MAFARKINSA NAKE CHAPTER B
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
🍁🍁
🍁
Wai ni yau celebration din menene ake agidan da ban sani ba,dariya husna da elham sukayi sannan elham tace momy suprise neh ai,lallai kam mu dai yau zamuci dadi manya na aiki a kitchen,dariya husna tayi sannan tace momy karfa ki zama acici fa. Gidanku nine acici koh cewar momy,murmuahi husna tayi tare da kama kunnenta girgiza kai momy tayi sannan ta fita daga kicin din.+
I think muyi celebration din a garden koh ya noor, eh zai mafi tunda mun gama yanxu muje mu shirya garden din sai muzo muyi wanka
Wow wannan aikinku neh haka cewar bobby daya karaso garden din yanxu,da haka kawai akace kuyi shi zakuce wai ku matane baza ku iya aikin karfi ba,kallonsa elham tayi sannan tace ya bobby kenan,toh ai ba mu muka kawo chairs da table din ba,Ado driver da yaya jibx neh suka taimaka mana,mu kawai decor mukayi,yanxu wanka zamuyi kawai sai muyi setting table,kaga yanxu 3:30 nasan su ya ammar da sis batool zasu iso after asr,so go and get dress muma zamu wuce yanxu.
Baby why are you silent,uhmmmm am just so overwhelmed as in yau zan ganta wow it a dream come true wallahi,murmushi sukayi dukkansu sannan suka jera suka shiga cikin gida,wuce part dinsu bobby yayi su ma wuce wa sukayi sukayi wanka sannan suka dauro alwala.
husna mu sa atamfa ko material,mu sa atamfa riga da skirt koh,okay musa wannan peach n lemon green din da mukayi ankon bikin deeja koh,atamfar nayi miki kyau kuwa sosai cewar husna,ai kema yana miki kyau sai sa nace musa,dinkin ya zau mana jiki daidai. Ni ban son makeup fah,simple kawai zaki min nasan halinki fa husna,dariya husna tayi mai sauti sannan tace don’t worry ai nasan ba biki zamu ba.
Makeup tayi musu light wan sannan suka saka kayansu,dakin ya noor suka wuce itama ta shirya tayi kyau da simple makeup dinta,suna kokarin fita sai kuma batool ta shigo,sis suka yi screaming tare da hugging dinta,wallahi batool baki da mutunci kina naija a abuja ma amma baki zuwa gidan nan ko,ni dai naga momy ba sirikarki bace balle kice ita kike kunya,atoh nima dai na gani ni da surukatace bana kunyarta ai,dariya elham tayi tace ai ke kin mayar da momy kakarki kam,dariya noor tayi tace sosai mah,abeg ya isa haka haba cewar batool,kunbi kun shake min wuya kamar kun kama criminal haba,dariya suka yi dukkansu don hausarta kawai abin dariya neh,tsaki tayi sannan tace whatever. Husna tace muje dai, tare da ya ammar kuke neh,eh yana tare da bobby amma sun fita wai zasu amso ice cream a coldstone,sannan su sis fareeda sun iso fah,elham tace wallahi cintia haushi take ban yarinya sai shegen iyayi,dariya ya noor tayi sannan tace amma elham ki cika yar rainin hankali wannan matar kike ce ma yarinya,tafa kai shekara kusan 26yrs fah,toh ya noor ai ba haifata tayi ba,ranan fa flirting ta rinkayi da ya musty,ji nayi kamar na shake ta,gwanda ta daina haukarta don munyi ma ya musty mata sef,waye kenan cewar husna,sis fareeda mana ke baki ga kallon da take mai bane,lol wallahi kuwa nima nagani sannan shima kaman fah yana sonta don naga suna shiri sosai fa,atoh gwanda dai ya fito da mata muyi mai aure kowa ma ya huta cewar momy da ta samesu suna gulmar mutane,dariya sukayi sannan sukace kai momy,batool ta gaishe da momy tare da cewa kai momy kinyi kyau yau fah,wai what the occasion neh,ai kema baki sani ba,kodai sayarda mu za ayi bamu sani ba,dariya batool tayi sannan tace kambu ai basu isa ba kam.Dariya suka yi dukkansu sannan suka fita suka karasa palour.
Bayan su gaisa da yan matan rahmer eatry suka musu iso zuwa wajan event din wato garden,bayan kowa sun zauna,su ya ammar ma sun iso da ice cream din sun zauna .
Husna da elham suka tashi suna gyara table din da aka ajiye small chops din da other eatries din,wayarta neh yayi ringing ta dago kai ta kalleta elham tayi murmushi sannan tayi picking,okay kawai tace sannan tace ina zuwa ta kashe wayar. Kallon mutanen wajan tayi sannan tace kunsan muna da special guest of hounor so sun iso yanxu zanje na tarbo su,murmushi bobby yayi yace shima zaije, au wai kaima kasan waye ne kenan cewar momy,murmushi yayi sannan ya girgiza kai kafin suka wuce shi da husna.
Ya umma it really you,husna ta fada sannan ta rungume ya umma tana hawayen farin ciki haka ita mah ya umma,murmushi bobby yake shi kuma, side hug yayi ma ya umma sannan yace welcome back ya umma,we missed you terribly,murmushi tayi sannan tace you cant imagine how i missed all of you.Murmushi suka yi sannan tace meet junainah and mukhtar my siblings,nainah ga husnata da bobby,murmushi tayi sannan tace heard alot about you guyx yesterday.Haka suka rinka magana har suka kai idan zasu sha kwanar garden din,husna tace okay ya umma wait here first idan nace ki shigo sai kizo,murmushi tayi sannan tace okay mah,dariya sukayi dukkansu amma mara sauti. Husna da bobby suka karasa garden din su momy sai duba bayansu suke don suga ko akwai wanda ke binsu abaya amma babu kowa,husna tayi murmushi sannan tace momy cool down,mugun kallo momy tayi ma husna sannan tace gidanku ne cool down din,yara sun bi sun raina ni sun mayar dani kakarsu,dariya noor tayi sannan tace momy dan Allah kiyi hakuri ki daina fadar haka,nima na kosa naga our guest of honour fah,amma idan kin tsaya kina fada ai zamu ta zama cikin suspense kenan, oh ni deeje yaran zamani,dariya sukayi sannan suka zagayo suka rungume momy,murmushi tayi sannan tace ni ku cikani kar ku karasani tun kan naga jikokina.Dariya suka kuma yi sannan suka koma suka zauna.Husna ta tashi d second tym tace yauwa momy ya ammar kune kawai anan ba ku san waye guest of hounor dinmu na yau ba,literary kusanta but baku san cewa itace ba, fareeda mah tace ai muma we have no idea ba,i know but literary you dont know her at all,i present to you our guest of hounor.
Tana gama fadar haka junainah da mukhtar su bullo sannan ita umma abayansu,saboda haka babu wanda ya lura itace,sai da suka kusa isowa ya ammar ya hangota,tashi yayi agigice sannan ya kara kusa da ita da sauri yana kiran sunanta,murmushi tayi mai tana hawaye,rungume ta yayi yana cewa i cant believe kina nan da rai all dix while,rocking bayansa ta rinka yi domin kuka yake kaman yaron karami,da kyar ta samu karfi guiwar magana,haba ammar kai da zakayi farincikin ganina wannan kukar ai bana farinciki bane haka,gashi zaka sa kowa kuka,kodai ka finson mutuwa tane dai,dago kai yayi da sauri yana girgiza kai,murmushi tayi sannan tace yau ko kai fa ta fada tana share mai hawayen dake fuskarsa,ya noor tace cry cry baby ai sai ka matsa nayi hugging din kawata kuma sis dina koh,dariya akayi gaba daya sannan ya matsa tayi hugging din umma tana cewa we really did miss you indeed.Same umma ta fada atakaice,momyce ta matso tana kallonta tace masha Allah mamana kece haka murmushi umma tayi sannan tace momy ashe kina kusa da mu bamu sani ba ta fada tana hawaye sannan ta rungume momy tana hawaye,haka ta rinka rungume kowa,da wanda ta sani da newfaces din,bayan rungume rungumensu ne suka zauna suka ci abinci da snack daga nan suka yada zango a palour,nan aka fara labarin yadda komai ya faru kama daga kan hatsarin har izuwa yanxu. Suna cikin haka ya musty ya kira wayar husna,domin sun fi shiri daman,picking tayi tana tsokanarsa,tana cewa ina amaryarsa fareeda,dariya yayi sannan yace ai kin mayar dani abokin wasanki ko,ka manta mu abokan wasa ne ta fada tana dariya,before i forget kayanku ya iso ance kuje ku amsa fah,okay oooooh ya musty laatest news,menene shi parrot of d house,kambu wallahi na fasa fada ma sai dai ka dawo ka gani tana gama fada ta kashe wayar.Dariya yayi sannan yace husna rigima,koh menene oho,amma idan ya dame ki zaki gaya min ai ya fada sannan ya cigaba da hada takardunsa zai koma gida don ya tashi aiki for today.Da yau yayi niyyar komawa gida amma saboda meeting din da yake dashi gobe yasa yayi changing mind dinsa sai weekend kawai,in ya so sai ya dawo tuesday.
😄😄😄😄😄😄
Tanx alot i love you guyx you alwayx make my day.
Pls vote n comment💋💋💋
Mamy wallahi ki gaya min yaushe zaki dawo,nifa na kosa na ganki ne,i really missed you kuma ya mukhtar sai takura min yake,dago kai mukhtar yayi yana kallonta,murmushi tayi mai sannan tace mamy lastest news,daga dayan bangaren kuma mamy tana murmushi neh kawai domin Allah yasa mata son umma aranta sosai,cewa tai diyar mamy menene lastest din toh,yauwa mamy ya mukhtar yayi sabon budurwa,dariya mamy tayi sannan tace Lallai kam kice wannan fah lastest news neh kam,mamy idan zaki dawo ki fa tawo min da bula,sannan mamy ya mukhtar fah kin siya min chocolate yake fah,dariya abin ya ba mamy,bayan tayi mai isarta sannan tace okay zan mai fada,yauwa mamynah,toh gaya min yaushe zaki dawo.Ina ga sai nextweek, domin zanyi wani abin gashi akwai bikin wata yarinyar kawata yakamata na halarta,kukan shagwaba umma ta fara,kai mamy bayan kince sati daya zakiyi gashi yanxu har ya kusa sati biyu sannan kuma kice zaki kara kusan kwana biyar fah,ni dai ban yarda ba ki dawo kawai wallahi.Murmushi mamy tayi domin kwana biyu lamarin umma bata mamaki yake yadda ta saki jiki da ita tana acting kamar itace mahaifiyarta,amma abin na mata dadi sosai kuma,sorry kinji cewar mamy.Tura baki umma tayi kamar tana gaban mamy sannan tace uhmm. dariya mamy tayi sannan tace okay kinsan meye idan na dawo zamuje umrah zan gaya ma mukhtar yayi processing komai,daga nan sai mu biyata Ukraine mu taho tare da Abbanku koh,yeeeeeeeeh ummah tayi ihu sannan tace yauwa umma wallahi kuwa sai kin dawo Allah ya tsare min ke,amin my daughter ta fada tana murmushi. Kallonta kowa keyi,bayan ta kashe wayar neh ta daga masu gira alaman tambaya,su ma daga mata gira suka yi,dariya abin ya bata,sai ta kwashe da dariya sannan tace Allah kun cika sa ido. Mukhtar yace naji bomb din da kika gama hada min wajan mamy wallahi saka min ido zata yi,ai na fi son haka kaga yadda kake kallon sista faiza kuwa wallahi gwanda ka rakani rahmer’s eatry kawai nayi hooking dinku up, kafin garin kallon ruwa kwado yayi maka kafa,dariya yayi sannan yace daman umma haka kike da surutu ban sani ba,dariya ya noor tayi sannan tace idan taso surutun ba,idan bata so ba kam ko kasa da sama zata hade ne baza tayi ba hakan nan taza dinka bin mutane da ido kamar wanda taga wawan zama.dariya umma tayi sannan tace amma fa kun iya exaggerating abu,yanxu dai am bored why not mu je coldstone mana mu sha ice cream,beside weekend neh fah, kowa ya yarda da shirin,tashi sukayi suna shirin shiga mota akayi horn, gate baba iliya ya wangale,motar ya musty neh ya karyo kai,bayan ya shigo neh yayi parking yana murmushi don ya hango husna tana karaso wa wajansa,high five suka yi sannan yace yadai jinjinran gidan,murguda baki tayi sannan tayi banzan da maganarsa don tasan neman magana kawai yake,ya hanya tayi mai sannan suka jera suna karasowa wajan sauran, tsayawa yayi bayan daya hangota,itama kallon nasa take itama,ido cikin ido mamaki yake wai idon shi har yanxu gizo take mai ko kuma ita dince take kallonsa,sai da suka kusa minti biyar awannan yanayin kafin,umma ta janye idonta, ita kuma ganin tayi yayi mata kwarjini ya kara kyau,karasowa yayi amma ya kasa magana sabida yana cikin shock,kallonsu mukhtar yake kishi kamar ya kashe shi domin so da kauna tare da kewar juna ya hango a idanunsa,gyarar murya yayi sannan yace zamu tafi neh or an fasa,murmushi husna tayi domin ta san abinda ke damunsa,ya musty itace ba gizo idonka ke maka ba cewar husna,yanxu dai bamu da time din explaining saboda zamu cold stone amma,baza mu dade ba,by then ka gama kintsawa,sannan nasan momy ma zata baka labarin komai,so kashiga ciki kawai,mota kowa ya karasa domin har ya mukhtar da ya umma har da ya noor sun shiga mota koh,ita kawai suke jira su tafi,tana shiga kuwa ya mukhtar ya ja motar ya bade ya musty da invicible kura sannan ya fice, shiru ya umma tayi acikin motar batace komai ba,ko da suka je coldstone mah,shiru tayi tana shan ice+cream dinta,ya noor kuma tana making call da habibinta husna tana chattin while shi ya mukhtar yana kallonta kawai yana nazari akan yanayinta,sai da suka gama shan ice cream a coldstone ne suka siya take away suka tafi,biyawa suka yi ta eatery din ya umma sannan suka taho gida,ajiye su kawai ya mukhtar yayi sannan ya wuce abinsa domin mood dinsa duk ya chaza,amma kafin ya wuce umma ta leka ta ce mai drive careful sannan ta shige witout turning back,mamaki yake yadda tayi ta san he is not in a good mood.Motar ya ja ya wuce abinsa kawai.Su kuma daman sun dade da shiga ciki abinsu.
💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋
💋💋💋💋
💋💋💋
💋💋
💋
Shi kuma mukhtar daya tafi gida tunani ya zauna yi mai ke damunsa,meyasa yake kishin ganin umma tare da wani,wai sonta yake kenan da gaske,ajiyar zuciya yayi amma ai ita babu soyayyarsa acikin zuciyarta ta dauke sa amatsayin yayanta ne kawai shi yanxu ya zai yi da zuciyarsa da ta kama son maso wani, gaskiya zuciyarsa batayi masa adalci ba data kamo da son wanda bata sonsa,wani ajiyar zuciyar yayi, zuciyarsa tafarfasa take mai wai shi haka zai ta rasa masoya,kodai Allah bai halarta mai mata bane anan duniyar,haka ya ringa sake sake har aka kira sallar magriba yayi alwala ya tafi masallaci.
Shi kuma mustapha bayan yayi wanka neh ya shiga part din momy nan ta fara bashi labarin abin da ya wakana,abin mamaki ya rinka bashi don ya san Abubakar din.+
Lokacin da su husna suka dawo afalour suka samu su momy da su ya musty ana fira,zama kusa da momy umma tayi sannan tace momy sannu da zaman gida yau babu aiki neh na yamma murmushi momy tayi sannan tace babu mamana bani zanyi news din ba yau,ina tsarabar coldstone din,momy ai ke bakya shan ice-cream amma dai akwai dambun nama da kifi da ya mukhtar ya kawo mana cewar umma,yauwa kamar kinsan baki na abu mai gishiri gishiri yake nema ba sugar ba,dariya kowa yayi afalour sannan elham tace momy ai har kin fi autar ki kwadayi wallahi,lahhhhh lallai Aisha elham wuyar ki ya isa yanka,murmushi elham take game da rufe bakinta da hannunta,kafar momy taje ta zauna ta fara mata shagwaba,umma tayi dariya tare da cewa ni dai tashi min kafar momynah kafin ki karasa min ita,kai ya umma nifa autar mata neh,ya musty yace ji wannan common tashi kafin nazo na balla miki dan kugun nan,baki ta tura game da tashi tana dire diren kafa kamar wata yar goyo, dariya Husna tayi sannan tace yauwa nayi capturing whatsApp here we come,zare ido elham tayi sannan tace kambu wallahi kar ki fara kisani a status dinki,ai sai ki hanani na gani cewar husna,zagaye falo suka fara yi elham na binta zata amshi wayar ta goge,girgiza kai momy tayi sannan tace gwanda nayi muku aure ko zan huta da wannan yaranta,ai ko autana bazaiyi wannan shirmen ba,dariya noor tayi sannan tace ai fa..
5day later
Momy ai zan rinka zuwa kinga ita mamy ita kadai neh agida amma ke ga noor,elham,da husna fah.Tab su wannan da in two weeks zasu tattara su bar min gidana. aifa momy zamu sha biki kinga ba karamin rawa zanyi ba,dariya momy tayi sannan tace kema da kin fito dashi kenan sai ahada da ke.Nooo momy ni fa na fisun ayi nasu tukun,kinga ni yayar amarya, ni kanwar ango,ni kawar amarya ta kara fada suna tafawa da noor,dariya momy tayi sannan tace sannu fah duk matsayin nan naki neh ke daya, eh man momy.
Wayar umma neh ya fara kara,dauka tayi sannan ta kara akunnen,okay toh gani nan fitowa kawai tace,kallon momy tayi sannan tace momy sai na dawo daga saudi zanzo afara shirin dani sannan momy wallahi ki gaya ma noor ta kai min dinki nah idan ba haka ba zamu samu matsala.babu ruwana ai kun fi kusa,hugging momy tayi sannan ta ja karamin akwatinta. Noor ta rakata har waje don su elham basa nan sunje rabon kati,bayan noor da mukhtar sun gaisa neh umma tayi hugging din noor tace zamuyi waya ukhty sannan your arabian gowns are on me tayi whispering akunnen noor sannan tayi smirking tana bude hokora,tana shiga motar ya mukhtar ya jasu sai da suka biya ta gidansu ta dauko Credential dinta sannan suka karasa gida. Akwatin ta ajiye kawai sannan ta shiga kitchen. Mukhtar ya bita kitchen din yana tambayar meye zata yi,girki zanyi mana,girki? gira ta daga mai alaman tambaya,daman kin iya girki neh dariya tayi mai isarta sannan tace just watch. Shiru yayi yana kallonta tana ta fitowa da ingredient,kaza ta fitar a fidge ta wanke sannan ta zuba a tunkunya sannan ta daura saman gas kafin ta fara zuba spices,komawa tayi saman vegetables dinta tana yanyankasu,kallonta yake yana zaune saman counter yana cin apple,wai mai zaki girka neh,murmushi tayi sannan tace friend rice zanyi da liver souce da pepper chicken sannan mu hadda zobo,simple girki zanyi ai,zare ido yayi yace wannan neh simple girki,sannunki fah.
Bayan minti talatin har ta gama hada friend rice din ta zuba a food flask liver souce din mah ta sauke tana juyewa cin coolar miya,daman ta gama pepper chicken,grating din cocumber tayi da pineapple hade da chitta,sannan ta tace ruwansu awani kwanon fito da zobon tayi wanda ta tafasa shi da bawon abarba da chitta da kanumfari ta tace tasa afridge,zuba ruwan da tache tayi sannan zuba flavour pineapple da strawberry sai ya bada kamshi mai dadi,sugar ta zuba sannan ta zuba ajug guda uku ta saka afridge,sauran cooler kuma takai saman dinning,dawa kitchen din tayi ta kimtsa kitchen din sannan ta koma dakinta don ta watsa ruwa,bayan ta fito neh tayi sallah sannan ta saka kayanta tayi light makeup sannan ta zauna jiran mamy don anje dauko ta a airport,tana zaune afalour harta fara barci ta jiwo sallamar mamy ta sauri da farka tare da mike wa taje ta rugumeta sannan ta karbi hand bag dinta,zama tayi adaki sannan tace mamy bari na kawo miki ruwa mai sanyi ki sha,ruwa ta dauko mata ta sha sannan tace,yauwa momy yanxu muje kiyi wanka sannan kiyi sallar sai mu fito muci abinci,zare ido mamy tayi sannan tace waya girka abincin,murmushi umma tayi sannan tace umma ni na girka,ajiyar zuciya mamy tayi sannan tace ai na zata wannan neh ya girka har naga idan ya mayarda min da kitchen dina,dariya umma tayi sannan tace,mamy muje kar ki tsaya jin maganarsa ya kara miki gajiya,dariya mukhtar yayi sannan yace zaki dito ki same ni ai zaki gaya min waya zai kara mata gajiya.Daki suka shiga ta hada ma mamy ruean wanka sannan ta fito mata da kayan barcinta riga da wando sannan ta shimfida mata sallaya da ajiye mata himar din sallarta.Dakinta ta wuce don tayi isha saboda an fara kiran sallar.
Mamy ya hanya ya mutanen bauchi cewar mukhtar,lafiya lau ya zaman gaurancin,kai mamy,dariya umma tayi wanda fitowarta kenan,zama tayi kusa da mamy sannan tace atoh nima nace ya fito da mata donmin aiyota ta kare amma yaki kuma ni na mai mata fah kawai dai bai shirya bane,gira ya daga mata,murmushi tayi sannan ta kalle momy tace muje mamy kici abinci kinji kar ya mukhtar ya dame ki da surutu har ki samu ulcet saboda yunwa,dariya mukhtar yayi yace umma kin raina ni wallahi,gwalo tayi mai sannan tace babu ruwana.
Dinning suka je bude cooler tayi ta zuba ma mamy abincin sannan ta zuba ma ya mukhtar kafin ta zuba ma kanta,ci suke mamy da ya mukhtar na mata santi ita kuma tana dariya tana cewa bari ta samusu waigi kar suje su fadi haka suka rinka raha har suka gama cin abincin.
Falour suka yadda da zango sannan suka daura firarsu daga ida suka tsaya har sai da suka kira sis junainah mah suna mata iskanci kala kala don ba’a family time da ita sai da mukhtar ya kusa sata kuka hankalinsa ya kwanta,bayan su gama fira da nainah neh aun kashe waya shine suka fara ba mamy labarin komai da ya faru lokacin da bata nan,abun mamaki ya ba mamy da kuma ta ji dadi,kuma tama sannan momy don wajan aikinsu daya,sai dai ba tare suke aiki ba ita mamy na radio ita kuma momy na T.V. Fira suka kiyi sosai take gayama mamy zatonsu aiko momy tayi confermin,har da dauko hoton mama wanda sukayi da yanuwanta sai gashi nan zahiri su ukun kam gashi kamaninsu daya,abun yayi ma mamy dadi sosai atleast yanxu zatayi barci mai dadi domin kullum barcinta rabi da rabi neh din tana tunanin idan umma tayi regaining memiry dinta sgi kenan zata tafi ta barta amma ai yanxu zata iya rokar alfarma abar mata ita,taji dadi sosai.Bayan su gama firansu neh suka yo kallo,karfe goma kowa ya tashi ya shiga daki don yayi barcinsa.Umma na shiga daki tayi waya da yan uwanta kafin tayi brush sannan tayi alwala ta kwanta.
💋MAFARKI💋
Zaune take awani lambu,wanda yake za gaye da fulawowi masu matukar kyau da tsari,ga wata irin kamshi dake tashi daga furen,ga garin yana bada sanyi sanyi kamar lokacin damina,sanye take da wata jan jallabiya mai ratsi ratsi golden da black flower tayi rolling kanta da bakin mayafi fuskarta dauke yake da simple makeup amma tayi kyau sosai,wage wage take amma bata ganshi ba,tana wai gawa ta damarta ta hango shi yana tahowa sanye yake da farar jalla biya bata iya hango fuskarsa don yayi haske dayawa amma daga launin fatar jikinsa kasan dan hutu neh,fari neh tas kamar balarabe,jikinsa sai sheki yake kamar wanda yayi wanka da mai gyada,gashi kansa akwance yake kamar na larabawa,yatsu hannunsa da na kafafu dogaye neh sosai yana da matukar tsawo sannan bashi da wani kibi amma kuma baza ka kirasa tsirir ba. Karasowa yayi ya zauna kusa da ita sannan yace saheebatul-noor da muryarsa mai dadin sauraro,murmushi tayi sannan ta shagwabe fuska tana cewa baka son na gan fuskarka koh,murmushi yayi mai sauti sannan yace,calm down matata kin kusa ganina azahiri so ki kwantar da hankalinki,sannan ki sa aranki ni naki ne babu dadi babu kari naki ke kadai,ina tsananin sonki hasketa.Murmushi tayi kawai tana kallonsa,shima ita yake kallon.
Masha Allah.
Pls vote and comment
💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔
💔💔💔💔
💔💔💔
💔💔
💔
💓MAFARKI💓
ajiya zuciya tayi sannan tace okay but yaushe zan ganka ina so na gan fuskarka,baby calm down zaki ganni very soon sannan baki ce min kina sona ba fa,baki ta turo kawai tana kallonsa,murmushi yayi mai sauti sannan yace toh shi kenan tunda baki shirya ba.
💓CIGABA💓
Da mamy tazo tada ta da asuba neh ta ga tana ta murmushi,murmushi itama tayi sannan ta tashe ta,mutseke ido tayi tana turo baki da taga mafarki takeyi kuma duk ta zata ba mafarki bane domin yau tafi ganinsa so close gashi hasken fuskarsa ya ragu tasa rai zata gan fuskarsa kawai mamy ta yanke mata barcinta,murmushi tayi mah mamy wanda take ce mata ta tashi tayi sallah,mamy girgiza kai tayi sannan ta tashi ta tafi dakinta,ajiyar zuciya tayi sannan ta mike tayi alwala tayi sallah,bayan ta idar da sallah tayi azikar dinta sannan tayi karatun alqurani kafin ta kwanta,tunani ta rinka yi duk lokacin da ta kusa ganin fuskarsa lokacin aike tashinta daga barci tayi sallah gashi lokacin da bata sallah kuma bata mafarkin nata,juyi tayi taayi asaman gadon kafin daga baya ta tashi kawai don barcin yaki zuwa,toilet ta shiga tayi brush sannan ta wuve kitchen, breakfast ta hada musu,kunun gyada da kosai tayi sannan ta soya chips da plantain incase akwai wanda zai sha tea tana gamawa tayi boiling ruwan shayi wanda yaji tafarnuwa,kanumfari,chitta,na’a na’a cinamon da habba.Zubawa tayi a flask sannan ta ajiye dinning table kafin ta shiga dakinta ta wasa ruwa,tayi simple makeup kafin ta saka bodyhug da straight skirt sannan ta dauko kimono ta saka da veil dinta asaman kai ta yafa,turare ta fesa kafin ta dau side bag dinta da wayarta,palour ta fito lokacin mamy itama ta fito kenan itama ashirye,murmushi sukayi ma juna sannan umma tace ina kwana mamy,ansawa mamy tayi sannan suka karasa dinning,kunun gyada ta zuba ma mamy sannan ta zuba mata kosai da chip tare da plantain din,ana cikin haka junainah ta shigo da sallamarta ita da abubakar tare da mukhtar yana binsu abaya,murmushi umma tayi sannan tace sista wannan sammakon fa,dariya nainah tayi sannan tace gwanda nayi sammako don abude jakar tsaraban dani donmin na gan mamy ta manta dani amatsayin daughter fa sai ke kawai take gani,dariya kawai umma tayi sannan tace ai fah ai ni kadai ce yarta,murmushi mamy tayi suna gaisawa da sadeeq,sama suka yi akayi breakfast dasu,junainah sai santin ruwan shayi take,shi kuma sadeeq bazaka gane make yawo azuciyarsa ba amma mukhtar cewa yake shi kenan kice ni nagama jin dadi tunda faiza is working under you,murmushi umma tayi sannan ta kashe mai ido ita kuma nainah ta tsaya kallonsu inconfusion,bayan sun gama cin abinci,mamy ta tashi ta shiga daki ta dauko jakarta da mukullin motarta ta fito lokacin umma tayi clearing table din ko,daki ta koma itama kafin mamy ta gama magana da su nainah don ta gyara fuskarta sannan tayi rolling din mayafin da kyau,after 5min ta fito da taji mamy ta kwala mata kira,fitowa tayi sannan suka tashi suka wuce don zasu embassy neh don ticket dinsu ya fito zasu amso sannan su biya gidan friend din mamy Anty luba.Suma nainah fitowa suka yi don daman asibiti zasu nainah ta matsa sai sun biya,shi mukhtar asibitin zai tafi don yana da patient din dake jiransa.+
Saudi Arabia
Wash mamy wallahi na gaji muna kaiwa masaukin mu zan keanta na huta kafin nan gobe zai na fara abinda ya kawo mu,mamy tace hakan ya kamata kam.
Suna kaiwa sukayi lodge in sannan aka dau musu dakin da suka yi reserving,suit neh mai daki uku,daki daya umma ta shiga tayi wanka tayi sallolin da ake binta sannan ta hau saman gado bata tsaya tunanin wani abincin ba,mamy ma wanka tayi sannan ta kwanta.
Da yake da daddare suka shigo so sai da asuba suka tashi barci,sallah sukayi sannan suka fito don dukkansu yunwa suke ji,gaishe da mamy umma tayi sannan suka sauka kasa don suyi breakfast, suna gama wa mamy ta koma daki ita kuma umma ta zauna tana chatting dasu Noor a group chat din da sukayi creating mai suna FAM n FRDNS,dariya take tace bari na koma daki sai muyi facetime toh tace musu,nainah tace ita bata yarda ba au bata gidansu momy balle itama aiyi facetime din da ita,gwalo suka saka mata da emoji din dariya,sannan husna tace ayya sis dix a single babex tym,dariya nainah tayi sannan tace ayya babex two week ya rage muku kuma ai so am going to sit calm and wait for my turn uhmmmmm zaku gane kurenku,emojin gwalo suka kara saka mata,haka suka rinka fira suna nishadinsu abinsu kamar suna tare.
Mamy waye yazo naji kamshin wani turare kuma nasan ba naki bane,ayya rushd neh wallahi yanxu ya wuce baku hadu ba kenan,nop bamu hadu ba don ban sansa ba so mayb mun hadu,okay ai yaron sista din mamarki ce nafisa shi kadai neh yaronta kinsan babansa dan dubai neh kuma babban dan kasune bai fiya sama ba sai sa da muka je lagos baki gan mijinta ba,shi kuma rushd bai san mutane lecturer neh a abuja state university amma duk da haka baya zuwa gidana,sai dai once awhile basa shiri kuma da nainah wai ta fiye hayaniya,dariya umma tayi sannan tace ai understand where he is coming from,mamy kinsan nainah akwai surutu,wallahi mamy ko baka son surutu idan ka hadu da junainah sai ta saka surutu,dariya mamy tayi sannan tace tabbas na yarda yarana talkertive neh amma dama dama ke baki kai su,zare ido umma tayi sannan tace mamy daina hada ni dasu ai ni novice neh ajikinsu,dariya suka yi su biyun sannan suka shiga suka dauko hijab sannan suka wuce masallaci,mamy ban tambayeki ba shi ma umrah yazo neh,noooo yazo wani aiki neh fah amma yace min zai yi umrah kafin ya koma gida okay kawai ma tace tana murmushi.
Masha Allah yau nice adakin Allah ina taba shi haka,alhamdullilah buri na ya cika,zama tayi ta jin gida da ka’aba sannan ta rinka shafawa ta mamaki,daga baya ta rinka zuba addu’ointa tare da nema ma iyayenta gafara da kuma kare yan uwanta da masoyanta daga mugaye da hanyar bata,sai data kusa awa biyu zaune awajan tana addu’a har mutane suka dan waste,lokacin da tashi taji kafarta yayi tsami donmin asamshi ta zauna sai data dan jikina da jikin ka’aban ta gyara tsayuwarta da kyau sannan ta wuce masaukinsu,tana shiga ta kara jin kamshin turaren dasu bata ce komai ba ta gaida mamy sannan ta wuce daki,kafin ta shiga mamy taje ce mata rushd ya zo yanxu ya tafi,Allah sarki tace kafin ta wuce dakin don ta gaji gashi kuma tayi kuka so muryarta yayi dishi dishi,girgiza kai mamy tayi sannan tace Allah ya sausauta miki zuciyarki rahma sannan kin saka abu dayawa aranki,ajiyar zuciya tayi sannan itama ta tashi ra shiga dakinta.
Mamy i cant bliv saura kwana hudu mu bar nan,wallahi kam cewar mamy,lokaci neh babu wuya,yanxu momy shopping zani anjima nayi ma su noor alkawarin jallabiyar arabian night so zanje shopping,toh bari na shirya mu je tare mana,noooo mamy ki bari kawai ki fada min abin da kike so sai na siya mik kawai beside nida sabuwar kawata zamu,waye sabuwar kawarki,shanza sunanta aka’aba muka hadu two day daya wuce,okay toh.
Shanza so what do you think of this abaya,it cute but i prefare d golden for you,crazy gal it not for me it for my siblings okay get d silver for d bride then you take black for yourself but def buy dat golden it suit your skin colour,cewar shanza domin ita yar india ce so bata jin hausa,haka suka rinka shopping daga baya suka tsaya wani eatry suka ji abinci kafin suka fito suka shiga wani shop din suka siya takalma kafin suka bar wajan #uka koma masaukinsu.
Mamynah yanxu next tomorrow dubai zaku wuce yayi maganar kamar ana forcing dinsa,eh mamy tace sannan tace zamu je mu samu Abbu dinku neh daga nan sai mu wuce nigeria tare,kai yaushe zaka dawo,shiru yayi kamar bazai amsa ba kafin yace Ammy tace akwai wedding Abuja but bazanyi making ba,saboda by then i will be in oxford zan karasa course dina so ni da naija i think it in four month time to come,okay Allah ya kai mu,ameen yace kafin yace zai tafi domin ya gaji da magana ko sannan ya san halin mamy yanxu sai ta saka shi surutu da bai shirya ba so gwanda ya rufa ma kansa asiri ya tafi abinsa,mamy tace har zaka tafi yace eh,tace gashi baka hadu da yar uwartaka ba duk lokacin da zakazo bata nan ta fita,mamy ta fiye yawo neh sai ya fada yana karasa kofa tare da cemata sai anjima,girgiza kanta tayi sannan tace sababinka yana da yawa,wanda zata aureka tana da babban aiki wallahi. murmushi tayi sannan tace amma ina ma kwadayin umma don tana da hankali amma ai wahalar da ita zakayi,mtsuuu tsaki tayi sannan tace nayi ma mukhtar kwadayin ta amma tunda bata so kam bazan mata dole ba kam,abin ma yazo da sauki tunda mukhtar ya samo mata.
DUBAI
Abba ni wallahi akwai earring din dana siya ma husna yana bayan mota zanje na dauko sai na dawo sai naci abin,girgiza kai abba yayi sannan yace as stubborn as ur mother grinning tayi sannan ta tashi ta wuce ta dauka bag din kayan da ta siyo wanda uber di ya dawo dashi don ta manta amotarsa so sai ya ba ma reception,tana amsowa ta wuce masaukinsu suka ciganba da cin abinci.
mamy yanxu wannan balaraben shine mijin Ammyn din lagos lallai kam,nifa na gansa downstairs dazu har dace mai mu dau selfie zanje na nuna masu husna nayi hoto da balarabe amma nah dubai dariya mamy tayi sannan tace gaskiya yanxu na yarda ya’yan fari akwai wauta,tura baki umma tayi amma batace komai ba.
Ayi hakuri da errors
Ps vote n comment
And tanx for all your msg yana kara bani kwarin guiwa.
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤
❤❤❤❤
❤❤❤this chapter is dedicated to
❤❤you my readers thank you
❤so much.Love you.
🌹NAIJA🌹
ya umma meye kike nufi baza kizo bane wai ,ohoho husna ina wani abu neh daman amma yanxu zanzo,ina jiran ya musty ya gama loading din snack din aboot kafin mu wuto,toh shikenan sai kinzo.Kallonta mustapha yayi sannan yayi murmushi kafin yace husna trouble,aifa duk so take ta rikita ni yau dinnan,sai sa ma naki zama agida nake gidan mamy idan ba haka ba ai sai ta sa nayi hauka don lamarinta sai ahankali. haka neh muje toh, okay bari na dauko jakata.+
Wow kuga amaren jibi umma ta fada bayan ta zauna tabarma da noor take zaune,lallan ku yayi kyau sosai,ya umma wai meye kika tsaya yi tuntuni,da yanxu an gama miki mun tafi fa,gidanku na tsaya yi,haba kin fiye korafi fa,turo baki husna tayi sannan tace toh ya umma ba kawai ina missing dinki bane,tabe baki umma tayi sannan tace sannu fah wani missing bayan aure zakiyi ki barni,raurau husna tayi da ido kamar za tayi kuka sai ta zama abin tausayi,shige wa umma tayi don bata son husna ta sata kuka tun yanxu,cewa take bari na chazo kaya aiyi min tawa.
why not ku tafi gida ku fara shiryawa kafin agama min tunda shiryawanku na musamman neh,kuma haka neh fah cewar noor,yanxu dai ku tashi mu tafi tunda kafa daya ya rage mata nasan zuwa four angama kuma ya bushe sai ta taho,zamu bar miki mota daya sai ki dawo da ita noor ta fada tare da ajiye mata key din highlandernta sannan tace ma mai lallan,maman sudais sai nazo amsar sakona,ta fada tare da daukar jakarta,okay toh cewar matar mai lallan,sai na dawo umma tace musu sannan suka wuce.
parking motar tayi aparking lot sannan ta garzaya cikin gidan da sauri don fitsari ya matse ta gashi kuma mutane sun fara hallartar kamun da za’ayi a harabar gidan,tana zuwa dakin husna ta shiga,taji dadin da babu kowa ciki,don haka bayi ta fada tayi fitsari sannan ta daura da wanka kafin tayi alwala ta fito,mai ta shafa sannan ta saka inner dinta kafin ta daura zani da doguwar himar sannan ta shimfida sallaya tayi la’asar sannan ta koma ta shafa turarukanu jikinta da kolacca,simple makeup tayi sannan ta saka ankon kayan kamun kafin ta zauna tayi dauri sannan ta fesa jikinta da arebian perfs masu dadi kamshi,takalmi flat ta saka sannan ta dau karamin gyalanta da pus tare da wayarta Hot8.fita tayi ta shiga dakin noor amma basa nan toh kilan su fita filin ashe ta fada azuciyarta,dakin momy taje nan ta tadda ammin lagos,hugging dinta tayi sannan tace ammi yaushe kika zo,yau dinnan ina gidan Abbanku,mamynki tace wai tunda safe kika fita,eh ina da abin yi a bakery sannan kuma zanyi lalle,okay yayi kyau toh muje waje har anfara amma bakya nan,ammy wanka nayi ai sai sa donmin yanxu na shigo,Allah sarki,yaushe zaki zo min lagos hutu toh,mamy ki bari a gama bikin sai muyi magana bakince one week zakiyi ba, sannan kinga mamy ina son na shiga school saboda yanxu husna saura mata shekara daya,ammar ya gama kinga babu wani biyan school fees masu so zanje nayi furfilling dream din mama,murmushi ammy tayi sannan tace,haka kike kamar mamarki,murmushi itama umman tayi sannan suka karasa wajan taron,wajen amaren taje tayi ta daukansu hotuna,sannan tace instagram dina yau zaiyi shaken saboda lastest wedding in town ta fada tare da musu wink,bayan akira amare sun taka rawa neh aka raba abin ciye ciye sannan aka cigaba da gudanar da sauran abubuwa,karfe bakwai saura aka tashi taron.
Wayyo ni na gaji wallahi umma ta fada tare da kara lankwashewa cikin kujerar dake garden din gidan momy don hanata tafiya sukayi,dariya noor tayi sannan tace sai sa ma yanxu zan gudu na kwanta kamar yadda su husna suka gudu, kar aga amare da wrinkles gobe,dariya dukkansu sukayi kafin ta wuce,sai aka bar umma da musty tare da bobby wanda shima mike war yayi sannan yace ya umma sai da safe,Allah tashemu lafiya.Juyuwa tayi ta kalli musty wanda shima din ita yake kallo,toh kai wannan angon fah bazaka je ka kwanta ba,murmushi yayi sannan yace zanje na kwanta amma idan ki yarda zaki aure ni,zare ido umma tayi sannan ta dafe kirjinta wani irin aure kuma ya musty,jibi neh fa aurenka,ajiyar zuciya yayi sannan yace nasani amma wallahi umma ina sonki sannan kuma ai zan iya auren mata biyu alokaci daya,yardarki kawai nake nema,kina cewa eh zanyi mah abba magana sai adaura ajibin.Kallonsa take idonta cike da hawaye wanda ke shirin zubowa,amma batace komai ba,cigabawa yayi da cewa dan Allah umma ki taimaka min ki cece zuciyata wallahi ina matukar sonki,idan don abin da na miki neh abaya wallahi nayi dana sani kuma na yarda kimin duk wani horon daya dace dani amma dan Allah karki guje ni,hawaye ne ke fitowa daga idonsa wanda ya saka itama ta fara fidda nata,saukowa kasa tayi daidai idan ya zauna saman carpet grass din,ta dauki hannunta wanda ke rawa ta daura saman hannunsa sannan ta fara magana kamar haka,ya musty hakika zuciyata ta kamu da sonka tun lokacin dana fara ganinka, ta fada hawaye na zubo mata,sannan ko daka yi min rashin mutinci awannan lokacin kwata kwata banji zafinka ba sai ma wani sonka daya kara shiga ta,sai sa nayi saurin nissantan kai na dakai,lokacin dana dawo abuja da zama zuciyata azalzalata ta rinkayi aka abinda take so, tafada tana shesheka,sannan ta cigaba sannan kawai sai watarana marwan ya ban shawaran kawo ka cikin rayuwata,nayi murna sosai ko da kuwa bazan sameka ba nasan zan rinka ganinka sannan za murinka waya,kawai kwasam sai nayi haddari na samu temporary memory loss,amma haka bai hana ina ganin gizonka cikin mafarkina ba,alokacin tambayar kaina nake waye kai kuma meye Dangartakarmu,tafada tare da kara fashewa da kuka,kallonta yake cikin mamaki ashe itama tana sonsa,kenan zata bari ya aure ta,har ya fara jin dadi azuciyarsa kawai sai ya jiyo muryarta tana cewa amma kawai ina regaining memorynah sai na gane ashe babu aure atsakanina da kai,da sauri ya dago kanshi yana kallonta duk ya rikice,bakinsa na rawa ya fara cewa maisa zakice babu aure tsakaninmu,share hawayen fuskarta tayi sannan ta mike tsaye ta fara tafiya,taku hudu tayi ta juyo ta ganshi zaune idan ta barshi,ce mishi tayi babu aure tsakanina da yan gidan nan domin momy ta shayar dani,daskare wa yayi awajan ita kuma ta juya ta karasa cikin gidan,tana shiga ta samu ta wanke fuakarta sannan tayi addua ta kwanta,amma barcin yaki zuwa,kawai sai ta mike ta shiga bayi tayi alwala sannan ta roke Allah zabin alkhairi arayuwarta,nan neh taji sanyi azuciyarta,kwanciya tayi barci nan da nan ya dauke ta.
Shi kuma mustapha dake cikin shock har wajan karfe daya ya kai awajan sai daya shiga cikin ya kwanta kafin abin ya rinka yawo mishi akwakawalwa,wai haka umma ke kinsa neh da zata bijiro da irin wannan zancen don karta aure shi,kallon agogo yayi yaga karfe biyu tayi,haka ya rinka sake sake har aka kira sallah,bayan yayi sallar azuba neh ya koma ya kwanta lokacin neh barci ya kama shi.
Ita kuma umma da tayi sallah sai ta tasha magani don kanta na mata ciwo sannan ta dan kwanta,karfe takwas daidai ta tashi sannan tayi brush tayi wanka tana fitowa ta saka kayanta sannan ta dau mukulin motar noor tafito da jaka da mayafinta ahannu,dakin momy ta leka ta ganta tare da mutane,bayan ta gaishe sune take cema momy zata gidan mamy ta debo kayanta da zatayi amfani dasu yau da gobe,momy tace mata toh shi kenan sai ta dawo,tana fitowa suka ci karo da mustapha abakin kofar fita daga falo matsa mai tayi ya shiga ta gaida shi ba tare da ta kallesa ba sannan ta wuce,binta da kallo yayi sannan yace azuciyarsa yakike son nayi da rayuwata neh rahma.
Dakin momy ya shiga sannan yace ma momy zaiyi magana da ita,palon dady suka karasa sannan tace mishi meye neh na ganka wani iri,wani abin neh ya faru,ajiyar zuciya yayi sannan yace momy wai dagaske neh babu aure tsakanina da umma?,zare ido tayi tana kallonsa don ita ta manta da wannan lamarin ma,waya gaya ma hakan,ajiya zuciya ya kuma yi sannan yace ita tace min haka,meye ka gaya mata har yasa ta furta ma hakan,momy sonta nake tun ba yau ba,daman tun farko momy taga take takensa amma lokacin bata san waye umma ba,numfasawa momy tayi sannan tace,hakikanin gaskiya sai dai kayi hakuri domin tabbas babu aure tsakaninka da rahma,domin nina shayar da ita lokacin mamarta bata da lafiya kuma bata da ruwan nono,ni kuma ina rike da noor lokacin, so sai na hada su na shayar dasu,saboda haka ina mai rokanka mustapha ka saka ma zuciyarka ruwan sanyi ka cireta azuciyarka domin haka bazai taba faruwa ba,toh kawai yace ma momy sannan ya tashi ya bar falon,momy jinjina lamarin tayi sannan tace Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi,sannan ta tashi don komawa wajan bakinta.
Ammy tab,ya rushd dinne na gani,ai ko zaman minti goma cikakke bayayi da jama’a idan ba haka ba tambaya mamy ita da take ganinsa kullum,dariya ammy tayi sannan tace rushd dinne baya son jama’a wallahi,naga alama duk lokacin da zai zo fa it either ina barci ko na fita da shanza,sai dai mamy tace min yanzu ya tafi,murmushi ammy tayi sannan tace haka yake baya zama awaje na minti goma,idan ba part dinsa bane,kullum yana cikin kamar matar kulle,wani lokacin mah sai naje nace masa ya fito muyi hira,sannan da munyi hirar 15min zai ce min shi zai je ya kwanta kansa na ciwo,dariya umma tayi sannan tace ammy sakaye yake miki don kar yace kin dameshi da surutu,dariya mamy tayi sannan tace sannu zabiya sai kace halinku ba daya bane,ai gwanda shi idan an dame shi yana cewa kansa na ciwo ke fa ai banza da mutane kike kamar baki ji ba,tura baki umma tayi sannan tace mamy wallahi na fishi fah idan na fara surutu kamar parrot,eh haka neh kam amma idan kika fara shiru kuma kamar dumkum,wallahi mamy ni…….wayarta ya katse ta,na bani yau noor zata yanka ni bari na tafi mamy,ammy sai na dawo don nasan baza mu hadu achan ba,tunda bridal shower zamuyi yau,okay adawo lafiya.
😬Vote n comment
Love you guyx
You all make my day by just voting n commenting thank you so much
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻
🌻🌻
🌻
Na sani na sani,amma kar ki yanka ni tukun ki tsaya kiji abinda ya faru,umma ta fada tana son dariya don yadda amaren suka tasa ta gaba,daga gira sukayi atare alaman tayi explaining,dariyar da take rikewa tayi sannan tace kinsan akwai traffic sannan kuma na tsaya muna magana da ammy neh wallahi sai sa,am sorry ta fada tare da hade hannayenta,murmushi suka yi sannan suka ce apology accepted,so what going on,an gama decor din neh,eh an gama cewar elham, kawai event din zamu fara okay toh bari na sa kaya sai na sauko nazo,cewa sukayi toh sannan suka wuce don daman su ake jira kawai.
Umma na gama shirinta cikin royal blue gown da black turban cap,tayi light makeup dinta,ta sako flat shoe dinta sannan ta dau wayarta ta fito,tana fitowa ta hango marwan da musty tare da bobby zaune a garden opposite BQ,gabanta neh ya fadi amma sai ta dake,marwan neh ya fara hango ta,daga mata hannu yayi alamar tazo,karasawa tayi ta zauna spare kujerar dake wajan tana facing din ya musty,koh kallansa bata karayi ba bayan gaisuwar da tayi mai,marwan yace haba umma kawai tunda kika dawo baki tani sai ta yan uwanki koh,dariya umma tayi sannan tace ji yadda kake magana kamar da budurwarka kake,dariya yayi sannan yace,ai na kusa fita sahun budurwa da saurayi,nema zanje nextlevel, dariya umma tayi sannan tace nima ai nextlevel din zanje tunda na zama yaya ta fada tana mai gwalo,dariya bobby yayi sannan yace,haka neh fa marwan yaya zaka rinka ce mata tunda zaka auri kanwarta,kai na manta mah har ni ma yaya zaka ce min,kai nawa nextlevel din dayawa yake,dariya umma da bobby suka sa sannan sukayi highfive,kallonsu mustapha kawai keyi amma bai ce musu komai ba,girgiza kai marwan yayi sannan yace wato taron dangi zakuyi min koh,toh guduwa zanyi yanxu daman,dariya umma tayi sannan tace idan ma baka gudu ba yanxu zan hada ka da su little cousin dinmu su dameka,dariya suka yi dukkamsu amma banda musty,kallonsa marwan yayi domin yaga alamar baya kusa,taba shi yayi sanan yace duk tunanin amaryar neh haka,murmushi yayi kawai tare da girgiza kansa.Tashi umma tayi sannan tace bari na kara naji anfara sa kidi na je na kwaso shoki,dariya marwan yayi sannan yace toh ayi rawa lafiya,insha Allah kanina ta fada tana kashe mai ido,dariya yayi yana tuna old dayx a shinkafi investment.+
Tana shiga taga amaren na rawa,shiga tayi suka rinka chashewa,bayan sun gawa rawarsu suka dau hotuna tare da cin snack da drinks din,karfe shida suka gama sannan suka fito,ganin angwayen suka yi a parking lot,ita kuma nainah Abubakar yazo daukanta,kallon umma tayi sannan tace yanxu bazaki rakani ba kenan,nop bazan rakaki ba cewar umma,wannan grumpy husband dinki tab,koh dariya bayayi,am avoiding siting n breathing the same air as him,sai ya ta mah mutum kallon uku saura kwata kamar grumpy a cindrella cartoon,dariya nainah tayi tana girgiza kai sannan tayi hugging dinta,see you tomorrow sis love,okay bye ta daga mata hannu,ita kuma ta karasa wajan mijinta.Tana zuwa yayi hugging dinta ko kunyar jama’ar gidan ma bai ji,murmushi tayi mai sannan tace wai mai sa baka shiri da umma neh ta fada baya sun shiga cikin mota,kallonta yayi cike da mamaki sannan yace dole ne sai nayi shiri da ita neh,ai ba muharramata bace,but ai yar’uwatace sannan kuma ina sonta,kai baka son abinda nake so na lura,ajiyar zuciya yayi sannan ya fada azuciyar,baki san na fi son haka ba,sannan yace mata waya ce miki bana son abinda kike so,gashi baka son yar uwata,ita din ne ta fiya iyayi,mamaki neh karara afuskar junainah,shiko tukinsa yake abinsa ko kallonta bai sake ba haka itama bata kara cewa komai ba.
Allah ya baku ikon gama soyewar kenan cewar umma,dariya suka yi sannan suka zauna saman gadon,sai murmushi suke kamar wasu wawaye,kallonsu umma tayi,sannan tayi murmushi sannan ta cigaba da shan ice cream dinta tana karanta novel a wattpad.
Wayarta ne ya fara kara,ajiye robar ice cream din tayi da wayar hannunta sannan ta mika hannunta ta ja purse dinta ta ciro karamar wayarta wanda ya fara kara kuma,amsawa tayi tare da yin sallama,bayan minti biyu tace uhmmmm dadi na da kai kajen hakuri,naji kawai kayi moving kayan zuwa daya dakin mana ko kawai ayi using wannan kafin nayi setling sannan zanzo na duba important thing dake ciki sauran kuma abayar kyauta kawai,sai da safe don ka katse min abinda nake,kai ya umma ni wallahi yanxu baki sona,dariya umma tayi sannan tace ammar grow up jare,sannan ta kashe wayar bata jira wani korafin nasa ba.
yauwa kun gama day dreaming din naku neh ko ya,dariya sukayi sannan husna tace ya ammar neh abi,eh fah duk rikata min kwakwalwata yake son yi wallahi.Dariya husna tayi sannan tace ya ammar kenan akwai rudewa wani lokacin.aifa kam,ya umma kinga yadda kike rawa dazu cewar elham,murmushi umma tayi,batool tace wallahi nema bansan cewa ya umma kin iya rawa haka ba,dariya umma tayi kuma sannan tace,na dai taka amma wannan ba rawa bane kenan haka suka rinka fira kafin tace bari ta basu wani shawarwari.
Gyaran murya umma tayi sannan ta fara magana,nasan banyi aure ba amma from d little i know and from what i have read zan iya fadan abu kadan,shi dai aure ba abun wasa bane kuma ya wuce soyayyar da ake yi awaje,wani sabon alamari neh,akwai ups and down dayawa,sai kun rinka hakuri da juna,zai bata miki rai zaki bata mai rai,but abu daya shi neh alokacin da daya ya hau ya kamata ki sassauta naki fushin domin idan ku biyu kuka taru kuka yi fushi akwai matsala,especially ke husna duk wannan zafin zuciyar taki daga gobe idan za’a fitar dake daga gidan nan ki ajiye shi abakin gate,shiru dukkaninsu suka yi suna jinta idon su cike da hawaye,kafin dai ta gama basu shawarwari dai sun bude famfonsu hawayensu yana zubowa,noor neh ta shigo tana tambayar meke faruwa,murmushi umma tayi sannan tace daga musu magana shine suke son sani kuka ni kuma nakiyi she ne na barsu su nayi,dariya noor tayi sannan tace mai sa ni ba’a bari ina nan akayi ba ai dana karu,ai ke yayata ce sai dai ki ban shawara nima,dariya noor tayi sannan tace kanne ma na ba yayyi shawara ai,sannan tazarar wata biyu neh kawai fah amma kina yi kamar wasu shekaru neh,dariya suka yi sun biyu.
Washe garin dauri aure,duk su tashi har sunyi wanka dukkansu mai makeup din da aka dauka tana nan tana ma fuskarsu aiki,umma dai tace babu mai fainta mata fuska,kaya ta saka tayi light makeup din data saba domin ita bata fiye son kwaliya ba. Yanxu ya umma bazaki bari amiki kwaliya ba kenan cewar elham,rabani dan Allah duk awahalar maka da wuya,dariya noor tayi wanda yanxu aka gama mata kwaliya,kaya suka saka su runka hotuna abinsu ko dar dar din da amare kiji su basa ji,wai nace amaren zamani kenan.
Angwaye kuwa sun yi wanka sun sha farar shaddarsu sun daura malum malum da hulunarsu,sunyi kyau sosai.Suna isa daman su ake jira aka fara daurin aure. Nah mustapha Ahmad shinkafi da fareeda suleiman.Sannan aka daura na Mujaheed mukhtar alfasary da maryam Ahmad shinkafi (noor),sannan Muhammad (ammar) Aliyu lamido da fatima (batool) umar lamido,sai Marwan salisu lamido da Aisha elham Ahmad shinkafi,sannan Aliyu (bobby)Ahmad shinkafi da Asmau Aliyu lamido akan sadaki naira dubu sittin sittin.Bayan daurin auren neh aka rinka taya angwayen murna da fatan alkhairi,sai da suka samu aka ragu tukun suka kira amarensu suna gaya musu they are official dia wives.Daga baya suka je gidan akayi hotuna
Dadare kuma aka shirya aka garzaya pinacle hall akayi grand dinner wanda ya kayatar da kowa,awajan akayi barin kudi masu manna dollar nayi masu manna naira nayi,abunka da bikin masu dashi,karfe goma aka tashi taro,aka watse kowa ya koma gida.Washa gari aka kai ko wacce gidanta,batool da noor gidanjensu a abuja yake while husna na kaduna and elham da fareeda na kano. Kuka sosai husna tayi wanda ta saka umma kukan da bata yi niyyar yi ba,kukan husna ya dawo ma umma da memories dayawa,da kyar aka samu aka babbare su daga jikin juna abin gwanin ban tausayi donmin sai da wasu suka zubda hawaye suma. Amare dai kowanne an kaita gidanta, yanzu sai dai ayi masu fatan alkhairi sannan kuma ayi musu adu’ar Allah ya tona asirin amarya da ango.
Pls vote,comment and share
Tankx love you xoxoxox m
💋💋💋💋💋💋💋💋
💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔💔
💔💔💔💔💔
💔💔💔💔
💔💔💔
💔💔
💔
Allah ya umma naji dadin da kika zo,duk da nasan ba waje nah kika zo ba kam,dariya umma tayi sannan tace,inji waye wai ba wajanki nazo ba,ni da yau yini zanyi agidanki,dariya batool tayi sannan tace babu wani ai hamymy nah ya gaya min cewa zaki zo ki duba anything important acikin kaya kin nan sannan sauran za’a bayar,murmushi umma tayi sannan tace hamymy koh,dariya batool tayi tare da rufe fuskarta alaman taji kunya,dariya umma tayi sannan tace ban son wani gulma gwanda ki bude fuskar dai,fira suka rinka yi suna raha kafin batool ta tashi don daura girkin rana,ita kuma umma sai ta shiga dakin maman na da dan tayi abinda ya kawo ta,tana shiga tayi ido hudu da hoton mama,hawaye neh suka zubo daga fuskarta,share hawayen tayi sannan ta zauna gafen gadon,hoton ta dauka tare da share dust din dake samansa da tissue din hannunta sannan tayi hugging hoton tare sakin ajiyar zuciya,i really miss you maaaah ta fada,ajiya zuciya tayi tare da ajiye hoton saman gado sannuan ta fara bude side drawers tana fito da kayakin dake ciki,wayarta neh yayi kara,ajiye tarkacen dake hannunta tayi sannan ta dau wayar,sunar husny baby ta ga ya bayyana murmushi tayi sannan ta dauka tare da cewa amarya agidan Aliyu hydar,murmushi husna tayi sannan tace ya umma ina yini don bata son biye mata ,lafiya klau ya gida ya rashinji,husna tace Alhamdulillah amma ai yanxu na dan rage rashinji,baby gaya ma ya umma na daina rashinji ta fadama ma bobby dake kusa da ita,au daman bobbyn na nan neh umma ta tambaya,dariya husna ta kuma yi sannan tace yanxu nan ya dawo,daga ido umma tayi taga karfe sha biyu da minti goma dai dai,saka wayar handfree tace ma husna,bayanta sa wayar a handfree neh umma tace bobby,susa kasan yayi sannan yace na’am ya umma ina wuni,share gaisuwar tayi sannan tace bobby kaje aiki yau kuwa,wani irin kallo yayi ma husna alamon zan kamaki ai,sannan yace uhmmmm ya umma yau na tashi da ciwon kai neh sai sa ban samu zuwa ba, girgiza kai umma tayi hade da murmushi kafin tace ka manta abinda kace ranannan a garden,cewa fa kayi zaka shiga nextlevel so ya kamata kayi taken nextlevel serious ka daina biye mah husna,insha Allahu ya umma ya fada ataikaice.Okay yayi kyau,sannan hajiya amarya adaina barin maigida a house abarshi yaje aiki,murmushi husna tayi sannan tace kai ya umma gwanda na hana shi fita fah ranan saturday zan koma school don zamu fara exams monday kinga zanyi missing dinsa,ooooooooh ni rahmatu,husna haka kika koma,toh kinfi karfi nah kam yanxu, dariya husna tayi sannan tace ya umma idan na dawo zaki zo koh ta fada don kawar da wannan zancen,tab ai ni da gidanki sai nan da shekara daya,kai ya umma kinga baki taba zuwa bafa,dariya umma tayi sannan tace yaushe kikayi aure wai,jibi two week fah,ni dai ya umma ban yarda ba,naji dai sai anjima am busy sef,toh ai anjimar zan kira ki,toh naji bye bye.
sallah ta tashi tayi don taga lokaci yayi, kafin nan ta karasa har hada kayan,ta ware wanda tasan zasuyi amfani dashi sauran kuma zata ba baba mai gadi. Tana gamawa ta saka wanda take so cikin akwanti daya sannan tasaka ma husna itama acikin akwatin daya sauran kayakin kuma ta zuba shi cikin katon ghana most go sanman tayi zipping dinsa.
Falour ta dawo ta zauna tare da kiran faiza,bayan ta amsawa wayar neh tace mata,tayi mata parkaging din one park of scotched egg and samosa zata biyo ta amsa,sannan ta katse wayar,sallamar ammar neh yasa ta dago kai daga har hada kayanta da take yi,murmushi tayi sannan ta amsa sallamar tare da mai sannu da dawa,amsawa yayi sannan suka gaisa,ana cikin haka batool ta fito daga dakinta tayi wanka ta chaza kayanta,murmushi umma tayi sannan tace bari na wuce ni kam,ammar yace tun yanxu,kallonsa tayi da mamaki sannan tace tun nine (9) nake gidan nan fah,sannan zan je na amsa sako wajan noor kafin naje bakery,kuma ina azumi haka ma ammy kuma nayi mata alkawarin zan mata girki yau,tab yanxu ya umma azumi kike ranan da zaki zo gidan nawa,murmushi umma tayi kawai,batool tace nima dai hakan na gani,haka dai suka dan taba fira kafin suka tashi suka rakata parking lot ta shiga mota ta tafi.+
Sannu fah ya kalleta bayan da ta kashe wayar,murmushi tayi sannan ta matso kusa dashi tare da zagaye hannunta awuyarsa sannan tayi kissing din lips dinsa ataikaice kafin ta dago ido ta kallesa,shima kallonta yake,magana ta fara yi a shagwabe,ni meye nayi kawai don nace zanyi missing dinka,lumshe idonsa yayi sannan ya kara matso da ita kusa dashi kamar zai mai data cikin jikinsa sannan yayi magana muryarsa kasa kasa,jaan do you want to drive me crazy neh,murmushi tayi mai wanda hakorinta ya nuna sannan tace i will love that if only you are going to be crazy about me,tana gama fadar haka ta hade bakinta da nashi,sumbatar juna suka rinka yi suna romancing juna,niko dana ga abin yafara wuce romance da kiss na dauki yan matan kafata na fita tare da rufo musu dakin.
Ni fa Mamy dambun shinkafa zanci yau babu wani tuwon da zanci,sai nayi mah ammy da abba aha,yauwa yar gari cewar ammy,nima dai na gani kawai muyi azumi mu kama cin tuwo ai wannan is not possible,dariya Abba yayi sannan yace halinku daya da ammyn naki ai,murmushi tayi sannan tace yauwa abba nextweek idan ammy ta tafi zan bita nayi oneweek sannan na dawo saboda lokacin za’a fara registration,wani course aka baki neh mah,Accounting neh okay yayi kyau Allah taimaka, ameen suka fada baki daya.
LAGOS💋💋
Ammy wannan mai aikin taki ta fiye iyayi wallahi,ni dai ta daina dafa abinci dani,sannan kitchen din kamar nata babu daman mutum yashiga sai ta fara mai kallon hadarin kaji,dariya ammy tayi sannan tace idan dai shaila ce sai dai hakuri nema wani lokacin haka take min,haka take kamar wata mai juju amma idan kun saba shi kenan tab aikuwa baza mu saba ba,dariya ammy tayi sannan na cigaba da bata labarin yadda suka hadu da abbu a dubai da haukar da tayi,dariya ammy ta rinka yi sannan tace you are just like Aisha wallahi,murmushi tayi sannan ta kwanta saman kujerar ta daura kanta saman kafar ammy kafin tace i miss her so much wallahi,shafa gashin kanta ammy ta rinka yi ita kuma ta sauke ajiyar zuciyar,mintina kadan ta leka fuskarta taga barci take murmushi tayi tana aiyana wani abin a ranta,kallon sunna tv ta cigaba dayi idan abin ya fado mata arai tayi murmushi,wayarta ce tayi kara,video call neh kuma rushd neh,picking yayi sannan suka gaisa suna ta magana cikin larabci,ido umma ta bude sannan tace ammy ke da waye,juyawa tayi ta kalleta sannan tayi mata alama da hannu ta matso,matsowa tayi ta kalle tab din,ido hudu sukayi wanda ya saka gabanta faduwa,kare mai kallo take yana kama da abbu sosai,as in carbon copy but yafi abbu kyau sosai,ammy neh ta dawo da ita daga tunanin da ta shiga,yayanki neh,kallon ammy umma tayi sannan tace ammy wannan neh yaronkin ta fada with wide eye,baki abude,kallonta yayi cike da mamaki,azuciyarsa koh tunani yake mai take nufi da wannan tambayar don yadda ya gan tayi da fuska kamar bai kai matsayin ta haife shi ba,kasa hakuri yayi sannan yace me kike nufin da hakan,ido ta gwalo wajen,azuciyarta tace wai daman yana jin hausa,wallahi wani zai ce koh A bai sani ba da hausa,kallon rainin wayau da yake mata neh yasa ta saita kanta don itama ta raina mai hankali cewa tayi,gani nayi ka fiye girma dayawa,gira ya daga mata alamon bai gane ba,azuciyarta tace dan rainin wayo ina daidai da kai,ma’ana ka fiye tsufa,dariya ammy take yi don tasan kam bazasu shirya ba tunda taga kallon da suke ma juna,juyawa umma tayi ta kalli ammy ignoring din mugun kallon da yake mata sannan tace ammy bari naje na dafa noddles don bazan iya cin abincin yar rainin hankalin nan ba,ita bazata tambaya mai mutum yake son ci ba kawai sai ta kama tayi mana wani jagwalgwalo,girgiza kai ammy tayi sannan tace okay,juya kai ammy tayi tana kallon rushd wanda ya hada girar sama da kasa shi adole fushi yake,ammy wallahi ni bazan yarda ba haka kawai ta gani dan yaro sabon jini dani tace wai nah tsufa,dariyar da ammy take rikewa neh ya kufce,sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru shi ko rushd ya shaka,kallonsa tayi sannan tace laifin wa toh jifa yadda ka ajiye gemu kamar wani mai zan kira ma ban sani ba,sai sa baka son zama a nigeria don ka bar gashin nan kamar yan kasarku, kuma kai baka barinsa kadan sai ka barsa yawani cika fuskarka kamar wani gwagwon biri,kai ammy wallahi kin daina sona,nama fasa dawo wan tunda baki sona,dariya tayi sannan tace nasan zaka dawo cos you are misaing meh ta fada tana murmushi arrrrrrrrgn yayi groan sannan yace idan na dawo na sameta sai na balla kafarta kam,dariya ammy tayi sannan tace,good choice don kuwa kai zan bari da jinya nima nayi tafiya ta sudan,haka suka rinka fira kafin daga baya suka yi sallama.
Basmy longest time,yakike ya kano ya kwana biyu,wallahi i really miss you,babu wani cewar basma,bayan baki neme ni ba,baki da mutunci fah,am so sorry wallahi abubuwa neh suka min yawa fadar umma,okay naji whatever na turo miki invitation card din biki nah ta email,saura karki zo,ni na isa yaushe neh bikin,in two week tym neh,okay shi kenan Allah ya kaimu,dole mah nazo daman i have unfinish business a kano sef,hayyyyy bikina zaki zo ba yin wani unfinish business ba,lol madam chill ayi naga za’a gama bikin naki koh,toh zan yi business din nawa after that so chill,haka suka rinka fira daga baya sukayi sallama bayanta ce mata zata turo mata asoebi dinta ta whatsApp.
Vote ad comment
Pls share
Love you all lovelies
💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓
💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓
💓💓💓💓💓💓💓💓💓
💓💓💓💓💓💓💓💓
💓💓💓💓💓💓💓
💓💓💓💓💓💓
💓💓💓💓💓
💓💓💓💓
💓💓💓
💓💓
💓
Ammy Abdulhakeem yazo zamu wuce,toh shi kenan sai kun dawo,falo ta shiga bayan ta dauko jakarta da mayafi,let go tace mai tana murmushi,bayan sun shiga motar neh har ya fita daga gidan ya kama hanyar Beach neh yace mata you look spectaculous,murmushi tayi sannan tace thank you,so wat do you tink about mah proposal ya tambayeta,why are you making it seem like a job offer,dariya yayi sannan yace rahma kina da abin dariya wallahi ya fada da gurguwar hausarsa,kallonsa tayi sannan ta juya ta kallon titi,tabbas abdulhakeem kyakyawa neh nah karshe ga ilimin addini da boko,sannan ga hakuri da kamala,very respectful,duk da mahaifiyarsace bayarabiya mahaifinsa bahaushe,amma duk tongue dinsa nah yarbawa neh sai dai kana ganinsa kasan bahaushe neh,his funny n caring amma tambayar anan shine ina sonsa kuwa,eh toh zan iya cewa ina sonsa amma dai bansan koh ya kai karfin ko ince zai iya kai matsayin har muyi aure ba.Kallonsa ta sake yi sannan tace,were are we going today,murmushi yayi sannan yace beach,wow tace sound like fun,tayi hqkan neh don ta bagar da wannan maganar,haka suka rinka magana suka share wannan zancen,da suka kai beach din mah,drink suka siya suka samu waje suka zauna suna fira suna sha ,cameranta ta fito da,duk abinda taga is interesting sai tayi capturing,haka ta rinka daukansu hoto ita da shi,shima wayarsa ya fito da iphone 11 pro max ya dinga daukarsu hoto,sai wajan karfe shida suka bar waje,biyawa sukayi ta wani eatry sannan suka ci abinci kafin tayi takeaway din icecream da bugger,siya mah ammy pizza tayi,murmushi tayi don yadda tasan mama mah taken son pizza,halin ammy da mama kusan daya sai dai babbancinsu ammy tafi mama raha ita mama ta fiye fada,murmushi ta karayi,biyan kudin abdul yayi sannan suka bar eatry.+
ammy nah dawo ta kwala mata kira bayan tayi sallama sannan ta zauna saman sofa, tare da ajiye kayan saman center table,shaila ce ta shigo falon,sannan take ce mata ai ammy ta fita amma tace yanxu zata dawo,oakay kawai tace ba tare da ta kalleta ba don bata son raini,ta kula yarinyar akwai rainin hankali kawai don taga ita ba yar naija bace,toh ba da ita za’ayi iyayin nan ba,tana wannan tunanin tablet din ammy ya fara kara,mike wa tayi ta dauko shi wajan dake charging,ganin da tayi rushd neh yasa zata bayyarda ko mai ta tuna neh ta koma ta zauna da wayar ahannunta,kaara wayar ta fara yi kuma,gyara zama tayi sannan ta amsa,ganin fuskarta da yayi neh yasa ya sha mur,dariya tayi kasa kasa sannan tace su kumurci kenan,meye kika ce,murtuke fuska tayi sannan tace babu komai,kallon ta yayi yana analysing dinta sannan yace ina ammy,kallonshi tayi azuciyarta tana cewa dan iyayi da na zata baza ka tambaya bane da kaga rashin mutunci kuwa,ta fita ta fada atakaice,ina taje i dont know tace,azuciyarta kuwa cewa take yanxu zai dame mutum da tambaya kamar wani makaho,ni kuma ummeeter nace toh ai makahon neh tunda ba akasar yake ba kuma bai san gaibu ba,katse mata tunaninta yayi da wani tambayar,bata gaya miki idan zata jeh ba kenan,aaaaah am finish nah jamb question neh ,wai ba yanxu na amsa wannan tambayar ba,toh bansan idan taje ba saboda nima yanxu na dawo ta fada,wani mugun kallon ya mata sannan yace ke duk idan kika je sai kinyi yawo neh,dariya ma ya bata toh mai zai hanata fita taga gari bayan Allah ya wadata mata idanuwa ganin wajaje,murmushi tayi na gafe baki sannan tace toh so kake na zauna indoors kamar wata matar aure,pls ooooo am single not married,i see ai baki sannan garin lagos ba tunda baki taba zama ba,eh basan garin ba amma ai abdulhakeem ya sani kuma yana kai ni ina ganin wajaje ai ta fada tana jujjuya idanuwa wanda ya kara harzuka shi,waye kuma abdulhakeem,yaron friend din ammy mana Anty bisola,au wannan,shiru yayi sannan yace mai ke tsakaninki dashi,kallon kasan ido tayi mai sannan tace mai ruwanka da abinda ke tsakanina dashi,murmushi yayi sannan yace ina son nayi saving dinki daga heartbreak neh domin anty bisola bazata bari ki aure yaronta ba,mamaki neh ya cika umma,akan meye ta tambaye shi,saboda baki kai matsayin haka ba,abinda ya fada ba karamin bata mata rai yayi ba amma sai ta danne fushinta ta ce masa meye kake nufi da hakan,murmushin mugunta yayi sannan yace saboda babu wanda zai bar yaronsa ya auri wanda bata gama university ba,dakikiya sannan kuma mara kamun kai,hawaye neh wanda bata san lokacin da ya zubo mata ba taji shi afuskarta,kallonshi tayi bayan tadago idonta wanda yayi jawur don wani irin zuciya daya taso mata,murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace,masha Allah,ya Allah na gode da kake nuna min masu sona da wanda basu sona,bari kaji wani abu rushd wallahi wallahi ni nafi karfin kace min jahila,ba alfahari ba amma bazaka taba kamo kafata ba domin na maka zarra,mai ka sani akan duniya,mai ka sani akan rayuwa,babu,saboda haka baka da wani right nayi judging dina,kuma kana kallo zan auri wanda yafika,ni ko kamarka banso,kuma dana ce wanda yafika ba wai ina nufin,kudi ko kyau ko iliminka mara amfani ba,ina nufin mai hankali,mai ilimi wanda yake amfanin dashi ba mai ilimi amma kuma bai da babbanci da jahili ba,ajiya zuciya tayi hawaye na zuba mata,sannan tace duk wannan da kake gani ta fada tana nuna falon da hannunta,aduniya zamu barta sabida haka kwata kwata bata ban sha’awa bata gabana,sannan kuma idan dai sunana rahma toh insha Allahu na fita harkanka har abada kuma wallahi da sannu zakayi dana sanin furucinka,dana sanin da kuwa bai da amfani domin daga yau bazaka sake ganina ba,abu na karshe kuwa shi bazan iya cewa zan yanke alakata da ammynah ba akanka don Allah ya bata da mara tunani amma ka sani girmanka da nake gani ya zube,tana kai nan ta ajiye wayar ta shige daki tare da kulle kofar,ammy da tun tuni ta dawo tana jin sa’in san su,jikinta duk yayi sanyi,daukan wayar tayi tana kallon rushd wanda shima duk jikinsa yayi sanyi, bai so barin anger dinsa yayi taken the best of him ba,ajiya zuciya yayi sannan ya dago kai yana kallon ammynsa,kallonsa ammyn itama take,sannan tace yanxu kai abinda kayi ya dace kenan eh ta tambaye shi,fuskar tausayi yayi sannan yace ammy wallahi i didnt mean too,ammy help me out,girgiza kai ammy tayi sannan tace,rushd at this moment i cant,kayi reopening din old wound,umma went through alot,kasan labarin yadda akayi na auri first husban dina ai,so tun lokacin da aisha tayi aure babu wanda yake zuwa wajanta,ni nayi aure bana jin dadin zaman gidan mijina,abubuwa sun min yawa saboda haka i could not reach her,lokacin dana bar gidan almustapha kuma da shekara daya na hadu da abbu dinka,domin shi frnd din therapist dina neh,so after two month da haduwarmu muka yi aure na bar naija,saninka abbu dinka ya taba aure sannan yana da yara biyu,kai kasan dagin babanka ba sona suke ba,sai sa na dawo nigeria don bazan iya jure kyarata da ake ba,but umma babbanta ya rasu tun tana karama aisha kuma daman bata yarda ta gama makaranta ba tayi aurenta,bayan aure kuma bata cigaba ba,so umma ita take dawainiya da gidan,duk da aisha ke providing abinci cinsu,but ita umma want her sibling to go too school tunda ita baza ta samu zuwa ba,shi paid ammar school fees and n husna’s own too,ko ni dinnan ai cant do what she did,labarinta abin azubar da hawaye neh,yanxu da she has finally set her self free from all reponsiblities shine tayi appyin a baze university,yanxu ka gaya min taya zan fara lallashinta,ajiyar zuciya yayi duk bai ji dadi ba,ammy wallahi i didnt mean to hurt her,she was just annoying me kawai sai nayi loosing cool dina,am so sorry wallahi,rushd for now just stay away from her kawai,kuma na tabbata kafin ta kara zuwa gidana sai idan baka lagos wanda nasan idan ka dawo kafin kaje wani country course kuma sai kayi shekara idan ba turaka dubai zanyi ba don naga ‘yata ba toh i dont know,ajiyar zuciya kawai yayi,murmushi ammy tayi sannan tace kada yasa komai azuciyarshi with time zata manta ta yafe mai,but tasan zai dau lokaci kam amma zata taya shi bata hakuri,kokari tayi tana jan shii da surutu don ya dan saki ransa kafin daga baya ta ajiye wayar.
Umma kuma tana shiga daki gado ta fada tayi kuka mai isarta kafin ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuska,alwashi ta dauka ta daina barin maganan mutane suyi effecting dinta.Sallar magrib tayi sannan tayi isha kafin ta fito,afalo ta iske ammy tana kallon peace tv, murmushi tayi mah ammy tare da tambayarta yaushe ta dawo,murmushi ammy tayi itama sannan tace tun dazo na dawo,naga pizza kuma na cinye,dariya umma tayi sannan tace daman naki neh,ammy ina ice cream dina,yana fridge shaila ta zuba,lallai kam shaila yau tayi abin kirki,itama ammy dariya tayi sannan tace tana ganin kayan take cewa akwai na sakawa afridge neh nace eh ta saka ice cream din,lallai kam,yauwa yau spag tayi so sai ataimaka mah abincinta,lol ammy kenan to bari na zubo mana sai muci tare koh muna kallonmu,murmushi ammy tayi yadda taga ta saki ranta abin ya mata dadi,kawo musu abincin tayi suka ci tare da wani drink da shaila tayi wanda itama bata san meye shi ba amma tayi alwashin koya don yayi mata dadi,bayan sun gama ci ta kwashe kwanunkan sannan ta dauko ice cream dinta,suna kallon zee world tana shan abinta tare da burger dinta,saisa mah taci abincin kadan.karfe goma ta ma ammy sallama sannan ta wuce daki don ta kwanta.
Mamy ina nan hanya yau kiyi min special,toh shi kenan sai kin dawo. Junainah mah tace tana ta kiranki baki dauka ba,ina sane mamy wallahi sababinta zatayi min,idan na dawo mayita da hujja,okay toh flight din karfe nawa zaki bi,na karfe biyar neh,okay toh sai kin zo.juyawa tayi ta kalli ammy wanda ita take kallon murmushi tayi sannan tace seriously ammy registration zanyi sannan kuma zanje kano biki amma idan nayi hutun first semester zan zo miki hutu,murmushi tayi sannan tace promise,tace promise,okay toh.haka suka rinka fira abinsu har lokaci tafiyarta yayi,ammy neh ta rakata airport,karfe biyar da minti biyar jirginsu ya tashi sai garin abuja.
Comment n vote
Tanxxxxxx
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Fitowa take daga airport tana jan jakarta hannunta rike da hangbag dinta da waya,kalle kalle take idan zata hango mamy,ji tayi ta bige mutum wayar hannunta ya fadi kasa,Ooops my baby,tayi fuskar tausayi sannan ta tsuguna ta dauki wayar,tana dagowa taga screen dinta duk ya farfashe duk da screen guard din,daga kai tayi ta kalle mutum da ya tsaya kamar kungi yana kallonta,waving hannunta tayi afuskarsa sannan tace bawan Allah lafiya,ajiyar zuciya yayi sannan yace mata Dan Allah kiyi hakuri ina sauri neh zan kama flight dina zuwa lagos in the next twenty minutes kwata kwata ban ganki ba,murmushi tayi sannan tace babu damuwa kayi sauri karka rasa flight din,murmushi ya mayar da mata sannan yace,okay toh thank you ,har ya kama hanya zai wuce ita kuma ta tsaya saka wayar cikin jakarta ta fito da karamar don kiran mamy,Baiwar Allah baki gaya min sunanki ba sannan dan Allah ko zaki iya ban number dinki,kallonsa tayi nah kusan second ashiri ba tace komai ba tana nazarinsa kafin tace sunana rahma,sannan ta basa number dinta,cewa yayi ya gode tare da gaya mata sunansa ismail,kafin ya wuce yana sauri sauri kallonsa tayi sannan tayi dariya tace bari dai kaje ka karya kafa,juyawar da za tayi kawai sai taga mutum agabanta,ba karamin tsorata tayi ba,jikinta duk akame yake,dariya ya fashe dashi,ita koh ahankali ta fara bude ido ta zuba su akan fuskarsa,tsaki tayi sannan tayi ajiyar zuciya kafin tace wallahi sai na gaya ka da mamy,dariya ya rinka mata suna tafiya yana jan jakarta,daman wani iyayi yasa ka wani zo daukata ta kara fada tana murguda baki,dariya yayi sannan yace nah you sabi,data ga ya mayar da ita mahaukaciya ma banza dashi tayi sannan ta cigaba da danna wayarta,msg ta gani daga unknown number,shiga tayi taga wasika aka turo mata kamar haka….
Salama alaikum yake maabociya kyau,naso da ba a irin wannan circumtance din muka hadu ba,but naji dadin dana same ki da saukin kai,sannan ina fatan zaki bani daman sake ganinki da kuma saninki sosai.
………Ismail turaki……..+
Murmushi tayi sannan ta girgiza kai kawai,kallonta mukhtar yayi sannan yace yadai,banza dashi tayi don har yanxu haushinsa take ji,wayarta neh ya fara ruri,dagawa tayi ta ga junainah neh,ooooh ni rahma tace sannan ta amsa da sallama,bayan junainah ta amsa neh ta kuma dora wa da cewa wallahi ni babu ruwa na dake,,,,,,,katse ta umma tayi da cewa sannu sarkin korafi,wato ke baki rasa abin fada koh wallahi kin fiye hayaniya haba,kuma dai menene cewar nainah,ai kinsan baki da gaskiya neh sai sa,dariya umma tayi sannan tace Allah ya huci zuciyarki mata agidan doctor sadeeq,murmushi nainah tayi sannan tace uhmmmm dont try to manipulate me kam,domin fushi nake,ki dai yi hakuri zanzo gidanki ranan monday idan na gama registration da sauri,okay Allah dai yasa ameen kawai umma tace don bata son jan zance da yawa,murmushi tayi bayan ta kashe wayar sannan tace wannan matar big case ce,ajiyar zuciya tayi kawai,shima dai mukhtar din bai amsata ba don yasan ba dashi take ba,ko yayi magana ba amsa shi za tayi ba,dan Allah ya mukhtar tsaya coldstone na siya ice cream,tsayawa yayi don shi kam sulhu yake nema,tare suka jera suka shiga,ice cream ya siya mata four cups kuma different flavour,sannan suka karasa gida,mamy neh ta rugumeta da ta fito daga motar tana mata sannu da hanya sannan suka karasa cikin gida suka bar mukhtar da akwati,zama sukayi suna ta fira kaman sun shekara basu hadu ba sannan daga baya ta shiga daki tayi sallar magrib kafin ta shiga wanka,tana fitowa ta shafa lotion dinta da turarukan jiki kafin tayi sallar isha don har an kabbara a masallancin layin tana taji,bayan ta idar neh ta wuce falo sukayi dinner,tana ci tana santi tana cema mamy tayi missing gida domin chan sai wani abincin larabawa ake,ita kuwa baza ta iya cin wannan kayan jagwalgwalo ba,dariya Abba da mukhtar suka rinka mata,mukhtar na cewa matsalar kai yan kauye birni kenan,dariya tayi taje eh taji,haka suka ci abincinsu cikin jin dadi daga baya kowa ya tafi dakinsa,barin ma umma da ta gaji,tana zuwa dakinta alwala tayi sannan ta hau saman gado,wayarta neh ya fara kara,Allahu akbar,wanene wannan neh,tashi tayi ta dau wayar tare da amsawa,amincin Allah ya tabbata agareki tare da ni’imoninsa,murmushi tayi azuciyarta tace wannan wani dan sabon dan kakale ne nasamu,ameen tare da kaima ta fada ataikaice,nasan baki gane wa ke magana ba,ni sunana ismail turaki,murmushi tayi sannan tace okayyyyyyyyy nah tuna kam yanxu,yaaa ka isa lagos din lafiya,lafiya lau Alhamdulilaah,ya gida ya iyayenmu ya tambaya, duk lafiya tace masa,masha Allah nasan barci zakiyi don kin gaji so bari nah barki ki kwanta daman dai ina son naji muryarki neh kafin nima dai na kwanta.Murmushi tayi sannan tace ta gode sai da safe ta fada ataikaice kafin ta ajiye wayar,addua tayi ta shafe jikinta sannan ta kwanta barci.
STORY CONTINUES BELOW

💋MAFARKI💋
Wani laifi nayi neh kake juya min baya yau,gani nayi kina son kiyi min kishiya,dariya maganarsa ya bata amma ta dake tace,ban gane ba,taya zaayi na ma kishiya bayan……Shiru tayi ta gagara karasawa don bata son furta kalman nan,juyowa yayi ya kalleta sannan ya girgiza kai tare da cewa bazaki fada ba kenan,kallonsa take kawai,ajiyar zuciya yayi sannan yace idan har kika min rival kin daina ganina kenan fah,hawaye taji yana sauko mata ita dai tasan tana sonsa amma taya zata tayin taraiya da aljani haka kurum,gaskiya bazai yiyu ba dole kam tayi soyayarta da duk wanda yace yana sonta,idan ya ga dama ya tafi mana ai tafi son haka,juyawa yayi yayi tafiyarsa abinsa,kallon bayansa ta rinka yi har ya bace daga ganinta,zama tayi a lambu tana kuka.
Farkawa tayi don an fara kiran sallah asuba,dira daga saman gado tayi ta garzaya bayi duk ji tayi kanta na mata ciwo,kallon fuskanta tayi a mirror,ganin jirwayen hawaye tayi afuskarta,wai daman kukan gaske tayi neh,mamaki take yi,alwala tayi sannan ta fito tayi sallah,tana idar wa tajawo quraninta ta fara tilawa,sai da gari ya waye tayi fes sannan ta ajiye ta fada bandaki tayi wanka tana fitowa tayi shafarta sannan ta saka straight skirt dinta da crop top,sannan ta taje gashinta ta kama da ribbon kafin ta saka hula,zama tayi gefen gadonta sannan ta jawo wayarta,kwakwata ma ta manta ya fashe,ajiya zuciya tayi sannan ta aiyana aranta idan tayi breakfast zata plaza ta siyo sabon waya don ita baza ta iya amfani da wannan fasashen wayar ba,karamar wayarta ta dauka don ta kira mai dinki ta ta tambaya koh ya gama mata,msg din ismail ta gani.
Salam,da fatan kin tashi cikin koshi lfy,dan Allah ina son jin muryarki idan kin tashi kiyi min flashing pls.
ismail turaki
Dariya mah abin ya bata wai flashing,ignoring dinsa tayi ta kira mai dinki,bayan sun gaisa yace mata ya gama tace zata zo ta amsa yanxu yace toh shi kenan,kallon agogon bangon daki tayi taga karfe tara da rabi,kimono ja mai ratsin lemon green ta dauko sannan ta hada da lemon green mayafi da black flat shoe tare da side bag dinta ta fito,dinning ta wuce ta bude flask taga fried yam neh da egg sauce ga kuma ruwan tea,kitchen ta shiga ta dauko bread don ita ta tsani doya sosai, tea ta hada sannan ta diba egg sauce din ta hada da bread din taci sannan ta sha maganin ciwon kai, tashi tayi ta shiga dakin mamy wanda itama yanxu ta gama shiri,mamy ina kwana ta gaishe ta,da fara’a mamy ta amsa sannan tace fita zakiyi neh,eh mamy zanje na amso dinki nah sannan zan biya bakery daga nan kuma zanje wajan momy mah nah gaisheta so dont miss me too much,murmushi mamy tayi sannan tace toh adawo lafiya sannan kiyi addua fah,insha Allah mamy sai na dawo,toh sai kin dawo mamy ta fada ataikaice……..
Amma yunusa kana ganin wannan zai shigeni neh,kasan na kara kiba fa anya bazai matse ni sosai ba,kasan bana son kayan daya matse ni fa,eh na sani but kince na miki irin na yayi sai sa na miki irin wannan kuma nasan zai yi fittin dinki sai sa,toh shi kenan tun da kace haka,yaushe zanzo na amsa material din nan kenan,gaskiya dinki yayi min yawa ya fadi mata, ya za’a ayi kenan,ni dai kayi kokari kayi min ranan friday fa zanyi amfani dashi,kuma kasan dinkinka kadai ke zama min ajiki da kyau,uhmmmm okay zan gani dai zuwa thursday kizo ki amsa,kai a’a yunusa zan dai zo wednesday,bikin fah akano neh kuma thursday nake son tafiya da safe saboda zan biya makarfi kayi hakuri kamin kafin dai thursday dinnan dai,toh shi kenan Allah ya kaimu wednesday din,masha Allah toh nawa kudinka,seven thousand neh,toh shi kenan zanyi ma transfer,toh shi kenan,sai na zo amsa,aha sai kinzo ya fada sannan ta wuce.
Wallahi sai sa nafi son aiki da masu kudi kana fadi suke baka basa tsayawa wani ja’in ja amma wasu musamman mutanen kaduna akwai son tayi wallahi,dariya sadeeq yayi sannan yace oga yunusa baka da dama,wannan mah da ita customer dinka ce amma baka rage mata koh kwandala,a’a toh ita ai harkan big garl suke ai,baka ga family dinsu yadda suke ba,kamar ba yan naija ba,kalla fatar jikinsu fa,tab barni na samu nawa nima,dariya yaran shagon duka suka yi suna mamakin son kudin ogansu.
Momyyyyyyyyyyyy ta kwala mata kira dagaa falo,mamy da fito wanta kenan daga kicin tace wa nake gani kaman mutanen lagos,dariya umma tayi sannan ta rungume momy,gaisawa suka yi ta tambaye ta mutanen lagos,nan dai suka bige da fira tana bata labarin kiriniyar yaran aunty rahma suna yi suna dariya,wayarta ne ya fara kara,oooh ni umma na zama business center ta fada momy na mata dariya,jakarta ta dauka don ta lalubo wayarta,bayan ta dauko neh taga ismail neh,dauka tayi tare da sallama,bayan sun gaisa neh yake tambayarta ko taga msg dinsa,da har zata ce bata gani ba sai kuma tayi tunanin mai amfanin karyan,ce mishi tayi ta ganin amma lokacin tana wani abu neh sai sa bata kira ba kuma daga baya ta fita so duk ta manta,bai ji dadi ba amma bai nuna mata ba,fira suka dan taba sannan yake gaya mata shi dan jigawa neh amma yana zama neh a kano,ya taba aure amma matarsa ta rasu sannan yana da yaro daya sunansa Aliyu amma yana kiransa amir saboda sunan mahaifinsa neh,haka dai suke ta fira daga baya kuma suka yi sallama,momy wanda tunda ta fara wayar ta mai da hankalinta kan gidan talabijin din neh ta juyo tare da cewa nayi siriki kenan,dariya umma tayi sannan tace kai momy,a’ah da gaske nake mana, murmushi umma tayi sannan tace momy ina autan naki,dariya momy tayi don tasan topic din take son chazawa,sun tafi coldstone amma na san yanxu zaki gan sun dawo,ana cikin fadan haka sai ga umm khairi ta shigo ranta abace tana momy wallahi ki shiga tsakanina da abul……..maganarta makale wa yayi ganin umma,zare ido tayi sannan tace yaushe kika dawo ni dana ke shirin binki lagos,dariya umma tayi sannan tace jiya na dawo,lagos din ya ishe ni,ice cream ta mika mah umma,karba tayi don itama mayyar ice cream ceh,abul neh ya karasa shigowa yana d biggest sisisi my one and only everylasting love,tabe baki momy tayi tana kallon ikon Allah,dariya umma tayi sannan tace abulkhair poet kake son zama neh,i thought science kake,saurin chafkewa ummulkhairi tayi sannan tace da wannan fish brain dinsa neh zaije wani science ya nan a art,wai shi theatre and performing art zai karanta,uhmmmmm naga alama kam,kumbura fuska abul yayi sannan yace wallahi yarinyar nan zan ballaki,ka ballani ina yayarka,tsaki yayi ya juya ya kalle mamy wanda ta mayar da hankalinta tv abinta domin duk wanda ya biye ma biyun nan shan kunya zai yi,momy kina jinta koh wai waya ce ki gaya mata waya fara fitowa neh mah,banza dashi momy tayi,haka dai suka dinga arguement,ita ko umma dariya ma suke ba ta don shirme suke fada akai,karfe hudu da kwata ta bar gidan bayan tayi sallah.Plaza taje ta siyo waya,tama rasa wanda zata dauka kawai sai ta dau iphone 7 plus,mai shagon neh yace mata ai akwai lastest din wato 11pro max,baki ta tabe sannan tace wannan mah gwada wa zanyi da zaran bai min ba zan dawo na siyar ma na karbi karamar wayata dai dai ni…………
Su umma an siya iphone,toh maisa baki siya 11pro max ba,ce maka akayi ina da kudin neh ta fada tare da murguda mai baki dariya mukhtar yayi sannan yace toh shi kenan ki fara using wannan kafin Allah ya hore sai na siya miki,koh kallansa bata yi ba don ta gane raina mata hankali yake don yasan tana da kudin siyan abinda yafi 11pro max mah.
Dariya tayi tace wallahi mutanen twitter akwai iya bada savage answer kalla fa ta nuna mai sannan suka kara kwashewa da dariya tare,ni kuma ummeeter an barni bansan abinda ake ma dariya bakuma sun ki nuna min kawai sai naji haushi nayi tafiyata abina nah bar musu gidan don nayi fushii 😀😀😀😀😀😀
💋💋Share
💋Vote comment
💋💋Love you
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟🌟
🌟🌟🌟
🌟🌟
🌟
Toh na dai nah fushi tunda rahma ta biyoni ta bani hakuri wai bai kamata na daina bibiyarta haka ba don yanxu za’a fara.shi ne na siyo sabon littafi da biro dan kar ya kare ace sai naje siyowa 😄😄😄😄😄😄😄😄😄
Longest chapter ever 💋💋
🌸Kefa ba’a iya miki tun yaushe nake gidan naki,tun sha biyu fah amma baki gode mah Allah ba cewar umma,toh ni dai dan Allah ki bari sai shida sai ki tafi nainah ta fada,ni dai kinsan bana son mijinki yazo ya sameni gidan nan don banson mu raba hali,sannan holdup ai yawa zaiyi a hanya sef kuma kinsan ina azumi, daman ke wallahi baki yi ba sai kin rinka zuwa gidan mutane ranan da kike azimi,idan ma kina yi neh don kar muci abinci agidanki toh sai munci sai dai kam idan baza kiyi aure ba nainah ta kuma cewa,dariya umma tayi sannan tace wallahi ke da batool baku da aikin yi fah,sai na korafi,eh munji din………Yanxu dai yaushe zaki kara zuwa,uhmmmmm inaga sai na dawo kano cewar umma,whatever na you sabi ta fada tare da rufe mata murfin motarta ta daga mata hannu,agaida gida,itama umma hannu ta daga mata sannan ta ja motar ta fice.+
ai naga kawu ko kaka habu zance ma oho a bikinsu noor amma yi nayi kamar bansan shi ba,nasan ya gane ni don zai ga ina kama da mama,don naga yana ta bina da ido,toh ke baza ki yafe masa bane momy tace, ai ni alokacin bani da time dinsa neh amma gobe ina zuwa kano zanje gidansa ma so ki kwantar da hankalinki zan yafe mah kawunki umma tayi dariya tana fada,ke gidanku cewar momy, dariya suka fashe da shi ita da kannenta biyu sannan suka cigaba da cin abincinsu,agidan momy zata kwana gobe zata bi ya musty wanda ita ko ganinsan ma bata yi ba amma momy tace wai tazo ta bisa,sannan abul yace tun jiya yazo amma tunda ta shigo gidan bata saka shi a ido ba,tana cikin tunani ta ji sallamarsa,sai da gabanta ya fadi,dake wa tayi don ta dau alwashin sai ta nuna mai kamar basu taba wani magana kamar na so arayuwarsu ba,sannan kuma tana so su dawo kamar yadda suke da ita da ammar ma’ana su rinka wasa da dariya abinsu,ta gaji da awkwardness din dake tsakaninsu.
Bayan ya zauna dinning ya gaida momy da dady neh,umma da twin suka gaida shi,jan twin ya fara yi da tsokana,kallanshi umma tayi sannan ta juya ta kalli momy dake shirin tashi don ta gama cin abincinta,cewa tayi momy da dai kin zauna kin mana shari’a,kallonta momy tayi sannan tace shari’ar mene kenan,tura baki tayi sannan tace toh momy kince idan naje kano na zauna gida ya musty gashi ni kuma ko kallan banza ban ishe shi ba,dagowa yayi da sauri ya kalli umma sannan ya mai da dubarsa kan momy wanda take cewa,mustapha mai ya hada ka da yar uwarka kuma,kafe shi da ido suka yi,murmushi yayi sannan yace ai bata ce wani abu ya hada mu ba sannan gani nayi ta daina min magana shine na kama kai nah,bude baki umma tayi sannan tace momy kinga na kawo kara amma yana son ya mayar da laifin kaina koh ta fada ashagwabe,murmushi momy tayi sannan tace oya gwanda dai kuyi sortin out differences dinku,saboda gidanka zata zauna bikin da zata je,kura mai ido umma tayi,murmushi yayi sannan yace momy we are cool ai babu abinda ya faru tsakaninmu,hararansa umma tayi sannan ta fara tattara kayan da suka yi amfani dashi,murmushi ya kara yi amma bai ce da ita komai ba ya tashi,don ya karasa kintsa kayansa yasa amota,don akwai shi da mantuwa,tana gama kwashewa ta yada zango falour,ummulkhairi ce kadai afalo,zama tayi kusa da ita suna kallon series din ONCE A KING AND A QUEEN a televista, shigowa mukhtar yayi ya zauna a two sitter tare da umma,juyowa tayi ta kalle shi sannan ta mayar da kanta kan,gidan talabejin din,shiko danna wayarsa yake yana murmushi,kara kallonsa tayi daidai lokacin yana murmushi,tabe baki tayi sannan ta fada azuciyarta,shi ko wannan meye yake ma dariya haka oho
STORY CONTINUES BELOW

bayan ya gama chatting din da yake neh ta juyo ya kalleta,fuskarsa babu yabo ba fallasa yace gobe karfe takwas dai dai zamu wuce so ki shirya da wuri,yana magana in a serious tone kamar yana zance da business partners dinsa,haushi abun ya bata, sai sa ko kallonsa ba tayi ba amma ta girgiza masa kai don ta san kallonta yake
shi ko mustapha yana kallon yadda ta daure fuska bayan ya gama bayaninsa abin ya bashi dariya sai ya dan murmusa,aranshi yace ya kamata nayi nisa dake don na samu nah cire sonki da nake ta dauwainiya dashi,amma sai dai kiyi hakuri da attitude dina for now ya fada aransa,haka suka rinka zaman kurame afalon suna kallo,bayan sun gama kallon wannan series dinne suka saka news suna kallo,karfe sha daya umma ta tashi ita da ummulk suka tafi daki don kwanciya,ummu kadai tayi mai sai da safe ita kuwa umma yi tayi kamar bata san da wani halitta awajan ba,don ba karamin haushi ya bata dazun ba
tana shiga daki taji wayanta na kara,amsawa tayi suka rinka fira da ismail kafin wani lokaci harta manta da haushin da mustapha ya dura mata,haka ismail ya rinka sata dariya,duk lokacin da take tare dashi sai ta rinka jin wani farinciki,duk da bai taba zuwa wajanta ba kullum awaya suke magana amma duk da haka tana ganin har ta fara son shi don duk lokacin da ya saba kiranta idan bai kira alokacin ba sai taji babu dadi,ita kuma bata son ta fara kiransa yanxu ta fisu ta tabbatar ko da gaske yake soboda bata so ya yaudare ta don bazata iya dauka ba,she has a fragail heart,sai da sukayi kusan minti talatin suna wayar su suna gaya ma juna kalamai masu dadi mai kwantar da hankalin masoya kafin suka yi sallama kowa ya kwanta.
washe gari bayan ta tashi barci ta duba lokaci taga karfe bakwai saura kwata mamakin irin barcin da tayi yau take,ko don bata sallah neh,tashi tayi ta shiga wanka,tana fitowa tayi shafarta sannan ta dauko wani purple material na riga da skirt mai flowers maroon sannan ta yafa karamin maroon gyale bayan ta daura dankwalinta,powder da kwalli neh kawai a fiskarta sai lip balm,maroon jakarta ta dauka sannan ta saka maroon weige dinta sannan ta ja trolly dinta falour,lokacin karfe bakwai da minti hamsin,samunsu momy tayi a dinning suna breakfast,zama tayi bayan ta gaishe su sannan ta hada tea tana sha,kallonta ya musty ya rinka yi,duk tayi mai kyau,saurin cewa yayi auzubillahi minal shaidanir rajim sannan ya kawar da idonsa akanta ya cigaba da cin abincinsa,ita kuwa ko kallonsa batayi ba bayan da ta gaishe shi,tea dinta take sha hankalinta kwance idan ta tuna msg din ismail tayi murmushi,momy nah lura da ita amma bata ce mata komai ba tana gama shan tea din ta dau wayarta ta kara duba msg din kafin ta rubuta mai reply,tana sending bayan minti daya sai ga kira ya shigo murmushi tayi sannan ta mike tare da amsawa
momy tayi murmushi sannan tace daga gani an sami mana suriki neh kam,dariya dady yayi sannan yace kin sama yata ido fa,ummu tace momy gaskiyarki neh wallahi momy,jiya da muka je kwanciya haka ta rinka damuna da waya,sai dana tashi na bar mata dakin,and the worst part momy idan tana waya ba kya jin abinda take fada sai dariyarta wallahi,kuma,,,,,,,,,abul yayi saurin katse ta kuma ke shegen sa ido abi,hararansa tayi sannan tace na raba da kai ne da zaka kwasa,haka suka rinka fada fadansu babu wanda yasa musu baki don sun saba,bayan minti sha daya sai ga ta ta fito,juyowa sukayi dukkansu suka kalleta,murmushi tayi kawai,momy tace har zamu nimanki faah,dariya tayi sannan tace kai momy minti goma kadai fa nayi au daman yana wuce haka kenan,hannu ta saka ta rufe fuskarta,dariya momy tayi sannan suka raka su mota sannan suka koma ciki bayan sun dau hanya
game take ta playing a wayarta,piano tiles ta saka eye piece a kunnenta tana jin music din dake playing tare da game din,data gaji da playing game din kuma ta saka wani film mai suna banshee ta cigaba da kallo daga idan ta tsaya,mustapha yana lura da ita,ita kuwa duk da ba yawan surutu gareta ba she is felling bored,deciding tayi ta kirasu husna facetime, ciro ipad dinta tayi daga jaka ta kunna data sannan ta shiga sykpe,kiran husna tayi don ta santa da barin data a kunne,elhamce ma ta dauka sannan tace,daman wayon da ake min kenan ayi ta kiran husna ni ba’a kirana abi,dariya umma tayi sannan tace afuwan ayi min uzuri,dariya tayi sannan tace babu damuwa yakike ya su mamy da momy duk suna lafiya,ina ma hanyar zuwa kano,woooo dan Allah,da gaske bikin basma mana okay har na manta,ya noor fah ita baza ta zo bane,tace sai gobe don tana da aiki a office sosai so zata shigo gobe da yamma,okay Allah ya kaimu dai,yanxu mai zaki ajiye min,dariya elham tayi sannan tace duk abinda kike so,gidana zaki sauka koh,kallo gefen mustapha tayi sannan tace momy tace na zauna gidan ya musty but zanzo gidanki yau ai kafin naje bridal shower din,ai tare ma zamuje ko.yes tare zamu so sai kin iso, husna taje karbo mana dinkinmu idan ta dawo zan gaya mata,okay no pee sai na iso.Aha
STORY CONTINUES BELOW

dambun naman da momy ta bata ta fito dashi tana ci,duk ta gaji da zaman mota sai sa bata son tafiya fah,sauke window tayi ta siya lacasera guda biyu da roban swan guda biyu,kallonta yake bai ce mata komai ba,cigaba da cin dambun nata tayi babu mai ce ma kowa komai,ita dai ta ajiye masa roban dambun nama daya da roban ruwa da lacasera amma bata ce mishi kala ba,shi daya ga bata mai magana ba kuma mutuminsa neh dambun kawai sai ya diba ya fara ci don kam ba zai iya fushi da shi ba,ta gafen ido take kallonsa azuciyarta tana cewa da ka tsaya sai na ma tayi,mtsuuuu tsaki tayi sannan tace wai me ya causing wannan holdup din nan,wallahi duk na gaji da zaman motan nan wallahi
da kyar suka samu suka wuce hold up din dake birnin yero,suna kai zaria suka biya ta city suka amso sako sannan suka wuce,karfe biyu da rabi dai dai yayi musu acikin garin kano,dukkansu biyu sun gaji,yana shiga yayi parking
fareeda neh ta fito don tarban mijinta,tana karasowa ta hango mustapha da umma,gabanta neh ya fadi murmushin da take yi ya dakushe,kallanta musty yake,don ya san za’a rina daman,juyawa umma tayi ta kalla abinda yake kallo,hango fareeda tayi tana karasowa,murmushi ta fara yi tana inlaw inlaw i hope ni dai aka zo tarba,murmushin karfin hali tayi wanda umma tsab ta gane murmushin bai kai ciki ba,amma ta dake ta cikaba da maganarta wanda fareeda ke amsa mata ciki ciki, ita fa daman sai sa bata so zama gidan nan ba amma momy wai ta zauna,ai shimfidar fuska ta wuce ta tabarma,idan fareeda ta saka rai ma kwana nawa za tayi agidan balle har ta takura mata,mtsuuuuu tsaki tayi da ta shiga dakin da aka bata amatsayin wanda zata zauna,tana shiga tayi wanka,tana fitowa husna nah kiranta,yadai matan aliyu murmushi husna tayi sannan tace yanxu zaki zo koh,eh shiryawa kawai zanyi sai na fito,dan Allah ki cema elham ta turo driver ya dauken,okay kunyi hakan da ita neh eh ita tace zata saka driver ya dauko ni idan na shirya,toh shi kenan zan gaya mata,okay bye sai na zo,aha
bayan tayi sallah azahar da laasar ta idar ta zauna tayi kwaliyarta like always ta dauko material din da aka dinka mata,dagawa tayi tana gani tace kam balai wannan zai min kuwa lallai ma yunusan nan,hala yaran shagonsa yaba dinki na,tabdi uhmmmm cire towel din tayi sannan ta saka kayan,ai kuwa mamaki tayi yadda kayan yayi mata cib cib,fitted gawon neh maroon da black mai flowers masu shinning ajikinsa,tayi zaton bazai mata ba don yadda ta kara kiba kamar wata mai ciki duk ta kumbura,ajiya zuciya ta sauke sannan ta daura black head sannan ta dauko black da maroon din karamin jaka da takalminsa sannan ta fesa jikinta da turaruka masu dadin kamshi,wayar ta dauka ta kira husna take tambaya ko akwai abinci tace a’a amma idan yunwa take ji zata daura mata indomie kafinta karaso,tace yauwa da kin taimaka,tana gama wayar ta fito falon lokacin karfe hudu da rabi dai dai,kamshin turarenta neh ya daki hancinsa da ta fito falo,daga kai yayi ya kalleta nah seconds din da bai wuce goma ba kafin ya cigaba da cin abincinsa,fareeda mugun kallo ta bita da shi aranta tana ayana irin rashin mutuncin da za tayi mata idan ta cigaba da kwaliya haka,ita ko umma kallon da suka bita da shi ya shakar da ita da har tayi niyyar musu sai ta dawo amma kawai sai ta wuce bata ce musu uffan ba,shi ma musty bai tanka ba
tana fita ta hadu da driver din har ya iso,shiga tayi suka wuce suna isa ta mishi godiya ta shige gidan da sauri don yunwa take ji,tana shiga palon elham da husna suka yi ihu suka rugume ta dariya ta rinka yi tana cewa ni dai kar ku karya ni dan Allah,ku raba ni da yarantar ku,kun girma amma sai yi kuke kamar wasu jinjiraye,kara kyalkyalewa da dariya suka yi bayan sun sake ta sannan suka kara da cewa gaskiya mu yara neh koh sisto cewar husna,girguza mata kai elham tayi sannan tace bari na karasa shiryawa altine zata kawo miki indomie,okay toh,shiga sukayi daga ciki don su shirya ita kuma altine ta karaso da indomie da soyayyar kwai n plantain hade da xobo mai sanyi,zama tayi taci tayi nak don rabonta da abincin kirki tun jiya da daddare,suna gamawa suka garzaya halimcy palace inda za suyi event din awani dan karamin hall.
basmatu amarya umma ta fada baya sun shiga wajan event din,darita basma tayi sannan suka yi hugging din juna suna firar yaushe gamo ,wayarta neh yayi kara tayi sauri dauka sannan tace basmy minti biyu bari na amsa wannan wayar,bayan ta amsa neh take gaya mai ai tana kano sannan tana wajan biki amma ya bari anjima zasuyi waya idan ta koma gida,okay nima yau na sauka akano amma kuma idan kin fito ki kirani dan Allah i will love to see you,okay babu matsala then,sallama suka yi ta koma, cikin hall din idan waka ke tashi kawayen basmy sai rawa suke haka itama basma daman akwai ta da son rawa,umma na isa ta shiga itama ana rawan da ita haka suka rinka chashewa daga baya kuma suka zauna suna ta firar yaushe gamo da cin snacks da drink dinsu sannan suka rinka selfie suna posting, karfe bakwai saura suka gama event din,basma take ce musu duk su tsaya su gaida abokan ango,friend dinta neh suka tsaya while sistas dinta suka wuce harda su husna ma don basma tace karsu damu umma zata samu ride, karasawa suka yi wani garden idan ango da abokinsa suka zauna suna fira suna dariya,ango suka ji yana cewa ai wallahi turaki har nayi tanadin irin rashi mutunci da zan ma da baka dawo daga lagos dinnan yau ba,dariya yayi sannan yace ai yanxu sai ka rike rashin mutuncin naka, sallama suka yi dukkansu,angwayen suka amsa musu,shiko turaki wayarsa yake dannawa bai dago ba,introducing din friends dinsa ango ya rinka yi sai daya kai kan turaki sannan yace and this is my best man ismail aliyu turaki,dago kai ismail yayi don yayi acknowledging present dinsu kar suce he is rude,dagowar da zai yi kawai sai ya ci karo da fuskarta,daman itama wayarta take dannawa kuma duk chatting take da shi,murmushi suka sakar ma juna,kallo kansu ya koma yadda aka gan suna kallon juna,gyaraan murya mahmud yayi angon basma,kallonshi ismail yayi sannan yace,menene,dariyar gefan baki mahmud yayi sannan yace itace hala,murmushi ismail yayi sannan ya kuma kallonta,basma tace an barmu duhu fah,mahmud yace dont worry dear zan gaya miki,tace okay sannan tayi introducing friends dinta,fateema,bilkisu,rukayya,hajara sai best lady dinta rahma, daga nan suka dan taba fira da angwayen kafin suka ce zasu wuce don an kusa kiran magrib, kawayen amariya suka shiga motar hajara don daman aciki suka zo,ita kuma umma ismail ya nace shi zai kai ta gida……..
dariya umma tayi sannan tace kai dai fadi gaskiya dai,dariya yayi sannan yace wallahi am serious fah,okay naji dai yanxu dai zan shiga ciki sai gobe,okay bye,
tana shiga ciki babu kowa afalo,daki ta shige abinta,ta cire kayan jikinta tayi wani sabon wanka don irin rawar da tayi duk tayi zufa jikinta nayi mata danko ,tana fitowa ta saka kayan barcinta sannan ta haye saman gado ta dauko kilishinta tana ci tana karanta littafi a wattpad.
wai umma bata dawo bane mustapha ya tambaye fareeda,bansani ba ta bashi amsar adakile,kallonta yayi da mamaki sannan yace kina gidan neh bazaki duba ko ta dawo ko bata dawo ba, shi ne zaki ka ma ce min baki sani ba, ke da gidanki za’a shiga afita baki sani ba kenan ya fada tare da yin tsaki baki ta tura sannan ta tashi ta nufi dakin da umma take ko sallama batayi ba ta banko kofar sannan tace au ashe kin dawo,dago kai umma tayi ta kalleta da mamaki,ita dai tasan agirma ta girma yarinyar nan amma don rashin ta ido shine zata wani banko mata kofa tana wani mata iyayi, ko don ta ganta a gidanta neh,ko kallonta umma batayi ba bayan na farkon da tayi mata,ita ko ta kulu tsaki tayi sannan tayi kukunanta kafin ta banko mata kofar,umma tace azuciyarta taki ta fisheki ni dai nan gani nan bari.
falon ta karasa tana kumbure kumbure tana cije cije,mustapha dake aiki a system dinta ya dago kai ya kalleta, harara ta banka mai dariya ma ta bashi,murmushi yayi sannan ya kashe system din kafin yace mata tazo ta zauna kusa da shi,sai da ta gama sha kamshi kafin ta karasa kusa dashi,rugumeta yayi sannan yayi kissing din kumatun ta,mai ya faru princess dina ya tambayeta,tura,bakin ta kara yi sannan tace babu komai,murmushin gefan baki yayi kafin yace toh mai sa kike ta dacin rai,ni bana wani dacin rai ta fada ataikace,haka ya rinka mata magana tana mai yanga,amma kuwa tana ganin kofar dakin da umma take ciki an budu tayi saurin kara shigewa jikinshi ta wani narke sannan tace,kasan ina sonka ko,murmushi yayi sannan yayi kissing dinta,ita kuwa umma wanda ta fito daukan ruwa neh ta gan abinda yafi karfin idonta,mutuwar tsaye tayi kirjinta na dukan uku uku,ita ta kasa zuwa kicin sannan ta kasa komawa dakinta,shi kuwa gogan naku mustapha bai san wainar da fareeda take toyawa ba domin shi kiss din da yayi niyyar mata ba mai zurfi bane,amma da yake ita da biyu tayi sai kawai ta zura halshenta cikin bakinsa shi kuma daya ji dadi ya biye mata……….
vote comment and share
love you guyx.
💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋
💋💋💋💋
💋💋💋
💋💋
💋
Sai da tayi kusan miti biyar kafin ta nemo natsuwata ta koma daki,duk ta rikice abun da take gani a film da ji alittafai yau ta gani da idonta,ajiyar zuciya ta rinka ajiye wa kamar wanda tayi gudu,tashi tayi ta shiga bathoom tayi brush tayi alwala sannan ta fito ta hau gado ta kwanta don ita kam ta fasa shan ruwan.+
Da kyar ta samu tayi barci don tana kulle ido abinda keh zuwa mata kenan,har ta kusa mantawa batayi addua ba saboda rikicewa.
washe gari da safe wayar noor neh ya tada ta abarci,bayan sun gama waya da noor take gaya mata cewa mamy tace wai bata san idan ta ajiye karamar wayar ba don bata ganshi ba,sai cewa tayi kawai ta barshi daman number victoria zata dauka aciki amma tayi mata magana a whatsApp jiya,ashe itama neman layin take bata samu ba shine ta kira batool,ita kuma ta bata wannan,okay toh shi kenan sai na iso,aha.Kwanciya ta kuma yi.
Ke na iso fa Noor ta gaya bayan da umma ta dau wayar,kina ina neh ta sake tambaya,ina gidan ya musty shiryawa nake zan fito in the next one hour,okay ni kuma yanxu na shiga compound dinsu basma ki same ni anan okay no pee,amma ya na ganki da wuri,ke dai bari ina zuwa na samu secretary dina tayi min aikin kawai sai na nayi sending mah chairman din sannan na tattaro inawa inawa na yo kano,dariya umma tayi sannan tace okay sai na iso toh,aha.
Shiryawa ta fara yi da sauri da sauri don tana son ta fita agidan nan as soon as possible,bata son mah ta hadu da daya daga cikinsu,domin she will feel more awkward around them,duk da su basu ganta ba,amma ita kunyar abin ma take ji sai sa tun safe bata bude kofarta ba,tana jin ya musty yana tambayar fareeda koh ta fito lokacin da zai fita take cemai a’a.
Atamfarta ta saka blue mai design din white and yellow flower asamansa,tayi kyau sosai acikin kayan kamar don ita aka zabo ankon,straight gown neh mai tsagu abayansa sannan gaban asamata zip ta wurin boost dinta kamar wata mai shayarwa,mayafi yellow ta dauka tare da yellow purse sannan ta saka black shoe mai rastsin yellow design.Arabian perfs ta fesa sannan ta unpulging wayarta ta fito falo,Tayi kyau sosai duk da ba wani makeup bane a fuskarta,daga powder sai lip balm da kwalli,curve dinta ya fito sosai ainun.
Tana fitowa ta hango fareeda zaune saman sofa tana kallon wani series,dago kai tayi suka hada ido, hararanta tayi sannan ta mike ta tako ida take sannan ta kalleta daga kasa har sama kafin tace agaskiya ya kamata ki daina saka irin wannan kayan ta fada tana ya tsine fuska kaman taga kashi,don bazai yiyu katuwa dake kuma baki da miji ki rinka dressing cikin gidana haka ba,don mamaki kasa magana umma tayi tana kallonta,ita kuma ta cigaba da cewa,sannan kuma gani nayi ke ba muhar………Katse ta umma tayi da cewa ya isa haka,ke ba don girman ya musty da nake gani ba har kin isa ki tsaya kina gaya min magana ban mammare ki ba,ni sa’arki ce? ko kani na ba sa’anki bane balle ma ke sa’ar husna fa,husna ma ta girmeki da shekara daya, toh wallahi ko husna bata isa ta gaya min magana haka ba amma saboda rashin ta ido shine zaki kalli idona ki gaya min magana don kinga kina matan yayana. Toh wallahi tallahi ko da wasa kika kara tara ta da maganar bazan wallahi sai na miki rashin mutuncin da tunda kika zo duniya ba’a taba miki ba,banzan jahila mara tunani da tarbiya kawai……..
Tana kai nan bata bar fareeda da tuntuni take kokarin katse mata hanzari don tayi magana ba, ta fice ta bar mata gidan,ita ko don zafin umma bata barta itama ta gaya mata na ranta ba ya sata kuka,kuka ta rinka yi kamar wanda aka daka,gaskiya idan bata rama ba anshata banza,da kyar ta samu ta lalashi kanta tayi shiru amma idonta yayi bulu bulu yayi jawur dan kuka.
STORY CONTINUES BELOW

Umma ta fita tayi sorting din napep ta hau sai gidansu basma,duk ranta abace yake,auzu ta rinka yi kafin taji sanyi aranta tana kaiwa ta biya mai adaidaita kudinsa sannan ta shiga.Nuna mata part din da amaren suke kanwar basma tayi,tana shiga ta gansu noor da sauran kawayen amaryan,kallonta hajara tayi sannan tace wannan babbar kawar amaryar bata yi bafa,sai yanxu take zuwa,hararan wasa umma ta wurga mata sannan tace hajjo sannunki,ki hadani da besty nah kinji,dariya sauran sukayi sannan fateema tace ai kunfi kusa,hotuna suka rinka daukawa,daga baya abokanan ango suka iso aka dau hotunan da su,fareeda ceh ta shigo fuskarta babu yabo babu fallasa,gaisawa tayi da mutanen dakin sannan ta dawo ta zauna kusa da elham suna fira abinsu ko kallon inda umma take bata yi ba don ta riga ta san abinda ta kulla mata,su noor da suka ga ba suyi magana ba basu dauka wani abu bane don sun san halin umma idan bata so yin magana ba,ita ko sai tsokanarta elham take yi daman itace mutumiyarta.
Atmosphere din kwata kwata bai yi ma umma dadi ba,karfe shida ta bar wajan ta koma gida,Bayan isha aka kai amarya gidanta dake kabuga daga nan kuma akayi shirin dinner,su umma kuma daman da shirinsu suka fito,dariya husna ta rinka yi ma ya umma da tagan micheal tana ta boyewa amma sai da ya ganta,gaisawa kawai sukayi sannan ta samu ta sampe,dinner yayi dadi Alhamdulillah sai dai ace Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a ta gari.
Bayan angama dinner ismail ya kawota gida,suka dan taba fira sannan ya wuce da alkawarin gobe shi zai kaita gidan kawu habu,kwankwasa gate tayi baba mai gadi ya bude mata bayan ta sanar mai itace Dan dare yayi sosai karfe sha daya ya wuce mah,suna gaisawa ta shige cikin gidan,tayi mamakin uwae gayyar bata kulle kofarta ba,tana shiga babu kowa afalo,dakinta ta wuce,brush kawai tayi ta gyara jikinta tare da yin alwala ta kwanta.
Washe gari bayan ta farka,tayi wanka sannan ta shirya don tana son zuwa gidansu basma ta gaida mamynta kafin ta wuce gidan kawu habu saboda tana son gobe da safe ta kama hanyar Abuja,tsaki tayi da taji cikinta na kukan yunwa,fitowa tayi don ta sama wa cikinta abinda zai ci,rabonta da abincin kirki tun indomie jiya,tana fitowa tayi hanyar kicin,babu kowa ciki,drawers din ta fara budewa bata ga komai ba sai su gishiri da sauran spicy ,tsaki tayi sannan ta leka dinning bata ga kayan tea ba,kofar store ta murda taji shi akulle,murmushi tayi sannan ta dau wayarta dake kan frizzer ta kira layin husna,yaushe zaki koma kaduna,anjima da yamma okay sai mu tafi tare na kwana sai na koma,sunday ihuuuu husna tayi sannan tace dan Allah ya umma da gaske kike wallahi naji dadi,bari nace mah ya bobby ya biyo ya dauke ki kafin ya karaso nan,a’a karki damu yanxu zan fita da ismail zai kaini gidan kawu habu daga nan zan karaso,okay sai kinzo,aha.
Juyawa tayi don ta fita daga kicin din,ganin fareeda tayi tsaye wajan tana mata kallon raini,bata bi ta kanta ba ta wuce ta fita daga kicin din,tana fita ta hango ya musty zaune saman dinning,da kamar zata wuce sai kuma ta tsaya ta gaishe shi don bata son ta bar gidan basuyi sallama ba,tana kokarin gaya mai ita zata tafi kaduna tare da husna,kawai sai ya buda baki ya fara jero mata jawabi akan yadda nan gidansa neh kuma matarsa ke da iko da gidan,ba zai yarda yan uwansa sa su rinka zuwa suna gaya ma matarsa magana ba har da zagi,idan baza su iya zama da rules din da ta saka agidan ba toh sai dai su daina zuwa shi ba zai lamunta cin mutunci ba,da sauri umma ta dago kai ta kalleshi don tunda ya fara magana kanta asunkuye yake tana tunanin abinda fareedar ta gaya mai har yake gaya mata magana haka,lallai kam ta furta sannan ta kalle shi ido cikin ido tace,nayi kuskuren tunanin we can set aside our differences,ahaka kake tunani ka aure ni,ganinka idan haka halinka yake zaka shiga aljanna idan ka ajiye mata biyu,toh bari kaji ni nan koda babu komai daya raba tsakanin mu, duk da hakan bazan aure ka ba ta fada hawaye na gaggaro mata,kana zaton ni banda zuciya neh ko kashi neh akirji nah,ta numfasa sannan ta kara da cewa gida ko toh gashi ka cinye shi,insha Allahu har abadan na fita daga rayuwarka da kuma iyalinka.Tana kai nan ta fashe da kuka ta wuce daki ta hada kayanta ta dauko jakarta ta fice daga gidan ko kallonsa bata karayi ba.
Ita kuwa fareeda dadi taji da taga ta raba shi da yar da yaso aduniyar nan fiye da kowa,shi kuma hannu yasa yana shafa fuskansa azuciyarsa yana fadin what have i done again.
Tana fita ta shiga adaidaita ta wuce gidan elham,baba mai gadi ta ba jaka tace ya shigar mata dashi bayan ta mai bayani sannan ta wuce gidansu basma,bayan ta gaida mamy da mutanen gidan neh tayi breakfast awajan don mamy tayi insisting,tana cikin ci ismail ya kirata yake ce mata yana waje,tace mai ya bata five minutes,tana gamawa tayi mah mamy sallama sannan ta fito,ganinsa tayi cikin motarsa tare da wani cutes boy,murmushi yayi sannan yace barka da zuwa gimbiyata,murmushi tayi sannan tace barka dai,karasowa tayi kusa dashi sannan ta tsuguna daidai yaron tana tambayar sunansa,gaya mata yayi suka yi shaking hand sannan ya suka shiga mota sai gidan kawu habu.
STORY CONTINUES BELOW

Wallahi babu komai kawu,Allah yasa mu dace dai,insha Allah idan na kara dawowa kano toh zan shigo sannan zan ba elham sako ta kawo maka,toh nagode yar nan Allah yayi mik albarka,ameen kawu sai an kwana biyu,yauwa toh ki gaida su dijen,zasu ji ta fada sannan suka wuce.
Da suka kai gidan elham ya rinka mata korafin yaso shine ya mayar da ita Abuja yanxu zata je tabi motar haya kenan,dariya tayi sannan tace sa ranka inuwa zan bi train kawai don hankalinka ya kwanta amma ai ni da noor neh mah,dariya yayi sannan yace okay beta,nextweek ki saka rai ina nan zuwa Abuja kawo ziyara,murmushi tayi sannan tace Allah ya kawo ka,fira suka kara dan tabawa kafin sukayi sallama ta wuce cikin gidan bayan ta bawa ameer pack of creamberry chocolate,
motar bobby ta gani,har ya iso kenan,karasawa ciki tayi tare da sallama,dukkansu suna falo daman ita ake jira,tana shiga suka danyi fira kafin suka dau hanya,bayan elham ta gama korafin cewa ita ba’a kwana gidanta ba,noor tace ku dai kun fiye korafi,tura baki elham tayi tare da cewa daman nasan bakwa sona ai,dariya husna tayi sannan tayi mata tare da gwalo tana cewa ba kince nine last born ba sai sai ake sona,dariya dukkansu sukayi don wani lokaci husna da elham akwai shirme.
Suna kai kaduna suka wuce wani eatery suka yi takeaway din abinda zasu ci kafin suka karasa gidan,wanka sukayi kafin duk suka fito bayan sun gama uzirinsu,abinci sukaci suka sha drinks din da suka siyo kafin aka dasa hira,karfe goma suka shiga don su kwanta.
Washe gari da safe bayan sun gama breakfast suka kama hanyar Abuja,suna kaiwa gidan momy ta fara sauka ta dauko sauran kayanta sannan ta wuce gida,anan ta samu junainah na jiranta,haka ta rinka damunta da surutun nan nata,da taga dai umma is not in the mood kawai sai ta kyale ta suka yi sallama ta wuce gida donmin dama wucewa zata yi umma ta dawo shi ne ta tsaya su gaisa.
Bayan wata biyu har sunyi resuming ta fara zuwa lectures har tayi sabuwar kawa fadeela amma ta girme ta da shekara uku,kullum tare suke yawo aschool,amma dai fadeela matar aurece,sai sa tayi mamakin cewa rahma bata da aure,da farko ta karyata kafin daga baya ta gasgata.Dariya lokacin umma take yi sannan tace ni fah ban damu da shekaru na ba,dia is no rush in marriage ai,murmushi kawai fadeela tayi sannan tace haka neh kuma.
lectures dinnan akwai wahala wallahi,na tsani takura Allah ta fada tare da yin tsaki,ke ko ni fadeela tace itama,Dan Allah muje canteen mu samu abun sama cikinmu,okay toh don gaskiya ina jin yunwa nima.
Lagos💋💋
ammy seriously kin gaji dani,su aysha da zaynab fah basa gajiya dani fah,tsaki ammy tayi sannan tace ai sai ka tattara ka koma dubai din,dariya yayi mai sauti sannan yace ai ban isa ba,yau ma zan koma Abuja ina da student din da zan dauka lectures dix month,prof obinna ya gama part dinsa saura nawa dana dr osas,so zanje nayi rushing dinsu na dawo wajan ammynah,pls idan kaje ka zauna wajan kawai saboda daughter tazo gidana hutu,murmuahi yayi sannan yace ammy ni dai sai anjima bari na kwanta kaina ya fara ciwo.Dariya ammy tayi tuna abunda umma tace mata akan wannan hali nasa.
Yana zuwa daki kwanciya yayi yana tunani har barci ya dauke shi.
TWO YEARS LATER
kinji wani dadi da nake ji da muka gama semester dinnan,yau zanje lagos hutu, ismail kamar yayi hauka daya ji nace idan yazo Abuja bazai same ni ba,kinsan Iyayenshi zasu zo ayi maganar sa ranan mu,uhmmmmm na sani kuma wallahi na kosa ki yi aure wallahi,don aure ni’imace,see dix one umma tace sannan tayi dariya tana Allah ya shirya ki maman faiza, dariya tayi sannan ta kalli yarta yar shekara daya da rabi da take barci akafarta,mukhtar neh ya shigo da sallama,amsawa tayi tare da gaishe shi sannan ta fara tsokanarsa,ango ango kasha kamshi dariya yayi sannan yace sahu daya muke ai,dariya umma tayi sannan tace ai sai ka riga ni,kai fah in three weeks neh ni kuma nace idan za’a sa asa shi ending of next year kawai,dariya mukhtar yayi sannan yace ismail dinne zai yarda,toh mai zai hana okay ooooo zamu gani ai dariya fadeela da mukhtar suke mata don tace asaka bikinta wata goma ina laifin wata shida,haka suka rinka raha yake cemata tare zasu dubai siyo laife da ita inji mamy,ihun dadi tayi sannan tace den zaka sameni lagos sai mu daga daga nan koh,hakan za’a ayi,flight dinki na yaushe neh,karfe shida neh toh shikenan nextweek zanzo,okay babu damuwa,aha. Raka fadeela tayi dan mijinta yazo daukanta,sannan soyayarsu yana burgeta,fadeela da naim inseperateable kenan,bayan sun gaisa da naim neh suka wuce shi da matar sa,gashi da barkwanci.
Wai kai zaka kaini airport,sallan ka yi lattin appointment dinka da faiza,gwanda kaje saaboda ni babu ruwana ehe,kallanta yayi domin shi kadai yasan abinda ya faru akano don shi kadai ta gaya ma wa,don ya dame ta akan meye ke damunta da yaga ta dawo bata walwala,dariya yayi sannan yace dont worry ai na gaya mata sannan mu ba haka muke ba remember,abi okay naji,toh muje,mamy sai na dawo bye ta daga mata hannu. amotar tsokanarta ya rinka yi,wai itace bestman dinsa,dariya tayi sannan tace,oga abeg nah lady i be ooooo,raha suka rinka yi har suka kai airport,suna zuwa tayi sauri ta shige don ta kusa makara,idan ta biye mah mukhtar kuma zai sata ta rasa flight dinta.daga ma juna hannu sukayi sannan tace agaida min antynah,murmushi kawai yayi yana kallonta har ta kule ma ganinsa kafin ya wuce……
vote,comment n share
Love ummeeter
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲
🌲🌲
🌲
Ammynah yaki ke, ta fada tana hugging dinta,lafiya lau daughter nah,ya hanya lafiya lau Alhamdulillah,ya karatu da su mamynki, dukkansu lafiya,mamy ke kadai neh gidam neh naji gidan shiru,a’a bani kadai bane su zainab sun tafi shopping ita da aysha,rushd kuma ya tafi dubai ganin kakanninsa,Abbi kuma as always business trip,aha.Amma gaskiya ya kamata abbi ya ajiye aiki haka ya huta abinsa,mai amfanin rushd wai,tana kaiwa nan sai tayi shiru kuma bata kara ba akan abinda ta fada,ammy na jinta amma tayi shiru bata ce komai ba,umma ta kara da fadin ina shaila neh tunda nazo ban ganta ba, ta fada don chaza topic don maganar da suke yi da farko yayi mata tsauri,bata son maganarsa kwata kwata.Ammy murmushi tayi don ta san abinda tayi sannan tace shaila ai tare suka tafi amma ita gyaran gashinta za tayi,okay………+
…….Wai waiye adon tafiya……
Alokacin da umma ta samu sabani da musty da matarsa shekara biyu da suka wuce,sai da musty yayi kusan wata uku fareeda bata gane kansa ba,sai ya ta zama shiru shiru,daga baya ya warware,amma sai da tayi da gaske,domin ya zama kamar wani miskili idan ba ayi mai magana ba bayyi,har momy sai da ta tambaye shi meye ke faruwa don ko daya zo Abuja mah bai fiya zama cikinsu ba kuma ko ya zauna ma baya wasa da rahan daya saba da kannansa…….
acikin shekara biyu nan da suka wuce abubuwa dayawa sun faru,ciki akwai graduation dinsu husna wanda ya faru bayan shekara daya da dawowar umma abuja,wanda bayan hakan neh mah suka kara haduwa da fareeda da mustapha,haduwar da bai musu kyau ba,don sai da fareeda ta takali umma ita kuma ta mareta,fada sosai su kayi this time da mustapha daya ji labari,ita kuwa ta gaggaya mai magana son ranta ta kara alwashin aranta ita da gidan shi har abada sai sa ma ta chaza lauyan da zai rinka lura mata da harkan business dinta.
Lokacin da fareeda ta haihu kuma,karyan ciwo tayi don karta je kano,sannan duk wainar nan da ake toyawa babu wanda yasani cikin family din nan.ko da husna da elham suka haihu bata bari sun hadu da fareeda ba balle shi uban gayyar,tayi shekara daya da wata daya bata saka su a ido ba,kuma abin yayi mata dadi haka don hankalinta ya kwanta sosai.Da yake ajere suka haihu da noor ita kuma fareeda bata samu daman zuwa ba,haka suke hide and seek atsakaninsu,ko nace umma ke boye boyen.
……….Cigaba……….
Salama ailakum,su zaynab suka banka sallama tare
Da shigowa niki niki da kaya ahannu,zaynab na ganin umma ta karasa da sauri tare da hugging dinta,masha Allah sis when did you arrive suka tambaya,just a couple of hour ago ta basu amsa sannanta kara da cewa how is the weather treating you,Alhamdullilah but the weather is too cold,yap that hamattan for you,zee introduce me to this cutie mana,tafada da yare,dariya ammy tayi,ita kuma zaynab tayi rolling idonta sannan tace,wannan ai cousin din broda rushd ce,ammy jnr sis daughter,wow she is so cute,kamar ba nigerian ba,sai lokacin umma ta gane mai aysha ta tambaya zaynab tunda da turanci tayi mata bayani,murmushi tayi sannan tace i bet this is the talkertive of a sister you told me about then in dubai,yap you are right my dear ta fada tana dariya,haka suka rinka fira suna dariya kafin daga baya suka karasa ciki don su ajiye kayan da suka siya suka bar ammy da umma nah kallo,shaila kuwa bayan sun gaisa da umma neh ta shiga kicin don daura sanwa bayan ta tambayi mai umma zata ci,mamaki neh ya kama umma ta tsaya tana kallon shaila kafin tace maccaroni is okay,bayan ta tafi neh ta juyo tana kalla ammy sannan tace ammy lafiyar shaila kuwa tambayata tayi mai zata girka min,murmushi umma tayi kawai don bata son gaya mata anything about situation din,saboda basa shiri da wanda yayi takulin matsalar,lallai kam za’ayi snow yau din nan, dariya ammy tayi sannan tace,baki da dama wallahi umma ji yadda kike exaggerating din halin nata,murmushi umma tayi sannan tace haka dai zaki ce ammy,haka suka rinka fira abinsu gwanin ban sha’awa,da daddare kuwa suka hadu sukayi dinner,sannan aka dora daga idan aka tsaya.am sleeping in your room sis,aysha ta fada murmushi umma tayi sannan tace babu komai,tare suka shiga dakinta sannan suka rinka fira don aysha akwai surutu,yawancin maganar mah ita ke yi,umma sai dai ta amsa da kai ko kuma tayi murmushi,sai wajan twelve ta bar su suka kwanta bayan sunyi brush da alwala.
STORY CONTINUES BELOW

wow i love this pink loofas is so cute zaynab ta fada tana kallon takalmin dreamly,toh ki dauka now cewar umma,……..sun fita strollin neh suka ga wani boutique ana siyar da kayan sawa kala kala,but i didnt bring my purse,my credit card is at home,then we will use mine,oh tanx sis i will surely pay back,oh no!!!!! dia is no need wat are sista meant for.
Haka suka rinka daukan kaya,harda siyan track suit wai zasu rinka morning jog da gymin.
ammy nah zaune adinning ta gan sun shigo niki niki da kaya,kallonsu take da mamaki a fuskanta,ku da kuka je strollin shi neh kuka bige da shopping,dariya aysha tayi sannan tace momy kayan neh muka gani da kyau,mun siyo miki takalmi sef,wallahi yayi kyau abbi na ganin kafarki zaiyi fall inlove with you again,lallai kam toh nagode,dont mention aysha ta fada tana grinning,toh kuje kuyi wanka kuzo kuyi breakfast,,,,okay!!!!……
Suna fadar haka suka shige daki don suyi wanka,bayan sun fito suka yi breakfast sannan suka zauna suna fira afalo,karfe biyu dai dai suka ji sallamar mukhtar,zare ido umma tayi sannan tace wa nake gani kamar ya mukhtar, ba next tomorrow zamu tafi ba,gira ya daga mata sannan yace ai gani nayi ammy ba mamanki bace ke daya,baki ta murguda mai sannan ta harare shi,dadi na da kai baka cin ribar zance,tana cikin magana saleem yayi sallama,murmushi tayi sannan tace baka ce min tare da fav cousin dina kake ba,sisi saleem yace sannan suka tafa hannu wato high five daman haka suka saba idan sun hadu,ina Abba wallahi nayi missing dinsa,yana yola, lallai kam ya kamata naje yolan nan dai,tunda shi abba ya zaba zama anan,kaima dai akwai son zama garin nan baka son Abuja,dariya yayi sannan yace kinsan duk business dina a canada neh so idan na dawo,inna rike ni take ayola,so take ta mayyar da kai fulanin dole ko ta hadaka da wata yar fillo,dariya yayi sannan yace gaskiya kam,ke kam daga ganin dan uwanki kin manta dani,murguda mai baki tayi sannan tace ai kai ya mukhtar ba’a zaman minti goma da kai baka bata ma mutum rai ba sai sa ai ta fada tana mai murmushi,kada kai yayi sannan ya kalli su aysha da ba komai suke gane wa ba yayi musu introducing din saleem da shima su yake kallon,murmushi yayi musu sannan yace mah umma sista nayi mata fa,zare ido tayi sannan tace yaushe kayi aure ban sani ba,dariya yayi sannan yace yanxu nayi sabuwar kamu,wannan nake so wanda ta ke zaune kusa dake,dariya umma tayi sannan tace daga ganin farar mace koh za kayi ma inkaw nah kishiya,dariya yayi sannan yace which inlaw ni fa banda budurwa,zare ido tayi sannan tace haba dai sai kace a film,santalelen saurayi kamarka,ka kusi ga kyau ace baka da budurwa ,ina ban yarda ba kawai dai ka ga farin fata zaka chanza sheka,dariya yayi sannan yace ko daya wallahi.
ita kuwa zaynab duk ta zargu don taga idan yayi magana sai ya kalleta,ammy neh ta fito take cewa kunyi breakfast neh,mukhtar yace yes sweet ammy,au daman ammy kinsan sunzo neh,tab ai tun jiya suka shigo bayan kun kwanta,mukhtar ya kirani wai suna bakin gate,shine suke ce min wai flight dinsu yayi delay sai sa suka yi dare,lallai kam,juyowa tayi ta kalli mukhtar sannan tace wani sabon kakale neh sweet ammy kuma,kashe mata ido daya yayi sannan yace kefa na lura da namiji Allah ya yo ki da kulle zaki rinka ma matarki don kishi,dariya ammy tayi sannan tace halinta daya da aisha ai,uhmmmmm ammy har da ke ake hade min kai,toh ai halinku daya da mama mah na gani umma ta fada tana murmushi,fira suka rinka yi awajan amma da turanci saboda su zaynab,aysha kamar jira take asakata cikin zance,nan ta zage sai basu labari take suna sha dariya,ita kuma zaynab duk atakure take don kallon da saleem yake mata………
Kano town
ya musty wai yaushe zaka je abuja neh ina son mu tafi tare neh, kaga baban Areef baya nan kuma yace be yarda naje ba, sai dai idan zaka je sai mu tafi tare,kallonta mustapha yayi sannan yace,tab inaga ni da abuja sai nan da two weeks idan zan kai fareeda bikin kanwarta,kai amma banji dadin wanan zancen ba,ai lokacin baban areef ya dawo,ni kuma ina son ganin momy wallahi nah kwana biyu,gasu batool ya noor da ya umma,har husna rabon da na ganta tun sunar danta ashraf……
Umm-areef ai mijin naki neh bai da yarda cewar fareeda,toh ina zai yarda da mutanen duniya bayanin duniya ta zama abinda ta zama,da da mahaifi ba ana zaluntar juna balantana wanda baka sani ba,ai kin kam da gaskiyarsa babu yadda zai bari rayuwar iyalansa su salwanta,kuma haka neh kin fadi gaskiya kam….
Toh wai ke maman ameer ai sai kice zaki one week to wedding din don ya kai ki da wuri nima na samu naje,dariya fareeda tayi sannan tace kinsan yadda na rukesa amma fur yaki,ya shafe idonsa da toka yace sai ana saura kwana uku zanje,haka nan na hakura wallahi.
Kai ya musty!!!!!! elham ta fada tana kallonshi,amma shi kam ko kallonta bai yi ba sai ma concentrating din da yayi akan laptop dinsa yana aiki abinsa………
kaduna
Abu-ashraf yadai yaushe zamu Abuja neh,am missing momy ya umma ya noor,ya ammar n also batool husna ta fada tana kallonsa, umm-ashraf am really busy this weeek,but ki bari idan zan tafi switzerland nextweek sai nayi dropping dinki abuja sai idan na dawo sai mu dawo tare what do you say yayi maganar hankalinsa na kan system dinsa,tura baki tayi sannan tace wallahi na kosa ka gama wanna aikin da aka baka ko zaka samu time dina. Juyowa yayi ya kalleta sannan yace haba habibty yazu ahakan mah cewa zakiyi banda time dinki,eh mana ta katse sa, kullum idan ka fita aiki baka dawowa sai magrib,shima fah idan ka dawo sallah kawai kake ka ci abinci sannan ka daura aikin daga idan ka tsaya,rike hannunta yayi sannan yace am sorry my queen,mother of my prince,i promise to make it up to you kinji,kiy hakuri ina gama aikin nan zan nema hutu sai mu tafi honeymoon din da ba muje ba koh,kinga anan ma sai mu sami princess din mu koh,dariya tayi tare da rufe fuska da hannunta alamon ta ji kunya,murmushi shima yayi sannan yace my naughty wife is shy,kiss yayi mata agoshinta sannan ya juya ya cigaba da aikinsa…………
Abuja
Momy wallahi kinga yadda areef ya kara girma,da na gan hotonshi da elham ta turo har ban gane shi ba yayi wani irin bukeke dashi,tambayarta nayi mai take bashi,gashi sak babansa Batool ta fada tana murmushi,ya noor neh ta chafke maganar da cewa toh ina kika bar haydar din,wannan shi ai sai shegan tsawon kafa babu kiba,sai siranta kamar maburgin kada miya,shida suhaim basan wanda yafi wani siranta ba batool ta fada ta girgiza kai,dariya noor tayi sannan tace ai suhaim duka ya hada ga siranta ga gajeranta,haba dai ba kya kirashi gajere ba,yaro da tsawonsa kam batool ta kara fada,momy neh ta katse maganarsu da cewa ai sai abar min mazan nawa su huta da korafinku,maganar ku kadai ya isa ya tsotse su,dariya noor da batool sukayi sannan batool tace momy kedai Allah ya hada ki kam da maza………..
Tanx………
Vote
Comment
Share
LOve ummeeter
🌲🌲🌲🌲🌲
Elham-umm-areef
Batool-umm-haydar
Fareeda-umm-ameer
husna-umm-ashraf
Noor-umm-suhaim
i hope kun fahimta waye waye koh……
Areef-Ahmad sunan baban elham
Haydar-sunan baban ammar
Ameer-suleiman sunan baban fareeda
ashraf-abubakar sunan kakan husna
Suhaim-mukhtar sunan baban mijin noor
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕
💕💕💕💕
💕💕💕
💕💕
💕
United Arab Emirate
Kwana biyu kenan da zuwansu umma dubai babu abinda suke sai siyayya,ayanxu haka sun hada akwati biyar,saura biyu shima sai gobe don sun gaji dayawa.
Suna isa hotel din da suka sauka suka yi ordering abinci kafin suka wuce daki,suna isa suka yi wanka kafin suka fito don yi lunch mintina bai wuce goma ba aka kawo musu abinda suka bukata,umma na gani ta karba ta ajiye a center table,bude nata tayi ta fara ci ko kallon mukhtar bata yi ba,dariya yayi sannan shima ya sauko ya fara cin nashi,sai da ta kusa koshi sannan ta dago kai,ta kalli mukhtar sannan tace amma abincin nan da dadi fah,dariya mukhtar yayi sannan yace yunwar neh haka,turo baki tayi sannan tacigaba da cin abincinta,dariya ya kuma yi sannan yace wai haushi kika ji,girgiza kanta tayi kawai bata dago ba,better don gani nayi gaskiya na fada saboda nigerian jollof kike ci ba wani hamshakin abinci bane,ana cikin haka saleem ya shigo tare da rushd suna dariya sannan suka yi sallama,mukhtar nai kadai ya iya amsawa,ita umma sha jinin jikinta tayi da ta gansa,don da tasan tare zasu shigo da ta bar falon,tun jiya take avoiding dinshi,tana jin lokacin da yake ce ma ya mukhtar da agidansu suka sauka amma yace kar ya damu akwai next time,karfin halin sai saita kanta tayi kokarin yi,daga nan ta daga kai suka hada ido,farko haduwarsu kenan face to face,kare mai kallo tayi,fari neh tas,kana ganinsa kaga balarabe,gashin kanshi baki wuluk neh,yana da yalwataccen gashin gira da ido dogaye,bakinshi jajur kamar ya sanya jan baki,hancinsa pointed neh am ba sosai ba,yana da built up body,fatar jikin shi ya nuna alamon hutu atattare da shi, farin jallabiyace jikinsa,bazaka taba tsamanin yana da hadi da yan nigeria ba,murmushi ya sakar mata wanda ya sa ta kusa rikicewa amma dayeke kar ta san kar ne,ita ma murmushi ta mayar me sannan ta mike tana tattara kayan da suka yi amfani dashi don saka shi cikin waste bin,kallo ya bita da shi sannan ya raya azuciyarsa,wai daman haka take,gaskiya camera akwai karya,she is so sexy n cute ya fada axuciyarsa.Match suka kunna na gulf wanda ake bugawa,fitowa daga kicin tayi zata wuce daki ta hango suna kallon match din gulf and bazata iya missing dinshi ba domin best game dinta kenan,karasowa falon tayi ta zauna kujerar da saleem yake zaune shi da mukhtar,tsakiyarsu ta zauna sannan ta mika hannu ta dauki remote da soda din dake saman table din,kara volumn tayi sannan ta kura ma tv ido,kallonta saleem da rushd suka yi suna mamakinta,mukhtar da ya lura da hakan murmushi yayi kawai sannan ya mayar da kallonsa gidan talibijin din,minti kadan sai red ninjas suka ci,ihu mukhtar da umma suka yi suna yafa hannu,saleem was shock don sun tsorata shi,kallonsa umma tayi sannan tace dont blame me am afreak for sport channels,and am behind d reds,red rocks,so go red ta fada tare da zama,murmushi saleem yayi yace red yau are just lucky neh kawai,dariya umma tayi sannan tace losers,sannan tayi mai.Dariya mukhtar yayi sannan yace she is alwayx like dat when it comes to match,yah yah wateva,just shiiiiiiii zanyi kallo,haka suka rinka kallo tana yi tana tsalle shi kuma rushd yana binta da ido don duk abinda tayi burgesa take gashi ya ji dadin company dinta yau dinnan,amma bai san yadda zai tunkareta ba don yana ganin ya fada sonta mai tsanani,and she is being her self around him,juyar da kansa yayi ya cigaba da kallon match din,yana tunanin mafita,don shi sonta yake amma bai san ko zata yafe masa abinda yayi mata ba.+
……..ABUJA NAIJA………
One week before dubai
A abuja kuma su magabatan ismail sun zo sun tambayi auren umma kuma an bashi ita,nan da wata shida za’a daura aurenta,abin yayi ma mamy da momy dadi,da har yola momy tace suje saboda kawu umar dake yola tunda shine madaurin aurenta idan ba babanta,but sai yace tunda sunzo abuja ai kawai Dady yayi maganar kawai ba sai yana nan ba
da wata uku aka so sakawa amma dady yace ai gwanda asaka lokacin hutu sai sa ya Kai lokacin hutun first semester saboda kar stress yayi ma amarya yawa……
Saboda irin jin dadin da mamy da momy suke yi neh yasa suka kira umma right away suna shaida mata,lokacin tana lagos, sai da gabanta yafadi,murmushi tayi sannan tace uhmmmmm momy kenan duk zumudin bikin neh haka,gidanku momy tace tana dariya,mamy kuma take cewa ai tayi sauri ta dawo daga tafiyar da tayi saboda su san ta inda zasu fara,dariya ta rinka musu tana cewa tarewa za tayi wajan ammy kawai,da haka har suka yi sallama.
su noor mah haka suka kiranta suna tayata murna,husna har da cewa finally zasu sha chasu domin sai anyi event din zo agani da sai yan gari abuja sun san dashi,dariya kawai umma tayi bata ce komai ba saboda yanxu tana cewa baza suyi event ba zasu fara sabon bayani,akan cewa wedding din da suke jira kenan so ba zasu yarda ta bata musu show ba,da haka suka yi sallama daga conference call din da suka hada,girgiza kai kaiwa tayi sannan ta juye ta kalli su zaynab dake kallonta,dariya tayi sannan take gaya musu abinda ya faru,murmushi aysha tayi sannan tace finally we are attending nigerian wedding,dariya umma tayi sannan take tambayansu daman basu taba zuwa bikin yan nigeria ba,zaynab tace ai wannan neh zuwansu na biyu naija,shima da kyar abbi ya barsu don yaga mijin Aysha ya rasu and she need a change of environment sai sa,kallonsu tayi da mamaki sannan tace mai sa abbi bai son kuzo naija sannan kuma daman aysha ta taba aure,murmush zaynab tayi wanda yafi kuka ciwo tana kallon aysha,sannan ta kuma kallon inda umma take zaune sannan tace kinsan ammy ba ita ta haife mu ba koh,and rushd baby broda din nah neh,aysha ta fada tana murmushi,dariya umma tayi sannan tace sannan kuma kunyi kama da kannensa ba,shi yayi girma kamar kazar agric,dariya suka yi dukkansu sannan aysha ta daura da cewa back den i was a very naughty child,lokacin da ummana ta rasu ina da shekara shida sannan zaynab kuma ba’a haife ta ba,muna xaune cikin jin dadi da annashuwa duk da ummana bata da rai,babu abinda nake nema na rasa,duk abinda nake so sai anyi min musamman abbi na,kwatsam sai abbi yayi tafiya amma da zai dawo sai ya dawo da mata,anan nen komai ya chanza,i was young and stupied ta fada hawaye na zubo mata,anty siyama kanwar umma like my abbi toh sai ta dinga gaya min cewa ammy is very evil wai ta auri abbi na neh don ta raba ni dashi,don farko ina son ammy sosai,itama ammy tana sona,don ita take min wanka ta ban abinci naci,tana pampering dina sosai,sai dai abinda yasa na fara yarda da batun anty siyama shi ne idan nayi abinda bai dace ba ammy kwaba ta take,sannan kuma tace punishment dina shine,no ice cream for me n chocolate for awhole week,kuma tasan yadda nake sonshi,daga haka abin ya fara ban haushi,kinga tunda daman banajin magana,kuma duk abinda nayi ba’a kwaba min,yanxu kuma na samu mai kwaba min sai nake ganinsa amatsayin mugunta neh kuma ba’a sona,kuma abbi na baya supporting dina,duk lokacin da nayi abinda ba dai dai ba sai ta min wannan punishment din,ina da shekara bakwai ta haifi rushd,daga nan abbi ya daura so akan rushd ta fada tana matse hawaye,sai abin ya kara min yawa,gashi ana hure min kunne, gashi abbi ya daina yin abinda nake so sai abinda ammy tace,daga nan na fara ma ammy rashin kunya da hada mata turzoma yadda abbi zai kore ta daga gidan,ina yar shekara takwas babu makircin da ban koya ba wajan anty siyama,da haka duk yan uwan abbi suka fara nuna ma ammy tsana,har aka ce ammy asiri tayi mai sai sa baya jin maganar kowa sai ita,haka ba karamin tada ma ammy hankali yayi ba,ranan taci kuka da kyar abbi ya lalashe ta,ana haka kuma anty siyama ta samu abinda take so,don jaddy yace sai dai abbi ya auri anty siyama,da farko kin yarda yayi ya tirje,sai da ammy ta roke shi sannan ya yarda,nan kowa ya kara gasgata maganar anty siyama na cewar wai asiri tayi ma abbi,lokacin rushd na da shekara biyu aka auri anty siyama,alokacin neh na fara gane mai ke faruwa don lokacin na fara wayau,gashi ya hadu da anyi groming dina akan hanyar makirci,duk abinda ke faruwa tsakanin abbi da ammy anty siyama zata turani na jiyo mata shi,sai na zama munafukar atskaninsu,duk abinda suka yi tare sai abbi ya ji shi abakin anty siyama,hakan yasa suka fara samun matsala da abbi,duk wannan badakalar da ake ammy bata chaza min ba,duk da rashin kunyar da nake mata,idan ta zaunar dani sai tayi min nasiha,amma bata sani ba,ko tayi min nasiha idan naje wajan anty siyama sai ta kara min nata asama haka rayuwata ta cigaba da tafiya,ina da shekara sha daya aka turani boarding school,lokacin rushd na da shekara hudu,ita kuma daman anty siyama ta haifa yarta zaynab kuma tana da shekara daya
naji haushin kaini boarding da akayi,duk ganina ammy neh ta saka hakan ta faru,sai na kara daukan karan tsana na daura mata,daga nan bana sanin abinda yake faruwa sai na dawo hutu,lokacin dana yi shekara uku amakaranta, na dawo hutun term neh na tarar anata daru agida,wai ashe ammy drugs take sha don karta kara haihuwa da abbi,abin ya bani mamaki,lokacin na fara tunani toh idan har ammy na son abbi sosai idan anty siyama ta fada kuma tana son kwace abbi ai haihuwa za tayi don idan ya mutu ta samu gado mai yawa,tunda anty siyama tace saboda kudi ammy ta auri abbi,wannan tunanin neh yasa nasan akwai wata akasa,ace karamar yarinya kamata ina da kaifin tunani awannan dan shekaruna ai dole atambayi idan na koya lamarin gidan aure ashekara sha uku,ana haka ban samu nayi bincike ba na koma school,dana dawo hutu naga duk ammy tayi baki ta rame saboda damuwa,ranar na shiga dakinta sai naga diary dinta,lekawa nayi nagan tana down stair afalo da baki,sai kawai na fara karantawa,wallahi sai da nayi kuka,alokacin shekarata sha biyar anan naga irin rayuwar da ammy tayi tun kafin ta auri abbi da kuma irin kashin da take ci yanxu agidansa,ita aganinta daman son karya ake mata tun farko zuwanta sai sa aka juya mata baya,bata san gadan zare aka hada mata ba,kuma da hannuna aciki ba, domin nice musabbabi faruwar komai, da ni akayi amfani aka dana ma ammy tarko kuma ta fada ciki.Ban gaya wa kowa komai ba sannan ban sa ammy ta gane abinda na gani a diary dinta ba,sai dai kawai na chaza na daina mata rashin kunya ina mata biyayya,bana bari tayi kuka,don idan na sameta tana cikin damuwa nan zan zauna nayi ta bata labari ina sakata dariya don ta manta abinda ya faru,haka hutuna ya kare har na koma makaranta,lokacin da na gama makaranta ina da shekara sha bakwai,saura collage shi kuma rushd na da shekara tara lokacin abbi ya kai shi boarding school don daman shi ya shiga makaranta da sauri,ita kuma zaynab na da shekara shida,alokacin neh ammy tace ita zata koma nigeria baza ta iya zaman dubai ba,gwanda ta je nigeria idan yanuwanta suke,da farko abbi yaki amma basan yadda akayi ya yarda ba,nayi nayi na bita amma abbi ya hana,alokacin neh na san babancin mugunta da gyara,anty siyama haka za tayi ta musguna min,shi kuma abbi daman ba fiye zama yayi ba balle ya san abinda ke faruwa,haka dai sai dai na zauna na sha kukata,zaynab ke zuwa tana bani hakuri,shima idan anty siyama ta kamata tayi mata duka, ana haka na samu admission a cyprus,na tafi shine na samu sassauci,tunda na tafi sai da nayi shekara biyu kafin na dawo,shima dana dawo gidan jaddy na sauka naki sauka gidanmu,lokacin neh muka bi abbi nigeria wajan ammy,ammy tayi farincikin ganinmu,har sai da tayi hawaye,amma ni nafi kowa jin dadin ganinta ayadda take don ta mayar da jikinta tayi kyau sosai masha Allah,ammy treating dinmu take iri daya ba ka gane cewa mu ba ya’yanta bane don duk friend dinta sun zata dukkanmu yaranta neh,wani lokacin mah sai ka zata rushd neh bare,don miskilancinsa tun yana karami yake dashi,gwanda idan yana tare da ni da zaynab yana maganar kusan fifteen minti but bayan haka baya karawa.Da hutunmu ya kare muka koma dubai
STORY CONTINUES BELOW

lokacin da nake final year dina abbi ya kirani na dawo gida,duk hankali na ya tashi don bai gaya min abinda ya faru ba,ina dawa na tar da ammy itama ta zo,alokaxin neh nasan cewa ashe anty siyamace bata da lafiya wai ashe tana da lukemia kuma yayi tsanani,ammy neh ta rinka jinyarta,anan neh anty siyama take neman yafiyar ammy take gaya mata duk abinda taa aikata don ta shiga gidan abbi da yadda ta rinka druging dinta don karta kara haihuwa,ammy baiwar Allah babu wani tunani ta yafe mata,bayan kwana uku da maganar ammy da anty siyama Allah ya dau ran anty siyama,ammy tayi kuka kamar uwartace ta rasu ba kishiyarta bace,bayan arba’in ammy tace zata koma nigeria,babu yadda abbi bai da ita ba amma taki,daya ga ta dage neh ya barta,amma abinda ammy bata sani ba abbi yaji duk abinda anty siyama ta fada……Tun daga lokacin da ammy ta dawo nigeria bata kara dawo wa ba sai da grandma ta rasu da kuma bikina……..Hawaye dukkansu suke barin ma zaynab da taji abinda mahaifiyarta ta aikata wanda bata sani ba,umma ne ta taso ta rugume zaynab tana ce mata tayi shiru ya isa haka.murmushi karfin hali tayi sannan tace kinga abinda yasa abbi baya so na zauna naija kenan,ta fada tana girgiza kai,baki umma ta rinka bata.
Ammy da tun dazu da tazo yin ma umma congratulation daji aysha na bada labari,itama hawaye take, da baya ta koma don karsu gane taji, daki ta koma tayi kukan da ta kai shekara talatin da,batayi ba,daga baya ta ba kanta hakuri.
Da daddare suka zauna suna dinner,kana ganinsu kansan akwai abinda ke damunsu,kallonsu ammy tayi sannan tace wani abu ya faru neh naji ku shiru yau,ko azumin magana kuke yi,kallon juna suka yi sannan suka saki murmushi,zaynab neh tace ammy dan Allah kice ma abbi ya barmu mu zauna dake,murmishi ammy tayi sannan tace matsalarku kenan,kada mata kai suka yi sannan tace no promises amma zan mai magana amma banyi alkawarin zai yarda ba,murmushi suka yi sannan suka mike su biyun suka yi hugging dinta,bata fuska umma tayi sannan tace i feel left behind,dariya suka mata sannan suka mata gwalo, da haka suka cigaba da fira gwanin ban sha’awa………
da suka koma kwanciya kuma adaren abubuwan suka rinka fado ma umma,ita da yanxu gidan mata biyu zata shiga yaya za tayi kenan,amma daga gani mahaifiyar ismail ba sonta take ba,ya za’ayi tace ya auri kanwar matansa,ni fa gani nake the same story na shirin faruwa amma different version,anya zata iya barin haka ta faru kuwa,anya ba ganganci take shirin yi ba,amma kuma ai tana matukar kaunar ismail gani take baza ta iya rayuwa idan babu shi ba,duk da bata nuna mishi wani son kirki amma ba karamin sonshi take ba, kasa barci tayi rannan sai da tayi sallah kafin ta samu saida hankalinta ya kwanta,sanyi taji aranta don ta gama yarda Allah zai zaba mata abinda yafi Alkhairi agareta duniya da lahira da haka barci ya kwashe ta…………..
Cigaba
………DUBAI……….
Tunda mun gama siyayya dan Allah mu dan yawata kafin mu koma gida mana,dix is my last coming too dubai single fah,dariya mukhtar yayi sannan yace kin sa rai zuwa da mijinki kenan,offcos garin zai yi dadin honeymoon ta fada in a serious tone don kar mukhtar ya sata dariya,saleem yace uhmmmmm umma kin fara fin karfina fa,dariya ta fashe dashi sannan tace,am trying to be civilize,murmushi yayi sannan yace tunda haka saka miki rana fa we no go here word,dariya umma tayi sannan tace hey you beta catch my leg,koh zan share ma hanya wajan zaynab,dariya mukhtar yayi sannan yace dont worry tana kin ma hanya ni zan ma,dariya umma tayi sannan tace you are a traitor daman ai,haka suka rinka raha daga baya suka shirya suka fita shakata abinsu,sunje wajaje dayawa daga nan tayi ma su mamy da su noor tsaraba,ammar daman yace ta siyo mishi gwal yana son ba batool as there three year anniversary gift,lokacin tsokanarsa ta rinka yi,wai shine kaninta amma ya fita tsufa,gashi ya fara grey hair,kuma ya fara ajiye yara so shi zai fara ajiye jikoki,dariya yayi sannan yace ya umma insha Allah na mace zaki haifa first saboda mu tsufa tare tunda kin man wayau kin aurar da mu,dariya ta rinka mai har da gwalo,lokacin da batool ta fito ta gansu suna wasa da dariya abin yayi mata dadi har take cewa,Allah ya umma wani lokaci acting kike kamar kece karama,dariya umma tayi sannan tace baki sannan ni da ammar five and six bane,wallahi kam kafin husna tazo ta zama five n half ta raba tsakaninmu ammar yace,sannan ya kara da cewa wannan yarinya can be a drama queen sometimes,dariya batool da umma suka rinka yi,yadda ammar da husna suke numa kishi karara akan umma abin is suprising,sannan tsakanin shi da husna duk wanda ya shiga ya sha kunya idan suna tare,sai sa babu mai son shiga tsakaninsu.
Park suka je washe gari wannan harda rushd ma,amma yi ta rinka yi kamar baya wajan don ta dau alwashi having fun,rollercoaster ta saka suka hau amma shi rushd yaki hawa wai shi ba yaro bane,ita ko kallonsa ma ba tayi ballantana ta tanka,azuciyarta kuwa cewa tayi daman bance ka hau ba ai,dan iyayi kawai…….Da suka gama having fun a park suka karasa wani ice cream stand suka sha sannan ta kara draging dinsu zuwa wani cup cake palace,anan suka yada zango,sai da taci cup cake flavour kusan biyar,za tayi ordering na shida mukhtar ya hana,kallonsa tayi sannan tace tasting nake fah,baka san ina satan recipe bane,dariya yayi sannan yace offcos na sani mana,ni dana san halinki,amma ai month end akwai problem,zare ido tayi sannan tace amma ya mukhtar ka daina jin kunya ta fa,dariya kawai yayi bai ce komai ba,don yasa abinda take son yi,tana son maze kunyar da yasata ciki neh,tunda yaga tayi shiru kanta asunkuye ya gane yayi nasara yanxu zata barsu su koma su huta,if possible bazata kara fitowa da sunan yawo ba har su tafi,dariya mugunta yayi,hararansa tayi wanda shi kadai ya gane manufar hararanta,kallon saleem tayi wanda ke danna wayarsa alamon wani abu mai mahimmaci yake,shi kuma rushd waya yake amma baza kace yana magana ba don ba’a jin abinda yake fada kwata kwata,da haka suka tashi suka wuce umma nah sending mishi invisble daggers,shi kuma yana dariya kasa kasa,saleem neh ya tambaya mai ya faru don shi hankalinsa baya wajan lokacin da abin ya faru,rushd neh kadai yaji amma ya maaze,ajiyar zuciya umma tayi jin bai ji abinda ya faru ba,dariyar da mukhtar ke rikewa neh ya fashe dashi sannan yace ai,,,,,,,da sauri ta katse da cewar,ai babu komai kawai mun gaji neh ta fada tana harararsa,saleem murmushi kawai yayi don yasan tunda ta fada haka bata son yaji neh,shi kuma bai pushing dinta ba …..Shima haka mukhtar bai kara cewa komai ba har suka karasa hotel din kowa ya shige dakinsa acikin suit din bayan ta tambayi saleem yaushe zai gama aikin da ya kawo shi,kuma yace gobe murmushi tayi sannan tace kenan zata shopping gobe da ya mukhtar kafin ka gama sai su wuce jibi tana fada ta karasa shigewa…….
Vote
Share
Comment
Much love Ummeeter
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲🌲
🌲🌲🌲
🌲🌲
🌲
Oh my my,it getting to an end,but still along way to go,six to seven chapters to go
You keep me guyx love you all xoxoxoxo
Dedicating this chapter to aysherudahmad and umma21
Love u guyx
You alway make my day.
Allah ya bar kauna 💋💋💋💋
It good to be finally at home Wallahi, ammy baki gaya min dubai haka yake da kyau ba,dariya ammy tayi sannan tace,ai na zata kin zaga da kika je da mamynki ai,tab wannnan tsohuwar ai zama tayi cikin suit babu idan take fita,dariya ammy tayi sannan tace bari ta jiki ni babu ruwana,dariya ya mukhtar yayi sannan yace nema dai babu nawa ruwan,hararansa tayi na wasan suka cigaba da fira gaba dayansu har da su zaynab,daman shi saleem ya koma canada daga dubai,amma fa bai koma ba,sai daya sa umma ta bashi number zaynab.+
wai kai baza koma abuja bane ko baka da aiki neh umma ta fada tana kallon mukhtar,murmushi yayi,sannan yace ai tare zamu tafi,you and who,ni tare da ammy zamu so you beta go,dariya yayi sannan yace kece babban abokin ango ne fah so ya kamata kina nan ai,daga hannu tayi ta taba goshinsa sannan tace amma jikinka bayi zafi ba dana ce baka da lafiya
ka gan zukekiyar budurwa kamar ni ka kira ni da aboki haba dai,dariya ya kara kwashewa dashi,ana haka ammy ta fito tana cewa dariyar meye ake neh,dariyar mukhtar ya dakatar sannan,yace wallahi ni da wannan daughter dinki ce tana da abin dariya,murmushi ammy tayi sannan tace kana dai fitinar ta da tsoka,wow ammy kamar kinsani,fira suka yi har mukhtar,yake gaya ma ammy flight dinshi karfe biyu neh,kallonsa umma tayi,sannan tace kaga sabi sabinka ba,ammy da bata tambayeka ba kana azarbaben gaya mata,ni nah tambayeka kaki gaya min,murmushi yayi sannan yace me kike ci na baka na zuba,ke da zaki kai ni airport so chill,harararsa tayi tare da cewa hell no ni ba driver dinka bane ta fada tana murguda baki,girgiza kai ammy tayi lamarinsu sai su,kana shiga tsakaninsu kuma su baka kunya,so gwanda ka samusu ido kawai.
madams kun fito kenan,nap din ya ishe ku,murmushi aysha tayi sannan,tace na tsaya pakaging din kayana neh,dariya ammy da umma suka fashe dashi,duk zumudin tafiyar neh haka aysha ammy tace,turo baki aysha tayi sannan ta zauna tana kukunai,suko dariya suka rinka mata.
ya mukhy ta kirashi tana dariya shekiyanci,kallon uku saura kwata ya mata sannan yace ango zaki ce, dariya ta dada yi sannan tace noted,idan kaje kace ma mamy ni dai na dawo lagos da zama,dariya yayi sannan yace nasan,mai sa kike son guduwa ai,toh ai ammyn ma barinki za tayi itama ba,kai zaka hanata bari nah,dariya yayi yana jijjiga kai sannan yace,shi dai ismail ya shiga one chance gaskiya,dariya umma tayi sannan tace tunda ba kai ka shiga ba ai da sauki,
Agogon hannunsa ya kalla sannan yace tom bari na shiga kar kisa nayi missing flight dina,murmushi tayi sannan tace kamar zanyi missing dinka fah,dariya aysha tayi sannan tace umma kin cika neman tsokana fa,murmushi umma tayi sannan tace ai abokin wasa na neh tana fada tana kashe mai ido.
Dariya yayi sannan ya mike saman kujerar da suka zauna,hannu ya daga musu sannan ya wuce
Mu biya mu sha ice cream,uhmmmm sannu bakin shan zaki,ni dai rakaki zan yi kawai saboda ban sha zaki,ina da sensitive teeth,dariya umma tayi sannan tace you are missing much,conneting din wayar tayi ta kunna fav wakar ta beginning by jeoboy,minning din wakar suka rinka yi ita da aysha kamar wasu posh american chicks. tsaya wa suka yi wani bakery mai suna “elite sweet”,suka siya ice cream,pizza mah ammy burger and cake, meat pie suka siya ma zaynab sannan suka wuce gida.
Suna kai wa,suka yada zango afalo suna cin guddies dinsu,daman sunce ma shaila kar tayi abincin rana da su so bata mayi girki kwata kwata ba,zama suka yi suna kallo dukkansu har da shailan mah,yanxu shaila mamaki take ba umma yanda take shige mata,fira suke ammy nacewa mai dinki yace ya gama ankonsu sai gobe,ayo ya kaisu su amso,umma tace ammy kawai ya amso da kansa tunda ya san wajan ni duk na gaji bazan kara fita ba sai ranan da zamu tafi,ranan lagos zai hallaka ni,i want to look posh at my yayas wedding,
wooooh look at who is talking kice za kiyi posh makeup kenan,sosai mah,can u bliv ban taba yin heavy makeup ba,likeserious zaynab ta fada tana zare ido,girgiza kai umma tayi,okay kenan ni zan miki makeup,kinsan am a makeup astist,so promise to make u inresistable, ismail zai zo ai koh,off cos wow kinga nice timing kenan,dariya ammy tayi sannan tace yaran zamani sai ahankali,dariya dukkansu suka yi sannan suka tashi don yin sallar la’asar.
STORY CONTINUES BELOW

Abuja here we come umma ta fada da suka shiga suka zauna akujeransu cikin airplane din,zaynab dariya ta rinka mata tana cewa u act like a baby sometime,dariya umma tayi sannan tace dia is no fun in acting serious all the time ai.
Kinsan mu uku aka haifa and we were isolated,so na saba wasa da kanne nah,sai sa am not the big sisi type,i play with everybody act like a baby too,saboda yana sani nishadi.wia is the fun in being grumping,dariya zaynab ta sake sannan tace i gat wia you are coming from.
Fira suke tayi har ba sun sa ankai ba sai da suka ji airhotess din na cewa za suyi landing,ajiyar zuciya sukayi sannan umma tace we have arrive finally.
Murmushi suka yi dai dai an bude kofar jirgin mutane sun fara fita,jakarsu suka dauka sannan suka kama hanyar fita.
Ango ango ka sha kamshi umma ta fada tana murmushi,kallonta yayi tare da mayar da mata da nashi murmushin kafin yace,ai na zata baza ki dawo ba sai ana gobe biki,dariya tayi sannan tace ai ammy neh ta saka da sai gobe zanzo,kasan biki ace na da namiji ake,it very boring tunda babu wani entertainment,kallonta yayi sannan yace waya gaya miki babu entertaiment,ai da baki dawo yau ba da barbeque night ya wuce ki yau,wooooow are you serious zaynab ta fada, sosai mah yace dai dai sun kai mota,ahhhhhhh ammy forgive my manner kinzo lafiya dariya ammy tayi sannan tace ai idan ka hadu da wannan talkertive din sai Allah,chuno baki umma tayi sannan tace ammy nifa bana surutu, dariya sauran suka yi tare da shigewa mota,umma na front sit,sauran nah back da ammy
Toh ya mukhtar menene dressing code din,normal engliah wears kawai,for mata black skirt ko trousers da red shirt while maza any shade of blue jeans and black shirt, uhmmmm nice yayi kyau,bari na gani,zee do you guyx have anytin to wear or say mun tafi shoping, shiru ta danyi tana tunani sannan tayi grinning kafin tace shopping!!!!!!,juyawa umma tayi ta kalli mukhtar sannan tace ya mukhtar ka ajiye mu a BS boutique zamu biyo cap mu dawo,girgiza kai yayi sannan yace,ku dai yi sauri domin kunsan outdoor neh so zamuyi amfani da guest house din Abba dake airport neh, wooooooh nyc but long joueney again,ai da nasan wajan neh da mun tsaya wajan kawai sai husna ta tawo mana da kayan sawan mu,anyway sai mun dawo ta fada kafin ta bude kofar ta fita tunda yayi parking,ammy neh ta leko kafin tace zan ce mai ya kai kayanku gidan momynki saboda chan baza ku takura sosai ba,okay tanx ammy love,murmushi ammy tayi kafin mukhtar ya ja motar suka wuce……..
Do you know what i feel like zaynab ta fada in and amused tone wanda yasa dukkansu suka bar abinda suke suka kalleta,gira ta daga musu sannan tayi murmushi mai sauti kafin tace,gani nake kamar am living all those novel farytale dinnan,idan kayi sabon saurayi sannan zaka je kayi spending weekend agidansa sai kazo shopping din lingerie,dariya suka fashe dashi dukkansu wanda mutane kalilan dake shopping sai da suka juyo suna kallonsu,umma daga hannu tayi ta kai dai dai gefen kanta sannan ta jujuya yatsar ta alamon kin fara hauka koh,dariya zaynab tayi sannan tace like serious fah,murmushi umma tayi tare da jijjiga kai kafin tace daga gani an fara son dan uwana neh sai sa,murmushi tayi tare da rufe fuska,dariya umma tayi sannan tace babu wani,banson gulma ehe,gwanda ki bude fuskarki,yanxu ki gama maganar sex sai kizo kina rufe fuska ma abin da bai kai shi ba,toh ni ban yarda ba,dariya aysha tayi sannan tace ai zaynab akwai bakar kunya (note d sarcasm) dariya umma tayi tana picking kayan da za tayi amfani dashi,wayarta neh yayi kara ta daga,husna ce take cewa ta siyo mata top ita bata da ja,okay kawai tace sannan take tambayarta inda take,cewar tayi ta sauka gidan momy amma yanxu tana gidan batool,okay am kawo mana kayanmu neh,gaskiya ban sani ba tunda ban nan,amma dai yanxu zan koma,daga nan suka yanke wayar
tun kafin su gama zabar kayar suka nema uber,yana karasowa dai dai da sun gama picking kayan,biya suka yi kafin suka fita tare da shiga motar suka karasa gida.
Suna isa bayan sun gaisa da momy neh suka shiga don yin sallah kafin suka fito suka ci abinci,lokacin dai dai karfe hudu da minti talatin,daki suka shiga watsa ruwa duk suka yi sannan suka shirya,husna ce ta shigo,tana ina maman ashrav neh, murmushi umma tayi kawai,tana isa dakin umma ta amsa ashrav,bayan sun gaisa da su zaynab ta juyo tana ma umma shagwabar da ta saba,dariya umma tayi sannan tace kunga yadda wannan mamar take kamar wani baby,toh ke idan kina shagwaba ashrav yayi mene,dariya su aysha suka yi duk da ba komai suka gane ba.Shiryawa itama tayi, kallonta umma tayi sannan tace wai wayace matan aure suje barbeque dinnan neh mah,dariya husna tayi sannan tace ki rufa min asiri karki fada idan bobby yake, idan ba haka ba wallahi hanani zaiyi,kinsa darun da muka yi akan zan je barbeque dinnan neh,uhmmmmm ai baban ashrav akwai matsifa idan yaso,inda kika san banda amfani,kamar ni banda masoya,rufe ido yayi ya zazzaga min,har da cewa zanje na ajiye masa yaro asanyi,gani katako dariya umma tayi sannan tace da kyau,kice kanina yashiga daddies mood kenan,tabe baki husna tayi sannan tace no b only daddies mood,time umma ta kalla sannan tace let go ya mukhtar ya fara kirana,fita suka yi dukkansu sanye da straight skirt da jan riga sannan suka yafa bakin gyale da jan takalma akafarsu.
Motar momy suka dauka matrix bayan sun saka kayansu abooth suka shiga
batool zata neh itama umma ta tambaya,dariya husna tayi sannan tace ai darun da na tsaya kallo kenan,shi ya ammar yace bazata je ba,ita kuma maman haydar tace taji amma fa idan shima baza shi ba,wai ya ammar har da cewa ya za’ayi ta shiga crowd da danyar goyo,abun ya ban dariya yaro dan shekara daya da wata uku ace danyar goyo,kai mazan nan case neh wallahi cewar zaynab,kunga wani irin possesiveness sai kace mu matan bamu san yaran namu,as if ba mu mukayi nakudar ba,gaya min fa yar uwa,sai da suka spending kusan awa daya kafin suka kai saboda holdup.
Suna kai lokacin har an fara gashe gashen nama,daki suka shiga dake cikin guest house din,daman bangare daya na mata daya na maza neh,shiga suka yi suka ajiye jakarsu kafin su kai yi sallar magrib,bari su kayi suka hada da isha kafin suka kara shiryawa sannan suka fita garden din inda aka shirya barbeque din,gashi akwai swimingpool am babu halin shiga.
STORY CONTINUES BELOW

OMG dan Allah kalli yadda wachan dajjajan ke kyalli umma ta fada,dariya husna tayi sannan ta fada ma zaynab akunne,she ix a freak for chicken,dariya suka yi sannan suka karasa shiga,Kowa ka gani murmushi keh yana fira da dan uwansa ,amma amarya da ango basu iso ba tukun ko nace basu fito ba,umma tace wai ina amaryar take,tanan suna shiryawa,okay daman na kirata tace suna hanya dazun,karasawa wajan kazar suka yi tare da daukan disposable plate,yanka musu akayi umma ko magana bata karayi ba ta samu waje ta zauna ta fara ci tana korawa da chi exotic,batool neh ta karaso ita da ammar,dariya husna tayi sannan tace da kyau sisi,kashe mata ido batool tayi sannan suka tafa hannu,ammar wajan ya umma ya karasa suna ta fira,junaynah tana ta tsokanarsa suna raha dukkansu uku,minti da bai wuce sha biyar ba amarya da ango suka fito nan aka fara shagali.
Ana cikin shagali umma ta je dauko drink,wajan juyowa ta bakade mutum,kallonsa tayi na mintin da bai wuce biyar ba sannan ta raba gefansa tayi wucewarta abinta,mustapha kuwa da shima drink yaje daukowa komawa yayi don ya kasa,tabbas yanxu yasan baya mata irin son da yake mata da amma ganinta kawai yana sashi kara dana sanin abinda ya aikata,ko babu komai ai yar’uwarsa ce bai kamata ya bada kofar da matarsa zata rai nata ba,shafa hannusa yayi akansa in fustration.
Ita ko fareeda tunda ta gan umma take monitoring din moves din mustapha,ganin da tayi suna kallon kallon kishinta ya motsa.Ni kuwa nace aiki ya ganta.
Kidi aka saka suka rinka rawa abinsu kowa na farinciki,ita kuwa umma ba abinda ya dameta,kallon banzan da fareeda take wurga mata bai dameta ba sai rawarta take,ko faizar da umma take zuwa ta shiga tsakiyarsu da mukhtar tana rawa bata damu ba sai fareeda da ko kallon banza mijinta bai ishe umman ba,gashi ba karamin shiri faiza suke da umma ba,umma tana kiranta anty faiza itama ma faiza na kirarta ya umma domin kawancen dake tsakaninta da husna,sannan kuma tana ganin girmanta sosai sannan suna wasa sosai domin wani lokacin umma cewa take ni ba yayarki bace ni amatsayin abokiyar zama zanzo so ki shirya,ita faiza bata daukar zancen amatsayin komai don da umma ta so auran mukhtar da bata hada su tun farko ba,kuma duk Idan zata nema tsokanar sai suna tare su ukun, musamman idan yazo bakery, har ta rinka ce mai,no dating around working hours
kwata kwata bata da boye boye, idan haka duk yan uwan miji suke toh da baza arinka samu matsala ba .
Sai wajan karfe goma da minti ashiri aka gama mutane suka rinka watse wa,su umma kuwa da daman da niyyar kwana suka zo daki suka koma ita da su zaynab da wasu cousin din su junaynah,junaynah itama tabi wannan mijin nata mara san mutane,daman su husna ba kwana za suyi ba.
Kayan barci suka sanya sannan suka saka himar suka fito falour don kallon,wani american film su gan anayi a galaxy mai suna Twitches,kallon suka zauna suna yi ko ina tsit kake ji sai karar t.v don su kadai neh, abokan ango sun kai amarya da kawayenta gida,motsi sukaji apart din maza wanda yasa su tsorata tunda sun san su kadai ke gidan,kallon kallon aka fara atsakaninsu duk sun sure shirin guduwa suke su koma part dinsu kawai sai suka gan abude kofa,ihu suka zudduma dukkansu suna neman hanyar guduwa,ihunsu ya saka duk ya firgice yana tambayar mai ya faru,muryar da suka ji neh yasa suka tsaya suna kallonsa,tsaki umma taja sannan ta fara kukunai tare da komawa ta zauna saman kujerar ta cigaba da kallon abinta rai abace,ai wannan sai ya kashe mutum ta fada aranta,haka safina da maryam mah suka koma suka zauna,zaynab tace haba akhy ai sai ka kashe mutum,daga ina ka pillo kuma yaushe kazo sef,murmushinshi yayi mai matukar kara masa kyau sannan yace lokacin kuna ta shedanancinku mana,tura baki zaynab tayi sannan tace muna dai having fun,komawa sukayi suka zauna suna kallon,shi kuma yanata satar kallon umma ta gefen ido,ita kuma tana jin alamon ana kallonta amma taki juyo kai sai kallonta take kawai abinta.Ahaka su mukhtar da abokansa suka dawo suka samesu,suma suka zauna akayi kallon dasu daga baya suka shiga don su kwanta.
Washe gari da safe suka koma gida bayan sunyi breakfast,umma na shiga gida ta fada dakin mamy tare da fadawa cikinta tana cewa mamynah nayi missing dinki fa,dariya mamy tayi sannan tace babu wani ai naji sakonki wajan mukhtar,dariya umma tayi sannan tace mamy ki dai na yarda da maganarsa fa uhmmmm hadani dake kawai zaiyi,tana fadar haka ta juya ta gaida mutanen dake dakin kafin ta mike, falon abba ta shiga ta gaida su tare da cewa,Abba irin kai da twiny kuna having twin time koh,murmushi kawai yayi domin idan yaga umma tuna mai Aisha take,halinsu daya da duk neman tsokanar ma,don lokacin haka take wa mamansu da babansu,sai tace mama wai ku mata da miji kenan kuna soyayya,tun mama na kwabarta harta daina.Tashi tayi tace bari ta shiga ciki,abba yace toh yar mamy,murmushi itama ammy take,umma na fita ammy tace kaima ka tuna kenan koh,girgiza kai yayi alamon eh,murmushita fadada sannan tace Allah yayi miki rahma Aisha.
Bridal shower su faiza za suyi babu yadda ta iya dole sai taje,amma ko da taje bata bari ko inuwar farida ya tabeta ba don bata son hayaniya,kuma ma bata dade ba tace ma faiza zata tafi,eatery dinta ta tafi ta shiga office dinta ta zauna tana ta tunanin rayuwarta sannan daga baya ta tashi ta koma gida, don gidan momy zata kwana yau.
Washe gari bayan sallah juma’a aka daura auren mukhtar najib muhammad da amaryarsa faiza yusuf akan sadaki dubu saba’in.
Bayan daura auren angwaye suka tsaya suna karban gaisuwa daga baya kuma aka garzaya gidan amarya don suyi hotuna,karfe takwas aka kai amarya gidanta aciki kuwa har da umma a yan dauko amarya,abin gwanin ban sha’awa amma kuma sai da fareeda ta san yadda akayi aka bar abin magana don gaggaya ma umma magana tayi wanda ba karamin kuluwa umma tayi ba amma bata ce komai ba ta fita daga gidan,mamakin da su husna da elham ke ciki kuwa ya hana su furta komai har sai da suka ji kukan faiza,kasa cewa komai suka yi su ma kawai cema faiza sukayi zasu wuce amma insha Allah zasu zo suyi sallama kafin su bar Abuja.Suna fita faiza ta juya ta kalli fareeda tare da cewa haba ya fareeda wannan wana irin cin mutunci neh,so kike ki saka tsanar dangin mijina araina ko so kike su su tsane ni,tsaki fareeda tayi sannan tace wani dangin mijin,kina nufin umma ai da dangin miji irinta gwanda babu,wannan da take kwace mazan mutane,zare ido faiza tayi da sauran matan dake dakin mah, sannan faiza tace miji wa ta kwace kenan,ajiya zuciya fareeda tayi sannan tace nawa mana,wani irin kallon faiza ta wurga mata sannan tace idan ta kwace miki miji toh mai sa zata auri ismail,ko baki gan yadda take yawo da wani bane wajen dinner,duk idan ta shiga yana biye da ita,murmushi fareeda tayi sannan tace ba dole ta auri ismail ba tunda bata samu yadda take so ba,tunda bata gaban mijina,dariya faiza tayi sannan tace toh saurara kiji na baki wani labari…………………………
vote
Share
Comment
Lot of love ummeeter
💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
💐💐
💐
Am inlove with this page
But dont know weather you guyx will follow my lead…….💋💋💋💋💋
🍁🍁Dariya faiza tayi sannan tace toh saurara kiji na baki wani labari………………………… kisani ba tun yau mustapha ke son ya umma ba,tunda kafin ya san da ke aduniyar nan yake sonta,duk da bai gaya mata ba duk wanda ya gan yadda yake kallonta ya san abinda ke zuciyarsa,amma matsalar bai gaya mata ba,toh ko da ya gaya mata ma ai bai da amfani,
keh fa dadi ya kamata kiji tunda adalilinta ya hadu dake,dan da bata zo Abuja ba,kuma da bata siya eatry dinnan ba,da an gaya miki zaki hadu dashi neh,duk da ance matar mutum kabarinsa,ai da dalili kuma itace dalilin.+
Toh ki sani kin tafka babban kuskure,lokacin da naji kina fadi mah sister rukky abinda kika aikata wallahi na zata wasa neh,amma dana gan yadda ya umma take ma mustapha kallon tsana nasan cewa da gaske kike,ki sani kin tafka babban kuskure arayuwarki,ai kishi ba hauka bane, wai tsaya ke angaya miki da akwai aure atsakaninshi da umma da kin isa kiyi wani abu neh
yanxu kin hada shi da yar’uwarsa ke kina ganin kin yi abin kirki kenan,Kin cimma burinki ko,irin kin raba mijinki da aurar wata mace koh,murmushin da yafi kuka ciwo faiza tayi sannan ta kara da cewa toh wallahi idan mustapha na da niyyar yin aure babu mai hanani ko ke baki isa ki haba shi ba,,,,,,,katse ta fareeda tayi da cewa ban gane meye kike nufi ba,meye sa kika ce babu aure tsakaninta da mijina,gani nayi ba mahaifinsu daya ba. Dariya faiza tayi tare da girgiza kai,tunda nace babu aure atsakaninsu ke dai ki yarda kawai ba sai na tsaya yin miki dogon bayani ba,
kallonta fareeda take cike da mamaki,gaskiya ni dai kiyi min bayani kar ki barni aduhu, Okay bari na gaya miki tunda kin matsa momy da kike ganin ita ta shayar da umma lokacin mamanta bata jin dadi sannan bata da ruwan mama,toh ki gaya min akwai aure atsakaninsu kenan,hannu fareeda ta daura akai tace na shiga uku mai na aikata kenan,
kinga abinda nake jiye miki kenan,kishi ya rufe miki ido,tun ba yau ba nake baki shawaran ki sassauta kishinki, amma kin ki jin maganata kin yi kunnen uwar shegu da maganata,yanxu ina gari ya waye mu,kinsan husna da elham ba barin maganar nan za suyi ba,ya kike so uwar mijinki ta kalle ki, kin san yadda kowa ke son umma kuwa,inaga babu abinda kika sani akan dagin mijinki,ke dai kawai dadi miji,toh ta hanyar umma zaki iya samun duk abinda kike so awajan dagin mijinki,amma keh kin tsaya kina kishi da wanda bata da maraba da noor ko elham awajan mijinki, ajiyar zuciya fareeda tayi sannan tace,ni faiza mafita zaki nima min ba kara zuba fetir asaman wutar dake ci ba,murmushi faiza tayi sannan tace ai yanxu lamarin is out of hand,sai dai ki bari muga abin da zai faru don kin riga da kin bata rawarki,ajiyar zuciya fareeda tayi tana jijina lamarin.
Kina tunanin ke ki ke da matsala ko toh, Kinga nima ai mukhtar sonta yake,zare ido fareeda tayi sannan tace kuma baki jin tsoro kar ta aure miki miji,wai ita wani irin farin jini neh take dashi wajan maza,dariya faiza tayi sannan tace ai tun farko mukhtar ya gaya min shi mata biyu yake da niyyar aura,amma tabbas da ya umma ce zata zama kishiyata da murna zanyi don bata da matsala ga sanin ya kamata,sannan tana da adalci saboda haka nasan bazan wulakanta ba,amma kinga tunda nasan ba ita zai aura ba nafi jin tsoro yanxu
maisa kika ce kinsan ba ita zai aura ba,murmushin gefen baki tayi sannan tace na farko ansa mata rana da wani but kafin nan ya umma ita ta hadani da mukhtar,duk da ranan dana fara ganinsa na ji na kamu da sonsa,sai da ta tambaye ni idan ina son sa,da farko naki magana shine take ce min gwanda na gaya mata ko ina kallo zata sama mai wata,dana ji haka nace mata eh ina son sa,bayan na gaya mata shi ne take ce min tana fatan bani da kishi dayawa domin yayanta yace shi ba mata daya zai aura ba,sai dana ji gaba na ya fadi amma na danne nace mata babu komai,ina zuwa gida nayi sallar dare na nima zabin abinda yafi alkhairi agareni awajan Allah ma daukakin sarki,bayan kwana hudu da yin haka da yazo wajan aiki,wato eatry dinmu shi ne ya umma ta kira ni office dinta sannan ta bar mana office din, nan yace min tunda yace ma umma ta zaba mai mata yasan baza tayi mai zabin da bai dace dashi ba,dana tambaye shi mai sa yaceta zaba mai mata,sai yace saboda ina sonta amma nasan bazan sameta ba saboda haka tun kafin yayi zurfi ya kamata ya cireta aransa tunda ita tayi broda zoning din shi,murmushi nayi don naga kokarinsa sannan naji dadin da bai boye min ba tunda tun aran nayi zargin budurwarsa ce ma fira muka dan yi don mu fahimta juna sannan ya tafi,bayan ya tafi shine nake tambayar ya umma ko tasan mukhtar nasanta,murmushi tayi sannan tace kar nasa wannan ya dame ni,sai sa ta zabe ni don tasan bazan watsa mata kasa a ido ba zan kula mata da yayanta,kuma na cire tunanin cewa zai yi wani auren kuma
idan nayi treating dinshi right zai manta da ra’ayin wani aure ta san halinsa sosai sai sa ta fadi min haka,har da ce min kar na damu zata bani tips din zama da miji idan muka zauna,wanda ina looking forward to that,domin ya umma akwai ilimi sosai,wasu na mata kallon babu abinda ta sani amma tabbas duk wanda zata zauna kishi da ita zata sha wahala idan har ta neman rashin zaman lafiya,ita irin matan nan neh da are very innocent,idan akace ma tayi wani abun ma bazaka yarda ba,idan kinji sermon din da ta basu husna sai kinyi mamaki,wallahi zaki iya rantsewa ta taba aure,kuma idan tana magana bata jin kunyar wanda take ma bayani,cewa take ilimi neh kowa ya karu dashi.Sai sa nake tausaya ma kishiryarta idan bata yarda sun zauna lafiya ba,duk da bata da hayaniya amma idan ka tabo ta sai kayi dana sani.
Haka suka rinka fira kafin abokan ango suka karaso,ita kuma ta tafi tana tunanin halin da ta jefa kanta aciki,gashi harda karya tayi ma abban ameer,yanxu da wani ido zata kallesa.
STORY CONTINUES BELOW

Momy daman akwai abinda ya shiga tsakanin ya umma da ya mustapha bamu sani ba,momy cikin rashi fahimta take kallon elham da husna wanda suka tsareta da ido don jin ko akwai basu sani ba,sannan tace kamar mene kenan,momy idan kinga rashin mutunci da fareeda tayi ma ya umma kuwa kamar wata sa’arta ko da ya musty yayanta neh kuma ita fareedar tana matsayin matarsa ne ai ido ba mudu bane yasan kima, cikin mamaki momy tace ita umma daman ta taba gaya muku wani abin ya hadata da su neh,a’a ammy babu,ina ma zata gansu ita da take Abuja su suna kano,sai dai idan lamarin ya dade da faruwa husna ta fada tana kallon elham,zare ido elham tayi sannan ta mayar da kallon kan momy tace momy gaskiya bamu da tabbaci amma idan kuwa abinda muke zargi gaskiya neh toh sun kai shekara biyu kenan da yan watan ni suna gaba kenan,dafe kirji momy tayi sannan tace da ran nawa zuri’ata zasu rinka gaba,kira min mustapha apart dinsa,sannan ke kuma ki kira min umma.
Naji wani magana da babu dadi amma tun kafin na fara magana gwanda ku gaya min da kanku me yake faruwa atsakaninku. Shan jinin jinkinsu suka yi,daman umma da ta fito ta ganshi afalo tasan shi kenan komai ma za’ayi ta ta kare kenan,daman tasan tunda su elham suka ji lamarin tasan baza su bari ba don tasan halinsu,ko elham ta bari husna baza tayi shiru ba,dago kai tayi ta kalli momy sannan ta turo baki kafin tace momy ni ban gane bafa,meye ya faru ta fada tana banka ma husna da elham harara,momy na kallonta,cikin murya da babu wasa acikinsa tace karku nema raina min hankali rahama,gabanta neh ya fadi domin momy bata taba kiranta da rahama ba ko sau daya,daga gani ranta ya bace,shi ko mustapha kamar an daura bakinsa ya kasa magana,juyowa momy tayi kanshi tace mustapha tun kafin rai na ya dada bace ku gaya min abinda ya shiga tsakaninku domin na samu labari bakwa magana kuma ya kai tsawon lokaci mai yawa.Daga kai su kayi suka kalli juna,harara umma ta banka mai sannan tayi tsaki wanda ita kadai zata iya juyo karansa sannan ta dafa kanta da hannu,ita wallahi andaura mata zafi biyu,mai momy take so tace yanxu bayan ita akaima abun amma atasata gaba ana tambayarta,ita basan ma fa mai tayi mai ba ya gaya mata bakaken magaganu,yanxun daga ina ake so ta fara magana……
Tsawa momy ta daka musu wanda ya saka dukkansu dake palour suka tsorata,su zaynab da har sun fara barci adaki ma sai da suka fito don ganin mai ke faruwa……..Hawaye umma ta fara yi ita arayuwarta bata son tashin hankali wallahi sai sa tun farko bata fada ma kowa ba
magana momy ta kara yi cikin kaukausar murya,bace cewa nayi kiyi min kuka ba magana zakiyi,wallahi ku ka bari na kara muku magana sai nayi mumunar saba muku ta fada,sheshekar kukan da umma take sai dayasa husna itama hawaye,sannan sauran kuma duk idonu su ya cika da kwalla.Magana umma ta fara kamar haka………….
Shekara biyu da dori da suka wuce,ana saura kwana biyu bikinsu Husna da sauran, muna zaune agarden dukkanmu,sai kowa ya rinka zamewa yana tafiya har aka watse aka barmu mu biyu, daga ni sai ya mustapha,magana take wanda duk mai sauraro idan yaji yadda take maganar yasan cewa tattare muryarta yake da tsanar abinda zai fito bakinta, ina shirin tashi na bar wajan nima sai kawai naji yana ce min wai sona yake ta fada tare da kara rushewa da kuka,tsit kake jin palour kowa yana mamaki amma banda husna wanda daman tasan yana sonta,sai da ta tsagaita da kukan kafin ta cigaba,hakuri na basa tare da gaya mai nima naso shi ada alokacin ban san gaskiya ba,amma yanxu sai dai yayi hakuri don babu aure atsakanina dashi sannan na gaya mai dalilin hakan,bayan haka sai komai ya zama very awkward atsakaninmu amma ni kuma bana jin dadin yadda muke zama bama magana,bayan bikinsu da wata uku naje kano bikin basma,momy zaki iya tunawa nace miki baya min magana har nake cewa kiyi mana sulhu har aka mayar da abin ya komai wasa,toh dana je kano ko da muka sauka gidansa matarsa bata min tarba mai kyau ba, ni kuma ban san dalili ba,hakan kuma bai dame ni ba kawai na barshi akan bata cikin mood mai kyau neh,na shiga ciki nayi wanka sannan na wuce inda zamuyi event din, ko abinci ba’ayi min tayi ba fa,amma bai damen ba tunda ko da tayi min tayi mah cewa zanyi sai dai idan na dawo,ina zuwa gidan elham naci indomie dana sa husna ta dafa min,daga nan muku garzaya wajan bridal shower din,bayan nan kuma na koma gida,ban fito ba sai washe gari,”……..tayi skipping inda ta gansu suna makingout don bata son kowa yasan ta gansu”ita abin kunya zai bata, washe gari ban fito ba sai wajen karfe daya saura,nayi shirin fita gidansu basma,lokacin noor ta kira ni wai ta iso kano ina nake na ce mata yanxu zan fito,wai ina fitowa shine fareeda ta tare ni da fada,ta gaya min mara dadi har da cewa na dai na irin wannan shigar agidanta,mamaki abin ya ban amma da yake ta ban haushi shine nima na gaya mata mara dadin kafin na fita abina,daga nan kuma da tazo gidan biki ta rinka min kallon banza amma ban tanka mata ba, ni kuma ban dawo ba sai wajen karfe sha biyu saura,ina zuwa na kwanta abina,washe gari ina tashi da safe sai na wuce kitchen domin yunwa nake ji kuma ban ci abin kirki ba tun bayan breakfast din da nayi a Abuja da indomie da naci agidan elham,ina shiga na bude drower din dake kitchen din amma babu komai sai spicy,mamaki neh yacika ni wanda ya saka na koma na duba saman dinning table ko ido na neh bai hango kayan shayin ba,dana ga babu shi neh na koma kicin din na bude store din ko aciki suka ajiye,amma kuma akulle yake gashi ni kuma yunwa neke ji kuma masu gidan basu fito ba,zan fita kicin din shine fareeda ta shigo kamar zata bankade ni, matsa mata nayi kawai don ban shirya ma masifarta ba da sanyi safiyar nan,ina fitowa ya musty na gani zaune adinning din,gaishe shi nayi sannan zan wuce sai ya tsayar dani ya fara bani history akan yada gidansa neh kuma ban isa na tsallaka dokar matarsa ba,abin ya bata min rai da mamaki don aganina gori yake min, sannan nasan akwai abinda matarsa ta gaya mai ne,amma ai koma mai nayi mai ko matarsa sai ya zaunar da mu yaji mai ya hada mu sannan yayi ma kowa iyakarta,hakan neh ya saka na gaya mai ga gidannan na barme kuma bazan kara shiga lamarin gidansa ba na tafi abina aranan,ni dana yi niyyar kuma kwana,ace wai naje gidan dan uwana amma ko ruwan gidansa ba taba sha ba,Daga nan kuma ban kara ganinsa ba sai zuwansa bikin nan,sai sa ko data haihu banje ba nayi zama na tunda ita gani take don mijinta neh nake rabanta,gani take kamar ina son mijinta,sannan kuma bana son tashin hankali.
Shi kuwa mustapha mamaki neh ya hana shi furta komai,ita kuma umma tana kainan tayi shiru bata kara cewa komai ba,sai elham ce ta karasa da fadin abinda ya faru yau.Jinjina kai momy tayi tana jinjina girman maganar,kallon mustapha tayi tare da tambayarsa idan yana da abin fada,murmushin da yafi kuka ciwo yayi sannan yace ni kuma abinda fareeda ta gaya min daban neh,lokacin dana dawo daurin auren basma,samunta nayi idonta yayi jawur alamun tayi kuka shine nake tambayarta abinda ya faru,shine take cemin wai umma neh tayi mata rashin mutunci don kawai tayi mata magana akan dressing dinta,ce min tayi har marinta tayi tare da zaginta fa cewa ita yar gida matsiyace sai sa bata san irin dressing din yayi ba,sannan ta dora da ce min wai ai tace don an taimaka an aure tane za tayi mata wani gan gani wai ita mai miji sannan kuma wai idan tayi wasa sai tasa an sake ta,,,,,,husnace ta katse shi da cewa kuji wani irin shahararran karya,ya umma bata duka yara balle manya tunda take ban taba ganinta daga hannu ga wani ba wallahi,fada ma sai ka bata mata rai take yinsa amma shi,,,,,,daga mata hannu momy tayi sannan tace ya isa haka husna.sauran yan palour mah mamaki suke domin duk wanda yasan umma yasan wannan ba maganarta bane,
Yanxu naji dukkanku sannan na gane cewa rashin fahimta neh ya jawo dukkan matsalar nan,amma mustapha kai ne mai babban laifi ace baza kayi bincike kafin ka dau mataki ba,haushinta kake ji don babu aure atsakaninku koh,toh ai ba ita zaka ji zafinta ba tunda itama ba son ranta bane,ni zaka ji haushi ai tunda ban maka daidai ba,tsugunawa mustapha yayi guiwarsa akasa yana cewa momy wallahi ba haka bane sharrin shaidan neh,girgiza kai momy tayi sannan tace ai ba abinda kayi min sannan ka bar shaidan ya huta,babu ruwansa alamarinka,duk abinda ya faru daku kuce shaidan,bayan kaki yarda da qaddara neh,nan na zaunar da kai na baka hakuri amma kayi burus da maganata irin ga banza ta gama baka baki koh,toh daman duk wanda ba zaiji maganar mahaifiyarsa ba yana tartare da shan wahala,hawaye ya fara sannan yace momy kiyi hakuri wallahi sharrin zuciyata ce,murmushi momy tayi sannan tace ni nace kayi min laifin ne,
ni dai momy kawai kice kin yafe min,murmushi momy tayi sannan tace so nake ka sani idan bama duniya duk kaine babbansu idan ka bari matarka ta iya shiga tsaknanin ka da yan uwanka,ya za ayi kenan,kenan zumunci tarwatsewa zaiyi idan bamu da rai ko,gizgiza kai yayi sannan yace ba zai tarwatse ba insha Allah momy,na gane kuskure na zan gyara insha Allah,yayi kyau Allah ya taimaka,sannan dukkanku ku sani idan dayanku yayi gigin yanke zumunci wallahi dukkanmu babu yafe muku ba…….Zare ido dukkansu suka yi sannan umma tace insha Allahu baza mu fara gigin yake zumuncinmu ba,baza mu bari shaidan yayi nasara akanmu kuma ba,
juyawa Mustapha yayi ya kalli umma sannan ya rike kunnensa am sorry sista bazan kara ba,murmushi kawai tayi mai sannan ta girgiza kai,shima murmushi yayi,fada momy ta kara yi musu sannan kowa ya koma daki ya kwanta………..ni kuma ce Asuba ta gari jikokin Lamido
Vote
Share
Comment
Love ummeeter