada mata hankali haka saira kadan tayi bari fah.
Hajiya tace wlhy bamu muka sanar da itabah amma ayi hakuri.

Suna isa gun Mayiesha tarike munawwar tace kakaini gun ummata inason naganta tasake fashewa da kuka.

Tace haba umma meyasa zaki mutu kibarni meyasa zaki mutu bakiga jikankibah wannan ranar wane suna zan mata ranar da nasan inada ciki a ranar ummata tarasu tasake fashewa da matsanancin kuka.

Munawwar yace Pls ki kwantar da hankalinki kada kisaka kanki cikin wata damuwar da zata taba abunda ke cikinki da kyar dai ya lallasheta.

Hajiya dai tarasa abunda ke mata dadi.
Sai da daddare bayan ta samu nutsuwa sannan aka sallamesu.

Suna komawa gida hajiya tace dan Allah Mayiesha kisakawa zuciyarki hakuri dukanmu lokaci muke jira Allah yaji qanta da rahama.
Dukansu sukace ameen
Hajiya tace gobe idan Allah yakaimu zamubi hanya zuwa katsina inshallah.

Yanxu zan tafi gida sbd nafara shirye shirye Allah yatashemu lafiya.

Mayiesha dai dakyar munawwar yasamu tasha tea sannan tasamu ta kwanta amma bawai zatayi bacci mai dadibah munawwar da kansa ya shirya musu kayanda zasuje dasu.

Bayan yagama ya sauko qasa ya tara duk masu aikin gidan yasanar dasu cewa zasuyi tafiya zuwa katsina sbd mahaifiyar Mayiesha ta rasu.dukansu

Da sassafe bayan sun gama sallar asubah sukayi wanka suka shirya sannan suka wuce zuwa gidan hajiya.
Achan suka karya sannan suka kama hanya.

By maryam ashutrah

Qarfe biyu dai dai suka isa garin katsina inda daga nan suka zarce zuwa gidansu mayiesha.

Suka tarar da mutane dayawa anata karban gaisuwa abba yana ganinsu yace sushiga cikin gida.bayan sun zauna sannan hajiya tayi mishi ta’aziya Mayiesha dai sai faman kuka takeyi.
Abba yace kiyi hakuri Mayiesha kowa zai mutu yanxu hakuri kawai za’ayi dakuma yi mata adduah.

Bayan kwana uku angama karban gaisuwa sannan suka sanar da abba akan Mayiesha tana da ciki yayi farin ciki sosai sannan yayi adduar Allah ya sauketa lafiya.

Hajiya tace amma mezai hana mukoma dakai chan abuja idan yaso saika zauna tare damu.
Abba yace a’a kawai kubanni anan sbd nafison zama anan tare da mutanena.

Hajiya tace to amma ai zama a haka kuma cikim kadaici ba dadi.
Yace hakane amma hakurine kawai nawa.

Tace to Allah yaji qanta da rahama.

Mayiesha na zaune a parlor tana cin abunci munawwar yashigo yana ganinta yace waton kinanan kina aikinki nacin abunci.

Tayi dariya tace idan kuma bancibah saika fara cewa banason cin abunci.

No bahaka nake nufibah amma fa naji dadi sosai dana ganki yau kin zake kina cin abunci kuma gashi har dariya kikeyi

Zaka fara zolayar taka kenan koh

Amma ai gsky na fada to amma yakamata muwuce abuja banda gobe sbd kinsan za’a fara exams

Hakane gsky amma kasan meye

Saikin fada
Wlhy banason mubar abba anan shikadai

To kinsan amma idan yayi magana baya chanjawa kuma yace shidai abarshi anan kawai.

To Allah yasa hakan yafi alhairi

To ameen.
Ranar jumuah suka dawo abuja inda suka koma makaranta ranar litinin.

STORY CONTINUES BELOW

Tana zaune tare da qawayenta a class suna jiran lecturer fatima tace wai Mayiesha kada kice ina miki shisshigi amma wanda kuke zuwa tare makaranta kullum wanene.

Mayiesha tace mijinane

Ameena tace wai kina nufin kinada miji shine baki tana sanar damunah.

To ai inaga fada muku bashida amfani shiyasa

Amina tace kenan kina boye muna abubuwanki dayawa
Fatima tace watakil bata daukemu qawayenta bane shiyasa.
Tace wlhy ba haka bane amma Pls kuyi hakuri.

Fatima tace to yaushe zaki gayyacemu gidanki

Mayiesha tace duk lokacinda kuka shirya kawai saikuzo

Sukace to shikenan.

Bayan sun tashi lecture sai Mayiesha tace to nidai zan tafi sai anjimanku
Amina tace yau kuma bazaki jira mijinkibah

Tace no akwai inda nakeso najene

Sukace to sai munyi waya tashiga motarta daga nan tawuce zuwa asibiti.
Bayan an gama mata awo ta karbo magani sannan tafice gida.

Munawwar yakirata yace yana fito kuma bangankibah tace wlhy na biya asibitine kuma daga nan saina farajin kasala shine kawai nazo gida

Yace wato shine kikabar mijinki makaranta to kiyiwa driver magana sai yaxo ya daukeni
Tace to shikenan.

A kwana a tashi har cikin Mayiesha ya fara girma inda taqara kyau da haske takuma qara kiba har munawwar yake zolayarta wai tana cinye musu abunci.
Su minal kuma sunyi mamaki sosai inda suka dinga yi mata jinini akan tanada ciki amma bata sanar dasubah.

Tana balcony sai faman assignment takeyi a laptop dinta sai wayanta yayi qara tana dubawa saitaga aminace kekiranta.
Ta dauka tace su amina kenan manyan gari.
Amina tace yakike yakuma baby.
Wlhy dukanku muna lafiya
Dama kiranki nace miki yau munanan tafe gidanki tare da fateema
To Allah yakawoku lafiya yanxunnan kuwa zan turo miki address din
Yawwa ashedai kingane to saikin ganmu
Yawwa takashe
Bayan ta tura mata address din sannan takira munawwar take sanar dashi qawayenta zasuxo
Yace toba damuwa nima bazan dadebah zan dawo
Tace kabiyomun da yoghurt marar suga
Yace to sarkin kwadayi zanzo miki dashi kikula da kanki sukayi sallama takashe.

STORY CONTINUES BELOW

Ta dauki laptop dinta ta haura sama tasake wanka tayi kwalliya tasaka atamfa mai ja da fari riga da skirt yayi Mata kyau sosai gashi kuma ya kwanta a jikinta.
Ta sauko qasa zuwa kitchen tacewa inno da larai su hada abunci mai dadi sosai da kuma juice din kwakwa zatayi baqi.

Sukace amsa da to hajiya.

Bayan minti goma sha biyar saigasu amina a gidan tace ashedai zaku gane gidan
Fatima tace ai kuwa bamu wani sha wahalabah gurin ganewa

To gaguri kuzauna.
Da suka zauna tace bari na kawo muku abunci
Fatima tace haba dai kada kidamu keda kinyi nauyi bari na dauko da kaina taje dinning ta dino musu abunci sukaci saida suka koshi sannan amina tace lallai gsky Mayiesha kinajin dadinki .

Mayiesha tace dadi kuma nameye
Tace na aure cikin irin wannan gida mana kuma gaki da miji hadadde ga ki kuma da mota taji da fada gashi kina rike manyan wayoyi sannan Allah ya albarkaceki da baby.
Mayiesha tace amina kenan aikuma dan bada dadewabah zakuyi auren kawai lokacine.

Fatima tace ai nikam ko’a yanxu idan nasamu wanda ya shirya aurena zanyi.

Mayiesha tace to Allah yabaku nagari.
Suna cikin hirar su munawwar yadawo gida yana shigowa parlo dukansu suka gaidashi ya amsa sannan ya fice zuwa daki.
Mayiesha tacd kudanyi kallo ina zuwa Pls
Amina tace ba damuwa tatashi ta haura sama gun munawwar.

Fatima ta kalli amina tace wlhy inasom irin rayuwarda Mayiesha takeyi anya nima bazan samu guri a gidannan bah kuwa

Amina tace haba dai Mayiesha fah qawarmuce kuma ta yarda damu sosai baikamata muyi hakabah kuma taya kike tunanin auren mijin qawarki.

Fatima tace to ai ba haramun bane kedai ki kyaleni zan gwada
Amina tace nidai ba ruwana cikin wannan abun.

Tana shiga daki munawwar yace matata ya gidan
Wlhy gida lafiya qalau ina sakona
Gashi kafin kifara mun shagwaba dinnan taki
Yawwa mijina nagode sosai yanxu katashi kayi wanka saina kawo maka abunci.
No kada kidamu kibari harki qare da qawayen naki
Ai mijina yafisu amfani sbd haka bari na kawo maka abunci
To shikenan matata.

Tana saukowa qasa su amina suka tashi

Tacd badai tafiya zakuyibah tun yanxu
Fatima tace eh wlhy akwai inda mukeson mu biya.
Ayyah to shikenan kudan jirani .

Taje kitchen ta dauko abuncin munawwar takaimasa daki sannan ta bude drawer dinta ta dauko dubu hamsin dakuma turaruka da mayuka sannan tasaka a jaka ta sauko qasa ta basu.
Amina tacd haba dai harda wata dawainiya
Mayiesha tace dawainiyar me kuma ai wannan ba komai bane na gode sosai da ziyara
Fatima tace badamuwa mudai zamu tafi sai mun hadu a makaranta.
Ta rakasu har mota suka shiga sannan takoma cikin gida.

By Maryam ashutrah

Suna cikin mota amina na driving tace Mayiesha kenan baiwar Allah kinga harda abun arziki tamana.
Fatima tace kada kidamu idan na auri mijinta zan baki wanda yafi wannan
Amina tace kedai kinar wannan tatsuniyar.+

Yau ne suka fara exam na gama aji na farko.

Munawwar na fitowa daga hall sai yaci karo da fatima.
Tace sannu bawan Allah dafatan ka ganeni
Yace no gsky ban ganekibah
Sunana fatima kuma a wannan makarantar nake da karatu  sannan ni qawar matarkace wato Mayiesha.

Ayyah to lafiya dai
Eh toh lafiya zance amma dama inasom muyi wata maganane

To fadi inajinki
Dama…
Kawai kifada sbd ina sauri akwai inda nakeson naje.
Okey to idan bazaka damubah sai kabani nomba dinka idan yaso saina kiraka.
Yace to badamuwa yabata nombar sannan yafice.

Tace a gsky daga gani wannan zaiyi sauqin kai tafice warta.

Mayiesha tana tasowa daga makaranta ya fice zuwa gidan hajiya.
Hajiya tace yau yana ganki kekadai ina gogan naki
Ai daga makaranta naxo nan shikuma nabarshi a school basu gama exams bah shiyasa.

Ayyah Allah yasarki to ya qarfin jiki kuma

Mayiesha ta sunkuyar da kanta tace lafiya qalau.

Hajiya tace yawwa dama nayi bincike akan university dinda nakeso kuje ta london kuma sun fara sakim admission sbd hakah inshallah nan ba jimawa zaku wuce.
To Allah yakaimu.
Ameen ‘yata.

Bata jimabah sosai sannan tafice gida.
Munawwar na dawowa yace wlhy yau na kwaso yunwa sosai
To ai saimuje kaci abunci koh
Yace gsky kam amma dai bari na fara yin wanka.
Yana shiga bayi sai wayarsa tayi qara Mayiesha taje kusa da wayan ta dauka tace kaii ai wannan kamar numbar fatima amma meyasa take kiranshi kada dai ace budurwarsace
Tabdi kenan shiyasa naga ranar da sukazo gidannan yana shiga daki sukace zasu tafi.
Wato ni fatima zataci amanata kawai saita fashe da kuka.

STORY CONTINUES BELOW

Munawwar yana fitowa sai yaganta tana kuka yace lafiya dai Mayiesha meya faru
Tace kada ka tabani kuma kada ka sake kiran sunana waton dama cim amanata kakeyi munawwar tasake fashewa da kuka.
Tace to wlhy yanxu xanbar gidannan saikaje ka daukota kuzauna tare.
Yace wacece kuma mekike magana akai nibanganebah anya kuwa lafiya kike kuwa.
Mayiesha taje ta dauki qaramin akwatinta sa saka kayanya ciki ta dauki gyalenta da makullin mota.

Munawwar yace Mayiesha yanxunnan nashiga toilet kafin nafito kawai sainaga kin chanja dan Allah meyake faruwa.
Itadai batace komaibah sai faman kuka takeyi ta dauki laptop dinta tasaka a jaka sannan tafita.

Yayi sauri yasaka jallabiyya kawai yafito harta iso parlo ya tareta yace Mayiesha kada kimun haka dan Allah kada kibarni bazan iya rayuwa bah.
Ta tureshi jefe tashiga motarta
Tafice.
Da sauri munawwar yaje ya dauko makullinsa shina yabi bayanta.
tana isa gidan hajiya tafito cikin sauri tana kuka.
Hajiya naganinta tace lafiya Mayiesha meya faru kike kuka.
Tace hajiya munawwar yaci amana ta wlhy ni bazan koma gidansabah.
Hajiya tace wai meyake faruwa ne.
Nan munawwar yashigo tana ganinsa tayi saurin haurawa sana tashige daki ta rufe.
Hajiya tace wai tafiya naganku a rikice me kayi matane.
Wlhy nikam ba abunda nayi mata haka kawai nashiga bayi ina fitowa naga ta rikice haka sannan ta dauko kayanta tayonan.
Hajiya tace ikon Allah to yanxu dai ka kwantar da hankalinka koma menene mubishi a hankali.
Munawwar yace hajiya hankalina bazai iya kwantawabah laifinme nayiwa Mayiesha hakane.
Hajiya tace to zauna bari naje naji menene.
Ta haura sama tayita knocking amma Mayiesha taqi ta bude

Hajiya tace hana Mayiesha kiyi hakuri kifito manah
Mayiesha tace ni bazam fitobah sbd banason ganinsa idan kuma zan fito to yabar gidannan.

Hajiya ta sauka qasa tace katashi katafi zan nemeka.

STORY CONTINUES BELOW

Haba  hajiya taya zakice naje nabarta anan.
Kabi umarnina kawai sanan idan nagane kaime bakada gsky to ranka sai yabaci.
Munawwar yace to hajiya yatashi taficewarsa.

Mayiesha najin fitarsa tasake fashewa da kuka sannan ta bude kofa tafito.
Ta tarar da hajiya a parlor tsaye
Hajiya ta rungumeta sannan ta zaunar da ita tace kin kwantar da hankalinki banason kina shiga damuwa yanxu kisanar dani meya faru.
Mayiesha ta kwashe komai ta fada mata.
Hajiya tace lallai wannan abun baiyi dadibah amma zan bincika nagame gaskiyar
Haba hajiya wace gaskiya kuma bayan wannan
Kedai kada kidamu yanxu kitashi kije ki huta.
Da sassafe tatashi ta shirya zuwa makaranta sanman tashiga dakin hajiya ta gaidata sannan tace zantafi school sbd inada paper dim safe.
Hajiya tace to kikula sosai kinji Allah yabada sa’a
Tace ameen sannan tafice.

Munawwar kuma tun jiya yakasa bacci sai tunani yaketayi saboda wannan shine karo na farko da suka samu matsala a rayuwarsu.
Da kyar yatashi yayi wanka sannan ya sauka qasa yasha tea saikuma ya dauki wayansa.
Yana kunnawa sai yaga missed calls dayawa.
Bai gane numba dinba sai yakira
Bayan tayi ringin sau biyu sai aka dauka yanajin muryar macece yace wacece ke.
Tace Fatima ce wadda ka baiwa nomba dinka jiya bayan kafito exams.
Yace ohh natuna ya akayine
Tace idan kashigo makaranta sai muyi magana sbd yanxu inada paper
Yace ba danuwa.yakashe wayar.

Ya dauki makullin mota da laptop dinsa yafice.

Mayiesha na shiga makaranta tafice zuwa hall dinda zata rubuta exam.
Amina ta ganta tayi mata magana amma tayi banxa da ita.
Tana fitowa exams zata tafi zuwa motarta sai amina tayo gunta tace lafiya Mayiesha inata miki magana kin wani shareni.
Mayiesha tace pls daga yau kifita har kata ba abunda zai sake hadani dake.
Ta juya kenan zata wuce saita hango munawwar da fatima.ta tsaya chak kamar wata gunki.

STORY CONTINUES BELOW

Munawwar ya gaisa da fatima sannan tace dana sirrin zuciyata ne nakeson nasanar dakai
Yace ban ganebah kamar me kenan.
Tace dama zuciyatace ta kamu da sonka

Yace dakata kin manta ke qawar matatace.

Mayiesha tayi sauri ta iso gunda suke ta janyo fatima ta kwasheta da wani irin Mari saida fatima ta fadi ta sake dagota takai mata naushi a baki har sau biyu nan take bakinta yafara jini.
Dakyar aka kwace fatima daga hannun ta ta kalli munawwar tace kai Wlhy kaji kunya karasa wacce zakayi soyayya da ita sai qawata ban yafebah wlhy.
Kekuma fatima zakici ubanki a hannuna idan har baki fita harkar mijinabah sannan kuma daga yau bani baku har abada yen iska kawai masu kwacewa mutane mazaje.
Amina tacd kinga fah kidena hadawa  dank sbd nikam ba ruwana a ciki.
Tasss taji a fuskarta tafin ta rufe bakinta tace ai duk shegiyar ce sannan ai abokin barawo shima barawo ne.

Tajuya tafice zuwa motarta ta ficewarta.
Munawwar ya kalli Fatima yace kinyi nasarar haddasa fada da matata wlhy bazan yafe mikibah sannan shima yaficewarsa.

Amina tace kinga abunda kika janyo mana yanxu koh.
Yanxu a makarantar nan kowa da abunda zai rika kallon dashi kenan.
Mayiesha na isa gida tafito daga motarta cikin sauri tashige cikin Parlo hajiya tajiyo kukanta a kitchen sannan tafito.
Tace yau kuma meya faru lafiya kiketa kuka haka.

Wlhy hajiya ko yanxu na ganshi da ita a makaranta suna ta hira.
Hajiya tace wai meyake damun munawwar ne.
Nan kuma tasake faduwa ta sume.hajiya da sauri ta riketa tace nashiga uku munawwar zai kashe yer mutane.da sauri takira yer aikinta tatayata saka Mayiesha mota sannan suka fito zamuje asibiti.
Suna shan kwana saiga munawwar yashigo da motarsa yana ganin hajiya ce aciki yayi sauri yabi bayan motar.
Suna shiga asibiti aka kaita emergency.
Munawwar ya qaraso gun hajiya yace mekuma ya faru da ita.
Hajiya ta juyo ta wankeshi da mari tace munawwar kanason kaga bacin raina koh to wlhy zaka gani kuwa meyasa kakeson kaje yer mutane.
Munawwar yace hajiya kisaurareni wlhy….
Tayi saurin katseshi tace kawuce kabani guri kafin nasaba maka.
Ya fice daganan taje ya zauna a mota sai faman kuka yakeyi.

Likitan tana fitowa tace jaririn lafiya qalau yake ba abunda yasameshi itama haka uwar amma a gskiya idan tasake fadawa irin wannan halin zata iya rasa ranta.
Hajiya tace inshallah hakan ma bazata kasancebah.
Yawwa to dan Allah a kiyaye yanxu dai muyi yi mata allurar bacci me sbd ta samu hutu zuwa anjima saiku koma gida

To likita nagode.

By maryam ashutrah

Bayan Mayiesha ta farfado ta huta sannan aka sallamesu suka koma gida.
Sosai hajiya take kula da ita.

Munawwar kuma banda damuwa ba abunda yakeyi haka dai yashirya yaje gidan abokinsa ahmad.
Ahmad yace lafiya munawwar ma ganka a haka ba nutsuwa
Wlhy wata mastsalace narasa yadda zanyi dakaina.
Yace fadamun ina saurarenka.
Ya fada masa komai abunda yafaru.
Ahmad yace lallai kuwa dole ka rikice amma yanxu kada ka damu nasan koda kaje hajiya bazata saurarekabah amma ni zanje nayi mata magana.
Yace yawwa friend Allah yasa ta fahimceka.
Ameen
Sukayi sallama yafice gida.
Da daddare Ahmad yashirya yaje gidan hajiya yana shiga suka gaisa sannan yace hajiya dama inaso nayi magana dakune akan munawwar.
Hajiya tace kaga ahmad nasan duk bakinku daya dashi basai kayimun wannan maganarbah nasan shine ya turoka to kaje kace mishi yakiyayeni.
Ahmad yacd hajiya da dai kun saurari abunda zan fada.
Tace ba abunda zaka fada na yarda dakai kawai katashi katafi.
Yace to nabarku lafiya yatashi ya fice daganan kawai ya fice zuwa gidan munawwar.
Bayan ya sanar dashi yadda sukayi da hajiya sanan munawwar yace to yanxu meye mafita.
Ahmad yace nimadai bansanibah amma  inada wata yer shawara.
To kafada mana
Mezai hana kadena zuwa gunsu sannan tunda kaga yau kagana exam dinka kawai ka shirya ya koma katsina idan kuma ka kashe wayarka.
Idan komai ya lafa sannan suka dena ji daga gareka nawasu kwanaki dole su zasu fara nemanka.
Yace good wannan shawarace mai kyau kuma haka za’ayi.

Washe gari ya kashe wayarsa sannan yafadawa ma aikatan gidanshi yabasu hutu sai idan ya nemesu.
Daga nan yabasu wasu yen kudade sannan ya fice zuwa Katsina.

Yana isa Katsina ya fice zuwa gidansu mayiesha.
Abba yayi farin cikin ganinsa sosai sai kuma munawwar yabashi labarin duk abunda yake faruwa.
Abba yace tabbas nasan mayiesha da kishi sosai amma kada ka damu idan ta sauko ita da kanta zata nemeka.

Bayan kwana biyu Mayiesha na kwance akan gadonta sai tunane tunane takeyi sai hajiya tashigo.
Tace Pls Mayiesha kidena wannan damuwar kada ya taba lafiyarki.
Mayiesha tace kinga fah hajiya ko gidannan yadena zuwa yaganni.
Sbd fatima ta fiye masa ni.
Hajiya tace kiyi hakuri bari nakira wayarsa.
Takira wayar har sau biyu amma a kashe.
Tace kinga wayarsa a kashene
Mayiesha ta fashe da kuka tace watakila yanxu haka suna tare shiyasa yakashe wayarsa.
Hajiya tacd barshi kawai zanyi magana dashi.
Da kyar hajiya tasamu Mayiesha taci abunci sannan ta kwanta.

Har kusan sati daya idan hajiya takira wayarsa sai taji a kashe.

Mayiesha tace nifa hajiya hankalina yafara tashi anya kuwa lafiya munawwar baya daukar wayansa kodai zamuje mudubane.

Hajiya tace gaskiya kam sbd yau kusan sati daya kenan wayarsa a kashe amma bari na saka jamil yaje gidansa yadubo.

Takira jamil tace pls kaje gidan Munawwar ka dunomunshi sbd yau kusan sati daya ina kiransa amma wayansa a kashe.
Yace to hajiya.
Ba’a dadebah yadawo yace ban tarar da kowa a gidanbah saimau gadi wanda yasanar dani cewa yanxu kusan kwana goma kenan munawwar baya gidansa.

Hankalinsu duka yatashi sosai.
Mayiesha tace duk lafinane nashiga uku ina munawwar yashiga.
Da sauri hajiya takira wayar ahmad amma yanuna shi rabonsa da munawwar an dade.
Hankalinsu duka ya qara tashi
Da sauri hajiya tace maza jamil yaje police station yakai rahoto a fara nemansa.

Mayiesha kam sai faman kuka take gashi taki taci komai.

Abba da munawwar na zaune a parlor suna hira sai munawwar yace amma abba yakamata fah kasake wani auren.

Abba yace ai kuma yanxu na tsufa auren me zanyi.
Eh dukda haka zaka samu wadda zata dinga yimaka girki.
Hmm munawwar kenan to shikenan idan ma zanyi auren wazan aura.

Ai bazawara zaka samu ka aura kokuma cikin yem uwa kanema.
Yace to zanyi shawara amma bana tunanin za’a samu wacce zata maye gurbin matata yanxu

Inshallah za’a samu.
To Allah yakawo ta
Ameen.

Mayiesha na kwance a palon hajiya sai kallon hoton munawwar takeyi tana hawaye.
Dan Allah munawwar kadawo gareni kodan sbd danka dake cikina wlhy na hakura.
Tatashi taje gun hajiya tace har yanxu ba’a samu inda yakebah

Wlhy mayies ba’a samubah nima na damu sosai kuma tun farko mukayi kuskure da bamu saurare shibah.

Hakane hajiya.

Da sassafe bayan abba da munawwar sun gama karyawa saiga kiran ahmad yashigo wayan abbah.

Ya baiwa munawwar yace ga ahmad ne yake kira.

Yana dauka yace yane dan gari.
Ahmad yace kai najifah an fara sanarwa a tv ana nemanka Wlhy kadawo kafin karasa matarka.
Yace aikuwa gobe gobennan zan taso zuws abuja.
Yace dadai yafikam.
Yana kashe wayar yace amma yakamata fah gobe na shirya zuwa abuja.sbd wai har anfara nemana a talabijin.
Eh toh hakane yakamata sbd daga dukkan alamu sun fara nadamar qim saurarenka yanxu kaga idan kaje dole  da kansu zasusi suji abunda yafaru.
Hakane abba.

Abba yace amma nima dani za’aje kam sbd naga inda kuke zama.
To badamuwa Abba Allah yakaimu.

Washe gari hajiya da mayiesha na zaune a palo suna hira sai Mayiesha tace wlhy hajiya sai yanxu nasan inason munawwar kuma bazan iya rabuwa dashibah.

Hajiya tayi dariya sannan tace waton ko kunyata bakyaji koh.

Yanxu dai kitashi muje supermarket mu gama siyayyar kayan jaririnki.
Mayiesha tacd wlhy yau nauyin jikina nakeji sosai
Ai daurewa zakiyi.

Suna shiryawa suka je wuse market suka gama siyayyan kayan jariri.
Suna dawowa suka saka sauran kayan cikin akwati.
Mayiesha tace wlhy hajiya wannan jaririn yasha kaya yanxu fah akwati goma kenan mukayi.
Hajiya tace gsky kam amma ai dole na gyara mijina dakyau.

Sai sukaji ance kokuma matata bah idan macece.

Suna juyowa sukaga abba tare da munawwar a bayanshi
Da sauri dukansu suka tashi Mayiesha batasan lokacinda ta rungume munawwar bah sai kuka.
Abba yace yaran yanxu bakuda kunya a gaban nawa.
Da sauri ta sakeshi tana rufe fuska.
Suka samu guri suka zauna Mayiesha tace shine kaje ka barni nikadai.
Munawwar yace kekadai kuma ai ga hajiya kuma keda kanki kikadawo gurinta da zama.

Abba yace ina wuni hajiya
Lafiya qalau wlhy ashedai kana tare da dan naka.
Abba yace ai muna tare dashi a katsina.
Munawwar yace inawuni hajiya tace lafiya qalau munawwar

Abba yayi kyaran murya sannan yace naji duk abunda yafaru kuma a gaskiya baku tsaya kuma fahimceshi bane inda kukayi kuskure kenan amma bari kuji daga bakinsa.

Munawwar yafada musu komai daga yadda sukayi da fatima yadda tasamu nombar sa dakuma plan dinda suka hada da ahmad.

Mayiesha ta fashe da kuka tace kayi hakuri munawwar na zargeka da abunda ba hakabane
Yace bakomai ai tun farko sakaci nane.
Abba yace to ai haka akeso a fahimci juma kuma alhamdulillah kuma kinga daga yau idan kuka samu matsala saiku tsaya ku fahimci juna.
Hajiya tace hakane Nima kayi hakuri da naki na saurareka
Yace ba damuwa hajiya komau ya wuce.
Abba yace kunga tunda komai yazama dai dai gobe zan koma katsina.

Hajiya tace baza’ayi hakaban kabari kadanyi kwana biyu anan sai azaga dakai kaha yadda abuja take.
Munawwar yace hakane kam gsky abba kuma kaga sai muje gidanmu tare.
Abba yace taya zan kwana gidan ya ta ai ba’a haka a al’adarmu.
Mayiesha tace haba abba kada kace haka mana.
To shikenan naji.
Bayan sunci abunci dukansu suka huta sannan Mayiesha ta shirya suka koma gida.

By maryam ashutrah

Da safe abba da munawwar na zaune suna kallon news itakuma tana kitchen tana hada breakfast.

Tana cikin soyar dankali sai taji an rufe mata ido tace to yanxu ma bazaka barni nayi aikinbah.

Yace naga ai aikinne yayi miki yawa a gaskiya dole yau nakira yen aikinki su dawo.
Tace da dai yafikam.

Suka gama hada breakfast din tare suka kai parlor.
Bayan sun gama munawwar da abba suka fita.munawar ya zazzagaya dashi ko ina a cikin garin sannan sukaje cash n carry suka danyi shopping sannan suka dawo gida.

Mayiesha na daki kwance tana hutawa sai taji cikin ta yafara ciwo.nan take abun ya fara tsanani da sauri ta dauki wayanta takira munawwar cikin sauri ya iso daki ya tallabeta sai mota.
Abba na gaban mota munawwar yayi driving suka wuce asibiti.

Suna isa aka shiga da ita labour room.
Munawwar yakira hajiya ya sanar da ita halin da ake ciki.

Ba bata lokaci saigata a asibitin.

Mayiesha tasha wahala sosai sai bayan awa uku sannan ta samu ta haihu.inda ta suntulo yer ta kyakkyawa fara tass.

Likitan na fitowa tace ina mijinta
Yace gani
Tace ina tayaka murna matarka ta haihu ta haifi diya mace.

Dukansu sukayi hamdalah sannan sai likitar tace yanxu dai tana dan hutawa zuwa anjima saiku shiga kuganta.
Munawwar kam farin cikiba daga nan bah.
Haka abba da hajiya.

Bayan awa daya suka shiga ciki hajiya ta dauki jaririyar ta kalleta tace amma wannan yarinyar mashallah akwai kyau gashi tana kama da mamanta.

Da sauri munawwar ya dauketa ya kalleta sosai sannan yayi mata kiss a gishi yace barka da shigowa duniya my daughter Allah ya rayamun ke.
Dukansu sukace ameen.
Bada jimawabah Mayiesha ta farka sannan ta karbi babyn ta takallah tace wannan yarinyar kin wahalar dani sosai amma dai Allah ya albarkaci rayuwarki .dukansu sukace ameen.
Da daddare aka sallamesu suka wuce zuwa gidan hajiya.
Sbd tace bazata zauna a gidan tabah sai tayi arba’in
Sannan tace jibi zamuje katsina  sbd achan nakeso ayi bikin tunda
D

uk yen uwana suna chan.
Dukansu sukace to Allah yakaimu.
Mayiesha tanashan kula sosai ga hajiya da kuma baby wacce dakeda yawan kukan banza.

Ranar biki yarinys taci sunan mahaifiyar mayiesha inda ake kiranta da MISHA.
Anyi taro sosai sbd har yen uwan alhaji abdulhakeem dake zama a kaduna saida suka halacci bukin sannan da qawayen hajiya wadanda ke zama a qasar waje dakuma na sassan nahiya daban daban.
Misha kuma tasha kaya kala kala.

Bayan sunyi kwana arba’in a katsina sannan suka fara shirye shiryen dawowa.
Munawwar yaje gun abba yace abba ya maganar mu
Abba yace wace magana kenan
Ta aurenka mana
Ohh munawwar kenan mun sasanta da wata bazawara dake hayin layinmu kuma ta amince saidai kawai yanxu ni ake jira.
Amma tana da ‘ya yer qarama.

Ai abba wannan ba matsala bane kuma kaga zakuci gaba da kula da ita tare amma ninakeso na dauke nauyin bikinan gabaki daya kawai idan an saka rana sai kafadamun.
Abba yace munawwar kenan waton kama fini son wannan auren
Wlhy abba kawai banason kana zama kaikadaine kaga akwai kadaici
Hakane maganarka munawwar Allah dai yashige muna gaba
Yace ameen.

Da suka koma abuja hajiya ba qaramin shirya Mayiesha tayibah sannan ta koma gidan mijinta.
Bayan munawwar ya sanar da Mayiesha da hajiya akan auren abba ba qaramin dadi sukajibah sannan suka saka albarka.
Hajiya tace amma fah yakamata yakasance kafin kuwuce london sbd kunga admission dinku yafito kawai abunda yarage shine kufara shiri.
Dukansu sunji dadi sosai sannan bayan munawwar ya sanar da abba shima yayi farin ciki sannan yace sunje sun samu iyayen matar kuma sunce ko nan da sati biyi ma yayi.

Munawwar yace to Allah kaimu.

Bayan ya sanar da hajiya dukansu suka fara shirye shirye daga lefe har izuwa hadimar biki duka hajiya ta dauka.

Bayan sati biyu akayi bikin alkasim wato abban mayiesha da habiba.
Bikin anyishi dai dai baiwuce tsaribah saidai hajiya sunyi hidima sosai gun walima.
Ana kawo amarya ya gabatar da ita gunsu hajiya.
Yace wannan itace ‘yata tilo wato mayiesha ameenatu
Saikuma munawwar mijinta sannan mahaifiyarsa wato hajiya salamatu.
Mutanen kirkine wadanda ba kamar su sannan bamuda kamarsu a duniya sbd haka kema inason ki kyautata musu sosai Allah yabamu zaman lafiya.
Tace inshallah zan kyautata musu sbd ai baza kaki mai sonkabah.
Hajiya tace to Allah yabaku zaman lafiya da kuma aure mai dorewa
Dukansu sukace ameen
Bayan wani dan lokaci suka tashi zuwa gida.
Inda akabar ango da amaryarsa😜😎
M

ayiesha na cikin bacci misha ta tashi sai faman kuka takeyi amma Mayiesha da nauyin bacci duk batajibah munawwar yatashi ya dauketa sannan ya dinga bubbuga Mayiesha dakyar tatashi ta karbeta.tace wlhy Misha tacika tsiwa.
Munawwar yace nidai kada kiyiwa ‘yata fada.
Da kyar aka saku takoma bacci sannan suma suka koma bacci.

Washe gari da safe sukaje sukayiwa su abba ban kwana sannan suka kamo hanya zuwa abuja.
Suna dawowa suka fara shirye shiryen tafiya London.
Bayan sun gama komai ranar jumuah suka shiga jirgi zuwa london.

Suna isa suka wuce masaukinsu wani babban gida me mai matukar kyau wanda anan hajiya ko alhaji suke sauka idan sukazo london.

BAYAN SHEKARA UKU🌼🌼🌼

suna sunata shirye shiryen dawowa musha tace ammi kenan zamu koma nigeria bazamu dawobah.
Mayiesha tace misha kenan zamu dawo wani lokacin amma dai bayanxu kusabah.
Munawwar yace ki kyaleta zan dinga kawoki idan kinaso kinji.
Tace yawwa daddy na.
Munawwar yace kinga gobe zamu wuce umra zamuyi kwana goma sannan daga chan kawai muwuce zuwa Nigeria.
Tace hakan ma yayi sosai.

Suna gama umra sannan suka kamo hanya zuwa Nigeria.

Suna isowa Nigeria aka aiko driver ya daukesu suka sauka a gidan hajiya.

Da sauri misha taje gunta tace granny nayi missing dindi kikace zaki zo amma baki zobah.
Hajiya tace kiyi hakuri banida lafiya ne shiyasa.
Mayiesha tace hajiya ya jikin naki.
Wlhy da sauki sosai Mayiesha
To Allah yaqara sauki.
Misha taje gun munawwar tace abba wannan shine gidanmu.
Yace no wannan gidan hajiyane gobe zamuje namu gidan.

Tace i hope yafi gidanmu na london kyau
Mayiesha tace misha kiyi shuru da bakinki kincika surutu.
Hajiya tace ku kyaleta tayi maganarta
Yanxu dai kuje ku huta sannan kuzo kuci abunci.
Suka tasho zuwa daki mayiesha tace misha zonan.
Misja tace no nikam ina nan gun Granny dina ita zata kula dani.
Hajiya tayi dariya tace sosaima kuwa baby na.

Bayan sun huta sannan suka sauko zuwa cin abunci suna gamawa suka fice daki domin su kwanta.
Misha kuma ta lakewa hajiya lallai saidai su kwana tare.

Mayiesha takira abba take sanar dashi dawowarsu .yayi farin ciki sosai sannan tace qarshen sati zasuzo nan katsina.
Yace Allah yakaimu.

By Maryam ashutrah

Da rana suka gama shirinsu sannan suka wuce zuwa gidansu.
Suna isa aka bude musu gate suka shiga.+

Misha tana fitowa tace wow daddy i love this house.

Yace to wannan shine gidanmu kuma anan zamu zauna.
Taje gun motar Mayiesha tace daddy wannan motar waye.
Yace motar mummyn kice waccan kuma tawa.
Tace to nikam ina tawa daddy.

Yace zan siya miki kema sai a rinka kaiki makaranta a ciki tace yawwa my daddy i love you.
Yace i love you too my misha.
Mayiesha tace nidai idan kun gama shirmen naku kusaman a ciki ta shigewarta.
Munawwar kuwa saida suka gama surutunsu sannan suka shigo.
Misha tace daddy where is my room.
Yace yana sama a gefen na mummyn ki anjima zamuje tare sai nasiyo miki toys da sauran kayan wasa a saka miki a ciki.
Tace muje ka nunamun sukaje dakin tace wow daddy this room is beautiful i really love it.

Yace it will even look more beautiful when we decorate it later.

Masu aiki suka fito dukansu sunayi musu sannu da zuwa.

Sannan suka wuce zuwa kitchen hada musu abunci

Sunayin wanka suka sauko qasa cin abunci sai mayiesha tace yawwa dama nayi magana da abba nace dasu zamuje qarshen wannan satin mugansu.
Yace ba damuwa Allah yakaimu.
yawwa dama inason nafada miki zan chanja muna motoci.

Tace abban misha amma ai naga wadannan ba abunda sukayi.
Yace ehh amma ai latest dinsu zamu siya.
Tace ba damuwa Allah ya qara budi na alhairi yace ameen.

Qarshen satin dukansu harda hajiya suka tafi katsina inda sukaje gidan abba.sun tarbesu da kyau sosai.
Mayiesha tacewa misha wannan grandaddy dinkine.
Wannan kuma Granny dinkice.
Tace umma i like them.

Abba ya dauki misha  yace yer baturiya mai wayo sosai.
Misha tace daddy na yakoyamun wayo.

Munawwar yace Mayiesha zan barku anan sai anjima sai nazo mutafi hajiya takirani akwai abunda zamuyi tace to Allah yakiyaye ya fice.
Misha ta saka kuka itakam a dole saitaje da daddyn ta dakyar suka lallasheta.

Hajiya da munawwar sukaje company din alhaji wanda bayan cike ciken takardu da sauransu ya zamanto a karkashin kulawarshi.sanann hajiya ta damka mishi harkokin business dinta dake qasar italy da paris.sannan da sauran companies din.
Yaji dadi sosai sannan yace hajiya kitayani adduah Allah yabani ikon rikewa tace Ameen.

Da daddare munawwar da hajiya suka zo gidan abba.inda matar abba ta dafa musu tuwon shinkafa da miyar taushe da man shanu.
Sunaci suna santi.
Munawwar yace gsky aunty kin iya girki sosai.
Tace nagode munawwar amma ai sbd ka dade bakaci abuncin gargajiya bane shiyasa.
Mayiesha tace kikyaleshi aunty kawai fah sbd yace kinfini iya girkine dukansu sukayi dariya.

Duk abuncin da sukeci itakam misha saishan cornflakes dinta takeyi acewarta bazataci tuwo bah.

Suna gamawa sai munawwar yace abba dama inason nabiya maka kaida aunty kuje umra wannan watan inshallah.
Abba yayi farin ciki sosai yayi godiya.
Aunty kuma harda yen hawaye acewarta ko abuja bata taba zuwabah gashi yanxu zataje umra.
Tayi godiya sosai.
Hajiya tace ka kyauta sosai munawwar haka akeso mutum yadinga kyautatawa yen uwansa.
Allah yayi muku albarka dukansu
Sukace ameen.
Basu wani dadebah suka fice zuwa gida.
Washe gari kuma suka koma Abuja.

Bayan wata biyu
munawwar yaqara zama wani irin babban attajiri ya gina masallatai da gidan marayu sannan yana taimakon mutane iya iyawarsa.

Hakama Mayiesha taginawa ummanta masallaci da rijiyoyi a katsina sannan tana taimakawa yen uwansu sosai dama talakawa. bayan haka tana kasuwancin atamfofi da sauran kayan mata tare da hajiya sannan kuma tana da ciki wata daya.to Allah ya sauketa lafiya

Misha kuma an sakata a makaranta inda take kokari sosai gurin karatu.gata kuma da wayo sosai.

Bayan wata takwas ta haifi danta namiji kyakkyawa wanda yaci sunan mahaifin munawwar wato abdulhakeem wanda akekira da mubeen.inda akayi buki na kece raini.

Hajiya tatashi bata danjin dadin jikinta inda suka tilasta akan lallai saitazo ta zauna dasu sbd basason tana zama ita kadai gashi tsufa yafara yau lafiya gobe jinya.

Tana zaune a babbar kujera tana dauke da mubeen.tace ina godewa Allah daya azurtani da ‘da irinka munawwar sannan da suruka kuma ‘ya mayiesha sai kuna jikokina kyawawa misha da mubeen  ba abunda zance saidai nace ALHAMDULILLAH.
(The family of M)

ALHAMDULLILAH
GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI ALLAH WANDA YANUNA MUN NAGAMA WANNAN LITTAFIN MAI SUNA MAYIESHA kuma ina mika dunbin godiyata ga masoyina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *