MAFARIN SO CHAPTER 8 KARSHE

MAFARIN SO CHAPTER 8 KARSHE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washe garin ranar su Aunty Deejah suka dawo, su Rabi’ah na zaune falo, faɗa suke akan ita sai ya barta taje gidansu Amrah da Zahra, shi kuma yace sai dai ta bari ya kaita da Yamma, tun yana lallaɓata har ya koma musu faɗa, da yake mai hali bai fasawa🤣. Tana niyyar jifanshi da filon kujeta, ya kamota ya kwantar a jikinsa duk sai tayi lak’was.

     Sallamar su Hayrah ne ta katsesu, da sauri ta zame jikinta daga nashi, duk suka tsaya suna kallon Rabi’ah kaman sabon abu, don basuyi zaton tazo gidan ba,

     Hannu ta ware musu alaman su taho,

     “what are uh waiting for? Come here”

   Ai da gudu suka taho rungumeta, duk suka mak’aleta suna murna, Ahmad ya rungume hannuwansa yana kallonsu,

     “Aunty kaɗai kuka sani ko?”

    Suka saketa, shima suka rungumeshi suna musu sannu da zuwa, sai ga su Aunty Deejah sun shigo, itama tasha mamakin ganinsu Rabi’ah, duk ta taga gidan a buɗe.+

Yayanta ya shigo, shima tsayawa yayi yana kallonta, daga fuskarshi zaka iya gane tsantsar farin cikin daya shiga na ganinta, yana son mata magana anma ya kasa, ya wuce su kawai,

        “Sannu da dawowa Yayana”

      “Yauwah” ya faɗa ba yabo ba fallasa, ba tare daya tsaya ba.

    Su Aunty Deejah daman haka akeso, da mamakin Rabi’ah sai taga ta sakar mata fuska.

       “Amaren Yola saukar yaushe?”

   Itama ta ɗan saki fuskarta,

       “kusan sati ɗaya kenan, munzo bamu iske ku ba”

      “bak’i sunma zama en gida ashe”

    “eeh fa, bamusan da dawowarku yau ba, ku huta Aunty bara na shiga kitchen don yanzu kune bak’in”

   Ta sakar mata murmushi, sannan itama tabi bayan Yayan Rabi’ah, su Hairah kam na mak’ale da Ahmad sunata zuba mishi fira.

     Sai da yaga Rabi’ah ta nufi kitchen sannan ya bita don ya taimaka mata.

Tare sukayi girkin da Ahmad cikin annashuwa kaman basu ba, da yake duk a gajiye suke saita kaima kowa ɗakinshi, daman ta saba sanda take gidan ita take kaima Yayanta, tare suka tafi da Ahmad ya tayata ɗaukan wasu kayan.

    Yana kwance kanshi na kallon silin, faran-faran ya amsa gaisuwar Ahmad da sannu da zuwan da yake mishi, har suka ɗan taɓa fira, anma ita sannu da zuwan data mishi dak’yar ma ya ansa.

     Tun tana daurewa, batasan sanda kuka ya k’wace mata ba, da duk’e anan wurin ta fasa mishi kuka, ganin hakan Ahmad ya fita ya basu wuri.

       “don Allah Yayana kayi hak’uri, ka yafemun zan iya jurar komai anma banda fushinka, kai kaɗaine gatana, don Allah ka yafemun, na anshi duk wani hukunci da kamun, a shirye nake dana k’ara ɗaukar wani indai zaka yafemun”

   Tayi shiru tana ci gaba da shasshek’ar kuka, yayi matuk’ar tausaya mata, tohm meye ma zaisa yaci gaba da fushi da ita? Shi kansa yasan ta azabtu hakanan.

     Dafa kafaɗarta yayi, ta ɗago fuskarta duk ta ɓaci da hawaye, yasa hannu yana goge mata hawayen,

     “Ya isa hakanan, waye ya faɗa miki ina fushi dake? Kawai na kasa mantawa da abunda kikayine, anma ya wuce kinji? Fatan bazaki k’ara aikatawa ba”

    Ɗaga mishi kai tayi tana  jin bak’in cikin da har yanzu Yayanta ya kasa gane gaskia, anma tunda dai ya daina fushi da ita saita samu kwanciyar hankali.

Ranar bata samu zuwa gidansu Amrah da Zahra ba, sai washe gari da Yamma suka shirya ita da Ahmad zasuje, harda su Hayran en rakiya.

      Bayan sun dawo daga gidajen nasu, sai da sukasha yawo sosai har bayan isha’i sannan suka nufi gida da nik’i-nik’in siyayyar da sukayi,

        Sunzo wuce hanyar da babu mutane sosai, can gefen titin Rabi’ah na ɗaga idonta ta hango wasu mata da miji, irin tsaffinnan tsugunne gefen titi mijin na zaune saman Wheel Chair, matar na gefe tayi tagumi,

    Hakanan Rabi’ah taji tayi matuk’ar tausayawa mutanennan, har sun kusa wucewa da motan tace ma Ahmad ya tsayar da motan, ba musu ya tsaya.

     Ta buɗe jikkarta, bata da canji, sai ta zaro dubu ɗaya ta mik’awa matar, tana ganin dubu ɗaya ne ta fara kwarara musu godia harda hawayenta, tausayinsu sosai ya k’ara shigar Rabi’ah, duk da cikin dare ne, sai takejin muryar kaman wacce ta taɓa ji, hakan yasa ta ɗago da fuskarta tana kallon matar, kallon sani take mata anma ta manta inda ta santa,

     Sai da suka wuce take cema Ahmad ita fa gani take kaman tasan mutanen can, ya nisa sannan yace,

      “nima fa abunda ke raina kenan, gani nake kaman nasan mijin nata”

    Har suna haɗa baki,

“anya ba mutanen nan bane da suka taimakemu?”

     Rabi’ah ta ɗaga mishi kai,

   “tabbas sune kuwa”

Nan take Ahmad ya juyar da motarshi, suna niyyar barin wurin sai gasu sun dawo, matar tayi sororo tana kallonsu, tare suka fita daga motan har zuwa wurin mutanen.

     Rabi’ah tace

  “Baba kun ganemu kuwa?”

   Tsohuwarnan ta ɗaga kai tana kallonsu Rabi’ah, tun kafin tayi magana, Ahmad ya rigata,

      “mune waɗannan mutanen da kuka taimaka mawa da wurin kwana cikin dare”

   Nan da nan fuskar tsohuwa ya sake kawo hawaye,

       “Allah sarki yarannan, tabbas na ganeku kuwa, ashe Allah zai k’ara kawo haɗuwarmu”

    “Baaba anma meya samu kawu ne? Kuma meya saka kuka baro daji kuka shigo gari?”

    Baba ta fashe da kuka, tama kasa basu amsa, Rabi’ah tace,

      “shikenan Baba, yanzu akwai inda zaku kwana?”

   Ta girgiza kai,

  “muje gidanmu,”

Tsohuwa zata mata gardama, bata saurareta ba, suka taimaka mata aka shigar da mijin a mota, sannan suka wuce  gidan.

Aunty Deejah na ganinsu ta saki baki,

      “mezan gani haka Rabi’ah? Kwashe-kwashe kuma kika koma yi mana?”

     “ba kwashe-kwashe bane Aunty, wannan mutanen suna buk’atar taimako”

    “taimako? Duk taimakon da suke buk’ata ai baya wuce na kuɗi, me zaisa ki kawo mana su nan?”

    “Yaya yana gidan?”

   “oho! Bakiji ina tambayarki? Meye dalilin da zaki kwaso mana mutanen da basu sani ba, waya sani ma ko masu cutar da mutane ne?”

       Kalaman Aunty Deejah sun ɓata mata rai, ita duk tunaninta ta saduda ne ganin zaman da sukayi daga jiya zuwa yau, kaman itama ta fara faɗa, sai dai ta taushi zuciyarta,

     “saboda muma sun taimaka mana da wurin kwana ba tare da sanin komu su waye ba”

     “koma su waye ki fitar mun dasu yanzunnan, nan gidana ne ba gidanki ba,”

     “gidan ki dai ko gidan Yayana?”

   Dai dai lokacin Yayanta na shigowa, yace,

       “ya isa haka? Su waye za’a fitar dasu?”

   Deejah ta nuna su da yatsa,

    “wannan kwashe-kwashen da tayo mana”

        “in banda abunki, wannan tsaffin ina zasu nufa cikin darennan?”

   Hakan yasa ta k’ara harzuk’a ko magana ta kasa yi, ya kalli Rabi’ah.

        “ina kikasan wannan mutanen?”

    “Yaya sune mutanen da suka taimaka mana da wurin kwana ni da Ahmad, ranar da muka dawo daga Kano motarmu ta tsaya”

    Ya gyaɗa kai,

        “dole ki taimaka musu mana, tunda sun taimaka miki wurin zubar da mutuncinki” inji Deejah

     Zuciyar Yayanta na tafasa, hannunshi a dunk’ule kaman yakai mata duka yakeji,

          “zubar da miji dai? Daman ba ma’aurata bane?” Baba ta tambaya.

     “a ranar dai ba ma’aurata bane”

    “tabbas nayi tunanin hakan, domin kuwa duk da ɗaki ɗaya muka basu, basu kwana wuri ɗaya ba, shi mijin nata ma, Awwh saurayinta kwana yayi Sallah, domin kuwa nida mijina ma raba daren mukai bamuyi barci ba, kuma tunda asuba ya tafi bai dawo ba sai da gari yayi haske sosai”

     Yayan Rabi’ah ya kalleta jikinshi duk yayi sanyi,

     “da gaske kike wannan maganar?”

    “na rantse harda Allah abunda na faɗa maka gaskia ne”

     Duk sai yaji baiji daɗi ba daya saka tsohuwa rantsuwa, idanunshi jajir yake kallon Rabi’ah da Ahmad,

      “kunsan hakan me yasa baku faɗamun tun farko ba?”

    Rabi’ah ma cikin sanyin jikin tace,

     “we tried Yaya, but uh were not ready to believe us”

     Sai yayi shiru kawai yana k’walla,

     “ki yafemun Rabi’ah, na zargeki ba akan hakk’nki ba”

   Aunty Deejah cikin tsawa tace,

      “mezan gani haka? Don ta maida kai sakarai, taje ta kwaso wasu mak’aryatan tsaffi shine har zaka yarda da ita?”

    Wani irin wawan mari ya sakar mata cikin zafin rai,

    Ta dafe kunci cikin firgici da tsananin mamaki, don ɓata taba tunanin zai iya ɗaga hannunshi a kanta ba,

       “sai yaushe ne zaki tarbiyya? Ni kike kira da sakarai? Kuma ki dubi waɗannan bayin Allahn da sunyi jika dake ki kirasu da mak’aryata?”

    Fuuu ta wuce ta barsu, yayi ma Rabi’ah umarni data basu wurin kwana kafin da safe, hakan kuwa akayi, takaisu inda zasu kwanta, yau ranta wasai tsabar farin cikin wanketa dasu Baba sukayi daga zargin da yayanta ke mata.

Tambaya ɗaya ta rage cikin ranshi, cikin daren ya fita yana tambayar mai gadi akan yawace-yawacen da Aunty Deejah tace Rabi’ah nayi, shima cikin mamaki ya bashi amsa,

     “ai gaskia Hajia tana daɗewa bata fita ba, kuma koda ta fita bata kai dare take dawowa, sannan kuma duk inda zataje tare dasu Hayrah suke tafiya”

    Ya sauke ajiyar zuciyah kawai, yana tausayawa Rabi’ah kan zarginta da yayita yi, da kuma hukuncin daya yanke mata cikin fushi.

     Shima Ahmad yana daga nesa yake jiyoshi da maigadin, take yaji nadama da haushin kanshi sun kamashi, daya tuna har gori ya taɓa yima Rabi’ah kan hakan.

Kowannensu da kunyar Rabi’ah ya kwana, washe gari bayansu Baba sunyi break fast sun ɗan huta, Ahmad yake tambayarsu dalilin ciwon k’afarshi,

      “wani lokaci ne, na fita wurin fataucina, cikin tsautsayi ina bin wata dabba da gudu na faɗi, tun lokacin nake fama da ciwon k’afa, munje asibitu duk en kuɗin da muke dasu sun k’are wurin siyan magani, sannan ance dole sai anmun aiki k’afar zata dawo dai-dai, kuma kuɗine masu yawa, ganin bamu dasu shiyasa na hak’ura da ciwon kawai, sai lokacin da muka rasa abinci muke fitowa nema cikin garuruwa, tunda bamu da k’arfin da zamu nema da kanmu”

      Su duka sun tausaya musu, Yayan Rabi’ah da Ahmad kowanne yafi so shine zai taimaka musu, dak’yar dai ya yarda akan Ahmad ɗin ya ɗauki nauyi, daman da takardun gwaje-gwajen da aka mishi, asibitin k’ashi dake jihar katsina sukaje dashi, da yake akwai ma’aitaka sosai ga kuma kuɗin, sai shirin aiki kawai.A gigice Rabi’ah ta shiga gidan kaman wacce aka jefa, Aunty Deejah rik’e da kaya zata kai kitchen, sai dai taji Rabi’ah taa fad’a mata tana kuka.

        “Na shiga Uku nah Auntie, sun tafi dashi” ta k’ara fashewa da kuka.

       “subhanallahi waye suka tafi dashi?”

    “shi d’in Auntie, wasu gardawan k’atti ne suka tare mu, sukai tafiyarsu dashi, nidai na shiga Ukunah”

     “kinga ki nutsu kimun magana, bara in kira Yayan naki”

   Dai dai lokacin yana fitowa,

     “lafiya dai nake jiyo wata murya kamar ta Rabi’ah?”

    Cikin muryar kuka tace,

“nice Yaya”

    “Kuda kuka tafi yanzu ba dad’ewa meya dawo dake?”

     Cikin kuka take fad’a mishi duk abunda ya faru.

Ahmad dake dad’d’aure, idanunshi jajir saboda tashin hankali, yana k’arewa kattin da suka tsareshi kallo, sai ga ogansu ya shigo fuskarshi rufe da mask, tsayayyen namiji mai ji da kansa, kallo d’aya zaka mishi ka gane hutun da yake ciki, fari ne tass a jiki da kuma inda yake iya gani na fuskarshi, ga wani irin k’amshi dake tashi a jikinshi,

      Suna ganin shigowarshi duk suka k’ara nutsuwa, ya zauna saman kujera, ya d’aura k’afa d’aya saman d’aya yana fuskantar Ahmad dake gurfane a wajen.

     (kar in barku da tunanin ko waye wannan saurayi? A tak’aice dai ina fatan baku manta da ABDALLAH ba, tun farkon page na MAFARIN SO, d’an govenor d’innan, wanda ma suka manta saisu k’ara duba shafin farko na MAFARIN SO)

     Abdallah ya saka hannu ya d’ago da fuskar Ahmad,

        “Barka dai Aboki”

Ya fizge fuskarshi yana huci,

     “Abokinka na ina?”

   “Abokin takaranah mana, akan neman soyayyar Rabi’ah, koda yake kai bakasha wahala ba, inanan ina neman hanyar da zan samu Rabi’ah, sai gashi daga zuwa kaa aureta kawai cikin sauk’i”

    Ya sauke ajiyar zuciyah, sannan ya koma ya jingina da kujerar yana kad’a k’afa,

        “ina gaf da fara gudanar da shirina, sai dai naji labarin harka auren masoyiyah ka tafi da ita, tun daga lokacin nake tunanin hanyar dazan sameka, shekara d’aya kenan sai yau Allah ya had’amu”

      “Rabi’ah ba matarka bace, kuma bata cancanci zama masoyiyarka ba, dalili kenan da Allah ya kawoni harna samu nasarar aurenta, me zatayi da mugu d’an fashi irinka?”

     Abdallah ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya, sai da yayi mai isarshi sannan yaci gaba da magana,

      “ni ba d’an fashi bane, tun kafin kaga komai har ka gane cewa mugu ne ni? Share kawai kana b’atamun lokaci, takardar Rabi’ah kawai zaka rubuta ka bani”

     “bazan tab’a rubuta ma Rabi’ah saki ba, har k’arshen rayuwatah”

        “wata k’ila k’arshen rayuwar taka yazo kam, kaga takaba kawai zata gama muyi auren mu”

   Ahmad ya k’ara tsurewa cikin tashin hankali.

** ** 

“Yayanah ka taimakeni, karsu cutarmun da Ahmad,  ka taimakeni su dawomun da Ahmad d’ina”

       “ki kwantar da hankalinki, zanyi duk abunda zan iya don ganin Ahmad ya fito, da k’arfina, da ikona, koda kuwa duk dukiyatah zata k’are insha Allah na miki alk’awarin mijinki bazai kwana a wurinsu ba”

    Hankalinta ya d’an kwanta, taci gaba da kwarara mishi godia, tana jin dad’in wannan soyayya da Yayanta ke mata.

      Nan yaci gaba da kiran jami’an tsaro, sannan ya tura musu numbern Ahmad domin trackn, duk ya kasa zama, ya kasa tsayuwa burinshi kawai yaga Ahmad ya dawo, hankalin Rabi’ah ya kwanta.

      Yamma sosai suka kirashi kan lallai sunyi trackn sun gano inda Ahmad yake.

** **

Ahmad yayi gyaran murya, zufa na tsattafowa a jikinshi, cikin karyar da murya yake kallon Abdallah ta cikin mask

      “Rabi’ah bata sonka, kuma na tabbatar bazata tab’a sonka ba, idan kana son mutum, da kulawa da kyautatawa kake jawo hankalinshi gareka, bawai ta tilasci ba, ka guji soyayyar da zaka amsa ta k’arfi, don bazata tab’a maka tasiri ba, idan har da gaske kakeson Rabi’ah, mezai sa ka rabata da masoyinta? Mezai sa ka rabata da farin cikinta? Idan har da gaske kana son mutum, bai kamata ka barshi cikin damuwa ba, ballantana har damuwar ta zama ta dalilinka ne? Ni banma yarda kana son Rabi’ah ba, tunda gashi yanzu kananan cikin farin cikin bayan ita kuma na tabbata ko a ina take tana cikin tashin hankali, ka taimaka ka k’yaleni da matatah idan har kana son farin cikin Rabi’ah”

      “niko nake son Rabi’ah, shiyasa ma zan aureta don in bata farin ciki”

       “kana da tabbacin zata samu farin ciki a tare dakai? Kana da tabbacin Rabi’ah zata so ka idan har ta gane kai ne ka kashe mata miji? Idan Allah ya rufa maka asiri a duniya, kana tsammanin zaka tsallake a ranar alk’iyamah? Ka rok’i Allah ya cire maka son Rabi’ah, sannan ya mayar maka da wacce ta fita zama alkhairi a wurinka, baka yi kama da mai kisan kai ba, karka bari zuciyarka ta rud’eka”

    Abdallah ya sauke ajiyar zuciyah, duk jikinshi yayi sanyi yana sauraren maganganun Ahmad, zuciyarshi tuni ta kare.

         “Na gode Ahmad, tabbas babu wanda ya cancanci zama da Rabi’ah bayan kai, hak’ik’a tayi dace da samun miji na gari, ni daman ba wai sonta ne yasa nake son aurenta ba, kawai inason d’aukar fansa ne a kanta, na gode sosai da wannan tunatarwa da kamun, Allah ya baka ikon kulawa da Rabi’ah”

      “Ameen Ya Allah”

  Cire mask d’in fuskarshi yayi, don a halin yanzu ya yarda da Ahmad sosai da sosai, kuma yaa janye k’udirinshi na cutar dashi

** **

Tare da Yayan Rabi’ah suka je, da police ana bin duk hanyar da wayar take lungu da sak’o cikin k’ungurmin jeji, har suka zo inda aka yasar da wayar anma babu Ahmad, sai dai sunyi sa’ar ganin sawayensu, don haka suka ci gaba da bi cikin sand’a, har sukazo d’an kogon da aka shigar da Ahmad, police suka zagaye wurin ta ko ina, sannan wasu suka shiga.

     Basu tarar da kowa ciki ba, sai Ahmad da suka gani duk an daddaureshi, da sauri suka kunceshi, sun duba ko ina cikin jejin anma babu su Abdallah ba alamunsu.

Sai da aka fara zuwa da Ahmad station, duk yanda suka so yace shi fa baisan kosu waye suka saceshi ba, bazai iya gane fuskar kowa a cikinsu ba, don dama yayi niyyar rufa ma Abdallah asiri saboda shiryuwar da yayi, suka gama bincikensu sannan suka wuce gida tare da Yayan Rabi’ah.

    

Suna shiga Rabi’ah ta rugo da gudu ta rungumeshi, cikin farin ciki tama manta da Yayanta a wurin.

        “Meyasa suka d’aukemun kai? Basu san yanda rashinka ke illata dukkan gab’obin jikina ba? Basu san halin da suka saka zuciyatah ba? Don Allah kamin alqawari, kamin alqawarin bazaka k’ara tafiya ka barni ba, donni ko mutuwa nafison ta d’aukemu a tare”

    D’ago da fuskarta yayi, duk ta ruk’unk’umeshi kaman lokacin ne za’a tafi dashi,

     “ina tare dake Rabi’ah, Ina sonki da yawa, don Allah ki zauna dani, ki kasance dani kullum muna fad’anmu mai dad’i, ki zauna dani koda kullum zamu ringa fad’a, ina sonki da yawa Rabi’ah”

        Murmushi tayi ta rufe idanunta kawai, ya jawo matarshi ya k’ara rungumewa, su Aunty Deejah sai dai kawai suka shige suka barsu, ganin yanda suketa sakasu jin kunya.

     Bayan kwana biyu sun k’ara hutawa, suka shirya suka koma Yola, a unguwarsu Ahmad suka koma da zama, kusa da danginshi, kowa sai nunawa Rabi’ah soyayya yake.

   Zama Rabi’ah da Ahmad, zama ne na soyayya, da amana, kulawa, da kuma kyautatawa, zama ne na masoyan da suka fahimci juna, don daman tun fari sun fahimci juna, sunsan abunda junansu keso, da abunda ke saurin b’ata musu rai, kowa na taka tsantsan wurin kyautatawa d’an uwanshi.

Alhamdulillah

Yau dai cikin ikon ubangiji na samu kammala littafin mafarin so lafiya, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mini.

MAFARIN SO/MATAR AHMAD

Dukanshi littafin nan sadaukarwa ne ga masoyan dake son junansu tsakani da Allah, wanda suke kula da junansu, suka tsarkake soyayyarsu har zuwa ga aure, Allah ka barmu da masoyanmu na gaske, masu son mu saboda kai, Ameen Ya Allah

R bata nufin komai, ba tare da AZ ba, RAZ, da kune rayuwatah ta kammalu, Ina sonku da Yawa Princess Amrah na, da My Zahra BB, Allahu ya barni daku, cikin aminci da yardarsa, kud’in aminai ne na k’warai

Gaisuwa ga Dukkan en k’ungiyatah mai albarka, abun alfahrinah, daku nake tak’ama ako ina

  NAGARTA WRITERS ASSOCIATION Allah ya k’ara daukakata, ya k’ara mana zumunci da son junanmu Ameen.

Godia mai yawa masoyanah a duk inda kuke na gode sosai da yanda kukaci gaba da hak’uri dani kuna bibiyar wannan littafi nawa, Rabi’ah sk msh na k’aunarku, ku saurareni kad’an Littafin MEYE SANADI? na hanya insha Allah, labari ne akan soyayya, da kuma illar kusanci, tare da rashin bin umarnin iyaye, bari dai in barku haka, don ance gani ya kori ji.

Rabiatu sk msh

Alhmdlh gashinan dai na cika alqawari na samo muku qarashen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *