MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 19 BY RABI’ATU ADAM SHITU

ina sa ne akan gwadaben da nake kai Daddy, yaki ne a tsakani na da Abbas, ina bukatar na ci nasara akansa ta ruwan sanyi”.

Ya jinjina kai “Ina bangaren ki ‘ya ta, ina goyan

bayan ki kuma zan tayaki wannan yaki, shin Umar yasan cewar da sakin da Abbas ya yi miki?”

“Ita ce kadai hanyar da yasa Umar ya amince ya ci

gaba da kula ni Daddy, Umar na cikin farin ciki mara misaltuwa”

“To abin da nake so dake shine mu fasa masa sirrin

abin da yake a dukunkune shine kadai zai kawo saukin yakin mu

Ta yi shiru “Ina shirin hakan Daddy, amma ina tsoron

Umar yana da matukar naci baya gazawa ta sauki Daddy, idan har mu kadubi abin a bai-bai zamu iya bankado abin da zai rufta da mu, ba mu samu nasara ba, kuma duniya ta san abin da aka Kala maka

*Yayi shiru, a wannan karon ya gano tsoro ne tsantsa a

cikin ran Yasmin, na kada a kama shi a tsare shi, saboda haka shi da kansa ya dace su yi wannan maganar da Umar, kuma shi da

Umar din ya dace su nemo mafita.

“Shi ke nan ‘ya ta, na fahimce ki na kuma gode da

sadaukarwarki a kaina

**Dady ka da kace haka, domin dukkan farin cikin ka

shi ne ka gan mu cikin walwala ba zan yafewa kaina ba idan na gaza sadaukarwa akan ka”.

Ta mike “Zan tafi Daddy”.

“Yaushe ne zaki fara zuwa nan akwai bukatar ki,

sannan a porject din su Umar ana bukatar ki, saboda an yi shara foundatin din za a fara ina ga kwana biyu masu zuwa, ya kamata a gan ki a wajen’

“Zan ziyarci wajen Dady”.

* *

Bayan kwanaki biyu tsakanin Yasmin da Umar sun

kasa samun jituwa domin duk a lokacin da Zulaihat ta ga Yasmin ta zo to sai ta tsiro tsirfar da za ta kusanci Umar, har ta yi masa . maganar da dole ta san yana tada zuciyar Yasmin. Yau kamar kodayaushe motoci uku ne suka isa harabar in da za a gudanar da aiki tsakanin Zulaihat da kuma Yasmin wadanda su ne suka fitar

da taswirar wajen da kuma yadda za a tsara gini-gine wadda shi kuma Umar ya yi je don ya yi na shi tsarin saboda akwai wayoyin da za a binne a kasa.

Saboda haka a wajen duk inda Umar ya saka kafarsa to Zulaihat ce za ta saka tata, suna cikin haka bacin rai da takaici ya ishi Yasmin. Yasmin ta na Kokarin yiwa Umar magana Zulaibat ta katse mata maganar ta, wani irin haushi ya kama Yasmin ba ta san lokacin da ta sakawa Zulaihat jiki ba ta fadi a cikin ramin da aka haka. Sannan taqi ba da hakuri, maimakon ta samu sanyi a zuciyarta na abin da ta yi sai ranta ya kuma baci saboda Umar ne ya kamo hannun Zulaihat ya fito da ita daga cikin ramin sannan ya karkade mata jiki.

Yasmin tana kallon su takaicin duniya ya ishe ta, sai da Zulaihat ta ga cewar ba ta ji ciwo ba, sannan ta fara masifa Wane irin abu ne haka ki kada mutane kuma ki kasa ba su hakuri

Yasmin ta galla mata harara “Ai da gaiya nayi miki, a wane dalili zan baki hakuri ka da na Kara taka waje ki tsaya min ko ki katse ni”

Tuntuni Umar ya fahimci in da al’amarin ya nufa don

haka sai ya daure fuska ya dubi Yasmin ya ce “Haba Yasmin me yasa zaki yi haka, idan da ta ji ciwo fa”.

Wata harara ta gallara masa, ba ta san lokacin da ta ce Sai ka rungume ta ka kaita Asibiti, Karewa kama hannu rungumarta za ka yi anan za ka fi burge ni”

Ta ja tsaki ta bar wajen motar ta ta shiga ta tafi. Yana

kiranta ko ta dakata.

Zulaihat tana kallonsa irin tashin hankalin da ya shiga

har ya so ya manta da laifin da Yasmin ta yi mata, hakan yasa ta ce “Mene ne tsakanin ka da matar aure?” Wata harara ya zabga mata “Ki na sanin maganar daya dace ki yi da ni Zulaihat”.

Shi ma ya tafi ya ba ta waje, can ya nufa yana duba

aiki duk da cewar hankalinsa yana ga Yasmin zuci-zuci yake su ta shi ya je ya ji halin da take ciki”

Lambarta da ya haddace ya goge a cikin wayarsa ya

fara jerantawa har ya gama sannan ya kira

ZUCIYATA

“Me kike nufi, aikin nan aikin ku ne kin tafi kin bar

wajen mene ne haka Yasmin?”Ka bar wajen”

Abin da kawai ta gaya masa tayi shiru. Cikin rashin

Fahimta ya ce “Ban gane na bar wajen ba, kina nufin mu tafi mu bar aiki idan an yi ba dai-dai ba kuma fa”

“Ka zo nan ina jiran ka in kuma da ita za ka zauna kaje ka yi ta zama”

“Yasmin ki nutsu mana, me yasa kike damuwa akan

tsakanina da Zulaihat, Zulaihat abokiyar aikina ce kawai.Uhmmm hakane, Dear ko”Yasmin me kike tunani ne wai”Komai, komai ma Umar, bana bukatar na ga wata mace a kusa da kai ko wace ce, matukar ba yan gidan ku ba, ka zo ka same ni a nan gaba kadan mu zauna a nan, in ta gama nata aiki maje mu yi na mu”

Tana fadin hakan ta katse wayar ya ma rasa yadda zai

biyo wa al’amarin lallai salon Yasmin ya sauya, ko da yake ya santa da kishin bala’i ko a can baya, sannan ya zama dole ta yi kishi da Zulaihat saboda babu wani abu a zuciyarta face kauna ta, ya zan yi ya fahimtar da Zulaihat, dole zai ba ta dama ta fadi abin dake cikinta domin ya gaya mata nasa burin,

Ba shi da zabi dole ya je kiran da Yasmin take yi

masa, dan bai san a halin da take ciki ba.

Zulaihat nemansa ta yi ta rasa, sai da wajen Karfe uku

ta gama abin da za ta yi ta zo wuce wa taga motar Yasmin din a kulle, babu kowa a ciki, nan ta raya zuwa ya yi ya tafi da ita a tashi motar. Hankalinta ya yi mugun tashi bata san lokacin da kishi ya turnuke ta ba.

Abbas na zaune a office dinsa Munir ya yi sallama ya

shigo. “Oga barka da aiki?”

Abbas ya jinjina kai “Ina labarin motsin gidan su

yaron nan?”

“Suna cikin kulawar mu, yayansa kanwarsa, da kuma

mahaifan nasa sai karamin kaninsu

Abbas ya jinjina kai “Mene ne shirin ka?”Abba ya tambaya Munir, Munir ya jinjina kai

“Shirina shi ne na gane motsin kowanne nan su cikin lokuta

“Ina batun Umar din a wane hali yake yanzu?’

“Ba ka ba mu aiki akansa ba…

Wayar Abbas ta yi Kara ya dauka “Inaji

Abin da kawai ya ce daga can aka fara magana “Ina

so na taimake ka ne domin ni ma in taimaki kaina idan za ka ba ni hadin kai?”

“Ta ya ki ka samu lambata Zulaihat?”

“Ba wannan ne matsalar ba, yanzu haka matarka da

Umar suna tare sun ajiye motar matar ka sun fita a tashi, ba ina yin komai ba ne don Umar ya samu galaba akan ka ba, ina yi ne domin ni na samu galaba akan Umar, matar ka tana neman ta tare min hanya, shin ka yadda mu hada kai domin kowa ya samu biyan bukatarsa”.Na amince, a ina kike yanzu?”

“Ina daf da karasowa kamfani”

“To ina jiran ki”

Ya ajiye wayar. Ya kai wa table din duka da karfi

hankalinsa a matukar tashe “Duk in da Yasmin da Umar suke ku tabbatar da cewar kún bi su, sannan ina so ka kawar min da shi”An gama oga”

Munir ya nufi hanyar fita daga office din “Ka

harhada kowane jan wuya da ka san ba zasu yi kasa a ido ba, kada ka yi min waya sai bayan kun cika aikin ku'”

**

Umar da Yasmin ba wani waje suka nufa ba, sai can

bayan gari in da suka saba haduwa in da suka sanya wa wajan suna da MAHADAR ZUCIYA.

Suka daga motar su wajen na nan kamar yadda yake a da, waje ne mai sanyi da yalwar inuwa saboda was bishiyo masu inuwa da suka yanyame wajen sannan daga can gaban wajen akwai kogin da yake gudana.

«Yaushe rabon ka da zuwa nan wajen?”

Ta yi masa tambaya da yake so shi ma ya yi mata.

“Tun ranar da ka bar gurin nan, ba na wuce lokacin da na in zuciyata na bukatar zuwa, ban taba sati ban zo ba kamar yadda mu kasaba, idan na zo nan ina yi iya hango ka a yayin da kake daukar tsakowa kana jifa da ita a cikin ruwan yayin da muke zaune muna hira cikin nishadi.

Hawaye ne yake bin kuncinta ya dube ta “Yasmin”

Ta dago jajayen idanuwanta ta dube shi hawaye ne

fal ciki “Ki share hawayen ki, ki ba ni dama zan fitar da mu daga cikin wannan ukuba da mu ke ciki, zamu zamo tare dake har abada”

“Ya kake so na yi, Umar ina son ka, ina so na rayu da

kai, ya zan yi, wacce dama zan baka, a lokacin da ya dace mu zauna tare da kai mu yi yaki da kullin da a ka yi min ka guje ni saboda kana tunani zan yaudare ka, me yasa ka yi tunani zan guje ka me yasa”

“Yasmin abin da ya wuce ya riga ya wuce, ki yi min

uziri ba ki bayyana min komai ba, sannan dama ina tuhumar ki akan wani abu da kike boye min, dole zan kullace ki da haka, amma a kodayaushe ina tunanin shin ta ya a ka yi me yasa a wane dalili, kin amsa min su yanzu na fahimci sannan na gane na yi kuskure ina so ki gaya min da me Abbas ya dabaibaye Daddy”

OFFICE

Yana kai komo Zulaihat ta shigo cikin office din,

“Abin da ki ka gaya min a wayagaskiya ne?”

“Gaskiya ne Abbas, akwai soyayya a tsakanin matar

ka da Umar”

“Na bincike komai na gano komai, shi ne Umar din

da Yasmin ta yi soyayya da shi, ina ta nemansa ban same shi ba, domin ta ki ni saboda shi Allah ya bayyana min shi, ya zama dole na kawar da shi domin na samu Yasmin. Yasmin ta wa ce”.

“Ban gane ka kawar da shi ba, ka da ka sake kayi abinda ba zamu fuskanci juna ba ni da kai Umar rayuwa ta ne”

Wani kallo ya yi mata “Kin san da cewar rayuwar ki

ne shi me yasa ba ki hana shi kula mata ta ba, ki fice min daga ni’

“Mun yi da kai zamu Kulla yarjejeniya domin shawo

kan matsalar a nutse, to muddin ka kashe Umar sai na raba ka da Yasmin sai na kashe ta ni ma, domin ka dandani azabar da za ka dandanar min”.

“Kafin ki kashe ta ni bari na kashe ki”. Har ya yun kura kanta da niyar ya shake mata wuya aka turo kofa.

Ranta ya yi bala’in baci “Ka hada kai da ni ba za ka ji

kunya ba, na sa ni Yasmin bata son ka, ni zan sa ta so ka zan kuma kawo karshenta da Umar cikin ruwan sanyi ka yi nazari, ina so na gaya maka idan ka kashe Umar wutar tsanar da Yasmin za ta lika maka minkin baninkin ce akan ta yanzu”

Daga fadin hakan ta fice ya bi ta da kallo Munnir

dake tsaye yana jin ta.

“An gano in da suke?”

“Ba a gano ba har yanzu amma suna can suna ta

bincike”

Abbas ya yi wata Kara mai karfi Munir yana kokarin

bashi baki ya ce ya fice masa ya ba shi guri.

Kayan shaye shayensa ya dauko ya kora sannan ne ya

samu ya lafke

Kai tsaye Zulaihat super market ta je, duk wani abun

na more rayuwa da ‘ya mace budurwa take dabukata ta siyewa,

-Yusra sannan duk wani abu na bukata da danamiji yake da bukata a matsayinsa na baligi ta siyawa Khalil kawo shaddodi sutura mayukan na kamshi jiki masu tsadar gaske.

Haka Bashir Baba kuwa da Umma sun sha siyayya ta

kawa. Sai da Khalil ya yi sawu uku yana kwasar jakunkunan a motar Zulaihat, haka ta dinga raba musu. Malam Bahaushe na cewa yaba kyauta tukuici.

Bayan sun gaisa a kadaice ita da Umma tana mata

godiya bisa irin kyaututtukan da tayi mu su. ZUlaihait ta yi nisa ta ce, “Umar ya zone?”

“Umma ta ce “A’a sai dai muna saka ran zuwansa

yanzu ko tun da duhu ya fara”.

Ta yi shiru ba tare da ta ce wani abu, Umma ta dube

ta “Lafiyana ga kin yi shiru, ko wani abu ya faru?”

“‘a ba wani abu bane, dama dazu ne na gan shi taro

da matar dan shugaban mu, sun fita

“Wace ce wannan, Umar din kuma?””Eh, shi ne Abbas din yake ta surutu akan Umar din, abin ya daure min kai, domin Umar bai iya kula mata ba, amma wannan yarinya sai nake ganin kamar yar uwarsa ce”

“Dakata dakata Wace ce, mene ne sunanta”

“Yasmin, sunan ta ‘yar uwarku ce ne”

“Yasmin, dagaske kike?”

Zulaihat ta dauko wayar ta ta dubo photon

Yasmin da suka dauka a lokacin da suka fara ziyarta

ma aikatan hoton da za a saka a cikin file din project

Mama ta kura ido don tabbatar da zarginta “Ita ce, ya a ka yi suka hadu, ki ka ce tana aure dan shugaban kamfanin Ku

“Haka ne mama ni na dauka ko ‘yar uwar ku ce

kusancin na su ya yi yawa”

Umma ta jinjina al’ amarin “Babu ko daya, ba matsala

zamu yi magana da shi, mun gode da dawainiyar ki a gare mu, Ina so ki gaya min gaskiya mene ne alakar ki da Umar, bayan aiki”

Kunya ta rufe Zulahait ta kasa magana Umma ta ce

shi ke nan, kin samu Umar in har kina son shi, ba shi da mata sai ke”

Ba ta iya gayawa mahaifinsa ba saboda girman abin

amma ta saka a ranta duk in da Yasmin take za ta neme ta, domin ta gargade ta akan danta shi kuma zai zo ya same ta.

Ta na gaban motar sa a dai-dai lokacin da suka dawo in da motar ta take.

“Ina son gabin Mama Umar yaushe za ka kai ne in

ganta”

Ya yi murmushi “In har kin shirya kin kusa zama tare da Mama Yasmin, amma ki taimake ni ki gaya min gaskiya lamarin nan ki daina boye min”

Ta yi saurin ficewa daga motar domin bata son ta ji shi

yana wannan maganar tana matukar tsoron abin da zai kawo shigar mahaifinta cikin matsala.

A lokacin da ta fito daga motar ta hango wata mota

daga can nesa da su sun kashe fitilo bata dauki lamarin da girma ba, ta shiga motar ta. Tana cewa Ka isar min da sako na?”

Yana nan cikin mota yana binta da kallo ta tashi motar

sannan ta tafi duk yana kallonta adaidai lokacin da ya juya motar sa ya ji tayar gaban tana fita da alamar wani abu ya taka. Da sauri ya fito daga motar ya garzayo. Ya sunkuya yana duban tayar dagowar da zai yi ya ji an damkeshi, ya yi yayi ya kwace ya kasa, wani murda murdan farata ya ga ni suna yo wa wajen, da sauri da suari suna zuwa ya zari wata yar Karamar wuka ya dasa masa ita a cikinsa.

Tun da Yasmin ta yi gaba take wage ta ga ya taho shiru

shiru ganin haka yasa ta taka burge a tunaninta ko hasken motar nan da ta ga ni Zulaihat ce, da ta ji shiru sai ta juyo kan motar da gudu.

Ta dawo motarsa ta ga ni a nan in da ta bar shi murfin motar a bude, da sauri ta fara kwala masa kira domin jikinta ya bata babu lafiya.

Karfe bakwai da rabi na dare sahu ya dauke saboda

dama yankin wajen guri ne da ba kowa yanzu ne za a gina unguwa a wajen, kafin ka cimma mutane sai ka tsallaka wancan side din.

Ta Kara kwala masa kira. Tana tafiya ta ji ta yi tuntube

da mutum. Da sauri ta dubi kasa. Umar ta ga ni akwance a kasa cikin jini. Yana shure shure da Kyar,

Ihu ta kwarara kafin ta fara salati duk da rikici ta jiyo

shi, jini har yanzu yana zuba daga cikinsa, da sauri ta zare mayafinta ta toshe masa. Tana kiran sunansa tana cewa “Umar ka da ka tafi ka bar ni, in ka tafi ban san ya ya zan yi wannan rayuwar ba, Umar kai ne Muradi na, kar ka tafi MAHADIN ZUCIYATA, ka da ka bar ni Umar.

Ganin halin da yake ciki yasa ta yi wani tunani motar ta

ta yi saurin dawo da ita dab da shi, da kyar da sidin goshi da karfin hali ta saka shi a gidan gaba in da ta yi parking din daidai wajen,

Ta rufe motar kai tsaye Asibiti ta nufa da shi tun ta rude ta kasa kiran kowa a waya.

Allah cikin ikonsa Asibitin da su ke zuwa dan duba

lafiyar sunan ta kai shi. Suka amshe shi bayan ta yi musu bayanai, suka shiga da shi, tun tana lekensa har ta durkushe kasa tana rusa kuka kowa ya zo wucewa sai dai ya bi ta da kallo yana tausayin halin da take ciki domin gani su ke mijinta ko mahaifinta ne ko mahaifiyarta ne suka rasu.

Yasmin bata samu kanta ba sai kusan awa daya da rabi da aka fito aka tabbatar mata da cewar an ceci rayuwarsa, yana nan an yi masa aiki, sai dai ana bukatar jini.

Anan dole ta rasa yadda za ta yi, wayar Yusra ta nema

ta kira “Yusra ki hada ni da Khalil yanzu zamu yi magana da shi”.

A lokacin Yusra na tare, da Khalil don haka ta mika masa ya tsaya yana kallonta “Waye?”

“Yaya Yasmin ce”.

Wata yar harara ya daka mata “Yasmin ba ni wayar?”

“Yaya Khalil ka fita waje zamu yi magana da kai?”

“Ki gaya min ina waje lafiya?”

“Umar ne na same shi cikin wani mawuyacin hali,

yanzu haka muna Asibiti da shi?”.

Khalil ya rude “Wane Asibiti ne kina ina me ya sami

dan uwana”

Kuka take yi ita kanta ta sanar da shi Asibitin Da shi da

mahaifiyarsa da Yusra Bashir ne kawai da ya riga ya yi bacci suka bari a gida.

Tana durkushe a kan wasu dogayen kujeru da suke

babban dakin

Khalil yana Kokarin kiranta suka hange ta a zaune da

sauri Mama ta kara sa in da take, “Me yake faruwa, ba na ce ki fita daga hanyar sa ba”.

Baba ne ya yi saurin shan kanta “Ki bi komai a sannu,

-ya ta ina Umar din yake?”

Har ajiyar zuciya take yi ta sanar da su “Yana ciki basu

bada damar a shiga ba, amma sun sanar da nicewar sun ceto shi”

“Hadari ya yi kome ne?”

Khalil ya yi tambayar cikin rikice”.

“A wajen aiki ne da mu kaje ban san me ya faru ba na

same shi cikin jini akwance a kasa, likitoci sun ce wuka aka caka masa a guibinsa an samu sa’ a bata rauna na shi sosai ba, kuma suna bukatar jini’

Baba ya numfasa “Ta ya a ka yi kuka kasance wajen

aiki daya da Umar?”

“Wallahi ban sa ni ba, kawai na je wajen mahaifina nan

kamfanin su, na hadu da Umar yana daga daya daga cikin ma’ aikatan da suka zo domin taimakawa kamfanin mu da wasu ayyuka na musamman, kamar yadda ya yi mamakin gani na ni ma haka na yi mamakin ganinsa”. “Ba zan yadda dake ba, an gaya min cewar kullum kuna tare da shi?”

Mijinta ya dube ta “Yaushe ki ka ji wannan?”

Za ta yi magana ke nan aka bude kofar “Ranki ya dade, zaki iya shiga ki gan shi”

Hannu ta daga dan yi wa Allah godiya Baba ya dube la

sosai “Yakamata ki je gida yanzu dare yayi”

” mu zamu je in da yake

mungode bisa taimakon da kika yi masa’

Kamar ta ce masa tana son ta je ta gan shi kafin ta tafi

sai wani nauyinsa ya kamata.

Babu ko mayafi akanta domin mayafin dake jikinta ya jike da jini. A haka ta nufi motar ta jikinta babu kwari ta yi zaune a ciki tana kuka tana cewa “Kada ka mutu ka bar ni kada ka mütu ka bar ni ka dawo gare ni abin so na, babu wani abu da zan tsinta a duniyar nan matukar baka numfashi, ba zan rayu ba in baka nan

MAHADIN ZUCIYATA

Tana zaune tana kallon harabar Asibiti jira take yi su

Mama su fito sannan ta koma dan ba za ta iya barinsa ba. Tana zaune a cikin motar ta taga wata mota jibgegiya ta zo ta tsaya, aka bude cikin ta sai ga Abbas ya fito.

..Tana kallonsa tana tunanin abin da ya kawo shi Asibitin nan a wannan lokacin, sun tsaya da wasu mutane suna magana taga ya dauki waya ya kira, wayarta ta yi Kara, ita yake nema, to ta ya a ka yi ya ji, waye ya sanar da shi tana nan. Nan take tunaninta ya sauya wato shi ne ya aikatawa Umar wannan abin babu shakka shi ne. Har ta bude kofa za ta bude sai wata zuciyar ta ce ka da ta fito ta zauna. Suka gama bincikensu a cikin Asibitin abin da ta yi saurin yi ta kira Likitan ta sanar da shi cewar ka da ta bar mijinta yasan ta kawo wani Asibiti kuma maganar ta tsaya daga ita sai shi. Ya tabbatar mata da zai tsare mata don haka ko da ya

gan su, suna ta dube dube bai bari sun hadu da shi ba ya tafi can saman. Da Abbas ya gaji tafiya ya yi.

Yana tabbatarwa da yaran su je su duba masa ko ina

matarsa ta yi da kuma jiyo masa labarin Umar.

Kamar yadda ta sanarwa da Dr Kamal cewar ya sallami

bakin da zarar sun gan shi ya sanar da su cewar babu wajen zaman

Hmmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *