Daddy ya Kara dubanta “Yasmin kina jin mu, ko da
yake zan yi magana da mahaifin ki, amma ke ma ki yi tunani”
Haushi suke ba ta gaba dayansu ta tsane su, babu
yadda za ta yi ne yasa ta ki iya zama da su guri guda domin tana musu kallon azzalumai son san irin zaman da take yi a gidan ba komai ba ne ya dame ta face kusantar ta da dan su, ta tsane shi ba ta kaunar sa
Abincin ta kawai ta fara ci don ta kammala ta tashi ta
ba su guri. Hajiya Zulaihat ‘ya ta mene ne matsalar ne?”Ta dube ta “Ba komai Mommy”
Daga haka duk abin da su ke cewa ba ta tanka musu
ba. Da ta ga ji da jin su ta ta shi ta nufi sashinta.
**
Umar bai ta shi barin gidan su ba sai kusan karfe
goma na dare ya hadu da Al’ amen sun dan yi hira sannan ya tafi gidansa da aka tanadar masa da sabuwar motarsa da a ka ajiye masa a Kofar gidan tun wajen La’asar, ya isa kataren gidan a cikin unguwar da Alhaji hashim yake kafin ka kai gidan, ya so a sauya masa amma dole ya hakura sai saboda baya so a dinga fahimtar saboda ita yake kin komai.
– Ya jima yana kallon tsarin gidan da yanayin yadda aka Kawata shi da kayan alatu. Babban falo ne da setroom a Rasa sai kiching da toilet a kwai kafar bene a falon sai dan Karamin daki store, sai sama da ya kunshe maka makan daki guda biyu da wajen shan iska mai girman gaske.
Hakika gidan ya yi matukar birge shi fiye da kima da
samu ya yi watsa ruwa ya kwanta. Yana daukar wayarsa ya ga kiran Zulaihat bai yi niyar ya kirata ba sai da ya ga sakon ta. Tana tambayar yazo masaukinsa.
Abin ya fado masa a rai watakila masaukinsa na kusa
da nata ka da ta ce za ta zo in da yake sai ya kira ta, yasanar da ita yadda ya ji dadin wajen da kuma kyawunsa, bai tambaye ta a in da take ba sai sanar da ita sai da safe zasu hadu a office gobe.
Zulaihat na matukar son Umar fiye da kima sai dai yaqi ba ta damar da za ta bayyana masa irin son da take masa, yana shigo da magana a duk lokacin da ya ga tana Kokarin kusantar sa da zance soyayyasai ya kawar da ita da barinta a wajen ko kuma ya dauko wani zance da ta aikata wani abu mara dadi.
Lamarin yana, sha mata kai sai dai ta dana dole akwai
ranar da za ta samu kan shi. musamman a yanzu- da suka kasance makotan juna
Office
Lokacin da Umar ya iso Kamfani kai tsaye babban office ya isa wajen Alhaji Hashim bayanan, ya je ne domin su yi wata tattaunawa, ganin bayanan ya bayar da sakon cewar idan ya iso a sanar da shi.
Lokacin da ya fito ya nufi office dinsa dai-dai lokacin
Abas ya fito daga office dinsa don aiwatar da wani aiki, suka yi kacibus da juna, kwata-kwata shi Umar bai gane shi ba a matsayin dan Hashim kuma mai babban matsayi a kamfani sai da ya ji wasu ma’ aikata suna kai gaisuwa ta girmamawa a gare shi.
Ya so ya yi masa sallama ganin yadda yake kallonsa kawai ya wuce shi.
“Malam, ba ka kula da mutane ne kai?”
Ya yi furucin cikin isa Umar ba tare da ya juyo ba yace “Ban fahimce ka, akwai sako da kake tsammanin zan ba ka”.
Abas ya ji maganar har cikin ransa, ba tare da Umar
ya tsaya ba ya shiga office dinsa. Abas ya jinjina kai saboda takaici ma hakura ya yi da in da zai je, ya koma ya kira lambar wayar mahaifinsa yana sanar da shi baya bukatar Umar a kamfanin don haka dole a fita da shi.
Da kyar mahaifinsa ya kwantar masa da hankali cikin
hikima. Don haka lokacin da Alhaji Hashim ya iso kai tsaye office din Umar ya je. Umar ya mike bisa biyayya ya gaida shi.
“Yallabai da kan ka”.
Alhaji Hashim ya zauna yana murmushi ya ce “Ka
san da kwarina ban fiya son jiki ba”
Umar ya jinjina hakan “Na ga zahiri a kuzarin ka,
Allah ya Kara lafiya da albarka a cikin rayuwa”
Alhaji Hashim ya jinjina kai alamar jin dadin
addu’arsa **Wani abu ya kawo ni, me ya hada ka da Abas ne
“Abas Abas, ban fahimce shi ba Alhaji “Ina ‘nufin da na ko baka gane shi ba ne jiyana
gabatar da shi a wajenka, yana da babban matsayi a kamfanin nan domin shi ne kusan komai in ka wuce ni ya kamata ace kuna da kyakkyawar alaka da shi”.
Umar ya dan yi murmushi ya fahimci komai don
haka sai ya ce “Kamar.. gaisuwa ranka ya dade, barka da zuwa”
„Yawwa ba ina nufin ya yi maka ba ku yi wa jun..
“Nagode da shawararka, amma* shi ma ka ba shi
shawarar kamar haka, hakan zai kyautata zaman mu”.
Shi kansa Alhaji Hashim ya kasa fitowa ya yiwa
Umar bayanin yadda yakamata domin Umar din ba wai kawai wadda za a taka ba ne ya kyale shi ma kyalle ne irin Abbas din to amma hakan zai kawo rudani ba karami ba a tsakani, saboda haka abin da zai cewar Abas shine ku girmama juna saboda hakan shi ya dace shi ba kamar kowa bane gayyatarsa aka yi, a hakan ma bai amince ba sai da suka zuba hannun jarinsu. Kuma yasan kansa yasan amfanin sa a wajen mu. Lallai zai yi wa dansa bayani gamsassu da zai fahimta
YASMIN HOUSE BUILD
Yasmin na zaune ta na wasu ayyuka da ta amsa a
wajen mahaifinta, ta na jiyo hirar Khadija da Rafia, a game da wasu ayyukan da aka kawo musu.
Wani abu ya fado ranta a lokacin da Umar ya zo
Office din ta. “Na ji dadin daganin ki a cikin mutane masu Kaunar ki, tabbas kin samu abokan zama masu kirki, su ma tamkar ki haka suke, ban yi tsammanin samun tarfa kamar yadda abokan aikin ki suka yi min ba musamman Khadija.
ya gama jawabin
Ya dan yi shiru yana murza yatsu, “Ina so na samu
soyayyar ‘yan gidan ku kamar yadda abokanan aikin ki suka so
“Za ka samu Umar wannan dole ne za ka samu”.
Ba ta yi aune ba tana cikin wannan tunani sai kawai ji
da ta yi Khadija na cewa “Lafiya” Ta dago da kai tana mamakin tambayar da take yi mata, ashe wai hawayene har ya wuce fuska ya fara zubowa kan kafadunta.
Khadija ta zauna kusa da ita ta saka hannu ta share
mata hawayen fuskarta “Haba Yasmin mene ne haka, me yasa kike so ki jawa kan ki ciwo ne, dan Allah ki daure ki yi hakuri ki daina dagawa kan ki hankali”
Yasmin ta Kara Share hawayen fuskarta saboda sun
gaza daina zubowa “Khadi ya zan yi, ban yi hakuri ba, shin ban yi dauriya ba, haba Khadi ka da ki yi min korafi ki rabu da ni na yin kuka ki rabu da ni na fitar da wutar da take cin zuciya ta
Khadija ta jinjina gami da rike hannuwan Yasmin
“Kin yi Yasmin kin yi Kokari fiye da tunani na, amm…
“Na daina, so kike na daina, kina so na daina son
Umar? Khadi ta ya ya, idan ma na daina zan iya manta cin amanar da na yi masa, Umar bai yafe min ba Umar ya kusan mutuwa saboda bakin cikin da na jefa shi, Khadi ya zan yi ya kike so na yi?’
«Hmm Yasmin ba ki ci amanar Umar ba, domin ni
shaida ce, kuma ina jiran ranar da zan hadu da. Umar ni zan warware masa komai, wannan ba cin amana ba
ne”
**Ka da ki so ma, mahaifiyarsa ta ce kada na kuskura
na kusance shi, ka da na kuskura na bari wata’alaka ta shiga tsakanin mu, na kasa daurewa na kira wayarsa na kasa magana a lokacin da wutar zuciyata ke ruruwa amma shauki da kaunarsa ke Kara kunnuwa cikin zuciyata. Wannan masifa ce babba Khadija”.
Khadija ba ta da wata dabara sai dai ban hakuri saboda ba ta da yadda za ta iya.
“Zan koma gida Khadija ki kula da komai”.
Ta dauki mukullin motar ta gami da jakarta. Ta na
shirin fita wayar ta ta hau kuka ta dauka. Mahaifinta ne?”
“Yasmin ‘ya ta kina lafiya?”
Ta kokarin danne damuwarta don ka da ya gane”
“Lafiya Kalau Daddy, ya aiki?”
“Aiki masha Allahu, na ce wadannan zanen da na
baki last week kin kammala ne?” “Eh Daddy na kammala suna mota na so jiyana shigo
na kawo maka na sha’afa?”
“To shi ke nan, yanzu bari na sa a zo wajen ki a amsa
ai kina office?”
“Eh, Daddy, amma zan fito yanzu kawai sai na shigo
na kawo maka na dan huta a office dinka
“To shi ke nan ‘ya ta dafatan ba matsala ko?”
– “Ba matsala Daddy”
“To shi ke nan sai kin Kara so ina jiran ki ‘ya ta”
Ba ta wuce mintina goma ba ta shigo cikin kamfanin, kai tsaye ofishin mahaifinta ta nufa, ma’aikata wajen na kai gaisuwa a gareta, dai-dai da lokacin da Umar ya fito daga office din Zulaiha, Yasmin ta gifta office din da kadan Umar ya fito yana jawo kofar. Kai tsaye office dinsa ya nufa, dukkaninsu sun juya wa juna baya suna jin sawayen juna, haka nan Yasmin ta ke son ta ga waye mai wannan sawayen kamar wani ne wadda ta sa ni, a hankali ta dakata ta waiga, ta na juya ya zo dai-dai da lokacin da ya isa office dinsa, don haka ba ta ga komai ba face takalmi a lokacin da sawayensa duka suka shige ta ji karar rufewar kofa.
Ta na zaune a office din mahaifinta ta samu waje ta
zauna suna hira bayan ta gama gabatar masa da komai yana yabawa Zulaihat ta shigo domin amsar wadannan zanen da Yasmin ta kawo.
Lokacin na farko da ta fara haduwa da Alhaji Sunusi, ta
shigo ta gaida shi. Ya amsa mata cikin mutumci da ambatar sunanta a matsayinta na abokiyar aikinsa yace “Wannan ‘ya ta ce, sunanta Yasmin”
Kallo daya Yasmin ta yi mata kawai ta ji wani irin
kishi ya kamata domin ita kanta Zulaihat kyakkyawa ce ga ado na ga ni na fada.
Suka mikawa juna hannu kowacce na kallon juna
“Amma ba a nan kamfanin take da zama ba, don jiya ban ganta Ba anan take ba sai dai tana dab da dawowa nan”.
Yasmin ta ce “Ba ki gaya min sunan ki ba?”
Zulaihat ta yi murmushi ta ce “Suna na Zulaihat na
kuma ji dadi da haduwa dake”
Hmmm