MAFARI CHAPTER 3 BY UMMU AZAMM
Www.bankinhausanovels.com.ng
Misalin karfe biyu na rana ya kammala da kome da ya shafi sabon wurin da zai fara aiki inda aka tura su shi da sojojin dake ƙarƙashin sa chan tsakanin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno ,”+
Karfe huɗu jirgin su na sojoji ya ajiye su a cikin garin maiduguri inda zasu kwana zuwa washegari su wuce inda suka nufa ,”
Tun isar sa babbar hedkwatar soji na birnin na maiduguri , hankalin sa ya tashi da ganin irin taron mutane maza da aka gaggarƙame cikin ɗakunan horo , a galabaice matuka , cikin azabobi da horo mai tsanani wanda a gaban idanun sa ma yaga an fidda gawarwakin jama’a daga cikin ɗakin horon da azaba ta kashe su ,”
Duk da cewa a matsayin sa na babban soja hakan ba bakon abu bane ,toh amma zuciyar sa ta taɓu da yaji daga bakin wani sojan nigeria cewa waɗannan mutanen , mutane ne waɗanda aka kama akan zargin suna da hannu wurin tada tarzomar boko haram da ba’a kai ga tabbatar da laifukan nasu ba ,sune a jibge a garƙame cikin horarwa da azabtarwa , yunwa da ƙishirwa ,rashin isashen muhalli ta yadda wasu a tsaye suke wuni , wasu a tsugunne ,wasu a tanƙware , wanda yawan su ya tasamma dubunnai ,”
Gagara samun nutsuwar zuciya yayi bayan ya koma masaukin sa ,zuciyar sa sai kai kawo take da tunanin san samar da mafita ga waɗannan bayin Allah waɗanda a zahiri akwai zalinci cikin irin wannan ajiyar da ake musu ,kamata yayi a miƙa su ga kotun ƙasa ta yankewa kowa hukuncin sa dai-dai da shi waɗanda basu da laifi a sake su , wannan hukuncin ajiye su ana gana musu azobobin da suke kai su ga rasa rayukan su yayi tsanani da rashin dacewa ,”
Har gari ya waye bai sake marmarin fita ba sai da suka tashi barin ainahin cikin garin maidugurin zuwa bakin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno , a tare da shi da tawagar sojojin su na niger da kuma ƙarin wasu sojojin nigeria , zuciyar sa cike da tausayin al’ummar da sanadin boko haram ta ɗaiɗaice suka bar ainahin cikin garin na maiduguri .
*******
Cikin kwanaki biyar ɗin da su yakaka da falmata suka ƙara cikin sansanin su basu tsinci kome ba sai tarin wahalwalun da suka sake jikkata gangar jiki da ruhin su ,”
Domin zuwa yanzu karfi da yaji su yakaka sun zama ƴan aikin matayen nan da aka haɗa su rayuwa a ɗakuna ɗaya da su,”
Ta bangaren yakaka matar da suke kwana tare wacce ake kira “fanne” ta maida ta baiwar ta wacce take yi mata bauta nata da na ƴaƴan ta , tun daga kan wankan yaran biyu har zuwa wankin bargunan su da kullum ta Allah sai yaran sun zabga fitsari , wankin ƴan tsirarun kayan yaran da koyaushe ba’a rasa shi da guntun kashi da fitsari wanda yakakan take shan wahala wurin wankin saboda rashin isashen ruwa da sabulun wankin ,uwa uba rainon yaran da suke kusan yini goye bisa bayan ta duk wata jigila da su take yi suna ɗane a baya , ta sauke wannan ta goye wancen ,uwar su kuwa tana chan cikin yaran mata tana zuba hira da ɗinkin hular ta ,”bata chas bata ass ,
Ga falmata kuwa duk da kasancewar ta miskiniya amma hakan bai sa ajus ta ɗaga mata kafa daga sanyata ayyuka ba ,” tun farar safiya idan ta tashi daga kan shimfiɗar da a yanzu ita kaɗai ke kwana a cikin gidan sauron sakamakon irin azabar da take ganawa falmatan cikin dare ya sa ta hakure ta samawa kan ta salama daga ,zagi hantara ,hauri , mangari da mintsinin da ajus take buwayar ta da su cikin dare , ta bar kwana a gidan sauron ta komo bakin kofa tana shimfiɗa zanen ta tana kwanciya bisa ,”
amma duk da hakan ita ke lalubawa ta naɗe gidan sauron ta kuma ninke kayan shimfiɗun da ajus ɗin ta kwana a kai , bata bar ta haka ba kullum ita take ɗebo mata ruwan wanka a bokiti da na tsarki a buta , daga bakin famfo inda anan suke samun damar haɗuwa ita da yakaka wacce ita ma take zuwa ɗibo ruwan hidimar fanne da ƴaƴan ta , famfon baki uku ne rak da shi kuma idan aka tayar da injin bada ruwan karfe biyar na asubah zuwa karfe bakwai na safe ake rufewa sai kuma lokutan sallah da shi ma na ɗan kalilan ɗin lokaci ne sakamakon rashin man tada injin tare da rashin wutar lantarki ,”2
STORY CONTINUES BELOW
dan haka yaƙi ne tukuru yake tashi wurin kokowar ɗibo ruwan wanda mai karfi ke ture na ƙasa da shi ya samu ya ɗiba ,”ire-iren su yakaka kuwa da kƴar da suɗin goshi da faɗawa cikin dagwalo tare da jin ciwo take samu ta cikawa falmata nata kayan ɗiban ruwan “da yakakan take tsaida ta a gefe ta hana ta shiga turmutsutsun ɗibo ruwan” ta kuma ɗibo nata , wanda mafi yawancin lokuta ake kashe injin bada ruwan akan bokitin ta ,” hakan ya sa har yau da suke cika kwanaki shidda wanda yake dai-dai da kwanakin su bakwai da barin mahaifar su ,fatar jikin su bata ga ruwan wanka ba sai dai ɗaurayar kafafu da hannaye zuwa fuskokin su da suke yi da ruwan alwala ,” dan haka duk suka bi suka sake hautsinewa tare da ficewa daga kamannin su ,suka zama yarkace yarkace tamkar sabbin mahaukata.6
Ɗan dama-daman yagana ce wacce daman ita ta ɗan fi su wayewa da buɗewar idanu saboda ta tashi a alkaryar da take da wadatuwar wayewa , dan haka bata yadda kowacce mace ta nemi taka ta, bata yadda tayi aikin bauta ga kowa , sannan kuma abokiyar kwanan ta ma yarinya ce budurwa sa’ar ta dan haka suke yin chanjaras daga ta nemi kawo mata wargi ,” damuwar ta yanayin rayuwar da take gudana ne a wurin da yanzu ta tabbatar ba gidan gwamnati bane , wuri ne na kazo na zo rayuwa ce irin ta daga ƙwari sai gwaiwa ,kowa kan sa ya sani rayuwa ce ta nafsi-nafsi ,uwa uba rashin wadatatcen abinci ,da ruwan sha ba’a maganar kayayyakin gudanar da rayuwa irin ta yau da kullum kamar su sabulan wanka da na wanki ,suturu da sauran su ,”
wanda tun zuwan su bata ga alamun za’a taimaka musu da waɗannan ba ,” ga fatara da ta addabe ta saboda rashin koh kwandala da take matsayin mallakin ta ,”
gefe guda na zuciyar ta tana tausayawa abokan tafiyar ta da a yanzu ta fisu ƴanci , ta kuma sha zama ta gwada musu yadda zasu ƙwaci ƴancin kan su daga hannun ƴan iskan mata azzaluman da suka maishe su bayin su ,2
sai dai daga yakakan har falmata babu mai kumajin iya kwatarwa kan sa ƴancin saboda rangwamen wayewar kai tare da ƙarancin shekaru ,5
ɗan gwara ma falmata idan ƙumu ta ƙuma mata kai ta kan iya yin hobbasa ta nemi matsera daga hannun ajus ɗin ta hanyan yi mata batar dabo ta gudu bayan ajujuwa cikin datti da guntun najasa tayi zaman ta ,”
amma ga yakaka babu fuss , akan ga ƙwanjin ta ne kadai idan aka taba mata sanyin idaniyar ta falmata a gaban idanun ta , amma akan kan ta kam raguwa ce ta kin ƙarawa ,”1
Dan haka kamar yau da suke zaune su ukun turmus a cikin rairayin da ganyayyakin bishiyar darbejiya ya lulluɓe ,yagana ta dubi fuskar yakaka da take duk jirwaye da lollori “( abun ka da farar fata )
“Nikam yakaka wannan mawuyacin halin da muke ciki a sansanin nan namu ya isheni , domin ban hango ranar yankewar wahalar mu ba a haka muna zaune cikin rashin sanin makomar rayuwar mu ya kamata mu samarwa kan mu mafita tun kafin ta ƙure mana ,”
dan zunkuɗa goyon yaron da ke ɗane baƙe-baƙe akan bayan ta wanda iskanci ne irin na yara ya sanya shi sanya kukan sai an goya shi domin yana yawon sa da gudun sa ko’ina ,”
“Hmm yagana kenan toh wace mafita kike tunanin muke da ita , mu da bamu da kowa kuma bamu san ko’ina ba sai nan ɗin ? Ai ina ganin haka zamu cigaba da hakuri har zuwa lokacin da ubangiji zai sauƙaƙa mana domin nasan yana sane da mu ,” ta karashe zancen tana mai kokarin maida ƙwallar da ta ciko mata a ido
STORY CONTINUES BELOW
Yangana ta nisa cikin kallon sashin da falmata take wacce gaba ɗaya ta maida hankalin ta ga gefen su tamkar dai idanun ta suna kallon wani wajen , da azahiri kunnuwan ta tarwai suke tana kuma sauraran tattaunawar tasu ,kawai bakin ciki da damuwa ne suke danƙare a kahon zuciyar ta
“,Amma ai kina ganin yadda wasu mutane dayawa a sansanin suke taɓuƙawa kansu wasu abubuwan ta hanyar kula da rayuwar su da ƴan kananun sana’o’in da suke , me zai hana muma mu yunƙura mu gwada sa’ar mu koh zamu samu damar taimskon kan mu da kan mu yakaka rayuwa a haka bazai yiwu ba ,”
Murmushin takaici yakaka tayi ganin yadda yagana ta hakikice akan batun neman sana’a
Yagana kin manta da ruwan ciki ake jaan na rijiya ? Ita kan ta sana’ar ai sai da jari ,mu kuwa bamu da ko sisi bamu da kadara toh aina kike tunanin zamu samu jari bare a kai ga batun fara tunanin sana’ar yi
Nasan bamu da jari yakaka toh amma ai ga “kolo”(abokiyar kwanan ta ) ita ma bata da jarin amma tana bi tana neman aikin kwangilar yin ɗinkin hula ,ana biyan ta muma mai zai hana mu nemi kwangilar mu dunga yi koh zamu samu ɗan kuɗin biyan kananun buƙatu ?
Jimm yakaka tayi cikin tunani a zahiri ita bata wani iya ɗinkin hula ba sai dai tana ganin bata da wata mafitar taimakawa kan su ita da falmata idan ba ta wannan hanyar da ƙawar kirki yagana ta zo da ita ba ,” dan haka ta ɗago da murmushi dai-dai lokacin da falmata ta waiwayo su tana me kafe gefen da take jin muryar yakaka da ido ,”
Yakaka bata iya ɗinkin hula ba koh riƙe allura a soka bata iya ba, asalima a cikin wannan halin bautar da muke ciki ina yakaka zata samu damar da zata zauna ɗinkin hula , yakaka kar ki ƙarbi abun mutane ki zo ki ɓata musu abu ya zo ya zama rigima da muguwar rawa gwamma ƙin tashi mu cigaba da addu’a Allah zai kawo mana mafita ,”
Falmara ta furta hakan karon farko tana me jin ciwon rashin idanun ta da babu abun da zai hana tayi ɗamarar karba kwangilolin ɗinkin hula har sai ta samar musu rayuwar da ta fi wacce suke yi yanzu inganci ita da yayar ta domin babu dare ba rana zata duƙufa soka allura da zarewa koh da zata tsire ƴan yatsunta da allura ,” sai dai tana jin baza ta iya barin yakaka ta yi ba saboda sanin irin tarin ayyukan da suke jibge akan yakakan wanda mafi akasarin su na wannan azzalumar matar ne fanne ” idan dai ba tsakar dare yakakan zata tashi yin ɗinkin hular ba bata hango tana da lokaci ba , tsakar dare kuma da wanne haske zata soka allura a matsayin ta na ƴar koyo ? Su da basu da koh ashana bare tocila ? Zata fi so yagana ta zo da shawarar wata sana’ar da ita ma za’a iya haɗuwa da ita ayi .
STORY CONTINUES BELOW
Shiru ne ya biyo bayan katse musu hanzari da falmata tayi ,kafin yakaka ta yunƙura cikin karfin zuciya
” zan iya falmata , yagana yaushe zamu samu kwangilar ɗinkin hular kuma aina zamu samu ? Wallahi zan yi koh da a tsaye koh a durƙushe ne zan kuma koya na kware cikin karamin lokaci ni dai fatana mu samu na kan mu ,”
ta ƙarashe zancen tana mai kamo hannun yagana wacce tayi shiru tana jimamin bahagon halin falmata ,3
Toh bari mu fara tuntuɓar kolo koh zata shige mana gaba domin ita ta san masu bada kwangilar saboda ta fimu daɗewa a sansanin ,”
_____
Saɓanin tunanin su yakaka akan saukin samun kwangilar ɗinkin hula sai ga shi har yau da suke kwanaki huɗu da fara neman aikin kwangilar ɗinkin hular ,amma koh hula ɗaya ta gagara samuwa a gare su , daga ita har yagana ,saboda kowa shakkar basu ɗinkin hular sa yake domin gudun kar su ɓata masa dan babu wanda ya tabbatar da ƙwarewar su , kamar yadda ita kolo tayi suna wurin ƙwarewa da saurin ɗinkin hula hakan yasa take samun kwangila sosai,”
Har dai yanzu da suka gama hakiƙancewa baza su samu ba ,”kolo wacce ita ma ƙwarai ta so su samu ɗinkin koh dan ɗasawar da suke ita da yagana a yanzu ,”
Mai zai hana toh ku nemi wata hanyar neman kuɗin yagana ? Cewar kolo
Kolo kenan ina muka ga jarin neman kuɗi ? kina ganin aikatau ma mun gagara samu .inji yagana wacce duk mamakin halin mutane na rashin taimako ya cika ta,
Akwai hanyoyin neman kuɗi mana ba iyaka ma mu da muke cikin birnin maiduguri ,”
Tun kafin ta ƙarasa yakaka ta tari numfashin ta toh ai kolo bakya ganin mu a kulle muke cikin sansanin mu ba’a kuma fita sai da dalili mai karfi kamar idan kana saye da sayarwa koh kuwa ka nemi iznin zuwa ganin wani naka cikin gari ka ci sa’a an bar ka
Idan dai har kun tabbatar kuna son fita domin zuwa neman kuɗi cikin gari ni kuwa zan muku hanyar da koh kwanaki nawa zaku je kuyi ku dawo idan ma kuma zuwa zaku dunga yi kullum kuna dawowa duk zan taimaka muku , ku dai da farko yanzu kuyi tunanin sana’ar yi , idan kun fitan
Cikin zumuɗi yagana tace toh ai ke kolo da kike fita cikin garin ke zaki fi mu sanin sana’o’in da zasu dace da mu kuma wanda zamu samu , ni dai ko ma meye zan yi , haka kuma nasan kawayena ma zasu yi ta furta hakan tana mai maida kallon ta ga yakaka wacce tayi shiru kamar ruwa ya cita , cikin ran ta wasi-wasin fitar su daga sansanin su take da fargabar abun da ka iya zuwa ya dawo a matsayin su na ɓaki da basu san ko’ina ba ,muryar kolo ta katse mata tunani
Toh kun dai ga ana aikatau a gidajen mutanen gari ,”ana bara , ana aikatau a gidajen saida abinci idan baka tare da ƙazanta ,ana yin aikatau har a cikin kasuwanni , idan kana so tashi biya idan kuma kana so biyan wata yanzu haka nima ina wanke-wanke da shara gidan wata mata amma tashi biya muke , kullum naira ɗari biyu take biyana kuma na ci abinci nasha ruwan leda ga kaya kuma tana bani ,
bata tsagaita ba ta cigaba da cewa tun da ku baku da naƙasa zaku iya yin aikatau ita kuma ƙanwar ku tayi bara a bakin kasuwa wallahi zaku yi mamakin kuɗin da zaku samu akalla ɗari bakwai zuwa dubu ɗaƴa a kullum banda kuma kwancen kaya da za’a dunga baku da sadakar ɗanyen kayan abinci ,
Cikin nazari yagana da yakaka suke kallon kallo yayin da falmata tayi jugum ta ƙurawa guri ɗaya idanu tana tunani ,”Shiri yakaka take sauri-sauri , tana yi tana taya falmata yin nata shirin , cikin mintocin da basu gaza goma ba har sun kammala , duk da dai kayan su na jikin su da suka cire suka sake mayarwa amma bisa ga dukkan alamu da su da kayan nasu sun ɗan samu tsafta domin sun ɗan yi haske , hakan kuwa bai rasa nasaba da wanka da wankin da suka samu damar yi tun a dare jiya bayan da suka tsaida shawarar fara fita neman na kansu cikin gari a ƙarƙashin jagorancin kolo da yagana ,
Kamar yadda kolo ta tsara musu shine su yakaka da yagana kowacce zata fita neman aikatau , yayin da falmata kuma zata zauna a bakin kasuwa tayi bara ,”
Da farko yakaka bata amince da yin barar falmatan ba , turjewa tayi sam tace sai dai falmata ta bita inda zata samu aikin ta zauna ta dunga jiran ta har zuwa lokacin da zata kammala ayukan sai su koma tare , abun da duk ta samu tayi musu hidima tare , kuma abun da duk ta ci , ta bawa falmatan ,
Sai dai ga mamakin ta firr falmata taki ta amince da tsarin ta , ta tsaya kai da fata akan lalle ita ma sai ta nemi hanyar taimakawa kan su wanda kuma hanyar a yanzu ɗaya ce ita ce yin bara , idan har kuwa baza ta amince tayi bara ba toh sai dai tayi zaman ta kawai a cikin camp domin bata ga amfanin bin ta da zata yi kawai ta zauna ba .1
Ala tilas ta amince mata domin gudun bacin ran ta, da kuma sanin cewa baza ta iya fita daga camp ɗin ta bar falmatan ba , toh ta bar ta a hannun wa ? Ga larurar da take tare da ita , amincewar ta shi ya zama dole sai dai bisa sharaɗin baza su nisanta da juna ba , dole a tsukin gurin da falmatan zata yi zaman barar ta anan ita ma zata nemi nata aikin .
_____
Yakaka , falmata ku fito mu tafi mana kar muyi rana , kolo ta riga ta gama magana da mai tsaron kofa
,”yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da take ƙarasowa bakin kofar ɗakin da su yakaka suke ,”
Gamu nan yagana mun gama shiri sai tafiya ,”
cewar falmata fuskar ta ɗauke da yalwatatciyar fara’a a karo na farko da yagana ta gan ta cikin farin ciki kwatankwacin wannan , wanda bata raba ɗaya biyu murnar zasu fara dasa harsashin cigaban su ne a karon farko cikin tsananin rayuwar da suka tsinci kansu ,”
Hannunwan su sarƙe da na juna suke sanya kafafun su domin barin cikin sansanin su da suka wanzu a cikin sa tun ranar da suka shigo birnin na maiduguri , yayin da sashi guda na zuciyoyin su ke cike da fata tare da burin zuwa su nemo na kan su ,gefe guda na zuciyoyin nasu kuma fargaba ne tare da taraddadin yadda fitar ta su zata kasance ,
Sansanin su a bakin babban titi yake dan haka basu sha wahala ba wurin samun motar bus da take jigilar mutane zuwa kowanne sashi na garin ,
Kasuwa monday market
Kolo ta furta bayan ta tsaida wata kwaraɓabɓiyar motar bus da take ɗauke da mutane jingim a cikin ta ,”
Shiga muje
Cewar conductor ( karen mota ) wanda ya wangale musu kofar motar ,
Ni ɗaya ce zan zauna akan kujera su akan inji zasu zauna ,”
cewar kolo dai-dai lokacin da take shigewa cikin motar domin yi wa kan ta matsugunni ,”
Wata zamiya kondoktan yayi tare da zabura ya babbake kofar motar ,”
Nai gamma waɗannan ƙattin ƴan matan har su uku ne zasu hau kan inji kut ? ,”
STORY CONTINUES BELOW
Kayi hakuri dan Allah yayana ka taimaka mana wallahi naira ɗari daya ce jal da ni , kuma ni zan biya musu domin su da ka gan su nan koh sisi basu da shi mu ƴan gudun hijira ne , ” cewar kolo cikin marairaicewa da karya wuya ,”
Kai ina bazai yiwu ba malama waɗannan sun yi girma da hawa kan inji a jere su uku rus ,
ya karasa zancen yana me jifan su yakaka da kallon banza wadanda suka yi tsilli tsilli a tsaye cike da taraddadin ganin samu da rashi ,sanin cewar idan aka ƙi ɗaukar su toh fa babu su babu tafiya dole su koma cikin sansanin su .
Tsalle konduktan yayi ya ɗale motar gami da bubbuga murfin tare da cewa “,Muje oga,”
Tsaya tsaya nima zan sauka tun da baza ka ɗauke mu tare da ƴan uwana ba ,” Burki direban motar ya jaa lokaci guda ya juyo cikin hargagi yake tambayar me ya faru ne ?
Konducto yayi masa bayani ,” sake tambaya yayi akwai sarari ne akan injin ,”
Akwai sarari oga sai dai sun yi girma sosai mutanen da ke kan sit zasu takura sosai ,”
Wani banzan kallo direban ya wurga masa da jajayen idon sa ,”
Ganin hakan ya sa da sauri konducton ya sauka gami da buɗe motar , yayi wa su yakaka alamun kira da hannun sa saboda har motar ta ɗan gifta ,”
Miƙo kuɗin ku
Cewar karen motar lokacin da direba ya daidaita motar sa akan titi
Da sauri kolo ta miƙa masa tsohuwar naira ɗarin da ta gama shan wahala a hannuwan jama’a
Azabar zafin inji da zafin ranar da motar ta ɗauka suka haɗu suka sa su yakaka , falmata da yagana haɗa gumi kirshiɓ suna ta ɗiga , yayin da suka kasa zama wuri ɗaya akan injin sai mutsu-mutsu suke suna jin zafin ƙunar da injin motar yake musu a ɗuwaiwai , uwa uba yadda suka takura suka cure guri guda kamar “kifayen gongon” gefe guda ga warin da konducton yake wanda ya buɗe hannayen sa ya tokare ɗaya hannun dai-dai fuskar falmata wari da tsamin hammatar sa na barazanar sanya su haraswa ,”4
Bayan tsawon lokacin da bai kamata ace sun yi shi ba daga tsakanin sansanin su zuwa bakin kasuwar , amma a sakamakon rashin kyaun motar ,tsufan ta da kuma tsayawa a sauke fasinja a ɗau wasu a hanya ,ya sa suka kusan shafe mintuna arba’in a kan hanyar da bai fi suyi mintoci goma zuwa sha biyar ba , “
Cikin jigata suka sauko daga cikin motar , fuskar kowaccen su na nuna wahalar da ta sha a yayin tafiyar ,”
Yawatawa da idanun su yakaka da yagana suke yi cikin mamakin ganin yawan jama’ar da suke ta hada-hadar su a wurin duk kuwa da cewa hantsi ne bai wuce karfe tara da rabi zuwa goma na safiya ba ,”
Toh ku zo mu tsallaka titi kun ga chan ita ce kasuwar monday market maiduguri ( ita ce babbar kasuwar da take ci a kullum cikin birnin na maiduguri )
kolo ke yi musu wannan bayanin .
STORY CONTINUES BELOW
Ba ƙaramin ɗauki ba daɗi aka yi cikin turƙa-turƙa kafin su yakaka suka iya tsallaka babban titin na Ahmadu bello da yake daura da kasuwar ta monday market ba ,”
BAYAN AWA ƊAYA
Duk wani zagaye sun gama shi amma basu yi dacen samun gurin da zasu yi aiki ba a zagayen har ma da ainahin cikin kasuwar , kama tun daga kan masu tuwo-tuwon da suke ciki da wajen kasuwar har zuwa kan goge-goge koh jiran shago , hasalima wurare da dama da suka je korar kare aka yi mu su ,”
Yagana , yakaka , kun dai ga yadda aiki ya gagara samuwa a gare ku a cikin kasuwa , hakan ya sa ya zama dole ku shiga cikin unguwanni ku kutsa koh gida-gida da wuraren sayar da abinci na cikin gari koh Allah zai sa ku dace , ni yanzu gaskiya rana ta riga ta ɗaga aƙalla yanzu sha ɗaya da rabi ta kusa kun ga na riga na makara zuwa gidan aiki na , duk da dai cewa daga nan zuwa cikin unguwar da nake aikin babu nisa amma yakamata ace tun tuni ina bakin aiki kamar yadda na saba , saboda haka ni zan tafi idan ya so anjima da yamma mu haɗu a tasha inda mota ta sauke mu ɗazu , amma kafin nan ita falmata yakamata ta samu wurin zama domin yin barar ta domin kuwa babu inda ya kai bakin kasuwa samun sadakha , dan haka mu matsa daga chan wurin gefen bankin chan ta tsaya ko ta zauna a wurin har zuwa lokacin da zaku dawo , ina mai tabbatar muku da zata samu kuɗaɗe sosai ,
Duk kalma guda da take fitowa daga bakin kolo dai-dai take da ƙaruwar luguden da zukatan su yagana ke yi , wannan fa shi ake kira ” anyi gudun gara an tadda zago ” toh su kuwa ina zasu fuskanta cikin wannan turmutsutsu da taron jama’ah ?
Ta ina zasu fara dilmiyar da kan su cikin gari alhalin basu da tabbacin zasu iya gane hanyar da zata dawo da su nan mahaɗar ta su , wanda a zahiri cikin zagayen awa ɗaya jal da kolo tayi da su a tsukin kasuwar , a halin yanzu koh tashar da mota ta sauke su baza su iya komawa ba saboda kan su ya riga ya juye , ina ga batun kutsawa cikin gari cikin unguwanni , ai wannan zancen ma bai taso ba ,”
Kusan a tare su ukun suka haɗa baki gurin fara magana ,” amma sai yakaka da falmata suka saurara domin bawa yagana damar faɗin abun da ke nata bakin duba da cewa ta fisu kusanci da kolo ɗin ,”
Kolo mun gode sosai da dukkanin dawainiyar da kika yi mana amma a gaskiya daga ni har yakaka babu wacce zata iya tunkarar cikin garin da nufin neman aiki ba domin kome ba kuwa dan gudun bacewa mu rasa hanyar komawa a matsayin mu na baki ,” jaan numfashi tayi lokaci daƴa tana mai sake marairaicewa , dan Allah kolo ki idasa taimakon da kika yi niyyar yi mana ki yadda mu biki zuwa unguwar da kike yin naki aikin idan ya so sai mu shiga gidajen cikin unguwar mu nemi aikin koh Allah zai sa mu dace ?
STORY CONTINUES BELOW
Ɗan jim kolo tayi cikin nazari a zahiri bata son su yakaka su bita su ga irin aikin da take yi sanin cewa ta boye musu gaskiyar aikin nata , amma ita sosai take tausayawa musu musamman yagana wacce take da wani boyayyen buri akan ta , “
Toh shikenan ku biyo ni amma da sharaɗi ,” kamar yadda kuka ce kun fito neman aiki ne dan haka baku da wani zaɓi akan irin aikin da zaku yi ,”domin unguwar da nake aikina ta sha banban da sauran unguwanni ,” nan ne gaba kaɗan tsallaken titin nan ta karashe zancen tana yi musu nuni da wata hanya da ta gangara kwari ta miƙe sosai daga gaban su ,”
Ke kuma ta juya ga falmata muje ki zauna akan dutsen chan ki ɓuɗe hannun ki ki fara bara , kar ki motsa koh nan da chan zuwa yamma zamu dawo mu same ki ,”,
Cikin rashin kuzari yakaka take taku domin raka falmata wurin zaman ta inda gefen titi ne daf da bakin kwalta kuma ta baya jikin bangon kasuwa ne da yake kewaye da shagunan saide-saide, gefe da gefe duk masu saide-saide ne na kayayyaki iri daban-daban wasu sun yi kashi-kashi akan buhu da algarara wasu a wulbaro wasu akan tire ,wasu kuwa ƴan tebura ne da su ,yayin da gaba kaɗan kuma wani babban gini ne mai kama da ma’aikata ( banki ) ,”
Dai-dai gefen wani ɗan tsoho mai sayar da kayan gwari suka cewa falmata ta zauna kan wani ɗan dutse ,’
Cikin nutsuwar da take halittar ta ta laluba ta ɗosana duwawun ta ,”,
Durkusawa yakaka tayi akan guwowin ta gami da kamo hannunwan falmatan tace ,”
Falmata dan Allah ki kula da kan ki kin ga inda muka ajiye ki ɗin nan ki zauna kar ki motsa koh nan da chan ,
“ɗaga kan ta tayi ta dubi sama taga akwai rangwamen hasken rana sakamakon manyan giza-gizan da suke yawo suna kare ranar ,
” idan kin ji kishirwa ga wannan”,
ta kunce bakin zanen ta ta ciro wata tsohuwar naira goma wacce ita falmata bata san inda ta samu ba ,”
ki sayi ruwa da shi ki sha idan kuma Allah ya sa kin samu sadakha idan kin ji me tallar abun sayarwa ki sayi wani abu ki ci ,
sake damƙe hannun falmatan tayi tana me jinjina hannunwan su da suke haɗe da na juna ,
falmata kar ki je koh ina ki jira ni dan Allah , kuma ki kula min da kan ki ,”
Yakaka ni fa sauri nake da Allah ki taso mu tafi ,”
cewar kolo cikin gundura da doguwar maganar da yakakan take yi da ƙanwar ta ta , wanda ita da yagana ba jin abun da take faɗa suke ba sakamakon ƙasa da muryar ta da tayi ,ga kuma hayaniyar motoci da ta muryoyin jama’ah ,”
Yunƙurawa tayi ta mike tare da cewa ‘” yi hakuri kolo mu tafi ,
idanun ta akan fuskar falmatan wanda a zuwa yanzu ta kasa fahimtar a wanne yanayi zuciyar falmatan ke ciki ,”
Tayi taku biyu ta ji hannun falmatan ya sarƙe a cikin nata ,”
“, Yakaka dan Allah kar ki ɗaɗe kuma ki lura da kyau da wurin da kuka ajiye ni kar ku manta wurin , sannan kuma kema ki kula da kan ki , Allah ya baku sa’a kije ki dawo ina jiran ki anan yakaka ,”
Daga haka ta zame hannun ta daga cikin hannun yakaka ta buɗe zazzaƙar muryar ta tare da ware hannuwan ta biyu ,ta fara rero kalmomin bara ,”
Alaro sadakah fisabilillah
Alaro sadakha fisabilillah
Gurbin fararen idanun ta cike taf da hawayen da suke sheƙi a cikin hasken ranar , zuciyar ta kuwa ta jima tana kwararar da hawayen maraici da wata irin kewa maɗaukakiya ,”10
Juyawa yakaka tayi cikin sassarfa tana mai bin bayan su kolo waɗanda har sun riga sun soma tafiya ,” lokaci guda tana mai share ambaliyar hawayen da suke shatata akan farar fuskar ta , “zuciyar ta kuwa wani irin raɗaɗi da zogi suke yi mata tana jin kamar baza ta iya tafiya ta bar ƙanwar ta anan ba , tana jin kamar idan ta bar ta wani abu zai taɓa ta , ” tana jin kamar ta kasa bata kariyar da ta kamata ,” sai dai sashi guda na zuciyar ta yana mai karfafa ta da cewa ta tafi ai ZATA DAWO TA SAME TA ,’ kuma a yanzu wannan hanyar ce kaɗai mafitar su domin tallafawa kan su .,” da haka suka tsallaka babban titin da ya raba su da sashin kasuwa ,”
Dai-dai zasu gangara gangaren (kwarin) unguwar da zasu neman aikin ta sake waiwayawa a karo na barkatai tana me sake kallon bigiren da ta ajiye ƙanwar ta ta , chan ta hango wata mata ta miƙa mata wani abu da take kyautata zaton sadakha ce aka fara bata ,” nan take fuskar ta ta yalwatu da kyakyawan murmushi har haƙoran ta suna masu bayyana cikin ran ta tana me yin hamdala ,
,”lokaci guda ta sanya kafafun ta tare da tattare zanin ta suna masu sauka cikin kwarin unguwar da ake kiran ta da ,”BULABURIN”, unguwar da tayi ƙaurin suna a birnin na maiduguri gurin tara lalattun mutane , kama tun daga kan ƴan shaye shaye , karuwai da ƴan daba ,” .Fuskar ta ɗauke da murmushin da ya zarce zuwa dariyar da ta bayyana ƴan gajerun jerarrun haƙoran ta ,take shafa tare da sunsuna tarin kuɗaɗen da ta samu ta hanyar barar da ta shafe awanni fiye da uku tana zaune tana yi , wanda bata kai ga sanin yawan adadin kuɗaɗen ba ,”+
Sake runtse kuɗaɗen tayi cikin tafukan hannayen ta ,lokaci guda kuma ta fara lalubar leɗar da ta saya awara taci ɗazu domin ta kulle kuɗaɗen nata a ciki ganin cewa kuɗaɗen sun taru a hannunta ,
zuciyar ta kuwa ƙwal kuma cike da farin ciki a rayuwar ta yau ne karo na farko da ta riƙe kuɗaɗen da suka kai haka yawa nata na kan ta , nan take taji ta sake gamsuwa tare da samun karfin gwaiwar cigaba da yin bara har sai yadda hali yayi , “
Gefe guda kuma tana Allah-Allah su yakaka su dawo ta nuna mata irin ɗinbin alherin da ta samo musu ,”
Soke kuɗin tayi a cikin zanen ta bayan ta ƙulle su a cikin leɗar , ɗan saurarawa tayi tana mai jin yadda rugugin hadari yake bada amo bisa ga dukkan alamu garin gangame yake da hadari ,duba da yadda ta ji rangwamen zafin rana da yake nuni da cewa hadari ya kare ranar ,” ,
Ji tayi hankalin ta yaɗan soma tashi sanin cewa a sararin Allah take ba cikin rumfa ba ,ita kuma bata shiri da dukan ruwan sama mummunan zazzabi da ciwon kai gami da tari yake samar mata ,”
Ɗan matsawa tayi ta gurin da take jin muryar dattijon nan wanda tun da ta zauna a wurin take jin sa yana hada-hadar saye da sayarwar sa ,”
Baba dan Allah ince koh hadari ne sosai haka a garin naji sai cida garin yake ?
Ƙwarai kuwa ƴata hadari ne gashi nan ya shata bakikkirin a sama ,” ya kamata ma kiyi haramar komawa gida ,’domin duk jama’a ma shirin tafiya suke ga la’asar ta riga ta gabato ,”
Tsugudi falmata tayi cikin fargaba tare da taraddadin rashin dawowar su yakaka har yanzu ,”
Tunanin ta ya katse ne lokacin da taji wata mummunar ƙara da tafi karfin a kira ta da rugugin hadari domin gabadaya sai da ta ɗimauce ,”lokaci guda ta miƙe a zabure gami da tsayuwa akan kafafun ta da take jin ƙasa na girgiza ,”
Waige waige ta fara yi lokacin da ta tsinkayo hayaniyar muryoyin mutane sun ƙaru tare da takun kafafun su da alama guje-guje aka fara ,”
Cikin tashin hankali ta sake matsawa wurin dattijon nan da take jin muryar sa sama-sama da alamun tashin hankali ,sai dai rashin jin isashiyar hausa da kuma yadda ta firgice ya sanya ta kasa tsintar koh da kalma guda daga cikin kalmomin da take ji a bakunan al’ummar wajen bare ta fahimta,”
Ba-Baba dan Allah meke faruwa ne ƙarar menene haka naji ?
Ƴata bom ne ya tashi yanzu yanzu a post-office , maza maza ki kama hanyar gida domin kuwa kasuwar ma yanzu za’a rufe ta sojoji zasu zo ,ai yau gari sai yadda hali yayi bom a post-office matattarar mutane ? Kai Allah dai ya kawo mana karshen wannan masifa ,”
STORY CONTINUES BELOW
Kalmar bom da ta sojoji ita kaɗai falmata ta fahimta cikin dogon jawabin da dattijon nan yake mata ,” a take wasu hawayen da bata san lokacin da suka samar da kan su ba suka fara sintiri akan fuskarta ,” dai-dai lokacin da taji an kai mata wata bangazar da tayi sanadiyar zubewar ta a ƙasa da bata raba ɗaya biyu ƙaton da ya bangajeta gudu yake yi domin ya samu isa ga mafakar sa kafin zuwan sojoji koh kuma tashin wani bom ɗin ,”
Ji tayi dattijon nan ya sanya hannu ya ɗago ta lokaci guda yana me fada akan rashin imani na wasu mutanen ta yadda har wannan garjejen ƙaton ya bangaje ƴar ƙanƙanuwar yarinya kuma miskiniya amma bai koh juyo ba ,”
Ƴata ina abokan tafiyar ki da suka ajiye ki anan suke ?? Koh kuma ina ne unguwar ku ? Kiyi maza fa ki samu ki bar wajejen kasuwar nan dan nan da mintoci ƙaɗan kowa zai watse ,”
Yakaka , yakaka , itace kawai kalmar da bakin falmata ya furta ba tare da ta jira jin ƙarshen zancen dattijon nan ba , lokaci guda kuma ta fara jefa kafafun ta ba tare da ta san inda take sanya kai ba koh kuwa inda ta nufa ,” ita dai burin ta ta sadu da yayar ta ,”1
AWANNI UKU BAYA
Tun da suka gangara gangaren unguwar yakaka da yagana suka ware idanun su sosai suna masu kallon tun daga kan tsarin gine-ginen unguwar har zuwa kan mutanen da suke cikin unguwar da mafi akasarin su kallo ɗaya za’a musu a fahimci ƙarancin tarbiyyar da take tare da su ,”
Unguwa ce irin ta yaku-bayi talakawa mafi yawan gine-ginen unguwar sun shiga ƙasa kana iya ganin kan ƙwanukan ,ƙananan gidaje da suke manne da juna ,waɗanda kallo ɗaya za’a musu a fahimci mutanen cikin su na rayuwar rashin wadata,”
Mafi akasarin matasan da suke yawo a unguwar irin ƴan shaye-shayen nan ne masu rabin kai a aske ga kuma uwa uba rangwamen tsafa da ta bayyana sarari a gare su ,
,”duk tashin muryoyin su irin na ƴan maye ne da take tafe da amon kalmar arziki ɗaya ashariya goma ,”1
Yaran su ƙanana kuwa kaso tara cikin goma yawo suke kafafun su babu takalma ,dauɗa ta samu mahallin zama na dindindin a jikin su da suturun su ,”
Ga Ƴan mata birjik waɗanda mafi yawa hannayen su zuwa kawunan su ɗauke yake da robobi zuwa bokitaye da fantekun ,ababen ci na sayarwa ,” sun sha kwalliyar gazal da jar hoda ,laɓɓan su na ƙyallin jan baki 24 awa ,”,
Duk ba wannan yafi girgiza zuciyar yakaka ba asalima ita bata hango wani aibu koh naƙasu a tare da mutanen unguwar ba idan aka ɗauke ashariƴar da suke amfani da ita cikin maganganun su wanda hakan yake bakon abu a wurin ta ,sai dai duk da haka ta ɗauki hakan a matsayin wayewa irin ta ƴan birni duba da cewa ita a wurin ta wayayyun mutane ne .,1
Abun da yafi takura yakaka da firgitata shine yawan karnuka tare da ƙyanwowin da take ganin giftawar su a cikin unguwar tamkar dai yadda akuyoƴi da tumakai suke yawo a garin su wanda hakan babban barazana ne a gare ta kasantuwar ta ma’abociyar tsoron karnai , yakaka tana ƙin kare yadda take ƙin mutuwar ta koma fiye da haka , dan tabbas da tasan zata haɗu da karnuka irin haka da ko daga cikin sansanin su baza ta fito ba bare har ta ɗauko kafa ta shigo wannan unguwar ,”,
Ga bangaren yagana kuwa yanayin tsarin unguwar ne sam bai mata ba a zaton ta zata ga sun doshi unguwar hamshaƙan masu kuɗi ne ,”inda zata yi kallon birni sai take ganin su a wata ƙazamar unguwa wadda koh a garin su ba’a sanya ta cikin unguwannin arziki ba ,’ duk sai ta ji tafiyar ta daina yi mata armashi .,
STORY CONTINUES BELOW
Sun ɗan yi tafiya mai nisa kafin su jiyo Kiɗan da suke ji sama-sama yana sake cika kunnuwan su a yayin da suke dosar wani wajen matattara jama’ah shi yasa suka maida hankulan su suna bin mutanen da suka fara cin karo da su a farfajiyar wajen da kallo ,”
Da farko rumfunan sayar da abinci ne birjik a wurin wanda aka kafa manya-manyan murhu aka ɗora manyan tukwane lamba talatin-arba’in an babbaka wuta a ƙarƙashin su da basa raba ɗaya biyu girki ake ,”
Daga gefe cikin wasu rumfunan kuma shimfiɗun tabarmai ne da suke cike da mutane a chakuɗe maza da mata , ba’a jin kome sai tashin muryoyin su da dararrakin su ,”
Daga gaban su nan ne wata babbar kofa take wanda kuma daga cikin sa wannan kiɗan kalangun ke tasowa ,”
Ɗaya daga cikin rumfunan sayar da abincin nan suka ga kolo ta nufa inda su ma basu yi wata-wata ba suka bi bayan ta zungui-zungui , daga bakin rumfar ta dakatar da su yayin da ita kuma ta shiga ciki inda suke jiyo tashin muryoyin wasu mata ,”
Kichibus kolo tayi da uwarɗakin ta ,wacce kallo guda za’a mata a ajiyeta a mizanin tatattun karuwan mcmc, duba da yanayin shigar ta na wata matsatsiyar doguwar rigar wani yadi da ya cire kowanne bangare na jikin ta kashi-kashi a sarari ,”uwa uba koɗaɗɗiyar fatar jikin ta da duk man sauya kalar fata ya maida ta dabbare-dabbare , sannan zaƙo-zaƙon faratan hannun ta da suka sha fenti ruwan ɗorawa zuwa gashin ɗokin da ta yaɓa a kan ta launin shanshanbale ,wanda bata samu koh da zarafin ɗaura masa ɗankwali ba ,”
Wata harara ta watsawa kolo da mitsi-mitsin idanun ta da suka sha koren fenti daga sama ,” ta tauna cingam ya bada ƙarar bas-bas-tas ,”
Dan ubanki kolo yau sai yanzu kika ga damar zuwa ? Duba agogo karfe nawa yanzu ? Karfe sha biyu saura , toh bari kiji wallahi a kuɗin ki zan cire dan ni ba’a min iskancin banza idan kin gaji da aikin ne sai ki faɗa na maye gurbin ki da mai so ,”
Kiyi hakuri madam wallahi na tsaya taya ƴan uwa na neman wurin aiki ne kin gan su chan ma tare muka zo domin basu samu gurin yin aikin ba ma ,” ta ƙarashe zancen tana mai nuno su yagana waɗanda duk abun da yake faruwa tsakanin kolo da uwarɗakin ta suna ji sarai daga inda suke .
Ɗan leƙawa madam ɗin tayi tayi wa su yakaka wani kallon sama zuwa ƙasa ,”
Ni dai na gaya miki zan cire kuɗin awa biyun da kika yi lattin su domin ni bana asara , ” ki wuce ki kama aikin ki ,” ku kuma “ta sake ɗaga murya yadda su yakaka zasu iya jiyo ta
Sai ku shiga daga ciki domin kun yi sa’a jiya-jiya sally fara ,ta bada cigiyar a ƙaro mata ƴan aiki biyu a madafar ta domin cikin tsoffin da da suke mata aikin ɗaya shekaranjiya ta mutu,”1
STORY CONTINUES BELOW
Turus yagana da yakaka suka yi duk da cewa sun fahimci abun da ta sanar da su toh amma inane cikin ? Kuma wacece” sally fara ” ?
Ganin yadda suka yi wiƙi-wiƙi suna kallon ta ya sa ta fahimci basu gane nufin ta ba ,” ƙas-ƙas ta sake yi da cingam sannan tayi wani turanci “,
Idiyot buladiful marafoka waɗannan ajawos ɗin koh fahimtata ma basa yi ,” ke kolo koh kuma ma ke zauna kiyi aikin ki ɗanliti zo tafi da waɗannan garorin ciki wajen sally fara kace ga ƴan aikin cikin madafa an samu ,” kai ku bishi dallah kun tsaya sai wani kif-kifta idanu kuke yi kamar an shaƙe akuya a mayanka idiyot buladiful5
Sum-sum su yagana suka bi bayan mutumin da aka ƙira da ɗanliti wanda tashin farko idan an hango shi yana tafe za’a zaci wata zarkaɗeɗiyar budurwa ce sakamakon shigar mata da yayi da yadda yake karairaya da lanƙwasa kamar tarwaɗa a cikin ruwa ,”uwa uba kwalliyar da ya rangaɗawa fuskar sa har da yari da ɗan kunne ,”
Suna shiga cikin babban harabar dodon kunnuwan su ya fara tsalle a sakamakon kiɗan gurmi da kalangu da suke tashi ,” a babbar harabar da tafi kama da wata ƙaramar makaranta ,” mata ne da maza waɗanda kallo ɗaya za’a musu asan mutanen banza ne suke ta kai kawo ,”
Wata ƴar hanya ɗanliti ya bulla da su sai ga su sun bullo a gaban wani waje mai kama da shagon cin abinci ga irin fararen kujeru da teburan su nan birjik a wajen ta tsakanin kujerun da duk babu kowa akai suka wuce suka fito wani babban fili wanda suka taras da wasu manyan murhu da Manyan yankakkun durum bisan su wasu mata na koƙarin haɗa wuta ,”
Wani wari da tsami kamar na ruɓaɓɓen abinci shi ya fara dukan hancin su kafin idanun su yayi tozali da wasu yamusassun mata ƙomaɗaɗɗu suna ta faman wanke jiƙaƙiyar ruɓaɓɓiyar dawa suna subda ruwan yana kwarara zuwa wata katuwar magudanar ruwa ,”
Larki , hema ,duduwa ina madam sally take ? Inji danliti ,”
Koh kafin su amsa masa sai ga wata koɗaɗɗiyar mace da take tsakanin shekaru arba’in da biyar zuwa hamsin ta fito daga wani lungu hannun ta riƙe da wani ƙaton luɗayin kunu da ya kai girman a haɗa kawunan yakaka da yagana ,”
Kai liti yaya anka yi ne eh ? Waɗanan ƙuya-ƙuyan kuma daga ina ?1
Daman madam jumai ce tace a kawo miki ƴan aikin ga su nan su biyu an samu ,” ya ƙarashe zancen sa yana farfari da ido tare da yarfe hannu ,”
Ta ƙundumo wata ashariya ta makawa madam jumai ,” kafin ta ce
Waɗannan ƴan shilan ne zasu min aikin ciki ? Waɗannan ne zasu tuƙa min DURUM ƊIN BURKUTU ? Tirƙashi waɗannan ai basu wuce suna bayan uwar su tana tatsa musu nono suna sha ba ?2
STORY CONTINUES BELOW
Wata dariya da ɗaya daga cikin matan da suke aikin wankin dawar nan tayi shi ya katse banbamin masifar da sally fara”, take yi ,”
Kin ji madam sally da wani zance ai da rashin tayi akan bar arha da kuma rashin ƙira karen bebe ya bata , ban da abun ki ai gwada su zaki yi ki ga koh zasu iya ,” bakya ganin kamar ɗaukar irin su ma yafi riba , zaki mori kuruciyar su da kyau kafin abar ta fara aikin ta , zasu daɗe suna yi miki bauta kina juya su sai yadda kika yi da su ? Ai madam kar ki bari wannan damar ta wuce ki ,” ta ƙarashe zancen tana sakin wata sakaryar dariya lokaci guda kuma tana chafe amshin wakar ƙidan kalangun da yake tar-tar kamar a gaban su mai kalangun yake kaɗa gangar sa, “
Ɗan jimm madam sally tayi kafin ta ce toh bari mu gwada ɗin da gwaji jirgin sama ya tashi ,” cikin kallon sheƙeƙe ta juyo ga su yagana waɗanda suka yi jugum suna sauraran maganganun matan da sun yi jikoki da su da mafi yawancin zantukan ma ba fahimta suke ba ,” dan haka sam basu kai ga fahimtar ma’anar kalmar BURKUTU ba ,”
Zan ɗauke ku aiki amma da sharaɗi idan naga baza ku iya ba zan sallame ku ,”
Cikin gurbatacciyar hausar yakaka da zuwa yanzu tafi yagana zaƙuwa da son ganin sun samu aikin yi tace
Mama zamu iya kowanne irin aiki ne ki bamu zamu yi koh yagana ? Ta maida tambaƴar ta ga yagana wacce bata samu zarafin magana ba illah gƴaɗa kanta da tayi alamun sun amince ,”
Meye sunayen ku sannan kuma daga ina kuke ? Ina ne unguwannin ku ? Sannan ina da dokoki na , da farko anan zaku dunga kwana koh kuwa zaku dunga zuwa ne kuna komawa kullum ?
Mu ƴan gudun hijira ne ,
Ni sunana yakaka ,kawata kuma yagana.
Zamu dunga zuwa ne kullum ,
Toh kullum karfe tara zata yi muku anan wurin ,sannan zaku tashi karfe biyar idan masu aikin dare sun zo ,”
Suka amsa da toh ,
Sannan kuma tashi biya kuke so koh biyan karshen wata ?
STORY CONTINUES BELOW
Suka haɗa baki wurin cewa tashi biya ,”
Zan baku abincin rana kaɗai zan kuma baku naira ɗari uku-uku kullum bayan kun gama min aiki ,”
Cikin tsananin murna da jin daɗi yakaka suke yi mata godiya kamar zasu kwanta mata ,” su ai sun gama samun rufin asiri naira ɗari uku-uku a kullum me suka manta ?2
Cikin murmushin ƙeta take kallon su kafin ta ce su zauna a gefe za’a zo a fara gwada musu aiyukan su ,
A gaban idon su matan nan suka haɗa wutar nan suka juye rubabbar dawar nan cikin manyan yankakkun durum ɗin suna yi suna juya ƙwanƙwaso tare da bin kiɗan kalangun nan suna rere waka, tamkar dai ƴan matasan ƴan mata ba tsoffin matan da suka doshi shekaru sittin ba ,
____
Bayan fiye da awanni uku da su yakaka suka ɗauka a wurin aikin su , zuwa lokacin dattijan matan nan larki da hema sun gama gwada musu duk aiyukan da zasu dunga yi kama tun daga kan shara da goge-gogen cikin shagon da ake sayar da tsattsamar giyar burkutun ,
da har kawo yanzu da ake aunawa su yakaka burkutun da zafin ta a cikin dogayen kofunan silver suna miƙawa ga mutanen da suke ta shiga da fita cikin maye da tamɓele , mata da maza , suna kuma karbar kuɗaɗen suna kaiwa duduwa wacce take matsayin mai tara kuɗin cinikin ,
su yakaka basu kai ga fahimtar burkutu giya bace domin basu san ta ba koh sunan ta ma basu taɓa ji ba, abun da suka fahimta kawai shine wannan abun da mutanen suke zuwa saya suke sha ,yana burkita mutanen tare da sanya su shiga wani mawuyacin hali na birkicewar tunani ,” ta yadda zasu ga mutum.tsaf ya shigo wurin cikin nutsuwar sa amma daga zarar ya kurɓe wannan ruwan zazzafar burkutun kafin ya bar wurin zasu ga mutum ya fara surutai da layi wasu ma har da amai da faɗuwa,”2
Wanda su da kan su a duk lokacin da larki ta buɗe murfin durum ɗin domin ɗebo ruwan burkutun , tururin sa da warin sa yana bugar da su ta yadda har suke jin kan su na juyawa ,” koh sau ɗaya basu yi gigin ɗanɗana burkutun sun ji irin ɗanɗanon ta ba hasalima ma ita yakaka koh ruwa bata sha ba abincin ma da madam sally ta saya musu ita nata juye shi tayi a leda ta kulle da niyyar sai sun koma sansanin su suci ita da ƙanwar ta , yagana ce ta cinye nata .,
Hankalin yakaka ya fara tashi ne lokacin da ta fara ganin hadari yana haɗuwa a garin , gashi kuma lokacin tashin su bai yi ba ,”
Zuciyar ta ta cika taf da tunani tare da zullumin halin da falmata take ciki , Allah-Allah take lokacin tashin nasu yayi ta tafi ga ƴar kanwar ta kafin ɓarkewar ruwan saman da ta san barazana ne ga lafiyar falmatan ,”
A karo na barkatai larki ta sake miƙawa yakaka dogayen kofunan da suke cike da barasa mai turiri , tare da umartar ta ta miƙa su ga mutanen da suka bada kuɗaɗen su yanzu , cikin rashin kuzari yakaka ta karbi kofunan tana mai ɗaga kan ta tana sake kallon ɓakin hadarin da ya shata layi a sama yake ta faman rugugi ,”
Dai-dai ta sanya kai cikin shagon taji wata irin ƙarar da ta razana ta sanya ba shiri ta saki kofunan dake hannun ta suka tarwatse ruwan ciki ya watsu a jikin mutane biyun da suke zaune daga farkon shagon akan kujeru suna kurbar ruwan su ,”
Zafin kakkarfan marin da ya sauka akan kumatun ta shi yayi sanadiyyar dawowar ta cikin hankalin ta da ta rasa na ƴan daƙiƙu sakamakon ƙarar tashin bom ɗin ,”
Dan uban ubanki shegiya baki da hankali ne zaki ƙona mu ? Ƴar mahaukaciya ko yau kika fara jin irin ƙarar tashin bom ɗin nan kina maiduguri ? Bace mana anan kafin mu tattataka ki ƴar*
STORY CONTINUES BELOW
Kusan dukkanin rabin mutanen da suke cike cunkus a cikin shagon suka kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya suna nuna ta , ita kuwa sai wuri-wuri da ido take sam zafin marin bai ɗimautata ba kamar kalmar bom da taji mutumin da ya mare tan ya ambata ,” bom aina kuma bom ya tashi ? Falmata ita ce kalmar da ta fara tasowa ta daga ƙarƙashin zuciyar ta ta kuma bayyana kan ta akan laɓɓan ta ,”
Da gaggawa ta sunkuya ta tsince kofunan da suke ƙasan kunnuwan ta sun toshe daga barin jin dararrakin mutanen da suke wajen , ta juya cikin sassarfa ta koma ciki ,”
A tsaye ta taradda yagana wacce itama alamun firgici yana bayyana baro-baro akan fuskar ta ,”basu samu damar magana ba sakamakon wayar da madam sally fara wacce take bullowa daga wani ɗan lungu a tsukin wurin da suke zaton gida ne ta cikin lungun , wayar da take yi ta ɗauki hankalin su ,”
Ni sally naga ta kaina bom a post-office ? Na shiga uku kadda dai yayi mummunar barna ? Tabdi Allah dai ya kwashewa waɗannan mutanen albarka tsinannun banza kana zaman zaman ka su aika da kai barzahu ,” toh yaya zaka shigo ɗin ne ? Ga fa ruwan yana jiran ka kar ya huce ,” ta karasa zancen ta tana sakin shewa tamkar ba ita ta gama bayyana jimami ƴanzu akan fuskar ta ba ,’
Da sauri yakaka ta ƙarasa gaban madam sally ta durƙusa ,” tare da sunkui da kan ta tayi shiru ,” dukkan su idanu suka zuba mata suna sauraron ta , tare da kallon jikin kayan ta da burkutun ya jiƙa ,”
Ganin tayi shiru bata ce kome ba ya sa madam sally fara jaan wani guntun tsaki ,”
Ke ban son iskanci meye zaki wani zo ki tare min hanya kuma ki ƙi cewa kome, idan aikin ne baza ki iya ba ki faɗa min sai na baki iya kuɗin awanni da kika min ki kara gaba
Da sauri yakaka ta ɗago kai jin ana shirin korar ta , cikin karkarwar murya da inda-inda tace ,”
Madam dan Allah ina ne inda naji ana cewa bom ya tashi ? Nan kurkusa ne ?
Kallon banza madam sally ta yi mata , kina nufin baki san post-office ba kina garin nan toh ta ina kuka zo ? Ku da kuka ce kuna camp ? Inda mota ta biyo da ku daga camp zuwa cikin gari ta sauke ku nan ne post-office kusa da kasuwa monday market ,”
Zuruf yakaka ta miƙe tana rarraba ido , da sauri kuma ta sake durƙusawa ,
madam dan Allah ƙanwata falmata , ƙanwata falmata tana bakin kasuwa tana bara , kuma bata san ko’ina ba makauniya ce ,” dan Allah ki taimaka ki min izni naje na zo da ita ,” ta karasa zancen ruwan hawaye yana sulluɓowa akan kududdukin ta ,”
Karo na farko madam sally taji ɗan tausayin yaran ya kama ta ,”
Babu kome kina iya tafiya ƴar uwar ki sai ta ƙarasa aikin tun da bai wuce awa ɗaya da rabi ba masu aikin dare su iso ,ungo kuɗin sallamar ki ,kiyi sauri kije kar a fara rurrufe hanya a hana wucewa ,’
Kallon yagana tayi wacce ta so da madam sally ta bar su sun tafi tare kamar yadda suka zo , sai dai babu yadda zata yi ita ma alfarma aka yi mata domin duka aikin da suka yi bai wuce na awa uku ba ,”
Yagana zan tafi zamu jira ku a tasha .
Yakaka zaki iya gane hanyar fita daga unguwar nan ? Kar ki ɓata fa
Zan iya ganewa yagana sai kun zo !
Daga haka ta matsa ta ɗauki ledar da ta ƙulle abincin ta a ciki , cikin sassarfa ta sanya kafa tana barin wajen ba tare da ta koh tsaya ta wanke wurin da ruwan burkutun nan ya bata mata zani ba ,”burin ta kawai ta iske ƙanwar ta a inda ta bar ta cikin ƙoshin lafiya ,”
Zamiya da zilliya ta dunga yiwa kattin mazan da suka buge tatil da giya a cike da wannan filin da ake kaɗa kalangu ,suna ta rawar banza da fitsara sun kama ƙugun matan banza ,”tamkar dai basu da masaniyar halin tashin hankalin da garin yake ciki ,”
Bata bi ta kan kolo ba kawai ta ɗauki hanyar da suka biyo a yayin tohowar su tana tafe tana jefa kafa tare da share guntayen ƙwallar da suke silalowa lokaci-lokaci daga gurbin idanun ta , zuciyar ta cike taf da fargaba ta ƙagu ta isa wajen falmata ,”
Ji tayi kamar ana ɗan taɓa ledar hannun ta , cikin hanzari ta waiwayo ,”
Shiɗewar wucin gadi tayi lokacin da tayi ido huɗu da wata mayunwaciyar karya baka kirin da ita tana dalalo harshen ta waje , ƙamewa tayi ƙyam tana jan numfashi da ƙyar suka yi kallon kallo na kusan minti guda da bakar karyar nan ,” kafin yakaka ta zabura tare da yankawa da gudu cikin matukar gigita da tsorata ,” karyar nan kuwa bata bata lokaci ba gurin rufa mata baya ita ma a guje tana haushi ,”1
Gudun fanfalaki yakaka take yi tana yi tana waiwayon karyar nan da zuwa yanzu suka zama su biyu ne suke bin ta tare da wani ƙaton kare ,”
Kutsawa take tsakanin layukan unguwar ba tare da tana lura da inda take bi ba , taimako take nema amma abun takaici duk da unguwar cike takd da mutane dattajai da matasa , cikin su babu wanda yayi yunkurin taimakon yakaka , sai ma dariya da ihun da matasan suke bin ta da shi har ta ƙulewa ganin su a guje , yara kuwa suma rufa masu baya suke yi da gudu suna ihu da dariya tare da kiran sunan kanukan suna tafi,”1
Tahowa yake daga cikin siririn layin da baya bullewa , fuskar sa sam babu annuri da alama akwai abun da ke damun zuciyar sa ,”
Tun a nesa ya fara jiyo hayaniyar su kafin ya hango shawo kwanar da tayi a guje tana mai jefa kafar ta cikin dagwalon kwatami bayan ta karnuka biyu su ma a guje kafin ya ga bullowar zugar yaran da ya jiyo ihun su biye da ita,”
Gadan gadan ta nufo shi , yana yunkurin kauce mata , yaji ta taho gabaɗaya ta faɗa cikin kirjin sa tare da zagaye hannuwan ta tsam da jikin sa , dai-dai lokacin da karnukan ke karasowa .!Cikin hanzari ya raba ta da cikin jikin sa ya sauya mata matsaya zuwa bayan sa lokaci guda ya sa kafa ya kaiwa bakin “karyar” duka ,a dai-dai lokacin da tayi nufin kaiwa ledar hannun yakaka wawura ,wanda hakan ya sa yakaka ta sake riƙe bayan rigar sa tamau tana me sake mannewa da jikin sa cikin karkarwa tare da runtse idanun ta ,batare da tayi la’akari da kyau gami da hasken lallausan yadin jikin sa ba ,
Ke dallah Sakar min riga koh bakya gani karnukan sun gudu ne ??
Cikin hanzari yakaka ta buɗe idanun ta da suke runtse tare da sakar mishi riga gami da matsawa daga jikin sa kunnuwanta suna jiye mata kamar ta san muryar sa .1
Ba tare da ya waiwayo ta ba ya cigaba da takun sa da nufin cigaba da tafiya inda ya nufa ,
Bayan sa ta bi da kallo bakin ta na son furta masa kalaman godiyar taimakon da yayi mata ,
idanun ta suka sauka a dai-dai inda ta kama a jikin rigar sa har zuwa ƙasa baki ɗaya ya baci da jar miyar da tasha gumurzu da karnai akan ta ,”
Zaro idanuwan ta tayi lokaci guda ta buɗe ƴar muryar ta ,”
Malam , malam
Ta kira sa
Waiwayowa yayi yana me sake tamke fuskar sa ,
Karaf suka haɗa ido , kallon-kallo suka yi yayin da idanun su suka sarƙe cikin na juna a karo na biyu ,
Kowannen su zuciyar sa ta buga da mabanbanta yanayi.,”1
Yakaka tayi saurin janye ƙwarar idanun ta lokaci guda mabayyanin bacin rai yana samun matsuguni akan ƴar fuskar ta a saboda hoton cin zarafin da yayi musu ita da kanwar ta da ya gifta ta cikin zuciyar ta a take ,”
Haɗiye kalaman godiya da ban hakurin bata masa riga da tayi niyyar yi tayi ,domin a ganin ta wannan mutumin bai dace da samun tattausan kalamai daga gare ta ba .
Cikin sauri ta taho kan ta a sunkuye ta kewaye shi , cikin dakewar zuciya ta sake nufar hanyar da ta billo daga kan ta ba tare da ta sake yadda ta dubi sashin da yake tsaye ba .
Tare da wani irin yanayi da yake ji daga ƙarƙashin zuciyar sa wanda ya kasa tantance wanne iri ne , ya bita da kallo , chan ƙasan zuciyar sa wani ƙaramin sashi yana mararin sake duban cikin ƙwarar idanun ta ,
wanda a zahiri bayan ƙwarar idanun nata da suke da wani irin maganaɗisu a gareshi babu wani abu da zai iya ɗorarwa na daga kammanni koh suffar yarinyar illa ma , ƙyama da haushin ta da yake ji tun a ranar da ya fara yin tozali da ita ,dan haka yanzu ma sashi mafi rinjaye na zuciyar sa danasanin taimakon ta da yayi yake , har ma yake kitsimawa cikin ransa da ace ya san ita ce da ya bar karnukan nan sun chasaa ta yadda ya kamata ,”bagidajiyar wofi ƴar ƙauye ” ya karasa tunanin sa yana mai fidda sautin dogon tsaki ,”mtsww”
Cikin taka tsan-tsan tare da taraddadin sake gamuwar ta da rundunar karnuka take ratsa layukan da nufin komawa kan hanyar ta da ta biyo domin ta samu damar nufar wurin da ta bar falmata ,
sai dai abun da ya firgita ta shine bacewar da tayi ta gagara gane hanyar da ta biyo .
Bulayi ta dunga yi ,ta bulla ta chan ta bullo ta nan gabakidaya kan ta ya juye ta samu makuwa ,
Cikin rishin kuka ta ɗaga kai tana kallon ruwan saman da ya fara sauka da matuƙar karfi , yayin da mutane kowa ya fara neman mafaka .
Share hawayen ta tayi tana me ƙanƙame jikinta saboda dukan da ruwan ya fara yi mata ,
sake mikawa tayi ta nausa inda take tunanin zai sada ta da bakin hanya ,idanun ta koh gani sosai basa yi saboda ruwan hawaye da karfin ruwan saman da yake sauka bisa fuskar ta .
Dai-daita tsayuwar motar sa yayi a gefen hanya saboda karfin ruwan da yayi yawa tare da ƙuncin da ya cika masa zuciya sun haɗu sun hana shi samun damar da zai jaa motar sa ya ƙarasa barin unguwar da yake ƙi fiye da kowanne bigire cikin duniya wanda kuma shigar sa unguwar ya zamar masa dole saboda dalili mai karfi .
STORY CONTINUES BELOW
Baya yayi da kujerar motar bayan ya ƙarawa kan sa karfin na’urar sanyaya waje , ya kwantar da kan sa wanda yake sara masa akai-akai ,
Sake juya kan sa yayi ta ɗayan bangaren da yake kallon layukan cikin unguwar yana kallon yadda kakkarfan ruwan saman yake wanko dauɗa da tarkacen sharar cikin unguwar yana watso su cikin wata ƙatuwar ƙwatami da ta shata a bakin layin ,
Tsumu yayi ya ƙurawa kwatar ido yana tunanin da yake ƙara dagula masa sauran farin cikin sa , har zuwa lokacin da kwatamin ya cika ya tunbatsa ya shafe a ƙasa tare da dai-daituwa da sauran ruwan da ya cika unguwar kasancewar ta a cikin kwari ,
Tun a nesa ya hango ta ita ɗaya tal akan layin tana jaan kafafun ta da suke nutse cikin ruwan dattin da ya kawo har zuwa ƙwaurin ta , ta tukuikuye cikin yagalgalallen hijabin ta sai rawar sanyi take tana karkarwa , karfin iskar da ruwan saman ke tafe da shi suna barazanar yin wurgi da ita ,
Tsaki ya jaa a karo na barkatai a fili ya furta “mahaukaciya” juyar da kan sa yayi zuwa ɗayan bangaren yana me lumshe idanun sa ,”
Chan daga cikin kwakwalwar shi yake jin kamar ana umartar sa ,”
Cikin sauri ya buɗe idanun sa da suka yi jaa a sakamakon runtse su da yayi da kuma sara masa da kan sa yake ,” cikin abun da yake ƙasa da minti guda ya buɗe murfin motar da matuƙar karfi gami da fita a guje ,”
Wani irin sura ta ji anyi mata tare da yin juyi da ita da ya sa leɗar abincin hannun ta ta subce gami da faɗawa cikin ruwan da yake kwaranya da gudu ya wuce da ledar .
A tsorace ta ɗago kan ta bayan da taji an ɗire ta a gefe ,ta watsa matsakaitan idanun ta akan fuskar sa da ruwan sama yake tsare ,
Ke wacce irin daƙiƙiyar mahaukaciyar yarinya ce ne ?
Cikin HARGITSIN nan sai yawo kike , ana ruwan sama ma baza ki samarwa kan ki mafaka ba ? Yanzu ba dan Allah ya sa na lura ba da kin je kin faɗa cikin kwatamin nan kin kashe kan ki a banza mahaukaciya ,” ya karashe zancen yana mai jin kamar ya rufe ta da duka .
Sarai ta fahimci ya zage ta saboda kalmar mahaukaciya da ya danganta ta da ita ,wacce cikin kalaman batanci da yayi amfani da su ita kaɗai ta gane ,’ da hakan ya haɗu da asarar abincin da ta ci uwar wuya akan samun sa , da yanzu take ganin wannan mutumin da bata koh kai ga sanin sunan sa ba a matsayin wanda ya jawo mata asarar abincin yake kuma binta da zagi , bacin ran haka ya hana ta fahimci sauran kalaman sa dake bayyana mata irin hatsarin da ta shiga sai ma zuciyar ta da ta ɗau zafi da yayi sanadiyyar sake ballewar ruwan hawayen ta .
Kewaye shi tayi tana mai sake jin tsanar sa cikin ranta ta sake nufar hanyar ta , bata yi taku biyu ba ta ji an fisgo ta , kafin ta ankara ta ji saukar kakkarfan mari a kumatun ta na dama kafin ta samu daman wartsakewa ta ji an fisgi hannun ta .
Bai sake ta ba sai da ya kawo ta jikin motar sa ya tura ta ta haɗu da jikin motar da karfi , bai bi ta kan ta ba ya zagaye ya buɗe motar ya shiga ya jaa kofar da karfi ya rufe tare da sake mayar da kan sa ya kwantar .
A hankali ya fara jin sanyin da motar ta ɗauka tare da wanda garin ya ɗauka baki ɗaya a sakamakon tsagaituwar ruwan saman da wata sassanyar iska da take kaɗawa suka haɗu suka fara sashi jin matsanancin sanyin da ya sanya shi buɗe idanun sa ya sauke akan bayan ta da take tsaye a inda ya hankaɗa ta koh ƙwakƙwaran motsi bata yi ba ,
Dauke kan sa yayi yana mai jin wani yanayi mai kama da matsanancin tausayi yana neman mamayar sa ,”
Ya yunkura gami da kai hannu ya kashe ac tare da kai hannu ya murɗa ɗan mukullin motar sa ,”
A firgice ta matsa daga jikin motar tayi baya tare da juyowa ta fuskanto motar tana mai sake takurewa saboda azabar sanyin da take ji ,”
Sai dai saɓanin ɗazu yanzu fuskar ta ta ɗan sake daga tsananin bacin ran da take nunawa hakan kuwa baya rasa nasaba da fahimtar da tayi cewa ya taimake ta ne , ya ceto ta daga hatsari a saboda bayan ruwan ya fara tsagaitawa ne babbar kwatamin ta baƴyana , wanda hakan ya sa ta fahimci taimakon da ya sake yi mata a karo na biyu ,
Baya yayi da motar sa ya karya kan motar ya hau titi sosai , sai a lokacin ya kallo in da take suka haɗa ido ,”
Da sauri kowannen su ya ɗauke kan sa ya jaa motar da matukar karfi wanda hakan ya sa ruwan da ke kwance kan titin ya sake fallatsuwa mata a jikin ta ,.
Tsayuwa ta cigaba da yi tana mai fuskantar titin tare da jin wani sabon tashin hankalin rashin ganin alamun mutane a bakin titin da zuwa yanzu ta fahimci ta nan suka shigo unguwar sai dai lokacin da suka zo wurin cike yake ta ko’ina da jama’a tare da rumfunan saye da sayarwar su na wucin gadi ,
yanzu kuwa babu jama’ar babu rumfunan su hakan ya sa baza ma ta iya tantance dai-dai wurin da suka bar falmatan ba
Da gudu ta tsallaka titin tayi diri-diri cikin rashin sanin takamaimai bangaren da zata nufa hagu koh dama , da sauri ta fara bin bangarenta na dama wanda ta nan suka bar falmatan sai da ta dangana har karshe ta je ta tarar da roundabout “shataletale” bata ga koh alamun falmatan ba , kai mutane ma tsilla tsilla take cin karo da su suma kuma duk hanya ɗaya suke bi , sai kuma tsirarun motocin da suke wucewa da gudu suna watsa mata ruwan kan titin ,
Dawowa da baya ta sake yi da nufin nufar bangaren hagu sai dai wannan karon ta sauya salon neman ,domin dagewa tayi tana buɗe murya tana kwalla kiran sunan falmata ,bata damu da kallon da tsirarun mutanen da take yin taho mugama da su suke yi mata ba , burin ta koh ita bata ga falmata ba falmatan ta ji muryar ta ta amsa mata ,”