MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 20 BY RABI’ATU ADAM SHITU

majinyata. Haka ta tabbata kusan sha biyu na dare suka fita. Sai da tabbatar sun hau abin hawa sun tafi sannan ta fito ta koma dakin.

Umar bai farfado ba kujera tasa a kusa da shi ta

kwantar da kanta a kan katifar da yake kwance, tana addu’o’in Allah ya farfado da shi.

Wajejen karfe biyun dare idanuwan Umar suka bude,

wajen kokarin mike wa ya tabo kan ta da hannunsa. Da sauri ta dago da kai la kai dubanta gare shi, ta rike masa kafadunsa “Ka da ka mike”.

Ya koma ya kwanta yana binta da kallo “In ka mike za

ka fama ciwon ka”

• Idanuwanta sun ci kuka sun Koshi ya bi ta da

kallo yana mai jin tausayinta

*Yasmin, me yasa baki wuce gida ba, na san dare ya yi

yanzu?”

“In tafi, in je ina Umar alhalin kana cikin wannan halin,

babu in da za ni, ina nan tare da kai ba zan iya nisantar ka ba, me ya faru ne bayan na tafi ina ta kallon madubi don na ga ka taho na ji shiru harna tsayana ji ka shiru, kawai sai na dawo a tunani na, Zulaihat tana nan, lokacin da mu katsayanaga hasken mota a can gaba, sai tumani na ya gaya min Zulaihat ce, su waye suka yi maka haka Umar?”

Ya dan jinjina kai gami da dogon tunani “Ba zance

kai tsaye su’ waye ba, wasu mutane ne, amma da dukkan alamu turo su a ka yi, Allah zai tona asirin su?”

“Wa kake zargi Umar, Abbas?”

Ya yi Shiru yana dubanta “Me zai sa Abbas?”

“Lokacin da na fita da su Mama suka zo, ban tafi

ba kamar yadda Baba ya ce, sai na zauna a mota bayan sun tafi na dawo, sai na ga Abbas ya zo, ta ya yasan cewar ina nan, saboda haka na san shine, shine ya aikata maka haka?”

Umar ya jinjina kai “Ka da ki yi saurin dora zargin

• ki akan kowa, da sannu koma waye zai bayyana, je ki kwanta akan kujerar can ki yi bacci Yasmin dubi idanuwan ki”

“Ka duba ciwon da yake jikin ka, idanuwana sun yi jajawur kai kuma jikin ka ya baci da jini, ba zan iya bacci ba, kuma ba zan cire zargina akan Abbas, idan ta tabbata shi ne lallai zai gane kuskurensa”

“Zan samu nutsuwa idan kin bar zancensa, zan ji

dadi idan na ga kin koma can kin kwanta kina bacci ina kallon kyakkyawar fuskar ki Yasmin?”

Yadda yake magana da Karfin gwiwa yasa ta ji

dadin har ta ji za ta yi masa abin.da yake so don ya kalle ta din kamar yadda ya fada.

“Idan na kwanta ka da ka cire idanuwanka akaina

kamar yadda na yi ta kallon ka kana bacci, ka yi kyau da bacci da ace a lokacin farin ciki ne da ba zan manta da daren yau ba, mun kwana a rufi daya da abin Kauna ta MAHADIN ZUCIYATA”

Ta na fadin hakan ta koma kamar yadda ya umarce ta ta kwanta tun suna kallon juna har bacci ya kwashe ta.

Umar yana kallon abokiyar rayuwarsa jigon kuma

MAHADIN ZUCIYAR TA har shi ma ya samu ya yi bacci”.

Da safe kafin ya farka daga bacci taje ta hado

masa kayan abincinsa, sannan ta yi wa direban baban ta umarni ya kawo motar Umar da ta umarce shi da ya dauka ya kaita gidan su..

Yana farkawa karfe takwas Kamshi ya game ko ina

a cikin falon. Kallon ta yake ya cike da jin dadi yana ganin kamar ma sun yi aure ne.

“Wai duk yaushe ki ka je ki ka hado wannan

abin?”

Ta dube shi ta yi dariya “Tashi za ka yi ka ci, ko

kuma tambayar yadda aka yi za ka yi”

Ya yi murmushi ta taimaka masa ya tashi zaune,

sannan ta zuba ta rike masa tana bashi shayin abaki yana sha.

Bayan ya koshi yasa ta a gaba sai da ta ci. “Jiyana

ga Mama Umar, na ji dadì da na ganta” Shi ma murmushi yake yi, “Ke ce ki ka gaya musu, na jiyo su sama-sama a lokacin allura na diba ta, amma na ji

Mama na fada, dafatan ba ta ce miki komai ba”.

“Fadan Mama bazai dame ni ba Umar, domin ta

nuna min Kauna, ta Kaunace ni irin son da sirikake yiwa

surukarta, sai dai na aikata laifi dole a yanzu Mama gani take

yi yaudararka na yi har na nisanta ka da ita, babu abin da za ta yi min na ji zafi sai ma ganin laifin da na aikata mata”

• Murmushi ya yi zai yi magana sai ga Yusra da

flask ta shigo da sallama, Khalil Bashir duk suka biyo bayansu”

Yusra ta bi Yasmin da kallo ba ta ko gaishe ta ba,

ta tafi wajen yayan nata. “Yaya ina kwana ya jikin naka?”

“Jiki na da sauki ba ki ga ba”

“Na suma ya kai sau ba adadi yaya in na rasa ka

ban san in da zan saka raina ba, jiya Ainty Zulaihat ta yi mana siyayya ina ta murna ka zo ka ga ni, ba ka ga hadadden

agogon da ta kawo wa Yaya ba, kai ta kashe kudi da yawa”

Yasmin dake zaune ta ji gabanta ya yanke ya fadi

“Ina wuni Yaya Khali!”

Ya amsa mata ciki-ciki lafiya, da sassafe haka ki

ka baro gidan mijin naki ki ka taho nan”.

Ta sunkuyar da kanta kasa Umar ne ya ce “Yaya

ka zo mu gaisa ma na Sannan ya Kara so “Ya jikin naka?”

“Jiki da sauki”

“Yakamata a yi report ga ‘yansnada”

“Duka Yasmin ta yi, ka da ku damu aiki ne ya gaji

haka, a samu makiya a ciki, Ina Baba”

“Sunje waien Likita shi da Mama saboda suji abin

da yake wakana

Suna zaune a office din DR Kamal yana musu

bayani “Ai duk wani abu da ake bukata Hajiya Yasmin  ta biya, a yadda al’amarin ya faru ta yi Kokari domin kamar ta na ya mace ta iyasa saka shi a ciki mota a halin da yake ciki har ta kawo shi Asibiti cikin lokaci ba Karamar nasara bace, ta cancanci yabo domin ta ceci rayuwarsa’

Mama ta danji Yasmin Kaunar da take yi mata

ta. Da ta shigo cikin dakin jinyar ta ga Yasmin din sosai ta sakar mata fuska dan har yanzu tana jin abin a ranta da badan Allah yasa ta kawo shi kan lokaci ba da babu yadda zai rayu.Da tuni ta rasa danta. •

“Ya ta har kin zo?”

Yasmin ta duka ta yi musu barka da zuwa da.

Mama ta dube ta sosai ta riko hannayenta ta ce “Nagode ya ta, na ji dukkan Kokarin ki nagode da kika ceci yarona Allah ya yi miki albarka ya baki zuri’a ta gari”.

“Mama ki daina fadin hakan, kaina na yiwa”.

Baba ya ce “Amma diyata, na tabbata idan mijin ki

ya ji kina tare da tsohon saurayin ki, ba zai ji dadi ba, yakamata ki ta shi ki koma gida mun gode sosai kada abin ya zama wani iri kuma ko?’ Ban..

.? sai ta yi shiru ta dubi Umar ya yi mata

murmushi tare da jinjina mata kai akan ta je din kada ta damu Bata tanka ba ta dauki jakarta ta fita. Dai-dai

hanyar fita suka ci karo da Zulaihat za ta shiga cikin dakin jinyar kallo kallo ya wakana a tsakanin su. Yasmin ji ta yi kamar ta koma, amma sai ta jure ta dauke kai ta tafi zuciyarta na mata daci. Kasa komawa gidan ta ta yi dakinta ta je na gidansu ta kwanta.

Mamanta ta dame ta da tambayar daga ina take jiya mijinta na nemanta ta nemi afuwar Maman cewar ta yi hakuri dan ta huta zasu yi maganar. Dakinta ta shiga ta kulle ta ci kuka ta godewa Allah sannan baccin dole ya dauke ta.

ASIBITI

Dakin jinyar ya kasance daga iyayensa sai Zulaihat

suna zaune suna hira. Kallon da Umar ke yiwa Zulaihat yasa ta zargi akwai wata a Kasa, don haka ta sha jinin jikinta.

“An ce ba su daukar masa komai ba, ba satar mota

ba, ba kuma satar kudi ko waya ba, su cutar da mutum kawai wannan akwai dalilin suna yin hakan”.

Ta fada lokacin da Mama ta zauna kusa da ita”.

“Koma su waye Allah ya yi mana tsari da su, tunda

Allah yasa yarinyar nan tana kusa da wajen har ta kai masa dauki babu abin da zamu ce da Allah sai godiya”.Ran Zulaihat ya baci ta dubi Umar har yanzu ita yake kallo ransa a bace yake da ita, to mai ta yi masa, ta kawar da fuskarta “In kuma mijinta ne fa Mama?”Mijin wa?”

Mama ta tambaya a cikin kidima. Kowa hankalinsa

ya dawo kan Zulaihat. Ita kuma ganin ta ja hankalinsu yasa ta ce “Mijin Yasmin din, dama ai da shine suke takun saka da Umar, dadin dadawa gashi ya gano cewar Umar shine Umar din da matar sa take so tun da jima wa”.Wata uwar harara ya dallara mata “Zulaihat Ina so. ki bar ni ni da ‘yan uwana ki je kya dawo bayan sun tafi”A ‘a kyale ta, yi min bayani”

Ta dauke kai daga korar da Umar ya yi mata

“Bashi da imani kuma ya fada cewa zai yi maganin Umar, ina ganin in ba shi ba babu wadda zai yi masa haka?”Khalil ya ce

“Na jima ina tunanin yadda a ka yi ta

san Umar yana wajen da ta je ta taimake shi, da kuma yadda ta daga hankalinta, tana yin hakanne domin ta rufa wa mijinta asiri”

Mama ta jinjina kai “Na yarda da kai, tabbas biri

ya yi kama da mutum

Umar da yake sauraren su ya lunshe ido “Mama ka

da ku dora wa kowa laifi akan abin da ya faru da ni, ita da

Hmmm